Author: Novels

  • Gidan Aunty Book 1 Page 15

    Gidan Aunty Book 1 Page 15

    Free page 15 🦋

    Karfe 8:30 na dare, amrah ce sanye da d’an karamin towel da ko gwiwa bai karasa mata ba,sai uban gashin attachment din dake yawo a bayanta ,waka ta saka tana tikar rawarfa sai da ta gaji dan kanta sannan ta kashe tana sauke ajiyar zuciya. Toilet ta nufa da nufin watsa ruwa ko d’an kwali babu akanta, ta karasa kenan zata kunna fanfo, abinda ta ganine ya firgita ta tare da sakin gigitacciyar kara, a guje ta juya da niyar komawa , amma kafin ta karasa wajan komar wata irin mage ce ta fito ta wajan fara tass da ita, wata karan amrah ta saki, tuni ta fita a hayyacin ta sai faman ihun neman agaji take, dan karamun towel dinta ma tuni ya fadi a jikinta, saukar bulalar dataji a fatar jikintane yasata sakin razanannan kuka, sosai bulalar ta shigewa, bata gama shafa wajan ba ta karajin saukar wata bulalar, kuka kawai ta fashe da shi, ba tsaya ba aka dunga zulamata wannan bulalar, gadan gadan farar Magen nan tayo kanta, ganin haka yasa amrah sakin wani gigitaccen kara tana zube a kasa sumammiya.

    *******
    Tana shiga daki ta fada kan gadanta sai faman murmushi take saki ita kadai, sosai take sakin murmushi idan ta tuno fuskarsa da irin yadda yake hade fuska, take fargaba da tsoransa ya kara shiga jikinta, musamman da taji ammi na kiransa da son.Lumshe idanuwanta tayi amma still shitake gani ,duk da tsananin tsoransa da ya dirar ma , amma sosai ya burgeta a iya ganin da tayi masa. Wanka ta tashi tayi kafun ta kwanta tana adduar bacci, mintuna kadan bacci ya dauketa.

    Sosai wasu irin halitta ke binta, yayinda tarike hannun wani da ba’a iya ganin fuskarsa, amma sai faman kareshi take daga cutar dashi dasuke kokarin yi, tun tu’ben da tayi ne yasa ta faduwa, shima Wanda tarikewa hannun ya tsaya har yanxu ba’a iya ganin fuskarsa, kafun suyi wani kwakkwaran motsi , wadannan halittun sun zagayesu sai tsalle suke saki , daya daga cikin sune yayi kanta yana zaro harshe , daidai yana kokarin cabkota wani irin girgiza ya karade ko ina, take a wajan wata katuwar farar macijiya ta bayyana a wajan, daga gefenta kuma wata farar kuliyace me shegen haske , sosai ta fito da farar farcinan, yayinda bakinta yake abune sai faman “meow meow “take cewa. Zabura wadannan halittun sukai kafun su fara Kai musu sara da faratansu, sosai macijin nan da Farar kuliya sukai musu jina jina lokaci daya suka bace batt ba aganinsu. A firgice tahee ta farka da ga mummunan mafarkin data fara duk jikinta yayi gumi sai faman zufa take hadawa, adduar neman tsari ta fara karantawa har taji nutsuwarta ta Daidai ta kafun ta mike tashiga bandaki, mintuna kadan tafito dauke da alwala, nafila tayi tare da adduoin da oumma ta koyasu hartaji ta kara samun nutsuwa kafun ta mike ta koma bacci.

    ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
    🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

    BUNKURE

    Duk da tsananin yadda bintalo ke ihun ta hakan be sa yaji tausayintaba sai ma kulle mata baki da yayi da kazamin bakinsa me shegen wari, sosai yake zuba muguntarsa akanta, tsabar wahala kusan sumanta uku , azaba na sawa ta farfado, iya rashin imani saida yayi mata yayi mata kaca kaca ko dan yatsanta bata iya motsawa, se hawayen azaba dake digo mata ta ido, azuciya kuwa ta tsinewa Dije yafi a irga duk da kasancewar ta mahaifiyarta. Saida ya gama lalatarsa sannan ya bawa Dije da ke rabe damar Shigowa ya tafi da ita cikin hade rai, duk jikinta yayi sanyi ganin irin aika aikan da yayi wa bintalo, amma ko saudaya batayi nadamar hakan ba tunda burinta zai ciki, cikin razananniyar muryarsa me tsoratarwa ya daka musu tsawa akan su bace da ganinsa, ganin yadda bintalo ta kasa ko motsine yasasa babbaka dariya” ku sawa ranku aikinku kamar ya tabbatune” sai ga wata kwarya nan ta fado kasa da dan karamun ruwa a ciki jaa da shi, ruwan yasa dije ta dauka ta kwarawa bintalo a gabanta, cikin Karkarwa ta dauka tare da kwara mata, wani irin gigitacciyar azabar kara bintalo ta saki da ya firgita Dije , kara babbakewa da dariya yayi tare da hade ransa , kusan mintuna uku bintalo na kukan azabar nan kafun ta sauke nannauyar nunfashi tare da mikewa da kanta, ganin hakan yasa dijen sakin ajiyar zuciya a haka suka ajiyewa boka kudin da suka zo masa dashi tare da fita da baya baya har suka bar wajan, sai lokacin bintalo ke taku da dingishi dukda azabar da take ji ta ragu babu ita,amma gudun kar a asirinsu ya tonu basu koma gida ba sai wajan shadayan dare lokacin babu wuta, sannan babu me gane halin da suke ciki, zuciyar dije sai faman zillo take akai ta aiwatar da kudurinta kan oumma da suka shige mata hanci , ga wani tsanar su da ke kara ruruwa a
    Zuciyar ta.

    ************
    Tunda ya tashi yau be fita ko ina ba sai bayan karfe goma na safe bayan motsajikinsa da yayi, Hakanan yau besan jin kowa a kusa dashi ga yunwa yana jin amma ya kasa motsa koda dan yatsar sane, coffee yake San sha dan haka ya mike cikin takun kasaitarsa kamar kullum, a hankali yake taku sanye Yake cikin black trouser da black singlet , sosai kakkarfar surar jikinta ta bayyana , farar fatar jikinsa sai sheki yake dauka, a hankali ya karasa inda coffee maker din yake, cikin yan mintuna ya gama hada coffee dinsa , a nutse ya zauna kan daya daga cikin sofa din wajen , sipping daya yayi wa coffee din tare da ajjesa, wani irin daci yaji coffee din nayi masa kamar zaisa amai, a hankali ya kara lumshe idanuwansa ko me ya tuna oho, sai gashi ya mike tare da nufar wani daki, ko cikakken minti ashirin beyi ba wani daddadan kamshi ya karade ko ina , a hankali kamshi ya kara kusan towa kafun mamallakin kamshin ya bayyana , sosai shigarsa tayi masa kyau , sanye yake cikin black suit sosai bakin suit din cikinsa ya fito da ainahin kalar farar Tatar’s a da sai sheki take , bakin nan kullum sai kara turuwa yake kamar mai shafa abu wajan, har yanxu fuskarsa a hade take amma sosai yayi kyau , ga diamond watche dinsa sai faman kyalli yake, wayace kare a kunnansa sai faman motsa baki yake ko abunda yake cewa ba aji, be tsaya a ko ina ba sai part din amminsa .

    A zaune ya sameta cikin shigar manyan mutane da ta saba , sosai tayi kyau cikin shigarta, kujerar da take zaune ya nufa tare da langwabar da Kai kadan, kallansa tayi tare da dauke kanta, bai ce komai ba sai hannunta da ya kamo ya dora a fuskarsa , a fusge ya furta “sorry ammi”, ajiyar zuciya ta sauke daman ba fushin take dashi ba ganin yaki zuwa haryanxu kuma tayi kewarsa ne yasa ta yi masa haka, a hankali ya furta “ina kwana ammi na “, murmushinta da baya boyuwa ta saki “ ka tashi lapiya son” lumshe mata ido yayi kawai batare da yace komai ba , ganin hakan yasan ammi tasan yan miskilancin ne a kusa, kadan suka taba hira yana amsawa kadan kadan,shafa gefan fuskarsa tayi” da alama wannan son din nawa ne ci komai ba” kara lumshe mata ido yayi tare da bude wa alamun amsa . Mikewa tayi “bari na dafa maka abinci ko” riko hannunta yayi tare da kallanta “ coffee” shine kadai abunda yace mata , jinjina masa kai tayi tare da nufar kitchen din, a tsaye ta samu tahee da asabe na aiki a kitchen , sosai tahee take jin dadin hakan sabida tana Kaunar taga ta iya abinci hala hala , ba tare da ta kalla taheen ba ta soma magana, “tahee hadawa son coffee kafun na kammala dafa masa abinci”, suman tsaye tahee tayi , zuciyar ta sai bugawa take gashi bata da dalilin musawa, kamar wacce zata saki kuka haka ta hada coffee din tare da fita falo , ko ina na falon mayataccen kamshin turaran da ke mata dadi ne ya cika wajan, Zuciyarta sai faman zillo take sabida tsoro, a hankali ta karasa inda yake bayan tayi sallama , cikin in ina ta soma magana “ina.. kwana”, kamar wacce tai da gunki ko motsi beba sai ma sarrafa wayarsa da yake cikin nutsuwa , kamar wacce zata saka kuka ta kara cewa “ina.. kwana”, yanxu ma be motsaba balantana tasa ran amsawar, siraran hawayene suka dan zubo mata kadan tare da sun kuyar da kai, kamar daga sama tayi saukar muryarsa “ fine” , wani murmushi ne ya subuce mata, sosai taji dadin amsawar dayayi, a hankali ya sa fararan dogon yatsunsa tare da dauka cup din, a hankali ya fara sipping, zuyawa tahee tayi da niyar komawa tazo daf da kitchen din ta tsinkayi muryarsa “ who permit you to leave”, sun kuyar da kai tayi tare da dawo wa ciki “ bakowa “ ta bashi amsa , tsawan mintuna goma tana a tsayen , kofin hannunsa ya ajje tare da kyara zama, another cup,”Tom “kawai tace masa tare da nufar kitchen din, har lokacin ammi na tsaye tana masa abinci da kanta, kallanta ammi tayi sai yanxu, sauke ajiyar zuciya tayi “wani cup din yace na hada masa”kallanta ammi tayi sai dai bata ce mata komai ba sai jinjina mata kai da tayi, wani cup din ta kara hadawa tare da nufar inda yake har yanxu zuciyarta bata bar bugawa ba, sallama tayi a falan kamar bazai amsa ba , sai ya amsa a hankali, batare da wani dalili ba lokaci daya taji kanta ya sara mata Daidai lokacin da zata mika masa coffee din, a maimakon ya sauka a hannunsa sai ya subuce ya zube a jikin hadaddan suit dinsa …….

             (😳😳Tahee )……

    Manage plx ….

    Masu comment ina Godiya sosai da sosai

    MASU BUKATAR COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581 .

    MASU BUKATAR A TALLATA MUSU KASUWANCINSU SU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 07041879581 AKAN NAIRA 500 KACAL.

    💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

    DUK KARFIN IZZATA ( star lady )

    GIDAN AUNTY (mss Lee )

    JINI DAYA (mrs bbk)

    YA FITA ZAKKA( maman sayyid)

    BABY (mhiz innocent)

    💖💖💖💖💖Mss Lee ✍️.

    ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JyvVuOvzYyF19np8UmFKV4

    💖💖GIDAN AUNTY 💖💖
    (a heart touching love story)

    Story & written
    By
    Mss Lee 💖

    PAID BOOK

    LITTAFIN GIDAN AUNTY NA KUDI NE AKAN NAIRA 300KACAL , MAI SAN CIGABA DA KARANTAWA HAR KARSHE ZAI BIYA KUDINSA TA WANNAN ASUSUN :
    7041879581 OPAY
    AYSHATOU GALADIMA , sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

  • Gidan Aunty Book 1 Page 17

    Gidan Aunty Book 1 Page 17

    BOOK 1 📕

    Free page 17🦋

    Duk binsu da kallo ammi tayi ganin lokaci daya duk sun tsorata,suma duk sai sukai shiru ganin irin kallan da ammi ta bisu dashi, tahee da zoya ma duk tsayawa kallansu sukai, kamar daga sama cikin sauri amrah tace “zani ammi”jinjina mata kai ammi tayi tana sauke ajiyar zuciya, kafun ta karasa kitchen taji saukar muryar sumayya” Ammi nasan kayan sunyi yawa bari na temaka mata”ta karasa tare da dallawa amrah harara batare da ta bari ammi ta ganiba, ita tahee dariya suka bata ma, ko za a yankata aibazata je inda za a ballataba,jinjina mata kai ammi tayi tare da karasa shigewa cikin kitchen din, cikin sauri amrah ta jiyo tana kallanta,”mtswww na tsani shishshigi Wallahi “, kallan rainin wayo sumayya ta bita dashi, “zaki hanani taka ko ina na gidan mune”, dogon tsakin da firdausi taja ne ya katsesu “malamai kunbi kun ishemu inda gaske sansa kuke kuje kuce a aura muku shi mana kinbi kun cika mana kunne” tana gama fadar hakan ta mayar da headphone din kunnenta, ba Wanda ya kara cewa komai sai kallan banzan da suke bin junansu dashi , ihsan kam sharesu tayi tacigaba da game din da zoya ta sa musu , zuwa zaune kusan yan mintuna su asabe suka fito da kayan da za akai masa, har yan rigen rigen tashi ake tsakanin amrah da sumayya,amrah ce ta fara karasa tare da amsa kayan hannun asabe tana yatsina fuska,itama sumayya ragowar kayan ta dauka tana hararar amrah, Tashi tahee tayi da niyar komawa daki ammi ta tsayar da ita, “Kema daughter jirani na aikeki part din dada da na ummey”tana gama fadar hakan ta shige wani daki, mintuna kadan tafito dauke da wasu designers bag guda biyu, lokacin har su amrah sun bar part din, purple din ta nuna mata na dada ,red din kuma na ummey, mikewa zoya tayi “ammi zan bita”murmushi ammi ta sakar mata “toh daughter “kama hannun tahee zoya tayi, kowa na mamakin ganin lokaci daya ta sake da tahee, Kai tsaye part din dada suka fara zuwa Tun a hanya zoya Kezuba mata surutu falon yayi saura daga ihsan sai firdausi dake jin waka.

    Zaune dada take kasan lallausan carfet din falon ta, kamshin farfesun kayan cikin da akai mata sai faman tashin kamshi yake, cikin sallah tahee ta shigo falon tare da zoya,amsa sallamar dada tayi tana sakar masu murmushi” sai yanxu kika tuna dani tahura, ai nayi fushi “,sun kuyar da Kai tahee tayi cikin jin kunya” kiyi hakuri dada ba haka bane”, dan ta bile baki dada tayi “ gaskiya kam ki gyara, ko d’an hirar nan ki dunga zuwa kina tayani tunda su wadancan bankadaddun ba zuwa suke ba, sarakine kawai shima kullum cikin fada muke”, kallan ta zoya tayi”dada nifa , kinsan dai ina zuwa ko”,sakin baki dada tayi tana kallanta” kiji tsoran Allah, ni nayi mamakin ganin ki ma yau, ba dai kyau karya kinsani”, dariya zoya tayi tana rufe dan karamin bakinta, sakon da Ammi tabayar abata tahee ta mika mata “Allah sarki,kilishi ba dai mutunci ba ,duk gidan nan ita da hajiya suhaima ne masu kaunata sai sadauki”ta karasa zan Canta tana Shan farfesun ta, kallan tahee dake wasa da hannunta tayi”kinga zamu bata sai wani jin kunyata kike kamar wacce akace miki na zama sirikarki”, sosai dada da zoya suke janta hira tun bata sake ba har ta sake da su, sun dad’e suna hira kafin tahee tace zata kaiwa ummey sakonta,’kin barin ta dada tayi har saida taci farfesun da ta zuba musu zoya sai faman dariya take musu, da zata tafi ma sai da tayi wa dada alkawarin dawowa anjima sannan ta barta,tsakanin part din dada dana ummey ba nisa shiyasa basu dade ba suka karaso, sai bin ko ina tahee take da kallo ganin irin kyan da wajan yake dashi, zoya na gaba tahee na bayanta har suka shiga hadaddan kayataccen falon, sosai falon yake da girma da tsaruwa,ta ko ina kamshi ne ke tashi da sanyin Ac, ganin babu kowa a falon yasa tahee zama kan lallausan carfet din falon me shegen laushi da daukan ido, a guje zoya tashiga wata kofa kusan minti 5 sai gasu sunfi to ita da ummey dake sanye da black abaya sosai kyawun ta na larabawa ya bude shekarunta, wacce ta ganine yasata dan sakin murmushi, tare da zama kan daya daga cikin lallausan kujerun falon, gaishe da ita tahee tayi , yayinda ummey ta amsa mata cikin kulawa, haka kawai taji yarinyar ta kwanta mata arai sabida nutsuwarta, sakon ammi tahee na mika mata, wani murmushin ummey ta saki,”kice mata nagode sosai kuwa, bata gajiya “yadda ummey ta yabi ammin sai kaunar auntyn tata yakara shigarta sosai take santa,mikewa tayi daniyar tafiya ummey ta zaunar da ita “ ina kuma zaki, yanxu zamuyi lunch “ komawa tahee tayi ta zauna bazata iya yi Mata musuba sabida kunyarta da takeji, kallan ummey zoya tayi” ummey kingama a part din dada guduwa tasoyi “,girgiza mata kai ummey tayi cikin yaren larabci “bana hanaki surutu ba”, sun kuyar da Kai tayi”ana asf”ummey bata kulataba sai kallan tahee datayi “daughter taso muje muci abinci”ba yadda tahee ta iya dole ta mike ,tare suka nufa hadadden dining din dake falon,sosai wajan dinning ya hadu kasancewar wajanshi daban a cikin falon bayan antaka 3stairs, dakanta ummey tayi serving Dinsu , sosai kamshi girkin ya cika ko ina , nut spicy herb rice da Greek chicken kebab ummey ta zuba mata ,sai wani yan bowl masu shegen kyau da ta zuba mata salad da sauran dishes din, cikin glass cup kuwa strawberry milkshake ne aciki me shegen sanyi, sosai abincin ya birge tahee amma ta kasa moshi ,sai godiyar da tayi wa ummey kawai, itama ummey serving din su tayi ita da zoya, har sun fara cin abinci ganin sai wasa tahee take da spoon din hannunta ummey ta kalleta” daughter ya naga ba kyaci, ko abincin be miki bane”saurin girgiza mata kai tahee tayi “a’ah ummey yanxu zan faraci” ta fada tare da soma cin abincin a hankali , ummey batace komai dan Sarai ta gane kunyarta tahee takeji,suna cikin cin abincin kuwa daddad’an kamshin turaren da basuyi tsammani bane ya cika dodan hancinsu,da ma duk wani kamshi dake tashi a falon,kasa cigaba da cin abincin tahee tayi zuciyar ta sai faman bugu yake, naman da yake bakinta ma ta kasa taunawa sai faman tsotsanshin take, a hankali cikin daddadar muryashi yayi sallama , amsawa sukai baki daya banda tahee da ta kasa mosi, zoya sai kallansa take tanaso taje wajan sa amma ya Hana ta intanacin abinci,kan daya daga cikin kujerun falon ya zauna tare da crossing legs dinsa , binsa da Kallo ummey tayi , tayi kewarsa sosai da sosai amma a zahiri sai dauka hankalinta be kansa, cikin kasa kasa da murya zoya ta kalli ummey” ummey please ki cewa akhii yazo muci abinci , this once only please “kallan ta ummey tayi tare da dauke kanta,ganin hakan yasa zoya kara marairaicewa “please ummey”, girgiza Kai kawai ummey tayi har lokacin kuma tahee ta kasa ko kwakkwaran motsine, duk maganganin zoya yanajinta Sarai amma a zahiri sai ka dauka bayacikin falon,cikin larabci yaji saukar muryarta” taso muci abinci”,kamar bazai motsaba sai kuma ya tashi a hankali tare da nufar dining din ba tare da yace komai ba, Daidai inda yake shigowa tahee tana facing din sa, sarkewar da idanuwansu yayi te yasata shakewa da abincin da ke bakinta, sosai take tari dan ba hakaramun Shakewa tayi ba…

    *********Tun lokacin da suka baro part din ammi suke wa juna kallan kaskanci, daman ba shiri suke da junansu ba musamman da ya kasance suna san mutum d’aya , har suka karasa part dinsa ba Wanda yace wa kowa kala,duk da fargabar dake tattare dasu haka ko waccen su ta shiga falon dan bakantawa yar uwarta, bakowa a falon kasa ganin hakan yasa amrah nufar center kujerun tare da ajiye tray din hannunta, itama summy cikin gadara tanufi inda amrah ta ajje nata inama ta dora natan, ganin hakan yasa amrah saukar da na sumayya, itama sumayya sai abun ya bata haushi ta dan kwalar da na amrah, cikin kankanin lokacin suka fara ture turen abinci,a lokaci daya suka sa hannu tare da ture abinci junansu, take a wajan komai ya fadi kasa ya fashe Daidai lokacin da king ya fito daga wata kofa,bin ku waccen su yayi da rinannun idanuwansa , a part dinsa zasuyi masa wannan iskancin,kwata kwata basu ankara da shi a falon ba, amrah da tafi tsiwa ta tunkari sumayya , lokaci d’aya suka fara danbe da junansu, bece musu komai ba sai koma daki dayayi , cikin kankanin lokaci yafito hannunsa goye a bayansa sosai ransa ya baci, basu ankara ba sai saukar belt da sukaji, cikin bacin rai yake jibgarsu,”how dare you”, sosai suka firgita, sai faman hakuri suke bashi, sai da yasan sun daku sannan ya kyalesu, cikin nutsuwarsa ya zauna kan kujerar dake zaman mutum daya tare da crossing legs dinsa, ko wannansu zubewa yayi a kasa tare da yin kneeling, kowannansu na nadamar zuwa part din, kara had’e ransa yayi tare da kallan tulum abincin da suka bata,”it them all”, daga nan be kara cewa komai ba, sosai sumayya taji wani kukan na zuwan mata dan bata dade da cin abinci ba, amrah ma sai faman zare ido take hawaye na zubomata, belt din dake gefe ya dauka cikin sauri ko wannansu ya karasa inda suka zubar da amincin har da Wanda suka tattake, suna kuka suna tusa abiinci da suka zubar, ko wannansu ba yunwa sukejiba,sai tura tula abincin suke abaki,da Dinsu daya ko zuwa ne ya zube mutum zea iya tsugunnawa yasha sabida tsabtar wajan, saida suka cinye abincin tass ko wannansu na nishi sannan yasu suka gyara ko ina nafalon,yana zaune kan kujera saida ya tabbatar sun wahala sannan ya tashi ba tare da yace musu komai ba ya bar part din tare da nufar part din ummey.
    🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
    🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
    BUNKURE
    Tun lokacin da suka dawo cikin dare Dije ke safa da marwa, sai tunanin yadda zata zuba wa su oumma magani abakin kofa take,ga bintalo dake kwance sai nishi take gabanta sai zafi yake mata,ta dade tsaye tana zagaye dakin kafun ta saki wani murmushin mugunta, samun waje tayi itama ta zauna ganin yadda bintalo ke ta faman nishi, ita kanta tasan da ita boka ya kusanta sai taji azaba balantana bintalo , amma duk da hakan bataji tayi danasanin yin hakan ba tunda Burinsu na daf da cika inyaso sai su koma wajan bokan ya basu abinda bintalo zayi anfani dashi takoma budurwarta..

    Yau tunda sassafe Dije ta tashi ko alwala batayi ba bare tayi tunanin yin sallah , maganin da boka ya bata take faman jujjuyawa, kafin cikin sanda tafito daga cikin dakin su ta nufi nasu oumma , bakowa kuwa a wajan kasancewar Gari be dade da wayewa ba , kofar dakin su tahee tashiga bubbugawa sai da taji motsin an nufo kofar tayi saurin zuba maganin tare da komawa baya taheer ne ya bude kofar da niyar fitowa,jiyai an hankadashi ya koma baya ,ga wata yar iska da ta kara de wajan, ganin yana kokarin komawa Dije ta daka masa tsawa “ina kuke muna fukan Allah kufito”, ganin tana kokarin tara musu mutane ne yasasu fitowa taheer agaba oumma na biyedashi, ganin sun tsallaka garin maganin yasa dijen kyalkyalewa da dariya , binta sukai da kallo ganin irin dariyar da take kafun kuma ta yatsina fuska “inna tace ubanme kuke bakufito kunyi aikin da kuka saba ba, ga ruwa can babu kuje kudebo danshine aikinku”, tana gama maganar ta tabar Wajan sai faman sakin dariya take, duk binta da kallo sukai ganin irin dariyar da take kamar zautacciya, basu koma dakin ba suka fara ayyukansu cikin kankanin lokaci suka gama ,taheer ya tafi wajan garba mefaci da yake koyan gyara awajan sa , dakin yayi saura sai oumma ita kadai.

    🦋🦋🦋🦋……

    Ruwa oummey ta mika mata, ita da zoya sai faman sannu suke mata, amaimakon tarin ya lafa sai ya kara taso mata, tashi tayi cikin fitar hankali Sabida yadda ma’kogwaranta ya rike mata, a guje tayi hanyar barin wajan, kokarin dakatar da ita ummey tayi amma kwata kwata tafita hanyacinta, dausasan hannayensa yasa tare da janyota, kokarin fuskewa take haryanxu tarin yaki lafa mata , ganin hakan yasa oummey nufar daki da niyar dakko first aid box, hannu daya kawai yasa yana taffing din bayanta, yayinda yake hura mata iska a saman fuskarta, ya dau dogon lokaci yana hakan kafun ta fara sauke a jiyar zuciya nunfashin ta nadawo Daidai, ruwan da oummey tazuba mata ya nuna mata batare da ya kara kallan inda take ba, ruwan ta dauka tare da shanyewa tass tana sauke ajiyar zuciya Daidai lokacin da oummey ke dawowa wajan ganin tarin nata ya lafane yasata sauke ajiyar zuciya….,,

    Comment and share ✍️

    LITTAFINA PAID BOOK NE AKAN 300 kacal , amma daga yau Tuesday zuwa ranar asabar duk Wanda zai biya 200 zai biya amaimakon 300 .

    Za’a biya kudin ta wannan asusun 7041879581 Opay, Ayshatou galadima sai a tura shaidar biya ta wannan number 07041879581.

    💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

    _🦋Duk karfin izzata
    _🦋Gidan Aunty
    _🦋Sarki sameer
    _🦋Ya fita zakka
    _🦋Jini d’aya
    _🦋Baby

    MSS LEE💖💖✍️✍️
    ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JyvVuOvzYyF19np8UmFKV4

    💖💖GIDAN AUNTY💖💖
    (a heart touching love story)

    Story &written
    By
    Mss Lee 💖

    PAID BOOK

    PLX WAYANDA ZASU BIYA KUDINSU DAN ALLAH KUYI HAKURI  ANSAMU KUSKURE BA OPAY BANE PALMPAY NE YANZU ZAN KARA RUBUTA MUKU DETAILS DIN

    7041879581 Ayshatou galadima , palmpay .

    GIDAN AUNTY NA KUDINE AKAN 300KACAL ,ME BUKATAR SAMUN CIGABA HAR KARSHE ZAI BIYA KUDINSA TA WANNAN ASUSUN 7041879581 PalmPay
    Ayshatou galadima sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

  • Gidan Aunty Book 1 Page 9

    Gidan Aunty Book 1 Page 9

    Free page 9 🦋

    ********
    Suna zaune tun safe basu fito ba, oumma ta dafa musu ragowar taliyar jiya sukaji ana faman buga kofar da karfi kamar za a karya,” maryam bazaku fito bane kuna ji ina magana”, tsaya wa duk sukai daga cin abincin da suke jin muryar kaka tabawa, cikin damuwa oumma ta fito bayan ta yiwa su tahee kashedin karsu fito, a tsats tsaye tagansu ko wannan su , kaka ta bawa sai faman zaginsu take , “inna ina kwana”, bata bari ta karasa ba kaka ta bawa ta katseta“ban kwana ba , nace miki ban kwana ba , wallahi maryam kiji tsoran Allah , yanxu daman bakin cikin nace zan aurawa waccan yar taki me kama da aljanu tanimu shine zaku bi dare keda ban ka daddun ‘ya’yan ki ku fasa mun randa, kunsan tsawan shekarun randa ta da zaku tashi ku fasa mun” bata bari oumma tayi magana ba ta dora “ toh wallahi bari kiji,ko kina so ko ba kyaso aure kamar ya d’aurune dan ba fashi, itama munafukan da suka ‘ki futowa dani suke magana, ku fito ka aiki can kutashi kuyi, uban me ya hanaku yin aiki ma yau” sun kuyar da Kai oumma tayi kafun ta fara bata hakuri”kiyi hakuri inna, bamusan Wanda ya fasa miki randa ba” bata karasa ba Dije da bakin ta ya kun bura cikin haushi ta fara”toh karya za ai muku , in baku ba uwan wane ze fasa mata randa, yan bakinciki , shiyasa nace muku zuwan mutanen nan ba alkairi bane “ta kara sa da juyawa tana kallan mutanan gidan. “Hindu ce ta kalli inna ta bawa “ inna shiyasa ai jiya nace kawai kisa tanimu ya turo ba sai an jira bintalo ba, dan wannan bakin halin nasu ma waya sani ko sunbi wajan boka “ ta karasa tana hararar oumma da ta sun kuyar da Kai har ynxu fuskarta tana a yadda take.

    A daki kuwa jin yadda suke zagin oumman nasu yasa tahee fashe wa da kuka , sosai take kukan bakin ciki akan abunda suke musu, ita ba Auran ne ya dameta ba suje su aura mata duk Wanda suka ga dama amma bazata kuma lamunta da cin mutuncin da suke wa oumma ba, sosai shima taheer ransa ya baci. Kara fashewa da kuka tahee tayi jin kaka tabawa nacewa auwalu ya kirawo mata tanimu asa musu rana , sosai sukai musu tatas ko hakurin da oumma take bayarwa basu saurara ba suka bar wajan , Dije sai faman d’ingishi take dan tayi alwashin sai ta ruguza farin cikin su , dan tasan bokan da oumma ta ke bine yasa ayi mata haka (nace uhmmmmm Dije jikin ki be gaya miki ba kenan🤭).

    Farin macijin dake la’be tun dasu ya kurawa tahee ido ganin yadda take kuka shima sai launin idanuwansa suka canza daga baki zuwa ja ,sai ya silale ya fita baki d’aya daga dakin ganin oumma na kokarin shigowa.

    ➰➰➰➰➰➰➰➰
    DADA
    zaune take cikin wasu lallausan kujera jikinta sanye da wasu fararan cotton din kaya , sosai kayan sukaiwa jikin tsufanta kyau,a center din gabanta wani dan madaidaicin glass jug ne cike da fura, sai faman tashi kamshin furar da yaji damu yake, kallan Aunty dake gefe a zauna tayi tare da gyara zamanta , inajinki Amina , cikin inda inda Hajiya Amina ta soma magana “ wai dada naga yan matan gidan duk sun tasa ne , shiyasa nake ganin me zai hana ayi Auran dangi, ko King ne a aura amsa amrah, naga kamar suna kyaunar junansu”, sosai dada ta zuba mata idanuwa kafun ta soma magana “amma dai haroon kike magana akai ko, ke yanxu Amina bazaki dena wannan halin naki ba , shi sadaukin Yaushe kike ganinsa har yace miki suna Kaunar juna”, kin kina ta soma tama kasa magana “ saurin da katar da ita dada tayi”bana san irin haka , inda shi sadaukin ne yace yanasan yar taki da babu abunda zai Hana Aki aura masa , amma tunda be fada ba kar nasake Jin wannan batu, zaki iya tafiya”, sosai ran hajiya Amina ya baci da magan maganun dada , dan tabbas tasan da hajiya kilishi ce ko uwar king din da babu abunda zai hana tayi naam da zancen, daman ta dad’e da sanin cewa dada ba kaunarsu take ba , amma fili sai ta saki murmushin nan nata “tuba nake dada , ban fada da wata manufa ba, na barki lapiya”, itama dadan jinjina mata kai tayi “akiyaye “,itama aunty mikewa tayi tana fadin “insha Allahu”, tare da kama hanyar fita daga falon, bin bayanta da kallo dada tayi kafun ta girgiza kanta tacigaba da sabgar gabanta.

    Kamshin da batayi tsammani bane ya cika mata hanci ,juyowa dada tayi domin tabbatarwa, shidin ne tsaye , fuskarsa kwata kwata ba annuri akai ,kallo daya dada tayi masa ta dauke kanta ,cikin kasan makoshi kamar bazai yi magana ba sai kuma ya bude bakinsa “Assalamu alaikum” dabadan hankalin ta na kansa ba da babu abunda zaisa taji sallamar tasa” Wa’alaykumussalm “ tabashi amsa itama ,ta kowa yayi ahankali tare da karaso wa inda take, a maimakon ya zauna a kujerar kusa da ita sai ya zauna akan kujerar da take , “barka da yamma dada”, ta bile baki dada tayi “sai yanxu ka bayyana kenan, Kai yanxu saraki da ban nemekaba da bazakazo ba kenan,kadai ji tsoran Allah “,amai makon ya bata amsa sai ya kwantar da kasan a kafadunta tare da dan kwa’be fuskarsa kadan,ture kafadarsa dada tayi tare da mikewa , cikin masifa ta soma magana “ kabari in kayi aure sai kawi wa matar ka haka , bani ba salan zawaran da sukeso su aureni su gudu sabida karyayyan kashi”,dan murmushi leben baki ya saki da ko dada dake kusa da shi bazata gane hakan ba, sosai yayi musamman da pink lips dinsa ya kara turuwa,harara dada ta sakar masa tare da ta’be baki “kajirani” tana gama fada ta mike da nufar kitchen dinta, bata dade ba ta fito dauke da wani dan karamun tray, cikin yanayinsa na rashin garaje ya mike tare da amsar dan karamin tray din da ta fito dashi, inda suke zaune suka koma sai a sannan dada ta karbi tray din, lafiyayyar tuwo ne da miyar kubewa d’anya da taji nama da Ganda , sai kifin da aka sa masa, sosai kamshin abincin yayi masa dadi amma sai ya dan kawar da kansa gefe, dungure masa kai dada tayi” toh d’an neman magana ni na yi da kaina”, sai a sannan ya jiyo fuska a sake amma kwata kwata babu murmushi akai,karban abinci yayi tare da fara ci bayan yayi Bismillah, sosai yaci tuwan dan ya dade beci abinci da yawa ba,tunda ya fara cin abincin dada take binsa da kallo, Itade tanasan jikan nan nata, maganar hajiya Amina ce ta fado mata arai, kamar zatai masa magana sai kuma ta fasa, tasan halinsa yanxu ze iya tsanar yarinyar ko yaje ya ‘bab’bala yar mutane. Ganin yadda take kallansa ne yasashi dage mata gira , waro idanuwanta dada tayi “yanxu ni sadauki kake dage wa gira daya , sai kace yar iska, toh maza maza tashi ka bar part dinnan, ga furar ka nan ma, ka ‘bacemun da gani” sallamar zoya ce ya katse dada , da sauri zoya ta karaso wajan king “akhi “,lumshe mata ido yayi tare da budewa”na’am ukhti”, dariya sosai ta saki jin ya kira ta da ukhti “akhii duk yau ban gankaba fa” ta fada tana marairaice fuska,kamar bashi ba , shima ya dan kwaikwayi muryarta “Nima duk yau ban ganki ba ukhti”, binsu da kallo kawai dada tayi tana tabe baki” da yake kin ga ubanki shine kika manta inda kikazo, toh ku tattara kubar min daki”marairaice fuska zoya tayi “Haba dadar mu”yanxun ma harararsu tayi “Oho dai “, king ne ce mata komai ba sai mikewa da sukai tare da daukan furarsu “sai mun kara dawowa dada”,ka tsesu dada tayi “bana bukata”, shima king din tabe baki kawai yayi suka bar part din, da kallo dada ta bisu tana sakin murmushi” kaidai ba me iya maka , zanga macen da zata iya hakuri da wannan baud’ad’d’an halin naka “.

    ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
    BUNKURE

    Kai tsaye macijin bai tsaya a ko ina ba sai cikin ban dakin gidan, Daidai kaka tabawa tana kama ruwa jitai kamar abu ya hau kanta, sai ta taba Wajan taji ba komai , sharewa tayi tare da cigaba da abunda take, dan karamin abu takumaji kamar yana yawo a jikinta, a  sukwane tayi mike tana karka da jikinta, abun be dena yawo a jikinta ba sai ma kara yawa da yayi, ihu dada ta saki da nufar hanyar fita daga bayin, dan karamun halittar da ta ganin a kofar bayin yasata komawa ciki da sauri tana zare ido”nashiga uku” jitai wasu murya yan kanana suma suna cewa “na shiga uku”, amaimakon tayi salati sai ta fara “laha’ila, ni tabawa na shiga uku me nake gani” ta karasa maganar tana fashewa da kuka duk ta hada uban gumi, wata muryar daban sa’banin ta dazu itama” laha’ila ni tabawa na shiga uku ne nake gani” aka karasa maganar da fashewa da dariya, wani kukan kaka ta bawa tasaki ganin yadda halittar ta nufota Gadan gadan yasa kaka ta bawa sumewa take a wajan .macijin nanne ya bayyana tare da karasa wa inda take Daidai bakinta ya buga mata jelarsa, take a wajan bakin kaka tabawa ya kunbura, batt ya bace shima da barin ban dakin.

    Su tahee duk sun fito suna aikin su, yau kwata kwata ba annuri akan fuskokinsu, ruwa suka fara d’ebowa kafaun su fara aikin gidan , tana cikin aikin taji zuciyarta ta fara washewa daga cunkushewar da tayi a kirjinta, shima taheer hakan yaji, lokaci d’aya suka sake tare da cigaba da ayyukansu yadda suka saba, ganin haka yasa itama oumma zuciyarta yin sanyi ganin duk sun saki ransu, kusan  awa daya suna aiki a tsakar gidan duk mutanan gidan sunshige ciki sabida ranar da ake me zafin gaske, ganin yadda ake kokarin bude bandaki yasa duk zubawa kofar ido, da kyar kaka ta bawa ta bude kofar sabida yadda bakinta ya kunbura sai faman din gishi take, binsu tayi da kallo ganin yadda suka tsare da idanuwa, bakin da ya kara kunbura ta bude daniyar zaginsu, zugin da taji ne yasa ra hadiye maganar tana matsar kwalla da bin gefensu ta wuce. Sosai dariya take so ta kwace musu ganin yadda ta wuce tana tsamin kashi, tana shigewa daki kuwa suka fara dariyarsu, TAHEER harda faduwa sabida dariya, itama oumman murmushi ta saki ganin yadda kaka ta bawa ta dawo kamar tsohuwar mahaukaciya, sosai suke dariyarsu, sai da suka gama dan kamsu sannan suka cigaba da aikinsu.

    **DIJE
    zaune take cikin dakinta da ya cika da uban shirgi ,sai faman tashin wari yake da d’oyi , ko ina na dakin yayi kaca kaca dashi ita kadai ce a dakin sai karamar nokia dinta dake hannunta , ta dad’e tana waya da kawarta jimmala kafun ta kashe tana dariyar mugunta, kamar jira ake kuwa tana kashe wayan aka tsinka mata mari, take a wajan tayi filinki sabida azabar marin da taji, bata dawo hayyacinta ba ta kara jin saukar wani marin a fuskar ta, kuka ta fashe da shi, sai faman waige waige take, ganin ba kowa a dakin yasa kudawa zuwan mata take a wajan, sosai ta kuma rud’ewa jin abu na yawo a jikinta,duk inda takai da tabawa sai taji ba awajan abun yake ba, sosai Dije ta rude sai faman marin kanta da take , tana marin tana kuka, ga majinan da ya cika fuskarta , sai faman tashin tsamin wari take…

    Comment and share

    💖 THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

    💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA💖
    👇
    💖DUK KARFIN IZZATA (star lady)💖

             💖GIDAN AUNTY (mss Lee )💖

                💖JINI DAYA ( MRS bbk )💖

    💖YA FITA ZAKKA(maman sayyid)💖

    💖SARKI SAMEER (xeenat love)💖

              Mss LEE💖✍️

    ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

    💖💖GIDAN AUNTY💖💖
    ( A heart touching love story)

    Story &written
    By
    Mss Lee💖

    💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

    PAID BOOK

    MAISAN AYI MASA TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

  • Gidan Aunty Book 1 Page 10

    Gidan Aunty Book 1 Page 10

    BOOK 1 📕

    Free page 10 🦋

    Shigowar bintalo dakin kamar wacce aka jefo ta ko sallama babu, yasa dije kamewa, komai sai ya tsaya mata, kallan kanta da dungayi ganin duk ta ya mutsa jikinta, kallan ta bintalo tayi rai a bace tana toshe hanci “Haba Dije , kazantar taki har takai kiyi kashi a jikinki, gaskiya kina bada ni , ji beki katuwar kawai sai wari kike faman yi , ga kashin ki me shegen d’oyi, ta karasa da hararanta. Dije ce ta soma magana “Haba bintalo , Kema kinsan haka kawai bazanyi kashi a jiki ba , lalurace ta sameni , ni kaina bansan ya akai hakan ta faru ba”, ta kare zance da zunbula hijabi, gudun kar yan gidan su ganta, tayi sauri tashige bayi bayan dan ruwan da ta dauka a buta.

    Su tahee ma ransu fess suka koma daki, bayan sun gama aikin su , haka suka yini a daki, lokaci zuwa lokacin tunanin dan iskan da akace za a aura mata yana fado mata arai.

    *******
    A kwana a tashi ba wuya wajan Allah SWT, yau watan su tahee 1 da ‘yan kwanaki a bunkure, abubuwa da dama ya faru ciki harda maganar Auran tahee da tanimu da tayi mugun tsana. A yan kwanakinan ba karamun wuya suke shaba wajan mutanan gidan, musamman kaka tabawa da dije datayi mugun tsanar su, kullum da kalar ukubar da zasuyi musu, abu daya ne ke kwatarsu , duk lokacin da kaka ta bawa ta wahalar da su ranar bata iya baccin arziki sai safiya , a lokacin su tahee ke samun damar hutawa . Taheer ma yanxu ya koyi faci, Inya futa tun safe bashi ke dawowa ba sai 6 na yamma, a gida kuwa daga oumma sai tahee, yanxu ma kwance take kan cinyar oumma tana taje mata uban tilin gashin kanta da ya zubo har gadan bayanta da cikon da yake dashi, “oumma”cewar tahee,”naam aunty tahee”oumma ta amsa mata cikin zolaya , dariya tahee ta saka, “Allah oumma ni banasan wannan gashin kan nawa wani lokuta, kallifa ko tajeshi bana iyayi da kyau, “aikinsan hanyar iliya me aski, sai kije ya aske miki”, turo baki kawai tahee tayi dan tasan magana oumma ta fada mata.

    Suna zaune sukaji an banko kofar dakin , duk kallan kofar sukai lokaci daya , bintalo dake tsaye se faman cika take ta kalli tahee ba ko sallama , “toh matar mashayi sai kije angwan naki yazo”, tana gama fadar hakan ta banko musu kofa. Tsaki tahee taja tana kokarin kontawa oumma ta dakatar da ita “tashi kije”bata ce wa oumma komai ba ta zura hijabinta tare da ficewa waje.
    A tsaye ta ganshi cikin wasu yan iskan Riga da wando, sai faman tashin warin giya yake, saurin toshe hanci tahee tayi jin zata yi amai, ga bakikkirin bakar fuskarsa sai faman naso nake , cikin Maye ya zuba wa tahee jajan idanuwansa” ke dan uwarki , shine zan dunga kiranki kina kin zuwa, ke gaki yar iska ko” ya karasa yana tangal tangal kamar ze fado mata, matsala tahee tayi baya tana binsa n da kallan tsana “inka gama zan wuce dan banda lokacin dan iska”, wayo idanuwansa yayi cikin maye yana kifkifta kana nun inaduwansa” ke, ni kike cewa dan iska dan uwarki, toh bari na nuna miki iskanci, kafun na bada sadaki zan d’anaki nasan zakiyi ruwa” ya karasa tare da daga hannunsa zai tabata, saukar marin da yaji a fuskarsa ne yasa shi tangal tangal zai fadi, ganin yana ganin biyu biyu ne yasashi kara ware mummunar fuskarsa “ kutumar ubancan , ya na fara ganin garin yana juyawa ko an fara hazo ne “be kammala maganar tasaba tahee da idanuwanta suka juye ta kara tsinka masa mari” saurin dafe fuskar tasa yayi har yanxu bakin nashi be mutu ba” auzubillahi, ko an fara tafiya lahira ne ban sani ba” saukar marin da yaki a fuskarsa ne ya sashi zabura da fita “shikenan  a fara sha hada , an fara mutuwa “, sai da ya bace wa ganin ta sannan idanuwan ta suka dawo Daidai ganin ba kowa a wajan yasata dage kafada da komawa cikin gida . Koda ta kowa cikin gidan oumma bata ce mata komai ma , itama tahee batace komai ba sai hirarsu da suka cigaba .

    ➰➰➰➰➰➰➰➰➰

    LAGOS

    Tun d’azu ta kasa zama sai faman zirga zirga take , Aunty kawai take jira ta shigo, ta dade a tsaye kafun hajiya Amina ta shigo falon duk rai a bace , kallanta amrah tayi kafun ta sauke a jiyar zuciya, “Anda ce aunty!?” Ta tanbayeta da sigar tanbaya , bata kulataba sai da ta samu waje ta zauna “ amrah ban taba sanin matar nan makira bace sai yau, wai harni tsohuwar matar nan zata karya ta”, tass ta bawa amrah labarin abunda ya faru ta dora da cewa” wai ni amrah kina shafa kwallin tayar masa da sha’awan da Malam ya baki “ cikin kun burin fuska Amrah ta amsa mata “ ina shafawa aunty, gasky ya kamata a koma wajan Malamin dan bazan taba yadda wata ta same shi in ba ni ba, ni ko baze aureni ba inaso mujiyar da juna dan inasan na d’ad’and’ana zumarsa kona kashe sha’awar dake tasomun”jin jina mata kai kawai hajiya Amina tayi, itama amrah bata kuma cewa komai ba ta shige daki, da kallo aunty Amina ta bita “ ba ke ba ai amrah ko ninan da zan samu damar d’and’anasa so nake , musamman yadda yake da kakkarfar jikinta, ni kadai nasan dad’in da zansha “ duk cikin zuciyarta take wannan sa’ke sa’ken kafun ta nufi haryan dakin ta itama .

    ***********
    Ya dan Jima a hospital yau sabida wasu Mara lapiya a dake dake cikin wani mayuwacin hali, successfully kuwa akayi musu aiki, bayan ya dawo ne zaki ya kawo masa files din company, ba karamun barnan kudi akai ba, makudan millions sun ‘bata, batare da kwakkwaran daliliba,duk account din da kudin ke fita ta wajansu anne mesu anrasa, Wanda hakan ya bashi alamar tanbaya , tabbas ana fitar da kudi sannan dasa hannun wasu daga cikin companyn , amma tanbayar su wanene suke fitar dashi, daya daga cikin secret agent din companyn king yasa a nemo masa, tare da bashi Umarnin binciko masa komai daya danganci file din companyn,suna gama aikin da zasuyi sukai futar gaggawa shida zaki yau ko masu tsaro be fita dasu ba.

    ➰➰➰➰➰tunda ta tashi yau da fargaba ta tashi, ganin kullum mutanan gidan sai sunyi maganar aura mata dan iskan da suka ce, komai cikin sanyi take yinsa, “tahee”oumma ta kira sunanta “naam oumma”sosai oumma ke kallanta”meke damunkine yau”murmushin ya’ke tahee ta saki “babu komai oumma kawai yau da fargaba na tashi”, murmushin manya oumma ta saki” in Auran nan kikesa wa aranki kicireshi, ki dunga yawaita addua in alkairi ne, in kuma sharrine Allah  ya nisan taki dashi”jin jina mata kai tahee tayi “insha Allahu oumma”.

    Bin bayan ta da kallo oumma tayi , abun na damunta sosai amma tana boye rauninta ne sabida kar tahee ta karaya, kullum adduar ta Allah ya zaba mata mafi alkairi.
    Shigowar tahee dakin ne yasa taheer sakin murmushi dan duk yaji zancensu,kara sakin wani murmushin yayi yana kamo hannun tahee din, be bari tayi magana ba ya dora da “nayi mafarki, nayi mafarki kinyi aure ,kin auri babban mutum da kowa yake san mallakarsa ba wancan dan iskanba, zakiyi rayuwa dasu sosai wasu zasu soki, wasu kuma zaki nuna miki ki”binsa da kallo kawai tayi duk da bata yadda da magan ganun saba amma hakan ya sanyaya mata zuciya .

    Karfe biyu na rana wasu manyan motocine suka shigo garin, kowa  sai bin motar yake da kallo ana d’aga musu hannu, Daidai kofar gidansu tahee motocin nan sukai parking yara da manya kowa ya cika wajan , cikin gida kuwa har an kawo musu labari, da sauri kaka ta bawa ta shige daki tare da dakko wata farar Leda data cukurkude, bude ledar tayi tare da dakko tsinken turaran wuta, bayan ta kunna turaren wutarne ta koma ta dauko sabuwar tabarmarta ta shinfida a tsakar gidan , komai cikin sauri take yinsa .

    A hankali ta fito daga cikin bayan wata tinted prado,bayan uban damin kudin data bawa security su rabawa mutane , ba kowa bace face hajiya kilishi, a hankali cikin takun manyan mutane ta nufi cikin gidan fuskarta dauke da murmushi, yayinda biyu daga cikin security din suka fara fito da kayan motar suna shigar dasu cikin gidan . Tun daga kan matasan gidan har manya kowa tsugunnawa yake yana gaisheta, cikin sakin fuska take amsawa kowa harta karasa zama akan tabarmar da aka shinfida mata batare da ‘kyan ‘kyanin komai ba. Sosai sukai hirar Yaushe gamo ta bawa kowa tsarabarsa , duk wannan abun da ake su tahee basu sai me ke faruwa ba , sai hayaniyar da suke ji tana tashi sama sama,anan ne suke mata gulmar dawowar oumma da Sanar da tahee, sosai hajiya kilishi ranta ya baci akan rashin sanar da ita da basuyi ba , da Auran da suke san yiwa tahee, ranta ba karamun baci yayi har suka fara dana sanin fada mata , bata nuna musu komai ba sai fadan da tayi musu da Nasiha me ratsa jiki , sun dade suna tattaunawa kafin ta mike ta nufi dakin su tahee, kwankwasa kofa tayi , TAHEE dake tsaye rike da tsintsiya ta bude kofar , cikin waro ido da tsananin farin ciki ta furta “AUNTY” itama aunty tata murmushi ne kwance a fuskarta, budewa tahee hannuwa tayi da sauri kuwa tahee ta nufe ta , ta rungumeta sosai tayi farin ciki da ganin auntyn Tata har hakan ya kasa boyuwa, kallanta hajiya kilishi tayi ganin yadda ta kara ramewa ga bakin da tayi, batace mata komai ba sai girgiza kai kawai da tayi bayan tahee ta bata hanyar wucewa, sallar da hajiya kilishi tayi ne yasa ko wannansu kallan kofa, take ko wannansu ya saki murmushi, TAHEER ne ya tashi daga inda yake ya bawa aunty ta su waje , bayan sun gaisa sun dade suna hira kafun hajiya kilishi tayi wa oumma jajan abin da ya faru , kallan tahee hajiya kilishi tayi kafin ta kira sunanta” taheera “ tagowa tahee tayi tana amsa mata “na’am aunty” cikin dan hade rai hajiya kilishi ta soma magana” naji labarin kince kinaso kiyi aure har ankawo kudin ki , hakane “, fashewa da kuka tahee tayi tana girgiza kanta ni bana san shi aunty”ganin yadda take kuka ne yasa aunty tausaya mata itama tayi mata hakan ne sabida ta san asalin gaskiyar “shikenan share hawayen to” kamar yadda ta satan kuwa share hawayen tayi” yanxu zan baki za’bi zaki bini ko zaki auri tanimu” saurin dago da idanuwan ta tayi da zubawa auntyn tata, murmushi hajiya kilishi tayi tana mikewa “ kuyi shawara toh “, ganin yadda ta mike din zata basu waje oumma ta dakatar da ita “itama yar kice ai wata shawara zatayi , duk yadda kikayi ai Daidai ne”,Murmushin farin ciki hajiya kilishi tayi “nagode sosai yaya, Allah ya bar zumunci, nan da munti 30 zamu tafi “ tana gama fadar hakan ta bar dakin.
    Dan kallan oumma tahee tayi cikin damuwa tace “oumma kin yadda na tafi ya barku” yar harara oumma tayi mata kafun ta mike “ idan ba kyaso ki bita sai kitsaya ayi miki auren inyaso sai ki tare” tana gama fadar hakan ta shige dakin. Kallanta TAHEER yayi “ shawarar da oumma tayi miki shine alkairi a gareki dan mutanan nan bazasu kyaleki ba sai sun aura miki shegen mutumin can , me kama da biri “jinjina masa kai tayi cikin damuwar dake fuskar nan, ganin yadda ta damu yasashi  fara janta da hira har ta sake. Suna zaune oumma tafi to tare da kallansu, sosai tayi wa tahee fada da nasiha akan ta rike mutuncin ta, ta zama me hakuri da kawaici a duk yadda ta sameta, sosai oumma tayi mata nasiha da nuna mata illar rashin yin azkar, har kuka tahee tayi ganin yadda oumma take Mata nasihan me ratsa jiki, ko wannansu dauriya yake, shima taheer ji yake kamar ya saki kuka amma ya dake tare da sakin murmushi, suna zaune a hakan hajiya kilishi ta dawo , kasan cewar tahee tayi wanka hijabinta kawai tasa tana sharar kwalla, TAHEER ya dauki jakar kayanta tare da fita dasu, oumma bata biyota rakiya ba gudun abinda ze je ya dawo . Cikin sanyin jiki tahee ta fito waje , tsatstsaye ta same mutanan yan gidan kowa sai faman harare Harare suke ba bakin magana , musamman Dije da har kwallar bakin ciki se datayi, bintalo ba sai faman zaginta take ganin ba a tafi da ita . Saida hajiya kilishi ta gama sallamarsu kafun ta kama hannun tahee ta shigar da ita mota, a haka motocin suka fara tafiya, tunda aka fara tafiya tahee tunani take , har aka karaso airport din bata sani ba sai da hajiya kilishi tayi mata magana , wata Hanya sukabi a cikin airport din da ya kaisu wani babban fili, wasu manyan jiragene awajan kusan guda uku, ko wanne da tanbarin AL_NAHYAN a jiki , daya daga cikin jiragen suka nufa jikin tahee sai faman rawa yake,Daidai bakin step din jirgin ta tsaya ta fara rarraba idanu, ruko hannunta hajiya kilishi tayi “karki damu ba abunda zai miki” saurin gyada mata kai tahee tayi zuciyarta sai faman bugawa take , ga hannun hajiya kilishi da ta rike gagam a haka suka shiga cikin jirgin, duk sauran bodyguard din Sara mata sukai tare da tsayawa a wajan jirgin….

    Comment and share ✍️.

    💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

    💖LITTAFAN SUNE KAMAR HAKA 💖
    👇👇👇👇👇
    💖DUK KARFIN IZZATA( star lady)💖

    💖GIDAN AUNTY (mss Lee )💖

          💖SARKI SAMEER (xeenat love )💖

    💖YA FITA ZAKKA (maman sayyid)💖

           💖JINI DAYA (mrs bbk)💖

    Comment and share ✍️.

    Mss Lee 💖

    ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

    💖💖GIDAN AUNTY💖💖
    (A heart touching love story )

    Story & written
    By
    Mss Lee 💖

    💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

    PAID BOOK

    MAISO AYI MISHI TALLAN KAYANSA YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

  • Gidan Aunty Book 1 Page 11

    Gidan Aunty Book 1 Page 11

    BOOK 1📕

    Free page 11 🦋

    Karfe 9:10 na dare jirginsu ya sauka a murtala muhammad international Airport (MMIA) dake Garin lagos, wasu dankara dan karan motocine sukazo daukarsu,da kyar tahee take daga kafarta jin yadda kanta ke sara mata, mintuna 35 ne suka kaisu AL_NAHYAN EATATE dake banana island ,tundaga kan Layin gidan kan tahee ke matukar sarawa ga wani irin tsananin bugu da zuciyarta kema ta,ko ina da yalwataccen haske kamar ba dare ba , ta ko ina sojojine ke Sara musu, sosai tahee ta  rike hannun hijabinta gagam ganin irin sojojin dake gidan , sabida ydda zuciyarta ke bugawa sosai ta kulle idanuwanta , direct motocin part din hajiya kilishi suka nufa,sau biyu hajiya kilishi na kiran tahee amma bata masa ba , ana ukunne ta tabata sosai tahee ta ware idanuwanta, kallan ta hajiya kilishi tayi na yan sakanni kafun ta soma magana “ lapiyan ki kuwa “ gyada mata kai taheera tayi sai kuma ta bude bakinta” Kai na ne ke dan ciwo aunty “, cikin damuwa hajiya kilishi ta kamo hannunta ta futo da ita daga cikin motar”sannu kinji, nasan gajiya ce muje ciki kisha magani sai ki kwanta”nan ma gyada kanta tahee tayi batare da cewa komai ba,kafarta ta taka da soma tayifa sosai wani azababban zafi ke ratsa kafarta , kamar wacce ta dora kafarta a garwashi, ko wacce addua tazo bakinta yi take , nan da nan taji zafin ya tafi, haka suka karasa ciki tana bun hajiya kilishi a baya, dakin dake gefen star case ammi ta bude , “Bismillah tahee”, shiga ciki tahee tayi bakin dauke da Bismillah kamar ydda hajiya kilishi ta umarceta,”ga ban daki nan , zansa a kawo miki abinci da magani sai kishi ki kwanta”cewar hajiya kilishi,”na gode sosai aunty ,Allah ya saka da Alkairi”bata bari ta karasa ba ta katseta”Godiyar ta isa haka kisa mu ki huta”tana gama fadar haka ta bar dakin.itama toilet ta nufa tare da kama ruwa sannan tayo Alwala , tana fitowa ta tarar da jakar kayanta, hijab ta dauka tare da nufar inda dadduma take shinfide,sallolin da ake binta ta rama tana cikin addua ne aka kwankwasa kofar, Tashi tayi tare da budewa , wata budurwace ta shigo sanye da blue din Riga da dark blue din skeat ,”good day ma”cewar ta, murmushi kawai tahee tayi batare da ta amsa ba, abincin dake hannunta ta ajiye cikin center table din dake kusa da ita , cikin gurbatacciyar hausarta tace” madam tace na kawo miki abinci sannan kisha magani ki kwanta,”toh na gode”, jinjina mata kai budurwar tayi tare da furo mata kofa , abincin da aka kawo mata ta bude lafiyayyan abincine me rai da lapiya a ciki,sai kunun aya da aka sa mata cikin wani mini glass jug, daga gefen tray din wasu Kayan mar marine aciki, kadan ta tsakuri abincin “da oumma da taheer sunanan tare za muci abincin , nasan yanxu Suna can su kadai”, cewar tahee harta kammala cin abincin, kuskure bakinta tayi tare da watsa ruwa , sannan ta hau kan lapiyayyan gadon dakin ,lilliba tayi jin sanyi na ratsata ta ko ina , bata dade da kwanciya ba bacci ya dauke ta .

    ➰➰➰➰
    A gajiye ya dawo gidan bayan zaki ya ajjesa, ko part din ammi be Jeba, Wanka kawai yayi tare da nufar down stairs , Kai tsaye kitchen din dake falon ya nufa, banban kitchen ne da ya gaji da haduwa komai na anfanin kitchen akwai shi a ciki,kitchen din sai faman daukan kyalli yake, coffee ya hada cikin coffee maker din kitchen din, kan daya daga cikin kujerun dining din kitchen din ya zauna, a hankali yake sipping coffee din dake hannunsa,bayan ya shanyene ya kara hada wani tare da barin kitchen din, stair case ya dau tare da nufar kofar hagunsa, taku kadan ya kai shi wasu kofofi guda uku, kofar tsakiya ya shiga , ya dau dogon lokaci a ciki kafun ya fito, stair case din da zai kaishi second floor ya hau, a hankali yake taka stairs din har ya karasa hawa saman, kan daya daga cikin kujerun falon ya zauna tare da fara operating din system dinsa, ya dade yana anfani da ita kafun ya kashe ta gaba daya , toilet ya nufa be dade ba ya fito tare da nufar faffadan gadonshi, remotes din fitulun part din ya kashe kafun ya kwanta cikin lallausan gadonsa, be dade da kwanciya ba bacci ya daukesa.

    Wutace sosai take ci, da anzuba mata ruwa Sai ta kara tashi kamar wacce ake hurata , ga hayaki da ya gauraye ko ina, daga cikin wutar kuwa hannu ake miko masa cikin azaba “Akhee habeeby!!Akhee habeeby!!”hannunsa ya Mika da niyar ya kamo Wanda yake cikin wutar… farkawa king yayi sai faman hada gumi yake bayan sanyin Acn da ya cika dakin, adduoi ya fara karantawa a hankali wata nutsuwa tazo masa ,wayarsa dake side din gadan sa ya kunna,4:30shine abunda agogon ya nuna masa, mikewa yayi tare da nufar toilet, wanka ya fara yi kafun yayo Alwala, ya dade yana nafila kafun ai kirin sallah, direct kasa ya nufa bayan ya idar da sallahn , sanye yake cikin white jallabiya , sosai farar jallabiyar tayiwa surar jikinsa kyau,gashin kansa sanye yke cikin bakin rawanin larabawa, sosai kyawun fuskarsa ya fito, musamman idanuwansa da suka kara haske sai kyalli suke duk da kasancewar fuskarsa a hade yake,a hanyar zuwa Masallaci suka hadu da abeey shima zasu tafi masallacin,a haka motocin su suk fita , a dawo wa ma tare suka dawo gidan,Kai tsaye part din dada suka nufa dukansu, ganin babu kowa a falon yasa su samun waje ko wannan su ya zauna. Mintuna kadan sai gashi ta fita sanye da hijabi a jikinta , ko wannansu gaishe da ita yayi , yayinda take amsawa fuskarta washe da fara’a, kankance ido king yayi” dada yau naga sai fara a kike ko an miki albishir da zuwa umarace”a hankali yayi maganar amma duk da haka sai da ta jisa, hararar sa dada tayi”A’ah gorin daurin aurenka aka kawomun”kara hade fuska king yayi tare da dauke idanuwansa daga kanta,tabule baki dada tayi “Kai dai Kasani mutum kullum cikin daure fuska ,kamar audiga ina dalili”, be tanka mata ba sai ma lumshe ida nuwansa da yayi, abeey kam murmushi kawai yayi, hira suka dada ta fara tare da su uncle musaddiq , abeey na sa musu baki lokaci zuwa lokaci na yana kallan king, ganin hirar tasu bame karewa bace yayi musu sallama tare da nufar part dinsa. Gym room dinsa ya nufa , tare da sa kayn motsa jiki , ya dade  yana motsa jiki kafun ya futo duk ya hada zufa ,kwantaccen gashin kansa ya zubo masa har wajan idanuwansa,Wanka yayi tare da shirya cikin wani hadadden suit red colour, daddadan kamshin turaransa ya cika ko ina , gashin kansa ya sha gyada yayin da gefe guda na fuskar sa gashin ya futo harwajan idanuwansa,pink lips dinsa ya turo sosai , yayinda fuskarsa take a daure,sosai yayi kyau cikin shigarsa , sai ta kara futo da ainahin kalarsa ta larabawa,cikin takun sa ya bar part din , direct part din ummey ya nufa, har lokacin zoya bacci take , be dad’e ba ya bar part din tare da nufar part din ammi.

    Yana shiga falan ya tarar da ba kowa a ciki sai yan aikin dake gyara dinning , suna ganinsa ko wanne jikinsa ya dau rawa, cikin rawar murya suka gaishe shi,da hannu kawai yayi musu alama , suna ganin haka sukai saurin barin wajan, kan daya daga cikin 2 sitter din kujerun ya zauna tare da crossing legs dinsa. Cikin shigar material ammi ta fito daga kitchen , hannunta dauke da tray din abinci, cikin na tsuwarsa ya mike tare da nufar inda take da nufin sauke mata tray din, girgiza masa kai tayi “no son,abincin daughter ne”, kallan ta yayi na yan sakanni kafun ya bude bakinsa” me ya kawo su part dinnan da sassafe”,hararar sa ammi tayi “Kai me ya kawo ka da sassafe, Kai tsaye ya bata amsa “to see my happiness “murmushi ammi ta sakar masa tana kara jin kaunarsa a ranta ,”ba abincin su amrah bane, wannan na sister dinka ce , you will see her soon”bai ce mata komai ba sai lumshe mata ido da yayi, itama Kai tsaye dakin da tahee take ciki ta nufa, akan dadduma ta tarar da ita , mikewa tayi tare da karban tray din hannun Amin ta ajje mata a gefe” ina kwana aunty”kallanta sosai Ammon tayi “from today ki kirani da ammi not aunty” jinjina mata kai tahee tayi sai kuma ta bude baki”insha Allah ammi” dariyar jin dadi ammi tayi “kin tashi lapiya, hope ciwan kan ya sauka”, “eh ya dena ammi”cewar tahee, “toh Allah ya kara sauki, ga breakfast nan in kin gama sai ki fito falo karkiyi ta zama a daki ke kadai”, jin jina mata kai tahee tayi “toh ammi na gode “, fita ammi tayi daga cikin dakin, TAHEE kuma waje ta Samu ta zauna “ya Allahu har na fara kewar ku oumma na da taheer dina “.
    A falo kuwa har yanxu king na zaune ya lumshe idanuwansa “if not for ammi, who dare to keep him waiting”,lips dinsa na kasa ya fara tsotsa kwata kwata bazaka gane yanayinsaba, shafa gefan fuskarsa da akaine yasashi bude idanuwansa,ammi ya tarar a tsaye sai faman murmushi take saki, dauke kansa yayi daga kallanta,”sorry my son”, dago da idanuwansa yayi tare da kallanta “it’s okay , ammi am hungry “,am coming” kawai tace tare da komawa kitchen , hadadden breakfast dinsa da tayi masa shida tahee takawo masa , tsabar sarauta a baki take bashi,kadan yaci tare da Shan kunun ayan da yake matukar kauna,bayan ya kammala cin abincinsa ammi ta kallesa “son Yaushe zaka dawo gida”Kai tsaye ya bata amsa” it can be possible da yamma , kina bukatar wani abune “girgiza masa kai tayi “no son na tanbaya ne kawai”,mikewa yayi tare da pecking din goshinta “am going now”, take care shine abunda ammi tace masa , jinjina mata kai yayi tare da barin part din.

    A daki Kuwa tahee wanka tayi bayan ta kammala cin abincin da ammi ta kawo mata, hijab dinta ta saka tare da kwashe kwanukan ta fito falo, Daidai lokacin da yan matan gidan ke shigowa, kallan tara saura kwata amrah ta bita dashi”ke kuma daga ina”,murmushin yake tahee ta saki”ina kwananku “wani hararan amrah ta bita dashi “bashi na tanbayeki ba”.ihsan ce ta katse mata zancen ta” easy amrah , ki bita a hankali mana”, kallanta ihsan tayi cikin sake fuska”yan mata ya sunan ki”, amsa mata tayi da “TAHEERA “tana sun kuyar dakai, lokaci d’aya zuciyar firdausi da amrah ya buga, “wow gaskiya kina da suna me dadi gaki kyakkyawa”,Shigowar ammi ne ya katse ihsan, “ah ah yan matana yana ganku a tsaye “, sumayyace tai saurin bata amsa “bakomai ammi mun shigone sai mukaga bakuwarki shine muke dan gaisawa”murmushi ammi tayi “kun kyauta kuwa , ku samu waje ku zazzauna , Kema tahee zo ki zauna”, kallan ammi tahee tayi “dama ina san wanke wadan nan kayan ne”girgiza mata kai ammi tayi “basai kin wahalar da kankiba”, wani dan button ta danna sai ga yan aiki guda biyu sun fito, kallan daya daga cikinsu ammi tayi “asabe ga kwanukwanan a hannun tahee su zaki kai kitchen”, toh hajiya cewar wadda aka kira da asabe,kwanukan hannun tahee asabe ta karba “nagode “murmushi asabe ta sakar mata ,”oya zo ki zauna “cewar ammi, waje ta samu daga kasa zata zauna ammi ta dakatar da ita, “ga waje zauna akan kujera”,batai musu ba ta hau daya daga cikin kujerun, “toh yan matana wannan sunan ta taheera ana ce mata tahee, Kema tahee wadaddan yayyunkine, wannan ta farkon ta nuna sumayya, sunanta sumayya,sai ihsan a kusa da ita , sai amrah da kuma firdausi”yawu firdausi ta hadiye”ammi ko itace wacce Kikace zaki kawo mana “, gyada mata kai ammi tayi, “tahee zata cigaba da zama tare damu, Inaso ku zauna kamar yadda nasan ku, hope zaku karbeta”, murmushin yake amrah ta saki “insha Allahu ammi”a haka suka dan taba hira kuwa da abunda yake sa’kawa a ransa, TAHEE ma duk a takure take ganin irin kallan da amrah take binta dashi,dama dama ihsan da ke janta da hira, sumayya da firdausi ko kallanta basa yi.

    Zuciyarta tafarfasa take ba abunda take nanatawa sai “bazai yuba, it’s impossible “ tare da mikewa …..

    Comment and share 💖
    Alkalamin Mss Lee ✍️

    💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

    LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA

                 👇👇👇👇👇
    DUK KARFIN IZZATA (star lady )

    GIDAN AUNTY ( mss Lee)

    JINI DAYA ( mrs bbk)

    YA FITA ZAKKA( maman sayyid )

    SARKI SAMEER( xeenat love)

    Alkalamin Mss LEE✍️✍️✍️✍️
    Ina Godiya masu commenting , I heart you all💖💖.

    ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

    💖💖GIDAN AUNTY💖💖
    (A heart touching love story)

    Story & written
    By
    Mss Lee 💖

    PAID BOOK
    MAISAN COMPLETE DIN GIDAN AUNTY YAMUN MAGANA TA WANNAN NUMBER 07041879581

  • Gidan Aunty Book 1 Page 20

    Gidan Aunty Book 1 Page 20

    BOOK 1

    Free page 20🦋

    Ganin wanda ya riketan yasa ko wannansu sakin ajiyar zuciya sabanin amrah da aunty ta da suka fara farin ciki, hatta sumayya sai da ta tausaya mata duk da ba kaunarta take ba, dada sai faman sallallami take ganin Jinin da yake fita a kafar tata, ganin ta kasa taka kafar ne yasa ta daukar ta gaba dayanta tare da nufar 3 sitter din kujerun, har yanxu fuskarsa a hade ba ko digon dariya ga kuncin da zuciyar sa take tun dazu, hannu yasa da niyar zare kwalbar ta saki karan azaba tare da sakin wani saban kukan, inda kwalbar tashige ya kurawa ido, tabbas yasan in yace zai cire da karfi zai kara raunana mata ne , inda ya kunbura ya kalla da lumshash shun idanuwansa, a hankali ya kai hannunsa wajan tare da Mara matsawa a hankali, kara goce kafarta tayi jin wani saban azaba da take ji,kowa na cikin falon hankalinsa a tashe yake musamman ganin yadda kafar ta kunbura,”son kodai asibiti zamu wuce”cewar uncle musaddiq , lumshe idanuwansa yayi ,bai san takura da zata kaishi da yin magana , shurun da yayi ne yasa abeey kallansa” baka ce komai ba , in baza aje hospital ba sai a tafi clinic room ai ko ”, a fiske ya furta  “no need abeey” kafun ya ciro wayarsa, wasu numbers ya danna tare da kaiwa kunnansa , bai jira anyi magana ba ya furta “ large first aid box” yana gama fadar hakan ya kashe wayar, dan gajeran murmushi ya saki , yasan tabbas akwia abunda yake damun gudan jininsa tun ba yau ba amma da muwar da ya gani yanxu ta nunka wacce ya saba gani, fatansa ya samu wacce zata gyara masa wannan murd’ad’d’en halin nasa. Kukan tahee ne ya fargar dashi tunanin da ya fada , kanta na cinyar ummey sai faman sannu suke mata,dada ma ganin ciwon kafarta na kokarin tashi yasata yin shiru, kara rintse idanuwansa yayi ganin tana kokarin sa masa ciwon kai, dabadan su abeey ba da ba abunda zai Hana be faffalla mata mari ba, ko cikakken munti biyar ba ai ba sai ga zaki da wani dogon first aid Box a hannunsa, king ya ajiyewa kafun ya gaishe da mutanan gidan, a hankali yake motsa hannunsa kafun ya bude first aid box din, abunda zaiyi anfani dasu kawai ya dauka tare da nufar kafarta, sosai take hawaye duk da ba a jin sautin kukan nata,kwalbar data shige mata kafa yake kokarin cirewa sabida zafi batasan lokacin da ta kama hannunsa ba tana rintse idanuwanta,fuskarta duk ta baci da hawaye , cikin sauri ya dago da idanuwansa jin  shock din da yaji  lokacin da hannunta ya taba fatarta,
    Sau daya ya kalleta tare da dauke kansa, be wani sha wani dogon wahala ba ya cire mata doguwar kwalbar ,bin kafarta data kunbura yayi da kallo kafun yayi mata dressing dinta,har yanxu akwai ragowar hawayen a fuskarta, kowa na falan sai faman sannu yake mata,sabanin aunty dake mata dan dole, amrah kuwa sai faman danasanin turatan dayi take ganin king ya tabata,a fakaice take goge kwallar ba’kin ciki, yana gama dressing din be jira cewar kowa ba ya far part din fuskarsa a had’e har yanxu.

    🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

    Tunda Dije ta koma gida neman hanyar da zata kuma sawa su oumma maganin nan tayi, ganin kowa hankalinsa ba ya kanta tashige nan garansu sai faman ya tsine take kuwa, taci sa’a kuwa tunda ta shiga bataji motsin kowa ba harta sa kafa zata shiga ciki jin motsin ana taba ban daki yasata barbada maganin nan cikin sauri tare da barin wajan , Daidai taheer na fitowa daga ban daki, bin kofar da aka ‘bane yayi da kallo a tunaninsa oumma ce ,ganin babu Wanda yake shigo musu ban gare sai neman Futuna, kofar dakin nasu ya nufa,kamar Wanda aka rufewa baki ko sallama beyi ba yashiga dakin, jiyai kansa ya sara masa, duk dakin ya canza masa, waje ya samu ya zauna kamar Wanda aka tsira kuma ya mike, sosai yaji dakin ya fita aransa bazai iya zama ba, har ya taka kafarsa da niyar shiga inda oumma take sai kuma yayi saurin ja da baya jin kamar ya taka kaya, sosai yaji jikinsa ya daukan zafi , da yayi baya baya kuma sai yaji zafin na raguwa, da sauri ya fita daga dakin jin zafin na raguwa ne yasasa rugawa da gudu da barin gidan baki daya duk akan idan Dije da ta la’be a kan soro ganin yadda taheer ya fitone yasata sakin dariya, a zuciyar ta sai gode wa boka take .

    A daki kuwa kusan awan oumma d’aya sai faman zagaye take ganin har yanxu taheer be shigo ba, kofar toilet din ta nufa tare da kwankwasawa”taheer !! Taheer!! Taheer!!’ Ganin ta kirasa har sau uku be amsa ba yasata bude ban dakin, babu kowa a ciki sai ruwan dake nuna anyi anfani dashi, batayi tunanin komai ba ta koma ta zauna kusan yan mintuna ganin be dawo ba har lokacin yasa hankalin oumma ya fara tashi, hijabinta ta dauka da niyar lekasa, a tsakar gidan ta samu wasu daga yan gidan zazzaune kamar yadda yazama al’adarsu, Dije dake zaune har lokacin ne Tasaka shewa” za a tafi yawan tazubar Din da aka saba cikin dare” oumma bata kulataba tayi ficewarta dan tasan kota musu bayani ba saurara zasuyi ba, ganin hakan yasa yan tsakar gidan fara kuskus. Duk inda tasan zai iya zuwa taje har wajan da yake koyan faci taje amma bata tarar dashi ba , sosai hankalinta ya kara Tashi sanin da tai masa ba ya dare haka ko zeyi ma zai fada mata kafin yayi, bata koma gida ba taci gaba da duba shi duk inda taje sai tayi musu kwatancan sa ko sun gansa amma babu Wanda yace ya gansa, hankalinta ba karamun tashi ya karayi ba ganin har karfe Tara da yan mintuna ba taheer ba alamunsa, sosai ta bazama nemansa har tayi nisa sosai da gida, kuka oumma kawai take fatanta Allah ya tsare mata d’anta, tunanin ko ya koma gida yana nemanta shima yasata juyowa daniyar komawa gida, Daidai zata tsallaka titi wata had’ad’d’iyar  bakar prado tai bal da ita, birki me Motar yaja cikin sauri tare da fitowa, shima na bayan motar be jira an bude masa ba ya bude da kansa cikin takun dattako ya karaso wajan, ganin yadda take zubar da Jini ga bakowa a wajan yasa ya kalli babban dansa dake gefensa, “khaleed kamata a sata a mota”,ba bata lokaci kuwa khaleed din da aka kira ya sata a mota ganin Jinin har yanxu be tsayaba yasa ba bata lokaci suka tada motar tare da barin Wajan batare da sun damu da sanin daga ina take ba, a Tunaninsa in ta samu lapiya sai tayi musu kwatance su dawo da ita.

    **ganin har karfe goma ta wuce ba taheer ba oumma yasa dije kara sakin wata dariyar mugun ta , bintalo ma dake zaginta ganin har lokacin nan basu dawoba yasa ta dena zagin nata sai faman washe hakwara suke burin su ya cika , a yan gidan kuwa babu Wanda ya damu da dawowarsu balantana suyi tunanin ko wani abune ya samesu , hajiya kaka tabawa kuwa tun safe tana daki sabida cikon kafarta da ya sata a gaba , duk abun nan da yake faruwa batasani ba , babu Wanda yayi tunanin sanar da ita, a ganinsu in oumma ta dawo daga barikinta sai tayi musu bayani..

    🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧

    Tun da ta tashi daga bacci taji zuciyarta na faman tsinkewa ,burinta  yau taji muryar su oumma dan sosai tayi kewarsu, kafarta da ta kara kumbura ta kalla kafun ta mike a hankali dakyar take taku har ta karasa ban daki, ta dau dogon lokaci a cikin bayin sabida ciwonta kafun ta fito daure da towel , komai cikin karfin hali take yinsa , pant din ta kawai ta saka tare da doguwar Riga batare da tasa bra a ciki ba,kadan ta shafa turarenta tare da komawa kan gadon, sosai kafarta ta kara kunbura dan basosai take takataba, kwankwasa kofar da akai ne yasata dago da fuskarta, ammi ce ta shigo dakin bayanta kuma  asabe ce dauke da babban tray a hannunta, ya jiki tayi mata tare da ajje mata tray din abincin, cikin tausayawa ammi ta kalleta, “sannu daughter, ko asibiti zamu tafi ne” saurin girgiza mata kai tahee tayi, “ah ah ammi ba sai munje asibiti ba zai warke ai”, sosai ammi ta kalleta “Anya kuwa daughter kalli yadda kafarki ya kunbura, gaskiya asibiti zamu tafi “ta karasa tare mikewa , saurin kamo hannunta tahee tayi kwalla harta soma taran mata” Allah aunty da gaske nake miki ya dena , saura kadan kuma shima ba sai munje asibiti ba”, ta karasa kwallar na sakko mata, girgiza kai ammi tayi daman Tasan halinta da mugun tsoran asibiti, shiyasa bata kuma cewa komai ba ta gyada mata kanta”shikenan ga abincin kinan Kici kafin na kawo miki magani”, katuwar ajiyar zuciya tahee ta sauke tare da sakin mata guntun murmushi “insha Allahu aunty”, bata kuma ce mata komai ba ta kama hanya tare da barin dakin, ganin ta fita ne yasata mikewa a hankali tare da dakko abincin da aka kawo mata , sosai taci abinda sabida yunwar da takeji, ta dade zaune a Wajan har ta fidda ran shigowar ammi sai taji an bude kofar dakin, ammin ce kuwa ta shigo,har ta bude baki da niyar yin magana ya shigo dakin fuskarsa a hade taka ina kamshin turarasan yacika wajan,saurin sunkuyar da kanta kasa tayi tana hadiye abunda ya tarar mata a makoshi, lokaci d’aya taji wasu hawaye na tarar mata, kallansa ammi tayi “son duba mata kafar naga har yanxu kunburun be sace ba”, be motsa daga jinginar dayayi ba har yanxu , har ammi ta bude baki da niyar sake magana ya bude lumsassun idanuwansa tare da zubasu a kanta a hankali ya soma tafiya kafun ya karaso gaban gadon, bin kunburarriyar kafar yayi da kallo ganin tafi kunbura fiye da jiya kafun ya dauke idanuwansa ya maida kan ammi,a fiske ya furta “man zafi” cikin sauri ammi ta karasa gaban mirror din tare da miko masa man da ya tanbaya, TAHEE sai faman zare ido take, akan kujerar dake gefen gadon ya zauna, hannun doguwar rigarsa ya fara nannad’ewa tare da tsuke fuskarsa, ganin hakan yasa ta fara sakin kuka kasa kasa,a hankali ya daura hannunsa kan kafar tasa, Baisan lokacin da yayi saurin daukewa ba sabida shock din da yaji , kusan sakanni ya dauka kafun ya mayar da hannun nasa kan farar kafarta da yayi jajur Sabida kunbura,kuka tahee ta saka jin azabar da taji be kulataba sai ma rike kafar da yayi gam yana kara hade fuskar tasa, ganin yadda tahee take kukane yasa ammi saurin barin dakin dan tasan in tazauna zata iya hanashi matsa kafar bayan ita ta kirashi da kanta. Tsurawa kafar ido yayi kafun yasaki iska kadan ta bakinsa, a hankali ya soma matsa wajan da ya kunbura cikin kwarewa, kara tahee ta saki tare da kankame hannunsa, kafarta take san kwacewa amma ta kasa sabida yadda ya rike kafartata, wani kukan ta kara saki gabaki daya tafita daga hayyacinsa, be kulata ba sai ma kara matsa kafar da yayi yana shafa mata maganin, Daidai inda yafi kumbura ya dora hannunsa , wata karar tahee ta saki da iya Karfiinta na karshe ta ture hannunsa da ya kara fama ciwon, a maimakon ya saki hannun sai kujerar da yake zaune tayi baya yayinda tahee ta fado ta gaba, gaba d’ayansu suka fadi kasan, shi yana kasa ita kuma ta fado kansa, saurin rintse idanuwansa yayi tare da fusgar nunfashin dake kokarin kwace masa, kara lumshe idanuwansa yayi lokaci d’aya kuma ya ware idanuwansa jin saukar lips dinta akan nasa tare da saukar tsayayyun breast dinta a jikin sa adaidai lokacin da ake turo kofar dakin ………
    (Tofaa 😂)…..

    Comment and share…..
    07041879581….
    MSS LEE 💖.
    ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

    💖💖GIDAN AUNTY💖💖
    ( a heart touching love story)

    Story & written
    By
    Mss Lee 💖

    PAID BOOK
    Littafin gidan aunty na kudine akan 300 kacal ,Sauran few pages na gama free pages dina , me bukatar ya karanta har karshe zai turo kudinsa ta wannan asusun 7041879581 palmpay Ayshatou galadima,sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581. Nagode …

  • Gidan Aunty Book 1 Page 13

    Gidan Aunty Book 1 Page 13

    Book 1 💖

    Free page 13🦋

    Sosai ta rintse idanuwanta , tsawan yan sakanni jin bata fadi kasa ba kamar yadda tayi tunani, hakan ya bata damar  fara bude idanuwanta a hankali cikin fargaba, akan fuskarsa dake hade sosai idanuwanta suka sauka , ta manta a yadda take sabida shagala da tayi da kallan kyawun fuskarsa, tsawar daya daka mata  a lokaci daya da sakin gefen rigarta ne ya firgitata,  ga kafarta dake mata zugi kadan kadan adalilin sakin ta da yayi ta fadi, a hankali ta saki wata yar karamar kara tana rike kafartata “are you mad” taji kausashshiyar muryarsa cikin dodan kunnanta, girgiza masa kai tashiga yi , sosai ta tsorata da yanayinsa ko kallansa ta kasa,ba karamin baci ransa yayi ba ganin yadda ta basa amsa “are you mute” takarajin saukar muryarsa, nan ma kai tashiga kokarin girgiza masa,wata gigitacciyar tsawar data sata mikewa ya daka mata , bata san lokacin da ta fara “kayi hakuri dan Allah “, ta karasa a hankali tana sun kuyar da kanta kasa , dan siririn tsakin da ko ita bata jisa ba yasaki tare da komawa inda ya tashi ,”clean this mess, and bring my coffee”, ya fada a takaice har ynxu fuskarsa ba a kanta yake ba, da sauri ta jinjina masa kai sai kuma tayi saurin bude baki “toh” tana gama fada ta koma kitchen, cikin kankanin lokaci ta gama hada coffee din da sai faman kamshi yake , cikin wani dan cup me shegen kyau , a hankali tayi sallama cikin rawar murya, kamar ba zai amsa ba kuma sai ya bude bakinsa a hankali”Wa’alaykumussalm “, ko ita da ke shigowa falan bana tunanin taji , cikin rawar hannu ta karasa inda yake , duk kamshin turaran sa ya cika mata kunne , so take kawai taga ta kebance, kusan mintuna daya bece komai va kuma be amsa coffee dinva, saida ta gaji dan kanta kafun tace “gashi”kamar me kokarin sakin kuka , nan din ba bai amsa ba saida ya mula dan kansa sannan ya saka fararan hannunsa ya dauka a hankali, wani sanyayyar ajiyar zuciya tahee ta sauke ganin ya karba , sai ta koma kitchen ta dakko abunda zata gyara inda ta bata , a hankali take yin komai duk da yadda zuciya da jikinta ke rawa,cikin kankanin lokaci ta gama gyara  komai ta mayar kitchen . Tana shiga bata tarar da asabe ba aciki, tunani ta fara ta tafi daki ko tajira ya tafi, dan harga Allah shakkar fita take, ta dau kusan mintuna ashirin a kitchen ganin lokaci yaja atunaninta ya tafi zuwa yanxu, Daidai ta kai tsakiya falon sabida yadda tasawa ranta ya tafi sai jin muryarsa kawai tayi a fiske “coffee” daga nan be kara cewa komai ba.”Innalillahi “ shine abunda tahee ta fada cikin zuciyarta kafun a hankali ta nufi kitchen kamar wata muna fuka , wani coffee din Ta hado masa, yanxu cikin rawar murya ta bashi, kamar dazu sai da ya gaji dan kansa sannan ya karba, ta juya da niyar komawa ta kara jin saukar muryarsa “wait”,ji tai kamar ta fasa ihu a wajan, gashi tana tsoran ta tsugunna kartaje tai wani laifin , tsawan mintuna goma tana tsaye bece da ita komai ba ,cikin dan guntun tunanin da ta fada ta kara jin saukar muryarsa “coffee”, kukane kawai tahee bata saka ba a haka ta koma ta kara hada wani coffee din ta na kawo masa bata jira cewarsa ba ta arta a guje sai cikin dakinta. A hankali ya dago da kyawawan idanuwansa “ is she mad “ ya tanbayi kansa sai kuma ya tabe baki tare da jan siririn tsaki a haka yaci gaba da sipping coffee dinshi a hankali,kusan 11 na dare yana falon kafun ya nufi nashi part din.

    A Daidai gaban dressing mirror din dakin ta tsaya sai faman haki take, ita kadai ta san karfin halin da tayi kafun ta rugo a guje , sosai zuciyarta take harbawa ga wani irin kasala da take ji, “amma kyakkyawa ne”ta fada a ranta sai kuma ta ja dan tsaki, tare da hade rai “coffee”,”coffee”,coffee”,ko wanne shi oho, bata gama tunaninta ba fuskarta ta hango mata yadda fuskarsa yake a hade, yawun bakinta ta hadiye”nide nashiga uku” sai kuma ta tsaya kamar me tunani “wata kila bakone shima , naga bayajin Hausa gashi dan balarabe dashi”da wannan tunanin ta kwantar da hankalinta, watsa ruwa tayi tare da kwantawa, lokaci zuwa lokaci tunanin mutumin na fado mata a rai musamman yadda dan karamin bakinsa ke cewa “coffee”.

    *******
    WASHE GARI
    Tahee na zaune kan lallausan medium carfet din dakin tana karanta azkar din ta aka kwankwasa kofa , bada izinin shiga tayi, a hankali asabe ta turo kofar bakinta Dauke da sallama sai faman kawar da Kai take gefe , TAHEE na kula da yanayin ta amma batace mata komai tunda itama Allah ya tseratar da ita .gaishe da asabe tayi, duk sai asabe ta tsargu ta kasa cewa komai har tazo fita sai ta Waiwayo kanta a kasa,”uhm dama hajiya ce tace idan kin kammala cin abincin ki same ta a falo”, toh kawai tahee tace mata kafun asabe ta bar dakin. Tana kammala cin abincin da aka kawo mata kamar yadda ammi ta umarcetan falo ta nufa, anan ta tarar da ammi na kallo a tv, ammi na ganin ta tamike “Yawwa daman ke nake jira , nasan kowa yana falan dada”, da karfi zuciyar tahee ta buga ,  tuno fuskarsa da tayi “nashiga uku , yanxu ya zanyi idan naganshi acan”, ammi ce ta katse Mata tunanin da ta fara ,”muje ko”murmushin yake tahee ta saki har ynxu zuciyarta bata dena bugawa ba ,a haka suka nufi part din dada kasancewar hijabi ne a jikinta.

    Zazzaune suke a falon dada , sai faman hiransu suke gwanin burgewa , shigowar su ammi ne yasa ko wannansu maida hankali kan har yar shigowa, amrah na ganin tahee take a wajan wani tsanarta ya darsu a ranta, ji take da za ta kashe mutum babu wannan da zata kashe face wannan maiyar. Cikin sanyin jiki ta gaishe da kowa na falon , ganin irin kallan da kowannansu ke binta dashi, sabanin ummey da abeey da fuskarsu ne dauke da murmushi, sai kuma dada dake faman washe hakwaranta. “Zonan kizauna kusa dani”cewar dada , a hankali tahee ta koma kusa da ita , nuna abeey dada tayi “kinga wannan , toh shine babban dana , kuma shine baban yaran gidan, daga yanxu Kema zaki dinga kiransa da abeey kamar sauran”, sai musaddiq da uncle Saleem da ta nuna, “ wannan kuma Itace babbar maman ku, ana kiranta da ummey, ga kuma matan kawunki musaddiq , ana kiran wannan ta farko mamy sai kuma momy gatanan, sai kuma ta karshen su da ake kira da aunty , ita matar kawunci salim ce, ga yan matan gidan kuma ,duk da nasan zuwanki zaki iya saninsu tunda kullum suna wajan maman yara, bayansu akwai babbar yayarsu dake aure a saudiya sunanta samareena (samreen😂) ana ce mata ukuti( ukhti)zaki ganta wataran,akwai maza guda biyu suna karatu a turai, sai sadauki” tana ambatar kalmar sadauki gaban tahee ya fadi , jitai dada na cewa “ zaki ganshi shima wata ran amma kiyi taka tsantsan , ah too in fada miki gaskiya, ga autar gidan kuma can” ta nuna zoya dake kwance kan cinyar ammi tana bacci,kadan tahee ta dago ta kalleta “amma kyakkyawace sosai “ ta fada a zuciyarta”Nima akwai yar autata da ban fada miki ba sunanta “zarmeen sai danta kwallin kwal wato mijina sha’aban “.kallan abeey da ummeey tayi “nasan ku ai duk kunsan da zuwan ta ko” eh dada duk suka bata amsa , har yanxu da Sauran guntun murmushi akan kumatun ummey,” toh sunan ta tahura” yalwataccen murmushi abeey ya saki “taheera dai ko dada”, gyada masa kai dada tayi “ au kai da kasan da sunan ma amma sai ka wahalar dani”, wani murmushi abeey ya kara saki batare da ya ce komai ba , kallan ta hajiya ameena tayi cikin sakin fuska” gata kuwa kyakkyawa da ita kamar ka sace”, sosai ran amrah ya baci da Jin kalaman auntyn tata, ranta ya baci sosai da irin yadda kowa ke karbarta, “Shegiya in ma asiri kikai musu nice zan karyashi “ ta karasa tare da binta da kallan tsana bata re da kowa ya lura da ita ba .

    *********
    **************
    Zaune take kan daya daga cikin daddiyar kujerar falon mahaifiyarta, tunda suka dawo daga falon dada take zaune a wajan hannun ta dauke da juice yayin da Dayan hannun nata ke dauke da wayarta sai faman latsawa take , sam hankalinta na kan abunda take a wayarta, jin taku a falon yasa ta saurin fita daga abunda take tare da sassaita nutsuwarta, hajiya hauwace ta shigo falan, tun zuwansu falon dada sai yanxu ne take dawo wa , cikin izza take taku har ta karaso kan daya daga cikin kujerun dake fuskanta sumayya. Murmushi sumayya ta saki, mamy daman ke ce , “nice mana akwai Wanda kike jiran zuwan sane “, tabe baki sumayya tayi ,”toh mamy daga tanbaya, tun dazu nake jiranki fa , amma daga zuwanki kina so ki bata mun fai “, washe baki hajiya hauwa tayi “Haba summy ta ne yayi zafi kinsa Nima wasa nake miki”, jinjina kai sumayya tayi” mamy baki kula da yar iskar yarinyar da aka kawo gidan nan ba , ki duba ki gani fa yanda kowa ke kaffa kaffa da ita ko mu da muke jininsu ba ai mana wannan abun ma , musamman dada  da ke faman nanike mata, wallahi in bamuyi wasa ba sai dai mu zama yan kallo a gidan nan , se abunda yar iskar yarinyarcan ta fada sannan za’ai , kina kallanta kinsan ba haka taxo ba , akwia wata kullalliya a kasa , ni tsorona kartaje ta asircemun king, sabida kinga yawanci king acan yake wuni kuma mu ba mu isa shigaba in yana nan, gaskiya mamy ya kamata ki dauki matakin gaggawa, bazan taba bari cikar burina ya tafi a banza ba , inaso nayi suna, inasan duniya ta san da za mana , inasan mallakar king ko ta halin yayane mamy”kin Hana na nuna alamun ina san sa a fili har waccan banzar take tunanin auransa, dole mamy na mallakesa sannan dukiyar gidan nan mu ya kamata muji dadin ta ba wasu ba”, ta karashe maganar tare da kurawa mahaifiyar tata idanu, sauke nunfashi hajiya hauwau tayi kafun ta soma magana “tabbas Kinyi gaskiya Nima na dade ina halkanta da hakan , a sannu zanyi maganin kowa dan bazan taba bari dukiyar da na kwallafawa Raina zubucewa ba , aure kuwa kamar anyi shine “. Sallamar ihsan ce ta katse musu zancensu , bin ko wannensu tayi da kallo tare da girgiza kai, tasan halinsu Sarai , fatan ta Allah ya shirya mata su, ganin yadda take bunsu da kallo ne yasa mamy mikewa tare da hararar ta sama sama ,bata jira cewar ihsan din ba tai wuce warts daki, itama sumayyan tashi tayi tare da nufar nata dakin,ganin duk sun watse ne yasata kiran number wayar da tayi saving da my yaya, bugu biyu ya dauka..

    🫧🫧🫧🫧🫧🫧
    Tunda ta dawo daga part din dada take safa da marwa , ita kadai tasan radadin bakin cikin da takeji, ta tsani yarinyar tsana mafi muni, ko ita lokacin da tazo ba a nuna mata kauna haka ba kamar yadda aka nuna wa waccan , “tabbas sai na lahantaki, lahanin da ko kyawun da akace kina dashi ze gushe, da kanki zaki bar gidan nan”, duk wannan zan tuttukan ita kadai amrah take yinxu kamar wata zautacciya, tunani ta fara me zatayi mata da zai kunsasa mata , ta dade tana tsaye a falon kafun ta saki wani shu’umin murmushi, kitchen Dinsu ta nufa, ba a dau dogon lokaci ba ta fito sai faman sakin murmushi take , direct part din ammi ta nufa dan tasan har yanxu su ammi Suna part din dada, ilaikuwa tana shiga bata tarar da kowa ba sai kamshin turare da sanyin  Ac dake tashi, jin motsi a kitchen yasa ta kara sakin wani shi’umin murmushin, ta dau kusan mintuna biyu tsaye a wajan, jin alamun taku kamar za a fito daga kitchen din yasata zuba mangyadan da debo a kan  hanyar da ta san dole koma wanene ta nan zai wuce . Taheee ce ta fito daga kitchen din hannunta dauke da bottle water tana sha dan ishirwane ya kaita kitchen din, bata san da mutum a falon ba , sai ji tayi an tura ta da karfin gaske, kafarta ta sulleba a cikin man da amrah ta zube, sosai ta saki gigitacciyar kara tare da tafiya Gadan gadan zata fada , ta rotan da taji anyi , a lokaci daya da gigitacciyar marukan da aka suke akan fuskar wanda bata sani ba ya kara girgitata, lokaci d’aya nunfashin ta ya dauke alamun ta suma .

    Share ✍️

    Littafin gidan aunty na kudine , akan 300 kacal , da zaran na gama free pages dina Wanda suka biya ne kawai zasu dinga samun update , mai don gidan aunty zai iya biyan kudin ta wannan account din 7041879581 opay, Ayshatou galadima sai a turo sheda ta wannan number 07041879581.

    💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖
    ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

    💖💖GIDAN AUNTY💖💖
    (a heart touching love story)

    Story &written
    By
    Mss Lee💖

    💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

    PAID BOOK

    Nakusa kammala free pages dina,littafina na kudine akan 300 kacal,
    VIP 500,
    special 1000
    mai bukatar cigaba da karantawa zai biya 300 ta wannan account din 7041879581 OPAY, AYSHATOU GALADIMA, sai a turo shaidar biya ta wnn number 07041879581.

    Wanda suke da bukatar a tallata musu kasuwancin su kuma zasu iya yimun magana ta wannan number 07041879581

  • Gidan Aunty Book 1 Page 6

    Gidan Aunty Book 1 Page 6

    BOOK 1📕

    FREE PAGE 6

    Yau ma da asuba suka tashi, bayan sun idar da sallah aikin gidan suka fara , TAHEER da TAHEERA suka debo ruwa kafin suyi wanke wanke, yau ko buga kofarsu da aka saba yi ba ayi ba, gidan tsit kamar ba kowa a ciki, suna kammala aikin nasu daki suka koma, wata tsohuwar 200 oumma ta  basu “nasan kunajin yunwa, kuje Wajan abu me kosai kuce ta baku kosai”, Godiya sukai mata tare da nufar kofar da zata sadasu da waje , a hanya suka hadu da Dije zata shiga ban daki , tana ganin su tai saurin shigewa bayi tana tsine musu, basu bi ta kansu ba dan yunwa suke ji . Basu dadeba suka dawo, ganin oumma na karatun azkhar dinta yasa basu kuma cewa komai ba har saida ta kammala . Kosan tahee ta Mika mata tare da dakko musu wani plate din robber , juye kosan sukai a ciki tare da faracin abinsu, bayan sun kammala ruwa suka sha tare da yin hamdala, sai lokacin suka fara yar hirarsu, musamman taheer da taheera , oumma na sa baki lokaci zuwa lokaci. “Oumma” cewar tahee, amsa mata oumma tayi da “uhm” ko muma kosannan zamu kwadayi ko za a siya,Jim kadan oumma tayi kamar ne tunani abinda zatace sai kuma ta kalli tahee” banki ta taki ba auta, amma kinsani ko mun fara ba barinmu zasuyi muyi ba, kinmanta abunda ya faru kwanaki”, turo baki tahee tayi jin oumma tace mata auta” wai TAHEER ne fa auta amma kullum ni kike cewa auta”, kallan up and done TAHEER yayi mata “shikenan zo mu kwada tsaho , duk Wanda ya fi tsaho a cikin mu shine babba”, dariya duk suka saki dan sun sa da biyu ya fada mata wato dan ya fita tsaho. Daga waje suna jin yadda yan gidan ke musu habaici da zagin su musamman Dije da yarta.

    Da azahar ma haka suka sha kwaki da gyada cikin raha da kaunar junansu, bayan sallar isha’ine suka roki oumma zuwa dan dali, sai da oumma ta ja musu kunne sosai sannan ta barsu sukaje. Suna tafiya suna hirarsu Daidai sunxo shiga dandali tahee taji abu ya soketa, wajan ta taba Daidai inda shatin maciji ya fito a ciki dan kadan, TAHEER ne ya ankara da zanan macijin yayi sauri ya sa hannunsa a wajan, kamar kiftawar ido shatin ya bace bat. Hararar ta TAHEER yayi “me yasa ba kya kula , yanxu da wani ne yaga tanbarin macijin nan bani ba me kike tunani”, girgiza masa kai tahee tayi “bansan ya Akai ya fito ba sabida naji kamar wani abu ya tsirenii a wajan, ina tunanin akwia abunda yake faruwa a masarauta, dole muje mugani “daidai taheer ya bude baki da niyar yin magana yaji an bangajesu tahee har da faduwa kasa, kashi tayi a fusace da niyar bin bayansu amma TAHEER yayi azaman rike hannunta,” kasake ni, Raina ya baci”, kin sakinta taheer yayi sai ma wani abu me kama da na fito da ya dakko ya fara busawa , cikin kankanin lokaci tahee ta fara sauke  ajiyar zuciya. “ ki dinga sassaita fushinki , banaso ranki yana baci , anjima zamuje daula”, gyada masa kai tahee tayi suka nufi wajan dandalin. Suna shiga aka fara gulmarsu ana zaginsu , iya kuluwa tahee ta kulu ganin yadda ake nunasu ana dariya, saurin damke mata hannu TAHEER yayi tare da girgiza mata kai suka kama hanyar komawa, jin muryar bintalo sukayi tana fadin “yanxu ma haka ana tunanin ba kawun mune ubansu ba , shiyasa ma ake nuna musu hantara ,kun manta uwarsu ba yar kasar nan bace kowa dai yasan halin buzaye da bun malamai “, saurin fusge hannunta tahee tayi, da nufar inda bintalo take , saukar marin da bintalo taji a fuskar tane yasa ta wuntsulo wa , tahee bata kyaletaba, ta kara tsinka mata wani marin, duk Wanda yayi kokarin binta sai tahee ta tsinka masa mari, taheer nagefe yana kallansu , sai faman sakin murmushin Mugunta yake, ganin tahee ta shako wuyan buntalo ne yasa shi nufar inda suke , yana zuwa da niyar rabasu shima ya samu nashi rabon dukan, kwata kwata tahee idanuwanta sun kulle, kara nufar su taheer yayi da niyar rabasu yanxun ma wani raban dukan ya samu, Daidai wajan kafadun ta ya samu ya daka da karfi, ko motsi bata karaba ta zube a kasa , bintalo ma sai faman zare ido take dan ba karamun shaka tahee tayi mata ba, duk kawayen ta da suka labe suka fito sai faman zugata suke akan abunda tahee tayi mata, ba Wanda ta kula a cikinsu sai kwallar bakin ciki da take, hanyar gida ta nufa kawayenta na taka mata baya , shima TAHEER kama tahee yayi suka nufi hanyar gidan.

    A soron gidan suka samu mutane shake a wajan, ga bintalo a gefe sai faman kuka take , kowa maida kallansa yayi kan su taheer dake shigowa, “muna fukan Allah har kun dawo,kenan toh wallahi bazata sabuba me yata tayimuku da zakuyi mata irin wannan bugun, ita uwar taku da yake tasan me kukai shiyasa ta makale a daki taki fitowa “cewar dije, kallanta TAHEER yayi kamar ma besan me ya faruba “aunty dije lapiya, ko Ance miki wani abune”, duk zuba masa ido suke bintalo kuwa tun bayan shigowarsu taji kamar abu ya shigar mata ido.hararar sa wata daga cikin kawayan Dije tayi” karya za ai maka kenan “, kallan ta TAHEER yayi sosai “ni bansan akan abinda kuke magana ba , in kuma akwai wani abun ai sai ta fada muji “,kallan bintalo dije tayi” maimaita abunda yayi miki ai ba karfin mu suka fi ba, ina daga  masu kafane”,narnar bintalo tayi”inna daman ba abunda sukai mun, nice bansani ba na bangajesu suka fadi”, salati mutanan gidan suka fara , yayin da kawayen dijen suka fara binsu da kallo. Wani dan iskan murmushi TAHEER ya saki tare da nufar dakinsu da tahee duk wannan abun da ke faru oumma na daki na bacci batasan me ke faruwa va.

    ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
    Cikin wani hadaddan company motocinnan suka tsaya, daga saman company din ansa A_N_business enterprise’s, yanda aka rubuta sunan company din shi kansa abun kallo ne , komai na cikin company din da glass akayishi amma baka ganin komai da ke ciki saida su mutanan ciki su ganka. A Daidai wani parking space motocin sukai parking, zaki ne ya bode masa kofa, har yanxu lumshash shun idanuwansa a kulle suke, sai yanxu ne ya bude su a hankali, kafafuwansa ya fara zurowa kafun ya fito daga cikin motar gabaki d’aya,tunda ya shiga company’n ma’aikata ke ta faman miko gaisuwa,da hannu kawai ya ke amsawa bata re da yace komai ba Wanda sun Riga da sun saba da yanayin amsa gaisuwar sa . Daga inda zai hau lifter duk sauran bodyguard din suka tsaya ,shida zaki ne kawai a lifter din , Kai tsaye floor 4 dake last floor suka nufa,baka jin ko wace irin hayaniya a wajan komai tsit kakeji sai kamshin da sanyin ac dake tashi ta ko ina. Wata kofa zaki ya bude masa daga samanta an rubuta C.E.O TAHNOON cikin wani stylish way , ha daddan office ne ya bayyana me shegen kyau da tsaruwa iya kyau office din ya hadu kamar ba a shigarsa amma ko ina tsaf tsaf yake , daga cikin office din akwai wasu dan ubansu set din kujeru masu shegen kyau daga kan table din akwia wani dan karamin hotan samari su biyu masu dauke da harafin M&T,a kan daya daga cikin set din kujerun ya zauna, wasu briefcase zaki ya miko masa, be amsa ba illa “seat “ kawai daya ce cikin cool voice dinsa, cikin girmamawa zaki ya amsa da “ thank you boss” kafun ya samu waje ya zauna,rikitattun idanuwansa ya Dora kan zaki kafun a hankali ya furta “explain”. Gyara zaman shi sosai zaki yayi tare da soma bayani” boss duk wata sai an furar da makudan kudi daga a susun bankin company dinnan, batare da cikakken dalili ko sa hannu ba ,a cikin shekarar nan an rasa makudan kudade masu yawan gaske tacikin wani asusun banki da haryanxu ba a ganoshi ba”.sannan ya cigaba da yi Mishi bayanin abubuwan da ya shafi company din, kamar ba sai amsa ba tsahon munyi biyu kafin ya bude bakinsa” ina bukatar bayani game da futar kudinnan, sannan ta Wana bank ake fitar dasu”, jinjina masa kai zaki yayi “okay sir “ tare da nu far hanyar fita, “called zuhra” yaji saukar muryarsa, nan ma “okay “ kawai zaki yace masa. Dafe goshinsa yayi da ya fara sara masa sabida doguwar maganar da yayi, ko mintuna biyu cikakku ba ai ba akai knocking din kofar, shiru ba a amsa ba sanna ba a kara knocking ba kusan tsawan 3 minutes , kafun ya bude baki “come in”. Da Sauri aka bude kofar tare da shigowa ciki, tunda ta shigo ta zuba masa manyan ida nuwansa,be dago ba amma yaji yanda take binshi da kallo, ya tsani kallo amma duk da hakan be matsa daga inda yake ba , bata Ankara ba sai jin dakakkiyar muryarsa tayi “get out”, sosai jikin ta ya fara rawa  sam hankali da nutsuwarta ya tafi akallon irin kyawun da yayi kamar kullum kara masa kyau ake , saukar marin da taji a fuskarta ne yasa ta shiga taitayin ta cikin rawar harshe ta furta “ am sorry boss” tare da nufar hanyar fita , sai faman tsine wa zuciyarta take akan gaggawanta dan ko zatai yawo tsirara king natane ( uhmm😟).ranshi ba karamun baci yayi ba amma a zahiri bazaka taba tantance Wana yanayi yake cigaba , system din gabansa ya dauka , ya dade yana anfani da ita ka fun ya ajje ta ya lumshe ido.

    Wutace keci sosai ta ko ina , da anyi kokarin kasheta karfin ta zai kara yawa, sosai wutar keci da wuta ga wasu bakin abubuwa dake yawa a wajan , gigitacciyar karar da aka sakine ya farkar Dashi daga baccin da ya fara . Launin idanuwansa harsun fara canzawa daga fari zuwa ja,gaba daya jijiyoyin wuyansa sun mike wata irin zufa ya fara , hannunsa na dama ya daga wani siririn diamond din  abun hannune ya fito me dauke da harafin M&T, gaba daya zuciyarsa ba dadi, bazai taba mantawa da bakar ranar nan ba. Zaki ne yashigo office din ganin halin da king yake ciki ba karamun shiga tashin hankali yayi ba, wata drawer yayi saurin nufa cikin gaggawa ya dakko wata allura, da kyar ya samu yayi wa king a wuyansa,kafun a hankali nunfashin sa ya fara dawowa daidai, launin idan sa da ya kada ya fara dawowa Daidai.

    5:30 sukabar company kai tsaye wani part yashiga acikin part dinsa, komai nacikin part din royals ne tunda ga kan kujerun falon da ya gaji da tsaruwa , be bata lokacin ba Kai tsaye bedroom din falon ya shin shima sosia dakin ya dahu iya haduwa.

    Ya dau kusan 10 minutes cikin toilet kafun ya fito sanye da white bathrobe kall dashi,jikakkiyar gashin kansa sai faman tsiyayar ruwa take. Wata kofa dake gefan Hagu ya shiga , ya dade a ciki kafin kamshin turaran sa ya kara de ko ina, a hankali yake fitowa daga cikin dakin , shigarsa ba karamin kyau tayi masa ba , yayi kyau sosai har ynxu fuskarsa a daure take .

    Masallaci suka dufa shi da zaki bayn an idarne suka dawo gida kai tsaye part din ammi ya nufa, ba kowa a part din,sai yalwataccen Hasken da ya cika falon, bin ko ina na falan yayi da rikitaccen idanuwansa, ringing din da wayarsa keyi ne ya katse masa, be dauki wayar ba har sai da  ta kusa tsinkewa ,daga cikin wayar bata bari yace komai ba tace “part din granny now” , tana gama fadar hakan ta kashe wayanta.

    *******
    Zazzaune ko wannansu yake a falon , ko wa ka gansa cikin farin ciki da annashuwa, daga gefe daya wasu yan matane su su hudu zAune a wajan sai faman hirarsu suke , daga Dayan side din ma wasu manyan mutane ne ke tattaunawa. A hankali kamshin turaransa
    Da baya boyuwa ya kara de ko ina na cikin falon, lokaci d’aya falan ya dauki shiru kowa hanyar shigowa ya zuba wa ido, a hankali yake taka kafarsa har ya shigo falon , fuskarsa kwata kwata ba alamun murmushi sai ma kara kadeta da yayi, sosai farin kayan jikinsa ya futo da tsantsan kyawunsa,motsa bakinsa yayi ciki ciki da yin sallama, a tare falon suka amsa dan ba wai sallamar sukaji ba ta motsin bakinsa suka gane. Zoyace ya taho da gudu da niyar rungumeshi, kallan da yayi matane yasata Jan burki “ana asf akhi( am sorry brother )kwalla harta fara tarar mata, lumshe idanuwansa yayi tare da bude mata hannusa guda daya , a guje ta karasa wajan sa tare da rike hannunsa” welcome back akhi , I missed you the whole day”, lumshe mata ida nuwansa yayi tare da budewa kasa kasa ya amsa mata “ me too”, direct inda mahaifinsa yake ya nufa, zazzaune ko wannansu yake cikin takaitaccen magana ya gaishesu, kowa amsa masa yayi sai faman binsa da kallo suke , abeey sai faman sakin murmushi yake . Hajiya Amina ( uwar gidan uncle musaddiq) wacce ake kira da mamy ce ta soma magana “ Kai dai king kayi wuyar gani, ba a ganinka Indai ba a part din dada ba ko na ammonia”, matar uncle Saleem ce ta Dora “ Aushe duk kanwar jace “. Murmushi ammi ta sakar musu “ Kude kawai kun fada ne”, mikewa king yayi tare da nufar wani sofa dake can gefe dasu, kallan dada zoya tayi, cikin tsokana ta kira sunan ta”dada”, harara dada ta wata a mata “kinibabbiya ba kiran Allah da annabi kikai mun ba, tunda kinga ubanki ai dole kikashen murya”,langwabar da Kai zoya tayi “Haba my dada nasan akhi na beci abinci ba , he need some coffee before eating”, tsaki dada taja “ ke kika sani kuma inma zagina kikai ba na hanaki yimun magana cikin yaran nasara ba, wani wai kamfin ( coffee)ke kika sanshi”,kowa na falon yadda dada ta kira coffee din sai da yaso basu dariya amma ba damar yi harta king maganar taso bashi dariya amma sai wani hade rai da ya kara.kallan akhi dake gefe zoya tayi, saurin daga mata hannu yayi alamun ba ruwansa ,maida kallan ta tayi kan ummey , itama dauke idanuwanta tayi  daga kanta,mikewa ammi tayi nida ba a sako niba bari na bada coffee din, kulle idanuwanta zoya tayi tana dariya ,daya Daga cikin yan matan ne ta mike, kallanta ummey tayi amrah ina zuwa, cikin in ina wadda aka kira da amrah ta soma magana “dama zan taya ammi ne”jinjina mata kai ummey tayi , direct kitchen din dada ta nufa , basu dade ba suka fito daga kitchen din cikin yanga amrah ta ajje masa tray din abincin, “yaya king sannu da hutawa”, kamar wacce tayi magana da dutse yana zaune ko motsawa beyi ba ballantana tasa ran amsawa, zoya na gefensa a haka ammi ta fito da cup din coffee sai faman tiriri yake dayan kuma kayan tea ne a ciki da yaki bornviter , mika wa king coffee din tayi , lumshe mata ida nuwansa yayi , murmushi ta sakar masa kafun ta mikawa zoya tea dinta.beci abincin da aka kawo masa ba sai coffee dinsa da yake sipping a hankali yana gama sha ya mike tare da ce musu “good night “yana gama fada ya kama haryan fita . Cikin daga murya zoya ta soma magana “Laylat saeidat akhi, uhibuk( good night brother, love you)”,girgiza Kai kawai king yayi da barin part din. Sai a sannan yan matan suka tare da cigaba da hirarsu, dummy ce ta kalli amrah , Lalle amrah da raban kin kusa Shan Mari a wajan yaya king, Kinsan halinsa Sarai ba a burgeshi, cikin kasa kasa ihsan tace Garin masoya baya nisa kunsan yadda take mugun sonsa,murmushi amrah ta saki jin abinda ihsan tace “dadi na dake ihsan kin fisu fahimtar abu”ni kadai nasan yadda nake sanshi kumashidin mallakinane, dariyar mugunta firdausi ta saki , cikin kasa kasa da murya tace “mugani a kasa”, hararar ta amrah tayi dan Tasan itama san king take shiyasa basa shiri sosai , duk wannan magan ganun nasu cikin kasa kasa da murya sukai ba mejinsu, dago idanuwanta amrah tayi bata saukesu akan kowa ba sai nan auntyn ta , itama auntyn Tata daga mata hannu tayi alamun jinjina, firdausi ma maida hankalin tayi kan mahaifiyarta lokaci daya suka sakar wa juna murmushi duk wannan abun da suke ba Wanda ya lura dasu .

    (Uhmmmm 🤭😟)

    💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

    Duk karfin izzata (star lady)
    Gidan aunty (mss Lee)
    Sarki sameer( xeemat love)
    Jini daya ( mss bbk)
    Ya fita zakka (maman sayyid)

    Comment and share

    ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

    💖GIDAN AUNTY💖

          ( A heart touching love story)

             By mss Lee

    💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

    PAID BOOK

    BOOK 1 📕

  • Gidan Aunty Book 1 Page 7

    Gidan Aunty Book 1 Page 7

    Free page 7 🦋

    Not edited

    Zaune Suke su biyu cikin wata katuwar masarauta me shegen kyau da daukan hankali, duk Wanda yazo wuce wa sai ya duka musu tare da gaishesu, TAHEER ne ya fito cikin wata kofa sanye da wasu kaya na alfarma masu tsananin kyau ba karamun kyau yayi a cikinsu ba , hannunsa dauke da wani siririn maciji fari tass dashi, Daidai inda tahee take ya nufa, zaune take cikin  shigar alfarma na kayan sarauta , gefe da gefe masu yi mata fiffi tane ko wananne kawunanshi akasa, tanbarin macijin dake bayanta ya fito radau dashi, murmushi ta sakar masa ganin ya karaso inda take, shima murmushin ya sakar mata tare da Mika mata kyakkyawar farin macijin, mikewa tayi sosai tare da karban macijin, a daidai kan cinyarta ta dora macijin , shima macijin lumshe idanu yayi kamar mai jin bacci, kallan taheer tayi da mamaki dauke a fuskar ta,” kyauta ne na baki yau shekara 300 daidai da haihuwarki, zai debe miki kyewa “cewar taheer, tsananin farin cikine ya bayyana a kan fuskar tahee “ oh my god , nagode SIF” , jinjina mata kai kawai yayi , har ta bude baki zata sake magana sai wasu siraran hawaye suka zubomata”ka tuna lokacin da Nonna ta bani kyautar maciji kamar haka , amma sun kashe mun shi, sun kashe mun nonna , sun kashe mun susan”, shima girgiza mata kanshi ya shiga yi”Lola Raina yana baci duk lokacin da na turo wannan bakar ranar, kamar randa suka rabamu da nonna da susan Muma baza mu kyalesu ba,ga memaw nan ki rikeshi kamar yadda kika saba da susan, shima zaki soshi sosai”, yana gama fadar haka ya bar wajan , murmushin yake ta saki tana hadiye abunda ya tsaya mata a makogaro,kallan memaw din dake kan cin yarta tayi kafun ta kira sunan shi,”memaw”, bude idanuwansa yayi masu kalar baki tare da fara yawo a jikinta yana zagayeta , hakan ba karamin nishadi yasa taba, sai faman yawo suke , saida suka gaji dan kansu sannan suka tsaya har lokacin mucijin be dena yawo a jikinta ba.TAHEE!!TAHEE!!! A firgice ta farka daga baccin da take bakin ta dauke da adduar tashi daga bacci, kallan ta oumma tayi ganin yadda ta jike da zufa duk da kasan cewar akwai dan zafi zafin da ake ,”lapiyan ki kuwa”cewar oumma , saurin girgiza mata kai tahee tayi “ mafarki kawai nayi”, shafa kanta oumma tayi “ki kwantar da hankalinki mafarki ba gaskiya bane sannan ki dunga addua “nanma gyada mata kai kawai tayi,tunda umma ta fita a dakin kuma bata motsa ba mafarkin da tai na yi mata yawo aka“ NONNA,LOLA,SIF,SUSAN,MEMAW!? Sudin su wanene!? Maciji fa !?” Macijin da ta gani a mafarkine yashiga yawo a kwakwalwarta, amma sanin cewa mafarki ba gaskiya bane yasata share zancen tare da mikewa ganin oumma na kokarin shigowa dakin.

    Bayan sallar azahar kamar yadda suka saba bayan sun kammala ayyukansu, zama sukai suna hira , lokaci zuwa lokaci tahee sai ta dako ta kalli taheer har yanxu mafarkin da tayi yana mata yawo a ka , duk lokacin da tayi tunanin mafarkin sai taji wani abu kamar ya tabata, yanxu ma dago da fuskar ta tayi tana kallan taheer, hararar ta yayi ganin tun dazu sai faman binsa da kallo take kamar wata me aljanu “na canza miki ka manni ne kike faman bina da kallo fisabilillah”,cewar taheer yana hararar ta , murmushin da yafuto da dimples dinta ta saki”gani nai ka kara kyau kamar wani balarabe “ ta karasa maganar tare da kashe masa ido daya,yanxun ma wani hararar ya mata “dadin abun bake kadai ce me kyau ba, da nice mace ma kyan da zanyi sai nasaka maza kuka”, dariya duk suka saki, oumma ta girgiza kanta “Allah ya shiryeku “.

    ➰➰➰➰➰➰
    A gajiye ya dawo gidan bayan mutane uku da yayi wa aiki a asibiti da kansa ,sai faman lumshe ido yake , amma a zahiri bazaka taba tunanin hakan ba , zaka dau ka yanayinsa ne haka , shaf shaf yayi wanka cikin armani white colour, sosai kayan sukai masa kyau , a maimakon gyara gashin da ya saba yan tajeshi kawai yayi ya zubo masa har bayansa, sosai yayi kyau a cikin shigarsa, wayoyinsa kawai ya dauka tare da nufar part din ammi, yau kwata kwata be sata a idanunsa ba amma a zahiri fuskarsa a hade take ba ko alamun yasan wani abu me kama da murmushi. Yana shiga part din ya tarar da su kowa da Riga da Wando sai faman rawa suke, amrah ce me koya musu yadda zasuyi step din rawar,kwata kwata basusan da shigowarsa ba , hatta kamshin turarensa da sukaji basu kawo komai a ransuba, dan kusan kullum da kamshin a cikin falon ammi. Folding din hannunsa yayi a kirji yana bin ko wannansu da kallo daya bayan daya ransa ba karamun baci yayi ba musamman irin shigarsu ko dan kwali babu, be tankamusu ba duk da yadda kan nasa ke Sara masa , sexy eyes dinsa dasuka fara canza kala daga launin fari zuwa ja ya zubamusu, ihsan ce ta fito sanye da hijab a jikinta hannunta dauke da cup sai faman tiriri yake, kallan su amrah tayi tare da girgiza kanta , “kunsan dai yaya king ya hana wannan raye rayen ko, Allah Inya dawo sai na fadamasa dan bazaku jajamun ba”, hararar ta summy tayi “ sannu kasa yanxun ma zaki iyazuwa, matsoraciyar banza kamar da gasken iya zuwa zakiyi”, girgiza kai firdausi tayi “Aah sumy Wana irin taje ta fada kinsan dai wallahi yaya king ya Kamamu ba karamun wuya zamusha ba musan man dressing dinmu, kuma kusan bama sawa sai in bayanan “, siririn tsaki amrah taja “matsalata da ku kun fiya tsoro wallahi, kafun ya dawo ba mun gama ba , ai baze san munyi ba , yanxu fa zamu gama step din rawar kafin ammi ta dawo”. Dukkansu yanajin abunda suke fadi , duk abunda suke yana ganinsu kwata kwata basu hankalta dashi ba, amrah ce ta kunna musu wata wakar, ta juya kenan a cikin salon rawar idanuwanta suka sauka a kanshi, sosai ta firgita , bakinta ne ya fara rawa kwata kwata ta rasa me zatace, kallanta summy tayi “ke kuma lapiya jikinki yake rawa”, girgiza mata kai kawai amrah take tama kasa magana ganin irin kallan tsanan da yake jifanta dashi “watan cin ubankune yayi”a zahiri kuwa yana yadda yake ko a fuskarsa bazaka gane yanayinsa ba duk da tsananin gajiyar dayayi. Ganin sai faman kallan waje taya amrah take jikinta na rasa yasa duk juyawa zuwa direction din,”Innalillahi wa’inna’ilaihi rajiun, shikenan mun kade har gay yan mu gashi ammi batanan “kowa da abunda yake sakawa a zuciyarsa  , iya firgita sun firgita musamman ganin yadda launin idanunsa ya koma ,firdausi har da faduwa kasa tsabar rudewa,duk zubewa sukai akan gwiwowinsu ko waccen su sai matsar kwalla take,sosai suka rude musamman ganin irin kallan da yake bin kowannansu dashi, a hankali ya taka kafarsa tare da nufar sofa din dake left side dinsu , kwallar bakin ciki ihsan ta share dan duk su suka ja mata, ta ja musu Allah ya isa ba a dadi cikin zuciyarta, ba wacce ya kalla a cikin su sai ma wayar hannunsa da yake latsawa, cikin rawar murya me san sakin kuka ihsan tahe hannayanta “wallahi yaya zanyi bayani”, be Motsa da ga yanayin da yake ba balle su sa ran ze amsa mata, Kuka Kawai ihsan ta saki tana toshe bakinta karta kuma yin wani lefin, su amrah kuwa kowa sai faman zare ido yake fatansu Allah yasa be ji abunda suke tattaunawa. Kamar daga sama sukaji saukar maganarsa “ coffee “ da Sauri amrah ta tashi duk da acikin yanayin tsoran da take, dan iskan kallan da yayi mata ne yasa ba shiri ta koma tana zare idanu, ganin hakan yasa atsorace ihsan ta mike ganin be mata magana ba yasa ta nufar kitchen din cikin sauri, sai faman ajiyar zuciya take , duk tabi ta rikice ta rasa yadda zata hada masa coffee din , cikin sauri Sauri ta dakko wayanta dake aljihun Wandanta. Yanda ake yin coffee din tayi searching, cikin rudewa ta gama fito da abunda zata hada masa coffee din jikinta sai faman rawa yake .

    Cikin dan karamin tray ta fito da coffee din kusan na uku kenan tanayi kafun tayi wannan din, ganin su amrah na frog jump ne yasa kafarta rawa idanuwanta harsun cika da kwalla, coffee din ta ajiye masa tana komarin fara frog jump din ne abazata taji saukar muryarsa “ Leave” , nannauyar ajiyar zuciya ta dauke da harshi saida yajita “ nagode yaya king, na….” Hannunsa kawai ya daga mata ,cikin sauri ta bar wajan cikin gudu gudu, tunda Allah ya kubutar da ita.

    Sosai suke frog jump ko wacce fuskarta jaga jaga da majina , ga hawayen da suke yi, da zaran sunji kuka zai kwace musu zasuyi saurin toshe bakinsu gudun wani punishment’s din. Duk fadin falon ammi haka zuke zagayeshi ko wacce ta fita daga hayyacinta ba damar yin kuka a fili.

    Yana zaune sai faman operating wayar hannunsa yake se yanxune ya dauki coffe din da aka hada masa” kurba daya yayi amsa ya ajjesa. “Yaya dan girman Allah da manzan sa kayi hakuri”firdausi ce tayi maganar hawaye sai bin fuskarta yake, lumshe gajiyayyun idanuwansa yayi, tariga ta hadasa da abunda baze iya musu akai ba, “God save you”yafada cikin zuciyarsa “Leave “, baki summy ta bude Baki da niyar yin magana amma ya dakatar dasu ta hanyar dafe kansa , sun gane me yake nufi hakan yasa a guje ko waccen su ta bar part din Daidai lokacin da ammi ke shigowa, da kallo tabisu ganin babu Wanda ya kula da ita kafun ta karasa shiga falon.

    ➰➰➰➰➰➰
    Karfe uku na dare ko ina yayi shiru kasan cewar ko wana bawa yana wutawa a irin wannan lokacin, wani macijine fari tas dashi ya fito cikin wani rani tare da kwanciya bayan tahee,cikin mafarkin da take tafara lalube lalube har hannun ta ya Kai……

    Manage plx🥹

    💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

    DUK KARFIN IZZATA (Star lady)

    GIDAN AUNTY( mss Lee)

    TAFITA ZAKKA ( maman sayyid )

    JINI DAYA ( mrs bbk )

    SARKI SAMEER (xeenat love )
    ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

    💖GIDAN AUNTY💖
    ( A heart touching love story)

    By mss Lee 💖

    💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

    PAID BOOK

  • Gidan Aunty Book 1 Page 12

    Gidan Aunty Book 1 Page 12

    BOOK 1 📕

    Free page 12 🦋

    Zuciyarta tafarfasa take babu abunda take nana tawa  sai “bazai yiwu ba , it’s impossible “ tare da mikewa , kallanta ammi tayi “ah ah amrah ina zaki”cikin dan rawar murya ta amsa mata “dama ina da lectures naga lokaci yana tafiya inaso na shirya”jinjina kai ammi tayi alamar gamsuwa “All the best daughter”, murmushin yake amrah ta sakar mata “thank you ammi”, tana gama fadar hakan ta bar part din, cikin sauri ta nufi part din auntyn ta, cikin sauri take tafiya ko kula da auntyn ta dake falon batai tai shigewa dakinta, ganin hakan yasa hajiya ameena bin bayanta , a tsaye ta tarar da ita sai faman safa da marwa take , “lapiyar ki kuwa amrah kika shigo duk a rude ko har kingansa “, jijjiga mata kai amrah tayi sai faman zagaye take , kallanta hajiya amena tayi ,” kiyi mun ba yani mana”,aunty akwai matsala “ cewar amrah “kinsan jiya ammi tayi tafiya , yanxu baki gani ba da wata yarinya ta dawo , itama wai anan zata zauna “ta be baki hajiya Amina tayi “to sai me dan ta kawo wata yar kauye”girgiza mata kai amrah tayi “ah ah aunty bazaki gane bane , kinsan sharadin da boka ya sa mana , baki ga yarinyar bane , kyakkyawace sosai , gata a cike ta ko ina kamar wata babba, koni da na ganta sai da naji sha’awata ta motsa, balantana king da yake namiji, dole yaji wani abu aka ta, banasan kwata kwata king ya ganta , Kema kinsan dalilin da yasa nake zuwa part din ammi sabida kawai acan zan iya ganinsa” bata bari hajiya Amina tayi magana ba ta dora “ aunty ya kamata kiyi wani abu,dan wallahi duk Wanda yayi kokarin rabani dashi sai nayi azalinsa, hakuri ya fara kare wa duk lokacin da na gansa sai sha’awata ta motsa”, jin maganganun amrah ba karamun jijjiga hajiya Amina yayi ba “dole na kaiwa boka ziyara dan bazan taba bari dukiya ahalin nahyan ta su bucemun ba, yanxu ki kwantar da hankalin ki karyi abunda zai sa a zargeki, dan Nima ko zanyi yawo tsirara sai dukiyar nan ta dawo waje na “tana gama fadar hakan ta har dakin, waya amrah ta dakko tare da kiran wata number, ringing 2 aka daga wayar , bata jira cewarsava ta soma magana “ Ina bukatar ka kashe mun kishirwar data tasomun, zan fada maka inda zamu hadu”, tana gama fadar haka ta kashe wayarta, sai faman lumshe ido take tana Cizan yatsa.

    *****Apart din ammi duk yan matan sun koma part Dinsu, part din dada ammi ta nufa da tahee, sai faman bin ginin gidan take da kallo musamman wani dogon building din glass da ya burgeta , da wasu irin flowers me hade da pink colour , sosai flower din sukai mata kyau, falon dada suka shiga komai yana nan kamar yadda yake sai faman tashin kamshi yake kamar ba a amfani dashi,”Assalamu alaikum”cewar su ammi, itama dadan amsa wa tayi tana gyara farin glass din idanta, zama ammi tayi kan daya daga cikin kujerun falon, tahee kuwa samun waje tayi daga kasa kan carfet ta zauna, hakan da tayi ba karamun burge dada tayi ba amma bata ce komai ba. “Sannu da hutawa dada”, murmushi dada ta saki “Yauwa maman yara, a ina kika samo wannan kyakkyawar yarinyar”, murmushi ammi ta saki,”ina wuni “cewar tahee, amsawa dada tayi taba bin tahee da kallo, nutsuwar yarinyar ya birgeta,” dada wannan Itace yarinyar da nace miki inaso ta dawo waje na, na kawo miki itane ta gaisheki”,murmushin jin dadi dada ta saki “kin kyauta kuwa, yan mata ya sunanki” dada ta fada na mayar da hankali kan tahee, sun kuyar da Kai tahee tayi sunana Taheera , zaro ido dada tayi sai kuma ta tabe baki, yaran zamani kowa dai da irin nasa sunan , shi wancan bod’ararran ansa masa tahanuni (tahnoon), ke kuma ga naki salan sunan wai tahura (taheera), sun kuyar da Kai ammi tayi jin yadda ta kira sunan su, gashi ba halin dariya , dada kuwa bilhakki da gaske take ko dariya a fuskarta, kara kallan tahee tayi,”nikin ganni nan , wallahi iyayena sunan kwarai suka samun, ina dalili ai ku sunayan ku sai ku wallahi”,itama tahee dariya dada ta bata amma sai tai saurin gimshe kayarta amma murmushin yaki buya a fuskarta.”sannan ki saki jikinki nan ma gidan kune , ko me sikeso ki tanbaya za a miki kinji tahura “,sosai murmushin da take boyewa ya fito har dan gaf din hakorin ta fitowa “nagode sosai hajiya”dada bata bari ta karasa ba ta dakatar da ita”yau naji wani batu, dada zaki dunga cemun kamar sauran”,jinjina mata kai tahee tayi “nagode dada”sosai tayi wa dada adduar da har yar kwalla saida ta share “Allah yayi miki albarka “kasa kasa tahee ta amsa “ameen”ita de ammi sai binsu take da kallo tana sakin murmushi, kallanta dada tahee maman yara , gasky wannan ‘ya a kwai hankali, nasan a gajiye kuke , idan ta huta sai a gabatar mata da kowa na cikin a halin ta san yan uwanta, cikin girmamawa ammi ta amsa mata”mun gode sosai dada, Allah ya huta gajiya”, ameen aka wai dada tace mata kafin su kama hanyar fita da ga part din, bin bayansu da kallo dada tayi kafun ta saki wani murmushi akan fuskarta .

    ************
    ILORIN
    babban waje ne katafaran gaske , me dauke da abubuwa mabanbanta a cikinsa , ba karamun makudan kudi aka kashe ba wajan gina falon, komai na cikin falon red colour ne tundaga kan carfet har zuwa kan labulayen dakin, hatta mutanan dake tsats tsaye ko wanne fuskarsa a rufe , matan sanye suke cikin jajayen kyalle iya gwiwa , yayinda mazan suka sanya dan karamun jan kyalle da ya bude al’aurarsu, magana suka fara cikin wani irin yare Mara dadin saturate, kasancewar falon babbane hakan yabasu daman Jan layi kowannansa dauke da glass cup ne Jan abu acikinsa, Yaren suka cigaba dayi , sunayi suna sunkiyar da kansu, wani hayakine ya cika falon , yayinda wata murya Mara dadin ji ta farara babbaka dariya, sannu a hankali ta koma ta jarirai, a haka karuwar muryar nan ta kuma karade ko ina da dariya , data gama sai kukan jarirai suma, an dau lokaci ana haka kafun hayakin ya dauke.
    Wata katuwar matace ta bayyana a falon , baka kirin da ita fuskarta dauke da wasu kananan kuraje ba kyan gani, durkusawa sukai baki dayansu tare da yi mata  sujjada(wa’iyazubillah), sosai suka shiga yi mata kirari”shugaba me share mana hawayen mu, kece farin cikin kowa ne halitta , kece maganin kukanmu, kamar yadda kika saba share mana hawaye “, dariya Matar nan ta fara kafun lokaci daya ta hade ranta kamar ba yanxu ta gama dariya ba, cikin kakkausan murya ta soma magana “ lokaci yayi, lokaci yayi da zaku mallaki duniya, duniya takuce , mu kuma mune abun bautawanku, saura Kiris komai yazo karshe, tabbas aikin ku ya fara zuwa gangara “, kallan daya daga cikin mutanan falon tayi, “abar kauna”shine sunan da ta kira , wacce aka kira da abin kaunace ta fito tsakiya, “tuba nake me sharemun hawaye , tuba nake shugaban dudduniya”, shafa kanta wannan bakar matar tayi , “tabbas kaso mafi yawa na aikin nan yana hannunki,dole ki tabbatar jinin da kika dade kika kiwo ya kwaranya ga dodon tsafi , muna bukatar jinin kafun nan da mako biyu”kara sun kuyar da Kai Wadda aka kira da abar kauna tayi “Godiya muke abun bautarmu tabbas babu me share mana hawaye seke”kara hade fuskarta tayi tare da bin abar Kaunar ta da mayataccen kallo,Tashi tsaye abar kauna tayi , tare da rungumar bakar matar nan, matseta sosai matar tayi ajikinta tana shinshinar wuyan ta kafun lokaci daya su bace a falon ,sun kuyar dakai ragowar mutanan falon sukayi kafun ko wannansu ya buga cinyarsa sau uku,suna gama bugawa wani bakin hayaki ya cika falon, lokaci d’aya hayakin ya dauke, sabanin dazu, yanxu ba kowa a falon.

    *************
    LAGOS

    zaune ammi take kan daya daga cikin sofa din falo, sosai taci ado cin ash din material sai faman walwali take , ga sanyanyan kamshi dake Tashi a jikinta, iya haduwa ammi ta hadu , har yanxu fuskarta dauke da murmushi akai kamar kullum, lokaci zuwa lokaci takan duba agogon wayarta , ganin 9:00 ta kusa yasa ta mike wa , hart fara taku zata bar Wanjan, daddadan kamshin turaran king ya cika falon, jiyowa tayi tana sakar masa murmushi, shima narkakkun ida nuwansa ya zuba mata yana binta da kallo, har ya karaso wajan, hannunsa guda daya yasa tare da kamo na ammi ya zaunar da ita, har lokacin be ce komai ba , kusan mintuna daya kafun ya ce mata”kinyi kyau” sosai hakwaranta ya fito waje jin abinda yace “kaima kayi kyau son , kamar Wanda ya dawo daga zance”, dan tabile bakinsa yayi tare da kawar da zancen,”coffee ammi” har ta bude baki da niyar bashi amsa wayar hannunta ta soma ringing, tana zaunan ta daga kusan mintuna biyu kafun ta kashe ,mikewa tayi tare da nufar kitchen , a tsaye ta tarar da tahee da asabe suna aiki, kallan asabe ammi tayi a hada coffee a kaiwa son , kinsan baya san jira , tana gama fadar hakan ta bar kitchen din, hannu asabe ta dora a ka “na shiga uku na lalace”sai kuma ta shafa kumatunta, tuni jikinta ya hau rawa, ita tahee dariya ma abun ya bata daga cewa takai coffee har da yar kwalla , bata ce Mata komai ba sai binta da kallo da take,girgiza kai kawai tayi atunanin tayi  coffee din ne bata iya hadawa ba shiyasa duk ta zure haka “kawo kayan na hada miki”, sosai asabe ta shiga yi mata Godiya kamar zata zugunnata mata, kayan coffee din kuwa ta dakko mata , tare da nuna mata coffee maker din, bata san yadda ake anfani dashi ba, da temakon asabe ta hada coffee din da ko a ido sai ya burgeka, neman hanya guduwa asabe , tana ganin tahee ta kammala hadawa, tace mata bari taje ta dawo, TAHEE bata gane ba sai jinjina mata kai da tayi , kusan yan mintuna ganin coffee din na kokarin jin sanyi yasa ta dauka hankali kwance tare da nufar falon, agaban idan asabe dake bayan kofa sai faman hada zufa take, da sallamarta t shigo falon, Sam ta manta coffee ne a hannunta sabida dandanan kamshin da ya cika mata hanci, kanta a kasa sai faman murmushi take, jin tana kara kusanto kamshin da takejine yasata lumshe idanuwanta,sosai yanayin falon yayi mata dadi, da bugawa kadan kadan da zuciyarta ke mata, bata ankaraba taji ta taka abu, a firgice ta bude idanuwanta, tsabar firgita bata san lokacin da kofin coffee din ya subuce mata ba ,baya baya tayi  zata fadi, sosai ta rintse idanuwanta dan ta sadakar faduwa zatai….

    Comment and share 😎
    Daga alkalamin Mss Lee 💖

    💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖

         💖DUK KARFIN IZZATA (star lady)💖

    💖GIDAN AUNTY( mss Lee )💖

           💖YA FITA ZAKKA( maman sayyid )💖

    💖JINI DAYA (mrs bbk)💖

          💖SARKI SAMEER( xeenat love )💖

    ‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA

    💖💖💖GIDAN AUNTY 💖💖💖
    ( a heart touching love story )

      Story &written
    By
    Mss Lee 💖

    💖💖THE TALENT TROUPE WRITERS 💖💖

    PAID BOOK

    Dedicated this page to masoyiya and the talent troupe writers, masoyiya I heart ❤️ you Lodi Lodi.