Author: Novels

  • Namijin Zuma 6

    Namijin Zuma 6

    Free page6
    Jin muryarta ya haifar masa dajin Wani irin sanyi me sanyaya ruwan jiki, ya sauke ajiyar zuciya 2tyms a jere ya lumshe Ido ya sake budewa kana yace. “mommy bani da lafiya wallahi…” Ya fadi a shhagwabe kmr me Shirin fashewa mata da kuka. Ya saba mata shagwaba Amma wannan Karan Se taji abun ya mata gatsal kmr bata saba ji ba. “Subhanallahi Meya sameka?” Ta fadi cikin sanyin murya sabanin farko data daga wayar. “Wani Abu nakeji mara dadih a jikina da zuciyata…” Ya fadi Yana mejin Sanyi a jikinsa kaso Dari na abinda ke damunsa ya ragu zuwa tamanin sbda muryarta kawai dayaji, shide be tabajin abinda yakeji ba a kanta kamar na yau,ada inyaji muryarta ba haka yakeji ba. “Kamar me babyna? Banason abinda ze dameka pls,, Ba munyi magana dakai ba a kan kan ka denasa damuwa a ranka Dan Allah kayi Adduarh itace maganin komi na rayuwar duniya, haba Jarumina!” Ta fadi tana mejin yanayi mara dadih a jikinta sbda ko a muryarsa ta tabbatar da Wani Abu na damunsa Amma setasha ko damuwarsa da na’eema ce. ‘ajiyar zuciya kawai Aeezad ke saukewa yana me sauraronta kawai shi kadai yasan meke damunsa, shide yasan ba dmwar na’eema bace a wannan karon kuma besan meke damunsa ba. “kaji babyna !” ta fadi jin yayi shiru sede ajiyar zuciyarsa kawai take juyowa ta cikin wayar. “Naji mommy insha Allahu zanyi Addu’ah kema kiyi min pls ….” ya fadi cikin sanyi. Nabeelah ta jinjina tabbas yasa damuwa a ransa sbda muryarsa ta nuna alamar nadama a ciki duk yayi sanyi shida bakinsa be mutuwa Amma yau murus take jinsa, ko maganar batsa babu a bakinsa. “Zanyi maka kaji na mamansa..Amma se kayimin promise zaka denasa damuwar komi a ranka Dan Allah ka dinga sanyayawa a kan komi hkri fa maganin zaman duniya ne …” ta karashe cikin muryar rarrashi da kwantar da hankali. “Thank you,,, proud of you …” “Nima ina alfahari dakai na mamanshi…Ka kwanta kayi bacci kaga time ya tafi dare yayi sosai ko baka koma kanon bane?” “No na koma…” “Okay Allah ya bada sa’ah ya tsareminkai gabas da yamma kudu da Arewa…” “Amin ya Allah mommyna…” “Seda safe ka kwanta zuwa 3 or 2 katashi kayi sallar ka gayawa ubangiji damuwarka nima zan tayaka Kai kukanka , Allah shike mgnin damuwowinmu…” Aeezad ya kara sauke ajiyar zuciya yace “Insha Allahu nagode mommyna sweet dreams..” ya karashe badan ransa naso ba, haka kawai ya tsinci kansa da rashin San ta ajiye wayar. “Nagode babyna bye…” Ba tare data jira cewarsa ba ta katse wayar,. Bayan ta katse wayar ya kasa cire wayar daga kunnensa seda wayar tayi 5mnt a kunnensa yana mejin muryarta na masa gizo, ya cire wayar daga kunnensa ya kure Screen din wayar da Ido, ya shafa creen din wayar ta kawo haske, picture dinta ne kan lock screen dinsa, tana zaune a farfajiyar hutawar gidansu, sanye take da doguwar rigar atamfa tasha daurin ture kaga tsiya yayin datai murmushi har wushiryarta ta bayyana, ba karamin kyau tayi ba, sumar goshinta ta kwanta luf-luf. Wani irin murmushi ne ya subuce masa yayin dayake kallon picture din nata kamar Yana gabanta haka yakeji a zuciya da kwanjinsa. “Kinada kyau na matsifa mommy!” Ya fadi yana me kara kureta da idanuwa, be taba sanin tanada kyaun daya wuce lissafinsa ba se yau. Bude wayarsa yayi yashiga gallery dinsa ya fara duba picture dinta da yaketa mata ba tare data sani ba, kaf wayoyinsa itace take cika masa gallery kuma duk photos din da yake mata ba tare da saninta yakeyi ba, itace a kaf lock screen and home screen na kaf wayoyinsa, sunyi fada da na’eema yafi a kirga a kan hakan tayi tayi ya cire yaki cirewa, har hajiya mommy seda na’eema ta gayama, hajiya mommy ta kira Aeezad Ta tambayesa meyasa zesa kaskantacciya a screen dinsa…” Aeezad yayi mata banza, Nan ta rufesa da bala’i da matsifa tace dole seya cire kaf pictures din nabeelah a wayoyinsa, cikin Mulki Aeezad yace ” am sorry hajiya mommy Wallahi bazan cire ba, ai kowa abinda yakeso shi yakeyi… Kuma in zaku lura ai a matsayin uwa mommy take a gurina…” Sam hajiya mommy bazata iya jaa da Aeezad ba Dan haka ta kyalesa kawai ita kanta Tsoronsa takeji wasu lokutan sometimes data gansa se taji zuciyarta na yawaita faduwa kwarjini yake mata, dole sede ta bawa na’eema hakuri a kan hakan. Dadin karawar abinda ya kara dasa musu kiyayyar Nabeelah a ransu kenan saboda ganin yadda Aeezad ya bata muhimmancin fin komi na rayuwarsa. Seda ya Kai 2:am Yana duba picture dinta haka kawai kallonta kesa masa nishadi,. Mikewa yayi ya nufa toilet ya dauro alwala ya fito ya fara jero sallolin dare Yana me Adduah Allah ya yaye masa abinda ke damunsa , danyafi tunanin boyeyyen ciwo yakeyi Wanda shi kansa besan Kona menene ba. Har seda yayi sallarh asubahi kana ya kwanta bacci ya barawo ya figesa, bashi ya tashi ba se 9:am, ya shirya ya tafi office 11:am. A office dinma yau kmr jiya se tunani tunani kawai yakeyi , ya kirata a waya yaci saah ta dauka bugu daya,, wuni sukayi suna waya, har ya bar office din, a voice dinsa nabeelah ta fara fuskantar kamar ya soma chanzawa, nutsuwar dole ta fara shigarsa.

    *Katsina state*
    Zaune suke a falon hajiya mommy kusan su biyar, hajiya mommy se kawayenta manyan mata su uku manyan mata ne kamar Hajiya mommy, Dayar ce karama wato na’eema . Duk kaninsu sunada kiba sosai, ba kamar ma ita karamar cikinsu, dukda a zaune take hakan be hanani gano itadin gajera bace, sede fara ce sol, bata da kyau kwata-kwata ga kananun Ido, gashi duk tayi kiba tako ina, irinsu ne akewa lakani da badan fari ba se bola. Zaune suke sun Sa table a tsakiya Wanda ke cike da kayayyakin motsa baki se sanyin AC da AC kawai keta ratsasu tako ina masu Aiki nata hidima dasu, sauran ukun duk Aminan hajiya mommy ne na bugawa a jarida, kallo daya zaka musu kasan sunci sun tada Kai, tinda hajiya mommy ta Auri Alhaji sunusi Ta dena kawance da talakawa sede Yan gayu masu kudi kawai. Hajiya mommy dake zaune kan kujerar 1ctr tana facing na’eema dake zaune da wayarta kirar iPhone 13promax a hannu tana kallon TikTok. “Ke tinda Allah yadawo dake lafiya ya kamata ki koma dakin mijinki Ko zuwa gobe ne…” na’eema dake kallon wayarta ta dawo da dubanta kan Hajiya mommy dake maganar ta tabe baki cikin mamaki tace “Ai benan mommy Na tambayi me gadi ta waya ya gayamin ya koma kano ai.. kuma ma ko Yana Nan gaskiya bazan koma yanzu ba. ” Hajiya mommy ta amshe da “Dole ki koma saboda kinsan de mijinki ba hankali ne dashi ba, na fuskanci ya fara kosawa gaskiya, danma Allah ya rufamin Asiri uban a tafin hannuna yake ..” Cewar hajiya mommy. Kaf kawayen hajiya mommy suka kwashe da dariya Hadi da hada baki gun cewar “Da kyau ta gurina ai bakya wasa…” hajiya mommy tayi Wani farr da Ido tace “ina zan tsaya wasa,,, ai kaf gidannan d’anne ya zamar min. Kadangaran bakin tulu….ita kuma wannan wawiyar tasha nono ta zubar Sam ta kasa maidasa kmr masa a tandaa.” Hajiya mommy ta karashe mgnrta tana kallon na’eema. Hajiya naja’atu babbar Aminiyar hajiya rafi’ah ta amshe da “ta yaya zata maidasa kamar masa kullum kina kan aikata kasashen waje sarin kaya?” Na’eema ta amshe da “Gaya mata dai mama.. ” cikin tsiwa tayi maganar daman bata da alamar kunya ko a Ido.. “A gayawa uwar ubanki me dattin talauci…” Hajiya mommy ta amshe da kundumoma na’eema manyan ashariya. Na’eema ta hade Rai tana kunkunai. “In ban aikaki kasashen wajen saro kayayyakin ba ubanki dake kabari zan aika ya saromin shigiya kawai! Yar bura uba, Nan dattin talauci ne ya kashe ubanki! shegiya Dan uban ubanki tashi ki barmin falona kuma gobennan ki shirya ki koma gidanki ,in mijinki yadawo ya taddaki gidansa,karki jamin yazo ya gayawa ubansa, tin uban be tafuka Wani Abu yazo ya tafuka a kansa, tinda azabar sonshi yakeyi kamar hauka..” cike dajin haushi da bakin ciki na’eema ta tashi ta bar falon ta cika fam ta batse, a rayuwarta ta tsani yarfi kuma mommy ta matsifar iya disga mutum a cikin friends dinta, ita kuma na’eema ga rashin kunya,ba tattausa harshe ko a kan uwa ne, a rayuwarta tana kaunar tafiye tafiyennan da takeyi , ko Dan pictures datakeyi tana nunawa duniya ta faso gari, uwa uba kuma tana facaka da kudi, ga yawon bude Ido tanayi tana ganin Yan Gayu da masu kudade. Hajiya wasila tace “wannan Karan kin matsawa yarinyarnan a kan seta koma gidan mijinta, bayan ke takema Amfani,saboda Allah fa yarinyar nan na Kokari …” hajiya mommy tace “Eh nasani hajiya Amma ni tsorona kada yaronnan ya gaji ya gayawa mahaifinsa kinga de ko be mgna wata rana se yayi magana, ni shine kawai problem dina… ” “Karki taba damuwa tinda kin riga kinsan hannunki…”cewar Hajiya najmu. Duk suka kyalkyake da dariya, hajiya nana ta nisa cikin nutsuwa domin duk tafisu nutsuwa da ilmi ita Dr ce, tace “Kawata gaskiya be kamata ace yarinyar Nan tayi wannan kibar ba Tari guda, alhalin ko haihuwar farko batayi ba,duba fa yadda tayi kiba duk gashi tafimu kiba, ke kanki uwarta tayi hudunki, mazan yanzu fa bawani So sukeyi mace tayi kiba ba, Nan da Nan seta narke inta cika kibarnan,..” Hajiya naja’atu ta amshe da “Ah Dr nana batta ta narka kibarta, yadda kowa ya kalleta zesan tana auran me kudi kuma babban soja Masu fada aji a Nigeria ..” hajiya wasila ta amshe da “Wallahi kuwa a batta ta barbaza kibarta …yooo taci tayi hani’an, uba kudi d’a kudi kaf dangi bana tsifa, a batta ta narka kibarta yadda zata kara bayyana a hajjajunta, Muma da kika ganmu Hana hajiya dande iya jikin kenan, Amma kiba ai kwarjini ce….” “Wannan de magana taku ce kune masu diya…”cewar hajiya rafi’ah, duk kaninsu duk suka murmusa .. hajiya nana ta rausayar da Kai tace “gaskiya de ni a ganina ya kamata ta rage,, kinga ita yarinya ce mu kuma mun manyanta a garemu kiba take kwarjini,ita Kam na’eema ai kunga yanzu take tashe, gashi Mijin nata shima yaro ne,gudun kada yaga wata yayi sha’awah mazann na yanzu se A hnkli daga haka se su jajibo maganar Aur…” “Aaahhhhhh kullll hajiya kulll da maganar Aurennan,, ke kinga alamar ni Rafi’ah ina raye za ayima diyata kishiya? Yooo ni Nan na da nake tsofai-tsofai Dani ma a Kanta ba Amin kishiya ba se ita datake yarinya danya a kaina… Allah kyauta, ya kade zancen kishiya,, ni wallahi wallahi a kan ama diyata kishiya kwara ni Amin kishiyari!” rafi’ah ta fadi tana huci Kai kace kishiyar akayo mata ynzu. kaf kawayen nata seda suka juyo suka kalleta jin furucin datai na karshe. “Kinsan me kikace kuwa Aminiyata?” cewar hajiya naja’atu baki sake. Hajiya rafi’ah dake girgizar kafafuwa cikin isa da takama da duniya tace “ina sane wallahi hajjaju. Sanin kankune a duniyar Nan kaf dinta na’eema kawai na mallaka a matsayin diyata, wlhi San da nake mata ko kaina ban masa wannan San, Sam banason abinda ze tabamin ita, kinga kuwa da ace an mata kishiya kwara ace ni akayima ita, nasan yadda zanyi da ita, itafa ga yarinta ga rashin wayau, uwa uba ba halinmu Daya da ita ba, ni ina iya kisan rayuka da yawa a kan mijina…Sam babu digon imani a zuciyata musammanma a kan kishiya,,kinga ita kuma na’eema akwai digon imani a zuciyarta bazata iya kashe kishiyarta ba,, ni Kam wlhi wlhi hajiya in akamin kishiya ko ban kasheta da makirci ba zan kasheta da hannayena, sede a wayi gari ta mutu, Kuna a rasa ta yaya ta mutu…wlhi duk abinda zan Aikatawa kishiyar da Akamin zan Aikata mafiynsa a kan kishiyar da Akama diyata,,” kaf sukayi tsit suna nazarin kalaman Hajiya rafi’ah, Hajiya naja’atu tayi tsit Sam batasan kawarta tayi nisa ta wuce tunaninta har haka ba. tabbas kmr yadda tace Sam bata da digon imani. “Allah ma ya kyauta…” Cewar Hajiya naja’atu, datai mgnr Hadi da sauke ajiyar zuciyar da ita kadai tasan kona Menene. Kaf suka amshe da Amin hajiya nana ta zarce dacewa “Ai duk me tsautsayin data shigo muku a matsayin kishiya tini sunanta R.I.P….” “ai kwara Matacciyar da aka ga gawarta ta fita gata…” cewar Rafi’ah datai maganar zuciya da murya babu alamar imani dai-dai da kwayar zarra. “hmmmmm Allah de ya nisanta me tsautsayi…” cewar hajiya wasila suka amshe da Amin. “Hajiya mu gama muyi sallar la’asar se muje ki kaimu sabon shago muga didimar Arziki Musa albarka…” Cewar naja’atu, daman shago rafi’ah ta bude shine sukaxo gani dasa Albarka. Nan aka chanza Hira zuwa hirar sabon shagon hajiya Rafi’ahWadda liyafa keta kankama.

    A bangaren Na’eema tanashiga dakinta tayi dealing number din Aminiyarta daya tal khadija, a Egypt dataje sarin kaya suka hadu da khadija rafi’u , suka kulla kawance gashi yanzu har sunyi 3yrs tare,. bugu daya khadija ta dauka. “Hajjaju da kanta uwar gidan Alhaji Aeezad,, yaushe kika dawo kasar?” cewar khadija daga cikin wayar. Na’eema ta tabe baki tace “Jiya nadawo khadyn buba…” “Meyafaru Naji kamar bakya mood ?” cewar khadija data fahimci na’eema bata mood a yanayin yadda ta amsa ta, da ace tana mood da yadda ta mata kirarinnan kyalkyalewa da dariya zatayi. Kmr na’eema na jira taja Wani dogon tsaki me shaddah da kisrah,kana tace “wallahi mommy ce ta bani mugun haushi…wai yau ni mommy kecewa in tattara in koma gidan Aeezad daga dawowata ko hutawa banyi ba, salon ya dawo ya maidani kamar dafaffen food me maggi…” Khadija ta kwashe da wata uwar dariya sbda karshen mgnr na’eema. “Yanzu meye abin dariya a Nan ?” na’eema ta fadi a kule. Khadija ta tsagaita daga dariyarta tana fadin “am sorry kawai kece kk bani dariya da kikace wai ya maidaki kamar food…wlhi kawata rashin juriyarki tayi yawa, ke kawai matsalarki sex in namiji nasan sex in baki jure masa a hakan wlhi komi zaki masa bakya burgesa….” Na’eema ta amshe da “shi wannan ko gindin zan wanke in basa ya hada da gabansa su zama daya bazan burgesa ba wallahi,yadda kikasan mommy haka yake Sam ba ayi masa gwaninta., Kmr yadda de kikaga mommy ga yarfin tsiya,..” khady tace “Ohhh Wani na Nema Wani na gudu,, ni kinga wallahi Rabon da Alhajibuba yayi sex Dani yafi 2yrs shifa a rayuwarsa inde kudi na shigo masa ba ruwansa da maganar sex dinsa dani, kingade aurena dashi 4yrs tsaf zan iya kirga sau nawa ya kusanceni daga lokacin zuwa yanzu, kullum se yacemin beda lafiya shi yayi ayyuka ya gaji, gashi ko romances be iya ba, in Yana taba nonuwa ke kyace yaki akeyi ,kamar ze tsinkeminsu daga jikina, nifa da akan yayi wasa Dani kwara na hakura na fawwalawa ubangijina, na kallo sex video na hkra..tin abun na damuna har na hakura, ina Nan zan samarwa kaina solution danni ba dutse bace du-du-du shekaruna ashirin da uku, tinda mukayi Aure ko bari ban taba yiba,, to in takaice miki tinda yake kwanciya Dani a fari, be taba kaimin karo ba har in kawo sede inyi wasa da kaina in kawo Byn ya gama sex Dani…ganinan ba alamar ciki ,shi Alhaji inde da kudi to mgna ta kare a garesa, kudinsa sunfi masa iyalinsa daraja…” na’eema ta ciza yatsa tace “inama ace shine Aeezad…” “inama ace ni Aeezad dinne mijina…” Khady ta fadi a ranta domin mgnr bata faduwa a fili, ta jima tana mafarkai da dama a kan Aeezad mijin kawarta, taso ace daman a talaka ya fito da kudi ko nawa ne seta dinga biyansa domin ya dinga cinta, Amma Kash seya fito ame kudi ta yadda bata isa ta tunkari gabansa Kai tsare ba balle da wannan maganar. A zahiri Khadija tace “Hmmm ki bari kawai Na’eema Allah baya ba me wuka nama…” da wata manufa khady tayi mgnr Amma sam na’eema bata ankare ba, tace “Tabbas da nice ke yadda kike watayawannan ai danaji dadih dako tunanin Namiji bazan ba balle gabansa…” khady tayi humming kawai, ita ba bakuwar kudi bace, na’eema ce bakuwar kudi, iyayenta asalin masu kudi ne na fitar hankali kuma dattawa ne, mahaifinta shiya hadata da mijin da take aure, Alhaji buba shiya ganta yace yanaso Aminin mahaifinta ne, ya taba aure yanada yarinya Daya mahaifiyarta ta rasu tin yarinyar na 15yrs yarinyar sa’arh Khady ce yanzu haka tana kasar waje karatu, tinda khady ta Auri Alhaji buba bata samu abinda takeso ba a tattare dashi , ita Kuma gata jarababbiya tanada tsananin bukatuwa da d’ana miji. Haka take zaman hakuri da Alhaji buba saboda bata da yadda zatayi ,ba halin taje gidansu mahaifinta baze barta ba , domin shi babban mutum ne ga dattako bawai irin mutanen Nan bane da basu da girma sena rigunan jikinsu. “Yanzu yazanyi kawata? Wlhi Sam banasan komawa gidan Aeezad ynzu…” Cewar na’eema da abun ke damunta tinda Mommy tace ta koma gidan mijinta tashiga dimauta. “Toh in baki koma ba meye amfanin Auren? Kinga kawata wlhi mijinki nada hkri inba shiba a zamanin Nan ba wanda ze jure yawon da kikeyi zuwa kasa-kasa ba izinin mijinki…kowa yaji ai yasan ba izininsa kk tafiye tafiye, ina kirge fa tinda akayi Aurenki 1month kkyi a dakin mijinki kika cigaba da barin kasa-kasa sarowa mommy kaya, mijinki fa babban mutum ne kowa yasan ba a San ranshi ba,ynzu kuma ki dawo kina kyashin komawa meye problem dinki ne kawata? Sex kou?..” na’eema ta amshe da ”After that shegen sa Aikin tsiya, kullum sena gyara masa room 2tyms, ga wankin toilet bayan uban gajiyar dayake taramin, dasafe inta masa aikace Aikace, ko maids dinafa baya fari su tinkaro part dinsa balle insasu gyara masa dakinsa…” Baki khady ta saki tace “gaskiya kawata kin cika San jiki, yanzu kawai wadannan sune problems dinki? Ke da maids kkeso su dinga gyara bed din da kuka kwanta?” na’eema ta amshe da “Ehh mana kajiki ke kuma, ni me Aikinsa ce dazanta masa whla,,shifa Sam beso yaga kin zauna, ga shegiyar tsaftar tsiya a haka komi kkyi baki iya masa ba, ke kanki a kazanta yake kallonki…” “Tabdijan…yanzu inYa cire boxes dinsa wake wanke masa’?” “Waze wanke masafa khady? Shike wanke kayansa da kansa, ko nawa panties din ban wanke ba se nasa…tinda baze iya bawa maids Ko yasa a matching ai sede yasha whlrsa shi kadai,ke namiji fa kome kika masa baya gani kwara ma karkiyi…” khady tace “Hmmm Allah kyauta…” A zuciyarta tana hasaso inama ace itace ke Auren yaro karami me danyar kaciya tabbas dayasha lailaya, seta kara danyatasa tass, itafa dama za a dawo mata da baya da babu abinda zesa ta AUREN Alhaji buba NAMIJIN KUNAMA, bashi da dadih se azabar zafin harbi. “Gobe zanzo in kawo miki kayan gyara ki gyara jikinki kafin ki koma ko zaki samu sauki a bangaren sex din ..” cewar khady. Badan na’eema taso ba tace “Okay se goben nagode best friend…” Daga haka sukayi sallahma.

     

    Wannan book din na kudi ne, gamesan Namijn zuma da Namijin duniya se biya 1500, in kuma days kkeso zaki biya 1k 0542703718 Saadatu Abdullahi gT bank.

    🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
    💖💖💖💖💖💖💖💖💖
    *NAMIJIN ZUMA*
    🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
    ❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥
    (Love and Romantic Story)

    This book is 1k 08101626484

    SAADATU BINTU ABDULLAHI (Writer of kyautar Allah)

  • Namijin Zuma 5

    Namijin Zuma 5

    Free page5
    *(Back To Story)*
    Karfe hudu da rabi na asubahi, ya sakko daga katafaren gadonsa bakinsa dauke da Adduarh, Sanye yake da kayan bacci riga da wando lallausar, a hankali ya dire kafafuwansa a kasan dakin wanda yake mamaye da lallausar carpet kamar fadamar audiga, hannu ya kai ya kunna hasken dakin wow! Komi acan-acan dakin yan gayu, tako ina an tsarasa irin tsarin Yan boko, komi na dakin dark and light royal blue ne, babban gadon royal ne dakin wanda a kallah ze dauki mutum biyar ba tare da an rasa space ba,. Hamma yayi cikin rashin jin dadih a jikinsa sam ba kwari, daman ba Wani baccin kirki yayi ba, shifa inde ba a jikin mace ze kwanta ba baya iya bacci, mommynsa tasaba masa da kwanciya a jikinta tin yana karami daya girma ne suka dena kwana daki daya,Amma har yakai 15yrs da daddare a kirjinta yake iya bacci, koda suka dena bacci daki daya Sam be iya bacci seyazo dakinta ya kwanta a kirjinta kana bacci ke dibarsa, in yayi bacci ne take fita ta bar masa dakinta ta nufa wani dakin. a duk kullum na rayuwarsa in zeyi bacci seya tuna da lallausar tula-tula din kirjinta dayake matashi dashi, da ace nonuwanta masu zubewa ne da tuni ya zubar dasu tass, sbda sune matashinsa, yasaba jin duminsu ganinsu ne kawai be taba yiba a zahiri. “Inde manyan nonuwa ne mommy karshe ce,,, akwai Arziki kaya Alaji…..” ya fadi a bayyane se murmushi kawai yakeyi, be taba kwana ya tashi ba tare dayayi tunaninta ba, amma na yau tunanin ya yawaita a garesa. Tako ina se kamshi kawai ke tashi a dakin,, direct bathroom ya nufa, zuciyarsa fal tunani tunanin surar jikin mommynsa,. Ya danna Kai bathroom din, shi kansa bathroom din abin kallo ne an kayasa tako ina, komi na kaf toilet dinsa zuwa bathroom dinsa nanma royal blue ne light and dark, gashi tsaf-tsaf, Aeezad nasan tsafta komi nasa a tsare yake irin na masu ilmi Sam bayasan hargitsi, yanasan tsafta, uwa uba kuma kamshi Yana kaunar kamshi, ya ginu da tsafta da kamshi ne tin a gurin mommynsa. Direct bathroom ya fada yayi wanka Nan da Nan ya fito ba bata lokaci daure da alwala, shi Sam baya dadewa a wanka yafi dadewa a shiri. Kugunsa daure da towel royal blue se Dan karamin light royal blue a hannunsa ya fito Yana me goge sumar kansa zuwa jikinsa, karasawa Waldrop’s din kayansa wadda ta manaye bango daya da rabi na dakin nasa, ya bude ya dakko jallabiyarsa Ash dark, Yasaka ta matukar yi masa kyau jikinta duk tsantsi, ya isa gaban mirror dinsa wanda ke cike taf da turarruka da mayuka na gyaran jiki Kai kace gaban mirror din na mace ne, shifa ko mace bata kaisa San kamshi da mayukan gyaran skin ba irin masu karawa sking laushi and glowing su yake using, cream din face da ban na jiki daban na tafin hannu daban, dan gayu neshi na last, baka isa kaga nakasu a jikinsa ba , yafi wata macen gayu, ko hair creams dinsa sunfi kala goma, yanasan gayu, shiyasa sometimes suke fada da na’eema sbda ita batasan gayu shi Kam Dan kwalliya ne, ita Kam sede ta zauna sandandan ba ado ba kwaskwarima, shiyasa ya kasa mancewa da Esther, dukda ita ba Muslima bace amma tasan darajar jikinta akwaita da tsaftar jiki be taba kusantar jikinta yaji wari ba,ita Kam na’eema sede inshi ya mata shelving din gabanta da hammatanta ko shelving din batayi, in zeci seyayi mata danshi a rayuwarsa beso yaga gaban mace da gashi kwata-kwata yafiso yashafa yajishi sumul bakomi. Kusan turaruka kala biyar ya feshi jikinsa dashi, kana ya isa inda aka kebance danyin ibada, Sallar ya tayar raka’ah biyu ya idar, ya jawo charbinsa ya fara lazimi, Aeezad nada ibada sosai a gurin Nabeelah yagani ya koya, inde ibada ce ita last ce ala kullu halin bata taba yarda tayi sakaci da ibada. Har aka kira asubahi Yana lazimi kana ya Mike ya kara feshe jiikinsa da perfumes ya fice zuwa masallacin dake cikin gidansa, gidansa nada girma sosai kai bakace zaman mutum daya bane. Be dawo ba seda gari ya fara haske kana yadawo gidan, yasake Wani wankan, ya shafa mayukansa seda ya kwashi 30mnt Yana shafa, ya gyara kwantacciyar sumar kansa, kana ya shirya cikin danyar shadda light golden dinkin yar shara, ya daura dankareren watch dinsa ya kara rikita jikinsa da kamshin latest turarukansa, ya zira hadadden takalminsa black ba karamin kyau takalmin ya masa ba ya amshi launin fatar kafarsa ta yan hutu. fitowa yayi compound din gidan rige da yar jakarsa da wayoyinsa, sojojin dake farfajiyar gidan suna jiran fitowarsa sunfi su ashirin suna ganinsa suka rugu a guje har suna rige-rige suka kame masa Hadi da amsar kaf abubuwan dake hannunsa cikin girmamawa. Daman already sunsan yau ze koma garin kano Dan haka already an shirya motocin tafiyar,motoci uku Daya tashi biyu na sojojin dake tsaronsa. Addu’ur’i yayi Kana ya isa ga motarsa launin Army green, aka bude masa yashiga still bakinsa dauke da Addu’ur’i aka maida murfin motar aka rufe,sojoji suka shiga nasu motocin Nan da Nan dreva yashiga yaja motar suka fice a gidan, ma’aikatan gidan nata masa Addu’ur’in dawowa lafiya. Tafiyar 3H ta kaisu garin Kano sbda yawan cinkoso da gyare-gyaren hanya da Ake tayi, da normal ne 2h ke kawosu Kano. Kasancewar yanada Ayyukan dazeyi a office dinsa, Dan haka direct office aka nufa dashi, yayi wanka yadansha coffee kana ya fara ayyukansa, ba jimawa aka kira sallar Azahar, ya fito zuwa masallaci. Bayan sun idar da sallar ya fito sukayi kicibus da Zaks, murmushi Zaks yayi fuska dauke da mamaki ya kame masa cikin girmamawa kana yace “yaushe kadawo gari bani da Labari Commander din Yan iska!…” Aeezad Ya watsa masa banzan kallo kana yace “banjima da dawowa ba ,direct office ma akayo dani…” suna tafiya zuwa office din Aeezad suke maganar. “Okay,, yaka baro me kayan Alatu…” Cewar Zaks, dai-dai suka iso office din Aeezad din , Zaks ya zauna a kan kujera, Aeezad ma kan kujerar ya zauna yana me duba system dinsa yayi kmr bejima me Zaks yace ba, tsaf kuma yajisa yasan me yake nufi, waishi nufinsa ya yabaro mommynsa haka Zaks kece mata wai me kayan Alatu, Zaks yasha ganin nabeelah fin a kirga tin suna school da Aeezad, domin shima Zaks din haifaffen katsina ne, aiki ne yakawosa Kano. “Yaka baro me kayan Alatu? Nonuwa raba-raba, duwaiwuka baja-baja..” Zaks ya sake maimaitawa ta sigar neman fitina. “Zanci ubanka dan kutmar ubanka da mgnr me kayan Alatunnan! Dan iskan area kawai!…” Aeezad ya dago ya fadi a fusace ,domin ya tsani sunan da Zaks ke kira masa uwa dashi. Zaks ya fashe da dariya yace “Banza jarababbe, kaide bazaka taba dena matsifa ba, daga tambayar yaka baro me kayan Alatu seka rufeni da jaraba,,” “look malam inka saba ganin matan banza da sigar iskanci karka sake a kan uwata nagaya mata uwata ba sa’ar ka bace, Kai zakaji dadih acewa uwarka me kayan Alatu,kaga malam karka kara wlhi, ko insa bindiga in tashi kanka Dan uwarka!…” Aeezad ya fadi cikin fada. Baki bude Zaks yace “abun harya kaiga kisan Kai,,Allah baka hakuri NAMIJIN ZUMA,…” (Esther ce ke kiransa da Namijin zuma saboda dadin gabansa datakeji yasa tasa masa wannan sunan, Esther ba bahaushiya bace amma taji hausa kmr jakar Kano. A Nan Zaks yaji ya rike, shima yake kiransa da Namijin ZUMA ga zaki ga harbi) Nan ya kara harzuka Aeezad Sbda baya kaunar ace masa Namijin ZUMA hakan na tunasar dashi rayuwarsa da Esther ta baya ana tado masa kwantaccen tsumi. “Tashi ka fitarmin a office! Dan iska mayen mata kawai!” ya fadi murya cike da zallar bala’i kamar ze hadiye Zaks. Mikewa Zaks yayi Yana narka uwar dariya Daman sam basa zama inuwa Daya dasun zauna dasunyi fada. Ya mike ya nufa kofar ficewa daga office din Aeezad yayi kwafa yace”Dan iska wanda kullum gindinsa na gaban mace…” Zaks ya juyo yace “Naji din in ban shiga gindin mace ba gindin namiji zan Shiga… Nasan de duk haushina rashin gindin dazaka cine ke dawainiya dakai…” Yana gama fadar hakan ya fice a office din a guje danya kula harda ma rashin cin gindi ke dawainiya da Aeezad shifa daman haka yake in beci gindi yadawo Zaks na ganewa sbda Abu kadan se yayita matsifa kaga fuskarnan bakikirin ba Annashuwa. Kwafa Aeezad yayi yaci gaba da Aikin gabansa,. Bashi ya bar office din ba se after magrib , aka dawo dashi dankareren gidansa dake cikin nasarawaGra, shi Sam baya zama a barracks yanada gidajensa a garuruwa da dama. Wanka yayi Yasaka kananun kaya na hutu kana yasa akayo masa take away din tuwon shinkafa Miyar kuka, a rayuwarsa yanason miyar kuka over, shi mutum ne ma’abocin San tuwo miyar kuka musammanma in mommynsa ta dafa kuma take feeding dinsa,har yanzu wasu lokutan ita ke feeding dinsa da kanta in beyi lefi ba kenan. Be tabajin damuwa da tunannikanta ba irin na wannan karon, ko Sallah zeyi yanayi Yana tunaninta komi na rayuwarsa dole se tunaninta ya fado masa Rai a fari ba haka yakeji ba a kanta gaskiya yasan de Yana tunaninta over Amma ba kmr na yau ba.”maybe ko Dan baka kirata kajita bane….” Wata zuciyarsa tace dashi hakan,Nan da Nan ya yarda da hakan ne ma. Bayan yayi sallarh isha’i Ya sake wanka ya shirya cikin kayan bacci na alfarma farare sol, ya hakimce a dankareren falonsa Wanda yaji kayan Alatu Kai kace akwai mace a gidan, duka gidajensa yanada ma’aikata Maza masu kula masa da gidansa danshi a rayuwarsa baya kaunar kazanta, ma’aikaciya mace cede bashi da ita saboda yanada tabbacin wata rana in jarabarsa ta tashi Yana iya afkawa yarinyar mutane, so kula da Kai yafi ban cigiya, in abunshi ya tashi wlhi Sam bashi da control dole seya shiga yakejin dadih,ko romances bayaso me tsawo tinda ya gane dadin gindi. Lumshe idanuwansa yayi, Yana me kara luntsuma a kan kayataccitar kujerar dake falon masu tsananin kyau da tsaruwa , kujerun falon Army green ne and golden light, ba karamin kyau falon yayi ba komi perfect,irin na masu kudi. Idanuwansa ya bude a kan tamfatsetsen Tv Daya mamaye bango daya na falon ,News yake kallo Amma sam baya Wani fahimta, tunaninsa na kan wasu abubuwa da dama a rayuwarsa da mommynsa. Wayarsa ya jawo kirar iphone 15promax, yana kaunar iPhone a rayuwarsa shiyasa inta fito kafin a sakarwa kowa yake saka manyan kudade ya siya yazamana shine first Daya fara using dinta. Lambar JARUMATA💖 ya lalubo, seda ya jima Yana kallon number din Yana Adduarh Allah yasa ta dauka, yauce rana ta farko Daya taba Adduarh Allah yasa mommynsa ta dauki wayarsa ya rasa dalilin hakan. Yayi dealing number din, Har Kiran ya tsinke bata dauka ba, ya kara dealing zuciya cike da kosawa da zakuwa, , kawai muryarta yakeso yaji, zuciyarsa dukta zaku. A karo na biyu ma kin dagawa tayi, ya kara mata kira na uku taki dauka , zuciya fal kuncin dabesan kona meye ba ya ajiye wayar gefensa, hatta launin jikinsa seda ya chanza yaji komi duk ba dadih, duk sanyin AC dake falon seya farajin zafin damuwa. Tsabar takaici Nan falon ya kwana, Bacci sede barawo, da asuba yana tashi ya kara kiranta 3tyms taki dauka, zuciyarsa ta kuma cushewa ko tea besha ba yayi wanka ya nufa office gashi yanada ayyuka dayawa , haka ya wuni yana Aiki time to time yana kiranta taki dauka har yamma yanata kiranta taki dauka, haka kawai yakeji kamar kansa ze kwance itadin kawai yakeso yaji,ya rasa dalilin hakan. Da daddare har Sha biyu na dare ya Kai yana kiranta seda taga kiran yayi yawa ta daga domin duk Kiran da yake mata a kan idanuwanta kawai batasone ta daga sbda yasaba mata irin haka data dauka kuma taji ba abun Arziki bane, Amma sede ta kula Kiran da yake mata a wannan karan yayi yawa, Dan haka seta fara tunanin anya kuwa lafiya. Ajiyar zuciya ya sauke jin ta dauki wayar yaji wani dadih a zuciyarsa wanda be tabajin irinsa ba tinda yazo duniya. “Meye ka damu mutane da kira Har cikin dare…” Cewar nabeelah datayi maganar da zazzakar muryarta.

    Wannan book din na kudi ne 1k only 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank 08101626484.
    🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
    💖💖💖💖💖💖💖💖💖
    *NAMIJIN ZUMA*
    🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝🐝
    ❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥

    https://chat.whatsapp.com/FxikBhpweXTLMbrEVc6xdS
    Free page group.

    SAADATU BINTU ABDULLAHI (Writer of kyautar Allah)

  • Auren Shehu Book 2 Page 6

    Auren Shehu Book 2 Page 6

    6

    Ha?e ran da yayi bai sa sun fasa ?arasawa har in da su ke ba, su uku ne namiji ?aya da mata biyu da za a iya cewa miji, mata da ?arsu ne don ?ar ba za ta wuce shekaru goma ba.
    “Me ya kawo ku nan Tanko”

    usman ya fa?i cikin tsawa, ya kara da

    “Bello me kake nufi kenan? So kake ka nuna ka isa a Rugar nan ko me ye dalilin ka na shigowa da wainnan iblisan?”

    Ya cigaba da fa?i yana mai kallon Bello wanda ya sha jinin jikin sa jin lafazan Usman. Gyara tsayawa zainab ta yi cikin nishadi wanda ya kira jinin sa ya mata aikin da ta dade tana yi baya kama shi, amma kuma kallo ?aya ta yi ma wanda ya kira da Tanko ta hango kamanni na jini tsakanin su sai dai shi din baki ne, sabanin Usman da ya ke farar fata. Duk da ba jin yaren ta ke yi ba za ta tsaya ta kalli dramar da za a yi.
    Haka ma sauran jama’ar gidan su ka fito suna mai kallan Tanko cike da mamaki da al’ajabi, dan kuwa babu wanda be san mugun halin Tanko ba. Daliban Shehu kuwa musammam kanana cikin su har rawar jiki su ke ganin yanda Usman ke bambami.

    “ka dubi girman Allah Shehu, ka dubi nasaba da martaban ka, ka dubi darajan yarinyar nan Cangwai da ta fito daga tsatsonka ka yafe mana”
    Macen ta fa?i tana mai share hawaye.
    “Baffa Allah ya masa cikawa bayan kun baro sa, ba mu da kowa shi ya sanya muka ce mu zo cikin ?an uwa mu zauna, wallahi duk wani mugun abu na bar shi a dajin falgore, Tanko mai kyawun hali ne nan, ka yafe mana”

    Tanko ya ca?e cikin fullanci yana mai rusunawa kamar zai yi sujada. Cikin lafiya da nuna rashin tausayi Usman ya furta

    “Rugar nan tsarkakakke ne babu ?igon mugun aiki a cikinta, saboda haka baku da matsuguni ku fice kafin na saukar da fushi na akanku”
    yayi maganar ya na mai nuna masu hanyar ficewa daga ?angaren nasu. Daga Tanko har matar shi zubewa su ka yi gwiwowi biyu, hawaye na zuba daga idanun sa ya ce

    “Ka taimaka Shehu, ba mu da matsuguni Shehu, duniya ta juya mana baya, idan ma ba za ka karbe ni ba ka duba Rahila da Cangwai, Raliya diya mace ce, ko ba komai Cangwai diyar ka ce….”

    “Cangwai ba diya ta bace!”
    Usman ya katse shi cikin tsawa yayinda ya kai kallan sa ga yarinyar da Tanko ya kira Cangwai, be gushe ba ya kara da

    “Na sani! Ka sani! Na san ka sani! ku kama hanyar ku tunkafin rai na ya fi haka baci”
    Maimakon su juya Tanko ya shiga waige waige yana mai rokon mutanen da ke wajen da su sanya baki Shehu ya yafe musu a nan ne ya hango zainab da ke tsaye. Ba shigar da tayi na doguwar riga ka?ai ya ?auke hankalinsa ba har da bambamta da tayi da sauran matan rugar, in bai yi ?arya ba irin matan birni da su kan sace don neman kudin fansa ne.
    ‘toh me ta ke yi a rugar shehu’ ya tambayi kansa. Gaba ?aya ta manta abin da ya ke yi ya saki baki yana kallon zainab tare da zantawa da zuciyar sa. Yanda ya saki baki ya na kallan ta ne ya sa Usman ya kai kallo gare ta, ganin Tanko ya sa shaf ya manta da ita. Wani irin bakin kishi da tun da ya zo duniya be taba jin irin shi ba ya taso masa har kahon zuciyar ta, musammam da ya lura Zainab din ma Tankon ta ke kallo

    “Me kike yi a wajen nan? maza shige ciki!”

    Shehu ya daka mata tsawa da firgici ya hana mata musawa cikin sauri ta shige bukkan, sai da ta shige sannan ta ji haushin kanta na yin biyayya da ya daka mata tsawar. Daga bakin assabari ta la?e tana kallon yanda mutane ke ro?on usman yana botsarewa.
    “Kai an yi azzalumi! komai aka yi wani zalincin ya ke aikatawa! Wannan masifa har ina! Ina ma ina jin abin da su ke fada! Ya Allah idan har wannan bawa zai iya aikata sharri da zalinci ga jinin sa, Allah kai kadai ka san irin zalincin da zai iya aikatawa kai na, ya ke kuma kan aikatawa, ya Allah ka mana maganin shi.

    “Zan iya karbar Rahila da kuma diyar tsohuwar mata Cangwai saboda raunin su na ‘ya’ya mata! Wajan ka dai babu shi Rugar Shehu, idan har hakan ya maka toh, idan be ma ka ba su ma din kana iya tafiya da su!”

    Cewar Usman wanda kallan da ya ga Tanko ya na yiwa Zainab ne dalilin shi na biyu na rashin yarda ya zauna a Rugar Shehu. Rahila matar Tanko ta na ji tana gani Tanko ya mata sallama tare da mata alkawarin zai dawowa da ya sami matsugunni. Kukan Rahila da Cangwai be sa Usman ya tausaya ma su ba, sai ma sallamar yara da yayi daga karatu, shi da Bello su ka tasa Tanko gaba, sai da su ka tabbatar yayi nisa da Rugar Shehu, sannan Usman ya ce da shi be hana shi zaman dajin ba matukar ya kiyaye kusantar Rugar Shehu.

    Tuni labarin zuwan Tanko ya kadaye Rugar, ranar da jimamin abin da ya faru aka wuni, ita kan ta Zainab sai da zuciyar ta ta dan yi rawa sanadiyar ganin rikidewar Usman cikin kankanin lokaci duk da sam ba ta fahimci ainihin abin da ya gudana a tsakar gidan ba.
    Usman kuwa tun bayan da ya tasa kyeyar Tanko, haka kuma ya tabbatar ya ja kunnan Bello be iya komawa sashan shi ba gudun kar ya kara saka Zainab a idanun sa, wani irin bacin rai ke addabar zuciyar duk sanda ya tuna yanda Tanko ya shagala ya na kalle Zainab, wacce ta tsaya kerere da ita ko mayafi babu.

    Sai bayan da ya idar sallar ishai sannan ya koma gida ya tarar Zainab na zauna sai surutai ta ke. Fadi ta ke

    “Babu ruwa, babu wuta, babu bandaki, babu siturar arziki! Babu waya! Babu club! Babu mai jin hausa! babu Jin dadi! Babu babu babu, babu civilization! bambamcin wannan daji da kabari shi ne can lahira ne! wannna wani irin rayuwa ce!…Ammy in ma ke ce ki ka kullace ni dan Allah ki yafe min, Dady…. Dady ka mutu ka bar ni da masifa Dady! Auren Shehu masifa ne Dady!”

    “Akwai maza amma ko?”

    Da sauri ta kai kallan ta ga Usman sam ba ta san da shigowar sa ba, tsaye ya ke jikin bango hannu sa harde a kirjin sa, yayinda hasken acibalbal ya haske fuskar sa, idanun sa har kyalli su ke tsabagen bacin ran da ya ke tattare da shi.

    “Na’am?”

    Ta mayar masa cikin rashin fahimta. Maimakon ya bata amsa, sai ya wuce ciki ya dauko wasu acibalbal har biyu, ya kunna haske sosai ya gauraya dakin, sannan ya dawo ya tsaya gaban ta, idanun sa cikin na ta ya furta

    “Maza da ki ka fi so a rayuwar ki, akwai su ko? Na ga yanda ki ka kasa boye maitar ki sanadiyar ganin Tanko….”

    “Tanko? Wanene Tanko?”

    Zainab ta tambaya dan kuwa gaba daya kan ta ya juye ta kasa gane in da Usman ya dosa. Zainab na murmushi bayan ta gano bakin zaren ta ce

    “Ya ba zan nuna maita ta ba bayan na ga namiji iya namiji? Ai wannan dajin kaf babu namiji da ya amsa sunan sa namiji kamar wannan….ya ma ka kira sunan sa?”
    “Zainab!!!!”
    Ya daka mata tsawa ya na mai kiran sunan ta na ainihi a karo na farko cike da gargadi, duk da hantar cikin Zainab ya kada ba ta fasa fadin
    “Ga shi baki, ga faffadar ka fada…..”
    “Zainab!!!!!”
    Ya kara daka mata tsawa tare da daga hannu kamar me shirin marin ta, har ta kai ga runtse idanu. Jin ba ta ji saukar marin ba ta bude idanun ta a hankali ta kai kallan ta gare shi. Idanun sa sun yi jajur sai huci ya ke
    “Me ya sa ka fasa? Ka mare ni mana! Ka dake ni! Idan har ba ka daga hannu ka dake ni ba Usman ba ka isa namiji ba!”
    Murmushin mugun ta ya sakar mata kana ya na mai ja da baya ya furta

    “Idan har duka shi ne zai gwada mi ki isa ta namiji, Ni kuwa zan dake Abu, Amma duka mai dadi Abu ba irin wanda ki ke tunani ba, Irin wanda za ki dena maitar duk wani damiji face ni Usman…”

    Ya na gama fadin haka ya fice da sauri dan kuwa yanda ya ke ji zai iya aikata abin da zai zo yayi dana sani.

    *Khadija Sidi*
    Auren Shehu 2

     

     

  • Auren Shehu Book 2 Page 7

    Auren Shehu Book 2 Page 7

    7

     

    Ta na mai nana ta maganar Usman cikin ran ta yanda ta ga rana haka ta ga dare, dan raban da ta sami ishesahen bacci tun ranar da aka wayi gari a Rugar Shehu.
    Kamar yadda kowa ya kwanta da sanyi jikin zuwan su cangwai rugar da tsoron abin da Tanko zai iya aikatawa saboda korar da aka masa haka aka tashi washe gari, hakan bai hana mata dakan hura da zuwa tatsar nono asubahin fari ba. Bukkar da ke kusa da ta Atuwayye , matar taubashin Shehu ya sauke Rahila da Cangwai saboda aminta da yayi da ita sannan zaman da su ka yi a ?asar Benue da mijinta lokacin da su ke ganiyar ka?e shanu ya sanya ta ?an fi sauran wayewa.
    Duk wannan kai komon da ake yi da Rahila ake yi, sakin jiki tayi tana aiki tana lura da rugar sosai, cangwai kuwa tuni ta shige cikin yan mata sa’annin suna ta hidimar gaban su.
    Ko da aka kammala girki, Raqiba aka kwalawa kira don ta kai ma Zainab nata.
    “Iyalle barshi zan kai”

    Rahila ta yi saurin fa?i don dama neman hanyar shiga sashin Shehu take.
    “Ayi haka, tun safe kike aiki fa, Allah ya miki albarka” fa?in Iyalle ta na mamakin sauyin halin da ta gani a tattare da Rahila.

    “Ba komi Inna, ai mu masu laifi ne, duk abin da zamu yi don mu rage nauyin zunubinmu za mu yi”

    “Aikuwa dai Shehu na son debbo ma, ga ta Ka?o maras daraja” .

    Hansai ta ca?e tana mai ta?e baki

    “Kinga ki iya bakin ki, ba da ni za a yi shari’a ba, in bai so ta ba wa zai so, da gani ai ka san yar birni ce”

    Cewar Iyalle tana mai tashi daga wajen. Kalaman nan ne su ka ?ara sanya Rahila son zuwa ko don ta gane ma idon ta matar da kyau, gashi dai zuwan su jiya ta shaidi cewa yana kishin ta.
    Da tunanin nan ne ta nufi hanyar sashin Shehu, da sallama ta shiga bukkar ba tare da ta jira an amsa ba duk da cewa zainab ba amsa sallamar su take ba.
    Zaune ta iske ta ta baje kayan ta a saman gado tana ?aga su, neman mai gwara gwaran da za ta sanya take yi kasancewar duk sun yi datti.
    Buga wayar ta take a tafin hannun ta kamar hakan zan sanya ma batirin charji har ya kawo

    “A ce mutum ya zama kurma a ?ungurmin dajin nan ta ina zai fara ga waya a kashe ba charji”
    Tace tana mai jan tsaki daidai lokacin da Rahila ke kai bakin ?ofa za ta fice daga ?akin. Jin haka ta juyo tana mai kallon hannun zainab, ko da ta shigo bata maida hankali ga hannun ta ba illa suturar da ta gani zube a gado musamman gajeren wandon zainab.

    “Laaaaaaa!!! Wallahi irin abin da mai gidana ke magana da mutane in sun yi kinnafin, salla ko me ma sunan”

    Tace tana ?ingere baki, duniya in akwai abin da ke birge ta yana bayan waya, don ta so Tanko ya bata ?aya wata rana da ya shigo da su ya ce mata ai kudi ne ma?udai in ya siyar da su

    “in sun yi mene? Ya aka yi ke kika iya hausa”

    Zainab tace cikin firgici da farin ciki. Firgicin ambaton kidnapping da kuma farin cikin wacce ta ke jin hausa, hakan ya sa Rahila ankarewa da subul da bakan da ta yi, ta yi saurin gyara maganar ta hanyar fadin

    “A’a wai in sun dawo daga wajen Sana’a na ke nufi…”

    “Laaaa hausa ki ke min? Ki na jin hausa? Kin iya hausa?”

    “Ai kusan rabin matan rugar nan in ba ma fiye da rabi ba suna jin hausa, Ce mi ki su ka yi ba da ji?”

    Cewar Rahila ta na mai duban Zainab wacce alamar mamaki ya bayya na a fuskar ta, kafin bacin rai ya maye gurbin mamakin, murya kasa kasa ta ce

    “Babu mahalukin da ya taba min, ko na mu su magana ba su nunawa sun gane bare su amsa, sai tsinannan dariya kamar mahaukata!”

    “Hmmmm kadan daga cikin aikin Usman kenan!”

    Cewar Rahila ta na mai jinjina kai na.

    “Usman kuma, akan wani dalili”
    zainab tace cikin ?acin rai

    “Zalunci! Ai babu azzalumi sama da Usman, Kinga da mahaifin Usman da na Tanko miji na uwa daya uba daya su ke, Amma Usman ya tunkude siriki na daga sarautar Rugar Shehu, haka kuma ya haye kujerat tare da ha?e dukiya gaba ?aya, ya kada shanu kaf be bar mana ko daya ba ya tai dajin ga, ya bar mu ba cin yau bare na gobe, bakin cikin haka ya kar siriki na har lahira, dole ta sa mu ka bi sahun Rugar Shehu, gaban ki dai aka yi komai jiya…..”
    Ta kare maganar ta matsar kwalla. Cike da tausayawa Zainab ta furta

    “Lalle ya cika azzalumi na gaske, tun da har ya iyayiwa jinin sa haka, ban yi mamakin abin da ya aikata gare ni ba……”

    Nan ta kwashe komai ta fadawa Rahila, ta kare da

    “Ni ban san yanda aka yi ba, zan dai tuna sanda na gama karatun jarabawar da zan zana, kawai sai wayar gari na yi na ganni kurgurmin daji hannun wannan azzalumin!”

    “Surkulle kenan! Ai kiranye ya mi ki!”

    Cewar Rahila ta na mai hango tarin dukiyar da Tanko zai samu ta sanadiyar Zainab, Dan kuwa kifi ne daga sama gashesahe, za su yi amfani da Zainab ta hanyoyi har biyu, na farko su kwaci Rugar Shehu ta hanyar hada baki da ita, Dan kuwa tun jiya ta gano Shehu na so da kishin Zainab, Zainab din ce dai ta kasa fahimta, haka kuma bayan sun kawar da Shehu su karbi kudi makudai na fansar Zainab, dan kuwa dai ba ta ga dalilin da zai sa Tanko ya ga Zainab ya mayar da ita salin alin hakan nan ba.

    “ikon Allah, yanzu dai tun da na same ki baki munafunce ni ba kamar saura”
    Maganar da ya dawo da Raliya daga wasikar jakin da ta fara. Jin Zainab na fadin

    “ki min hanyar barin wajen nan ni kuma na miki alkawarin dukiya mai yawa sannan zan sa a kama azzalumin nan”
    ya sanya Raliha murmusawa, kana ta bata amsa da
    “In dai daga bangare na ne kar ki ji komai”

    “Ni damuwata ma yanzu kaya na da duk suka yi datti, kazamai ne kaf dajin nan!”

    Zainab tace ta na mai daga bumshort din ta biyu da su ka rage ma su tsafta.

    “Laaaa wannan kamfai ne ko fatari?”

    Yanda Rahila ta yi tambayar ne ya sanya Zainab dariya tare da fadin

    “Bumshort sunan sa”

    “Toh toh shi ma din a kasan tufa ake sawa ko? Kamar dai kamfe ko?”
    “Ah ah, hakan nan din shi ake sawa, kuma kyau ya ke sosai, musammam in aka saka da yar riga kamar wannan…”
    Ta yi maganar ta na mai daga shudiyar rigar ta, idanun Raliha har rawa ya ke tuni ta fara sakar zuci. Jin Zainab ta furta

    “Ina ma birni na ke da na sa kin ga rayuwa, wannan dajin ma ina mutum zai saka….”

    “Za ki iya mana!”

    Rahila ta katse ta cikin farin ciki.

    “Zan iya me?”

    Zainab ta tambaya da zuciya daya.

    “Sakawa, wannan hanya ce mafi sauki na tunzuru Usman, dan kuwa na lura ya na matukar kishin ki….”

    “Mtswww kishin wa? Allah ya sauwake!”

    Ta katse ta a fusace. Rahila na mai girgiza kai ta ce

    “Na ce dai yanzun nan ki ka gama fadin na taimake ki ki bar dajin nan?”

    Zainab ta girgiza kai alamar “eh”

    “Toh ki saurara da kyau ki ji, mutum kamar Shehu sai fa kin masa bita da kulle dukan kabarin kishiya! Ni ba zance mi ki ga hanya daya da zan iya taimaka mi ki da shi ba matukar ba surkulle za mu yi ba, Usman kuwa babu surkullen da zai ci shi, ko siriki na ya buga ya bar shi….”

    “Wani sirikin na ki? Ba kin ce ya rasu ba?”

    Zainab ta tambaya cikin rashin fahimta, hakan ya sanya Rahila saurin gyara maganar na ta

    “Ina nufin kafin ya rasu, eh kafin ya rasu din, toh dai abin da na ke nufi za mu ta gwadawa ne ko Allah ya sa a dace, yanzu dai ki fara da wannan shawarar da zan baki, ki saka wannan ki tai har fadar Shehu, na san matukar manya su ka gan ki da wannan shiga dole Usman ya ji kunya da kishi, kin ga a dole ya mayar da ke gun iyayen ki”

    Zainab na mai tunanin ya aka yi wannan azancin be zo mata tun da ba ta amsa ma Rahila da toh.

    “Anjima zan zo in je in wanke miki”

    Rahila tace kafin ta fice tana barin zainab da auno kalar azabar da za ta sa a ma Shehu in ta isa gida. Ita kuwa Rahila tunanin yanda za ta isarwa mijin ta da wannan kyakkyawan labarin, dan ta san halin Usman duk hakurin shi matukar aka kai shi bango ya kan yanke hukunci mai tsauri, ko shakka babu idan har hakin ta ya cimma ruwa ya kori Zainab, mijin ta ya sami nama har gida, tsaf kame ta zai yi yayi gaba ko ba komai sa dan farfado.

    Bayan fitowar Rahila Hansai ke tambayar ta dalilin dadewar ta a bukkar, tare da mata kashedi ta ce dai baki ta saki baki ta na ma Kado zance da Hausa ba, in haka ne ta kuka da kan ta. Cikin nuna kyamkayami ta ce

    “Tir Allah wadar na ka ya lalace! Ina ni ina Kado maras daraja kamar wannan dai?”

    Hansai na jinjina kai ta ce

    “Gwara dai, babu ruwan ki da ita”

    Zainab kuwa Raliya na fita ta aikata shawarar da aka bata. Shudin rigar ta damammiya ta saka, tare da bumshort din ta shi ma shudi, komai ya fitu zanzan duk da ramar da ta yi. Dan mitsitsin mayafi daya daga cikin doguwar rigar ta ta daura, dan shi kadai ya rage mata sauran duk tayi tutu akai.

    Cikin annushuwan abin da ta ke shirin yi ta sa kai ta fito, wato ba Hansai da sauran jama’ar gidan ba, hatta Rahila da ta bata shawarar sai da ta bude baki cikin al’ajabi.

  • Auren Shehu Book 2 Page 3

    Auren Shehu Book 2 Page 3

    *Khadija Sidi*
    Auren Shehu 2

    3

     

    Allah yayi dare gari ya waye, carar zakara tare da kukan shanu, gami da guje guje da ihu da yara ke yi ne ya sanya Zainab sanya hannayen ta bisa kunnuwan ta, tare da runtse idanu, ga wani zugin azama da take ji a kafafun ta, haka kuma kan ta ya mata nauyi. Tun tana jin komai tamkar cikin mafarki, har ya fi karfin kunnuwan ta ya kai ga sanya ta bude idanu a hankali. Maimakon ta ga silin da fanka sai ganin karare ta yi jere reras, idanun ta ta rufe a karo na biyu ta na mai fatan farkawa daga mafarkin da ta ke. Ko da ta sake budewa ta ga dai har lokacin rufin kara idanun ta ke gane mata ta shi zaune a firgice ta na mai bin bukkar da idanu, bukka ce maidaidaciya wacce aka gina da jar kasa mai dauke da yayin ciyawa da rufin kara. A kideme ta kai kallan ta ga in da ta ke kwance, sai a sannan ta lura da gadon kara mai dauke da matacciyar katifar da ta ke zaune kai. A hankali ta ke karewa bukkar kallo tundaga ledar da ke shimfide kasan bukkar, har zuwa koren akwaitin karfe da ke aje gefe kusa da katan kwaryar da aka rufe da wani fefe, sai butoci guda biyu, na roba da na karfe.

    “Mafarki na ke!”

    Cewar Zainab ta na mai duban kayan da ke jikin ta, sam ta kasa tuna sanda ta sanya shi, abun da za ta tuna kadai shi ne sanda ta ke karatu cikin dare ba kayan ba ne jikin ta. Ta na jinjina kai ta kara fadin

    “Da na gama karatu bacci ya sace ni, shi ne na ke mafarki! Da kabari kato ake yin shi da sai na ce mutuwa na yi, bari dai na koma bacci ko Allah zai sa na farka!”

    Ta na maganar ne yayinda ta koma ta kwanta tare da rufe idanun ta. Jim kadan taurin gadon karen ya dame ta, haka ma hayaniyar yara da ta ke jiyowa daga waje ya sa duk yanda taso ta koma bacci ko Allah ya sa ta tashi ya gagara. Tsaki ta ja ta na mai tashi da sauri da niyar ta fita ta tsawatarwa ma su hayaniyar, ko da ta taka kafarta wani raradi ne ya ziyarci kwakwalwar ta har sai da ta koma ta zauna da sauri tana fadin

    “Wayyoo Dady!”

    Sai a sannan ta lura da yanayin kumburi da kafafun ta su ka yi. Hakan ne ya karasa ta tsorata da halin da ta tsinci kan ta ciki. A haka ta yi karfin hali ta tashi ta na mai takawa da kyar wanda duk sanda ta taka sai ta cije lebe har ta kai ga assabarin da aka saka bakin kofar daki, hannun ta biyu ta saka ta daga shi nan ta yi tozali da abin da tun da ta zo duniya ba ta taba gani ba, kanta ya zuye ya na mai sarawa ganin bukkai ba adadi, gabas da yamma kudu da arewa, Rugace ta gargajiya tsantsa in da jama’ar wajan mata da yara ke kai kawo cikin kwanciyar hankali.

    Matan sanye da rigar saki irin na fulani mai hade da zani, in da wasu su ka sanya fari, wasun su shudi ne jikin su, duk da akwai dankwali kan su, sun saki jiki rabashe rabashe su na hidimar su, daga mai share na su bangaran bukkar, sai mai kwasar manshanu daga cikin kwaryar nonon da ta tatso tare da taimakon yara mata guda hudu wanda ba su fi shekara goma sha uku ba, can gefe kuwa mata ne guda shida wanda dudu ba za su haura shekara ishirin ba amma gaba daya cikin su ya sake saboda wahala, musammam kirgin su wanda ya ya kwanta sharkaf kamar tsumma, sun zage dantse wajan dakan geron fura. Kusa da su mata biyu ne zaune daga gani ka san kishiyoyi ne, suna cin abinci hannu baka hannu kwarya, daya daga cikin su dauke da yaro akan cinya ta tana ba shi nonan da tsabagen yanda ya kwanta kai ka ce tsumma ne. Daga can gefe kuwa tsoffine guda biyu zaune suna koyawa yara mata guda biyu da ke zaune gaban su sakar riga, wanda za su kimanin shekara goma. Sai kuma yara maza da ke wasan langa sun yi kacaca tsabagen wasan bazan da su ke yi cikin kasa. Sai kuma

    Yaran ne su ka fara ganin Zainab wacce ta saki baki da hanci ta na kallan sarautar Allah. Shirun da yaran su ka yi ya ja hankalin iyayen su ka ankare da Zainab. Kamar yanda ta bude baki ta na kallan su haka su ma su ka bude baki su na kallan ta cike da mamaki. Sun ji labarin Shehu ya dawo da Kado Rugar Shehu, wanda har aka mu su kashedin kada wanda ya yarda yayi wani yare cikin Rugar face fulatanci, musammam ga Kado, Amma sam ba su taba tunanin irin wannan kadon Shehun su ya kawo Ruga ba.

    Kallon Zainab su ke tun daga dankwalin da ke kan ta, zuwa doguwar riga mara hannu da ke sanye jikin ta, surar Zainab, da kuma yanayin fatar ta da ya fita daban, duk da yawancin su farare ne, ita baka ce amma yanda fatar Zainab ya ke subul subul ya na sheki kadai abin kallo ne.

    Tuni su ka fara kuskus a junan su, in da yara su sa tafi suna fadin

    “Kado! Kado! Kado”

    Hakan ne ya sanya Zainab sakin assabarin da sauri cikin faduwar gaba, ta na dingishi jikin ta har rawa ya ke ta komo cikin bukkar. Cikin yanayin tashin hankali ta ke kara duban bukkar, gani ta ke kamar za ta ga wata alama da zai bayyana mata halin dimuwar da ta tsinci kan ta ciki.

    Ganin jikin wani abu kamar akwaitin ta leko ta karkashin gado ya sanya Zainab ta karasa gaban gadon da dingishi, dan gaba daya ji tayi zafin kafar ya dena damun ta. Cikin zafin nama ta janyo akwatin, ganin nata ne da gaske ta ji wani dan sanyi cikin ranta yayinda ta bude da sauri ta na mai mamakin yanda aka yi akwaitin ya je in da ta ganshi ta zuge zip din akwatin, haka kuma kayan ta da ke ciki ya bata mamaki dan kuwa ba za ta iya tuna sanda ta jera kayan cikin akwatin ba.

    Ciki ta yi kacibus da wayar ta, da murnar ta ta dauko wayar, hannu na rawa ta kunna ganin a kashe ta ke. Allah Allah ta ke ya gama kunnuwa ta samu ta kira waya ko Allah ya sa ta sami mafita, amma ko da wayar ta kunnu ta shiga cikin wajan kira sai taga anbuga mata waya a adadi, kuma duka miskul ne, kiran Ammy ya fi sau goma, haka ma na Falmat da sauran yan ajin su. Sakon waya kuwa su ma ga su nan birjik.

    Jin wayar na kugin neman chaji ne ya sa Zainab dena duba kira da sakonnin da aka tura mata, ta shiga kokarin kiran Ammy kafin wayar ta mutu, Nan ma wani tashin hankali ne ya ziyarci idanun ta, domin kuwa wayar nunawa ta yi ba za ta iya kiran kowa ba sanadiyar rashin sabis, haka kuma wajan da ke nuna alamar sabis a wayar ma ya dauke gaba daya, a sannan Zainab ta dada jaddada kalmar ‘babu sarki sai Allah’

    Zufa na ketowa daga goshin ta rufe akwatin, hannun ta ruke da wayar ta tashi tsaye ta na dingisawa ta sanya silfas din da ke aje kusa da akwatin na ta, ta ja akwatin yayinda ta bude assabari ta fito waje, cak ta tsaya ganin yanda yaran nan da iyayan su duka su ka baro abin da su ke, su ka yi da’ira bakin kofar bukkar Shehu kamar masu jiran tsammani.

    Babban abin da ya kara tsorata Zainab shi ne yanda su ka karu dan kuwa har na gona sai da yaran nan su ka je su ka kira su zo su ka ga Kado a dakin Shehu. Zainab na mai ja da baya cikin dakiya da rashin nuna tsoro ta ce

    “Ban san ko su waye ba! Ban san wata duniya na ke ba! Ban kuma damu da na sani ba! Roko na daya dan Allah….ku nuna min hanyar da zan koma tawa duniyar! Kada ku cutar da ni…..”

    Inda Iyayen yara su ka zubawa Zainab Idanu ba tare da sun tanka mata ba, yaran kuwa matsawa su ka yi kusa da ita suna kokarin taba akwatin ta, Zainab ta matsar da shi cike da kyamkayamin yara, ba ta ankara ba daya daga cikin yaran ya kai hannun sa kan wayar da ta har ya na taba hannun ta, cikin tsawa Zainab ta furta

    “Stay away from me stupid boy kawai mara kunya da tarbiya! Sai na ci uban ka wallahi!!!!”

    Yaro yayi baya da sauri haka ma sauran yan uwan sa, wanda daga baya su ka sanya dariya su na mai tafa hannu sanadiyar karar rashin chajin da wayar Zainab ta yi ta na mai kawo wuta. Zainab na girgiza kai ta ce

    “Innalillahi wainnailaihi rajiun!”

    Ta na ja akwaitin ta ta nufo iyayen yaran in da su kuma suka fara ja da baya, yara kuma ba su fasa shafa akwatin Zainab ba, inda ta ke kokarin hana su ta hanyar jijjiga akwaitin, ce mu su ta ke

    “Dan Allah ku taimaka, ku min magana ko na sami sauki”

    Ga mamakin ta sai ji tayi sun fara mata magana amma da fulatanci, a fusace Zainab ta ce

    “Dallah ku yi min hausa ba na jin yaren da ku ke min! Sokwaye kawai!”

    Maimakon ta ji hausan da ta ke bukatar ji, sai ma dada yara mata su ke cikin yaran fillo. Hakan ya sa Zainab fusata, ta na jan akwaitin yayinda ta ke dingisawa ta bi hanyar da ta ji ta kwanta mata ta na tafe yara na biye da ita suna tafa hannun ganin yanda Zainab ke jan akwaitin ta mai taya ne ya fi burgesu, tafi su ke suna fadin

    “Kado! Kado! Kado! Kado”

    Haka kuma masu kiriniyar cikin su ba su fasa kokarin taba akwati da wayar Zainab ba, haka su ka mayar da ita tamkar zararriya yayinda hawayen bakin ciki ya cika fal idanun ta. Fadi ta ke

    “Madness! Mad people everywhere! Wallahi zan ci uban ku! Shegu ‘ya’yan asara!”

     

    Usman kuwa tun sassafe ya tafi fadar shi da ke can gefan bukkokin Rugar Shehu. Zaune ya ke da dattawan gari da kuma matasa, kasancewar shi ne ranar zaman fada na farko tun tafiyar Usman ya sanya babu wanda ya je kiwo ko gona, kowa ya hallacci zaman. Maganar Zainab kowa ke son ji daga bakin Zainab, Amma shakkar Usman ya sa su kasa bude baki su tambaye shi.

    Zaune su ke kan tabarma karkashin katuwar bishiyar mangaro da ta yi mu su lema, Usman sanye cikin farin yadi da farin rawani wanda shi ya banbantashi da sauran jama’a da ke sanye da kayan saki, a matsayin shi na Shehu.

    Ana tattaunawa ne akan sabbin tsari da dokokin da Usman ya kawo wanda za su shafe wanda su ke yi a da, sun hada da wajabta sanya mayafi ga duk wata mace baliga, dena shiga sassan da ba na iyalin ka ba kai tsaye ba tare da neman iso ba, dena koyar da karatun surkulle in da za a musanya shi da karatun qur’ani zalla.

    Tun daga nesa ya hango ta tafe, yara da iyayen su biye da ita, haka shi ma Muhammadu Bello wanda ke zaune gefan Usman ta hannun dama ya hango ta, tun daren jiya ya ke fargaban tashin Zainab, ilekuwa sai ga abin da ya ke tsoro na faruwa. Usman na mai aje takardar da ke hannun shi ya tsaya cak yana tsimayin karasowar ta, haka ma sauran yan fada wanda su ka lura da inda hankalin Shehun na su ya tafi, su ma su ka zubawa sarautar Allah idanu yayinda Zainab ke dada matsowa gare su.

    Tun da ta hango mutane zaune zuciyar ta ke Allah Allah ta karasa gaban su kila ta samu masu hankali ciki, idan har ta damu da zugin azabar da kafarta ta ke mata, ba ta nuna ba, sai dai dinkishin da take yi ne zai tabbatar da azabar da ta ke ciki. Ganin wani zaune tsakiyar mutanen, da kuma yanda shigar sa ta banbanta da na su ya tabbatar ma Zainab da shi ne shugaban Rugar, cikin fatan neman doki ta karasa. Zuciyar ta daya ta fara kokarin kutsawa ta cikin tarin mazan domin karasawa ga Shehu ta na fadin

    “Ku matsa dallah! Malam matsa dallah!”

    Duk da ba dukanninsu ne su ka fahimci abinda ta ke fada ba, ganin yanda ta tasar mu su da sauri su ka dara mata hanya, suna mai binta da kallo cike da mamaki har ta kai ga gaban Usman, idanun ta kan yaran da tun da su ka iso gaban Usman kowa ya nutsu kamar ba su ba ne su ke mata tafin atile ba, Zainab ta ce

    “Kai ne shugaban wannan shedanun yaran da mahaukatan Iyayen su…..”

    Juyowa da ta yi ta kalli Usman wanda lafazan Zainab ba karamin tunzurashi yayi ba, ya tashi tsaye haka ma sauran yan fada su ka yi yunkurin tashi amma ya musu alama da hannu da su zauna. Zainab na girgiza kai ta ke nuna shi da dan yatsa, tsayin shi, fadin shi, da idanun shi ne ya kara tabbatar mata da Usman din ne, Abu na farko da ya tsirga zuciyar ta shi ne zaton ta ya tabbata, Usman ya cika dan garkuwa da mutane, gashi ya dauko ta duk da ta kasa tuna yanda aka yi . Cikin faduwar gaba ta saki akwatin hannun ta yayinda ta zube kasa, ta zauna dirshen ta na duban kasa tamkar mai nazari.

    Yanda Zainab ta firgita da ganin shi, da kuma yanayin da ganin na shi ya sanya Zainab ciki ba karamin faranta ran Usman yayi ba dan a tunanin shi ta karaya ne. Jin Zainab ta furta

    “Ya aka yi ka kawo ni nan? Menene dalilin ka na kawo ni nan?”

    Usman ya tsaya ya na duban ta kamar yanda sauran jama’ar su ka zuba mata Ido. Ganin be da niyar amsa mata ta tashi a fusace dan masifa ma mancewa ta yi da kafar ta, sai da ta taka kafar ta cije lebe cike da azaba, ta na dingisawa ta karasa gaban Usman hannu a kugu take magana cike da tsiwa

    “Dan ka na dan garkuwa da mutane ba wai zanji tsoran ka ba ne! Tun ranar farko da na dora idanu kan ka na san kai wanene! Dady ka yaudara har ka masa rufa ido ya kasa gane kalar ka! Haka Anty Sauda da Ammy su ka ki yarda da ni akan a min katangar karfe tsakanina da mugu irin ka! Nawa ka ke bukata? Nawa ka ke bukata ka mayar da ni gidan mu?? matsiyaci kawai!”

     

    Ganin yanda Zainab ke yiwa Shehun su magana cikin tsawa da tsiwa ne ya sa matasa tashi tsaye cikin fushi suna mai yiwa Zainab ihu, da harshen fulatanci su ke fadin

    “Karyar ki ta sha karya kado! Ki tuba ko kuwa muna tasar miki da bugu”

    Ganin haka Zainab ta yi baya a tsorace kamar mai shirin ranta a na kare. Usman ya daka mu su tsawa cikin harshen fulatanci, ya ce

    “Kada ku kuskura! Mata ta ce! Ni kadai na ke da ikon hukunta ta!”

    Gaba daya su ka runsunar da kai sannan su ka koma wajan zaman su suka zauna, hakan ne ya bawa Zainab damar cigaba da tsiwa duk da cikin ranta ta gama tsorata da Usman, tsoran ne ba ta san nuna masa gudun kar hakan ya bashi damar cutar da ita, cikin karfin hali ta furta
    “Ihun ku na banza ne dan ba ku bani tsora! Ku tambayi dan uwan ku ku ji yanda ya sha dakyar hannun sojoji!”

    Usman ya kai kallan sa ga Muhammadu Bello, wanda ya kawar da kai gefe yayainda ya tuna kashin da ya sha a barikin soja. Cikin danne zuciya Usman ya mayar da kallan sa ga Zainab, wacce ba ta gushe ba ta cigaba da fadin

    “Wallahi tun kafin na sabar maka ina mai baka umarnin ka yi duk yanda ka yi na wayi gari a nan ka mayar da ni makaranta! ba na san iskanci ban da lokacin batawa jarabawa na ke Idan ba haka ba sai na lahira ya fi ka jin dadi, kai ba kai ba har wa’annan yen koran na ka”

    Ta karasa maganar ta na mai nuna jama’ar wajan da dan yatsa.

    Cike da isa Usman ya koma wajan zaman shi ya zauna kamar ba da shi Zainab ta ke magana ba. Daya daga cikin dattijawan ne ya kada baki cikin harshen fulatanci ya ce

    “Shehu ka gafarce ni, wannan mata taka sam ba ta da tarbiya, ba ka tunanin zaman ta a wannan Ruga za ta iya lalala ta mana tarbiyar yaran mu da matan mu?”

    Sauran dattawa su ka goyi bayan shi ta hanyar jinjina kai. Wani ya kara da

    “Shehu duk matan da ke Rugar nan, ga ‘ya’yan mu amma ka rasa wacce za ka aura sai Kado? Wacce ba ta san darajar Shehu ba bare na al’ada ba? Ji fa yanda ta tsaya kerere gaban mu muna dattawa, ba kunya bare tarbiya”

    Shehu na murmushi ya mayar musu da amsa cikin hausa ya ce

    “Ba a san rai na aka daura min ita ba, sadakar ta mahaifin ta ya bani! Tabbas ba ta kai darajar matan Rugar Shehu ba, dan haka kada ku damu tamkar baiwa ta ke a Rugar nan”

    Yanda Zainab ta kai hannu baki ta na kallan shi tamkar wacce ta ke shirin burma masa wuka, ya sa Usman canza harshe, dama yayi hausan ne saboda ta san abin da ya ke fada, ya na murmushi yayinda mazan wajan daga samari har dattawa ke kallan Zainab cike da mamaki, matan wajan kuwa dariya su ka sa bayan Usman ya dada maimaita musu cewa sadakar Zainab aka bashi, haka kuma ba takai matan rugar su daraja ba. Cikin ihu kamar mai shirun rufe shi da duka ta ke fadin

    “Ka yi hausa mana! Idan ba munafunci ba ka yi yaran da na ke ji! Ni ba sadaka ba ce! Ba zan taba zama matar ka ba! Ni ba baiwar ku bace! Bloody fool! Ka mayar da ni na ce!”

    Hankali kwance Usman ya ce

    “Ni na kawo ki nan? Ko kin ga sanda na dauko ki? Ki tuna yanda aka yi ki ka zo sai ki koma da kan ki, matukar ba haka ba ki shirya zama karkashi na a matsayayin miji ke kuma baiwa ta…….”

    “Ba za ka taba zama miji gare ni ba! Uban kuturu yayi kadan! Ni ce baiwar ta ka? Ka san dawa ka ke kuwa? Da na zauna karkashin ka gwara na kwanta kabari!”

    Ta katse shi a fusace, ta na mai daukar akwaitin ta ta furta

    “Fine zan nemi hanya ta da kai na, Amma dukkan ku ku kuka da kan ku! Sai kun dandana gudar ku!”
    Ta fara jan akwaitin ta, wayar ta dake ta kukan neman chaji ta duba ko alamar sabis ya dawo, fadi ta ke

    “Wawaye jahilai kawai! no wonder aka ce a guji iskancin bakauye! Kun ci sa’a network di na ya dauke da ban ma tsaya musayar magana da almajirai irin ku ba, ka yi da diyar halak”

    Ko da ta karasa wajan yara da iyayen su mata, sai su ka ki dara mata hanya, a fusace ta ce

    “Dallah ku matsa min na wuce! Duk karnin manshanu ku ke da warin rana! Ga warin talauci! Kai wannan masifa har ina! Kazamai kawai!”

    Ganin da gaske ba su da niyar matsawa ya sanya ta juya ta kalli Usman

    “ka fada mu su su bani hanya ko na ci kaniyar su wallahi!”
    Usman ya kawar da kai gefe ba tare da ya tanka ba, Bello ne ya taso ya ce da mata da yaran su bata hanya ta wuce cikin harshen fulatanci sannan su ka buda mata hanya, sai a sannan Zainab ta gan shi da kyau, ta gane shi ne kanin Usman da aka kamo. Ta na duban Bello ta ce

    “Halan ba ka bashi labarin kashin da ka sha ba ne shi ya sa be daddara ba! Toh tun wuri ka masa bayani idan ma giyar wake ya sha gwara ya wattsake! Sakakkaru kawai!”

    Tana gama maganar ta ja akwaitin ta. Bata kula da kugin yunwa da cikin ta ya ke mata ba, bare ta tuna da sallar asubahi da ke kan ya, ta na takawa da kyar ta doshi wata yar siririyar hanya da take tunanin shi zai fitar da ita hanyar da zai sada ta ga titin barin Rugar Shehu, nan kuwa bata san dokar daji ta kara nufa ba. da sauri Bello ya dawo wajan Usman ya ce

    “Ta tafi fa Shehu, hanyar da ta dosa hanya ce da zai kara batar da ita cikin dokar daji, ka ga yanda ta ke tafiya da kyar, gashi akwai hatsari sosai cikin dajin kasan bata daya daga cikin mu, halittun dajin ba su san da zaman ta ba kada ta je ta hakala, ba za ka dakatar da ita ba?”

    Usman na duban mata da yara ya ce kowa ya koma harkokin sa, haka kuma ya gyara zama in da ya ba da umarnin su cigaba da tattauna abin da su ke tattaunawa kafin zuwan Zainab. Ganin haka Bello ya san Usman be da niyar amsa masa, dan haka shi ma ya koma wajan zaman sa, zuciyar na da tunanin dangantakar da ke tsakanin Zainab da Shehun su, da kuma halin da Zainab za ta iya shiga cikin dokar daji.

     

  • Auren Shehu Book 2 Page 11

    Auren Shehu Book 2 Page 11

    AUREN SHEHU 2

    11

    Rahila ba ta iya jiran dare yayi ba ta yi amfani da damar annushuwar da Usman ya ke ciki ta tambaye shi ko ya na da labarin in da Tanko ya ke ba tare da ta nuna dama ta san in da ya ke ba bare ma a gano ta saba satar hanya.

    Tausayin Rahila ne ya kama Usman musammam yanzu da ya san darajar soyayya, Dan haka ya ce da Muhammad Bello ya raka Rahila ta ga mijin ta, idan ma ta na so ta koma wajen shi ne gaba daya ta na iya komawa babu laifi in ya so duk sanda ta ke da bukatar shigowa Rugar Shehu neman abinci ko wata bukatar mai muhummanci kofa a bude ta ke gare ta. Ta na murna ta yi bankwana da jama’ar rugar, in da ta yiwa Zainab alkawari cewar tafiyar ta ba ya na nufin lalacewar maganar su bane, shi ne ma dalilin da ya sa za ta wajan Tanko, duk yanda su ka yi da Tanko za ta dawo ta fada mata, haka kuma za ta na kawo mata ziyara a kan kari.

    Cike da farin ciki ta riski mijin ta Tanko wanda sam be nuna farin cikin sa na ganin Rahila dauke da kaya niki niki ba, a tunanin sa Usman ya karota ne, sai da ta masa bayani tare da albishir da ta zo masa da shi sannan ya dan saki ran sa.

    Bayan Bello ya masa sallama ya juya ne Tanko ya kada baki ya ce

    “Ban so dawowar ki waje na ba, kamata yayi ki zauna can in da za ki fi ganin duk abin da ya ke faruwa, yanzu da ki ka kwaso kafa ki ka dawo uwar me za ki min a nan?”

    Cikin sosuwar rai Rahila ta furta

    “Kai kuwa Tanko ai zato na farin ciki za ka yi da zuwa na, na ga kowani namiji burin shi ya kasance tare da iyali saboda jiki da jini….”

    “Toh yar jaraba! Jaraba ce dai ta dawo da ke! Ke jikin ki ma duk ya sake amma ba za ki hakura ba?”

    Jiki sanyeye Rahila ta furta

    “Haba kai kuwa, ai sai ana son ka ake mararin ka..”

    “Toh uwar jaraba wuce mu je na mi ki abin da ki ke so, Amma dai zaman ki a nan ba zai yiyu ba! Dole ki koma Rugar Shehu!”

    Rahila ba ta yi zuciya ba ta bi bayan Tanko, sai da ya ba ta hakkin ta sannan ya shiga zayyana mata yanda za a yi su cafke daga Usman har Zainab, in da ya ce ta shedawa Zainab yanda ta yi yayi daidai, ta kara dagewa wajan samin yardar Usman, hakan ne kadai zai sa su iya cin nasara. Su ka yi sallama Tanko na farin cikin burin su ya kusa cika, dadin dadawa kuma ya kusa samun Zainab, wacce tun da ya gan ta be da mafarki sai na ta, duniyar nan kab be da buri da ya wuce samin Zainab ko da kuwa na wuni daya ne.

    Babu wanda be yi mamakin dawowar Rahila ba, cike da bakin cikin Tanko ya hana ta zama da shi, ta mu su karyar ga mata yan uwan ta me zai sa ta je can gefe ta ware kan ta, zaman cikin Rugar Shehu shi ya fi mata alkhairi. Sai da ta faki idanun matan Rugar sannan ta iske Zainab a daki, ta kwashe yanda ta yi da Tanko na game da Usman ta sheda ma ta, tare da sakon Tanko gare ta, kana ta kara da

    “Kin ga kenan yanda ki ka yi ba karamin dabara ba ne, yanzu ki dada jan shi jiki, ki sa ya yarda da ke sosai ya saki jiki da ke, kya iya nuna masa ma kin kamu da son shi…..”

    “Mtswww Allah ya sauwake na kamu da san wannan bagidaje!”

    Zainab ta katse ta a fusace. Jin haka Rahila ta dada godewa Allah, kenan hasashen ta ba daidai ba ne, Zainab dai ba ta fadama san Usman ba, gudun kar daga baya ta ba su matsala.

    ****
    Can birnin Kano kuwa anyi cigiya da shelar neman Zainab, haka kuma an bi sahunta har Mambila amma an kasa gano takamamman in da ta ke, musammam yanda Jama’ar garin su ka yi kyameme su ka nuna ba su taba ganin Usman ba bare Zainab, hatta dajin Rugar Shehu sun shiga, amma gajen hakuri ya sa su ka juyo saboda yanda dajin ke da ban so tsoro, gani su ke bil’adama ba zai iya rayuwa ciki ba.

    Kudin da Ammy ta kashe na sadaka da sauka ba adadi, tun tana sa rai ta na yarda da maganar yaran General da Anty Sauda, har ta fara karaya, ta yanke hukunci ziyartar kasa mai girma dakin Allah ta yi addua, idan har. Zainab na raye Allah ya bayyana ta, idan kuma ta mutu Allah ya nuna mata kabarin ta ko ta sami kwanciyar hankali.

    Da wannan niyya, da kuma burin ganin Halitta Ammy da Falmat su ka tashi zuwa kasa mai tsarki.

    ***

    Cikin kankanin lokaci jama’ar Rugar Shehu su ka kamu da kaunar Kado kamar yanda su ke kiran zainab, daga manyan su har zuwa yara. Ya kasance ko magana ta yi ya zaunu ba a mata musu, haka ma ta shige cikin zuciyar Usman ta zauna daram, Dan kuwa shawarar Rahila ta dauka, jan shi ta ke a jiki ta na masa soyayya irin ta yan birni musammam Zainab ta gama gogewa a wannan fanni.

    Wani sabon al’amari shi ne yanda Usman ya tashi tsaye kan Muhammad Bello, duk wata hidima da ilimin tafiya da Rugar Shehu kokari ya ke ya koyawa Bello, haka kuma ya sanya ranar auren Bello da Raqeeba wata daya kacal, Allah ya so dama Bello ya jima ya na muradin Raqeeba duk da ya fahimci ba shi ne gaban ta ba, shi din ne ya ke san maso wani sai kuma faduwa to zo daidai da zama.

    In da Bello da jama’ar Rugar Shehu aka shiga shirye shiryen biki, Amarya Raqeeba a nata bangaran bakin ciki ne ya mamaye zuciyar ta, ta na ji ta na ana gani za a daura mata Bello bayan Usman ta ke so, Kuma mahaifiyar ta ta san da haka amma ta ce ko da wasa kar da ta sake wani mahaluki ya ji zancen nan in ba haka ba sai ta tsine mata.

    Rahila ce ta fara gano halin da Raqeeba ta ke ciki ana gobe Bikin Sharon da aka shirya musammam dan auren Bello, in da sati daya ya rage auren na Bello. Rahila ta yi ta bugun cikin ta har yarinyar ta hakura ta sheda mata soyayyar da ta ke yiwa Usman, da kuma maganar mahaifiyar ta na kar ta bari kowa ya sani.

    Hakan yayiwa Rahila dadi, dan kuwa kwana biyu ko maganar Usman Zainab ba ta yi mata, ta na ganin hashashen ta dai zai kasance gaskiya, Zainab ta fara san Usman, dan haka ta yi amfani da damar ta shiryawa Raqeeba duk yanda za ta yi, sai da ta tabbatar Usman ba ya nan sannan ta tura ta dakin.

    Zainab kwance bisa gadon kara, tunanin Ammy da su Falmat ta ke, ta na mamaki ace har ta yi wata hudu wani uwa duniya amma a kasa samin wanda zai biyo sahun ta? Wani zuciyar kuma ta raya mata kila an bi ba su same ta ba ne. Kamar daga sama ta juyo sallamar Raqeeba, Zainab ta tashi zaune tare da amsa sallamar, da fara’ar ta ta bata izinin shigowa, Raqeeba ta shigo kan ta a kasa ta zube gaban Zainab.

    Cike da fara’a Zainab ta furta

    “Ha’a Amarya ta shi zauna gado mana, kya zauna a kasa?”

    Maimakon ta tashi sai ta fashe da kuka har da shassheka. Hankalin Zainab ya tashi, cikin sauri ta sauko kasa gurin Raqeeba yayinda ta shiga rarrashin ta tare da tambayar ba’asi. Da kyar ta iya lallaba Raqeeba ta yi shiru, cikin lallami da lumana Zainab ta ce da Raqeeba

    “Me ya faru? Me ya sa ki kuka haka? Auren ne ba ki so?”

    Raqeeba ta gyada mata kai alamar
    “Eh”

    “Auren dole za su mi ki?”

    Ta gyada mata kai. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani ta furta

    “Kin fadawa Usman ba kya so?”

    Ta girgiza mata kai alamar
    “Ah ah”

    “Me ya sa ba ki fada masa ba? Kin fadawa Hansai?”

    Nan ma sai ta sa mata kuka, da kyar ta samu ta yi shiru har ta sheda mata abin da maifiyar ta ta ke so. Cikin jimami Zainab ta furta

    “Shi wanda ki ka ce ki na so, wanene shi?”

    Budar bakin Raqeeba sai cewa ta yi

    “Shehu….”

    Dam! Maganar ya doki kunnan Zainab yayinda gaban ta ya yi mummunar faduwa, kishi ne ya taso ya tsaya mata kahon zuci, ba ta san sanda ta furta

    “Shehu? Usman miji na ki ke so?”

    Raqeeba ta gyada kai, ta lura sarai da halin da Zainab ta shiga kamar yanda Raheela ta ce mata zai faru, haka kuma ta ce kada ta sake ta nuna ta san abin da ta ke, dan haka Raheela ta yi burus ta kara da

    “Idan babu shi ba zan iya rayuwa ba, ya san ina san shi ba tun yau ba, Amma ya ce na auri Bello, mun san ba kya san shi, kamar yanda mu ma ya sha fada mana ba ya kaunar ki……”

    Kamar takobi haka maganar ta soki zuciyar Zainab, musammam da ta ji Raqeeba ta kara da

    “Sadakar ki aka ba shi, tsoran hukuma da kuma yanda ya ke jin dadin kwanciya da ke ya sa be mayar da ke gida ba, Amma ya ce da zarar kin gundire shi ko kuwa ki ka haife cikin da ki ke dauke da shi zai……!”

    “Shut up!”

    Zainab ta dakawa Raqeeba tsawar da sai da jikin Raqeeba ya dau rawa tsabagen firgita. Ita kan ta Zainab din jikin ta rawa ya ke saboda bacin rai, ta na mai nuna mata hanya ta ce

    “Tashi ki fita”

    Maimakon Raqeeba ta fita, sai ta yi kamar yanda Rahila ta ce ta yi duk da ta tsora ta ainun, ta na mai ruqo kafar Zainab ta furta

    “Dan Allah ki taimaka min kada ki bari Shehu ya san na mi ki wannan maganar, matukar ya san na fada mi ki ya na sawa a daure ni, koma a kar ni har lahira shiya sa ma mahaifiya ta ta haneni ga fadawa kowa, ki min rai ki taimake ni”

    Ganin yanda ta marairaice sai tausayin ta da tausayin kan ta ya kamata, lalle Raqeeba abar tausayi ce tunda har ta fada soyayyar azzalumi kamar Usman. Cikin sanyin murya ta furta

    “Na ji, ki sakar min kafa ki kuma fitar min daga daki, in dai Usman ne na kusa barin rayuwar shi har abada!”

    Jin haka Raqeeba ta tashi da sauri ta fice gudun kar Zainab ta gane shara ta take.
    Nan bakin gado Zainab ta zube, so ta ke ta yi kuka amma ta nemi hawayen ta rasa.

    “…..mun san ba kya san shi, kamar yanda mu ma ya sha fada mana ba ya kaunar ki……”

    Maganganun Raqeeba da ke yawo cikin ran Zainab kenan. Ko da ta tuna

    “Sadakar ki aka ba shi, tsoran hukuma da kuma yanda ya ke jin dadin kwanciya da ke ya sa be mayar da ke gida ba, Amma ya ce da zarar kin gundire ko kuwa ki ka haife cikin da ki ke dauke da shi zai……!”

    Ta yi saurin shafa cikin ta, nan ta ke wani tunani ya bugi kan ta, tun da tazo Rugar Shehu ba ta taba yin al’ada ba, duk da dai nata mai wuyar sha’ani ne ba kowani wata ta ke yi ba, Wani lokacin kuma ta kan yi sau biyu a wata. Haka kuma tun da ta fara sakarwa Usman jikin ta kusan kullum sai ya kusance ta, Tuni ta fashe da kuka ta na fadin

    “Allah ya isa! Allah ya isa ba zan taba yafe ma ka ba Usman duniya da lahira! Allah ya isa!”
    Babban tashin hankalin ta shi ne gaba daya ta manta zuciya ba ta da kashi, kamar yanda ta ke kokarin sace zuciyar Usman, tuni na ta zuciyar ta yi rauni, ba ta iya yin cikakken minti goma ba tare da ta yi tunanin Usman ba, haka har Allah Allah ta ke dare yayi su kebe, dama ga ta Allah yayi ta mace mai yawan bukatar mijin ta.

    Sai da ta yi mai isar ta, sannan ta share hawaye bayan ta gama yanke hukunci ta kwallawa Rahila Kira, wacce dama ta yi lamo ta na tsammanin kiran. Da saurin ta ta shigo, ganin yanda idanun Zainab ya kumbura su ka yi suntun ta fara tambayar ko lafiya. Murya shake Zainab ta furta

    “Ki ce da mijin ki Tanko na shirya tsaf, ya gaggauta kawo mafita idan ba haka ba zan yi gaban kai na!”

    Cike da munafunci Rahila ta shiga doka salati ta na tambayar Zainab shin ko menene ya faru. Zainab ta ce ita yar sako ce ta tafi ta kai sakon ta. Rahila ta amsa da toh ta fice jiki na rawa kamar wacce za ta yi tsuntsu dan sauri.

    Nan cikin gonar Bello ta wuce Usman da Bello, yanda ba ta lura da su ba haka su ma ba su ga giftawar ta ba. Musammam Bello wanda maganar Usman ta sa kan shi yayi tsawa. Cikin jinjinawa ya ke maimaita

    “Za ka bar min sarautar Rugar Shehu?”

    Usman na mai murmushi ya gyada masa kai, in da Bello ke masa kallan zararre. Zaune su ke karkashin bishiya da ta mu su lema, dukkanin su sanye cikin fararen ruguna yar shara. Bello na kallan fuskar Usman wanda tun da ya gane yanda Zainab ta ke satar kallan sa duk sanda be daura rawani ba ya dena saka rawanin gaba daya sai dai hula, Bello ya furta

    “Akan wani dalili zan gaje ka bayan kana raye?”

    “Murabus na ke so na yi”

    Usman ya ba shi amsa a takaice, ya kara da

    “Shi ya sa na ke ta sa ka a hanya, ban dawo Rugar Shehu dan na zauna ba, na dawo ne sanadiyar kiran Iya, Iya kuma ta kwanta dama mun kuma baro kabarin ta can falgore, bakin cikin haka ya sanya ni dauko Abu daga birni, na kawo ta daji dan kuwa a nawa wautar hakan ne zai sa na rama babban asarar da ta ja min, da zalincin da ta ma ka, Amma na huce yanzu Bello, ba zan iya jure ganin Abu cikin wahala haka ba, ba ta saba da rayuwa irin ta mu ba….”

    “Toh ka sake ta mana…”

    Bello ya katse shi da iya gaskiyar sa. Murmusawa Usman yayi, kana ya ce

    “Ai ko da da Allah be jarrabe ni da soyayyar Abu ba ba zan iya sakin ta ba saboda alkawari mai girma da na daukarwa mahaifin ta, bare yanzu da son ta ya bi jiki na jini da tsokana, ina san mata ta Muhamadu, ina san ta lillahi warasulihi, ba zan iya rayuwa babu Abu ba”

    Shiru ne ya biyo baya, kafin daga bisani Bello ya nisa ya ce

    “Shin ita maidakin ta ka ka ji ta bakin ta? Idan ita kuma ba ta da wannan ra’ayin fa? Shi fa kado ba shi da tabbas…”

    “Ko ban yarda da komai ba, na sheda Abu ta na kauna ta, Abu na ta na so na, daren yau zan sheda mata soyayyar da na ke mata, Zan nemi yafiyar ta akan dauko ta da na yi daga birni duk da dai ni banyi dana sanin hakan ba, Rugar Shehu shi ne tsatson soyayyar mu”

    “Yanzu Shehu akan mace za ka bar sarauta? Ka bar shanu? Ka bar yan uwa ka tai birni?”

    “In ka dauke yan uwa duka sauran abubuwan da ka lissafa na dade da barin su, sai dai wannan karan zan yi amfani da dama ta na gina gidan gona cikin birni, yanda za mu bunkasa tattalin arzikin Rugar Shehu a can birni, in Sha Allah ko ban iya yin yanda Shugaban kasa ke da hashashen kawo cigaba birni ba, zan kwantata, haka kuma zan sayar da wasu daga cikin shanu wanda su ke mallaki na domin ginawa Abu gida irin na yan birni”

    Ya kare maganar ya na murmushi yayinda ya ke ayyana irin gidan da zai gina mata cikin ran sa. Jikin Bello sanyaye ya ke duban sa, ya sha ji ana cewa asiri ba ya kama Usman, Amma ko shakka babu wanda Zainab ta yiwa Usman bakara min asiri ba ne. Cewar Bello cikin ran sa.
    Aure s

  • Auren Shehu Book 2 Page 15

    Auren Shehu Book 2 Page 15

     

    AUREN SHEHU 2

    Kamar yanda Ammy ta mata alkawari babu wanda ya kara tunkarar Zainab da maganar zubda ciki, hakan ya sa ta dan sami kwanciyar hankali, musamman da Anty Sauda ta hada na ta ya nata ta koma Maiduguri.

    Cikin sati daya Usman ya hade kayan sa, bayan ya shawo kan su kawu Iliya da kyar sun yarda ya sake barin Rugar Shehu. Ana saura kwana uku ya tafi aka daura auren Muhamad Bello da Raqeba. Iyalle ce ta karbi rukon Cangwai duk da a zahirin gaskiya sun gano ba diyar Usman ba ce, rashin Rahila da Tanko ya sanya dole su hakura su zauna da ita.
    Muhamad Bello ne da kan sa ya raka Usman har Yola gidan Alhaji Ibrahim Balla kamar yanda ya yi alkawari. Ya karbi bakwancin Usman hannu bibbiyu musammam da ya ga harkar cigaban da ya zo da shi. Cikin gidan gonar sa ya bawa Usman masauki na musammam, cewar shi zai iya zama kafin ya bude ido shi ma ya sami na shi.

    Alhaji Ibrahim Balla magidanci ne mai kimanin shekaru hamsin da biyar a duniya, matar shi daya haka kuma dan sa daya tilo kamar tsoka daya a miya, amma hakan be sa ya sangantar da dan na shi ba wanda ake kira Umar. Ya tashi da tarbiya, dattako dadin dadawa kuma ga gata, ilimi wayews da ado tamkar dawisu. Umar saurayi ne mai shekara talatin da biyar a duniya, kasancewar ya karanta health economics a Fannin digiri ya koma yayi development studies a masters ya sa ya zama shi ne jagaba wajan habbaka sana’ar mahaifin na sa, wato sana’ar gidan gona.

    Cikin kankanin lokaci Alhaji Ibrahim ya lura da halayyar Usman, da kuma amanar sa, hakan ya sa zuciyar sa kwadaita masa hada shi da dan sa Umar wanda kusan duk abin da ya shafi gidan gonar shi ke tafiyar da shi. Ga kuma ilimin Isalama da ya tabbata Usman na da shi wanda ya ke da yakinin lalle Umar zai amfana sosai, da wannan ya yi kokarin kulla abotan Usman da Umar, duk da kuwa ya san in dai aka zo fannin wayewa hali ya sha bambam.

    In da Allah ya kawo abin da sauki, sai ya hada jinin Umar da Usman, yanda ado da wayewar Umar ke burge Usman, shi kuma Usman kamala da ilimin addinin Usman ke burge shi, musamman da ya ji ya na larabcewa da wasu daga cikin abokan sana’ar su da su ke Larabawa, sannan duk wani muhadara da majalisin malamai Usman na kokarin zuwa wani lokaci har gayyatan Umar din ya ke. Kullu yaumin Umar na kokarin jan Usman jiki kamar yanda mahaifin sa ya ba shi umarnin, duk dai Usman na dan janye jikin sa ba dan komai ba sai gudun kar ya kwafsawa Umar, duk wata harka da ya shafi shiga cikin mutane sai Usman ya nemi ya janye jiki, har sai Umar yayi da gaske kafin ya yarda ya bishi. Duk wanda kuwa ya kuskure ko kallan banza ne ya yiwa Usman lalle kuwa a ga fushin Umar.

    ***

    Hutun Halitta wacce ita ce mai debewa Zainab kewa ya kare, Sudais ya ce lalle ta hado nata ya nata ta koma Saudi ba zai iya zuwa Nigeria ba kamar yanda ya mata alkawari ba saboda yanayin aiki da ya yi yawa.

    Da yamma likis Halitta shirye tsaf, sanye cikin bakar doguwar riga, suna tafe suna hira Zainab ta raka ta har mota in da Ammy da Falmat ke zaune suna jiran ta su kai ta Airport. Har ta zauna ta dubi Zainab wacce ke tsaye ta na duban ta. Sanye da hijab ruwan dorawa da ya kai mata har kasa, gaba daya ta sauya ba walwala ba farin ciki, kullum cikin damuwa ta ke har ta kai ya fara nunawa a jikin ta.

    “Dan Allah Yakura ki rage damuwa ko dan cikin da ki ke dauke da shi”

    Cewar Halitta cike da damuwa. Ta kara da.

    “Zan mi ki addua in Sha Allah……”

    “Idan har irin adduar da kuka min ne har Allah ya sa na dawo gidan ba na so, da ba ku min ba da yanzu ina tare da miji na…”

    Jin haka Ammy ta kauda kai gefe. Falmat cikin ran ta cewa ta yi ‘aha dama zancen kenan Yakura ta zama sai ka ce mayya!”

    “In Sha Allah zan mi ki adduar mafi alkhairi a rayuwar ki”

    Cewar Halitta. Zainab ta kada baki ta ce

    “Usman ne mafi alkhairi Halitta”

    Halitta na mai murmushin yake ta furta

    “In dai shi ne toh Allah zai warware komai Yakura, bi’izinllah”

    “Allahumma amen, Allah ya tsare ya sauke ku lafiya”

    “Ameen ameen, ma yi chatting, ko da yake ke fa ko wayar ma ba ki da shi bare na chat, ki taimake ni Yakura, kira daga Saudi tsadi, ki samu yar waya sai mu ke gaisuwa ta social network, ki taimaka”

    Zainab na murmushi ta bata amsa da

    “Yar ana ce zai yi tunani akai”

    Da haka su ka yi sallama jikin kowa a sanyaye.

    ***

    Watannin Usman uku suna kasuwanci tare da Umar Balla. Hidimar da ke gaban sa be sa ya manta Zainab daidai da sakan daya ba, da ita ya ke tashi da ita ya ke kwanciya cikin ran sa. Wani sa’in sai yayi da gaske ya ke iya jure rashin ta. Har Umar ya kai ga ganewa akwai damuwar da ke tattare da shi, amma ko da ya tambaye shi dalili ce masa yayi babu komai kawai yakan dan yi tuntuntuni ne akan Rugar Shehu da kuma yanda zai bunkasa Rugar a sami cigaba.
    Tafe su ke cikin motar Umar, kan hanyar dawowar su daga Mambila in da su ka je su ka yi cinikin shanu. Umar wanda ya ke baki, be da tsayi sosai amma kuma ba a kira shi gajere ba, haka kuma kyawun sa na ba yabo ba fallasa, sanye ya ke da kanana kaya, bakin wando da jar riga mai gajeran hannu. Usman da ke gefan sa sanye da wannan shigar ta sa da ya saba, riga yar shara, da rawanin sa da ya koma yi tun bayan tafiyar Zainab. Hankalin Umar kan kwalta ya furta

    “Ni kuwa da za ka bi shawara ta Usman da fili za ka siya babba ko da kuwa a wajan, ka gina gidaje ciki in ya so ka kwaso duka jama’ar Rugar ta ka, ku yi zaman ku ciki ”

    Cikin kaguwa Usman ya furta

    “Shin ka na ganin haka me yiwuwa ne? Kai mutane na fa ba kamar na ku ba ne, zaman bukka ya fiye mu su zaman binni da wahalar ta, Ni dai da ka ganni nan ni ke da kwadayin birni…”

    Dariya Umar yayi jin furucin Usman, dan kuwa ya san har ga Allah ya sosa masa in da ya ke masa kyakayi. Kana ya ce

    “Ina ce so kake ka bunkasa Rugar ta ku? Ka na tunanin wannan tsarin da Shugaban kasa ya ke so ya aiwatar mai yiyuwa ne? Ko ba ga yanda kudanci da wasu bangare na arewacin kasar nan ke sukar tsarin ba? Ka ga wannan Ruga settlement din ba abu ne mai faruwa nan kusa ba, Amma kai a karan kanka za ka iya kwatantawa ta ka Rugar, tun da babu laifi Allah ya ba ku arziki na dabbobi kwarai da gaske, da kuma taimakon yan kasuwa na nan Nigeria da kuma na kasashen waje wanda za su sa hannun jari a tada hanyar arziki mai girma, ina mai tabbatar maka za ka shahara kwarai”

    “Kai wannan maganar ta ka ya sa ni tunani Umari, wa ya ga jama’ar Rugar Shehu kusa da birne!”

    Umar na dariya ya furta

    “Kai ba ma kusa da birni ba, idan ma cikin birni ka ke so ka kawo su ai ba abu ba ne mai wuya, dama naira ce wuyar, kuma Allah ya hore, ana nan ana nan sai ka aure matar birni, dama ana ta min maganar ka, ana ta kawo sakon gaisuwa fa”

    Gaban Usman ne ya fadi, yayinda da Zainab ta fado zuciyar sa. Cikin kokarin waskewa da maganar aure ya furta

    “Wace matar birni ce za ta so bagidaje dan kauye Irina? Ai mata sun fi son wayayyan mutum”

    Umar na duban sa ta wutsiyar ido ya ce

    “Wai kullum aka yi magana sai ka ke kawo wayewa wayewa wayewa! Wai kai wata irin wayewa ka ke magana?”
    Zuciyar Usman daya ya furta

    “Wayewa ai shi ne boko, ka ga kai da ka ke dan boko Umari hatta shigar ka daban ta ke, yanayin ka daban kai komai na ka ya fita daban ba kamar ni dan daji dan Ruga ba, wanda ko aji ban taba shiga ba bare a kai ga jami’a, ko zo a kashe ka da turanci ba ban sani ba….”

    “Da larabci fa?”
    Umar ya katse shi ya na mai take mota ganin ya sami sararin hanya.

    “Ah wannan Alhamdulillah ai har labari sai na baka da shi”

    Kai Umari ya gyada, be gushe ba ya kara da

    “Wannan larabcin da ka iya ya fi turancin da ka ke ihun ba ka iya ba, ilimin da ke da shi na addini ya fi wannan bokon da ka ke tunanin shi ne wayewa, da ilimin boko shi ne wayewa da tun lokacin manzo (SAW) za a fara boko, addinin islama shi ne wayewa, ba ka taba yin bokon ba ne, da ka yi da za ka gane cewa komai da ake koyarwa a bokon musammam na bangaran kimiyya akwai su cikin alqur’ani da hadisin Manzo (SAW)”

    Usman na mai gyada kai ya furta
    “Allahu akbar”
    Umar ya kara da

    “Wannan rudun da ka ke gani na duniya, ba wayewa ba ne, wannan ba komai ba ne illa zamananci, ka ga wannan shiga tawa da ka ke gani ya ke burge ka, nan da shekaru masu zuwa sai ka ga ana kiran sa da old fashion, ma’ana an bar yayin sa, zamanin sa ya wuce, Allah shi ne zamani Usmanu! Haka kuma mutane nawa ne ga su yan birnin kuma yan boko amma hakan be sa sun kasa shirme ko rashin azanci a rayuwar su ba? Soboda sun yiwa wayewa fahimta daban har ya kai su ga halaka. Haka kuma ita jami’a da ka ke gani, waje ne koyan rayuwa, waje ne in da mutane iri iri daga sassa daban daban ke taruwa domin koyan ilimin boko, toh amma daga karshe ba ilimin kadai ake koya ba, har da dabi’u na dan Adam, mai kyau da mara kyau sai dai wanda yayi dace, da kuwa ilimin addini shi ma ya na da gurbi irin yanda boko ya samu a zukatar bil adama da kuwa boko ya zama ba koman komai ba”

    Umar ya fadi ya na mai kallan Usman. Ya kara da

    “Ai kai ma wayayye na Usmanu, in kuma ka na so ne ka zama dan zamani zan maisheka dan zamani na koya maka shigar yar birni, Amma fa idan matan birni su ka sako ka gaba ba ruwa na”

    Ya karasa maganar ya na dariya. Shi ma Usman din dariyar ya ke, nan kuwa be san Umar har zuciyar sa ya ke magana ba, dan kuwa daga lokacin ya sha alwashin wanke Usman tas ya mayar da shi dan zamani kuma dan birni.

    *****
    Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, in da Zainab ke renon cikin Usman, tare da fama da son shi da tsananin kewar sa, har ta kai in ta yi sujjada ta kan roki Allah ya cire mata soyayyar Usman daga zuciyar ta, amma sai ya zama tamakar abin ma dada karuwa ya ke, dan haka sai ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido. Halitta ce ta dage sai da Zainab ta sami waya, amma iyakar ta WhatsApp, bayan shi ba ta wani social network. Zainab the slay Mama ta zama salihar Dady a zahiri da badini, haka kuma ta na kokarin yiwa Malam addua sosai,

    Bangaran Usman kuwa yanda Umar ya dage akan mayar da shi dan zamani ya sanya shi mika wuya wajan daukan darasi, ta suturun Usman ya fara, sai da ya tabbatar Usman ya ba da dukkanin kayan sa na ruga sannan tasa shi gaba ya masa ordering shaddu getzner na gani na fada daga SAFFAD Fabrics and more na Hajiya Safiyyah Ummu abdoul, . Rabin shaddu farare ne guda ishirin, sai kuma shudi, ruwan kwai, da kalar toka guda goma. Haka kuma ga material na maza da su boyel. Kanana kaya da takalma ne ya sa ka abokin sa mai shigo da kaya da Uk ya kawo masa. Tun Usman na kokawa akan kudin da Umar ya ke sa shi kashewa, sai gashi shi ma ya zo ya na alfahari da su bayan isowar kayan ya ga kyan su.

    Dinki irin na zamani wanda yawanci irin na Umar din ne ya sa aka yiwa Usman, kai hatta roll on sai da Umar ya koyawa Usman yanda ake amfani da shi. A hankali ya ke kokarin fito da Usman gari duk da ba karamin fama ya ke sha da shi ba wajan saka kananan kaya, sai Usman ya ce masa shi wallahi ya na jin kan sa tamkar tsirara musammam idan rigar mai karamin hannu ce. Ran da kayan sa na Uk su ka iso ranar Umar ya zo har gidan gona ta tasa Usman a gaba lalle ya saka daya daga cikin su ya fito ya same shi ya na jiran sa cikin mota.

    Umar na zaune cikin mota har ya fara tunanin sake komawa ciki ya taso kyeyar abokin na sa, sai gashi ya fito cikin kananan kaya, shudin riga mai haske, da shudin wando mai duhu, shi kan sa Umar be san sanda ya saka ihu ba ganin yanda kayan ya karbi Usman kwarai, fadi ya ke

    “Yo mutumina! Lalle yau za mu dau magana!”

    Cike da kunya Usman ya karasa gaban sa, sai a sannan Umar ya lura da silifas ruwan dorawa da ke kafar Usman. Ya na dariya har da kwarewa ya furta

    “Toh Malam Shehu! Wannan silifas da ka sha haka ina zuwa?”

    Usman na mai kallan kafar sa, da iya gaskiyar sa ya furta

    “Yo menene toh? Silifa din ma ba ni sawa?”

    “Ka ga wannan magana ta ka sai ka canza Alhaji, kar a ga gaye iya gaye amma in ya bude baki sai aji maganar yar Rugar Shehu”
    Usman ya kai masa duka, Umar ya kauce ya na dariya, ya kara da

    “Haka kuma tsakanin ka da silifas dan Usumanu sai dai a bandaki, wallahi babu in da zan kara zuwa da kai da silafas kafar ka!”

    “Sai na yi zamana! Kai ni fa da na san haka za ka uzzara min da ban ce ina san wayewar nan ba!”

    Umar na dariya ya wuce ciki ya na mai furta

    “Zamananci dai ko, na fada ma ilimin addanin musulunci shi ne wayewa, wannan da ka ke koya zamananci ne, gishirin zaman duniya”

    Usman na duban shi har ya shige ciki, cikin ran sa ya na mamakin yanda ya saba da Umar sosai, dan tun da ya ke be taba yin aminci da abota da kowa ba kamar Umar, cikin kankanin lokaci su ka saba da juna sosai kullum su na tare, haka kuma Alhamdulillah harkar gidan gona ta karbe shi, haka kuma shawarar Umar da ya bi shi ma da alama za ta bulle masa. Ya siyar da shanu fiye da dari biyu da hamsin daga cikin shanun sa, da kudin su ka yi cinikin wani katan fili duk da dai yayi wajan gari kadan amma babu laifi wajan da kwanciyar hakanli da kuma tsaro kasancewar yayi kusa da daya daga cikin check point na sojoji, in da dama nan su ka yada zango kusan na dundundin.

    Umar ya fito dauke da daya daga cikin sau cikin da aka turowa Usman. Da kyar Usman ya yarda ya saka. Haka su ka fita ya na masa mitar ya takura masa, shi fa takalmin nan ya matsa masa. Asibitin hakurin da ya ke zuwa ya kai Usman, ga mamakin sa sai gashi dentist din da su ka gani ta ce Usman ba ya bukatar wanke hakori, hakoran sa are so perfect, sai dai Umar ne ke bukata. Ko da Umar ya koka sai Usman ya murmusa kana ya ce

    “Kai ne fa Umar ka fadakar da ni cewa addinin mu shi ne wayewa, Manzo (SAW) ya ce ba dan kar ya takurawa al’umar sa ba da ya ce su dinga asuwaki kafin kowacce alwala. Ka ga ban san brush da wannan abun da ku ke shafawa kai ba, Amma na san aswaki da Manzo ya koyarda da mu, shi ya sa baki na ke da tsafta da haske”

    Umar na gyada kai ya furta

    “Hakkun ka yi gaskiya, Amma kuma wannan karan za ka kara da zamani, idan mu ka gama da asibitin nan za mu biya shopping mall mu siyo su brush da abin goge bakin ka ga sai ka kara wasai ko?”

    Darawa Usman yayi, kafin ya kara magana Umar ya kara da

    “Ka bari fa Usmanu, yanda ka zama gaye din nan sai fa mun yi da gaske, dan wallahi ba ka bina bashin rantsuwa matan da za su fara binka sai Allah, musammam ga ka da dukiya, fata na dai kada ka yi zaben tumun dare, na kuma san kai mai sani ne, ka ji tsoran Allah ka kuma roki Allah ya kare ka daga kaidin shedanun mata, ya kuma ba ka mace ta gari…..”

    “Amen summa amen”

    Cewar Usman, cikin ran sa kuwa Zainab ya ke hangowa. Tunanin ko ta cigaba da rayuwar ta yanda ta ke a da ya ratsa zuciyar sa, be san sanda ya furta

    “Innalillahi wainnailaihi rajiun! Allahumma ajirni fi masibati haza wakallifni khairan minha!”
    A tsorace Umar ke kallan sa ya na tambayar lafiya? Me ya faru. Shi kuwa Usman bakin kishi ne da ya taso ma sa ya turnuke kirjin sa ya sanya shi salati. Amsawa Umar yayi da babu komai, kawai ya tuna wani abu ne. Yayi saurin barin wajen gudun kar Umar ya gane halin da ya ke ciki, dan kuwa sirri irin na Usman ya sa har yanzu be taba bawa Umar labarin Zainab ba.

    *****
    Sanda cikin Zainab ya cika wata tara chif, ya rage saura sati biyu EDD din ta ya cika Halitta ta dawo Nigeria. Ganin yanda Zainab ta bude ta zama katuwa zama da kyar ta shi da kyar Halitta ta sako ta a gaba da tsokana, duk dai ita ma din dauke ta ke da na ta yaron cikin wata uku cif.

    Wata ranar lahadi da yamma likis, Zainab da Halitta sun dawo daga strolling, Halitta ke raka ta kusan kullum safe da yamma. Su ka tadda Anty Sauda zaune gaban Ammy ta hada kai da gwiwa ta na ta sharbar kuka. Hankalin su ba karamin tashi yayi ba dan kuwa a tunanin su ko General ne ya mutu. Muryar Halitta na rawa ta furta

    “Anty Sauda lafiya? Ammy lafiya? Wani abu ya sami Genaral ne?”

    “Ba gwara wani abu ya same shi ba da cin fuskar da ya min! Ni General zai ci Amana?”

    Jin haka Zainab ta samu waje ta zauna cike da mamaki, shin dama akwai ranar da Anty Sauda za ta kuka da General? Mutumin da ta ke ikirarin ta gama da shi ko tsinke ta aje be isa ya tsallake ba sai da izinin ta. Zainab ba ta yi mutuwar zaune ba sai da ta ji Anty Sauda ta furta

    “Wai Genaral ya rasa wacce zai auro min sai yar aiki! Da ilimi na! Da wayewa ta! Da arziki na amma ya auri yar aiki na? Wata jaka yar kauyen kayayau! Har ya na ikirarin matukar ba zan iya zama ba toh kofa bude ta ke!”

    Jikin Halitta yayi sanyi kwarai, haka ma Falmat wacce shigowar ta kenan ita ma ta tsinci maganar. Ammy kuwa ta dade da kasa magana tsabagen al’ajabi. Zainab ce kadai ta furta

    “Tooooh yar kauye fa Anty Sauda? Ki na nufin yar kauye dai kamar miji na Shehu?”
    Ta yi maganar da manufa biyu wanda in aka dauki Anty Sauda babu wanda be fahimci in da Zainab ta dosa ba, Anty Sauda ta furta

    “Irin su fa tsinannun tsintattun mage! Kuma ita ma din bafulatana ce waya sani ma ko Rugar su daya shi ne ya min shune tsinannun! Sai na yi maganin su! Wallahi bokan ta ya mata karya yanda na sha wahalar mallakar Malam sai ba ta isa ta zo da ruguje min ba! Yarinya ce fa kankanuwa! Ga ta bagidajiya! Kin san mazan nan daga na barta ta na masa girki saboda business ya dan fara hawa kai na, shi ne ta yi amfani da damar ta ta masa barbade….”

    “Assha kin ga inda kuskuren na ki ya ke Anty Sauda, wayewa da ganin ke kin isa ya sanya ki ka bari wacce ki ke tunanin bagidajiya ce kuma yar kauye ta aure mutum mai daraja kamar General! Kenan akwai lokacin da wayewar ba ta amfani…!”

    “Yakura!!!”
    Ammy ta dakawa Zainab tsawa, in da Anty Sauda ta saki baki ta na duban ta. Zainab ta dubi Ammy ta furta

    “Ammy kar ki hana ni magana! Ranar wanka ba a boye cibi! Ina ga nan Anty Sauda ta zauna ta gama kare min tatas! Har fadi ta ke ilimi na da jami’a ta be amfana min komai ba na rasa wanda zan so sai dan kauye! Da ke da na shiga jami’ar ko wayewar ita ce mizanin auna darajar dan adam ko azanci na dan adam! Ita ya aka yi ga shekarun, ga wayewar, ga arzikin ga ilimin amma ta yi sakaci irin wannan? Da wayewa, ilimin boko ko shiga jami’a shi ne mizani azancin dan Adam da wayyayu dayawa ba su halaka ba! Da yan kauye dayawa ba su cigaba ba! Wannan abun da ya faru da ke kukan kurciya ne Anty Sauda!”

    Kuka Anty Sauda ta saka, fadi ta ke

    “Ni Yakura? Ni ki ke gasawa maganganu haka? Na dade da sanin ba ki da kunya amma ban taba tunanin za ki iya shafawa idanun ki toka ki gasa min cin kashi haka ba!”

    “Yakura ki bata hakuri! Ba ki kyauta ba!”

    Cewar Ammy cikin tsawatarwa. Sai da ta yunkurin tashi da kyar, ta dubi Anty Sauda ta ce

    “Allah ya ba ki hakuri tunda Ammy ta ce na baki hakuri, Amma sam ban yi dana sanin maganar da fada mi ki ba, rayuwa dai is a circle, na dade da gane haka ina kuma fatan ke ma za ki gane”

    Ta wuce ciki ba tare da ta damu da kukan da Anty Sauda ta ke yi ba, bare fadan da Ammy ta bita da shi. Nan ta ke Anty Sauda ta ja jakar ta tace ta fasa zama gidan Ammy. Sai da su ka yi da gaske sannan ta hakura, ta ce amma Ammy ta mata tsakani da mara kunyar diyar ta. Ita kan ta Ammy mamakin yanda rayuwa ta juya ta ke, Halitta da Zainab wanda da ba sa ga maciji ne yau su ka zama tamkar aminan juna, Anty Sauda da Zainab wanda su ka saba kullawa su kunce babu wanda ya sani ne yau kuma ba sa ga maciji. Lalle kam rayuwa na da ban mamaki.

    Tun kafin EDD din Zainab ya cika, ana sauran sati guda Zainab ta tashi da nakuda, wuni daya ta yi cur ta na yi sannan Allah ya sauke ta lafiya ta haifo dan ta namiji mai kama da Shehu sak tamkar yayi kaki ya tofar. Ita kan ta Zainab da aka daga mata shi sai da gaban ta ya fadi kasancewar shi jinjiri be sa ta kasa ganin Usman a fuskar sa da komai na sa ba.

    Ko da aka miko sa hannun ta, ta na hawaye ta masa huduba ta saka masa suna Usman. Yanda ta ke yi ya sanya nurse din tambayar ta ko dai uban dan ya rasu ne? Zainab na duban Usman junior ta furta

    “Eh ya rasu tun kafin na san ina dauke da cikin dan sa, Amma gashi Allah ya kara dawo min dashi, sai dai wannan karan jini na ne, tsatso na”

    Cike da tausayawa nurse ta furta

    “Allah sarki, Allah ya ji kan sa ya kuma raya dan sa”

    Zainab ta amsa da “amen”

    Babu wanda be yi murna da haihuwar Zainab ba, hatta Anty Sauda sai da ta aje fushin ta gefe da ta ga dan da Zainab ta haifa. yaro sak uban sa, kai ka ce balarabiya ta haifo sa. Jin Zainab ta saka sunan Usman ba Malam da kowa yayi zato ba sai da aka yi dan kananan maganganu. Zainab kuwa ta ce da dai ita ta haifo kayan ta, kuma Usman ta ga daman saka masa, za kuma ta kira shi Shehu, ta ga wanda ya ke da ikon canzawa dan ta suna.

    Ranar suna aka sha shagali, Hajja Kilishi da na ta ayarin sun yiwa Ammy kara kwarai dan kuwa sai bayan suna da kwana biyu su ka tafi.
    ****

    Bangaran Usman kuwa ya na can ya na hidamar kafa Rugar Shehu cikin saban gidan gonar da ya ke ginawa sam be san an masa takwara ba. Umar ya mayar da shi dan zamani, dake dama mutum ne mai ilimin addini gashi ya hada da zamananci nan da nan ya zama goge. Kullum cikin masa tayin aure ake, abokan sana’ar su ne, mata masu kawo kan su kai har ma daga bangaran Alhaji Ibrahim Balla, Amma kullum Usman cikin zillewa ya ke. Har Umar ya gaji ya fito ya tambayi Usman shin lafiyar sa kalau kuwa? Usman ya bashi amsa da kada ya damu, dake su na shirin zuwa Rugar Shehu domin taho da wasu daga cikin shanun Usman, ya ce ya bari idan su ka dawo zai masa bayanin komai. Da haka su ka dauki hanyar su na Rugar Shehu.

    Amma ko da su ka isa Mambila, aka yiwa Umar bayanin tafiyar kasa da za su yi kafin su karasa Rugar Shehu nan yayi kememe ya ce ba shi iyawa. Usman dai ya je ya dawo shi zai yi tsimayin shi nan Mambila. Hakan ko aka yi, Usman shi kadai ya niki hanya har Rugar Shehu.

    Ganin yanda Usman ya canza kasa gasgata zatan su na Shehun na su ne da gaske. Nan fa Usman ya zama abin kallo kamar yanda Zainab ta zama farkon zuwan ta Rugar Shehu, bambamcin dai shi wannan mamakin yanda Usman ya canza gaba daya ne ya rufe su. Kowa burin sa ya taba Usman. Shaddar da ke sanye jikin sa, hular kan sa kai hatta takalmin kafarsa abin kallo ne gare su. Cikin su har da masu fadin babu shakka cikin wannan injin kyera mutane da aka ce akwai a birni aka sanya Usman, ya zama dan birni tamkar kado.

    Bayan komai ya lafa ya mu su bayanin abin da ya ke tafe da shi. Wato na mayar da Rugar Shehu cikin birni. Kamar yanda yayi hashashe, dayawa daga cikin su sun yiwa maganar mummunar fahimta, ciki har da Kawu Iliya. Amma ko da Usman ya tsaya ya mu su bayani mai gamsarwa sai su ka dan sauko, Amma duk da haka su ka ce bazai yiyu kowa yaye a bar daji ba. Duk sanda Usman ya gama shirin sa ya zo wasu daga cikin jama’ar Rugar su bishi, a fara ganin yanayin zaman da yanda zai kasance, idan har abu yayi kyau saura jama’a su bi bayan su, idan aka sami kishiyar haka kuma toh lalle wanda su ka bishi sai su dawo gida. Haka kuma shanu mallakan sa ne, ko da kuwa dubu zai kore zuwa birni ba zai talauta Rugar Shehu ba, dan haka babu mai tsayar da shi, adduar su dai kawai Allah ya idda nufi, ya kawo mu su alkhairi.

    Kwanan Usman biyu kacal a Rugar Shehu, ana gobe zai koma Bello ya zo masa da sakon Raqeeba na ta na so ta gan shi. Usman ya ce toh bisimillah mana. Nan cikin bukkar shi ta zauna tare da mijin ta Bello. Usman na daga zaune can gefe yayinda zuciyar sa ta masa nauyi jin maganganun da ke fita daga bakin Raqeeba. Ta kwashe abin da ya faru tsakanin ta da Zainab, da kuma yanda ta tunzura ta har ta yarda ta hada baki da su Rahila ta fada mu su. Cike da nadama ta kare da

    “Abu mai kaunar ka ce kwarai, sharrin shedan ya sa na aikata abin da na aikata amma sam babu laifin ta, laifin ta daya shi ne zafin kishi, dan sai a sannan ni kai na na gane Abu mai kaunar ka ce…..”

    Ganin Usman ya runtse idanu ya sanya Raqeeba kasa magana, cikin neman agaji ta ke kallan Bello wanda tun da ta gano ta kamu da san shi ta fada masa abin da ta aikata. Bello ya gyara muryar sannan ya furta

    “Ta yi kuskure, tun da ta fada min na nuna mata bacin rai na…..”

    “Tun da ta fada ma ka? Ka na nufin ta ma fada ma ka amma ka kasa sheda min Muhamadu?”

    Ya na kokarin kare kan sa ya furta

    “Ah ah watan jiya ta sanar da ni, dama jira na ke….”

    “Ya salam matar ka ta cutar da ni, ni Kuma na cutar da Abu! Har ka san wannan maganar amma ka kasa fada min? Watan jiya? Kasan kwana nawa na yi kullum da kewan Abu? Ka san dare nawa ya shude kullum da ita na ke mafarki? Kasan kwanaki nawa na yi kullum zuciya ta na kukan rashin ta? Haba Muhamadu Bello! Haba dan Allah!”

    Cewar Usman yayinda ya tashi a firgice ya shiga hada kayan sa. Alama Bello ya yiwa Raqeeba da ta tashi ta tafi. Tsoran fushin Usman ya sanya ta kiran su Kawu Iliya. Su ka tadda Usman ya dau jaka har ya fito. Sun yi sunyi su bashi hakuri ya bari gari ya waye sai su tafi amma Usman yaki. Gani ya ke kowani sakan idan ya wuce ba tare da ya na hanyar Kano ba asara ne a gare shi. Dole suna ji suna gani su ka bar shi ya dau hanyar Mambila cikin daren.

    Sai da gari ya waye tangararan rana ta hudo kai sannan ya isa Mambila. Nan ma abinci kawai ya ci sannan ya tasa Umar a gaba lalle su dau hanya Kano. Yanda dawo masa afujajan ya sanya Umar shiryawa su ka dau hanya ba tare da ya masa mu su ba. Tun da su ka dau hanya Usman ya je rama baccin da be yi daren jiya ba. Umar ya daga masa kasa har sai da su ka isa Jalingo, bayan sun yada zango hotel din da su ka saba sauka ya je har daki ya same shi.

    Babban daki ne wanda ya kai matakin dakunan da alhazawa su ke kamawa. Bayan ya buga masa kofa ya bude masa, ya sake komawa ya yi zaman sa bakin gado, sanye da farar singileti da gajeran wando. Umar ya dube shi ya ce

    “Na lura tun da ka dawo ba ka cikin hayyacin ka, me ke faruwa? Me za su yi Kano?”

    “Abu zan dauko”

    “Wacece Abu Kuma?”

    Umar ya tambaya cikin nuna rashin fahimta. Nan Usman ya bashi wani bangare daga cikin rayuwar shi da Zainab ba tare da ya tona sirrin da ya shafi dakin auren sa ba. Kafadar shi Umar ya dafa sannan ya ce

    “Sai yanzu na fahimci dalilin da ya sanya ka ki kula kowa. Lalle ni zan raka ka har Kano, Amma fa gaskiya ba za mu je haka yanda ka ke a burkice ba Malam! Sai ka nutsu ka kuma kwantar da hankalin ka!”

    “Shin ka na ganin Zainab za ta yafe min?”

    Umar na jinjina kai

    “Matukar ta na san ka kamar yanda ka nuna min, za ta yafe ma ka Usman, dukkan ku kun yanke hukunci ne cikin rashin sani da gaggawa, duk ilimin ka, ita kuma duk wayewar ta be sa kun iya gujewa kaddarar ku ba, yanda za ka sani ajizanci ne na dan adam, shi dan adam ajizi ne Usman”

    Kai Usman ya gyada kawai. Umar ya masa sallama, ya bar shi nan zaune ya na fargaban yanda zai tunkari Zainab bayan wata da watanni da tura ta gida.

    Kamar yanda Umar ya ce, sai da ta tabbatar Usman ya nutsu sosai, sun kuma shirya zuwa gidan surukai da kyau sannan su ka dauki hanyar Kano, Usman ya so su bi jirgi, Amma Umar ya dage sai dai su tafi a mota. Daya daga cikin manyan motocin Alhaji Ibrahim Balla ya dauko dan har lokacin Usman be iya mota ba, bare ya mallaki ta kan sa, Umar kuwa ganin za su je gidan surukai da aka dade ba a hadu ba ya ga dacewar a je da babba harka yanda za su cika ido da kyau.

    Da ya ke tun asuba su ka bar Yola, kuma Umar ya taka motar sosai, karfe hudu a Kano ta mu su. Kai tsaye Prince hotel su ka wuce in da su ka kama dakuna biyu. Dan zumudi jikin Usman har rawa ya ke. Umar na duban sa cikin zolaya ya ce

    “Wallahi in ba ka dena wannan rawar jiki da zumudi ba babu in da za mu je yau sai gobe”

    Fuska murtuke Usman ya furta

    “Sai in ga me hana ni fita! Da ka san yanda na ke ji Umar da ka tausaya min”

    Umar na murmushi ya ce
    “Ni ma zolayar ka na ke, maza ka je ka shirya, ka tabbatar ka kure a daka yanda ko Abun ta ka baza ta gane ka ba, bare masu gadin nan da ka ba ni labarin su”

    Cike da farin ciki Usman ya bi bayan wanda zai nuna masa dakin sa, ya na mai bawa Umar amsa da

    “Yau kuwa zan ba ka mamaki Umari, dan ko kai kan ka ba za ka gane ni ba”

    Haka su ka yi sallama su na wasa da dariya. Usman be bata lokaci ba nan da nan yayi wanka. Wata danyar farar getzner wacce aka mata aiki da shudin zare dinkin babbar riga ya sanya. Bayan ya feshe jikin sa da tuare mai tambarin ‘Boadicea the Victorious’, ya dau hularsa da aka saka da manyan zare kalar aikin babbar rigar sa sai dai kuma akwai wasu kalolin da su ka ratsa jiki, hular ta sha wanki da kari ya sanya. Daga agogon hannun sa har zuwa takalmin kafarsa kudi ne. Shi kan shi da ya kalli madubi, mudubi sai da ya kara dubawa. Lalle kam sutura ita ce mutum!

    A restaurant ya sami Umar ya na cin abinci, ko daga shigan Usman ba sauran jama’ar da ke wajan ba, hatta Umar sakin baki yayi ya na duban sa har ya karasa teburin da ya ke.

    “Butar shayi mutumin nan ka hadu! Wannan ado duk na zuwa biko ne?”

    Cewar Umar cikin zolaya. Kujera ya ja ya zauna, kana ya ce

    “Ka yiwa girman Allah ka min adalci ka bar wannan abincin mu tafi, wallahi da ka san halin da na ke ciki da ka tausaya min Umar”

    Baki cike da shibkafa Umar ya ce

    “Adalcin shi ne ka bari na cika timbi na Alhaji, da dai ace zuwan dadi ne da sai na sa ran za a ba mu na dare, Amma hakan nan siddin mu taso tun daga Yola har Kano ka hana cin abinci? Babu wannan maganar”

    Cikin kosawa Usman ya furta
    “Sai ka ta ci ai, idan ka gama ina jiran ka a mota”

    Ya tashi ya fice in da matan da ke wajan su ka bishi da kallo. Shi kuwa gaba daya hankalin sa yayi gaba, in ba Zainab ya sa a Ido ba ba zai sami nutsuwa ba.

    Sai da Umar ya take tumbin sa sannan ya fito su ka dauki hanya. Ko da su ka karasa gidan Malam su ka yi hon, Jauro ya ga motar da ke fake bakin kofa tuni ya bude mu su gate ba tare da ya damu da ya duba su waye cikin motar. Umar ne ya fara fitowa bayan sun yi fakin farfajiyar gidan, da sauri Jauro ya karasa gaban sa ya ba fadin

    “Barka da zuwa Alhaji, sannu da zuwa Alhaji”

    Ganin dogan mutum fari sol, ga kyau ga kwarjini ga kuma sutura, ya fito daga motar, Jauro be sanda ya zube kasa ba cikin fadanci, fadi ya ke

    “Allah shi ja zamanin ka, barka da zuwa”

    Shi kan sa abokin aikin Jauro bude baki yayi ya na kallan sa, dan kuwa tun bayan tafiyar musu ya can ji gurbin sa, be taba ganin Jauro ya rikice kamar yau ba. Shi kan sa Usman ya san tabbas Jauro be gane sa ba. Ya na shirin tambayar in da Zainab ta ke sai ga Anty Sauda ta fito. Ganin mota mai numfashi fake farfajiyar gidan da kuma mazan da su ke tafe cikin motar tuni ta karaso ta na tambayar

    “Baki mu ka yi ne? Ko wajan Falmat ku ka zo ne?”
    Har kasa su ka tsugunna su ka gaishe ta, Anty Sauda na fadin

    “Ku tashi, ai ba sai kun tsugunna ba”
    Umar ne ya ce da ita wajan Zainab su ka zo. Duk yanda ta so ta buye disappointment din jin Zainab aka zo nema sai da ya dan nuna a fuskar ta. Ta kan ta ta yi mu su jagora har cikin falon Dady, sai da ta tabbatar su zauna sannan ta wuce ciki ta shedawa Ammy halin da ake ciki, ta kare da

    “Wallahi matasa ne daga kin gan su kin ga ‘ya’yan manya, Amma na san rashin mutuncin Yakura yanzu sai ta watsa ma na kasa a Ido, na ga tun da ta haihu ta ke jin maganar ki da kyau, ko za ki lallba ta fita su gaisa?”

    “Toh Yakura ce ai ba a mata abin arziki, bari na gwada sa’a ta, a ina ki ka ce ke?”

    Cewar Ammy cikin fargaban abin da zai je ya dawo.

    “Su na can falon Malam”
    Ammy ta ce
    “Toh bari na gwada”

     

     

     

     

     

     

     

  • Auren Shehu Book 2 Page 8

    Auren Shehu Book 2 Page 8

    *Khadija Sidi*
    Auren Shehu 2

     

    8

    Yanda kowa ya ke kallan ta ya sanya Zainab shakkar irin shigan da ta yi a kara na farko. Matan sun yi tsit in da masa yara ke kokarin rufe idanun yaran su gudun kar su ga tsairaici.

    ‘Mata da yara kenan su ka shiga dimuwa saboda shigar da ta yi ina ga maza matasa da dattija da ke zaune fadar Shehu? Lalle babu maras daraja kamar wanga Kado’

    Cewar Rahila cikin ran ta tana mai adduar Allah ya sa Zainab ta tabbata ballagaza ta taka har fada. Ganin Zainab ta dauki kafa tinkis tinkis ta na shirin fita Iyalle da ta kasa jurewa ta sha gaban ta cikin tsawa ta furta

    “Waiyazubillah! Ina za ki fita haka tsurara? Wannan wani irin rashin daraja ne!”

    Tafa hannu Zainab ta ke jin hausa radau bakin Iyalle wacce dimuwar ganin Zainab ya sa ta manta ta yiwa Zainab hausa.

    “Ikon Allah da kin iya hausa shi ne da ki ka min kunne uwar shegu?”

    Sai a sannan daga Iyallen har sauran matan gidan su ka ankare da subul da bakan da Iyalle ta yi. Cikin wayencewa ta na mai sosa kyeya ta karya harshe ta koma fulatanci. Hakan ne ya batawa Zainab rai ba tare da ta yi la’akari da shekarun Iyalle ba ta furta

    “Dakin uwar ki zani! Na san kin ji wannan ma!”

    Kuka Iyalle ta sa, ta na mai tafa hannu in da sauran matan gidan su ka shiga bata baki, Rahila ce mai ruko Hansai wacce ta ke kokarin damko Zainab da niyar bata kashi.

    Cikin wannan hali ta sa kai ta fice daga gidan. Kamar yanda shigar Zainab ya girgiza ahalin gidan Shehu, haka ma sauran jama’ar Rugur, musammam maza domin kuwa shiga irin ta Zainab ko da wasa ba su taba ganin irin ta ba, dan a wajen su ba ta da maraba da tsirara. Babban abin da ya ke jan hankalin jama’ar rugur kuwa jikin Zainab ne, dan kuwa Rugar Shehu kaf babu mai irin shi, yawanci yara mata da sun fara dirgen dangin, mama ya dan tasa a kirjin su ake mu su aure, haka kuma maman ba ya zuwa koina daga sun haihuwa daya sun shayar sai ya zube sharkaf, dan haka akasalin Rugar daga wanda na su ya dan fara tasawa haka kuma duka an mu su baiko, sai na matan aure da ya zama silifas.
    Wasu matasa da su ka kasa hakuri bin ta su ka ke yi a baya, Zainab kuwa ba ta fasa nufar Fadar Shehu ba. Bello wanda ya baro fadar kenan da niyar kai sako gidan Shehu ne ya fara ganin ta, ganin haka yayi ba shiri ya juya da saurin sa domin yiwa Usman gargadin masifar da ta dumfaro shi.

    Cikin tashin hankali Usman ya bar fadar, abin ku da dogo nan da nan ya cimma Zainab tun kafin ta karasa fadar.
    Ganin yanda ya tunkaro ta kamar zakin da ya shekara dari be ci abinci ba ya sanya matasa juyawa da sauri, ita kan ta sai da gaban ta ya fadi, Amma hakan be sa ta fasa tunkarar sa ba. Wani irin damka ya kai wa hannun ta har sai da ta saki kara, be kula ba haka kuma be iya duban ta ba gudun abin da zai iya aikatawa nan bainar jama’a matukar be danne zuciyar shi ba, ya soma jan ta kamar leda ba tare da ya ce mata uffan ba.

    Duk yanda ta so ta cije ta ki bin sa abin ya gagara, ta na ji ta na gani haka su ka wuce sashin Shehu da sauran bukkoki, Zainab na waige waige cikin neman doki amma ganin yanda kowa ke dauke kai sanadiyar fushin Shehu ya sa Zainab saduda ta mai jiran tsammani. Ganin ya kutsa da ita dokar daji ya sa Zainab farin ciki, hakin ta ya cimma ruwa Usman yayi fushi gashi zai fitar da ita hanya…..wata boyayyar bukkar da ta hanga ne ya sanya murnar ta komawa ciki, musammam da ta ga sun nufi bukkar bilhakki. Cikin kokarin kwatar kan ta Zainab ta ke fadin

    “Dallah malam ka sake ni! Ka sake ni! Ina ka ke ja na!”

    Idan Usman ya tankawa Zainab toh dutse ma ya tanka. Bukka ce kwallin kwal sai garken Shanu wanda tsayawa fadar adadin su ma bata lokaci ne. Daga dayan gefen kuma yar karamar gona ce, sai kuma bishiyon kayan marmari da su ka hada da mangoro, leman tsaki, ayaba, fasadabur da dai sauran su.
    Maimakom kufar karar da ta saba gani, kofa garwa ce jikin bukkar wanda duka daya Usman ya mata da kafadar sa ta bude, ya na mai jan Zainab su ka shige bukar sannan ya sake ta ta fadi kasa. Juyawa yayi ya jawo kofar ya rufe ta hanyar sanya mukulli da kwado ya datse.

    Cikin faduwar gaba Zainab ta ke duban kofar, kafin daga bisani ta bi bukkar da kallo, bukkar na da girma sosai dan ta ma fi bukkar Shehu girma kadan, Amma idan aka dauke tabarmar kaba da ke shimfide tsakar dakin babu komai ciki. Da sauri Zainab ta tashi ta na mai fadin

    “Da ka kawo ni nan uban me za ka….”

    Yanda Usman ya juyo ya sanya ta zuke zancen ta, idanun ta cikin na sa da su ka yi jajur tamkar garwashi Zainab ta ja da baya a hankali ta na mai fadin

    “Usman……”

    Hannu biyu ya sa ya cire rawanin kan sa a saukake, karo na farko da ya bayyana mata fuskar shi hakan me ya sanya Zainab ruke numfashin ta. Ta sha ji ana cewa kyawu kamar mutum shi yayi kan sa, kokuwa ace kyawu kamar aljan ba ta taba gasgata akwai irin wannan kyawun ba sai a yau. Lokaci guda Usman ya rikide mata ya koma mata tamkar balarabe.

    Ta san Usman fari ne, haka kuma ko ina ta ga manyan idanun Usman da kuma bakin gashin gira da na idanun sa za ta gane Usman din ne, haka kuma tun asali ba ta rena tsayin hancin sa ba, bakin lallausar gashi da ya taho tun daga kan sa, ya bi layin saje haka kuma ya sauka ta bakin sa ya na mai zagaye bakin ne ya kara kawata fuskar shi, ta zaci duk duniya babu gemu da shaje da zai kai na Sudais mijin Halitta kyau ba, ashe ba a banza Usman ya ke boye fuskar shi ba.
    Ganin Usman ya sa hannu ya cire rigar jikin sa, yayinda faffadar kirjin sa wanda ke rufe ruf ruf da lallausar gashi ya bayyana, ga kuma kaunji nan duka hannayen sa ya sanya Zainab ja da baya. Yanayin bacin ran da ya ke ciki, wanda ya hadu da kyawun sa ya mayar da shi tamkar hatsabibi mai hatsabibin kyau.

    “Usman…..me ka ke yi?”

    Cewar Zainab cikin rawar murya ta na mai fitar da idanu.

    “Hakkin ki zan baki Abu! Na ga kin fara fita hayyacin ki har ki na fitowa tsirara nema na….”

    Cewar Usman yayinda ya nufota ya na kokarin kwance tazuge. Ganin haka haka Zainab ta fara ja da baya tana fadin

    “Kar ka zo kusa da ni! Wallahi kar ka zo kusa da ni! Da na hada jiki da kai gwara na hada da kare! Kar ka zo…!”

    Ina tuni ya kai ta makura, ta yi saurin gocewa ta na kokarin arta a na kare Usman ya cafko ta, sai gasu duka a kasa, ta na ihu, yayinda ta ke kokarin kai masa duka da yakoshi, Usman fe fasa hada jikin su ba yayinda ya sa hannun sa daya ya ruke duka hannayen na ta biyu cikin nuna mata karfi.

    Duk yanda ta so kwatar kan ta abin ya gagara, tun tana zagi da tsinuwa, ganin da gaske Usman ya ke hakkin na sa ya ke kokarin karba har ya kai ga raba ta da tufar jikin ta, Zainab ta shiga hada sa da Allah, fadi ta ke

    “Dan Allah Usman kar ka min haka! Dan Allah Usman…..dan Allah…..”

    Sam baya hayyacin sa bare ya san abin da Zainab ke fadi har sai da ya karbi hakkin na sa, Zainab ta tabbata matar shi ta sunna. Cike da mamakin kasancewar ta budurwa ya ke duk lalacewar ta da nuna tsairaici, ba kamar tsohuwar matar shi Cangwai ba. Yanzu shi ne namiji na farko da ya fara sanin Zainab a matsayin ta na diya mace! Abin da ya ke nanatawa cikin ran sa kenan yayinda ya ke jin zuciyar sa cikin wani irin yanayi da tun da ya zo duniya be taba jin irin shi ba.

    A hankali ya kai kallan sa gare ta a karo na farko tun bayan da ya iya sakin ta, in banda ajiyar zuciya babu abin da ta ke, hawayen ke fita daga lumsasshen idanun. Takan yi wasa da komai amma ban da budurcin ta, ta yi tattalin sa duk da takan ji kunyar kasancewar ta budurwa duk sanda abokan huldar ta su ka sako ta gaba da tsokana, cewar su har yanzu ba ta da yancin kan ta, haka kuma an so kakarin raba ta da shi ba sau daya ba sau biyu ba amma Allah na bata nasarar tsallakewa sai yau, babban takaicin ta shi ne a rasa wanda zai aikata mata hakan sai Usman…

    “Dan Allah dan annabi ka raba ni da rai na kamar yanda ka raba ni da martaba na, dan Allah ka kashe ni, idan ba ka kashe ni ba ni zan kashe kai na…..”

     

  • Auren Shehu Book 2 Page 2

    Auren Shehu Book 2 Page 2

    khadija sidi*Auren Shehu 2

    2

     

    Zainab na biye da Usman duk in da ya sa kafa nan ta ke dire na ta. Dan sahu ya tara ba su zame ko ina ba sai tashar Kano Line amma su ka yi rashin sa’a motar Taraba ba ta tashi sai sassafe. Direba ya dubi Zainab da gaba daya alamun gajiya ya bayyana a fuskar, a zahirin gaskiya idan aka dauke mayafin fulbe da ke yafe jikin ta, sam yanayin ta da zubin ta be nuna wani alaka tsakanin ta da Usman ba, Dan kuwa kana ganin Usman ka ga bafulatanin usul wanda babu wata alamun wayewa a tare da shi. Cikin dabarar Jin ko wacece Zainab ga Usman Driver ya kada baki ya ce

    “Halan mikakkiyar tafiya ka yi tare da uwargiyar ta ka?”

    “Eh mikakkiyar tafiya mu ka yi, haka kuma ita za mu tasarwa, shin ko akwai irin gidan kwana da ake biya nan kusa? Sai mu kwana washagari mu dau hanya”

    Usman ya bashi amsa ba tare da ya fadi abin da Driver ke da muradin ji ba. Ganin yanda Driver ke kallan Zainab ba kakkautawa ya sanya Usman fadin

    “Ni ta ita na ke ji ma, a gajiye ta ke….”

    Driver na mai sosa kyeya ya ce

    “Toh ka ga yanda za a yi, gida na nan kusa ne, ina da daki mai dauke da gado da katifa cikin zaure, haka kuma akwai bandaki ciki, ban fiye san saukar bakin da ban sani ba ciki, Amma ganin halin gajiyar da wannan baiwar Allah ke ciki, mu je sai na ba ku shi a kan naira dubu biyar…”

    “Dubu biyar be yi yawa ba?”

    Cewar Usman yayinda ya kai hannu aljihun shi domin jiyo lafiyar tattalin arzikin da ke ciki. Jin haka Driver ya ce

    ” Kai fullo ba dai san sisi ba, toh ai babu damuwa, kawo uku toh, ai matafiyi abin a tausaya masa ne”

    “Toh babu laifi, gashi nan kirga ka gani”

    Ya mika masa kudin da ya fidda daga aljihun sa. Driver ya dirga dubu uku cus sun cika. Sannan ya ce

    “Toh Madallah sai ku shigo mota mu tafi nan tsallake ne ba nisa, ka ga da sassafe kafin shida sai mu fito mu yi lodi mu dau hanya”

    “Abu shiga gidan baya mu tafi”

    Cewar Usman cikin dakiya. Jin Zainab ta furta

    “Toh Shehu mijin na”

    Ya sanya Driver sake waigawa ya kalli Zainab kafin ya shiga motar ya tada cike da mamaki, ya tabbata dai wannan gabjejen bafulatanin Ruga majin wannan kyakkyawar yarinya ce, Driver ya dau hanya ya na al’ajabin yanda Usman ya tsinci dami a akala.

    Kamar yanda Driver ya fada gidan na sa be da nisa da tashar. Dakin da yayi alkawarin bawa su Usman ya sauke su, babu laifi dakin be fiya dauda sosai ba, gadon gyare ya ke tsaf haka kuma kasan dakin shimfide ya ke da leda. Haka kuma akwai wutar lantarki. Daudar dai daya ne na rashin shara da dakin be samu ba. Shi ma din kafin su shiga Driver ya turo yaro daga cikin gidan sa aka share, tare da cire zanin gadon da ke shimfide bisa gadon, ya shimfida wankakken sai kamshin sabulun wanki ya ke, Sannan ya sa aka kunna mu su maganin sauro na igiyar leko, ya kuma debo ruwa ya zuba a robobin cikin bandaki. Yaron na shirin fita Usman ya tambaya ko akwai in da ake siyar da abinci nan kusa? Yaro ya ce babu sai dai akwai wajen me shayi ya na Kuma dafa indome. Usman na mai godiya ya sallami yaron da sauri saboda yanda wayar Zainab ta ishe su da kara. Ya na duban Zainab wacce ga wayar a hannun ta amma ta kasa dagawa saboda be ba ta izini ba.

    “Waye ke kiran ki?”

    Ko da ta duba wayar ‘Ammy na’ ta ga an rubuta, budar bakin ta sai cewa ta yi

    “Wani suna ne wai Ammy na, haka dazu ma wasu su ka ta kira ban san su ba”

    Zainab ta bashi amsa a sanyaye.

    “Ki tura mu su sako na lafiyar ki lau, kada a sake kiran ki”

    “Toh Miji na Shehu”

    Cewar Zainab yayinda ta aikata umarnin sa. Yanayin gajiya da ta ke ciki da kuma yanda surkullen da ya mata ya kamata sam be saka tausayin ta ya tsirga zuciyar Usman ba, sai ma tsananin kiyayyar ta da ya ke ji cikin ran sa, da kuma bakin cikin da ke ziyartar zuciyar sa a duk sanda ya tuna ita ce sanadiyar rashin ganawar karshe tsakanin sa da Iyar sa.

    “Ki kashe wayar kada ki sake kunna ta, zan fita na siyo abinci”

    Cewar Usman cikin kokarin ficewa daga dakin, har ya kai kofa ya sake juyowa ya kara da

    “Ki jawo kofa ki sa sakata idan na fita, kada ki budewa kowa idan ba ni ba ne, Ki yi wanka da sallah idan har ki na yi…….”

    Ya na jiyo amsar ta na

    “Toh Miji na Shehu”

    Ya fice zuciyar shi na tafasa na ba gaira ba dalili, shi kan shi ya san iya yan watannin nan gaba daya baya cikin hayyacin sa, babu abin da ke masa ciwo sai rashin Iya, yanayin da Bello ya shiga a sanadiyar Zainab da kuma dukan kawo wuka da aka yiwa Bello, duka a sanadiyar auren Zainab.

    Bayan tafiyar Usman Zainab ta sa sakata kamar yanda Usman ya umarce ta, cire kayan ta tayi, tare da daura dan karamin towel din da ta saka cikin akwaitin ta. Cike da kyamkayami ta shiga bandakin, ba ta yarda ta tsugunna ba gudun daukar cutar bayan gida. Har ta gama wanka ta dauro alwala Usaman be dawo ba. Wata rigar baccin ta saka iya gwiwa mai dan karamin hannu sannan ta sanya hijabi har kasa ta shiga gabatar da sallah.

    Idawar ta ke da wuya ta cire hijabi kan ta daure da kallabi ta ji ana buga kofa, ta karasa gaban kofar tare da fadin

    “Waye?”

    “Shehu”

    Ya bata amsa a taikaice. Cikin rawar jiki ta bude kofar tare da fadin

    “Sannu da zuwa”

    Hanun sa rike da bakaken ledoji guda biyu, da kofi wanda ke fitar da turirin zafin bakin shayin da ya ke ciki ya wuce ba tare da ya tanka mata ba. Sai da ya aje ledojin da kofin shayin sannan ya daga ido ya kalle ta, tuni yayi saurin kawar da kai, cikin mummunar faduwar gaba, kan sa ya sara ganin yar rigar da ke jikin ta, da kuma yanda ya bayyana surar jikin ta duk da dai rigar ba matsattsiya ba ce, Zainab din ce MashaAllah. Cikin tsawa da fada ya ce

    “Me ki ke jira a nan Abu? Ki rufowa mutane kofa ki zo ki saka hijabin ki! Kada ki sake yawo haka matukar ina wajen!”

    A gigice Zainab ta rufe kofar tare da sa sakata, ta karasa da sauri hannu na rawa ta dau hijabin ta ta saka, can gefe ta sami waje ta zauna har lokacin gaban ta be bar faduwa.

    Jin ta shiru ya dago kai ya dube ta, ganin yanda ta zauna ta yi shiru kamar ba tsigalalliyar Zainab din da ya sani ba, da Kuma kwallar da ta ciko idanun ta be sa yayi dana sanin ihun da ya mata ba, sai ma danasanin ganin surar ta da yayi da har lokacin ya ke masa yawo a idaniyar sa. Murya ya gyara ya na mai neman nutsuwar karfi da yaji, ya mata nuni da yatsa tare da fadin

    “Ki zo nan ki ci abinci ga shayi nan shi za ki fara sha kin ji ko?”

    Ya na maganar ne cikin dakiya. A hankali ta taso ta zauna in da ya umarce ta, shi ne ya bude mata ledar indomie din, yanda ya ga ta na ci hannu baka hannu kwarya ya tabbatar masa da cewa da yunwa ta wuni. Na shi ledar ya ja dan kuwa ji ya ke ya na bukatar ka?aicewa a wannan lokaci, a hankali ya ja jikin sa ya fita ya bar mata dakin. Bakin kofar dakin ya zauna duk yanda ya so ya ci abinci ya kasa, tunani kala kala ke yawo cikin kwakwalwarsa, sam be da niya kuma ba zai yi danasanin tafiya da Zainab ba! Hakan shi ya fi cancan ta mutane irin ta!’

    Furucin da zuciyar sa ke jaddada masa kenan har ya dan sami karfin gwiwar cin indomie din. Haka ya zauna a soro, ‘ya’yan Driver na kai kawo haka na makota, har kafa ta dauke aka ma rufe gidan gaba daya. Nan soro cikin sauro ya kwana, da asubar fari ya buga mata kofa, ya ce ta tashi ta yi sallah ta yi wanka za su wuce.

    Sai da aka idar da sallah sannan Zainab ta yi wanka. Ta na jiyo shi shi ma yayi na sa wankar tare da goge baki da dakakken gawayin da ya kullu tun daga Rugar Shehu. Cikin bandakin ya shirya tsaf ya fito cikin kayan saki riga da wando, haka kuma be fasa nada rawanin sa da bakin yadi ba. Ya na mai duban shigar da ta yi na bakar duguwar riga ya ce

    “Ki cire kayan nan ki sanya hijabi”

    Ga mamakin sa sai ga Zainab na kokarin zare ruga gaban sa, cikin tsawa ya ce

    “Wai ke wata irin mara kunyar Bingel ce Abu???”

    A dibirbice dan kuwa tsawar Usman rikita ta ya ke ta ce

    “Ya zan yi miji na? Kai ka ce na cire rigar…”

    “Mace da kunya aka santa duk da na dade da sanin ke ba ki da ita ko na miskala zarratun! Idan kin ga dama ki yi tsirara kafin ki saka hijabin!”

    Ya na gama fadin haka ya bude kofa ya fice. Zainab ta yi kasake ta na kallan sa cikin tunanin laifin me ta yi har ran Mijin ta Shehu ya baci haka. Jin ya na buga mata kofa ta yi saurin saka hijabin haka ba tare da ta cire rigar ba, ta hade komai na ta cikin karamin akwatin ta ta fito.

    A mota ta tarar da su, Driver ma ya fito ita kawai ake jira. Dan haka ta na shiga kai tsaye tasha su ka wuce. Nan tasha ya siya mata shayi da bredi ta ci kayan ta ba musu. Haka kuma ya siya mata silifas na roba ya ce ta cire mai tsinin da ke kafar ta, ya dau mai tsinin ya bawa wata yarinya mai tallar masara cikin tasha. Karfe shida daidai mota ta cika, su ka dauki hanyar Taraba.

    Tafiya ce mikakkiya su ka sha, gashi sam hanyar ba kyau, ga checking point da yawa duk in da su ka tsaya kuwa sai sojojin nan sun tanka Zainab duk da can gidan baya su ke zaune tare da Usman. Yawanci su kance kamar sun san fuskar Zainab.

    Ba su suka isa Taraba ba sai shida na yamma. Dake dama Driver da su ka kwana gidan sa ne ya ja su, Wajan kwana be basu wuya ba. Kamar yanda ya bata umarni ba ta cire hijabin ta ba, har sai da ya ce mata za ta iya cirewa ta yi wanka idan ta na so idan ya fita. Ya na ficewa ta cire hijabin ta sha iska.

    Washagari da sassafe su ka sami motar Mambila. Shi ma din sai yamma likis su ka tasarwa shiga garin. Dake Mambila bisa dutse ne ko Dirobobi sai kwararru ne su ke iya hawa dutse, Zainab ba bata san sanda ta rugume Usman kam ba, ta na mai dora fuskar ta kan fadarsa sai da ya ji tsigar cikin sa ya tashi, haka kuma duk yanda ya so ya zare ta daga jikin sa ta ki, har sauran yan cikin motar suna mu su dariya. Haka babu yanda zai yi ya barta kwance jikin sa yayinda zuciyar sa ke bugawa tamkar za ta fado.

    Haka tafiyar awanni ta zame masa tamkar gwale gwale. Suna Isa Mammbila ya banbare ta daga jikin sa ya fito daga motar ya bar Zainab ciki ta na mai raba idanu ta fito daga motar. Baki bude ta ke duban in da take, wato Allah mai hilitta yayi hilitta a kasar Mambila, ba ga kasar ba ba ga halittun da ke kasar ba.

    Gari ne mai kyawun gaske da yalwataccen ni’ima, haka ma matan kasar don idan kaga wata ta keto daga gefan duwatsu gashi har mazauni ka ce gamo ka yi tsabagen kyau. Ganin dawowar Shehu da dama sun ga tafiyar shi ba karamin dadi su ka ji ba, sun karbe su hannu bibbiyu in da ya gabatar mu su dayl Zainab matsayin matar shi.

    Daki na musammam aka ba su, haka kuma an ba su abinci mai kyau, ga fura da nono ga kayan marmari na daga ‘ya’yan itace. Yanda su ke yarawa da Usman da kuma yanda ya ke musu fara’a ya sanya Zainab zuba masa idanu, ta na mamakin dama ashe Shehu mijin ta ya na dariya?

    Usman ya so wucewa a ranar amma jama’ar Mambila su ka hana shi, su ka ce ya bari gari ya waye ido na ganin Ido duk da dai ba su san ainihin dajin da Rugar Shehu ta ke ba. Haka bai sa ran sa ba ya hakura su ka kwana, cikin dare matan da su ka zo su ka buga masa kofa tare da tambayar ko ya na bukatar yar tayin hirar dare Allah yayi yawa da su. Shi kuma be fasa ba su amsa da matar shi ba ta saba kwana ita kadai ba, Kar ya fito kiri kiri ya ce ba ya so wata ta kullace shi ta aikata masa wata kullalliyar. Sai ya tabbatar kafa ta dauke sannan ya fito waje ya bar Zainab ciki ta na baccin ta hankali kwance. Kofar dakin da aka bashi ya samu ya kishingida, Zainab ya ke gani cikin kayan bacci duk sanda ya runtse idanun sa, haka kuma sassanyar kamshin turaren ta da ya mamaye rigar sa sanda ta rungume shi a cikin mota. A fusace ya mike tsaye, tafiya ya ke tamkar zai tashi sama tsabagen bacin rai. Wani dan dutse mai rubar ruwa ya nufa, ya na mai cire rawanin kan sa ya tsaya karkashin sa ruwa na kwaranya bisa kansa ya na sauka gangar jikin sa. Sai da ya dau kusan minti talatin a wannan halin, zuciyar sa ta dan yi sanyi sannan ya fito ya zauna gefan dutsen. Wani irin iska ke kadawa ya na shiga jikin sa, idanun sa runtse kansa bisa dutse Allah ya kadai ya san awannin da ya bata nan zaune ya na ambaton sunan Allah. Sai da ya bushe tsaf zuciyar sa ta dan yi sanyi sannan ya tashi ya koma masaukin sa.

    Da sassafe bayan sun yi sallama, an kuma hada mu su goma ta arziki na guziri su ka tasarwa Rugar Shehu haikan. Dake tafiya da mata sai a hankali duk yanda Usman ya so su yi sauri su isa Rugar Shehu ko ya rage tarayya da Zainab, abin ya gagara. Tun suna shiga dajin suna ganin yan tsirran mutane da yawancin su fulani ne masu kiwo ko mafarauta, har su ka dena ganin kowa sai bishiyu da halittun dajin da ba a rasa ba. Duk sanda lokacin sallah yayi Usman kan ce su tsaya su yi sallah, haka kuma be bar Zainab da yunwa ba duk da dukkan alamu ya nuna ta jigata kwarai da tafiyar kasa da suke duk da silifas ne kafar ta tun da su ka baro Kano.

    Ko da su ka tsaya sallar la’asar nan Zainab ta kakare, tsabagen tafiya kafarta har ta fara kumburi. Amma Usman be tausaya mata ba bare ya ce su yada dogon zango, sai dai ta sami saukin daukar akwaiti, dan da tafiyar ta yi tafiya shi ya dauki akwatin.

    Yana yin duhu da gari ya fara be sa Usman ya fasa tafiya ba, da taimakon tocila su ka cigaba da kutsawa cikin daji, Allah kadai ya san adadin macijai da Usman ya kashe, tun Zainab na saka masa ihu tare da dane jikin sa, har gajiya ya sa tsoran ta ya gushe, tafiya ta ke tamkar za ta fadi, ganin haka Usman ya ?auke ta cak ya saba a kafada, ba ta jima ba baccin wahala ya dauke ta, a haka har su ka isa Rugar Shehu wajan karfe shabiyu na dare.

    Rugar duhu dulum yawanci jama’ar rugar sun kashe fitilar su ta aci balbal sun kwanta. Sai matasa yan kalilan ciki har da Muhammadu Bello ne zaune suna hira, ganin mutum dauke da wani abu bisa kafada ga kaya nan hannun sa ya ruko ya na tafiya niki niki ya tasarwa Rugar Shehu ya sa su Muhamadu Bello zabura, su na mai daukar gororun su suka nufo Usman, cikin harshen fulatanci su ke fadin

    “Kai hattara Nan! Waye Nan!”

    “Usman! Shehun ku Usman!”

    Usman ya ba su amsa ya na mai tadda su. Ganin da gaske Usman ne, dauke da mace su ka sauke gogorun su cike da mamaki, Amma aka rasa wanda zai iya budar baki ya tambayi baasi. Bello ya karbi akwatin hannun Usman har rumfar Shehu su ka raka shi, sannan su ka juya da tambaya fal bakin su.
    Bello ne kadai ya tsaya taimakawa Usman ta hanyar bude ma sa kofar kara, ya daga assabari yanda Usman zai iya wucewa ba tare da ya buge Zainab ba. Bello na biye da shi su ka shiga dakin yayinda ya aje akwatin Zainab gefe. Bisa gadon kara Usman ya kwantar da Zainab tare da gyara mata kwanciya.

    “Shehu ka dawo mana da sabon abu a wannan ranar”

    Cewar Bello ya na duban Zainab da har lokacin bacci ta ke. Shiru ne ya biyo baya yayinda Usman ya zauna gefan gado yana duba kafar Zainab da ta kumbura. Ganin Usman be da niyar tanka masa ya saka Bello sake fadin

    “Wacece wannan matar? Daga ina ka dauko ta? Shin ba ka gudun ace Shehu ya zama dan garkuwa da mutane kamar Tanko dan Baffa…..”

    “Bello!”

    Usman ya dakatar da shi cikin tsawa hakan ya sa shi kame bakin sa. Ya juya zai fita ya ji Usman ya ce

    “Ina so ka duba cikin garke, ka tatsar min nonan saniya mai dauke da juna biyu ka kawo min yanzun nan!”

    Kallan sa Bello ya tsaya yi cikin faduwar gaba, kenan da abin da Shehu yayi ya dauko baiwar Allah nan ba wai cikin hankalin ta ta biyo shi ba…..

    “Ka na nan tsaye ne?”

    Cewar Usman wanda ya lura da halin rudanin da Bello ya shiga. Cikin azama Bello ya fice, Jim kadan Bello ya dawo dauke da kwaryar nonon da ya tatso, ya tadda Usman na shirin kunnan wani ice da su ke amfani da shi wajan koran soro.

    Ya mikawa Usman kwaryar, bayan Usman ya karba yayi Bisimillah sannan ya fara karanto wasu adduo’i a zuci bakin sa na motsi, ya na gamawa ya tofa cikin kwaryar nonon yayinda ya fara kokarin tada Zainab. Cikin magagin bacci ta ke jin maganar Usman ya na fadin

    “Tashi ki Sha Abu”

    Hakan cikin mamagi Zainab ta kurbi nonon, ba ta jima da sha ba bacci mai nauyi ya sake dauke ta. Usman na duban Bello da ya tsura masa idanu cike da al’ajabi ya ce

    “Ka jira ni daga waje”

    Bello ya sa kai ya fice. Bayan fitar shi Usman ya cire hijabin da ke jikin Zainab saboda zufa da ke tsattsafowa daga jikin ta sanadiyar nonan da ta sha, ya rage daga ita sai doguwar riga ruwan hoda mara hannu, kan ta rufe da dankwali. Sai da ya karanta ayatul qursiya da falaqi da nasi ya tofe ta tsaf ya fito ya tadda Bello tsaye ya na ciran sa.

    “Mata ta ce Muhamadu Bello”

    Cewar Usman ya na mai kokarin cire rawanin sa. Mamaki ne ya bayyana fuskar Bello, kana ya ce

    “Dama da gaske ka na da aure? Kar dai ita ce matar da ake neman sakin ta daga waje na?”

    “Ita ce sanadin kashin da aka baka sanda Iya ta aiko ka kira na, haka kuma sanadiyar ta Iya ta kwanta dama ba tare da mun gana ba”

    Usman ya bashi Amsa. Shiru ne ya biyo baya kafin daga bisani Bello ya furta

    “Ya aka yi ta zama matar ka? Dama ka yi aure ban sani ba?”

    “Zan maka bayani daga baya, yanzu na gaji matuka”

    “Shin ya aka yi ta yarda ta biyo ka? Nonon da ka bata yanzu kar dai……?

    Bello ya kasa karasa maganar cikin shakkar tambayar da zai yi. Usman na mai girgiza kai ya ce

    “Kiranye?”

    Bello ya girgiza kai. Usman na mai murmushin mugunta ya cigaba da fadin

    “Tabbas shi na mata, shi ne hanya mafi sauki da zan iya taho da ita, ka ga wannan yarinyar da ke kwance bisa gado na? Hatsabibiya ce, fitinanniya ce dan haka kada ka taba tausaya mata! Idan har ka ga na mata wani abu na alkhairi toh ka tabbata darajar mahaifin ta za ta ci, na kuma ba ta makarin kiranyen da na mata ba don komai ba da dai ina bukatar ta cikin hayyacin ta, ina so na gan ta cikin kunci kamar yanda zuciya ta take cikin kunci!”

    Jikin Bello ne yayi sanyi kwarai, tun da ya zo duniya be taba ganin Usman cikin halin bacin rai da neman daukar fansa kamar yanda ya ke a yau ba, shi da ya sha duka ma be kullece ta kamar yanda Usman ya kulla ce ta ba, lalle Zainab abar a tausaya mata ce tunda ta iya tado fushin mai hakuri, tabbas ta kai bango.

    “Ka na nufin babu soyayyar ta cikin ran ka?”

    Cewar Bello cikin adduar Allah ya saukaka. Usman na mai girgiza kai ya furta

    “Daukar fansa shi ya kawo Abu Rugar Shehu, Abu ce mace ta karshe da zan iya so a duniya!”

    Ya na gama fadin haka ya wuce ya bar Bello cikin tunani da sakar zuci.

  • Auren Shehu Book 1 Page 15

    Auren Shehu Book 1 Page 15

    15

     

    Yanda Ammy ta fito afujajan da kuma sumbatun da ta ke ne ya sanya su Halitta rudewa, kamar yanda ta ke kuka, haka su ma din kukan su ke. Cikin kankanin lokaci su ka shirya, gaba daya sun manta da Zainab da ke can BQ, sai da su ka shiga mota, dukan su uku gidan baya su ka zauna, direba na shirin tayarwa sannan Halitta ta furta

    “Yakura, Ammy ba a fadawa Yakura ba”

    Ammy na share hawaye ta furta

    “Ai kuwa dai, kai na yayi zafi wallahi! Halitta je ki sanar mata”

    Halitta ba ta so Ammy ta aike ta wajan Zainab ba, haka babu yanda ta so ba ta fita ta same ta ta yi dai dai ta na bacci hankali kwance. Yanda Halitta ta tashe ta cikin gaggawa fada fada, da kuma sakon da ta fada mata na hatsarin Malam ya sanya ta tashi a gigice har ta na neman fadowa daga kan godo. Fadi ta ke

    “Innalillahi na shiga uku! Ina Dadyn ya ke? Yaushe za mu tafi Maidugurin?”

    “Idan har kin iya shiryawa da wuri za ki iya tafiya da mu, dan kuwa har mun shiga mota Allah ya sa aka tuna da ke…”

    Halitta ta bata amsa tare da juyawa ta fice, ta na jiyo kukan Zainab wacce ke fadin

    “Tsabagen wulakanci ni din ce za a mance fisabilillahi! Dady be da lafiya har ku shiga mota sannan za a tuna da ni? Wallahi kin yi da yar halak Halitta! Duk wannan munafuncin da ki ke kulla min za ki gani a kwaryar cin tuwan ki…..”

    Sai da kusan minti goma sha biyar ya shude suna jiran Zainab, Ammy ta kule har ta ce da direba ya ja mota su tafi, sai ga ta nan har da yar jakar ta da ta tsaya shiryawa, idan aka dauke Zainab wacce ta shirya tsaf cikin bakar rigar abaya, daga Ammy har su Halitta hijabi ne jikin su. Kafar nan ya sha takalmi mai tsini kamar mai zuwa club. Taikaici ne ya sa Ammy kau da kai gefe yayinda ta karaso, boot ta bude ta aje jakar kayan ta, sannan ta dawo jikin mota daidai saitin Falmat, ta na mai nuna ta da dan yatsa ta ce

    “Malama kin san dai ba za ki sani zama tare da Direba ba ko? Gwara ma ki fito ki bani waje!”

    “Kun ji irin halin sakarcin na ta ko? Sai da na ce mu tafi mu barta ku ka ce ah ah! Dan uban ki idan ba za ki shiga mu tafi ba ki sha zaman ki! Kai Malam Habibu ja mota mu tafi!”

    Cewar Ammy a fusace ta na mai watsa ma Zainab harara. Ganin direba ya tada mota ya sa ta bude gidan gaba ta zauna ta na zumbure zumburen baki da guna guni babu wanda ya tanka mata. Su Jauro na mu su Allah ya tsare hanya, tare da fatan Allah sa Malam be ji rauni sosai ba su ka dauki hanyar Maiduguri.

    Gudu direba yayi sosai dan kuwa Ammy ji take kamar ta rufe idanun ta ta bude ta ganta a Maiduguri. Tafiyar awa biyar sai gashi sun yi ta a awa hudu, dan kuwa baikwai daidai a Maiduguri ta mu su. Sun tarar gidan Malam da ke New GRA babu kowa sai mai gadi, gun shi su ka sami labarin mutuwar Direban da ke jan motar Malam, cewar Maigadin take Direban ya rasu be ko shura ba, haka kuma ya sheda mu su cewa Malam ma ya na can kwance rai a hannun Allah a nan UMTH (University of Maiduguri Teaching Hospital).
    Asibitin Ammy ta ce a kai su ba tare da ta tsaya jin sauran bayanan tashin hankali da Maigadi ke fada mu su ba. Tun kafin su isa asibitin ta ke kiran number din Hajja Dudu amma ya ki shiga, da kyar bayan isar su asibitin sannan ta sami numbar Gana, shi ya sheda mu su suna Emergency and accident.
    Tun daga nesa su ka hangi Hajja Dudu, Hajja Kilishi, Madu dan Malam na biyu sai kuma ‘yayan Hajja Kilishi mata guda biyu, Zinaru wacce ita ke bin Madu, sai kuma Kori wacce ita ce sa’ar Zainab. Kukan da su ka tarar Hajja Kilishi da sauran yaran na yi ba karamin daga mu su hankali ya yi ba, Gana da Madu ne kawai su ka iya daurewa duk da dai su ma din idanun su cike ya ke fal da kwalla, musammam Gana wanda gaba daya jinin Malam ya bata gaban farar rigar sa sanadiyar rungumosa da yayi sa’ad da aka dauko su daga wani dan karamin asibiti kusa da kauyen da su ka yi hatsarin.

    “Menene wannan jikin ka Gana? Ina Malam? Kar ka ce min jinin Malam ne haka jikin ka!”

    Cewar Ammy ta na mai ruko hannun Gana. Kai kawai ya girgiza mata dan kuwa tsoro da tashin hankali ya sa ya kasa magana, a kan idanun sa Direban Malam ya cika, haka kuma har lokacin salatin Malam ne ke masa yawo cikin kunne. Salati ya ke yi da karfi wanda duk wanda ya ji ya san Malam na cikin tsananin ciwo, Malam be dena salatin nan ba har sai da su ka iso Maiduguri, sai kuma tsit. Har Gana ya fasa kuka a tonanin shi Malam ma ya cika, shigar su asibitin aka sheda ma sa Malam na raye, sai dai yayi doguwar suma ne mai kama da mutuwa, wato ya shiga “Coma”

    “Gana ku fada min mana, ku amsa min dan Allah wani hali Malam ke ciki!”

    Ammy ta sake tambaya ta na mai fashewa da kukan da take ta kokarin dannewa.

    “Malam ya na ciki, kusan awa hudu kenan da aka shige da shi, Amma har yanzu dai shiru, hana rantsuwa dazu wani likita ya ce da mu suna iyakan kokarin su, Bayan wannan ba mu kara ji daga gare su ba Hajiya”

    Madu ne ya amsa mata ganin Gana be da niyar magana. Jin haka su Halitta su ma su ka kara saka na su kukan, waje ya kaure da koken iyalan Malam kai ka ce Malam ya cika, tun Madu na kokarin tsawatar mu su, har ya gaji ya sa mu su Ido, sai jama’ar wajan ne ke ba su baki.

    Su Ammy ba su jima sosai da zuwa ba Likita ya fito, ganin sa gaba daya su ka yo kan sa kowa da tambayar da ya ke masa, hakan ya sa ya nemi ganin Hajja Kilishi da Gana a Office, Ammy ta ce ba ta san zance ba kafar ta kafar Likita, ita ma din matar Malam ce. Su uku su ka dunguna zuwa Office din Likita.

    Bayan Likita ya yi kokarin kwantar mu su da hankali ne ya sheda mu su cewar sun yi iyakar kokarin su domin ganin Malam ya farfado daga doguwar suman da yayi Amma abin ya ci tira, dadin dadawa kuma ya sami “Spinal cord” injury, ya ji ciwo kashin bayan sa

    “Innalillahi wainnailaihi rajiun!”
    Cewar matan Malam suna mai fashewa da kuka. Cikin dakiya Gana ya furta

    “Haba mana dan Allah! Ku shiru ko ma ji bayani daga bakin sa, yau ko mutuwa Malam yayi kukan nan na ku ba zai amfana masa sa komai ba sai ma azabtar da shi da zai yi!”

    Jin haka duka su ka yi kokarin yin shiru, Gana na mai kallan Likita ya ce

    “Yaya kenan? Menene shawara ko fitar da shi za mu yi zuwa karsar waje?”

    Likita na duban Gana ya ce

    “Zan ba ka shawara tsakani da Allah, kada ku wahalar da Malam, ku bar shi nan gida Nigeria, a kuma masa addua, sauki na Allah ne, Allah ya yassare masa”

    Jin haka gwiwowin Gana sun yi sanyi kwarai, dan kuwa jiyayi tamkar likita na fadin Malam ba zai tashi ba. Da sanyin gwiwa su ka yi sallama da likita, in da ya ce a bar Malam ya kwana emergency ward suna monitoring din shi ko Allah ya sa a dace.

    Madu da Gana aka bari za su kwana wajan Malam. Duk yanda Ammy ta so ganin Malam ba a bari ta gan shi ba saboda gudun abin da ganin na shi zai haifar mata ta, haka duka su ka koma gidan Malam. Kamar yanda aka saba duk sanda su ka zo hutu Maiduguri, bangaran da aka ware na musammam domin saukar baki su Ammy su ka sauka. Manyan dakuna uku ne kowannan su da bandaki ciki, sai kuma madaidaicin Parlour mai dauke da kanan kujeru ruwan kasa. Halitta da Falmat dama tare su ke zama duk sanda su ka zo, Ammy da na ta dakin da ta saba sauka, sai kuma karamin ciki Zainab ke kwana ita kadai.

    Idan aka dauke Zainab babu wanda ya iya runtsawa daren ranar, Musammam su Hajja Kilish da su Zinaru, mutuwar Direban nan ya tsaya mu su rai dan sun saba sosai. Mutum ne mai kirki da haba haba da mutane. Daren ranar sarkin Musulmai ya sanar da ganin watan Ramadan, aka kwanta da niyar tashi sahur domin daukar azumi.

    Washagari da sassafe su ka koma asibiti, ba a mayar da Malam patient ward ba, Amma an bar su sun ga Malam. Ganin yanda aka daure kirjin Malam, ga robar samar da numfashi baki, hannun sa makale da robar ruwa, ga kuma na fitsari nan wanda yar robar ta fito ta cikin jallabiyar da su Gana su ka sanya masa daren jiya. Gashi fuskar Malam kumbure sosai goshin sa an daure da bandaje saboda tsayar da jinin da ke zuba da gan kan shi da ya fashe, babu wanda be zubda hawaye ba, lalle mutum ba a bakin komai ya ke ba.

    Matan sa duka biyun hannun shi su ka ruke, Ammy ke furta

    “Malam dan Allah ka warke ko na nemi yafiyar ka, na yi nadama, dan Allah ka yafe min”

    Zainab kuwa kallo daya ta yi masa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, Wai Dadyn ta ne kwance haka kamar mutum mutumi! Yanda su ka mayar da dakin tamakar gidan makoki, ya sanya Gana tsawatar mu su, tare da fadin

    “Duk wanda ya san zai zo mana asibiti ya mana kuka dan Allah yayi zaman sa gida, ba ma bukatan zuwan sa!”

    Hakan ya sa duk wanda kuka ya zowa sai ya fita yayi kayan sa waje gudun fadan Gana. Yan uwa da abokan arziki, ciki har da daliban Malam, Wanda ke sauraran tafsirin sa duk sanda aka fara azumin Ramadan, sun yi cincirindon zuwa duba Malam, Amma babu damar ganin shi likitoci sun hana. Asibitin nan babu wanda be san da kwanciyar Malam Birma ba, haka lungu da sakon Maiduguri haka labari ya zaga ko ina.

    Sai da Malam ya kwana uku Emergency Ward aka mayar da shi Aminity 4. Jikin sa dai ba canji, ya na kwance sai an tayar sai an kwantar, su Gana kullum suna cikin wanke kayan jinyar sa, da yi masa wanka idan ya kama. Satin Malam uku a asibiti aka fara shirye shiryen fita da shi India. Ammy da ‘ya’yan kuwa hado nasu ya na su su ka yi su ka tare a Maiduguri karo na farko da kan iyalan Malam ya hadu sosai, kowa ya dukufa wajan ibada da rokawa Malam sauki alfarmar wata Mai girma.

    Ranar da aka akai azumi ishirin da biyar, Ammy ce a wajan Malam, ita ta karbi Gana da Madu ta ce su dan je gida su huta.

    Zaune ta ke kan kujera, ta kurawa fuskar Malam Ido ta na mai kukan zuci. Sam ba ta lura da motsin da hannun Malam ke yi ba tsabagen nisan da zuciyar ta ta yi na tunani da begen Malam. Ganin murfin idon Malam ya motsa ya sanya ta kara matsawa kusa da shi da sauri yayinda bugun zuciyar ta ya karu. Kamar gizo haka ta kara ganin murfin idanun Malam sun motsa, haka ma yatsun hannun sa. Cikin ihu ta ke kwallawa su Zainab wanda ke zauna daga waje kira.

    Da gudun su su ka shigo ciki, Ammy na goge kwalla ta ke fadin

    “Ku duba ku ga yau Malam ya motsa, Alhamdulillah Malam ya motsa! Maza ki kira likita ku fada masa Malam ya motsa”

    Ganin hannun Malam na motsawa Halitta ta fita da sauri sauri gudu gudu kiran likita, Zainab da Zinaru kuwa hannun Malam su ka ruko, daga mai fadin

    “Alhamdulillah Daddy dama na san za ka tashi”

    Sai mai fadin

    “Malam ya tashi, Alhamdulillah Malam ya tashi”

    Likitoci uku ne da Nurses biyu su ka biyo Hilitta jin motsawar Malam, a zahirin gaskiya sun ma fitar da rai da tashin sa. Cike da mamaki iko na Allah su ka umarci su Ammy su ba su waje. Nan su ka bar su ciki suna duba Malam, su Ammy kuwa sai kiran yan uwa da abokan arziki su ke suna sheda mu su Malam ya motsa. Sai da su ka dau kusan awa daya sannan su ka sami damar ganin Malam, su Gana da Hajja Kilish tuni su ka karaso jin labarin farin ciki.

    Rashin baki be hana Malam aika ma iyalan sa da murmushi ba ganin yanda su ka zagaye shi. An cire masa rubar taimakon numfashi, sai na fitsari da na ruwa ne kadai ya rage jikin sa. Kowa burin sa ya ruke Malam, ko kuwa Malam ya kai kallan sa gare shi. Hajja Kilish kadai farfadowar Malam da kuma ganin sa ya dan kashe mata gwiwa musammam rashin maganar sa, duk da likitoci sun tabbatar mu su cewar a hankali Malam zai fara maganar.

    Sai da la’asar su ka yiwa Gana da Madu Sallama domin su koma gida a yi girkin bude baki.

    Ana gobe Sallah da sassafe Usman da Isa su ka dauki hanyar Maiduguri, Dan tun da Malam yayi hatsari ba zo sun duba shi ba. Shadaya da rabi su ka isa Maiduguri kai tsaye asibiti su ka wuce. Likitoci sun hana yan dubiya ganin Malam sai dai iyalan sa kadai, Amma Gana yayi magana su ka shiga. Duk da Malam ba ya iya magana, ganin su Usman sai gashi ya na fara’a sosai.

    Shi kuwa Usman ganin yanda Malam yayi fari sosai ya kara tsayi ya sanya shi zubda hawaye, cike da mamakin hawayen Usman Gana ya ce

    “Ai Malam Usman jikin Malam Alhamdulillah, yayi kyau fa sosai Malam ya sami sauki, ji fa yanda yayi fari sol da shi, kashin bayan sa ne ya sami matsala shi ya sanya ba ya iya zama ko tashi, ba ya iya motsa kafafun sa, Amma ka ga ai yana dan motsa hannun sa, da kuwa ko hannun ma ba ya motsawa wallahi!”

    “Allahu akbar, Allah ya bawa Malam lafiya”

    “Allahumma amen, in Sha Allah sauki ya fara samuwa, bayan sallah da sati daya ma za a fitar da shi India, mun sami wani asibiti na kwararrun likitoci a can”

    Madu ya amsa mu su, ya na duban Usman ya kara da

    “Na gane Malam Isa sosai, shi dai Malam Usman ne ban waya ba, ko shi ne sirikin namu ne? Mijin Yakura?”

    Dab! Gaban Usman ya fadi jin an ambato auren da ya ke kwana da shi ya ke tashi da shi a kulli yaumin. Gana na mai murmusawa

    ” Ya ce eh fa shi ne, Malam Usman wannan shi ne Madu, shi ne ke bi na”

    Nan Usman da Madu su ka kara gaisawa, in da Madu ya masa nasiha akan hakuri, a cewar sa zama da mace irin Yakura sai hakuri, dan kuwa mace ce mai taurin kunne. Sai da Gana ya dan zungure shi sannan yayi shiru, Usman kuwa cikin ran sa fadi ya ke be da buri da ya wuce a sauwake masa wannan karfen kafan da aka daura masa, wato auren Zainab.

    Ana yin azahar su Usman su ka yiwa Gana da Madu sallama, ga mamakin su sai ga Malam ya na ta motsa hannu kamar ya na son yiwa Usman magana, hakan ya sa Gana fadin

    “Tun da Malam ya kwanta ban taba ganin yayiwa wani mahaluki yanda ya ke ma ka ba Usman, ka ga fa kamar so ya ke ya ma ka magana”

    Cike da tausayawa Usman ya matsa gare shi, yana mai duban Malam ya sanya hannun shi cikin na sa, ganin har lokacin Malam be dena motsa hannun ba Usman ya ce

    “Malam Gana shin ko za a sami takarda da biro? Ina ga kamar akwai abin da Malam ya ke son ya fada min”

    Gana be ki ta Usman ba ya nemi yar takarda da biro, ya bawa Usman. Hannu na rawa Usman ya sanya biro cikin yatsun Malam, sannan ya dura hannun Malam bisa takardar. Ga mamakin kowa sai ga Malam na kokarin rubutu, amma ina rubutun ba ya fita tamkar na yaro dan koyo. Sai da Usman ya taya shi ruke biro, da ikon Allah sai ga Malam yayi dan rubutu da ajami sanin Usman be iya boko ba. Kalma biyu ya rubuta

    “Zainab…. Amana….. ”

    Ya na rubuta haka ya saki birun, Usman ya daga rubutun da ya fi kama da jagwalgwalon yara, da kyar ya iya karantwa, hanun sa cikin na Malam ya furta

    “Na ma ka alkawarin Malam, Ni da Zainab mutu ka raba”

    Cikin nuna jin dadi Malam ya murmusa. Jiki sanyaye Usman ya tura takardar da Malam yayi rubutu cikin aljihun sa, su ka yi sallama su ka tafi. Tafiyar su ba da dadewa ba Ammy da Falmat su ka ta zo. Ganin yanda Malam yayi fari sai murna ya kamata, fadi ta ke

    “Kai Alhamdulillah ji yanda jikin Malam yayi fari, yayi kyau wallahi”

    Madu ya ce

    “Wallahi fa Hajiya, Amma tunda ya kwanta ba mu taba ganin fara’arsa ba kamar na yau da wannan bawan Allah Usman ya zo”

    “Allah sarki ashe ya zo”

    Cewar Ammy cikin faduwar gaba, dan kuwa ji ta yi ba za ta iya jiran Malam ya warke ba, gwara ta nemi yafiyar sa ko ta sami sauki cikin ran ta. Kamar yanda ta kudiri niya, sai da ta nemi gafarar Malam kafin ta tafi, ta na magana ta na zubda hawaye hakan ya sa Malam girgiza mata kai, sai da ta ga ya na murmushi sannan ta gamsu. Duk sanda ta dan gifta ta wajan gadon sa sai ta ga ya ruko hannun ta, hakan ba karamin dadi ya ke mata ba, ta san ta isa matar so, tunda ciwo be hana Malam nuna mata so da kauna ba. Cikin so da kewar Malam ta yi masa sallama, har ta juya za ta tafi ya kara ruko hannun ta. Ammy na mai darawa ta furta

    “Ka yi hakuri Malam, da sassafe zan dawo na kawo maka tuwan sallah in Sha Allah”

    Malam na darawa yayinda kwalla ya dan gangaro daga idanun sa ya dan motsa kan sa. Ita ma Ammy kwallan ce ta fara cikowa idanun ta, ta yi saurin zame hannun ta ta fita, idanun Malam na kan ta har ta fice.

    Daren ranar da ke daren duba watan sallah ne gari sai hidima ake. Gana da Madu ma zaman hira su ka yi bayan sun sha ruwa, hiran Usman da auren shi da Zainab su ke. In da Madu ke nuna jin dadin shi akan hukuncin da Malam ya yanke na auren Zainab, cewar shi

    “Ka san Allah Gana da ka san yanda yarinyar nan Yakura ta lalace a Instagram da sai ka koka, ai na nuna maka wani hotan ta ka musa min ka ce ba ita ba ce, har da kwaba ta kar da na bari Malam ya ji, ai ga irin ta nan, yanzu da komai ya fito zahiri wa gari ya waya? Bari ma ka ga na nuna maka wasu da ga ciki”

    Ya shiga Instagram ya na neman shafin Zainab, Amma ga mamakin sa babu shi babu alamar shi. Cikin cije ya yatsa ya ce

    “Kash yar banza ashe ta yi deleting, Shi ya sa Hajiyar mu ta birgeni da ta hana su Zinaru kowani Social Media! Wallahi ba karamin jan hankali yara mata ya ke ba, musammam masu rawan kai irin Yakura!”

    Gana na mai mikewa bisa carpet din da su ka shimfida tsakiyar daki ya ce

    “Toh sai dai Allah ya dada kare mana su, ba dai an aurar da ita kowa ya huta ba, Madu bari na dan mike kadan, dan Allah ka sheda min idan an ga wata, Allah ya sa ba talatin za a yi ba, azumin asibiti babu dadi”

    Madu ya amsa da “toh” yayinda ya cigaba da danne dannen wayar sa. Cikin yardar Allah aka sanar da ganin wata, gobe sallah. Madu ne ya kira su Hajja Kilish ya fada mu su, tare da jaddada mu su lalle a kawo mu su karin kumallo da wuri.

    Ranar Sallah rana ce da iyalan Malam ba su taba manatawa da ita ba. Motsin Malam ne ya tada Gana da asubar fari, ganin halin da Malam ke ciki, jiki sankare idunun sa sun kafe ya sanya shi ihu ya na salati ya ke fadin

    “Madu Malam! Innalillahi wainnailaihi rajiun! Madu Malam, Madu kira likita!”

    Hakan ya sa Madu fita a guje. Hannun Malam Gana ya ruko, ya na hawaye ya ke fadin

    “Innalillahi wainnailaihi rajiun! Lailahailallah Muhamadur rasulillahi! Lailahailallah Muhamadur rasulillahi!”

    Malam na mai damke hannun Gana ya tsinci kan sa ya na mai amsawa da karfi ya furta

    “Lailahailallah Muhamadur rasulillahi sallahu……”

    Sai tsit, Gana ya na ji ya na gani an zare ran Malam, kullu nafsin zaikatul maut

    *Khadija Sidi*

     

    *Khadija Sidi*Auren Shehu

    (15 continuation)

     

    Kafin likita ya karaso har Gana ya sa tafin hannun sa bisa fuskar Malam, ya na mai karanto adduar neman rahama ya rufe idanun Malam, tare da jan zani ya rufe fuskar sa, sannan ya zauna a kasa dirshen ya na kuka kamar kankanin yaro.

    Ko da Madu da likita su ka shigo, Madu ya ga Malam rufe sai ya rufe Gana da fada, akan wani dalili Gana zai rufe Malam! Yaushe ya zama likita! Shikenan ya kashe mu su Malam!

    Gana ya cigaba da kukan sa ba tare da ya kula Madu ba, wanda sam ba cikin hayyacin sa ya ke ba. Likita be fasa yaye zanin da Gana ya rufawa Malam ba, ya sanya safar hannu na roba, ya dan kara duba gawar ya tabbatar ya cika da gaske, sannan ya zare robar ruwan da ke hannun Malam, ya fara kokarin zare na fitsari wanda ba a yi cikakeken awa daya da saka shi ba, Amma azarbar fitar rai ya sa shi cika har ya na komawa sama.

    Ganin likita ya kara mayar da zani ya rufe Malam nan Madu rungume gawar Malam, ya na fadin

    “Hasbinallahu wani’imal wakilu! Allah ya yafe maka kurakuran ka Malam! Allah ya ji kan ka! Allah ya sa annabi ya san da zuwan ka!”

    Cikan kankanin lokaci aka hade komai na Malam. Gana ne ya kira Hajja Kilish ya ce kada su kawo mu su abinci, ga su nan ma an sallami su, Malam ya sami sauki, gida za su taho. Ita dai ta amsa da toh, azahiri kuma jikin ta ne ya dau rawa yayinda bugun zuciyar ta ya karu, dan kuwa jikin ta ya bata akwai abin da ya faru, hakan nan ba za a sallame su ba, in ba dai saukin mutuwa ya samu ba. Aikuwa zatan ta ya tabbata sai ga su Gana da gawar Malam, sun shimfide mata tsakar falo.

    Hajja Kilish neman kuka ta yi ta rasa, ta na zaune daidai kan Malam ta ke tsawatar su Ammy da yara, wanda su ne su ka fi kowa ihu da kuka, fadi ta ke

    “Kul kada ku kara mana ihu a nan! Sakayyar da za ku masa kenan? Ku dena mana kuka na ce!! Yanzu Aleesha har da ke? Malam fa ya na jin ku!”

    Zinaru kuwa aljanu ta ringa tayarwa. Hajja Kilish tare da Gana da Madu ne su ka wanki gawar Malam, su ka masa sutura. Ko da aka dauki Malam za a fita da shi Hajja Kilish ta tashi da sauri za ta ruko makarar amma ina tuni ta yanki jiki ta fadi sumammiya, ba ita ta farfado ba sai bayan da aka sallaci Malam aka kuma kai shi gidan gaskiya. MashaAllahu Malam yayi mutane matuka. Su Usman da daliban Malam ba su sami janaiza ba, dan kuwa sai da aka yi awanni da birne Malam su ka iso. Sun zubda hawayen rashin Malam kwarai sanda aka kai su kabarin Malam su ka masa addua.

    Kamar yanda Malam ya ke yawan fada idan ya mutu kar a masa zaman makoki, su Gana sun yi kokarin hanawa amma ina hakan ya ki yiyuwa, kullum gidan cike ya ke fal da jama’a, yan unguwa, yan uwa da abokan arziki abin takaici shi ne yanda gidan mutuwar ya so ya zama gidan biki, iyalan Malam da su aka yiwa rashi ne kadai ke cikin bakin ciki da kuka, in da ake bikin sallah su kuma su ke fama da bakin ciki da alhinin rashin Malam. Ranar da Malam ya cika kwana uku su Usman su ka nemi yiwa su Ammy gaisuwa, duka iyalan Malam sun fito an gaisa, ban da Zainab wacce a cewar ta zafin mutuwar Malam daya ya ke da zafin ganin fuskar Usman. Ganin ba ta fito ba Usman be tambayi ina ta ke ba, yayiwa su Ammy gaisuwa su ka juyo Kano ya na mai tunanin yanda rayuwa za ta kasance akan alkawarin da ya daukarwa Malam.

    Ranar da Malam ya yi bakwai Ammy ta so komawa Kano, yan uwan Malam ne su ka ruke ta da ta zauna nan gidan Malam ta gama takaba tare da yar uwar ta Hajja Kilishi, tunda ko ta je Kano ma gun wa za ta koma? Duk yan uwa suna nan Maiduguri. Da wannan ta hakura ta zauna.

    Sai da Malam ya yi sati biyu da rasuwa, jama’a ka dan dauke kafa. Gidan ya fara shiru, gashi babu wanda ya ke cikin walwala musammam mutum hudu, kusan za a ce mutuwar Malam ta fi duka, wato Hajja Kilish, Madu da Gana, sai kuma Halitta. Gaba daya ta rame ta lalace, sai ta kara fari da manyan idanu.

    Zainab kuwa bayan mutuwar Malam, babban burin ta shi ne a gama alhinin mutuwa a zo a raba auren ta da Usman, dan kuwa ko sama da kasa za ta hade ba za ta yarda da auren ba, musammam yanzu da aka wayi gari babu Malam a doran kasa.
    Da la’asar sakaliya Madu da Gana su ka karbi bakwancin Shiek tare dan shi Sudais da kanan sa mata biyu, Zara da Ummi, kasancewar sanda aka yi rasuwar ba sa nan suna Saudiya. Bayan sun yiwa su Ghana gaisuwa ne Madu ya shigar da matan cikin gidan wajan su Hajja Kilishi, tare da sheda mu su cewar Shiek da Sudais na Falon waje, idan sun shirya za su shigo su yi mu su ta’aziya.

    Ya ko ci sa’a Hajji Kilishin zaune ta ke tare da Ammy. Kanan Sudais su ka mu gaisuwa, tare da neman su Zinaru wanda dama su su ka sani, duk da dai suna kwadayin ganin amaryar yayan su da aka ce diyar amaryar Malam ce da ke zaune birnin Dabo. Zinaru da Kori ne su ka fito jin zuwan su Zara. Suna cikin gaisawa ne Madu ya dawo biye da shi Sudais da Shiek ne.

    Bayan sun yiwa su Hajja Kilish gaisuwa, Shiek ke tambayar Ammy ina su Halitta su ke, da fatan ba su koma Kano ba ko. Ammy ta ce
    “Eh suna nan tare da ita, Kano ai ta yi mana nisa in ba dai Zainab wacce ke da miji a can ba, bari a kira su, Kori kira yan uwan ki”

    Kori ta tashi ta shiga kiran su. Tun tashin ta gaban Sudais ke faduwa, ya zubawa kofar da Kori ta fita idanu, da ke shi ne ke zaune kurar da ke kallan kofar, Shirin ganin matar da Shiek ya zaba masa ya ke cikin zulumi.
    Jim kadan Kori ta dawo biye da ita Falmat ce sanye da hijabi har kasa, kallo daya Sudais ya mata ya tabbatar ba ita ba ce amaryar ta sa tsabagen kuruciya da fuskar Falmat ta nuna karara duk da kiban da ta ke da shi. Cike da ladabi ta durkusa har kasa ta gaishe da Shiek da Sudais. Su ka amsa tare da mata gaisuwa. Ammy ta gabatar da Falmat a matsayin autar ta.

    Zainab wacce har cikin ran ta ba ta yi niyar ganin baki yau ba, da kyar ta tashi daga kan gado, bakar abaya ta ja ta dora bisa yar karamar rigar da ke jikin ta, ta ja mayafin abayar ta rufe kan ta. Za ta wuce ta hango Halitta cikin dakin su, bisa sallaya. Tun da ta ji sakon isowar Sudais ta ji wani bakin ciki ya kara ziyartar zuciyar ta, ta ma kasa tashi bare ta fito su gai sa.

    “Malama wanda aka bawa ke ya zo,, you better bring your ass to the parlour, aha bari na je na ga wani local champion Daddy ya bawa”

    Cewar Zainab cikin tsoka na, ta wuce ta na yiwa Halitta yar dariyar mugunta. Tun kafin ta karasa falon ta fara jin wani irin ni’mantaccan kamshi, zuciyar ta daya ta sanya kafar ta hakan yayi daidai da hada idanu da shi, gaban ta yayi mummunar faduwa har ta tsinci kanta ta na mai fadin

    “Hasbinallahu wani’imal wakilu!”

    Ta sha ganin maza wanda su ka amsa sunan su maza ma su kyau, Amma ba ta taba ganin wanda ya tafi da imanin ta kamar Sudais. Sudais wankar tarwada ne mai duguwar fuska da ke dauke saje da gemu baki wuluk har sheki ya ke, ba wani dogo ko siririn hanci gare shi ba, girma da tsayin hancin sa yayi dadai da fasalin fuskars sa, haka kuma idanun sa da ke manya dan ko ita Zainab ba za ta nuna masa kyawun idanu ba. Kasancewar zaune ya ke kan kujera be boye tsayi da fadin da ya ke da shi ba, sai ma kwarjini da ya mata. Idan ko gayu da wayewa ne kallo daya za a yiwa Sudais a san gidan shi aka zo, murmushin da ya sakar mata, gefan kumatun sa biyu su ka lutsa wato alamun dimpol ne ya dada rikita Zainab wacce ta tsinci kanta ta na mai shigowa Falon da sauri gudun kar sauran yan falon su lura da halin da ta tsinci kan ta ciki. Cikin ran ta fadi ta ke

    “Innalillahi kar dai wannan shi ne mijin da Dady ya so aura min? Ya ilahi Allah wallahi da ni ya fi dacewa! Wayyo ya hadu! He should be mine! Da ni ya dace!”
    Da kyar ta iya daurewa da gaishe da Shiek ya amsa tare da mata gaisuwa, sannan ta kashe da Sudais, wanda ya amsa ya na mai duban ta da kyau. Tun shigowar ta ya so kare mata kallo, Amma yanda ta ke kallan sa ya sa shi kasa tsayawa ya kalle ta da kyau har sai bayan da ta shigo ta zauna kusa da Falmat. Ko shakka babu ya amince da abu daya, Zainab ta amsa sunan kyakkyawar mace ta ajin karshe, kuma ga dukkannin alamu wayayyiya ce kuma yar gayu, sai kuma akwai abinda ya ke so da be gani a tattare da ita ba, shi kan sa ya kasa gane menene abun, haka kuma ya tsinci kan sa ya na mai fatan Allah ya sa ba ita ba ce matar da Shiek ya zaba masa ba.

    Gaisuwa ya mata, ta na cikin amsawa yaji sassanyar muryar Halitta ya ziyarci kunan sa ta sigar sallama wanda shigowar ta yayi daidai ta furucin Ammy na

    “Wannan ita ce Zainab, wanda mu ke kira Yakura ita ce babbar su”

    “Allah sarki ita ce Malam ya sheda min maganar auren ta ranar da na masa ganin karshe, Allahu akbar duniya kenan”

    In da Zainab ta ji kamar ta kurma ihu jin furucin Shiek akan auren ta, Sudais kuwa wani dadi ne ya ziyarci zuciyar sa yayinda ya zubawa Halitta idanu, sanye ta ke cikin hijabi fari kal har kasa, kan ta sunkuye har ta shigo falon ba ta kalli Sudais ba bare ta lura da kallon da ya ke mata

    “Alhamdulillah for you, Alhamdulillah, she so MashaAllah! Na gode Abba da wannan zabi na ka”

    Cewar Sudais cikin zuciyar sa, wanda ya fadada fara’ar sa dan kuwa ya kasa boye farin cikin sa na ganin Halitta, ta yi masa har cikin zuciyar sa.