Author: Novels

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 24

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 24

    EPISODE 2️⃣4️⃣

    Yau nazo da gangariyan rahoto wato PRACTICAL CHINA IMPORTATION class💃💃
    Ga inda zaki koyi asalin ilimin saro kaya daga china, za’a koya miki ko dubu 20 kikeda shi zaki iya fara saro kaya Wayyoo Allah na, babu wani dogon zance kuzo mu shiga WAITLIST din nan tare💃

    Danna link ki shiga group din waitlist
    https://chat.whatsapp.com/FIKdtOLn4vjGOQ1bHuI9l0

    24
    Sauka kasa yayi zuciyanshi na masifan tafarfasa yabude mota yashiga ko gaisuwan da maigadi kemai be iya ya amsaba yaja motan shi sabida yanda ranshi ke soyuwa yanar gidan, he’s just angry da kowa, Hajiya tunda takoma kano taki daukan wayanshi, koya kira Meena yanason magana da ita bata amsa tace agayamai idanba ya nemi Ummi bane he shouldn’t bother about talking to her, ga kuma Ummi dazata kama tabar gidanshi tanamai zuciya akan abinda baitaka kara ya karyaba dan shi har yau baiga wani takamaimen abu dayamata ba, kuma takama takashe waya irin she doesn’t even wants him to look for her, she’s done dinnan, saikuma Alhaji Musa yana wani gayamai ya sake Ummi shi zai aura sabida an gayamai shi auren dan ya saketa ne yayi, now kuma Hadiza ta tsareshi ta titsiyeshi kaman danda ta haifa saiya mata bayani mesa yayi abinda yayi, why is everyone doing yanda yaga dama dashi he’s just so tired, mesa the peace he’s yearning for at this age yakasa samu? Why? Mesa stubborn women ne suka cika rayuwanshi? Da kyar ya iya kai kanshi office yawuce sama yashiga office nashi yama rasa ina zesa kanshi yaji dadi.

    Yanda zuciyan Hadiza ke bugawa zaka dauka kararrawa ake bugawa aciki, hannunta har lokacin nakan kuncinta da Nura ya mata, bakinta kuma asake tabishi da kallo har saida taji tashin motanshi sannan tawani zube zaune awajen, kuka ke zuwan mata sosai amman tahana kanta no bataso tasake zubarma da wanda yamata bakin zagi haka, yau itane Nura zai hurting nata haka for the second time dan auren Ummi was first, wannan kuma nabiyun, ita Nura zai kira zero! Ita, a Cinderella, Nigerian kardashin, business mogul queen, Oga wife like her, yasan how many online business vendors ke shishige mata, all matan abujan nan da gangan suke zuwa shagonta abaje bajinta ayi shopping just sabida aburgeta tayi kawance dasu, infact duk randa take shago anmafiyin ciniki, wani kalan gyarane batayi, saloon treatment daban daban, even a sex din this days she’s trying alot, inhar namiji zai ciki yakawo kuma how dare he calls you zero? Da ace Nura tun farkon aurensu ya nuna yadamu da sex he wants it da babu yanda zatayi dole ta dinga bashi, she’s not lying but itada Nura nazama gida daya for 2months abu bai shiga tsakaninsu ba, wani kalan maita yarinyar nan tazo tazuba ajikin mijinta cus she don’t recognize Nura anymore, ita Nura zai daga hannu ya ketama mari? Why is he so angry? Bata taba ganin Nuri na wannan fushin masifan ba, metamai dazai mata kalan marin nan??? Parking motan dataji anyi yasa ta zabura ta mike tayi stairs tasan shine halan yadawo ya lallasheta ne daidai tana karasa saukowa kasa daidai ana bude kofan falonta ana shigowa.
    Baraka da Zeena ne suka shigo rikeda wani hamper na snacks da fruits aciki suka hada ido dasauri wani irin kunya Hadiza taji ganin kawayenta ne ga gidanta kacha kacha ga jan idanunta maybe akwai hawaye aciki dasauri daga Baraka har Zeena suka karaso cikin falon, Zeenah tayi wajenta da gudu tana bude hannu tace “oyoyooo my Sick baby sannu, wlh nida hubs munje Maldives ne ai I told you about the birthday trip dazaimin saisa banzo na gaidaki ba I just greeted you a IG da naga kinsa, jiyan nan nadawo yanzu ma shago mukaje akace kin dawo gida nacema Baraka let’s go gidanki, sannu Haddy, how are you feeling now”? Murmushi Hadiza ta kakalo tana kallon Zeenah dataci gayu tasha gwalagwalai tayi kyau takara kiba sai sheki take, tace “na warware tass nida harnayi resuming zuwa shago ma” dasauri Baraka data ijiye hamper anan falo ta taho wajen benen tace “sannu Hadiza Allah baki lpy, ya duk na ganki wani iri haka” tai maganan tana mika hannunta dasauri zuwa kumatunta tace “an mareki ne naga kaman shatin hannu” dasauri Hadiza zata juyar da kanta Zeenah dabata luraba takama habarta tana zaro idanu tace “what happen to your face? Kinga hannu shaaaa a fatan fuskanki yayi jazur sabida farin fata, who slapped you”? Wani kalan fizge fuskanta Hadiza tayi tace “dalla kubarni waya isa ya mari Hadiza aduniyan nan are you guys for real? Zoku zauna bari nakawo muku drinks” tawuce zata tafi dasauri Zeena takama hannunta dan she’s just like Hadizan saisa itace best friend nata.

     

    Tace “Besty kaman ya bari ki kawo mana drinks I don’t understand, in your own house kene ke serving guest drinks ina yar aikin ki?” Zeenah tamata tambayan kai tsaye dan cikin duka mutanen Hadiza banda yan uwan ta najini babu wanda ta fadiwa Nura yayi aure dan abin kunyane agareta, zatai magana Zeenah tace “tell us we three are childhood friends ku munma juna dariya kanmu mukamawa remember yanda mukema Baraka fada, what’s happening? Who slapped you haka a fuska? Sannan ina yar aikin ki? Why is your house so dirty haka? Look at falon nan see dinning why is everywhere so scattered and disorganized, I don’t even wanna talk about yanda kika rame cus I wanna believe rashin lafiyan dakikayi ne yasaki kika rame but who slapped you this hard eh”? Baki Hadiza tabude zatai magana kun gane irin kukan nan da baka bashi izinin zuwa ba amman kawai sai yazo without permission shiya kufce mata da sauri Zeenah ta yarda jakanta tace “ohhh no come here sweetheart it’s okay, it’s okay, who hurt my Didi this much? What’s going on Didi talk to me, Baraka zo” dasauri Baraka ta zo dukansu suka rungume Hadiza kafin Zeenah tace “muje sama mu sauna kawo mata ruwa Baraka” gyadamusu kai tayi Zeenah tawuce da crying Hadiza sama Baraka kuma tawuce fridge ruwa a dauka suka wuce sama, Zeenah tabude ruwan takai bakinta tace “sha Hadiza” kadan ta kurba ta ijiye ruwan, ahankali tace “menene Hadiza talk to me who slapped you”? Cikeda Jin nauyi da kunya but sun riga sun kamata babu yanda zatayi tace “Nura ya mareni!” Daga Zeenah har Baraka zaro ido sukayi cikeda mamaki Zeenah tace “Nura yamiki wannan kalan marin?” Gydamata kai Hadiza tayi tana fuzarda iska, rai abace Zeenah tace “baki suing nashi for domestic abuse ba are you okay Hadiza? Your husband is abusing you haka, maisa baki daukomai yan sanda ba”? Dasauri Baraka tace “haba Zeenah wani kalan yan sanda kokuma tayi suing nashi sabida just this one time mari is not something dayake faruwa kullum shekaransu nawa tare yataba marinta ne” cikeda masifa Zeenah tadagama Baraka hannu tace “kinga just keep quiet and allow me talk to my friend ke dama kin saba tolerating all sort of trash daga mijinki saisa he doesn’t respect you, Hadiza and you are two different people, she knows her rights unlike you akanme, akuma kan wani dalili Miji zai kama yana taba lafiyar jikinta tai shiru look at her precious face, kinsan da kasan waje ne kalan hukuncin dazaihau kan Nura kuwa look at her face for crying out loud yadauka jaka ya auro ko tumakiya, yadauka bakida gatane am calling my lawyer inama jakana” ta jujjuya ganin bataga jakanta ba yasa ta mike tawuce kasa rai abace, Baraka ta kalli Hadiza dake goge kwalla tace “yanzu zakiyi suing Nura sabida ya mareki Hadiza? Me aciki dan Nura ya mareki yana marinki da ne? Why are you and Zeenah like this eh? Nura fa baban yaranki guda biyu ne shi zaki maka a kotu? Ko darajan yaranku bazaici ba”? Shiru Hadiza tayi daidai Zeenah na karasowa tace “say whatever you wanna say Hadiza is not you and can never be you, duk matan dazata zauna miji na dukanta anytime dayaga dama jakace kuma yar akuya, kuma dakikiya ni Zeenah nafadi haka, and idan tabari wannan to slide to Nura yadingayi kenan kalleni nan Hadiza” Hadiza takalli Zeena tace “ask Baraka dazu da dasu Hanna da Saudat da some members na meeting dinmu zamuzo fa but mukace bazamu iya jiransu ba, da dasu mukazo da bakiji kunyan duniya ba? Da gulmanki saiya zagaye Abuja fa ana mijinki na dukanki, waye Nura? Duka kudin gudanawa gareshi da he feels zai iya miki kome yaga dama haka, waye ubanshi? Shida kudinma nemansu yayi ba haihuwanshi akayi aciki ba, look at you Hadiza yazaci idan kin rabu dashi zaki rasa mijin aure ne? Koya dauka shi Autan maza ne? Kinmasan how beautiful you are kuwa Hadiza? Wlh yarabu dake saikin sami mijin dayaci ubanshi akomi, just like me yanzu minister nake aure, da Bala yafara dukana dayaga I know my right namakashi a kotu ya biya ai yagane koba komi na batamai clean record nashi, sunanshi is registered under domestic violence yanada record dazai bishi ko’ina, sannan na barshi, u were there for me lokacin look at me yau married to minister dakeda mata biyu nine ta uku but nice yar gaban goshi, ki watsar dawani soyayyan nan ki yaki Nura fa, wlh kuka rabu da Nura zaki sami mijin dayaci ubanshi akomi barinma yanda aka sanda ke a abujan nan da business naki haba, kina daga cikin top housewives of Abuja fa dake representing Abuja who d f*ck is Nura? Take action against him now kafin ki zama Baraka part two” rushewa da kuka Hadiza tayi tashiga fadamusu duka abinda ke faruwa tundaga auren Ummi, mutuwan zaune sukayi sai kawai Zeenah tafashe da kuka tace “Baraka let’s go tashi mutafi Hadiza bata dauke mu as family ba, Baraka koda you were going through something, dudda bazakijin shawaran mu but sharing heals right and we are always there for you cus an zama daya we never abandon you” Baraka tace “kwarai, I don’t agree with ways naku but I’m always grateful to have the two of you as friends dina I know sometimes kumun dariya kuji haushina kaman zaku daken but baku taba kai magana ta waje ba it remains among us, and both ke da Hadiza always helps me financially, idan something come up a meeting na association namu zakumin anko baku taba bari an gane inada wata matsala ba kallonmu ake dukanmu ukun daya, I know kuke ganin abu ya bambanta dani but friendship naku is genuine, Hadiza why will you be going through something like this bazaki fadamana ba”? Cikin kuka tace “zakumin dariya barinma ke Baraka I remember yanda nake miki dariya ina kiranki wawiya mara wayau, that’s why” girgiza mata kai Zeenah tayi tace “the three of us are one saidai sauran kawayen mu su mana dariya but never us Hadiza, Nura babban shegen dan buhun uba ne, kici uwarsa wlh yagane ke ba kanwar lasa bace, being a wife doesn’t make you a slave, shi wani kalan mara imani ne, look at how big this house is, taya zaki fara kiyi shara kiyi mopping kiyi wanke wanke ki tattara kayan yara ki wanke a washing machine ki shanya, kiyi kuma nashi, kiyi girki ki wanke plates, u are working class woman fa your business needs you naaa Hadiza this is pure wickedness Nura bayason ci gabanki he wants your business to crumble saisa yakeso kina all those aiki ke kadai without help how will you manage? Ko kula da yara aka barki yimusu wanka feeding them, homework getting them ready for school is it easy? Kananun yara gareki fa 4yrs and 2yrs how will you manage”? Ahankali Baraka tace “ni yarana hudu nike komi” Zeenah tace “you are not working so karki hada kanki da Hadiza you are housewife” takalli Hadiza tace “clean your tears kada ki kara wasting hawayenki akan da namiji barinma wanda yayi betraying naki kaman Nura, wlh da yarinyar nan nanan yau da saina sa an kulleta a barrack su mata jina jina a kwakule tsinanniya, ita harta isa ta yaudareki ta aure miki miji suna cin gindi da daddare suna ihu suna nema su kasheki kuma kika zauna, are you mad Hadiza? Yau idan zaki mutu let’s assume baida wata matan ma kafin 40days wlh Nura yakara wani aure ballema ya auri yar aikin ki shagalinsu zasuyitayi abar family ki da kuka cus yaranki bayi zasuyi ba they’re still very small yan uwan ki kawai zasuyi bakin cikin ki Nura, Nuran uban meyeshi kin nanama kanki sonshi mugun mutum is he the only man on this earth? My dear clean your tears” goge hawayen ta Hadiza tayi tanajin karfi na zuwan mata wannan ne kalan shawarma dataso Anty Jams tabata amman bata bataba, sai shawaran dayasata cikin wahala kawai all this while.
    Zeenah tace “Hadiza it seems you are lost kin manta waye ke lemme remind you girlfriend” Zeenah na kallonta tace “Hadiza you are a strong independent woman wacce ko da namiji ko ba namiji you can live your life and survive on your terms, you are a feminist Hadiza!” Wani karfi Hadiza taji yashiga jikinta, Zeenah tace “idan zaki mutu die of normal course badan namiji ba, a man is too small yabaki ciwon zuciya! Ke with ko without Nura you have you can have a better life, kinada booming business worth millions of naira, you have cars, kinada yara tell me mekike bukata awajen Nura da zai dinga marinki bayan yaci amanarki yana miki tinkaho”? Ahankali tace “babu! I can do everything for myself, I can live my life yanda naga dama, I have money to sponsor any desire na, inada gida dana siyama kaina a kano” Zeenah tace “good now kin soma dawowa, ke Nura ya auran miki yar aiki baki tadamai hankali ba kika cigaba da zama dasu ana cusa miki bakin ciki, yarinya na kada takashi agabanki left and right ba kunya ba tsoron Allah in your own house, gidanki fa Hadiza asiri Nura yamiki ko yamiki rufa ido da rufa baki ma duka? Ya taushe miki bakine da bakici kutumar buhun bura ubansu ba dagashi har yar aikin kihanasu kwana agidan” ahankali Hadiza tace “looking back wlh I’m regretting daban tadamai hankali ba, Zeenah banmasan meya shigeni ba those days, bansan wani kalan wayau Nura yamin ba kawai yadinga kwanciya dani yanamin some things that I can’t even explain, bansan wani kalan brainwash and mind wash yamin ba but anyi an gama, yashani kuma na warke, Is time to let him know know that I am still that Hadiza kuma daidai nake dashi, first and famous bari na samo yan aiki dan koni I hate dirty, zan dauki yan aiki guda hudu, 2Nanies masu kula da Aman da Amali, sai biyu masu gyaran gida da aiki, Nanies din su Aman inason yan Philippines dinnan irin yan shekaru 40 educated ones dazasu din tayasu yin homework, sai I want a chef mai girki yar tsohuwa hakanan sai mai shara da gyaran gida kuma yarinya age 12-15 haka kada tawuce 15yrs, I don’t care konawane salary su i will pay” dasauri Zeenah tace “lemme call my personal person goben nan zakiga tasamo miki” tace “kira nima I will call my lawyer I just have to sue Nura let’s settle this score, koda zanyi withdrawing lawsuit din daga baya but yagadai i can take action idan yataba lafiyan jikina sabida karya kara kuskure yace zai taba educated independent woman like me” ihuu Zeenah tayi tahau tafi tace “now you are talking, my friend is back kicima Nura kutumar babakeren uba, ke maza fa sunfi tsoron maicin ubansu” dasauri Hadiza tace “I believe you ai sanyin danayi kwana biyu yasa raini ya gitta tsakaninmu wai harda marina, ni Nura zai daga hannu ya mara, kinga snap my face i will use it as evidence” tabama Zeenah wayanta, karba Zeenah tayi tadauki hotunan fuskan Hadiza harda cemata “yi kaman wacce taci kuka takoshi” Hadiza tai haka tai clicking snap tabama Hadiza wayan, duba hotunan tayi ranta na kara baci sabida yanda yatsu biyar suka fito a fuskanta dodar dan da duka karfinshi na maza yamata marin saida taga duhu.
    Mikewa tayi tace “kutashi muje lemme go nayi gyaran jiki and facials kafin hannunshi yazama permanent tabo a fuskana.
    Tashi sukayi sai kawai ta rungume Zeenah tace “I love you best friend, you are better than my own blood sister, you just brought back light into my life” Zeenah tace “absolutely no man aduniyan nan ya isa yace zai takamu wlh, we know our right, mari fa ko a shari’a batada kyau, ai Nura deserves more, ki yarda wani stupid love who love help kuyi settling score yakoma yana tsoronki zakiga wlh zai shiga taitayinshi” Hadiza na murmushi tace “da ina cin ubanshi ma yafi sona, yanzu dana dena wai Nura ne yasamu liver daga hannu ya kodamin mari ni Hadiza, I will mess him up wlh”. Suka wuce suka fita daga gidan.

     

    Jama’a like I said I just wanna portray the major issues dake kawo rabuwan aure a zamanin nan sabida ku gani kusan daga ina mistakes din ke zuwa, ta yanda zamu karanta mu gyara idan munayi dan believe me most of us munada one of two dabi’un Hadiza Allah dai ya kyauta yakuma shiryan damu.

    But then I have a question, what do you think can change mata masu strong opinion din Feminism???

    Note dukan mace baida kyau fa, please maza masuyi su dena, cus kahadu da macen datasan kanta she can ruin you completely da career ka so adena dukan Mata maza 🔊
    Dukan mace ke jawo case din dambe between mata da miji, daganan kaga an kashe juna, ko mata ta kashe miji ko miji ya kashe mata, ko ajima juna rauni mai muni Allah ubangiji ya shirya damu.💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

    ✍🏻M SHAKUR

    EPISODE 2️⃣5️⃣

    *ROYAL JELLY* *(MAIDA TSOHUWA YARINYA)* 🔥🔥🔥💃💃💃💃 Wani kayan sai amale wannan supplement shi akecema maida tsohuwa yarinya ita Kuma yarinya ta koma jaririya😂💃💃💃💃💃💃💃💃💃 Ina kuke Mata masu aji waanda sukeso suga suna walwali kamar tauraro toh gafa dama tasamu kiyi washar washar abinki…..🔥🔥🔥🔥⭐⭐⭐⭐ ⭐👑 Royal jelly nasa jikin mace yayi glowing mace jikinta yayi Kamar tangaram😍😍 ⭐👑 Royal jelly natsoro da gashin mace yayi kyau ⭐👑 Royal jelly na gyara mace ciki da wajenta ⭐👑royal jelly na fidda shape din mace…💃💃 ⭐👑 Royal jelly na Hana fatar mace tamukewa , yasa tayi looking fresh ⭐👑 Yanasa mace yayi looking under age dinta💃💃💃💃💃kiji ana wacce ke kullun kamar wata budurwa🔥🔥🔥🔥 ⭐👑 Royal jelly nakara hasken Ido yakuma gyara gashin ido 🔥🔥🔥 ⭐👑 Royal jelly na tsirar da farce da kwarinshi… Idan kinji ana maganar glowing to kici birki a royal jelly 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥⭐⭐⭐👑💃💃💃

    https://chat.whatsapp.com/KU8Mqd2Mo530Pc14hc7QOG

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 25

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 25

    25
    Waiwaye baya kadan.
    Yau kwanan Ummi uku agidan kanin mijin Ya Aisha dashi da matarshi basu da matsala matarshi saita zama mata nabiyu da Ummi tayi kawance a duniya, itadai Ummi binsu take bazata iya kirga wajajen da aka kaita ba tayi thumb print, anmata passport menene menene.
    Dukta rame sabida yanda tunanin Nura ya addabi zuciyanta kusan bata iya baccin dare most time da safe bayan asuba take bacci.
    Yauma kaman kullum tana zaune matar gidan ta shigo da waya a hannunta tace “gashi Ya Aisha ce” amsan wayan Ummi tayi matar tawuce tafita ahankali tace “Hello Ya Aisha ina wuni” murmushi tayi tace “Ummi ya kike hope yau kin tashi lpy, baki kuka jiyaba ko” dan murmushi Ummi tayi tace “banyiba” shiru Anty Aisha tayi chan tace “Ummi Hajiya nacikin damuwa sosai sabida ke ciwonta na neman yatashi, tace nasa akaiki kano immediately” dan bugawa kadan zuciyan Ummi yayi dan wani kalan kunyan Hajiya taji tanaji Ya Aisha tace “nasa Ahmad yamiki booking flight jirginki is by 1, kije wajen Hajiya Ummi tace bata yarda kizo Egypt wajena ba, nayi nayi nayi da ita taki, namayi magana da Gwaggo yanzu kafin kafin nakiraki ta yarda kije Kanon tunda Hajiya takoma kano” cikin sanyin murya Ummi tace “Hajiya nada ganin likita a Abuja mesa takoma kano”? Dan murmushi Ya Aisha tayi ganin even cikin damuwa Ummi still cares about Hajiya tace “sabida ke mana antaba mata diya” hawaye Ummi taji sun zubomata tace “Ya Aisha nama mamana laifi nasan tana fushi dani taya tana gari zan kama nabar gida batare dana jirata ba” Dan murmushi Ya Aisha tayi tace “kada ki damu Hajiya bata iya fushi damu yaranta ba, zata yafemiki, yanzu tashi ki shirya, idan kikakai kikai settling zan kara magana da Hajiya nafiso kizo nan kiyi karatu abinki, yau koda baki tareda Nura this is the least abu dazan miki Ummi kinfi haka wajenmu” Gyadamata kai Ummi tayi sukai sallama.
    Wanka Ummi tayi ta shirya Matar Ahmad tamata kyautan sabon atampa da takalmi suka kaita airport sai kano ita Ummi abin har mamaki yake bata yanda itane tane hawa jirgi haka tana sauka ga mamakinta taga Meena da gudu Meena ta rungumeta saikuma ta kama hannunta har zuwa wajen wata babban jeep da direba ke gaba yana jiransu suka shiga sai gida, wowww gaskiya Nura naji da Mamanshi babban hadadden gıda ya ginamata durmemen gaske fa ga motoci biyu, da jeep dawata karaman Camry, ga masu taya Hajiya aiki dan indai tana gari tana bada abincin sadaka duk ranan duniya da magrib haka almajirai da yara zasuyi layi akofar gıda.

    Suna shiga babban falon gidan Hajiya suka gani zaune kan babban lallausan carpet nata rikeda charbi a hannu hada ido sukayi da Ummi data sauke idanunta kasa da sauri ta tsugunna ahankali tace “Hajiya ina yini” ba yabo ba fallasa tace “sannu da zuwa Ummi” takalli Meena tace “kaita dakinta ki kawo mata abinci taci tahuta” Meena takalli Ummi da kanta ke kasa tace “tashi muje ciki Ummi” kasa tashi Ummi tayi Hajiya tace “tashi kuje ciki Ummi” da kyar Ummi ta iya tashi tabi Meena sukaje ciki wani lafiyayyen dakine aka kaita ahankali Ummi da idanunta sukai ja tace “Meena Hajiya fushi take dani” hannunta Meena takai ta share saman idanunta tace “bake kadaiba, harda ni, da Ya Nura, da Ya Aisha ma data boyeki bata tashi gayama Hajiyaba sai jiya, nihar tausayi tama bani da Hajiya ke surfafa mata, amman yanzu tunda kinzo nan matsala yazo karshe damuwanki yasa taketa fada, kibar Hajiya da Ya Nura itane daidai shi kuma kada ki damu Hajiya batada riko zata sauko, jeki alwala bari na kawo miki abinci” gyadamata kai Ummi tayi tawuce tafita tazauna tai shiru Meena ita ke keeping nata company Hajiya baruwanta dasu.

    Wuraren 10 Ummi ita kadai adaki dan dakin Meena daban dudda taso tazo ta kwana da Ummi Hajiya ta hanata Ummi taji takasa bacci, Hijabi ta dauka tasaka tabude kofa tafito, dakin da Meena ta gwadamata dazu shine na Hajiya tawuce tadade gaban dakin kafin tayi sallama ahankali tareda budo kofan kadan Hajiya na zaune tasa wani farin glasses a idanu da wata yar littafin azkar a hannunta takalli Ummi tareda yin shiru batace komiba, ahankali Ummi tashigo dakin tareda maida kofan tarufe tazo har gaban gadon sai kawai tayi kneeling taredakai hannayenta takama kunnenta tabude baki zatai magana saikuma takasa tafashe da kuka sosan gaske yanda kasan Mama da yarinyanta datai babban laifi tace “Hajiya wlh nasan namiki laifi nafi kowa sanin haka, na tafka shirme nayi kuskure banyi tunanin abinda ya chanchanta daniba, dan Allah Mamana kiyakuri ki yafemin wlh fushin ki na cimini zuciya sosai” tafashe da kuka sosai fa kaman ana dukanta, Hajiya shiru tayi tana kallon Ummi sosai kukanta ya tsuma zuciyanta bana wasaba, da ace wani zai shigo dakin nan zau dauka ita ta haifi Ummi sabida yanda yarinyar tabata girma tana kuka iya kuka agabanta, zamanin nan da wuya kasami suruka dazatazo tana kuka tasa guiwa akasa tana rokonka gafara kan laifin dabai taka kara ya karyaba, Alhamdulilah yau tana kara godewa Allah daya kawo Ummi rayuwan Nura, cus yarinya ce ta arziki, ga kunya ga ladabi ga biyayya, banda haka Ummi ta daraja ta tadauketa matsayin uwa, ahankali ya ijiye littafin hannunta tareda nunama Ummi gefenta tace “zoki zauna anan” kasa tashi Ummi tayi tana girgiza kai, kayattaccen murmushi Hajiya tayi tace “Ummi komi yawuce amman nan gaba kada ki kara abinda kikayi, shi aure hakuri ne Ummi, dole yau kaga daidai gobe kaga ba daidaiba, maza mazane! Abinda ya batamin shine ina gidan, ina garin baki tunanin ki jirani ba ki sanar dani kika kama hanya kikai tafiyan ki, Aisha ta sanar dani komi nace sam ban yarda ba, ke matar aure ce Ummi bai dace ta daukeki ta tsallakar dake gabaki daya daga Nigeria zuwa wata kasar batare da sanın mijinki ba ai Nura yasan abinda tayi bazai taba yafemata ba gwara koma menene kina gidana ni mahaifiyarsa” Hajiya tadanyi shiru tace “Nura bai kyautaba I support tafiyanki sabida inaso shi da kanshi ya gane amfaninki ya gane ko yana sonki koba yayi, Nura dana ne amman bazan yarda ya cuci kowace yarinya aduniyan nan ba, idan bai nemeki bazan taba cemai gakiba, amman kisani indai kinyi aure dole ki kulla dammaran zaman aure, aure ba abin wasa bane Ummi kina jina”? Gyadamata kai Ummi tayi, Hajiya tace “mujira gudun ruwanshi, gidanan nan naki ne kome kikeso kiyi, zan sakaki awani islamiyya na matan aure da akeyi karfe goma zuwa sha biyu kullum banda asabar da lahadi, asabar da lahadi akwai wani school haka danakeso ki shiga English school ne zaki shiga Meena ma tashiga dudda ta gama school, amman banda magana da maza ke matar wani ce kina jina” gyadamata kai Ummi tayi, Hajiya tace “idan Nuran yazo zanyi magana dashi idan zamanki kano shiyafi ma kiyi zamanki anan dudda ba lallai ya yarda ba dan shi mutum me da yanaso iyalinshi aduk inda yake amman zanyi idan ya yarda yanada gidanshi anan kiyi zaman ki, sannan kiyakuri da komi daya faru kinji” gyadamai Hajiya kai tayi sunyi magana sosai Hajiya sai bata shawarori take tana advising nata har wajen shabiyun dare sannan tasata taje ta kwanta.
    **

    After 1 nadare Nura yadawo gidan dakin Aman yawuce yayi kwanciyan shi, 4:30 yatashi as usual sai kawai yawuce dakin Ummi wanka yayi awajen yabude wardrobe yanada wasu kaya awajen ya shirya tsaf dan baiso yadawo gidan idan yafita asuba kawai yawuce yafita masallaci yaje 6 yadawo yashiga mota yabar gidan, office yatafi yazauna yayi shiruu zai iya cewa tunda yake aduniya baitabajin kalan kuncin nan da rashin farincikin nan dayakeji ba, lumshe idanu yayi yatashi daga kujeran sai kawai yazo tsakiyan office din yasami dogon kujera yazauna ahankali ya lumshe idanu kusan awa biyu yana ahaka kuma ba bacci yakeba, knocking akayi tareda bude kofanshi aka shigo Alhaji Musa ne yana sanye da manyan kaya hade fuska tamau Nura yayi ya yunkura yatashi da sauri ya dan dafe kanshi dayaji ya saramai da sauri Alhaji Musa yazo wajen yace “Nura lafiyan ka kalau bakada lafiya n……” hannu Nura yadaga mai yakalleshi da jajayen idanunshi yace “mekazo yi a office dina”? Bin Nuran yayi da kallo saikuma ya zauna kan center table yace “kai dalla chan maganan danayi ranan ne har yanzu azuciyanka I just did that danka gane kanason Ummi ne” kallonshi Nura yayi Alhaji Musa yace “wlh da gaske, listen abokina koda ace lokacin daka auri Ummi you were not sure kana sonta ko baka sonta believe me idan nagaya maka yanzu kanayi, kai kaga yanda ka chakumo ni ne Nura saida na firgice yanda kasan dan gidan dambe kaman wani wrestler, na shaku fa a hannunka wuyana har yau ciwo yake saida naje Likita ya dubani” dan murmushi kadan Nura yayi baice komiba, Alhaji Musa yace “Nura kaga you are too soft ne, kadena bari mata na chaza maka kai abanza awofi, kaifa namiji ne kaine me mulki, yau ko mata biyu kakeso ka karo atare zaka iya, da karfinka da kudinka ai wlh sai inda mai yakare so common chill, amman dai kaje ka dauko Ummi yaci ace by now ka kira Kakanta, kadaina nuna musu taurin kai hakan rainine Nura, am sure inda Hadiza ne da yanzu ka kira gida ko kamaje dan kaga Ummi ne is that why kake abinda kakeyi”? Girgizamai kai Nura yayi yace “Ummi hurt me deeply Musa, even Hadiza dake abun mahaukata bata tabamin abinda Ummi tayiba, ban taba having issue ta kama tabar gidana ba, Hadiza belive in fighting her battle da kanta bata gudu ba, she’s not a coward” Alhaji Musa yace “yo ai yarintar kenan, Hadiza ta girmi Ummi, banda haka Ummi batai karatun da Hadiza tayiba yarinyar is not expose, a kauye fa aka haifeta ta girma, the poor thing must’ve felt bata da kowa she’s alone, bakada time nata, baka dauki wayanta ba tazo kuma kamata koran kare without speaking to her ko kallonta, gaskiya Nura baka kyautaba yaushe zamuje mu daukota” dan ijiyan zuciya Nura yasauke yace “tunda gobe Alhamis mubari asabar” Alhaji Musa zaiyi magana akai knocking kofanshi Nura yace “come in” secretary Nura ne tashigo dawani sealed file haka a hannunta tace “sa yanzun nan wani yakawo maka wannan daga Attorney’s Chamber na Maitama” Alhaji Musa yace “Kanada wani court case ne, ina lawyer ka maiya hadaka da yan Attorney’s Chamber nan bayan kasan barayi ne” karban file din Nura yayi looking confuse yace “ni I don’t have any business awajen kodai mistake akayi”? Saikuma yaga sunanshi full name nashi agaban file din yace “ba mistake bane ga sunana” yakalli secretary yace “you can go” tawuce tafita Nura yashiga bude file din, yaciro takardun ciki yashiga karantawa kaman wanda akacema yayi freeze kawai yayi freezing dasauri Alhaji Musa yace “lafiya menene?” Dasauri ya karbi file din gabaki daya daga hannun Nura yana karantawa dasauri yakalli Nura yace “ana nemanka gobe by 10:AM nasafe a kotu, Hadiza tayi suing you for domestic abuse!!” Sosai Alhaji Musa ke kallon Nura dayayi mutuwan zaune ranshi abace yace “meya faru kuma I thought kacemin kun shirya kun maida komi past, why is she suing you for domestic violence? Kasan hakan zai iya sa kaje prison for good 3yrs kuwa? Is Hadiza trying to ruin you and your career or what, meka mata?” Sai alokacin yasaki dan murmushi da zai nuna maka how hurt he’s deeply yakalli Alhaji Musa yace “I slapped her jiya!” Cikin tsananin fushi Alhaji Musa yace “wlh there’s nothing you can tell me Nura mata yar boko batayi bane aduniya sam sam! Allah ya wadaran matan I know my right, I know my right, kai!” Musa yayi ihu ranshi yayi matukar baci danko ba’a gayamai ba yasan waye Nura ba mutum mai dukan mata bane koda ya mari Hadiza jiya shi yasan wlh ba karamin abu bane zaisa Nura yadaga hannu ya Mari Hadiza ba.

    Ganin yanda Nura yayi shiru yakasa motsin kirkima saiyaji yabashi tausayi, look at Hadizan daya wulakanta Ummi sabida ita thinking ta chanza yanzu zasu more rayuwa su dawo lovers din dasuke ada, dudda yaki admitting wulakanci yama Ummi but just look at abubuwan da Hadiza keyi, meke damun matan zamanin nan ne? Ta ina namiji da mace suka taba zama daya iyye? Wai what is wrong with matan yanzu ne haka iyayensu sukayi? Ba’a musu tarbiya bane agida? Iyayenmu mutane masu daraja mazajensu ne, kusan bauta musu ma suke, basu ganin yanda iyayen su ke rayuwa da mazajensu? ilimi haukane? What is keda mijinki dayane, ke kawai abarki kiyi komi yanda kikaga dama? Miji yace A, kice B har zuwa Z, ace kiyi kice bazakiyi ba, mesa wasu matan keda brain din fish??
    Zama yayi kısada Nura ahankali yace “idan kaje goben just buy lawyer nata kawai akashe case awajen kafin alkali yazo, da kudinka a aljihu karka wahala abanza” murmushi Nura kawai yayi ahankali yama kasa cewa komi sai chan yace “Musa bani labari dan Allah” Musa jiyayi idanunshi sun cicciko da hawaye Nura yabashi tausayi ana wani zamani da kullum mata ake tausayama cus mata are weak waye, waye, waye but wlh idan akai looking deep akwai wasu matan da kawai sunfi karfin mazajensu ne duk ta yanda zaka kalli abin, infact matan ke soyama mazansu aya a hannu not the other way round, Hadiza na yanda taga dama da Nura kodan taganshi mutum mai hakuri ga yafiya sannan yana sonta, Nura is this type of person that hates hurting mutum baida riko that is just Nura, jibi dai abinda yamai jiya na ya saki Ummi ya aura da wanine yau bazai kulashi ba but because Nura is just Nura magana daya biyu sun shirya kuma har abada ya manta da maganan kenan, that is just Nura is his personality his nature bazaka iya chanza wa ba, ai shi kanshi wani zubin yakanji haushin Nuran for yanda yake barin Hadiza na getting away da so many things, haka kawai Allah ya yo shi, Nura hates hurting mutum, Nura nada hakuri, Nura nada yafiya, sannan Nura ya tsani takurama mutum inhar u are happy da abu zai barki kiyi, da ace zai iya zuga Nura dudda ba’a shiga tsakanin miji da mata dan just imagine abinda yama Ummi balle ma shi Aboki daya zugashi ya hakura da auren Hadiza kawai gabaki daya, taje ta auri namiji da baida matsala da mata maiyin feminism shikenan.
    Amman banda jakanci da bahaggon tunani irin na Hadiza mutumin da yau shekara nawa kuna aure bai taba dukanki ba yau saiki makashi a kotu yana uban yaranki bazaku iya resolving issue din agidaba saikin tonamai asiri a duniya, and jahilcin da mata keyi is saisu dinga maka abi suga kaman kai sukema not knowing anything dazaiyi affecting Nura is affecting her as well koda ba directly ba, duk abinda yayi affecting Nura ayau will affect yaranta koda ace ma basa tare, if something affects yaranta ai yayi affecting nata as well so then menene riban tonama kanku asiri aduniya?? Sabida mijinki ya mareki sau daya in 10yrs kına tonama kanku da yaranku asiri wlh Hadiza is so shameless bamata da kunyan duniya.

    Dafa Nura yayi ganin baison maganan yace “kasan Maman Humaira tasoma sakan mini gurasa fa dana nunata ke kinga nabi Alhaji Nura kauye yakaro aure nima fa auren nan nakeso nayi shine ta natsu”
    Sosai Alhaji Musa yadinga ma Nura hira, office dinshi dabaije ba kenan har 1 nadare wlh suna tare just because baiso yanarshi shi kadai cikeda damuwa sannan suka koma gida.

    Yauma adakin Aman ya kwana 4:30AM yatashi yayi wanka yasa kaya yabar gidan zuwa masallaci around 6 yadawo gidan zai bude mota ya shiga aka bude kofan falo Hadiza ne tafito tana sanye da bubu yana kokarin shiga mota tace “wato kaga sammaci bazama kazo ka rokeni, be on your feet and genuinely bag sabida nai withdraw the case ba” kallonta Nura yake daga head zuwa toe sai kawai ya shiga mota bai cemata uppan ba, abin ya masifar kular da Hadiza kaman ta kurma ihu wato ita zai maida mahaukaciya dasauri tazo wajen yana kokarin tada motan ta tsaya wajen kofan tabude cikeda rashin kunya dan yanda kasan zata makeshi tace “ohhh ni kakema girman kai imagine level na ignorance naka, don’t worry zakayi ladabi a prison yau stupid wicked man kawai mayaudari kawai” hannunshi yasa yakalleta yace “saki”ihu tamai da saida gateman yafito da gudu tace “bazan saki ba Nura!” Kallonta Nura yake idanunshi har sun kada sunyi ja, Hadiza tace “zanyi maganinka Nura, wlh zanyi maganinka dan kai karamin da duniya ne, muhadu by 10” tawani bugamai kofan motan Allah yasa hannunshi baya wajen da wlh saiyay sustaining injury jan motan Nura yayi batare yabar gidan, Hadiza jitayi ranta na baci har kasan zuciyanta bata wani so suje court dinba taso yazo ya lallasheta kawai ta kira ta janye case din saisama ganin bai biyota ba ita tazo nan tunda ta tashi take gadinshi yadawo daga mosque a window ta falo, tana ganin yadawo tafito with hope zaiyi sulhu da ita, koyadan mata magana mai kyau amman jibi yanda yamata banza ya mai data mahaukaciya sai taji gwarama data makashi kotun, juyawa tayi takoma ciki.

    Karfe goma daidai motan Nura yayi parking gaban kotu inda Alhaji Musa ke tuki already Lawyer Nura na kotun, fitowa sukayi jiki asanyaye suka wuce ciki gaban court room din yaga lawyer shi tsaye yana ganinsu yace “yauwa muje ciki yanzu Alkali zai shigo”.

     

    Ance a woman can make or break a man kun yarda???

    Hadiza made this statement kana ganin karo aure shine zai baka peace din dakake nema to bazaka taba samun peace din nan ba, from abinda muke gani Nura ko yakasa samin peace din dayake craving right???

    What action kuje ganin yakamata Nura yadauka akan Hadiza??
    Yakokarin ya gyarata ta baki taki, yayi ta love taki, yayi ta family taki, Mezaima Hadiza ta gyaru????

    But then again NURA yabani tausayi is not easy wacce ka keso tai hurting naka😭
    Hadiza fans I have just one question danake so namuku, inhar Love bai chanza Hadiza ba, me kuke ganin zai iya cire wannan feminism din daga jininta???💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

    ✍🏻M SHAKUR

     

    EPISODE 2️⃣6️⃣
    https://chat.whatsapp.com/KO6bdcXjxmh2l6pM6T0meI

    In mutum yanason yayi register Kuma yayi siyayyar 🌟3 free registration ne
    Kuma Ina adashen products din GHT in mutum beda halin Siya Nan take

    08066136431

    Note: Ni ba lawyer bace! Though I consulted some lawyers irin su Majal and co😍 Incase kunga mistakes no mind me, I be health personnel ejor❤️

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 22

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 22

    22
    Hadiza na zaune kan gado wajejen 8 tana kallo a MacBook dinta da aka kawo mata su Rabi Hafsat da Mama suka shigo dakin suna shigowa wani tsalle sukayi suka rungume Hajiya Hafsat tace “barka Ya Hadiza congratulations” dasauri Hadiza da duk jikinta ke ciwo ta turesu tace “zaku karyani me kuke murna haka” cikeda jin dadi Rabi tabama Hadiza labarin komi dasauri Hadiza takalli Anty Jams tace “wai haka? Shine kikazo jiyan nan kikai shiru”? Dasauri ta kallo Mama tace “Mama da gaske wai yar aikin nan ta gudu Hajiya kuma ta tafi” hade giran sama da kasa Mama tayi tace “nidai tunda kin sami lafiya nima gaskiya tafiya zanyi yau” Rabi tace “Wlh Ya Hadiza da gaske barsu Mama da Anty Jams yan Qalallahu wa Qala Rasulu ne su, but Ummi dai tagudu kuma mijinki ne yamata wulakanci jiya yagayama mamanshi ido da ido bazaije nemanta ba ko bikinto shine Hajiya tai zuciya ya tafi yau” wani ihu Hadiza tayi ta dirko ta rungume su Rabi saita fara rawa da waka. “Jarusalema ikayalami eeeee lonolonse…….” Yanda su uku ke rawan daga Mama har Anty Jams tsayawa sukayi suna kallon yan iskan yaran baki abude, Mama tace “stop celebrating other’s downfall duniya juyi juyi ce yau turn dinka gobe nawani, life is like a roller coaster Hadiza, Rabi’a da Hafsatu” Hadiza tace “Mama Allah ne ke sakamin wlh ba maganan roller coaster anan karma yakama yarinyar nan cus taci amanata gashinan da kanta da dauki kafanta ta tafi, the God am serving can never shame me, ni wlh namaji na warke tas tas, tas, azo asallameni wayyyooo dadi Nuri na is all mine again, Nuri kabiyani” ta kankame Rabi cike da jin dadi Anty Jams ta tabe baki.
    Wajajen 10 Nura ya shigo asibitin da sallama yashiga dakin Hadiza na kwance tana kallonshi tana murmushi cikeda so, dab da gadon yaje yasa hannu yaja hancinta yace “wannan kallon fa” murmushi tayi sosai tace “Mijina yayi kyau ne naga, ina kwana” murmushi yamata yace “close your eyes” dan zaro idanu tayi tace “menene”? Daure fuska yayi hakan yasa tarufe da sauri suma su Rabi duk kallon Nuran suke dumbfounded kofa yakalla yace “come in” Drs da Nurses na asibitin ne suka shigo da katon cake da ballons dayawa a hannunsu an rubuta Happy Birthday Didi akan cake din su Mama da Anty Jams duk murmushi sukayi gabaki daya kowa ya manta yau birthday nata har ita kanta ta manta, yakalli Hadizan yace “open your eyes now” ahankali tabude kawai aka fara waka.
    “Happy birthday to you, Happy birthday to you, Happy birthday to Hadiza Happy birthday to you…..” fashewa da kuka sosai Hadiza tayi tana kallon Nura kaman ta tsaga jikinshi tashige takeji karban cake din yayi yadaura akan cinyanta yana mata wani kallon soyayya yace “happy birthday Didi, oya blow you candle” blowing candle tayi akahau ihu ana tafi ta yanka cake din red valvet tace “wowww my favorite Thank you Nuri, I love you, thank you all” takalli sauran Drs da Nurses din tamusu godiya duk akacici cake din adakin aka watse Hadiza sai kallon Nura take she can’t believe Allah yabata miji dake sonta haka yake kuma son yaransu juyowa yayi suka hada Ido ya harareta yace “you are 33yrs yanzu, no more tsiwa da rashin ji da stubbornness” pledging tayi tace “nadaina I promise” Mama ta tabe baki tace “Allah sa” fuskanta ya shafa yace “bari nadan leka office kinason wani abu” girgixamai kai tayi tace “saika dawo Allah tsaremin kai” lumshe mata ido yayi yace “Ameen”yafice.
    Mama tace “kinyi sa’an miji Hadiza saidai kice Alhamdulillah I hope you will change for good wlh kika rasa Nura kin rasa miji har abada” Anty Jams tace “nama Majal magana nabiya kudi nama tura mata number ki zata saki group dinta na matan aure mai suna Somach dan ubanki saura kada ki natsu ki koyi abubuwa you are 33 yanzu Allah ya chanza ki, namiki order wasu kayan mata from MAMMI HAJIA, shedanun cikin magungunan ta namiki order da HQ ADDICTION, RUWAN BAGAJA da OGA MUST SALUT, gobe tace zatamin delivery tun anan asibiti zaki farasha sabida yabi jikinki” murmushi Hadiza tayi tace “thank you Anty Jams dina don’t worry this time I will make you all proud of me, dagajin sunayen magungunan nan zasu tsula tsiya” Anty Jams tace “dole Nura yaga chanji wlh”

    ****
    Yau Hadiza ta cika one week a asibiti yau aka sallamota suka dawo gida yaranta sai murna suke gobe da sassafe yan uwanta zasu koma kano girke girke suka mata daban daban aka lollada a freezer da uban stew kusan cikin roban fenti duk wani aiki dake gidan sun mata dudda babu wani abinda ke damunta ta warke tass though tanata appointed da psychologist daya ga wata mai zuwa but she’s fine sai uban kayan mata MAMMI HAJIA take sha.
    After Magrib yashigo gidan duka akaci abinci tare yakara yin sallama da yan uwanta yawuce masalları sallan isha’i shida Aman.

    Wajajen 9 suka shigo gidan yana rikeda Aman dayayi bacci, bakowa a falon sama yawuce yaje dakin Aman din ya kwantar dashi sannan yawuce dakin Hadiza batare daya kalli dakin Ummi ba Hadiza na kwance kan gado tasaka wani arnen rigan bacci pink shara shara, wani kalan kallo Nura yamata yana maida kofan yana rufewa murmushi tamai tace “nayi kyau”? Tai wani juyi agabanshi yace “kin tashi kaina Didi” wucewa yayi yarage kaya tabishi da kallo kaman zata hadiyeshi sannan yabude bayi yashiga dan ya watsa ruwa shiru tayi tana tuna karatın da Majal tamusu kan wanka tareda miji na kara love, kayan jikinta tashiga cirewa ahankali tawuce bayın tabude ahankali Nura na kasan shower kaman daga sama yaji an rungumeshi tsantsan ijiyan zuciya yasauke murya Chan kasa yace “Didi” murmushi tayi cikin yar karaman murya yace “I didn’t get the chance to thank you properly kayi dawainiya dani sosai this past few days not to even talk of kudaden daka kashe for my cardio test da tp to and fro na yan uwana suzo, the suprise birthday and everything, u are indeed my soulmate, Nuri I love you over” wani kalan juyo da ita yayi gabanshi yabi jikinta da kallo ahankali yace “kome namiki kaina namawa Didi me and you are one!” Zata sake magana yawani fizgota jikinshi yana mannata bango manna mata kiss yayi a forehead ya manna mata a hanci kafin ahankali yasauke bakinshi kan nata yafara kissing nata tana maidamai da martani, Ummi ne tafado mai rai he just remembered how she loves kissing him is like whenever it comes to kissing she do most of the work kaman zata cinyemai baki. “Nuri!” Hadiza takirashi bakinta cikin nashi ganin ya tsaya and he’s lost in thought, dasauri ya kalleta yacigaba da kissing nata yana budemata kafa he knacked Hadiza well cikin bayin nan to his biggest suprise batai complaining yajuyata nan ko chan ba full cooperation tanashi, he can’t lie he enjoyed it takara dadi sama da yanda yake jikinta and she’s so tight sosai yau and so warm maganin Hajja mammi yayi aiki, itama Hadiza unlike her the sex yamata dadi bata taba sanin Nura at clocking 50 will this good ba, what a rude f*cker, wanka sukayi suka fito suka hau gado kashe wuta sukayi ta rungumeshi da sauri tareda kai bakinta saitin nashi tace “I love you Nuri” ahankali yace “I love you too Didi” daura kanta tayi kan kirjinshi yana rubbing bayanta ahaka bacci yayi awon gaba dasu.
    Washe gari by 8 suka wuce yara dama tun safe suka tafi school Hadiza takalli Nura daya wuce sama tace “bazakaje aiki ba yau” yana murmushi yace “sameni asama today is all yours ba inda zani” murmushi tayi sosai tabiyoshi sama harya kwanta kan gadonta da gudu taje tahau kanshi yace “shikenan zata karyani ke bakisan na soma tsufa ba”? Tana turo baki tace “kai Nuri shairi har wani kiba gareni kuma ni banga tsufan dakake fadiba kamafi wasu samarin iya cin mace” dan kanne mata ido yayi yace “wlh shinakeso ma yanzu kinyi dadi sosai jiya, ride me Didi dagani sai ke gidan” ba musu kaya sukahau ciccirewa juna Hadiza tahau riding nashi dan yanzu bata gardama one two three tagaji sai kawai Ummi takara fadomai arai dasauri yakauda tunaninta ya kwantar da ita yahuayi, ranan wuni sukayi suna more rayuwansu yanda kasan sababbin Amarya da ango.

    Washegari
    Yau dukansu zasu aiki Nura shiya shirya yaran da kanshi, Hadiza ta sauka kasa hada musu breakfast.
    Nura na sama Aman takalmin makaranta yace “Dady har yanzu Anty Ummi bata dawo ba”? Kallon Aman Nura yayi dasauri, Amal tace “Dady I miss Anty Ummi so much” sai kawai yaran duk sukai kaman zasuyi kuka dasauri Nura yace “don’t worry kwanan nan zata dawo okay, muje yanzu Momy ta gama breakfast muci okay” wucewa kasa sukayi atare duk sukai breakfast din mota yazo Nura yafita yakaisu Hadiza ta tashi yace “lemme shower Nuri natafi” dasauri yakalli dinning da kitchen din daya hangi wanke wanke dayawa a sink yace “what about the plates din baki wanke ba the kitchen is looking dirty Didi” Dan tsayawa tayi tareda yatsine fuska tace “bazan wani dadeba zan dawo kasan online sales din dazanyi has been on hold sabida rashin lafiya na, yau kawai zanje ne muyi sorting out everything new kayan danai order zasu iso next week” ahankali yace “okay nine wuce” daga sama tace “adawo lpy” tashi yayi yafice zuwa office Musa ya tarar a office dinshi yace “waikai tunda kayi Amarya ka zunda mu” dan tsaki Nura yayi yasami waje ya zauna saikuma yayi shiru tareda daura hannunshi saman kanshi dasauri Musa yace “lafiya”? Kaman Nura bazaiyi magana ba yace “Ummi tayi zuciya tabar gıdana ta tafi garinsu” cikeda mamaki Musa yace “mene? Kai dalla banson this expensive joke, yaushe kukai auren dahar zatai yaji meya faru”? Gayamai komi Nura yayi Musa yace “haaabaaa Nura, haba kaikuwa dudda ina namiji koni banji dadi ba, Allah sarki Ummi the poor thing must’ve felt all alone wlh dole ta tafi yanzu dai yaushe zaka je daukota dan is obvious kayi kewanta” tabe baki yayi yace “ni kewanta da danedai zan gayamaka eh, yanzu ko tayi shekara ma karta dawo, gida biyu maganin gobara, ni zatama zuciya, haba yau idan inaso zan iya auro mata uku akanme zatace zatamin zuciya babu wani dalili mai kyau, kai kasanni bana batawa mutum rai hakanan maisa bazata min uzuri ba, takari zamanta baxaniba” sosai Musa ke kallonshi kai tsaye danshi yafi Nura iya duniyanci yace “saketa in aura Nura dan Allah!”.

    Da sauri Nura yakalli Musa gabanshi yawani fadi danjin maganan yayi kaman saukan aradu sai kawai lips nashi yahau rawa yama kasa magana sai kallon Alhaji Musa yake dake kallonshi kyur ba kunya ba tsoron Allah, cikeda kara gasgatama Nura yace “wlh Nura da gaske nake yoo idan naboye maka zan boye ma Allah ne damukaje bikinka kasan yanda naketa nanatawa azuciyana inama nine kai, inama nataba zuwa gidanka naga Ummi, from the way you are talking Nura bakason yarinyar nan Hadiza itace matarka da Allah yabaka, ku biyun kun dace da juna, yarinyar nan Ummi ka aureta ne kawai to pepper Hadiza kadawo da ita hayyacinta, tunda bukatanka yabiya Hadiza tadawo daidai tadaina gasaka ni ka taimakamin kasaketa na aura wlh wlh ina bala’in son Ummi Nur……” “get out!” Nura yadakama Alhaji Musa tsawa dayasa Musa yace “waikai lafiya komi ke baka haushi kwanan nan, naji zan fita amman dan Allah bani number ta, ban number Ummi” yamikama nura wayanshi wani kalan zabura Nura yayi yatashi kaman zaki idanunshi sunyi jazur yawani kama gaban babban rigan Alhaji Musa cikin tsananin bacin rai kaman zaiyi dambe da Musa yace “matar tawa kake cemin nasaka kana sonta zaka aura” bawai yaji haushi abinda Nura yayi bane amman yasa hannunshi tacire hannun Nura daga gaban babban riganshi yace “Nura bari kaji ni bazan rabaka da matarka ba kuma bazan taba neman matan aure ba kai kasan wayeni bana irin harkan nan, I’m simplying telling you tunda tagama amfanin dazata maka baka sonta yanzu, kasaketa ni zan aureta dan wlh Ummi tamin right from day one dana ganta, kuma ni auren so da kauna zan mata nabata gata da komi ba irin selfish auren dakayi da itaba” “to baza’a saketa ba!” Nura yayi maganan yana tura Musa, Alhaji Musa yace “kana saki kaman na aure yasin nidai tunda yanzu baka tunani da kyau kaga tafiyata zan kiraka kahuce karka manta dan Allah kasaka na aura! And try send me her number!” Bugo kofa Nura yayi azafafe.💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

    ✍🏻M SHAKUR

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 15

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 15

    EPISODE 1️⃣5️⃣

     

    Kun tuna albishir din danace zan muku yau???🥰
    Here we go, MATAN KO MAZAN chapter 1 is coming to an end just few more episodes to go which nakega zan gama mukushi within this week now here comes the EXOTIC NEWS konace the most EXCITING PART of the news shine Chapter II namu wanda is about CHEATING!!!!

    Did you know acikin kaso dari na ma’aurata 90% na cheating?? Ko kiga mijin yanada babes awaje ko kiga matan nada samari awaje, Ex dina, class mate dina, Classrep dinmu, ko dan office dinta. Cheating a aure yanzu ba yaro ba babba, da sababbin auren da tsofaffin all both mata da mazan nayi.

    Some mata nada samari awaje while some matan kuma yammata garesu, kunsan mata da yawa na gida are into lesbianism kuwa???
    And our Men kusan some of them bada mata suke cheating ba da yan uwansu maza sukeyi???

    Like I said, dana tashi yin book dinnan MATAN KO MAZAN I interview ma’aurata da dama, divorcee da Momies wayanda sun haifi kamata, da Aunties, so I decided to pick on the big, big major matsaloli dake kashe aure ayau to write about them in other to Educate yan uwana mata da maza, to show you how to fight that battle and to let you know every problem nada solution, so idan kin dade ko ka dade kana cheating on your partner thinking bazaka iya dainawa ba this book is here to help you overcome this addiction na cheating, I will pieces this Cheating of a thing, the stages and yanda ake dainawa, abinda mutane dayawa basu saniba shine Ma’aurata na cheating ne sabida dalilai da bazasu wuce 1 zuwa uku ba;
    1- For revenge, wata feels tunda Mijina is cheating on me I will cheat on him back.

    2- Rashin gamsuwa, dayawa maza
    Dayawan maza cheats because they feel matansu are lacking in a thing or something in za other room, same with mata maybe baya gamsar da ita or he’s too tiny.

    3- Addiction, addiction ina nufin wayanda suka saba sleeping around tun kafin suyi aure, so bayan auren bawai suna cheating sabida partner dinsu yarasa wani abu bane ko basa gamsuwa sunayine sabida sun riga sun saba bazasu iya rayuwa da one sexual partner ba, kun gane….

    SAIDAI!!!
    Is not going to be FREE this chapter and I employ each and every one of you to support me, this Chapter two is about to BLOW YOUR MIND💃

    Payment is just 1k, pay into 6353995766 M Shakur world Moniepoint saiki turomin evidence of payment ta whatsapp wa.me/+2347012181461 sainai adding naki a PAID GROUP DIN.

    If you wanna speak to me akan wani abu chat me up a whatsapp 07012181461, ko send a message ta IG @mshakur_world ko tiktok @mshakurr

    Thank you and I love you remember CHANGE IS NOT EASY just like yanda Hadiza is struggling yanzu ta chanza, baka tashi rana daya ka chanza is process the most important a process din is determination wato JAJIRCEWA!!!

    15
    Wuraren 2:30 Hadiza tai parking motanta gaban school na su Aman sai kallon gate na school din take she can’t even remember the last time tazo school nan kowani function sukeyi da ake bukatan iyaye saidai Nura yaje ita bata zuwa, Anty Jams dake kallonta tace “sauka kije ciki ki daukosu” ijiyan zuciya tasauke feeling wani iri for the first time all this while taji yes da gaske ne tayi neglecting yaranta sosai, cultural day, parent forum, end of the session party duk wani abu na school dinsu Nura ke zuwa, koda Aman yayi graduation na gama prep Nura yaje hoton Aman yana saniye da graduation gown da babban shi ne kawai a hoton, shiga cikin school din tayi daidai lokacin teachers sun fito da yaran za’a sakasu a school bus bamasu lurada itaba hannunta Hadiza tadaga tana kakalo murmushi tai waving nasu tace “Amali, Aman” dasauri duka yaran suka juyo tareda teacher su dabata lurada Hadiza ba ta taho wajen da sauri tace “ohh sorry Madam ban ganki ba good afternoon Ma” Gyadamata kai Hadiza tayi tana kallon yaranta daketa kallonta da mamaki, Hadiza tamika hannu zata kama Aman yadauke hannunshi da sauri yana turomata baki yana hararanta sai kawai jikin Hadiza yayi sanyi tasa hannu tadauki Amal ajikinta cikeda wayancewa tace “princess İdanun Mommy naciwo saisa sukai ja kinata kallona” teacher tace “no wonder nima I wanted to ask” takalli Aman tace “follow your Momy Aman” cikin dan yake Hadiza na kallon Aman daya dauke kai tace “don’t mind him I don’t know why he’s angry let’s go Aman” tasake miko hannunta wannan karan buge hannun Hadiza Aman yayi saitaji hawaye zai zubomata dasauri cikeda kunya tayi gaba da Amal tace “okay then come on your own tunda bakaso nakamaka” tayi gaba da Amal, ihuu Amal ta kwala tana fizge kanta daga Hadiza tace “leave me I want to go to my brother, Anty Ummi said I should never leave my brother alone koda yaushe muna tare, he’s my best friend leave me Momy” Amal ta tsandala ihu dayasa Hadiza tasaketa da gudu aiko Amal ta fanfalo zuwa wajen Aman dake tsaye akumbure teacher na lallabashi yabi mamanshi, Amal na zuwa ta rungume Aman cikeda yarinta tace “Ya Aman don’t be angry, let’s go, come” Aman dayaki tafiya Amal ta kalla, fashewa yayi da kuka yace “I don’t like her, I don’t want to go with her Princess, she will start shouting very soon” ganin yayanta na kuka sai itama Amal tahau kuka sai abin yafara jawo attention na mutane da sauri gudu gudu Hadiza tajuya tabude mota tashiga takifa kanta kan matukin mota tace “I can’t do this Anty Jams, I can’t, yarinyar nan tariga tayi brainwashing yarana Aman hates me sooo much” dan ijiyan zuciya Anty Jams tasauke batare datace ma Hadiza komiba tabude motan tasauka ta tafi wajen yaran bata wani sha wahalan shawo kansu ba sun santa sosai suna sonta Aman yace “where is Batool?” Murmushi tayi takama hannunshi tace “tana kano, muje gida kunji” binta sukayi bayan tasasu tarife takoma gaba Hadiza tatada motan taja bini bini tana kallon yaran dake wasa abunsu su biyu abaya, gashi kansu ahade they’ve learn to love each other and support each other so well kuma is all thanks to Ummi, parking tayi agaban Burger King tajuyo takallisu cikin kakalo murmushi tace “Amanu zakaci burger and fries muje na siyamaka anan burger king?” Batare daya kalleta ba yace “I hate burger” dasauri Amal cikin zakin murya tace “yes Mommy Ya Amanu doesn’t like burger, Ya Aman likes pizza, chicken pie and hotdogs, nikuma I love shawarma mai 2big sausage irin wanda Anty Ummi kemana ko Ya Aman”? Gyadamata kai yayi yana murmushi yace “muje gida and tell Anty Ummi tamana ko”? Dasauri Amal tace “yesssss Anty Ummi is the bestttttt cook, teacher said if a person can cook is called Chef” atare yaran sukace “Anty Ummi is the best chef” yanda Anty Jams ke kallon yaran haka Hadiza ke kallonsu ganin bazata iya magana ba yasa Anty Jams tace “kaga Amanu Mommy ku zata siyamuku duka favorite dinku tunda pizza kakeso bari aje debonaires ko dodo pizza ko” yana kallon Anty Jams yace “Momy is busy she never take us anywhere” buga Hadiza Anyy Jams tayi aboye hakan yasa Hadiza tanuna kanta tace “Aman I will never be busy for my sweet boy again kome kakeso zan saya maka kaji, pizza da mene da mene kakeso”?Sosai Aman yake kallon Mamanshi kaman yanaso yagane wani abu still dai cikeda rashin sakewa da ita dakuma haushinta yace “pizza and bubble tea na Nutella irin wanda Daddy ke sayomana” gyadamai kai Hadiza tayi feeling a bit better ganin yamata magana yanzu takalli Amal tace “princess ke me kikeso” Shiru Amal tayi tana juya idanu looking super adorable tace “mommy I want a biggggg giant shawarma with ice cream mai cone ba cup ba” murmushi Hadiza tayi feeling kaman ta fashe da kuka tace “okay Baby na Mommy will buy everything dakukeso ko, juyawa tayi dasauri ta tada motan cold stone sukaje dake hade da Dominos pizza nan suka bada order komi suka zauna ana kawo kwalin pizza Hadiza ta karba tana murmushi tajuyo tabama Aman karba yayi yana kallon Hannunta yace “ina na Anty Ummi? Daddy always buy mine and na Anty Ummi” Amal tace “yes me too one ice cream for me one for Anty Ummi, one shawarma for me one for Anty Ummi” duk yanda Hadiza ta daure saiga hawaye dasauri ta share zatai musu magana Anty jams ta girgiza mata kai alamun asayo na Ummi inhar tanason tayi winning yaranta, ahankali tace “Tom bari asayo nata” bada order na Ummi sukayi suka kara jira nan aka gama komi Amal ta karbi na Ummi nan da nan yasaki yana murna itama haka Amal dukansu kowa yadauki nashi da na Anty Ummi suka koma mota Hadiza tashiga motan bayan tasasu abaya sai gida suna kaiwa gida wlh kafin tagama parking da kyau Aman yafice da komi yana shouting sunan Anty Ummi tundaga nan waje Amal biyeda shi.

    Ummi na zaune adakinta taji yaran na kwalamata kira dasauri ta tashi tafito ko kadan batasan suna tareda Hadiza ba danta dauka Hadiza na wajen aiki bene tayi ta na sauka tana kaiwa last staircase yaran na zuwa wajen da abubuwa a hannunsu cikeda murna suka wani rungumeta. “Oyoyooo Anty Ummi” daidai Hadiza na bude kofan falon tana shigowa suka hada ido da Ummi, faduwa gaban Ummi tayi ahankali tashira cire yaran daga jikinta tace “Aman oya to kuje kucire uniform” daidai lokacin Anty Jams na shigowa Aman da Amal suka bata abubuwan hannunsu “Anty Ummi take ur own pizza” Amali tace “Anty Ummi ni ice cream da shawarma nakawo miki take” daga Hadiza har Anty Jams tsayawa sukayi suna kallonsu cikeda rashin sakewa Ummi ta kakalo murmushi batare data karbaba tace “to kuje ku ijiye a dinning sai aje acire uniform, awanke hannu saikuzo muci tare” Dasauri suka tafi dinning suka ijiye sannan sukazo sukabi gefenta sukai sama da gudu mikewa tsaye Ummi tayi ahankali takalli Anty Jams danta santa ahankali tace “sannu da zuwa Anty, ya hanya yakuma su Batool” danne komi Anty Jams tayi tace “suna nan lpy Ummi” ahankali Ummi tajuya harta fara hawa stairs Hadiza tace “namiki iyaka da yarana baki jiba, kome namiki ke kikaja, kifita daga harkan yarana baki basu” wucewa Ummi tayi sama batare datace komiba Anty Jams ta harari Hadiza tace “ai saiki wuce sama kije ki tayasu chanza kaya, kiyi salla sannan ki sauko ki daura abincin dare tunda girkin ki ne, wuce muje nima bari naje nai salla” duk suka wuce sama.

    Ummi tanajin yaran na kiranta nabuga kofan dakinta amman takasa amsasu ko fita duksai taji batajin dadin komi dan wlh tanason su Amal bawai pretending ba yaran akwai shiga rai gasu kyawawa sosai.

    Da taimakon Anty Jams tana kara nunnunama Hadiza wasu abubuwan dan bawai bata iya girki bane tsabagen rashin yi ne yasa ta manta suka dafa lafiyayyen fried rice da peppered chicken suka hada juice yaran sukaci pizza su suna ijiye na Ummi Anty Jams ta tayasu yin homework sai tambayan Ummi suke.

    Bayan magrib Nura yashigo gidan da sallama dasauri yaran dake tareda Anty Jams suna homework suka taho wajenshi da gudu suka rungumeshi daukansu duka yayi yace “Aman ka kara nauyi wai zaka karya Dady” dariya Aman yayi sosai cikeda son Babanshi yace “Dady ni ban kara nauyiba, Dady where’s Anty Ummi bamu ganta ba” Amal tace “Dady Momy takaimu mun sayi ice cream shawarma and pizza mun sayo mata tace muje mu chanza uniform saimu fito muci tare but munata nemanta we can’t find her” yana kallon yaran nashi with love yace “zan nemota” ihu yaran sukayi suna kara rungume shi yashigo cikin falon cikeda girmamawa ya gaida Anty Jams ta amsa tana murmushi tace “barka da dawowa Nura ya aiki” anatse yace “Alhamdulillah sannu da zuwa, bari naje sama nadan watsa ruwa” tace “to Nura” wucewa yayi sama da yaran manne dashi suna bashi labarin komi daya faru yau, dakin Hadiza yafara bude kofa yashiga tana zaune gaban madubi tana kokarin saka earring tana sanye dawani blue jean da shirt nude mai shegen kyau tayi lafiyayen makes up a fuskanta tana kallonshi ta madubi, yana rikeda yaran yakaraso inda take yana kallonta yace “zaki fitane”?Girgizamai kai tayi tareda juyowa takalleshi asanyaye ahankali kaman ba itaba tace “sannu da zuwa Nuri na” duk yanda Nura yaso boye mamakinshi kasawa yayi yau shine Hadiza ke cema sannu da zuwa sai kawai yasa hannunshi daya yajawota tareda bata side hug yace “kinyi kyau sosai right kids?” Dasauri Amal dake jikinshi tace “right Dady Momy tayi kyau” Aman yaki magana sai kawai Hadiza ta tsugunna gaban Aman tareda shafa kuncinshi tace “bazaka ce Momyn ka tayi kyau ba?” Turo baki Aman yayi yace “kinyi kyau” murmushi sosai Hadiza tayi tace “thank you my first born” kasa boye mamakinshi Nura yayi sai kawai ya ijiye Amal kan gado yace “ku zauna da Mommy ku bari naje nayi wanka nazo” wucewa bayın Hadiza yayi tabishi da kallo cikeda so tana wani kalan jin dadi yanda bai nemi Ummi ba har yanzu Aman wucewa yayi yabar dakin itakuma Amal tacigaba da wasanta ita kadai akan gado wanka Nura yayi yafito ya shirya tsaf cikin jallabiya yanayı yana satan kallon Hadiza dayaga tanama Amal wasa akan gado cikeda mamaki ya feffesa turare sannan yawuce wajen kofa dadan sauri daidai yasa hannu Hadiza tajuyo tace “ina zaka? Abinci is getting cold kai muke jira fa babu wanda yayi dinner” juyowa yayi yasake kallon Hadiza kafin ahankali yace “keda Amal kuje lemme call Ummi sai duk muyi dinner tare” harya bude kofa cikin zafin murya Hadiza tace “Nuri!” Juyowa yayi ya kalleta suka hada ido strictly Hadiza tace “I cooked for you not for her” anatse Nura yace “yau girkin kine Hadiza you cook for the entire house not only me, kuje kasa ganinan” yana maganan bai kara jiran wani magana nataba yawuce Hadiza jitayi kaman ta kama da wuta hannunta da jikinta sun fara rawa na bacin rai knocking Nura yayi gaban kofan Ummi yace “bude kofa Ummi” tashi Ummi tayi ahankali tabude kofa suka hada ido da Nura tayi wanka tasaka wani jan material da aka mata fitted doguwan Riga mai kyau ta daura dan kwalin dan komawa baya tayi yashigo dakin tareda maida kofan yarufe ahankali Ummi tace “barka da dawowa Yallabai, ya yininka ya kasance yau? Dafatan komi yatafi lafiya, ya Hajiya kuma” batare daya bata amsaba yajawota jikinshi warm hug yabata tareda lumshe idanu ahankali yace “komi lafiya lau Babyna, nasan bakiyi dinner ba let’s go” adan tsorace Ummi ta girgizamai kai tace “kaje kuyi idan kun gama zan sauko nayi ni” hade giran sama data kasa Nura yayi yace “kinason nayi fushi dake?” Dasauri ta girgizamai kai anatse yace “da iyalina zan dingacin abinci so wuce mutafi” yayi maganan yana kama hannunta suka fito zare hannunta tayi dasauri daga cikin nashi suka cigaba da tafiya har kasa Hadiza na zaune a dinning hakama Anty Jams da yaran suna ganin Ummi sukai ihuuu suka taso da gudu zuwa wajenta. “Dady a ina kaga Anty Ummi, ina kikaje Anty Ummi” murmushi tamusu tace “muje muci abinci zan fada muku” duk rirrike mata hannu sukayi suka tafi dinning zama Nura yayi Ummi ta zauna kan kujeran dake kusadana Amal Hadiza kaman kartai serving abincin but bataso tabatama Anty Jams rai hakan yasa tashiga zuxzuba abincin, Nura tafara zubamawa tazubama Anty Jams ta zubama Aman da Amal sannan tazubama kanta ta maida kulan tarufe Anty Jams tama Hadiza wani kallo da idanu ta dauke kai kaman bata ganta ba nura baice mata komiba daga plate nashi yayi yamikama Ummi yace “ci abinci” saishi yatashi yadauki plate yashiga zuba wani Hadiza namai wani kallo zuciyanta na tafarfasa tass Nura yagama diban iya abincin da zaici ya zauna saikuma yakalli Ummi dayaga takasa taba abincin babu wasa kan fuskanshi yace “nace kici” gyadamai kai tayi ahankali tadauki spoon ahankali Aman yace “Anty Ummi eat dady food have plenty chicken” debo abincin Ummi tayi ahankali zatakai baki Hadiza ta mike batai wata wata ba ta kabar da spoon din cikin tafarfasan zuciya tana huci tace “ke har kin isa sabida you are shameless nama mijina girki kice zakici wulakantacciyan yar aiki irinki eh, nazauna akan dinning da ni da family dina kema kizo ki zauna zakici abinci tareda mu bar wajen nan!” Hadiza tai ihu dayasa Ummi ta yunkura zata tashi chak Nura yakama hannunta yace “sit down and eat nace” yasake daukan spoon nashi yasa a abincin yace “zauna” zama Ummi tayi ahankali, azuciye wannan karan Hadiza tasa hannunta tadaga plate na abincin Ummi ta kabar akasa tace “dakici abincin nan Ummi gwara yayi asara” cikin fushi Nura yace “Hadiza!” Itama cikin fushi Hadiza takama waist dinta tace “Nura! Miye?! Wat!” Cikin tsananin fushi yace “this is the second time kike wulakanta abinci agidan nan kinsan mutane dubu nawa ne yanzu aduniyan nan da basu sami kalan abincin nan sunci ba? Kinsan hukuncin maiyin annubazaranci da abinci kuwa?” Cikin tsantsan tsananin fushi tace “I don’t care Nura all I know is yarinyar nan bazataci abincin dana tashi nashiga kitchen na dafawa mijina ba wlh” ahankali Nura yace “okay ni kika dafamawa ko nima bazanci ba ki tattara komi kici” yayi maganan yanajan hannun Ummi zai wuce Hadiza tasha gabanshi tace “Nura for how long ban maka girki ba? Kullum korafinka is ban maka girki ba, yau nashiga kitchen dakaina na ijiye komi and cook lafiyayyen abinci for you amman kana barin abincin sabida this stupid girl? Nura kai har ka isa namaka girki kafasaci sabida wata banza? Wai waye kai kakejin wannan isa isan da takama takaman how dare you Nura Hadiza ta shiga kitchen tamaka girki and leave the food for her”? Cikin fushi Anty Jams ganin Hadiza harta manta da duka fadan da tamata dazu tace “Hadiza!” Cikin fushi Hadiza tace “Anty Jams don’t call me please don aganın gaban idanunki shiya fara, shine neman fadana, namaka girki sabida kai bakın makiri ne, munafuki, annamimi saikabar abincin matarka sabida yar aikinta wani kalan bakın dan iskan mugu ne kai Nur……..” jikake tasss! Anty Jams ta zubama Hadiza mahaukacin mari da saida Hadiza taga stars dasauri Hadiza ta dafe kuncinta tana kallon Anty Jamila cikeda mamaki dake huci tace “Anty Jams” cikin tsananin fushi Anty Jams tace “what kind of a woman are you Hadiza kina zubawa mijinki zagi haka? Kinsan hukuncin mata mai zagin mijinta kuwa??? Duk matan dake zagin mijinta wutan lazza ake sata ranan gobe kiyama, what’s all this childish behavior? Ke wace kalan fitinanniyan, masifaffiyan mata ce Hadiza yar bala’i are you from ghetto? Must everything be handle with violence awurinki? Kina tunanin ihu da zagi da haukan nan dakikeyi will solve anything for you?” Cikin serious fushi Anty Jams takalli Nura tace “And you what is wrong with you Nura are you even a man? Akan mene zaka dinga taking this nonsense from this girl bazaka mata shegen duka ba ka farfasa mata baki? Waye Hadiza duka dukanta guda nawa take? Nura wannan ba shiru shiru bane sannan ba hakuri bane this is a disease ke damunka, bazan maka karya ba kaika bata Hadiza to this extend datakeyin yanda taga dama cus tasan bazaka mata komiba? Kana ganin soyayya kake mata haka tana irin haukan nan kamata shiru and let her go free? Nura are you a child da matanka zata dinga zaginka haka?? No Nura ko kanina na jini bazan yarda matansa na zaginshi hakaba wlh Nura, bazakai punishing Hadiza ba if she’s not ready tayi zaman aure dakai ka saketa and chase her out taje and experience life maybe tayi learning lesson nata, Nura I seriously hate the way settings na gidanka is going, enough please you need to wake up for once kayı acting like a man kaci uban marakuyan yarinyar nan, common Aman da Amal kuzo muje mu kwanta wlh gwara na kwana da yunwa danaci abincin chan Thank God akwai pizza and shawarma asama” tawuce sama fuuuu su Aman duk suka bita itama Ummi wucewa sama, Nura yadade yana kallon Hadizan dahar lokacin take rikeda kuncinta kafin yawuce sama shima fuuuu, wasu hawaye masu zafi ne suka fito daga idanun Hadiza tajuya takalli dinning din abincin kowa na wajen sai kawai ta zauna akasa wajen tafashe da kuka sosai tace “shikenan babu mai sona aduniyan nan, ba yarana ba, ba mijina ba ba yayata ba wacce mukafito ciki daya, why is it that nobody is willing to understand what am going through anan? Mijina yaci amanata yaci amanata, ya auromin yar aikina batare da saninaba, ance kaza kaza yasa yamin kishiya sabida bana this and that which na yarda, I tried my best to change Allah yaga zuciyana I cooked this food with so much love for Nuri, I cooked it with love for my husband to please him and to show him I’ve changed but yakama yazomini da wata, what is wrong because na nuna ba ita nama girki ba? Karya nayi? Ita nama girkin? Akanme zanyi pretending nabawa wacce na tsana abinci? Why am I not allowed to express myself, to express my feelings, to express my anger, anmin laifi an dakeni yanzu kuma ance ban isa nayi kuka ba, ba’a ganin laifin yar iskan shameless yarinyar dahar tanada guts ta sauko tafito tazo tazauna a dinning tace zataci abincin mijina, nayi serving mijina abinci yadauka yabata sabida tantiriyan mara kunya ce tadauka zataci akanme zan barta? Godddddd Ya Allah! Maisa nobody is looking at things daga my own perspective? I love Nuri with everything I got and I hate wata atare dashi banda ni, God oooo why are you tasting me this way?? Maisa ban mutu gabaki dayaba na huta cus at this point banjin I can continue living in this agony and sorrows ba gwara na mutu, no one is supporting me wayyooo Allah zuciyana” tai maganan tana wani irin kuka mai sosa rai tana buga kanta abango Nura da all this while yana staircase tsaye yana jinta jikinshi yayi sanyi wani kalan tausayin Hadiza yake bana wasaba he will say this again and again baitaba sanin wannan reaction din zaiyi getting from her dayay auren nan ba, yadauka still halin ko oho, I don’t care dinta zata cigaba dayi cus yasan baya gaban Hadiza at all, she no just send him ne at all but all he’s getting is total opposite of abinda yayi expecting from her is as if auren nan daya kara awoken feelings dinshi in her heart banda haka yakara mata wani strong love nashi azuviyanta yanaga sisters to be honest he hates seeing any mace in pain balle kuma Hadizan shi.

    Yadade awajen sannan yashiga saukowa kasa Hadiza na kuka sosai bin stairscase din tayida kallo ganin Nura ne ke saukowa saita kara kara karfin kukanta ko kallonta baiyiba jitayi kaman ta mutu dinning ya wuce hannu yasa yadauki plate na abincin yadawo ga mamakin Hadiza zama yayi anan kasa agabanta ya ijiye abincin da bottle water ahankali ya debo rice din yakai bakinshi tareda lumshe idanu yace “uhmmm delicious” wani irin tsumewa da kuka Hadiza tayi mai kashe zuciya tana kallonshi tanajin wani irin so dabata taba sani tanama Nuri ba, kusan 5spoon yayi sannan yadebo yakai bakinta yace “eat is very sweet” hawaye na zuba daga idanunta tabude bakinta ahankali yasa mata taunawa tashigayi ahaka tana kuka sosai yake feeding nata har saida shi da ita suka cinye abincin tass yasha ruwa yabata ragowan tasha still hawaye sun kasa daina zuba daga idanunta tashi yayi yakai plate din kitchen ya man maida sauran abincin flask yadauki broom ya share shinkafan kasa tass ya kashe wutan falo yazo ahankali yadagata wlh bamata da karfi ahankali yadauketa chak a jikinshi Hadiza takasa daina kuka son Nura datakeji kaman zai hallakata haka takeji dakinta yabude yashiga da ita tareda maida kofan yarufe ya kashe wuta yayi gado da ita ahankali ya kwantar da iya yana kallon fuskanta da side lamp dake wajen kaman yanda take kallonshi yunkurawa yayi yatashi zai wuce tarike hannunshi karaf hakan yasa yajuyo yakalleta tana kuka in a very very vulnerable state cikin tsantsan so da narkewan zuciya tace “Nuri I’m sorry! Nuri I’m so soo sorry! Nuri kayafemin kaji” kusan mutuwan tsaye Nura yayi Hadiza fa is unapologetic so is he dreaming datake cemai ya yakuri, cikin kuka tace “Nuri bazan iya rayuwa without you ba cus u are my entire life, you gave me happiness, peace and freedom, Nuri u are the best man aduniyan nan and I love you with every every thing in me, Nura I love you a whole lot” yana kallonta still har lokacin cikin kuka tace “I know I’ve been a pain in your ass, I’ve been nothing but trouble, Nura I know am very stubborn but stubbornness dina baya nufin ban sonka wlh ina sonka kishi ne ke dawainiya dani nakasa coming to terms with yarinyar chan matankace my heart is heavy Nura help me I don’t think I can do this alone” gently Nura ya kwanto kan jikinta tareda daura fuskanshi kan nata ahankali cikeda so yace “Hadiza!”Cikin sheshekan kuka murya chan kasa tace “Nuri na! Dan darajan Allah kasaki yarinyar nan banson na haukace gabaki daya, wallahi wallahi zan chanza bakaga yau dakaina naje na dauko yaran nan ba, I took care of them na saya musu pizza I did everything sannan nayi girki, wallahi Nuri I will change and become a good wife, I will give you all my love, na kula da kai and give you the best of the best cus kaine sanyin idaniyata, please Nuri promise me zaka saketa” girgizama mata kai yayi murya chan kasa yace “I can’t Hadiza! I can’t” yanda take kuka dazakaji saika mata kuka murya Chan kasa Nura yace “son da nake miki babu abinda yaragu koya sauka, bazata taba iya sa narage sonki ba, har yanzu Nura is very much your own, just take care of me, give me all your love, pamper me nobody can come between us I promise you this, I am yours, yours only Hadiza, Nura naki ne sai yanda kikai dani circle dina dake mubiyu ne kadai ciki ki kuladani batare dakin kawo kowaba I want you to be blind akaina ki manta inada wata matan, uhm babyna” yay maganan yana manna mata kiss kissing juna sukahau yi yana bude wandonta yadago tareda ja kasa ya yar yacire jallabiyanshi ya yar da boxer yadagota itama yana ciremata riga grabbing her boobs yayi squeezing da kyau kwantar da ita yayi yahau kanta yakai joystick nashi bakinta zai saka ciki yace “s*ck me” juyarda kanta tayi dasauri cikin raunanniyan muryanta tace “Nuri kasan banson inashan gaba fa is somehow abakina, yana sani inji kaman am about to puke” bai damuba yakoma baya yadaga kafafunta yakai kanshi zaisha mata down there da sauri ta fizge kafafunta tace “wannan wani irin barbaric fettish ne haka Nuri? You see abinda nake fadi ko kaga abubuwan da karuwan yarinyar nan takoya maka ko” dagowa yayi strictly yace “stop calling her with that name” zata kara magana yahada bakinshi da nata kawai ya danna mata shi ciki, forget Nuri nada dan shekaru but he’s still good in bed, he f*cked Hadiza so good tafara neman kwace kanta dan to be honest Hadiza ba sex freak bace, batawani damu da sex ba ita ganin sex take as damuwa, tun tana daurewa Nuri na different styles da ita tanajin dadi har abun ya gimsheta zaiyi wheelbarrow da ita ta fizge kafafunta cikeda korafi tace “wai Nuri yaushe kadawo jarababbe ne haka? Are you a monster mehaka kawani babbaremini kafafu, kadage kana abu daya saikace aljanna ake rabawa awajen, please kabarni haka nai bacci is almost 2AM nadare haba kafayi first round” hannunta tasa ta tureshi tareda fizge kafafunta tajuyamai baya kawai yayi shiruuuu yana kallonta rikeda boner dinshi a hannu tana nishi, maganganun Anty Jams ne suka dawomai fill arai he needs to show her he’s d man, hannu kawai yasa ya fizgota a zuciye yana kama kafafunta dasauri Hadiza tace “mehaka Nuri”? Da karfi ya shigeta yafara riding nata crazily tana kokawa dashi almost 15min yayi yasamu yayi exploding yasaketa tareda kwanciya gefe yana maida ijiyan zuciya Hadiza sai tsoki take ta tashi tawuce bayi tayi tsarki tadan gyara kanta, wato haka yakeyi da yarinyar chan Nuri da baida jaraba sai suyi wata babu abinda yashiga tsakanin su, idanma zasuyi one round shikenan but jibi Nuri yau kaman maye, fitowa tayi tazo ta kwanta gefenshi taja bargo sai bacci.

    Kun tuna albishir din danace zan muku yau???🥰
    Here we go, MATAN KO MAZAN chapter 1 is coming to an end just few more episodes to go which nakega zan gama mukushi within this week now here comes the EXOTIC NEWS konace the most EXCITING PART of the news shine Chapter II namu wanda is about CHEATING!!!!

    Did you know acikin kaso dari na ma’aurata 90% na cheating?? Ko kiga mijin yanada babes awaje ko kiga matan nada samari awaje, Ex dina, class mate dina, Classrep dinmu, ko dan office dinta. Cheating a aure yanzu ba yaro ba babba, da sababbin auren da tsofaffin all both mata da mazan nayi.

    Some mata nada samari awaje while some matan kuma yammata garesu, kunsan mata da yawa na gida are into lesbianism kuwa???
    And our Men kusan some of them bada mata suke cheating ba da yan uwansu maza sukeyi???

    Like I said, dana tashi yin book dinnan MATAN KO MAZAN I interview ma’aurata da dama, divorcee da Momies wayanda sun haifi kamata, da Aunties, so I decided to pick on the big, big major matsaloli dake kashe aure ayau to write about them in other to Educate yan uwana mata da maza, to show you how to fight that battle and to let you know every problem nada solution, so idan kin dade ko ka dade kana cheating on your partner thinking bazaka iya dainawa ba this book is here to help you overcome this addiction na cheating, I will pieces this Cheating of a thing, the stages and yanda ake dainawa, abinda mutane dayawa basu saniba shine Ma’aurata na cheating ne sabida dalilai da bazasu wuce 1 zuwa uku ba;
    1- For revenge, wata feels tunda Mijina is cheating on me I will cheat on him back.

    2- Rashin gamsuwa, dayawa maza
    Dayawan maza cheats because they feel matansu are lacking in a thing or something in za other room, same with mata maybe baya gamsar da ita or he’s too tiny.

    3- Addiction, addiction ina nufin wayanda suka saba sleeping around tun kafin suyi aure, so bayan auren bawai suna cheating sabida partner dinsu yarasa wani abu bane ko basa gamsuwa sunayine sabida sun riga sun saba bazasu iya rayuwa da one sexual partner ba, kun gane….

    SAIDAI!!!
    Is not going to be FREE this chapter and I employ each and every one of you to support me, this Chapter two is about to BLOW YOUR MIND💃

    Payment is just 1k, pay into 6353995766 M Shakur world Moniepoint saiki turomin evidence of payment ta whatsapp wa.me/+2347012181461 sainai adding naki a PAID GROUP DIN.

    If you wanna speak to me akan wani abu chat me up a whatsapp 07012181461, ko send a message ta IG @mshakur_world ko tiktok @mshakurr

    Thank you and I love you remember CHANGE IS NOT EASY just like yanda Hadiza is struggling yanzu ta chanza, baka tashi rana daya ka chanza is process the most important a process din is determination wato JAJIRCEWA!!!💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 16

    EPISODE 1️⃣6️⃣
    As usual da asuba yatashi yawuce bayi wanka yayi yafito ya shirya tsaf cikin jallabiya sannan yazo bakın gadon yatadata ta hanyar dagota yana kallon her sleepy face yace “Hadiza” bude idanunta tayi takalleshi ahankali, softly yace “tashi kije kiyi wanka kiyi salla, fix something for breakfast and get the kids ready for school” dudda baccin dake idanunta but jin ayyukan daya lissafo mata saida tabude baki zatai magana saikuma tai shiru tunawa da fadan Anty Jams, ga mamakin Nura dan he was expecting her to nag sai yaga ta gyadamai kai tace “to” wani irin sweet smile yasaki baisan lokacin daya sumbaci goshinta ba yamike yawuce yafita daga dakin Hadiza tabishi da kallo wani wutan sonshi na ruruwa aranta, tana zaune awajen taji yabude kofan dakin Ummi wani irin bakın ciki taji yataso mata batasan sanda ta runtse idanunta gam gam ba, kasa motsi tayi awajen chan saitaji yabude kofan yafita ahankali ta tashi tawuce bayi tayi duk abinda zatayi tafito ta shirya cikin wani jean da riga mai kyau tasa dankunne tai salla tafito tana zuba kamshi tayi dakin yaranta Anty Jams tagani tana shafama Aman datama wanka mai, kallo daya tamata tadauke kai maida kofan Hadiza tayi tarufe tazo wajen ahankali tace “ina kwana Anty Jams” sabida Aman Anty Jams tace “fine” takalli Aman tace “greet Momy ka” batare daya kalli Maman ba yace “good morning Momy” shafa fuskanshi Hadiza tayi tace “morning Son” karasa sakamai kaya Anty Jams tayi tace “jeka wajen Amali” wucewa yaron yayi yafita daga dakin Anty Jams tamike zata fita dasauri Hadiza takama hannunta tace “Anty Jams idan kikai fushi dani rayuwan zata kara zama baki kırın agreni, the husband i have dazan iya magana dashi shine yasani in this situation, I can’t tell my friends abinda yasameni they will just laugh suce banida any influence agidana, kene komi nawa Anty Jams dan Allah kiyakuri, Anty Jams wlh, wlh naji maganan ki, I tried so hard jiyan nan na danne nakasa, look at it fa nashiga kitchen nama mutumin nan abincin dayay shekaru yana complain banamai, saiya dauka yabama wata is it fair? Nura namin mugunta da baki gani sabida anganshi shiru shiru? Anty Jams I can’t pretend to even save my own life maisa kikeso nayi pretending kaman everything is cool? Why do you want me to pretend as if is okay yadauki abincin dana dafamai, na zubamai yabama shegiyan butulun yarinyar chan eh? Why do you want me to pretend??” Juyowa Anty Jams tayi dasauri takalleta ta hanyar rage murya yanda babu wanda zai jiyosu tace “sabida as a woman dole ki koyi pretending, faking it da sauran su you have to learn ai shine kissa da kissisina, yanzu take a look at this girl ba lallai bane tanason yaranki tsakani ga Allah ba but yanzu idan zaki shekara kina gayama Nura Ummi batason yaranshi bazai taba yardaba why? Because dudda tana yar kauye ta iya wasan? Agaban babbansu zata iya nuna tafison yaran nan sama da rayuwanta, Hadiza u are educated but u lack wisdom, bakida hikima ko kadan, bakida dabara bakida wayau, waya gayamiki being real pays a zamanin nan da ake? Kowa is faking it pretending to be who he’s not, Allah kadai yasan waye mu sabida shine kadai yake duba zuwaga zukatanmu, you always allow your heart to control you baki using kanki, head is a monster while the heart is a toy very fragile, wani zubin is good to use head, idan u wanna catch Nura a palm na hannunki you need to stop showing him kin tsani yarinyar nan, and you have to stop being razz, loud and mahaukaciya like attitude nakin nan, yanzu yanda kike so hyper nan yarinyar nan bazata taba fito da true colors nata ba sabida Nura yaganta for who she is, amman idan kinaso to expose her inner aim you need to calm down make peace da kowa the ball is in your court har yanzu, wlh Nura na sonki Hadiza, I keep saying it kada ki bari soyayyan nan ya gushe, control anger naki, learn to swallow pride da kishinki sometimes not everything must be said, ki iya kissa da kisisina ki iya buga siyasa, idan kika kara all this attribute akan knowledge dinki wannan yarinyar saidai tazama yar kallo agidan nan wlh kinajina”? Ahankali Hadiza ta gyadamata kai, saikuma ahankali tace “Anty Jams yanzu yau saina bata breakfast na safe”? Gyadamata kai Jams tayi tace “da nine kema dakaina zanje nakirata bazan bar Nura yakirata ba, Hadiza show this girl she can’t play with you, Kece the real mastermind na game din nan, you set the rule, Nura is yours kinaji, ki nunama Nura love agabanta itama ta shaka, nasan hala tanachan maybe tanajin dadin kunyi fada yau Show her keda Nuri baku iya fushi da juna kinji” Dan murmushi Hadiza tayi abun na shiganta tace “to, yanzu mezan dafa for breakfast”? Anty Jams na mata wani kallo tace “Hadiza ohh Allah, da gaske kin dawo tantiriyan yar iskan yarinyar kin manta girke girken abincin safiya dakikeyi agidan ubanki ko to jeki tambaya YouTube, shegiya rubabbiyan fandararriyan yarinya” dariya Hadiza tayi tawuce tafita daga dakin tana hararan kofan dakin Ummi tadauka kasa.

    Kitchen tashiga tafara aiki, bawai wasaba jitake kaman ta kurma ihu kaman zata zare haka takeji, dudda tanada kitchen tools that made cooking so easy but nahhh! She hate this cooking thing, tana cikin kwashe chips daga air fryer akai hugging nata tabaya dasauri ta juyo hada idanu sukayi da Nura da sauri ta turomai baki kaman yar yarinya tace “good morning” wani irin murmushi yamata dake kashema Hadiza zuciya yace “sannu da aiki Madam Boss Lady, Hajiya Hadiza damusan gida” murmushi tamai saikuma tace “bahaka kakeso na shiga kitchen naita wahala ba look at the way naketa zufa? Nuri why all this stress bayan Allah ya horemana baka ganin yanda business partners naka a living agidansu, why at my age and stage of life zan dinga shiga kitchen when I can hire the Guinness world record breaker Hilda tazama cook dina agidan nan ko wata or wani famous Chef, when the money is not an issue why stressing me Nuri?? Look at yanda nake zufa is it fair?” dasauri Nura yasaketa yana wani kallonta from head to toe saikuma yarike baki yace “dole nasaka miki AC guda uku a sabon kitchen dinki na sabon gida come here my lioness” sai kawai yajawota jikinshi taredakai hannunshi yana sharemata dan zufan daya keto mata daga goshi yace “bari me kikeso natayaki yi?” Bata tabajin dadin tambayanshi kaman na yau ba dudda tasan he’s just trying to block maganganunta ne yasa dasauri ta rungumeshi kaman zata shige jikinshi tace “just kaimin flask dinnan dinning kazo kaji” sakinta yayi yace “to Madam” daukan flask din yayi like a gentleman yawuce yafita dashi yakai dinning ya ijiye ya tsaya daganan yana kallon yanda take aiki a kitchen tana yatsine fuska yana fada da every tool dazata dauka he just wish Allah sa tadaure ahaka and he feels like appreciating and encouraging her, dan jim yayi saikuma ya ciro wayanshi daga Aliiyu ya shiga danne danne Hadiza na cikin aiki a kitchen taji wayanta yayi kara dasauri ta ijiye abinda tarike tazo kan island tadauki wayan kawai taga alert of 5M from Nura ansa narration as gift, dasauri tajuyo da kanta hada idanu sukayi yadan dagamata gira dawani irin sauri tazo kawai ta rungumeshi tace “Thank You Nuri na, you are just the best husband” murmushi yamata yace “and you are the best stubborn wife” dariya tayi kaman ba itaba taja hannunshi tace “kasan menene Nuri inaso nayi running sales na duka items dake shagona 30% off, nasan customers dina will rush everything zasu saye tass inaso nakawo new designs na kaya da turaruka harda kudin nan daka bani zan kara in kawo new abubuwa da yawan gaske nadan kara furnishing shagon, sales din saiya zama strictly online sales no walk in sabida muyi gyare gyaran da fentin da kyau” Gyadamata Kai yayi yace “okay Allah bada sa’a, if you need more fund along the line just let me know” murmushi tayi tare suka karasa aikin suka fito da komi yaran da Anty Jams suka sauko adan kunyace Nura ya gaidata zai wuce sama Hadiza takama hannunshi ahankali tace “Ina zaka?” Yana kallon kwayan idanunta yace “zan kira Ummi muyi breakfast” wani kalan daci taji aranta amman saita daure tajawoshi tazaunar dashi tace “don’t worry I will call her ai komi yawuce, nariga namaka alkawari dakai da Anty Jams I will never cause trouble again” Sosai Nura ke kallonta, murmushi Hadiza tamai tashafa kirjinta tace “trust me” tamike tawuce staircase Nura yabita da kallo tundaga kan staircase tafara kwalama Ummi kira, “Ummi, Ummi baki tashi bane breakfast is ready” sakın baki Nura yayi hakan yasa Anty Jams tace “Hadiza is a good person Nura kawai tana sonka ne over, and is not easy coping with kishiya but zaka gani eventually komi zai daidaita just try and be just, sannan caution duk wacce zatai misbehaving” gyadama Anty Jams kai yayi.

    Hadiza tana kaiwa gaban kofan ta tsaya tai jim saikuma takai hannu ahankali zata bude kofan Ummi tarigata budewa hada ido sukayi da sauri Ummi tasauke kanta kasa ahankali tace “Anty yakuri ina cikin bayine dakike kirana ina kwana, gani” Hadiza dake kallonta daga sama zuwa kasa hijabine ajikinta jitayi kaman ta shaketa tadai daure iya daurewa tace “bismillah zomuje muyi break” dadan sauri Ummi tadaga kanta takalli Hadiza, Hadiza tace “muje mana, kosaina kama miki hannu”? Dasauri Ummi ta girgizamata kai Hadiza tajuya zata wuce dan she can’t stand looking at the girl dasauri Ummi takama hannunta ahankali tace “Anty” tsayawa chak Hadiza tayi batare data juyoba, fitowa Ummi tayi daga dakin gabaki daya tareda jawo kofanta tarufe ahankali Ummi tace “Anty dan Allah kiyakuri kome namiki ki daina fushi dani, gidan nan gabaki daya ba dadi idan ranki yana abace, wlh niba muguwa bace ko butulu bazan taba cutardake ba, bansan dawo da magana baya amman ban auri Babban su Amal dan cin amana ba na au…….” Dasauri Hadiza tace “kin aureshi dan kina sonshi ne ko?” Tajuyo tazubama Ummi idanunta dahar sun kada sunyi ja hakan yasa Ummi tayi shiru, murmushi Hadiza tasake kakalowa tace “ai kin sanar dani ranan nan wuce muje muyi breakfast” Hadiza ta fizge hannunta tayi gaba da sauri cus idan takara 2secs zata iya hallaka Ummi halan, ba karfi a guiwan Ummi tashiga saukowa har kasan Nura yabisu da kallo yanajin wani kwanciyan hankali zuwa Hadiza tayi tazauna kusada shi Ummi tazo taxauna kusada Aman bayan ta gaida Nura da Anty Jams Nura sai kallonta yake yana murmushi Hadiza na lura dashi, zubama kowa abinci tayi ta zubama Ummi ma, Nura sai mamaki yake aka shiga cin abinci, da gangan Hadiza tawani kwanto jikin Nura tana nunamai ketchup dake gefen lips nata tace “Nuri ohh noo sharemin ketchup a saman bakina” batare daya kawo komiba ya yagi tissue yakama kanta yashare mata yace “har yanzu baki daina shan ketchup ba saikace wata yar Karaman yarinya” cikeda son gumama Ummi Hadiza tace “ni ai babyn kane har yanzu right” adan kunyace Anty Jams tace “Ana kirana awaya nidai bari naje sama nasan su Batool ne” dariya Hadiza tayi tasa chips abakinta tawani yi grabbing face na Nura unexpectedly tace “haaaaam bude bakinka kaci” dan kallon yaranshi Nura yayi dake magana da Ummi datayı kaman bataga komiba tana dan hira dasu tana basu chips nasu abaki, cikin whispering cikeda kunya Nura yace “wat is this Hadiza? Children are he……” kafin yakarasa maganan tawani manna bakinta kan na Nura ta turamai Irish din ciki cikeda iskanci, wani kalan wawan kwarewa Ummi tayi dasauri Nura ya juyo yakalleta yana hadiye chips din da Hadiza ta zubamai abaki dayawa bakinshi yacika tam yace “ummm sorry Ummi” maganan shi ma baya fita da kyau, zai bata ruwa Hadiza tarigashi tace “ga ruwa Ummi sannu halan su Aman sukasa kika kware” karba Ummi tayi daidai lokacin schoolbus na zuwa kwasan yaran yazo duk suka mike from dinning kowa najan lunchbag nashi, Nura yatashi yakaisu waje suka fita Hadiza ma ta tashi daga dinning din tayi wajen kofa akabar Ummi kadai awajen atare suka shigo falo suna shigowa kaman ba Hadiza ba tawani tsalle tahau bayan Nura tana ihu kaman yar karaman yarinya tace “kaini dakina Nuri muje muyi wanka kaine zaka saukeni a shago yau I don’t feel like driving” dan satan kallon Ummi Nura yayi kanta akasa ga Irish agabanta daba wani ci takeba ba yanda ya iya yace “muje” dan baiso yace tasauko yabata kunya ga Ummi awajen suka wuce sama Hadiza na counting step, “bene one, bene two, bene threee…waiii Nuri shillani zan fadi…….” wani hawaye masu dumi Ummi taji sun zubomata daga idanu, kawai saitaji yau kaman ita bakomi bane awurin Nura ba, sai taji wani tsoro, shakku da fargaba sun dirku aranta na kada yazo yasaketa fa dama Hadiza tabata 2weeks gashinan sun shirya yasoma mantawa da ita sai wasan soyayya suke agabanta itada bata taba ganin ya goya Hadiza ba tunda take gidan nan, share fuskanta tayi da bayan hannu dasauri, tama kanta alkawari koma menene tashigo gidan nan kenan Billahillazi La’ilahaillahuwa, zatai kome zatayi Nura itama yasota sama da yanda yake jinta aranshi yanzu, duk yanda taso kada tayi kuka kasawa tayi dan wani daci daci takeji tundaga bakinta har duka jikinta kaman taci shuwaka ganin yanda Nura no even send her today soyayya da wasa sukeyi agabanta, haka ta dinga taba abincin tama kasaci sai kawai ta tashi tayi clearing table din takai komi kitchen tashiga gyara kitchen din just to forget dacin datakeji.

     

    Har daki Nura yawuce da Hadiza tana bayanshi sai dadi takeji kaman an mata busharan Aljannatul Firdaus, ga mamakinta bayi yayi da ita daidai zai bude kofa tace “ai nayi wanka sauke ni anan Nuri” batare daya sauketa ba ya bude bayın yashiga yace “nima ai nayi wankan but ba cewa kikayi muje sama muyi wanka tare ba” yayi maganan yana shiga ciki da ita dasauri ta diro daga bayanshi zata wuce tafita ya fizgota tareda mannata abango yace “dawo nan” dasauri takalleshi zatai magana yakai yatsanshi kan lips nata hakan yasa tayi shiru kafin gently yakai hannunshi yashiga cire boturan riganta dasauri takama hannunshi tace “Nuri wai mezakamin? Wlh nagaji Nuri you know very well ni ban wani cikason takura ba tun farkon aurenmu why all of a sudden kadawo this type? Kayi shekaran jiya, kaji jiya yanzun kuma again haba Nuri”? Yana kallonta yace “mesa bakiso? Bani miki dadi ne”? Wani takadirin kallo tamai saikuma ta turo baki tace “ni har yawa dadinka yakemin, kawai Nuri na tsani nayita jika gashina ne every now and then kasan I can’t blow dry gashina dakaina ni kenan kullum naita zuwa saloon sabida kar gashina yayi tsami har yanzu gashina da danshin ruwa fa na dazu” bakinshi yakai saitin nata murya chan kasa yace “koma mezakice kice u can’t escape, I must f*ck you abayin nan aike kika kunnani” Hadiza naughty dariya tayi tace “sannu fire, you such a bad ass man Nuri wlh ka lalace, you’ve rotten” wani fizgota yayi jikinshi yana jan jeans nata kasa saikuma ya mannata abangon yana daga hannunta sama ya danne a tiles kawai yasakin musu shower na ruwan sanyi, ihu Hadiza ta tsandara Nura ya kyalkyace da dariya yana sliding in, Hadiza tace “you so wicked Nuri, ga cold water gaka kuma habb…….” Kasa magana tayi sabida wani twist and turn da Nura yamata aciki sai kawai ta kankameshi, almost 30min suka bata abayin sannan sukayo wanka suka fito zama yayi bakın gado kusada ita yana kallonta tana shiryawa yace “zanje na dauko Hajiya nadawo da ita nan gidan kaman daga sama Hadiza taji maganan wlh saida gabanta yafadi dasauri takalleshi, yana kallonta yace “please don’t give me any more trouble kinji Hadiza? Hajiya bata da matsala, idan tazo just apologize to her and komi yawuce okay” gyadamai kai tayi ahankali tace “tom” murmushi yayi daidai yagama sa kaya yamike yace “yi maza ki karasa shiryawa ki sameni awaje bari nama Anty Jamila sallama” gyadamai kai tayi yana fitowa dakin Ummi yabude yashiga but bata ciki saukowa yayi dasauri jin motsi a kitchen yasa yayi kitchen dasauri adaidai kofa ya tsaya juyowa Ummi tayi takalleshi suka hada idanu ahankali tace “barka da fitowa” saikuma ta daukekai tacigaba da goge gogen datake, jin yayi shiru yasa batare data kalleshi ba tace “me kakeso nadafa maka yau”? Sosai Nura ke kallonta she looks so cold yau, shiga kitchen din yayi yakarasa inda take ya tsaya dab da ita normally yazo close to her like this tana daina aikin datake amman wannan karam saita cigaba da sauri sauri ma, ahankali yace “Hajiya Ummi” batare data daina abinda takeyi kota kalleshi ba tace “uhm na’am, nace mezan dafamaka y…..” hannunta daya kama yarike yasa takasa karasa maganan ta tsaya chak batare data juyoba, murya Chan kasa dake kashe zuciyan mace yace “meya faru baby na? Fushi kike da mijinki eh Ummi na? Akalleni mana” ga mamakinshi fizge hannunta tayi da gudu tawuce kofan kitchen tabude tafita backyard taje wajen bango kawai ta kifa kanta abango tana kuka kaman yar yarinya yana jiyota daganan kitchen, ijiyan zuciya Nura yasauke aranshi yace “ijiye mata biyu ashe is this energy draining, double responsibility, double valaba” wucewa yayi ahankali yabita yaje inda take tana kukan ahankali yadagota yace “waya tabamin ke menene menayi ma gimbiyar matan duk duniya?” Cikin kuka Ummi tace “bakamin komiba ni kawai kewanka nakeyi” saura kadan Nura ya kwashe da dariya yadai daure yayı shiru dan yasan kishin yanda ya goya Hadiza agabanta suka barta dinning ita kadai kesata kuka, cikeda dabara kaman dan yaro age dinta yace “to ai ganinan yau ni nakine ke kadai, haba Babyn Nura, Hajiya Ummi ikon Allah, eh ya isa daina asaran hawayen nan please” yayi maganan yana goge mata fuska wani kalan narkewa tayi ashagwabe tana kallonshi tace “kana sona Dadyn Amal”? Dasauri yace “mesa kika tambaya wannan tambayan”? Kaman zata fashe da kuka tace “ni kabanı amsa” murmushi yamata yayi cupping face nata yace “ina sonki sosai Ummimy, Ummuke Matar Nura” murmushi tamai tace “to shikenan” hugging nata yayi gently to his chest yana patting bayanta yace “kada ki kara tunanin bana sonki kinji shaidan ne now stop crying kimin girki mai dadi yanzu zanje na dauko Hajiya, kada ki kara tunanin bana sonki” gyadamai kai tayi cikin muryan dake sosarai tace “jinin jikina, ruhina da gangar jikina sun riga sun kamu da tantsagwaran tsantsan kindirmon sonka Baban Amali, naduba gabas kainake gani, naduba yamma kainake gani, naduba arewa kainake gani nakuma duba kudu kainake gani, Baban Amanu kasan da cewa rayuwana tariga tasoma ginuwa akan kifiyoyin tafarfashashen sonka dasuka chaki zuciyana? Ayanzu haka danake maka magana tsokan zuciyana da jinin dake cikinta sun riga sun kulla babban alaka nahar bayan rayuwa da kifiyoyin sonka, ina mai tabbatar maka Ummi bazata rayuba idan babu Noor dinta, Baban Amali da Amanu ina maka tatacchen so da babu ko gudan tsaki acikinsa!” Matseta sosai Nura yayı yanajin sonta na ratsa every bit of him murya chan kasa yace “Ummi koda ace soyayyan daname miki nada tsaki ballema babu, to kalaman nan naki sun tache tsakin tass! Inason Zainabu Abu Hajiya Ummi ikon Allah” murmushi tayi dayaji sautin sosai ajikinshi har yayi calming nata down sannan yasaketa yakama hannunta yace “kınada account kuwa”? Girgizamai kai tayi alamun a’a, yana jinjina kai yace “gobe to idan Allah yakaimu zan kaiki saiki bude akwai tukuicin dazan baki, wannan kukan dakikayi saida tukuici” murmushi tamai tace “godiya nake” yana rike da hannun nata yace “mujeto” binshi tayi suka koma kitchen yace “bye” bye tamai yawuce yafita daga kitchen din Hadiza yağanı a falo ta hade rai amman bai kulata ba yayi sallama da Anty Jams bayan ya ijiyemata raps na kudi already akwai direba dazai kaita airport dan 9 zata fita sannan suka fice Hadiza sai daga murya take sabida Ummi taji, har shagonta Nura yakaita sai dadi takeji tana wani soyewa dashi sabida yan plaza su ganshi tasa yafito yashiga shagonta baxaiyi karya ba business wise Hadiza is good, business nata sai booming yake wlh and he’s really proud of her sake rakoshi tayi ya shiga katon jeep nashi yatafi.

    Please Ladies stop being sentimental akaratun nan just be neutral, every character in this novel is to teach you something badan kuji bad nayi rubutun nan ba kodan na raba kanku dan group dina yadawo mini arena na fada, gbas gbos everywhere😂 dan Allah kudaina just read, learn and ku gyara gidajen auren ku❤️.

    Yanzu fa ana zuba kishine anan wato kowa na zuba nashi salon, anyways I am loving this new Hadiza fa😂😂😂 but Ummi ma tarike wuta, I must give it for her resilient nature, the fear na loosing Nuri is there but the gurl keep pushing sai tying all the knots take and I sincerely hope kuna daukan karatun nan.

    Love you feel free to chat me up if you have anything to say 07012181461.
    Whatever you do ki tabbatar kin shiga class Dina na MATAN AURE❤️❤️❤️💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

    ✍🏻M SHAKUR

     

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 19

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 19

    19
    Ihun da Nura yayi saida yatada kowa na gidan.
    Azabure Ummi tabude ido ta tashi zaune da sauri tashiga waige waige ganin Nura baya dakin, jin ihunshi for the second time yasa dawani kalan sauri ta diro daga gadon dan tasan ba lafiya ta nemi hijabinta har kasa tasaka dan ba kaya ajikinta tafito da sauri daidai Nura nafitowa daga dakin Hadiza da jallabiyanshi ajike dauke da Hadiza da kayan bacci ne kawai ajikinta komi na jikinta diddiga yake da ruwa a sheme hannuwanta na lilo daidai lokacin Meena itama na haurowa saman Aman da Amal duk sun bude kofa sun fito, mugun faduwa gaban Ummi yayi daga ita har Meena atare sukace “meya faru”? Nura baimabi takansu ba yashiga sauka kasa Amal tafashe da kuka cikin magagin bacci tana sosa ido dasauri Ummi ta dauketa tana kama hannun Aman dayace “what happen to Mom”? Bata iya bashi amsa ba takamashi sukai kasa da Hajiya Nura yaci karo dake tsaye gaban bene ganin Hadiza a hannun Nura kaman jaririn da aka haifo daga ciki yasa tace “Subhanallahi meke faruwa”? Arude Nura yace “Hajiya bansaniba abayi na sameta ahaka, dubamin ita Hajiya bata numfashi, Hajiya dubamin ita” dukawa Nura yayi rikeda Hadiza awajen dasauri Hajiya ta duka takai yatsanta kasan hancin Hadiza but shiru, saikuma dasauri tasaka karamin yatsanta cikin kunnenta takai babban yatsanta wajen sajenta tayi shiru saikuma tacire dasauri takai hannunta damanta idanunta tabude duk Nura nabin mamanshi da kallo dan Hajiya ita kewa mata dasuka rasu wanka a unguwansu akano.
    Ganin yanayin idanunta yasa Hajiya tace “Innalillahi Wa Innailaihi Raji’un!” Dawani kalan sauri Nura daya gama rudewa yace “noooooo! Hadiza this is not our promise Hadiza, Hadiza” dasauri Ummi tajuya dasu Aman da Amal dake kuka sukai sama baikamata yara na ganin irin wannan abunba, Meena ta taushe bakinta jikinta na rawa, hannunshi Nura yakai yana bubbuga kuncinta yace “Hadiza wake up, wake up don’t do this to me Hadiza, don’t do this to me!” Yayi ihu yana jijjigata ajikinshi yace “tayaya kikeso na raini Aman and Amal ni kadai on my own without you? Don’t betray me this way, I want to spend all my life dake Hadiza kitashi ban yarda ba, wake up” ya dinga jijjigata kaman zai karya mata wuya dasauri Hajiya takama hannunshi tareda girgizamai kai tace “Nura!” Ihu yayi yace “Hajiya nooooo, tasan alkawarin mu, she can’t leave me so soon, a……..asibiti…” kaman wanda yatuna wani abu tashi yayi da sauri ya dauketa yafice da ita bayan yadauki key anan tray dasuke ijiye keys, bude bayan mota yayi yasata yashiga gaba yaja motan da mugun gudu bini bini yana tuki yana kallonta da kyar cikin ikon Allah yakai asibitin su babban private clinic ne.
    Yana parking yawani fito ya fanfala da gudu cikin hospital din. “Doctor help me” yayi wani ihu dayasa some few nurses da Doctors suka fito, ganin Alhaji Nura dan nanne hospital nasu yasa duk sukayi wajenshi yama kasa magana waje kawai yake nuna musu yace “my…..my” sai kawai yayi waje da sauri Doctors suka bishi daya daga cikin likitocin yana sa Nurses afito da gado suna zuwa wajen motan kaman Nura zai fashe da kuka yace “she’s not breathing namata CPR still batai responding ba” dasauri Dr yashiga saka stethoscope yace “minti nawa kenan yanzu da daina nunfashinta”? Cikin mugun damuwa Nura yace “I don’t know I just met her abayi haka, Dr please do something please, I don’t care do whatever u have to do, she can’t go like this, tanada yara biyu yan kanana, please karufamin asiri and do something” daukan Hadiza akayi aka daura agado idan kaga yanda ake gudu da ita akan gadon idan kanada hawan jini zai iya tashi Nura zai bisu cikin dakin aka hanashi aka rufo kofa, tadan karamin window kofan yake lekawa ganin ansa almakashi ana yaga rigan jikinta ana mammakala mata wasu mashina akirji gabaki daya doctors biyu da nurses hudu sun haukace ana hada defibrillator dan ayi shocking zuciyanta, hade hannu Nura yayi yakai yashafa kanshi yana juyi saikuma yasake hada hannayen duka hankalinshi atashe yace “Ya Allah karka dauki ran Hadiza yanzu please Ya Allah, nayi alkawari zanyi azumi uku kadawo min da ita, I need to tell her how much she means to me, nagayamata ina sonta haryau har gobe, and I never intend on hurting her in anyway, Hadiza is my soulmate, Maman yarana guda biyu, my life partner, Ya Allah nasan tayi kuskure da dama but please give her a second chance please give her a second chance to amend all her mistakes ya Allah ka taimakamin” wayanshi ne yashiga ringing hakan yasa ya tattaba Aljihunshi yaciro ganin Ummi ne yasa arude yadauki wayan yakai kunne cikeda tashin hankali yace “Ummi” cikeda damuwa Ummi tace “Ya jikin Anty naga ayanda kafita saisa nakira naji ko kunkai lpy, su Amal nata kuka meya sami, Mommy su bansan mezan gayamusu ba” arude Nura yace “Ummi kutaya Hadiza addu’a ki gayama su Aman suma Maman su addu’a, Ummi banson Hadiza tamutu, she means a lot to me, Maman yarana, nariga nafaro rayuwana da ita, tayaya zan cigaba da rayuwa babu ita eh Ummi?” Yanda Nura ke magana zakasan bemasan meyake fadiba cikeda so dakuma tausayin mijinta tace “in sha Allah babu abinda zai sami Anty kaji Baban Amali, Allah ubangiji yatada kafadanta, ka koma wajensu kada anemeka, kada kadamu zan kula da kowa na gida kaji Mijina” cikeda so yace “nagode Ummi ki tayani bawa Hajiya kulawa kar jininta yahau” gyadamai kai tayi tace “to Mijina zanyi, ka manta damu anan ka maida hankalinka wajen Anty tafi bukatarka, Allah yabawa Anty Lpy” ta katse wayan, komawa gaban kofan yayi daidai ana bude kofan Dr daya yafito dasauri Nura yace “doc…..” anatse Doctor yace “she’s alive!”.

     

    Wani kalan rungume Dr Nura yayi saikuma yasake shi da sauri yaxube awajen yayi sujjada yatashi sauran likitocin duk suka fito da Nurses sai godiya yake musu head Dr yace “zaka iya shiga ka dubata but kada ka tadata kafin ka sameni a office” dasauri cikeda farin ciki yace “to, to, nagode Dr” dasauri yashiga ciro wayanshi yayi dialing number Ummi dasauri ringing daya tadaga cikeda farin ciki yace “Ummi Hadiza na raye! Tafarfado” dasauri Ummi tace “Alhamdulillah Alhamdulilah!” tahau fadama su Hajiya akan wayan duk sai hamdalasuke, ahankali Nura yana jinsu yace “ina Amal da Aman”? Ita tama dauka ya katse wayan da sauri tace “Amal na kuka gatanan na goyata tayi bacci, shikuma Aman gashinan kan cinyana idanunshi biyu yayi shiru kanason kaga Mommy ka ko”? Tai maganan a tana shafakan Aman, Gyadamata kai Aman yayi ahankali, “bashi wayan” Dasauri Ummi tabama Aman wayan cikin sanyin murya yaron yace “what happen to my Mom Dady?” Murmushi sosai Nura yayi yanzu yakara tabbatar yes Allah ne yabama Hadiza second chance tunda gashi yau Aman ne ke wannan damuwan kan mamanshi yaron da is always angry with her, cikeda so da lallashi yace “Momy was a bit sick but yanzu she’s fine, tana bacci anjima zanzo gida na kwaso ku kuzo ku ganta kaji” gyadamai kai Aman yayi Nura yace “you are the only man in the house, bana nan kaine incharge so promise me you will take care of your Grandma, Aunt, Anty Ummi and little Amali, promise me zaka kula da kowa” ahankali Aman yace “I promise Dad, take care of my Mom” murmushi Nura yayi yace “to zanyi, Daddy loves you and Amali a lot ko kada kadamu anjima zanzo gida ok” “okay Dady” katse wayan Nura yayi yawuce yabude dakin ahankali ya shiga, Hadiza na kwance kan gado da kayan patient an saka mata oxygen mask a hancı har lokacin she’s still connected to some machines zuwa yayi gaban gadon ya zaune tareda kama hannunta da sauri yakai bakinshi yayi kissing yana kallonta yayi shiru, she looks so peaceful tana baccin nan babu wanda zai ganta yace fitinanniyan mata ce, sake kissing hannunta Nura yayi murya chan kasa yace “thanks for pulling through, you scare the hell out of me today Hadiza” yayi shiru yana kallonta saikuma ya rungume hannunta akirjinshi yace “I love you very very much Hadiza despite all your crazy and annoying attitude but still ina sonki that’s why I’ve been putting up with your shit all this years, ni kaina I wonder why nakeson stubborn mata irin ki, but yazanyi the love is just unconditional kada ki karamin abinda kikamin yau okay! Kin tsorata Nurin ki sosai Hadiza” yayi shiru saikuma yasake kai hannunta kan bakinshi ya manna mata kiss yana kallon fuskanta yace “bantaba tsanan kiba for once duk kalan abinda zakimini, infact sometime nakan gayama kaina ma I should be grateful inada matan da will always say what’s on her mind the way it is, babu kwana kwana that’s you Hadiza, you are so real ba kaman sauran mata ba that use to be cunny and sly, nasan halinki tsaf ciki da waje saidai na gayama mutane who u are, you are just stubborn, gaki da anger issue but u are not wicked Hadiza, and u are not evil, u don’t even have that time, baki cikin sahun matan dake bin malamai ko bokaye so sometimes I feel kome zakiyi I can put you with it because bakida mugun nufi azuciyanki kuma baki shirka and idan akwai soyayya kome zakimin zan iya hadiyewa and be the man saisa ake ganin kaman nina bataki” yayi shiru yana kallon fuskanta yace “I just want you happy, I want you to enjoy your self saisa I gave you all that u desire, Hadiza banyi aure dan to hurt you ba infact I did it for you, I did it for my children and for myself, you were not willing to change and I don’t wanna force you, danaga kin aminta da Ummi, keda baki yabon kowa but kika yabama Ummi not once, not twice yasa I looked at the girl to see menene in this girl da matane the whole Hadiza ke yaba” yadanyi shiru ahankali yace “ke kikamin auren nan Hadiza and I was still considerate to marry the girl wacce keda yaranmu kukai approving sabida karna saba miki, I don’t think akwai a man that can love his wife this much kaman ni” yayi shiru yace “I thought bana gabanki cus u don’t value me Hadiza, u don’t look at me with love and affection dakikemin kafin muyi aure, rather koda yaushe kallona kike like your mate, bantaba sanin u will react this way da auren nan ba cus banga soyayyan dakikemin ba is as if yayi disappearing, to my biggest suprise naga auren yasa kin dawo dumu dumu kinasona saisa danaga haka I always give you my attention, and my love cus I don’t wanna hurt you, I took care of you, pamper you, always showing you how much u mean to me that babu abinda ya chanza a soyayyan danake miki eh Hadiza. I want you ki tashi mu rufe wannan chapter na fada kullum, mudawo kaman yanda muke da and forget everything and live as one okay happily ever after” yayi maganan yana tashi ya manna mata kiss a goshi sannan yakara gyaramata bargo yafito yawuce office na doctor.

    Zama Nura yayi kan kujeran dake facing Doctor su dake duba file na Hadiza da glasses a idanu, saida yagama yadago yakalli Nura dake kallonshi yace “Alhaji what your wife had today was SCA, watto sudden cardiac arrest!” Sosai Nura ke kallonshi Dr yace “well all I can say miracle kawai yadawo da ita duba da lokacin daya daukeka da ganinta da bata CPR, dakuma kawota nan hospital still ta farfado is just God!” Ahankali Nura yace “Alhamdulillah Ya Allah, Hamdan Kaseeran Dayyiban Mubarakan fii” Dr yadan sauke ijiyan zuciya yace “zanyi managing nata a hospital for 7days dan I need to rule out daga ina wannan matsalan yafara cus this is her hospital bamu santa dawani matsalan zuciya ba nor hawan jini so inaso zan mata some test dazamu duba complete lafiyan zuciyanta tundaga kan arteries da veins da komi na zuciyan, zatayi EKG, MUGA, MRI, Exercise stress echocardiogram test, gashi u need to make payment” yabama Nura takarda ya karba dasauri yana dubawa Dr yace “Alhaji Nura” anatse Nura yace “na’am Dr” Doctor yace “so far so good we don’t know meya jawoma this issue and banso nayi digging into personal life dinku but ina ganin bayan munyi ruling out the heart issue I will refer her to a psychologist cus I think matanka is suicidal!” Dasauri Nura yace “no, no Dr, Hadiza musulma ce nasan we are having one or two issues but nasan bazata taba tunanin kashe kanta ba” Dr yace “yet kasameta abayi akasa ta kunnama kanta ruwa she knows the dangers of that, banda she’s risking jikinta ma cold that could result to pneumonia, she’s also an adult 32yrs da 2kids more of the reason why dole nayi referring nata to psychologist cus I believe batama san metakeyi ba duba da what’s at stake, what life nata means to you, to her kids and to her family” Shiru Nura yayi yakasa magana kana ganin fuskanshi kasan he’s feeling guilty he’s not just happy, ahankali Dr yace “it’s okay you have to be strong anan” gyadamai kai Nura yayi batare daya iya magana ba, Dr yace “I will suggest ka kira all family members nata, duk wani masoyanta should be here for her, koda wasa kada ku kara batamata rai for now, kutaru make her happy and show her how important she is to all of you, like I said bansan mene asalin problem din ba but I strongly believe your wife is depressed and suicidal dan haka you people should show her love” gyadamai kai Nura yayi, Dr yace “Alhaji Nura daga yanzu do kome zakayi kayi dan karta sake having this cardiac arrest dan believe me she might not be lucky the second time!” Gyadamai kai Nura yayi yace “İn sha Allah this is the first and last time” Dr yace “you can go” tashi Nura yayi yafice ahankali yafita waje wani dan dakali yasamu yazauna yayi shiru yana kallon paper expensive scans da test din zuciyan da za’amata sannan yaciro wayanshi yakira Jams ya sanar da ita komi da ake ciki yace “zai samata kudi tama kowa booking flight su taho da Mama da sisters dinta Hadiza needs love that she might be suicidal” katse wayan yayi yatura mata 1M sannan yakira Hajiya ya sanar da Hajiya ma komi, anatse Hajiya tace “Hadiza bazata taba kashe kanta ba Nura kasan likitoci da zancen banza wani zubin” Nura feeling so bad yace “Hajiya duk ni naja komiko”? Tashi Hajiya tayi daga falon ganin Ummi tafito daga kitchen tawuce dakinta ta zauna anatse tace “no Nura bakai bane kaddara ce” muryanshi na rawa yace “Hajiya I push Hadiza so hard da tana kokarin kashe kanta ko Allah yasan ban auri Ummi dan kuntata mata ba Hajiya u know me kinsan danda kika haifa am not a wicked person, inason mata ina kuma tausayinsu sabida matane kannina gabaki daya” cikeda so dakuma lallashi Hajiya tace “don’t beat yourself too hard Nura, mata munada zafin kishi, wasunmu sun iya handling kishi wasu kishin zai iya hallakasu stop blaming yourself Son, aure ba haram bane Alhamdulillah da ranta yanzu abinda zance maka is tundadai case din yakai haka karaba musu gida kaji” shiru yayi hakan yasa Hajiya tace “you have too nasan yanda kakeson yaranka su taso kansu daya but dole ka hakura dan at this point akwai cutarwa tunda Hadizan ba lafiya gwara yanzu ka dauke Ummi daga gidan nan ka kaita wani waje, idan kagama sabon gidan ka maida Hadiza chan saika ijiye Ummi anan kaji” gyadama Hajiya kai yayi yace “to” anatse Hadiza tace “kayı sallan asuba”? Sai a lokacin yaga gari yamadan soma haske ahankali yace “banyiba bari naje nayi” dasauri tace “tohhh” ta katse wayan.

    Karfe goma family Hadiza na asibitin dan Max air suka samu na 7:30 shima dan anyi delay, da mahaifiyar Hadiza, da Anty Jams, da kannin Hadiza guda biyu dake binta Rabi da Hafsat dukansu kowa yayi aure duk jugum kowa yayi a asibitin har lokacin Hadiza bata tashiba, Mama dake kallon Nura dake rikeda hannun Hadiza tace “kaje gida kayi wanka ka kimtsa Nura” girgiza mata kai yayi yace “bazan iyaba Mama, bari saita tashi ai Dr yace nan da awa daya alluran zai saketa ta farfado” saikuma da sauri yakalli Anty Jams yace “ga car key na jeki dauko mata su Aman idan ta tashi ta gansu zataji dadi Batai musuba Anty Jams takarba key Rabi da Hafsatu sukace zamu biki bata hanasu ba duk motan Nura suka shiga ta tada Rabi tace “wlh sainaci kutumar uban yar aikin nan dan durun uwatta” wani kallo Anty Jams tamata tana tuki tace “kinsan Allah idan abinda kike shirin yi kenan zan iya kwana naje na saukeki a asibiti” cikin fushi Hafsat tace “Anty Jams waike mesa kike abu kaman Mama, inda mu Hadiza takira da tuni bamu zo mun tayata koran shedaniyan yarinyar ba takama takiraki bayan tasan u will just talk like Mama look at her yau, inda ta mutu shikenan fa mun rasa yar uwanmu Nura yacigaba da rayuwanshi like nothing happen mukuma fa? Munrasata har abada, duk yanda zaki kalli abin Nura yariga yaci amanar Hadiza daya auri yar aikinta, ai da kishiyan gida gwara ta waje, yarinyar da Ya Hadiza tadauka aiki tamata komi I remember lokacin da Ya Hadiza muna waya tana yaban yarinyar wai tanada kirki tanason su Aman saisa take biyan yarinyar 50k ni kaina saida nayi ihu nace yar aikin kike biya 50k abinda akano 5k ko 8k ake biya duk wata, tacemin yarinyar nada kirki ne but shine munafukar ta aure mata miji akanme Ya Hadiza bazata hadiyi zuciya ta nemi mutuwa ba is it easy? anty Jams are you even relating the pain Ya Hadiza is going through everyday agidan nan tana kallon yarinyan” ta share hawayen daya zubomata da sauri tace “Wlh sabida Nuran ma babba ne kuma akwai Mama awajen da bazan gaidashi ba, munafuki kawai mayaudari mugu sai yanzu dayaga takusan zuwa barzahu shine yaşan yana sonta” Rabi tace “bar munafuki ai maza! Maza! Wlh namiji ba dan goyo bane, namiji butulu! Namiji mayaudari! Maza yan duniya! Ba kunya ba tsoron Allah ba kawaici ya auremata yar aiki!!! Wlh kaman naita surfafamai zagi dana ganshi!” Anty jams kasa cemusu komi tayi dan itama bawai she’s happy bane she’s just feeling bad ganin kanwarta in that state saida sukakai gidan tayi parking tajuyo takallesu tace “Hafsat, Rabi’a na rokeku da girman Allah kada kuyi wani abu kungamai mahaifiyar Nura na gidan bawai kuma lafiya gareta ba please” da magana ciki ciki sukace “munji” duk suka sauko suka shiga cikin gidan, Hajiya ce ke zaune a falo ga Meena agefenta dake zuba mata kunu ganinsu yasa tace “a’a su Jamila ne”
    Cikeda fara’a duk suka shiga gaigaisawa akayi anawa juna jaje, Anty Jams tace “ina yaran Baban su yace nazo na daukosu daganan zamu dan daukanma Hadiza kaya adaki” dasauri Hajiya tace “suna sama yanzun nan Ummi tahaura dasu dan yimusu wanka kuje kuhadama Hadiza kayan kafin nan tagama shiryasu nima ina ganin zan biku asibitin nan naje na ganota” Anty jams tace “Hajiya kina fama da kanki dakinyi zamanki agida wlh ai Alhamdulillah tunda she’s out of danger” Hajiya tace “ina kafana kafanku kuzo kuyi Kari nasan bakiyi ba” duk sukace Alhamdulillah suka wuce sama Meena tabisu da kallo zata mike Hajiya takama hannunta tace “me haka ina zaki saikace sata zasuyi agidan”? Dasauri murya chan kasa tace “wajen Ummi zani” girgiza mata kai Hajiya tayi tace “hakan zaiyi kaman munada wani manufa zuciya Jamila nada hankali ai yi zamanki anan” badan tasoba ta zauna.

    Daidai Ummi tafito daga bayi dauke da Amal a hannunta Aman tariga tamai yana zaune bakin gado da towel yana jiranta tafito ta shafamai mai su Rabi suka bude kofa suka shigo chak Ummi ta tsaya dantama tsorata cikinsu Anty Jams kadai tasani da duk suke kallonta, tsayawa tayi gaban bayin ahankali tace “sannunku da zuwa ina kwana” azuciye Hafsa tataho gaban Ummi tasa hannu ta karbe Amal azuciye ta nuna Ummi da yatsa tace “kina nema ki kashe mahaifiyar su shine kuma kike nan nan da yaranta bakar munafuka” dasauri Rabi tai wajen ta nuna Ummi daga sama zuwa kasa awulakance tace “ke kina gani kin auremata miji ko hmmm je asibiti kiga menene soyayya wlh na tausayi miki dudda bakijin turenci but zan miki u mean nothing to Nura, keba komi bane awajen Nura ba, Hadiza Itace komi nashi, mata ta daukeki tabaki aiki, ta biyaki da kyau, tabaki ci sha sutura but kici amananta ta hanyar aure mata miji abinda kikama Hadiza Allah yasa ama yaranki! Ama kanninki! Ama jikokinki ke duk Wanda kika hada jini dasu Allah yasa amusu!” Dan lumshe idanu Anty Jams tayi tace “Rabi and Hafsat please ku dauki yaran nan kuzo mutafi dakin Hadiza” daukan Aman Rabi tayi suka kwashi kayansu dasuka gani akan gado wanda Ummi tafito dashi suka juya harsukai kofa Rabi tajuyo takalli Ummi da kanta ke kasa tace “kuma wlh idan kina Tuna’nın kin kwace mata miji kinyi kuskure ki rubuta ki ijiye saikin dawo abin tausayi kuma yar kallo agidan nan danko Nura kije asibiti kigani nadaman aurenki yake, mema yakaishi gashi yanzu kin zama sanadin matarshi uwar yaranshi dayakeso na neman ta mutu, duk wani addu’a da bokaye da malamanki gwara ki kirasu dan amiki addu’a Allah sa kar Nura ya koraki, tana maganan suka fice wasu hawaye masu zafi Ummi taji sun zubomata dasauri ta share tafito daga dakin tawuce ta shiga dakinta ta tafi bayi dasauri ta duka tafashe da kuka sosai.

    Har suka gama abinda zasuyi sukabar gidan Hajiya har sawa Meena tayi taje takirata dantamata sallama zata bisu asibiti tace ma Meena taba bayan gida.

    Ahankali take bude idanu dasuka mata nauyi sosai, dummmm kunnenta yakeyi kaman wacce ake kwalama kira daga mesa haka takeji taji ana. “Momy, Momy, Momy wake up” rawa rawa idanunta keyi dasauri jin muryan Aman and Amali daga nesa chan na gayamata ta tashi kafin tabude idanun nata a juye tana kallon sama ganin mutanen da idanunta basa gane mata su da kyau blurr blurr take gani saichan taji murya daga nesa ance “can you see me” sake runtse idanunta dasauri tayi sannan tabude su Dr tagani akanta saikuma taji an rike mata hannu da sauri takalli hannun ganin Amali da Aman suna kallonta suna kuka har lokacin suna kiran Momy yasa azabure ta taso zaune Dr yace “woo wooo calm down kada ki tashi” dasauri tasaya dayan hannunta dake rawa zata shafa kan zaman dake kuka sosai yana shesheka Dr yatayata kama hannun tadaura kan fuskan Aman rike hannun yayi yace “Momy don’t be sick again I will never be angry with you again I promise” gyadamai kai tayi Amal tace “me too Momy” ganin yanda Hadiza ke yunkurawa tanason daukan yaran nata yasa Dr yadago gadon tayi zaman kwanciya yasada yaran yasasu ko Wanne aside nata rungumeta sukayi kuka hawaye ne suka fito daga idanun Hadiza ahankali Dr yaciremata oxygen din cikin murya mara karfi tace “A…..man, Aaa….mal” “yes Momy” kankamesu tayi kafin in a very weak voice tace “I……..na…..Da…….dy….” Dasauri duk suka dago suna mata pointing Nura dake tsaye dab da bed din yana kallonsu yana murmushi wani kalan kallon Nura tayi sai lokacin ma taganshi da duka mutanen dakin sai kawai tafashe da kuka sosai tana mikamai hannu dasauri Nura yaje rungumeshi Hadiza tayi sai a lokacin karfin kukanta yakaru ta kankame Nura sosai tanajin mugun sonshi aranta tace “Nuri kayakuri kayafemin duk abinda namak……” hannunshi yadaura kan lips nata yace “shiiiii u talk too much daga tashinki just get better I love you My Didi” hawaye na bulbulowa daga idanunta tace “I love you too my Nuri” Dr yace “tunda dai love moment ake bari naje anjima madawo atafi da ita for lab investigation, yanzu have this moment” yawuce yafita Nurse tabishi sakinta yayi Ahankali tana kallon yan dakin tace “Hajiya” dasauri Hajiya taje wajen gadon tace “naam Hadiza ya jiki”? Cikin kuka tace “Hajiya kiyakuri kinji nasan namiki laifi wlh Hajiya haushinki nadinga ji gani nayi kaman kene kika sashi yamin kishiya da yar aiki na, bake kadaiba kowama haushinshi nakeji har Anty Jams dake gayamin gaskiya da ina bayi naji numfashina yana tafiya I was trying nakira Nuri like azo ataimakamin but nakasa naji wani murya nagayamin bazakizo ba sabida na cutarda ke sannan na zargeki abisa laifin da baki aikata ba kuma baki tsaneni ba, Hajiya naji dadi da Allah yatasheni nayi alkawari dan nemi gafaranki Hajiya kiyakuri kinji” share mata fuska Hajiya tayi tace “Hadiza nobody is above mistake komi yawuce awaje bantaba rikeki ba kinji”….
    ***

    Yau kwana uku Hadiza na asibiti tun ranan Nura bai kara kiran Ummi ba ko gida baya dawowa shike kwana da Hadiza saidai akaimai kaya, yan uwanta ne ke dawowa gida kwana su shiga kitchen suyi girki saiya zamto Ummi kullum taba daki muddin zata fito tahadu da Hafsat ko Rabi saisun yada mata habaici, takira Nura sau uku bai dagaba tamai text daban daban duk ba reply Hajiya kadai da Meena ke kula da ita dudda bata nunamusu komiba Hajiya ko ankawo abinci idan sun gama girkawa ko Ummi na sama saita kirata tazo aci abincin da ita hakanan zata sauko not feeling among, idanun Ummi sun fada babu abinda yafi damunta yanda Nura bai kirata ba ba reply kullum saitai kuka kafin tayi bacci.

    Yau kaman kullum wuraren 12 tana zaune ita kadai a falo Meena tashigo dakinta tace “tashi muje asibiti tare” dasauri Ummi tace “ba’ace naje ba, kinga ko Hajiya batace najeba hakama Baban Amali karnaje wani abu yasami Hadiza” Dasauri Meena tace “Hajiya takirani tace muzo tare Allah shayi akasa nahada, tashi kisa Hijabi muje bolt na kira yana waje ya iso” badan tasoba ta tashi hijab kawai taja maroon har kasa tasaka tabi Meena suka fice daman kowa na asibitin har Hajiya suka wuce.

    Wuraren 1:15 sukakai hospital din Ummi sai kallon asibitin take yahadu sukai ciki har zuwa gaban dakin da Hadiza ciki Meena na gaba ta window dakin Ummi ta hangi Hadiza zaune kan gado ga Aman da Amal sun rungumeta kaman zasu koma ciki Hajiya na bata kunu da spoon tanasha su Yayyinta da Mama ana hira kowa na nan nan da ita, daidai Meena tasa hannu zata bude kofan su shiga ciki kaman daga sama sukaji muryan Nura yace “Meena!” Dasauri suka juyo Ummi ta tsare Nura da idanu sabida yanda tai kewanshi yaune rana na hudu dabata ganshi ba dasauri sauri yake tahowa yana leken dakin kaman mara gaskiya yana zuwa wajen cikeda fada yanuna Ummi yana kallon Meena yace “wayace ki kawo Ummi asibitin nan eh Meena?” Wani kalan dum! Dum! Dumdum!! Ummi taji azuciyanta ta tsaya chak tana kallon Nura dake kallon Meena ranshi abace kawai yasa hannu ya karbe flask din daga hannun Meena yace “wuce kije ki komarda ita gida” daidai lokacin sukaji Hadiza tace “Hajiya kaman muryan Nuri na nakeji ko” dasauri yayi kofan yace “gani nan My Didi” yashiga ciki ba Ummi kadaiba har Meena jitayi ranta ya sosu da abinda Nura yayi daurewa Ummi tayi iya daurewa takalli Meena cikeda Fara’a tace “kingani saisa nace miki bai dace nazo ba Hadiza batada lafiya, baidace ta ganni ba kiramin bolt nabishi nakoma gida kesaiki zauna” Meena batace komiba cikeda bacin rai tashiga tafiya tana neman bolt Ummi dan juyawa tayi takalli cikin dakin Nura na kusada Hadiza ta daura kanta a kirjinshi yana shafa mata kalaban kanta da wani kalan shaukin so dayan hannunshi yana nuna mata hotunan bikinsu sai murmushi suke both ita da shi looks so happy, hawaye Ummi taji sun zubomata da sauri tasa hannu ta goge tajuya dasauri tawuce awaje tasami Meena daidai bolt yazo Meena zata shiga Ummi takama hannunta tace “Meena dan Allah sabida ni kada ki fasa zuwa wajen Hadiza ki gaidata please kije nizan koma gida ni kadai please dan Allah” Meena da idanunta sunyi jaaa tace “Ummi sakeni” cikin lallashi Ummi tace “inhar kinasona da gaske ki koma nizam koma gida please Autan Hajiya” badan tasoba takoma Ummi tashiga motan bolt yaja motan suna fita daga asibitin Ummi tarushe da kuka sosai dasauri mai bolt yajuyo yace “Hajiya lafiya”? Cikin kuka muryanta bama yafita da kyau tace “bakomi kawai mutafi” yanda take kuka harda shesheka saitaji ta raina kanta duba da yanda Hadiza keda komi, she’s surrounded da family dake sonta ga Miji ga yara saitaji ta raina kanta, batada kowa batada komi! Allahu Akbar! Ranta ya sosu yau takara tuna ita marainiyace Mamanta ta rasu! Babanta yarasu! Kakansu kadai gareta data tsufa tukuf sai kannenta yara su Shatu su biyu 12 and 13yrs, jibi yanda Nura yayi da ita yau kaman wulakantacciya mara daraja! Yasa she felt like she’s nothing to him! Yasa taji she don’t belong anan a family nan, ahankali ta bude yar jakan data dauka taga tanada kusan 15k aciki cikin muryan kuka tace “direba dan Allah kaini tasha dazan sami motan Adamawa yola” Dasauri direba yace “location zamu chanza kenan jabi garage za’a samu” cikin muryan kuka tace “kaini” nan yakaita har inda ake lodin Adamawa Yola tabiya direban 2k tana zuwa tabiya 13k kudin mota amman sai dare motan zai tashi tafiyan dare ne tanemi waje kawai ta zauna takifa kanta kuka take mai tsuma rai bana wasaba, gani take ko Mudi baitaba hurting nata this way ba dan shi physical damage yamata na duka dasauransu, Nura just crushed her fragile zuciya dake cike da dumbin sonshi azuciyanta kafin yakoreta gabadaya agaban jama’a gwara takoma kauyensu ya biyota da saki takara rushewa da kuka.

    Wayyo Allah na Ummi😭

    Kai Maza maza maza!! One word for men please cus suna bani ciwon kai.
    What exactly keep a Man?? Sex? Happiness? Respect? Ko Loyalty???
    The list is long but in your opinion what keep a Man?💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

    ✍🏻M SHAKUR

    EPISODE 2️⃣0️⃣

    @TRENDYOUTNET Modest fashion world ne inda zaki samu professional kayan zuwa office masu kayatarwa, kyawawa, masu suturta jiki da mutuntawa, idanma casual kaya kike nema na sakawa yau da gobe duka tanada sunadashi all you have to do is chat them up ta wannan number
    wa.me/+2349093300112
    Kokuma zaki iya zuwa shagonsu dake nan Shop C22C 2nd floor Platinum Mega Mall opposite Ultra Modern Market Behind Next Cash and Carry Jahi, Katampe Road Abuja
    And u can also check shagonsu a IG @trendyoutnet don’t forget to follow them🔥 cus anayi baki😅

     

    20

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 12

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 12

    Episode 12
    Wani irin kallo Hadiza kema Nura kaman wacce hankalinta ya gushe ta tsare bakinshi da yanda labbunshi ke motsi da kallo kanta yayi wani dummmmmmmmmm, kunnuwanta sunyi wani shuuuuuuu kaman irin ana hura tsakiyan gwangwani kanta yamata nauyi kaman an daura block kawai kallon Nura take da bakinshi dake motsi, tanajin wasu maganganun wasuma bataji, anatse Nura yace “for now anan zamu zauna dukan mu kafin nan da 2month an gama gidana zamu koma kowaccen ku nada flat dinta, for now ita zata dauki dakina ke kina dakinki ni zai zamto banda daki, duk wacce yake girkin ta zan kwana adakinta wanda zan raba muku 2-2days, da zan iya daukan dayan dakin dake kusada naki but sabida baki gwara kawai ni nahakura da rashin dakin ai is just 2month or less ma, kece Babba Hadiza ga Ummi nan amana, Ummi kece karama ban yarda ki sabama Hadiza ba, kuyi zamanku lafiya nariga nabiya kudi yau za’a hadoma kowaccen ku akwati, sannan Hadiza ki duba gidan komene babu saiki sanar dani nakawo kinji” sosai Hadiza kecikin wani kalan state dabazata iya tantance kowani yanayi take ciki ba hakan yasa takasa magana shock yarufe mata baki, shi Nura har kasan ranshi yaji dadin shirun datayi dan baiso tai haukan nan agaban Ummi koma menene tamai shi adaki kokuma kawai dai not in present of Ummi dan baison abinda zaisa Ummi ta rainata, kallon Ummi yayi yace “tashi kitafi dakinki asama saida safe” gyadamai kai tayi tamike tawuce tana tafiya ahankali tayi hanyar staircase daidai ta daga kafanta zatahau bene cikin wani irin murya dashi kanshi Nura baisan Hadiza nada itaba tace “Um……….mmi!” Chak Ummi ta tsaya tareda juyowa dasauri gabanta nafaduwa, awani kalan zuciye Hadiza ta taho zatai wajen karaf Nura yarike mata hannu yace “ina zaki” cikin wani buhun uban ihu Hadiza tace “sakeni Nuri kafin na daukeka da mari, tell yar aikin chan tabarmini gidana right this minutes dan I just want to assume all abubuwan dakagama fadi yanzun nan wasa kake is a prank Nura, let’s pretend you are just joking, baka isa kamin kishiya ba Nura, Nuri nace baka isa kamin kishiya ba! Kai baka isa ka kara aureba Nuri! So tell this village girl to get out of my house right this minute before na salwantar da rayuwanta! Nuri ka gayama yar aikin chan tabarmini gida” Hadiza tai maganan tana tura Nura so kawai take ta fizge kanta taje wajen da Ummi ke tsaye gaban bene, “Hadiza!” Nura yakira Hadiza azafaffe yana rikeda ita ya jijjigata yace “look at me” juyoda kanta tayi from kallon Ummi datakeyi, kallonshi tayi da jajayen rinannun idanunta tana kallon cikin kololuwan idanunshi kaman yanda yake kallon nata yace “nakara aure Hadiza! Nayi wani aure Hadiza! And Ummi na aura! Na aure Ummi! Yes Ummi is my wife! Matata………” “Noooooooo!” Hadiza tayi wani kalan ihu da saida gidan yadauka tadaura duka hannayenta biyu akan kunnenta takara kurma ihu dako maigadi zai iyaji tace “nooooooo! Nooooooo! Nuri I said No! Yar aikin chan can never, ever become your wife!” saukowa su Aman dasukayi ji ihu yasa Nura yajuya yakalli wajen, wajen Ummi yaran suka tsaya tareda rikemata hannu Aman yace “Anty Ummi menene”? Nura na kallonsu yace “kaisu sama su kwanta Ummi” gyadamai kai tayi takamasu sukai sama dagudu Hadiza ta yunkura zatai wajen kaman mahaukaciya tace “karki sake kije saman gidana, zokibar gidan nan” dasauri Nura yariketa gam yakalli Ummi data dake tsayawa yace “go” wucewa sukayi yaran duksun tsorata ganin abinda Maman su keyi, Nura saida yaji karan sun rufe kofa sannan yasaki Hadizan, babu alamun wasa kan fuskanshi yace “Hadiza nakara aure because of so many reasons which I don’t wanna go into details of that dan kin fini sani, please ki kama kanki don’t start with this your drama” Nura yamata magana babu alamun wasa akan fuskanshi, Hadiza na wani kalan kallonshi da idanunta dasukai jazur ganin ya chanza mata kaman bashiba dan da dane tai abubuwan nan shareta zaiyi bazaimace wani abuba saikuma tadaga hannunta tanuna kanta muryanta yayi sanyi kaman kankara tace “Nuri ni? Ni? Wai ni Hadiza kama kishiya Nuri?? Nura!?” Takira sunanshi cikeda mamaki, shiru tasakeyi tana kallonshi tana kara kara kallonshi, sai kawai takai duka hannayenta ta kama gaban riganshi kaman akace ta dakeshi zata iyane tace “Nuri ni zaka yaudara haka da yar aiki na? My slave fa? Wacce kecin kashin gidana dana yarana? Yarinyar dani nakira agency aiki aka kawomini ita all u ever did was to pay salary nata, Nuri wai am I dreaming did u just say ka auri Ummi yar aiki na? Nuri wannan wani kalan bakin cin amana? Yar aiki na fa Nuri, Ummi, Ummi this Ummi dakemini gyaran gida da wanke baya da wanke wanke ita kaje ka auro?? Nooo I don’t believe this it’s a lie, Nuri wai ni Hadiza kama kishiya da yar aikina”? Yana kallonta yace “let it sink in your brain nakara aure, and yes yar aikin taki Ummi na aura haramun ne? Ummi is my wife now so cikani” sake chakumeshi HADIZA tayi da kyau zuciyanta na tafarfasa kaman ta mutu takeji tace “amman Nura kacika annamimin, makirin, munafuki maci amana da tsoron Allah, Nura wato all this while you’ve been fooling me kana soyayya da yarinyar nan kazo kasata tacemin zataje kauyensu duba kakarta kuka tafi kaje ka aurota, Nura yau 14days sau daya nayi magana dakai u don’t return my calls, u don’t reply messeges dina, Nura ni Hadiza kama kishiya wai Ummi, Ummi dai yar aiki na? Nizaka yaudara kaci amanata Nura, eh”? Hannunshi yadaura kan nata yacire daga gaban riganshi yace “bandawo gidan nan to fight with you ba so just respect yourself kidena haukan nan kar co wife naki ta rainaki” kaman ya zubama Hadiza fetur wucewa tayi stairs tace “durun uwan cowife, ita Ummi hartanada liver aure mini mijina? Wlh Nura auren nan trust me dream kakeyi baka isa bane kuma kayi kadan kamin kishiya na rantse mama da Allah sainasa gidan nan ya gagareta zama billahillazi la’ilaha illahuwa, babu macen data isa ta auri mijin Hadiza kai ko yar boko mata masu usuli da daraja basu isa su auremini mijina ba balle kuma yar aiki, mijina Ummi ta aura ni? Aiko tanaso ta mutu” da gudu gudu take hawa stairs daidai takai falon sama Nura daya biyota ya fizgota azuciye tai ihu tace “saken mini hannu Nuri” kobi takanta Nura baiyiba dakinta yabude ya jefata ciki yashigo shima tareda maida kofan yana rufewa yana saka key yazaro key ya jefa a aljihu dasauri ta taho wajen kofan tayi ihu tana dukan kofan da hannu tace “kabude mini kofa nafita I need to show that girl her proper place which is trash, wlh, wlh I will never share mijina da wata balle kuma Ummi yar aiki, kabude kofa! Nura open this door ko na fasa kofan nan” “Enough!” Nura yadaka mata tsawa da saida tadan firgita dan kaman zai daketa, nunata yayi da yatsa yana kallon kwayar idanun ta da idanunshi da sukai jajir yace “enough of your nonsense Hadiza! The only reason I even let you back into this house sabida Hajiya ne! Aure is not a do or die matter, idan kinga bazaki iya cigaba da zama amatsayin matata ba let me know I will let you go, but wannan haukan naki nagama dauka Hadiza your time is up, koki natsu and live peacefully under me ko u can leave the Marraige nagaji, nagaji da stupid, wild attitude naki always barking woo woo kaman karya haba! Don’t you get tired of shouting? Why do you think violence is always the way out for you? Kina behaving kaman ba mace ba, is something wrong with you upstairs I can take you to the asylum adubamini ke, nayi aure and so wat?” wani kalan kallo Hadiza kema Nura tunda ta aureshi yau kusan 10yrs kenan dan bata haihu da wuri ba yaune rana na farko da Nura yabude baki yamata masifa haka, bawai basa fada bane no sunayi but masifa ya kwakkwance mata haka yaune rana na farko, sosai take kallonshi Nura jikinta na bar-bar duk yanda taso ta daure ta cije tahana kanta saita kasa sabida yanda yakirata karya, harda mahaukaciya ma dan cewa yayi zai kaita asibitin mahaukata aduba ta, yana kuma threatening nata da rabuwan aure kawai saiga hawaye sharrrr ya sauko daga idanuwanta masu mugun zafi, muryanta babuma karfi balle kuzari tasake nuna kanta tace “Nuri ni? Ni kake gayama bakaken maganganu haka? Nuri nika tsana haka? U just called me a dog, mahaukaciya and so much more, Nuri you hate me sabida kayi aure? You hate the sight of me, Nura ni zaka cima mutunci ta hanyar auren yar aiki na? Idan ka tsaneni haka kagaji dani zaka iya cika ragowan saki biyun dasuka rage why marry maid dina? Kasan yanda nakeji azuciyana Nuri ni, kaci amanata, ka yaudareni, ka munafinceni” wucewa tayi dasauri taje gaban gado tazauna akasa ta kankame kanta tana shaking kaman ta haukace, saikuma tafara buga kanta ajikin gado jikinta ko’ina da bakinta na rawa tana maganganu. “yar aikina, yar aiki, Nuri ya auro mini yar aiki na, Nuri ya tsaneni, ya tsaneni, ya tsani ganina, ya cuceni, ya wulakanta ni, ya toxarta ni, Nuri zoka kasheni nasan bana duniya namutu kayi auren nan, aure fa? Aure Nuri yayi aboye sai yau bayan sati biyu yake fadamin kuma yar aiki na, Ummi, Ummi, Ummi uhmmm Ummi”.

    Nura kawai yayi shiru ya tsaya yana kallonta he can’t even remember the last time dayaga Hadisa na kuka haka maybe tun kafin aurensu, cus irin hard ass ladies dinnan ne ita, she’s in total shock dan bamatasan tana kukan ba, strong woman Hadiza ke kuka hakayau, he wanted to ignore her amman kuma saiya kasa ganin yanda take hitting kanta is getting serious sai kawai yawuce tabashi tausayi, kishiya koyaya batada dadi azuciyan mata but yazaiyi she pushed him yayi? Wucewa yayi yacire kayan jikinshi yarage daga singlet sai boxer, sannan yadauki wani bottle water daya gani adakin yataho inda take gently ya tsugunna agabanta ahankali yakai hannunshi yadaura kan fuskanta yana cire kanta daga jikin gadon dasauri ta kabarda hannunshi tana kuka wiwi komi najikinta rawa yake tace “kada kasake tabani da hannun nan daka taba wata, Nura nika yaudara haka kaci amanar alkawarin mu, Nura nizaka wulakanta ka tonama asiri ni Hadiza the mother of your kids, Nuri what have I done to you to deserve this eh? How can you comfortably hurt me this much? Nuri haka ka tsaneni?” girgiza mata kai yayi ya ijiye ruwan agefe ganin yanda jikinta ke rawa she’s seriously having a panic attack gumi na keto mata tana zufa duk kalan Ac dake dakin, ahankali softly yace “come here Hadiza, u are not in right state of mind yanzu kome nagaya miki bazaki gane menake cewa ba, zonan” da karfi yasata ajikinshi tana ihu kasakeni, sata akirjinshi yayi da karfi yana patting back nata kaman yakara cemata takara karfin kukan wani kalan kuka take kaman anmata rasuwa yacigaba da patting nata lovely yace “shiiii it’s okay” kankameshi Hadiza tayi sosai da sauri ita kanta batasan iyakan son datakema Nura ba sai yanzu dayay hugging nata kaman yana waking feelings din datake dashi for him she became so vulnerable and weak, yau batada karfin nuna she’s a strong woman dan zancen kishiyan nan hit her so damn hard, kuka take bana wasaba harda shesheka singlet din Nura ya jike sharkap da hawayenta, she’s just crying, crying bana wasaba kaman zata mutu takeji, wani luteten dunkulelen bakin ciki takeji bana wasaba, sosai Nura ke lallashinta ta hanyar buga bayanta yana manna mata few kissing agefen wuya like a baby, tana jikinshi cikin kukan tace “Nuri dan Allah kada kamin kishiya kaji, Nuri dan Allah wlh I can’t stand naganka da wata zan iya haukacewa barinma yar aiki na, dan Allah kaji Nuri mena maka zakamin kishiya da Ummi eh”? Yana bubbuga bayanta yace “Hadiza u are a very very stubborn woman, when I married u bahaka kikeba, I loved you kaman ba gobe you know, waye baisan kalan soyayyan damukayi ba, but everything changed damuka dawo garin nan, tunda na aureki baki taba cemin kinason kaza na hanaki ba, I change kayan daki anytime kikcemin kinason a chanza, I change cars for you, banwani damu da zuwa vacation ba but kinaso ke we go on vacation every year banda Umara da every now and then nake kaiki, have I ever wronged you kona hanaki abinda kikeso? Farko farko ai kinamin girki rana daya kawai kika ijiye, bakimin komi, baki damu dani ba nor my children wanda kinsan banda abinda nakeso aduniya kaman su, I can’t talk to you kafin nayi miki magana daya kinyi magana dari, kinamin ihu aka kaman yaron dakika haifa, bakiganin girmana ko darajata, Kona Hajiya, all I ask is for your attention and care, respect sannan kisa ido akan yarana but kin nuna ban isaba ban isa incemiki yi kazaba agaban idona zakice no, Bana iya tankwaraki ko kadan, u feel nidake daya ne, abu kadan kice feminism bazaki bari nayi demeaning naki ko belittling naki ba, you’ve been maltreating me doing as u wish, Hadiza ni ba yaro bane am 49 clocking 50 Allah yahoremini arziki da abinyi all I want yanzu is peace of mind and watch my kids grow na barmusu this company suyi taking over but kinki cooperating, u pushed me so hard and kinfi kowa sanina banda son mata banda biye biye, I’ve always been a one woman’s man but u made me look outside Alhamdulillah bantaba zina arayuwana ba and bazantabayi ba that’s the reason nakara aure don na sami kwanciyan hankali” cikin kuka sosai tana wani kalan sauke ijiyan zuciya tace “to saika auri yar aikina” Yana tapping bayanta har lokacin yace “Ummi ce the only macen dake rayuwana banda ke, kema kinsan ko kallo mata basu isheni ba, halinki made me notice the girl, yarinyar is a very good girl, she’s young, smart hardworking, she can cook and above all yarana na sonta sosai sais…….” jin zafin yanda Nura ke yabon Ummi yasa cikin kuka Hadiza tace “banson ji, toka saketa dagayau kome kace nayi zanyi please ka saketa na yarda ta kwana agidan nan yau gobe da sassafe tabar mana gidanmu I promise zan chanza kome kakeso zan maka amman kasaketa please Nuri karufamini asiri, I can cook nima, gani hardworking, smart, intelligent kuma I’m educated unlike yar aikin, kasaketa wlh zan chanza namaka alkawari” ahankali Nura yajaye jikinshi dagana Hadiza yakalleta batare dayace komiba, fashewa da kuka sosai tayi takai yatsanta ta taba harshenta tace “na rantse da Allah Wallahi Wallahi Nuri kaji na rantse ko kasaketa zan dawo sak Hadiza na nada, nadinga maka komi, bazan kara bata maka raiba, please karufamin asiri kada kasa duniya tamin dariya akaji ka auri yar aikina, please kasake ta kaji Nuri” dan lumshe idanu Nura yayi yabudesu yakalli Hadiza dake kallonshi tace “kaji Nuri kasaketa” girgiza mata kai yayi ahankali yace “bazan iya sakin Ummi ba Hadiza!” Dum! Gaban Hadiza yabuga dasauri harsaida takai duka hannayenta saman kirjinta wani sanyi na ratsata tace “mesa Nuri bayan nagaya maka zanyi komi infact nama gama daukan yar aiki har abada, dakaina zan dinga komi and take care of su Amal maisa bazaka saketa ba? U don’t need anything from her again, nice dama kuma nace zan chanza dagayau, maisa bazaka saketa ba”? Yana kallonta right in the eye yace “sabida nariga nakamu da sonta kaman yanda nake sonki!”
    Tunda Allah ya hallito Hadiza bata tabajin wannan kalan pain din datakeji azuciyanta yanzu ba jin mijinta nagaya mata da bakinshi cewa yakamu da son wata kuma yana gayamata right before her eyes wai bazai iya rabuwa da itaba sabida yana sonta kaman yanda itama yake sonta wato harya soma raba musu komi equally irin ita da yar aikinta duka abu dayane yanzu azuciyanshi, kawai saitaji kaman zuciyanta ya buga kawai tai baya luuu bawai ta suma bane tanaji sarai yanda yake kiranta da yanda yariketa yana shafa ruwa a fuskanta kawai her energy is just on a zero level idanma akwai minus zero energy level nata na wajen, kaman ya lura da hakan hakan yasa Nura yadauketa ahankali yadaura kan gado ya kwanta gefenta tareda kashe wuta ahankali ya rungumeta cikeda lallashi yace “I still very much love you Hadiza don’t hurt yourself okay, you are my first love Hadiza, Maman yarana, yaran dasuka zame mini haske arayuwana, u gave me the most beautiful, adorable and sweet kids aduniyan nan no one yataba bani kalan gift din dakika bani Hadiza how can I even hate you eh my Didi”? Bakaramin tausayi tabashi ba, wlh yayi auren nan but ko kadan baimayi tunanin kalan wannan reaction din zatayi ba he was just expecting haukanta as usual baitaba sanin she will be this down ba and weak tana kuka haka having panic attack hakaba, so dama tana sonshi, batason taganshi da kowace mace but shine takemai all abubuwan datake, lallai kishi babban abune awajen mata.
    Gently yadaura bakinshi kan nata hannunshi yana share hawayen dake fitowa daga idanunta yana kissing nata kafin ahankali yafara yunkurin making love da ita cikeda rashin karfi dakuma kuka cikin muryan bakin ciki tai ihuu tace “kada kasake ka sadu dani Nuri gabanka daya shiga jikin yar aikina bazai kara shiga jikina ba wlh kajini” hada bakinshi yayi da ita bai kara bari tayi magana ba dudda batada karfi saida tai kokawa dashi dan bataso yamata wani abuba but still saida yayi sexing nata da karfi da yaji she have no option but to succumb jikinta ya mutu gabaki daya kawai sai kuka takemai, dole ma Hadiza taso mijinta tayi kishinshi, Nura nada kirki ne sosai lallashinta yake bana wasaba yadinga shafa kanta duk uban bakin cikin datake ciki saida soyayyanshi yayi suppressing nashi bacci yayi awon gaba da ita sai ijiyan zuciya taje saukewa ajikinshi he cant lie is just soothing sex ne kawai wannan to calm her down dan sex na rage bakin ciki da damuwa, that fun da excitement dinnan ajikin Ummi kadai yakeji, lullubeta yayi da bargo yatashi bayinta yawuce yaje yayi wanka yafito kayanshi yasake maidawa yayi wajen kofa ahankali yabude yafita yaranshi yafara dubawa yayi mamaki ganin duk Ummi tamusu wanka sunsa kayan bacci tarufesu da bargo tarage musu AC addu’a yamusu yafito dakinshi wanda yake dakin Ummi yanzu yawuce ahankali yabude kofan tana kwance akan gado tai lamo dudda ba bacci takeba dan takasa bacci tun bude kofanshi taji, zama yayi ahankali bakin gadon yakalli fuskan Ummi feeling a bit bad cus baimata saida safe ba hannunshi yakai ya shafa kumatunta tareda dukowa ya manna mata kiss akai yace “good night Hajiya Ummi” sannan yamike yaje gaban wardrobe ya debi some clothes nashi yawuce yafito tareda rufe mata kofa yakoma dakin Hadiza hawaye Ummi taji sun gangaro mata daga ido kawai jitayi tana bama kanta tausayi most maganganun Hadiza tajisu dan maganan Hadiza ihu ne, maganganunshi ne batajiba but duk taji abinda Hadiza tafadi da cewa yasaketa datayi zata chanza shiyafi komi tada mata hankali saitaji takara raina kanta tana tunanin kodai Auren nan kuskurene, ita Allah yasani ba kwacema Hadiza miji tayiba babu wani mugunta aranta but tasan harga Allah dan bazata iyama Allah karyaba tanason Nura tana mutuwan sonshi, batajin zata iya rayuwa ba yasaketa ina! Tanason mijinta fa kome zatayi zatayi dan yazauna da ita karya rabu da ita, tuna yanda har kaman ya sadu ma da Hadizan dan taji Hadiza nacewa kada ka sake yasadu da ita da gabanka daka sadu da yar aikina, hawaye ne yazubo mata tasan ita yar kauyene bata waye kaman Hadiza ba sannan batai karatu ba but tanada hankali, sannan ta girma, ashirin da uku tana neman da hudu ba wasa bane, tasan menene miji sannan tasan banbancin miji mara kirki damai kirki, dan ta taba Auren mara kirki mugu yanzu yanda Allah yabata miji mai kirkin nan, wlh zatai kome dazatayi ta siye zuciyanshi takuma kara siye danginshi ta samanma kanta lafiyayyan wuri axuciyanshi, koda basuyi wani soyayya kafin aure ba yau alkawari takeyi zata samama kanta waje, bazata tabama Hadiza mugun abuba kawai dai bazata bari wani mahaluki aduniyan nan kap yarabata da Alhajinta bane, dan bata tabajin tanason abu kaman yanda takejin son Alhaji ba, yanda Allah yabata miji nagarin nan dare daya batare datai wani abuba bazata taba bari ya subuce mata ba tashigo rayuwan Alhaji tashigo kenan har abada Wallahi kuwa!.
    Tai maganan tana goge idanunta tasake juyi agado takasa bacci, sati biyun nan datayi tana kwana ajikinshi saitaji yau baccin ya gagareta, tashi tayi tafada bayi tafito daure da alwala tahau kan dadduma tayi salla tafara addu’a kan soyayyan ta da aurenta da Nura.

    Auuuucchhh I’m too emotional naso nacigaba but let’s take a moment of silence for our lioness Hadiza da Nura yay shattering ego nata today😎
    Poor thing couldn’t hold back those tears 😭 ashe ta iya kuka😂

    Auuu now I feel bad for HADIZA wlh, kishiya fa batada dadi but kuna ganin misali da Nura zai saki Ummi zata chanza????

    Wai HADIZA ce ke kuka haka our strong fire for fire, feminist woman😂😂

    Ummi dai tace taga miji, kuma tasamu gidan miji, zama daram injita mutuwa kadaice zata fitar da ita daga gidan mijinta Nura😂

    Allah karabamu da kishiyoyi irin Ummi mayun maza😂😂😂

    Anyway my people don’t forget to join MATAN AURE CLASS dina with just 1k today and tomorrow 💃
    [9/29, 3:52 PM] AMINA KABIR CAPS: 💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

     

    ✍🏻M SHAKUR

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 13

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 13

    EPISODE 1️⃣3️⃣
    My people wai kunji labarin BUKKISH FABRICS N MORE??
    Ku saurara kunji bantaba ganin masu harkan Atampas, laces dakuma lafiyayyun gangariyan ready to wear kaya ba dake badawa akan sari kwashakwasha kaman BUKKISH FABRICS N MORE ba, both
    wholesales n retails sunayi, sunefa akama taken PAY LESS STAY IN FASHION, wato ki biya kudi kadan amman ki saka kayan yayi adama dake, ku tura musu message now ku kwashi kaya with little kudi, danna link din nan kimusu magana👇🏼
    wa.me/+2349034368170
    Zaku iya duba shagonsu a TikTok- Bukkish fabrics n more

    13
    Wuraren 5 Nura yatashi daga bacci, Hadiza dake gefenshi yakalla har lokacin bacci take, sauka daga kangadon yayi yawuce bayi, wanka yafito ya shirya cikin wani jallabiya yana zuba kamshi yazo gaban gadon yadago Hadiza like a baby softly yace “jekiyi wanka kizo kiyi salla My Didi” bude idanunta tarr Hadiza tayi takalleshi yamata wani irin kyau yau saita ganshi yafi koda yaushe kyau dasauri takai hannunta tadaura kan fuskanshi tana kallonshi everything is coming back to her daya faru da ita jiya, cikin murya mai raunin gaske tace “Nuri mafarki nayi ko? Ai baka auri Ummi yar aiki na ba ko”? Dan murmushi kadan Nura yayi yakai hannunshi yacire hannunta dagakan fuskanshi yace “tashi kije kiyi wanka kiyi salla Hadiza” yana maganan yawuce yabude kofa yafito dakin Ummi yabude yashiga bata kan gadon harta gyara gadon, yabi dakin da kallo komi a gyare tsaf jin karan ruwa abayi yasa yaje gaban bayin ya tsaya tareda knocking cikin cool voice yace “wankan me kikeyi? Mafarkina kikayi?” Ummi nacikin bayin akunyace tace “wanka kawai nakeyi, ina kwana Mijina dafatan kayi bacci mai dadi kuma katashi lafiya?” Dan ijiyan zuciya Nura yasauke ahankali, he loves how Ummi always greet him, gaisuwa takemai not common gaisuwa but gaisuwa mai dauke da details, baki yabude zaiyi magana saikuma yace “ba’a magana abayi, maza kifito kiyi salla natafi masallaci” “uhm Uhm” tafadi amatsayin amsa hakan yasa yayi murmushi yace “naughty gurl” wucewa yayi yasauka kasa, yau monday he wants to see Hadiza ta chanza, he wants to be miji mai adalci, he just pray and hopes Hadiza will cooperate which he’s highly doubting it, dan yau girkin ta yakamata ita zatai girkin breakfast dasauransu, ijiyan zuciya kawai yasauke yatafi masallaci he’s just hoping zai dawo yaga tayi dama ga gidan na bukatan gyara.

    Bayan Ummi tayi salla wani lafiyayen super tadauko tasaka cikin atampopin daya dinka mata dogon rigane fitted tazauna gaban madubi ta shafa hoda tasa kwalli tashafa wani pink janbaki sannan tayi dauri bayan tasaka dan kunne, shiru tayi tanason tafita taje ta daurama yaran nan girki zasuje school but tana shakkan Hadiza deep down kuma tasan idan tabari babu mai musu at the same time tana tsoron kada ace tayi shishigi bayan yau girkin Hadiza ne amman kuma tanaso tanunama Hadiza bawai dantaci mutuncin ta ta auri Nura ba ita kawai tanason Nura ne, kusan 3min tayi ahaka sanan tabude kofa kaman munafuka tafito ta maida kofan tarufe batare data bari yayi karaba tawuce tasauka kasa falo tafara gyarawa agurguje da dinning ta tattara duka kwanukan cokalan tawuce dasu kitchen tashiga hada abincin gida tanama Hajiya girki tana gyara kitchen din duka at the same time.
    6 Nura yashigo gidan yau bai wani zauna a masallaci ba dan baiso Hajiya tafito daga daki ta nemi Ummi da bala’i, falon daya gani harya chanza kama yasa yayi shiru dan kawai ranshi yagayamai Ummi ne barin dayaji motsi a kitchen kitchen din yawuce a kofan ya tsaya yana kallonta tuwo take tukawa, ahankali yashiga cikin kitchen din dasauri Ummi tajuyo jin motsi ganin Nura ne yasa tayi murmushi tace “Sabahal khayri Baban Amanu” takowa yayi yazo inda take sai kawai ya rungumeta ta baya yana shakan kamshin datake yayi shiru itama saitai shiru tanajin saukan ijiyan zuciyanshi, bai damu dadan zufan datakeba ya goga gefen fuskanshi anata kaman mai whispering yace “maisa kika shiga kitchen yau ba girkin ki bane”? Dan shiru tayi kaman bazata ce komiba cikeda hikima tace “Anty tana zuwa aiki ni bana aiki, shine nace bari nafito nakama mata ta hanyar yin abincin kari saikuma inaso nama Hajiya girki dazataci kafin ta tafi asibiti, tunda nadawo nizan dinga mata abinci, ita nakema tuwon alkaman nan” shiru Nura yayi yana rungume da ita abayanta, akwai wani kalan hikima da Ummi kedashi da wlh ko educated mata dasaukai karatu daidaikune kedashi, yarinyar is good with words, Ummi is smart, tanada broad hikima kan zaman aure wanda yasan aikin Gwaggon tane, yanda ta tashi da safen nan tanama mahaifiyarshi girki abin warm his heart, dago kanshi yayi ya manna mata peck akumatu yace “godiya nake Hajiya Ummi” dasauri tace “nika dainamin godiya dan nama Mamana abinci” murmushi yasakeyi saikuma kawai yasaketa tareda juyoda ita yayi hugging nata so tight yace “thank you Hajiya Ummimy na” akunyace tazare jikinta daga nashi tace “tuwo zai kone” murmushi yamata sabida baiso tai wani abun yace “bari naje natada yaranki namusu wanka na shiryasu” dasauri Ummi tace “kabarshi zan musu zansa sanwan miyane nazo sama” girgizamata kai yayi yace “aikin zai miki yawa just do the cooking zan musu wankan” yawuce kofa saikuma yajuyo yace “kimini shayi” gyadamai kai tayi tace “angama maigidana” murmushi yayi yabita da kallo kaman yazo yamata wani abu saikuma dai yadaure yafita dan murmushi Ummi tayi dudda tanada damuwa tana cikin shakku da fargaban karya saketa bazata taba nunamai ba tama kanta alkawarkn nan.

    Nura na zuwa sama baimaje dakin Hadiza ba dakin yaran yaje direct Aman yafara tarawa yakaishi bayi yasamai brush sannan yafito yaje dakin Amal yadauketa yakaita bayi yamata brush da wanka yafito da ita da towel yakoma dakin Aman yamai wanka shima wlh aikin yara is not easy yafito dashi da towel ya kwashi kayanshi sukazo dakin Amal anan yashiga shiryasu sunamai hira yana wasa dasu.
    My people wai kunji labarin BUKKISH FABRICS N MORE??
    Ku saurara kunji bantaba ganin masu harkan Atampas, laces dakuma lafiyayyun gangariyan ready to wear kaya ba dake badawa akan sari kwashakwasha kaman BUKKISH FABRICS N MORE ba, both
    wholesales n retails sunayi, sunefa akama taken PAY LESS STAY IN FASHION, wato ki biya kudi kadan amman ki saka kayan yayi adama dake, ku tura musu message now ku kwashi kaya with little kudi, danna link din nan kimusu magana👇🏼
    wa.me/+2349034368170
    Zaku iya duba shagonsu a TikTok- Bukkish fabrics n more

    Nan da nan Ummi tagama abincin Hajiya tahada breakfast tasoya chips ta sossoya eggs da sausage ta hadama su Amal abinci a lunch bag tadauko tafito zata ijiye a dinning tahada ido da Hadiza dake tsaye a dinning din tana sanye da riga da wani palazzo trouser mai shegen kyau na material pink tayi folding hannunta a kirji tana kallon Ummi da jajayen idanunta dasuka kumbura sukai jazur kaman mai ciwon ido abinku da faran fata, chak Ummi ta tsaya anan gaban kitchen din takasa karasowa dinning din ayanda zuciya ke diban Hadiza jitake kaman tazo ta shake Ummi tamutu gabaki daya, daga kafanta tayi tafara tafiya ahankali akuma zuciye tace “how dare you Ummi kika aure mini miji? Ni Hadiza kika aurama miji? Kin manta lokacin dana taimaka miki kina neman aiki ido rufe wayanda kikema aiki ada sunyi japa sun koma Canada anata gantali dake a Abuja ana nema miki gidan aiki baki samuba, na taimaki rayuwanki nabaki aiki nakuma biyaki da kyau, yan aiki da ake biya duba ashirin, dubu shabiya but ni nace zani dinga biyan ki dubu hamsin sabida duka gidana zaki kula dashi da yarana sabida bani zama ina fita aiki, sakkayan dazaki mini kenan ki aure mini miji, mijina Ummi? Nura na?” Ihu Hadiza tayi tana tafiya tace “ki daga fuska ki kalli kwayar idanuna bakar munafuka, algunguma, makira bakar mayya, butulu, shedaniya watsassiya, sai bayan kin aureshi zakizo ki kasa kallona kina sunnar da kanki kasa kaman baiwar Allah, dagakai ki kalleni Ummi, nace ki kalleni!” Hadiza tai maganan tana ihu daidai tana kaiwa gaban Ummi ta finciko gaban riganta gamgam tawani kalan jijjiga Ummi ta mugun makureta tana kallon fuskanta tace “wulakantacciyan yarinyar irinki harta isa ta aure mini miji, ni Ummi kina yar aiki na, sabida ina fita na barmiki gida kikai using opportunity nan kika auri miji na eh”? Hadiza tai maganan tana buga Ummi abango saida Ummi tasaki lunchbag din kasa tai kara Hadiza ta makure mata wuya tace “wlh, wlh, yau saidai afutar da gawanki ki daga gidan nan, ke! Dakikiyar yarinyar irinki tayi kadan tace inyi kishi da ita, bazan taba iya raba Nuri dakowa ba balle ke jinjiran yar iska kinajina? I will kill duk wacce tace zata auri Nuri na, dagani sai shi har lahira” “Hadiza!” Nura daya sauko tareda yaran suna surutu ya hangosu da gudu gudu ya sauko daga bene yazo wajen da sauri ya bambare hannun Hadiza daga wuyan Ummi yace “are u mad kasheta zakiyi”? Tari Ummi tahauyi sosai tana nishi idanunta sunyi ja, cikeda fada Hadiza tasake yowa kan Ummi tace “Nuri ba ruwanka awannan fadan is between me and this this munafukar makiran yarinyar” dasauri Nura yatura Ummi bayanshi daidai su Aman suna zuwa wajen da gudu zasuyi wajen Ummi suna “Anty Ummi sorry” rikesu Hadiza tayi dasauri tana tafarfasa tace “ku zonan ina zaku?” Dasauri Aman yace “wurin Anty Ummi, u hurt her Mom” cikin ihu Hadiza kaman zata make Aman tace “waye Ummi? Me kuka hada da ita? Who is that girl to you? Dagayau baku ba ita Aman kaida sister ka, Ummi is a bad evil person, babu wanda yataba cutata arayuwan nan kaman ita, bantaba nadaman abu arayuwana kaman nai nadaman ranan dana dauketa aiki ba, kar wanda yasake kiran sunanta cikinku agidan nan, Ummi is the worst evi…….” “Hadiza!” Nura yasake kiranta ranshi abace dasauri Hadiza takalli Nura tace “what!? Nura I said what kake kirana? Don’t tell me ka yarda cewa yar aikin nan son yarana take? Okay bakaso nagayama yarana she’s evil, Lemme tell you something today Yarinyar nan bata taba son yarana ba, she just use them tayi winning heart naka da nawa damuka yarda ta zauna gidanmu, bata taba son yarana ba, she use them taja ra’ayinka kasota, tunda ta kyallara ido taga muna biyanta 50k instead of 20-15k da ake biyanta a inda tabasa aiki ta kudurci aniyan saita aureka, saita zama matarka, saisa taja yaran jikinta sabida tasan you love yarannan morethan ur life sune the way to your heart, your weakest point Nura, open your eyes and see Ummi played you and me, Nuri Mezakayi da this village evil girl yar aiki fa eh Allah kadai yasan mazan mutane nawa taci, I will post her pictures on social media to makesure babu wanda yakara daukanta aiki a abujan nan tunda she’s a witch, ka barni naci bura’uban yarinyar nan Nuri tasan cewa Allah dayane” Hadiza takaima Ummi nushi Nuri yatare hannu ta hanyar rike hannunta gam cikin kakkausan murya yace “karkiyi kuskuren tabamin mata Hadiza stop all this thing!” Nura yayi ihu saikuma cikin turenci yace “I’ve given this respect leave this girl alone before I disrespect you in front of her” tafi Hadiza tayi tace “akwai disrespect daya wuce na kariga ka aurota ka kwanta da yar aikina taga kalan buranka dani uwar dakinta keci akwai Eh Nura talk!” Hadiza tai ihuu dayasa Nura ya runtse idanu yabude su ahankali yakalli Aman da Amal daduk ke kallon Maman nasu sunyi tsuru tsuru, dan juyowa kadan Nura yayi yakalli Ummi dake labe abayanshi yace “tafi dakinki” gyadamai kai tayi tawuce Hadiza zatayi kanta Nura yariketa gam, Hadiza tabita da kallo tana duramata ashar tace “munafuka, jibeta kaman bushashen kifin dayay kwantar a kasuwa oporoko, banda ma namiji kanshi kaman kan jarirai ne mezakayi da yarinyar nan mai kama da fiffiken kunkurun dayay shekara dari da uku aduniya eh, makira zuciyanta yafi fatar jikinta baki, tanaji da lebe kaman wacce ke aiki agidan giy……” “Hadiza!” Nura yayi maganan yana fizgota su Aman suka fashe da kuka Nura yakalli yaran saikuma yasaketa yace “look at yaranki ko breakfast basuyi ba zasuje school kina haukan nan bakisan zaiyi affecting mental health da cognitive development nasu ba” cikin fushi tace “eh bazasuyi breakfast dinba ka gayama yarinyar chan bata ba yarana, kada ta kara dafa musu abinci kota musu wani abu, wlh ko hannunta nagani akan jikin yarana kome namata ita taja and kada ka ta kara shigan mini kitchen” Nura yana wani kallonta yace “kitchen banaki bane, duk wani abu naki na kitchen din nabaki dama ki kwashe ki ciresu daga kitchen din zan sayo wasu nasa cus Ummi will enter this kitchen and cook for me” Nura yakallesu yace “zo kuyi breakfast” rike hannun yaran tayi tace “Nura bari kaji yesterday you took advantage of my fragile state kayi yanda kaga dama dani not anymore, billahillazi Nura zan nuna maka cewa yimini kishiya was the worst mistake daka tabayi arayuwan ka, bakana fadin bakada kwanciyan hankali ba yanzu kafara ganin asalin rashin kwanciyan hankali, muzuba nidakai I will deal with you and deal with that thing daka kawomin gidan nan as matan ka, bakasan ba’a wasa da fire ba because u will get burn, Nura I will treat you f*ck up wallahi kuwa” sosai Nura ke kallon Hadiza but sabida yaran saiyayi shiru yatako har gabanta yaduka yakama Aman da Amal dake kuka looking terrified ya karbe su daga hannunta yace “bani yarana” yajuya zaiyi dinning dasu kafin yaje Hadiza tarigashi zuwa dinning din duka abincin da Ummi takai dinning dan breakfast Hadiza ta kabar, dasauri Nura yaja Aman baya dan yadauki Amal gudun karya kone da ruwan zafi yana kallon Hadiza, ahaukace ta duka ta kwashi lunchbox na yaran da Ummi ta watsar akasa dataji shaka dazu ta bude tana ciro komi tana zZzagewa akasa tace “baza’a aci abincin yar aikin ba, yarana bazasu karacin abincinta ba, nace baza’a ciba, angama cin abinci again, Nura that peace dakace bakasamu dani ba ajikin yar aikina zaka samu wlh, wlh, wlh bazaka sameshi ba, Nura u will never know peace now dakamin kishiya I swear by Allah” sosai Nura ke kallon Hadiza kaman ba itane tagama kuka jiya kaman wacce ke shirin mutuwa ba, baice mata komiba yajuya yakoma falo yazauna yaciro wayanshi yakira school din yaran yace abasu breakfsat da lunch yau daidai motan school din zuwa, lallashin yaran yayi yadauko juice a fridge yabasu sannan yafita yasasu a school bus sannan yadawo cikin gida Hadiza na tsaye a tsakar falon tarike waist nata tan kallon Nuran.

    Baiko kalleta ba yawuce zaiyi stairs tabishi da sauri tana ihu tana surfafa masifa tace “bakaji kunya na ba sabida kaine babban munafukan mazan duniya, Nura the president of MMA! Mugayen Maza Association, zaka kama ka auremini yar aikin dana samo nakawo gidan nan, kabita har kauyensu ka aureta kaje kayi honeymoon da ita batare daka dauki wayana ba for that 2weeks, shine kanada audacity kazo da daddare ka lallabani kana samin jikinka ajikina jikinka daya hadu dana yar aikina eh Nura? I looked up to you kullum as a role model cus Nadade banga namiji mai hankalin kaba, but I was wrong gaskiyan bature ne dayace a fool at 40 is a fool forever dan tell me why will a sensible, educated wise old man zai kama ya aurowa matarshi yar aikinta? Nura yar aikina ka auromini sabida daidaicewa da wawatsula” uppan Nura baice mataba wardobe nata yabude yadauko kayanshi yawuce yafito daga dakin duk tana binshi yaje dakin Aman ya ijiye komi kan gado yafada bayin yayo wanka yafito yadauki cream din Aman yashafa still surfafa bala’i Hadiza take tsaf yagama yafito yasauka kitchen yaje yadauki babban kulan dake kan Island Hadiza takawo hannunta anan ne Nura yace “idan kikai kuskuren ko gigin taba abincin mahaifiyata Hadiza I will show inda haukanki ya tsaya anan nawa yafara” yana maganan yawuce ta yafita tabiyoshi tace “ai dama nasan kai mahaukaci ne dan mahaukaci kadai zai auroma matarshi yar aiki” fita yayi anan gaban kofa ta tsaya tana kallonshi dan bataso tafita tana fada, estate dinsu da ake ganinta as don aga tana fada, abincin ya ijiye a bayan mota ya kulle motan yadawo cikin gida Hadiza tasake binshi kitchen din yashiga ragowan friend Irish daya gani a pkate da egg yadauka, spoon yadauka yafito Hadiza nabiye dashi tace “ina zaka da abincin nan eh, Nuri ina zaka da abincin nan”? Dakin Ummi yabude yashiga biyoshi Hadiza tayi ciki ga mamakinta Nura just pushed her outside yamaida kofan yarufe yasa key tahau buga kofan da gudu tana ihu. “Nura ni kai pushing outside like that eh? Wlh wlh sainayi maganinka dakai da karuwan nan daka ijiye adaki” kallon Ummi yayi dayagani kwance kan gado kaman marainiya idanunta sunyi ja amman ba kuka takeba zama kusada ita yayi kan gadon yana ijiye abincin agefe murmushi Ummi tamai tace “shine saika kawomin abinci maisa kakemin aik…..” hannu yadaura akan bakinshi alamun tamai shiru hakan yasa tai shiru yakai hannunshi yadagata wajen window dakin yayi da ita ya yaye window yadaga wuyanta yana dubawa yana tattabawa ganin yadanyi ja yace “dazafi” dasauri ta girgizamai kai tace “ba zafi” yana kallon kwayan idanunta ahankali yace “mesa baki gudu ba dakikaga zata miki wani abu ko kiyi ihu ki kira sunana what it tamiki wani illan?” Murmushi tamai tacire hannunshi daga wuyanta tace “Anty bazata min wani illa ba ba muguwa bace, kawai fushi take sabida mun mata laifi” dan shiru Nura yayi yana kallonta saikuma ahankali yace “Ummi aure ba laifi bane like I said ranan nan ko nan gaba naji ina bukatan wata matan zan iya nakara aure, mata hudu zan iya aura” Ummi na kallonshi tace “Anty na sonka sosai, kuma soyayyan yasa take fushi haka” yana kallon kwayan idanunta yace “kefa?” Murmushi tamai tace “nima ina sonka sosan bala’i, tafashashen so ma nake maka my Noor bai huce ba” yana kallon bakinta yace “Allah yar matata”? Dan dariya tamai tace “da gaske, ba Hajiya zakakai asibiti ba lokacin na tafiya kazo kaje” dan ijiyan zuciya yasauke yace “banso na bar gidan nan ahaka” dasauri Ummi tace “babu abinda zai faru kaje ka kai Hajiya asibiti abincinta na kitchen a flask kadauka” ahankali yana kallonta yace “nadauka” ganin ya tsaya yana kallonta yasa tace “menene?” Yana kallon kwayan idanunta yace “Aman da Amal yaranki ne kada ki rabu dasu sabida Maman su kinji” murmushi tamai tace “tom Baban Aman da Amal” rungumeta yayi ahankali yace “kiyakuri da abubuwan da Hadiza tafada miki kinji, kada ki riketa azuciyanki, kiyakuri Hajiya Ummi” dudda taji wani iri amman tadaure tafita daga jikinshi dasauri tace “komi yawuce katafi” Gyadamata kai yayi yace “biyoni ki rufe kofan da key” biyoshi tayi yace “kiyi breakfast zan dawo yanzun nan” gyadamai kai tayi yabude kofa yafice tasa key dasauri ganin Hadizan na tsaye awajen yawuce Hadiza tasakebin Nuri tana masifa tace “tell this girl ko dakin yarana takara shiga wlh saina watsar da ita, karta kara taba wani abu that belongs to me in this house wucewa Nuri yayi yawuce yashiga motanshi yabar gidan Hadiza ta dawo sama tashiga surfafa zagi na uwa da uba ma Ummi, Ummi tayi shiru.

    Tashi Hadiza tayi ganin taki kulata tazo gaban dakin ta bubbuga tace “kifito mana idan ke diyar halas ce yadade da tsufa a inda yatafi yanzu, dagani saike agidan, kifito muyi magana woman to woman mace to mace, cus inada wasu abubuwa dazan fada miki kifito Ummi kibude kofan nan kifito” Hadiza tai dariyan keta tana tafiya tace “dan kauye dan kauye ne, ni wlh at this point ma tausayi kike bani Ummi, bari nafada miki wani sirri dabaki sani ba for free” tasake shiru tace “kinga Uwargidan miji itace kokon rayuwanshi, Ummi bar ganin kin zauna agidan nan kinga nida mijina munada yan matsaloli sai kikai yan dabarun ki na gidahuman kauye kikaja ra’ayinshi ya aureki to tsaya kiji wani abu dabaki sani ba game da mijina Nura” Hadiza takara murmushi tace “Nura kwata kwata dakikan mata dabasuyi boko ba basa burgeshi kije ki tambaya kiji, Baban Nura professor ne a BUK abinda yadawo dasu kano kenan daga zamfara, Hajiya wannan dakike gani tsohuwan secondary school English teacher ce, kannen Nura kap dukansu graduate ne dasuka gama jami’a har Meena Kwanan nan tagama bautan kasama, kinganni nan Nura bai yarda ya aureni ba saida nagama jami’a gabaki daya muna dawowa garin nan yasa nacigaba da karatun wuce jami’a wato masters sabida dan boko ne shi, yanason yaga matarshi yar gayu yar boko tanuna ma business partners nashi, kinsan mesa nake gayamiki maganganun nan”? Hadiza tasake dariya tace “sabida ke dakikiyace jaka kuma, Nuran dakike gani kin aura yau Nuran daya sami yar karaman matsala da Hadizan shice, kije kano ki tambaya abaki labarin kalan soyayyan damukayi, ban bashi jikina ba damuwa da sha’awa kinsan mutum shiru shiru mara magana yasa yaga kaman yana sonki wlh Ummi kindaiji na rantse miki Nura baya sonki sabida baki cikin kalan ko siffofin matan dayakeso” wani abu Ummi taji ya tsayamata awuya chak yaki wucewa takasa hadiyewa, Hadiza tace “bansan ko kinji magananmu jiyaba, jiya nace yasakeki zan chanza Ummi kinsan meyace mini”? Hadiza tai maganan cikeda tsantsan tunzura mutum saikuma ta kyalkyace da dariya tana tafi tace “wohoho ta yanda zaki gane kin tafka shirme Ummi kin auri mijina kin dauka kin sami gidan mijin cemin yayi nafara chanzawa tukunna yagani, idan na chanza nakoma Hadizata nada zai sakeki ki tafi mucigaba da rayuwanmu mukadai hankali kwance” dasauri Ummi ta tashi daga gadon zuciyanta na rawa tanajin wani iri, Hadiza tace “haka yadinga lallabani har saida ya samu nabashi hakkinshi that means keba komi bace awajenshi ba sati biyu dakukai kuna amarci kaman yanacin kashi haka yaji saida ya kwanta dani jiya yajishi daidai, yajishi damdam yajishi yakoshi, kuma kada ki manta rashin jituwan damuka samu dani da dashi yasa yaje yama nemeki” hawaye Ummi taji sun sauko daga idanunta, Hadiza tace “Ummi ki rubuta ki ijiye kwanan nan Nura zai sake ki kibar gidan nan dan bazai taba hada jini da jakan kauye ba da turenci nan nan bata iyaba wlh saiya sake k…….” Bude kofan Ummi tayi dasauri tafito idanunta sunyi jazur tahada idanu da Hadiza for the first time tunda tadawo gidan tace “Hadiza kinyi kadan ki rabani da Nura” sosai Hadiza ke kallonta ganin idanunta sunyi ja maganan ta shigeta kenan yasa ta taka zuwa gaban Ummi Ummi ta tsaya chak tana kallonta ba gudu ba jada baya, Hadiza namata wani kalan kallo tace “nabaki daganan zuwa sati biyu saikinbar gidan nan dan baki da waje awajen mijina” Ummi na kallonta tace “Hadiza ban auri Nura dan na kuntata miki ba, shiya nemeni da aure na aureshi kuma magana daya zuwa biyu zan fadamiki, nifa nayi miji kuma naga wajen zama, zama kuma daram! Wallahi ko ana hamaza hamata bazan rabu da mijina ba, barima kiji mutuwa kadaice zata iya fitar dani daga rayuwan Nura!” Hannu Hadiza ta daga zata kaima Ummi mari Ummi tarike hannun gam idanunta sunyi masifan ja kirjinta na tafarfasa itama jin ance Nura zai saketa tace “Hadiza kul!” Ummi tazare mata idanu kaman yar daba tace “dazu nariga nabarki kinmin hukunci sabida nasan ban kyautamiki ba na auri mijinki daya nemeni amman yanzu kikai kuskuren dukana Hadiza kin tuna kalan dukan da Meena tamiki”? Ummi tayi maganan tana kallon kwayan idanun Hadiza kaman yanda Hadiza ke kallonta mamaki yagama kasheta, Ummi tace “wlh saina miki dukan dayafi wanda Meena tamiki domin shiru shiru ba hauka bane, dan hakin daka raina shine yafi tsole ido, kul Hadiza! Wallahi kul! Duk abinda zakiyi kiyi but Ummi tariga tayi miji, kuma taga gidan miji, danhaka zama daram, dam, damm ehe! Sai kija please ki rungumi sorry dan haka askus me” ta yarda hannun Hadiza a air tawuce takoma dakinta tarufo kofa tasa key Hadiza tasaki baki mamaki ya cinyeta har zuwa bone marrow, she was like wattt! Ita village girl dinnan tama rashin kunya haka? Askus, askus? Did she just said excuse me as askus me? Sai kawai Hadiza tahau dariyan kuka, she’s laughing so hard and crying so hard as well, ita Nura zai auroma wannan jahilan askus me yar kauyen yarinyan???? Wow lugubrious!!!!!

     

    Mata Mata mata sau nawa nakira mu???
    Please we should all learn to stop abusing opportunity sabida idan wasu suka sami that opportunity there’s nothing u can do in this world dazaisa su saki that golden opportunity daya shigo musu.

    That is what happened between Hadiza and Ummi, Allah yama Hadiza kyautan close to perfect husband but she abuse everything and toss him outside like a coin, Ummi grabbed that coin tace atafau koda za’a guntule hannunta ne she won’t let go off wannan coin din, wazakuyi blaming wacce tai tossing coin din ko wacce grab the coin???

    Sainaji daga gareku and always remember shi opportunity sau daya yake zuwa miki.
    Allah ya kiyaye and see you’ll Saturday Fanmily and Askus me❤️

    WEEKEND PROMO💃💃

    I have special announcement masu son shiga class na MATAN AURE you can all pay 1k now kafin Monday yakoma 2k, registration is still ongoing kafin murufe.
    🔊🔊🔊🔊🎊🎊🎊🎊🎊

    Don’t miss MATAN AURE dina class for anything, I will give you all!!
    Sirri zan baku da dama
    Zan koya muku how to love mijinki in your own way kaman yanda Ummi keyi.
    Shagwaba, iya magana 🥰
    Uwa uba iya kwanciya❤️, yanda ake siyan zuciyan miji, how to steal heart na Inlaws naki and so much more.😍
    Idan kina tunanin asiri ko kayan mata ke siyan zuciyan miji come to my group na nuna miki gaskiya.
    HAUSA CLASS NE BA TURENCI BA

    REGISTRATION IS 1k NOW

    6353995766 M Shakur world Moniepoint
    Send ur evidence of payment ta PC zanyi adding naki a group.
    click on this link and chat me up directly +2347012181461💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

     

    ✍🏻M SHAKUR

     

  • Matar Makaho 100

    Matar Makaho 100

    😥END😥

    Page1⃣0⃣0⃣
    Wani irin magana ne haka nabila?toh nidai baza’ayi wannan haukar dani ba, kinji na fad’a miki taya yaro da matarsa koh sanin dadin aure basuyi ba, gani tsohowar banza nazo nasa bakina a sha’aninsu salon nayi bakin jini a wajen baiwar Allah, yarinya na ganin girmana najawa kaina raini wallahi da sakel ki barni na mutu da mutunci na.

    Kuka nabila ta sake cikin maganar shagwaba tace, ni shikenan babu inda zanje naji dadi, dedena naje mata da zancen zagina tayi kema shine xaki mini haka?

    Jin abinda tace yasa mahmah kashe wayar ta aje ta fita a d’akin.

    Ammar yazo sun gaisa da khadija kuma ba laifi ta sake jiki dashi kad’an, kuma yana samun hankalinta, Amma ba karamin kunyar muhammad yake jiba duk lokacin da zaizo sai ya tambaye khadija a waya yayan ta na nan intace eh tofa ba zuwan zaiyi ba.

    Bayan sati uku Ayau ne dubun Al’umma suka shaida d’aurin auren sarki yusuf mutallaf tare da Amaryar sa zainab Rabi’u ubangari sai kuma Abdulsalam Abdul’Aziz shugaba da Amaryar sa Amina Ahmad Adara, d’auren auren da ya samu halaktan manyan mutane daga nijar har nigeri’a tabbas yan uwan zainab sun nuna mata gata a bikinta.

    Bayan d’auren Auren ne mahafin Ammar ke wa yusuf zancen khadija, wanda yace sai dai aje nijar ayi batun Auren tunda canne mahaifarsu kar yan uwa suga ana musu wariya.

    Su sumayya da muhammad harda khadija ayau sukabi gida gidan yan uwa domen musu sallama, washe gari taje abuja tama mahaifiyarta sallama zasu tafi nijar wajen dangin mijinta, kuma daga wajen zasu wuce America.

    Ayau ne sumayyya dasu khadija da mahmah tare da tawagar sarki da Amaryar sa,suka nufi nijar, sun samu kyakkyawar tarba, saidai fa sumayya ta fuskanci sauyi a wajen nabila wanda hakan yasata shawa nabila mur, ganin duk lokacin da taga Al’ameeen zatana wani kwarkwasa shikam baima nuna yasan tanayi ba, ga lawiza da kishi ke cinta, Amma dai ta kwantar da hankalinta ganin yanzun tana samun kulawa a wajen mijinta fiye da da.

    Nabila tayita nacewa mahmah akan zancen ta da muhammad, wanda abin yasa mahmah tarar yusuf da zancen, kai tsaye yace mata, mahmah banki bin umurnin kiba amma mama inkin duba duk abubuwan da suka faru Nine na fata ballo ruwan, da ace nayi biyayya ga mahaifina da duk abinnan bai faruwa ba, duk da bawa baya wuce kaddararsa mama bazan iyyama muhammad wannan zancen ba,A tausayawa yaron nan yasha wahala A rayuwar sa yanzun lokacine daya kamata Ya huta, duba da irin halakcin da yarinyar nan ta masa bata cancanci haka ba, in shine ya taso da zancen aure bazan hanasa ba, Amma mama bazan iyya tikasta masa ba kiyi hakuri bawai don yana d’ana ba, zaki iyya tuntubarsa duk Abinda ya yanke shikenan.

    Jikin mahmah yayi sanyi kuma taji shawaran da d’anta ya bata don/a dalilin Auren dole yusuf yasha wahala, hakan yasa bata ma tinkare muhammad da zancen ba.

    Gidado da badaru dayake ba boko sukayi ba, kuma yanzun sun wuce shiga makaranta, yasa sarki bada umurnin a sasu a islamiyya, da kuma yaki da jahilci koh karatun hausane da turanci su iyya,ya bude musu manyan shaguna a kasuwa,in sunje boko sun dawo sai kuma su tafi shago, asabar da lahadi suje islamiyya.

    A kasuwa gidado ya hadu da indo kanwarsa na bara, cikin wani irin yanayi ya tisata har inda suke da zama, aiko suna zuwa saida yayi hawaye ganin wani kazamin waje kusa da bola innarsa ke rayuwa gata a kwance ba lafiya ga yarsa cikin datti ,sai abinda indo tayi bara ta sama musu, d’aukar su yayi wanda a lokacin inna koh sanin wake kanta batayi ba.

    Sarki a washe garin ya tura su saudiya da inna,saboda ciwonta ya kazanta blood Cancer ne, yayinda indo ke zaune a gidan sarki tare da lantana karama.

    Muhammad da sumayya sun wuce America tare da yaransu suna mai kewar kasarsu da yan uwansu.

    Bayan tafiyar su akayi auren Gidado da nabila sai badaru da wata yarinya yar tsohowar unguwansu, sarkin shayi ma Yusuf ya had’asa da wata bazawara an had’asu aure.

    Jikin inna yayi sauki inda sarki yasai musu gida ita da indo da yar gidado , d’aya shashin kuma gidado ne da nabila, dataga ba sarki sai Allah ta aure sa abinta.

    Su sumayya basu dawo ba saida sukayi shekara d’aya, lokacin auren khadija da Ammar sukazo, khadija tayi weac dayake har lokacin tana Nigeria a abuja wajen hafsa, yayin da yaran sumayya suka cika shekara 1 da watanni a lokacin kowa yaga sumayya da muhammad sai sun basu sha’awa, gaskiya ne mahakurci mawadace, mai hakuri yana tare da riba, sannan duk mai biyayya ga iyaye zaiga Amfaninsa wata rana.

    Ana bikin Ammar da khadija suka koma wajen aikin Ammar a maiduguri bayan aure ya maidata makaranta, don result nata yayi kyau sosai, su sumayya sun koma America bayan biki.

    ***************
    Bayan wasu shekaru………
    Wani matashin magidanci ne tsaye a wani hadedden compound mai d’auke da shuke shuke mai ban sha’awa, sanye yake da kakin sojoji a jikinsa wandone da riga, kansa ba hula sai gashinsa dake kwance baki kirim yana sheki, yayi farine tas yayin da idanunsa ke d’auke da bakin glass, dukar da kansa yayi yana kallon agogon sa mai masifar tsada, dake hannunsa d’an yamutsa fuska yayi hade da dan sakin tsiririn tsaki,ganin 7:21pm Amma har yanzun gimbiyar tasa bata fitoh ba bare yaransa, jin karan bude kofar falonsu da akayi yasa sa saurin d’agowa.

    Sanye take da siket baki mai kauri yana nan kamar pencil Amma ba’a tsaga baya ba,sai takalmi mai tsini a kafarta dake d’auke da socks baki, shirt ne a jikinta white mai botur da dogon hannu, wanda tayi stokin dashi, Have sunnah ne a wuyanta baki, da agogo fari a d’aure a farin tsintsiyar hannunta, sai jakan office dake rataye a hannunta d’aya Tabar daya hannun na lilo, fuskar nan nata yayi fayau babu kwalliya alamu dai jin dadi ya samu waje, rike take da wani kyakkyawan yaro fari yana sanye da uniform na primary bazai wuce shekara 5 ba, ga wani yaron na binta a baya zaikai 7 shima yana sanye da uniform hannunsa d’auke da jaka d’aya hannun kuma lunch-box nasa.

    Da sauri ta kara hanzartawa ganin fuskar mijin nata a hade, don tasan tabbas sun sasa jira don yau dai sun makara.

    Yanzun ke kullum in zamu tafi aiki da safe sai kin sani lettin kike jin dadi, ki duba yanzun minutes 30 ina tsaye ina jiranku?

    “Don Allah kayi hakuri dear wallahi neman socks in na’ima nake wai bataga d’aya ba”

    Toh surutun ma ai ya cinye lokacin daya saura manan, yace yana kamo yaron dake hannunta ya bude seat back ya ajesa, kallon mai shekara bakwan yayi, Au kaima salim(takwaran salim marigayi, muhammad ya hana a masa inkiya yace a barsa da sunan sa)so kake na d’aga kane koh me? kana tsaye.

    Washe fararen hakoransa yayi cikin dariya ganin yau ran baban nasu a bace, yace, sorry Dady.

    Shiga gaba sumayya tayi ta aje jakanta akan cinyarta da mamaki Al’ameen yake kallonta, wai sumayya ina sauran yaran ne?

    “Au wai basu shiga bane tare fa muke futowa dasu”

    Kinsan Allah sumayya yau in kikayi tsiya sai kija mota da kanki tunda dai naga kowa nada shi, ya fad’a a hankali yanda yaran bazasu ji ba.

    “Kayi hakuri toh” kawai tace tana fita a motar daidai lokacin wasu yaran mata da zasukai shekara 10 masu tsananin kama da juna, gasu kyawawa sanye suke da uniform suna gudu da school back a hannu d’aya nabin d’ayar da gudu.

    Da sauri sumayya ta kalli wance ake binta da gudun, tazo ta makale a bayan Dadynsu,”Na’ima mekika mata”?

    Momy wallahi babu abinda na mata.

    Kallon na’ifa dake hawaye a gefenta tayi, tana tsaye batabi na’ima bayan dadyn sun ba” meta miki kika biyo ta”?

    Wallahi momy colour nata d’auka guda hudu, kum drewing zanyi dashi fa.

    Ke na’ima ina naki colour da zaki d’auka mata nata?

    Dady toh banga nawan bane bafa.

    Da sauri sumayya ta karbi maganan jin Amsar data bawa muhammad”Daman ke haka kike kome naki ba’a gani, kina ganin da safen nan harkin batar da socks naki daker na gane inda kika aje, kome naki baya lastic wannan biro in aka saima yar uwarki sai yayi 1 month tana amfani dashi, amma ke koh kwana bayayi sai kice ba pen ah ah pen ya bata, don haka oya bata colourn ta koh na saba miki”?

    Ba musu ta bude jakanta ta mikawa na’ifa abinta, sai kuma ta fashe da kuka.

    Muhammad dake tsaye ne ya dubeta, toh wai kukan na menene?

    Dady kuma fa bangama drewing ba gashi uncle yace duk wanda baida colour waje zai korasa bazai masa makin ba.

    Ina dai akan colour ne?muhammad ya tambaye ta.

    D’aga masa kai tayi alamun eh.

    Toh muje a hanya saina sai miki sabo koh?yanzun ku shiga mu wuce mun kusa makara.

    Dady nimafa bani da calculator?

    “Da sauri sumayya ta dubi yaron ta, kaji tsoron Allah khaleefa(yusuf) ba jiya naga calculator a jakan ka ba”

    Momy Abokina kullun sai uncle ya bugesa wai bayida calculator, shine na tambayesa mai yasa ba’a saya masa ba, wai Auntin sa(step mother)in dadynsa ya basa kudin saita kwace, shine na basa kyautan nawa jiya.

    “Masha Allah yaron kirki haka nakeso Allah ya muku Albarka”

    Gabaki d’ayansu suka Amsa da Ameeen .

    Jan motan muhammad yayi mai gadi ya walgale musu makeken get nasu suka fice.

    Sai da suka bi ta bookshop ya sai musu abinda suke bukata, yaran ya fara saukewa a school, kafun ya kama hanyar bank da sumayya, tun a hanya ta makala ID card nata a wuya, suna isa bank ta sabi jakanta sukayi sallama ya wuce wajen aikin sa.

    Misalin karfe 4:30 na yamma muhammad ne zaune a office yana aiki, yaji ring na wayan sa kamar bazai d’auka ba don aiki yake mai muhimmanci,d’auka yayi yana kallon mai kiran nasa da sauri yayi picking yasa a kunne,Assalamu Alaikum

    Ta d’aya bangaren Ammar ya Amsa wa’alaikumu salam, Captain muna fa Airport azo ya d’auke mu.

    Da sauri muhammad ya mike cikin mamaki yace What? kana nufin kun shigo Lagos koh note’s babu?

    Surprise muke son muku.

    Amma gaskiya ka kyauta gamunan zuwa, suna yanke wayar neman wayar sumayya yayi ya kirata

    sumayya dake zauce akan kantan customer care tana aiki taji wayanta na ringing d’agawa tayi tasa a kunne ganin sunan maikiran nata, “Hello Rabin Raina”

    Hello sweetheart kin koma gidane?

    “No Rabin Rai yanzun nake kokarin fita, musa driver na haraban bank yana jirana”

    Ok kice masa ya wuce dasu salim, ke ki jirani ina zuwa?

    “Lafiya dai naga kace mini yau sai 6 zaka dawo kana da aiki”?

    Lafiya yanzun Ammar yake sanar dani sun shigo lagos suna Airport.

    Ok saika zo tace tana yanke wayar, number musa driver ta kira ta shaida masa ya wuce kawai gida, sannan yacewa bahbah(tsohowar mai Aikinsu)ta kara wasu abubuwan cin zasuyi baki.

    Ba’a jima ba da wucewar musa saiga muhammad jakanta kawai ta d’auka ta shiga motarsa suka wuce Airport, suna isa Jakanta sumayya ta bude ta zaro Abayan ta sakawa tayi daman akwai have sunnah a jikinta dukansu suka sauka a motar waya Al’ameen ya d’aga ya kira Ammar.

    Tsaye suke suna duduba masu fitowa, daga nesa sumayya ta hango Khadija da katon cikinta a gaba tayi kyau kamar ba khadin goggo ba hutu dajin dadi sun ratsa ta, sai Ammar dake rike da hannun yaran su biyu mace da namiji,macen baka kamar babanta sabanin na mijin dayake fari, da sauri sumayya ta dagawa Khadija hannu da sauri suka karaso garesu da gudu, yaran suka rungumi muhammad suna masa oyoyo uncle da murna suka tattaru sai gida.

    Suna isa gida suka samu yaransu a tsakar gida, bahbah ta musu wanka, suna zazzaune a gaban malamin su dake can gefen flowern tsakar gidan, ai lokacin da suka gu momynsu ta sauko a mota da Ummi(khadija)gasu Amira(Aisha) da mukaddas yasasu rugawa da gudu suka nufesu da gudu, duk irin kwala musu kira da ustax keyi, ina sunyi gunsu da gudu da sauri suka rungume yaran suna murna.

    Koran su sumayya tayi hardasu Ameer suka wuce wajen karatu, tace sai ustax ya tadasu sai su shigo duka.

    Suna shiga cikin part daban sumayya ta sauke su khadija da mijinta, ta basu waje su kimtsa itama d’aki ta shiga ita da muhammad.

    Bayan mangariba zaune suke akan daining dukansu suna cin Abinci, Ga yaransu a zazzaune Suma ana ci dasu, hira ake na yaushe gamo, kallon sumayya khadija tayi.

    Aunty Gaskiya shagunan ki sun habbaka last months munje jalingo, nida maimuna mukaje shagon gaskiya nasha mamaki ganin harda saloon ga gyaran jiki duka?

    “Wallahi kuwa khadija kinsan yanzun shago hudu nake running Na make-up saloon gyaran jiki, lalle kuma gaskiya Alhamdulilh matar shagari na iyya kokarinta yarinyar ta burgeni akwai Amana”

    Gaskiya ne Aunty nima na yaba da nutsuwar Rufaida.

    “Ai shiyasa na bar mata kula da shagunan a hannunta sannan ita ke iban ma’aikata da masu training”.

    Toh Allah ya kara budi.

    “Ameen khadija waini ina labarin kamila ne”?

    wallahi aunty tadaiji sauki yanzun ba kadangarun sai daifa Abin ya taba kwakwalwanta.

    “Toh Allah ya sauwaka,Yajikan momy(safina)da rahama”

    Ameen suka amsa dukan su,bayan sun gama cin abinci Yaran suka wuce ciki yayinda su sumayya ke hira falo, sallan isha’i sukayi sukaci gaba da zaman falo ana hira.

    Da gudu Na’ifa take saukowa daga upstair hannunta d’auke da system in sumayya tana kwala mata kira ga sauran yaran na binsu baya.

    Da mamaki sumayya ta kalleta ganin vedio call suke da mutanen nijar, karban system in tayi ta aje musu akan center table dake falon, duk suna zazzauna akan kujeran da take gaisawa suke da su nabila indo Aunty zainab da nana(Aisha takwaran mamansu muhammad)sai muwaddat dake rike da sabuwar jaririya a hannunta, gaggaisawa suke tare da mata barkar haihuwa akan basu samu zuwa ba cikin khadija wata 8 amma insha Allah zasu zo auren muhibbat.

    Bawa su muhammad da Ammar system in sukayi suma suka gaisa da yusuf dake cikin iyalansa cikin farin ciki don yara biyu zainab ta haifa masa Aisha da muhin, sosai akayita hira harda mahmah data kara tsufa sosai ga lawiza duka don yau akayi sunan muwaddat duk suna hade.

    Sai kusan 9 sukayi sallama khadija da mijinta sukayi part da suke sauka in sunzo, dayake yaransu dasu Na’ima zasu kwana, had’a kansu sumayya tayi har bedroom na maza wanka ta musu dukansu tasa musu kayan bacci ta kwantar dasu, tufa masu Addu’a tayi taja musu kofa, d’akinsu na’ima ta shiga ta samu har suma sunyi wanka dasu Amira dayake duk zasu iyya ma kansu, Addu’a tasasu sukayi ta rufe musu kofa bayan ta tabbatar sun kwanta.

    D’akin ta ta shiga, wanka tayi ta sanya wani d’an iskan kayan bacci riga da wando jikinta sai kamshi yake ta wuce d’akin mijinta, tura kofar tayi da sallama ta shiga.

    Zaune yake akan gado yana aiki a laptop ganinta yasa sa kashewa ya aje akan drowern gado ya zuba mata ido ganin irin kyaun da ta masa.

    Da sauri sumayya ta karaso garesa faduwa tayi a kansa wanda yasa dole ya koma kan gadon suka kwanta, yayinda yake kasa tana samansa fuskar su ya hade waje d’aya Cikin kasa kasa da murya yake mata magana, wai Rabin Raina menene sirrin ne kullum dad’a kyau kike kamar yau Aka kawo mini ke?yana maganar yana mammatsa mata jiki.

    Murmushi sumayya tayi sai kuma ta tuno wani abu cikin dariya tace,kai menene haka?

    Dariya ya sake tuna masa da ranan su na farko, shima Amsa ya bata, yi hakuri gado nake nema zan kwanta ne?

    Itama ta sake basa Amsa, wallahi bazan kwanta dakai gado d’aya ba gadai kujera acan jeka kwanta.

    Gabaki d’ayansu dariya suka sake a tare cike da farin ciki suke romancing na juna, hannu muhammad yasa ya kamo blanket in ya lulubesu.

    *Alhamdulil!!!!!Alhamdulilah!!!!!!!! Alhamdulilh!!!!! nagode Allah daya nuna mini wannan rana cikin koshin lafiya, harna kawo karshen labarin matar makaho, duk wanda nama ba daidai ba ina neman afuwarsa*

    *MATAR MAKAHO FAN’S INA MATUKAR ALFAHARI DAKU, DON DA KARFAFAWARKU NA TAKA WANNAN STEPS DANAKE KAI AYAU, WA’INDA NAGA COMMENTS NAKU DA WA’INDA BANGANI BA WA’INDA NAMA REPLY DA WA’INDA BANMA WA BA, ALLAH YABAR KAUNA INA GODIYA*😃

    *SANNAN INA MAI MUKU ALBISHIR HADE DA SANAR DAKU SABON LABARI NA DAKE TAFE MAI SUNA*
    🏵 *ALKAWARIN MASOYA* 🏵
    *WANDA NAKE DA TABBACI HADE DA YAKININ ZAI MATUKAR KAYATAR DAKU INSHA ALLAH*😎

    ✨Ruqeenjalal ke muku sallama✨

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 20

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 20

     

    Saida tayi kuka ta koshi sannan tadago kanta taciro wayanta daga jaka tareda mikewa tabar wajen taje chan wajen wata bishi ya ta duka awajen, duk duniyan nan batada kowa banda kakanta duk wani abu data iya yau aduniya kakarta ta koyamata, Kakarta is her everything.
    Dialing number ta tayi yana ringing ta daga tace “Yar Albarka kinganni nan fa tundazu nake jinki araina amman Shatu nake jira tadawo tazo ta tayani kiranki amman ina tanachan tana buga yar gala gala, ya kike yar Albarka ya mijin naki da kowa da kowa”? Kungane feeling dinnan da yaro yakeji idan yana cikin damuwa yaji muryan iyayenshi kawai sai Ummi ta rushe ma Gwaggo da kuka, hankali tashe Gwaggo tace “ke! Meya faru kike kuka haka? Waya tabamin jikata iyye? Rabonda naga kinyi kuka haka tun zamanin azzalumin nan Mudi, meya faru kike kuka Ummi? Ya isa, ya isa, bagani ba, da raina fa Ummi kike kuka haka sokike Mamanki tayi fushi dani bayan tabani amanan ku, dena kuka kinji komeme ina nan fa, da raina kuma oya ya isa, zan iya saida raina naga bakuda matsala arayuwan nan, ishuru Zainabu ishiru kinji, wayataba mini yarinyata mai hakuri da kawaici da kunya? Wayatabamin jikana?” Cikin wani kalan kuka Ummi tana shesheka tace “Nura!” Salati Gwaggo tayi da sallallami tace “Nuran ne yasamin ke kuka haka? Mutumin danaganshi tsofai tsofai dashi zai iya haifanki sau biyar shine zai sakamin jika kuka haka? Shi baisan badan naganashi tsoho babban mutum mai hankali daban yarda nabashi ke ya aure ba, wato yagama tsotse kuruciyanki zai fara miki tijara, meya miki? Share hawayenki fadamin meya faru, fadamin daga tushe zuwa reshe share hawayen ki imaza, inajinki” share fuskanta Ummi tayi kaman yar baby tana kuka ahaka dai tabama Gwaggo labarin komi dake faruwa gabaki daya bata boyemata komiba har zancen kannin Hadiza, Gwaggo tace “amman mijinki yabani kunya Ummi, sabida shi tijararre ne katon banza, da girmanshi da tsufanshi bai amfaneshi ni zaizo har gidana ya auremini ke, wato auren huce takaici yayi, yazo ya chusama jikana soyayyan shi a zuciya haka sannan ya wulakanta mini diya? Jibi yanda jikana ke kuka a tasha gaban dubbannin mutane sabida shashashan Nura” Gwaggo tayi shiru tana karajin yanda Ummi ke kuka ko ba’a fada mata ba taji tsananin soyayyan Nura atattare da Ummi, wannan karan ne yatta tafada soyayya bata taba son wani ba Ummi, lokacin da akamata auren Mudi bamatasan menenen soyayya ba, da ace Ummi batason Nuran datace mata tadawo gida dan dudda tana yar kauye tasan darajan jikokinta, lokacin da Mudi ke kirbama Ummi duka tasan taje ta dauko jikanta tadawo da ita gida, tayi shige da fice akauyen nan maigari da manyan gari tasa aka raba auren, dudda Mudi nashigowa har gida yadakesu still batasa Ummi takomamai ba saidai tasan yanda tayi tafitar da Ummi daga kauyen, ina bata yarda awulakanta jikokinta ba. Ijiyan zuciya tasauke ahankali tace “Zainabu” ahankali Ummi tace “na’am Gwaggo” Gwaggo tace “Ummi dudda mu yan kauye ne ba yan binni ba Ummi nabaki tarbiya nakoya miki dabarun zaman duniya ke Ummi ko birnin sin aka kaiki zaki iya zama cikin mutanen yan boko sannan ki samama kanki lafiyayyen waje dan haka share fuskanka, Alhamdulillah ina raye ban mutu ba, Nura ne dai ko wlh sai yasan yayi rashi dan jikata daban take acikin jikoki dubun dabara!” Gwaggo tace “dudda za’ace kinyi gajen hakuri dakika taho ai aure ya gaji yau ayi fada yau ashirya but ni kakarki nayi na’am da tahowan ki Ummi idan Mata da Miji natare inhar akwai soyayya to ka tsaya koma wace ukubace zaka iya jajircewa ka maganceta amman in babu soyayya a auren gwara kayi gaba, abinda Nura yamiki ya nuna kaman dama chan baitaba sonki ba yakawai aureki sabida ya farkan da sumammiyan matanshi Hadiza ne yanzu kuma data farka baida bukatanki dan haka saurareni nan Ummi kibawa Nura tazara harsaiyasan amfanin ki, ke koda baya sonki ke wlh ma yayi karya yace baya sonki, Ummi nabaki tarbiya da dabarun zaman duniya duk wanda yazauna dake saiyaji yana sonki Nura na sonki kawai bairiga yasan dahaka bane amman yanzu zai sani, kalleni nan bazaki dawo adamawan nan ba, sabida zai biyoki nan barni dashi yazo nemanki wlh wlh daina mishi wankin bargo zan solleshi tas, saizan yarana nada daraja kuma babu abinda bazan iyaba akanku ku ukun nan, kinsan mezakiyi yanzu?” Dasauri Ummi tace “a’a” tace “kowa yariga yasan ke yarinyace mai tarbiya da hankali ce baikamata kitashi farat daya kibar gidanba yakamata ki sanar da wani babba yanzu Hajiya na asibiti kada ki kirata dubama da bawani lafiya gareta ba kira kanwar Nura dakika gayamin kwana kin baya kunyi waya wacce bata kasan kiraya maza maza ki gayamata cikin hikima kinji” Gyadamata kai Ummi tayi Gwaggo tace “koyaya kukayi ki kirani kisake sanar dani wayata na hannuna”.

    @TRENDYOUTNET Modest fashion world ne inda zaki samu professional kayan zuwa office masu kayatarwa, kyawawa, masu suturta jiki da mutuntawa, idanma casual kaya kike nema na sakawa yau da gobe duka tanada sunadashi all you have to do is chat them up ta wannan number
    wa.me/+2349093300112
    Kokuma zaki iya zuwa shagonsu dake nan Shop C22C 2nd floor Platinum Mega Mall opposite Ultra Modern Market Behind Next Cash and Carry Jahi, Katampe Road Abuja
    And u can also check shagonsu a IG @trendyoutnet don’t forget to follow them🔥 cus anayi baki😅

     

    Kiran Ya Aisha tayi ringing daya Ya Aisha ta katse wayan takira Unmi back kafinma Ummi tayi magana tace “Ummi ai dama ina shirin kiranki yau nace kwana biyu bamu gaisa ba, to ya kike” cikin muryan Ummi da baya fita sosai tace “lafiya l…..” “Ummi, meya sameki kikai kuka haka har muryanki ya chanza”? Ya Aisha tai tambayan da sauri Ummi tarasa mesa aka tambayeta sai tahau kuka da kyar tace “Ya Aisha kiyakuri kada kiyi fushi dani saisa nakiraki inaso ki lallashi Hajiya itama kada suyi fushi dani amman zan tafi kauyenmu wajen Gwaggona gani nan atasha” dasauri Ya Aisha tace “mene! Ummi! Mesa zaki tafi? Meya faru? Fadamin kinsa gabana nafaduwa menene”? Ahankali Ummi ta rairamata komi daga AzuwaZ Ya Aisha zuciyanta yafara tafarfasa sosai tace “sabida yar gwal dinshi zai wulakanta ki? Ai wlh Ya Nura kaman na dakeshi wani zubin bantaba ganin kalan mutum mai zuciyanshi ba Mata tazagi mahaifiyar ka ka kasa komi haba” tayi shiru tana sauraron yanda Ummi ke kuka tace “Ummi kema saiki tashi kitafi mesa baki fadama Hajiya ba? Hajiya bazata taba bari Nura ya wulakanta kiba wlh yayi kadan yayi irin abin nan agabanta ai shi yasan waye Hajiya idan tai fushi ko duka kano zasu hadi ba’a iya lallaso ta kuma wlh bazakije Adamawa ba zai gane yamiki laifi yaje har garinku ya auroki marainiya dake shine yanzu zai fara wulakantaki wa zaki kalla kiji dadi? Zaman wa kike? Yan uwan Hadiza sumiki kinyi shiru sunzo gıda sun gaje kitchen though nagane dalilin dayasa Hajiya bata musu magana ba amman dudda haka gwara dakika barmai gidanshi dan suka dawo ma wulakancin saiyafi nada….” Ya Aisha tahau surfafa masifa kafin chan tace “Ummi kiyakuri kinji amman dan Allah kada ki rabu da Yayana but na yarda yanzu kada ki koma gidan kiyi fushi dashi amman dai kada kirabu dashi wlh zai koma gidan jiya kin tsamoshi daga kangin dayake ciki kin maidashi mutum kin rufamai asiri kuma ke Ummi kinma Ya Nura komi fan Allah kada kiyi fushi dashi yanzu kinsan mezamuyi zan kira wani kanın Mijina yazı ya daukeki ya kaiki gida zanyi arranging komi amiki international passport da visa da sauransu Mijina duk yanada hanyan da za’amiki fast saikizo wajena Ummi zan gyaraki wlh sai Nura yamiki kuka kafin ki koma wajenshi kinji dan Allah Ummi kada ki koma garinku” Ahankali Ummi tace “Gwaggo na bazata yardaba nariga nagaya mata zan dawo gida” dasauri Ya Aisha tace “kira Gwaggo hadamu conference call kin iya hada conference call”? Ahankali Ummi tace “a’a” Dasauri Ya Aisha tace “turamin number ta” tura mata number Gwaggo tayi sunyi waya mai tsaye sannan Aisha tasake kiranta tace “Gwaggo tace takirata” kiran Gwaggo Ummi tayi tana dauka Gwaggo tace “kije wajen kanwar nan nashi Alhamdulillah yan Yan uwan shi duka suna sonki, kidena kuka zamuyi magana idan kinkai gidan kanin mijinta ki kashe wayanki but kullum kidinga kunnawa kina kırana sau daya muna magana inji lafiyanki kuma nagayamata kada tafada ma kowa kina wajenta tace haba bazata fadi ba, bari Nura yadawo daidai zai gane yayi rashi, jikata daya ce tak acikin mata miliyan” katse wayan tayi Ya Aisha takira tace “me Gwaggo tace”? Ahankali Ummi tace “tace naje wajenki” murmushi Ya Aisha tayi tace “Alhamdulillah Alhamdulilah kina tashan jabi ko” Gyadamata kai Ummi tayi tace “um” nan da nan ta katse wayan kafin chan tasake kiranta tace “gashinan zuwa nabashi number ki kada ki kara kuka Ummi, kinga maza wlh halin maza saisu saisa wasu ke cewa gwara kaci ubansu dan sunfison matan dake basu wahala suke basu kashi ada ban yarda da maganan ba but wlh yanzu akan yayana uwa daya uba daya na yarda, idanma tunani yake baki da gata wlh baiyi tunanin da kyau ba Ummi nadade banga Kakan dakeson jikokinta kaman Gwaggon ki ba ko ita kadai ta ishi ya Nura ai zaije kauye nemanki wlh saitaci mishi mutunci, butulu kawai gwara da kika bar musu gidan indai Hadiza ne gashi ga ita ai hali zanen dutse mai hali baya fasa halinsa ayi soyayya agama yanzu idanunshi zasu budene ya nemeki”.
    Sosai Ya Aisha take mata hira awaya just to ensure bata kara kuka ba har Faisal yazo ganin call waiting na shigowa wayanta yasa Ummi tace “wani number nakirana Ya Aisha” dasauri Ya Aisha tace “shine dauka” katse wayanta tayi tadauka suka gaisa yace “ina gaban yola line kina ina”? Tashi tayi ta taho wajen harta ganshi suka gaisa yabude mata baya tashiga tazauna yabata ruwan gora mai sanyi ta karba tamai godiya suka tafi gidansu mai kyau babba ne matanshi dakeda tsohon ciki tama Ummi sannu da zuwa suka kaita daki lafiyayye matan tazauna da Ummi sannan tafita takawoma Ummi abinci da drinks da kayan sawa da yawa tasamata a sip Ummi tamata godiya.💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

    ✍🏻M SHAKUR