Author: Novels

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 3

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 3

    EPISODE 3️⃣

    BONUS💃
    Sosai kirjinta yabuga da sauri ta sauke hannayenta kasa tadaina rawan tasauke kanta kasa shima daga kallonshi gabanta nafaduwa dumdumdum.
    Wucewa Nura yayi dasauri sama zuwa dakinshi yakasa daina ganin fuskan Ummi dana yaranshi how happy all of them were, yanda itada Aman kema Amal rawa, bayi yafada dasauri ya watso ruwa yafito yashiga shiryawa dan yafita meeting din dayake dashi is by 2, cream yadauka zai shafa saikuma ya tsaya maisa ya kalleta haka smiling ya tambayi kanshi? He was lost dayana kallonta, yar aikinsu ce fa but he was finding all abubuwan datakeyima yaranshi super cute, dan ijiyan zuciya yasauke saikuma yacigaba da shafaman.

    Ummi daduk takasa natsuwa itama a kitchen ta tambayi kanta maisa yake kallonta, tun yaushe Alhaji yaganota tana rawa haka? Duk wani kalan kunya kunya da nauyi nauyi taji tanaji, IPad din Aman tadauko ta kunnamusu anan kitchen din dan bazata rabu dasu ba tashiga gyaran gidan duka tanaso tana gamawa tamusu wanka, itama taje tayi saita daura abincin dare.

    Shiryawa yashigayi cikin suit dan dawasu representative na China company zai hadu dasu yanaso yabasu contract nayin titin cikin estate dayakeyi, yana cikin daura agogo wayanshi yahau ringing kallon wayan yayi ganin Sis yasa yakai hannunshi ya danna call din batare daya daga wayanba yacigaba da saka agogo daga ta dayan bangaren akace “Ya Nura ina yini” “how are you Aminatu ya jikin Hajiya kunje asibitin”? Kasa magana tayi sai bakinta yahau rawa, dasauri yasa hannunshi yadauki wayan gabanshi ya mugun fadi yakai wayan kunnenshi dasauri yace “what happen jikin Hajiya ne meya faru?” Cikin kuka tace “dazun nan tafadi abayi yanzu haka muna asibiti” bugawa kirjinshi yahauyi sosai anatse yace “Dr Tanimu ne ke ganinku”? Dasauri tace “eh shine” dan ijiyan zuciya yasauke yace “daina kuka ya isa babu abinda zai sami Hajiya kinji” kaman yana gabanta gyadamai kai tayi, cikin dan taushin murya yace “is okay, zanyi magana da Tanimu I think zan muku booking flight gobe kutaho nan Abuja taje babban asibiti anan don’t cry again hankalinta zai tashi, akwai kudi awajenki”? Dasauri tace “eh akwai” ahankali yace “to stop crying bari nai magana da Dr Tanimu” nan da nan ya katse wayan yakira Dr sunyi magana da dadewa sannan ya katse wayan dakanshi yamusu booking first flight na gobe da safe sannan yasake kiran sister nashi yace zasu biyo jirgin safe gobe suzo koya ake ciki tadinga gayamai yatashi ya idasa shiryawa duk mood nashi ya chanza sannan yafito anan falo yaga Aman da Amal suna kallon cartoon a iPad nasu duk an musu wanka sunyi kyau gwanin ban sha’awa kaman ya debesu yafita dasu Amal kaman ba itane mara lafiya ba karasawa yayi inda suke ya duka yamusu peck agoshi yace “Dady zaitafi aiki” dasauri Aman yace “Dady zan bika office” shiru yayi kaman mai tunani yana shafa kansu yace “shikenan zanje daku amman sai ranan Saturday jibi kaga gobe akwai school yau bakuje ba dukanku” Dasauri Aman yace “hadda Anty Ummi zamu itama taje taga Daddy’s bigggggg office” ya ware hannunshi biyu yana nuna how big office na babban shi is, dan murmushi yayi yana kallon Aman din kafin ahankali yace “yes Son hadda Anty Ummi” dasauri Aman yace “love you Dady u the best Dad ko Amali? Dadyn mu is the best” dasauri Amal yace “yeeeessssss Dady is the best” murmushi yayi yace “my princess and my Aman are the best nima” harzai tashi yace “ina take?” Aman yace “Anty Ummi”? Gyadamai kai yayi dasauri yace “itama taje tai wanka adakinta” jinjina kai yayi yamike yace “to natafi bye” bye sukamai yawuce yafice.

    Wani babban shago ne girmanshi zaiyi wani super market din sama da kasa ne, kasan abayoyi ne irin na yan millions din nan designers dan babu abayan yan 100 ashagon saikuma sama asalin designers bags da shoes ne latest collection ma kuwa, zaune take cikin wani office dake nan sama babban office ne na gaske dawasu mata guda biyu suna hira, daya daga cikin matan biyu ne tadaura tissue kan idanunta tana kuka Hadiza taje tsaki tace “kodai nazo nai magana da mijin nan naki ne Baraka”? Dasauri Baraka tazare tissue dagakan idanunta takalli Hadiza idanunta sunyi jazur tace “so kike ya koreni? Not everyone is as lucky as u are kinada miji kaman Nura mai hakuri da share magana, idan nama Ubale abinda kikema Nura saiya lakadamin duka halan saiya korani gida” wacce ke kusa da itane ta tureta tace “dallachan ai gashinan saisa sai gallaza miki azaba yake waya cemiki anama maza good girl yanzu??” Dasauri Hadiza tace “ahh tohh tell her ooo my dear, tell her Zee cus good girl no dey pay again, kima miji good girl ya tattakaki yayi using naki do dambu yaje ya watsar a shadda, ai yanzu zaman Auren fire for fire ake yana baki kada kibari yakai kasa give him back gbasgbos kawai saikaga yasha jinin jikinshi yasan keba kanwar lasa bace, kinga Nura ko giyan wake yasha yasan bai isa ya tunkareni da nonsense nashi ba cus bana ma dauka ne kuma gashinan nasama ma kaina lafiya I do duk abinda naga dama duk abinda raina yaso agidana to waima tsaya idan nai aure banyi whatever naga dama agidana ba yo menene fa’idan auren? Menene banbancin gidan mijina da gidan iyayena? Abeg ke waye Ubale yana cemiki kule kicemai chass wlh zakiga kun zauna lafiya” dasauri Zee tace “Allah yasa ta dauka, itane kullum yamata ihu kaman ubanta, fita saiyaga dama yake barinta, yahanata business ya kulleta agida kullum ciki yake duramata won’t you speak up kinuna mishi kefa duk lokacin dakikaga dama fita zakiyi ki kwatarma kanki yancinki, ki nunamai kedashi are equal sabida yana namiji baya nufin zai dinga juyaki, munafa zamanin feminism ke duk inda namiji yau yataka aduniya kema zaki iya takawa to akanme zaki maida kanki slave dinsa? Jibemu kawayenki yanda muke more rayuwa muncigaba ke kinachan kina bautama mijin dake hanaki fita sana’a, yakuma miki ihu” tissue takara dauka dan maganganun su nasata jin badadi datasan hakane da da Zee tazo daukanta batabita ba, tace “nidai kubarni duk randa nazo wajenku saikun sani ina feeling bad inajin kaina kaman banda sa’a aduniya, kaman I’m the unlucky one, Ubale na sona ina sonshi kuma ya isa yace nayi nayi karnayi karnayi ya is…….” Mtswwwww Hadiza taja tsaki dayasa Baraka tai shiru takalleta Hadiza tace “takuraki dai baya bari kiyi yanda kikaga dama, imagine yaranki uku har yanzu kece ke komi agidanki, girki, kula da yara uku fa da sauransu ke jakace Baraka? In nice ai sai na mutu, Idan yana sonki bazai sama miki yar aiki ba haba akan mene zaki dinga shiga kitchen kina girki awan nan zamanin da masu kudi ke hiring intercontinental chef yana musu girki agida that’s my next plan ma ni nadauko professional Chef daman na share zancen ne bayan na sami wannan current yar aikin nawa Ummi but still zan dauko” dan murmushi Baraka tayi tace “Allah baki sa’a, kowa nada abinda works for him, ninaji naga kuma zan iyane ne, mubar maganan please kona tashi nayi tafiya ta gida daman Zee takawoni, I don’t have to be like you ladies, tundadai ba dukana ko wahalar dani mijina keyiba ko neman mata Alhamdulillah” dasauri Hadiza tace “to abar maganan amman wlh sabida kawai ke kawarmuce duk tare muka taso da tuni mun rabu dake danni banga dalilin dazaisa kene ke duka aikin gidanki ba mijinki na miki ihu kaman wata jak…….” Karan da wayanta yayi yasa takasa karasa maganan takalli screen din ganin Nuri yasa tai murmushi sosai tajuyo da wayan tace “kun gani” tanuna musu screen din wayanta tace “tsakanina dashi kar tasan kar ne amman jibi yanda yake bibiyana maza fa saida hash treatment kana musu taurinkai ki nuna musu ke fire for fire ce cus sun iya raina mace kai mai sanyi irinsu Baraka” Zee tace “kwarai kuwa Aminiyata”.

    Tashi Zee tayi takalli Barakan tace “muje mu duba abayoyin to” tashi tayi tabita suka fice ba walwala kan fuskanta, Hadiza na kallon kiran sai murmushi take dake kara fito da kyawun fuskanta saida wayan yayi gab da katsewa ta dauka takai kunne ayangance tace “ka gama nunamin matsayina menene kake kirana kuma yanzu”? Dan shiru Nura yayi yana jinta ba sallama bakomi kafin yamace wani abu tai magana, yana addu’a duk wani namiji dabai Riga yayi aure ba to Allah yarabashi da auren mai baki kaman na Hadiza, saikuma chan yace “Hajiya tafadi abayi yau an kaita asibiti but hankalina bai kwanta ba namusu booking flight na safe gobe zasu taho nan da ita da Amina zan kaita hospital taga kwararren Dr, specialist” wani abu Hadiza taji ya tsaya mata arai zai cigaba da magana ta tareshi tace “wai Nuri what gives you the right kadinga making decision regarding our family on your own eh? Wai meke damunka ne zakace Hajiya bama ita kadaiba harda kanwanka suzo gidana bazaka fadamin ba kaji me zance kafin nan kai kadaine agidan? Kodon kaga gidanka ne? Koma da gidanka ne ai nima ba zaman banza nake agidan ba aure ne yabani gidan dan haka u have no right to invite koma waye into my home without telling me, without seeking my approval” tunda Nura yake baitabajin urge na yadaga hannu ya mari mace ba sai yau wlh he feels kaman yadaga hannu ya kifama Hadiza marin da saiya maida fuskanta keya, keyanta yadawo fuska, mahaifiyarshi ba lafiya bama ta tambaya yaya jikinta ba or anything sai maganan gida, menene agidan? What is house? Me Hajiya zatayi agidan? Yau shekaransu nawa da aure Hajiya bata taba zuwa Abuja bama ballema gidanshi so menene abinda matan nan ke fadi? What can a sick old woman zata possibly iya miki agida tana fama da kanta fisabilillahi?Yanada mahaifiya mara lafiya da zatazo garin abuja for the first time yaje yakama mata hotel ne sabida matanshi batason wani yazo wajensu???

    Daurewa yayi yarike zuciyanshi yana controlling anger yadan sauke ijiyan zuciya Hadiza tabugamai ihu da tsawa tawaya. “Ina maka magana kamin banza are you deaf ne or what Nuri? What gave you the right to invite a third party to my house baka fara sanar dani ba” shi Hadiza ke kira deaf??? Innalillahi, cikin wani irin murya datai sanyi sosai tsabagen bacin rai yace “mahaifiyata ce third party Hadiza? Maman mijin dakike aure uban yaranki, kakan yaranmu itane 3rd party”? “Well u can translate it duk yanda kaga dama is none of my business just listen to wat am about to say” tadan gyaran murya tace “first of all bada yawuni aka kawota ba don’t expect anything from me babu abinda ya shafeni da dawainiyan ku, sabida Hajiya bazan fasa fita aiki na ba, kuma bazan shiga kitchen ba, kuma bani acikin tafiyan zuwa asibiti ko rakiya kai infact banda any business with anything dazai faru daga goben nan zuwa harta bar gidan, dan haka kaika sani ni please sai anjima I am busy with work, I don’t have time for ur unnecessary demand” ta katse wayan Nura yadade yana kallon wayan kafin ya fuzar da iska kaganshi dole kai saluting nashi dan namiji ne mai hakuri dayay composing kanshi bai duramata zagi ba, dama kiranta yayi yaroketa kada taje aiki gobe sabida su Hajiya sannan kuma ya tambayeta me da me babu agida amman jibi abinda tayi rasa abinda zaiyi yasa yayi dialing number Gardner na gidanshi ruwa ringing daya ya dauka anatse Nura yace “Amadu banda number Ummi danje ka buga kofa ka bata wayan” dasauri Amadun yace “gasuchan inajin muryansu a garden takai yaran suna buga kwallo bari nakai mata” anatse Nura yace “ok”.

    Bata wayan Amadu yayi yace “gashi Alhaji yakira zai magana dake” sa wayan tayi a kunne kaman yana gabanta ta duka tace “Alhaji ina wuni” baisan what just happen ba amman har cikin zuciyanshi yaji sanyi aranshi na muryanta, dan ijiyan zuciya yasauke ahankali yace “Ummi mahaifiyata da kanwata zasuzo gobe dasafe Mamana bata da lafiya zataga likita agarin nan” da zuciya daya Ummi tace “Subhanallahi Allah yakara sauki, Allah yasa kaffara ne, Allah kuma ya iso dasu lafiya ya tsare hanya” Wallahi he cannot even explain wani kalan dadin addu’an ta da sanyinsu dayaji aranshi, jin yanda yayi shiru yasa Ummi tace “Alhaji kanaso na gyara musu wajen kwanan su ne namata abincin da marasa lafiya keson ci”? Harga Allah ta dauka abinda takira yafada kenan cus ana bata wayan abinda yafara fada mata kenan mahaifiyarshi ba lafiya kuma gobe zatazo. Yarinyar nan is not just good with kids tanada great sense of humor tanada hankali tasan meyakamata and tanada natsuwa, though abinda yakira was yanaso ya tambaya menene babu agida but tambayanta made hum wanna talk to her more, ahankali yace “menene abincin marasa lafiya Ummi”? Kai tsaye dan babu komi aranta tace “meke damun Mama Alhaji”? Yanda tafadi Mama ba Hajiya ba dan yasan batasan Hajiya ake kiranta ba wani sanyi yaji aranshi baisan lokacin dakaman wani dan karamin yaro yace “ciwon sugar da hawan jini ke damunta” dan shiru Ummi tayi kafin ahankali tace “abincin dayakamata tanaci abinci ne da babu sugar aciki, babu Gishiri kuma dan Gishiri yana kara hawan jini, zan mata tuwon Alkama ko tuwon garin plantain dabai nunaba amman duka biyun bamu dashi agida, da miyan ganye, Gwaggo na a kauye nada hawan jini da ciwon sugar duk nasan irin abincin datake ci dake taimakamata bata cika ciwo sosai ba, idan Mama tazo itama zan dinga dafa mata zakagani zata ji sauki da izinin Allah” dan murmushi kadan yayi a tsane yace “nagode Ummi kituramin sunan abubuwan da zan sayo dakuma abubuwan da babu agida, saiki gyara musu wajen kwanan” Ahankali tace “to” dan shiru yayi itama tai shiru tana jiran taji ko akwai wani abun jin shiru yayi yawa yasa tace “hello” batare daya amsa ba yace “inaso naci tuwon shinkafa da miyan taushe ki dafamin kinji” yanda yayi maganan ataushashe saida taji wani iri dasauri tace “too” yasake shiru itama tai shiru tana sake jiran maganan shi maganan su Aman da Amal dayaji suna Anty Ummi come come let’s continue yasa yace “to saina dawo ko” ahankali tace “too Allah dawo dakai lafiya” lumshe idanu yayi tareda zare wayan daga kunne he just wish da matanshi yayi dis dogon magana wlh babu abinda yake craving yanzu aduniya irin kwanciyan hankali, Allah ya azurtashi, yakuma bashi yara, kwanciyan hankali ne kawai yarasa, yesterday yafara magana da yarinyar nan why is he enjoying conversation da ita haka?.

    See y’all Saturday 🥰

     

    Let’s keep HADIZA in one place, one of the major abu dake kawo matsala agidan miji is shigowan baki, guest ko visitors aturence.

    Mata will always say ban isa nakawo baki batare dana sanar dakai wane ko wance zatazo ba.

    Maza kuma sai sun gama cema mai zuwa Allah kawoshi lafiya za’a cemiki babe wane ko kaza na hanya fa zaizo ko zatazo tamana kwana biyu hakan na batama Mata dayawa rai.

    My question is, is it okay for mijinki ya yarda kowa yazo kafin yazo yafada miki daga baya wane ko kaza zaizo?
    Koko yakamata yafara neman yardanki ne kafin wane ko kaza yazo?? Cus I keep wondering gidan aure belongs to waye exactly??
    Does it belongs to the wives ne sabida ai cewa ake za’a kaiki gidanki ko it belongs to mijin kadai ne koko gidan aure belongs to the TWO OF YOU???

    To idan gidan na dukanku ne biyu maisa ba’a making decision kan wanda zai shigo tare???

    Mata ayanzu daku nake ko sabida maza sunsan mun tsani ace wane ko kaza zaizo ne koda an gayamana bazamu yarda ba saisa gwara suyi accepting wane yazo kafin asanar damu cewa wane zaizo rana kaza????

    How do you think za’a iya magance yawan issues da ake samu idan za’ayi baki agidan miji??

    Let’s discuss this👇🏼
    [9/18, 9:17 PM] +234 706 542 1229: 💫 MATAN??? Ko MAZAN???💫

     

    ✍🏻M SHAKUR

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 6

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 6

    EPISODE 6
    Dum dum dum!! Hadiza taji kalman sakin ya daki zuciyanta kaman saukan aradu cus ko amafarki, like ko amafarki dai wannan bata taba tunanin Nura zai taba bude baki yace yasake ta ba, duk yanda takeson tai kokarin controlling yanda hannunta ke rawa kasawa tayi wani kalan reflex rawa hannayenta suka fara tama kasa magana sai idanunta data kwalaloo kaman zasu fadi akasa tana kallon Nura daya hade rai kaman wanda baitaba murmushi ba aduniya ya nuna mata kofa yace “get out of my house, out!” Yadaka mata tsawan da saida ta firgita, ganin taki motsi yasa yayi inda take azuciye yasa hannunshi yakama hannunta datake rike da key motanta yawani jata dan ranshi yabaci ainun ta daukoma Mamanshi da kanwarshi Police haba nooo enough! Dasauri Hadiza tashiga cewa. “Nuri, Nuri, Nuri” bude kofa yayi yafito da ita har zuwa wajen motan ta yace “get out of my house” dasauri tace “Nuri ni zaka cewa kasaka are u for real? Wait mafarki nake? Nine zaka saka because of your family now can u see why I was against zuwan family miji cause all they bring into your home is chaos? Nuri ni Hadiza zaka saka? Ni zaka kora from my home”? Wani kallo yamata yace “you are dumb, foolish and you are crazy Hadiza, bakin halinki yasa I don’t have any feelings left for you azuciyana, duk matan da have no regard towards my mother can never have space in my life or home dan haka get out, go and do your feminism awani waje not inda uwata take” yana maganan yawuce ciki ya maida kofa yarufe da key yabarshi ta yanda she can’t come in, Hadiza was completely in a state of shock ita Nuri zai saka, ita Hadiza, wajen kofan tayi tadaga hannu zata buga saikuma tace ai sai su Meena su mata dariya damai gadi, tama zubar da ajinta kenan rokonshi zatayi yabude mata kofa kome? Yasaketa tayi tafiyanta mana, deep down zuciyanta cike yake fal da damuwa sai tambayan kanta take ita Nuri yasaka just now? Ita Hadizan nan saki fa? Saki dai datakeji anama wasu matan itama yau anmata so yanzu she’s a divorcee? Ta tambayi kanta saikuma ta juya tashiga motanta tazauna takai awa daya ahaka dataga dai da gaskene yasaketa ta tada mota ta tafi yanzu inama zataje ta tambayi kanta taje gidan kawarta ne? Ina zata? Parking tayi cikin premises na shagonta tai dialing number yayanta ringing daya ta daga kafin Anty Jamila tai magana Hadiza tace “Anty kinga yasakeni ko”? Shiru Anty Jamila tayi irin shirun son gane abinda tayi, saikuma tace “ai yamiki kyau gashinan jikinki yayi sanyi hankalinki yafara dawowa” cikeda karfin hali da tsiwa tace “jikin wa yayi sanyi? Da ace namai laifi ne sai jikina yayi sanyi? Ni Nuri zai saka sabida yan uwanshi wlh zai gane he’s mistaken idan yana tunanin yasakeni kuma na sakun mai wlh karya yake yacimini mutunci haka yakoreni wl…..” takasa karasa maganan sabida kukan daya taso mata tai shiru Anty Jamila tace “kinason mijinki Hadiza, kina mutuwan son mijinki amman bakin hali da al’adan yahudu da nasara yasa kin zama shaidaniya, shine your eye and accept keda shi are not one amman kin dage ke da shi are one kin dage, kin dage kaman bakar mayya accept cewa ba komi ne arayuwan nan must always go your way ba, idan haukan dakikeyi ko feminism din dakikeyi na solving matsala go and solve this one mana da feminism din look at abinda shegen feminism din yasa kika girba saki and this is just the beginning saikin rasa mijinki sannan zaki gane kene da kanki kika saka kanki a wahala, yanzu bama wannan ba Meya hadaku”?

    Dudda akule take ahaka tabawa Anty Jamila labarin komi salati Anty Jamila tayi tace “wlh da niyyata muna gama maganan nan nakira Nura nabashi hakuri amman wlh, wlh bazan kiraba saidai Mama takirashi, Hadiza uwarsa kika zaga? Wai aljanu gareki ne koko kin fara having mental disorder ne? Konine bazan tsaya wata tazagi Mama agabana ba sai inda karfina yakare, Meena tamin daidai ke baki girmama nagaba dake ba tayaya nakasa dake zasu girmama ki? Kadan kika gani Allah yab…….” Ihu Hadiza tayi tace “ni dama nasan u will never support me what’s wrong with abinda nakeyi? I am just going with the trend? A home belong to the woman so she should be the one to call the shot, Anty Jamila fisabilillahi da aurena agidana amman bazan fadi ajiba banda say, haka akeyi eh? Nasa yar aiki tamin girki yahanata, yasa yan uwanshi suzo bazai tambayi permission dina ba ita Hajiyan haka aka mata eh? Ta kawai shigo gidana tahanani sakat ana cewa batada lafiya kinga abincin danaga tana zakalkala aciki ne tana zuba surutu? Tanaji aka sakeni aka korani bata fito tasa baki ba that’s shows plan work ne, All I ever yearn for and I ever do was to be incharge of my home, kome zai faru inhar it has to do with gidana nizan fadi ayi ba Nura ba, duk fadan dazanyi dashi akan abinne, idan zaimin haka nima zanmai komi yanada abokai yasan haka akeyi a Abuja har kunya nake kar kawayena suzo suga abinda ke faruwa agidana su bahaka sukeyi agidan su ba” dan ijiyan zuciya Anty Jamila tayi tace “Hadiza baka forcing control da ownership, Nura zai iya bari kina calling shots agidanshi idan yaso amman means dakike bi is not right, tell me one thing dakike yima mijinki tell me?” Cikeda bakin takaici kaman ta make Anty Nafisa ganin taki fahimtan ta tace “Anty Nafisa pls pls understand nan ba kano bane this is FCT for crying out load, city of wealth, a Abuja u don’t have to do anything for mijinki as a wife, a woman is a queen dayakamata tanada ma’aikata which I have, su yakamata suyi komi, in this aspect banyi any laifi ba nagaya miki I’m just going with the trend zamanin damuke kenan, I don’t have to cook, sweep, take care of the kids or anything akwai masuyin aikin abiyasu duk wata Anty Nafisa nan ba kano bane kigane there’s nothing extraordinary anan abinda ke faruwa kenan wlh” hmmm! Anty Nafisa tasauke ijiyan zuciya dan lamarin Hadiza mai girma ne tace “Hadiza kinyi nisa are you saying yanzu kuka koma Italy al’adan Italians zaki dauka kicema mijinki dan Nigeria dole sai yayi? When will u understand mijinki bazamfare ne girman kano, Sana’a ce takawoshi Abuja, Nura is educated but rayuwan bokon nan da wayewa tamasu kudi dakikeso shi baya gabanshi, ace yana aurenki bazaki bashi ruwa dakanki yasha ba menenen ma amfanin ki? Wai kuma ahaka bakimai komi kuma kinaso shi yamiki komi, kome kikace yace Naam ko tunda gaki mamallakiyan Nura sannu Hadiza mai fadi aji, yanzu kina ina?” “Shago na” cikeda isgilanci Anty Jamila tace “maisa bakije gidan kawayen naki ba to”? Ahankali tace “ai abin kunya ne suji abinda yasameni, that means I don’t even have any power or influence agidana inhar mijina zai koreni daga gidana sabida yan uwanshi wlh wlh abin nan yamini ciwo Anty Jamila, you have no idea yanda matan Abuja are powerful agidan su amman ni Nura bazai bari nai enjoying that luxury ba, kuma wlh wlh wlh zai sani” anatse Anty Jamila tace “Hadiza keba yarinya bace you’re 32, ke kinsan abinda kike bai dace ba, uwarmiji uwarkice, ita tahaifo abinda kikeso and nurture him, groom him into the man he’s today, miji ba abin wasa bane dazaki dinga experiment naki akanshi, this is just 1saki Nura yabaki, idan ba u wanna loose him for ever ba ki gyara, all it takes is apology, kije kibama mahaifiyar shi hakuri kibashi hakuri ki gyara the way kike abubuwa agidan ki before it will be too late for u kina jina? Idan zaki dawo kano ne kidawo, zandai gayama Mama nasan zata kirashi amman ni Allah yasan bazan iya kiranshi ba take care Allah kuma ya ganar dake kafin lokaci yakure miki”.
    Katse wayan tayi tadade zaune amota saida aka tafi magrib sannan tafito ta tafi sama tabude shagon tashiga tamaida tarufe tawuce sama office nata ta shiga kwanciya tayi kan dogon kujeranta tayi shiru tanada kudin kama hotel ta kwana abinta amman takasa, takasa zuwa wajen kawayenta kada amata dariya tagama cika baki, da kyar ta lallaba taje tai salla wasa wasa har 12 nadare takasa bacci sai juye juye take yanzu shikenan Nura yasaketa ya koreta daga gidanta shikenan bata da gata? Itane yau da kwana a shago? Hakanan kawai saitaji tana kewan yaranta koba komi kobadan suzo wajenta ba amman muryansu da hayaniyansu datakeji da Ummi is something sai kawai taji tayi kewansu sosai din nan, lema lema dataji akan fuskanta yasa takai hannunta dasauri ta taba ashe kuka takeyi dasauri ta tashi zaune tace “no feminist don’t cry, with or without Nura I can create my world why am I sad? Dan yace yasakeni, yakoreni daga gidanshi? Why nakejin badadi nakasa bacci 9 nayi bacci jibi lokaci yanzu nakasa why?, Yanzu Nura harya isa yacusamin bakin ciki? Then menene amfanin the belief I stand for? The whole feminism an fito dashi ne dan anunama mata they don’t need men or approval na men to survive on this world, all she need is herself” share fuskanta tayi tass tace “Nura kayi kadan kasamin kunci” ijiyan zuciya tasauke tafara fadama kanta words of affirmation. “I’m Hadiza diyar Tijjani, I’m strong, independent and beautiful dudda tsinanniyar yarinyar nan tamin scars din yakushi yanzu awuyana, I’m smart, unapologetic, resilient and bold, I don’t need a man ko anybody to be happy, Hadiza is enough for kanta, a man can’t downgrade or belittle Hadiza, I’m as tall as the mountain ,as hard as rock, as thick as thicker, no one can break Hadiza saidai ni nai breaking, I’m unbreakable, I’m happy, I’m happy, yesss I am happy!!” Tafadi ma kanta tana murmushi tana dukan kirjinta saikuma wasu munafukan hawaye suka kara fitowa daga gefen idanunta tadaura hannunta akan fuskanta tafashe da kuka sosai tace “na shiga uku why am I sad? Nura ni zaka saka awanan sad mode din? Ni Hadiza zakama saki Nura? Ni kanwarka zatama duka sannan kayi throwing dina out kahadan da saki jibeni a shago zan kwana? Ni Nura?? Wlh saina gwada maka kayi da diyar halas wlh kuwa” wani shegen kunci takeji the state datake ciki ita kanta batasan Nura is this important to her ba sosai take sonshi but bata saniba, she’s extremely sad takasa bacci, kaman ta hadiye zuciya takeji tamutu.

    Wajajen 3:30AM Hajiya ta tashi daga bacci, Meena tagani agefenta dasu Amal duk suna bacci komi daya faru dazu dawo mata yayi sauka tayi daga gadon da dafa bango tafito dakin Nura taje sallama tayi ahankali ga mamakinta bude kofan yayi yana sanye da jallabiya hannunshi rikeda charbi dasauri yariketa yace “Hajiya kin tashi” shigar da ita dakin yayi yamaida kofa yarufe akan couch na dakin ya zaunar da ita shikuma yazauna agabanta akasa yakama hannunta yarike ahankali yace “Hajiya kiyakuri sabida ni Hadiza tamiki rashin kunya yau” girgixamai kai tayi kafin tazare hannunta daga nashi daya rike ta tallabo fuskanshi cikeda tsantsan soyayya irin na d’a da mahaifi tace “maisa baka taba sanar dani abinda ke faruwa agidanka ba? Nura yaushe Hadiza takoma haka? Kamata wani abu ne”? Duk yanda yaso ya daure kasawa yayi ahankali yadaura fuskanshi sanan cinyan Hajiya murya chan kasa yace “Hajiya nagaji I’m tired, sometimes I feel maisa namayi aure? Da auren nan gwara rashin sa but then nakalli yarana Aman and Amal sainace Alhamdulillah Allah has already blessed me with the most beautiful kids aduniyan nan” yayi shiru yace “Hajiya I don’t have peace of mind idan nabar gidan nan kaman kada nadawo tunanin yarana kesa nadawo, babu one single thing da Hadiza kemin amatsayinta na matana and bantaba mata wani abuba, Hajiya sometime ina zama na gayama kaina indai this is wat comes out of auren educated mace to gwara auren gidahuma jahila dazata maka biyayya and be a wife for you cus Hadiza is a wife for herself not for me, tanada masters in business Administration tanada business kudin sun shiga hannunta, yanzu taga am useless koda ace yau zan rabu da ita tanada future she has money, and money is everything idan kanada kudi baka bukatar komi kuma zata iya kula da kanta, everything data mini I tolerated it dudda she’s 32 but kallon mahaukacin yarinya nake mata Hajiya she insulted you today tayi magana dake kaman ita ta haifeki saisa nace tabarmini gida taje na sake ta saki daya” dasauri Hajiya ta kalleshi dago kanshi yayi idanunshi sunyi jaaa sosai yace “Hajiya kin sanni sama da kowa kinsan inada hakuri kawaici juriya dakuma yafiya yaune rana na farko dazan rokeki Al farma kada kice nadawo da ita please I want a break from this auren mu besides I’ve grown feelings for someone kuma inaso naje garinsu na nemi aurenta” Hajiya na kallon fuskanshi tace “Ummi?” Dasauri yace “tayaya kika sani Hajiya”? Dan murmushi tayi tace “sabida nina haifeka” dan shiru yayi chan yace “Hajiya nakamu da son Ummi sosai, tagayamin ta taba aure tama haihu……” yabama Hajiya labarin yace “Hajiya inason Ummi sabida some odd dalilai” ahankali yace “Hajiya nakamu da son Ummi sabida duk wani abu da Hadiza kedashi ita batada shi” yadan sauke ijiyan zuciya yace “inason ta sabida she’s not educated, sabida batada kudi, sabida she’s not independent, sabida she’s innocent, sabida she’s polite, sabida she respects me, sabida she pay attention to me, sabida tanason yara na, sabida she feed me, sabida tana magana dani calmly her voice is so soothing to my heart, I love her sabida she’s weak, fragile, sabida she’s a soft woman not strong woman, ina sonta sabida matace da idan na aureta nine zan zama ragamar rayuwanta and she will let me be the husband and above all nayi istikhara akanta naji azuciyana na natsu da ita, Hajiya inason na aureta amman saikin bani go ahead” murmushi Hajiya tayi tana kallonshi hannunta takai ta share dan guntun hawayen daya fito daga gefen idanunshi tace “na amince kaje kauyensu ka nemi aurenta amman da sharadin kadawo da Hadiza” dasauri yakalli Hajiya, murmushi tamai tace “Nura no marraige is perfect, kowani aure da crisis din dake ciki har Ummin idan ka aureta you guys will have ur differences and issues but what makes Marraige works and last is the ability to work on your issues understand each other better, forgiveness and moving on without holding grudge, kaga all this fadan yanasa akara fahimtan juna, kuskuren Hadiza shine tunanin datake itada mijinta daidai kuke wanda bahaka bane u are the leader and she’s your subordinate dole ta bika, but I’m sure yanzu she learnt her lesson sabida duk ranan da mace zata kwana awani waje ta dalilin saki ranan bata iya bacci mai kyau ko itace da laifi ko ba itace da laifi ba, saki babban abune, saki is powerful, duk randa aka yishi alarshin Allah na girgiza, duk randa akai saki shaidan na party’s jin dadi, duk inda Hadiza take yanzu tana cikin damuwa sosai, kayakuri kadawo da ita kodan yaranku, kada ka manta Annabi yace akama mace saki daya yakamata tana zaune agidanta ne kacigaba da bata ci da sha har zuwa ka maidata dan haka bring her back karka sabama koyarwan addinin mu” dan ijiyan zuciya yasauke yace “dazu Mamanta takirani tabani hakuri I just told her naji” dasauri tace “yauwa ka kyauta, yaushe zakaje neman auren Ummin? Ka sanar da ita kana sonta?” Girgizama Hajiya kai yayi yace “saina kaita kauyensu zan fada mata inaso sai mun koma
    Munga Dr gobe naji mai zaice game da ke, kafin nasan ranan dazan kaita” shiru Hajiya tayi ita bataso tacigaba da zama agidan nan ahankali tace “koma me ake ciki gobe daga asibiti ka kaini gidan kanin marigayi mahaifinku daganan suma ai zasu dinga iya kaini asibitin ballama nasan magani zaa bani ace nadawo bayan one week, koma menene inason jibi ka maida Ummi gida ka sanar da yan uwanta banson yanda soyayyanta ya kullu aranka tana zama karkashinka shaidan is real kana jina kaje garinsu jibi ayi magana muji me ake ciki idan da hali zasu baka sai adaura auren achan ma sai kaje tareda kanin Babanka da wasu abokan naka, da Meena kuma Ubangiji Allah yasa albarka ni kaina na yaba da natsuwan yarinyar kuma ta kwanta mini arai.

    Ba karamin fada mahaifiyar Hadiza tamataba kuma tace tabama Hajiya hakuri da Nura, washe gari ba dudda idanunta a kone suke amman kana ganinta tai zuru zuru sanda Mamanta tagaya mata Nura yace takoma har ijiyan zuciya tasauke aboye baro shagon tayi wajajen 8.
    Around 9 takai gidansu tana parking motanta Nura na fitowa daga gidan rike da Hajiya da Meena suna hira suna dariya yayi wani irin kyau yana sanye da soft material milk yasa sunglasses a idanunshi, hada ido tayi dasu dasauri ta dauke kai haderai tayi tamau ta taho saida tazo dab dasu tace “sannu ya jiki” bata jira amsan Hajiya ba tawuce ciki tabude kofa ta shiga ta bugo kofan Nura yajuya yakalli kofan Hajiya tace “muje kaga 10 fa likita zai ganmu” wucewa sukayi suka tafi.

    Tunda Ummi taga Hadiza tadawo ta shiga ta natsu tana gama aikinta ta tafi bayan gida a garden ta zauna akan kujeran lilon su Amal da wayanta a hannu tana buga game, ringing wayanta yayi dasauri ta kalla batasan number ba amman tadauka takai kunnenta ahankali tace “hello” anatse Nura yace “Hajiya Ummi” batasan lokacin datace “laaaaa Alhaji yakuri bansan kai bane, ina yini, Ya Hajiya kunkai asibitin? Wani abu kake bukata nayi?” Duk ta jero mishi tambayan atare, cikin kwantacciyan murya yace “Hajiya natare da Dr, tagama ganinshi kuma zan kaita chan Gwarimpa anan zata cigaba da zama gidan kannin Abba na” “okay” Ummi tafadi but zaka iyajin nuna jin dadin ta a muryanta, ahankali yace “kinada katinki na kasa? National identity card?” Dasauri tace “eh inada shi” shiru yasakeyi yace “kituramin hoton shi ta whatsapp sannan ki shirya kayanki gobe zan maidaki kauyenku Adamawa ko?” Maganan yazomata abazata dasauri tace “eh” saikuma chan asanyaye tace “wani laifi nayi”? Ahankali yace “kin manta alkawarin dana miki zan kaiki kiga Gwaggon ki shine zan cika” murmushi tayi taushi tace “Allah yasaka maka da alkhairi” murmusawa yayi shima yace “kinga kayanki cikin kayan danasa gateman yakawo miki?” Dasauri tace “naga slippers dina na dauka, naga wasu kaya duk sainakai store na ijiye” cikeda so yace “nakine akwai wani black abaya mai stones ahannunshi shinakeso kisaka gobe kinji” gyadamai kai tayi kaman yana gabanta tace “to nagode Alhaji” shiru yayi bai sake cewa komiba tagaji da shirun tace “hello” kaman daga sama yace “zaki aureni Ummi?.

    Matan Abuja!
    Matan Abuja!!
    Matan Abuja!!!
    Haaaaa, HADIZA has been making countless reference daku, the women of Abuja come close are you all the way Hadiza ke suffanta ku? Ance idan miya yayi yaji??? Ai dole yaji ne zai saka miyan yaji ko??
    So kunada dogon explanation you guys need to come clean🤣

    But then again all I see in Hadiza is so much soyayya for her man but this stupid mentality nata is leading her astray, why must you be the one to call shots agidan mijinki? To shi mijin is there for what? Name ko fame????

    Hello Ladies both married and unmarried are you learning one or two lessons from this novel nawa???

     

    But again kuma let’s not be sentimental, mu kalli Hadiza da kyau, all she ever wanted is power which is normal akwai dominating mata dama, itama tanason kawayenta susan tana juya mijinta but maganan yayanta is valid sabida kunje Italy saikice saikin maida mijinki Italian???
    Share your 2cents ladies and gentlemen ❤️
    See you asabar💃
    [9/18, 9:17 PM] +234 706 542 1229: 💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

     

    ✍🏻M SHAKUR

  • Matar Makaho 86-87

    Matar Makaho 86-87

    Page8⃣6⃣&8⃣7⃣
    Babane tsaye akan kafarsa yana gyara yayin dake kan bukkar sa, da mamaki Al’ameen yace ikon Allah baba menake ganin nan?

    Da sauri baba ya juya da mamakin ganin Muhammad ya dawo daidai lokacin nan, Alhalin ba lokacin ake tashi aiki ba, lafiya ka dawo yanzun?

    Kai zan tambaya dai baba, na ganka tsaye akan kafafunka, kaida ka karye?

    Zoka zauna muhammad muyi magana?yace yana zama akan taburma.

    Ba musu Al’ameen ya zauna a kusa da baban.

    Muhammad ina fatan kaga abinda nake so ka gani koh?

    Da sauri Al’ameen ya warware rawanin sa, kamar ya baba kuma me kakeso na gani?

    Muhammad Abinda yasani yin haka badon kome bane, illah don naga kaje da kanka gidan sarkin nan, tunda na ganka jikina ya bani wani abu, kamar dake tsakanin ka da muhibbat da muwaddat ya baci sosai, haka sarki ma duk da rabona dana ga fuskar sa, bazan iyya tuna ranan ba Saboda dadewar da nayi bana gani, Amma fa ka sani nasan sarki tunkan yahau mulki, yanda kaga fuskar ka, haka fuskar sa yake sai dai ka nuna masa yaranta?

    Me kake nufi baba bangane ba, wai sarkin da naga fuskar sa a rufe kana nufin yana kama da yara biyu dana gani innan?

    Kwarai muhammad duk da dai akan samu mutum, ya samu mai kamar sa a duniya Amma kaman ku dasu Akwai alamun jini.

    Baba ni bani da kowa a nijar fa bansan kowa a nan ba.

    Toh Amma kaman nin ku, ku hudun nan yayi yawa muhammad?

    Bamu hudu bane mu biyar ne, da kanwa ta.

    Muhammad niba yaro bane, Amma tunda kace haka shikenan, amma dai zaka cigaba da zuwa aiki har lokacin da na yanke akan zancen kafata, tunda ba kariyar gaske nayi ba baikamata na koma ba yanzun?

    Shikenan baba zan cigaba da zuwan,har randa zaka koma aikin, ina su gidado ne tunda na shigo ban gansu ba?

    Sunje kasuwa yi mana sayayyan kayan abinci.

    Tashi muhammad yayi ya ibi ruwa ya shiga band’aki wanka yayi ya shige d’aki ya kwanta, tunanin duniya ya dame sa, duk sanda ya lumshe idanunsa yaran nan yake gani wanda baba yace masa muwaddat da muhibbat wai suna kama da sarki, kenan suna kama dashi, kai shikam bai gane kan Al’amarin nan ba, wani zuciyar na kawo masa wani tunani, amma kokarin tunkude sa yake don yasan abune da kamar wuya.

    Yana kwance har gidado da badaru suka dawo kasuwa, yana jinsu suna ta girki da jido ruwa Amma bai koh fita ba.

    Har suka kammala aikin dare abinka da gidan gauraye, bayan sunci abinci suka wuce masallaci.

    Daren nan sukutum muhammad baiyi bacci ba, sai kusan asuba bacci ya d’auke sa.

    Washe gari muhammad yaje aiki kamar jiya bayan sun gama shayin safe, yaukam had’a masa akayi da yawa a tire, ya wuce dashi falon , da sallama ya tura kofar falon ba kowa a falon sai kamshin turare dake tashi aka tsakar falon, wucewa falon maimartaba yayi a hankali ya tura kofar da sallama.

    Sarauniya ce cikin Alkimba a zaune akan kujera hannunta dauke da kumshen lalle ja abinka da farar fata sosai yayi kyau, sai sarki dake kujeran sa na special kamar kullum fuskar sa a rufe, sai muwaddat da muhibbat dake zaune akasan kushin sai tsohowar nan dake zaune a kujera tana magana da nabila, ke nabila nafa fahimci babu wanda ya bata ku sai lawiza(sarauniya) ace mutum ya dage sai yayi turanci abinda bama amfani muke dashi anan ba?

    Kai mahmah karfa ki manta a abroad nake karatu kuma ashan basu san wani abu wai French koh buzanci ba, da turanci kawai ake Amfani kinga kuma nan gaba muwaddat da muhibbat suna gama secondary suma chan zasu, shiyasa nake saba musu tun a gida mahmah, nabila tace.

    Murmushi sarauniya lawiza tayi tana kallon mijinta da kwata kwata hankalinsa baya wajen su, hankinsa bama a wajen su yake ba, hawaye ne ya cika mata ido, ta rasa yaushe ne ita da yaranta zasu samu lokacin sa? abu tsawon shekaru abu d’aya, tun yaransa na kanana suke korafi har yanzun sun girma har yabi jikinsu, Abban muwaddat……bata karasa ba sukaji sallamar muhammad.

    Amsa masa mahmah tayi, ya karaso cikin falon yana gaidasu da turanci lawiza da su muwaddat ne suka amsa sarki kam koh d’ago kansa baiyi ba bare Amsa gaisuwa, mahmah kam baki ta kama sai kuma tayi shuru batace kome ba.

    a kan table ya aje shayin ya siyaye a kofuna yazo ya aje musu, yana kokarin tashi saiga wasu zaratan maza sun shigo falon cikin sallama, maza ne guda biyu d’ayan zaikai shekara 40 d’ayan kuma zaikai 33 zama sukayi akan kujerun falon suna gaida mah mah da buzanci bayan ta amsa suka juya wajen sarki sauka gaidashi hannu kawai ya d’aga musu.

    uncle Ango, nabila tace tana dariya

    Hararan ta mai shekara 33 yayi ke wallahi bana wasa dake? zan saba miki fa.

    Dariya muwaddat ta sake kai uncle jiya mafa aunty Amarya tazo school namu, ta kawo mana special Anko in mu na yaran Ango.

    Ganin bakin yasa muhammad siyaye musu shayi suma, don shidai duk hiran da suke baji yake ba, kasancewar da yare suke magana, yazo ya jera musu a gaba, har zai mike kawai kafarsa ya taka na nabila,

    ai da sauri ta mike cikin masifa, kai wallahi kaji na rantse maka ka fita idanuna, kai wani irin masifa ne,haka kawai kabi ka sani a gaba da fitina tunda ka fara aiki a gidan na kake takalata tun jiya?

    Kiyi hakuri don Allah bada sanina bane, muhammad yace da sauri yana matsawa gefe duk da sumayya ta masa rashin mutunci a farkon zamansu, Amma bata taba masa a cikin mutane ba, koh zata masa masifa sai insun kasance su biyu, amma wannan a gaban sarki take masa zagi haka bataji kunyar mulki ba? a take yaji wani irin tsanar yarinyar.

    Ke nabila matsalata dake kenan rashin hakuri da rashin kunya, d’aya daga cikin mazan ya fad’a yana mamakin rashin kunyar nabila

    Gaskiya nabila halinki sai Allah ace ke a rayuwar ki rashin kunya ne baya baki kunya a gaban Abba kike irin wannan tsewar kamar ba sarki bane a gaban ki?

    Kunya ne ya kamata da sauri ta sunkuyar da kanta kasa, cikin sanyin jiki ta fita a falon, muhammad ma hakuri ya kara basu ya fita, yana fita yaga nabila tsaye alamu dai shi take jira.

    Wallahi wallahi in baka fita idanuna ba zan maka rashin mutuncin da ba’a taba maka ba, matsiyaci kawai shashasha duk cikin turanci take maganar.

    Kala muhammad baice mata ba ya nufi kofa, sai masifa take Amma shi koh juyowa baiyi ya kara ganinta ba, yana gaba tana baya har suka fitoh a flat in sarki ta shiga nasu, muhammad kuma ya wuce sashen shayi.

    *****************
    Sumayya na bude kofar falon khadija ta gani tsaye da kaya a hannu, da mamaki tace”tsayuwar me kikayi a nan kuma, kika kasa shigowa koh rashin gaskiya ne”?

    Ah ah aunty yanzun nake kokarin shigowa.

    “Aiko kwara ki shigo inkam” tace tana koma ta zauna a kan katifa.

    A hankali khadija ta karaso falon kayan dake hannunta ta kai d’aki, sai kuma ta makale taki fitowa gabaki d’aya fargaba ne a Ranta, ganin fuskar sumayya a hade.

    “Khadija wai tsayuwar me kike a bakin kofar nan ne da bazaki shigo falon ba”?

    A hankali ta shigo falon tana rabe-rabe a jikin falo a nesa da sumayya ta tsaya.

    “Waike khadija meye haka? zama zakizo kiyi muyi magana”

    Kiyi hakuri Aunty wallahi ni bansan da maganar wayar nan ba, kawai sai naga ya bani shine fa danaki karba ya shigo falo.

    “Nidai bance kome ba nace kizo ki zauna muyi magana”

    A hankali ta matso ta zauna a bakin katifar.

    Kallonta sumayya tayi “menene tsakanin ki da kalamu-wahid”?

    Wallahi Aunty babu kome a tsakanin mu dashi kawai fa mutunci muke, kuma aunty koh soyayya zanyi sai nayi da d’an yaron nan?

    “Oh yaro koh lalle kam waya gaya miki ba’a auren yaro ai da ba’ayi da bazan aure yayanki ba”

    Kai Aunty yayana fa ya baki shekaru 4 rus fa, Amma kalamu bazai girmeni da 2 years bama.

    “Kwadaiji dashi wallahi ina nan ina zuba ido, kuma ga wayar taki saiki rike, tace tana mika mata kwalin wayar”

    Amsa khadija tayi da sauri ta ruga d’aki da gudu tana murmushi don wallahi ba karamin son waya take ba.

    “Khadija dawo nan”

    Jin abinda sumayya tace yasa khadija dawowa ta zauna.

    Kinga khadija waya a zamanin nan cikin kaso goma ya kwashe kaso 7 na hanyar lalacewar yara, sauran 3 nan sune ake amfanuwa, ki kula da wayar nan ban baki ita don kiyi abinda ranki yake so ba, kinga waya sirrin mutum ne wani bazaka taba tunanin koh yatsa aka saka masa a baki zai tauna ba, Amma in aka amshe wayarsa abinda za’a gani bamai kyau bane?na barki ki rike wayar nan ne saboda kalamu Amma ki rufamin asiri ki ji tsoron Allah ki kiyaye shiga inda bai dace ba”

    Insha Allah aunty zan kiyaye.

    “Yauwa sannan zaki iyya hawa online Amma ban yarda ki d’aura hoton ki ba sam banaso”

    in Allah ya yarda Aunty

    “Toh tashi ki tafi d’akin”

    D’akin khadija ta shiga ta had’a wayarta daman oready ya saka mata wayar a cherge, ya saka mata sim suka, tana kunna wayar aiko ta shiga latsawa, ya sauke mata facebook whatsApp da instagram harda telegram duk ya bubbude mata account, call ne ya shigo wayar da sauri tayi picking ganin rubuta daya bayyana Nurul-Qalbi a screen in, tana d’agawa taji yayi sallama hade da kiranta da kanwar sa.

    da masifa ta fara magana, Allah ya sauwaka ka zamo yayana wallahi wane kai kaji na fad’a maka.

    Shuru yayi bai mata magana ba, jin baiyi magana ba yasa ta dawowa hayyacinta cikin kunya ta Amsa sallamar, tana masa godiyan waya daya bata.

    baiyi magana ba har lokacin, ita ma shuru tayi kamar yanda yayi,sai da yayi minti biyu yace mata ta hau whatsApp ya mata messenge.

    Kashe call in tayi ta hau whatsApp ganin akwai enough card a wayar.

    Khadija kamfa gabaki d’aya yau waya ya d’auke mata hankali sosai, tana gama girkin ta, ta nuke a d’aki sai hira suke da kalamu, Abin har yaso bawa sumayya dariya daga zaran khadija taji motsen zata shigo d’akin saita kifa wayar ta kama baccin karya, Amma batace mata kome ba tunda yanzun hutun makaranta suke, sai kalamun yazo zata masa fad’a maganar karatunsa karya biye shashanci.

    Ranan fa khadija a d’aki tayi shimfida a kasan tiles ta kwanta da waya a hannu, sumayya ita kad’ai ta kwana a falo.

    ***************
    Yau kwanar muhammad 25 yana zuwa aiki gidan sarauta, zuwa yanzun ya fara fahimtar Halin mutanen gidan sosai, especially nabila ba karamin haushin yarinyar yake jib, bad’an kad’an ba, yau tun Asuba yayi wanka yabar gidansu, kasancewar yaune za’a fara bikin kanin sarki(Ramadan) kamar yanda yaji ana fad’a, shiyasa tun asuba zasu tafi aiki, don shirya shayi mai yawa da zai d’auke mutanen biki zasu wuni sha, duk lokacin da aka nemi shayi a samu kar ya kasance babu, aiko hakance tun safe da sukaje basu zauna ba daman har yanzun ba’a sakar ma muhammad hannu ya girka shayi shi kad’ai ba, anfi sashi ya rarrabawa mutane.

    yau haka ya wuni aiki saiya kaiwa flat innan yana dawowa a bugo telephone in kitchen ace yakai shayi, gabaki d’aya yayi mugun gajiya.

    Haka muhammad sukayi ta fama da aiki har na tsawon kwana 4, sai yau aka d’aura aure, da misalin karfe 4 na yamma liyafa aka had’a a tsakar farfajiyar gidan, manyan sarakuna da manyan kasa ne makil a ciki, masu kudi da shuni, tunda aka fara bikin sarki bai hallaci koh wani liyafa ba sai d’aurin aure da wanda yanzun ake, muhammad ne ya karaso filin yana raba shayi koh wani table yana aje musu nasu dayake taron na mazane da mata, kuma tarone na manya yasa Al’ameen yake bin kome sannu sannu karyayi kuskure koh laifi, kwala masa kira nabila tayi ganin ya wuce table nata da suke xaune da kawayen ta, bai aje musu shayi ba zai tafi next table, kai malam bazaka kawo mana namu shayin ba!!

    Cikin haushi yazo zai dongora mata shayin a gaban table inda suke, by mistake kafarsa ta harde da cafet inda aka shimfid’a a kasa, kawai shayin ya watsale sai jikin kawar nabila, ihu kawar ta saka wanda yaja hankalin jama’a, ai nabila na ganin haka batayi wata-wata ba ta tsinke muhammad da mari.

    Kafun ta sauke hannunta muhammad ya bata wasu tagwayen mari hagu da dama, masu masifar zafi ihu da sake cikin azaba don a tsawon rayuwar ta bazata iyya tuna lokacin da aka bugeta da wayon taba.

    Yayan nabila dake gefen su ne ya mike cikin zafin nama ya d’aga hannu zai wanke Al’ameen da mari, da sauri Al’ameen ya cafke hannunsa cikin matsanannin cin bacin rai ya nuna mustapha da yatsa, jikinsa har rawa yake cikin kakkauran murya yace karka kuskura ka tabani..

    Ai bai karasa maganar ba Ramadan(Ango)daya karaso wajen don abin sosai yajawo hankalin jama’a ganin mai aikin gidan sarauta ya mare yar gidan, cakumo kwalar muhammad yayi cikin zafin nama hade da kai masa naushe a fuska, da sauri Muhammad ya kauce a zafafe wanda yayi sanadin yagewar kwalar rigansa da ramadan yake rike dashi.

    A take Ramadan ya ja da bawa tare da kwalo ido waje, jikinsa har rawa yake yana nuna wuyan Al’ameen, sai kuma cikin sauri yasa hannu akan rawanin fuskar sa zai…………

    ✨Ruqeenjalal✨

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  • Matar Makaho 96-97

    Matar Makaho 96-97

    Page9⃣6⃣&9⃣7⃣
    Duk masu Aljanu sun zuzzube a kasa, muhammad da gudu yayi falon cikin gidan duk da yaga tashin hankali a cameroon Amma wannan tashin hankalin tabanne koh mutum baida Aljanu indai yaga kamila sai tsikar jikinsa ya mike, yana shiga falon yaga an watsar masa da jinjiraye akan kujera, kawayen dada tuni sun ruga daki da sauri ya ciccibi yaransa ya manna a kirjinsa yanemi gefen daining ya tsaya yana jijigasu.

    Ta gefen sumayya kam bayan d’akunan gidan suka nufa mahmah dake dana da jiki, gudu take kamar kazan Agric irin sunyi naman nan, kowa fa gudu yake abin dariya abin tausayi a take ramadan ya kira yusuf ya sanar dashi, Ammar ma abie ya kira don su harga Allah abin ya basu tsoro especially ganin yanda kadangarun makwanta ke biyowa ta gini da gudu suzo wajen kamila, gasu bataliya guda.

    Ba’a d’auki lokaci ba saiga Abie ya shigo shikaran kansa abin ya masa tsoro, Amma sai yayi ta maza ganin nafisa, babban get in ya wangale galala gabaki d’aya ana kallon cikin gidan, nuni yama nafisa dasu fita waje su tsaya, ba musu ganin get a bude ta kora mai kadangaru suka fitoh bakin get suka tsaya suna hangen cikin gidan.

    Daidai lokacin yusuf da mijin nafisa suka iso a tare, don shima wani abokinsa dake unguwan ne ya kirasa akan yaga kamila da nafisa sai gudunsu mutane kiyi.

    A get yusuf ya sauka suka nufo inda abie ke tsaye, yana ma nafisa masifa akan sun shigo sun dagawa jama’a hankali, ita kuma sai hakuri take basa akan tazo tana son ganin muhammadsumayya da hafsa taji labarin duk suna gidan nan.

    Daker aka shawo kan abie da wasu mazajen unguwan akan yayi hakuri aji meke tafe dasu, rukiya yusuf yayi ma masu Aljanun suka farfado, matan da suka gugudu ma duk aka tarkatosu, sumayya kam d’ankwali ya fadi koh takalmi babu, muhammad har lokacin yaransa na hannunsa,shimfid’a manyan taburmaye akayi a gefe guda hudu, gefen maza daban na mata daban kowa aka ajesa, wasu da dama kam sun gudu gida wasu kuma na cikin d’akuna, sun rantse bazasu kara yarda su kara kallon kamila ba, haka masu Aljanu duk an hanasu fita.

    Zama akayi sarki kam kujera aka kawo masa ya zauna, yasa aka shigo da nafisa kamila kam a wajen get akace ta zauna saboda kadangarun ta.

    Yusuf ne ya kalli nafisa, baiwar Allah lafiya kikazo kika d’agawa mutane hankali da wanshan abin?

    Kuka nafisa tasa a hankali ta kalli mijinta, sam bataso yau ta sanar da sirrin ta a gabansa ba tsoron kar auren ta ya mutu gashi batasan inda zata shiga ba.

    Wai ba magana ake miki bane kinsan waye a gabanki kuwa, sarkine da kansa ki kama kanki baya magana biyu?

    Kayi hakuri nasan yau koh naki koh naso sai gaskiya tayi halinta, shiyasa na gwammaci kunyar duniya data lahira, gwara na nemi yafiyar su koh Alhaki zai barni.

    Shuru kowa yayi ya zubawa nafisa ido don jin me tazo dashi.

    Abubuwan da suka faru a shekarun baya da suka wuce, nidai sunanan nafisa Abdullahi kamar yanda wasu suka sani macece maison abin duniya gabin bokaye, bayan nayi aure da mijina saboda halayena ya rabu dani, lokacin na haifi yarinyata kwalli d’aya da Allah ya bamu mai suna kamila, duk yanda naso na koma gidan mijina sam yaki amince wa hakan yasa na shiga islamiyya saboda a lokacin bana zuwa boko sam, mun hadu da safina ne A makarantar islamiyya muka kulla kawance, a lokacin don ance hali sai yazo d’aya ake abota, kawancen mu yayi karfi a lokacin safina ke sanar dani bata da buri saina auren Abdulsalam Amma goggon ta(dada) bata bata goyi baya ba.

    Ni kuma jin haka yasa na bata shawara muje gun wani malami danaji labarin sa, nima so nake na koma gidan mijina ba musu safina ta samo kudi muka kama hanya har Ardo-kwala wajen wani hanshakin boka.

    Bayan munje da bukatan mu yake sanar damu Auren safisa da Abdul bazai taba yuwa ba, mundin yana tare da hafsa don soyayyar su na daban ne kuma mai karfi, dole rabasu shine zai iyya taimakawa ta samu Abdul salam.

    Babu musu mukace mun Amince a rabasu, nima na shaida masa bukatana nason komawa gidan mijina aiko cikin sati d’aya baban kamila ya dawo yace shi kaf duniya saini, na koma gidan mijina aiki yayi kyau sai dai aikin safina shuru baici ba, haka muka koma wajen bokan nan yake sanar damu saimun kawo idanun jariri, kafun mu iyya dishar da soyayyar dake tsakanin su,yaji kwata-kwata baya ganin farin hafsa sai bakinta, sannan bazai iyya rabasu ba sai safina ta had’a da kirsa.

    Babu musu na samo wasu rikakakun yan daba muka biyasu suka sato mana jinjiri, haka ba tausayi aka kwakule idanunsa a take ya mutu koh shurawa baiyi ba, muka kaiwa boka ido yayi aiki aiko koh sati ba’ayi ba rashin zaman lafiya ya wanzu a tsakanin ma’auratan nan, yayinda na baiwa safina shawara ta shiga sacewa mutanen gidan Abubuwa daga karshe ta likawa hafsa.

    Aiko shawarata taci don cikin wata d’aya akayi hakan kuma aiki yayi Abdul ya sake hafsa.

    Bayan nan muka koma wajen boka ya mana wasu aikin gabaki d’aya ya rikitar da dada da yan uwanta akan sai Abdul ya Aure safina kuma duka aikin bokane.

    Bayan auren kuma safina tazo da bukata akan tanason a raba sumayya da Abdul don ta fahimci yana tsananin son yarsa, shawara na bata akan basai mun koma wajen boka ba ita ta d’auki mataki da kanta, amma abin mamaki har Kashe mata aure dukan sumayya yajawo wannan dalili yasata tayi sanyi ganin babu yanda ta iyya da sumayya.

    A lokacin da sumayya takai shekara 14 sai gabaki d’aya hankalin safina ya tashi ganin irin kyaun data tashi dashi, gashi koh a gidan su farin jinine da ita gashi kowa na dangi baida magana sai sumayya, kome sumayya hakan yasa safina fara kishi da sumayyar.

    Kasa hakuri tayi muka koma wajen boka akan a raba tsakanin sumayya da ubanta, dayan gidan su suji sun tsaneta yanda zatayi rayuwa cikin kaskanci, Amma boka yace hakan bazaiyu ba sai an diga magani a idanun yaro matashi mai tashen balaga kuma ya kasance tauraren sa nada karfi, wannan zance da mukaji yamatukar d’agawa safina hankali don ita tana da tsoro ba kamar ni ba.

    Nikam jin haka sai wani tunani ya fado mini na Al’ameen dake likewa yarinya ta, kwata kwata bana sonsa da yarinyana,gashi nayi iyya kokari na babanta ya rabasu yaki itama duk irin lallama da dabara da zan mata ta rabu dashi Amma taki, hakan yasa na kirawo wa’innan yan daban da suka taba sato mana jinjiri na basu hoton muhammad dake wajen kamila na d’auka, na musu kwatancen makarantan su a ranan suka kama muhammad bayan sun bugar dashi suka daukesa har Ardo-kwala wajen boka, sai da akayi sati baya cikin hayyacinsa, ana masa wankan magani da digawa a ido, kafun aka mayar dashi bayan gari aka jefar.

    Wannan shine dalilin makantan Al’ameee, ta karasa maganar tana kuka, jama’ar dake wajen salati suka buga, Muhammad kam gabaki d’aya jijiyoyin kansa su mike bacin raine karara a fuskarsa wanda kallo d’aya zaka masa kasan ran maza ya baci, mikewa dada tayi tsaye habba nafisa mai muka miki? yanzun da haden bakin safina aka aikata wannan mummunan aiki, Sai kuma ta fashe da kuka take surutai ya fara tashi kowa yana furta Albarkacin bakinsa.

    D’aga hannu sarki yayi tare da bada umurni kowa yayi shuru, aiko shurun akayi ya bawa nafisa dake kuka damar ci gaba da bayaninta.

    Bayan an gama aiki kuma yaci, sai dai sam bai kama Abdul ba iyya yan gidan ne sukaji basa kyaunar sumayya sam, sai kuma Abdul ya d’agata ya maidata hostel wanda hakan ya rage musguna mata da ake, kuma hakan baiwa safina Dadi ba, taso abar sumayya a gida taci kwakwa.

    Duk yanda mukayi babanta ya rabu da ita abin ya gagara karshe dai haka mukayi hakuri aka cigaba da rayuwa, kamila ma taki muhammad a lokacin ganin ya makance.

    Lokacin da sumayya ta zama cikekkeyar budurwa hankalin safina ya tashi hassada take da sumayya karta samu mijin dayafi ubanta kudi, koh wani mai mulki kwata kwata so take taga sumayya ta kaskanta a rayuwa wannan dalili yasa muka koma wajen boka daman sumayya nada wani hali na raina wa mutun ArZiki, aiko da halin nan nata aka samo mafita wajen mata magani yanda samari zasuji basa sonta kwata kwata wanda majority zasuce halinta ne ya ja mata.

    Bayan nan sumayya ta rasa manemi sai dai ba’anan gizo ke saka ba, sumayya na samun kudi sama da safina don tana aiki, ga kaunar da mahaifinta ke mata, shawara na bata muje wajen wani bokan aiko munsamu wannan aiki da wanshan ya kasa wannan yace zai mana amma da sharadi, shine sai an nemi makahon yaron da mukama asiri, mu had’asa aure da sumayya wannan ne zaisa ta fita a zuciyar Abie,yanda mukasa muhammad yana kallon baki, haka su dada ke kallon bakin sumayya, kuma duk adadin sex da zasuyi, haka aiki zai kara karfi tamkar muna bawa shuki ruw, tsanar ta a zukatansu zai karu, amma aiki zai lalace mundin aka rabasu misali d’aya na wani kasa d’ayan na wani kasa aiki zai karye.

    Ba musu muka abince daman safina ta shanye kowa a gidan, kowa tsoron ta yake sai abie kawai baya shayin ta, wannan dalili yasa ta samu su babuji da dada ta tilastasu akan aurar da sumayya kuma ita ta sama mata miji ba musu suka amince jiki na bari.

    Mu muka nemi mamman dayaje ya samu muhamamd akan shine uban sumayya, zai basa auren ta amma dayake Al’ameen nada tunani sai yaki Amince wa, karshe dai wajen Bappa suleman akaje don munji labarin yanada son kudi, mamman ya sake masa kudi masu yawa akan zance, wanda gaskiya lamari sharri muka ma suamyya akan tayi ciki saurayin da zata aura ya fasa, a taimaka a had’ata da muhamamd ba musu ya amince da zancen.

    Bayan auren sumayyya da muhammad magani yaci Abdul ya tsane yarsa, duniya kaf babu wanda yaki jini irinta, muma sosai muka sakawa rayuwar sumayya ido duk wani motsenta muna sane dashi.

    A lokacin An jima da sakar mini yata kamila wance ta koma makaranta tana ci gaba da karatunta da bata samu tayi ba, kusam ta dawo rayuwar muahmamd wanda bansan da labarin ba saida taje gidan Adara aka mata duka, a lokacin raina ya baci kuma na jama kamila kunne akan ta rabu da rayuwar yaron nan in tanason kanta da lafiya, amma bata daddara ba ita da kawarta suka je mutum biyu wajen boka………………………………………har sanadin haka ta samu wannan matsala na kadangaru wanda na tabbata Alhakine yake bibiyata.

    Munyi neman duniya wa bokan nan don mu biyasa koh mu basa hakuri ya rabu da ita, Amma ina bamu gansa ba duk malaman da muka kira shuru ba sauki, a lokacin na shiga tashin hankali ita kuma safina a lokacin take jin dadin ta, naje wajen ta akan ta taimaka mini akan zancen kamila koh da kudine don kaf abinda muka tara ya kare a wajen jinya amma haka safina ta murza ido bata tuna irin hallaci dana mata ba ta hanani koh biyar, ni kuma abin yayi matukar bata mini rai hakan ne yasa na d’auki kayan dakina na sayar na biya yan dabanda suke mini aiki tsawon shekaru, akan su kashe mini muhamamd yanda aikin safina zai lalace sannan nima na huce takaicina akansa, tunda ata dalilinsa rayuwar yata ya shiga garari, don haka kowa ma ya rasa.

    Aiko yan ta’andan nan sun bani tabbacin batar muhamamd wanda zancen yaje har kunnen safina, kuma ta zargi nice wanda har gida tazo mukayi fad’a kasha kasha, ta tafi ban sake bi takanta ba, sai kawai labarin rashin lafiyar safina ya riskeni, da kuma dawowar muhammad gida.

    Shine nazo neman yafiyar ku don Allah ku yafe mini sharrin shaid’an ne?

    Ai kece shaid’aniyar in kam, munafuka wallahi bazan taba yafe miki ba har abada kin cuceni kin rabani da matata kin muzguna ma rayuwar yata, Allah ya isa tsakanina daku kuma bala’i yanzun kika fara gani.

    Jin abinda abie yace yasa dada mikewa tsaye da hannu tayi pointing in mutanen gembu, maza maza su tashi su tafi gidan shugaba su tattari safina a yau innan su maidata wajen dangin uwarta babu ita babu safina har Abada, ita tana ta bauta mata ashe shaid’aniya ce.

    Baban kamila mikewa yayi yanzun nafisa har kisan kai kike? toh kiji daga yau bani bake kuma bara kiji na sakeki saki biyu daman babu igiya d’aya a tsakanin mu, ki tattara yarki ku kara gaba koh gidana karki koma don bakizo da kome ba, bazan iyya zama daku ba, kuka nafisa tasa da sauri ta rike kafar baban kamila tana neman yafiyar sa tunkudeta yayi ya kama gabansa.

    Duk yanda yusuf yaso wajen yayi shuru abu ya gagara ganin yan gidan Adara sun rufarwa nafina da duka, waya Ammar yayi wa ofishin yan sanda cikin kankanin lokaci sukazo daker aka kwace nafisa anso tafiya da ita, Amma yusuf ya hana yace a barta kodon Albarkacin kamila dake d’auke da wannan matsala taje duniyace, haka ta mike daker tana koran kamila suka bar unguwan gwanin tausayi.

    Hafsa a ranan kuka tasha bana wasa ba kuma itama ta basu labarin, bayan rabuwarsu akan cikin bai zube ba, jinine ya zuba kuma mahaifinta yace sai an zubar da cikin Abdul salam, baza’a haifa masa a gida ba ganin yanda ransa ya baci yasa kanwar mamarta d’aukar ta ashan ta haifi kalamu bayan haihuwar sa ne matar cousin nata kabeer ta rasu, bayan shekara d’aya da mutuwarta sai ya nemi ya auri hafsa kuma ba musu findon ta amince dayake kowa yasan halin ta macece mai nutsuwa, kuma bayan auren su ta rike yaran kabeer hannu bibbiyu, wannan dalili yasa sa rike d’anta itama kamar nasa hatta su babayo basa nuna wa kalamu ba yan uwansu bane harya girma, bayan kalamu ta haifi yara uku shamsiyya(tayi aure a maiduguri) falmata da musa (auta) duk yaran hafsa ne da suka haifa da kabeer.

    Sosai abie ya nuna nadamar sa kuma ya nemi yafiyarta tare da sanar da ita insha Allah gobe gobe xasu je maiduguri har wajen mahaifinta ya nemi yafiyarsa wannan umurnin yusuf ne kuma hardashi zasu.

    Washe gari haka aka tattaru duka aka wuce maiduguri duk yanda akayi sumayya ta zauna saboda yanayinta amma ina tace da ita za’aje taga kakan ninta da kanwarta shamsiyya, ba yanda aka iyya haka aka tattaru harda Ammar suka wuce maiduguri.

    Da isarsu suka sauka a gidan sarki yayinda Ammar ya nemi Alfarmar su muhammad su bisa gidan Uncle nasa su kwana, bazasuji dadi ba in sukasan yazo Maiduguri ya kwana a wani wajen, ba musu ramadan da muhamamd suka bisa jin yace musu babu kowa a gidan daga uncle nasa sai matarsa da yarsu babba.

    Unguwane mai kyau suka shiga cikin wani gida madaidaici mai kyau,sunyita sallama Amma shuru ba’a amsa ba, hakan yasa Ammar nufar kofar falon ganin kamar a bude, aiko yana turawa yaga kofar ta bude, bismillah yama su muhammad ba musu suka shiga da sallama, amma shuru.

    Macece zata kai shekara 44 zaune akan sallaya a falo ta fuskanci gabar rabin fuskar ta kawai suke iyya hanga zaune take tayi tagumi kana ganinta kasan tayi zurfi a tunani.

    Girgiza kai Ammar yyi saboda wannan abin ba sabo bane agunsa, abune da ya saba da ganinta a haka, da sauri ya nufi wajen da take ya tabata Aunty!!!!!

    Da sauri ta dawo hayyacinta, ta dubesa a dakile tace Ammar yaushe kazo?

    Yanzun nazo kina sana’ar taki ina zakisan na shigo?

    Shuru ta masa alamu dai batada yawan magana, koh ince damuwa ya maidata haka.

    Ganin ta masa shuru yasa sa tambayar ta, aunty ina mom?

    Basanan Ammar kai kad’aine?

    Ah ah Aunti babba nida abokai nane, yace yana nuna mata su Ramadan dake tsaye, yayinda shi kuma muhammad ya zuba ma fuskar matar ido yana kallonta, kallo irin na tsana, koh shekara dubune bazai manta da wannan fuskar ba.

    Ai tana kallonsa jikinta ya soma rawa da sauri ta mike tsaye sanye da hijab, tana nunasa da hannu sai kuma ta yanke jiki zata fad…………..

    ..
    ✨Ruqeenjalal✨🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 2

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 2

    EPISODE 2️⃣

    Binsu da kallo Nura yayi yadan sauke ijiyan zuciya koba komi tayi shiru yanzu, komawa falo yayi yakunna wuta yazauna kan kujera, yadawo ko chanza kaya baiyiba, bai wanka ba ranshi yabaci, kunna tv yayi yana kallon news dudda hankalinshi bawai yana wajen bane dan damuwa ne cike fal aranshi. Yana zaune awajen Amal tafito da kanta rikeda karamin bowl da aka soya kwai mai kyau aciki tace “Daddyyyy Oumu Oumu” tana nunamai bowl din, dan murmushi yayi tazo kusada shi daukanta yayi yazaunar da ita saman kujera kusadashi tahauci, ruwa Ummi tabiyota dashi a water bottle nata mai kyau ta ijiye agabanta takoma chan nesa dasu wajen dinning tazauna akasa duk atakure take dan batama saba ganin mai gidan ba, kusan 1yr tana aiki agidan itada yaran sukafi zama agidan nan, sai yau ne take ganinshi hakan yasa duk takejinta atakure. Dauke kanshi Nura yayi dagakan tv ya kalleta yanda tazauna akasa kaman wata mara daraja irin yar maulan nan dukta takure tana wasa da hannunta bini bini tana kallon Amal dakecin kwai abinta da hannu kusada shi yasa yadanji wani iri, he always hate yan aiki to be honest yaune rana ma na farko daya taba kallo fuskan yarinyar nan dake musu aiki agida kuma this is almost 1yr take gidan nan, ba yabo ba fallasa yace “jeki kwanta kiyi bacci” kanta akasa cikeda respect tace “saita gama cin abinci na wanke mata hannu na gyara wajen nasata bacci tukunna zan iya bacci” dan jinjina kai yayi saikuma yayi shiru bai kara cewa komiba, yakai hannunshi yataba wuyan Amal din jikinta yadan rage zafi maybe sabida ruwan daya watsa mata neyamaida idanunshi kan TV, tass Amal tacinye kwan ta cillar da plate kasa tace “akoshi” dasauri Ummi ta taho ta duka tadauki plate din da cokalin adan kunyace dan she’s not comfortable yanda Baban ke wajen tamika mata hannu tace “zo aje a wanke hannu” makemata kafada Amal tayi zata kama Babanta da hannun kwai dasauri ya matsa yace “je princess awanke miki hannu” turo baki tayi takalli Ummi dake kallonta, cikeda dabara da iya wasa da yara tace “zomuje muyi wasa da pampoo akitchen” wani kalan dirkowa Amal tayi abin harsaida yabama Baban mamaki tazo gaban Ummi da dugudu tace “ruwaaa, pampoo” da sauri Ummi taduka ta dauketa tana murmushi tace “yauwa Amalulu na muje, idan Aman yatashi gobe shima mu soyamai Omu Omu ko”? Gyadamata kai Amal tayi sukatafi kitchen, dan ijiyan zuciya yasauke to some extend kam she’s good with kids kawaidai shi bayason yan aiki ne and he don’t trust hygiene dinsu, dan ijiyan zuciya kuma yasauke idan ba yan aikin ba yasan Hadiza ba aikin nan zatayi ba ko sama da kasa zata hade.
    Tass ta wanke mata hannu ta share mata baki tare suka wanke plate da spoon din tace “yanzu sai bacci ko, nagoyaki”? Gyadamata kai Amal tayi Ummi ta duka tace “yauwa babuuu Amalily” da gudu tahau bayanta tana murna dariya tayi bataso tasake fitowa daga kitchen din hakan yasa sai kawai tacire dankwalin kanta ta warware ta goyata dashi, wasu manya manyan kitson hannu ne akanta shiku ya tsufa sosai amman tanada bakin gashi mai kyau da santsi, zagaye kitchen din tashigayi da ita tana jijjigata tana mata waka ahankali. “Amal Amal yar gayu, Amal yar kyakkyawa, Amal yar fara saidai tana fitsari agado” dan ihu kadan Amal tayi tana hamma Ummi tai dariya tace “to nadaina Amal bata fitsari agado, Amal jaruma ce gimbiya mai kafafun zinare yi bacci to” haka tadinga jijjigata tana zagaye katon kitchen din nan da ita dantai bacci. Gajiya yayi da zama afalo dan dama jira yake agama wanke mata hannu yadauketa suje sama gashi kusan 30min shiru basu fito daga kitchen ba, baki yabude zai kwalama Yarinyar kira yakasa, shi wlh ya manta sunanta kuma is somehow yakirata yar aiki, dan tsaki yayi yamike tareda kashe tv yatafi wajen kitchen din, kofan abude hangota yayi tana tafiya a kitchen din tana jijjiga Amal data fara bacci abayanta suna zagaye, ko kadan bata luradashi ba dan bekai gaban kitchen dinba, yanda yaga take zagaye take jijjiga Amal abayanta gently tapping her bombom ta saman zanin goyo tana mata wake haka sai kawai hakanan yaji yaji wani iri aranshi, he can’t even understand idan guilt yakeji ko anger, wannan wani kalan rayuwane ace mahaifiyar Yarinyar na bacci anbar yar aiki da yarinya bata runtsaba tsakar dare, tun 9 yanzu kusan 3 idanunta biyu, is she not human being ita? Ko machine ce? Kowa fa deserves this sleep, dare mahutan bawa, koda aikinta ne there’s nothing bad idan Maman yarinyar natare dasu to help her out, abin is really really somehow azuciyanshi, jiyayi ranshi yamai badadi dauke kai yayi tareda dan gyaran murya batare daya karasa kitchen dinba, dasauri Ummi tajuyo jin gyaran murya, batare daya kalli kitchen dinba yace “kawota taje ta kwanta” dasauri Ummi tace “to” goyon tashiga kwancewa kafin ta sauketa tafara jan dan kwalinta ta jefa akanta sannan ta dauketa a hannu tariga tai bacci ta taho ahankali har zuwa gabanshi tamikamai ita tace “gata Alaji” dan juyowa yayi yakalleta ahankali yasa hannunshi ya karbeta yace “sannu da kokari, jeki huta kema” “to” ta amsa tana tsaye awajen, wucewa yayi itama tawuce falo takashe wuta sannan takoma dakinta ko 1min bata karaba sai bacci.
    **

     

    Wuraren 5 yabude ido sabida zafin jikin Amal data kwana dakinshi, tashi yayi zaune yakai hannunshi yatabata yarinyar nan needs hospital wucewa yayi yashiga bayi ya watsa ruwa yafito daure da alwala yawuce yasauka kasa motsi dayaji a kitchen yasa yawuce kitchen yar aikin yagani tana sharara da goge goge jin knocking kofa yasa ta dago kanta dasauri ganinshi yasa ta duka tace “ina kwana Alhaji” juyawa yayi yace “lpy lau kibar aikin nan kije ki shirya Amal ina dawowa daga masallaci zamu kaita asibiti” bai tsaya jiran amsanta ba yawuce, wanke hannunta tayi ta tafi sama azuciyanta tace Allah sarki Amal dina, dakinta taje ganin bata ciki yasa ta tafi dakin Aman yana baccin shi shikadai batanan to ko dakin Maman take bude dakin tayi da sallama bata wajen hakan yasa tai tunanin dakin Baban, idan da sabo tasaba shiga dan ita ke gyara dakin ta wanke bayi, bude kofa dakin tayi tadauki Amal dake bacci tawuce dakinta wanka tamata ta shiryata tsaf itama tai salla nan da nan tai parking jaka taje kitchen agurguje tamata air frying chips da sausage tasa mata a cute flask nata da ruwa tahada komi da yaro ke bukata, itama taje ta chanza kaya zuwa wani dan dogon Riga baki ba laifi yanada kyau but irin outdated one din nanne shima Anty tabata ta yana gyalen akai tazauna a falo rikeda Amal da yanzu bamata da karfi, shigowa yayi gidan ganinta zaune akasa afalo rikeda Amal data shiryata tsaf in this short time yasa yace “let’s go” dan kallonshi tayi saikuma ta tashi da sauri, harya zauna agaban mota yaga tafito ta kinkimo Amal da katon jakan a hannu tana tafiya da kyar kaman zata fadi yasa kawai yafito yataho da sauri, tsayawa Ummi tayi gabanta nafaduwa ganin yanda ya dumfarota, hannunshi yamika mata yace “bani jakan” bashi tayi yajuya itama tabishi bude bayan motan yayi ya ijiye jakan ya tsaya yana jiranta tana tahowa tashiga baya rikeda Amal saida tai settling down yamaida kofan yarufe yakoma gaba yashiga yatada motan yaja duk wani motsi da Amal zatayi saita tambayeta menene, ciwo, zafi, me kikeso, zakisha ruwa sannu ko Amal dina abinda baitaba ganin Mamanta tayiba.

    Wani babban asibiti suka tafi wannan karan shiya sauko yabude musu baya da kanshi yadauki jakan yabar mata Amal dayaga tai lakur ajikinta suna shiga aka karbesu sukai ciki office na Dr suka shiga, wani baturen Dr ne yace “meke damunta”? Kallon Ummi Nura yayi yace “meke damunta” ahankali tace “zazzabi take tun kwana biyu bata iyacin abinci, but nafada ma Anty tadubata tace chanjin yanayi ne, jiya tanata tari sai zazzabi, kuma idan tashiga flowers na gidanmu jikinta na kaikayi, idanunta namata kaikayi shima, jiya batai bacci ba kagani kuma yanzu batada karfi ko kadan” tanuna Amal dake jikinta kaman zatai kuka, sosai Nura ke kallonta saikuma yadauke kai yama Dr bayani da turenci Dr yace “za’a basu gado cus tana running temprature da yawa kafin a debi jininta aga meke damunta, tashi yayi zai debi jininta da sabuwan alluran daya bude dasauri Ummi takalli alluran tadan kankame Amal ajikinta, ahankali Nura dake lurada ita yamika mata hannu yace “kawota” batai musu ba bashi Amal tayi Dr yadebi jininta hawaye taruwa yayi a idanunta yabda Amal ke kuka nan da nan aka kwantar dasu awani private room sai kuka Amal take tana mikama Ummi hannu, kasa zuwa Ummi tayi ganin Babanta natare da ita tashi Nura yayi yakalli Ummi yace “zo ketake nema” kaman jira take dasauri taje rungume Amal Ummi tayi tace “likitan nan ko saimun kaishi wajen police yama Amal allura da zafi”? Gyadamata kai Amal tayi a shagwabe, Ummi tace “sannu ko, zakisha Capri ri”? Dan yatsine fuska Nura yayi irin menene Capri ri kuma, Gyadamata kai Amal tayi, dasauri Ummi tabude jaka tadauko caprisone tace “tadaaaaa” wani kalan murmushi Amal tayi dashi kanshi Nura saida yayi murmushin yadan tabe baki yaciro wayanshi aranshi yace “omelette Omu Omu, Caprisone kuma Capri ri ikon Allah” tana cikin bata juice din wayanta dake pocket din jakan kayan Amal yashiga ringing da sauri tasa hannunta daya taciro wata screen touch Vivo ne dataji jiki sosai ganin Anty yasa ta amsa takai wayan kunnenta cikeda girmamawa tace “Hello Anty ina kwana” daga ta dayan bangaren Hadiza tace “kina ina Aman yatashi”? Cikin kwantacciyan murya tace “Uhmm Anty munzo asibiti da Amal ne, jikinta ya rikice” Hadiza najin haka tasan mijinta ne yakawosu asibitin cikeda masifa tace “to yanzu wazai yima Aman brush da wanka yabashi breakfast eh? Ko nine danake shirin fita aiki yanzu zan tsaya nayi all of this, maza maza ki bar Amal wajen Babanta ki kira bolt yazo ya maidoki gida ai nakoya miki yanda ake yin bolt dan nasan nace kifita kije kibi mota along bacewa zakiyi babu inda kika sani, maza maza kira bolt and come back home kima Aman wanka kibashi breakfast ki shiryashi yatafi school kafin school bus yazo keko school bus yazo idan sun tafi ki kira bolt ki kaishi school din dakanki, kina jina tunda ke mahaukaciya ce dakikiya yar kauye dayace kizo kutafi asibiti bazaki iya gayamai zakiyi aiki ba kika bishi, nabaki 3min karki bari su cika ban ganki agidan nan ba, sabida jakanci da dakikanci irin na yan kauye ina biyanki danki kulamin da yara da gida akanme zaki wani asibiti bayan babanta natare da ita, idan kinsan kin gaji da aikin ne bazaki iyaba ki gayamin na sallameki wata tazo ha’aa nida kudi na ko yan aiki guda dari nakeso zan samesu wlh yau yau din nan, zan koreki wlh kika batamin rai” da sauri Ummi tace “kiyakuri Ant……” dip ta katse wayan tashi Ummi tayi dasauri tace “ina zuwa Amal” tajuya dasauri hada ido tayi da Nura dake kallonta hakan yasa da sauri ta tsugunna daganan wajen gado tace “Alhaji zanje gida Anty tace nabar Amal awajenka zanje in shirya Aman yatafi school” kai tsaye yace “koma ki zauna bazaki ba” dasauri ta kalleshi ganin yacigaba da danna wayanshi yasa takoma ta zauna ahankali but gabanta sai faduwa yake kusan 4min da gama wayan wayanta yahau ruri hannu yamika mata yace “bani wayan” daukan wayan tayi tazo har gabanshi ta duka tabashi wani iri wayan yamai a hannu screen din dukya faffashe wannan ai zai iya yagamai fatan kunne saida wayan yakatse yay dialing number ta da wayanshi yatashi tareda ijiye wayanta kan kujera yawuce yafita dan baiso wani yanajin wayanshi da ita waje yafita wajen parking space daidai ta amsa wayan kafinma yayi magana cikin fushi da ihu tace “sabida kaike biyan salary nata kahanata zuwa ko to daga this month kadaina nizan dinga biyan salary nata lemme be in charge of her nai controlling nata to my satisfaction Alhamdulillah inada kudina, but akan mema zaka hanata dawowa ga Aman ko brush baiyiba bai wanka ba yana kuka yunwa yakeji kuma kasan zan tafi shagona yanzun nan maisa kakemin haka? What kind of man are you? Why do u always look for opportunity to belittle me kanunama kowa banda power over anything in our house eh? What is your problem dani? Bakin ciki kake inada kudi kafison kullum ina kasanka ina rokonka do this for me do that for me”? Shiru Nura yayi saikawai yaciro wayan daga kunnenshi ya katse wayan dan talking to Hadiza is impossible, ita ko kunya bataji ta haifi yara saidai wasu su tayata kula da yaran, gatada baki kaman reza talking to her is just too impossible dukan motanshi yayi ya jingina da motan yayi shiru is this how life zai cigaba da tafiyan mai? Bayagane gaba balle bayan Hadiza, ance communication is a key in Marraige but communicating da Hadiza is impossible kafin kayi magana daya tal tayi dari da hamsin, babu one single abu datakemai na mata, she doesn’t take care for him, karma aje batun girki he can’t even remember the last time da Hadiza tadau ruwa ruwan nan dai bottle water tabashi yasha, he can’t even remember wen was the last time yaci abinci agidanshi, shi bayacin abincin yan aiki itakuma batayi saidai kullum yaci abinci awaje ko agidan abokai, tun yana korafi yan aiki na shigo mishi daki harya dena dan yagane idan basu gyaraba dakinshi baza’a taba gyaramai ba, he can’t remember the last time data gaidashi, is as if he doesn’t exit awajenta whenever he tries to talk to her tace yafara fitina da bala’in da korafin da mita shi yabarta tagaji, she’s not remorseful akan abubuwan datake she feels itadashi equal right sukedashi sabida tana matanshi he can’t step and match her ko control her, sabida tana mace doesn’t mean zata kwantarmai dakai that’s just her mentality, Hadiza is very stubborn ga baki Ya Allah, wlh yagaji baison mata biyu dan ko daya bakar wahala take bashi aduniya, baison broken home dan yataso Mamanshi bata tare da babanshi he don’t want that ma yaranshi, baison neman matan banza abinda baiyiba yana yaro shine yanzu zai fara when he’s approaching 50 haba bazai tabayiba but he’s just tired yarasa ta ina zaibi ya gyarama Hadiza zama ya gwada zama waje yakai 1-2 nadare amman ko ajikinta yadawo ma tai bacci abinta he’s just soo tired of everything he’s not happy in his home.

    Wajajen 10 aka sallamesu da magunguna a hannu suka dawo tunkafin sukai gate na estate dinsu ya hango Aman dinshi kan kujeran security da pajamas ajikinshi da ledan popcorn idanunshi sunyi jaa, jiyayi zuciyanshi takama da wuta parking yayi yafito dasauri security dayake zaune kusada shi yace “Yallabai barka da dawowa Madam ta ijiyeshi anan gashinan yanata kuka yace yunwa yakeji shine na saya mishi Popcorn yamai jiki”? Sabida yanda ran Nura ke daci gyadamai kai yayi Aman yarike hannunshi yakalli fuskan Baban kaman zaiyi kuka gwanin ban tausayi, kaman dan maraya yace “Daddy where’s Anty Ummi am hungry she’s the only one that gives me food and play with me, Mommy never gives me food or play with me” suppressing anger dinshi yayi yaduka ahankali ya shafa kan yaron yace “muje Anty Ummi na bayan mota da princess don’t cry again okay”murmushi yayi yay bayan mota da gudu yabude yashige shikuma ya tsaya yama security godiya tareda bashi kudi sannan yazo yabude gaban mota yashiga ya zauna yaja mota ta glass na gaba yake kallonsu duka yaran sun kankame Ummi suna hira da ita, sai biye musu take kaman yarinya itama, wlh zaka dauka itane mahaifiyar yaran kawai dan ita black beauty ne yaran kuma fararene tas su kaman turawa amman kana ganinsu kaga strong affection tsakaninsu, sunma manta dashi a motan sai hira suke Aman yarike Ummi gam yanata zuba kaman bashi yayi kaman orphan dazuba, akofar gida yayi parking duk suka sauko tana rikeda Amal, Aman shima yarike mata hannu suka wuce ciki yabisu da kallo direct kitchen suka wuce zaunar dasu Ummi tayi kan kujerunsu dake kitchen din dake gaban island, tashiga yimusu girki agurguje dan Aman yunwa yakeji tana attending to them, ta dafa lafiyayyen taliya na manza fevorite dinsu da kaza ta zuzzuba musu a plate tajuye sauran kuma a kula mai kyau takai dinning ta ijiye sannan takoma kitchen tana bama Amal abaki dantaci da kyau, koda yashigo gidan dan tuntuni yana waya awaje kamshi ne yamai sallama wani kalan yunwa yaji yanaji dinning yaje yazauna kaman wanda ke tsoron wani abu bude kulan yayi daidai Ummi tafito da tray na ruwa da fresh juice a hannu dantaji zuwanshi ta ijiye kan dinning taduka tace “ko adafa wani abune daban Alhaji” girgixa mata kai yayi yace “a’a wannan yayi” tashi tayi takoma kitchen, kaman mai tsoro yadau fork yasa yadebo kadan yakai bakinshi yatauna dadin dayaji wlh saida kunnenshi yayi siiiii, baisan sanda yadauki plate yadeba ba shi arayuwan shi yanason home made food rashi yasa almost few restaurants ne baisaniba a Abuja ba yaune rana na farko dayaci abincin yar aiki and wlh yamai dadi sosai tass yacinye yatashi ga mamakinshi rawa yaga tanama Amal tana kai abinci bakinta da wayau dantaci, ga magani dayaga ta fito dasu ta zuzzuba a marfi dan an fadamata yanda zata bata asibiti, shima Aman yataso yana tayata rawan sunama Amal rawa dukansu biyun tana dariya sosai fa tana karban abincin tabata maganin ta shanye tass ba gardama ko kakarin amai suna mata waka Aman na tafi kaman suna studio, jinshi kawai yayi yana murmushi ance some yan aiki suna faking love ko sabida parents na yaran but shi all he sees ana is genuine love, kuma yaran loves her suma dearly hakanan samin kanshi yayi yana kallon Ummi sosai, yarinyar black beauty ce tanada tsayi akalla zatai 23 ko 24, yar kauye ce from her dressing but she’s kind and tanason yaran shi kuma her smile is contagious dan gashi shima yanata yi, sannan the way she dance is annoyingly cute, kaman Ummi taji ana kallonta juyowa tayi da fuskanta ta kallo falon karaf suka hada ido da Nura dake kallonta tana rawa ma Amal.

    Wanna talk to me about something??? Chat me up anan;
    wa.me/+2347012181461
    [9/18, 9:17 PM] +234 706 542 1229: 💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

    ✍🏻M SHAKUR

    Novel din nan is FREE bana kudi bane.
    Chat me up don saki a group

    wa.me/+2347012181461

  • Matar Makaho 88-89

    Matar Makaho 88-89

    Page8⃣8⃣&8⃣9⃣
    Da sauri muhammad ya damke rawanin sa, ya hana Ramadan bude masa fuska, menene haka? banaso karka kuskura ka bude mini fuska.

    Har lokacin jikin Ango rawa yake cikin mamaki yace a ina ka samu sarkan nan, waya baka wanene kai?da karfi yace security.

    Jama’an gurin duk sun mike banda sarki dake zaune akan kujera duk rikicin da ake baiko d’ago kansa ba bare yasan abinda ke faruwa.

    Mustapha ne yayi magana a rude wallahi sarkan ne, sarkan magadan masarauta ne, a ina ka samo sarkan nan?yana maganar yana kai hannunsa wuyan Al’ameen zai duba sarkan.

    Da sauri Al’ameen ya buge hannunsa, Shuru yayi yana kokarin barin filin, da sauri Ramadan ya jawo sa baya yana kwalawa Yayansa kira, da sauri sarki ya juyo yana kallon Ramadan da mamakin kiran gona da yake masa?

    Yaya sarkan magada ne a wuyan wannan me kawo shayin, kuma yaki bari aga fuskar sa, bamu yarda dashiba suspect ne?

    Ai kafun ma ya gama magana saiga sarki ya sauko a kujera da hanzari ya nufi inda suke tsaye, daga isarsa hannu yasa a kamo sarkan yana kallo sai kuma jikinsa ya fara rawa ya kamo rawanin fuskar muhammad.

    Da sauri muhammad ya dafe Hannun sarki dake kan fuskar sa yana girgiza masa kai, alamun rashin son hakan.

    Shima sarkin girgiza kai yayi, hakan yasa muhammad sauke Hannunsa akan na sarki.

    A Hankali yake warware Rawanin kansa, tsaf gashinsa ya bayyana mai masifar tsawo da sheki, a hankali ya warware na fuskar sa, da sauri ya dafe kirjinsa cikin tsananin mamaki da sauri yace muhammad!!!!!bai karasa ba kawai hancin sa ya fara tsiyayo da jini a hankali ya fara lumshe ido sai kuma ya yanke jiki zai fadi, da azama muhammad ya taro mahaifinsa da sauri ya rungumi abinsa cikin matsanan ciyar mamaki jin sarkin ya Ambace sunan sa.

    Zuwa fadawa sukayi aka kewaye sarki muhammad ne ya ciccibi sarki har cikin flat nasa, atake gida ya rude da koke koke, ga masu tsananin mamakin muhammad da abinda ya had’asu da sarki harya Ambace sunan sa?

    Bayan Ankai sarki d’aki likita da abokan aikinsa suka rufu a kansa, yayinda Ahlin gidan ke make a babban falon fada, daga maza har mata harda wa’inda muhammad bai taba ganinsu ba, mikewa yayi zai fita a falon da sauri Mahmah ta riko hannunsa, ina zaka yaron nan?

    Gidan mu mana ba aiki bane ya kawoni mama?yace yana kallon nabila dake rakube a jikin kujera fuska jajjawur ga jini ya taru a idanunta da gani dai ta maru.

    Wani irin ka tafi kuma kaje ina baka ga Halinda d’ana yake ciki ba? kuma na tabbata yana farfadowa kai zai nemi gani.da gorancen hausar ta take magana.

    Toh ni kuma so nake na tafi gida ranki ya dade, in Allah ya kaimu gobe ai zanzo aiki duk maganar da zamuyi sai muyishi?

    Ramadan ne ya mike,Hala nan dajine da bazaka iyya kwana a cikiba?

    Ban saba kwana gida irin wannan ba, kasa bacci zanyi, yace yana fita a falon babu wanda yayi yunkurin hanasa, sai rakasa da ido sukayi.

    Muhammad na zuwa gida gabaki d’aya abin duniya ya damesa, amma baicewa baba kome ba, shima baiyi magana ba duk da yaga sarkan wuyan Al’ameen Amma baice kala ba.

    Yau koh abincin dare kasa ci yayi, badaru da gidado ne sukaci gabaki d’aya jikinsa yau A sanyaye yaki kome yanayi a sake kamar mai ciwon fata.

    Har dare bai rumtsa ba, tunani kawai yake a ransa, donshi dai bai gane inda abinnan ya dosa ba, menene Alakansa da mutanen nan shi zaman kasar ma ya isheshi kuma ya rasa hanyar da zaibi yabar kasar gabaki d’aya, yau wani irin kewar iyalinsa yame dason jin duminta, ba irin tambayar duniya dasu gidado basu masa ba Amma bakome yake ce musu.

    Da misalin karfe 2:30 sukaji ana bugun kofar gidan, babane ya fita zai duba koh lafiya yayinda muhammad ke kwance duk da idanunsa biyu Amma bai mike ba.

    Baba bai jima da fita ba sai gasa ya shigo d’akin su muhammad, mikewa yayi yana kallon baba.

    Muhammad ka fitoh ana sallama dakai?

    Da mamaki yace dani kuma baba, sallamar ma tsakar dare?

    Ka tashi daga gidan sarautane.

    Gaskiya baba kace musu su bari sai gobe, koma menene in gari ya waye sai ayi bawai a tadani tsakar dare ba kamar tashin duniya.

    Muhammad yaushe ka koma mara kunya ban sani ba?

    Kayi hakuri baba

    Tashi kawai kaje kaji da wani sako aka turosa?

    Mikewa yayi kawai ya sanya kayansa ya fitoh a d’akin, kallon mutumin da aka aiko wajen sa yayi, lafiya malam?

    Lafiya muhammad ana neman ka a fada.

    Tsakani da Allah in Ana son ganin mutum sai azo tsakar dare ya kirasa ai naga gari zai waye?

    Babane ya kallesa, muhammad ka iyye bakinka banason irin wa’innan kalami, bai dace da kai ba, don haka ka bisa kuje bakasan menene dalilin kiranka ba, ya kamata kaje kaji.

    Baiyi magana ba kawai ya nufi hanyar kofar gidan, binsa a baya mutumin yayi daman da mota yazo ba musu muhammad ya shiga suka wuce.

    Daga isarsu masarauta gidan kaman rana koh ta ina fitilune haske kaman farin wata, ga mutane a tsatsaye kamar rana bakin dake gidan duk basu tafi ba, Al’ameen na fita a motar gabaki d’aya aka ringa binsa da ido har suka ratsa babban falon sarki, suna shiga mahmah da lawixa harda su ramadan muwaddat nabila duk suna cike a falon wasu kamma kuka suke fuskar lawiza da mahmah jazir alamu kuka sukasha, da sallama ya shigo falon amsa masa sukayi suna mikewa tsaye gabaki d’ayansu, binsu yayi da ido sai kuma ya nufi kofar d’aya falon, ya shiga yana shiga duka suka rufa masa baya zuwa ciki, tunda ya tinkare kofar bedroom yake jin salati ga sunan sa da ake kira da sauri ya cusa kansa adakin.

    Sarkine kwance akan gado yana tari jini na biyo bakinsa yana Ambatun sunan muhammad, ai Al’ameen baisan lokacin da yayi super ba ya isa garesa koh tsawon shekaru nawane bazai taba manta wannan fuska ba bare shekarun da baiwuce a kirgasu ba, hawaye ne ya cika masa ido ganin halinda mahaifinsa abin sonsa ke ciki, duk da ya rayu da takaicin gudunsu dayayi Ya kuma sha Alwashin duk randa ya gansa zai basa mamaki shima, amma bai d’auka zai gansa a irin wannan halin ba, karasawa yayi garesa a hankali ya kamo hannayensa dake dafe a kirjinsa cikin kuka yace Abbajoooo!!!me nake gani haka ka rufa mana asiri kar maraicin ya mana yawa?

    Ai jin muryar sa da sauri yusuf ya mike ya rungume d’ansa a zaune, tunda ya hau karagan mulki ba’a kara ganin hawayen saba sai yau, hawaye ne yake siyaya a idanunsa, ganin haka yasa muhammad fashewa da kuka mai matukar karfi yana banbare Abbajon sa a jikinsa, tare da kallon doctor dake gefe, habba bawan Allah jini nefa kebin bakinsa kun barsa haka?

    Kayi hakuri yallaboi wallahi tun da ya farfado anyi anyi ya tsaya a basa taimako yaki gashi ciwonsa baison damuwa Amma yaki ya saida hankalinsa.

    Jin haka yasa muhammad kokarin mikewa tsaye,Ai da sauri yusuf ya rikosa da karfi tamkar uwar da za’a rabata da jaririnta, fuskar muhammad ya rike sai kuma ya soma magana a hankali, tabbas jini yafi ruwa kauri, babu tantama wannan jini nane muhammad nane koh babu sarka a wuyanka akwai alamun jini muhammad ku yafe mini.

    Ah ah Abbajo ka rufa mini asiri karkace haka kayi hakuri ka rayu damu yana magana yana kuka.

    A hankali sarki yace muhammad dukkan mai Rai mamaci ne in lokaci yayi dole mu amsa kiran mahalincin mu.

    Don Allah Abbajo kabar irin wa’inan magana, likita kazo ka taimaka masa, da sauri likitan ya maso da taimakon muhammad suka gogi masa jinin dake bakinsa ya taimaka masa ya shiga toilet ya shanja kayan daya baci, daidai ya fitoh har muhammad ya sauya zanin gado.

    Yana fitowa ya kwanta likitan ya d’aura masa ruwa da Allurai ya fita, a hankali yusuf ya kama hannun d’ansa sosai ya zurawa muhammad ido yana kara tasbihi a zuciyar sa yaushe yabar muhammad yaro karami d’an shekara 13 Yau shine ya zama cikeken mutun tamkar shi a lokacin da ya barsu muhammad?badon shekaru ba koh yau duk wanda yaga muhammad zaice shine.

    Na’am Abbajo.

    Ya Aishan Adara?

    Jin tambayar da ya masa sai da gaban sa ya fadi, a halinda mahaifin sa yake cikin nan bai kamata ya kara d’aga masa hankali ba, cikin sanyin jiki yace, Tana Lafiya Abbajo.

    Murmushi yusuf yayi cikin karfin hali, nasan xuwa yanzun ta rage masifa koh? nama san itama ta tsufa kamar ni?

    Hhh bata tsufaba tana nan da kyawun ta daka sani, kuma yanzun sam bata fad’a da kowa.

    Ah ah muhammad fadi gaskiya dai nasan maman ku, saidai in ba’a bata mata rai ba?

    Dafa gaske nake.

    Ta yafe mini?

    Babu abinda ka mata abbajo asalima ita ke neman yafiyar ka, don gaskiya yayi halinsa bayan bakai, meyasa Abbajo kayi fushi ka tafi ka barmu, kana rayuwan ka cikin mulki da kudi mukuma baka damu da kalar rayuwar da muke ba?

    Girgiza kai kawai yusuf yayi baibawa muhammad Amsa ba, ya sake jefo masa wani tambayar, ya jikin salim nasan zuwa yanzun kam yagirma don zai fika jiki kasan jikin mamanku garesa?

    Kwarai ma kuwa abbajo salim ya warke sosai sai godiyan Allah.

    Su lawiza da suka jima a bakin kofa suna kallon ikon Allah wai me yusuf yake nufi da yaron nan ne basu gane ba, kasa magana sukayi ganin kamar ma basu san da zaman suba sai hira suke, hakan yasasu juyawa suka fita a d’akin ganin lokaci d’aya jikin yusuf yayi sauki gashi sam ba hausa suke ji sosai ba, duk da su mazan suna hausa tsabanin mata da kwata kwata bayi suke sosai ba sai jifa jifa,

    Haka yusuf da muhammad suka ringa hira na yaushe gamo, Amma sam muhammad bai fad’awa yusuf mutuwar Aisha ba koh salim, sai asuba da sukayi sallah doctor yazo ya cirewa yusuf laidan ruwan, suka kwanta tare a Royel bed na sarki bacci ya d’auke su.

    **************
    Sumayya ciki ya shiga wata bakwai yanzun sosai tayi wani irin kumbura, har yakai yanzun bata iyya tashi da kanta sai khadija ta kama hannunta ta jata da karfi saboda nauyin cikin, abincin ma yanzun bataci daga ruwan zafi sai tie koh nama.

    Kalamu-wahid da khadija yanzun kam an dinke sosai suka shaku kalamu na zuwa gidan sumayya akai-akai gashi yanzun har kwaryan tuwo yake dashi akofar sumayya na rana,kamar yau sumayya ta gaji da kwanciyar da khafija keyi a kasan tiles hakan yasa ta kiran ta hade da mika mata kudi taje ta sai karamin katifa, Amsan kudin tayi tace bari tayi wanka.

    Tana shiga d’aki messenge ta turawa kalamu akan zata fita, kafun ta shiga wanka.

    Tana fitowa shiryawa tayi ta fita da niyar tafiya kasuwa, tana nufar get ta bude da murmushi a fuskar ta ganin kalamu tsaye sanye da jamfa wando da riga yayi matukar masa kyau abinka da bakin mutun sanye da farin kaya, mota ya bude mata ta shiga shima ya zagaya ya shiga yaza suka cillah kasuwa.

    Duk yanda yaso ya saya mata katifa da kudinsa taki yarda, yace zai cikimata ta d’auki babba, amma taki tace aunty zatayi hulo itakam babu ruwan ta.

    Tare suka dawo kasuwa ya sauketa a get nasu, ta shiga da katifar ta da kanta don tace karya shigo kar aunty ta mata fad’a, sunje kasuwa dashi bada izininta ba, ba musu shima ya shige gidansu bai matsa mata ba.

    Bayan isha’i sumayya ne kwance a falo, yayinda khadija na cikin daki suna hira da kalamu a waya, kamar a mafarki taji sallamar sa a bakin kofar falon su, da sauri ta mike zaune tana mamakin sa na rashin fad’a mata yana zuwa Alhalin kuma waya suke da juna yanzun, kalamu!!!!

    Ta cikin wayar taji yace ke don Allah fitoh ki bude mini kofa.

    Ba musu ta fitoh a d’akin kallon sumayya dake falo a kwance, tana bude kofar ya shigo gaida sumayya yayi ta Amsa masa sama-sama don yanzun koh yawan magana bata so.

    Aunty daman wajen ki nazo?

    “Khadija basa wajen zama”

    Zama yayi akan kushin da khadija ta aje masa, itama ta koma gefe ta zauna.

    Aunty daman nace mezai hana khadija ta shiga islamiyyar mu ?nayi magana da ita tace nini tun saukar ta na farko bata kara komawa tushi ba.

    “Gaskiya ne kalamu koni ina son khadija ta koma islamiyya, nama laila magana akan koh akwai islamiyya a kusa, shine tacemin yaranta babansu ke koyar dasu, ni kuma bana son khadija taje wajen sa d’aukar karatu”

    Gaskiya ne Aunty kinga kuma zuwan weekend ne aje 3 adawo 5 ?

    “Shikenan kalamu sai Allah ya kaimu next week sai na had’aku ka kaita don ni ba iyya taka kafar nake sosai ba”

    Eh aunty daman na kammala mata kome yanzun ma uniform na kawo mata da form sai a cika mata sati mai zuwa ta fara zuwa.

    “Lallai ma kalamu toh Allah dai biya ka”

    Ameen ya Amsa yana kallon khadija dake murmushi a boye.

    “Yauwa kalamu daman akwai abinda nake son na fad’a muku kaida khadija”?

    Zuciyar suce a tare ya buga da sauri suka kalli juna sai kuma suka juya suka kalli sumayya har suna had’a baki, Aunty Allah dai yasa lafiya??

    “eh daman akan kune, ba kome bane illah abu d’aya zuwa biyu, ina so daga yau…………..

    ✨Ruqeenjalal✨

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  • Matar Makaho 90-91

    Matar Makaho 90-91

    Page9⃣0⃣&9⃣1⃣
    “Daga yau banason kara gani koh jin ka kira khadija a waya yafi sau biyu a rana, na gaji da halinku kunce ba soyayya kuke va ?sannan kai bakada aiki sai kiranta karfa ka manta kai d’alibin kiwon lafiya ne, bai kamata kana wasa da karatu ba”?

    Insha Allah Aunty za’a kiyaye.

    “Sannan ke kuma khadija kinga dai kokarin shiga ss 2 kike, kuma niyata in kika dage saina miki registration in waec next year, amma tunda wasa zaki saka a ranki bismillah zakiyita zama har 21 years a secondary”

    Shap wayaga maman aji, kalamu yace yana dariya.

    “Kaga banason shashanci kalamu, ina muku fad’a kana sako wasa”

    Sorry Aunty zamu kiyaye yace yana kallon khadija, ke akwai sauran shinkafa ki zubamin yau nanne na tuwo ta dafa?

    Babu kawai khadija tace tana mikewa ta shiga daki.

    “Kaga kalamu tashi akwai macaroni data dafa a tukunya kaje ka iba tunda kitchen in ba bakon ka bane, karku dameni da surutu kaina ciwo yake”.

    Mikewa yayi ya shiga kitchen in ya ibo makaroni da miyar kifin gesha, yana ci yana latsa wayarsa don yanzun sumayya bata surutu kamar da.

    *************
    Muhammad basu farka ba kuma ba’a tadasu ba sai kusan 10 na safe suka farka don kansu, wanka sarki yayi sosai yaji sauki jikinsa yayi karfi, kaya ya saka muhammad ma wanka yayi yasha jumfa da aka kawo masa mai masifar kyau da tsada, abincin karyawa aka jera musu a daining tare suka karya su biyu suna hira gwanin sha’awa, a hankali sarki yace muhammad wai nikam ban tambaye ka kaninku ba?

    Wanne kenan Abbajo?

    Kanin salim mana.

    Ai macece khadija tananan.

    Allah sarki yanzun fa shekarun ta 18 da wata 9 ta kusa 19?nasan itama yanzun ta kusa nabila koh?

    Eh Abbajo ta girma abinta.

    Allah ya raya mini ku ta farkin islama?

    Ameeen, haka suna ci suna hira har suka gama yusuf ya gyara rawanin sa yana rike da hannun muhammad sukayi fada.

    Ana bude musu kofa suna shiga saida gaban muhammad ya fad’i, ganin wasu jajayen buzaye, cikin su harda baba da gidado da badaru a zazzaune, sosai fadar ta cika makil da manya da yara alamu dai yusuf yasan da taron, sake hannun muhammad yayi ya zauna a kujeransa yama muhammad nuni da kasan cafen.

    Ba musu muhammad ya zauna a hankali, yayinda mutane kibinsa da kallo na mamaki sosai.

    a hankali yusuf yasa hannu ya ja rawanin fuskar sa, take fuskar nan mai kamala da dattako ya bayyana koh yaransa basu samun ganinta a araha irin na yau, kowa na kasa yusuf ne kawai a kujera.

    Gyaran murya yusuf yayi, Asslamu Alaikum warahamatullahi wabarkatuhu.

    Gabaki d’aya jama’an dake falon suka amsa masa sallamar.

    Na gode Allah daya nuna mini wannan rana, wanda ban taba tsammanin ganinsa nan kusa ba, koh ince ban taba sa ran ganinsa ba,Ayau xan sanar daku yan uwana don duk fadar nan yan uwana ne in aka cire mutane uku,ayau xan sanar daku abinda nasan dayawan cikin ku zasuyi mamaki, muhammad Al’ameen, d’aya daga cikin masu aikin gidan nan D’anane, kuma shine a gabana.

    Gabaki d’aya falon ya d’auki surutan mutane, daker aka samu ya lafa, yaci gaba da magana, nasan dole jama’a zasuyi mamaki Amma banda mahmah mahaifiyata, don ita tana d’aya daga cikin mutanen da suka san da wannan magana,mahmah ya kira sunan mahaifiyar sa dake xaune a gefe.

    Na’am .

    A taushashe yace, Mahmah ina son ki sanar dasu Asalin abinda ya faru shekarun baya da suka wuce, bani da koshin lafiya sosai kuma inbabu damuwa ina son kiyi da hausa wa’inda basa ji, Ramadan yana fassara musu.

    Gyara zama mahmah tayi ta fara magana kamar haka.

    *SHEKARUN BAYA DA SUKA WUCE*
    Masarautar karfe shine cikekken sunan masarautar gidan nan, wanda ke d’auke da tambarin zaki ya samo asaline tun bayan shekaru da suka shude, ka’idar masarautar ne duk yarima mai jiran gaso za’a makala masa sarka na magajin masarauta, sarkane daya samo asali daga makafan masarauta, duk wanda ya d’aura sarkan badai tsafi jifa koh tsibbo ya kamasa ba saida ikon Allah.

    mutallaf shine cikekken sunan mahaifin yusuf, a lokacin sarki ne yana da matarsa ta farko mai suna Hauwa-kulu sai dai Allah bai basu haihuwa ba har girma ya soma kama mutallaf don a lokacin harya haura shekara 50, hakan yasa kasa kara aure ya auro Hajara cikin ikon Allah shekara na zagayo wa hajara ta haifa masa yarinya mace, duk da yaso d’a namiji Amma hakan bai hanasa murnan samun mace ba, aka saka mata sunan hauwa-kulu yama uwar gidan sa takwara, haka hajara tayi ta haihuwar mata har hudu rus, sosai tsoro ya shiga zuciyar mutallaf, koh baida rabon d’a namjine kasancewar su a zuriyarsu ana yawan haihuwar mata, sama da maza gashi yana son magaji ga girma ya kamasa, Amma daga baya saiya maida lamuransa ga Allah, yaran nan kaf a wajen hauwa suke ita ke kula dasu kasancewar ta bata taba haihuwa ba kuma zaman lafiya suke da hajara.

    Hajara ta sake samun ciki sam wannan karon mutallaf bai kwallafawa ransa namiji zai haifa ba sam, cikin ikon Allah hajara ta haifi d’a namiji yaro yaci suna yusuf, tunda aka haifi yusuf mutallaf ya d’auki son duniya ya d’aura masa bama shi kad’ai ba duk wani masoyinsa nason yusuf, kuma aka d’aura masa sarkan magajin masarauta, saida hajara ta haifi yusuf daga shi bata kara haihuwa ba.

    Yar kaninta hauwa ta d’auko tana riko mai suna zahra, lokacin yusuf nada shekara goma sha biyar, sosai zarah keson yusuf ganin saukin kansa babu izzah koh nuna isa mutum ne na mutane, bai d’auki son mulki ya sakawa ransa ba wannan yasa zahra keson maganar sa.

    A lokacin da yusuf ya cika shekara 20 yayi haddan Alkur’ani mai girma da haddisai, yana cigaba da karatunsa na gaba da secondary, hauwa ta kwanta ciwo wanda kafun ta mutu saida ta nemi Alfarman mutallaf daya had’a aure tsakanin yar d’an uwanta zahra da yusuf, koh bayan ranta za’a tuna da ita a masarautan karfe, kuma zuriya vai kare tsakanin ta da mutallaf ba, babu wani shamaki mutallaf ya Amince mata.

    Bayan mutuwar hauwa mutallaf ya tada maganar auren yusuf da zahra, daman zahra nason yusuf wanda kowa ya sani sai dai shi yusuf inne bayayinta a lokacin, yaso gardama da nuna shifa Aure ba yanzun ba sai ya girma, Amma mahaifinsa ya murza ido akan lalle lalle auren Addanayen sa da za’ayi guda biyu Kafshatu da maisara tare za’a had’a da nasa, yusuf yayi iyya yinsa akan bayason zahra, abasa dama ya nemo wance zai aura Amma ina mutallaf yace bazai Aminta ba.

    Rana bata karya Saidai uwar deya taji kunya, a ranan da aka zartar amatsayin ranan d’auren auren yusuf da yan uwansa ya cika, Amma abin takaici an waye gari babu yusuf a gidan Sarauta.

    Sarki ya shiga tashin hankali Amma daga baya saiyayi zuciya akan duk inda yusuf yaje wata rana zai juyo gida, in ma bai dawo ba yama kansa, haka aka d’aura auren zahra da wani d’an uwanta.

    Tunda sarki ya rasa yusuf ya shiga wani irin matsanancin damuwa, ganin an share shekara goma babu yusuf babu a lamansa a lokacin hajara ta sake haihuwar na miji zulkiflu, sosai sarki yayi murna ya samu wani d’a na miji, sai dai ganin girma ya fara kamasa gashi shekaru naja yana sonyin murabas Amma babu magajiiiii.

    Shekaru sunja Amma shuru babu yusuf babu labarin sa, har hajara ta sake haihuwar wani d’a na mijin (Ramadan)dayake daman ita akwai kuruciya a tare da ita, Yusuf kam bai dawo ba shekaru sai tafiya suke har mahaifin sa ya kwanta ciwon ajali mai tsanani, a lokacin zulkiflu ya girma yakai saurayi, ga yan uwansa mata duk sunyi aure su hudu gashi mazajen su manya ne a kasa wasu kuma sarakuna.

    Hade Hannu sukayi aka bazama neman yusuf kasa da kasa Amma ina ba’aga yusuf ba gashi jikin mutallaf sai kara tsanani yake, baida magana saina d’ansa yusuf yana son ganin d’ansa kafun numfashinsa na karshe.

    Rana tsaka saiga shi an gano yusuf yana NIGERIA Kuma a ranan aka samu labarin An kaisa prison, bai kwana ba aka cirosa washe gari sai gasu a NIGER Har gaban mahafinsa dake kwance aka dukar dashi.

    Ganin halinda yusuf yaga mahaifinsa a take kuka ya kamasa tare da neman yafiyar mahaifinsa, sai a lokacin nadama tazo masa ganin yanda uban ya tsufa matuka, shekaru sunja, da ba’a d’aukosa ba da shikenan daker ya sake ganinsa sai wani ikon Allah.

    Mutallaf dake kwance cikin ciwo yace bazai taba yafe masa ba har sai ya masa Alkawari?

    Ba musu Yusuf yace ya Amince a take mutallaf yace koh bayan ransa bai yarda ya sake taka nigeria ba, koma menene zai kaisa baiyarda ba sannan ya masa Alkawarin zai auri lawiza(kanwar zahra) don cikawa hauwa burinta na had’a jini da zuriyar su.

    A take yusuf yasa kuka yana sanar da mahaifinsa cewa yana da mata da yara a nageria, a basa dama ya d’auko su kuma ya Amince da auren lawiza.

    Kin Yarda mutallaf yayi ganin haka yasa yusuf D’aukar wannan Alkawari, shi kuma mutallf ya yafe masa duniya da lahira tare da sakamasa Albarka, anyi haka washe gari aka d’aura auren yusuf da lawiza sati mai zuwa aka nad’a yusuf a matsayin sarkin masarautar karfe, a wannan rana mutallaf yabar duniya.

    Tunda yusuf ya zama sarki shikenan Rayuwar sa ta sauya bashida aiki sai tunani gabaki d’aya ya kwallafa ransa akan nigeria, yaso tura mutane aje a duba rayuwar da iyalansa keyi Amma hajara ta gargadesa akan rashin biyayya ga mahaifinsa da karya Alkawari, sannan tace bata son kowa yasan da maganar.

    Yusuf rayuwa suke da matar sa lawiza za’ace sai a hankali, batasan wan abu wai dadin aure ba, asalima yusuf ya samu ciwon zuciya wanda kullum gaba gaba yake duk wani abinda za’ayi don ganin yusuf ya dawo da walwalarsa anyi Amma abin yaci tura.

    Hatta yan uwansa da dangi ya shanja musu ba kamar yusuf da aka sani daba.

    Bayan wasu shekaru lawiza ta haifi yara biyu mata muwaddat da muhibbat, sai nabila yar kafshatu ce wance hajara ke riko a gidan sarauta.

    An dawo labari……….
    Tabbas yusuf nada yara ni shaidace mahmah tace tana hawaye.

    Jama’a da dama dake fadan sunsha mamakin abinda ya faru wai yusuf nada iyali, Amma ba’a sanar da kowa ba acikin zuriyar su, sannan wasu suna ganin rashin kyautawar abinda aka ma yusuf, lawiza kam kuka ta sake yanzun daman yusuf nada wasu yaran kamar muhammad, amma tana matsayin matarsa a kasa sanar da ita, mikewa tayi zata bar falon, alamu yusuf ya mata data koma ta zauna, ba musu ta koma ta zauna.

    Al’ameen ne ya dubi mahmah yanzun kina nufin kice mini kece mahaifiyar abbajo?

    Kwarai nice hajara kakar ka uwar yusuf…

    Yanzun kun kyauta kenan abinda kuka ma mahaifina ace mutum an yanke masa alaka da yaransa duk wani hakkin su daya rataya a wuyansa ? kai koh ashariya wannan ba daidai bane, mijinki bai kyauta wa mahaifina ba.

    Ya kyauta masa muhammad, nine ban kyauta ma mahaifinka ba, a Ranar da aka nad’a yusuf kafun mutallaf ya bar duniya munyi wani magana dashi akan yusuf……………

    ✨Ruqeenjalal✨

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    Page9⃣2⃣&9⃣3⃣

  • Matar Makaho 98-99

    Matar Makaho 98-99

    Page 9⃣8⃣&9⃣9⃣
    Zata fadi da sauri Ammar ya tarota cikin tashin hanki Ramadan ya bude firij inda ya gani a falon ya ibo ruwa watsa mata sukayi ta farfado cikin kidima take magana ina yake na tabbata d’an yusuf ne, don Allah ku taimaka ku kaini wajen sa na nemi yafiyarsa na tabbata muhammad ne, don salim baya kama da yusuf.

    Da mamaki suka juya baya don yima Muhammad magana, sai kawai sukaga wayam babu shi ga kuma mamakin ina matan nan ta sansu.

    Kuka take tana rokonsu su taimaka su kaita wajen muhammad, kwantar mata da hankali sukayi akan tayi hakuri ya koma inda suka sauka ne, kuma tare da yusuf suka zo, ai tana jin haka ta mike da sauri ta tsaya takalmi ta saka ta nufi kofar gida.

    Ganin haka yasa su Ammar binta suna tambayarta ina zata?

    Amsa ta basu akan gidan sarki zata wajen dasu yusuf suka sauka, jin haka yasa su binta a baya suna had’ata da Allah ta tsaya yanzun dai yana hutawa, amma ina bude get tayi zata fita daidai lokacin Alhaji suka dawo tsayawa yayi da motar sa yana tambyar zainab in zata? da mamaki don sam inba dalili mai karfi ba zainab sai tafi wata uku bata leka kofar gida ba.

    Tambayarta yayi ina zata Amma ina ta kasa basa Amsa shuru tayi ta tsunkuyar da kai, Ammar dake gefenta shiyake sanar da uncle insa ga inda zata, sata yayi ta koma amma kememmen Zainab taki komawa sai hawaye dayake bin fuskar ta, daka mata tsawa Alhaji yayi akan ta wuce ta koma ba musu ta juya tana kuka ta koma cikin gida, Ammar kam dariya abin ya basa watoh duk girman mace in batayi aure ba saikaga wani yaranta a tare da ita yanzun kamar Aunty zee ke kuka don ance bazata wani wajen ba.

    Komawa ciki sukayi dukansu harda uncle in Ammar da mom, shiga falon sukayi duka suka tsinci zainab na kuka a zaune zama sukayi baban ya fara rarrashinta don abin na zainab tsawa baya gyarasa.

    Tambayar Ammar yayi cikekken bayani, Ba musu Ammar ya zayyana masa kome dayafaru da labarin su yusuf kuka zainab tasa tana sambatu akan kome ya faru dasu yusuf itace ummulkaba’isin kome daya same su.

    Ajesu Alhaji yayi akan su zauna gobe daga shi harsu in saisu tafi wajen yusuf in tare.

    Aiko washe gari da sassafe suka wuce gidan sarki Amma basuyi sa’a ba duk basanan sunje gidan su hafsa, waya Ramadan ya d’auka ya kira zulkifilu akan ya tambaya musu sunan unguwan da suke.

    Bayan sun isa gidan da sallama suka shiga falon bayan an musu ido, zainab sai boye fuska take ganin sun had’a ido da yusuf dake mamakin ganinta da ubangari.

    Zama ubangari yayi suka gaggaisa da juna anan ne ubangari ke neman yafiyar yusuf tare da rokonsa daya yafe ma zainab, duniya ta koya mata Hankali, duk da sun dawo Maiduguri Amma har yanzun batayi aure ba, kowa yazo wajenta sai tace bata so gashi yau tana da shekara 44 harta fara tsufa Amma shuru kullum cikin istigifari dake da nadamar abinda ta Aikata, ga mutuwar khairat daya shiga jikinta sosai don Allah yusuf da muhammad su yafe musu.

    Daker aka samu muhammad ya yafe don yusuf kam a take ya yafe mata tare da neman izinin Aurenta, don zainab ta basa tausayi matuka tsawon shekara 44 ace batayi aure ba, yasan sonsa ke wahalar da ita duk da tsufa yaxo, Amma xuciyarta bai tsufa ba, ba musu Aka daidaita kome baban hafsa ma ya yafe ma abie, abin gwanin sha’awa su muhammad basu bar maiduguri ba saida aka saka sartin auren yusuf aka biya sadaki, Amma auren sai yusuf yaje nijar zasu dawo d’auren aure, duk wanda yaga fuskar zainab a lokacin zaisan lallai so ba karya bane don ta kasa boye farin cikinta.

    Daga maiduguri Hafsa da kalamu dasu falmata suka wuce Abuja,saboda karatunsu, muhammad da Sumayya suka wuce Taraba harda mahmah dasu dahdah, yusuf dasu ramadan sun wuce nijar daga Maiduguri.

    Bayan komawar sumayya dasu Abie jalingo sukaci gaba da kula da jariransu yayinda muhammad ya kai khadija wajen hafsa tacigaba da zuwa makaranta daidai su tashi tafiya nijar in sumayya ta gama jego.

    Kudi yusuf y sakarwa Al’ameeen a account ba kad’an ba, kamar yau suna zaune a falo su uku dashi da sumayya sai mahmah dake bawa na’ima madara gaggo na sallah a d’aki, hira suke anan ne muhammad ya kalli sumayya, ina so ki bani shawara matata cikin fulatanci yayi maganar sanin mahmah bataji.

    Murmushi sumayya tayi tana kallon mijinta sai kuma ta basa amsa da hausa gudun kar su ware mahmah, “ina jinka dear”
    Jin haka yasa mahmah mikewa ta basu waje.
    Yauwa don Allah ki tayani nazari in sama wa yan uwana mafita don nayi nazari Abinda ke damun Adara abu biyu ne, akwai jalinci akwai bin jini na gado, akan halinsu shiyasa nake son na shawo kan lamarin nan kuma na rasa mafita ta ina zan fara?

    “Gaskiya naji dadi daka ji a ranka Adara yan uwanka ne, baka kullace su a rai ba akan abinda suka maka ba, har kana nema musu tsira”?

    Taya zan gujesu sumayya bayan dangin mahaifiyata ne, da kinsu ake da Abbajo bai yarda ya auri mami ba.

    “Gaskiya ne ni a nawa shawaran abu na farko da zaka fara shine ka tarasu, kayi musu magana akan duk wanda yake da wance yake so koh wance take da saurayi tsayaye zaka aurar dasu, babu koh sisin iyayen su sannan ka gyara musu gidan tunda akwai fili saika ma samarukan d’akuna room and falo, suyi aure a ciki ka nema musu jari matan kuma asasu a islamiyya yara a had’a musu da boko, su kuma su inna ka basu jarin 50k ga kowance su kama san’a, sai maganar shagari kaje ka sanar dashi akan ka basa shagon halak malak kaga zaifi samun natsuwa akan ya zauna da tantama tunda Ammar yace ya baka kyautane”

    Gaskiya sumayya ngode matar Aljana Allah ya barmin ke baby, amma ya zanyi dasu bappa sulaiman?

    “Ameeen dear, ni a ganina kamar daman ai suna da sana’arsu kadai taimaka wa mata da yara matasan zaifi in yaso daga baya saika basu abinda kaga ya dace”

    Haka koh akayi washe gari muhammad yaje gidan adara kuma ya sanar da shagari ya barmasa shagon kyauta, yaron har kuka yayi gwanin tausayi, sannan yanzun yasan khadija tafi karfinsa shiyasa ya fara kula wata yarinyar school nasu dake matsa masa.

    Takardun makarantan sa muhammad kawai ya d’auka a dakinsu, sauran kayan d’akin ya baiwa matan gidan Adara kyauta harda na kitchen.

    Kafun wata d’aya duk samarin gidan adara da suka kai aure duk sun fitar da mata, haka ma matan don daman suna son auren, rashin kudine kawai, mazan ma wa’inda basu da budurwa jin auren bati da za’a musu yasa su neman yan mata cikin lokaci kankani, gashi ansa yara a boko ansa mata a islamiyya harda mazan ma.

    Anyi bikin gidan Adara na gani na fad’a wanda ya samu hallartar jama’a da yawa kowa na tofa Albarkacin bakinsa, akan muhammad da Halakcin daya musu.

    Sumayya ta kammala wankan jegon ta sati d’aya kenan, yau tun safe daga ita har muhammad in suna cikin farin ciki,adalilin khadija da kalamu da zasu zo yau don anyi hutun makaranta Khadija an kammala ss 1 zasu tafi 2, gashi yau daga ita har kalamu zasu zo Taraba tun asuba suke sanar dasu akan zasu bi fly, wanka sumayya tayi goggo tama yaranta wanka suka shirya cikin shiga ta Alfarma harda muhammad zasu je gaida maman Ammar, daga nan zasu bi Airport d’auko su Kalamu 4:00 na yamma.

    Dayake yanzun muhammad ya iyya tuki shiya d’aukesu a motar zuwa Gidan su Ammar, suna fita a motar dayake zuwan bazata sukayi basu sanar da Ammar zasuzo ba, tsayawa muhammad yayi a tsakar gidan yayinda sumayya ta wuce ciki rike da na’ima ta bar masa na’ifa da sallama ta shigo falon Amma babu kowa shuru kakeji,zama tayi koh masu gidan zasu fitoh Amma har minutes biyu bataga kowa ba, gashi Al’ameen sai kiranta yake akan yajita shuru saboda shi baya shiga gidan mutane ba tare da neman izini ba.

    Mikewa tayi ta nufi wani kofar dake gefen falon don a tunaninta koh dakin su maimuna ne a falon harta kama handle in kofar zata bude sai kuma ta dakata jin maganar dake tashi a d’akin.
    Muryar hajiyar Ammar ke magana, yanzun Ammar kanada wance ta fini ne ka zauna kana cutar da kanka ni bangane kanka ba gabaki d’aya ka chanja yau ciwo gobe lafiya?

    Ammar ne ya bata Amsa, Mom babu fa abinda ke damuwa kawai dai banajin dadi ne.

    Wani irin bakajin dadi, abinda ke damunka harda tunani da damuwa ba haka kake ba Ammar nice fa na haifeka?

    Mom daman wallahi na jima ina son khadija sai kuma yayi shuru bai karasa ba

    Wace khadijar?

    Kanwar Al’ameen

    Toh sai akayi yaya cewa tayi bata sonka?

    Ah ah mama ban fad’a mata ba,daman naso na sanar da sumayya maganar sai kuma bakina yayi nauyi kar tace daman da wani manufa nake taimakon su, gashi banason yarinyar ta rainani.

    Gyara zama mom tayi yana kara kallon Ammar tun ba yauba tasam d’an nata akwai son girma.

    Toh shine ita da Auntin nata suka gudu Abuja ba tare da na zayyana mata abinda ke raina ba, kuma yanzun kawai saina ganta da yaron nan kalamu kanin sumayya, kinga yanzun ai babu halin nace mata ina sonta tunda yanzun soyayya suke koma na fahimci tana son yaron.

    Ammar ka bani mamaki wallahi ita tace maka soyayya suke?

    Hamma mom kowa yagansu yasan masoya ne kuma nasan koh da ba sonsa khadija take ba Albarkacin sumayya zata yarda ta aure kalamun bare ma tana sonsa.

    Kaga Ammar kafito ka sanar da yarinyar nan kana sonta bakasan me Allah zaiyi a lamarin nan naku ba, ka kwantar da Hankalinka kaji inso samune ma ka shirya kaje abujan?

    Mom muhammad ya sanar dani khadija na zuwa.

    Toh maza ka tashi ka shirya samun ta ganka tsaf dakai kabi yayanta Airport gobe kuma sai kaje gidan su ku gaisa kaga saika sanar da ita Amma ka dubi yanda duk kabi ka rame……..

    Jin abinda suke cewa yasa sumayya sauri tabar bakin kofar, jin alamun mom zata iyya fitowa da sauri ta bude kofar falo ta fita waje, muhammad dake tsaye a rumfa har yanzun rike da babyn sa, dan yanzun sunyi wayo sosai,ya tambaye ta Lafiya tun d’azun Ammar bai fito ba?

    “Muje kawai ba kowa a gidan”

    Da gaske?

    “Don Allah ka shiga mu tafi gidan mu pls nace maka basa nan”

    Ba musu muhammamd ya shiga motar yaja suka wuce gidan su sumayya.

    Yad’an jima a gidan kafun kiran Ammar ya shigo wayarsa, sallama yama su dada ya wuce, bayan fitar Muhamamd ne dada ke sanar da sumayya akan ta kara ma abie magana akan Amina(goggo)ya aureta don ita hankalin matar ya burge ta, Amma duk yanda dada tayi akan ya yarda Ya nemi Amina tunda dai bata tsufa ba, da yarantanta Amma yaki Amince wa.

    Sumayya karan kanta taji dadin Abin don babu shakka goggo macece ta gari duba da zaman da suke da ita yanzun a gida d’aya sam bata da dumuwa.

    Sumayya ta samu Abie akan maganar daker saida takai ruwa rana kafun ya Amince da zancen, A ranan dada ta sasa dole sai ya wuce gidan su Al’ameen sun daidaita da goggo tunda yanzun yaran basa gida sai mahmah ne kawai.

    Muhammad da Ammar su sukaje suka d’auko su khadija a Airport gidan su Abie suka sauka daman sumayya na gidan sosai suka musu tarba ta musamman, Sannan a nan suke xancen Abie ya tafi zance gun goggo, aiko muhamamd yaji dadi don daman tunanin da yake kenan in ya tafi karatu abroad kamar yanda uncle zulkiflu yace masa next month zasu tafi America an sama masa gurbin karatu harda sumayya da yaransu don gida yusuf ya kama musu ashan haya, yanzun ma bikin Abbajo suke jira.

    Lokacin da abie ya dawo sosai yayi farin cikin isowar d’an nasa hira ne ya kara barkewa a tsakaninsu sai dare su sumayya suka tashi tafiya, kiran kalamu tayi da Khadija a compound ta tambayesu shin soyayya suke kuma su fad’a mata tsakanin su da Allah?

    Dariya suka sake a tare sannan khadija tace wa sumayya ai tsakaninta da kalamu babu zancen soyayya asali ma Abota ce kawai da shakuwa don kalamu kamma yana da budurwa yar school nasu sunsha gaisawa da khadija a wayar Kalamu.

    Hakan sosai yama sumayya dadi sallama sukayi da yan uwanta.

    Sun isa gida muhammad kam kwanciya yayi ya barsu da khadija anan sumayya ke sanar da ita Zancen sonda Ammar ke mata, da kuma bata shawarwari da tuna mata irin Alkharin Ammar a karesu ya cancanci ta sosa koh Albarkacin Halakcin sa, saida ta tabbatar jikin khadija ya mutu murus kafun ta mata sallama ta wuce d’akin mijinta khadija kam tare da mahmah zasu kwanta.

    Washe gari da safe bayan sun karya Al’ameen ke tambayar ta dalilin sasa su bar gidan su Ammar bayan kuma Ammar yace masa suna nan,sumayya ke sanar da muhammad zancen Ammar da abinda ta jiyo suna tattaunawa sosai muhammad yayi murna ba d’an kadan ba, haka mahmah khadija kam kunyane kamar zai kasheta, especially jin muhamamd ya shirya ya fita wai kar Ammar yazo ya samesa a gidan tunda wajen khadija zaizo.

    Sumayya da khadija kitchen suka shiga bayan matsawa khadija datayi kafun ta yarda, suna aikin girki yayinda mahmah da goggo ke falo suna rirrike da yaran sumayya.

    Wayar mahmah ne yayi kara a d’aki mikewa tayi da na’ima a hannunta ta shiga dakin ta d’auko wayar, ganin nabila ne yasata d’auka da sauri.

    Ta bangaren nabila jin mahmah ta dauka jiki a sanyaye tace hello

    Kedai nabila anyi yar banza, sallamar ma bazakiyi ba sai wani d’an banzan hello wai gaki baturiya koh?

    Yi hakuri mahmah Assalamu alaikum

    Amsawa mahmah tayi tana tambayar nabila lafiya?jin muryarta cike da damuwa

    Dada kewarku nake yaushe akki (muhammada)zai dawo?

    Toh watoh shi kike kewa kenan banda ni?

    Yi hakuri harda kene mahmah

    Toh make damunki nabila in baki fad’amin ba wa zaki fadawa?

    Mahmah wallahi nifa son Akki nake don Allah kisa baki a maganar nan ki sanar da abba kice ke kikeso a had’amu ki taimaka mini mahmah………

    ✨Ruqeenjalal✨🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci A ranan 30/8/2021 na fara rubuta Wannan novel na matar makaho, gashi A yau 28/10/2021 na kammala cikin Yardan Allah kuskuren danayi a ciki Ubangaji ka yafe mini🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲🤲

    Free book🤧

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 4

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 4

    EPISODE 4️⃣
    Wuraren 7:30 Hadiza tashigo gidan gabaki daya ranta amugun bace yake, Aman da Amal sai Ummi ne afalo dukansu ukun suna zaune kan dogon kujera suna kallon videos letters sound for Amal dudda Ummi bawani boko tayiba iya kanta JS3 but ta iya all this basic things na school shima sound din dan bata iyabane zamanin su da ABCD sukai karatu ba da sounds ba saisa suke koya tanan youtube yanda Amal ke koya itama haka take koya dan sabida koya musu, jin an bude kofa kai tsaye ba sallama yasa suka jujjuyo dukansu hada idanu Ummi tayi da Hadiza dake mata wani kalan kallo dayasa dasauri tamike tsaye daga kan kujeran ta duka kasa danta gane kallon me take mata cike da girmamawa tace “barka da dawowa Anty, ina yini” Hadiza da dama ta shigo da mugun bacin rai dan tun kiran da Nura yamata ashago ranta yake abace tace “ke ban gayamiki koda wasa kada duwawunki yazauna akan kujerun gidana ba, ke kinada darajan dazaki zauna inda nake zama ne yar aiki dake, ubanwa yagaya miki yan aiki nada matsayin zama akujerun gida” Ummi da kanta ke kasa ahankali tace “kiyakuri Anty mancewa nayi Amal muke koyama karatu” baki Hadiza tabude zatai magana daga Aman da Amal da duk suka tashi suna kallon Maman nasu Aman yace “stop shouting at Anty Ummi Mommy” dasauri takalli yaron ta ballamai harara, turo baki Aman yayi yace “u are always fighting and screaming Mommy our school teacher tace anger causes sickness” hararanshi Hadiza tayi bata tace “nakusan fasa bakin nan naka mara kunya kawai” turo baki yayi dan haushin Mommy shi yakeji sosai sabida yanda koda yaushe fada takema Anty Ummi su, bata sake cewa komiba tun maganan Aman tacire heels din dake kafanta awajen tawuce dinning straight taja kujera ta zauna tana sauke jakanta kan table din tace “idan kinga dama kizo kibani abinci” tashi Ummi tayi da sauri ta taho dinning din Aman kuma yakoma kan kujera yayi zamanshi yadauki IPad itakuma Amal tayi hanyar dinning din cikeda shagwaba tace “Mummy babuuuu, ki goyani zanyi bacci” cikeda masifa Hadiza ta nunata da yatsa tunkafin takarasa dinning din tace “don’t even come here wuce kitafi wajen Aman kiyi karatu yanzun nan nadawo zaku fara damuna, goyon kaniyanki zan miki, jeki jira yar aikinku tazo tagoyaki, Oya go back” juyawa Amal tayi tafashe da kuka dasauri Ummi takalleta kaman tadaina serving Maman taje ta dauketa, ta tsani taga yaran na kuka wlh har cikin ranta, ahankali tawuce wajen Aman tafada jikinshi rungumeta yayi yace “stop crying Amali Anty Ummi is coming yanzun nan kinji” Gyadamata kai tayi yana share mata fuska yace “let’s play game”.

    Tunda Ummi tafara serving tuwo a plate Hadiza ke kallonta zuciyanta na wani kalan tafarfasa kawo tray gabanta Ummi tayi ta ijiye bata idasa jaye hannunta ba Hadiza ta daga tray gabaki daya ta mike tsaye ta kwarama Ummi akai da tuwon dake a leda da miyan taushen da kwanukan da cokulan duka suka bare akanta wani kalan mahaukacin azababben mugun ihu Ummi ta kwala tafashe da kuka dayasa su Aman suka firgita dukansu suka juyo ganin Anty Ummi ta tsugunna a dinning ga miya tundaga saman dan kwalin kanta har goshinta da idanunta ta kullen gam tana ihu sosai jikinta nawani kalan rawa kaman wace ta zare tsabagen azaban zafin datakeji na miyan dakuma yajin miyan a idanunta yasa suka taho wajen da gudu Aman yace “Anty Ummi” cikeda masifa Hadiza tanunata da hannu tace “kina gidana, kinacin abinci na, nabaki makwanci, nabaki kayan sawa, nabaki sabulun wanka dana wanki, sannan ina biyanki kizo bazakimin biyayya ba, sau nawa ina gayamiki ni bancin tuwo sau nawa nake gayamiki? So kike nayi kiba nai katon ciki? Zanje sama nai wanka ki tabbata kin dafamin wani abun kin kawomin dakina kafin nagama wanka inba hakaba wlh saina koraki daga gidan nan this night” ta dauki jakanta tawuce sama fuuuuu, tsugunnawa daga Aman har Amal sukayi agaban Ummi da jikinta har bari yake sabida zafin miyan dan bata dade da gama miyanba ta juye a kulan gidan ga kulan su irin na millions din nan ne masu rike zafi kaman me, dudda Aman yaro ne amman saida yakai hannunshi yacire tuwon daga jikinta yana kuka sosai ya yar akasa yace “Anty Ummi sorry stop crying” Amal tace “Mommy is badddd mommy” sosai Ummi ke kokarin tabude idanunta takasa sai kuka take dudda kukan take na tausayin kanta tariga tai alkawari komenene zatai hakuri tana bukatan albashinta dashi Gwaggo ke zuwa asibiti dakuma shi ake tara kudin auren kanninta, dole ta jure komi itane hanyan cin abincin gidansu, so take ta mike but tama kasa hannunta Aman yakama Amal ma takama dayan yace “let’s go Anty Ummi ki wanke fuskanki” gydamusu kai tayi tana tsayar da kukan datake ta yunkura zata tashi tama kasa saita kara fashewa da kuka daidai lokacin an bude kofa da sauri su Aman suka juyo ganin Baban su shima ya shigo ya tsaya chak yana kallon daga yaranshi har Ummi dake kuka sosai kaman anyi mutuwa agidan ga jikin Ummi duk miya, fuskanta ma haka takasa bude idanu yasa yayi wajensu dasauri baima cire takalmi ba yace “Subhanallahi meya faru faduwa kikayi Ummi” Tsayar da kukan tayi dasauri muryanta na rawan sheshekan kuka tace “eh” tana yunkurawa zata tashi dasauri Aman yace “is Mommy Dady, ita ta kwara mata the whole tray na abinci akai Anty Ummi has been crying” warware handky daya ciro Nura yayi daga aljihunshi baiyi wata wata ba yakai kan fuskanta cikeda damuwa ahankali yace “tsaya” batai musu ba tsayawa tayi kwashe miyan kan idanunwanta yayi tass, miyan yayi fasha fasha awajen harda gashin idanunta, sannan ya kwashe na goshinta dana kumata batare daya taba na wuyanta ba dudda baka ce but he could see yanda fatan fuskan yayi ja, ijiye handky yayi dasauri kafin ahankali yakai hannuwanshi duka biyun yakama kafadanta dagashi har ita atare duka sukaji wani iri dasauri tayi kokari fizge kanta strictly yace “stop banson gardama, tashi muje” yanda yayi maganan ba wasa hakan yasa bata kara gardama ba, yana rikeda ita haka yayi kitchen da ita su Aman suka bisu bude kofan kitchen din yayi zuwa nan backyard gaban wani tap dasuke dashi awajen, yabude tap din yajuyo yakalli Aman yace “je bayin Anty Ummi kadauko mini sabulun wankanta” “okay Dady” Aman ya amsa yajuya da gudu shikuma yabude tap din yace “tsugunna” ahankali Ummi ta tsugunna, gently yadinga tara ruwan da hannunshi yana watsa mata a fuska har saida miyan ya fiffita duka da wayanda sukenan asaman gashin idanunta daidai Aman yakawo sabulan, ga mamakinshi sabulun vivo yagani ahankali ya karbe yakama hannunta yasa sabulun aciki yace “wanke fuskan mugani da sabulu” shafa sabulun tayi ta dirdirje da kanshi yake zuba mata ruwa tana wankewa tass ta wanke fuskan, igiyan wajen ya kalla ganin wata singlet dinshi wanda yasan itane ta wanke yajawo yabata yace “share fuskanki saiki bude idanun nagani”

     

    Share fuskan tayi ahankali sannan tashiga bude idanun yajin dataji yasa tamaida idanun ahaukace tarufe tafashe da kuka kunsan yanda yaji ke birkita mutum tace “wlh da kwai yaji sosai Alhaji, wayyoo Gwaggo na nashiga uku” shi arayuwanshi yanada tausayi, ya tsani aga ana hurting mutane in general balle kuma yaga mace in pains, da sauri yasa hannunshi ya karbi hanky yamikama Aman yace “hold it nagani“ sabulun yadauka daga kasa yasa a hannunshi ya fara wankewa sannan ya murza sabulun a hannunshi ahankali yadan kalli fuskanta yanda ta kankame idanunta gam jikinta har lokacin rawa yake tana dan kuka, dan ijiyan zuciya yasauke sannan yakai hannunshi gently yashafa sabulun a fuskanta kaman yanda ake wankema yaro karami fuska, fuskanta is sooo soft kaman na dan yaro, almost 30sec yayi yana chuda fuskan sannan ya kunna pampoo yashiga wanke mata fuskan tass kafin yakarbi singlet din ya share fuskan da kyau ya tsane dogayen eyelash nata kafin ahankali yana tsugunne agabanta yaciro wayanshi dudda akwai haske wajen bauuu flash na wayanshi ya kunna yabama Amal yace “princess haskamin fuskanta” dasauri Amal ta karba ta haska fuskan Ummi, shima yana kallon fuskanta dake sheki yaji wanki da sabulu yace “bude idon nagani” gently tashiga bude idanun dake rawa sosai na haggu tabude tass na dama ne tabude kadan dan tanajin yaji sai yarfe hannu take ta rude sosai ganin yanda takeyi yasa ahankali yace “tsaya” tsayawa tayi ijiye singlet din yayi kan jikinshi yakai duka hannunshi ahankali yayi cupping fuskanta dasauri Ummi takalleshi tadade rabon dataji namiji dab da ita haka, ahankali babu komi aranshi yakai hannanyenshi ya ware kwayar idannun nata dake mata yaji kafin gently Ya hura iskan bakinshi ciki wani kamshi Ummi taji da sanyi daya ratsa jikinta feeling inama ace zata sami miji dazai dinga kula da ita haka kaman yanda Alhaji keyi yanz, Alhaji nada kirki gashi kyakkyawa fari dashi kaman wani balarabe ga bakin saje, tsayar da hura idanun yayi ganin tabude su rass tana kallonshi kaman yaune rana na farko datake ganinshi shima zuba mata idanu yayi yana kallon kwayar idanunta yanda suke walkiya sabida hasken flash da Amal ke hasko musu, idanun sunyi ja na kukan dataci da yanda tai looking so helpless dakuma yanda take kallonshi hakanan saiyaji kaman yasata ajikinshi ya lallasheta, there’s something about her da kawai he finds interesting baisan menene ba. “Anty Ummi yadena yajin”? Maganan Aman yadawo da dukansu daga duniyan tunani atare dukansu kowa ya janye idanunshi, Nura ya mike tsaye da sauri yawuce ciki batare daya kara kallonta ba itakuma ahankali tamike tsaye tana goge wuyanta, gyadama Aman kai tayi tace “yadena” dasauri sukazo kusa da ita suna kallon fuskan hakan yasa ta tsugunna dukansu taba fuskan nata sukayi cikeda so sukace “sorry Anty Ummi” murmushi tayi sosai cikeda kokarin cheering nasu up tawani daga hannunta sama tace “Anty Ummi jaruma ce kaman Amalili, ko Mudi da Kumurci tsorona suke menene yajin miya dashima bazai tsorata dani ba” haba zokaga yanda sukahau dariya, Aman yace “Anty Ummi yaushe zaki kaimu kauyenku muma muga Mudin nan da Kumurci” hannunta takai kan kumatunta kaman mai tunani kafin tace “wata rana zamuje” ihu sukahau yi suna tsalle Nura daya dade yana kallonsu ta window kitchen murmushi yayi yawuce yadauki mop yafice gyara dunning din yayi da kanshi.
    Shigowa sukayi a kitchen din fita tayi taje dakinta ta chanzo kaya zuwa wani atampa dogon red yamata kyau sosai.

     

    Tana fitowa hada ido sukayi da Nura dake zaune a dinning yanacin tuwo adan kunyace ta sauke kanta kasa tazo wajen ta duka har kasa tace “Nagode Alhaji, kana bukatan wani abune dazan kawo maka”? Sosai yake kallonta red yamata kyau dudda babu wani special abu game da atampan but yamata kyau, jin shiru baice komiba yasa tadago kanta ahankali hada idanu sukayi da sauri yadauke kai itama maida nata kasa tayi dasauri, ahankali yace “bana bukatan komi, thank u” mikewa tayi harta juya tafara tafiya kaman daga sama taji yace “abincin yayi dadi sosai, thank u Ummi” dadan sauri tajuyo ga mamakinta kallonta yake suka sake hada idanu sukayi, faduwa gabanta yayi dasauri tasauke kanta kasa tasake juyawa zata shiga kitchen batare datace komi ba yace “mezakiyi a kitchen”? Ahankali tace “Anty zan daurama wani abinci batacin tuwo” strictly yace “wuce kije ki kwanta kihuta” dudda bataso ba dan batasan mezai biyo bayaba kasa musu tayi tawuce takoma dakinta ta kwanta.

    Fess yagama cin abinci yakai komi kitchen dakanshi yafito yaje sama fitowa yayi da paracetamol, bottle water yadauka mara sanyi yaba Aman yace “kaima Anty Ummi kace nace tasha” gyadamai kai tayi yawuce da gudu yatafi dakinta Amal na binshi yakoma falo yazauna yana saka news duk yanda yaso yama gane meke faruwa a news din kasawa yayi yawuce sama fuuu, bude kofan dakin Hadizan yayi ranshi abace tana zaune gaban dressing mirror daure da towel tana shafe shafen ta na night routine batare da tajuyo ba tace “ki ijiye abincin kiwuce kifita dakikiya kawai next time try this nonsense kinbar gidana kenan jaka kawai yar kauy…..” “Hadiza!” Nura yakirata da kakkausan murya saida gabanta yafadi dan baitaba kiranta da zafi haka ba juyowa tayi da sauri ta kalleshi ganinshi tsaye a tsakiyar dakin yana kallonta ranshi abace, haderai itama tayi tace “badai kahana yarinyar nan dafamin abinci ba dan idan kayi haka u will see the other side of me Nura” wani kallo yamata yace “inason naga other side of you din today are you crazy? Ke wace kalan senseless mata ce? Kissan kai kike kokarin yi agidana? Are you trying to kill that girl?” Hannu ta dagamai tace “please lower your tone ni matarka ne ba some yan aiki dazaka dinga dagama murya ba Nuri, I’m your wife not slave so keeep muryanka down by now kasan I don’t take that shit, namiji yazo yana wani mini ihu akai saikace ubana kuma ma idan na kasheta sai me? Eh? Ba yar aiki bace, yarinya mara galihu duk irinsu ne irin yaran da akauyen su akekai yara maza almajiranci mata kuma akaisu aikatau kota mutu sai me mezai faru? Almajirai nawa suka mutu wani abu yataba faruwa? Ai yara da iyayensu suka nuna basu da gata mutane ma basa gatanta su so bakaina farau ba dan yar aiki ta mutu agidana ehe” Sosai Nura ke kallon Hadiza shi baimasan tayi nisa haka ba sai yau wato tanada answer for anything, at this point baimaso maganan nasu yayi nisa dan kar zuciya ya debe shi yadauketa da mari hakan yasa cikin kakkausan murya yace “duk randa kika sake trying nonsense din nan wlh saikin bar gidane duk wani abu dake gidan nan fara tundaga kan gateman suna karkashina ne, hakki na ne nakare kowa na tsaresu dan haka don’t ever try hurting mutanen dakemin aiki inba hakaba u will leave this house!” dudda maganan ya mugun mugun sosama Hadiza rai amman daurewa tayi dan bataso yagane tai wani kalan shewa. “Ahayyeeee nanaye ance dama idan baka mutu ba bakagama sanin halin maza ba, Nuri ni kakema gorin zaka kora daga this rat hole dakake kira gida”? Ta nuna dakinta da ko’ina da hannu, tsaki kawai Nura yayi yajuya yafita tabishi da sauri dan idan bata bashi amsan maganan nan ba hankalinta bazai kwanta ba kai zazzabi ma zai iya kamata, tana biye dashi yana tafiya tace “zan iya gina gidan dayafi nakan nan sau dubu a kyau dakuma girma Nura kada kayi kuskuren yimini gorin gida, duka duka yaushe kayi kudin lokacin dana aureka kagama masters akan architecture kanama wani building agency aiki har kazo kabude naka kampanin na harkan filaye da gine ginen estate anan Abuja, who do you think you are dazaka min gorin gida nixaka kora Nuri, au ina maka magana ka maidani mahaukaciya kayi tafiyan ka wlh wlh yanda ka batamin rai dinnan saina huce akan mahaifiyark…….” Chak Nura ya tsayar da tafiyan dayakeyi akan staircase yajuyo ahankali yakalleta itama daidai tana tsayawa dab da shi tana kara rike gaban towel nata da kyau tana kallonshi tace “da ilimina da sana’ata da darajata har ka isa kazo kana gayamin na kara dukan wata yar aiki sainabar maka gidan ka, sabida yar aiki Nuri zakace zaka koreni, what on earth do you take yourself for? Are you God? Sabida kaganni mace kadauka I am weak ne I can’t defend myself? Zakace zaka korini daga gidanka u think bazanyi speaking up ba, Listen Nuri, me and you are two equal people! Baka fini da komi ba, duk inda kasa kafa nima zan iya saka kafan, nasan kimata nasan daraja ta and my worth u cannot downgrade me or downgrade my status and for batamin rai din nan dakayi this night wlh saina batama mamank…….” Azuciye Nura yadaga hannu zaikai mata mari kaman daga sama sukaji Aman yace “Daddy!” Chak Nura ya tsaya da hannunshi batare dayakai marin ba, he don’t ever wants yaranshi to have a memory of him yana dukan mahaifiyar su, dunkule hannunshi yayi tareda saukewa kasa ahankali yajuyo yakalli Aman din, dasauri Aman yazo ya rungumeshi tsamtsam yana kuka sosai yace “Daddy sorry kayakuri Mommy is sooo baddd but don’t slap her okay Dady, beating girls is not good katuna ranan dana daki Amal haka kagayamin” daukan yaron Nura yayi ya rungume ahankali tareda mannamai kiss akai yama kasa magana yashiga tafiya dashi yana sauka, Hadiza dake kallonsu tace “ai naso ka maren wlh danai suining naka for domestic violence, try that next time kagani I will mess you up Nura” sauka yashiga yi kasa yana dauke da Aman a hannunshi gaban dakin Ummi yakaishi yace “shiga” shiga yayi sannan yajuya yawuce yafita daga gidan yashiga motanshi yamabar estate din gabaki daya zuciyanshi daci takemai da gaske idan Allah yabaka mata nagari wlh ka gode kama kara godemai dan shaidanun mata azaba ne, they will so push you to the wall kaji kaman zaka kashesu, yayi tafiya mai nisa sannan yayi parking yakalli wayanshi yadade yana kallo kafin yasauke ijiyan zuciya yakai hannunshi yadauka yabude yaciro wani lomba yakira wayan na gab da katsewa aka dauka daga dayan bangaren wata yar dattijuwan manyantaccen murya ne tai magana. “Nura barka da dare ya wurinku yasu Amalily?” Ahankali yace “lafiya lau” saikuma yayi shiru all this years baitaba daga waya yakai karan matanshi ba sai yau jin yanda baiyi magana ba yasa tace “lafiya Nura Maiya faru? Ina ganin wayan nasan da wani abu duba da lokacin dakama kirani, what happened?” Ahankali yace “Hadiza bansan menene damuwanta ba, tunda na auri Hadiza Anty Jamila for once bantaba kokarin takata ba ko shut her up, ni mutum ne dana tsani takurama mata ko basu damuwa I have 4 sisters dukansu mata nataso da sanin yanda ake girmama mace kare mace dakuma daraja mace” Anty Jamila tace “kwarai Nura wannan haka yake zan shaideka ako’ina” ahankali yace “the whole idea da concept na feminism ya shiga kanta, I’m not saying feminism is wrong no, ko Allah yasani inaso naga matata tacigaba, banki duk matakin dazan taka aduniyan nan matata ta takashi ba, I empower her nabata jari tafara business nakaita su dubai oman Egypt dasauran kasashe alokacin sabida ta saro abayoyi tafara, bansan gobeba I believe empowering matata will go a long way for yaranmu incase of gobe dabata da tabbas, bantaba ma Hadiza kallon wata baiwa ko yar aiki ba rather I see her as life partner dina wacce nakeson to go through every phase na Rayuwa together mu tsufa together but ita bahaka take ganin komi ba, gani take anything daya kamata tayi agida nima yakamata nayi nida ita we are equal, yimin girki gaidani bani abinci is not her duty duka abubuwan nima nayi we are equal afterall, gaidani akan me zata gaidani nima na gaidata…” dasauri Anty Jamila tace “subhanallahi” dan ijiyan zuciya yasauke yace “Anty Jamila the whole feminism din nata haukane kawai, rashin kunya menene menene babu wanda bata mini nakasa gane kanta balle kafanta, i can’t even talk to her kafin nayi magana daya tayi dari, Anty Jamila I am tireddddd nagaji, I want peace of mind at this my age” yanda yayi maganan saida yabama Anty Jamila tausayi tasan yanda Nura keda hakuri tasan for Nura yadauki waya yakirata takaishi bango anatse tace “Nura kayakuri kayakuri shikenan abinda zan iya fadi kaga wannan halin shine dalilin dayasa maza da yawa basason bama matayensu freedom har subarsu suyi sana’a dan wasu matan dazaran sun soma taba kudi shikenan sai sudinga jin kansu kaman giwaye suma yanzu sun faso, amman kabarni da ita zan kirata zan kira Mama kuma” ahankali yace “please kada ki sanarda Mama tana fama da hawan jini saisa nakiraki ban kirata ba” murmushi tayi tace “to shikenan amman dan Allah kayakuri” ahankali yace “to saida safe agaida yara” yakatse wayan yadade ahaka yau bacin ran yasa he wanna be alone ma inda bahaka ba zai iya kiran abokan shi yaji inda suke yaje yasamesu, yayi kusan 3hrs awajen sannan yatada mota yabar wajen.
    Domin magana dani M shakur koso nasaki a group dina chat me up tanan wa.me/+2347012181461

    Yana katse wayan Jamila ta danna mata kira wayan harya katse bata dauka ba akaro nabiyu ne tadauka tace “Hellooo Anty Jamila” cikin fushi Jamila tace “ke wace irin mahaukaciya ce Hadiza? Ni wlh I don’t even need to ask you nasan kene da laifi dan nasan kalan hakurin Nura tunda yau dakanshi yadaga waya yakirani nasan kin mai babban laifi” tsaki Hadiza taja dayasa Anty Jamila tasake baki, cikin fushi Hadiza tace “ohhh kiranki yayi yahada mini munafinci? To wlh zaizo gidan nan yasameni ina jiranshi” jin yanda yake magana kaman tana jiran wani saran wasanta yasa Anty Jamila tace “Hadiza are you okay kuwa? What has gotten into your head? Nuran kike magana haka akanshi?” Cikin fushi sosai Hadiza tace “Anty Jams bazaki gane bane, Nuri finds every little way to belittle me, nan Abuja ne fa ba kano ba but kullum so yake ina shiga kitchen namai abinci, a Abuja yan aiki ke girki matan gida relaxing take bayinta namata aiki, inada yar aiki ai nama baki labari wacce nace miki su Aman na sonta, ita ke kula dasu I am busy da shigo gida nawa yake so naraba kaina? Sai nasa yar aiki tamin wani abu yahanata yimin sabida shike biyan kudin shine nacemai yadena daga this month nizan cigaba dabiyanta sabida I should be the one in control of her, ina shago dazu yakirani wai Mamanshi zatazo gobe taga Dr kinji fa Anty Jamila sabida ya rainama kanshi wayau danni bai isa ya rainamin wayau ba, gidan nan belongs to two of us baida right dazai kawo koma uban waye into this house without asking permission dina, what did he take me for eh? Wlh wlh jiransu nake suzo goben dagashi harsu saina kuntata musu bakin cikin da bazasu kara marmarin zuwa gidana ba me akeyi da yan uwan miji banda hauka mtswwww” “Innalillahi wa innailaihi raji’un” Anty Jamila tafadi tana tafi da hannunta cike da mamaki tace “Hadiza giyar kudi ko giyar karatun wannan femi ah’ahhh Feminism ko oho dai ke damunki” Hadiza tace “feminism wai? I know my right I can fight for my right duk inda nake aduniya tunda mata suka gano this feminism sun samu yanci sun samu cigaba, a woman can stand aduk inda namiji ya tsaya aduniyan nan” “dalla rufemin baki sai idea bature yasa kin rasa mijinki tukunna zaki dawo hankalin ki” Anty Jamila tamata ihu tace “wannan ba shine tarbiyan da aka baki agida ba, keda mijinki can never be equal ko awajen Allah domin ko aljannanki na karkashin tafin kafanshi, mata dakika ganmu daga rib guda daya na maza aka hallito mu, kada ki mata, Allah yafadi acikin suratul Nisa’i aya na 34, Arrijalu qawwamuna Alan nisa, bari madai naja miki ayan gabaki daya
    ٱلرِّجَالُ قَوَّٰمُونَ عَلَى ٱلنِّسَآءِ بِمَا فَضَّلَ ٱللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍۢ وَبِمَآ أَنفَقُوا۟ مِنْ أَمْوَٰلِهِمْ ۚ فَٱلصَّـٰلِحَـٰتُ قَـٰنِتَـٰتٌ حَـٰفِظَـٰتٌۭ لِّلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ ٱللَّهُ ۚ وَٱلَّـٰتِى تَخَافُونَ نُشُوزَهُنَّ فَعِظُوهُنَّ وَٱهْجُرُوهُنَّ فِى ٱلْمَضَاجِعِ وَٱضْرِبُوهُنَّ ۖ فَإِنْ أَطَعْنَكُمْ فَلَا تَبْغُوا۟ عَلَيْهِنَّ سَبِيلًا ۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيًّۭا كَبِيرًۭا ٣٤

    Men are the caretakers of women, as men have been provisioned by Allah over women and tasked with supporting them financially. And righteous women are devoutly obedient and, when alone, protective of what Allah has entrusted them with. And if you sense ill-conduct from your women, advise them ˹first˺, ˹if they persist,˺ do not share their beds, ˹but if they still persist,˺ then discipline them ˹gently˺. But if they change their ways, do not be unjust to them. Surely Allah is Most High, All-Great.

    Allah ne yafadi da kanshi, idan kuma u are talking about rights da yanci ne tun zamanin Annabinmu ya kwatoma mata yancinsu idan wani yaji kina magana haka idan ba’asan Nura ba zaa dauka wani abu bawan Allahn nan yake miki, kin sami miji nagari bawan Allah shiru shiru mara magana kinamai irin abubuwan nan ke kinada baki kice sai da izinin ki mahaifiyarshi zatazo gidan danda tahaifa, matan da komu nan last week saida muka kirata muka mata yajiki wlh maganan ki yasama ina jin kunyan Nura, Hadiza sau nawa da ni da yarana harda Mama muke zuwa gidan ki every now and then duk wani abu dazai shigo damu Abuja gidanki ne masaukinmu we don’t even ask for permission sabida anzama daya, ace yau mahaifiyarshi zatazo for treatment na rashin lafiyanta kina maganganu haka ina imanin ki? Wani kalan tsantsan son kai ne wannan”? Cikin kunkuni Hadiza tace “ai dama side dinshi zaki dauka nasani mutum yana nema ya maidani yar aiki bazakice komiba ace nine zan shiga dakinshi na gyara namai girki bayan inada yar aiki mai yi” Anty Jamila tayi shiru na kusan 5min sannan tace “danace basai na sanar da Mama ba but Hadiza kinyi nisa Mama dole ta shigo zancen nan, yar aiki itane ke gyara dakin mijinki tamai girki? How many minute zai daukeki kima mijinki girki? Bawai nace yar aiki is bad bane ai ko ni inada yar aiki tadan taimaka maka da one or two things but that does not mean zaki barmata ragaman gidanki menene haka Hadiza ke kina ganin wayau ne hakan kin cika yar boko ko? Kin waye kinada kudi kinyi kawaye matan Abuja kema kin dauki sahunsu kirasa wanda zaki mawa sai mutumin da shine yabaki jarin mutumin that made u Hadiza” ihu Hadiza tayi tace “me aciki Anty Jams ai sai nabiyashi kudin daya kashemin nafara business din harda riba indai hakan zaisa yafita harkata yabarni na Sarara nayi yanda naga dama” dasauri Jamila tace “wai kinsan wane kike aure kuwa? Nura fa kampanin shi shike tashe yanzu ko su cosgrove abayansu suke, ga kyau ga aji ga hakuri baki tunanin yazo yahadu da wata kinamai haukan nan yakaro aure abinshi” har cikin ranta Hadiza taji maganan ya soketa dasauri tace “Nuri baida ra’ayin mata biyu tun kafin muyi aure yamin alkawarin ni kadaice matarshi har abada and Nuri baya taba karya alkawari, he’s a man of his words” dan murmushi Anty Jamila tayi tace “to inhar bakison alkawarin nan ya karye take care of mijinki ki sauke pride din nan youu are under him and u will always be, kidaina mai kallon keda shi are equal kina rainashi, keda mijinki can NEVER BE EQAUL, and Bari nagaya miki ki gaggauta gyarawa kafin Nura ya rufe babinki yabude sabon babi,_ saida safe kuma zan sanar da Mama yanda mukayi” ta katse wayan batare data karabi takanta ba shiru Hadiza tayi tana kallon wayan ranta ya mugun sosu da kalman kishiya. Da Yayanta tayi tsaki tayi ta yarda wayan gefenta tace “shiya isa yama mini kishiya, tsorona bazai ma barshi yayi wannan kuskuren ba, banda hakama mata basa gaban Nuri sai business kuma Nuri baida ma yawan sha’awa kaman nine saimuyi watanni bamubi takan shimfidan juna ba ninama fison haka dan ba haihuwa nakeson nakarayi ba inaso nai maintaining this body da shape shi aina zai taba samun kyakkyawan mata fara hausa fulani komi yaji irina” tayi dan murmushi tanajan bargo takoma bacci abinta.

    MAISA WASU MATAN KE GANI SUDA MAZAJENSU ARE EQUAL????
    [9/18, 9:17 PM] +234 706 542 1229: 💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

  • Matan Ko Mazan Book 1 Page 5

    Matan Ko Mazan Book 1 Page 5

    ✍🏻M SHAKUR

    EPISODE 5️⃣
    Ummi kwata kwata takasa runtsawa koyaya ta kulle ido ganin lokacin da Alhaji ke kallonta take, da yanda ya kula da ita dazun dinnan the same way yake handling su Aman that’s yanda yayi handling nata, abun yaki fita daga zuciyanta, the entire scene ya narkan da zuciyanta sosai dan har yanzu kamshin turarenshi takeji yanda yazo dab da ita, she can still feel dadin kamshin iskan bakinshi lokacin daya hura mata, mirginowa tayi daga dan katifan datake kai zuwa kasan tiles, sanyin tiles din yawani kara tsuma zuciyanta ta bude idanunta tana kallon POP sama fuskan Alhaji take gani wlh Alhaji akwai karisma da haiba dawani irin kyau ahankali tace “inama ya aureni” dawani kalan sauri tadaura hannunta saman bakinta kaman irin wacce tafadi taboo din nan, tayi aiki agidaje 4 wannan ne na 5 bata tabajin kaman mijin ko Alhajin gidan datake aiki ya aureta ba sai wannan sabida yanada mugun kirki, gashi da sanyin zuciya, sannan yanada natsuwa, yanada daraja mutane sannan yana son yaranshi sama da komi kawai mata ce baiyi sa’a ba wlh inda itace matanshi ko zaiga gata dan miji irin Alhaji da baida matsala hakan nan wlh kula zatayi dashi sama da yanda yake kula dasu Amal ma kula zatayi dashi kaman wani jariri tana bashi duk abinda yakeso aduniya, ahaka bacci yayi awon gaba da ita da tunanin Alhaji aranta.

    Wuraren 1 yashigo gidan da kanshi ya kwaso duka kayan daya sayo dazu na cefene yakai kitchen ya ijiye komi sannan yawuce sama dan kwanciya.

    As usual biyar yafito sanye da jallabiya tunda yabude kofanshi kamshi ya daki hancinshi ahankali yake sauka daga staircase harya karasa sauka kasa wutan ko’ina akasan akashe wutan kitchen ne kawai akunne ga kofan kitchen din abude wajen dinning yaje ya tsaya yana kallon kitchen din Ummi yagani tana girke girke daban daban ga su lunch bag na Aman da Amali akan island yau zasu school, tana sanye da Riga da skirt yana ganin kayan yagane su kayan Hadiza ne tun tana yammata sun kode sosai amman dudda haka sunma Ummi kyau that means tayi wanka kafin tashigo kitchen folding hannunshi yayi yana kallonta tundaga kan slippers green dake kafanta zuwa kanta dake daure da dan kwalin atampan jikinta, tanada tsayi sannan tanada hips dudda ba sosai ba but sunada curve irin yaran nan ne da suna samin kula zasu cicciko yanzu wahala ne yasa suke looking haka ma, dan lumshe idanu yayi yabude ya tsare fuskanta da kallo ahankali Yatambayi kanshi am I falling for this girl? Dan ijiyan zuciya yasauke yajuya yawuce yafice zuwa mosque yana deep tunani shiba yaro bane yasan when zuciyanshi keson abu.

    Wuraren 7 nasafe yashigo gidan Hadiza yagani a dinning taci gayu sosai cikin wani exclusive atampa ta buga dauri tanacin lafiyayyen breakfast chips da pepper soup sai shayi agefe, itakuma Ummi na tsugunne a tsakiyan falo tana feeding Amal a baki Aman na kusa da su daduk ta shiryasu cikin kayan makaranta suna ganin babansu da gudu sukai wajenshi. “Daddyyy Assalamu Alaykum Dady ina kwana” murmushi yayi yadauki kowannensu yamusu peck yashigo dasu falon yace “ku karasa breakfast yanzun nan school bus zaizo” basuyi musu ba suka koma, anatse Ummi da kanta ke kasa tace “ina kwana Alhaji” batare daya kalleta ba yace “fine” sannan yadau remote yana chanza tasha 8 zai fita hakan yasa kawai ya ijiye remote din yawuce sama ko kallon HADIZA baiyiba itama bata kalleshi ba saima karasa cin abincinta datayi tawuce tadauki car key tace “ki dafamin couscous da daddare ke” ahankali Ummi tace “to Anty, saikin dawo Allah bada sa’a” yatsine fuska tayi bata amsaba tawuce tafita tashiga motanta tabar gidan, bata dade da fita ba motan su Amali yazo Ummi takaisu suma suka wuce tafito tana gyara wajen taje dinning ne ta gyara inda Hadiza taci abinci sannan tawuce tana duba girkin datake ma Kakan su Amal dazata zo, tana cikin tuka tuwon Alkaman taji kamshin turare dasauri ta juyo hada ido tayi da Nura daya shigo kitchen din yasa wani blue gizna shadda wlh yayi kyau na bugawa a jarida faduwa gabanta yayi dasauri ta dauke kai ta saki muciyan a tukunya zata duka yace “cigaba da abinda kikeyi” batai musu ba tacigaba saikuma tadan juyo hada idanu suka sakeyi ahankali bakinta nadan rawa tace “kana bukatan wani abu ne Alhaji”? Dan girgiza kai yayi yaja daya daga cikin kujerun dake gaban island din yazauna yace “me kike tukawa”? Atsanake tajuya takalli tukunyan tace “tuwon Alkama, kace Hajiya da safe zata iso saisa nake mata nasan basuyi kari ba suka shiga hanya, itakuma sister ka zan dafa mata abu daban” yana kallonta yace “nikuma fa” dan kallonshi tayi ga mamakinta murmushi yasakan mata dasauri tace “breakfast dinka nakan dinning amman idan kanason wani abu daban ne zaka iya fadamin namaka yanzun nan” “hmmm!” Yasauke ijiyan zuciyan dashi kanshi baisan karanta yafito ba maganan yatabamai zuciya dan wannan ne abinda matanshi bata tabamai ba just look at yanda yarinyar nan tabashi girma da daraja da kima kome yakeso yafadi zatamai that king treatment shitake mai, kawai saiya dago yakalleta yace “dafamin shayi mai kayan kamshi” dasauri tace “to” zare muciyan tayi daga tuwon tadan diga ruwa ta rufe tarage heat din tawuce ta wanke hannunta tashiga hadamai shayi shikuma yaciro wayanshi yana tabawa dan kawai tasaki jiki amman wlh kusan kome takeyi idanunshi binta suke, nan da nan tahada shayin tadauko wani hadadden flask jug tazubamai tasaka a tray tadauki cup da spoon da sugar kaga yanda take plating zaka dauka taje culinary school ne nan ko tsabagren experience ne a aikatau, tadauko tray din tazo har gabanshi ta ijiye sannan ta duka tace “nazuba maka?” Ahankali yace “yes” mikewa tayi yana kallon hannunta farcenta farare kal dogaye masu kyau tazubamai tace “sugar cubes nawa zansa ko asa zuma?” Kaman wani yaro dan he’s just enjoying the way take neman permission nashi for komi this is luxury da baya samu yace “zuma” dasauri tajuya tafita daga kitchen din taje dinning tadauko zuma takawo ta zubamai sannan tajuya tadauki cup din tadaura kan tray nashi tajuyo tabashi kallon fuskanta yayi sannan yasa hannu ya amsa yace “thank you Ummi” wucewa tayi takoma wajen tuwon tashiga kwashewa kaman daga sama taji yace “waye Mudin kauye?” Juyowa dasauri tayi takalleshi hada ido sukayi yana kurban tea juyawa tayi tacigaba da kwashe tuwon tana mamaki a ina yatabajin takira sunan Mudi saikuma ta sauke ijiyan zuciya tace “tsohon miji na ne” dasauri Nura yakalleta yace “kin taba aure”? Gyadamai kai tayi tace “eh amman an dade tun ina shekara sha uku-sha hudu aduniya” yana kallonta yace “meya rabaku”? Tsayar da kwashe tuwon datakeyi tayi saikuma ta kalleshi yanda ya tsareta da ido yasa ahankali tace “dukana yake, kullum kullum duka, hakanan kaman idan bai dakeni ba bayajin dadi rayuwanshi, shine…..” takasa maganan tai shiru takai hannu ta goge hawayen dasuka zubo mata dasauri tajuya tacigaba da kwashe tuwo Nura yace “shine meya faru”? Ahankali tana kwashe tuwon tace “shine rannan dayamin wani bakin duka saida na haifo bakwaini, inada cikin wata shidda lokacin, amace yafito yaron, saida nayi jinya na kusan shekara daya inata fama da yoyon fitsari, Gwaggo na ta hadashi da mai anguwa akan saiya sakeni kuma abimini hakkina dan ya illata mata jika tun bayan haihuwan dole dayasa nayi ban warkeba, to da kyar yasakeni amman dudda ina rashin lafiyan yakan biyoni har gidanmu yamin duka har suma inayi, ko baizoba kullum cikin fargaba nake zaizo, Maman mu tarasu Gwaggo mu ce kadai garemu kuma batada karfi ta tsufa, ahaka dai na warke but ina cikin tsoro kullum, saisa dataji wata mata dake zuwa kauyenmu kwasan yara aiki taje ta roka da kyar akace za’a daukeni, to aboye aka fitar dani daga kauyen mu kada Mudi yaganni, tundaga nan nazo birni tun ban gane abubuwa harna gane yanzu nima, amman inaso nakoma kauyenmu naga Gwaggo na da kannina Salamatu tai aure harta haihu Maimuna da Ikilima ne za’ayi bikinsu kwanan nan kuma inaso naje amman Gwaggo na bataso nazo tsoro take kada nakoma kauye Mudi ya kasheni, yanzu ance yafi da zama takadiri ya gagari kowa, tsoron shi ake har mai gari, amman nayi kewan garinmu da gidan mu da Gwaggo na da kannina sosai bansan ya Allah zaiyi dani ba bansan kozan kara sa kafa a kauyenmu ba” tai maganan tana kai hannunta saman fuskanta duka biyun tadanyi sheshekan kuka mara sauti, shiru Nura yayi yana kallonta tabashi tausayi sosai ahankali yace “kinaso nakaiki kauyenku kiga yan uwanki”? Dasauri tazare hannayen ta dagakan fuskanta takalleshi da rinannun idanunta yanda ya tsareta da idanu yasa gently ta gyadamai kai, murmushi yayi yace “I promise zan kaiki kauyen ku, and namiki alkawari ba Mudi ba ko mudari yake bai isa yamiki kallon banza bama balle ya dakeki kinji” gyadamai kai tayi ahankali, murmushi yadan mata yace “kada ki kara kuka bayama fuskanki kyau” akunyace tai murmushi shima murmushi yayi yace “idan Hajiya tazo dazaran nagama kata katan asibitin ta zan kaiki gida ko” gyadamai kai tayi dasauri, tashi yayi yakalli agogon hannunshi yace “bari natafi daukosu nasan jirginsu yatashi yanzu kafin nakai airport sun sauka, kinason nasayo miki wani abu”? Yamata tambayan da saida ta kalleshi da mamaki ganin ya tsaya yakuma tsareta da ido tace “Amali tadameni tun jiya zatasha yoghurt babu yoghurt agida” jinjina kai yayi irin yaji din nan yace “ke me kikeso”? Sunnar da kanta kasa tayi akunyace tace “slippers wannan yakatse dazu na naneshi da wuka mai zafi saisa na iya sawa” yanda takejin kunyanshi na burgeshi sosai, anatse yace “to” yajuya zai wuce dasauri tace “Nagode Alhaji Allah kara girma, saika dawo Allah ya tsare” juyowa yayi yace “Ameen Hajiya Ummi” dasauri takalleshi wucewa yayi yafice yana murmushi mota yashiga, saida yafara tsayawa a super market yayi sayayya harda cream da shower cream mai kyau yasa mata da su turaruka da wasu abaya daya gani a super market din da idanu ya gwada tsayinta haka yabiya kudi yafito, haryakai airport labarin Ummi yake tunani yaushe kauye zasu dainama yara Auren wuri ne haka, yanzu sabida wani katon mugu aka koro yarinyar nan aiki, yayi traumatizing nata tun tana 14, small girl fa, hmmm Allah ya kyauta.

    Daidai yana parking awajen parking wayan Amina nashigowa fitowa yayi daga motan yana daukan wayan yace “okay ku jirani a arrival din gani nan zuwa” wucewa yayi tun kafin su ganshi ya hangosu, wata tsohuwa ce fara mai zanen kalangu a fuskanta zaune kan wheelchair dawata budurwa da akalla zatai tsaran Ummi ke gungurawa ga akwatinan su kan cart a gefe tareda mutumin dake turawa, ahankali tsohuwan matan tadago idanunta dan taji alamun danta ajikinta hakan yasa sai waige waige take, ta baya yazo yahada idanu da Amina daya mata alamun kartai magana sannan yataho kawai Hajiya ganinshi tayi agabanta ya tsaya bai damu da airport sukeba tsugunnawa yayi yasa guiwowinshi akasa yana kallon fuskan mahaifiyar tashi data washe baki ganinshi tace “me haka tashi tashi kayanka zasu baci, yanzu kasan banda karfi balle na wanke maka” ahankali yakai duka hannayenshi yatallabo fuskan mahaifiyan nashi yace “bance kada ki kara ciwo ba eh Hajiya?” Cikin barkwanci tace “ai dazai tasomin saida nace kai rashin lafiya ka manta kashedin da Nura yamaka ne kakeso kadawo kuma” dan murmushi yayi duk rashin lafiyan Hajiya bakinta is always there baya fatan tai rashin lafiyan dazai hanata magana har abada In sha Allah. Rungumeta yayi ahankali yace “barka da zuwa Mamana, Allah yabaki lafiya Hajiya, Allah yasa kaffara ne” bayanshi ta shafa tace “Ameen Ameen ai naji sauke Amina ai bata kyautamini ba banso ta tadamaka da hankali ba wlh, tashi daga kasa kaga jama’a sai kallemini d’a suke yasa guiwa akasa” batare daya saketa ba yace “albarkan mahaifiyata nake so” murmushi tayi tace “Allah maka albarka Nura, Allah ya lura dakai kaman yanda kake lurada ni, Allah yasa yaranka sumaka yanda kamini Nura, yanzu tashi mutafi kaji dan albarka” anatse yace “to Hajiya” sannan yadago yabama mai cart hannu suka gaisa sannan yakalli Amina hannu yabude mata dasauri ta rungumeshi tace “Yaya ina yini” kanta yashafa yace “lafiya lau Autan Hajiya” wheelchair ya karbe yashiga tura Hajiya da kanshi har mota saida ya zaunar da Hajiya tazama comfortable sannan ya sallami mai cart suka shiga mota suka tafi, Hajiya sai kallonshi take ta madubi tanamai hira tace “amman kai rashin lafiya ne ko Nura? Naga kafada sosai”? Dan murmushi yayi yace “aiki ne wlh Hajiya” ijiyan zuciya tasauke tace “to Allah yabaku sa’a kadinga hutawa kanacin abinci akai akai kaji ko” “to Mamana” ya amsa yana murmushi, tace “nataho maka da danderu” baki yabude yadan juyo zai kalleta dasauri tace “kul maida hankali tuki kake” dan dariya yayi yace “Meenah ya akayi akabar Hajiya tawuce da danderu”? Dan dariya tayi tace “ba anga batada lafiya ba babu wanda yayi musu da ita” murmushi kawai yayi yace “inason Mamana Ameena sosai” Hajiya data washe baki tace “nima inason d’ana sosai” Ameena ta turo baki tace “Hajiya nifa” dan dariya Hajiya tayi tace “Inason ku duka akwai wanda ma yasamu soyayyata irinki Auta na” ahaka suna family hira sukakai gida Nura yace “specialist danai consulting yace zai ganmu by 12 yanzu zakici abinci kihuta anjima saimuje asibitin ko” yayi maganan tareda yin Parking yafito da ita sabida dakali da kafanta tayi tafiya tana rikeda shi suna tafiya ahankali Ameena biye dasu tana kallon hadadden gidan, bude kofa sukayi suka shiga ciki wani lafiyayyen kamshi yamusu sallama dasauri Ummi tafito daga kitchen tazo har tsakiyan falon ta duka tace “sannu da zuwa Mama, ya hanya ya jiki, Allah yabaki lafiya Mama, Allah yasa kaffara ne” washe baki Hajiya tayi tana kallon Ummi tace “waye wannan yarinyar mai ladabi ba irin su Auta ba da basu gaida mutane da kyau, ga iya addu’a, waye ita”? Dan murmushi kadan Nura yayi yace “Ummi sunanta” daidai Hajiya na zama, Hajiya tasauke ijiyan zuciya tace “jiki Alhamdulillah Ummi, sannu kinji Allah miki albarka tashi tashi ki zauna, ina Hadiza? Nasan jikoki na ana makaranta ina Hadiza?” Hajiya takara tambayan da zuciya daya tana waige waige neman Hadiza, cikeda hikima Ummi tace “tadanje tadawo wani uzuri yakamata amman tace na kula dake da kyau kome kikeso namiki” sosai Nura ke kallon Ummi yanda yarinyar keda hikima baitaba sanin zata iya fadan magana hakaba, dariya Hajiya tayi tace “ayyooo” kallon Amina data shigo da jaka Ummi tayi gateman biye da ita da kayansu da sauri ta tashi tace “kawo nakai miki daki jeki zauna kihuta kinsha hanya” murmushi Meena tayi tace “thanks” kai kayan sukayi sama sannan Ummi tadawo tashiga kitchen a tray tajera abincin Hajiya da ruwa a bowl mai kyau na wanke hannu tafito takawo har gaban Hajiya, Hajiya tace “Ayyah sannu da aiki Ummi, Allah dai yasa cimata ne dan yanzu bakomi nakeci ba, cuta batayi ba” tai maganan tana bude kulan ganin tuwon Alkama da miyan zogale dayaji ganye yasa Hajiya tace “laaaaaaa Hadiza tamin girkin nan kafin tafice” dasauri Ummi tabude baki zatace eh Nura yace “Ummi ta dafa miki Hajiya” kara kallon Ummi Hajiya tayi saikuma ta nunawa Meena Ummi tace “kinga girkin sa’onninki ko ke sai shegen kiwuya, wai wannan kamshi haka bari naci abincin nan akasa zan zauna ma” da taimakon Nura tazauna akasa ta wanke hannu takai abincin baki saita kalli Nura takuma kalli Ummi takara kallon Nura again tace “Ummin nan dai danake gani tai girkin nan”? Gyadamata kai Nura yayi sai kawai Hajiya tace “Allahu Akbar wlh tayi girkin yanda nakeso, kaga ba gishiri ba magi, sannan bata sakamin jan nama ba hanta da Koda kadai ne amiyan, cimata tamin kuma yanda nakeso, bani jakana Meena kigani” bata jakanta Meena tayi Nura ya karba, dasauri Hajiya tace “ciro duka kudin dake purse dina” murmushi yayi ba musu yaciro dubu goma da dari biyar ne ta karba tamikama Ummi tace “ga tukuicin ki dan kin dadada mini rai kinsa natuna na diyata Aisha mai bin Nura tana aure a eygpt ita kadai kemini abinci irin wannan taste din wannan tarban da akamin bazan taba mancewa da ita ba, nagode ko Ummi amshi kudinki” akunyace tace “Mama kibar shi ni nadafa miki ne kawai wlh” Hajiya tace “laaaa ungo amshi nace” dan satan kallon Nura tayi shima kallonta yake ahankali yace “bazaki amsa kudin Hajiya ba kinsan kalan makon Hajiya kuwa? Ba kasafai akecin kudinta ba, ke kinyi sa’a tabaki” dariya duka sukayi harda Ameena, Hajiya tace “atoh dan haka karbi abinki” gently Ummi tasa hannu ta amsa ahankali tace “nagode Mama Allah ya ninka miki dubun su” Hajiya tace “Ameeen Ameeen” Ummi na murmushi takalli Ameena tace “nadafa miki shinkafa dafa duka dakuma taliya na manja wanne zan kawo miki” dasauri Ameena tace “taliyan manja” harzata tashi saikuma tadan kalli Nura dake kallonta kasa kasa tace “Alhaji mezan kawo maka bakayi breakfast ba kaima” abincin Hajiya yakalla yace “zanci abincin Hajiya” gyadamai kai tayi tawuce kitchen karaf akan idanun Hajiya yanda Nura ke kallon yarinyar amman batace komi ba, saida sukaci sukai kat Ummi takawo mata juice na cucumber kadai data mata Hajiya tasha sosai sannan Nura yakaita sama dakinsu dakin dake kusada na Hadiza inda Hadiza ta kwana ranan ta gyara Hajiya ma sai complain take ita batason sama Nura yace yafiso ta kwana inda zai dinga jin motsinta hakanan ta hakura.
    Wuraren 12 suka fice asibiti Ummi tasake gyara gidan.

    Sai wajajen shidda saura suka suka shigo gidan da gudu daga Aman har Amal sukazo suka rungume kakansu abinci Ummi takawo, tama Hajiya unripe plantain porridge datasa shuwaka da bushashen kifi da daddawa aciki shima ba maggi ba gishiri sai kamshi daddawa da kifi sun bama abincin taste, tayi jellof rice da naman rago ma sauran mutane, duk suka baje harda Nura za’aci abinci anan falo, Ummi takoma gefe ta duka Hajiya tace “kema taho nan kici, an taba haka ki mana girki saiki koma gefe, tahonan” dan satan kallon Nura tayi shi harya faracin faten Hajiya ma, da idanu yamata tazo nan, hakanan taje tashiga cikinsu suka faracin abinci, ita da Ameena da su Aman shinkafa sukeci, tunda tafara aiki yaune rana na farko data ji kaman tana gidansu Hajiya ne Gwaggon ta Amina kuma yan uwanta, sai hayaniya su Amal keyi anacin abinci, no wonder Alhaji keda kirki mahaifiyar shi batada matsala at all. Nura yace “Hajiya dan ban juice din cucumber dinki nasha” jug din Hajiya ta kalla tace “kai Nura na tsammaka na tsammaka harna gaji da sammaka wai kaine mara lafiyan nan ne”? Dariya akayi Ummi itama dan boye dariya ta tayi ganin yanda Hajiya keda barkwanci, takalli Nura tace “inje inmaka kaima Alhaji”? Batare daya kalleta ba yace “a’a kihuta zansha na Hajiya” kofi Hajiya ta dauka ta tsiyaya mai rabi ya karbe ita ta shanye rabin tace “Allah miki albarka Ummi zaki koyama wannan shashashan Autan nawa kafin mu koma” gyadama Hajiya kai tayi, Hajiya tace “Auta dukta cinye ke bakici komiba” dasauri Ummi tace “naci sosai wlh” kashigo falon ji zakayi inama haka farin ciki zai dawwama agidan, Nura yana lura da yanda bini bini Ummi kecin abincin tana duba Amal da Aman, chan kuma saita debo tai feeding Amal da mostly wasa take da abincin at this point bazaiyi karyaba yarinyar ta shiga ranshi sosai barinma dayaji labarinta dazu, yaji ta taba aure har ta haihu dudda pre matured birth tayi amma saiyaji yakara natsuwa da ita, wato saisa takeson yaranshi kuma saisa takeda hankali koba komi tanada experience, baison yayi mu’amala da yara masu danyan kai that knows nothing akan aure koba komi tasan menene aure kuma tayi zaman aure, tayi rainon ciki, sannan tayi nakuda, hakan is perfect for him.
    Sake lura da yanda yake satan kallonta Hajiya tayi daidai nan aka bude kofa aka shigo dukansu suka dago kai cikeda fara’a Hajiya tace “oyoyo oyoyoo, sannu da dawowa Hadiza” tundaga inda Hadiza ke tsaye tabi kowa na falon da kallo da yanda falon yayi kacha kacha dudda bawai kacha kachan yayi ba kayansu ne jaka da gyaluluwa dasuka zuba akan kujera dan dawowansu kenan Ummi ta taresu da abinci sai abincin da Amal da zuzzubar a falon rice din, daidai nan idanunta yasauka akan Ummi dake cin abinci tareda Amina dakuma yaranta akasa tana kokarin bama Amal abinci abaki hankalinta kwance dan akasa take zaune technically batayi laifi ba yau. “Ke menene aikinki? Jibi yanda gidana yayi kacha kacha zama kikayi kinacin abinci? Kina yar aiki waya gayamiki kinada darajan zama inda mijina yake kici abinci eh”? Yunkurawa Ummi tayi jikinta yayi sanyi zata tashi dasauri Hajiya tace “dakata Ummi” takalli Hadiza dake tsaye awajen da taje tace “ninace taci abinc……” “Hajiya dan Allah kidakata badake nake magana ba” Hadiza tayi maganan rai abace dasauri daga Nura har Ameena suka juyo suka kalleta da mugun mamaki itama Hajiya tayi tsuri tana kallonta dan batasan haka Hadiza tazama tasan ta dai da rashin son aiki ko sunzo babban salla Kano dama ba zama take agidanta ba saidai ta gudu gidansu so bata wani zauna da Hadiza one on one na dogon lokaci ba, ganin abun zai zama wani kala yasa dasauri Ummi ta tashi zata juya strictly Nura yace “dawo ki zauna kicigaba da cin abincin ki” cikeda tsoro Ummi takalli Nura gabanta na faduwa tadan kalli Hadiza dake kallonta rai abace ahankali takoma ta zauna abun ya mugun mugun yima Hadiza ciwo dan yaune rana na farko daya nuna bata isaba agaban yar aikin yawanci ba agaban idanunta suke tsiyansu ba, zuciyanta wani kalan baki yayi takalli Nura tace “muzuba nidakai badai anzo har cikin gidana ana nema ajuyamaka kai ba tun yanzu an fara kulla kisisina da shairi ko da sunan rashin lafiya amman bakin mutum rass yazauna yana zakalkalan abinci to wlh muzuba dani dakai” Ameena jitayi kirjinta na tafarfasa badan Ya Nura na zaune wajen ba da wlh saita durama Hadiza ashar wucewa tayi fuuuu tayi sama kunyan duniya rufe Nura yayi abinda matarshi tama Hajiya jiyayi ma abincin ya isheshi kowama hatta yaran jisukayi abincin ya ishesu Hajiya ta kalli Ameena tace “tashi keda Ummi ku gyara wurin” kunya yasa Nura yamike yama kasa kallon kwayan idanun Hajiya yajuya yace “bari nazo Hajiya” baima jira amsanta ba yafice dasauri Hajiya tabishi da kallo saitaji dan nata yabata tausayi.
    Kayan daya sayo dazu yasa mai gadi ya kwashe yakaima Ummi sannan yaja mota yabar gidan.

     

    Abin yama Hajiya ciwo sosai, ya sosa mata rai, ta haifi yaran dasuka girmi Hadiza, yaranta mata uku biyu sunyi aure saura daya, ita Hadiza zatama rashin kunya haka. Dawowa daga kitchen Meena tayi ganin ba Yayanta awajen tazauna kusada Hajiya tace “Hajiya Hadizan nan yar iska ce kuma wlh wlh ta ijiye iskancin ta a inda tasabayi let her not try that nonsense da ke inba hakaba ni kadai na isheta wlh dan idan nakira su Ya Aisha har gida zasuzo sumata shegen duka ba Egypt ba Ya Aisha zata iya barin ko’ina take aduniya tazo muma duk wacce ta zageki shegen duka……” hannu Hajiya tadaga mata tace “banson maganan nan Auta, Matar yayanki ne” cikin fushi Meena tace “koma waye dama nasha gayamiki halinta tunda kika fara rashin lafiya sau daya bata taba kiranki taji yajikinki ba, yar iska kawai mahaukaciya wacce batasan darajan iyaye ba idanma kinci abinci na kanin ubanta kikaci kona danki, okay saitaga kina shurin mutuwa ne zatasan baki da lafiya dakikiya kawai” Hadiza dataji duka maganganun Meena dan saukowa tayi zataci abinci takoma sama saikuma gobe, takarasa saukowa takalli Ameena dabama ta lurada itaba tace “did u just call me dakikiya Ameena”? Dasauri daga Hajiya har Meena suka juyo suka kalleta Meeena zatai magana Hajiya taja hannunta cikeda hikima irin na manya tace “a’a badake takeba Hadiza wani labari take bani daya faru a kano” kwafa Hadiza tayi tace “gwara dan wlh dasaita bar gidan nan yanzun nan kema kibita” fizge hannunta Meena tayi daga hannun Hajiya tamike tsaye tai wajen Hadizan dan rainin wayon ta yayi yawa ta nunata da hannu tace “an kiraki dakikiya dake nake Hadiza idan baki koreni daga gidan nan ba baki cika yar halas ba” Hajiya datake daga zaune tahau yunkurin tashi tana kwalama Meena kira itama Ummi tafito daga kitchen da gudu tazo wajen yaran ma haka daidai Hadiza na nuna Hajiya tace “kinga dakikiya chan not me” Meena batai wata wata ba ta daurama Hadiza mari abaki jikake tasss!!!! Haba sai jini Hadiza ta kurma ihu tadaura hannunta kan bakinta dataji lema lema tacire hannu taga jini ahaukace tace “ni kika mara”? Ta chakume gaban rigan Meena da karfi, dambe sukahauyi ba kama hannun yaro Hajiya tafashe da kuka sosai Ummi tashiga rabasu amman ina basa rabuwa, dukan juna suke sosai bana wasa ba, Meena ta fizge ribbon din gashin nan taja gashin kaman zata cire mata su daga tushen kwakwalwa, da gudu Ummi tayi waje Mai gadin su takira yazo da kyar aka iya rabasu aiko Meena ta bala’in lallasa Hadiza bakinta sai jini yake ta yayyakusheta a wuya da hannu, dudda itama Meena ta daku a hannun Hadizan amman bata sami any ciwo ba kaman yanda tama Hadiza kowa sai nishi yake, shiga tsakaninsu gateman yayi Ummi tarike Meena tace “dan Allah kuyakuri” cikide zuciya Meena tace “kada kice na yakuri Ummi ba’a haifi wacce zata zagan mini uwa agabana banyi wani abu ba, am I even my mother’s daughter idan agabana za’ahau zagin Mamana nai yi shiru eh? Is she mad? Ba’a bata tarbiya agidan su bane? Idan ba’a bataba ni I will give u, dagayau kowace uwa kika tashi zagi zaki tuna diyar wata ta taba miki duka dakika zagan mata uwa, you are very very very stupid to insult Hajiya kinji, shegiya mai halin matan da iyayensu sukama baki” cikin ihu da kururuwa Hadiza tace “wlh, wlh, wlh yau saina kulleki a police station na rantse da Allah, ni kika daka kin san wacece ni anan Abuja? Number one, the most successful business owner anan Abuja, kinsan award guda nawa ke cikin office dina? BBC waye waye duk anyi hira dani, nizaki zo har gidana ki daka? Wlh wlh u are a small girl yau zan nuna miki your place” tana maganan tayi kofa bayan ta fincike key nata awajen tray na car key ta shiga motanta tafice dasauri Ummi tasaki Meena tayi wajen Hajiya dake kuka shikuma gateman yace “ayi hakuri ayi hakuri” yawuce yafita.
    Dukawa Ummi tayi takai hannunta tana sharema Hajiya fuska tace “Hajiya kiyakuri” da kyar Hajiya ke iya magana tace “Ummi kiramini Nura gobe goben nan zan koma gida Meena batajin magana nasha gayamata zuciya batakai mutum ko’ina, kowani zagi Hadiza tamini sai mene ita ta zaga basaita bartaba akanme zatai dambe da Matar yayanta eh akan mene daga zuwa na garin nan yau yau din nan? To ko warakata na nan nahakura kiramin Nura idan akwai jirgi yanzun yanzun nan ma komawata zanyi kano” yanda Hajiya ke kuka tana bama Ummi wayanta yasa takira Nura, yana dauka yace “Hajiya” ahankali tace “nice kazo gida Hajiya na nemanka” hakanan jikinshi yabashi wani abu daman baiyi nisa ba duka duka yana ta gaban estate nasu fruits yaje saya yasan yanda Hadiza tadawo saitai rashin mutunci saisa baiyi nisa ba at all dasauri ya katse wayan, ijiye wayan Ummi tayi tadauki Amal dake kuka sosai ta goya Aman ma ta lallasheshi dan duk kuka suke sunga anci uwar Maman su, taje wajen Meena dake wajen dinning zaune akasa yanda Hajiya ke kuka yasa she’s feeling so guilty dan yanzun nan hawan jininta zakaga yatashi, yana isowa gidan ko parking baiyi da kyau ba yafito yashigo gidan Hajiya yagani tana kuka sosai yaranshi suma kuka Ummi sai jijjiga Amal take ga Meena akasan dinning idanunta sunyi jazur kayanta ya chukurkude kaman wani abu yafaru dasauri yayi wajen Hajiya ya duka yace “subhanallahi hajiya menene haka?” Cikin kuka tace “kaga Ameenatu yarinyar chan bazata taba daina jamini bala’i aduniya ba, duba jirgi yanzun nan idan an samu mukoma kano nahakura da asibitin Nura bazan iyaba bazan iya da tashin hankali ba” rungume Hajiya yayi yace “ya isa Hajiya ya isa daina kuka muje ki kwanta gobe da sassafe saiki koma” yay maganan trying to just calm her down, yace “ya isa ko I’m here now, everything is gonna be fine”.

    Sama yakaita yana zuwa wani allura yamata a hannu da Dr yace adinga mata idan anga hankalinta yatashi nan da nan bacci yadauketa yasauko kasa yazo inda Meena take zaune yace “Meya faru?” Baki tabude zatayi magana saikuma tafashe da kuka cikin kuka tafada mai duka abinda yafaru batai karyaba zaiyi magana daidai an bugo kofa an shigo Ummi ce dawasu yan sanda guda biyu ta nuna Meena tace “officer ga tachan” tashi da sauri Nura yayi yana kallon Hadiza da yan sandan guda biyu wanda ganin Nura yasa basu karasa shigowa falon ba duk suka tsaya anan mini parlor dasauri yakaraso inda suke ya mike musu hannu yace “officer lafiya”? Mutumin yace “Madam dinka ne tashigar da kara kan mother Inlaw ta da sister Inlaw sunzo har gidanta sun mata taron dangi anmata duka, kuma munga shaida bakinta da wuyanta saisa muka biyota muyi arresting sai amusu sulhu a police station” ijiyan zuciya yasauke yajuyo yakalli Ummi dake faman jijjiga Amal tana kuka tarike hannun Aman yace “ku tafi sama keda Meena dakin Hajiya ku rufo kofa” dan yasan Hadiza zata iya kamasu da duka kuma, gyadamai kai tayi tawuce takama Meena duk sukai sama, Hadiza tace “ba sama ba ko lahira kukaje sai anyi arresting naku yau wlh” officers din duk suka kalli Hadiza Nura yace “bismillah ku muje waje” binshi sukai waje Hadiza tabiyosu officer da kanshi yace “ki barmu maza muyi magana mana Madam” tsayawa tayi saikuma ta buga tsaki takoma daki, explaining komi Nura yamusu yama nuna musu some magungunan Hajiya dake motanshi yabasu hakuri kan kada suyi arresting kanwarshi, ganin kamalan shi da natsuwan shi duba kuma da babban mutum ne, a well known businessman anan Abuja kuma ba yaro ba sannan sunga yanda Hadizan keyi itama borkonon kanta ce yasa sukai Na’am dudda haka saida suka amshi 20k a hannunshi kafin su tafi, suna tafiya ya tsaya ya jingina da mota yadan sauke ijiyan zuciya baiso ya yanke decision cikin fushi yakai 5min awajen sannan yakoma ciki afalo yaga Hadiza jikin window tana ganinshi ta taho tana ihu tana tafi tace “u bribe them and send them away sabida kar ayi arresting sister ka da Maman ka ko? To rest assure wlh wlh I will so deal with them, wlh saisun barmin gida, babu wani mahaluki dazai shigo gidana and snatched my peace of mind for me to menene amfanin karatun danayi? Ina zaman zamana wata Maman miji ta dawo gidana da zama is that even fair? Ba manyan asibitoci ne a Kano? Why here why Abuja? Let’s be fair fa Nuri, lokacin da Maman ka ke gidan mijinta mother inlaw dinta tazo ta tare mata agida? Then why me? Kuma ace ban isa nayi complain ba? Still sun shigo ur sister nada taurin zuciyan ta daken ni? Ni Hadiza? Wlh u have to choose one koka tattarasu kaje ka nema musu hotel ko ka maidasu kano, this house belongs to me and you Nuri aure yabani gidan nan, dan haka wlh sai sunbar gidan nan” girgiza mata kai Nura yayi, cikin kakkausan murya yace “wlh saidai ke kibar gidan nan not my mom! ki tattara kayanki kibar gidan nan don’t sleep in my house Hadiza, Na Sake Ki SAKI DAYA!”.

     

    The foundation of Marriage is built on trust, respect, biyayya and love which I think Hadiza broke all awajen Nura, now do you all support sakin daya mata? Or do you think he should’ve done something entirely different???

    Now the major abu da matan aure fears dayasa basason yan uwan miji suzo is because Men always tends to take side din yan uwansu and neglect side na matan su tambaya na anan shine Nura shima yadauki side din yan uwanshi kenan?? Or kuna tunanin he should’ve done better???

    As a woman can you stand kiga an zagi mahaifiyarki data haifeki? Do you support action din Meena or not? Dan two things are involve Hadiza matan yayan tane sannan Hadiza ta girmeta far far and surprisingly Nura bai cema kanwarshi Meena anything ba….hmmmm share your two cents on this😞

    Now overall tambayata is kuna tunanin basics na mata akan basason yan uwan miji suzo gidansu uhmmm to some extend sunada gaskiya dan maza always takes side na family su gaskiya ne???
    How should a family Man dazai sami kanshi a tsakiyan conflict tsakanin relatives nashi da matanshi address the matter??

    See y’all Saturday 💃
    [9/18, 9:17 PM] +234 706 542 1229: 💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

    ✍🏻M SHAKUR