Category: Hausa Novels

  • Arubuce Ta Ke 49

    Arubuce Ta Ke 49

    Page 49

    Awanni kusan hudu kenan tana abu guda,baya ga kitchen din data yiwa kaca kaca kota ina,kamar wadda ke girkin mutum ashirin,sannan daga bisani ta samu ta kammala tuwon shinkafa miyar kubewa iya yadda taga latifa tana yi,ta zuba cikin sabbin warmer masu kyau da aka hado cikin siyayyar cefanen da aka kawosu jiya.

    Dafe bayanta tayi bayan ta kammala gyare kitchen din

    “Shi tuwo dama haka yake da wahala?”ta fada tana yatsina fuska,duk da can qasan ranta farinciki ne fal,wai yau itace da yin girki cikin kitchen dinta,ba kwaba ba hantara babu bakiyi dai dai ba,ta juya ta soma diban warmers din takai saman dining,ta jeresu da kyau,tana kallonsu tana murmushi,har cikin ranta dadi take ji idan ta tuna wai yau ance tayi girki.

    Dakinta ta koma tayi wanka,ta shafa powder a kyakkyawan fuskarta mai santsi da sheqi dauke da tambari na quruciya,dubai abaya wine color da tasha adon duwatsu masu walwali ta fidda ta sanya,ta daura dankwalin saman kanta,ta kuma shafa turarukanta kamar yadda ya taba gwada mata yadda ake sanyasu,tun daga ranar kuwa ta dauke tsaf,yadda ya kwatanta matan haka take sakawa,ita kanta sai taji tafi jin dadinsu.

    Sosai abayan ta haska jar fatarta,kamanninta suka fito sak na ainihin tushen yankin data fito,ta koma gefan gadonta bayan ta dauko wayarta dake saman madubi,ta bude ta shiga wata game da taketa daukan hankalinta ta fara bugawa cikin qwarewa.

    Hankalinta yayi nisa sosai a game din,har bataji qarar motarsa zuwa shigowarsa cikin gidan ya kuma tura qofar dakinta ba,sai ya tsaya riqe da handle din qofar dakin,zai iya lissafa adadin shigowarsa dakin,idanunsa saman fuskarta,tattausan siraran labbanta sunata qyallin lips balm,tana ta juyi saman gadon,duk sanda taci game din sai tayi dan tsalle kadan na murna sannan taci gaba.

    Idanunsa ya dauke sannan yayi gyaran murya kadan ya hada da sallama,daga idonta tayi daga kan wayar zuwa kansa,saita aje wayar gefanta tana masa sannu da zuwa,sannan a dabarance tana laluba maballan gaban rigarta taji sun rufu da kyau?,ta kuma tsareshi sosai da ido taga ko.yana kallonta?.

    Sarai yaga abinda takeyi,amma sai ya kauda kai ba tare da yakai idanuwansa kan qirjin nata da yake ganin basu da maraba da qirgar dangi a wajensa ba

    “Tare da baqo nake,ki kawo abincin” kai ta gyada masa,ya saki handle din qofar ya juya zuwa falon,yana duba wayarsa daketa ringing.

    Ba kowa ke kiransa ba sai hafsat,tunda satin ya wuce taga baizo weekend ba hankalinta ya gaza kwanciya,gaba daya zuciyarta cike take da wasi wasi da kuma fargaba,duk kuwa da bayanin da yayi mata na cushewar aiki da ya samu a kaduna fiye da dukka garuruwan da yake zuwa aiki,amma zuciyarta ta kasa aminta da hakan,duk inda yake baya wuce satin nan dai baizo bauchi ba ko don hajiyarsa,sai wannan karon?,sai wannan lokacin daya tafi da wannan sadakar yallan?,anya ba holewarsa yakeyi ba?,anya bai samu wani abu bane daga gareta?.

    A kullum kwanan duniya kira uku zuwa hudu ne sai ta yiwa widad shi,ta tambayi ya suka kwana?,ya suka tashi?,ya suka yini?,ya dawo gida kuwa?,me ya faru a tsakaninsu?.

    Sam widad din bata boye mata komai,rashin wayo da qarancin shekaru yasa bata dsuki wannan din a mazaunin komai ba,face ma qauna soyayya da kulawar da mommy hafsa din ke nuna mata,wannan yasa ta sake ganin kimarta,ta kuma sake ganin girmanta,hakanan taji tana qaunarta,shi yasa dukkan abinda zata umarceta dashi take aiwatarwa kanta tsaye,wannan dalilin ne kuma yasa tayi riqo da hudubarta yadda ya kamata,don ya zame mata kamar tishi ne akan tarbiyyar ummu,sai faduwa tazo dai dai da zama,tana nisantarsa iyakar iyawarta,tana kuma qauracewa duk wani abu da tasan mommy hafsa ta gargadi akai.

    Ta sani ta kuma fuskanta,sam qarya bata cikin dabi’ar widad,da gaske haka take tun a gida,duk da samun wannan tabbacin,hakan bai sanya zuciyarta da ruhinta sun aminta sun kuma kubuta daga zargin abbas ba, don haka taketa kiransa,tanason taji yaushe zai zo din.

    Ajiyar zuciya ya sauke,yau inda ace buqata ce da hafsat din dole.ya ajjiye dukkan abinda yakeyi yaje ya sauke mata ita,to amma yafi kowa sanin wacece ita,tana iya share wata guda koma fiye bata buqaci komai daga gareshi ba,saidai shi din ya nema,a yanzun ma.ya tabbatar ba wani qwaqwaqwaran dalili ne da ita ba na kafewar ya taho din,ya bata dukkan wata dama da zata fadi uzurinta amma amsa daya ce

    “Kawai son ganinka nakeyi”

    “Kiyi haquri,indai ba babbar buqata ce dake ba……akwai aikin da nakeyi a nan din,banason kuma na matsa daga kaduna sai na kammalashi,aikin yana buqatar sirri kula da kuma takatsantsan” amsar daya bawa hafsan kenan,ta furzar da iska dgaa bakinta,zuciyarta na raya mata ta shirya ta tafi Kaduna kawai,to amma sanin girman laifin data aikata masa wanda yayi silar haramata mata Kaduna kwata kwata yasa ta sake jaddadawa kanta wannan ba mafita bace,zata bi ta hanyar da tasan dole yazo gida koda baiso ba.

    Sai data nema yalwataccen mayafi ta yane jikinta dashi sannan ta wuce falon,idanun abbas din a kanta,hakanan yaji abinda tayin ta burgeshi,bai gaya mata ta yafa din ba,amma tasan ya kamata,ta tsugunna har qasa ta gaida ameen abokinsa,sannan ta wuce ta soma dauko warmers din tana jera musu bayan ta shimfida table mat a qasan.

    Ta tsara komai yadda ya dace,har cikin ransa yaji abinda tayi ya burgeshi,ruwan sha dana wanke hannu duka akwai a wajen,abinda hafsat bata taba yi ba,dai dai da tissue daya dace ko yaushe a sameta saman dining sai ya nema,ita kuwa ta koyo hakanne daga wajen ummu,haka taga tana yiwa alhaji.

    Har ta juya zata wuce daki,sai taga ana hasko wani cartoon da take mugun so,fasa shiga dakin tayi,ta dawo ta zauna fuskarta cike da fara’a,kadan abbas ya waiwaya ya kalleta,kamar zaiyi magana saiya fasa,ganin irin excitement din dake kan fuskarta na ganin cartoon din,ya maida kansa ga warmer din,ya bude ya sanya hannunsa ya dauko malmalar tuwon farko.

    Tun baikai ga budeta ba ya fahimci an samu babbar matsala,duk da haka bai fasa ba,ya wareta yana sakinta saman plate,take kuwa tuwon ya dare biyu,suka hada ido da ameen din,sai abbas din ya basar,ya bude warmer din miyar,koriyar kubewa shar,wadda aka qarantawa kayan hadi ta bayyana,bama kayan hadi ba,harda kayan dahuwa,wake yayi tsuru tsuru yaja gefe,ga danyan manja a sama ya hade rai.

    Serving spoon yasa ya kwaso musu ita da qyar ya zuba akan plate din,ya maidata ya rufe ya saka musu cokula yana cewa da ameen

    “Bismillah” dukka dauriyarsa amee din ya gayyato,ya matso ya dauki cokalin,suka sanya lomar farko a tare da abbas din.

    Spoon din ya ajjiye sannan ya miqe yana duban abbas

    “Kasan nayi mantuwa a office,zan koma,daga can gida zan wuce” yadda ameen din keta rattaba bayani ya bawa abbas dariya,amma sai.ya qushe abarsa,gulma ce da ganin qarshen mutum tasa yace zaya biyoshi

    “Okay….sai na fito” ya amsa masa,sai ameen din ya juya yana cewa

    “Amarya,ni zan koma ko,ina godiya sosai,sauri nake.ban samu naci abincin ba,amma…… next time”

    “Ka gaida gida” ta furta a sanyaye sanda ta kalli abincin taga kamar babu abinda ya dandana,idanunta nakan plate din har ya fice a gidan.

    Dukkan alamu sun nuna.girkin nan nauyi dadi ko ma’ana ba sam,jikinta a sanyaye,ta tabbatar shima ajiye mata abincinta zaiyi,ba iya ci zaiyi ba,musamman data hangi yadda tuwon ya baje abinsa,ya koma kamar shinkafar da bata samu wadatacciyar dahuwa ba.

    A mamakance ta maida dubanta ga fuskarsa,sai kai abincin bakinsa yake,kamar babu wani abu da baiyi dai dai ba a girkin,karo na uku suka sake hada idanu tana masa kallon mamaki

    “Zonan” ya fada a tausashe yana yafitota da hannunsa,saita aje filon data dora saman cinyarta,ta miqe a sanyaye ta nufeshi.

    Idanunta na tara ruwan hawaye.

    Gabansa ya nuna mata,ta zauna a hankali tana sake ja baya kadan,qaramin murmushi ya subuce masa yana kallon qwayar idanunta,sannan ya tsame hannunsa daga abincin bayan yaci wani adadi mai yawa

    “Tuwo yayi fa dadi,gyaran kadanne” da farko shuru tayi tana dubansa,fuskarta dauke da alamun mamaki,daga baya kuma sai murmushi ya subuce mata,cikin wani irin zumudi da sakewar da bata tabayi dashi ba

    “Allah?,ashe dai na iya girki” ta fada cikin murna,kai ya gyada mata yana kallonta

    “Kin iya,amma na fiki iyawa ai” ido ta fidda waje tana dubansa

    “Namiji dama ya iya girki?” Ya jinjina mata kai qaramin murmushi na fita daga fuskarsa

    “Iyawa kai,ki shirya daga gobe zan fara koya miki irin nawa” sosai taji dadi da fadin hakan da yayi,ita din tanason taga ta iya girki irin na anty madina da anty deena.

    Cikin ransa yakejin dole haka zai samu lokaci cikin lokutansa ya ware ya koya mata wasu abubuwan kafin ya laluba makarantar koyon girki ya sakata,at least koda girkin ta iya zai rage wani abun.

    Washegari da safe shi yayi mata knocking ta fito,ta rusuna ta gaidashi tana sanye da kayan bacci masu kauri riga da wando da wando,tana biye dashi suka isa kitchen,ya sama mata kujera yace

    “Zauna a nan ki gani” murmushi ta sake tana kallonsa,sanye da wani wando na sojoji da farar shirt,ta zauna din sannan ta jefa masa tambayar dake cinta tun daxu

    “Wai kai police ne kuma soja ne?” Sai daya juyo ya kalleta da manyan idanunsa,sai tayi tsuru tsuru kuma tana dafe bakinta,tana jin kamar tambayar tayi yawa,kai ya girgiza yana sakin fuskarsa

    “Ni police ne me kama masu laifi” saita jinjina kai tana murmushi kawai.

    Cikin kitchen din taci gaba da zama,kome zaiyi sai ya nuna mata,saidai tana daga gefe tana d’ari d’ari dashi,bata bari tazarar dake tsakaninsu tayi kusa,ya lura amma dariya kawai take bashi,daga baya bayan ya gama hada komai,ya bata yanke yanke yace tayi masa tana daga zaune.

    Cikin awa daya da rabi suka hada breakfast mai kyau tare,ta dinga murna tana jin dadi,shi kam saidai ya bita da ido,bayan sun kammala yabar mata kitchen din ta gyara,shi kuma ya wuce dakinsa yin wanka,ta gyara ta kwaso komai ta kawo falon,saita zube saman kujera tana maida numfashi,don tadan gaji,sai data huta sannan ta wuce itama dakin don yin wankan.

    A ranar ma ya samu sauqin aiki,don haka da rana ya dawo gida,ganinsa a gida da rana ba qaramin dadi yayi mata,ashe mutum rahama ne,cikin zuciyarta ta dinga jin wani dadi,duk da babu abinda ke hadasu daga sannu da zuwa zai wuce dakinsa ne,bayan ya fito suka sake shiga kitchen tare,ta dinga murna da zumudin son ganin me zasu dafa,abinci sassauqa sukayi,itadai tana ta mamakin yadda namiji ya iya girki haka,bayan sun gama kowa yaci nashi ya sake shiryawa ya koma.

    To da daddare ma haka,sabon girki sukayi,duk abinda yakeyi idanunta na kanshi tana biye,haka ce taci gaba da kasancewa,cikin satin gaba daya aiki biyu ya dinga yi,yayi na office ya dawo gida ya koya mata abinda ya sawwaqa,wani lokaci idan bai samu dawowa da rana ba,to da daddare akeyi.

    Cikin satin sai gashi an samu ci gaba,ta riqe wasu abubuwan,da yake widad din badai kai ba,kuma tana da qaunar yin girkin,sai gashi a satin ta iya hada breakfast,hakanan abincin duk daya koya mata ta fara gwadawa,yana kuma yi,saidai hannun baikai ga fadawa sosai ba.

    Ranar wata alhamis bayan sun gama girkin dare ya fiddo foam yace ta matso ta bashi bayananta zai cike,foam ne na wata makarantar secondry ta ‘yammata daya samar mata zata ci gaba da zuwa,tsananin murna yasa ta fada jikinsa ta qanqameshi tana godiya,sai kuma ta sakeshi da sauri taja baya,jikinta nayin wani irin sanyi,kada fa mommy ta gane ta rungumeshi,tayi tsuru tsuru,har sai daya fahimta,ya dade da fahimtar wannan,koda a kitchen da suke ayyuka tare duk abinda zai kawo haduwarsu waje guda tana daga baya baya,ko abu zai bata sai ya ajjiye take dauka,hakanan suna gama komai take qulewa daki ta kulle abinta,shikam dariya take bashi,kamar yanzun,baisan me take tunani ba,shikam indai abinda take tunani ne idan yayishi yace yayi me?,saiya girgiza kai kawai yana boye murmushinsa cikin fuskarsa ya fara cike mata foam din,bayan ya gama ya miqa mata yana cewa

    “Idan zan fita gobe zan karba na fita dashi,and….ki shirya jibi zamu je bauchi” ta karba foam din jikinta a mace,sai taji inama ace kano yace mata zasuje?, tabbas da ranar ba zata iya bacci ba.

    *Arewabooks: Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 39

    Arubuce Ta Ke 39

    Page 39

    Cikin girmamawa latifa dake zaune gaban widad wadda ke lafe cikin kujera kamar wata ‘yar mage tana hawaye ta amsa sallamarsa,idanunsa a kanta ya qaraso shigo wa,sai ya janye idanuwan nasa ya tsaya tsakiyar falon yana rungume da hannayensa.

    Gaidashi latifan tayi,ya amsa a mutunce sanann ya sake maida dubansa ga widad tare da tura tambayarsa ga latifa

    “Lafiya dai ko?,ba wani matsala?” Gyara tsaiwarta kadan tayi

    “Uhmmm,wallahi gata nan,tunda suka tafi take kuka,nayi nayi da ita amma taqi yin shuru,yau ko abinci bata ci ba”

    “Ya salam” ya fada yana lumshe idanunsa hadi da. Budesu lokaci guda

    “Matsala kan matsala” ya furta qasan ransa,saiya sauke hannuwansa ya fara takowa zuwa inda take kwance,ganin haka sai latifa ta juya ta nufi daki.

    Dab da ita ya tsaya yana dubanta,ita kuma saita cusa kanta cikin pillow tana sake sakin sabon kuka,batason ganinsa kwata kwata,saboda shi ya jawo mata,qila da tuni yanzu suna wajen anty madina suna hirarsu abinsu,qila da tuni yanzu suna falon ummu suna kallo da hirarrakinsu,da tuni yanzu ba cikin pillow take kwance ba,da tuni kanta yana kan cinyar ummu tana sosa mata kai,a hankali ya rage tsahonsa ya tsugunna a gabanta,saiya sarqafe hannayensa guri guda yana kallonta,ta takura sosai a kwanciyar da tayi,amma baisan ta yaya zai gyara ta ba,yana jin tashin sautin kukanta,amma baisan ta yaya zai fara lallashinta ba,idan nawwara ce ko mimi chocolate zai hadasu da ita,to amma ita din aita dara a rarrasheta da chocolate.

    Duk yadda ya kamo zaren lallashinta ya kasa daidaitashi da tunaninta,bayason qarya sam a rayuwarsa,kuma ba maqaryaci bane duk rintsi,amma a yanzun da aka hadashi da rainon yarinya dole sai ya hada da canza maganganunsa

    “Tashi muje” ya fada a hankali,abu na farko da yazo kanta shine gida zai kaita,don haka ta daga kanta da wani mugun hanzari,ta sauke manyan fararen idanunta da suka sauya launi saboda kuka tana dubansa

    “Gida zaka kaini wajen ummu?” Sai ya gyada mata kai,yana kallon yadda farar fuskarta tayi pink sosai saboda kuka,kafin ya gama tunanin sa tuni ta diro daga kan kujerar,ta nufi hanyar daki tana kiran sunan latifa ta dauko musu kayansu

    “Wait….zo mana kiji” ya kirata yana miqewa da sauri,saita tsaya cak,sannan ta saka hannunta tana maida gashinta baya,saboda ya rufe mata idanu bata ganinsa da kyau

    “Hijab kawai zaki dauko,kayan sai daga baya kinga suna da yawa,itama ki barta a nan zata biyomu”

    “To” kawai tace masa,saita qara wuta zuwa daki harda hadawa da sassarfa.

    Tafin hannunsa yasa ya dafe goshinsa,ya Allah…..a sanda kake buqatar ka huta……wannan wanne sabon raino ne ya sameshi?.

    Tunda latifa ta ganta afujajan ta kuma gaya mata me yace sai tayi murmushi kawai ta miqa mata hijab din tana cewa

    “Allah ya kiyaye hanya,saina taho” ta zura hijab din tayi gaba abinta.

    “Na shirya” ta fada a shagwabe tana karya wuya sanda ta dawo falon,kallon fuskarta sosai yayi,hijab din ya qara mata kwarjini,sai ya juya a hankali ba tare da yace mata komai ba ya soma ficewa,tuni tayi tsalle ta dafa masa baya,don kafin ya fice ma harta tarar dashi,jinta a gefansa ya sanyashi waiwayawa,dai dai sanda itama ta daga kai ta kalleshi,sai suka hada idanu,wani abu mai nauyi taji ya saukar mata,sai tadan dakata har sai daya gota mata da kusan taku uku sannan tabi bayansa.

    Da kansa ya bude mata seat din gaba ta shiga,sannan ya zagaya ya shiga shima ya tada motar,ta sauke ajiyar zuciya wadda ke hade da sheshsheqar kukan da tasha,sai taji hankalinta ya kwanta sanda suka hau kwalta,zata koma wajen ummunta.

    A hankali yake tuqin,ya rage speed na motar sosai,sai widad tayi relaxing sosai jikin kujera tana kallon yadda suke wuce titunan garin bauchi a hankali,kamar zata masa maganar cewa baya sauri,amma sai taga sannu sannu dai tunda sun fito zasu isa wajen ummun.

    Cikin nutsuwa da salo na janye hankali ya dinga bi tituna tituna da ita,tun tana zuba idanu taga sun dauki hanya dodar harta haqura taci gaba da bin unguwannin da suketa wucewa da kallo,wani waje ya burgeta,wani gurin taga kamar kano,wani gurin kuma taga kano tafi wajen kyau.

    Agogon hannunsa ya kalla,dai dai sanda ya nuna masa sha biyu saura na dare,saiya juya kan motar yayi reverse,ya koma asalin titin da zai maidasu gida.

    Tun tana zaune saman kujera tana chart su mimi na wasa a saman carfet,har bacci ya daukesu,sai a sannan ta lura da yadda lokaci yaja,to a ina ya tsaya?,ta tambayi kanta bayan ta gama kwantar da yaran,qirjinta ya buga sanda zuciyarta ta raya mata yana can da yarinyar yana neman hadin kanta qila kamar yadda ta samesu ran nan,tunanin da ya sanyata fara neman spare key din gefen nasa,wanda ta jima rabon da tayi amfani dashi,jikinta har rawa yake,bata ankara da rigar jikinta ta bambanta da zanin jikinta ba ta zaqulo muqullin ta fito da wani irin sauri.

    Cike da qwarin gwiwa ta sanya key din ta buda sashen nasa,wayam ba kowa a falon,wata zuciyar ta gaya mata suna can kan gadonsa yana cin amanarta,saita qara hanzari ta cusa kai bedroom din nasa,nan ma babu kowa,ta tsaya jim tana tad’i ita da zuciyarta,sai taji ranta yana raya mata qila yana sassanta acan suka yada zango,ta sake juyowa a birkice tana fita a sassan nasa.

    Tunga taja ta tsaya ganin alamun qofar falon na kulle ta ciki,wannan ya sake tunzurata,zarginta kuma ya fara hauhawa,ta fara bugun qofar da qarfi.

    Da hanzari latifa ta taso,wadda tuni bacci ya dauketa,gabanta ya dinga faduwa din irin qarfin bugun da akewa qofar

    “Allah yasa lafiya,Allah yasa ba wani abu bane ya faru” ta dinga fadi cikin zuciyarta sanda take kan hanyar zuwa ta bude qofar.

    Kallon kallo suka yiwa juna na sakanni kafin latifa ta tuna wace,saita sake fuska

    “Barka da dare” ta fada tana duban fuskar hafsat,bata amsa ba illa cewa da tayi

    “Tana ciki ne?” Kai ta girgiza

    “Sun fita,tun dazu kuwa,nima su nake tsimaye” saura kadan tayi subutar bakin sako ashar,Allah ya taimaketa ta danneta can qasan ranta,wani abu mai zafi da quna ya soma mata suya a qirji,wata mace abbas ya saka a gaban mota suka fita?,me yake nufi?,zai daidaita matsayinsa da yarinyar da ita take mata kallon bata da maraba da babu?,don cin fuska tana can tana zaman jiransa,bai gaya mata ma cewa ya fita din ba saidai taji a bakin wata?,saita juya ba tare da tace mata komai ba ta fara barin wajen,latifan ta bita da kallo ranta cike da tambayoyi,daga bisani ta maida qofar ta sakayata,ta koma falon ta zauna saman kujera tana hamma tare da duba lokaci,bataso ta koma bacci suzo kuma suyita bugu.

    Dab da zata isa sashenta qarar bude qofa da kuma hasken motarsa ya risketa,saita tsaya cak tana motar,kafin ta fara takawa zuwa wajen,tanason taga idanun abbas,da wanne baki zai mata bayani kuma?.

    Yana kashe motar tana isowa saboda saurin data kwaso,ya sauke Glass din motar a hankali yana dubanta kafin yace

    “Bakiyi bacci ba?,inata so na kiraki kuma saina sha’afa” hakan daya fada ba abinda yayi mata illa sake tunzurata,ya manta ma kenan da ita?,takai dubanta ga widad wadda jikinta ya gama yin la’asar,ta kwantar da kanta a seat din motar,bacci gaba daya ya cika mata idanunta,duk da haka ta hadiye

    “Qanwarki keta rigima nadan fita da ita” sosai tayi namijin qoqarin danne wani mulmulallen abun daya taso ya tsaya mata a wuya,bataso sam ya tabata da niyyar dagata ko taimaka mata ta fito,don haka tayi saurin zagayawa side din ta bude mata qofar tana cewa

    “Ayyah…..haba widad?,banda abinki da haka kowa yake sabawa, kowacce mace a matsayin baquwa take zuwa gidan aure,amma yau da gobe sai kiga ta saba” ta qarashe maganar tana bude murfin,tana jin kamar ta fincikota,amma hakanan ta tsaya harta fito din

    “Ka wuce ka huta,bari na rakata” ta fada tana kallonsa.

    Wani narkakken kallo yake binta dashi,gaba daya ta gama bashi mamaki ta kuma kwance masa kai,hafsat dinsa ta sauya fiye da yadda rai da zuciyarsa suke raya masa zata iya sassauta kishinta,kodon tana duba qananun shekarunta ne?,yana nan a tsaye har sukayi nisa,tana riqe da hannunta tana lallashinta da bata maganganu,saiya maida murfin motar ya rufe,ya sanya key din a aljihunsa ya soma takawa zuwa sashen sa yana jin gajiya nabin dukka gabbansa,babu abinda yafi buqata a yanzu irin ya watsa ruwa a jikinsa ya kwanta.

    Sai data tabbatar tayi nesa da widad daga inda abbas yake sannan ta fito tabar sashen,bayan ta gama mata lallashin qarya da nuna kulawa,wanda qasan zuciyarta cike yake fal da tsana da kuma qiyayyar yarinyar,tana jin kamar ta budi idanu taga babu ita kwata kwata cikin gidan.

    Latifa ce ta sakata a gaba kan sai taci abinci,da yake a gajiye take,kuma yunwar take ji da gaske saita zauna taci din,tana tsaka da cin ma baccin ya kwasheta ko.hannu bata wanke ba,sai tatifa ce ta gyara wajen ta kuma tasheta ta koma dakinta.

    Washegari tunda wuri latifa taga kiran ummu,bata yi jinkiri ba ta daga,don dama tana da niyyar kiran nata,bayan sun gaisa widad ta fara tambaya,bata boye mata ba ta gaya mata yadda suka wuni jiya,muryar ummun ta canza,da alama ita kewar widad din tata takeyi,sai tace takai mata wayar.

    Bacci takeyi amma sanda tace mata ummu ce sai gata ta wartsake sarai,ta karba wayar tana kiran sunanta hawaye na shirin balle mata,tausayinsu duka ya kama latifan,sai ta fice tabar mata dakin bayan taja mata qofar.

    *Arewabooks: Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 43

    Arubuce Ta Ke 43

    Page 43

    Gefan gadonta ta zauna hannuwanta rufe da fuskarta tana kuka sosai,me yasa abbas bazai fuskanceta su zauna lafiya ba?,yasha gaya mata zai bata mamaki,bata taba zaton irin wannan mamakin zai bata ba,ba ruwansa da harkar mata,kamar ma baida damuwa dasu,wannan yasa ta saki jikin cewa duk wani mataki da zai dauka a kanta bazai wuce ya qaurace mata ba,ita kuma bata da wannan damuwar,bata da yawan buqata,tasa buqatar ma damunta takeyi.

    Wayarta ta jawo dake gefan gadon ta soma laluba number kyawunta zatayi abinda ta saba wato kai qara,saidai tana kallon agogo taga dare yayi,wata zuciyar na ingizata ta kirashi,wata zuciyar na cewa tayi haquri ta barwa safiya,saita aje wayar,amma kuma yadda zuciyarta ta cika ta tumbatsa da bacin rai da kuma fushi,sai taji ba zata iya kwana ita daya da wannan baqincikin a cikin ranta ba,don haka ta sake daukar wayar ta kira number anty ummee.

    Cikin sa’a ta shiga,tana shiga din kuma ta daga

    “Ke lafiyarki a wannan tsohon daren?” Ta jefa mata tambayar jin ta fashe mata da kuka

    “Anty kaduna zai dauketa jibi su tafi”

    “Ita wa?,au amaryar taki?” Kalmar tayi mata ciwo,amma saita gyada kai kamar tana wajen

    “To sai kuma me ya faru?”

    “Na gaya masa ni.ban yarda ba,shine yake wani gayamin wai aini na zabi haka, mukayi fada dai dashi na baro masa dakin” wani tsaki anty ummee taja

    “Dadina dake wallahi baki da qwaqwalwa kwata kwata wani zubun hafsatu,ke da zaki nuna murna,kice hakan da yayi shine dai dai,zasufi sabawa da juna?” Ido hafsat ta zaro,kukanta ya tsaya cak

    “Anty?,suje su kebe su biyu wani abun ya faru kenan fa?,kaduna fa nake gaya miki,gidan da daga shi sai ita”

    “To ubanme ma zakije kiyi a garin da baki da ko kashi?,kibar kowa naki asalinki da tushenki a nan,suje sai sun dawo,sannan ma kuma sai akace miki haka zaki barta idan sun tashi tafiyar?,tsaya kiji,bude kunnenki da kyau” tarawa anty ummee nutsuwarta tayi,duk da tanajin babu wata mafita data wuce tayi masa bore,ko ya tafi da ita ko ya aje yarinyar a gida,saidai cikin minti biyar da fara sauraran anty ummee fuskarta ta washe da farinciki.

    **********Tun daren jiya bai kwanta ba sai daya tabbatar ya hada duk kayan da zaiyi tafiyar dasu ranar asabar din,idan da sabo kusan ya zame masa jiki,a shekarun da sukayi da hafsat zai iya irga sau nawa ta taba hada masa kaya wai don zaiyi tafiya ko zai koma bakin aiki.

    Bai kwanta ba sai kusan biyu na dare,a nan ma tunani ya hanashi sakat,yayita juyi from side to side,yanata bitar halayen hafsat,ya yarda matar aure ta qwarai dace ne,bai taba kawowa hafsat din zata sauya haka ba,bai taba kawowa cewa haka halaye da dabi’unta suke a zahiri ba,bai samu bacci ba sai wajen uku da rabi na dare,asuba nayi yayi alwala ya wuce masallaci.

    Bai shigo gidan ba sai wajen qarfe tara na safe,ya tsaya taron magidanta da akeyi a unguwar duk qarshen wata,kafin sannan hafsat takai ta kawo a sassansa ya kusa sau uku,so take ta aiwatar da shirinta tun da wurwuri,plan din anty ummee yafi kwanta mata fiye da nata plan din,saboda idan tanason barin garinta to tana qaunar mutuwarta.

    Sunyi sabani,tana komawa sassanta yana shigowa gidan,kamar ko yaushe a matsayin widad na baquwa sai ya fara da sashenta.

    Dai dai lokacin suna bedroom din widad din,latifa ta gama musu breakfast,harma sunci,don basa iya cin abincin hafsa,wanna yasa ma basa jiranta,itama kuma ana kwanaki biyar ta daina kawowa,saidai ta aiko a kirata tazo suyi dinner,sai akaci sa’a widad din mai wahalar sabo ce bata zuwa.

    Sabbin kaya latifa ke ware mata,saboda ta soma shirin komawa kano,amma dai bata bari widad din ta sani ba,don kada ta birkice mata

    “Wadan nan kayan dasu zakici gaba da kwalliyar,kinji dai abinda anty deena ta gaya miki?” Kai ta gyada

    “Bakiga kullum sai nayi abinda tace din ba”

    “Eh amma har yanzu baki qara zuwa wajen uncle din naki ba,kuma na gaya miki a can ake kwana” ido ta fiddo,waisu basa jin kunya suke mata zancan ta kwana da namiji?,bayan ummu ta gaya mata ko hannunta aka riqe ciki zatayi kuma mutuwa zatayi?,kafin tace komai anyi knocking qofar,latifan tasan ba wanda zai.shigo kansa tsaye saimai gidan,don haka ta zube kayan hannunta tana yiwa widad nuni da.hannu akan ta bude qofar.

    Itakam bata gane komai ba,ta sauko daga saman gadon,ta isa bakin qofar ya buda a hankali manyan idanuwansa suka fada cikin manyan fararen nata idanun,ta saki qofar cikin rashin sabo da d’ari d’ari taja baya tana cewa

    “Ina kwana?”
    “Lafiya qalau” ya amsa mata yana duban kayan jikinta,kayan bacci ne riga da wando masu taushi da kauri,wandon iyakarsa qauri,rigar ce ma mai dogon hannu,ya kauda ganinsa yana sanyo kansa cikin dakin,sai tahau raba idanu tana duban latifa dake jiran ya gama shigowa su gaisa ta basu waje,gabanta tana dan faduwa.

    Gaidashi tayi ya amsa,sai ta juya ta nufi qofa,widad din batayi qasa a gwiwa ba tabi bayanta zata fice itama cikin jin tsoro

    “Zo nan” ya kirata a hankali,saita waiwayo fuskarta a narke kamar zata saki kuka,ya kalli siraran labbanta jajaye data tabesu

    “Bari na dauko hijabi na” ta sake fada tana sanya jelar dankwalinta tana faman boyon na shanunta da suka fara bayyana kansu ta cikin rigar jikinta.

    Dariya taso bashi acan qasan zuciyarsa,ya fuskanci me take boyewa,ko me zasu sakashi ji wadannan qananun abubuwan oho,ya fada a ransa,saiya sanya hannu ya jawo hijabin da ya gani a gefansa ya miqa mata,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,tana ta faman cukuikuye gaban rigarta ta qaraso ta sanya hannu ta karba hijabin ta zura,sannan ya nuna mata waje ta zauna.

    “Kice ta shirya miki kayanki,gobe in sha Allah zamu tafi kaduna” da farko daya fara zancan hada kaya harta fara murna,ta dauka zaya ce gida zasu,amma sai taji yana kiran wata kaduna,ta fiddo manyan idanunta waje da suka fara hada hawaye

    “Kaduna?…..”sai ta kasa qarasa maganar,kai ya jinjina mata yana nazartarta,ta fiya tsoro, tsoronta yayi yawa,kuma ya lura maza kawai takewa haka

    “Eh,gobe da safe” shuru tayi tayi qas da kanta qwalla na zuba,bai lura kuka take ba,yamiqe yana cewa

    “Bakwa buqatar komai?” Saita jinjina masa kai kawai,ya taka a hankali ya fice,cikin ransa yana ayyana yadda zasuyi rayuwa a kaduna da ita ahaka a yadda take,itama din bata wuce raino ba.

    A haka latifa tazo ta tarar da ita,ta sata a gaba da tambaya,sai ta gaya mata,sannan ta dora da cewa

    “Ni gida zan tafi ba wani kaduna,wajen ummu zamu tafi” zama sosai latifa tayi tana kwantanta mata lamarin aure,ta kuma gaya mata gaskiyar ta taho kenan,ita da gida saidai ziyara,saita rude mata,ta dinga rusa mata kuka tana lallashinta,daga qarshe dai sai data kai ga kiran alhj mahmud.

    Cikin hikima irin ta d’a da mahaifi ya dinga bata baki,tare damata alqawurin zaizo can din,kuma ta fadi kome takeso zaisa a kawo mata

    “Ni banason komai,kawai komai a gidan,kullum shima sai ya tambayeni idan inason wani abu” wannan magana tata ta sake kwantar masa da hankali,ta kuma qarawa abbas martaba da bayyana asalin nagartarsa,abban nata bai barta ba har sai da ta sake sosai sannan sukayi sallama.

    Tsaf latifa ta hada mata kayan da dukka tasan ya kamata ta tafi dasu,itama ta faka nata kayan a boye.

    Bayan fitarsa sassan hafsat din ya wuce don yaga yaransa,a falon yayi sallama,sunata wasa da kayan bacci a jikinsu,babu alamun an musu brush da alwala ba bare wanka,fuskarsu duk jirwayen bacci da sauransu.

    Tana tsaye a dining area tana gyara kayan breakfast din data hada tun safe,bayan ta hana idanunta barci.

    Satar kallonsa takeyi,ya mata wani irin kwarjini da kyau,wani irin annuri ke fita daga fuskarsa,abinda ke qara mata soyayyarsa kenan da kuma kishinsa,kome ya sanyawa jikinsa karbarsa yakeyi.

    Cikin nutsuwar nan tasa ya duqa yana tarbar yaran nasa,suka shige jikinsa kowa a cikinsu yana son masa hira shi kuma yana biye musu,ta gaji da tsaiwa ganin baiko waiwayota ba,ta soma baro wajen zuwa inda suke tsugunne

    “Ina kwana” ta fada ranta yana suya,a dakeka a hanaka kuka?,wanne irin al’amari ne wannann

    “Lafiya”ya amsa a taqaice,ranta ya sake sosuwa,halin nasa ya motsa kenan,shi duk abinda ya faru kenan bai ga nasa laifin ba sai nata?.

    “Ga abincinka nan an gama”

    “Am okay alhamdulillah” ya bata amsa yana miqewa dauke da nawwara,sai itama ta miqe,zuciyarta na tafasa amma tana yunqurin danneta

    “Amma kada ka yimin haka,tun dazu na tashi saboda kai fa?”

    “Nace na qoshi” ya amsa mata bayan ya zube mata manyan idanunsa,abinda ya sage mata gwiwa ta koma baya ta jingina da kujera

    “Abinda ya faru jiya ne kenan har yanxu bai wuce ba?” Waiwayawa yayi yana sake kallonta,shi take ma tambaya kenan?,bai amsa mata ba sai ta baiwa kanta amsa

    “Kayi haquri,inasonka dole nayi kishinka,kishin ne ya sanya idanuna suka rufe,amma ya riga ya wuce,Allah ya tsare hanya” ta qarashe maganar tana jin kamar ta saki kururuwa,ita kadai tasan me takeji a zuciyarta,wani irin kisan mummuqe ne takewa zuciyarta,wadda bata saba da boye boye irin haka ba,komai nata gaba gadi take yinsa.

    Lokaci daya xuciyarsa yaji zuciyarsa ta karye,ta kuma sassauto,amma baiji gamsuwa akan lamarin hafsat din ba,ya santa,kamar hawainiya take akan wasu al’amuran,bashi da tabbacin ta fada din da gasken gaske

    “Kaji?,nace kayi haquri” ta kuma fada,a wannan karon duk yadda taso tare qwallar baqincikin dake idanunta sai da suka sulmiyo,abinda ya qarasa karyashi kenan,son sam baya qaunar kuka,sai ya sauke nawwara yacewa mimi taja nawwaran suje dakinsu su dauko brush dinsu.

    A tausashe ya sanya hannunsa ya jawota zuwa jikinsa,tun baice komai ba ta saki kuka mai nauyi,wanda ke dauke da saqonni da yawa da zuciyarta keson fesarwa,baki da ruhi sun gaza amintuwa da hakan saboda burin cikar wani buri.

    Baice komai ba sai hannu da ya sanya a bayanta yana dan bubbuga wa kadan kadan,har zuwa wani lokaci,ya dagata yana duban fuskarta

    “Is okay,wipe your tears” ya fada bayan ya miqa hannu ya yago mata tissue din dake kusa dashi,bata musa ba ta karba ta fara goge fuskarta ta,saidai zuciyarta har yanzu tana jinta kamar an fusgeta daga qirjinta an jefa gidan bread.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[3/6, 3:12 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 47

    Arubuce Ta Ke 47

    Page 47

    Komai nasa ya tattare a falon,abinda yasa widad ta fahimci ya gama zamansa a nan kenan

    “Muje na rakaki daki,zan kwanta” jiki a sabule ta miqe din,yana gaba tana binsa a baya har zuwa dakin,tana zaune a gefan gado ya zuzzuge dukka glasses na window din sosai,ya kunna ac ya daidaita mata temperature dinta,duk abinda yake tana binsa da kallo,duka jikinta babu dadi,dan wankan da takeyi ma data yiwa anty deena alqawari bata samu yi ba,ta kuma riga ta saba da yinsa zuwa yanzu,ya tako a hankali yana ajjiye remote din acn sannan yace

    “Kin iya addu’ar kwanciya bacci?” Kai ta gyada masa

    “Da kyau,kiyi kafin ki kwanta” ta sake gyada masa kai,ba wannan bane a gabanta,tana qiyasta yadda abubuwan tsoro zasu kawo mata farmaki cikin dakin idan ta kwana ita kadai,babu abinda ranta da zuciyarta basu kawo mata ba,batasan sanda tayi wuf tabi bayansa ba sanda taga ya nufi qofa.

    Tsaiwa yayi yana kallon ta,hawayen nan da basu da wahala a fuskarta suna fita

    “Mene kuma?”

    “Tsoro nakeji”

    “A’ah….wai meye abun tsoron ne?” Kasa amsa masa tayi,illa d’ari d’ar da taketa yi,shuru yayi ya zuba mata idanu,yanason tuna abinda ya dace yayi

    “Yanzu me kike so?” Saita kalleshi da dara daran idanunta masu haske sosai,bakinta yana dan rawa,ta kasa cewa komai,ganin haka sai yace da ita

    “Muje dakina ki kwana” da sauri ta girgiza kai tana fidda ido waje

    “To ki koma dakinki ki kwana” ya sake bata second option,nan ma ta girgiza kanta da sauri.

    Ranshi ne ya baci,har yaja tsaki a fili,wacce irin yarinya ce ita?,duk option din da aka bata bai mata ba?

    “Ba zaki dakina ba,bazaki dakinki ba,to zaman gadinki zanyi?” Ya tambayeta emotion din fuskarsa yana sauyawa zuwa bacin rai.

    Maimakon amsa saita sakar masa kuka sosai,abind ya hasalashi ya sakar mata tsawa,tsawar data sanyata durqusawa a wajen tana kuma sakin wani kukan tare da kiran sunan ummu.

    A take jikinsa yayi sanyi,yaga kuma rashin kyautawarsa muraran

    “Sai ka dinga haquri da ita,kana kwatanta mata abubuwa,bata zama cikakkiyar budurwa ba,da quruciya har yanzu a tattare da ita,to zaka yita ganin yarinta,sai kayita haquri kana gyara mata,amma data gane abinda kakeso da wanda baka so,zakaji dadinta fiye da kowa” maganar da sukayi da hajiyansa ta qarshe ta dawo masa,wannan yasa temper dinsa ta sauka,ya tako a hankali ya tsaya a gabanta

    “Get up….tashi” ya fada a tausashe,saita miqe din tana sanya gefan dankwalinta tana goge fuskarta,duk da hawayen sunqi tsaiwa

    “Yanzu ya kikeso ayi?” Ya tambayeta yana narkar da idanunsa cikin nata,itama kallonsa takeyi,ya fuskanci ko a jikinta bata jin nauyin kallon qwayar idanunsa,ta gaza bashi amsa sahihiya,ya kuma gane tsoron hada daki takeyi kawai dashi,kamar kuma yadda take tsoron kwana ita kadai,tsahon wasu sakanni da shuru ya biyo baya sai ya gyada kai

    “Shikenan,ki kwanta a daki,zan zauna a falo har kiyi bacci” a hankali ta gyada kanta,hakan yayi mata,yafi ace ya koma dakinsa ya kulle ba kowa a kusa,duk da dakunan kusa da juna suke.

    A gaba ya sanyata har dakin nasa,ya dauki duk.abubuwan da zai dauka ya ajjiye a falon,ya maidata dakin ya tsaya harta kwanta sannan ya ja mata qofar ya dawo falon ya zauna saman kujera hadi da jingina filo bayansa da gefansa don yafi jin dadin zama,sannan ya buda wani qaramin littafi ya soma dubawa.

    Fakare tayi cikin bargon data lulluba har kanta tana rarraba ido,lokaci lokaci tana dan jiyo motsinsa daga falo,wannan ne ya sanya mata nutsuwa,har sannu a hankali bacci ya saceta ba tare data sauya koda kayan jikinta ba.

    Awa guda y bayar sannan y shigo dakin,ganin qarar qofar dakin bai sanyata ta motsa ba ya fahimci tayi bacci,sai ya koma da baya yana sake rufe mata dakin,ya koma falon ya kwashe kayayyakinsa ya wuce nasa dakin

    “Case closed” ya fada a ransa,amma yana tunanun haka zasu maimaita da ita gobe?,kenan wani sabon duty dinne ya sameshi

    “Ya rabb” ya furta yana furzar da iska daga bakinsa,ya ajjiye komai a muhallinsa y wuce bandaki don yayi wankan da rigimarta ta hanashi yi.

    Tunda gari ya waye ta dawo falon ta zauna,bayan ta dafa ruwan zafi kamar yadda latifa ta koya mata,ta hada da cup da tea flask din ta dora saman table,tun daxu take jiyo motsinsa cikin dakin,amma bata yi qoqarin shiga ba,saidai ta zubawa qofar dakin idanu tana qiyasta sanda zai fito.

    Yana taba handle din ta sake zubawa qofar idanu,ya fito a hankali cikin police uniform,sun masa wani irin kyau kai bakace uniform na ya sanya ba,haiba da kwajininsa sun fita sosai,tsayayyen namiji da siffar qarfi ke bayyana a halittarsa,qafafunsa saye cikin baqaqen boots,yana shirin rufe qofar ya lura da ita,sai ya waiwayo yana dubanta da mamaki kan fuskarsa,da yaji shuru yayi tunanin har yanzu tana daki baccin takeyi,dalili kenan da bai tasheta ba.

    Sosai ya sake mata kwarjini,wani tsoronsa ya sake shigarta,sai ta dauke idaninta ganin yadda yake kallonta,tura baki gaba, itafa duk wanda yake kallon mata dan iska ne a wajenta,ta sauke qafafunta qasa sannan tace

    “Ina kwana?” Bai amsa ba sai daya rufe qofar dakin,sannan ya tako zuwa wajen yace

    “Lafiya lau….” Ya fada yana duban kan dining din,sannan ya sake dubanta

    “Kinci abinci ne?” Kai ta girgiza

    “Akwai kayan tea a cupboard na kitchen din,zan fita anjima za’a kawo kayan cefane,ba wata damuwa?” Kamar jiya yauma fuskarta kamar ta fashe,yana nufin ita kadai zata wuni a sassan kenan?,wai Allah,ya zatayi,lallai zata mutu da tsoro indai yace zai sake kaiwa dare,ganin batace komai ba sai ya dora

    “Akwai mutane cikin gidan nan,zaki iya shiga ku gaisa,ko kuma idan na dawo saiki shiga” ya fidda kudi ya ajiiye mata

    “Sai na dawo” ya fada yana nufar qofar,binsa tayi da kallo,kamar ta zura da gudu ta bishi

    “Don Allah kada ka sake kaiwa dare irin na jiya” ta fada muryarta tana rawa,waiwayowa yayi yana kallonta,ba tare daya shirya ba murmushi ya subuce masa,shi kam ya jima baiga matsoracin mutum ba irinta

    “In sha Allah” yace mata sannan ya fita.

    Ta kusa minti talatin a wajen tana jin yadda gidan yayi mata shuru,sai da cikinta ya fara kiran yunwa sannan ta miqe,kana kallonta zakasan a tsorace take,duk da akwao motsi jifa jifa daga harabar gidan,kitchen ta shiga tana neman inda kayan tea din suke,tsahonta bazai kai ba,sai tasa kujera ta taka ta dauko ta dawo dining din ta doma qoqarin hada tea din,gana daya ta rude,saboda ummu ko latifa ke hada mata,koda ta gama hadawa ta dandana sai taji test din baiyi mata ba,ta bare baki kamar zata saki kuka,haka ta runtse idanu tana kurba har ta kusa shanyewa,dai dai lokacin da wayarta ta dauki tsuwwa,ta firgita da ringing din wayar daya soma fita,don a bazata yazo mata,saura kadan cup din hannunta ya subuce,ta ajjiye kofin ta nufi dakin da sauri.

    A can qasan gado ta gano wayar,a lokacin ana sake kira karo na uku MOMMY ta gani,shine sunan data sakawa hafsat,ta saki murmushi tana jin dadi,itace ta fara kiranta,cikin zumudi ta daga

    “Hello…..ina abban mimi?” Abu na farko da hafsat ta fara fadi kenan,ba tare data damu tayi sallama ba

    “Mommy ina kwana?,inasu mimi?” Ta maida mata da tambaya,ba tare data bawa tambayarta ta farko muhimmanci ba,saboda ba wannan bane damuwarta ba

    “Lafiya lau….ina abban mimi?”

    “Ya fita mommy”

    “Jiya a ina kika kwana?”

    “A dakina”

    “Shi kuma abban nasu fa?”

    “Ban sani ba,na rigashi yin bacci” gaban hafsat ya fadi

    “Da kika farka kenan a dakinki kika ganshi?” Kai ta girgiza kamar tana gabanta,gabanta kuma yana faduwa cike da fargabar kada ta karanci ya rungumeta,babban abun kunya kenan,tana kuma tsoron kada zancen yaje kunnen mutane a dauka ita din ‘yar iska ce

    “Daga dakinsa naga ya fito sai ya tafi office”

    “Karkimin qarya fa widad?” Kai ta langabe muryarta nayin sanyi

    “Allah ki tambayeshi ma” ta furta zuciyarta na addu’ar Allah yasa kada yace ya rungumeta idan ya tashi bata labari.

    Ajiyar zuciya ta sauke,hankalinta yana kwanciya

    “Shikenan,ina fata baki manta komai ba?”

    “Eh momy”

    “Da kyau,ki kula da kyau kinji ko?,ki kula”

    “To mommy…..mommy amma ki bani mimi ko….” Bata tsaya jinta ba ta gintse wayar,iya abinda takeson ji kenan,sauran koma meye ba damuwarta bane,ta aje wayar gefan gadonta tana furzar da iska

    “Shegiyar yarinya,kike cewa wani wai na tambayeshi,abbas din zan yiwa wannan tambayar?,ko ke ban isa na miki makamanciyarta a gabanki ba” sai kuma murmushi ya subuce mata

    “Anty ummee kinyi a rayuwa” ta fada a fili,ta duqa tasa qaramin muqulli ta bude drawer din jikin gadonta da take bawa kulawa ta musamman,kudade ne a ajiiye a ciki,ta fiddosu ta fara rigasu tana hade kansu waje guda,ranta na mata fari sol,yau sai taji gidan ya mata dadi,musamman idan ta kalli sassan widad din ra ganshi a rufe,sai taji kamar ta tafi kenan.

    Tana cikin maida kudin kira ya sake shigowa mata,ganin sunan mai kiran saita hade ranta,taja tsaki ta dauke kai,anty shafa ce yayarta,tasan kiranta baya rasa nasaba da zancan kudi,kullum zancanta na ta kawo wani abunne,ita kuwa kudinta bana tabawa bane,don haka ta maida wayar silent ta miqe tana kallon agogo.

    Sha biyu saura na rana,ko brush batayi ba bare ayi zancan breakfast shara ko gyaran gida,tana son abbas tana son ta kasance ko yaushe dashi,to amma idan suna tare irin wannan sakewar ce bata samu,shi yasa ba kasafai take damuwa da nisantar juna a tsakaninsu ba.

    Tunawa tayi tabar yara a falo,har tayi hanyar toilet saita sauya akalarta zuwa falon,tana addu’ar Allah yasa basuyi mata barna ba.

    Tun daga nesa ta hangi mimi tayi dafa’an a tsakar falon,ta fasa kwalin cornflakes ta cika madara kwano ta dama da ruwa tana ta durawa nawwara,tsawa ta kwaza mata,sannan ta fidda danu tana duban kwanon

    “Innalillahi” ta fada da qarfi,sannan ta nufi mimi da sauri, batayi wata wata ba ta gabza mata mari,gaba daya yarinyar ta jawo mata asara,kudin da ya bayar a siya wadan nan kayayyakin ta lankafesu,ta fitar da tsohuwar madarar daya taba siyawa yaran tasu tashan tea,ta ajjiye a dining tace suyi amfani da ita kafin ya dawo,yanzu ta daga madarar dukanta ta zazzage musu.

    “Uban wa yace ki taba?” Ta fada tana kama kunnen yarinyar,cikin kuka tace

    “Mommy,nawwara ce takejin yunwa” sai lokacin ta tuna bata basu komai ba ashe,ta saki kunnen nata tana huci

    “Ba sai kizo ki gayamin ba,kin tashi kin cuci mutane kin musu barna,matsa ki bani waje” haka ta sanya tsintsiya da ta gyara gurin,tana yi tana mita,yaran na rabe a gefe,mimi na hawayen murde mata kunnen da tayi.

    *Arewabooks: Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/7, 11:54 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 44

    Arubuce Ta Ke 44

    Page 44

    “Ma sha Allah” shine abinda latifa ta fada bayan ta gama feshe widad da turaruka masu taushin qamshi

    “Duba ki gani” ta fada tana matsar da ita gaban madubi,murmushi ne ya subucewa widad bayan ta kalli kanta da kanta ta madubin,tayi kyau irin yadda takeso,yau latifan tana da nutsuwar data mata ado haka

    “Gaskiya nayi kyau” ta fada tana dariya hadi da kallon latifa,sai dariya ta kama latifan

    “To sai a bani tukuici ai”

    “Duk kudin da uncle yake ajjiyewa ki dauka” ta fada tana murmushi,girgiza kai latifa tayi

    “A’ah,ba ruwana da kudin miji da mata,tashi kije qila sun fito,sai kun dawo” tana murmushin maganar da latifa ta fada da kuma farincikin yadda tayi kyau a saman fuskarta ta fita zuwa farfajiyar gidan.

    Dai dai lokacin da gafsat ke tsaye gaban motar abbas,sanye da baqar doguwar riga mai sulbi da jan mayafi babba data yafawa kanta,fuskarta kamar ko yaushe,babu alamun kwalliya ko d’is,sai maiqo maiqo da takeyi,don tana tsaka da barci mimi ta tasheta akan ta fito inji abbansu zasu wuce shopping.

    Sam bata ankara da widad ba sai data kusa gab dasu, qamshin ta dake kadawa cikin iska shine abu na farko daya fara jan hankalinta ta gane akwai baqo a wajen,sosai ta zuba mata idanu,sai taji gabanta ya fadi,wanne irin kyau yarinyar nan ke dashi?,ta tambayi kanta da kanta,take taji gaba daya ta muzanta,duk da cewa dama ba wani ado tayin ba,rigar da ita ta kwanta baccin,ganin bata jima da sanyata ba kuma a motar gida zasu fita su dawo yasa batayi wani sha’awar canzawa ba.

    Kafin ta dawo daga duniyar tunanin data lula widad ta iso wajen,sunata kakaci ita dasu mimi suna qyalqyala dariya abinsu

    “Ina yini momy” ta fada fararen jerarrun haqoranta suna bayyana,sautin siririyar muryarta ta karade kunnenta,ta kuma dawo da ita hayyacinta

    “Lafiya…..lafiya lau” ta fadi tana bude bayan motar da sauri

    “Ku shiga ku zauna,mimi ku shiga” ta fada tana duban idanun widad,kama hannunsu nawwaran tayi,ta fara saka mimi sannan itama ta shiga tana ci gaba da jansu da wasa.

    Wata ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,har yanxu qirjinta bugawa yakeyi,kyawunta yana damunta,yana kuma son ya zame mata barazana,tafi yarda dari bisa dari kyawunta na daya daga cikin abinda ya fusgi hankalin abbas dinta,ta yaya zata gusar da wannan abu dake shirin zame mata barazana?.

    “muje ko” ta tsinci muryarsa dab da ita,sai ta dan bishi da kallo har sai daya kusa shigewa motar,ta taka jiki a mace ta isa gaban motar ta buda daya side din ta shiga.

    Wani baqon qamshi ne ya ziyarci hancinsa,ya soma shirin tada motar yana zuqar qamshin,sai daya tada ita sannan ya waiwaya ya kalli hafsat

    “Yaushe kika sayi wannan turaren?” Kishi ya kamata,bataso tace ba ita bace ya farga da yarinyar,idan kuma tace itace tayi qarya,duk da haka ta gwammace wa qaryar,sai tadan murmusa

    “Eh,cikin bikin nan na siya”

    “Yayi dadi sosai” ya sake fada yana dan waiwaya sashen da take,duk da baiji yana busowa daga nan ba,murmushin yaqe ta saki tana basarwa,zuciyarta na bugawa,tana addu’ar komai ya tafi dai dai.

    Sun dauki hanyan babban super market din suke siyayya lokaci bayan lokaci,motar shuru,bakajin komai sai muryoyinsu widad mimi da nawwara,a hankali muryarta ke shiga kunnensa,itama ta saje dasu abinta,zuciyarsa cike fal da tunanin ita din fa wai matarsa ce,sai kawai ya gyada kai qaramin murmushi yana qwace masa,saboda shi kansa yasan akwai jagwal,baisan kuma ya zata kasance masa ba.

    Murmushin da yaja hankalin hafsa,ta dan juya kadan tana kallonsa,sai shima ya kalleta ya basar yaci gaba da tuqinsa,ita sam irin hirar nan ta debe kewa don kana driving ma bata iyata ba,sai suyi tafiyar awanni amma saidai kowa yaci kansa,imma ya kunna radio imma ya zubawa hanya idanu kwanyarsa ta cika da tunane tunane har su iso inda zasu.

    Su suka fara yin gaba zuwa cikin super market din,cewa widad tayi ta tsaya dasu mimi zata dauko mata duk abinda ya dace,bata wani damu ba ta jasu gefe suka zauna,haka tayita zagaye,tana hada duk abinda ranta ya mata a kwandon data dauka,ba wani abun azo a gani take zaba ba,don ba iya zaben tayi ba,majority tare suke shiga da abbas din,shike zabar mata abinda yaga ya dace da ita,takanyi mita a fili da zuci

    “Wannan asarar kudine kawai,ni da kudin ka bani da yafi” dubanta kawai yakeyi

    “Abinda zaki sakamin din ko kimin amfani dashi na kalla naji dadinne asarar kudi?” Takan basar kawai,itama batasan tana wannan subutar bakin ba a wani lokacin.

    Sai data gama zane zabenta sannan suka hadu a wajen biyan kudi,yaga abinda ta diba,takaici ya hanashi cewa komai,ya biya kudin kawai suka fito,baisan yaushe zata koyi siyan abubuwa masu amfani ba,sa’annan kamar ita zata biya kudin,ta saka tsaiwa ta dauki kayan daya dace.

    Kai tsaye gidan hajiya ya wuce dasu,tunda hafsat taga titin da yahau tasan can zasuje,sai ta bata rai,amma dai batace komai ba,don batasan bata wasan nata.

    Yana tsaiwa a qofar gidan widad tayi zaraf ita dasu mimi suka fice,yadan bisu da kallo kafin ya dawo da dubansa kanta,itama shi take kallo,ranta ya sake baci,sai take ganin kamar widad din yake kalla

    “Amma zaka jiramu mu gama ne saimu wuce gida ko?,don inason nadan kwanta,bana jin dadin jikina yau” dubanta yayi kawai,tunda suka fito din batace masa bata jin dadi ba saida sukazo nan,saiya soma zare seat belt dinsa,har ya bude murfin motar sai kuma yace da ita ba tare daya waiwayo ba

    “You know what?…..idan zakaso saniya ka sota har qahonta,domin kuwa no matter what ba yadda za’a yi su rabu,mahaifiyata itace duniyata,silar nasarar rayuwata” a birkice ta juyo tana kallonsa,bataso ya fahimci emotion dinta ba,ta buda baki zata jefa masa tambayar rainin wayon ya buda motar ya fice ya barta a ciki.

    Katsam hajiya taga shigowarsu,farinciki ya cikata,murmushi ya wadaci fuskarta,tana marabtarsu tana duban widad,tare dason gano wani canji tattare da ita.

    Ta sake haske dai ta kuma sake fresh,amma girman da taso taga tadan qara babu shi,alamu dake nuna babu komai kenan daya wanzu tsakaninsu.

    Tana tsaka da wannan tunanin yayi sallama da muryarsa mai zurfi ya shigo,idanunsa suka sauka a kanta sanda take zaune gaban hajiyan hankalinta kwance kamar tana gidansu,fuskarta ta wadata da murmushin da zai iya cewa tsahon satin biyun da tayi gidansa bai taba ganinsa ba,ba wani alamun surukuta a tare da ita,yo ina ta gama saninta ma.

    “Maraba lale,saiga baqin yamma” hajiya ta fada sanda yake duqawa gabanta daura da widad din yana gaida hajiyan,dai dai sanda hafsa ta sanyo kai cikin falon,sai idanunta suka qara kusancin dake tsakanin widad din da abbas,bugun zuciyarta ya dadu,wani abu ya kama wuyanta,tayi ta maza ta kauda kanta tana zuqar numfashin wahala,sannan ta qaraso falon tana sakin sallama da shaqaqqiyar muryarta.

    “Ah,kacemin tare kuka?” Ta fada har cikin ranta tana jin dadin ganinsu gaba daya

    “Eh munje sunyi siyayya ne,saboda gobe in sha Allah zamu wuce”

    “To yayi kyau,ma sha Allah” hakanan ta duqa itama ta gaidata don ganin idanun abbas din,ba komai a fuska ko zuciyar dattijuwar ta amsa tana tambayar ta yara,bayan lafiya lau data ce bata sake cewa komai ba,taja gefe daya ta zauna ta tsuke bakinta,amma idanunta yana kan komai dake wakana cikin falon.

    Yadda taga hajiyan ta maida hankalinta gasu widad din ya qona ran hafsat sosai,ta yita mutsu mutsu cikin kujera cikin bacin rai,tana jin kamar ta tashi ta fice tabar musu falon,sauqinta daya harda yaranta take ja da wasa,don su mimi suna kan cinyarta suna ta harkokinsu,amma ita wannan sam baiyi mata ba,daga qarshe ta buge ta amsa waya ta fice harabar gidan.

    Huci ta dinga yi tana fidda iska mai zafi daga bakinta,zuciyarta kamar zata fito,bata iya jurewa ire iren wadan nan abubuwan,akan abbas zuciyarta na gaya mata komai zata iya yi.

    Ana idar da sallar magariba suka baro gidan,a hanyar komawa ma tamkar kurame,shi ya riga ya saba da irin wannan zaman,uwa uba kuma dama shi din ba mutum bane mai son magana,yayin da hafsat din keta cin daci,gaba daya zuciyarta babu dadi.

    Qaramar leda ta dauka ta debi wasu abubuwa d’ai d’aiku ta bawa widad,bata damu ba don ba damuwarta din bane,tasa hannu biyu ta karba tana godiya,shi kuwa baisan me ya faru ba,an masa total dai ya biya kudi,yana tsammanin kowa ya dauki abinda ransa keso.

    ***********Kuka take sosai tsahon awa guda cur da sukayi suna tafiya bisa hanyar bauchi zuwa kaduna,duk yadda zai mata tayi shuru yayin amma kamar ma bata san yana magana ba,har ransa ya baci ya shareta taci gaba da kukanta.

    Tun sanda motar samuel ta daga da latifa kano,su kuma tasu ta dauki hanyar kaduna ta birkice da kuka,bata taba tsammanin latifan tafiyarta daban da tasu ba.

    Sai data kusa rufe awa biyu sannan kukan ya fara ja baya,jikinta ya fara saki,sanyin yammaci gajiya da kukan data sha suka saukar mata ds bacci,a hankali ta langabe kanta gefe tana sauke ajiyar zuciya mai nauyin,alamun taci kuka ta godewa Allah.

    Dubansa yakai gareta kadan kafin ya dauke kansa yaci gaba da tuqinsa,cikin ransa yana sauke ajiyar zuciya,wannan aure ne ko rigima sabuwa ta sameshi?,ya tambayi kansa.

    Karo na biyu ya sake maida dubansa gareta,sai ya rage speed na motarsa ya gangara gefan titi ya tsaidata,ya miqa hannunsa a hankali ya sauke mata kujerar yadda zata ji dadin kwanciyar,ya koma seat dinsa ya zauna dai dai,sannan ya sake kunna motar suka ci gaba da tafiya.

    Yammaci lis suka shiga garin kaduna,kofar wani babban gida ya tsaya,ya danna hon,babu jimawa mai gadin ya iso ya bude gate din,fuskarsa cike fal da murmushi,da alama farincikin ganin dawowar abbas dinne,aiko yana sako hancin motar zuwa parking lot na gidan ya biyo bayan motar da sassarfa yana fadin

    “Barka da zuwa oga” qaramin murmushi ya saki,yana hangoshi ta madubin,mutum badai barkwanci,ya tsaida motar dai dai sanda ya qaraso gefan window dinsa.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/6, 3:13 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 34

    Arubuce Ta Ke 34

    Page 34

    Batulu dake zaune gefe tunda suka shigo gidan ta tabe baki,itakam ba haka taso ba,abubuwa da dama ta samesu ba a yadda take fata ba

    “To da alama dai uwar gidan nan tayi sake da yawa” ta fadi can qasan ranta,babu abinda take tunawa illa zamansu da fatima kafin su samu tabar musu gidan,koda yaushe mahmud ya tashi fatima dai…..fatima ce,basu samu salama ba saida tabar gidan,ko yanzun sun san cewa bawai tanar zuciyarsa bane gaba daya,rayuwarsa dai ta bari.

    Basuci da yawa ba suka ture abincin,can bayan awa daya saiga wasu sabbin coolers din,suna shigowa hajjaa ta gane daga gidan hajiyan abbas ne

    “Yanzu zakuci abinci ku ture” ta fada tana dariya sanda take bude coolers din,lafiyayyen abinci ne sosai,harda wani na daban tace na widad ne,sai ta miqawa nujood

    “Kai mata daki taci” nujood ta sutumi qawatacciyar warmer din dake fidda qamshi tun kafin ta bude ta wuce dakin da suka baro widad din. Su kuma a sannan suka sake sukaci suka qoshi.

    Saman katifa ta sameta,tana ta daddanna wayarta,wadda har yanzu batasan amfaninta ba idan ba game ba,dab da zata taho dai anty madeena ta saka mata numbers din mutane,ta kuma koya mata yadda zatayi wasu abubuwan

    “ga abincinki inji surukarki” nujood ta fada tana dariya,mayafin kanta tana gefe ta galla mata harara

    “Wai meye haka don Allah nujood”

    “Allah da gaske hajiya ce tace naki ne” ta zauna gefan widad din tana bude warmer din

    “Kedai kinji dadinki,kowa sai tattalinki yakeyi,kinga gidanki widad?,kinga kitchen dinki?,mtsewww,inda abbana zai yarda nima auren nan zance ayimin” kallonta kawai widad din keyi,ita kuma ji take dama itace su,tun sanda ummu ta fara mata fadan komai yace tayi tayi ta soma jin wani abu mai kama da takura ya sauka arayuwarta,kullum zancan ummu

    “Mijinki ne,babu musu a tsakaninku,ki girmamashi kamar yadda zaki girmama babanki da alhaji dani,ya fini matsayi yafi babanki matsayi” to wai banda abun ummu ta yaya zatace ya fisu matsayi?,idan tace tayi girmamashi tayi masa biyayya ta yarda da wannan,amma banda finsu matsayi (hankalinta baikai wajen ba).

    Tare suka soma cin abincin da nujood,tana ta bata labarin kayan da aketa jera mata, murmushi kawai takeyi,ita.mamaki abun yake bata,wai duk girman abu sai ace nata ne,har nan ma wai gidanta ne?.

    Koda suka gama saita labe ta cikin labule tana ganin yadda ake shirya falon,nujood na sake zugata ta tsaya ta kalla,har sai data gaji sannan ta koma ta zauna

    “Wallahi idan nice ko?, tabdi,sha’anina zansha babu takuramin” ta fada tana fadawa saman katifar,sai suka qyalqyale da dariya a tare.

    Da daddare aka sake kawo musu wani,muneer qanin abbas ya shigo da kansa bisa wakilcin abbas din,yayi musu sannu da zuwa,ya kuma tabbatar basa buqatar komai,sannan ya ajjiye musu kudi yace injishi.

    Sai wajen sha daya da rabi na dare ya shigo gidan,zuwa lokacin ya tabbatar kusan kowa yayi bacci cikin gidan,idan ma akwai wanda baiyi ba d’ai d’aiku ne,don haka kai tsaye ta wuce sashensa.

    Ya sameshi yadda yakeso,harma yayi mamaki,cike da tantama da kuma shakkar hafsa dince ta gyara ko sakawa tayi a gyara masa,bai sani ba,sai ya aje wannan tunanin,ya soma rage kayan jikinsa ya zubasu a laundry basket,ya wuce bandaki ya soma tara ruwa mai dumi sosai a bathtub,sai daya cikashi taf sannan ya fada ciki yana sauke ajiyar zuciya,bayan ya cikashi da turaren wanka mai sanyin qamshi.

    Luf yayi a ciki,idanuwansa a lumshe,yana jin hayaniyar daya wuni yana debowa tana sauka daga kanshi,sai daya kashe minti kusan talatin sannan ya wanke jikinsa daya tsumu da qamshin turaren wankan da kuma dumin ruwan daya jiqa kansa a ciki,ya zari daya daga cikin lausasan towels dinsa wanda qamshin shower gel da body mist dinsa suka kamashi da kyau,koda kuwa an wanke ya daura ya fito.

    A bakin madubi ya tsaya ya dauki wayarsa yana laluban layin hafsat,duk da bashi da hope kan zata daga,saidai cikin sa’a gab da zata katse ta dauka din

    “Ka dawo ne?” Abinda ta fara tambayarsa kenan,hakan kuma sai yayi masa dadi,saboda ya jima baiji magana cikin nuna kulawa kamar haka daga bakinta ba

    “Yeah,can u come to my room?” Ya fada da lallausar muryarsa da sauti can qasa

    “Why not?,gani nan zuwa” ta fada tana ajjiye wayar tata,sai ta miqe kanta tsaye ta soma canza kayan jikinta zuwa night gown,sannan ta shiga kitchen ta hada masa abinci ta kulle sassan nata,don taci alwashin yau din acan zata kwana ta fito.

    Duk da dare ne,hakanan babu cikakken haske a sassan widad din sai data zubawa part din nata harara,taja wani mugun tsaki kamar zata cire harshenta

    “Zakici ubanki da kyau,saboda tsaurin ido yarinya kamar wannan wai tasan soyayya?,tasan aure?,auren ma mutum kamar abbas,zaki gayawa aya zaqinta” ta sake fada tana jinjina kai tare da tabbatarwa da kanta hakan.

    Sanda ta shiga yana shafa mai ne,saita ajjiye abincin,fuskarta kadaran kadaham,ta koma gefan gado daga bayansa ta zauna,ya waiwaya kadan yana duban fuskarta,sai kuma ya dauke kai ya maida dubansa gabansa yana daukar body mist dinsa

    “Kinyini lafiya?,ya yaran” sai data dan yamutsa fuska kadan bayan ta tabbatar bazai ganta ba,tayi qoqarin saita muryarta,don tana jin kamar wani abu ya mata tsaye ne a hanyar shaqar numfashinta

    “Lafiya lau,yara kuma suna gida” ta cikin mudubin yadan dubeta kafin ya kawar da qwayar idanunsa

    “Har yanzu?,for now ya kamata ace sun dawo gida ko?,i missed them alort” baki ta tabe,bataga alamun hakan ba,ya shiga hidimar qara aurensa abunsa zai gaya mata haka?,da daa ne da tuni ya aika da mota ko kuma ya taka da kansa ya debo yaransa,amma yanzu saboda dalilin aurensa baiyi hakan ba,sai zancan a dawo masa dasu kawai yakeyi

    “Sai gobe idan Allah ya kaimu,zasu taho tare da nazeera,zata tayani hada abincin baqi” ajjiye body mist din hannunsa yayi ya waiwayo gaba daya yana kallonta,ya harde hannayensa aqirji,da gaske fa tana bashi mamaki,kamar ba hafsa na.

    Taji a jikinta sarai ita yake kallo,idanunsa ba normal idanu bane irin na kowa,zaiyi wuya ya kalleka dasu bakijisu har cikin qashinka ba,saita kauda kanta gefe,bataso su hada idanu,bare ya karanci komai ta cikin idanunta da wannan qwarewar aikin nasa da yake amfani dasu wani lokaci a kanta.

    Batasan tahowa yake ba sai da hancinta ya shaqi mayataccen qamshin nan nasa dake kashe mata jiki da zuciya,saman sofa bed ya zauna dab da ita,har gwiwarsa tana gogar tata,ya kamo hannuwanta sosai ya riqe cikin nashi,sai taji hawaye na shirin sauko mata,saboda yadda zuciyarta ta karye da tuna a yanzun abbas din sunan mijin mace biyu yake amsawa,so samu ta fusge hannunta,ta kalli idanunsa ta gaggaya masa magana,amma kuma hakan ya bata da tsarinsu,dole tayi laqwas,tana jin yadda azababben sonshi yake motsa mata.

    Da wata irin murya mai laushi yake mata magana,har yanzun bai saki hannunta ba

    “Idan nace miki banjin dadin wannan karamcin da kika yimin ba nayi qarya,kinyimin abinda babu wadda zaiyimin sai ke din,kin bani nutsuwar cikawa da sauke wannan nauyin,bansan da bakin da zan miki godiya ba hafcy” sunan da ya kirata dashi,wani suna ne mai dadadden tarihi a tsakaninsu,wanda ya jima bai kirata dashi ba,kuma kusan itace silar faruwar hakan.

    Dukka wadan nan maganganun da yake gaya mata gani take kawai rainin hankali da rainin wayo ne,maganganu masu zafi takeson gaya masa amma saita buge da janye hannunta daga nashi

    “Tunda dai ka samu yadda kakeso kuma ba shikenan ba?” Ta fada tana duqawa qasa ta soma serving dinsa,tasan idan ba haka tayi zata fallasa kanta ne kawai,saboda ta soma tsarguwa da irin kallon da taga yana binta dashi

    “Bismillah ga abinci nan”ta fadi tana matsawa gefe

    “Kiyimin alqawari zaku zauna lafiya ke da ita”

    “Banyi ba” ta fada a zafafe,saboda yadda takejin ta fara kaiwa maqura,haqurinta ya fara qarewa,ya zuwa sannan takai bango.

    Ita ta fara janye idanunta daga kallon qurillar da yake mata

    “Zanyi iya bakin qoqari na,zan mata yadda zanwa qanne na,amma idan ka taimakawa hakan ta hanyar nuna mata mutunci da kimata” ta qarashe zancan hawaye yana sauko mata.

    Karamin murmushi ya sake,sai ya bude mata hannayensa,with coolness yace

    “C’mon,is okay”.

    Yadda taso din hakance ta faru,a sassan abbas din ta kwana,ya sake tsumata da muguwar soyayyar nan tasa data sake dasa mata matsanancin kishinsa,ta kuma sake cin buri da alwashin hana kowacce diya mace lasar wannan tsadadda zuma daga gareshi.

    Tare suka kintsa sukayi alwalar asuba,abinda ya dade bai faru ba,shi ya sanya jallabiyya yadau hula da carbinsa ya wuce masallaci,ita kuma bayan ta idar ta maqale daga gefan gado,zuciyarta nata lasafta mata irin abubuwan da zasu ci gaba da biyowa baya cikin gidan bisa tsarinta da kuma yadda taso,tana jin bacci,tana kuma son komawa,amma tana son ta sake yin wani abun da zai qara wanke ta a wajensa,ya kuma share mata filin da zata aiwatar sa qudurinta hankali kwance.

    Sanda agogo ya kada shida saita miqe tana fita a sashen zuwa nata,ta kuma fada kitchen tanata qunquni da surutan hanata rawar gaban hantsi,tsahon rayuwar aurenta batajin ta tana shiga kitchen sau uku a irin wannan lokacin,koda abbas kuwa yana da fitar sassafe,saidai ya hadawa kansa komai,kafin ta tashi ma ya fice abinsa.

    Daga masallaci sai ya wuce sassan widad din don ya gaida baqi,yasan cewa dole akwai manya a cikinsu,duk da rabinsu suna masaukin da gwamnan bauchi da kansa ya bayar yace a sauki baqin.

    Yadda ya gaidasu cikin girmamawa da dattako ya qara shiga ransu inna laila,dukkan wata haiba da nutsuwa tasa gami da sanin darajar dan adam ta bayyana,widad ita da nujood da anty madeena suka kwana a dakinta,anty madeena tunda tayi sallah ta fito nan wajensu ta barsu a dakin,don haka cikin hikima inna laila tasa aka taso nujood a dakin,saura widad kawai.

    Har ya miqe zai juya inna laila tace dashi

    “Tana ciki ai” sam bai kawota cikin ransa ba,to amma ya kamata ya dubata,tunda yanzun dole tana qarqashin kulawarsa,bugu da qari kosa yaushe akwai wani sashe na zuciyarsa dake sake tunasar dashi muryar hajiya cikin sautin dake gaya masa amana ce ita a wajenka,ka riqeta amana.

    Da qanqanuwar sallama a bakinsa ya tura qofar ya shiga,qamshin sabbin furniture da turarukan wutan da aka ajjiye cikin dakin saman mirror suka cakuda suka bada wani kalar qamshi suka daki hancinsa.

    Sake maimaita sallamar yayi amma ba’a amsa masa ba,ya dan sake takawa zuwa ciki kadan,sai ya hangota daga gefan gadon,kwance saman lallausar sabuwar dadduma,ta qudunduna sosai cikin hijabinta jakar daddumar,da alama dasu tayi sallah,tana kuma idarwa baccin ya dauketa a wajen.

    Takawa yaci gaba da yi har ya isa gabanta,yadda ta cure sosai kamar maijin sanyi ko jariri a cikin mamarsa yasa ya fahimci kamar sanyi takeji,saiya waiwaya inda ac din dakin yake,sun qureta ne da yawa,ta kuma hadu da sanyin asuba,ya laluba remote saman bedside drawer ya kasheta,sannan ya maida dubansa ga fuskarta da rabinta ne kawai ya bayyana.

    Idanun nasa ya dauke,yaja da baya ya nufi qofar fita,dai dai lokacin da hancinta ya cika sa qamshin wani tutare na daban,saita buda idanunta da sauri,take ta hangi bayansa sanda yake ficewa a dakin,saita miqe da sauri ta zauna tana jingina bayanta da gado tana kuma raba ido

    “Me yasa ya shigo?,haka kawai tana baccinta” saita kalli jikinta
    “Allah ma dai yaso hijabine a jikina” ta fada tana sake jan hijabin tana rufe qafafuwanta,kamar ce mata akayi zai dawo.

    *AREWABOOKS:HUGUMA*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[2/27, 10:43 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 40

    Arubuce Ta Ke 40

    Page 40

    Kuka sosai ta sakarwa ummun,da qyar ta samu ta shawo kanta,cikin hikima da dabara irin ta manya ta dinga lallabata,har sai data gamsu ta kuma ji alamun sakewa da tayi sannan ta fara tambayar ta inda wayarta take,sam ta ma manta da wani batun wayarta,sai a sannan ta tuna tun randa suka iso da nujood ta gama game da ita tace ta saka mata a bedside drawer dinta.

    Kusan awa guda suka shafe da ummu a waya,har alhaji ma ya karba,Aafiya da rafi’ah da suka shigo suma dukkansu suka karba,sai da kudin ummu ya qare tsaf kiran ya yanke da kansa.

    Maganganun da sukayi da ummu yasa ta samu sassauci,sai walwalarta kadan ta dawo,ta sauko daga saman gadon da wayar riqe a hannunta da niyyar kaiwa latifa.

    Tana shirin bude kofar dakin aka turo qofar,sai ta danja da baya tana kallonshi yana shigowa dakin,sanye yake da wani yadi mai taushi,a ido kawai zaka fahimci bashi da kauri,saboda kana iya hangen fara qal din vest din dake jikinsa.

    Baya ta sake ja tana rakubewa,gabanta kuma yana faduwa,har ya qaraso cikin dakin,ya taka a hankali ya qarasa gaban madubinta ya tsaya

    “Ina kwana?” Ta gaidashi tana dan russunawa,sai ya maida dubansa a kanta,gaba daya a darare take, baisan me yasa ba,amma ya gama karantar dabi’unta tsaf na rashin sakewa da jama’a,da alama tana da wuyar sabo,shikam tako ta ina baiga ta inda wannan hadin zai zama me alfanu ba,saidai ya sani cewa,abinda babba ya hango,yaro ko ya hau dala da gauron dutse bazai hangoshi ba

    “Lafiya lau,ya kwanan baqunta?” Ya fadi yana gyara daurin agogonsa,bata san ya zatace ba sai tayi shuru kawai ta sadda kanta,ita kawai Allah Allah take ya fita mata a daki,kada latifa tazo ta gansu su biyu.

    Sai daya gama gyara agogon sannan ya maida kallonsa a kanta

    “Shikenan babu wani abu da kuke buqata?” Kai ta gyada masa da sauri,sai ya jinjina kai,ya sanya hannu a aljihunsa ya fidda kudi ya ajjiye mata,don dabi’arsa ce,haka yakewa hafsan,koda suna da komai baya taba fita ya barta hannu babu komai.

    Ido ta bude sosai ta zarosu waje tana kallon kudin,har ya kusa fita daga dakin sannan ta ankara,da hanzari tace

    “Don Allah ka dauke,kada latifa ta gani,ni banaso” qaramin murmushi ne ya subuce masa duk da bai shiryawa hakan ba,ya waiwayo yana kallonta da manyan idanunsa

    “Ba zata komai ba koda ta gani din,daga yanzu duk abinda na baki babu wanda zai miki fada don kin karba,right?” Jikinta a sanyaye ta gyada kanta,don dai ita ta sani ummu na fada sosai gasu basma ma idan wani ya musu kyauta suka karba,tana kallonsa har ya fice daga dakin,sai ta matsa kusa da kudin tana kallonsu ba tare data taba ba.

    Ja baya tayi kadan jin an sake buda qofar an shigo,latifa ce,idanunta nakan fuskar widad din

    “Kun gama wayar ne?” Kai ta gyada mata

    “Eh tun dazu,kinga kudi wai ya bani” ta fada a shagwabe cike da sakarci tana dubanta

    “Kuma Allah bani na roqshi ba” ta sake fada qwalla na cika mata idanu,dariya kufcewa latifa,ta yarda widad bayan quruciya ma harda sangarta irin ta goyon kaka ke damunta,qarasawa tayi inda take tsaye ta kama hannunta ta riqe

    “Don ya baki kudi ba komai bane,mijinki ne kinji, komai zai baki hakanan kome zaiyi miki ba haramun bane kin gane?”, Kai ta gyada kawai bawai don ta fahimci me take nufi ba

    “Kuma ya akayi ya fita baki masa rakiya ba?”

    “Mu jera tare?” Ta tambayi latifa tana fidda idanu,saita jinjina mata kai

    “Eh mana,bakiga ummu na raka alhaji ba?” Shuru ta danyi tana tunowa,ta gyada kai a hankali

    “To daga yau kema haka zaki dinga yi masa kinji ko?” Fuska ta noqe,itadai wannan ai iskanci ne,batason irin wadan nan maganganun,haka dai ta gyadawa latifan kai,sannan ta sakata a gaba suka wuce kitchen.

    A ranar latifa ta fara gwada mata yadda zatayi wasu abubuwa cikin kitchen,kamar tsaftaceshi da inda zata dinga ajjiye komai a muhallinsa cikin kitchen din,yadda zata wanke kwanuka da sauransu.

    Da yammaci tana falonta a zaune bayan sun gama komai ta dinga jin hayaniyar yara,sai tayi mamaki don bata dauka akwai yara a gidan ba,daga nan ta yaye labulen falon nata,sai ta hangi su mimi suna wasa,tana son fita amma ita komai na gidan d’ari d’ari takeyi dashi,don haka taci gaba da kallonsu ta nan,har suka gama wasansu suka bar wajen.

    Tun qarfe shida ta gama lafta shinkafarta da miya,ta zubata cikin food flask,bata damu da jimawar da zaiyi kafin ya dawo ba,ko kuma gumin abincin da zai iya komawa cikin flask din ba.

    Fuskarta ta dauraye kawai,ta cire zanin jikinta ta nemo mahadin rigar ta saka,sannan ta tasa su mimi a gaba suka wuce sashen widad,tayi hakanne saboda ta hanashi dadewa acan,kada ya shiga yaje ya zauna,ko abinda ya faru jiya ya maimaita kansa,cikin ranta tana jin ko a jiyan ma kirsa ce kawai irin tata,ta sani cewa mace duk qanqantarta kaidi ne da ita,kada tazo tana tufka ta baya tana warware.

    Kan widad na saman cinyar latifa tana kitsa mata kalba tana warewa saboda santsin gashinta,sa’annan kuma ba wani kama mata takeyi da kyau ba,tana mata ne shigen yadda ummu ke mata idan tanason tayi baccin rana,latifan na bata labarun ban dariya,wanda ya sake sanyawa zuciyarta ta kuma saki.

    Koda tayi sallama hannu bibbiyu latifa ta karbeta,widad kuwa kamar ko yaushe binta tayi da kallo kafin ta zamo ta gaisheta kamar yadda take gaida dukan wanda ya girmeta,hakan kuma sai ya yiwa hafsat dadi,ta sake jin lallai itace a sama,ta dinga bin falon da kallo a fakaice,kafin ta koma satar kallon widad din,bata da matsala da komai,tana kuma jin komai zai tafi dai dai,damuwarta daya irin kyawun da yarinyar take dashi,tana tsoron kada wannan ya zama mabudin nasarar jan hankalin abbas…

    “Inaaaa,bazan bari ba” ta tabbatarwa kanta da kanta cikin zuciyarta,zatayi dukkan mai yuwuwa ta hana wannan kyan tasiri a fuska da idanunsa.

    Kusan da latifa suke hirar,ita widad ta maida hankalinta gasu mimi,kasancewarta mai son qananun yara,duka sai suka ja hankalinta,tana ta duban fuskar nawwara da taga tana mata kama da fuskarshi

    “Ke dawa kike kama?” Ta tambayi yarinyar tana dan murmushi,mimi tayi wuf tace

    “Da daddynmu mana,ni kuma da mommy na,wai shine su anty bara suke cewa ta fini kyau,wai daddy yafi mommy kyau” daga idanunta widad tayi ta dubi fuskar hafsat dake magana da latifa,eh itama taga wannan duk da qarancin shekarunta,amma dai tasan kyau

    “Eh wallahi,ya fita kyau” widad ta fada hankalinta kwance cikin yanayi na quruciya.

    Rigime mata mimi tayi ta soma qwalawa uwar kira

    “Mommy,kinji anty ma tace daddy yafiki kyau,kuma nawwara ta fini kyau?” Dariya latifa tadan saki tana kama baki,widad din tayi wauta,amma da alama ma ita a wajenta ba komai bane,yayin da hafsat ta kafe widad da idanu,wani abu mai kama da bacin rai yana motsa mata qasan ranta,sai kuma ta buge da murmushin yaqe

    “Tsokanarki takeyi,kuma ni nafi daddynku kyau,saidai ya nunamin manyan ido kawai” cikin murna mimi ta waiwaya tana duban widad

    “To kinji ko?” Dariya ta saki tana jawota jikinta

    “Wasa nake miki,kema kina kama da daddyn naki ai” kau da idanunta hafsat tayi daga kansu, zuciyarta na raya mata wani abu.

    Yau dinma kai tsaye sassan hafsat din ya fara isa,bai taras da kowa a falon ba,don haka ya sanya kai bedroom dinta,yana taka lallausan sabon carfet din daya sauya mata dab da bikin nan,amma har datti ya fara cikashi laushinsa ya ragu ainun.

    Dakin yaran ya fara budewa,komai a hargitse a zaune da duwawunshi,ash and baby pink ne color din dakin,amma pink din har ya dauki hanyar zama ash din shima,ya taka a hankali yana tattare kayan sawarsu dake watse a qasan dakin,sun cakude waje daya,ba zaka banbance wankakke da wanda baida wanki ko kuma guga ba,ya kwashe gaba daya,ya buda laundry basket dinsu da niyyar zubawa,sai ya sameshi a cike fam da kaya.

    Ransa ya sosu,baiga amfanin yaron da ya aje saboda ya dinga musu wanki ba,bayan duk wata sai ya ajjiye kudinsa,to kudin ake bashi a banza ko kuwa,ya daga kayan da niyyar zubasu a haka yaci karo da undies din hafsat din,harda brassieres.

    Kishinsa ne ya motsa,ransa ya sake baci fiye da dazu,sai ya watsar da kayan yaran gefe daya,ya soma birkito kwandon,nan ya dinga cin karo da undies dinta,ya dinga tarasu a gefe,har ya gama kwashesu tsaf,sannan ya zuba kayansu mimi din,ya buda toilet dinsu ya leqa,dole ya dawo baya da sauri,saboda abun babu kyan gani,mutum ne shi me masifar tsantsami,idan kanaso kaga fadansa to yaga qazanta.

    Dogon tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa,yana dai tunanin me aikin da bayaso daga qarshe daqyar idan ba ita zai sa a daukowa hafsat din ba,ya gaji da ganin wannan qazantar gaba daya,to amma kuma hakan kamar daure mata qarqashi ne,kada ta sake sangarcewa ta miqe qafa,tun a baya yaqi a kawota dinne saboda gudun ta sake tabarbarewa,amma a yanzu dukka alamu suna nuna daukotan ya kusa zame masa wajibi.

    Dakin ya janyo musu ya wuce nata dakin,shima dai kamar dakin yaran,shikam natan harda tsami tsamin kayan wanki,bai saka kai da yawa ba ya dawo da baya yana ambaton sunan Allah,sai kawai ya juya ya fice daga sashen gaba daya.

    Duk da ransa babu dadi haka ya daure ya nufi sashen widad din,tunda dai itama matarsa ce kamar hafsat din,tana kuma da haqqi a kansa kamar ita.

    Sanda yayi sallama a falon yayi dai dai da sanda widad ke maimaitawa mimi karatun makarantar bokonta,yarinyar kuwa nata kamawa tana amsawa cikin jin dadi,don baqon abune a wajenta,mamarta bata taba tsayawa ko sau daya ta duba assignment dinta ko ta bibiyi karatunta ba,abbas din keyi mata assignment idan yana gari,idan baya nan kuma haka zata koma da litattafan ta, aunties dinsu sunsha rubuto letter suce ta kawo gida,hafsat ke karba,tana gama karantawa take yagawa,ta rubuta reply da cewa ayi haquri,mamanta ba mazauniya bace amma za’a gyara,har sun gaji da rubutun sun qyaleta,saboda suna ganin kudin ubanta ke tafiya,su basu da asara.

    Rige rigen zuwa yi masa sannu da zuwa sukeyi,widad ta bisu da kallo tana jin damuwarta da kewarta na raguwa,dan zaman awannin da sukayi dasu sun debe mata kewa matuqa.

    Tunda ya shigo din take bibiyar dukka motsinsa da idanuwanta,tana son taga shin ko zai kalli sassan da widad din ke zaune?,ko kuma zai saci kallonta ko sau daya ne?.

    *Arewabooks: Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[3/2, 10:44 AM] +234 802 297 0646: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 48

    Arubuce Ta Ke 48

    Page 48

    Tana cikin wannan mitar aka buga qofar falon

    “Waye na?” Ta fada cikin fada fada,ranta fal quncin mimin ta karya mata budget

    “Nine,sale ne”

    “Shigo” ta fada kanta tsaye bayan taja tsaki,duk da tasan abbas baison haka,don baya bari a shigo masa har inda iyalinsa suke kai tsaye.

    Da sallama yaron ya shigo yana sunkui da kai,don bai saba shigowar ba,ga hafsat din da daurin qirji,sauqinta akwai t-shirt a jikinta,a samanta taja zanin ta daura

    “Ina kwana hajiya”

    “Lafiya lau ya akayi?”

    “Eh dama me yiwa engine service ne yazo,za’a bada kudin a siya kayan aikin,sai mechanic din da zai dauki motar oga ya kaita garage za’a mata service itama” tsuke fuska tayi,don tasan kudaden daya wara ya bata saboda a duba motar da engine din suna da yawa

    “Bakaniken ya dauki motar,amma shi me yiwa engine service kace ya barshi kawai,sai mai gidan ya dawo”

    “To….amma engine din yana bada matsala fa,jiya ma…..”

    “Abinda nace kayi zakayi ko raayinka zanbi?”

    “Sorry madam” ya fada yana juyawa yabar falon,cikin ransa yana Ala wadai da dabi’arta,sarai yasan an bata kudaden,fitar dasu ne ba zata iya ba.

    Tsaki taja tana duban yaran

    “Ku wuce muje na dafa muku abinci” jin xancan abinci sai mimi ta ware,sukabi bayanta zuwa kitchen din,saidai tana ganin ta buda kwalin indomie yarinyar ta bata rai,ta gaji da ita,don jiya da daddare ma ita ta dafa musu

    “Indomie mommy?,bana ci nidai” cikin takaici ta kalla yarinyar,ubansu ya batasu da kala kalar abinci,ita kuwa ba zata iya dorama kanta wannan wahalar ba

    “Ba zakici ba ubanme zakici?”

    “Irin abincin gidan hajiya”

    “Meye abincin gidan hajiyan?”

    “Tuwo ko dambu”

    “Nabi tuwon da gudu,zakici ubanki wallahi,idan bakici ki zauna haka,yunwar cikinki” saita bare kwalin ta dauko guda biyu ta zuba a tukunyar.

    Kusan dai a gantale suka tsakuri taliyar,bata tsaya ta mata ma dahuwar arziqi ba bare darajar hakan ya sanya suci da yawa,daga qarshe ma.idan ta debo ta baiwa nawwara sai ta tankwabe hannunta,da yake ita din tafi mimi fada,sai ta tattarasu ta barsu ta shiga sabgarta,dole da yunwa ta ishesu suka dawo suka ci a haka bayan tayi sanyi.

    ¢¢¢¢¢¢¢¢¢ Hirar da suka sha da ummu da abbanta na kusan awa biyu ya sanya tajita tadan sake,sai kuma dan motsin da take jiyowa lokaci lokaci cikin gidan ya sanya bata matsu da yawa ba,ta dan saki jiki ta soma kade dakin da gyarashi kamar yadda latifa ta koya mata,sannu a hankali sai gashi ta gyara dakin fes,sadai fa tadan dauki lokaci,ta shiga toilet ta wanke fes,ta kama qugu tana dariyar farinciki na ganin yadda ta gyara dakin kamar ba ita ba,ta kama baki tana murna

    “Ashe dai na iya,amma ummu ke hanani,bari na kira umma latifa na bata labari” ta koma gefan gadon tana kaffa kaffa kada ta bata zanin gadon data d’ameshi da kyau,ta fara duba number latifa wadda basu jima da gama waya da ita ba itama,Latifa na daga wayar ta fara bata labari

    “Iyeee shalelen ummu,girma yazo,haka akeso,kiyita tsafta kamar ummunki,saura girki” dariya tayi tana sake bata labarin wahalar data sha,latifa na biye mata,ummu ja gefansu tana murmushi,duk da rabin hankalinta nakan shalelen tata.

    Wunin ranar bata wani ji yunwa ba,koda taji yunwa dinma tea ta hada tasha ta kwanta abinta.

    Kafin magariba tayi wanka,ta shafe jikinta da turarukan da latifa ta hado mata a kayanta,kusan sai data shafa kowanne turare,har ya soma yawa ya fara hawa ka,kowanne mai sanyi da dadin qamshi ne,amma yawan da yayi yasa ya jirkita,amma ita ko a jikinta,wata dubai abaya ta saka,ta dawo falo ta maqale jikin window tana leqen harabar gidan,gabanta yana dan faduwa kadan kadan,saboda ganin magariba ta gabato babu shi ba alamarsa.

    Ana qwala kiran sallar magariba motarsa tana shigowa cikin gidan,samuel ne ya kawoshi,shi ya koma shi kuma ya shigo ciki.

    “sannu da zuwa” ta furta tana jan dankwalinta daya zame saboda santsinsa daya hadu da sulbin gashinta,ta miqe tsoron nan nata yana bayyana,tanason karbar masa ledar daya shigo da ita kamar yadda ta saba duk sanda taga kaya hannun babba,amma tana shakka matsawa inda yake,a haka har ya qaraso ya ajjiye,ya zauna yana tube takalman qafarsa

    “Lafiya kika wuni?” Kai ta gyada masa,sai yadan lumshe idanu yana gyada kai,qamshin jikinta gaba daya ya cika falon,kamar anyi barin turare

    “Samomin ruwa nasha” hanyar kitchen din ta kalla,baiyi duhu sosai ba,don haka da sauri tayi hanyar,a nufinta tayi sauri ta dawo kada wajen yafi haka duhu.

    Binta yayi da kallo,ko yaushe ya kalletan sai ya dinga jin mamaki na shigarsa,wai matarsa ce wannan,ta dawo da ruwan ta russuna ta miqa masa kamar yadda ta saba yi tun a gida.

    Hannu yasa zai karba,yadda tayin yana burgeshi,duk da abub mamaki bane,duba da gidan data fito,muhsin kadai ya ishi a shaidesu,don ko cikin abokansu daban yake,wani abune da zai iya cewa baisan lokaci na qarshe da hafsat tayi masa ba wai don zata bashi abu.

    Sakin ruwan tayi da sauri sanda hannunsa ya sauka akan nata,jikinta ya dauki rawa,taja da baya tana yarfe hannu jikinta yana rawa,hawaye na shirin tarar mata a ido,shi bai kula bama,don ya duqa zai dauke ruwan bayan ya furta

    “Subhanallah” sanda ya dago harta samu waje ta rakube,ya bita da kallo yana mamakin yadda take matuqar tsoron tarayya dashi,kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya bude gorar ruwan ya fara sha,sannan ya miqe yana cewa

    “Zanje sallah,idan na dawo zaki shiga ciki ku gaisa da mutanen gidan,ga abinci nan a leda ki dauki naki” kai ta gyada masa gabanta na faduwa,bata samu nutsuwa ba har sai da yayi alwalar ya fice,ta bishi da kallo tana hararar hanya qwalla na gangaro mata,yanzu idan ummu ko mommy suka ga wannan abun da yakeyi fa?.

    A falo ya tsaya jiranta,ta fito yafe da mayafin abayar bayan ta cire hijabin da tayi sallar dashi

    “Koma ki samo babban mayafi,akwai mutane a waje” yayi maganar sanda yake dage labulen falon yana sake duba farfajiyar gidan,jikinta ta kalla,itadai bataga wani aibu a haka ba,amma sai batace komai ba ta koma ta lalubo mayafi cikin kayanta ta fito,suka jera zuwa cikin gidan.

    Babban gini ne,don yadan fi nasu girma da kayan alatu,sanda ta shiga ta samu matar gidan a falo,ta karbeta da fara’a,saidai tunda ta gaidata ta rasa me zata cemata.

    “Ban gane fuskar taki ba,ko kanwar amaryar abbas ce?” Qas tayi da kanta tana jin nauyi yana kamata,saita girgiza kai alamun a’ah

    “Ko amaryar ce da kanta?” Saita daga kai alamun eh,matar ta maida kanta sosai tana kallon widad din sosai,abbas data sani,abbas dake da.babbar mace kamar hafsat yaje ya auro wannan qwailar?,lallai Allah mai iko,sau tari mazan da suka fiya izza da kuma jin kansu daga qarshe haka suke qarewa,har gwara wannan din,kyakkyawa ce data amsa sunanta,komai nata mai ban sha’awa da daukan hankali,nan gaba kadan idan ta ida zama cikakkiyar mace lallai ba shakka sai an kalleta an qara,dole hankalin hafsat din ya tashi,amma a fili sai tace da ita

    “Ma sha Allah,Allah ya bada zama lafiya kinji amarya” bata iya amsa mata ba,sai shuru data sakeyi kawai kanta a qasa,gaba daya bata jinta a sake,tun asali dama ita din bamai saurin sabo bace,tana da wuyar sakewa da baqin fuska,don haka bata wani jima ba ta miqe tace zata tafi

    “To ina zuwa” ta fadi tana miqewa ta shige ciki,ranta da zuciyarta fal mamaki,ba jimawa ta fito da wasu kayan barci set uku ta bata,hannu biyu widad ta saka ta karba sannan ta fito.

    A inda ta barshi ta sameshi,ya sake mata jagora suka koma ciki,tana ta kallon gate,ji take kaman ta fita ta miqe qafarta,suna shiga falon ta miqa masa kayan kamar yadda takewa ummu a gida idan an mata kyautar abu

    “Gashi” ta fada tana ajjiye masa kusa dashi,dai dai lokacin da ledar ta zame,matan dake jikin takardar sanye da irin kayan baccin dake cikin ledar suka fito.

    Kusan tare suka dauke idanunsu shi da ita,taja baya da sauri qafafunta na sarqewa zata wuce ciki

    “Zonan” yayi kiranta yana karantarta,da baya da baya ta dawo,ita a lallai ba zata iya kallonsa ba,har abun yaso bashi dariya,ya dake da yanayin dakiyarsa da kuma miskilancinsa

    “Dauke abinki ki tafi dasu”

    “Banaso” ta fada kai tsaye tana maqale kafada,a mamakance yake kallonta

    “Bake ta bawa ba?”

    “Ni ta bawa,amma banaso,bana saka irinsu” dariyar da yaketa riqewa ta subuce masa,amma saita fita ta sigar murmushi

    “Zauna” yace da ita yanata kokawa da dariyar tasa,ta baya ta zauna har yanzu taqi yarda su hada ido dashi.

    “kinsan amfanin wadan nan kayan?” Fuska ta qara daurewa,tana sake tabbatarwa basu hada ido ba,kai ta girgixa masa ba tare da tayi magana ba

    “Oya….open your mouth,ban jiki ba”

    “Ban sani ba,kayan ‘yan iska ne fa” tayi maganar tana narke fuska,kamar zata saki kuka.

    Wannan karon duk yadda yaso boye dariyarsa sai data fidda sauti,yayi qoqarin daidaita kansa,da gaske ta jahilci aure,da alama aiki je jajur a gabansa a kanta,bai tsawwala sai ya samu komai daga gareta ba,amma aqalla ta gama sanin meye auren kansa,don da alama batasan meye shi ba.

    “Kwashesu ki tafi” ya bata umarni a taqaice,ta baya ta zuro hannunta ta jawo ledar zuwa gabanta,sannan ta miqe da sauri sauri tayi dakinta.

    Tana shiga ta jefa ledar saman sofa bed tana zumbura baki kamar zata fashe,ledar ta qarasa yayewa kayan suka fito sosai,bata gama kula da hotunan jiki bama sai yanzu,ta qarasa tana daga kayan saita jefar zuciyarta a a cushe

    “Lallai matar nan ma ‘yar iska ce ashe itama,don me zata bata wadan nan kayan?” Hadasu tayi ta cukuikuye ta jefa cikin sif,ta koma saman gado ta lafe a cikin bargo abinta,idanunta ta rufe,tana fata bacci ya dauketa tun tana iya jin motsinsa,basai waje yayi shuru ba.

    °°°°°°°°°Washegari ma haka ya fita,bai tsaya yin breakfast ba,yauma ita dinma kamar jiya,bayan ta gama ‘yan gyare gyarenta da zata iya,saita dawo bakin window din falon ta zauna,lokaci lokaci tana yaye labulen tana leqa farfajiyar gidan,abinda ya tayata zama kenan,duk da yace mata tana iya shiga cikin gidan ta zauna a can,kota debe kewa,amma kasancewarta mara saurin sabo taji gwara tayi zamanta a nan har zuwa sanda ya dawo gida.

    To tsahon kwanaki biyar kusan haka rayuwar ta dinga gara musu,da safe idan zaya fita aiki zai sameta ne a falo,sabida yafi dakinta haske,zatayi masa a dawo lafiya bayan ta gaidashi,ya ajiye mata kudi ya kuma tambayeta bata da matsala,sannan ya mata sallama,takan bishi da idanu tana jin kamar ta bishi,wani lokacin yana ankare da ita,wani zubin hankalinsa yayi gaba,zata gyara dakinta data fara sabawa dashi,ta gyara falo ta goge shi tasa,duk da cewa tana daukan lokaci kafin ta gama,amma yana kintsuwa,kyan sharar nata da gyaran nata yake gani,saboda tafi hafsat nesa ba kusa ba, at least ita bata barin qura ko datti,sabanin hafsat din da ko ina a birkice yake,duk da suna da komai a store,to amma bata taba dora girki ba,yana sawa a kawo mata abinci,idan ya dawo tana cikin falon,amma wata qurya ta daban,a can zata zauna ba um ba um um,tana kallonsa kawai,duk da tana buqatar hira da wanda zatayi hira dashi,sai idan yaga tana gyangyadi kota gaji zai rakata ta kwanta ya dawo falo yaci gaba da sabgoginsa kafin ya tattara shima ya wuce nasa dakin.

    Duk sanda tsautsayi yasa ta farka cikin dare kuwa da qyar da sudin goshi take komawa baccin,saboda dan banzan tsoro,a rayuwarta bata taba kwana daki ita daya ba sai a wannan karon.

    Bangaren hafsat kuwa kullum a rana saita kirata,ta tambayeta me ya faru a jiya,me yake faruwa a yanxu,amsa kawai take buqata,tana ji zata katse wayarta,saidai idan weedad dince tabi bayan kiran tace a bata su mimi.

    Zuwa sannan fa fara jin dadin wayarta,da kanta da kanta ta koyi yadda ake sarrafa abubuwa da dama a cikinta,ta dauko games kala kala da suke debe mata kewa sosai,wannan yasa dogon wunin kadaicin da takeyi ya ragu sosai.

    _wannan kenan_

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/7, 11:54 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 46

    Arubuce Ta Ke 46

    Page 46

    Space ya bata,ya zauna daga nesa yana kallonta har sai data gamsu don kanta ta tsagaita kukan,don ya fuskanci kukan da take harda na sakalci ma,sanann ya miqe yana duba dakin ko zaiga abincin da yace a kawo mata amma baiga alamunsa ba,waiwayawa yayi yana dubanta

    “Ina abincin da nace a kawo miki?” Baki ta tabe sosai irin na yaran da suka gwanance wajen shagwaba

    “Naji ana knocking,inajin tsoro ne bazan iya fita ba” dan qaramin bakinta me dauke da jajayen lips yabi da kallo,wannan da alama ba abinda ta sani sai sangarta da sakalci,ya janye idanuwansa yana laluba aljihunsa ya fidda wayarsa,a nan ya samu tarin miscall na wanda ya aika din,yana kiransa kafin yace komai ya gaya masa yayita bugu ba’a bude ba

    “Ba matsala,am back,zaka iya kawowa” ya fada yana nufar qofar dakin da zummar ficewa,saidai tun bai sanya qafarsa a falo ba ta miqe ta rufa masa baya.

    Tsayawa yayi bayan ya zame wayar daga kunnensa sannan ya waiwayo yana kallonta,saita dauke kanta gefe tana turo baki gaba gami da tabeshi

    “Ina zaki?”

    “Ni binka zanyi,Allah ba zan zauna a nan ba” saiga hawaye yana biyo bayan maganarta

    “Saqo zan karbo”

    “Zan bika” ta sake fada wasu hawayen na sake zubowa

    “Yanzu zan dawo,just a compound din gidan nan ne” wannan karon maqale kafada tayi saboda kuka ya riga da ya subuce mata

    “Oh god” ya fada yana dan lumshe idanunsa hadi da budesu duka lokaci guda,kafin ya sake cewa wani abu anyi knocking,sai kawai yayi gaba,ta kuwa take masa baya yana dauke qafarsa tana saka tata.

    Takeaway na abincin ya karba ya maida qofar ya kulle,daya juyo sai kuma tayi tsaye tana jin banbarakwai,ya tako taja baya hadi da yin gefe ta bashi hanya,ya isa tsakiyar falon

    “Dauko plate a kitchen da spoon” ya fada yana ajjiye ledar,hadi da zama saman kujerar sannan ya fara qoqarin cire agogon hannunsa.

    Jin shuru bata amsa ba,bata kuma motsa ba ya sanyashi dago kansa,tana tsaye ta marairaice fuska kawai tana kallonsa

    “Bakiji bane?” Ya tambayeta da kaurin murya

    “Tsoro….”

    “Subhanallah” ya furta a hankali,sai kawai ya miqe ba tare da yace komai ba,nan ma batayi qasa a gwiwa ba ta rufa masa baya,tana tsaye ya dauko plate din,ya hado da spoons da bottle water da drink na kwali guda daya sannan suka rankayo suka fito.

    Wannan karon a qas ya zauna sosai,ya bude ledojin ya hada komai da komai kowanne plates d’ai d’ai ya tura mata hade da ruwan da kuma lemon,ya sanyawa nashi palate din spoon ya fara diban abincin yana ci bayan yayi bismillah,hannunsa daya riqe da wayarsa yana dannawa.

    Shuru tayi tana kallon plate din nata,tun asali ita din bata saba cin abinci ita kadai ba,tun tasowarta,saboda ta taso mutum ce mara son cin abinci,wannan yasa kowanne lokaci da ummu sukeci,suna ci tana hilatarta har sai taci me yawa,idan kuwa tana azumine ko kuma tana makaranta taci kafin ta dawo wanda zaiyi wuya ma ta rigata ci din,saita hada mata da wani cikinsu Aafiya,ko ta tafi sassan anty madina taci cikin jama’a,shine fa take ci da dan dama,ko zuwanta bauchi kullum da latifa sukeci,to a yanzun saita kasa tabuka komai,har yayi nisa da cin nasa abincin.

    Bai kula ba sai da yayi nisa sosai,ya daga idanunsa ya kalleta,itama shi take kallo,ta narke fuska kamar wadda kukan da tayi bai isheta ba tana neman qari ne

    “Dauki kici” ya fadi yana mata nuni da abincin da ido,saita girgiza kai

    “Na qoshi” mamaki ya kamashi,baici ace bata jin yunwa ba,yasan tun sanda suka fito rabonta da abinci,saiya rasa yadda zai mata taci.abincin,don daga qarshe ma baya taja ta rungume qafafunta kamar wata marainiya.

    Ajiyar zuciya ya sauke yana ajjiye nasa plate din,shikam ya gamu da gamonsa,da alama rainon zaiyi da gaske,suraj da suke chart dashi a lokacin ya turawa gajeran saqon tambaya

    _”If you want a child to eat and he refuses, what will you do for him?,ina buqatar taimakon,its urgent please”_. Sai daya tura masa sticker din dariya sannan ya amsa masa

    _”yar rainon taka hala?,ka lallabata,malam ka kuma koyi magana,wannan ba hafsat bace,ita din ba zata gane shuru ba,be a child like her for a while,sannan ne komai zai daidaita”_

    _”thanks,i will tray_” ya amsa masa sannan ya kashe data dinsa ya ajjiye wayar

    “Oh God, give me courage” ya fada can qasan ransa yana kallonta

    “Let’s share the food,come closer” ya fada yans miqa hannu yaja plate din,makarantar da tayi mai tsada ce sosai,don haka ko a iya js data tsaya tana jin turanci fes tana kuma iya mayarwa,don haka taji sarai abinda ya fada,to amma fa ita tsironsa takeji,ta sani tun a gida cin abinci da maza ba abu bane me kyau,uwa uba hudubarta tana nan a kanta fes bata bace ba,ya zataci abinci da wani?,to amma kuma yunwa takeji,idan kuma bai tayata ci din ba tabbas tana iya kwana da yunwa

    “Uhnnn,bismillah” ya sake fada yana juya spoon dinsa a ciki,jiki a mace,a kuma mugun darare ta matso,nesa da plate din ta zauna,saidai tana kai hannu tana diban abincin,tana yi kuma tana satar kallonsa,amma sai taga sam shi hankalinsa baya wajen,wannan yasa ta dan sake sakewa ta soma cin abincin a nutse.

    Duk da ya qoshi hannunsa kadai ya zame amma bai tashi daga wajen ba,har sai da yaga ta cire nata hannun,takai goran ruwan mitsitsin bakinta ta fara sha,har cikin ransa yaji ya sauke nauyi,zuciyarsa tayi wasai,sanda ya dawo ya samu bataci abincin ba ji yayi kamar yaci amanar hajiya,ya kasa sauke nauyin amanar daya karba ya kuma dauka tun ba’a kai ga kwana ba.

    Zaman kurame sukayi a falon,shi yana aikace aikacen sa a waya,ita kuwa tana takure gefe daya duk da tv tana aikinta,saidai ita hankalinta ya kasu kashi biyu,duk wani motsi da taji saita waiwaya da sauri taga meye,shi kuwa ya zauna ne don ya debe mata kewa ya kuma rage mata dare,duk kuwa da yanason tashi,yana nan a zaune sai kiran hafsat ya shigo wayarsa,abinda ya bashi mamaki kenan,ya kuma yi hanzarin dagawa yana tunanin ko wani abunne ya faru?,qila ita ko wani cikin yaranne babu lafiya,saboda sam ba dabi’arta bace ta kirashi don yayi tafiya,komai nisan zangon da zaiyi,koda da nufin jin yadda ya sauka,saidai idan shi din ya sauka ya kirata ya shaida mata ya sauka lafiya,ta kuma bashi yaransa suyi magana,indai kaga kiranta to wani abunne ya faru,ko kuma wata buqatar ce ta taso.

    A tsanake ya daga wayar yana mata sallama da lallausar muryarsa data saukar mata da wani zazzafan kishinsa,zuciyarta nata ayyano mata kasantuwarsu da widad a dai dai wannan lokacin,duk kuwa da tana da wani yaqini da kuma qwarin gwiwa abinda ta dasa zaiyi tasiri sosai,saboda saran da tayi akan gaba.

    Muryar data amsa masa sallamar da ita ta sake sanyashi a mamaki,ya manta rabon da yaji wannan tune din daga gareta,tun wani zamani can baya,suka gama gaisawa yana jiran yaji ta kawo complain ko wani damuwa sai baiji wannan ba,sai hira da taketa qoqarin jansa dashi.

    To anan dai ya biye mata,don shima yana da buqatar irin wannan kulawar,yana yunwar samun kulawa irin wanann amma ta zame masa jidali a wajen hafsat din,ya kishingida kadan yana sauraren hirar da take masa,duk kuwa da cewa qarfin hali kawai takeyi,daga can harta gundura,bawai don ta gaji dajin muryarsa ba,muryarsa na daya daga cikin abubuwan da bata taba jin ta gaji dasu ba.

    “Wai ina qanwata ne?” Ta jefa masa tambayar fa tun dazun so samu ta zama ta farko,to amma he is very smart,zai iya sansano wani abu,shi yasa ta kaita tsakiyar zancansu

    “Bata mu gaisa mana,nayi mata ya gajiyar hanya?,ina fata ba zaka sake tara mata wata gajiyar ba” maida idanunsa yayi kan fuskarta da a yanzun ta bada hankalinta ga tv,saboda wani cartoon da suka juya haskawa,hasken tvn ya haske fara tas din fatarta da kyau,haka kawai zuciya ta d’arsa masa abinda hafsat din ta fada akan widad,ya danyi imagination akai na wasu sakanni,sai yayi sauri ya ture daga ransa yana fadin

    “She’s too young”

    “Hello” muryar hafsat dake tawa ta ratsa ta tunaninsa,saboda raya mata da zuciyarta tayi tana jikinsa ne yana debe kewa da ita

    “Ina jinki”

    “Tana ina?”

    “Bata kusa…..sai wani lokacin” haka kawai taji zuciyar ta bata yadda da abinda ya fada ba,don haka ta bishi da

    “Okay” taja qaramar keypad dinta ta soma trying number widad din,amma aka sanar mata a kashe wayar take,take tajin hankalinta ya tashi,abbas baya son barin waya a kunne a sanda suka kebe,haka yake,koda tata wayar karba yake ya kashe,yakance

    “I need a rest,ina buqatar kadaicewa da iyalina” bai fiya barinta kunna waya ba idan yana gida weekend a sanda suna tashen buga soyayyarsu.

    Haka kawai taji hirar duka ta fice mata a kai,don haka ta nema suyi sallama,bai matsa ba,don yaga qoqarinta,abun shekara da shekaru,shi yayi mata sallamar,yama rigata kashe wayar ya ajjiye,abinda ya sake saka mata zargi a ranta kenan,tayi jifa da wayar gefanta,ta koma da baya yaraf ta kwanta tana duban ceiling,dole ta kira yarinyar taji.me ya faru a yau,dole ta kirata ta dora mata bita.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/6, 3:13 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 35

    Arubuce Ta Ke 35

    Page 35

    Tun gari bai kammala wayewa ba suka tashi da aikin qarasa kintsa gidan,saboda suna son wucewa a ranar,saidai hakan bata samu ba,don abbas ya sake dakatar dasu yace su sake kwana,wannan ya basu dama suka buqaci mota,ya kira samuel daga office yazo ya kawo musu tare da yi musu jagora,inna laila,batulu anty deena anty halima da hajjaa suka sada widad da gidan hajiyan abbas.

    Fadin irin dadin da hajiyan taji bata baki ne,bata zaci zuwanta ba sam,saboda taga ba kasafai ake hakan ba,tunda ba unguwa daya suke ba,yadda ta dinga nan nan dasu zai baka mamaki,farincikinta ya gaza boyuwa,ta kirayi gwaggo fanteka donta tayata karbarsu.

    Duk abinda akeyi fantakea din da kallo take binsu,saidai ta saci ido ta tabe baki,idanuwanta qir akan fuskar widad

    “Ashe…..ba banza ba,ashe sadakar yalla ya kwaso,kai jama’a,kashin hafsatu ya bushe,ba abinda ba zata gani ba,idan Allah ya tsare ma bata fiddata gidan ba” wannan ta dinga maimaitawa a ranta tana binsu da kallo,musamman da taga kowanne a cikinsu daga yanayin fata zuwa halittarsu da sumar kansu batayi kama sam da hausa fulani ba.

    Duk da batasan da zuwansu ba haka ta cikasu da abinci kala kala,kasancewarta mace mai karamci,baka rasata da abubuwa irin wadan nan.

    Tun basu bar gidan ba ta kira abbas ta shaida masa,shima yaji dadin yadda suka karrama masa mahaifiya,yasan zasu fita,tunda muhsin ya gaya masa,don hajjaa tace ya gaya masa,amma baisan can zasu kaita ba.

    Sai yamma lis suka dawo gidan,a sannan hafsa tana daga jikin window dinta tanata leqe,har yanzu batakai ga ganin fuskar widad ba,sai giftawarsu data gani kawai.

    Dan kwalinta ta cire ta jefar,ta koma ta zauna jabar saman kujera tana fidda wani hucin azababben kishi dake cinta,tunda zancan nan ya bullo har kawo yau bata sukuni ko qanqani,gaba daya a birkice take jinta,hatta da yaran tace kada a dawo dasu sai gobe ko jibi,sai kawai tasa hannunta a fuska ta fashe da kuka mai cin rai,tana tsananin son abbas tana kuma kishinsa,batasan yadda zata jurewa wannan al’amarin ba,abu mafi dagula mata hankali shine sadakar yalla da akace ya auro,tana sane da yadda suke fidda mace da yaranta daga gidan,ta yaya zata kaucewa wannan?,saita tayi cikin bedrooms dinta gudun kada wani yaji gunjin kukanta,don kukan take da buqatar yi sosai.

    Su biyu ne a dakin ita da nujood,sun nutse abinsu saman gadon da yasha shimfida da lafiyayyen zanin gadon da yake tafiyayye tun daga yemen,sai hira suke abinsu suna dariya,babu abinda ya damesu,ita sam bata wani tuna wai amaryace,nan din gidan aurenta ne,zamansu a haka dasu anty madeena yana mata dadi,hankalinta kwance,bata tuna tafiya zasuyi su barta.

    Dai dai nan anty deena data gama hada kayanta tsaf ta tura qofar dakin ta shigo,saita saki baki kawai tana kallonsu,gadon da aka gama gyarewa aka sa masa zanin gado mafi tsada suka haye tsakiyarsa abinsu?

    “Qaniyarki nujood,sauko” anty deena ta fada tana mata daquwa

    “Gadon amaryar zaki kama ku haye?,ke baki mata fada ba ita batayi miki ba?” Nujood din tana dariya ta sauko,sai widad tayi tsam da ranta tana kallon anty deena,itakam batason ana nuna banbamcin nan sam,yanzu meye laifi don sunyi kwanxiyarsu ita da nujood din a nan

    “Ke kuma bakiji inna laila na kiranki ba tun daxu mijinki ya shigo kizo ku gaisa?” Kanta ta dauke sannan ta tura baki gaba,ita wannan miji da aketa cewa,ita an takurata fa da zancansa

    “Ni banji ba”

    “Bakiji ba amma na gaya miki ana kiranki a falo ko?” Nujood ta fada gudun kada tayi laifi

    “Ya isa naji,jeki falo nujood” anty deena ta fada tana wucewa ciki,ba musu ta miqe ta fice,ita kuma ta isa babbar wardrobe din widad,ta bude tana duba kayan dake ciki.

    Wata lafiyayyar gown ta atamfa ta dauko mata hade da mayafinta ta ajjiye mata,kusan duka kayanta a tsume suke da wani irin turaren kaya na itace mai matuqar qamshi da daukar hankalin duk wanda ya jishi,ta duba inda suka adana mata kayan ado ta fidda mata sarqa dan kunnen da abun hannu masu matuqar kyau,sannan ta dauko mata sabbin undies,saita juyo tana kallonta ganin wata guntuwar pad

    “Kin taba yin period ne?” Gaban widad ne ya fadi,saita daburce lokaci guda,saboda bada kowa take magana irin wannan ba idan ba ummunta ba,ganin ta rude sai anty deenan tayi murmushi

    “Ni kikejin kunya?,to ai kowa ma yana yi,kin taba yi ne?” Kai ta gyada.mata a hankali,sai anty deena din ta sauke ajiyar zuciya,duk sanda ta daga idanu ta kalli widad din sai taji fargaba da tausayinta,babu tabbacin zata yita zama a haka ba tare da komai ya hadasu ba,tasan halin mazan yanzu sarai wajen rashin haquri,duk da cewa yana da mata,amma sometimes masu matan sunfi fitina,saboda sunsan yadda abun yake

    “Sau nawa kikayi?,kuma yaushe ne yinki na qarshe?”

    “Sau biyu inayi,yau sati biyu” kai ta jinjina,saita koma gefenta ta zauna,cikin dabara take mata tambaya kan jinin haila da kuma wankan tsarki,cikin ikon Allah komai ta sani,saboda ba baya bace ita din wajen zuwa islamiyya,sannan ummu ta zauna da ita ta mata bayanin komai. Sosai anty deena taji dadin hakan,saita dubeta

    “Shiga bandaki ki sake wanka kizo ki shirya zaki je ki gaida mijinki,tunda mukazo baku gaisa ba,ko kun gaisa?” Bata kawo komai a ranta ba ta girgiza kai alamun a’ah,saboda dazun tana bacci ya shigo,sai fitarsa ta gani,yanzun kuma tana nan suna hira da nujood

    “Amma anty deena sanda zamu gidan hajiya fa nayi”

    “Wannan daban yake,duk sanda kikasan zaki wajensa ko kinyi wanka ki dinga sakewa kinji?,ki dauko kayan kwalliyar nan da aka kawo miki kiyi kwalliyarki ki saka sababbin kaya,maza tashi qanwata ta kaina” murmushi kawai tayi,ta tashin ta shiga bayi ta hada ruwa kamar yadda ta umarceta,tayi wankanta da kyau.

    Kusan ita ta shiryata,wani irin tururin qamshi na fita a jikinta

    “Muje na rakaki,amma zan dawo,kya taho ke kadai” kai ta gyada mata,bata wani damu ba,kawai tana jin dadin yadda tayi kyau abinta,suka jera da anty deena din tana mata wani karatu cikin hikima widad din na jinta.

    Daga dan nesa kadan da part din nasa ta juya,ita kuma widad din ta wuce tana dosar wajen.

    A darare,cike da baqunta da kuma tsoro,kasancewar a sannan sha daya kusan na dare ta murda handle din falon,saidai a kulle ta jishi,sai ta saka hannu tadanyi knocking,tana rayawa a ranta indai ba’a bude ba tafiyarta zatayi,to amma me zata cewa anty deena?,tunda tayi mata alqawarin zuwa,kuma bata iya qarya ba bare tace taje ta dawo ne.

    Dai dai lokacin da yake zaune qasan carfet,ya bude babbar farar takarda mai girma wadda ke dauke da map na garin kaduna,system dinsa na kunne hakanan akwai wani dan madaidaicin allo dake tsaye a gefe,yayi wasu zane zane da qananun rubuce rubuce da shi kadai yasan ma’anarsu,akwai babban aikin da yake tunkara,wanda yakeson gabatar dashi a sirrance,kamar yadda ya saba,kusan nasarar aikinsa kenan,a duk sanda zai gabatar da aiki na kama masu laifi da sauransu,yakan shirya komai a boye ne,dagashi sai amintattun sa irinsu samuel,sai lokacin gabatarwa yayi sannan.

    Idanunsa daya tsurawa takardar yana karantar map din ya daga yana duban qofa,yana tunanin hafsa ce,saboda ta kirashi taji ya dawo ba jimawa,to amma kuma knocking din ba irin nata bane,sai ya miqe a hankali ya juya allon,ya kuma kifa takardar,ya matsar da butar coffee din da yaketa sha a madadin abinci ya nufi qofar.

    Tuni fuskarta ta soma narkewa da tsoro,ta sake daga hannu cikin saarewa zatayi bugun qarshe ya buda qofar,iska mai sanyi da taushi dake kadawa a gurin ta yayibo dukka qamshin dake jikinta ta jefo zuwa hancinsa,dai dai sanda ya sauke kallonsa ga baby face dinta,fararen idanuwanta tarwai a haske wajen hadi da hasken falon daya sake haske fuskarta.

    Idanu ta zuba masa kamar zata saki kuka,shima idanun ya zuba mata,sai kuma ya janye gefe yana bata hanya,tsaiwa tayi kamar ba zata wuce ba,ta wurga idanunta ta gefensa tana hango cikin falon,tanaskn tava da mutum ko su kadai ne?,hango system dinsa da tayi sai ranta ya bata bashi kadai bane,wannan ya bata sukunin rabawa ta gefansa sosai ta wuce zuwa ciki,tun daga ranar da ummu ke gargadinta da kebewa da duk wani namiji ko kusantar inda suke bata qara bari sun hada inuwa da kowa ba,nan nan kusa kuma data sake tsawatar mata fiye da baya,watanni uku baya sanda ta fara period,ta sake jadda da mata batun.

    Wata ajiyar zuciya ce ta subuce masa,yayi tsaye a wajen kamar mai jiran wani,saidai yana shaqar qamshin ne da yayi masa dirar mikiya,hannunsa ya miqa ya maida qofar ya turata,widad dake zaune a darare a qasa tadan fidda ido waje kadan,kai…..ya zai rufesu su biyu?,saita tsirashi da idanu sanda yake takowa zuwa ciki,tana masa kallon tuhuma.

    Yana shirin zama suka hada idanu,farare sol din idanuwanta suka hadu da nasa manyan idanun,sai yadan lumshe nasa kadan,ya janyo computer dinsa gabansa yana cewa

    “Bakiyi bacci ba?” Kai ta gyada a maimakon ta amsa masa,sannan tace

    “Ina wuni?”

    “Kin yini lafiya?” Ya amsa mata yana daddanna system din ba tare da ya sake dubanta ba

    “Lafiya lau,dama anty deena ce tace nazo na gaisheka,wai bamu hadu ba dazu” yadda tayi maganar cike da quruciya da kuma sakalci shigen na yaran fari ya tilasta masa daga kai ya kalleta,suka sake hada idanu a karo na uku,qaramin murmushi ne ya subuce masa,kallonsa take kanta tsaye kamar mai masa kallon tuhuma,ya karanci me take nufi a cikin zancanta,amma yana sa yaqinin ita din bata fahimci komai ba,ta taho abinta ne gaba gadi

    “Anty deena ta kyauta,kinga ta fiki kirki,sai ita tayi tunanin kizo ki gaida mijinki” ya bata amsa yana sake maida hankalinsa ga system din nasa

    “Uhmmm” ta fada cikin rashin sabo da kuma baqunta.

    Coffee din gabansa ya tura mata yana sake kallonta,saita girgiza kai alamun a’ah,saboda ummu ta hanata karbar abun hannun maza,yana nan kuma daram a kanta bata manta ba,bai sake cewa komai ba sai kawai ya miqa hannunsa,ya jawo allonsa yaci gaba da aikinsa,abun da ya dauki hankalin widad kenan,ta dinga binsa da kallo

    “Dama malamin makaranta ne?,amma kuma nujood tace mata har bindiga ce dashi,to amma wa yake koyawa karatu bayan shi kadai ne a dakin?,inama zai dinga koya mata,tayi missing makaranta da karatu sosai,tanason karatu” ire iren wadan nan tunanukan ta dinga yi,har sai da taga aikinsa yakeyi sosai cike da qawa zuci,ta dan fara motsawa,so take ta koma,amma kuma tasan ba zata iya fita ita kadai ba,saidai ya rakata,amma kuma ta kasa buda baki ta gaya masa.

    Marker din hannunsa ya ajjiye yana fesar da iska daga bakinsa,yayi taku biyu baya a hankali,sannan ya duqa dab da ita,idanu suka sake hadawa,sai ya kauda kai ya soma zuge jakar dake aje a gefanta,wasu tsofaffin takardu ne da yasa samuel ya kawo masa su zai duba wani abu a jiki,yasoma zarosu,sai tsanya tayi tsalle ta biyosu har guda biyu,daya ta fada gefe dayar kuma kai tsaye ta fada jikin widad.

    Gigitaccen ihu data saki ya sanyashi watsar da takardun hannun nasa,kafin ya ankara tayo kansa tana tsalle gami da kiran wayyo Allah,wayyo ummu,taso rudashi amma ya tattara hankalinsa waje guda,saidai duk yadda yakeson dawo da ita nutsuwarta widad batasan yana yi ba,mayafi tuni ta cillar dashi,dankwali ma ya zame,lafiyayyen baqin gashinta dake fitar da qamshi ya tarwatse.

    Suciyarsa tayi wani mugun bugawa sanda ta shige jikinsa tana,sassalkan gashinta ya wanzu a fuskarsa,ihu take da zazzaqar muryarta dake cike da tsoro tana fadin ya cire mata

    “Calm down,ki nutsu,tsanyace fa kawai” ya fada muryarsa na dan rawa kadan,saidai ko daya bata jishi ba,tsoro ya cika kwanyarta a lokacin.

    *AREWABOOKS:HUGUMA*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/27, 10:37 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*
    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)