Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 44

Sponsored Links

Page 44

“Ma sha Allah” shine abinda latifa ta fada bayan ta gama feshe widad da turaruka masu taushin qamshi

“Duba ki gani” ta fada tana matsar da ita gaban madubi,murmushi ne ya subucewa widad bayan ta kalli kanta da kanta ta madubin,tayi kyau irin yadda takeso,yau latifan tana da nutsuwar data mata ado haka

“Gaskiya nayi kyau” ta fada tana dariya hadi da kallon latifa,sai dariya ta kama latifan

“To sai a bani tukuici ai”

“Duk kudin da uncle yake ajjiyewa ki dauka” ta fada tana murmushi,girgiza kai latifa tayi

“A’ah,ba ruwana da kudin miji da mata,tashi kije qila sun fito,sai kun dawo” tana murmushin maganar da latifa ta fada da kuma farincikin yadda tayi kyau a saman fuskarta ta fita zuwa farfajiyar gidan.

Dai dai lokacin da gafsat ke tsaye gaban motar abbas,sanye da baqar doguwar riga mai sulbi da jan mayafi babba data yafawa kanta,fuskarta kamar ko yaushe,babu alamun kwalliya ko d’is,sai maiqo maiqo da takeyi,don tana tsaka da barci mimi ta tasheta akan ta fito inji abbansu zasu wuce shopping.

Sam bata ankara da widad ba sai data kusa gab dasu, qamshin ta dake kadawa cikin iska shine abu na farko daya fara jan hankalinta ta gane akwai baqo a wajen,sosai ta zuba mata idanu,sai taji gabanta ya fadi,wanne irin kyau yarinyar nan ke dashi?,ta tambayi kanta da kanta,take taji gaba daya ta muzanta,duk da cewa dama ba wani ado tayin ba,rigar da ita ta kwanta baccin,ganin bata jima da sanyata ba kuma a motar gida zasu fita su dawo yasa batayi wani sha’awar canzawa ba.

Kafin ta dawo daga duniyar tunanin data lula widad ta iso wajen,sunata kakaci ita dasu mimi suna qyalqyala dariya abinsu

“Ina yini momy” ta fada fararen jerarrun haqoranta suna bayyana,sautin siririyar muryarta ta karade kunnenta,ta kuma dawo da ita hayyacinta

“Lafiya…..lafiya lau” ta fadi tana bude bayan motar da sauri

“Ku shiga ku zauna,mimi ku shiga” ta fada tana duban idanun widad,kama hannunsu nawwaran tayi,ta fara saka mimi sannan itama ta shiga tana ci gaba da jansu da wasa.

Wata ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,har yanxu qirjinta bugawa yakeyi,kyawunta yana damunta,yana kuma son ya zame mata barazana,tafi yarda dari bisa dari kyawunta na daya daga cikin abinda ya fusgi hankalin abbas dinta,ta yaya zata gusar da wannan abu dake shirin zame mata barazana?.

“muje ko” ta tsinci muryarsa dab da ita,sai ta dan bishi da kallo har sai daya kusa shigewa motar,ta taka jiki a mace ta isa gaban motar ta buda daya side din ta shiga.

Wani baqon qamshi ne ya ziyarci hancinsa,ya soma shirin tada motar yana zuqar qamshin,sai daya tada ita sannan ya waiwaya ya kalli hafsat

“Yaushe kika sayi wannan turaren?” Kishi ya kamata,bataso tace ba ita bace ya farga da yarinyar,idan kuma tace itace tayi qarya,duk da haka ta gwammace wa qaryar,sai tadan murmusa

“Eh,cikin bikin nan na siya”

“Yayi dadi sosai” ya sake fada yana dan waiwaya sashen da take,duk da baiji yana busowa daga nan ba,murmushin yaqe ta saki tana basarwa,zuciyarta na bugawa,tana addu’ar komai ya tafi dai dai.

Sun dauki hanyan babban super market din suke siyayya lokaci bayan lokaci,motar shuru,bakajin komai sai muryoyinsu widad mimi da nawwara,a hankali muryarta ke shiga kunnensa,itama ta saje dasu abinta,zuciyarsa cike fal da tunanin ita din fa wai matarsa ce,sai kawai ya gyada kai qaramin murmushi yana qwace masa,saboda shi kansa yasan akwai jagwal,baisan kuma ya zata kasance masa ba.

Murmushin da yaja hankalin hafsa,ta dan juya kadan tana kallonsa,sai shima ya kalleta ya basar yaci gaba da tuqinsa,ita sam irin hirar nan ta debe kewa don kana driving ma bata iyata ba,sai suyi tafiyar awanni amma saidai kowa yaci kansa,imma ya kunna radio imma ya zubawa hanya idanu kwanyarsa ta cika da tunane tunane har su iso inda zasu.

Su suka fara yin gaba zuwa cikin super market din,cewa widad tayi ta tsaya dasu mimi zata dauko mata duk abinda ya dace,bata wani damu ba ta jasu gefe suka zauna,haka tayita zagaye,tana hada duk abinda ranta ya mata a kwandon data dauka,ba wani abun azo a gani take zaba ba,don ba iya zaben tayi ba,majority tare suke shiga da abbas din,shike zabar mata abinda yaga ya dace da ita,takanyi mita a fili da zuci

“Wannan asarar kudine kawai,ni da kudin ka bani da yafi” dubanta kawai yakeyi

“Abinda zaki sakamin din ko kimin amfani dashi na kalla naji dadinne asarar kudi?” Takan basar kawai,itama batasan tana wannan subutar bakin ba a wani lokacin.

Sai data gama zane zabenta sannan suka hadu a wajen biyan kudi,yaga abinda ta diba,takaici ya hanashi cewa komai,ya biya kudin kawai suka fito,baisan yaushe zata koyi siyan abubuwa masu amfani ba,sa’annan kamar ita zata biya kudin,ta saka tsaiwa ta dauki kayan daya dace.

Kai tsaye gidan hajiya ya wuce dasu,tunda hafsat taga titin da yahau tasan can zasuje,sai ta bata rai,amma dai batace komai ba,don batasan bata wasan nata.

Yana tsaiwa a qofar gidan widad tayi zaraf ita dasu mimi suka fice,yadan bisu da kallo kafin ya dawo da dubansa kanta,itama shi take kallo,ranta ya sake baci,sai take ganin kamar widad din yake kalla

“Amma zaka jiramu mu gama ne saimu wuce gida ko?,don inason nadan kwanta,bana jin dadin jikina yau” dubanta yayi kawai,tunda suka fito din batace masa bata jin dadi ba saida sukazo nan,saiya soma zare seat belt dinsa,har ya bude murfin motar sai kuma yace da ita ba tare daya waiwayo ba

“You know what?…..idan zakaso saniya ka sota har qahonta,domin kuwa no matter what ba yadda za’a yi su rabu,mahaifiyata itace duniyata,silar nasarar rayuwata” a birkice ta juyo tana kallonsa,bataso ya fahimci emotion dinta ba,ta buda baki zata jefa masa tambayar rainin wayon ya buda motar ya fice ya barta a ciki.

Katsam hajiya taga shigowarsu,farinciki ya cikata,murmushi ya wadaci fuskarta,tana marabtarsu tana duban widad,tare dason gano wani canji tattare da ita.

Ta sake haske dai ta kuma sake fresh,amma girman da taso taga tadan qara babu shi,alamu dake nuna babu komai kenan daya wanzu tsakaninsu.

Tana tsaka da wannan tunanin yayi sallama da muryarsa mai zurfi ya shigo,idanunsa suka sauka a kanta sanda take zaune gaban hajiyan hankalinta kwance kamar tana gidansu,fuskarta ta wadata da murmushin da zai iya cewa tsahon satin biyun da tayi gidansa bai taba ganinsa ba,ba wani alamun surukuta a tare da ita,yo ina ta gama saninta ma.

“Maraba lale,saiga baqin yamma” hajiya ta fada sanda yake duqawa gabanta daura da widad din yana gaida hajiyan,dai dai sanda hafsa ta sanyo kai cikin falon,sai idanunta suka qara kusancin dake tsakanin widad din da abbas,bugun zuciyarta ya dadu,wani abu ya kama wuyanta,tayi ta maza ta kauda kanta tana zuqar numfashin wahala,sannan ta qaraso falon tana sakin sallama da shaqaqqiyar muryarta.

“Ah,kacemin tare kuka?” Ta fada har cikin ranta tana jin dadin ganinsu gaba daya

“Eh munje sunyi siyayya ne,saboda gobe in sha Allah zamu wuce”

“To yayi kyau,ma sha Allah” hakanan ta duqa itama ta gaidata don ganin idanun abbas din,ba komai a fuska ko zuciyar dattijuwar ta amsa tana tambayar ta yara,bayan lafiya lau data ce bata sake cewa komai ba,taja gefe daya ta zauna ta tsuke bakinta,amma idanunta yana kan komai dake wakana cikin falon.

Yadda taga hajiyan ta maida hankalinta gasu widad din ya qona ran hafsat sosai,ta yita mutsu mutsu cikin kujera cikin bacin rai,tana jin kamar ta tashi ta fice tabar musu falon,sauqinta daya harda yaranta take ja da wasa,don su mimi suna kan cinyarta suna ta harkokinsu,amma ita wannan sam baiyi mata ba,daga qarshe ta buge ta amsa waya ta fice harabar gidan.

Huci ta dinga yi tana fidda iska mai zafi daga bakinta,zuciyarta kamar zata fito,bata iya jurewa ire iren wadan nan abubuwan,akan abbas zuciyarta na gaya mata komai zata iya yi.

Ana idar da sallar magariba suka baro gidan,a hanyar komawa ma tamkar kurame,shi ya riga ya saba da irin wannan zaman,uwa uba kuma dama shi din ba mutum bane mai son magana,yayin da hafsat din keta cin daci,gaba daya zuciyarta babu dadi.

Qaramar leda ta dauka ta debi wasu abubuwa d’ai d’aiku ta bawa widad,bata damu ba don ba damuwarta din bane,tasa hannu biyu ta karba tana godiya,shi kuwa baisan me ya faru ba,an masa total dai ya biya kudi,yana tsammanin kowa ya dauki abinda ransa keso.

***********Kuka take sosai tsahon awa guda cur da sukayi suna tafiya bisa hanyar bauchi zuwa kaduna,duk yadda zai mata tayi shuru yayin amma kamar ma bata san yana magana ba,har ransa ya baci ya shareta taci gaba da kukanta.

Tun sanda motar samuel ta daga da latifa kano,su kuma tasu ta dauki hanyar kaduna ta birkice da kuka,bata taba tsammanin latifan tafiyarta daban da tasu ba.

Sai data kusa rufe awa biyu sannan kukan ya fara ja baya,jikinta ya fara saki,sanyin yammaci gajiya da kukan data sha suka saukar mata ds bacci,a hankali ta langabe kanta gefe tana sauke ajiyar zuciya mai nauyin,alamun taci kuka ta godewa Allah.

Dubansa yakai gareta kadan kafin ya dauke kansa yaci gaba da tuqinsa,cikin ransa yana sauke ajiyar zuciya,wannan aure ne ko rigima sabuwa ta sameshi?,ya tambayi kansa.

Karo na biyu ya sake maida dubansa gareta,sai ya rage speed na motarsa ya gangara gefan titi ya tsaidata,ya miqa hannunsa a hankali ya sauke mata kujerar yadda zata ji dadin kwanciyar,ya koma seat dinsa ya zauna dai dai,sannan ya sake kunna motar suka ci gaba da tafiya.

Yammaci lis suka shiga garin kaduna,kofar wani babban gida ya tsaya,ya danna hon,babu jimawa mai gadin ya iso ya bude gate din,fuskarsa cike fal da murmushi,da alama farincikin ganin dawowar abbas dinne,aiko yana sako hancin motar zuwa parking lot na gidan ya biyo bayan motar da sassarfa yana fadin

“Barka da zuwa oga” qaramin murmushi ya saki,yana hangoshi ta madubin,mutum badai barkwanci,ya tsaida motar dai dai sanda ya qaraso gefan window dinsa.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
[3/6, 3:13 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Back to top button