Category: Sakayyah Complete Hausa Novel

  • Sakayyah 9

    Sakayyah 9

     

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 9_

     

    NA

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE NE ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Kana in saki a Groups da na buɗe ba SAKAYYAH in da zaki karanta abinki salamun ƙaulum min rabbil rahim. Nama lfy fata lfy. Ba ruwan ki da jiran na sata na Allah ya isa*

     

     

    Cikin nitsuwa yake tafiya, tare da taka steps ɗin a hankali, yana  sauƙa ƙasa, yayinda hankalishi baki ɗaya ke bisa system nashi dayake kan hannunsa na dama yana daddanashi da hannun hagunsa, bisa dukkan alamu.

    Abu mai mahimmanci ne yakeyi.

     

    A dai-dai lokacin kuma Khausar ta iso bakin steps ɗin, cikin sauri take tafiya, da alamun tsoron kada malami ya rigata  shiga aji ne.

    Da sauri take tattaka steps ɗin tanayi sama.

    Steps biyu ta taka ana uku, taji juyo da kanta da sauri dan jiyo muryar M Jameel na ce mata.

    “Khausar sai yanzu?”.

    Ba tare da ta tsaya ba, kana bata kuma juyo kanta ba taci gaba da tafiya a haka, hannunta na kan da ƙarfe dake gefen steps ɗin cikin yanayin sakewarta da M Jameel ɗin tace.

    “Wallahi tun ɗazu muka iso fa Malam”.

    Yana mai binta da ido yace.

    “To kuma meya hanaki shiga class?”.

    Still bata janye kanta daga kallonsa ba, kana bata tsaya daga haurawa saman da takeyi ba tace.

    “Raudat ce ta tsaidani a side ɗin su”.

    Da sauri yace.

    “Da me ta tsaida ki?”.

    Ɗan guntun murmushi tayi tare da cewa.

    “Wai ƙwarone ya shiga idonta, shinefa tai ta ihu taƙi sakina dole saida aka cire matashi Allah sai kaga yadda idonta yayi jazir”.

    Kanshi ya sunkuyar yana ɗan murza zaɓen azurfan dake yatsar  yace.

    “Ayya kwaro bai kyauta ba ya shiga idon Gimbiya Raudat”.

    “Ai dai kam fa”.

    Ta faɗina tana mai ƙoƙarin juyo kanta.

    Cikin tsokana yace.

    “Gashi kuwa har Malam Moddibo ya shiga ajinku”.

    Cikin sauri ta kuma juyo kanta da dama bata gama juyashi ba cike da kaɗuwa tace.

    “Da gaske?”.

    Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

    “Tun ɗazuma kuwa”

    Cikin yanayin tsoro ta ɗan zaro manyan udanunta tare da cewa.

    “Na shiga ukuna”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.

    “Ato kiyi sauri ki hau, in kinyi sa’a ya barki ki shiga”.

    Jin haka yasa ta juyo da sauri tare da taka step ɗin gaba kana tayi kwanan haurawa kam steps ɗin da zai sadata da sama.

    Wanda kuma dai-dai lokacin Moddibo ma ya taka step na ƙarshen kwanan.

    Unexpected taji tayi karo da mutu.

    Shi ma Moddibo ba zato ba tsammani yaji kanta ya bugi ƙirjinsa yayinda hannunta ya bugi System ɗin dake hannunsa ya subce ya tafi ƙasa da sauri ya sunkuyo ya cafe system ɗin da kana ya miƙe tsaye,

     

    Ita kuwa Khausar cikin sauri ta ɗago kanta dai dai lokacin kuwa ya ɗago kansa shima ido cikon ido suka kalli juna kamar a fuzge ya furta.

    “Again?”. a lokacin guda kuma, cikin tsananin takaici da zafin rai ya ɗaga tafin hannunsa na hagu ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari mai masifar zafi gami da raɗaɗi.

     

    M Jameel kuwa jin sautin sauƙan marin ne yashi ɗago kansa da sauri.

     

    Ita kuwa Khausar wani irin gigitaccen ihu mai cike da rauni tare raɗaɗi ta saki, tare da dafe kuncinta kana ta rumtse idonta wanda duhu mai tarin yawa ya mamaye mata gani, kana tayi taga-taga ta koma baya zata faɗi, jin ta tafi suuuuu ƙafarta ta sule yasa takuma sakin wani ƙaran tare da buɗe idanunta, sai kuma tayi sauri ta medasu ta rufe sabida ganin wasu irin taurarin masu wutsiya da tartsatsi suna gilmawa ganinta sabida zafin marin da yasa suka mamayewa ganinta.

     

    Gaba ɗaya ta sadakar domin tasan muddin ta faɗo nan to ita da karaya sun zama aminan juna.

     

    M Jameel kuwa kanshi ya riƙe da hannu bibbiyu tare da faɗin.

    “Innalillahi!!”.

    Wanda faɗin hakane ya jawo hankalin Malam isa da yazo wucewa ta gefensa.

    Shima ma Malam isa idonsa ya rumtse da ƙarfi tare da cewa.

    “Yah Salam”.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin takaici yayi sauri miƙa hannunsa da nufin kamo hannunta amman ina tuni tayi nisa.

    Sai yatsunta biyu ya samu ya riƙe da masifan ƙarfi.

    Wanda saida suka bada sautin ƙas-ƙas.

    Cikin zafin nama ya fincikota da ƙarfi wanda hakan yasa ta afka jikinsa.

     

    Ita kuwa Khausar jinta a jikin mutum ne yasa tayi masa wani irin sahihin rugguma mai cike da razani dan gani take kamar dai har yanzu bata tsira ba.

    Kanta ta cusa cikin ƙirjinsa tana mai shaƙan turarensa mai masifar ƙamshi.

    Wanda a take nitsuwarta ta fara dawowa.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin tsoro da wani irin masifeffen abu da yaji ya soƙi tsakiyar kansa har zuwa cikin ƙahon zuciyarsa kana ya harba masa wasu irin masifaffun baƙin al’amuran a cikin jijiyoyin jikinsa da suka sa jikinsa sakin wani irin masifeffen karkarwa da sabauta aniyarsa, ya ware hannunsa tare da rumtse idanunsa da masifan ƙarfi.

     

    M Jameel kuwa ajiyan zuciya mai ƙarfi ya sake tare da jingina bayansa da jikin ƙarfen.

    a hankali ya kuma sakin numfashi tare da kallon yadda Moddibo ya buɗa hannayensa duka biyu kana ita kuma Khausar tana kwance bisa ƙirjinsa tayi lip tana ruggume dashi da masifan ƙarfi.

     

    Wani irin shu’umin dariya mai sauti M Jameel ya sake.

    Wanda hakan yasa Moddibo buɗe idanunsa kana dai-dai lokacin yaji gaba ɗaya tsikar jikinsa na tashi.

     

    Malam isa kuwa sunkuyar da kansa yayi yana murmushi.

     

    M Jameel kuwa dariya yake tare da nuna Modibbo da Khausar ɗin wacce tuni fuskarta tayi jazir shatin yatsun hannunsa sunyi ruɗu-ruɗu a farar fatarta.

    Cikin sauri Moddibo ya ɓalle hannunta daga jikinsa tare da matsawa gefe da sauri.

    Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da watsa mata kallon da yasa hantar cikinta kaɗawa.

    Wanda cikin rawan jiki da rawan murya cike da rauni tace.

    “Ana Aspet ya Mu’allim Allah mi larai ma on! Please! Kayi haƙuri”.

    Ta ƙare mgnar cikin tsoro tare da gwamusa yaruka hudu duk a wuri ɗaya dan neman afuwa.

    Shi kuwa Moddibo juyawa yayi tare da ratsa gefenta ya wuce kana cikin wata fusatacciyar murya mai matuƙar firgitarwa yace.

    “Biyoni!”.

    Cikin ɓarin jiki tace.

    “Toh”.

    Sannan ta miƙe tabi bayansa.

     

    M Jameel dake riƙe da System ɗin yana juyawa yayi saurin bin bayansa da faɗin.

    “Alhamdulillah kamar babu abinda ya samu System ɗin”.

    Shi dai Moddibo ko juyawa baiyi ba bare kuma ya tankawa M Jameel.

     

    Malam Isa kuwa dake ƙasa ido ya zirawa Khausar dake sauƙwa dafe kuncinta da kunne ya da tun da tasha marin ya bada sautin kauwww har yanzu ƙaran takeji, kana ga idanunta da suka kaɗa sukayi jawur asanda ta saƙƙo yace.

    Fattanah sam bakya yin abinda ya dace a rayuwarki”.

     

    Cikin zafin raɗaɗin marin da fuskarta keyi ta ɗago Idanunta da suke sake girma da ja ta kalli Malam Isa sai kuma tace.

    “Wallahi bansa niba ne na juya ina kallon Malam Jameel ne dake yimin magana ne mukayi karo”.

    Bata jira jin abinda zai ce ba tabi bayan M Jameel dake biye da Moddibo.

     

    Cak Khausar ta tsaya daga bakin Office ɗin, karo na farko kenan arayuwarta da zata fara shiga Office ɗinsa, duk da cewa da basu da office da yawa, amma yanzu gyaran da akayi an haɗa Malamai biyu akan Office  ɗaya Office din ba wasu masu girma bane, haka zalika ba ƙanana bane, sannan duk kusan ajere suke.

    Ahankali Khausar ta maida Idanunta bakin office ɗin da akasa wasu irin flowes masu launi mai kyau da ɗaukar hankali aka jera suna fitar da wani irin sanyayyan ƙamshi.

    Cikin Office ɗin kuwa Madaidaitan deks ne da kujeru ɗaya na fuskantar gabar ɗaya na fuskantar yamma daga gaban ko wanne kuma akwai kujeru guda biyu daga kan deks ɗin daga gefen damar sa akwai wani Cubet kamar kanta dake ɗauke da tarin littattafai na addini da kuma na boko cikin wajen kamar dai Library haka wurin yake.

    Daga gefen hagunsa kuma flowes ne masu  kyau da tsari daga jikin bangon kuma Room hitane ne maƙale abango yana fitar da ɗumi mai daɗi a jiki,

    Sai kuma labulayen window da suka kasance farare sol Sanyayyan iska na kaɗawa daga bangon kudu dake kallon yamma TV ne maƙale abango daga tsakiya kuwa wani irin dakekken turkey carpet mai yawan gashi fari sai ratsin maroon kaɗan. sosai Office ɗin yayi kyau.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin nutsuwa da kuma zafin da zuciyarsa keyi masa ya zauna akan kujeran dake gabar yana fuskantar yamma yayin da M Jameel ya zauna akan kujeran dake yamma yana fuskantar gabar kana da sunan ko wannensu ajiki kujerarsa.

     

    Ita kuwa khausar cikin tsananin tsoro ta ƙarasa shiga office ɗin tare da tsugunnawa agaban table ɗin da Moddibo ke zaune.

    Ta riƙe kunnenta Muryanta Araunane wanda ke nuni da tsantsar tsoro da tashin hankali tace.

    “Malam kayi haƙuri bansan kana tahowa ba”.

    Shi kuwa Moddibo ko kallonta baiyi ba saboda yanda zuciyarsa ke tsananin ta farfasa ya tabbata idan yace zai daketa to zai iya karyata ko kuma ya sumar da ita hakan yasa ya janyo kujeran dake kusa dashi ya ɗaura ƙafafunsa akai kana ya lumshe idanunsa tare dasa hannu ya janyo Hiramin dake kansa ya rufe saman Idanunsa.

     

    Cikin tsantsar nutsuwa da kuma sanyayyan sautin muryarsa mai zaƙi ya fara rara Ƙira’a acikin suratul Rahman yasan hakan shine kaɗai zai sanyaya masa ransa da zuciyarsa yasan muddin yace zai daketa ayanzu zai iya sumar da ita ko kuma karyata.

    Saboda abubuwan da yarinyar ke masa yayi yawa.

    Sabida tsabar raini da rashin kunya fa har gidansu ta bisa tayi masa rashin kunya sannan ta jima sa ciwo ayatsun ƙafansa wanda ya ɗauki tsawon kwanaki yana fama da ciwo.

    Kana  yaje ƙauyen su nan ma bata barshi ba saida ta bisa tayi masa rashin kunya ta nemi jefa shi acikin ruwa da wannan masifeffen sanyin garin nasu,

    kana amakaranta ma bata barsa ba shin tsaranta ta mayar dashi kome?.

     

    Ita kuwa khausar cikin Sanyayyar Muryanta me cike da tsoro tace.

    “Ayyah malam na tuba kayi haƙuri wallahi bansani bane”.

    Ƙin tanka mata Moddibo yayi ya cigaba da rera karatunsa cikin zazzaƙan muryansa.

    Shi kuwa M Jameel Gyaran murya yayi hakan yasa Khausar tayi saurin Kallonsa da manyan Idanunta da suka kaɗa sukayi jawur.

    Da ido yanuna mata Moddibo alamar ta cigaba da basa haƙuri.

    Kai ta gyaɗa sannan ta cigaba da cewa.

    “Ayyah Malam na roƙeka kayi haƙuri bazan sake ba”.

     

    Acan sama ajinsu Khausar kuwa wani irin tsarin gini ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali wasu irin windon Glass ne tsala-tsala masu tsayi da kyan tsari sannan ga flowes masu fitar da sanyayyan ƙamshi kana ga Room hita  guda biyu gaba da baya daga farkon shiga class ɗin kuwa wani irin Black Board ne mai tsari irin wanda ake amfani dasu a manyan makarantu, kana ga wasu irin kujeru na zaman ɗalibai masu taushi da kyau, agaban ko wani kujeran ɗalibi akwai sunan sa ajiki, hakan yasa duk ɗalibar data shiga baza tasha wahala neman wajen zamanta ba wanda kuma manna sunan ake bisa alamu in an tashi kawai ɓarewa za’ayi a saka sunayen sabbin waɗanda zasu shigo ajin, kujeran Khausar shine na farko acikin jerin kujerun dake gaba da sunanta manne kamar haka _Khausar Usman Abubukar Lelewal._

    Samira Sani ce ta ɗan juya Idanunta kan kujerar dake gefenta.

    Wanda sunan Khausar dake manne kujerar afarkon.

     

    Wani irin ya mutsa fuska tayi tamkar wacce taga wani abin ƙi cikin taɓe baki da tsanar mamallakiyar sunan tace.

    “Ikon Allah wannan shine suna mai buƙatar hadda sunaye huɗu duk masu tsawo!”.

    Ta Ida maganar tare da bankawa kujeran harara tamkar Khausar ɗin na kai, kana ta zauna daga baya inda sunan ta ke kai.

     

    Asma’u dake gefe azaune tace.

    “Ha’a sunane de ai ba wani abu ba kuma duk sunayene masu inganci da Kekkyawar nasaba naga dai sunanta sunane na ɗiya ga Annabi  Muhammad (S.A.W) sannan sunan mahaifinta sune na sahabin Manzon Allah (S.A.W) haka zalika sunan kakanta sune na sahabin Manzon Allah (S.A.W).

    Lelewal kuwa naga suna ne da kowa ke fatansa”.

     

    Abeeda Sule ne ta watsa wa Asma’u harara tare da faɗin.

    “Ke kuma wayasa bakin ki?”.

    Taɓe baki Asma’u tayi kana tace.

    “Ai gaskiyane daga kallon sunan baiwar Allah zata fara ƙanan magana”.

    Ɗaya daga cikinsu manyan matan ajin nasu ne wacce bata fiye magana Hajia Khadija tace.

    “Da wannan hatsaniyar da kukeyi tunda Moddibo ya fita tun ɗazu akan zaije ya dawo bai dawo ba aigwara kuje ku duba ko lafiya mai ya tsaida shi aji ba kowa kuma shine muke da First period?”.

     

    Cikin zumuɗi Samira Sani tace.

    “Gaskiya ne kam bari naje na kirasa”.

    ta ida maganar tare da ficewa ta sauƙa ƙasa.

    Cikin yauƙi ta nufi Office

     

    Tana isa idanunta suka sauƙa akan Khausar dake riƙe da kunnenta, ga kuma Idanunta da suka sauya,

    yayin da shi kuwa Moddibo idanunsa ke lumshe yana rera karatun Alkur’ani cikin Sanyayyar sautin muryansa daya haɗu da ɗumin room hita ga ƙamshin daddaɗan tularensa.

    Numfashi mai nauyi ta fesar  tare da tsirawa yalwataccen sajensa daya ƙawata kyawun fuskarsa idanu sai kuma ta maida kallonta kan zara-zaran yatsun hannunsa dake kan table yana ɗan bubbugasu ahankali cike da shauƙi tace.

    “Wowww”.Faɗar hakan da tayi shi ya janyo hankalin M Jameel yayi saurin juyawa ganinta tsaye acikin Office din yasa shi faɗin.

    “Lafiya?”.

     

    Sai asannan ta dawo cikin nutsuwarta still Idanunta na kan Moddibo tace.

    “Malam Barka da safiya”.

     

    “Barka dai”.

     

    Still idanunta na akan Moddibo tace.

    “Malam dama munzo kiran Malam Moddibo ne, shine muke dashi tun ɗazu ya sauƙa, akan cewa zai zo ya ɗauki wani abu sannan kuma bai koma ba”.

     

    Da ido M Jameel ya nuna mata Moddibo da har zuwa lokacin idanunsa ke lumshe yana karatu sai dai ya rage sautin muryansa ya koma fita asaman laɓɓansa.

     

    Shi kuwa Moddibo jin Muryanta yasa ya janye Hiramin dake fuskarsa kana ya buɗe idanunsa da har zuwa yanzu akwai alamun ɓacin rai acikinsu, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kansa gefe.

    Ita kuwa Samira gefe ta koma ta tsaya.

    Khausar kuwa lumshe Idanunta da suka kaɗa sukayi jawur tayi sai kuma ta buɗe su still Hannunta nakan kunnenta tace.

    “Ayyah Malam kayi haƙuri”.

    Shi kuwa Moddibo juyawa yayi tare da kallon M Jameel yace.

    “J ka da keta”.

    Da sauri M Jameel ya juya tare da nuna kansa da babban yatsa kana yace.

    “Ni!?”.

     

    Cike da tsuke fuska Moddibo ya gyaɗa masa kai kana yace.

    “Eh ka daketa!”.

    Zare Ido M Jameel yayi tare da cewa

    “Meyesa?”.

    A kufule Moddibo yace.

    “J kadaketa nace!”.

    Kallon mamaki M Jameel yake masa tare da cewa.

    “Akan me zan daketa?”.

    Cike da ɓacin rai Moddibo yace.

    “Idan fa ka bari nace ni zan daketa zan sumar da ita fa!, zan karyata fa!!”.

    Cikin tsananin fusata ya ida maganar.

     

    Ita kuwa Khausar tuni jikinta ya hau rawa Allah ya sani bata son duka, sannan mari ɗaya daya mata ya mugun gigita mata ƙwaƙwalwa wanda har zuwa yanzu take jin raɗaɗin sa asaman fuskarta.

     

    Fuskarsa babu walwala yace.

    “Idan har nace zan daketa zan sumar da ita”.

    Ita kuwa Khausar jin azaban mari ɗaya daya mata, aranta tace Ashe Allah ya rufa min asiri da yasa duk lokacin da nayiwa Moddibo laifi baya duka na yake sa Malam Adam display master ke dukana na tabbata dashi yake dukana kullum da tuni ya kasheni!.

     

    Cikin hanzari ta juya tare da kallon M Jameel ta miƙa masa hannu Muryanta na rawa tace.

    “Malam ka dakeni!”.

    Girgiza kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.

    “Ni dai kam bazan iya ba bazan iya dukanta ba Moddibo, ka dubi fuskarta fa mari ɗaya da ka mata kalli fuskarta fa ai ya wadatar wani hukunci ya rage bayan wannan?”.

    Ya kare mgnar a hankali

    Moddibo kuwa cikin fushi yace.

    “Kada keta in kuma baza ka daketa ba zan daketa da kaina fa”.

    Cikin sauri M Jameel ya fara girgiza kai  yayi cikin wata Sanyayyar murya me cike da zallar jin ƙai tare da tarin tausayi gami da rauni yace.

    “La! La!! La!!! A.J  bazan iya ba! Wlh Bazan iyaba ba wannan ba hurumina bane hurumin taɓa ta awajenka yake bani da karsashi ko ƙwarin gwiwar da zan iya taɓa ta!”.

    Ya ida maganar cikin wani irin salo na daban, kana dai-dai lokacin  Amina tazo Office ɗin domin kiran M Jameel ya shiga ajinsu wani irin sarawa kanta yayi jin yanda yake cewa bazai iya ba.

    Da sauri ta dafe ƙofar office ɗin jin jiri na ɗibarta kadde ace dokon soyayyarsa za tayi abanza, kadde Khausar yake so yanda ya ƙarashe maganar na nuni tamkar itace rayuwar sa.

     

    Da sauri Moddibo ya juya ya kalli M Jameel jin yanda yayi magana da kuma yanda ya lanƙwasa harshensa abun ya bashi mamaki.

    Azuciye Moddibo yace.

    “In daketa kenan?”.

     

    Langwaɓar da kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.

    “Kayi haƙuri ina mai bada haƙuri amada dinta ka nemi wani punishment ɗin ka bata amadadin wannan, amma nikam bazan iya dukan taba sannan kaima banaso ka daketa!”.

    Baki ɗayan su kallon Mamaki suka bi M Jameel dashi ganin yanda yake lanƙwasar da murya tare da nemawa Khausar ya fiya, ita kuwa Amina wasu hawaye ne masu zafin gaske ne na tsananin kishi da baƙin ciki, suka zubo mata  saurin ta sanya hannu ta share.

    Kwantar da Murya M Jameel ya kuma sakeyi ya cigaba da cewa.

    “Kallifa A.J mari ɗayan nan da kamata kalli fuskarta fa ka daketa awaje mafi daraja”.

     

    Moddibo kuwa  lumshe idanunsa yayi kana ya buɗesu akan M Jameel tare da cewa.

    “J kadaketa ni idan nace zan daketa bazai mata daɗi bafa”.

    Sake Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana yace.

    “Kayi haƙuri Moddibo ni bazan iya dukanta ba!”.

     

    Ita kuwa Samari Sani na tsaye agefe ta harɗe hannayenta aƙirji yayin da ta zubawa Moddibo ƙananun Idanunta ko ƙyaftawa ba tayi.

    Ita kuwa Amina Idanun ta nakan M Jameel da idanunsa ke kan Khausar zuciyarta nayi mata zafi.

     

    Khausar kuwa kallon M Jameel ta sakeyi akaro na barkatai tace.

    “Malam Jameel ni dai ka dakeni”.

    Kai ya girgiza mata tare da faɗin.

    “Bazan iya dukan ki ba Khausar!”.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin tsananin ɓacin rai ya juya ya kalleta a kufule yace.

    “Toh inda keta da kaina!?”.

    Girgiza kai M Jameel yayi sai kuma yace.

    “A’a asassauta mana dan Allah”.

    Ƙwafa Moddibo yayi da faɗin.

    “Shikenan kije ki kaɗe ɗan kwali sau ashirin”.

     

    Cike da tsoro ta zaro ido domin kaɗe ɗan kwallon da yace  yana nufin ta cire ɗan kwalinta tasa abokitin ruwa ta matse kana ta kaɗe har sai ya bushe,

    sannan ta sake sakawa cikin ruwa ta matse kana tayi ta kadewa har sai ya bushe.

    Tofa jin haka ne yasa a tsorace ta zare Ido Jin hukuncin daya yanke mata ba zata manta lokacin daya sata kaɗewa sau goma ba awannan lokacin ma saida tayi sati biyu gaɓɓanta na ciwo ko abu zata ɗauka da ƙyar take iyawa.

     

    Cikin yanayin neman alfarma M Jameel ya sake langwaɓar da kai kana yace.

    “Dan Allah ka sassauta mata karage mata”.

    Jin Muryan M Jameel yasa ita ma ta kalli Moddibo cikin wata raunatacciyar murya tace.

    “Dan girman Allah Malam kayi haƙuri karage min”.

     

    Shi kuwa Moddibo wani kallo ya watsa mata cikin haɗe girar sama dana ƙasa yace.

    “Kada ki sake haɗa ni da girman Allah da kinsan darajar girman Allah da zaki mutunta Malama ki,

    kije kiyi shabiyar kinci darajar girman Allah.

    idan kika sake cemin dan Allah in rage miki kuwa nida ke bibbiyu!”.

    Gyaɗa kai tayi kana tace.

    “Toh shikenan”.

    Shi kuwa M Jameel kallon Moddibo yayi cikin jujjuya  ido  yace.

    “Ina neman alfarma abarta tashiga aji tayi karatu idan antashi Break sai tayi”.

     

    Shi kuwa Moddibo Ɓata fuska yayi yace.

    “Bana son ganinta a aji Idan naganta a aji zan kakkaryata in wurgar ta window”.

    Ita kuwa Samira Sani cikin lanƙawasa harshe tace.

    “Malam Moddibo mu tafi”.

    Sake tamke fuska yayi tare da juyawa ya watsa mata wani bayyane  harara sai kuma ya nuna mata ƙofa alamar ta ɓace masa da gani.

     

    Sum sum ta  juya da sauri  ta fice.

    Da harara yabi bayanta Aransa yace.

    Shegiyar yarinya mai kama da Mayya,

    sai shegen kallon jaraba tasani gaba zakiyi dan rashin kunya.

     

    Samira Sani kuwa tana shiga ajinsu ta lumshe Idanunta tare da kallon gefen ko wannen kujera dake ɗauke da flowes ta saki murmushi mai cike da jin daɗi,

    tasan wannan aikin Moddibo ne domin kaf cikin Malaman shike son flowers.

    Hajia Ruƙayya ce ta dubi Samira data shigo kana tace.

    “Ni kam ya banga Khausar ta shigo ba har yanzu kuma ɗazu na hangota kafin na haura”.

    Juye Ido Samira tayi tare da faɗin.

    “Tana can tayiwa Moddibo rashin kunya yana cin Ubanta, shegiyar yarinya fitsararriya ‘yar marasa tarbiyya!”.

     

    Asma’u ce ta juya ta kalleta rai a haɗe tace.

    “Haba Samira meyesa zaki zagi iyayenta ai bai kamata ki zagi iyayenta komai yaya iyaye nada daraja”.

    Harara Samira ta wurga was Asma’u kana ta buɗe baki da niyyar magana ta fasa sakamakon shigowar Moddibo.

     

    Ganin shigowar Moddibo yasa ta tsuke bakinta tare da neman waje ta zauna cike.

    Cike da ladabi suka gaishesa cikin harshen larabci tare da faɗin.

    ”صبحل خير ىاعثتذ“

    Ya Amsa da.

    “صبحل نور كىفل قراء“.

    Suka amsa da.

    ”الحمد الله“

    Kasancewar Tafseer zasuyi dake yanzu lokacin Islamiyya ne yasa yace.

    “Kuyi muraja”.

    Cikin bawa ko wanne harafi hukuncinsa suka shiga karanta suratul Muhammad har zuwa karshe.

    Bayan sun gama kawo haddan ya jinjina kai tare da faɗin.

    “Sai gobe Insha Allah zamu fara tafsirin sa”.

     

    Aɓangaren M Jameel kuwa tare suka jera da Amina suka nufi ajinsu yayin da azuciyar Amina yayi baƙiƙƙirin data tuna yanda M Jameel ke karyar da murya akan Khausar har suka isa ajin tunanin da take aranta kenan yanayin yanda tsarin ajinsu Khausar yake haka ko wanne aji yake cike da ƙwarewa M Jameel ya shiga yi musu ƙarin Mi’atu Hadith daga na Arba’in bayan sun karanta masa.

    Ko wanne aji da Malami aciki suna darasi.

     

    Ita kuwa Khausar ita kaɗai ce tsaye aharabar Makarantar cikin gajiyawa ta ɗaga boket ɗin ruwan ta koma rana wai ko zata samu yafi bushewa da wuri, tsoma ɗan kwalin tayi aciki kana ta matse sannan ta fara kaɗewa.

    Nannauyan ajiyar zuciya ta saki tun akaɗewa na uku taji hannunta ya sage aranta tace.

    “Insha Allah Ina komawa gida zan nemi ɗankwali mai shara-shara mara nauyi wanda kodan irin rana ta yau ta faru zaimin sauƙi.

    Cike da gajiya ta miƙe  ta riƙe ƙugunta da hannu ɗaya ta lumshe idanunta sosai ta gaji.

     

    Shi kuwa Moddibo daga can sama acikin ajinsu Khausar yake kallonta tana kaɗe-kaɗen ganin ta tsaye ta riƙe ƙugu gaban ƙirjinta duk ya jiƙe da fuskanta, ganin ta tsayanne yasa ya buɗe glass ɗin window dake saitin ta tare da ziro hannunsa ya ƙyasta yatsunsa da ƙarfi wanda hakab yaja hankalin Khausar da saurin ta ɗaga kanta.

    Ganin abinda yayi yasa da sauri ta cigaba da kaɗewa tana mai rintse Idanunta.

     

    Har Moddibo ya gama teaching ɗinsa ya fita Khausar nakan punishment Koda ya saƙƙo ya ganta Harara ya watsa mata kana a kufule yace.

    “Ba zaki shiga ajiba yau har sai kin gama abinda nasaki”.

    Fuska ta Shagwaɓe  tare da langwaɓar da kai tace.

    “Ayyah Malam dan Allah kayafemin duk ɗan Adam ajizine!”.

    Harara ya watsa mata ya wuce batare daya bata amsa ba,

    bayansa tabi da kallo tana tura ƙaramin bakinta, to har wani malami ya sake shiga yayi darasi Khausar bata gama ba sai sha biyu dai-dai lokacin tashin matan Aure sannan Yara da ‘Yan mata suyi suci abinci su koma ajin boko.

     

    Hajiya Ruƙayya ce da Aunty Khadija ne suka  fito tare da ƙarasawa kusa da Khausar dai-dai lokacin da Khausar ke faɗin.

    “Wayyo hannuna”.

    Ta faɗa tana matsa yatsunta dake raɗaɗi.

     

    Dafata Hajiya Ruƙayya tayi kana tace.

    “Ayyah sannu Khausar kece bakyaji me kika yiwa Moddibo!?”.

    Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da marairaice murya tace.

    “Allah babu abinda na masa kawai ina tahowa ne mukayi karo dashi har System ɗinsa ya faɗi kuma ma naji malam Jameel yace System ɗin beyi komai ba amma sai da ya sani wannan kaɗe-kaɗen sabida in baici zalina ba baya jin daɗi rayuwarsa ta duniya”.

    Ta ida maganar da faɗin.

    “Affan zo”,tare da miƙa masa hannu.

    Murmushi Aunty Khadija tana mai jujjuya kai.

    Ita kuwa Hajia  Rukayya

    Miƙa mata yaron dake ta faman ƙyalƙyala mata Dariya Aunty Ruƙayya tayi Sai kuma tayi saurin janye hannunta tana cewa.

    “Wayyo Aunty Ruƙayya hannu na ya gaji yaukam bazan iya riƙe sa ba”.

    Ta ƙare mgnar tana ƙara matsowa  kusa da Aunty Ruƙayya kan kumatunsa ta sumbata tana faɗin.

    “Affan gaye”.

    Shi kuwa yaron sai dariya yake ƙyalƙyala mata tare da miƙa mata hannu alamar yana so ta ɗauke sa dan sosai yaron ya saba da ita saboda Aunty Ruƙayya na zumunci da Mommy Khausar sannan Khausar na shiga lokaci zuwa lokaci.

     

    Samira Sani da Abeeda Sule ne suka ƙaraso wajen Kallon Abeeda Sule Samira tayi da faɗin.

    “Ai Moddibo shike maganin tantirai marasa mutunci ’ya’yan Fitsararru awannan makarantar yana min dai-dai!”.

     

    Sake hannun Affan Khausar tayi ta juya ta kalli Samira da kyau tace.

    “Waye ‘Yar marasa mutuncin?

    Akwai ‘Yar marasa mutunci daya wucike ne ‘Yar magulmata Munafuka kawai! Inbanda munafurci da gulma da biye-biyen bokaye Me kuka iya!?”.

    Afusace tace.

    “Ke Khausar zanci Ubanki fa!”.

    Wara ido Khausar tayi kana tace.

    “Ubana kuma, uhmm saide Kici naki uban domin ni kam nawa Ubana tuni Ubangiji ya daɗe da yimasa sutura sai dai kije kici naki ‘Yar matsiyata?”.

    Ta ida mgnar cikin tsiwa,.

     

    Abeeda Sule ne tace.

    “Ke akwai ma ƴar matsiyata irinki, kina tsammanin bamu san cewa munsan ke Agwola bace acikin gidan sarki da kike nunawa kamar gidan ku ne?”.

     

    Dariya Khausar tayi kana tace.

    “Dan Allah rufe mana baki ‘Yar Alhaji sule baka layya kibari tukunna in Babanki ya fara layya saiki faɗa wa mutane Magana?”.

     

    Zare ido Abeeda tayi tare da hayayya ƙowa tace.

    “ ‘Yar iska ni zaki cewa Ubana baya layya”.

    Taɓe baki Khausar tayi tare da faɗin.

    “Ke rufe min baki ai bani na faɗa ba Inkiyarsa ce hakan, ko ba sunan sa bane? Alhaji Sule baka layya!! ko kuma ni nasa masa ko kuma dan tsoronki sai inki kiransa da sunan da aka sa mishi”.

     

    Hajiya Ruƙayya ce tace.

    “Khausar rabu dasu”.

    Gyaɗa kai tayi.

    Ita kuwa Samira cikin takaici tace.

    “ ‘Yar banza kawai agola”.

    Dariyar rainin hankalin Khausar tayi sannan tace.

    “Eh koma menene inma ni Agolace inada daraja sannan ina da tushe dama ni ban ɓoyewa cewa Agola bace Ni saboda idan kinga sunan su Amina da sunana kin san ba yar gidan bane,

    Ni sunana Khausar Usman Abubukar Lelewal sukuwa kinga ba haka sunan su yake ba daga nan ma mutum yasan Ni Agola ce ko dama anɓoye miki ne?”.

     

    Hannunta Hajiya Ruƙayya taja suka bar wajen zuwa gefe tace.

    “Khausar kifita har ƙansu  kiyi abinda ke gabanki kinga duk yau baki samu karatu ba”.

    Kai Khausar ta gyaɗa mata sannan tayi mata Sallama ta tafi.

    Asma’u ce ta ƙaraso wajen Idanunta akan Samira da Abeeda dake zagin Khausar cikin yanayin sanyin muryanta tace.

    “Khausar kifita sabgar wa’annan yaran dan Allah keda su ba ɗaya bane kada ki ringa biye musu muta nen da ƙwaƙwalensu basa ja, kinga fa yanzu da ya kamata suna SS 3 nefa daƙiƙancinsa kesa kullum basa gaba sunan a jaɓe har muka isosu”.

    Yamutse fuska Khausar tayi kana tana matsa yatsun hannunta tace.

    “Kinsan Allah Asma’u Indai basu fita sabgata ba zan basu mamaki zan nuna musu Khausar Usman Abubakar Lelewal ba kanwar lasa bace”.

     

    Hannunta Asma’u ta riƙe tace.

    “Ni dai dan Allah ki fita sangarsu ai ko kare bai haushi shi kaɗai tukunna wai me kika yiwa Moddibo ya saki Punishment?”.

     

    Rau-rau da ido Khausar tayi sai kuma ta ya mutse fuska tare da jan tsaki kana tace.

    “Mutum yana nan kamar wani sabon boss sam fuskarsa babu fara’a yana nan sai baƙin mugunta.

    Kuma wallahi Wuta bal-bal ban yafe masa ba, ai bani kaɗai nayi kuskuren ba shima yayi yana tafiya kamar makaho, kuma yaseen saƙo na baki ki faɗa masa ehe”.

    Ta ida mgnar cike da tsiwa da murguɗa baki

    Asma’u kuwa  dariyar  dake cinta ta danne kana tace.

    “Aikuwa gashi nan abayanki yana ma jinki ba sai na faɗa masa ba”.

    Arazane Khausar ta saki ihu  tare da rintse Idanunta cikin tsananin tsoro da rawan jiki ta juya tana mai faɗin.

    “Dan Allah! Dan Allah!! Dan Allah!!! kayi haƙuri Allah bada kai nake ba kuskuren harshene ni da kainama nakeyi”,

    Ta ida maganar tana buɗe Idanunta jin be tanka taba ga mamakinta bata gansa ba.

    Kallon Asma’u tayi wacce zuwa lokacin ta saki dariyar ta tace.

    “Fattanah sarkin tsiwa dama gwada ki nayi inga da gaske saƙon kika bani”.

     

    Harara Khausar ta zabga wa Asma’u amma batace Komai ba.

    Murmushi Asma’u tayi tare da jan hannunta zuwa resting chair dake cikin harabar makarantar suka zauna Asma’u ta fito da kula da ɗauke da pride rice da yaji kayan hadi da namar kaza suka ci.

    Bayan sun gama cin wannan Khausar ta buɗe bata kukan.

    Peper checking ne guzurin zabbin data dawo dasu.

    Sunaci suna ɗan hirarsu dai har suka gama,  suka mike tare da zagaya classes din makarantar suna kallon yanda aka tsara makarantar kamar ba shiba.

    12:10  suka koma aji.

    Bayan komawar su Malam Isa dake ɗaukar su Economist ya shiga ya koyar musu sosai Khausar da Asma’u ke fahimtar karatun 1:15 dai-dai suka fita sallah.

     

    Bayan sun fita Al’wala sukaje wajen da aka tanada dan alwala sukayi gefen maza da ban na mata da ban Amma masallacin guda daya ne saidai anraba daga tsakiya anyi katanga mata zasu shiga ta gefen dama maza tagefen hagu.

    Bayan sun idar da Sallah ƙarfe 1:30 suka koma aji wasu Malaman suka sake shiga.

    Sosai Malaman suka dage wajen koyar dasu domin anƙara musu Salarie sannan ankawo sabbin Malamai hakan yasa babu period din dake wucewa ba tare da anshiga ba  5:00 dai-dai suka tashi motar su Khausar tazo ta ɗauke su.

     

    Washe gari.

    Ma haka suka gudanar da karatunsu kamar na jiya.

    Acikin satin karatu suke gadan gadan babu kama ƙafar yaro saboda suna son dai-dai-ta komai na lokacin daya wuce ahutu koda wasa Khausar bata sake yin ganganci wani abu ya haɗa ta da Moddibo ba bare tayi masa laifi da zaran ya shiga ajinsu zata tattara duk kan nutsuwarta akansa tana sauraron abinda yake koyar musu kuma sosai take fahimta yayin da ita kuma Samira Sani zata tsaya aikin Kallonsa aduk sanda ya shiga musu shikuwa Moddibo duk yana lura da yanayin ko wannensu.

     

    Yau Alhamis ya kasance babu makaranta suna hutu.

    Khausar ce zaune a falon Mommy ta tana duba Mi’atu Hadith,Mommy dake Bedroom ta ƙwala mata kira Amsawa tayi tare da ajiye Hadith ta fita.

    Bakinta ɗauke da Sallama tashiga Bedroom din Kallonta Mommy tayi tace.

    “Khausar ɗibi wannan kayan ki kaiwa Hajiya Bunayya kala ɗaya nasiya mana”.

    Kallon mamaki Khausar ta yiwa Mommy anma wannan basabon abu bane ko yaushe Mommy na zaune zuciya ɗaya da ita tana kyautata mata, amma ita Hajiya Bunayya ba da zuciya ɗaya take zaune dasu ba.

    Gyaran Murya Mommy tayi tace.

    “Khausar tunanin me kike?”

    Murmushi Khausar tayi tare da ɗiban kayan tace.

    “Toh”,Mommy sannan ta fice.

     

    Bakinta ɗauke da Sallama ta shiga falon Hajiya Bunayya kana ta nemi waje ta zauna aɗaya daga cikin kujerun dake falon tace.

    “Ummah gashi Mommy na ta siya musu iri daya”.

    Washe baki Hajiya Bunayya tayi tare da kallon turamen Zannuwa da tsadaddun less ɗin tace.

    “Aaaa lalle kam Khausar Nagode Allah yayiwa ƙanwata al’barka muje inyi mata godiya”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa dai-dai lokacin Hajiya Lami mahaifiyar Samira Sani tayi sallama suka shigo atare.

    Kallon Khausar Hajiya tayi tace.

    “Khausar jeki nayi baƙi kice mata Nagode zan shigo anjima”.

     

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da ficewa yayin da Samira ta bita da mugun kallo.

    Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi kana ta mika mata hannu suka tafa Dariyar ƙeta Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Kalli Sokuwarki wai kaya ta saya mana iri ɗaya”.

     

    Dariya Hajiya Lami ta fashe dashi tare da cewa

    “Aaaa Ikon Allah sokuwa ta ƙarshen zamani kuwa wato hadda siya muku anko”.

    Tsaki Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Bar ‘yar banza mai kama da ‘ya‘yan mayu tazo ta liƙewa mijina”.

     

    Hajiya Lami tace.

    “Aikam wa’annan mutanen sai Allah aike kika sake kika basu dama, kika bar mijinki ya ƙara aure ni yanzu Baban Samira ya isa yace zai ƙara aure ne, sannan bayan kin bari yayi auren ma kika barta tahaifi santalelen yaro me jikin girma bayan shi hadda ‘yan biyu da kawunansu kamar ‘Ya‘yan ruwa ga shegen gashi kamar ‘ya‘yan Aljanu”.

     

    Ƙwafa Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Ai wallahi nayi sake amma daga ‘yan tagwayen babu ita ba sake haihuwa ina lura da ita kwannan kamar cikine da ita to bazan bari ta haife sa ba zanje wajen boka Kar’uzu azubar dama duk cikin ta uku kafin ’yan biyu ni nake sawa azubar  shegiya ai bazan barta ba kenan yanzu ma inada  niyya zanje wajenki jibi muje wajen Malami”.

     

    Gyara zama Hajiya Lami tayi tare  da faɗin.

    “Aini ma abinda ya kawoni kenan Hajiya Bunayya in sanar miki”.

    Kallonta Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Toh Meye faru?”.

    Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe tace.

    “Akwai wani Malami ne amakarantar su Samira take sonshi”.

    Cikin don jin ƙarshen zancen Hajiya Bunayya tace.

    “Toh wani Malami?”.

     

    “Wai shi malam Moddibo tana masifar sonshi shi kuma yana nan kamar Waliyi ko ta kanta bayayi”.

     

    “Ikon Allah”.

    Cewar Hajia Bunayya

     

    “Toh fa shine nake son zamu kai sunansa wajen Malami ya jawo mana hankalinsa da tunaninsa”.

    Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Eh hakan ma yayi shine dai-dai, gwara ajashi ya dawo yana binta, nima dama abinda zai kaini kenan harda batun Amina itama wani Malamin su take so”.

     

    Cikin mamaki Hajia Kamu tace.

    “Ita kuma wani Malamin take so?”.

    Da sauri Hajiya Bunayya tace.

    “Eh wani Malami take so wai shi M Jameel shi kuma baki ɗaya hankalinsa nakan wannan ‘yar matsiyatan!”.

     

    Cikin zato ido Hajiya Lami tace.

    “Wa kenan?”.

     

    “Khausar mana”.

     

    Hajiya Lami kam baki ta saki  tare da riƙe haɓa kana ta saki salati tace.

    “Ikon Allah Uwarta ta hanaki rawan gaban hantsi, sannan itama Khausar tun yanzu zata hana ‘yarki rawan gaban hantsi, ta hana ta samun abinda take so, to ko lallai kinada aiki ja a gabanki

    Yakamata muyi aggawan zuwa mu ɗauki mataki dan bata isa ba amma shi Jameel din ɗan gidan waye!?”.

     

    Murmushi Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Ɗan gidan Alh Bashir Mafindi.

    Ko da yake yanzu anfi saninshi da  Maidala ne”.

    Kai Hajiya Lami ta jinjina tace.

    “Kai-kai lallai kice babban kamu ne ina zamu yarda muyi wasa dashi waye bai san Alhaji Bashir Maidala ba”

    .

    “Ai dai kam  ɗan masu kuɗi ina zamu bari muyi wasa da wannan damar tamu.

    Ai wlh koda zan tafi tsirara bazan taɓa bari ya auri Khausar ba, sannan Insha Allah zanyi kokarin ganin anja mana hankalinsa yaji ya tsaneta ya riƙa cin Ubanta kamar yanda Moddibo keyi mata amakaranta shine abinda yafi mana a’ala da kwanciyar hankali”.

     

    Acan waje kuwa Khausar ce tsaye aƙarshen Barandar Hajiya Bunayya cikin tarin al’ajabi da mamaki ta jinjina kanta bayan ta gama sauraron abinda suka faɗa…..!

     

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki Ka mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nane🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 26

    Sakayyah 26

     

    SAKAYAH

     

    26

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

     

    Isrnejg. Acan ɓangaren gidan Lamiɗo kuwa Ramadan ya fito daga Bedroom da gudu kai tsaye Bedroom din Mommy ya nufa afalo suka ci karo da Hajiya Bunayya wani irin kallo tabisa dashi dai-dai lokacin da Khausar ta fito sanye cikin riga da skirt na less ɗinkin ya zauna ɗas ajikinta kana ta sanya Blue Black hijabi mai Facemaks jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin turaren Oud Ma’aruf fuskarta ɗauke da simple Make-up.

    Cak ta tsaya tare da kallon Hajiya Bunayya data tsirawa Ramadan idanu ganin tsayuwar Khausar yasa Hajiya Bunayya sakin murmushi tare da cewa.

    “Ikon Allah Ramadan ƙafa tayi sauki sosai”.

    Sai kuma ta juya tana cewa.

    “Ki cewa Aysha ankawo kayan tazo ta gani ta zaɓa mana”.

    Girgiza kai Khausar tayi tare da kallon Ramadan dake cewa.

    “Addah Khausi ƙafana tayi sauƙi”.

    Murmushi tayi tare da shafa kansa kana tace.

    “Alhamdulillah Ramadan amma ka daina wannan gudun har yanzu ƙafanka baiyi ƙwari ba”.

    Kai ya gyaɗa mata kana yabi bayanta zuwa Bedroom ɗin Mommy bakinsu ɗauke da sallama.

     

    Ƙara sawa Ramadan yayi tare da faɗawa jikin Mommy kana yace.

    “Mommy ƙafana yayi sauƙi badan Addah Khausi tace kar inyi gudu ba da nayi kin gani”.

    Murmushi Mommy tayi tare da shafa kansa kana tace.

    “Masha Allah mun godewa Allah, ka riƙa bi ahankali insha Allah zaiyi sauki”.

    Khausar na murmushi tace.

    “Mommy zanje gidan su Asma’u”.

    Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

    “Toh Allah ya kiyaye ki gaishe su amma kada ki daɗe Allah ya tsare”.

    Kai ta gyaɗa kana ta fice.

     

    Tare da Sallama ta ɗan tura ƙofar Falon.

    Tana shiga Idanunta ya sauka akan M Jameel dake zaune kan 2 sitter murmushi ta sakar masa kana tace.

    “Laa Yah Jameel”.

    Murmushin ya maidamata tare da faɗin.

    “A’a Lelewal kece yau agidanmu?”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Eh mana Yah Jameel na kawowa Ummi ziyara ne kuma nayi kewar Asmeey”.

    Wara ido yayi tare da cewa.

    “Iyeee Lelewal wato wariya zaki nuna min ni bakiya kewata ba? Rabona dake tun randa kuka karkare makaranta fa”.

    Rufe fuska tayi tare da cewa.

    “Kai Yah Jameel nayi mana, duk makarantar ma nayi missing ɗinta da kowa nata”.

    Murmushi yayi kana cikin yanayin fara’arsa yace.

    “Yanzu naji bayani amman harda Modibbo kinyi kewarsa?”.

    Da sauri ta tura baki tare da cewa.

    “Kewar masu sona nayi banda maƙiyana”.

    Dariya mai sauti yayi tare da cewa.

    “Maƙiyi kuma, kai a’a kam Lelewal”.

    Ita dai Khausar juyawa tayi ta kalli Ummi

    kana tace.

    “Ummi ina yini?”.

    Cike da kulawa Ummi tace.

    “Lafiya lau ya Ramadan da ƙafa?”.

    Gyara zama Khausar tayi kana tace.

    “Yaji sauƙi Ummi yanzu yana takawa ko ina”.

    Atare suka ce Masha Allah Ubangiji Allah ya ƙara sauƙi”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Ameen”.

    Kana suka ci-gaba da hira wanda duk mafi yawan hiran nasiyya M Jameel yake musu kan sukula da rayuwar duniya kana suka sance masu riƙe al’ƙawari tare da kare mutuncin su.

    Ganin rana ya fara yasa Asma’u ta kalli Khausar tare da cewa.

    “Khausy mushiga kichen muyi girki”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa ta cire hijabinta tabi bayan Asma’u abakin ƙofar ta tsaya tare da juyawa falon kana cike da kulawa tace.

    “Yah Jameel mai za’a dafa maka?”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Duk abinda kika dafa min Khausar ina so zanci”.

     

    Jinjina kai tayi tare da sakar masa da murmushi kana tace.

    “Toh shikenan Yah Jameel Insha Allah zanyi maka abinda zaka so da izinin Ubangiji”.

    Khausar na shiga kichen suka fara aikin cikin nutsuwa da ƙwarewa Dambun shinkafa da yaji Vegetables suka Atake kichen ɗin ya gauraye da ƙamshi Warmers me kyau ta ɗauka ta zuba masa kana ta ɗauki Bowl ta haɗa masa Fruit Salat mai sanyi sannan ta ɗaura Ababban faranti ta fito.

     

    Kallon M Jameel dake hira da Ummi tayi kana tace.

    “Yah Jameel gashi na kawo maka”.

    Wara ido yayi kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Wai Lelewal duka Ni kaɗai?”.

    Kai ta gyaɗa masa kana tace.

    “Eh aina Malamina ne yanzu ma zan gasa maka nama gashin tukunya”.

    Jinjina kai yayi tare da cewa.

    “Lallai Khausisi naji daɗina na dafa tudu biyu ga Malami sannan kuma yaya saura cikon tudun dafawa na uku”.

    Murmushi tayi tare da zama gefensa kana tace.

    “in sha Allah in akwai na huɗuma duk zaka taka Yaya Jameel”.

    Yana sa Fruit Salat abakinsa ya lumshe Idanunsa kana ya kalli Khausar tare da cewa.

    “Uhm Yummmy na daɗe bansha Fruit salat mai daɗi irin wannan ba Lelewal da alama dai na musamman ne”.

    Asma’u data fito daga kichen ta wara ido kana tace.

    “Kai Yah Jameel har nawa?”.

    Kai ya jinjina mata tare da sanya dariya kana yace.

    “Iyee sosai ma Asmeey nifa yau komai jinsa nake na daban, girkinma tun tuni yake cika min hanci da ƙamshi”.

    Kallon yanda yake dariya Khausar tayi wanda har ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana idanunsa alumshe haskensa ya sake bayyana kana sajensa sunyi luf-luf suna sheƙi.

     

    Ajiyar zuciya ta sauƙe still Fuskarta ɗauke da murmushi tace.

    “Yah Jameel kaima yau na da banne kyawunka ya sake nunkuwa tamkar Balarabe”.

    Bashir da Asma’u kuwa  haɗa baki sukayi wajen cewa.

    “Wallahi kuwa Muma duk akwanakin nan haka muke kallonsa”.

    Wara ido yayi still Yana Shan Fruit Salat ɗin yace.

    “Uhm ko dai dan na kusa Aure ne yasa kuke kallon kyawuna”.

    Saurin Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.

    “Sai kace gobene auren.

    Murmushi yayi tare da faɗin.

    “Uyumm Ummina”.

     

    Sai kuma ya maida Kallonsa kan Khausar tare da cewa.

    “Lelewal zaman gida ya kusa ƙarewa ko?”.

    Kai ta jinjina tare da cewa.

    “Eh Yah Jameel Insha Allah result ɗin mu na fitowa za’a samomin Admission”.

    Jinjina kai yayi tare da cewa.

    “Masha Allah, haka muke fata, ku dai kiyaye ku tsare mutuncinku a duk inda kuka riski kanku”.

     

    “Insha Allah Yah Jameel na maka alƙawari zan kasance fiye da hakan ma”.

     

    Kallon Asma’u Ummi tayi tare da cewa.

    “Kawo mana abincin muci”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa tare da miƙewa ta zuba musu ababban faranti Khausar kuwa drinks ta kwaso musu.

    Kana suka zauna kallon Ummi M Jameel yayi tare da langwaɓar da kai kana yace.

    “Ummi ya aka cire ni adangi gaskiya nima ajuye muci tare”.

    Murmushi Khausar tayi tare da cewa.

    “Toh Yah Jameel bari na zuba mana”.

    Ta faɗa tare da juye nasa akan faranti kana suka zauna tare da sanya farantin Atsakiyarsu Ummi da Khausar na facin juna Asma’u da M Jameel na facing juna haka suka gama cin abincin cike da nishaɗi.

     

    Suna gamawa ana kiran sallar Azahar M Jameel ya Miƙe tare da shiga toilet ya ɗaura alawala kana ya nufi masallaci Asma’u da Khausar kuwa wajen suka gyara tare da kwashe kwanukan suka kai kichen kana suka wuce Bedroom ɗin Asma’u suka ɗaura alwala tare da gabatar da sallah bayan sun idar suka fito zuwa falo.

     

    Bayan an isar da salla.

    M Jameel yana shigowa ya kalli Ummi dake zaune kan 2sitter kana yace.

    “Toh Ummi zan tafi ina jin jikina aɗaɗɗaure tun jiya da daddare fa rabona da wanka ji nake kamar nayi wata banyi wanka ba”.

    Cikin sauri Khausar ta miƙe tare da cewa.

    “Yawwa Yah Jameel dan Allah ka sauƙeni agida Mommy tace kar in daɗe”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh Lelewal muje mana”.

    Kai ta gyaɗa tare da riƙe hannun Asma’u kana suka fita.

     

    Ummi kuwa haka nan ta tsinci kanta da ɗago kai ta zuba masa Ido batare da tace komai ba.

    Ahankali ya kalli Ummi ganin shi take kallo yace.

    “Ya dai Ummina?”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da girgiza masa kai kana tace.

    “Bakomai ba zaka bari sai anjima ba?”

    Girgiza kai yayi tare da cewa.

    “Um-um Ummi ina so in tafi sauri nake”.

    Cikin sanyin murya tace.

    “Toh saurin me kake?”.

    Langwaɓar da kai yayi kana yace.

    “Toh Ummi banyi wanka bafa ba kuji na fara tsami ba?”.

    Wara ido Asma’u tayi tare da sanya dariya kana tace.

    “Ƙamshi dai kake Yah Jameel”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Gwara dai Inje inyi wanka”.

     

    Dai-dai lokacin wayarsa ta hau ruri yana cirowa yaga Moddibo murmushi yayi tare da kallon Ummi kana yace.

    “Kinga fa Moddibo na kira na yanzu zaice ko Breakfast baiyi ba yana jirana, haka yake dake cin abinci bai damesa ba idan bana nan sai yace yana jirana, yaita takura min da kira idan kuma ina nan yaƙi ci”.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “Toh yanzu tafiya zaka yi?”.

    Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

    “Eh Ummi”.

    Cikin sanyin murya tace.

    “Toh ka kira Baban nawa yazo nan kuci abincin”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Ummi zan tafi Insha Allah da yamma zan zo musha hiran mu”.

    Sai kuma ya matsa kusa da ita tare da ranƙwafawa kanta ya kai bakinsa dai-dai kunnenta kana yace.

    “Ummi sai anjima da daddare zanzo insha Allah musha hiran mu sannan in faɗa miki matar da zan Aura da kuma matar da na zaɓawa A.J na”.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “Toh shikenan Babana Allah ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya Ubangiji Allah yama SAKAYYAH da mafificin Aljanna”.

    Murmushi yayi tare da durƙusawa agabanta cike da jin daɗin Addu’ar ta yace.

    “Ameen Ummina Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

    Ummi kuwa hannu ta sanya acikin sumar kansa tana shafawa kana tace.

    “Allah ya rufa maka asiri duniya da lahira Allah yasa kagama da duniya lafiya Allah yasa Aljanna ce makomarka Allah ya tsareka da dukkan sharrin abinƙi Ubangiji ya raba ka da sharrin mai sharri”.

    Tafin hannunta ya riƙe kana yace.

    “Allah ya amsa addu’o’in ki Ummina, shiyasa nake da yaƙinin cewa duk abinda ya sameni, na tabbata ƙaddarar ce da  Ubangiji ya rubuta minne amma addu’ar ki ba zai taɓa bari wani mummunan abu yasame niba Nagode sai dai in daga Allah ne”.

    Bashir daya shigo kuwa Ido ya zuba musu yana kallon yanda Ummi ke sanya masa albarka tare da adduo’i shi kuma yana Amsawa da Ameen.

    Da sauri ya isa ya durƙusa gefen yayan nashi tare da cewa.

    “Ayi addu’o’in damu”.

    Murmushin Ummi tayi tare da shafa kansu,l.

    Asma’u da Khausar kuwa tuni suka fita suna jira ganin shiru bai fito bane yasa Khausar leƙawa Falon kana tace.

    “Yah Jameel baza mutafi ba. Mommyna fa tace kada in wuce Azahar”.

    Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

    “Gani nan zuwa Lelewal”.

    Kai Khausar ta gyaɗa kana suka cigaba da hira da Asma’u.

    M Jameel kuwa fita yayi har ya isa baranda sai kuma yayi baya tare da leƙawa falon kana yace.

    “Ummi yau ba rakiya ne ko dan bamu zo da Babanki bane?”.

    Ummi kuwata

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da Kallonsa kana tace.

    “Na’am Jamilu”.

    Langwaɓar da kai yayi kana yace.

    “Ummi yau dai dan ban zo da Babanki ba ba rakiya”.

    Murmushi tayi tare da faɗin.

    “Toh muje in rakaka Babana”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh Nagode”.

    Sannan suka fita afalon kai tsaye jikin motarsa ta nufa ta buɗe masa.

    Murmushi yayi tare da shiga kana ya maida kallonsa kan Bashir tare da cewa.

    “Bashir yau dai na ƙwace maka fadar ka”.

    Murmushi Bashir yayi tare da kallon M Jameel kana yace.

    “Ba komai Yah Jameel na bar maka lokacin kane ai”.

     

    Ahankali Ummi ta tura Murfin motar tare da rufewa.

    M Jameel kuwa Ido ya zubawa Ummi ta ɗan tsakanin glass din Motar batare daya jaba Itama Ummi Idanu ta zuba masa tare da juya masa hannun alamar ya dai?.

    Sauƙe glass ɗin motar yayi tare da sanya babban yatsan sa acikin bakinsa yana ɗan ciza farcen a hankali.

    Cikin tsare sa da ido tace.

    “Ya dai?”.

    Sauke glass ɗin motar yayi tare da zuba mata Ido.

    Girgiza mata kai yayi still baice komai ba.

    Matsawa jikin Glass din tayi kana tace.

    “A’a wai meye haka?”.

    Ƙasa cewa komai yayi still Idanunsa na kanta.

    Sunkuyawa jikin Glass din Motar tayi kana tace.

    “Ya dai?”.

    Ahankali ya lumshe idanunsa tare da jan dogon numfashi kana ya fesar cikin rawan murya yace.

    “Ban sani ba Ummi”.

    Da mamaki tace.

    “Baka sani ba kuma?”.

    Kai ya gyaɗa mata still ya tsansa na bakinsa.

    Cike da kulawa tace.

    “Toh me kake so?”.

    Juyawa yayi ya kalli faɗin ilahirin gidan nasu kana ya kalli Asma’u da Bashir  sai kuma ya dawo da Kallonsa kan Ummi kana yace.

    “Ummi ku nake so”.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “Kai ko Jameelu ba’a rabaka da zolaya”.

    Ta faɗa tare da kallonsa tsakiyar idanunsa ga mmkinta sai taga still baiyi murmushi ba kamar yanda ya saba ba.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “To ko dai ka manta wayar kane?”.

    Hannu ya sanya tare da shafa aljihun gaban rigarsa still yatsansa na cikin bakinsa yana gyatsawa a hankali kana yace.

    “Um-um Ummi ban manta wayata ba gashi a aljihuna”.

    Cikin yanayin damuwa da jinƙai irin na mahaifa tace.

    “Toh Meye ne?”.

    Kanshi ya ɗaura a kan hannunta dake kan glass ɗin motar, tare da lumshe idanunsa kana ya janyo tafin hannunta ɗaya ya kife akan goshinsa tare da buɗe lumsassun idanunsa da suke sheƙi, shiru yayi kamar mai nazari.

    Sai ya kuma lumshe idanu.

    Khausar dake gefe tayi dariya tare da cewa.

    “Kai Yah Jameel bisa dukkam alamu dai yau kam Shagwaɓa kake ji dashi?”.

    Ahankali ya buɗe idanunsa dake lumshe batare daya juya ba kana cikin raunin murya yace.

    “Uhm Lelewal baza ki gane ba”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Yah Jameel zan gane mana gashi yau Shagwaɓa kake yiwa Ummi”.

    Ummi kuwa sun kuyowa kansa tayi sai taga ya kuma lumshe idanunsa yayi shiru Kamar mai tunani hannunta dake goshinsa ta ɗago tare da cewa.

    “Menene? Shin wai meke damunka? Me kake son faɗa min mana?”.

    Cikin sanyin murya yace.

    “Ummi”.

    Sai kuma yayi shiru.

     

    Ahankali ya buɗe Murfin motar ya fito tare da jan hannunta suka nufi cikin falon kana ya kalli su Asma’u tare da cewa.

    “Ku jirani”.

    Da kallo Khausar, Asma’u da kuma Bashir suka bisu, amma babu wanda yace komai kowa da tunanin da yake Aransa.

    Suna shiga falon ya zaunar da Ummi kan 1sitter kana ya durƙusa agabanta cikin raunin murya yace.

    “Ummi ba abinda kikeso in miki?”.

    Cikin raunin murya tace.

    “Meyesa kake hakane, shin wai idan ina da ɓuƙatar abu, bani da kaina nake kiran ka in faɗa maka ba Jameelu?”.

    Araunane ya kalleta tare da cewa.

    “Ummi ki tuna dai! ba abinda kike so in miki kada damar ta wuceni fa Ummi? Ki tuna dai”.

    Ya ƙare mgnar yana murza tafin hannunsa kan rumfa sawunta

    Saurin Kallonsa tayi kana tace.

    “Kamar ya damar ya wuce ka Jameelu?

    Na faɗa maka bana ɓuƙatar komai”.

    Cikin raunin murya yace.

    “Toh bani wayar ki Ummi”.

    Ahankali ta miƙa masa wayarta dake hannun kujeran karɓa yayi tare da shiga text messages ɗin ta, ya duba Alart gani yayi duka-dudu  kudin dake ciki baifi dubu ɗari biyu da hamsin da biyar ba.

    Kallonta yayi kana yace.

    “Ummi kina da buƙatar kuɗi”.

     

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Ga kuɗi kuma mai zanyi dasu?.

    Me zanyi da kuɗi komai fa kai kakeyi min Jamilu”.

    Girgiza kai yayi tare da zaro wayarsa acikin al’jihunsa Atake yayi charking balance tare da cewa.

    “Nima bani ba kuɗi da yawa acikin account ɗina”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

    “Ta yaya kuɗi zai zauna acikin account ɗin ka Jamilu nasan ka haka Allah yayi ka kana da yawan kyauta zaka bawa wannan ka bawa wancan”.

     

    Girgiza kai yayi tare da cewa.

    “Allah yabamu mu bayar Ummi”.

    Jinjina kai tayi tare da cewa.

    “Ameen”.

    Atake ya Mata transfer million ɗaya zuwa account dinta.

    Kana yace Ummi ga Million ɗaya na miki transfer”.

     

    Cikin sauri ta kallesa kana tace.

    “Me zanyi dasu Jameelu?”.

    Hannunta ya damƙe acikin nasa kana yace.

    “Ummi duk abinda kike so kiyi dashi, tunda kin ƙi ki faɗa min abinda kike buƙata ina ji kamar akwai nauyin da ban gama sauƙewa ba gani nake kamar kinada wata buƙatar”.

    Ya ida maganar muryarsa na rawa sosai sai kuma ya kama gwiwoyinta da hannu kana ya kife kansa akan cinyarta.

     

    Cikin sanyayyar murya mai cike da rauni yace.

    “Ummi”.

    Ummi kuwa cikin sanyin murya tace.

    “Na’am”.

    Still muryarsa na rawa yace.

    “Idan akwai abinda na miki kiya femin”.

    Cikin sauri ta kallesa kana tace.

    “Wai Jameelu Meyesa kake yin haka ne?.

    Wai meyesa?”.

    Girgiza kai yayi tare da faɗin.

    “Ai ɗa baya rasa laifin da yake yiwa Mahaifiyar sa, ko babu abinda na miki a yanzu, ai kin ɗauki nauyin cikina tsawon wata tara da kwanaki tara, kin sha wahalar naƙuda kafin ki haifeni, kinsha jidalin rainona, nayi miki kashi nayi miki fitsari na miki tumɓuɗi da amai, na hanaki bacci  a lokacin da kowa ke bacci

    Ummi kiya femin domin wannan ma shine babban  abin neman yafiya ga iyaye, idan kuna akwai abinda na miki yayin kuruciya da girma da kuma yayin rarrafe wata ƙil har cizonki nayi yayin shayarwa dan Allah da Manzonsa duk ki yafe min, kiyi min aikin gafara”.

    Ya ƙare mgnar cikin wani irin raunataccen muryar mai rawa.

    Kai ta girgiza kana cikin raunin murya tace.

    “Ba kayi min komai ba kuma na yafe maka duniya da lahira na yafe maka komai na raunin cewa ko da haihu da rainonka bayan haihuwa, duk na yafe maka shi tun kafin yau”.

    Wasu irin tagwayen numfarfashi masu nauyi ya rinƙa sauƙe tare da cewa.

    “Alhmadulillah Ummina ngd matuƙa.”

    Ita kuwa Ummu cikin sarƙewan murya taci ga da cewa..

    “Meyesa kake min irin wa’annan abubuwan bana sofa”.

     

    Dariya yayi kana yace.

    “Toh Ummi dan ɗa yanemi yafiyar Uwarsa sai yazama laifi?”.

    Girgiza kai tayi tare da Kallonsa kana tace.

    “Toh ni babu abinda ka min ka tashi mu tafi Allah yayi ma sakayya da mafifiyaciyar Al’jannah mai cike da ƙololuwa  ni’ima tashi muje in rakaka”.

    Ta faɗa tare da miƙewa kana ta riƙe hannunsa kamar yaro haka suka fito kana ta buɗe masa murfin motar tace.

    “Toh kashiga Allah yayi maka al’barka”.

    Kai ya gyaɗa tare da shiga.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “Toh kaje Ubangiji Allah ya maka albarka Allah ya tsareka Allah ya rufa maka asiri Ubangiji ya maka sakayya da mafi kyawun abin sakamako Allah yatsare min kai Allah Ubangiji ya Albarkanci rayuwar ka Allah ya azurtaka da arziki mai albarka da yara na gari”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum Ummina”.

    Ya ida maganar tare da zuba mata Ido.

    Asma’u kuwa ita ma shiru tayi tare da zuba masa Idanu tana kallon yanda yake kallon Ummi.

     

    Khausar kuwa Kallonsa tayi kana tace.

    “Yah Jameel gaskiya zan tafi idan kai ba zaka tafi ba”.

    Kallonta yayi kana yace.

    “Toh mutafi Lelewal baki sani bane duk saurin da kikeyi nafi ki sauri fa bakisan inda zanje bane fa shiyasa”.

    Tura baki tayi kana tace.

    “Yah Jameel Ina zaka je”.

    Murmushi yayi tare da kallon Asma’u da Bashir kana yace.

    “Ku kula da kanku sannan ku riƙe kada ku manta da alƙawarin da kuka min ga amanar Ummi na kafin na dawo”.

    Murmushi sukayi tare da gyaɗa masa kai kana suka ce.

    “Insha Allah Yah Jameel Allah yatsare sai kadawo.

    Murmushi kawai yayi tare da jan motar suka fita saida Ummi taga motar ya ɓacewa kallonta kafin ta sauƙe ajiyar zuciya ta koma cikin gida Asma’u da Bashir na biye da ita.

     

    Acan mota kuwa Anutse M Jameel ke Driving kana ahankali ya juya ya kalli Khausar data tsirawa tiri idanu kana ya sauƙe numfashi daga zuciyarsa ya fara tunanin Maganar da zai mats kana cikin sanyin murya yace.

    “Lelewal”.

    Juyawa tayi ta kallesa tare da cewa.

    “Na’am Yah Jameel”.

    A hankali ya furzar da iska kana a hankali cikin tattausan lafazin yace.

    “Inne mi alfarma awajen ki mana?”.

    Anutse ta kallesa kana tace.

    “Toh Malam Jameel Allah yabani ikon yin duk al’farman daka ke so awajena”.

    Cikin jin daɗi ya buɗe idanunsa dake lumshe ya kalleta kana yace.

    “Kinyi alƙawarin duk abinda nake nemi al’farmar zaki yimin?”.

    Kai ta gyaɗa masa kana tana wasa da yatsun hannunta tace.

    “Na sani malam Jameel baza ka sani yin haramtaccen abu ba sannan baza ka sani yin abinda yafi ƙarfi naba kuma kafi ƙarfin neman alfarma ko wani abu awajena ina hana ka saidai ka bani Umarni Yah Jameel faɗa min me kake so inyi maka? Kai tsaye bani umarnin kawai ni kuwa in cika maka umarninka da sauri”.

    Jinjina kansa yayi still Yana driving Cike da nutsuwa kana yace.

    “Alhamdulillah naji daɗin Lelewal Thanks”.

    sai kuma yayi gyaran murya tare da juyowa ya kalleta, itama shi take kallo ganin yadda fuskarsa ta koma alamun daga can cikin ƙahon zuciyarsa abinda zai faɗa ɗin zai fito cikin yanayin neman al’farma cikin iyawa da ƙwarewa ya juya harshe zuwa sahihin Larabci mai cike da Kekkyawan lugga ya fara mgn da larabci yayinda itama Khausar ta  juya harshen zuwa larabcin.

     

    Aƙalla sunyi magana daya ɗauki tsawon minti goma sha biyar, kafin suka koma magana da yaren Hausa Inda M Jameel ya ƙare maganar da cewa.

    “Nagode Khausar Nagode Nagode Lelewal Ubangiji Allah ya miki albarka”.

     

    Khausar kuwa cikin wata raunan’niyar murya tayi ƙasa da kanta yayin da ruwan hawaye suka cika kwarmin Idanunta kana tace.

    “Ameen”.

    Ahankali M Jameel ya cigaba da Driving kana Yana cigaba da yi mata nasiyya akan rayuwa.

    Ahankali Khausar da Idanunta ke kan madubin side ɗin da take ta juya tare da kallon M Jameel kana tace.

    “Yah Jameel kamar wannan motar binmu fa take”.

    Kai ya gyaɗa mata kana cikin sanyin murya yace.

    “Eh nima na lura da haka Khausar tun ɗazu ma”.

    Jinjina kai tayi tare da cewa.

    “Toh Yah Jameel ka rage gudu mugani mana muga kodai mudin suke bi”.

    Kai ya gyaɗa tare da rage gudun still sai motar dake bayansu itama ta rage gudun.

    Ahankali M Jameel ya cigaba da Driving yayin da still motar ke bin bayansu.

    Suna isa wani babban super market M Jameel ya kalli Khausar da hankalinta ke kan motar kana yace.

    “Bari mushiga cikin Super Market ɗin nan mugani idan ma mu suke bi ai zasu tsaya”.

    Suna Parking suka fita tare da shiga cikin Super Market din M Jameel  ya ɗiba mata turaruka tare da Choculate da sweet da kuma Biscuits yana tsinta yana faɗa mata wasu kalamai da larabci, duk da dai ba ji nake amman yadda fuskarta ke nuna kalaman masu nauyi ne yake sanarmata.

    Kana kamar kimanin minti talatin da shigarsu suka fito ga mamakinsu sai suka ga wannan motar ta faka agefen nasu kai tsaye suka shiga motar M Jameel ya mata key ita ma wannan motar sai akamata key aka tayar sunbi ta bayan motar idanun Khausar ya sauƙa akan  Motar tana kallon fuskar mutanen ciki, duk da nesa ne ta gane cewa mutanen ne da  ta gani Arugar Jauro Yaya sannan itace abakin makarantar su kana taga still Motar ta cigaba da binsu.

     

    Lokaci ɗaya tsoro da damuwa ya shigeta cikin yanayin tsoro ta kalli M Jameel tare da cewa.

    “Yah Jameel Motar nan mu take bi”.

    Jinjina kai yayi tare da faɗin.

    “Nima naga alama amma watakila arashi ake samu sunyi”.

    Kai ta gyaɗa still zuciyarta na cigaba da bugawa da masifar ƙarfi suna cikin tafiya motar ta ɓacewa kallon su.

     

    Anutse M Jameel ya Kalli Khausar kana yace.

    “Kin gani kawai arashi ake samu may be suma zasu shiga Super Market ne sannan hanyar mu ɗaya shiyasa haka”.

    Murmushin yaƙe Khausar tayi kana tace.

    “Haka ne kam”.

    Aranta kuwa cewa tayi to kodai mutanen sun gane ta ganeta ne shiyasa suke bibiyar rayuwarta wata ƙil ita suke son su kasheta kana ta raya dole idan ta koma dole ta faɗawa Mommy.

     

    Anutse M Jameel ya juya tare da kallon Khausar data zurfafa cikin tunani kana yace.

    “Lelewal muje mu gidan su Moddibo ki gaishe da Kakarmu”.

    Da sauri ta dafe ƙirjinta tare da cewa.

    “Gidansu Moddibo kuma?”.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “Babu abinda zai miki Khausar”.

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Nikam ina tsoro Yah Jameel. Abu kaɗan ya fara masifa ko agidan mu ma faɗa yake min bare kuma naje gidansu”.

    Cikin sanyin murya M Jameel yace.

    “Nayi miki alƙawari ko hararanki ba zai yiba, Insha Allah bare kuma ya miki faɗa zai miki maraba, ki yarda dani”.

    Kai ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.

    “Toh shikenan”.

     

    Suna isa gidan yayi Parking a coumpund din farkon kana ya fita cike da nutsuwa yake tafiya tana biye dashi a baya, a kuma dai-dai lokacin da Moddibo ke kokarin fitowa daga falonsa,  cikin sassarfa ya nufeshi.

    Shi kuwa Modibbo wani irin sassayan numfashi ya fesar tare da tsaida idanunsa kan J ɗinsa.

    Shi kuwa M Jameel murmushi mai cike da farin ciki yayi tare ƙara sawa wurin Modibbo rungume shi yayi da ƙarfi.

    Wanda haka yasa shima Modibbo yayi masa wani irin amintaccen

    runguma mai cike da son juna a tare suka sauƙe ajiyan zuciya cikin sanyin sauti  Modibbo yace.

    “J nayi fushi da kai”.

    Cikin sanyin Muryan M Jameel yace.

    “Kada kayi fushi dani A.J idan kayi fushi da J ɗin ka dawa zaka sulhunta”.

    Cikin sanyin Murya Moddibo yace.

    “J ka tafi gidan Ummi ka barmu mu kadai agidan, sam gidan nan ba daɗi idan baka nan shiru baki ɗaya gidan bai mana daɗi ba”.

     

    Murmushi M Jameel yayi kana a hankali yace.

    “A.J Rungumeka da nayi alfarma nake nema awajenka.

    Saboda muyi maganar sirri akwai baƙuwar da nazo da ita dan Allah dan darajar Annabi A.J ko hararanta kada kayi”.

    Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da cewa.

    “Ayyah A.J ka tayani cika al’ƙawarin dana ɗauka dan Allah kada ka tozar tamu ka tuna ba haushe yace baƙonka Annabin ka sannan Annabi Muhammad (S.A.W) yace duk wanda yayi imani da Allah da rana ta ƙarshe to ya girmama baƙon”.

    Kai Moddibo ya jinjina kana yace.

    “Toh J naji dama ya za’ayi na tozarta matar da J na zai aura har abada bazanyi hakaba?”.

    Hararansa M Jameel yayi tare da faɗin.

    “Kai dai kayi min al’ƙawari koma wacece ai zaka ganta”.

    Kai kawai Moddibo ya gyaɗa.

    Tare da cewa.

    “Nayi al’ƙawari”.

    Ahankali M Jameel ya sakeshi tare da matsawa.

    Da sauri Moddibo ya ɗan yi gefe da kansa lokacin da idanunsa suka sauka akan Khausar da Idanunta ke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

     

    Khausar kuwa cikin wata Sanyayyar murya mai cike da rauni ta kawar da kanta gefe tare da cewa.

    “Ina yini”.

    Kamar yanda ta kawar da kai gefe haka shima ya kawar tare da faɗin.

    “Lafiya”.

    Daga nan ya juya yayi gaba.

    Khausar da M Jameel suka jera atare zuwa sashen Innayi bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga.

     

    M Jameel kuwa cikin yanayin sa yace.

    “Innayi ga baƙuwa na kawo miki ku gaisa”.

    Daga cikin Innayi tayi murmushi tare da cewa.

    “Sannun ku da zuwa ko dai matar ce ka kawo Min?”.

    Murmushi mai sauti yayi kana yace.

    “Ehahea lallai Innayi kenan ke dai ga tanan ku gaisa dama zan wuce da ita gida ne.

    Kuma A.J nata kirana shiyasa nace bari na fara zuwa nasan idan bai ganni ba wataƙil hankalin sa bazai kwanta ba”.

     

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauke kana yace.

    “Hmmm Yayi maka kyau da kazo a gaggauce ai da sai ka ajiyeta kafin kazo”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.

    “Ai kawota nayi ta gaida Innayi kuma bamu gama tattaunawa da itaba”.

    Taɓe baki Moddibo yayi ba tare da yace komai ba.

     

    Khausar kuwa ahankali ta tsugunna tare da Gaishe da Innayi.

    Kallonta Innayi tayi kana tace.

    “A’a wannan ai kamar na ganeki kamar ƙawar Asma’u ko?”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da sakin murmushi kana tace.

    “Eh nice Innayi”.

    Jinjina kai Innayi tayi tare da cewa.

    “Yasu mamanki?”.

    Cike da nutsuwa Khausar tace.

    “Duk suna lafiya”.

    Ƙoƙarin miƙewa Innayi tayi kana tace.

    “Bari akawo miki abin taɓawa”.

    Cikin sauri Khausar ta girgiza kai tare da cewa.

    “Nagode Innayi yanzu daga gidan Ummi nake ta cika min cika na da abinci”.

     

    Saurin kallonta Moddibo yayi jin yanda take magana Anutse kamar ba ita ba baki ya taɓe tare da mgnar zuci.

    “Ganta kamar gaske haka take da nitsuwa”.

    M Jameel kuwa kallon Innayi yayi kana ya juyi ya kalli Khausar yace.

    “Mu tafi ko”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Toh”.

    kana tayi gaba M Jameel da Moddibo suka fito atare a hankali suke tafiya, a hankali lips ɗin M Jameel na motsawa alamun mgn yakeyiwa Modibbo, shi kuwa Modibbo kai kawai yake jinjina mishi tare da tsaresa da ido, a haka har suka isa bakin motar Moddibo da kanshi ya buɗe masa gaban motar ya shiga kana yace.

    “Dan Allah kazo kada ka barni. Ni kaɗai sam bana jin daɗin gidan”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da yiwa motar key kana yace.

    “A.J ka jika randa akace babu nifa?”.

    Cikin sauri Moddibo ya rumtse idanunsa da karfi, sai kuma ya buɗe su da sauri ya kallesa tare da cewa.

    “Jhhhh”.

    Ya ja sunan a cikin maƙoshinsa.

    Murmushi M Jameel yayi tare da jan motar,

    Shi kuwa Modibbo hannunsa ya harɗe a ƙirji yana kallonsa har  suka tafi.

     

    Kai tsaye unguwar su Khausar suka nufa suna tafe yana tsokanarta, a haka har suka isa yana isa yayi Parking ta fita tare da yi masa godiya kana tayi cikin gida.

     

    M Jameel kuwa Anutse ya juya akalar motarsa kai tsaye gidansu ya nufa yana isa yayi Parking tare da fita kai tsaye sashen Abban sa ya nufa yan shiga sukayi ta hira har La’asar tayi, atare suka je masallaci suka gabatar da sallah kana bayan su. Idar ya fito ya nufi Sashen sa yashiga bai sake fita ba sai da akayi Maghariba kana ya nufi masallaci bai fito ba sai da aka Idar da Isha’i sannan yana dawowa ya nufi sashen Abbansa lokacin shima Abbah bai dade da dawowa daga masallaci ba.

    Cikin lumshe ido yace.

    “Abba zanje wajen Moddibo za muyi magana”.

    Jinjina kai Abba yayi tare da cewa.

    “Allah ya tsare amma idan dare yayi ka kwana a can bana son tafiyar daren nan, kasan duniyar nan babu gaskiya”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana ya fice yana murmushi.

    Motarsa ya shiga da addu’a kana yayi Hong mai gadi ya buɗe masa ya hau kan titi yana maiyin murmushin, wayarsa ya zaro, whatsApp ya shiga kan number’n Moddibon ya kusa kai.

    Cikin sakin murmushin yayi mishi voice ɗin 1 mitune And 33 second

    Ba zato ba tsammani yaji an sako hannu daga bayansa an ɗaura masa bindiga akai kana cikin wata magautacciyar murya akace kana juyawa zan fasa maka ƙwaƙwalwar kai da sauri ya saki wayar tasa ta faɗa kan cinyarsa garin ta sule ɗin ne kuma yatsarsa ma nuniya tayi sending din voise ɗin nasa da sauri ya ƙara taka motar jin mutumin ya ɗana kunaman bindigar yana cewa.

    “Maza mu tafi kada kayi min gardama dan ko motsi kayi zan fasa kanka…!

     

     

     

     

    Dan-dan yanzufa aka fara labarin ku biyuni, da kekkyawar yaƙini da ƙarfin zuciya.

     

    *By*

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 17

    Sakayyah 17

     

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 17_

    *LAST FREE PAGE*

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *DAGA WANNAN PAGE ƊIN FREE PAGES SUN ƘARE, IN MA KIN SAKE GANIN LITTAFIN SAKAYYAH A WAJE TO. NA SATANE NA ALLAH YA ISA ne, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal yar ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 kiyiwa da Annabi in dai kin san kin sayane don ki fitarmin da littafin na kiyi min mgn in mayar miki da kuɗinki. In kuma kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina, wasu Groups ɗin, kiyiwa Allah da Manzonsa ki bar kuɗinki na yafe cinikin bana buƙatar sa*

     

     

    Alhamdulillah su Moddibo sun sauƙa lfy a ƙasa Mai Tsarki cikin ikon Allah Mabuwayi gagara Misali sunyi Umarah sun samu goma shabiyar na watan acan cike da ɗumbin farin ciki.

    Yau yakasance ranace ta Sallah angama azumi lfya. Al’ummar Musulmai na duniya sun cika da farin ciki kowa kagani fuskarsa ɗauke da yalwataccen farin ciki, kana kowa yayi shiga ta haiba da kamala.

    Alhamdulillah bayan an saƙƙo daga sallar  idi ko wani gida kashiga zaka samesu cikin farin ciki da shiga ta kamala kana da Lafiyayyan abinci.

    Kamar yanda ko ina na faɗin duniya ya cika da farin cikin wannan ranan haka yakasance Agidan Lamiɗo.

    Acan falon Mommy kuwa hallare suka gaba ɗayan su Khausar ce tsaye riƙe da waya ahanununta cikin shiga ta alfarma da kamala wani rantsatstsen less ne Blue da ratsin fari ne ajikinta ɗinkin riga da skirt yayin da skirt ɗin ya fitar mata da shape din  ƙugunta rigan kuwa tayi ɗass ajikinta ma dai-dai-tan dukiyar fulaninta sun cika fam yayin da tayi ɗaurin ƴar Minister ta zubo yalwataccen sumar kanta zuwa baya daga gaban goshin kuwa ya kwanta luf-luf wuyanta maƙale da sarƙan Gwal da ɗan kunnensa kana fuskarta ɗauke da simple make up daya sake ƙawata kyawun fuskarta.

    Yayin da Raudat ma ke sanye cikin irin shigar dake jikin Khausar sai dai nata ɗinkin dogon riga ne.

    Haiydar kuwa sanye yake cikin wata Bugaggiyar shadda Sky blue anyi masa ɗinkin samarin zamani rigar ta tsaya iya gwiwarsa, kansa sanye da hula yalwataccen sumar irin na fulanin Usul yana kwance lib aƙeyarsa haka ma Ramadan sanye yake cikin irin shigar Haiydar Yayin da Mommy ke sanye cikin Atanfa mai Golden mai masifar kyau anyi mata ɗinkin riga da zani fuskarta ɗauke da simple make da Khausar tayi mata.

    Baki ɗaya falon wani sanyayyan ƙamshi yake fitarwa wanda ya haɗu da ƙamshin jikinsu.

    Cike da tsantsar farin ciki Khausar dake ɗaukar su hoto ta juya ta kalli Mommy kana tace .

    “Kuce Chesss”.

    Dariya suka fashe dashi kana suka ce.

    “Cheeessss”, Akuma dai-dai lokacin ta ɗauki hoton.

    Sosai hoton yayi kyau kallo ɗaya zaka musu ka tabbatar da cewa suna cikin tsantsar farin ciki da annushawa tare da nutsuwa.

     

    Suna cikin hoton Hajiya Bunayya tashigo cikin shiga ta alfarma da kamala sosai tayi kyau.

    Zama tayi bayan tayi Sallama Idanun ta akan Mommy tace.

    “Barka da Sallah ƙanwata fatan anyi Sallah lafiya?”.

    Murmushi Mommy tayi kana ta zauna kusa da ita tare da cewa.

    “Ayyah Yaya ina shirin zuwa wajenki ma”.

    Murmushi Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Ayyah babu komai nima cewa nayi bari na rigaki zuwa in samu ladan gaisuwar. Fatan munyi Sallah lafiya?”.

     

    Jinjina Kai Mommy tayi kana tace.

    “Lafiya Lau Alhamdulillah Yaya Ubangiji Allah ya amshi ibadun da ayyukanmu na Al’khairai Allah ya nuna mana na baɗin baɗaɗa da rai da lafiya”.

    Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa kana tace.

    “Ameen ya Allah Ƙanwata”.

     

    Khausar kuwa kallo ɗaya tayi mata ta kawar da kai gefe.

    Hajiya Bunayya kuwa kallonta ta mayar kan Khausar dake ɗaukar Haiydar, Ramadan, da Raudat hoto, cike da makirci tayi wani murmushi kana tace.

    “Khausar Barka da Sallah”.

    Anutse Khausar ta juya ta kalleta babu walwala afuskarta muryarta ta saisaita kana tace.

    “Yawwa Barka dai Ummah”.

     

    Hajiya Bunayya ta mayar da kallonta kan Haiydar dake tsaye gefenta hannunsa ta kama tare da damƙa masa key da murmushi afuskarta tace.

    “Ga Barka da Sallah ka Babana”.

    Zare ido Haiydar yayi tare da buɗe hannunsa ya kalli sabon key ɗin mashin dake cikin tafin hannunsa,

    cike da tsananim farin ciki mara misaltuwa ya faɗa jikin Hajiya Bunayya tare da rungumeta cike happy ya saƙi ƙara kana yace.

    “Wayyo Ummah na Nagode. Allah ya saka da al’khairi. Allah yaƙara miki nisan kwana mai amfani. Allah yarabaki da sharrin Mutum da Aljan, gaskiya nayi farin ciki kinyi surprise ɗina da kince sai bayan Sallah da kwana biyu.

    Cike da farin ciki tayi murmushin gefen baki kana tace.

    “Ameen,Ameen Babana, Eyyyy dama sunce sai bayan Sallah da kwana biyu sai kuma suka kawo jiya da daddare”.

     

    Khausar kuwa cike da takaicin halayyar matar ta riƙa watsa mata harara wani irin haushin ta takeji, aƙasan ranta kam cewa take shegiya muguwa aniyar ki ta biki da izinin Allah babu abinda zai samesa.

     

    Mommy kuwa kallon Khausar dake bin Hajiya Bunayya da harara tayi kai ta girgiza tare da cewa.

    “Khausar jeki ɗauko mana abinci a kichen ki kawo kin tsaya kin tsare mutane da ido baza ki iya taya ɗan uwanki samun abin farin cikin da yayi ba”.

    Zumɓura baki Khausar tayi  tare da miƙewa batare da tace Komai ba tashiga kichen.

     

    Haiydar kam Kallon Mommy Yayi kana yace.

    “Mommy Ummah ku tashi nayi muku hoto”.

    Miƙewa sukayi da murmushi afuskarsu Haiydar yashiga ɗaukar su.

    Khausar kuwa fitowa tayi hannunta riƙe da Warmers dake ɗauke da soyayyun kaji ta ajiye a dining kana ta koma ta sake ɗauko wasu Warmers ta ajiye.

    Dai-dai lokacin da Mommy ke cewa.

    “Yaya mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi Agaskiya nayi farin ciki”.

    Fuskar Khausar ta ɓata kana tace.

    “Haba Mommy irin wannan godiyar sai kace wacce aka biyawa Kujeran Hajji”.

    Kallonta Mommy tayi kana tace.

    “Ai kujeran hajjin ne Khausar, mutumin daya so ɗan ka arayuwa har yayi masa alkhairi ai babu kamarsa ”.

    Kai Khausar ta girgiza kawai aranta tace Mommy har yanzu baki san wacece wannan makirar matarba, shiyasa kike yabonta wannan matar da kike gani tafi kwalba sharri afili kuwa cewa tayi.

    “Hmmmm Allah ya kyauta”.

     

    Murmushin da be wuce saman laɓɓaba Hajiya Bunayya tayi kana ta miƙe tare da cewa.

    “Nikam zan wuce”.

    Miƙewa Mommy tayi tare da cewa toh mungode Yaya Allah yaƙara girma da ɗaukaka”.

    Ita kuwa Hajiya Bunayya ficewa tayi Yayin da Haiydar yabi bayanta zuwa sashen Lamiɗo.

    yana shiga yace.

    “Abba gashi Ummah ta siya min Mashin zan hau?”.

    Kai Lamiɗo ya gyaɗa kana yace.

    “Babu damuwa tun da kana son hakan, amma kafin nan sai an sake koya maka mashin ɗin na tsawon wata biyu kafin ka fara hawa kai ɗaya kaga ai ka sake koya”.

    Jinjina kai Haiydar yayi kana yace.

    “Toh shikenan Abba babu Matsala ”.

     

    Bayan sallah da kwana biyu jirginsu Moddibo ya sauƙa a Nigeria cike da farin ciki Moddibo, Innayi da M Jameel Ummi suka dawo gida yayin da Hajja Nana ma ta sauƙa ta Ɓadamaye cike da farin ciki da kuma murna.

     

    **********

     

    Ahaka rayuwa ta cigaba da tafiya komai yana tafiya dai-dai cikin ikon Allah Akwana atashi asaran mai rai, sekonni na juyawa izuwa Mintuna, Mintuna na tafiya izuwa awanni.

    Yayin da awanni ke juyawa izuwa kwanaki, kwanaki na tafiya izuwa Makonni.

    Yayin da Mokonni ke juyawa izuwa Watanni. A hankali kuma  watanni ke tafiya Izuwa shakara ko shekaru…

     

    Alhamdulillah su Khausar sunyi nisa kiwo aski yazo gaban goshi, yanzu suna shirye shiryen zana jarabawar Ƙarshe na kammala secondary School WEAC and NECO baki ɗaya kansu ya ɗauki zafi basu da wani lokaci saina karatu sosai suka maida hankalin su suna karatu tuƙuru domin fitowa da kyakkyawan sakamako Inda yanzu ya rage saura Exam biyar ya rage su kammala Neco.

     

    Khausar ce tsaye gaban Dressing mirror jikinta ɗaure da towel da tsawon sa ya kai gwiwarta,

    Zuwa yanzu ko ina na jikinta ya cika fam, dukkan ƙirar girma maƙerin budurci ya ƙenƙesa matashi, musamman Dukiyar fulaninta da kuma hips dinta da suka cika ƙugunta, yalwataccen sumar kanta irin na Fulanin Usul ya sake tsawo da sansti.

    Manyan Idanunta sun sake girma tare da lumshewa siririn dogon hancinta ya sake tsawo yayin da madaidaicin bakinta ya sake tattarewa izuwa pich collor, yana yin ƙiranta kamar kolbar Coca cola Yayin da Tsananin kamanninta da Kajol ya sake bayyana ayanzu tana da shekara goma sha tara a duniya.

    Cikin sauri ta shafa Lotion ɗin ta tare da shafa powder sama-sama sai kuma ta shafa kwalli amanyan Idanunta lipstick kaɗan ta shafa asaman laɓɓannta cikin sauri sauri ta sanya Uniform ɗin ta daya sha guga tulin sumar kanta tayi acuci dashi kana ta feshe jikinta da turarukanta masu masifar daɗin ƙamshi da sanya nutsuwa.

    Cikin Sassarfa ta fito falo harara Mommy ta maka mata kana tace.

    “Ke dai Khausar ba zaki canza ba kin girma amma kullum shiririta kike ƙarawa tun yaushe Ake jiranki, ga Amina ma can tanata jira amma sai ɓata musu lokaci kike”.

    Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da riƙe kunnenta kana tace.

    “Sorry Mommy”.

    Fuska ta tsuke tare da ce wa. “Kin dai san Amina in ta gaji da jiran ki”.

    Cikin ɗan sauƙe numfashi tace.

    “Uhumm ai yaseen in ta gaya min mgn ramawa zanyi in banda asarama tun tuni yaci ace ta gama, amman kullum taba cikin dakon aji har wai sai yanzu zamu gama tare”.

    Mommy na juya zata fita tace.

    “A’a ni bana son fitina”.

    Ta ida mgnar tana fita,

     

    Haka yasa ta biyo bayan Mommy da ɗan sauri yayin da ko wanni gaɓa na jikinta ke motsa wa baki ɗaya alamun Budurci sun bayyana ajikinta ta ko wanni fanni ta zama cikakkiyar budurwa ƴar gayu First class.

    Bayan motar ta buɗe ta shiga bayan ta ƙarasa wajen gani tayi duk Amina ta wani babbaje.

    Kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace.

    “Ɗan matsamin in zauna”.

    Kallon banza Amina ta watsa mata cikin ya mutse Fuska ta kalli Khausar kana tace.

    “Keɗin har nawa kike da wannan wajen ba zai ishe ki ba?”.

    Cikin juya ido tace.

    “Kinsa cikakkiyar sura ta ƙasaitattun mata Allah ya min dole wurin bazai isheni ba tunda ba irin baki bane”.

    Cike da fusata Amina tace.

    “Eh lallai yarinyar nan wuyanki ya kai yanka, amman dadin ta dai bada ɗuwawunki nake zamaba kuma bada ƙugunki nake ɗaura zabi ba”.

    Taɓeki tayi tare da juyawa ta kalleta.

    Har kamar zata yi magana sai kuma ta fasa ganin yanda lokaci ke tafiya sannan ya Exam na Geography zasuyi tasan muddin aka fara Moddibo na iya hukuntata baya ga haka ga kuma alamun yau akwai  hadari a garin wanda yau kimanin kwana tara kenan ba’ayin musu ruwan saman ba.

    Gefen Haiydar ne ya matsa mata ta shiga kana Driver yaja suka tafi.

    Suna Isa Khausar tayi saurin ficewa tare da nufar Hall da zasu zana Exam ta nufi Hall ɗin yayin da Iska mai sanyi ya soma kaɗawa gari ya fara duhu suna cikin rubuta Exam ɗin hadari ya fara haɗa gangami sosai a hankali gari ya fara duhu.

    Basu wani ja lokaci ba suka kammala rubuta Exam ɗin atare Khausar da Asma’u suka fito.

    Asma’u ma ta zama cikakkiyar budurwa komai na Budurci ya bayyana ajikinta.

     

    Juyowa Khausar tayi  ta kalleta ƙirjinta rungume da Questions da suka gama rubutawa,  murmushi ta ɗan yi kana tace.

    “Asmeey ki gaida min Ummi dan Allah, wallahi nayi missing ɗinta, rabo na da ita fa ya kai wata biyu”.

     

    Hararanta Asma’u liƙa mata kana tace.

    “Ai baki da kirkine sannan babu saƙon  ki da zan fada mata in da gaskene kizo”.

    Ta ƙare mgnar tana mai ɗaga kanta ta kalli sama, ganin yadda gaba ɗaya garin ya rufa yayi duhu.

    Da sauri Khausar ma ta fara juye-juye tana cewa.

    “Yah Salam wannan hadari haka, ina Haiydar suzo mu tafi, kar ruwa nan ya rutsamu a nan.”

    Murmushi Asma’u tayi tare da cewa.

    “Allah yasa ya rutsa kin dai muga ta tsoro”.

    Ta ida mgnar tare da yin murmushin mugunta dan tasan yadda Khausar ke masifar tsoron walƙiya da tsawa.

    “Ba Amin ba”.

    Khausar ta faɗa tare da tura baki.

    Ita kuwa Asma’u dariya tayi tare da jan hannun Bashir sukayi gaba saboda yanda hadarin ke sake gangami ko ina yayi ɗib.

    Murmushi Khausar tayi kana tace.

    “Bashir dan Allah kagaida Ummi, dan naga yau mutuniyar Black Stomach take ji dashi”.

    Asma’u na ƙoƙarin shiga mota tayi murmushi kana tace.

    “Oho dai ance zuwa da kai ai yafi saƙo”.

    Khausar kuwa murmushi tayi tare da bin bayansu ganin Haiydar yayi gaba.

    Da ɗa  sassarfa ta  tashiga bayan motar ta zauna kusa da Haiydar tana ɗan kallon harabar makarantar da duk aka watse sai mutane ɗaɗɗaya har malamai da alamun sun tattafi da sauri ta juya ta kalli Haiydar kana tace.

    “Ina Amina kuma?”.

    hannu ya buɗe mata alamar bai sani ba, bata sake cewa komai ba,

    ta lumshe idanunta tare da jingina bayanta da jikin Kujeran sassayan iskan  hadarin dake bugawa na ratsata.

     

    Acan harabar makarantar kuwa Amina ce da Samira Sani ke tafiya.

    Cikin taɓe baki Samira ta kalli Amina kana tace.

    “Ni wallahi tunda nake ban taɓa kallon mutum Irin Moddibo ba ace mutum kamar dutse sam baya fahimtar komai”.

    Murmushi Amina tayi kana tace.

    “Hmmm ke dai Samira bari M Jameel ɗin ma meyene, duk tsawon lokacin da muka ɗauka muna aiki da maganin fa yanda yake wani shan min Ƙamshi”.

    Harara Samira ta watsa mata cike da takaici tace.

    “Amma Wallahi Amina baki da godiyar Allah ki dubi yanda mutumin nan ya fara sake miki, yana amsa gaisuwar ki da fara’a, yana kula ki da ace nice nasamu wannan damar, awajen Moddibo ai dana godewa Allah”.

    Jinjina kai Amina tayi kana tace.

    “Haka ne kuma amma gaskiya har yanzu sai mun sake sabon shiri akansu domin har yanzu Malam Jameel yafi ji da wannan shegiyar yarinyar akaina”.

    Da wannan hira suka isa jikin motar wani matsiyacin kallo Amina ta watsawa Khausar dake bayan mota Idanunta alumshe cike da gadara da kuma Izzah ta ya mutse fuska kana tace.

    “Iyeee ƙarfin hali yau naji Agola da ƙarfin hali, motar na gidan Ubankine da zaki shiga baya kiyi kane-kane aciki, to ni kuma a ina zan zauna ji yanda kika tara ƙannenki kuka lafe abaya ku gaku ramukan kura ko daga ke sai ƙannen ki, wai ma tukunna ni akanki zan zauna ne!? Da kika wani baza masaka-masakan duwaiwaka”.

     

    Ahankali Khausar ta buɗe Idanunta dake lumshe ta zuba mata su tana kallonta cike da mmki, amma ba tace komai ba sai gyara zamanta da tayi tare da buɗa mata inda zata zauna.

     

    Ya mutse fuska Amina tayi cike da jaraba da kuma gadara ta dubi inda Khausar ta matsa mata kana tace.

    “Wannan wani irin iskanci ne da raini ne ko kuma ni sa’ar kice ke badan kinyi sa’ar Babanki ya mutu ya bar uwarki tayi zawarci babana ya kwasa ba ai koda hanyar da nabi baki isa ki biba. Agola kawai mara galihu ƴar matsiyata”.

     

    Cike da ɓacin rai Khausar ta ɗago kanta babu walwala afuskarta ta kalli Amina tare da cewa.

    “Wai Meyesa kike son zagina ne? Baga shi na gyara niki ba wannan ɗan ɗuwawun da kamar an ɗaurawa kare zani me zai hana filin isarki, baki shigo  kin zauna kinga wurin bai ishi tsamurarrun mauzanki da suke kamar an matse lemon tsamiba kawai saboda kin saba da Akuyanci da kuma karnukan ci sai kin tsaya anta masifa dake da raba hali, saboda ke Jaka ce baki san darajar mutane ba,  zaki tsaya kina ta goranta min akan wani Akwalar mota! To ki sani ni dai bazan zagi iyayenku ba musamman mahaifinki da yake mumini uwarki kuwa zaginta ma asarane don ko zagi akan mai tsarki yake fatan a aikeshi”.

    Harara Amina ta watsa mata kana Afusace tace.

    “Eh koda Akwalar ce aiba Ubanki bane ya saya idan kuma Ubankine ya saya sai inji? koda yake nasan har matsiyacin Ubannaki ya mutu bai taɓa mallakar irin wannan na kansa ba!”.

    Cike da matsanancin ɓacin rai Khausar ke kallonta idan akwai abinda tafi tsana aduniya kana yake saurin fusata ta shine zagin mahaifinta.

    Azuciye ta sauƙa daga motar yayinda Haiydar da su Ramadan ma suka sauƙo,

    cikin nuna Amina da yatsa tare da ƙanƙantar da idanunta kana tace.

    “Kada ki sake zagin Ubana domin Ubana yafi ki daraja koda Agaban Ubangiji”.

     

    A yatsine Amina ta watsa mata mugun kallo kana tace.

    “An zage sa ƴar iskan yarinya mai hana ruwa gudu ƴar matsiyata”.

    Cikin wani irin fushi Khausar ta ɗaga hannunta tare da kife Amina da wani irin azabebben mari hagu da dama cikin nunuta da yatsa tace.

    “Ki sake zagar min  Uba kiga abinda zan gwada miki”.

    Dafe kuncin Amina tayi cike da Mamaki take kallon Khausar kana tace.

    “Ni kika mara Khausar?”.

    Harara Khausar ta watsa mata da manyan Idanunta kana tace.

    “An mare ki”.

    Ahankali Habu Driver ya leƙo kansa tare da faɗin.

    “Khausar kiyi haƙuri”.

    Sai kuma ya kalli Amina dake huci kana yace.

    “Amina kema sam baki kyauta ba taya zaki zagi Ubanta ai duk Abinda zakuyi tsakaninku ne”.

    Wani shegen kallo ta watsa masa Afusace tace.

    “Habu ka rufe min baki ka fita Idona na zagi Uban nata idan taji haushi tabar mana gidan mu ta tafi gidan Ubanta ƴar matsiyata ƴar jarababbu Angola ta bar nan garin ta koma can dajin nasu mana”.

    Ta ida maganar tare da shiga motar taja murfin ta rufe da ƙarfi.

    Sai kuma ta sauƙe glass ɗin motar  tare da cewa “Haiydar, Ramadan, da Raudat ku shigo motar tunda ku dai ta  Ubanmu ne”.

    Cikin takaici Haiydar ya girgiza kai alamar a’a su tafi.

    Ita kuwa Khausar ciki takaici ta ɗaga Raudat da Ramadan ta sakasu cikin motar tare da nunawa Haiydar ƙofar motar alamun ya shiga.

    Murya a cushe yace.

    “Toh kefa Adda Khausy”.

    Cikin danne fushinta tace.

    “Kada ka damu zan shiga Napep”.

    Zai yi mgn tayi tayi saurin cewa.

    “Dan Allah kada kace komai shiga kuje”.

    Ta ƙare mgnar tana turashi ciki, dole ya shiga.  Ita kuwa Amina tsaki taja tare da cewa.

    “Dole su kam shiga ke kuma sai kije can kishiga naki na Uban”.

     

    Kallon Habu tayi kana tace.

    “Haba kaja motar mu tafi”.

    Da mamaki Habu drive ya kalleta kana yace.

    “Haba Amina taya zamu tafi mu barta anan dubi hadarin daya taso sannan babu kowa a haraban makarantar ya za’ayi mutafi ne”.

    Harara ta galla masa kana tace.

    “Mu tafi kuma wallahi idan ka ƙi na rantse da Allah saina sa Ummah tasa akoreka”.

    Ahankali Haiydar ya juya ya kalli Amina wanda tun da suka fara magana bai sa baki ba yace.

    “Haba Addah Amina Meyesa haka Fisabilillah ai koma menene bai kamata ki hanata shiga mota ba dubi hadari fa kuma kin san yadda take tsoron yanayin ruwan sama”.

    Harara ta watsa masa kana tace.

    “Rufe min baki an hanata ɗin rufe min baki ɗan Iskan yaro zaka nuna min ƴan Ubanci kenan ruwan ya cinyata, ta mutuma kawai kowa ya huta”.

    Da ɓacin rai Afuskarsa ya kalleta kana yace.

    “Ni dai bazan nuna miki ƴan Ubanci ba, saboda bamu tashi da shiba, kuma wallahi idan na koma gida na faɗawa Ummah ma ke kanki kinsan sai tayi miki faɗa”.

    Dogon tsaki taja tare da cewa.

    “Kayi sauri kada ƙuda ya rigaka”.

    Jin haka yasa Haiydar yin shiru sai kuma ya kalli Amina tare da cewa. “Matsa min In ɗauki jakata bazan iya tafiya in barta anan ba”.

    Girgiza kai Khausar tayi kana tace.

    “A’a Haidar kada ka ɗauka ka shiga dasu Ramadan ku tafi nima yanzu zan biyo bayanku”.

    Amina kuwa kallon Habu Driver tayi kana tace.

    “Mu tafi”.

    Jin haka yasa Khausar jan marfin motar tare da rufewa kana tace.

    “Pless dan Allah Haiydar zauna ku tafi, in Sha Allah babu abinda zai sameni”.

    Dole ya zauba ba don ya soba,

    Shi kuwa Habu ba yanda ya iya haka yaja motar ya tafi.

     

    *Yar uwa littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan page ɗin na gama Free page, in dai kin ganshi a waje to na satane, a Groups ɗina na sakayya ne ɗai ya halatta, 1k ne biya ki karanta cikin Salamah 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA ban yafe ba a karanta min littafi ba’a biya ba in kin tura kuɗin ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

     

    Khausar kuwa shiru tayi tare da bin motar da kallo har ya fice aharabar makarantar,  ahankali ta juya ta kalli cikin makantar babu ɗalibi ko ɗaya duk sun watse haka zalika ma Malamai duk sun watse shiru tayi sai kuma ta ɗaga kanta sama ganin yanda hadari ya taso ga iska dake kaɗawa da ƙarfi.

    Tamkar kazar da ƙwai ya fashewa aciki haka ta fara jan ƙafanta har ta fice acikin Makarantar tsayawa tayi abakin titin koda zata samu Napep amma takai minti biyar babu abin hawan da yazo ya gifta sakamakon hadari daya taso sosai a garin yasa dukkan ababe hawa tsagaita zirga-zirga tana nan tsaye har aka fara ɗan yayyafi hakan yasa ta fara tafiya ahankali a gefen titin.

    Ba tayi nisa da makarantar ba taji an buɗe gate ɗin makarantar da ɗan sauri ta juya, akan motar Moddibo Idanunta suka sauƙa da sauri ta kawar da kanta gefe kana ta cigaba da tafiya.

    Acikin mota kuwa Moddibo ne da M Jameel yayin da Moddibo ke  Driving M Jameel na gefen me zaman banza.

    Kallo ɗaya Moddibo yayiwa bayanta ya ganeta, baki ya taɓe Aransa yace yau kuma wannan wani sabon rashin kunya tayi musu suka sauƙeta, sai kuma ya ɗage kafarɗarsa alamun ita ta jiyo.

    M Jameel kuwa sam bai ganeta ba saida suka gifta wajenta sannan yaga fuskarta.

    Da mamaki ya furta.

    “A’a Lelewal”.

    Cikin sauri ya ɗaura hannunsa kan Moddibo tare da cewa.

    “A.J tsaya Please dubi duk ɗalibai sun watse amma sai ita kaɗai mai ya tsayar da ita anan kuma ga hadari baƙiƙƙirin dubi fa yanda garin yayi duhu ko Babba hadarin na bashi tsoro yakeyi!”.

    Juyawa Moddibo yayi tare da Kallonsa cikin yanayin nutsuwarsa yace.

    “To ina ruwanka da ita!?”.

    Wara Ido M Jameel yayi kana yace.

    “Ban gane ina ruwana da ita ba? ɗalibarmu cefa! sannan kullum a mota ake kawo su sannan zuwa ake aɗauke su, kana mun ganta ba’a tafi da ita ba sannan ka duba ita kaɗai ce a layin nan dubi fa yanda layin babu kowa”.

    Kallon gefen Ido Moddibo yayi masa kana ya taɓe baki.

    Da sauri M Jameel ya cigaba da cewa.

    “Haba A.J ya za’ayi kace haka?”.

    Moddibo kuwa juya idanunsa yayi kana yace.

    “Toh Meye haɗin mu da ita? kasan Meye Uzurin daya tsayar da ita?

    Sannan kasan Meye dalilin tsayuwarta! Wata ƙil ma wani bishiyoyin anguwar takeson hawa”.

     

    Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.

    “Ai koma mene sai mu tsaya mu tambayeta ko?”.

    Kallonsa Moddibo yayi kana yace.

    “Nifa bazan tsaya ba”.

    Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana cikin sanyin murya yace.

    “Dan Allah A.J da darajar Annabi Muhammad (S.A.W) mu taimaki yarinyar nan.

    Yanzu idan Asma’u ce zaka iya barin ta awajen nan ne?”.

    Da sauri Moddibo ya kallesa kana yace.

    “Asma’u kuma mai ma zai tsayar da ita anan mai zai haɗa ta faɗa da wasu har tayi musu rashin kunya su sauƙeta amota, ai Asma’u baza ta kasance haka bama!”.

    Sake Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana yace.

    “Amma kayi tunani ƴa mace ce ita ko addininmu ya koyar mana da kula dasu da kuma kula da al’amuran daya shafesu A.J bai kamata ba na roƙe ka dan Allah ba danni ba kuma badan ita ba dan Allah da kuma darajar Manzon mu kayi haƙuri ka tsaya! In ma bazaka ɗauketa ba, ni ka sauƙin bazan iya tafiya in bar Khausy cikin wannan yanayin A.J bazan iya barin ta ananba”.

    Ya ƙarashe mgnar cikin wata iriyar raunatacciyar murya mai fito da sirrin dake binne cikin zuciyarsa.

    Hannu Moddibo ya sanya tare da dafe goshinsa alamar ya gaji da damuwar M Jameel ahankali yasanya lallausan tafin hannunsa ya shafa sajensa ba tare da yace komai ba ya taka burki ya tsaya.

    Yana mai kallon yadda M Jameel ya sauƙe numfashi.

    Ganin ya tsaya ya sanya M Jameel sakin murmushi tare da buɗe motar ya fita cikin sassarfa da ɗan gudu ya nufi inda Khausar take dan sun ɗanyi mata nisa kana ga yayyafin da aka fara da ƙarfi da kuma rugugi alamar ana gaba da kecewa da ruwa mai ƙarfi.

    Moddibo kuwa da kallo yabi M Jameel ta mirror motarsa.

    Aransa yace Ohhh J ji yanda yake gudu kamar wani yaro ko ya gani a wannan ƴar nan har yake jinta cikin zuciyarsa.

    Khausar kuwa tana ganin M Jameel ta saki nannauyan Ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Yaya Jameel”.

    Cike da kulawa ya kalleta tare da cewa.

    “Lelewal mai yafaru yana ganki anan ke kaɗai, bayan baki ɗaya student’s sun watse”.

    Ahankali ta kallesa sai kuma tayi saurin lumshe Idanunta tare da cewa.

    “Wallahi Yaya Jameel Amina ce ta hanani shiga motarsu yau kam masifa take ji dashi”.

    Girgiza kai yayi tare da faɗin.

    “Subhanallah gaskiya bata kyauta ba, maza zo ki shigo mota mutafi”.

    “Toh”,tace tare da bin bayansa cikin sassarfa yayinda ko wanne gaɓa na jikinta ke motsawa.

    Ɗan guntun tsaki Modibbo yaja, tare da kauda kansa daga kan madubin, ganin yadda suka wani jero da J ɗinsa.

    Suna isa wajen motar M Jameel ya buɗe mata bayan gefen da Modibbo yake tashiga, sannan shi kuma ya zagaya  ya shiga a hankali Khausar ta ɗaga kanta tare da kallon gaban motar ai kuwa idanunta suka sauƙa akan Moddibo da batasan yana cikin motar Ba gashi ta zauna asaitin bayansa.

    A kuma dai-dai lokaci  ruwa ya kece tamkar da bakin ƙorya, key Moddibo yayi wa motar tare da figarta a dan guje suka fara tafiya.

     

    Kallon Moddibo M Jameel yayi kana yace.

    “A.J kasan zamu biya ta gida ka sauƙe ni tun safe Abba ke kirana wai Inje Yana son magana dani muje ka sauƙe ni”.

    Kallon sa Moddibo yayi tare da cewa.

    “Baza ka bari sai anjima ba?”.

    Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.

    “A’a muje dan Allah ka sauƙe ni saboda bansan me yake sona dashi ba yanata ne mana tun tuntuni”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.

    “Toh naji”.

    Yayi mgnar tare da haharan M Jameel ɗin,

    Sannan ya cigaba da Driving ɗin sa.

    Shi kuwa M Jameel murmushin yayi tare da ɗan mishi alamun zunɗe.

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan page ɗin na gama Free page, daga gobe in dai kinga littafin SAKAYYAH a wani wuri to na satane, yar uwa ki biya 1k ne kacal ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin kowa a kanki littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa kada ki karanta in baki biyaba 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

     

    Khausar dake zaune abayan motar kuwa ƙanƙame jikinta tayi saboda yanda ɗumin motar ke ratsata sam cikin motar babu sanyi da yawa ba kamar waje da iska ke kaɗawa ba.

     

    Sanyayyar Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da gyara Questions peper dake hannunta ta sake rungumesu aƙirji sai kuma ta gyara zaman wuyan hijabinta wanda har tattausan gashin gaban goshinta mai sansti ya bayyana.

     

    Baki ɗaya cikin motar a wadace yake da wani irin ni’imtaccen sanyayyan ƙamshi mai daɗin shaƙa yakeyi, Ahankali Khausar ta maida kallon kan bayan Moddibo da take fuskanta sanye yake  cikin ɗanyen Boyel fari ƙal yasha guga sosai yayin da kansa ke sanye da hula zanna bukar wadataccen sumar ƙeyansa ya kwanto lib-lib gwanin kyau sai sheƙi da ƙyalli yake zubawa.

    Ƙeyar tasa ta zubawa ido sai kuma ta gallawa ƙeyar tasa harara  tare da murguɗa masa baki.

     

    Tana ɗago Idanunta suka sauƙa akan Idanun Moddibo ta madubin jikin motar yana kallonta cikin mugun sauri tayi ƙasa da kanta zuciyar ta na mai bugawa da ƙarfin tsiya.

    Moddibo kuwa Ƙoffa yayi tare da haɗa harshensa da hoƙorinsa ya fitar da wani sauti kana yace.

    “Hmmmm!”.

    Kallon sa M Jameel da Idanunsa ke lumshe yayi kana cike da kulawa yace.

    “Ya dai A.J?”.

    Shiru Moddibo ya masa tare da watsa masa Harara!.

    Ware Ido M Jameel yayi tare da shafa sajensa kana yace.

    “Ya dai kake ta harare-harare acikin mota!”.

    Ƙin tanka masa Moddibo yayi ya cigaba da Driving ɗinsa tare da ƙara tsuke fuska.

    Khausar kuwa shiru tayi sai kuma ta sake ɗago kanta ahankali ta kalli madubin ganin ya kawar da kansa gefe yasa ta sake liƙawa ƙeyansa harara tamkar  idanunta zasu manne bisa ƙeyar tasa, kana ta ɗago hannunta na dama ta ɗan haɗe kan yatsun tare da buɗe su ta watsa masa alamar Jarabebbe! Mayatacce!! Masifeffe!!! Fitinenne!!!! sai kuma ta sake watsa masa Harara tare da kai hannunta ƙeyarsa kamar zata kai masa ronƙwashi.

    A kuma dai-dai lokacin ya ɗago ya kalleta ta madubin.

    Azabure taja baya tare da jinginar da bayanta da jikin kujeran zuciyarta na bugawa.

    Cikin fushi Moddibo ya watsa mata mugun kallo tare da cewa.

    “Anh zan karyaki wallahi kakkarya ki zanyi in watsar dake atiti inyi tafiyata, ƴar rashin kunya fitsararriya”.

    Ita dai Khausar rumtse Idanunta tayi da masifan ƙarfi tare da sake rungume question peper ta aƙirji gam-gam.

    M Jameel kuwa daya ta kure jikinsa waje ɗaya idanunsa alumshe saboda sanyi da ake yayi saurin buɗe idanunsa yayi tare da kallon Moddibo dake Driving tamkar bashi yayi maganar ba cikin tsaresa da Ido yace.

    “Ha’a wai mai yake faruwa a motar nan ne kake abubuwa iri-iri daga Harara, Ƙoffa, tsaki, tsuke fuska,  yanzu kuma sai cewa zaka kakkarya!,To waima wa zaka karya ne kam?”.

     

    Cikin fushi Moddibo ya juya ya kallesa kana yace.

    “Ai duk wanda zan karya ya sani!

    Karya yarinyar nan zanyi fitsararriyar banza mara kunya idan kina sake kuskuren kallon min ƙeyata saina gutsitsi-tsiraki na ƙwaƙule miki manyan mayatattun idonun ki masu kama da na yan maye na jefar! A titi ko na samu salama”.

    Lokaci ɗaya tsoro ya dirarwa Khausar jin wai zai Kakkarya ta ya ƙwaƙule mata ido cike da tsoro ta kuma ƙara rumtse Idanunta tare da ta kure jikinta ajikin kujera ita kanta batasan dalilin da yasa yake mata haka ba ita dai tasan da zata samu dama itama karyashin zatayi ta kuna tsitstsige gemunshi.

    Akuma dai-dai lokacin suka isa ƙofar gidan su M Jameel Moddibo yayi Parking.

    Ɓude Murfin motar M Jameel yayi tare da fita duk da ruwan da ake tsugawa bai hana sa saka kansa ta cikin glass ɗin side da Khausar take ba, cikin ƙasa da murya yace.

    “Lelewal be careful don’t Misbehaving kinga bana nan yaseen kika mishi ba dai-dai a titi zai wurgaki ya tafiyarsa”.

    Kai ta gyaɗa masa cike da alamun tsoro sai taji kamar ta fita ta bisa.

     

    Shikuwa M Jameel kallon Moddibo yayi tare da cewa.

    “Toh Allah ya tsare Allah ya kaiku lafiya A.J Amana ce, dan amana A.J ka kularmin da ita”.

    Daga haka ya juya da gudu ya nufi cikin gida zuwa lokacin duk ya jiƙe saboda yanda ruwan ke sauƙa da ƙarfi.

     

    Acikin motar kuwa lumshe idanu Moddibo yayi ba tare da yaja motar ba.

    Khausar kam ƙasa da kanta tayi aranta tace wannan dai akwai bahagon mutum, fisabilillah yana kallon yanda ake tsuga ruwa kamar da bakin ƙwarya amma yaja ya tsaya jifa yanda ruwan ke sauƙa.

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan na gama Free page, 1k ne kuɗin samun damar karantawa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, biya ki karanta cikin Aminci*

     

    Sun kai kusan minti biyar ahaka ita batace komai ba, haka zalika shima baice komai ba banda sautin ƙaran ruwa babu abinda ke sauƙa ɗago Idanunsa yayi dai-dai lokacin da itama Khausar ta ɗago Idanunta ta kalli madubin cikin motar,

    idanunsu ne suka sarƙafe cikin na juna.

    Harara ya watsa mata kana cikin wata razananniyar murya da shi kansa  bai san yana da ita ba yace.

    “Uban me kike abayan mota koni.

    Driver kine harda wani hakimcewar ki abaya a dole kega Sarauniya kin samu Driver!

    Kifita idona fa, nifa ba J bane zan karya kifa”.

    Cikin sauri ta buɗe bayan motar ta fita aranta tace Gwanda inyi yanda yake so dan yanda yake kiran zai karya nin nan inda yazo da tsautsayi sai yajawa Mommy asarata, gaban motar ta buɗe ta shiga amma duk da haka saida ta ɗan jiƙe sabida ruwan da ya fara ƙarfi, tana zama yaja motar suka tafi.

    Akuma dai-dai lokacin ruwan ya sake kecewa da ƙarfin gaske tamkar da bakin ƙwarya ake tsuga ruwan.

     

    Khausar kam lumshe Idanunta tayi aranta tace ya Allah ka kaimu gida lafiya ka rabani da wannan bawa naka lafiya,

    domin akwai rata tsakaninsu da gida sosai ahankali ta buɗe Idanunta ta kalli titin da yayi shiru babu hayaniyar sai ƙugin motarsu da kuma yanda tayun ke fesar da Iska da ruwan kan kwalta fuuuu kana har zuwa yanzu garin ɓakiƙƙirin yake duk da kuwa yadda ake sheƙa ruwan alamar har yanzu ruwan bashi da niyyar ɗauke wa.

     

    Suna cikin tafiya akayi wani irin walƙiya mai haske.

    Da sauri Khausar ta rumtse idonta tare da furta.

    “Bismillahi”.

    A lokacin guda kuma ta sake buɗesu da sauri sabida

    jin wani irin rugugi da akayi mai bada sautin rududuuu-duuuuhhh kana ga walƙiya daya haska da wani irin sauri Khausar ta rungume jikinta waje ɗaya aranta tace.

    _“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakil Subhanal Lazi yusabbihul ra’adu bi handihi  wal Mala’ikatu min hiyfatin”._

     

    Cikin tsananin tsoro tayi addu’ar domin arayuwarta babu abinda take masifar tsoro a damuna kamar tsawa da walƙiya  sam bata yarda ta haɗa ido da walƙiya da zaran taga za’a yi walƙiya zata rufe Idanunta ta sunkuyar da kanta.

    Shi kuwa Moddibo tafiya ya cigaba dayi yayin da titin yayi shiru babu hayaniyar komai sai bishiyoyi dake rangaji ruwa na sauƙa akansu Sanyayyar iska mai cike da Ni’imah na kaɗasu baki ɗaya shaguna dake gefen titin arufe suke baki daya garin babu hayaniya sai jefi-jefi suke hango Mutane.

     

    Suna cikin tafiyar aka sake wani walƙiya mai masifar haske ja, alamun yanzu za’a ƙara kecewa da ruwa.

    Atsorace cikin ɗaga sautin murya tace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

    Ta ida addu’ar tare da kife kanta akan gwiwarta yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa A ɗan juya kai Moddibo yayi kalleta, domin shi kansa zuciyarsa ta harba sabida walƙiyar saida ta ɗauke masa ido saboda yanda walƙiyar tazo da haske mai ƙarfin gaske sosai yaji tsoron walƙiyar amma sai yayi addu’a aransa kana yana cigaba da tafiya bai tsaya ba.

    Bayan walƙiyar ba daɗewa aka saki wata tsawa mai sautin rututuuuu alokaci ɗaya zuciyarsu ta buga domin ji sukayi tamkar ƙasa zai tsage.

    Atake wani matsananci tsoro ya sake lulluɓe Khausar yayin da jikinta yashiga rawa tamkar mazari kanta ta kife acinyarta zuciyarta na cigaba da bugawa da masifan ƙarfi kana har zuwa lokacin kanta na sunkuye akan ƙafafunta tun daga wannan rugugin.

    Yayinda gaba ɗaya mazauna garin Gembu Mebila suke cike da taraddadi sabida bisa dukkan alamu yau da tsawa da rugugin ruwan yake sauƙa.

     

    Acikin haka ne aka sake walƙiya mai masifar haske irin walkiyar nan mai zuwa tamkar an watsa dogon bulala koko tafiyar maciji,

    Da masifar haske da tarsatsi yazo tamkar an watsa bulala Sharrrrrr sai kuma a take aka saki wata iriyar tsawa mai masifar ƙarfi yabi yo bayansa wanda ke fitar da sautin felelelelelelelen  da masifar karaji da gigita dukkan bani adam

     

    Cikin wani irin tsananin tsoro da gigita Khausar ta saki ƙara mai masifar  sauti tare da furta. _“Hasbunallahu wani’imal wakil. Subhanal Lazi yusabbihul ra’adu bi hamdihi wal Mala’ikatu min hiyfatihi”._

    Atake aka sake sakin wani walƙiyar haɗe da wata iriyar firgitacciyar tsawa mai masifar kara mai razana dan adam dasa hanjin mutum kaɗawa.

    Cikin tsananin tsoro da masifar gigita ta dari ta ɗago kanta a kiɗime ta afkawa jikin Moddibo yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa shi kansa Moddibo wani irin tsoro ne ya kamasa saboda hasken walƙiyar saida ya tsaga glass ɗin gaban motarsa tare da bada sautin ƙarararassss!!!.

    Wani irin bugawa zuciyarsa keyi da masifar ƙarfe yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ya ɗauki rawa ƙoƙarin taka burki yake amma ya gagara saboda yanda ta takure jikinta ajikinsa ta kanainayeshi, bashida wani kataɓus ɗin motsa wa, sabida yadda ta kife kanta afaffaɗan ƙirjinsa hannunta ɗaya na zagaye da bayansa yayin da ta cusa hannunta na dama akan maransa.

     

    Moddibo kuwa wani irin masifaffen rawa jikinsa ya farayi tamkar mazari yana wani irin tsuma ji yake tamkar ana tsikara masa allurai ne agaba ɗaya ilahirin jikinsa lokaci ɗaya wani irin baƙon yanayi ya ziyarcesa ga fargaban tsawar da har zuwa lokacin bai gama tsayawa ba.

    Tsawan na tsayawa wani mai masifar rugugi ya sake sauƙa.

    Wani irin masifaffen tsuma jikin Khausar keyi yayin da numfashinta ke fusga saboda tsananin tsoro Allah ya sani tana masifar tsoton tsawa hakan yasa ta sake ƙanƙamesa tamkar zata tsaga jikinsa ta shige ciki.

     

    Shi kuwa Moddibo baki ɗaya jikinsa tsuma ya shiga yi saboda yanda ta kanainayesa kar-kar-kar haka jikinsa ke rawa  yayin da baki ɗaya tsikar jikinsa ya miƙe daga tsakiyar kansa har zuwa babban yatsan ƙafarsa yaji wani irin yanayi wanda bai taɓa jiba a iya tsawon rayuwarsa, sai  yau kuma yanzu ya jishi.

     

    Wani irin harba zuyarsa da sashi mafi daraja a jikinsa sukayi a tare da wani irin azaban ƙarfi.

    Akuma lokacin aka sake sakin tsawa da walƙiya.

     

    Ita kam Khausar cikin tsananin gigita da tsananin tsoro kana da ficewar hayyaci ta sake rungumesu tare da sake tura hannunta ka maransa yayin da yatsun hannunta suka sauƙa akan cibiyar sa.

    Tsawar da aka sake yine ya razana illahirin wani abu mai rai dake yankin Gembu,

    yayinda hakan take a wurin Modibbo ma wani  cikin rashin sanin makaman kamawa ya ya buɗe hannayensa ya rungumeta da azaban karfi tare da taka burkin motar da ƙarfi wani irin sautin ƙuuuuuuu motar tayi tare da cigaba da tafiya sabida tsantsin kwaltan da yayi sabida ruwan sama da kuma tsantsin sabbin tayoyin da ƙyar ya samu motar ta tsaya a tsakiyar titin, sake Rungumeta yayi da masifar ƙarfe kana ya cusa kansa atsakanin kafaɗarta da wuyanta.

    Lokacin da aka kuma sakin wani irin rugugin nan da zakaji kamar ƙasa na amsawa.

    Atake zuciyarsu ya buga da mugun ƙarfi tare da bada sautin dib-dab-dib-dab-difffh yayin da yake jin wani irin masifaffen abu na tsirgar masa lokaci ɗaya lafiyarsa sa ta shaida mushi  kasantuwarsa cikekken Namiji.

    Ita kuwa khausar tana jin yatsarta cikin ɗan hudan cibiyarsa amma tsananin tsoron da take ciki yasa ta kasa fahimtar menene sai cusa kanta da ta kumayi a kirjinsa.

    Shi kam Moddibo wani irin rungumeta yayi da masifar ƙarfi yana mai sakin wani irin amintaccen nish….!

     

    *Free page sun ƙare daga wannan, ko kin ga littafin a wani wuri na satane, littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ɗin da nan kadai zanke posting*

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

    *By*

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 19

    Sakayyah 19

    SAKAYAH

     

    19

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

    Spjnyh.  Miƙewa Haiydar yayi kana ya nufi ƙofar falon fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Oyoyo Uncle Naseer”.

    Khausar dake zaune kan 1sitter sanye cikin riga da baƙin wando Pencil da riga pinch color mai gajeren hannu gaban rigar an rubuta Never Give Up manyan boobs ɗin ta sun cika gaban rigar yayin da bajejjen ƙugunta ya baje acikin wandon, kanta sanye da hular Net baƙi gashinta ya zubo ta gefen wuya, a hankali ta juyo ta kallesa tare da faɗaɗa fara’ar dake saman fuskarta kana tace.

    “Laaa Uncle Naseer”.

    Shi kuwa Naseer ido ya zuba mata yana sakar mata da wani irin shu’umin murmushi yayin da yashiga bin ilahirin jikinta da kallo wani irin kallon Up and Down yake mata yana jin komai nata na kars burgesa soyayyar ta na kuma ninkuwa a ransa.

    Cikin wani irin salo kana still Idanunsa na kanta ya wani lumshe ido afili ya furta.

    “Masha Allah Matata ta girma”.

    Mommy dake zaune kan 3sitter tayi murmushi tare da cewa.

    “Masha Allah Naseer mutanen India kwanan nan mukayi magana da Aunty Jameela kece min ka kusa dawowa Ashe-ashe dawowa yazo ma”.

    Murmushi yayi kana cikin yanayin zumuɗinsa yace.

    “Aidai kam suma Surprised ɗin su nayi babu wanda yasan dawowana akwanan nan kawai sai ganina sukayi”.

     

    Cike da kulawa Mommy tace.

    “Masha Allah sannu da zuwa ka iso”.

    Raudat da Ramadan dake zaune suka mike tare da zuwa suka riƙe hannunsa,hannun Raudat ya riƙe tare da ɗagata sama kana yace.

    “Iyeee Baby Raudat Masha Allah an girma anyi kyau. Amma dai duk da haka Matas tayi miki wayau ta fiki kyau”.

    Murmushi Mommy dake zaune tayi kana tace.

    “Haka dai kace”.

    Ware ido yayi kana idanunsa akan Khausar yace.

    “Allah kuwa Mommy dubi fa Khausi na tafita kyau”.

     

    Khausar kuwa lallausan tafin hannunta tasa ta rufe fuskarta.

    Sai kuma ta miƙe ta nufi kichen ta ɗauko drinks da Snacks sai kayan Friut tafi to masa dashi.

    Har zuwa lokacin batayi magana ba sai dai da zaran sun haɗa ido zata sakar masa da ɗan guntun murmushi kamar yanda shima yake sakar mata.

    Haiydar kuwa da sauri ya saki hannun Naseer kana ya nufi sashen Hajiya Bunayya yana faɗin.

    “Ummah,Ummah ga Uncle Naseer kizo ku gaisa”.

    Miƙewa Ummah tayi fuskarta ɗauke da murmushi Amina ma miƙewa tayi tana murmushi tabiyo bayansu.

     

    Cike da farin ciki Amina tace.

    “Uncle Naseer mutanen India”.

    Washe baki Naseer yayi domin shi mutum ne mai fara’a da son nuna shi wani ne, kana ga fafa da iyayi baya ga haka yana da budeɗɗen ido da son holewa.

    Ita kuwa Hajiya Bunayya  kallonsa takeyi da murmushi afuskarta tace.

    “Naseer sai ganinka mukayi babu sanarwar anyi karatu angama ka dawo Nigeria kenan?”.

    Sha fa sumar kansa yayi yana shan Fruit da Khausar ta kawo masa yace.

    “Wallahi kuwa Ummah nazo ganin Matata ce muyi aure in ɗauke ta mutafi.

    Amma Ziyara nazo yi muku zan koma da matata, dan bazan iya zaman Nigeria ba”.

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Ayyah Naseer ai nan ma muna da waja-je masu kyau kodai India sunfi mu Weather mai kyau ne?”.

    Girgiza Kai yayi tare da cewa.

    “No Mommy bawai Weather mai daɗi ba kawai dai can ɗin zan samu aiki ne sannan gaskiya ni yanzu bazan iya rayuwar Nigeria ba”.

    Ya ida maganar yana ya mutse fuska cike da Iyayi.

    Murmushin da bai wuce saman laɓɓaba Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Aikam dai kam yayi kyau Allah ya taimaka bari na koma ina aiki”.

    Ta ida maganar tare da miƙewa dan Allah ya sani ya ƙona mata rai da batun ya aure Khausar su koma India.

    Amina kuwa siririn tsaki taja cike da jin haushin yanda Naseer ke Shish-shigewa Khausar ta miƙe tabi bayan Hajiya Bunayya suka fice.

     

    Bayan fitarsu Mommy ta miƙe tashiga Kichen Haiydar ma miƙewa yayi tare da ɗaukar Ramadan da Raudat suka fita danmai yi musu lesson yazo.

    Falon ya rage daga Khausar sai Naseer, Ahankali Khausar ta miƙe da niyyan barin falon cikin sauri Naseer yace.

    “Ohh My dear Wife Why are you going?”.

    Murmushi Khausar tayi aranta tace Ohh Uncle Naseer sam bazai canza ba, wannan kalma ya riƙe ta tun yarinta alokacin batasan ma’anarsa ba amma yanzu da zaran ya faɗa kunya take ji wai matarsa ko kunya faɗa agaban su Mommy baya ji.

    Anutse ta dawo ta zauna a inda ta tashi, cikin tsareta da Ido yace.

    “Tunda baki gaisheni ba bari in gaishe ki”.

    Cikin sauri tayi ƙasa da kanta kana tace.

    “A’a Uncle Naseer ina yini ya karatu fatan ka dawo Lafiya?”.

    Sumar kansa ya shafa kana yace.

    “Karatu Alhamdulillah ya naki karatun??”.

    Murmushi Khausar tayi kana tace.

    “Alhamdulillah Uncle Naseer nan da kwana goma zamu gama Secondary school Insha Allah”.

    Washe baki yayi yana binta da wani irin  kallon yace.

    “A’a Masha Allah Abu yayi kyau kenan abu zai tafi dai-dai yanda aka tsara”.

    Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

     

    Ɗago kansa yayi tare da miƙewa ya koma kusa da ita.

    Cikin wata narkakkiyar murya ya kalleta tare da cewa.

    “Khausar ina fatan baki manta da maganar mu bako?”.

    Murmushi tayi still ba tace komai ba sai ƙasa da tayi da kanta tana cigaba da wasa da yatsun hannunta”.

    Shi kuwa Naseer sake narkar da muryarsa yayi tare da faɗin.

    “My Khausi kinsan dai ina sonki, ke tawa ce inaji Ajikina Ubangiji ya halicce ki ne domin ni kaɗai kinsan ina matuƙar ƙaunarki ina burin ki kasance matata ke ta dabance ina miki sahihiyar ƙauna bani da burin daya wuce mu zamto ma’aurata in mori ni’imar da Allah ya halitta miki”.

    Batare data ɗago kanta ba tace.

    “Uhm”.

    Shi kuwa wani narkar da fuska yayi tare da lanƙwasar da harshe kana yace.

    “Meyesa ne komai nace sai kice Uhm?. Yanzu ke kanki bakya jin kina so kiyi Aure ne? aike kanki kin girma kin kai matakin da akan kanki zaki buƙaci na miji atare dake musamman ma na miji irina wanda zai iya gamsar dake tare da biya Miki duk kan buƙatunki ko ba haka bane?”.

     

    Lokaci ɗaya Khausar ta kwaɓe fuska cikin yanayin rashin jin daɗi da kuma rashin tsammanin abinda ya faɗa ta ɗago kanta tare da Kallonsa sai kuma ta kawar da kanta gefe fuska a tsuke.

    Shiko sake narkar da murya yayi tare da tsira mata Idanu kana yace.

    “Shifa rayuwar nan baya tafiya dai-dai dole sai ansamu dai-dai-to atsakanin halittar Namiji da mace, rayuwar nan bata da wani daɗi idan har babu mace akusa da namiji, haka itama mace rayuwar bata mata daɗi idan har babu Namiji akusa da ita, musamman idan anfara tafiya irin matakin shekarun kin nan daga Sha tara, Ashirin, Ashirin da ɗaya,Asirin da biyar, Talatin,har zuwa talatin da biyar dole tana buƙatar Namiji”.

    Ya sake narkar da murya yana binta da wani shu’umin kallo yace.

    “Muyi Aurenmu Khausar zaki ci gaba da karatunki a India sai kije kiyi karatunki acan”.

     

    Ƙasa ta sake yi da kanta kana cikin yanayin ɓacin rai ta ɗago batare data yarda sun haɗa ido ba tace.

    “Ni bana sha’awar zuwa India nafiso in zauna an ƙasata kusa da Mommy na bana buƙatar duk wani abu da zai nesanta ni da ita da kuma ƙasata domin duk abinda India take dashi ai muma muna da shi harma fiye da nasun”.

    Cikin sauri ya sake Matsawa kusa da ita tare da sanya hannunsa zai kamata.

    Da mugun sauri ta kauce ranta babu daɗi ta kallesa kana tace.

    “Ya haka Uncle Naseer mai yasa zaka kama min hannu?”.

    Ido ya lumshe yana jin sautin muryarta na ratsa shi sai kuma ya buɗesu akanta tare da cewa.

    “Ohh My God wai Khausar har yanzu baki waye bane?  me haka kamar ba ƴar zamani ba!? Dan na taɓa ki ai bawani abu bane kada ki manta tun kina ƙarama ko su Abba sun sani ke mallaki nace idan Ubangiji ya nufa”.

     

    Fuska ta sake ɗaurewa kana cikin sauri tace.

    “Toh kabari sai Ubangijin ya nufa kasamu. Shaidu sai inzama mallakin naka”.

    Ta ida magarta tare da miƙewa tabar wajen.

    Binta yayi da kallo bajejjen ƙugunta wanda duk takun da tayi sai sun motsa tamkar da gangan take juyasu.

    Dai-dai lokacin kuma Mommy ta fito daga kichen yana ganin ta ya miƙe tare da cewa.

    “Mommy bari in isa wajen Yafendo Dadu”.

    Shi ɗin ɗan ƙanwar Gimbiya Dadu ce,

    Ya ida maganar tare da ficewa kai tsaye sashen Gimbiya Dadu ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama ya shiga falon.

     

    Gimbiya Dadu dake zaune tana shan Fruit ta Washe baki kana tace.

    “Nasiru lallai mutanen India masha Allah sannu da zuwa”.

    Zama yayi daga gefenta yana murmushi kana yace.

    “Yafendo fatan mun sameku lafiya?”.

    Cike da farin ciki tace.

    “Lafiya lau Nasiru ina ƴar Uwata ƴar Autanmu”.

    Zamansa ya gyara tare da cewa.

    “Tana lafiya tace in gaisheki”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Ayyah Ina Amsawa”.

     

    Gyaran murya yayi tare da fuskantar Gimbiya Dadu kana yace.

    “Yafendo na gama karatuna yanzu na dawo sannan na dawo da burin yin Aure. Ya maganar mu da khausar tana nan dai ko?”.

    Ajiyar zuciya mai nauyi Gimbiya Dadu ta sauke tare da lumshe Idanunta kana ta saki wani shu’umin murmushi tare da kallonsa kana tace.

    “Sosai ma kuwa maganar ku tana nan mai zai hanata da izinin Ubangiji maganar ku tana nan baka da matar data wuce Khausar yau ɗin nan zan yiwa Abbansu maganar”.

    Cike da farin ciki ya saki sanyayyar ajiyar zuciya kana yace.

    “Kai Alhamdulillah Yafendo na naji daɗi”.

    Murmushi kawai tayi shi kuwa miƙewa yayi bayan sun sake taɓa hira ya tafi.

     

    Bayan kwana uku.

    Ahankali Khausar ta sauƙa daga motar dake kaisu makaranta hannun riƙe da Raudat ta nufi ajinsu ta kaita kana ta dawo tashiga ajinsu Lokacin har an fara raba booklet kallonta Malam Isma’il dake raba Booklet ɗin yayi kana yace.

    “Lelewal mai yasa kike son zuwa letti ne Exam ɗin ma baza ki fito da wuri ba?”.

    Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da cewa.

    “Ayyah Malam ayimin afuwa”.

    Harara Samira Sani dake bayan ta ta watsa mata cike da tsanar ta Asma’u dake gefen ta ta girgiza kai domin ita dai ta rasa me. Khausar ta tsare musu suka tsaneta.

    Khausar kuwa zama tayi Malam Isma’il ya bata Booklet da kuma Quatons peper Na Arabic da zasuyi yau ma kamar kullum tun kafin a gama rabawa Khausar tashiga answering Questions ɗin cikin mintunan da baza su gaza ashirin ba ta kammala.

     

    Acan office ɗin Moddibo kuwa zaune yake ya jingina bayansa da jikin kujera yayin da ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya akan deks ɗin Idanunsa na lumshe.

    Cikin sauri ya buɗe Idanunsa tare da jan dogon tsaki.

    Domin da zaran ya rufe idanunsa babu abinda yake gani sai moment da suka kasance da yarinyar cike da damuwa ya sauƙe numfashi kana aƙasan ransa yace.

    “Na godewa Allah da yasa karatun yaran nan yazo ƙarshe kana naji daɗi da cewa sun gama Exam ɗina, bazan sake shiga ajinsu ba”.

    Da sauri ya runtse Idanunsa haka nan yake jin kunyar kansa da kansa ya rasa ta yanda zai fassara al’amarin yasan tun farko yarinyar bata da kunya bare kuma wannan abu ya faru shin taya zai iya haɗa ido da ita?.

     

    Anan sashin su kuwa.

    Atare Khausar da Asma’u suka fito daga Area class ɗinsu har zasu wuce suka hango M Jameel tsaye.

    Abakin Office ɗin su Moddibo.

    M Jameel ne tsaye ya jingina bayansa da jikin ƙofar yayin da Amina ke tsaye gefensa cikin iyayi da yauƙi ta kashe murya tare da cewa.

    “Malam sai gobe idan Allah ya kaimu zan dawo ko Principal ya dawo na amshi result ɗina”.

    Anutse M Jameel ya juya ya kalleta tare da cewa.

    “Ok Allah ya kaimu ki gaida gida”.

    Sake karya murya tayi cikin tsaresa da ido tace.

    “Toh gida zaiji Malam kaima ka gaida gida”.

    Jinjina kai yayi batare daya sake kallonta ba yace.

    “Gida zaiji”,Juyawa tayi tabar wajen.

    Dai-dai lokacin da Asma’u da Khausar suka iso a tare Kallonsa Khausar tayi tare da cewa.

    “Barka da rana Yah Jameel”.

    Murmushi ya sakar mata kana yace.

    “Yawwa Khausi bar ka dai yanzu kam an zama manyan ƴan mata ankusa agama Secondary school a huta  a shiga babin girma ko?”.

    Jinjina kai tayi cikin jin daɗi ta kalli Asma’u kana tace

    “Ai lallai dai kam bari kawai Yah Jameel jinmu nake tamkar ansaki tsuntsuwa daga sheƙarta.

    Wani irin daɗi mukeji mun kusa mu rabu da rayuwar bauta rayuwar duka cin zali, kaɗe ɗan kwali, harara, tsawa, hantara,”.

    Kallon ta M Jameel Yayi tare da juya idanunsa zuwa office ɗin ya mata alamar Moddibo na ciki.

    Cikin sauri ta sanya hannunta ta rufe bakinta tare da barin wajen bayanta Asma’u tabi tana ƙyalƙyala dariya tare da cewa.

    “Khausar ga Moddibo na miki magana wai kije”.

    Dariya M Jameel yayi ganin

    Cikin sassarfa Khausar ta fice daga wajen batare data yadda ta juya ba.

     

    Moddibo kuwa na zaune a office duk Maganar da sukayi akunnensa da zaran sautin muryanta ya ratsa kunnensa zaiji tsikar jikinsa ya tashi tamkar ana stikaresa da allura hakan yasa ya runtse Idanunsa da ƙarfi kana yayi shiru.

    Allah ne kaɗai yasan yana yin da yake ciki.

     

    Khausar kuwa na fita wajen motarsu ta nufa ta samu duk su Amina su shiga ita kadai ake jira tana zama Driver yaja suka tafi.

    Asma’u kuwa na fita ita da Bashir mai Napep ɗin su ya iso ya ɗauke su suka tafi.

     

    Washe gari da yamma bayan Khausar sun dawo makaranta misalin ƙarfe Uku ta fito cikin wata Bugaggiyar shadda milk color anyi masa ɗinkin dogon riga da kuma zubi da akayi sa da Coffee zare fuskarta ɗauke da light Make-up yayin da tayi ɗaurin Aysha Buhari ta zuba  jelar gashinta ta gefen dama dake fitar da sanyayyan ƙamshi kana ta yafa milk colour gyale akafaɗarta Hannunta riƙe da jaka Coffee haka ma takalmin Half cover coffee color jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin tularen Balila da  kuma Sedection.

    Kai tsaye Bedroom din Mommy ta nufa bakinta ɗauke da sallama tashiga ganin Mommy Bata ciki yasa ta fito tare da nufar kichen.

     

    Tsaye ta samu Mommy tana yanka albasa.

    Mommy na ganinta tace.

    “Har kin gama shiryawa?”

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Eh Mommy na gama shiryawa”.

    Jinjina kai Mommy tayi tana cigaba da yanka albarsar tace.

    “Idan kinje ki Gaishe da Ummin Asma’u”.

    Kai ta gyaɗa tare da gyara rikon Handbag din ta kana tace.

    “Insha Allah zata ji Mommy”.

    Dai-dai nan suka jiyo Sallamar Naseer afalo, cikin sauri ta kalli Mommy sai kuma ta ɓata fuska lokaci ɗaya ta nemi fara’ar dake fuskanta ta rasa.

    Kallon mamaki Mommy tayi mata kana tace.

    “Ya dai haka daga jin muryan sa kin wani tsuke fuska sai kace wanda yazo miki da wani mugun abu”.

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Babu komai Mommy”.

    Girgiza kai Mommy tayi tare da fita tana cewa.

    “A’a wa nakeji kamar Naseer mutan India”.

    Yana zaune kan kujera ya gyaɗa kai tare da cewa.

    “Eh Mommy nine”.

    Dai-dai lokacin da Khausar ta fito miƙewa yayi idanunsa akanta yace.

    “Wooow Masha Allah”.

    Sam ya mance da Mommy dake tsaye a wurin.

    Gaba ɗaya imaninsa ya tafi gareta cike da zalama ya nufi Khausar tamkar zai rungumeta yana faɗin.

    “Wowww my dear Wife you look so georoures, Fantastic, beautiful  you look so Pretty”.

    Khausar kuwa ganin yanda yake matsota zai Rungumeta yasa taja baya da sauri tare da cewa.

    “Nagode.

    Mommy kuwa kallon ikon Allah take ganin yanda baki ɗaya hankalinsa ya tafi kan Khausar da alama ya mance da tana wajen.

    Gyaran murya tayi tare da cewa.

    “A’a Naseer ka zauna mana akawo maka abin taɓawa mana”.

    Girgiza kai yayi da faɗin.

    “A’a Mommy Nagode”.

     

    Itako Khausar ɓata fuska tayi babu walwala atare da ita tace.

    “Mommy na tafi”.

    Cikin sauri ya mike tare da bin bayanta kana yace.

    “My dear Wife Ina Zakije?”.

    Ataƙaice tace.

    “Unguwa”,

    Cikin yanayin zumuɗinsa yace.

    “Bari in sauƙe ki”.

    Mommy kuwa ita kanta rawan kansa ya bata tsoro ganin yanda yake nuna zalamarsa afili kamar kura yaga ɗanyen Nama!”.

    Da sauri Mommy ta kallesa tare da cewa.

    “A’a Naseer ka bari basai ka kaita ba ai zata shiga Napep”.

    Zare ido yayi tare da cewa.

    “A’a Mommy na isa kamar ni  ace Matata tashiga Napep no, impossible kamar Matar Naseer Ibrahim ɗancanji amma ace Matata na hawa Napep Ina bai yiba bai yiba”.

     

    Ita kuwa Mommy aranta tace Ohhh wannan yaro dai Allah yamasa kurari bawai basu da arziƙinba mahaifinsa nadashi amman kurarinsa yafi kuɗin nasu yawa bashi da aiki sai cika baki.

    Khausar kuwa tuni ta fice cike da takaicin zumuɗinsa.

    Da sauri yabi bayanta yana cewa.

    “My dear Wife ki tsaya mana let me drop you”.

    Banza Khausar tayi masa tayi ficewar ta.

    Kashe murya yayi tare da cewa.

    “Dan Allah ki tsaya mai yasa kike yin haka?”.

    Ba tare data juya ba kana cikin ɗaure fuska tace.

    “A’a Uncle Naseer ka bari kawai zanje da kaina gidansu Asma’u nefa Napep ma zan shiga”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Yawwa muje kinga nima sai ingaishe da Umminta kinga dama na daɗe banga Asma’u ba yau ya kamata mu gaisa”.

    Khausar kam sake ɗaure fuska tayi tare da cewa.

    “Yaya Naseer Allah da kabari kada in saka wahala nasan baza ka rasa abinyi ba”.

    Langwaɓar da kai yayi tare da marairaice fuska kana ya karyar da murya tare da cewa.

    “Please My dear Wife allow me to escort you kinsan dai Ina ƙaunarki sannan ina son kasancewa da ke banaso kidinga nesanta kanki daga gareni”.

    Siririn tsaki taja aranta kana tayi gaba abinta domin har ga Allah zalamarsa na bata tsoro.

    Shi kuwa da sauri ya nufi Parking space tare da ɗaukar motarsa yazo ta gefenta tare da buɗe mata kana ya karyar da murya tare da cewa.

    “Please Wife to be kishigo mana”.

    Dai dai lokacin da gate man ya buɗewa Lamiɗo da Gimbiya Dadu suka shigo bisa duk kan alamu daga asibiti suke anje duba lafiyar Idonta dan bayan ta fito hannunta na riƙe da ledan magunguna da kuma tambarin asibiti.

     

    Gimbiya Dadu kuwa tun da ta sauƙa daga mota Idanunta nakan Khausar ta wani kafeta da Ido tare da sake laɓenta na ƙasa.

    Khausar kuwa cikin rawan jiki da tsinkewar zuciya tayi saurin koma wa bayan Naseer zuciyarta na bugawa da mugun ƙarfi cike da tsoro take karanta duk wata addu’a da tazo bakinta.

    Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.

    “A’a Nasiru ya dai ina zakuje kaida Mutuniyar taka?”.

    Cikin yanayin zumuɗinsa da rawan kai ya shafa ƙeyarsa tare da cewa.

    “Abbah zan kaita gidansu Asma’u ne dan banaso ta hau Napep”.

    Jinjina kai Abba yayi kana yace.

    “Yayi kyau Allah ya kiyaye hanya, Khausar sai kun dawo”.

    Kasa cewa komai Khausar tayi still tana tsaye bayan Naseer zuciyarta na cigaba da tsinkewa ganin har zuwa lokacin Gimbiya Dadu na Binta da ido burinta su haɗa Ido.

    Gyaran Murya Lamiɗo yayi kana yace.

    “Khausar shiga mota ku tafi”.

    Cikin sauri tace.

    “Toh Abba”.

    Kana ta fito daga bayan Naseer tashiga gaban motar.

    Kallon Gimbiya Dadu Naseer yayi kana yace.

    “Yafendo sai mun dawo”.

    Ya ida maganar tare da buɗe mazaunin Driver ya shiga kana yaja motar suka fice ahankali ya dai-dai ta hancin motarsa suka hau kwalta.

     

    Sai asannan ya juya ya kalli Khausar da fuskarta babu annuri kona misƙala zarratin zaman blutooth dake kunnensa ya gyara ajiyar zuciya ya saki yana bin ilahirin jikinta da kallo hannunsa ya kai tare da ranƙwafawa kanta zai riƙe yalwataccen sumar dake gefen wuyanta zai shinshina.

    Cikin sauri Khausar ta kauce tare da watsa masa wani kallo.

    Tsuke fuska yayi tare da marairaice murya kana yace.

    “Haba My Wife mai yasa zaki min haka kibari mana in sinsina gashinki naji wannan Sanyayyar ƙamshin da yake fita”.

    Sake tsuke fuska Khausar tayi tare da tura ƙaramin bakinta kana tace.

    “A’a nidai Yaya Naseer ka bari bana so”.

    Langwaɓar da kai yayi kana cikin wata murya mai ɗauke da zallan shauƙi da sha’awa yace.

    “Toh na bari ai yanda kike so haka za ayi hope dai kina sona?”.

    Ƙasa tayi da kanta tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta amma ba tace komai”.

    Sake narkar da muryarsa  mai ɗauke da zallan sha’awa kana yace.

    “Dan Allah kice kina ƙaunata ko zanji daɗi kinsan na daɗe ina dakon soyayyarki azuciyata, Khausar kece rayuwata bazan iya rayuwa idan babu keba kece muradin raina, kece fitilar dake haskaka rayuwata ina miki sahihiyar ƙauna wanda bana yiwa kaina”.

    Lumshe idanunsa yayi tare da kallon fuskarta zuwa ƙirjinta kana yace.

    “Kece wacce zuciyata keda burin kasancewa da   ita, kece farin cikina muddin ban mallakeki amatsayin matata ba bazan taɓa samun nutsuwa ba, My Khausi saboda ke nadawo Nigeria ba dan keba wlh bazan dawo ba.

    Duk yawan kyakkyawawan matan dake India babu wacce ta burgeni ta kuma kwanta min arai sai ke duk kyawunsu kallon maza nake musu!”.

     

    Ita dai Khausar batace komai ba sai wasa da take da yatsun hannunta.

    Naseer kuwa karyar da murya yayi tare da lashe lips ɗin sa kana yana binta da wani shu’umin kallo ya lumshe Idanunsa tare da cewa.

    “Khausar inada burin mallakar ki ke kaɗai ce zaki iya sarrafani, akan shimfiɗata sannan ke kaɗai ce zaki iya bani farin ciki akan shimfiɗa ta”.

    Lokaci ɗaya Khausar ta sake haɗe fuska cike da takaici tarasa Meyesa Naseer yake mata wasu irin maganganu marasa kan gado.

    Al’amarin Naseer yafi kama da irin mayaudaran mazan nan na zamani.

    Shirune ya ratsa motar har suka isa ƙofar gidansu Ummi yayi Parking daga waje, Ahankali Khausar ta ziro ƙafanta da suka sha jan lalle.

    Dai-dai lokacin Asma’u ta iso.

    Ganin Khausar yasa ta faɗaɗa fara’ar fuskarta kana tace.

    “A’a Khausisi, Lelewal tawa”.

    Murmushi Khausar ta sakar mata tare da gyara zaman gyalenta kana tace.

    “A’a ina kika je?”.

    Asma’u na gyara wuyan hijabinta ta kalli Khausar tare da cewa.

    “Wallahi kitso naje”.

    Jinjina kai Khausar tayi kana tace.

    “A lallai dai kam”.

    Juyawa tayi ɓangaren da Naseer ke tsaye ya zuba mata ido ɗauke kanta daga garesa tayi kana ta mayar da kanta kan Asma’u tare da cewa.

    “Asmeey ga Uncle Naseer”.

    Sai alokacin Asma’u ta ganesa da murmushi afuskarta tace.

    “Laa Uncle Naseer Mutanen India fatan kazo lafiya. Khausar tace min kadawo toh Allah yatemaka”.

    Kai ya jinjina cike da Iyayi kana yace.

    “Wallahi na dawo amma fa saboda My Khausi nazo, ana ɗaura mana aure kuma zan ɗauki abata mukoma can”.

     

    Murmushi Asma’u tayi tare da kallon Khausar da ta tsuke fuska kana tace.

    “Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairi”.

    Da sauri ya amsa da.

    “Ameen”.

    Khausar kuwa hannun Asma’u ta riƙe zasu shiga gida.

    Da sauri yace.

    “Ya dai haka My Khausar ba zaki tsaya mu ɗanyi hira ba?”.

    Ataƙaice ta girgiza masa kai tare da cewa.

    “A’a”.

     

    Shafa kansa yayi tare da lumshe idanunsa kana  yace.

    “Toh ƙarfe nawa zaki koma gida sai inzo in ɗauke ki”.

    Babu walwala atare da ita tace.

    “A’a ba sai kazo ba Uncle Naseer zan koma”.

    Wani irin zare ido yayi tare da girgiza kai kana yace.

    “A’a My Khausi kar ki min haka.

    Ni dai ki faɗa min ƙarfe nawa zanzo ɗaukarki”.

    Ƙaramin tsaki taja aranta tare da cewa wannan mutumin ya fiye naci afili kuma juyawa tayi ta kallesa tare da cewa.

    “Toh ka dawo ƙarfe shida na Yamma”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh shikenan My Wife sai nazo”.

    Ya ida maganar tare da shigewa motarsa yaja.

     

    Bayan sun shiga cikin gida Khausar ta juya tare da kallon Asma’u kana tace.

    “Ya dai naga kamar Ummi bata nan?”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa tare da cewa.

    “Eh Ummi ta tafi gidan Innayi. Ni kaɗai ce sai Bashir dana bari yana mana gadin gidan shiyasa ma ana gama min kitson na dawo.

    Jinjina kai Khausar tayi kana tace.

    “Ayyah yayi kyau”.

    Kai tsaye Bedroom din Asmau suka shiga fridge Asma’u ta buɗe ta kawo mata drinks da Fruit.

    Kallon Friut ɗin Khausar tayi tare da zabga ta gumi.

    Zama Asma’u tayi daga gefenta cike da kulawa tace.

    “Ya dai Khausar tunanin me kike?”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare cire gyalenta ta ajiye kana ta kalli Asma’u tare da cewa.

    “Ni wallahi lamarin Uncle Naseer ya fara damuna”.

    Asma’u na ninke hijabin data cire ta kalli Khausar tare da faɗin.

    “Mai yafaru?”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare da lumshe Idanunta kana tashiga zayyanewa Asma’u abubuwan daya yima tun daga zuwansa har yanzu daya kawota kana ta ɗaura da cewa.

    “Asma’u Uncle Naseer yana bani tsoro abubuwan da yake gwada min sun fi kama dana mayaudara idan yana wani abun tamkar yana da wani nufi akaina, sannan yana yawan nuna zalamarsa akaina, ya rinƙa wani abu kamar maye!”.

     

    Dariya Asma’u tayi tare da cewa.

    “Wataƙil tsanananin son da yake miki ne kike ganin kamar haka, kinga tun kina ƙarama kamar da wasa ya fara ce Miki matarsa har gashi girma yazo wataƙil tsananin soyayya ne sannan kinga ya zauna a ƙasar da al’adun mu ba ɗaya dana suba  kinga ƙasashen India wannan sai ahankali runguma da sumbata basu ɗauke shi abakin komai ba may be shiyasa kike ganin yake miki haka kuma kinga ai ya riƙa dole zaiso mace”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da furzar da iska mai zafi kana tace.

    “Anya kuwa Asma’u abin nasa is too hight ɗazun fa agaban Mommy saura kaɗan ya rungumeni saida na kauce”.

    Dafe kunci Asma’u tayi tare da kallon Khausar da fuskarta ke ɗauke da alamun damuwa kana tace.

    “Toh tunda har haka ne ki kiyaye al’amarin sa”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare da lumshe Idanunta kana tace.

    “Zan kiyaye insha Allah amma gaskiya ya fara bani tsoro baki ɗaya al’amarin sa azalamance yake”.

    Jinjina kai Asma’u tayi tare da cewa.

    “Amma duk da haka yana sonki”.

    Kai Khausar ta gyaɗa kana ta buɗe Idanunta dake lumshe tace.

    “Na sani Uncle Naseer na ƙaunata, amma kuma wani lokaci soyayyar tafi kama da Sha’awa”.

    Girgiza kai Asma’u tayi tare da cewa.

    “No Khausar kada ki fassara shi da haka, sannan kinga yanzu lokaci yayi da zaki bawa Uncle Naseer dama kinga dama ga Maganar da Hajja Nana tazo da ita cewa kina gama Secondary school za ayi batun Aurenki kinga yanzu munzo gangara koma ince mungama kawai”.

    Shiru Khausar tayi tare da lumshe Idanunta tana jin wani iri azuciyar ta.

     

    Asma’u ta cigaba da cewa.

    “Sannan kin gani tayi miki maganar Yayanki Aliyu idan har baki amince da Naseer ba kika fitar dashi amatsayin wanda kike soba dole Yaya Aliyu za’a liƙa miki, kuma kinga Yaya Naseer tunda ansan Asalin sa sannan ansan komai nasa, kuma ke kanki kinsan yana masifar sonki”.

    Ƙaramin tsaki Khausar taja tare da kallon Asma’u kana tace.

    “Kayya Asma’u Asalin nasa har wani kyau gareshi!?

    Mahaifiyarsa fa ƙanwar Gimbiya Dadu ce Uwar su ɗaya ubansa ɗaya, kuma duk ɗabi’u da hallayar Gimbiya Dadu babu wanda mahaifiyarsa ta bari, sannan kuma shine ɗan Auta wajenta Ni Wallahi tsoron su na nake ji wallahi nama fi tsoron mahaifiyarsan”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe  kana ta cigaba da cewa.

    “Amma shi Uncle Naseer bashi da matsala Saboda zuciya nason mai kyautata mata, shi kuma tun ina ƙara ma yake nunawa kowa cewa. Ni ta da bance ni ta musamman ce awajensa, na ɗaukesa ne tamkar wani sashina amma banjin Uncle Naseer awani mataki na daban sannan batun Yaya Aliyu kuwa gaskiya saidai Hajja Nana tayi duk abinda zatayi, amma ni bazan Aure shiba babu ta yanda zanyi na aureshi”.

    A hankali ta furzar da iska mai zafi daga bakinta kana ta kalli Asma’u da itama ita take kallo.

    Idanunta ta lumshe cikin sanyi murya tace.

    “Ni inaji azuciya ta ina da muradin da nake da ita na, musamman da nake buƙata inada muradin da nake so Asma’u ina da wani abun da nake so,  wanda ni kaina bansan menene ba.

    Amma Uncle Naseer ba irin Nature da nakeso ajikin namiji yake dashi ba dama yanada ilimi Addini kamar Yah Jameel ne to da ya tsarkaka, dama ace ɗabu’unsa irin na Yah Jameel ne da ya cikemib ko wanne gurbi”.

    Ajiyar zuciya Asma’u ta sauƙe kana tace.

    “Allah ko?”.

    Tayi mgnar a fili yayinda zuciyarta ke saƙa wasu zantukan, ita kuwa Khausar kai kawai ta gyaɗa mata.

    Cikin sauƙe numfashin Asma’u tace.

    “Allah ya mana zaɓi mafi alkhairi dai”.

    Cikin lumshe ida Khausar tace.

    “Amin”.

    Hira suka cigaba dayi, ƙarfe biyar dai-dai Khausar ta miƙe tare da ɗaukan gyalenta ta yafa kana ta kalli Asma’u tare da cewa.

    “Asma’u Ni zan tafi”.

    Saurin Kallonta Asma’u tayi tare da cewa.

    “Toh ba kince sai ƙarfe shida zaki tafi ba?,Kuma ina Uncle Naseer zai zo ya ɗauke ki!?”.

     

    Baki Khausar ta taɓe kana tace.

    “Guduwa zanyi kafin yazo ɗin dai, ai shiyasa nace masa shida kinga yanzu biyar zan tafi”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da cewa.

    “Toh idan yazo fa?”.

    Ka faɗa Khausar ta ɗage tare da taɓe baki kana tace.

    “Sai kice masa na tafi”.

    Ta ida maganar tana ficewa da sauri.

    Asma’u tabi bayanta dan yi mata rakiya.

     

    Misalin ƙarfe shida saura kwata Naseer yayi Parking aƙofar gidansu Asma’u tare da danna Hong.

    Asma’u dake sauraran zuwansa ta sanya hijabi ta fita zaune ta samesa acikin mota kana tace.

    “Bata daɗe da tafiya da taga iska ya taso”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Nagode”.

    Kana ya figi motarsa yabar layin kai tsaye gidansu Khausar ya nufa lokacin daya isa ankira maghariba direct masallaci ya wuce ya gabatar da sallah kana ya wuce gidan kai tsaye sashen Gimbiya Dadu ya shiga.

    Shigarsa ba daɗewa Haiydar ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama kana ya gaishesu tare da ajiye kulan abincin Gimbiya Dadu.

    Har ya juya zai fita.

    Naseer ya kallesa tare da cewa.

    “Please Haiydar kace da Khausi tazo zamuyi hira”.

    Kai Haiydar ya gyaɗa kana yace.

    “Toh Uncle Naseer sannan ya fita”.

    Kai tsaye masallaci ya wuce sai Misalin takwas saura kwata ya koma sashen su bakinsa ɗauke da Sallama.

     

    Khausar dake zaune kan 1sitter sanye cikin Neavy blue riga da wando na bacci mai santsi wanda ya sauƙa har ƙasa rigar kuma mai hannun Spaghetti ne kanta sanye da hular Net jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin tularen ta yayin da hannunta ke riƙe da wayar Mommy tana latsawa.

    Da sauri Haiydar ya kalleta tare da cewa.

    “Addah Khausar na manta ban faɗa miki ba, ɗazu kafin na wuce Masallaci Uncle Naseer yace. In faɗa miki kije ki same shi a sashen Gimbiya Dadu yana son ganinki”.

    Nanda nan Khausar ta canza fuska tare da cewa.

    “A falon Gimbiya Dadu kuma!?”.

    Harara Mommy ta watsa mata kana tace.

    “Toh cin yeki Gimbiya Dadu za tayi ko kuma me Ni nalura wani shan ƙamshi kike yiwa Naseer fa, idan kinsan bakya sonshi ki fito fili ki faɗa, sannan ki fito da wanda kike so, tun kafin kakar ki tazo ta buwayemu da batun Aurenki.

    Kinga dama ta ajiye target ne kina gama Secondary school magana ya ƙare za azo ayi miki aure”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙa kana ta cigaba da cewa.

    “Idan kuma kinƙi baki da hujjar da zaki ƙi Auren Aliyu, dole kibi zaɓin ta dan haka ma gwara ki tsaida zuciyarki kisan me kike ciki don in duniya duk zasu taru babu mahluƙin da zai hana batun wai kin gama secondary School za’ayi miki aure, tunda har Hajja Nana ta rantse, dan haka gwara kawai ma ki tsaida zuciyarki, ki fidda mijin da zai iya barinki kici gaba koda kinyi aure, kuma da fidda wanda kike sone, zamu samu hujjar nuna mata kinada wanda kike son”.

     

    A hankali Khausar ta janye idonta daga kallon Mommy kana tace.

    “To amma ni gaskiya ba zanje.

    Falon Gimbiya Dadu ba”.

    Ɓata fuska Mommy tayi babu walwala atare da ita tace.

    “Maza ki wuce kije idan ita kura ce to ta cinye ki”.

    Miƙewa Khausar tayi badan ranta yaso ba sai dan ganin yanda Mommy ta ɓata rai yasa ta ɗauki hijabinta dake fitar da ƙamshi sanya kana ta fice.

     

    Acan ɓangaren su Moddibo kuwa zaune suke aɗakin Innayi shi da M Jameel bayan sun kammala cin abinci Anutse ya miƙe tare da kallon Innayi da suke magana da M Jameel ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.

    “Innayi saida safe”.

    Kallon sa M Jameel da mamaki afuskarsa yace.

    “Zaka je ka kwanta fa kace?”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa tare da lumshe idanunsa kana yace.

    “Eh”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da faɗin.

    “Ok nima zan tafi gida”.

    Ahankali Moddibo ya buɗe Idanunsa dake lunshe kana yace.

    “Mu kwana anan mana tunda har ƙarfe takwas tayi”.

    Girgiza kai M Jameel yayi tare da miƙewa kana yace.

    “A’a ina so Inje gida”.

    Kallon yanayin fuskarsa Moddibo yayi tare da cewa.

    “Dan Allah mu kwana mana”.

    Ataƙaice M Jameel yace.

    “A’a tafiya zanyi”.

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauke tare da cewa.

    “Toh shikenan ni zanje in kwanta”.

    Ya Ida maganar tare da ficewa.

    Da kallo Innayi da M Jameel suka bisa har ya ɓacewa Kallonsu.

    Moddibo kuwa yana shiga falonsa yayi saurin yarfe hannunsa tare da jan tsaki  tare da jan numfashi kamar wanda yaci yaji lokaci ɗaya lips ɗin sa suka kama rawa cikin yanayin damuwa ya dafe kansa tare da cewa.

    “Ya salam³,Wannan wani irin al’amari ne meke mai wuyar ɗauka haka?”.

    Cikin mutuwar jiki ya wuce kichen tare da ɗaukan Cup ya ɗauraye ya zuba ruwan Tea kana ya yanka lemun tsami ya matse sannan ya zuba zuma ya kafa kansa ya shanye tass, ajiye Cup ɗin yayi ya fita zuwa Bedroom ɗin sa yana shiga ya kwanta ko minti ɗaya baiyi da kwanciya ba yayi saurin miƙewa ya zauna cikin sauri ya sake komawa ya kwanta tare dayin ruf da ciki cikin wani irin yanayi yasanya hannunsa duka biyu ya danne mararsa saboda wani masifaffen harbawa da yakeyi.

     

    Acan ɓangaren Gimbiya Dadu kuwa cikin sanyi jiki Khausar ta buɗe ƙofar falon tare da Sallama tana shiga ta…!

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki littafin 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, kana in saki a Group ɗin da zanke posting nashi, yar uwa koda kinga LITTAFIN SAKAYYAH A WAJE TO na satane, in dai kin san baki biya kadama ki karanta.*

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

    *By*

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 13

    Sakayyah 13

     

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 13_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama, ba haƙƙin kowa akanki. Littafin 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ɗin littafin inda zan rinƙa posting.

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

     

    Khausar kuwa cikin tsare Hajja Nana da ido ta riƙe ƙugu tare da cewa.

    “Gaskiya nikam bana son irin wannan mulkin mallakar naki”.

    Da sauri Mommy ta ɗaga mata hannu fuskarta babu walwala ta kalli Khausar kana tace.

    “Kifita, daga nan Khausar!”.

    Lokaci daya fara’ar data shigo da shi ya gushe  ɓacin rai ya mamaye mata zuciya juyawa tayi ta fice daga Bedroom ɗin Mommy ta nufi nata tana shiga Bedroom ɗin ta jiyo  Muryan Asma’u afalo.

    Kai tsaye Bedroom ɗin Khausar Asma’u ta shiga tare da cewa.

    “Assalamu Alaikum”.

    Atare Dije da Khausar suka amsa da.

    “Wa’alaikum Salam”.

    Asma’u naganin fuskar Khausar ta ware Ido kana tace.

    “Ya dai mutuniyar naga fuskarki haka?”.

    Wani abu mai masifar ɗaci Khausar ta haɗiye Idanunta akan Asma’u dake tsaye ta gyara zamanta tare da faɗin.

    “Babu komai ƙara so ki zauna”.

     

    Zama Asma’u tayi tare da tsare Khausar da ido ganin yanayin damuwa atare da ita.

    Kallon Dije Khausar tayi sai kuma ta juya ta kalli Asma’u tare da faɗin.

    “Wannan Itace Dije”.

    Murmushi Asma’u tayi Idanunta akan Dije ta ajiye Handbag din dake hannunta kana tace.

    “Sannunki”.

    Murmushi Dije tayi tare da faɗin.

    “Yawwa”.

     

    Juyawa Asma’u tayi tare da kallon Khausar kana tace.

    “Khausar wacece ban ganeta ba”.

    Muskutawa Khausar tayi tare da gyara zamanta kana tace.

    “Dije ce wacce nake baki labarin ta a Jauro Yaya”.

    Jinjina kai Asma’u tayi tare da faɗin.

    “Ohh Ayyah na tuna ta itace tazo ita da Hajja Nana suka zone?”.

     

    Khausar kuwa kai ta gyaɗa mata kana tace.

    “Eh”

    Murmushi tayi tare da faɗin.

    “Ai lallai dai kam kice muna da manyan baƙi Dije amma zamu daɗe ko?”.

    Kai ta girgiza tare da yin murmushi kana tace.

    “A’a yau zamu koma ”.

    Ware ido Asma’u tayi tare da faɗin.

    “A’a yau zaku koma kuma?”.

    Sai kuma Asma’u ta juya ta kalli Dije kana tace.

    “Shaf-shaf haka?”.

    Ita dai Khausar na gefe ta jingina bayanta da jikin gado Idanunta alumshe tana tunanin maganar Hajja Nana.

    Kai Dije ta gyaɗa tare da faɗin.

    “Eh ai da Yaya Aliyu muka zo”.

    Murmushi Asma’u tayi kana tace.

    “Ayyah ai kam munji daɗin ganinki”.

     

    Asma’u kuwa juyawa tayi tare da kallon Khausar wacce ta tsirawa waje ɗaya Idanu cike da kulawa Asma’u ta dafa kafaɗar ta kana tace.

    “Wai Meye ne kike ta haɗa rai!?”.

    Iska mai zafi ta furzar tare da kallon Asma’u fuskarta babu walwala ta saki Ajiyar zuciya kana tace.

    “Kina ji wata magana da wannan tsohuwar tazo dashi wai batun Aurena!kuji min tsohuwar nan da wani iyayi ta bari Iyayena suyi magana akai na mana ita kuma kaka wake maganarta!?”.

     

    Asma’u kuwa Dariya mai sauti tayi tare da cewa.

    “Iyeeee kice zamu sha bidiri!”.

    Dije tayi murmushi kana tace.

    “Barta dai kuma ma kinga mijin data samun ne kyakkyawa fa?”.

    Baki Khausar ta kuma taɓewa tare da wurga musu Harara kana tace.

    “Toni ina ruwana dashi?,

    Ni bana so kada ma ayimin wannan maganar tsakani da Allah shi yafara Auren yayata fa Asma’u”.

    Da sauri Asma’u ta ɗago kanta tare da cewa.

    “Addarki kuma?, Dama ba kece ƴar farin Mommy ba?”.

    Jinjina mata kai Dije tayi tare da cewa.

    “Eh ba ita bace ƴar fari Akwai Addarta Nenne Amma ta rasu kuma itama Yayanta Aliyu aka aura mata sunyi aure da shekara biyu ta samu ciki tazo wajen haihuwa ta rasu!”.

    Asma’u ta jinjina kai tare da cewa.

    “Allah sarki Allah ya gafarta mata,.

    Ohh Ashe shiyasa Mommy bata kunyar kiran sunanki nida duk atunanina kece ƴar fari har nace Mommy ƴar zamani ce bata ɓoye sunan ki”.

     

    Kai Khausar ta girgiza kana tace.

    “A’a ba nice ƴar fari ba ni ta biyu ce”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da faɗin.

    “Ohhh lalle kam kice zamu sha biki”.

    Khausar kuwa fuska ta tsuke kana tace.

    “Zaku sha bikin waye?”.

    Dariya Asma’u tayi tare da cewa.

    “Bikin ki mana”.

    Cikin haɗe rai Khausar  kai ta girgiza tare da faɗin.

    “Asma’u kiyi min fatan alkhairi mana, kina jin tsohuwar nan da shiririta da shirme wai ko bayan sallah za ayi ko menene oho?”.

    Dije kam kai ta girgiza tare da cewa.

    “Bafa cewa tayi bayan sallah ba ita dai alissafinta ki gama karatunki sai anyi idan yaso in kinaso kici gaba da karatunki sai Yaya Ali ya saki ki cigaba dayi a Adamawa bayan sallan baɗi take nufi”.

     

    Fuska Khausar ta ya mutse kana tace.

    “Aima Allah ya kiyaye abar mutum yayi karatunsa mai zurfi mana sannan ai mutum nada tsarin rayuwarsu da kuma yanda yake so ya kasance haka kawai sai atakura min”.

    Dariya Asma’u tayi tare da cewa.

    “Mu dai kar ki mana baƙin ciki ki hana mu shan biki”.

    Harara Khausar ta maka mata kana tace.

    “Ai sai kuyi shagalin ku kuka ɗai”.

    Dije na dariya ta dubi Khausar kana tace.

    “Yo ina zamuyi shagali ba Amarya ai dan ke za’ayi”.

    Baki Khausar ta taɓe kana tace.

    “Ai lalle dai kam”.

     

    Mommy ce tashiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama kallon Asma’u tayi kana tace.

    “A’a Asma’u kece yaushe kika zo”.

    Asma’u kuwa zamewa tayi daga kan gadon tare da cewa.

    “Ban daɗe da zuwa ba Mommy Ina yini?”.

    Mommy ta amsa da.

    “Lafiya lau alhamdulillah yasu Umminki?”.

    Miƙewa Asma’u tayi tare da zama agefen gadon kana tace.

    “Tace agaisheki”.

    Masha Allah Mommy ta faɗa tare da maida kallonta kan Dije kana tace.

    “Dije kizo Hajja Nana na kiranki wai zaki rakata gidan Aminiyarta”.

    Ta ida maganar tare da juyawa ta fice.

    Miƙewa Dije tayi tare da kallon Khausar kana tace.

    “Khausar mu tafi mana”.

    Fuska Khausar taya mutse kana tace.

    “A’a kuje kawai Allah ya kiyaye hanya ni bazan jeba, muyita faɗa da ita a gidan  mutane muna raba hali agidan mutane duk inda mukaje sai ansan mu”.

    Murmushi Dije tayi tare da faɗin.

    “Toh shikenan mun tafi”.

    Sannan ta fice kai tsaye ɗakin Mommy ta wuce sannan ta samu Hajja Nana atsaye.

    Hajja Nana na kallonta tace.

    “Wuce ki kira su Aliyu mu tafi”.

    Kai Dije ta gyaɗa sannan ta fice.

    Mommy kuwa Jakar data haɗa wa Hajja Nana tsaraba ta ɗauka sannan ta fice.

    A coumpund ɗin ta samu Yaya Aliyu da Yaya Abba tsaye jikin mota cike da girmamawa da kuma ladabi Ya Aliyu ya kalli Mommy tare da cewa.

    “Toh Mommy mun gode Allah ya saka da alkhairi Allah yabar zumunci”.

    Murmushi Mommy tayi tare da cewa.

    “Amin, Allah ya tsare muku hanya”.

    Hajja Nana ta amsa da.

    “Ameen”.

    Tare da buɗe bayan motar tashiga Dije ta zauna agefenta Yaya Aliyu na gefen mai zaman banza Yah Abba kuwa shike Driving suka fice daga gidan.

    Sai da Mommy taga fitar su sannan ta koma cikin gida.

     

    Yaya Abba kuwa kai tsaye gidan su Moddibo ya nufa.

    Hajja Nana nayi masa kwatance har suka isa gida suna shiga gidan.

    Cikin sauri Yaya Ali ya lumshe Idanunsa kana yace.

    “Masha Allah wlh Ina son garin Gembulan nan saboda yana da kyawun tsari dan yafi Adamawa kyawun tsari da komai akwai yanayin sanyi da daɗi”.

    Jinjina kai Yaya Abba yayi yace.

    “Aikam sosai ma”.

    Yaya Ali ya juya tare da kallon Hajja Nana kana yace.

    “Hajja Nana wannan kuma gidan  wacece ɗinkin ne?”.

     

    Murmushi Hajja Nana tayi alokacin da take sauƙa amotar ta kalli Ali kana tace.

    “Ƙawata ce tare mukaje da ita aikin hajji na farko na biyu ma tare muka je sannan ko daga baya muna yawan zuwa   Umarah tare da ita”.

    Murmushi Yaya Ali yayi tare da cewa.

    “Ai dai lalle kam kice gidan Aminiyar kice?”.

     

    Dariya Hajja Nana tayi tare da cewa.

    “A’a sosai ma kam”.

    Dai-dai lokacin da suka isa ƙaramin gate ɗin da zai sadaka da farfajiyar tsakar gidan Innayi.

    Innayi dake zaune ta hango Hajja Nana da baƙi abayanta,

    Cike da fara’a ta miƙe da sauri fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi mai cike da jin daɗi ta matso kusa da Hajja Nana kana tace.

    “Aaaa Lalle marhaba Hajjaju Makkatun Masha Allah Hajiya Nana mutanen Makka lale marhaba ku iso”.

    Ta faɗa tare da juyawa ta shiga ɗaki tare da ɗaukan lallausan Chanis capet ta shimfiɗa musu.

     

    Sai kuma ta fito cike da farin cikin daya kasa ɓoyuwa afuskarta kallon Yaya Ali tayi tare da cewa.

    “Wannan shine  Mijin namu na Adamawa da kike bamu labarin?”.

    Kai Hajja Nana ta gyaɗa tana murmushi kana tace.

    “Eh”.

    Innayi ta juya ta kalli Hajja Nana kana tace.

    “Ku shiga”.

    Sannan ta kalli Yaya Abba da Yaya Ali kana tace.

    “Ku ƙara so”.

    Ta faɗa tare da ficewa Innayi ta nufi sashen Moddibo tare da cewa.

    “Moddibo, Moddibo ga baƙi munyi”

    Shi kuwa Moddibo atare suka miƙe da M Jameel suka fito.

    Ɗan sake fuska Moddibo yayi kana yace.

    “Sannunku da zuwa ku iso”.

    ya faɗa tare da matsa musu.

     

    M Jameel na ganin Yaya Abba ya miƙa masa hannu fuskarsa ɗauke da murmushi kana yace.

    “Ha’a Abba kaine?”.

    Murmushi Yaya Abba yayi kana yace.

    “Ni ne dai”.

    M Jameel yayi dariya kana yace.

    “Sannu ku da zuwa”.

     

    Yaya Abba na bin bayansu yace.

    “Laaa Jameel nan gidan kune?”.

    M Jameel yayi Murmushi tare da shafa sajensa ya kalli Yaya Abba tare da faɗin.

    “Eh gidan mune!”

    Murmushi Yaya Abba yayi da faɗin.

    “Masha Allah”.

    sannan suka shiga falon din wanda tuni Ya Ali da Moddibo suka shiga.

     

    Innayi dake tsaye ta juya tare da cewa.

    “Moddibo zoka kawo musu abin taɓa wa”.

    Daga ciki Moddibo ya miƙe kana yace.

    “Toh Innayi”.

    Sannan ya fice tare da bin bayanta.

    Juyawa Innayi tayi tare da kallon Moddibo dake biye da ita kana tace.

    “Kashiga daga ciki ka gaida ƙawata Hajja Nana dana ke ce maka munje aikin Hajji na farko dana  biyu kuma yawanci Umarah ma tare muke zuwa ɗakin mu ɗaya tun da take zuwa gidan nan bata taɓa samunkaba,

    Kai ya gyaɗa da faɗin.

    “Na’am”.Ya ida maganar tare da shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama Idanunsa ya sauƙa akan tsohuwar da yaje ya yamata ta’aziyya a Jauro Yaya.

    Cike da nutsuwa da kuma ladabi ya zauna daga gefenta kana yasa hannu ya shafa sajensa cikin yanayin rashin walwalarsa yayi ƙasa da kansa tare da cewa.

    “Sannun da zuwa”,Ya gaisheta batare daya nuna ya ganeta ba.

     

    Hajja Nana kuwa Kallonsa tayi kana tace.

    “A’a kamar nasan wannan fuskarta fa, kwanaki kamar kunje da wani abokin Malam Liman mai suna Malam Arɗo ko?”.

    Kai Moddibo ya jinjina still Kansa a ƙasa kana yace.

    “Eh”.

    Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.

    “Ayyah sannun ka ashe dai Jikana ne Allah yayiwa rayuwarka albarka Allah yabaka zuri’a ɗayyiban”.

    Still Kansa A ƙasa ya shafa kwantaccen sumar  kansa mai sheƙi da yalƙi kana yace.

    “Ameen Ngd”.

    Ya ida maganar  a taƙaice tare da miƙewa ya fice.

    Tiren da Innayi ta haɗa Gasassun Zabbi da  M jameel yasa ta gasa musu, shinkafa da miyar dage-dage da yaji naman kaza sai Akwashi dake ɗauke da ƴaƴan itatuwa ta miƙawa Moddibo amsa yayi kana ya nufi sashen sa dashi.

     

    Bakinsa ɗauke da Sallama yashiga tare da ajiye Tiren akan center table dake tsakiyar falon kana ya maida kallonsa kan M Jameel dake ta hiran Yaushe gamo da Yaya Abba kai ya girgiza tare da cewa.

    “J miƙo musu ruwa acikin fridge ka barsu haka gashi har na dawo baka kawo musu komai ba”.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “Wallahi muna ta hiran yaushe gamo da Abba nasan sa mun taɓa haɗuwa dashi a Adamawa”.

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da jingina bayansa da jikin kushin kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.

    “Ayyah ashe kunsan juna”.

    Kai Yaya Abba ya gyaɗa alamar Eh.

    Ya Ali kuwa hankalin sa ya mayar kan wayarsa yana latsawa.

     

    Acan ɗakin Innayi kuwa zama Innayi tayu tare da kallon Hajja Nana kana tace.

    “Yanzu ma kinzo wajen jikar tamu ce?”.

    Kai Hajja Nana ta gyaɗa kana tace.

    “Eh wallahi”.

    Murmushi Innayi tayi tare da cewa.

    “Shine baki zomin da ita ba”.

    Baki Hajja Nana ta taɓe tare da faɗin.

    “Barta ba shiri muke da ita ba fitsararriya ce yanzu ma nazo ne akan batun aurenta da yayan ta amma na lura ma kamar batason abin ko yayane ohon mata kinsan ƴaƴan yanzu da tsaurin ido su suke zaɓawa kansu maza yanzu ma na barta tana can tana kumbure kumburen baki”.

    Murmushi Dije da ke kurɓan tes tayi aranta tace Dramer Hajja Nana da Khausar bai ƙarewa.

     

    Innayi kuwa murmushi tayi kana tace.

    “Ayyah ai da tazo na ganta kice mu shirya akwai shan biki?”.

    Dariya Hajja Nana tayi kana tace.

    “Ai dai kam Insha Allah akwai shan biki dan biki yana nan yana tafe”.

    Innayi kuwa kai ta gyaɗa kana tace.

    “Lallai abu yayi kyau amma dai zamu kwana”.

    Girgiza kai Hajja Nana tayi kana tace.

    “A’a yanzu ma zamu tafi dan mun sallami can kam da zan tafi da jikar tawa ma to sai mahaifiyata take ce min bata da lafiya don haka na barta saboda tana taimakawa mahaifiyar tan da ɗan aikace-aikacen yau da kullum”.

     

    Kai Innayi ta jinjina tare da faɗin.

    “Ayyah Allah yabata lafiya.

    Yaushe zamu koma Umarah bana zaki je na Ramadan?”.

    Hajja Nana kuwa kai ta jinjina kana tace.

    “Eh Insha Allahu zanje in Allah ya yarda amman ta Adamawa zan tashi kefa zakije kuwa?”.

    Murmushi Innayi tayi tare da cewa.

    “Nima zanje in Allah ya yarda amman kin san ni ta nan Jaligo zan tashi”.

    Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da faɗin.

    “Abu yayi kyau Ubangiji Allah yasanya alkhairi Allah ya bamu sa’a”.

     

    Innayi ta amsa da.

    “Ameen”,kana ta cigaba da cewa.

    “Nima zamu tafi da jikina da kuma abokinsa tare za muje”.

    Dariya Hajja Nana tayi kana tace.

    “A’a abu yayi kyau to sai mun haɗu acan ɗin”.

    Hiran yaushe gamu suka cigaba dayi yayin da Dije ke gefe tana yagar Gashesh-shen Zabbi da nonon shanu mai ɗumi.

     

    Acan falon Moddibo kuwa bayan sun gama gaisawa Yaya Abba da Yaya Ali suka sha fruit din kana suka ci gashshen Naman  dake fitar da ƙamshi tare da ruwan Tea mai zafi.

    M Jameel ya kalli Yaya Abba daya koma ya zauna tare da rufe Warmers din Cike da kulawa ya sake Kallonsa kana yace.

    “Abba ya bakuci abincin ba”.

    Murmushi Yaya Abba yayi kana yace.

    “Wallahi aƙoshe muke yanzu ma dan kar kuce munƙi cin komai ne amma Alhamdulillah”.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “Toh shikenan”.

    Miƙewa sukayi Atare jin Innayi na cewa.

    “Moddibo kufita Hajja Nana zasu wuce”.

    Da to Moddibo ya amsa kana suka fita cike da kulawa M Jameel da Moddibo suka kalli yaya Abba da yaya Ali atare suka haɗa baki wajen faɗin.

    “Toh mun gode da ziyara Allah yabar zumunci”.

    Yaya Ali ya amsa da.

    “Ameen”.

    Sannan Yaya Abba yashiga mazaunin Driver Yaya Ali kuma ya zauna gefen mai zaman Banza yayin da Hajja Nana da Dije suka zauna abaya M Jameel ya miƙa kansa ta window tare da ajiye wa Hajja Nana kuɗi akan cinyarta tare da cewa.

    “Allah ya tsare”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Allah ya muku albarka nagode”.

    Motar Yaya Abba yaja suka fice saida motar ta fita layinsu kafin Innayi, Moddibo,da kuma M Jameel suka koma cikin gida.

     

    Cikin awa biyu Hajja Nana suka isa Jauro Yaya Washe gari Da safe yaya Ali ya koma Adamawa dashi da Abba suka tafi.

     

    A ɓangaren Khausar kuwa tunda daga ranan da Hajja Nana tayi mata maganar aure ta watsar da maganar kasancewar Momynta bata sake yi mata maganar ba ita ma bata sake tada maganar ba hakan yasa bata ɗauki maganar da muhimmanci ba ita kuwa Mommy tasa aranta tun daga Ramadan ya kawo kai ta samu dama ta yanda zata roƙowa ƴar ta al’khairi idan har Aliyu al’khairi ne agareta Allah ya tabbatar mata da al’khairi idan kuma ba al’khairi bane Allah ya zaɓa mata mafi al’khairi shima kuma Allah ya musanya masa da mafi al’khairi.

     

    Yau ya rage azumi saura kwana biyu da hantsi Mommy na zaune afalo taji Sallamar sabon mai gadinsu da aka kawo kallon Khausar dake riƙe da hisnul Muslim tana Azkhar tayi sai kuma ta maida kallonta ga Haiydar dake danna wayarta ta gyara zamanta tare da cewa.

    “Haidar jeka duba lafiya Namadi ke Sallama”.

    Kai Haiydar ya gyaɗa kana yace.

    “Toh Mommy”.

    Sannan ya miƙe ya fita.

    Kallon Namadi dake tsaye yayi kana yace.

    “Lafiya kuwa”.

    Kai Namadi ya gyaɗa tare da faɗin.

    “Kayane Alhaji ya aiko dasu Azo ashiga dashi ciki”.

    “Ok kashigo dasu”. Ya faɗa tare da juyawa ya koma ciki.

     

    Kallon Mommy Haiydar yayi kana yace.

    “Kayan azumine Abbah ya aiko dasu shine Namadi zai shigo dasu”.

    Jinjina kai Mommy tayi tare da cewa.

    “Ok”.

    Da Sallama Namadi yashigo kansa ɗauke da buhun shin kafa ya ajiye a store kana ya koma ya ɗauko na ɗanyen shinka yakai, sannan ya kuma kimawa ya rinƙa shigo da catton ɗin indomie, Catoon ɗin Spaghetti, Cotton ɗin Macoroni, Couscous, Buhun fulawa, Buhun niƙeƙƙen garin gero na kunu, buhun wake, buhun sugar Corn Flakes, Madara, Patoto, Doya Crate din ƙwoyi Jarkan mai Jarkan man ja haka ya riƙa shigowa da tarkacen kayan buƙata na Ramadan.

     

    Kamar yanda ya kawo sashen su Khausar haka ya kai sashen Hajiya Bunayya.

     

    Yayinda hakan take a kowani gida haka magidanta suka riƙa shiga da kayan azumi domin shiryawa wannan wata mai falala.

     

    Acan ɓangaren gidansu Moddibo kuwa shida M Jameel amota Moddibo ke driving yayin da M Jameel ke gefen mai zaman banza sai kuma wani yaro daga baya mai suna Iro wanda ke musu aika hong sukayi aƙofar gidansu Moddibo kana suka shiga cikin gidan bayan Iro ya fita ya buɗe musu.

    Innayi na zaune atsakar gida akan kujera ƴar tsugunno taji ƙaran mota na shiga cikin harabar gidan aranta tace yau lafiya Moddibo ke shigowa da mota har cikin gidan.

    Moddibo kuwa  kusa da Innayi yayi Parking motar tare da buɗe Murfin motar ya zira ƙafarsa ɗaya awaje ɗaya kuma na ciki M Jameel da Sadik kuma suka fita kusa da Innayi M Jameel ya zauna shi kuwa Sadik Boot ɗin motar ya buɗe tare da fito da buhun far n gero,  Buhun wake, Buhun shinkafa ɗanye da gumi, Catoon ɗin indomie, Catoon, Spaghetti, Bushesh-shen kifi crate ɗin ƙwoyi, Gongwanaye mayen madara da Vournvita buhun, Sugar kwalin Lipton sai kuma naman rago da aka gyara gaba ɗaya ga kuma na shanu ga kifaye duk Sadik yasa su a fridge

     

    Kallon Moddibo Innayi tayi sai kuma ta maida kallonta kan M Jameel dake kusa da ita tayi tare da cewa.

    “Lalle kayan Azumi sun saƙƙo ga Azumi sai ƙaratowa yake yau saura kwana biyu ko uku”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.

    “Ai dai kam Innayi azumi yazo”.

    Ya ida maganar tare dasa hannu acikin aljihunsa ya ciro Bandir ɗin kuɗi kimanin dubu ɗari ya miƙawa Innayi tare da faɗin.

    “Innayi gashi babu yanda banyi da Moddibo ba yabarni in saya miki kayan Azumi amma dake ɗan baƙin haline baya so in samu lada yaƙi furrr yace komai shi zai siya gashi wannan ki riƙe kiyi yadda kika ga dama dasu”.

     

    Kallon kuɗin Innayi tare da Girgiza kai kana tace.

    “Ayyah Jameel am bana son wannan shungullan yanzu ni kuma me zanyi da wannan kuɗin kabar su Jameel am ni ba ɓuƙatar su nake ba”.

     

    M Jameel kuwa zama ya gyara tare da fuskantar Innayi da kyau kana cikin wata raunan’niyar Murya ya lumshe idanunsa tare da cewa.

    “Tunda muke tare daku tsawon shekaru Innayi daga ke har Moddibo ban taɓa ɗaukar abu in baku ku karɓa ba, duk abinda na baku sai kun mayar min dashi baya, ban sani ba wataƙil shi Moddibo yana ɗaukar Maganar Aunty Karima keyi amatsayin matakin ƙin karɓan abu awajena”.

    Lumshe idanu Moddibo yayi tare da jingina kansa da Murfin motar yana sauraron abinda aminsa ke faɗa.

    Ita kuwa Innayi idanu ta zuba masa tana nazarin kalamansa.

     

    M Jameel ya cigaba da cewa.

    “Abinda Moddibo bai saniba koya karɓi abu awajena ko karya karɓa ita gani take komai na rayuwarsa Ni nake masa dan haka gwara ma ya karɓa idan yaso ta tuhumesa da tushe”.

    Ya furzar da iska mai zafi kana ya cigaba da cewa.

    “Kema kuma Innayi ina ganin maganar mutane kike ɗauka da suke cewa Babana ke daukar ɗawainiyar ku amma ni nasan ba haka bane. Allah ne kaɗai ya barwa kansa sanin yanda kuke rayuwarku duk da aminantakar dake tsakani na da Moddibo har yau ɗin nan bansan taya kuke mu’amala da rayuwarku ba bansan ta yanda kuke samun abinda kuke biyan buƙatar rayuwarku ba kama daga karatun Moddibo kab babu aƙaramar makaranta zuwa hidimar fitanmu Makarantar waje ina sane ina kuma tunawa Naira biyar kun ƙi karɓan tallafi awajen Babana ku keyin komai abinda yasa mutanen gari suke ɗaukar haka suna lura da Moddibo ba wani sana’a yake ba sannan ana mamakin irin buƙatun da kuke yafi ƙarfin samun ku ko kuma tattalin ku Innayi!”.

     

    Dariya mara sauti Innayi tayi tare da jinjina kai kana ta tsaida idanunta akan Moddibo daya dafe kansa sai kuma ta kalli M Jameel daya dafe kansa tayi murmushi tare da cewa.

    “Abun aduhu ne Jamilu barshi kawai babu ɓuƙatar sai ansani,  shi kansa Moddibo bai san komai akan al’amuran rayuwar nan ba bare ya gaya maka”.

    Moddibo kuwa Sanyayyar Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kallon M Jameel ya buɗe masa hannunsa alamar kaji dai  nima bansan komai ba a cikin abubuwan da kake son sani.

    Sai kuma Moddibo ya numfasa tare da lumshe Idanunsa kana cikin sanyin murya mai cike da rauni ya kalli Innayi tare da cewa.

    “Kagani ni kaina ban san komai  ba kama daga lokacin dana ke karatu.

    Ni dai nasan tana min komai idan nayi magana sai tace gadon Iyayena da suka bar min ne, bansan inda ta ɓoye kuɗin ba na girma ma yanzu ta bani gadona ahannuna taƙi ko gani take har yanzu ban kai ba oho.

    Kai kuma kana tuhumata kamar acikin aminantakar mu akwai abinda nake ɓoye maka, bayan kuma J ka sani babu wani shamaƙi tsakaninmu”.

    Ya ƙarisa mgnar tare da

    runtse idanunsa a take kuma ya  buɗe su akan M Jameel da shima shi yake kallo, a hankali ya furzar da iska mai sanyi tare da cewa.

    “J ba’ayi wani abu na duniya da ni Aliyu zan iya ɓoye maka ba, aminantakar mu ta wuce babin in ɓoye maka wani abu”.

    Jinjina kai M Jameel yayi yana kallon amininsa cike da tausayawa.

     

    Innayi kuwa murmushi tayi tare da jinjina kai amma ba tace komaiba ba.

    Moddibo kuwa kallon Innayi yayi kana yace.

    “Yanzu kuma hidimar da nake kai kan ka kasan inda nake samu tunda muna aiki kuma ana biyan mu sannan kuma. Ni kaina wataran saidai inga tayi min abu misali yanzu mota dai ni bansa araina ba kafin in ankara har ta saya anyi komai kafin ma mu dawo”.

    Numfashi ya sauke  kana ya cigaba da cewa.

    “Babu yanda banyi da ita ta faɗa min ba idan ma a kuɗin gado nane tunda na girma ta bani abuna zan iya sarrafawa”.

    Hararansa Innayi tayi kana tace.

    “Anƙi abaka”.

    Shiru M Jameel da Moddibo kai ya jinjina ba tare da tace komai ba sai tsirawa Innayi ido da sukayi.

    Miƙewa M Jameel yayi yace.

    “Bari mu tafi Innayi”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Allah ya tsare”

    Suka amsa da.

    Amin

    Shi kuwa Moddibo Kallon Innayi  yayi kana yace.

    “Innayi har yanzu yarinyar nan bata zoba?”

    Jinjina kai Innayi tayi tare da cewa.

    “Dama wannan shekarar Ummin Asma’u tace in bari zata turo min Asma’u dan ƴaƴan ƙabilun in sun zo gaba ɗaya lalata sukeyi sannan basajin magana to Asma’u zata zo ta tayani”.

    Cikin kula ya kalli  Innayi  kana yace.

    “Innayi anya Asma’u zata iya ayyukan da suna da yawa fa kinga akwai abincin da za’a dinga fitarwa na masallaci”.

    Jinjina kai Innayi tayi kana tace.

    “Zamu iya ai naga Asma’u tana da kuzari kuma nima da kuzarina da kuma lafiyata zan iya”.

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Toh Allah ya temaka”.

    Ta amsa da.

    “Ameen”,Kana tace.

    “Ai girkin ma na iya tsawon kwana goma sha biyar ne zamuyi”.

    Kai M Jameel ya Jinjina kana yace.

    ”Eh haka ne Innayi”.

    Sallama suka mata sannan M Jameel ya Miƙe.

    Dama already Moddibo na cikin motar yaja suka tafi.

     

    Kai tsaye kasuwa Moddibo ya sake nufa Kallonsa M Jameel yayi kana yace.

    “Mai zamu kuma yi a kasuwa?”.

    Ba tare da Moddibo ya juya ya kallesa ba ya lumshe idanunsa kana yace.

    “Idan muka je za kaga ni”.

    Shiru M Jameel yayi har suka isa kasuwar kamar yanda Moddibo yayiwa Innayi siyayya haka ya sake sayan wasu Kallonsa M Jameel yayi tare da cewa.

    “Wannan kayan na waye haka?”.

    Anutse Moddibo yace.

    “Ina ruwanka”.

    Daga haka yaja motar suka fita kai tsaye hanyar gidan Ummi ya nufa.

    Da sauri M Jameel ya juya ya kallesa kana yace.

    “Ai baka isa ba Ummi ba zata karba ba ai kai ma idan zan kaiwa Innayi abu hana wa kakeyi”.

    Moddibo kuwa baki ya taɓe kana yace.

    “Ai ba Umminka kai ka ɗai bane harda ni dan haka kabarni in  samu lada”.

    Murmushi M Jameel yayi Amma baice komaiba.

     

     

    Koda suka isa aka shigar da kaya, M Jameel yayi wa Ummu bayanin yadda sukayi.

    Ita kam Ummi sai ta riƙa sakin murmushi bayan ta gama jin jawabin M Jameel sai kuma ta kalli uban kayan da aka shigo dasu ta juya ta kalli Moddibo daya tanƙwashe ƙafafunsa tare da sunkuyar da kansa ƙasa tayi murmushi fuskarta ɗauke da murmushi cike da ƙaunarsu ta saki ajiyar zuciya kana tace.

    “Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwar ku Ubangiji Allah ya baku ƴaƴan da zasuyi muku biyayya fiye da yanda kuke mana”.

    Atare suka amsa da.

    “Ameen”, Bayan sun sake taɓa hira suka miƙe tare da yimata sallama suka tafi…!

     

     

     

     

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 11

    Sakayyah 11

     

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 11_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE fa ya kusa ƙarewa*

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine wannan Free page ne ƴar uwa 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ɗin.*

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

    Cikin lumshe Ido Mommy ke cin perpesoup ɗin yayin da daɗinsa ke ratsa ilahirin jikinta,

    kallonta Hajiya Bunayya dake murmushi tayi tare da ɗiban romon da cokali takai bakinta kana ta buɗe Idanunta dake lumshe.

    Tace.

    “Gaskiya Yaya Nagode wallahi bakiji yanda naji daɗin Perpesoup ɗin nan ba, dama sai tunanin a binda zanci nake tuntuni sai kuma gashi Allah ya kawo ki”.

    Murmushi mai cike da Ma’anoni Hajiya Bunayya tayi kana ta muskuta tare da gyara zamanta tace.

    “Lallai de kam aidama sanyin nan saida abu mai ɗumi da ɗan yaji-yaji”.

    Yayin da aƙasan ranta wani irin farin cikine mara misaltuwa wanda har yakasa ɓoyuwa asaman fuskanta.

    Ita kuwa Mommy Sosai take cin perpesoup ɗin tana mai lumshe Idanunta yayin da daɗin sa ke ratsa har ƙwaƙwalwar kanta tace.

    “Yaya perpesoup ɗin nan yaji kayan yaji”.

    Dariya Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Dama Alhaji nayiwa nace bari na zubo miki dan nasan zaki ji daɗin sa”.

    Kai Mommy ta gyaɗa da faɗin.

    “Aikam gashi yamin daɗi sosai”.

     

    Acan ɗaki kuwa miƙewa tsaye Khausar tayi daga kan stool tare da riƙe ƙugunta ta bayan ta gama nin ke kayan asaman laɓɓannta ta furta.

    “Wash Allah!, Gashi yanzu na gama gyara kayan nan, amma Raudat na zuwa ɗaukan abu ɗaya zata wargaza shi kab, ya zama kamar ba’a taɓa gyarashi,  amma Insha Allah next time, Idan ta ƙara har gitsashi, sama Zan mayar dan kayanta, ta yanda idan tazo baza ta iya ɗauka ba sai ta kirani in bata yafiye min sauƙi”.

    Ta Ida maganar tare da fitowa falon tana riƙe da ƙugunta da hannu ɗaya yayin da ɗaya hannun ke dafe asaman wuyanta.

    Cike da mamaki take kallon Hajiya Bunayya dake zaune yayin da Mommy ta ke shan perpesoup ɗin da kaɗan ya rage asaman Plate ɗin.

     

    Cikin yanayin tashin hankali da razana Khausar ta ɗaga Muryanta tace.

    “Mommy me kike ci?”.

    Anitse Mommy ta ɗago kanta dan sam batasan ta fito ba sai da taji muryanta, gyara rikon Plate din Mommy tayi kafin tace.

    “Perpersoup ne ko zaki cine?”.

    Ita kuwa Khausar kai ta girgiza cikin rawan murya tace.

    “A’a nikam bazan ciba Mommy kekam Komai kika samu sai kinci, ba zaki tsaya ki duba ingancin sa da kuma rashin ingancin saba”.

    Baki Mommy ta sake tana kallon Khausar da Mamaki.

     

    Ita kuwa Hajiya Bunayya wani mugun Harara ta galla mata cike da tsanarta tace.

    “Komai ta samu saita ci ke kin isa ki hanata cine?, Khausar!, Khausar!!, Khausar!!! ki kiyayeni fa”.

    Ta Ida maganar tana dariya irin abin awasa takeyin sa, yayin da kuwa azuciyarta ba haka bane.

    Ita kuwa Mommy taɓe Baki tayi tace.

    “Yaya rabu da ita itama kanta kwaɗayin ya kawota ƙilan so take in bata”.

     

    Fuska Khausar ta ɓata cike da damuwa tace.

    “Wallahi nikam ba zanci ba Mommy kema Meyesa zakici, kema daga ganin abu saiki hau ci, batare da kin duba ingancin sa ba Allah ma dai yasa kinyi Bismillah”.

    Dafe kai Mommy tayi tace.

    “Aikuwa de Wallahi kwaɗayin sa yasa na shafa banyi Bismillah ba, Anma bari nayi.

    Bismillahi feh Auwalihi Wa’ahirihi”.

    Ta faɗa tare da cigaba da shan perpesoup ɗin.

    Wani banzan kallo me cike da tsana Hajiya Bunayya ta watsa wa Khausar aranta tace, shegiyar yarinya, wannan yarinyar saina bi takan ta tukunna zata gane kurenta, bari dai ingama da matsalolin dake gabana”.

    Ita kuwa Khausar kallon mahaifiyarta da har zuwa yanzu take shan perpesoup ɗin tayi tace.

    “Wai Mommy ba zaki haƙura dasha haka ba?”.

    Girgiza Kai Mommy tayi kana tace.

    “Kema Idan zaki ci ga shican akula Khausar ban hana kiba, amma wannan tambayoyin naki sun fara isata”.

     

    Ƙwafa Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Ƙyaleta bare ma ni bazan bar mata ba ina kedai ya isheki?”.

    Cikin sakin fuska Mommy ta gyaɗa kai tare da faɗin.

    “Eh Alhamdulillah ya isheni”.

     

    “Aiko buƙatar maje haji salla, ba zan bar matashi ba, tunda dai ke kinsha ai hikenan, idan tanaso ta biyoni ɗakina”.

    Ta ida maganar tare da ɗaukan kularta ta fice bayan ta yiwa Mommy sai anjima.

     

    Zama Khausar tayi agaban mahaifiyarta cikin raunin murya da yanayin damuwa tace.

    “Mommy meyesa!?, Rayuwar nan fa ba yanda kika ɗauke ta da yanda zuciyarki take ace haka na kowa yake  da munji daɗin duniyar nan fa, amma Mommy meyesa daga kawo miki abu zaki ɗauka kici yanzu kuma idan abin cutarwa ne fa?”.

     

    Kallonta Mommy tayi cikin tsukr fuska kana cikin fushi tace.

    “Khausar ki kiyayeni fa, bana son wannan baƙin halin da kike ɗaurawa rayuwarki fa. Ni bakiga ina nunawa matar nan baƙin hali ba haka zalika itama da zuciya ɗaya take zaune damu,  zaman lafiya mukeyi babu kishi bare tsangoma ko hassada, amma meyesa zaki sawa ranki rashin yarda akan n

    Me kike zaton zata cutar dani, babu abinda zata yimin dan haka ki kiyaye”.

    Ita kuwa khausar hawaye da ya cika mata Idanunta  tashiga ƙoƙarin mayarwa  sabida takaici, mahaifiyarta ta ɗauki duk kan yarda da amana ta basu, amma sukuma da wannan damar suke amfani ganin sun cutar da rayuwarta.

    Ƙasa Tayi da kanta kana tace.

    “Shikenan Mommy Komai na faɗa miki ba zaki yarda dani ba, amma babu komai Ubangiji Allah yatsareki ya kuma kareki”.

    “Ameen”Mommy ta amsa a kufule.

    Ita kuwa Khausar cikin mutuwar jiki ta miƙe tare da wucewa Bedroom ɗinta tana maijin wani irin zafi azuciyarta.

    Da kallo Mommy tabi bayanta tana ayyana abubuwa da yawa akanta, tarasa ina Khausar ta ɗauko wannan halin baki ɗaya bata da yarda muddin Hajiya Bunayya zata kawo mata abu ko Haiydar saita tsaya tana musu tambayoyi akai, da faɗin kada suci kada suyi kaza da kaza.

    Jin ƙiran sallah magriba yasa ta miƙe tashiga Bedroom ɗin ta dan gabatar da Sallah.

     

    Aɓangaren Khausar kuwa tana shiga ɗaki ta lumshe Idanunta tare da manna bayanta da jikin ƙofa.

    Hawaye masu ɗumi suka zubo mata jikinta na bata da wani makircin da Hajiya Bunayya ta shiryawa mahaifiyarta sam bata yarda da wannan perpesoup ɗin da takowo mata ba,

    shin wai ma ta wani hanya zatabi ta fahimtar da mahaifiyar?.

    Sosai ta zurfafa acikin tunanin da take har aka shiga Masallaci sai, asannan ta sauƙe gauron numfashi tare da nufar toilet cikin nutsuwa ta ɗaura alwala kana ta fito,   tare da shimfiɗa darduma duk da yanayin zullumi da take ciki bai hanata tattara nutsuwarta zuwa ga Ubangiji mabuwayi gagara Misali ba,

    bayan ta sallame ta ɗaga hannayenta biyu zuwa sama kana tace.

    “Ya Allah baka zalinci sannan kai ka hana zalunci atsakaninmu ya Allah baka gyan-gyaɗi bare bacci ya Allah kada ka bawa wannan baiwar taka daman cutar damu ya Allah ka  kare  mahaifiyata al’farma Annabi da al’ƙur’ani”.

    Kana ta shafa addu’ar tana mai zubar da hawaye har aka idar da Isha’i bata fita ba saima miƙewa da tayi ta kwanta agado lamo cike da tunanin rayuwa da haka bacci mara daɗi ya ɗauke ta.

     

    Cikin ikon Allah haka Mommy ta kwana lafiya lau batare da wani mugun abu ba, tun Khausar na jira taji Mommy tace wani wajen nayi mata ciwo ko kuma taga zubewan cikin Mommy kamar yanda Hajiya Bunayya ta faɗa taji shiru,

    hakan yasa ta watsar da abin aranta yayin da Aɓangaren Hajiya Bunayya baki ɗaya kunnenta ke sauraron jin wani labari daga bakin Mommy sai dai shiru amma tace bari ta kara jira kaɗan ta gani.

     

    Yau kwanan Mommy uku da cin perpesoup ɗin da Hajiya Bunayya ta kawo mata tana zaune a Bedroom ɗin ta cike da kasala.

    Cikin rumtse idonta ta zabura tare da dafe ƙasan maranta da yayi wani masifan murɗawa ahankali ta furta.

    “Wash! Allah na”.

    Sai kuma ta koma ta zauna tare da lumshe Idanunta yayin da hannunta na dama ke dafe asaman maranta sai ka ta miƙe  tare da fitowa falon tana takawa ahankali.

    Khausar dake zaune a asaman 3sitter Jikinta sanye da half gownt na bacci  yayin da ta tura tulin sumar kanta acikin hular Net Idanunta na kan takardan Geography dake riƙe ahannunta yayin da Nahawu ke ajiye gefe ta ɗago manyan Idanunta ta zubasu akan Mommy dake ya mutse fuska alamar bata jin daɗin jikinta, zama tayi akan 1 sitter kana a hankali tace.

    “Khausar har yanzu baki shiga ba?”.

    ta ida mgnar tana mai cije lips ɗinta.

     

    Ita kuwa Khausar kai ta gyaɗa mata tace.

    “Eh Mommy karatu nakeyi,  gobe Idan Allah ya kaimu zamu fara Exam ɗin First term, lokacin ai ya tafi amma Mommy lafiya na ganki haka?”.

    Ta ƙare mgnar tana kafe mata ido.

    Ya mutse fuska Mommy tayi tare da lumshe Idanunta still cikin na damƙarta tace.

    “Wallahi cikina ke ɗan min ciwo Khausar”.

     

    Cike da tausayawa Khausar tace.

    “Cikin ki kuma Mommy?”.

    Kai Mommy ta gyaɗa tace”.

    “Eh”.

    Ita kuwa Khausar ajiye takardan hannunta tayi tare da tsirawa mahaifiyarta ta Ido cikin tausayawa tace.

    “Mommy kodai in faɗawa Abba Azo atafi Asibiti ne?”.

    Kai Mommy ta girgiza kana tace.

    “A’a ai beyi tsanani har haka ba”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da sauƙe numfashi tace.

    “Toh Allah ya sawwaƙe”.

    Mommy da hannunta ke dafe asaman cikinta still Idanunta na lumshe tace.

    “Ameen”

    Miƙewa Mommy tayi ta koma kan 3sitter ta kwanta kamar minti biyu da kwanciyarta ta sai kuma sake miƙewa ta zauna tana yamutse fuska.

     

    Ita kuwa khausar cikin yanayin damuwa tace.

    “Sannu Mommy kode in Kira Abba ne?”.

    Girgiza kai Mommy ta kumayi sannan tace.

    “A’a tashi ki koma ɗaki nima yanzu zan shiga na kwanta”.

    Girgiza kai Khausar tayi tace.

    “A’a Mommy Zan zauna dake”.

    Lumshe idanu tayi tare da cije laɓɓanta na ƙasa tace.

    “Kada ki damu kije ki kwanta na faɗa miki naji sauƙi kuma nima yanzu zan shiga na kwanta”.

     

    Cikin sanyin jiki ta mike kana tace.

    “Saida safe Allah yaƙara sauki”.

    Mommy ta amsa da “Ameen”.

     

    Ita kuwa Khausar tana shiga ɗaki ta zube akan gadonta tare da faɗa wa duniyar tunanu, a haka bacci ya ɗauke ta kasancewar dare yaja batayi bacci ba ga kuma gajiya.

     

    A ɓangaren Mommy kuwa haka ta kwana cikin mawuyacin hali tare da murƙusoso cikin matsanancin ciwon ciki.

    Washe gari.

    Da safe bayan Khausar na idar da Sallah tayi Azkhar ta nufi ɗakin Mommy bakinta ɗauke da sallama.

    Mommy dake kishingiɗe kan darduma ta ɗago kanta tare da amsa sallamar Khausar.

     

    Kusa da ita Khausar ta tsugunna tare da riƙe hannunta tace.

    “Mommy ina kwana ya cikin naki?”.

    “Murmushin Ƙarfin hali Mommy tayi kana tace.

    “Naji sauƙi Khausar kije ki haɗa muku abin Breakfast kada lokaci ya ƙure”.

    Kai Khausar ta gyaɗa kana tace.

    “Amma da sauki Mommy kodai daurewa kike yi?”.

    Murmushi Mommy tayi tace.

    “Eh jeki shirya muku”.

    Kai ta gyaɗa sannan ta fice kai tsaye kichen ta nufa.

     

    Tana shiga tasa ruwa kadan atukunya yanda zai wadatar mata bayan ya tafasa ta ɗan zuba mai kana ta zuba Couscous kamar minti goma ta buɗe taga ya dahu yayi sar gwanin kyau, amfanin ɗiga man kenan.

    Sauƙewa tayi sannan ta buɗe fridge ta ɗauko miyan stwe da yaji naman kaza ta ɗumama sai kuma ta dauko lunch box din Raudat, Ramadan da Haiydar da kuma nata ta zuba musu, sai kuma ta koma ɗaki tashiga toilet tayi wanka Agurguje ta fito ɗaure da towel mai ɗan girma sannan ta cirewa Raudat kayanta tayi mata wanka bayan sun fito tashafa mata mai kana ta sanya mata Uniform sannan itama ta shirya cikin Uniform da yayi matukar amsar jikinta hannu Raudat taja suka fita dai-dai lokacin da Haiydar suka fito da Ramadan cikin shiri ko wannensu ya nufi inda lunch box ɗin da yake ya ɗauka kana suka fice harabar gidan suka shiga mota.

     

    Kamar ko yaushe motar na parking Khausar ta fito riƙe da hannun Raudat,

    Sai da ta kaita ajinsu sannan cikin sauri ta juya ta kama hanyar koma ajinsu daga baya taji ankira sunan ta da faɗin.

    “Lelewal ke kullum sai kowa ya riga ki shiga cikin aji ko?”.

    Ahankali ta juya tare da sauƙe manyan Idanunta akan Malam Isa dake tsayi  murmushi tayi da faɗin.

    “Ba haka bane Malam na tsaya kai Raudat ajinsu ne shiyasa”.

    Kai ya gyaɗa still Idanunsa akanta hakanan yarinyar ke burgesa ahankali yace.

    “To ki tafi kar araba musu questions paper ba kyanan”.

    Kai ta gyaɗa tare da juyawa cikin sassarfa da sanin darajar kanta take tafiya har ta isa cikin ajin.

     

    Aɓangaren Amina kuwa koda M Jameel yashiga class da niyyar raba musu questions paper ƙasa tayi da kanta ta amsa batare data kalli fuskarsa ba domin koda gaishesa ne ta dena tunda ta lura da baya buƙata kallon fuskanta, to shima M Jameel Sosai yaji daɗi da yarinyar ta daina gaishesa, dan ko kaɗan baya ƙaunar kallon fuskarta, bare kuma wata magana ta haɗa su.

     

    Acan gida kuwa tun bayan tafiyar su Khausar Makaranta cikin Mommy ya tsananta da ciwo da ƙyar ta yunƙura ta miƙe tana mai rintse Idanunta jini taga yana bin ƙafafunta da sauri ta dafe cikinta da ƙyar ta iya furta.

    “Ya Allah wannan ciwon cikin kuma na menene?”.

    Da ƙyar taja ƙafanta zuwa jikin beside drawer ta ɗaga wayarta tare da kiran number Hajiya Bunayya, kafin ya katse Hajiya Bunayya tayi picking tare da Sallama.

     

    Mommy kuwa cikin azaban ciwon da cikinta ke mata ta rintse Idanunta kana tace.

    “Yaya”.

    Da sauri Hajiya Bunayya ta katseta da faɗin.

    “Ƙanwata lafiya naji muryanki haka?”.

    cike da yarda  ta rintse Idanunta cikin yanayin azaban ciwon da cikinta keyi tace.

    “Wallahi Yaya cikina ciwo yake tun daren jiya, haka na kwana banyi bacci ba yanzu kuma gashi jini ya ɓalle min!

    Dan Allah ki faɗawa Alhj mutafi asibiti”.

     

    Hajiya Bunayya kuwa da damuwa amuryanta tace.

    “Subhanallahi! bari na faɗa masa yanzu ma kuwa”.

    Sannan ta katse wayar ta nufi ɗakin Lamiɗo ranta fari Sol burinta ya cika abakin ƙofa suka haɗu yana shirin fita.

    A take ta wani marairaice fuska kana cikin yanayin damuwa tace.

    “Yanzu Mommyn Khausar ta kirani.

    Wai jiya da ciwon ciki ta kwana yanzu kuma jini ya ɓalle mata”.

    Ai bai ma gama sauraron abinda zata faɗa ba ya ratsa ta ya wuce sashen Mommy cike da damuwa.

    Hajiya Bunayya kuwa da harara tabi bayansa kafin taja siririn tsaki ta mara masa baya.

    Tana shiga Bedroom ɗin ta samu Lamiɗo tsugunne akan Mommy da sauri ta tsugunna daga gefensa ta riƙo hannun Mommy.

     

    Cike da tausayawa kamar za tayi kuka tace.

    “Sannu Aysha ciwon ciki amma baki yi magana ba, gashi har ya tsananta jini na zuba”.

    Ta ida maganar zufa na karyo mata wanda in kagani zakayi zaton na tsananin damuwa ce, nan kuwa na tsananin farin cikin burinta ya cika ne.

     

    Lamiɗo kuwa miƙewa yayi tare da naɗe hannun rigarsa zai ɗauke ta Ganin haka ne yasa Hajiya Bunayya tayi saurin miƙewa tare da tallafo Mommy jikinta suka fita,

    agidan baya suka zauna Lamiɗo kuma ya shiga gefen mai zaman banza Driver yaja suka tafi Hajiya Bunayya sai faman sannu take yiwa Mommy.

     

    Suna isa asibitin aka karɓe su kai tsaye emergency aka nufa da ita ganin cikin ya riga ya zube yasa likitoci suka nufi wani ɗaki da ita tare da yi mata wankin ciki kana suka yi mata allurai nanda nan bacci wahala ya ɗauke ta Lamiɗo kuwa kasa Matsawa daga kusa da ita yayi ya cike da kulawa ya zauna a bakin gadon tare da riƙe tafin hannunta cike da tausayinta.

     

    Hajiya Bunayya data shaƙa ta cika kuwa.

    Wani lalataccen harara ta watsawa ƙeyansa cikin ranta tace, tabbas sai tayi wani abu akan wannan rawan jikin da yake mata.

    A zahiri kuwa dafa kafaɗar sa tayi,  ahankali ya ɗago kansa ya kalleta da idanunsa dake cike da damuwa amma baice komai ba.

    Cike da kirsa ta ƙirƙiri murmushin da bai kai zuciba kana tace.

    “Dan Allah ka rage damuwar nan, babu yanda zamuyi da ƙaddara haka Ubangiji ya tsara wannan ɗin ma ba rabo bane, ayanzu addu’ar lafiya take da buƙata awajenmu”.

    A hankali ya sauƙe nannuyar Ajiyar zuciya tare da mayar da Kallonsa ga Mommy dake bacci tamkar babu abinda ke damunta.

    Lumshe idanunsa yayi yace.

    “Ina matuƙar tausayawa Aysha tun bayan haihuwar Haiydar take fama da wannan matsalar sannan ko wanne cikin sai ya wahalar da ita kafin ya fita”.

    Da sauri Hajiya Bunayya ta katsesa da faɗin.

    “Ya zamuyi da rubutacciyar ƙaddara, ai kaga da Ubangiji yaga dama ai cikin Raudat da Ramadan ya zauna”.

    Kai ya jinjina amma baice komai ba.

    Ita kuwa cikin ɓoye farin cikinta ta sauƙe ajiyar zuciya da faɗin.

    “Zan koma gida kafin ‘yan makaranta su dawo, naga lokaci yaja amma Insha Allah anjima zan dawo”.

    Kai ya gyaɗa ba tare da yace komai ba still Idanunsa na kan Mommy.

    Hajiya Bunayya kuwa ficewa tayi ranta fari fess kana tasa Driver ya maida ta.

     

    Acan Makarantar su Khausar kuwa koda suka gama Exam ba abasu damar tafiya ba bayan sunyi sallar la’asar suka shiga haddar Alkur’ani sai ƙarfe biyar aka tashe su, kana suka shigo mota suka nufi gida, motar na parking Raudat ta fice da gudu ta nufi sashen su

    Tana shiga falo ta fara  kiran.

    “Mommy! Mommy!! na mun dawo”.

    Jin shiru yasa ta nufi Bedroom ɗinta da gudu ta buɗe ta shiga tana kiran.

    “Mommy!, Mommy!!, Ina kika shiga”.

    Still Bata ganta ba da gudu ta juya ta fito falon dai-dai lokacin Khausar kuma ta shigo ƙara sawa kusa da Khausar tayi ta riƙe hannunta kana tace.

    “Addah Khausy Ina Mommy?”.

    Kallonta Khausar tayi kafin tace.

    “Bata ɗaki ne?”.

     

    Kai Raudat ta gyaɗa mata alamar Eh,

    Sake hannunta Khausar tayi kana ta nufi kichen ta buɗe wayam tagani alamar bata nan komawa tayi ta shiga Bedroom din ta ɓude still ba tanan jikin toilet ta nufa ta manna kunnenta ajiki tare da faɗin.

    “Mommy Mommy kina ciki kuwa?”.

    Jin shiru yasa ta tura ƙofar toilet din still bata nan fitowa tsakiyar falon Khausar tayi tare dasa hannun damanta ta riƙe ƙugunta tana tunanin ina Mommy ta shiga haka, bayan tasan bata fiye fitar yamma ba kuma koda zata fita tun safe kafin su tafi makaranta zata faɗa musu bare kuma yau da suka barta bata jin daɗi.

     

    Da sauri ta kalli Raudat sai kuma tace.

    “Jirani anan ina zuwa”.

    ta faɗa tare da ficewa kai tsaye sashen Hajiya Bunayya ta nufa bakinta ɗauke da sallama tana faɗin.

    “Ummah”.

    Shigar ta yayi dai-dai da lokacin da Hajiya Bunayya ke riƙe da waya tana cewa.

    “Kedai Hajiya Lami bari buƙata ɗaya ta biya saura ɗaya, tana can kwance a asibiti cikin ya zube yabi makwarari, saura ɗayan daman  jira nake inga ya zata kaya ne ki shirya jibi zamu koma”.

    Komai Hajiya Lami ta faɗa ohon musu, ita dai Hajiya Bunayya  cikin jin dadi ta kece da wata mahaukaciyar dariya mai nuni da tsantsar farin ciki.

    Lokaci ɗaya kuma dariyar nata ya tsaya ganin Khausar tsaye, sai kuma ta katse kiran tare da kallon Khausar.

    Kafin tace wani abu Khausar tayi saurin cewa.

    “Ummah ina Mommy mu?”.

     

    Hajiya Bunayya ta wani langwaɓar da kai kana tace.

    “Ayyah Khausar am Mommy ku tana asibiti bata da lafiya wallahi cikinta ya zube”.

     

    Da sauri Khausar da kanta ke ƙasa ta ɗago ta kalli Hajiya Bunayya tana sake maimaita kalmar cikinta ya zube akasan ranta lokacin ɗaya hawaye masu zafin gaske suka cika kwarmin Idanunta.

    Sai kuma tayi saurin maida hawayen ta kafin tace.

    “Shikenan ɓuƙatar magauta tabiya hankali ya kwanta. Allah ya raya mata wa anda ta haifa. Ubangiji ya tsaresu daga sharrin mai sharrin”.

    Ta ida maganar tana ƙoƙarin fita.

    Da sauri Hajiya Bunayya tace.

    “Ke Khausar zo nan Me kike nufi?”.

     

    Anutse Khausar ta juya tare da sauƙe manyan Idanunta da suka sauya launi zuwa ja ta zubawa Hajiya Bunayya kana tace.

    “A’a Ummah babu abinda nake nufi, kawai dai addu’a ce nayi”.

    Cikin tsuke fuska Hajiya Bunayya ta watsa mata Harara da faɗin.

    “Sannan su waye ne Magautan?”.

     

    Ware hannu Khausar tayi tare  da faɗin.

    “Nikam ban sansu ba,  amma dai nasan Allah Mabuwayi gagara Misali ya sansu kuma zaiyi maganin su, domin ai bahaushe yace rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya,  suji tsoron ranan da Ubangiji zai musu kamun talala!”.

     

    Cike da Mamaki Hajiya Bunayya tace.

    “Wai Khausar me kike magana kamar habaici kike min ko kuma hannunka mai sanda!?.”

     

    Ware ido Khausar tayi tace.

    “Haba Ummah in Miki habaici kuma ayanda kike ƙaunar Mommyn mu kinfi ƙarfin habaici ko hannunka mai sanda kin wuce haka sai dai mgnar ce tazo kamar zaurance”.

     

    Ɓoyeyyen Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta saki domin tayi zaton yarinyar ta gano lagonta ne.

    Khausar kuwa murmushi tayi tare da faɗin.

    “Bari na tafi asibitin kar dare yayi”.

    Da sauri Hajiya Bunayya ta gyara zamanta Idanunta akan Khausar tace.

    “Toh kibari in ƙara sa abinci mana sai ki tafi dashi”.

    Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.

    “Toh amma bari na shiga gidan Aunty Ruƙayya kafin ki ƙarasa”.

    Kai Hajia Bunayya ta gyaɗa tare da faɗin.

    “Toh ki gaisheta”.

    Kai kawai Khausar ta gyaɗa Sannan ta wuce sashen su.

     

    Tana shiga Bedroom direct toilet ta wuce ta cire Uniform ɗin ta sannan ta watsa ruwa bayan ta fito ta dauki dogon rigar material pinch colour ta sanya, kana ta nufi kichen Agurguje ta dafawa su Haiydar jollof ɗin shin kafa da yaji bushesh-shen kifi da kayan ƙamshi nan da nan kichen ɗin ya ɗauki ƙamshi Warmers ta ɗauka ta juye sannan ta tafasa musu tea kana ta ɗura musushi, sannan ta fita falon dai-dai lokacin da Haiydar ya shigo.

     

    Kallonsa Khausar tayi tare da kiran sunansa tace.

    “Haiydar”.

    Ya amsa da.

    “Na’am”.

    Cikin sanyi tayi ƙasa da muryanta tare da faɗin.

    “Dan Allah Haiydar ka kwana anan kai da Ramadan, Raudat kuma zamu tafi da ita asibiti sai mu kwana da Mommy”.

     

    Kai ya gyaɗa mata sai kuma yace.

    “Nima ai inaso naje na dubata”.

    Jinjina kai Khausar tayi tace.

    “Ba damuwa kazo mutafi dukan mu amma yanzu zan fara shiga gidan Aunty Ruƙayya in sanar mata, idan yaso kai da Ramadan ku taho tare da Ummah,

    In yaso sai ku dawo tare amma kubar min Raudat dan zamu kwana tare”.

     

    “Toh shikenan Allah ya bata lafiya”.

     

    “Ameen”,

    Tace kana ta juya ta tafi har ta kusa fita ta sake juyawa ta kalli Haiydar dake tsaye Ahankali tace.

    “Dan Allah Haiydar ka kula, bakomai za’a baka kaci ba, akwai abinci na dafa muku sannan duk wani abu da zaku buƙata akwai”.

    Da sauri ya dafe kansa tare da faɗin.

    “Ke dai jeki da rashin yardan ki kedai haka Allah ya halicce ki baki da yarda”.

    Cikin sanyi ta girgiza kai kana tace.

    “Shikenan ni dai ban san sai yaushe zaku yarda dani ba”.

    Ta ida maganar tare da ficewa”.

     

    Kai tsaye gidan Aunty Ruƙayya ta nufa.

     

    Tare da Sallama tashiga Babban falon da yaji kayan alfarma kujerun set biyu aciki Black and Ash sai kuma babban tv plasma dake Manne abango daga ƙasansa kuma horm teater ne ƙasan falon kuma shimfiɗe yake da chanis capet.

     

    Aunty Ruƙayya dake bedroom ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tace.

    “Khausar kece sannu da zuwa, shigo ciki”.

    Da sauri tace.

    “A’a Aunty sauri nakeyi ai”.

    Cikin kulawa tace.

    “Yo yasu Mommy ki?”.

    Murmushi Khausar tayi tace.

    “Wallahi Aunty Ruƙayya Mommy ce ke asibiti bata da lafiya, shine nace bari nazo na faɗa miki, Ni yanzu ma zan wuce ko za muje tare?”.

     

    Cike da tausayawa Aunty Ruƙayya tace.

    “Ayyah Allah ya bata lafiya zanje bari ina zuwa mu tafi tare”.

    Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.

    “Toh”.

    Aunty Ruƙayya kuwa bedroom ta shiga tare kiran mijinta a waya, bayan ya bata izinine, ta ɗauko key mota da mayafinta suka fita,

    suka shiga mota,

    jingina kai Khausar tayi da jikin motar kalaman Hajiya Bunayya nayi mata suwwa akunne.

    Juyawa Aunty Ruƙayya tayi ganin yanda Khausar ta zurfafa cikin tunani yasa tace.

    “Ki riƙa yi mata addu’a”.

    Kai kawai Khausar ta iya gyaɗa mata.

    Cikin Mintuna kaɗan suka isa Asibitin bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga ɗakin da aka kwantar da Mommy saboda Hajiya Bunayya ta faɗa mata.

     

    Kwance akan gado suka tarar da ita yayin da Lamiɗo ke gefenta akan kujera hannunsa riƙe da kofin tea yana miƙa mata da faɗin.

    “Ki tashi kisha”.

    Yana jin Sallamar Khausar ya juya yana kallonta har ta isa kusa dashi.

    Cike da kulawa yace.

    “Khausar har kun dawo?”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Eh Abba ya jikin Mommy!?”.

    Sai da ya ɗan kalli Mommy dake jingine da pillow sai kuma ya mayar da Kallonsa kan Khausar yace.

    “Da sauƙi”.

    Sai asannan ya lura da Hajiya Rukayya ya ɗan yi murmushi da faɗin.

    “Hajiya Ruƙayya sannu da zuwa”.

     

    Zama tayi akujeran dake kusa da ita tana cewa.

    “Yawwa ya Hajiya Aysha da jikin kuma?”.

    Ɗan Murmushi yayi kana yace.

    “Da sauƙi”.

    Tana kallon Mommy tace.

    “Ubangiji Allah ya ƙara sauki”.

    Ya amsa da.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

     

    Khausar kuwa bakin gadon ta ƙarasa ta riƙe hannun Mommy acikin nata.

    Cikin raunin murya tare da tausayawa mahaifiyar tata tace.

    “Sannu Mommy ya Jikin?”.

    Lumshe idanu Mommy tayi kana ta buɗe su a hankali tace.

    “Da sauƙi Khausar bana jin komai in dan ta nice ma, da su sallame ni in koma gida mu kwana tare, dan bana jin ciwon cikin yayi sauƙi babu inda yake min ciwo!”.

     

    Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da faɗin.

    “Masha Allah Mommy Allah yaƙara sauƙi Ubangiji ya ƙara tsarewa ya kare”.

    A ranta kuwa cewa tace.

    Ayyah da ace duk addu’o’in da takeyiwa Mommynta tun randa taci ferfesun da ace tana haɗa addu’ar da yaron cikin wata ƙil da bai zube ba.

     

    Shafa kanta Mommy tayi cike da ƙaunar ta tace.

    “Ameen Khausar ki kwantar da hankalin ki ba najin Komai”.

    Ta faɗi hakan ganin yanda Khausar tayi zuru-zuru da ita.

    Hajiya Ruƙayyance ta kalli Mommy kana tace.

    “Hajiya Aysha ya ƙarfin jikin!?”

     

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Dasauƙi Hajiya Ruƙayya ya ‘Yar taki ya kuma rigima a makaranta!?”.

    Kallon Khausar Hajiya Ruƙayya tayi kana tace.

    “A’a yanzu ai ta daina ta fara girma!”.

    Jin haka yasa Khausar tayi murmushi.

     

    Lamiɗo kuwa miƙewa yayi idanunsa akan Mommy yace.

    “Toh shikenan bari na tafi dama ganin babu kowa ne yasa nake zaune bari na samu naje nayi wanka dan tunda muka zo ban samu na koma gida ba”.

     

    Hajiya Ruƙayya tace.

    “Ayyah ai babu komai Alhaji kaje”.

    Jinjina kai Mommy tayi tace.

    “Allah ya tsare”.

    Ya Amsa da.

    “Ameen”sannan ya juya ya fice.

    Tafiyar Lamiɗo babu daɗewa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka zo Raudat na riƙe da hannunta.

     

    Suna shiga Hajiya Bunayya ta zauna daga gefen gadon tare da kallon Mommy tace.

    “Sannu ƙanwata ya ƙarfin jikin?”.

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Ai naji sauki Yaya”.

    Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi cikin yanayin tausayawa tace.

    “Allah ya baki lafiya”.

    Hajiya Ruƙayya kuwa kallo ɗaya tayi wa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami taji sam basu kwanta mata arai ba musanman ma Hajiya Bunayya dake wani shish-shugewa Mommy.

    Ta dai daure tace.

    “Sannunku da zuwa”.

    Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka haɗa baki wajen cewa.

    “Yawwa ya mai jikin”.

    Ataƙaice Hajiya Ruƙayya tace.

    “Da sauƙi”.

     

    Hajiya Lami kuwa jikin gadon ta matasa Idanunta akan Mommy tace.

    “Ayyah Sannu Hajiya Aysha Ashe ga abinda ya faru kuma? Amma wannan abu yayi  yawa ai gwara Alhj yayi ƙoƙari ya fitar dake waje wannan matsalar ko yaushe da ansamu ciki ya zube ai babu daɗi!”.

     

    Kafin Mommy tayi magana Hajiya Bunayya tayi saurin cewa.

    “Kede bari Hajiya Lami abin nan yana damun mu, gaba ɗaya mun kasa gane menene ainihin matsalar, amma hankalinmu na tashi kullum cikin yanayin nan, abin babu daɗi yanzu ciki takwas kenan yana zubewa abin ai babu daɗi!”.

    Taɓe baki Khausar da Hajiya Rukayya sukayi alokaci ɗaya.

     

    Ahankali Mommy ta gyara matashin data kishingiɗa akai kana tace.

    “Uyummm ya za’ayi da abinda Allah ya tsara, amma ni inaga nin ba wani matsala bane, tun da gashi na haihu bayan haihuwar Haiydar ma haka nata fama da ɓare-ɓaren nan, kuma daga baya da Allah ya kawo Ramadan da Raudat an haifesu ba komai ai”.

     

    Cike da kirsa Hajiya Bunayya tayi yaƙe kana tace.

    “Hakane kam, toh Allah ya kawo masu albarka”.

    Hajiya Lami kuwa harara ta gallawa Mommy tare da taɓe baki aranta tace shegiya me iyayin jaraba keda haihuwa sai dai kiga anayi.

     

    Idanun Hajiya Ruƙayya da Khausar na kan Hajiya Lami alokacin data taɓe baki ta harari Mommy,

    Juyawa Hajiya Ruƙayya tayi ta kalli Khausar tare da jinjina kai itama Khausar kai ta jinjina.

     

    Miƙewa Hajiya Ruƙayya tayi tare da kallon Mommy tace.

    “Toh Hajiya Aysha Ubangiji Allah ya ƙara sauki sannan Allah ya tsareki daga sharrin abin ƙi ni zan wuce!”.

    A hankali Mommy ta ɗan yunƙura tare da lumshe Idanunta kana tace.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum Hajiya Ruƙayya Nagode”.

     

    Hajiya Lami da Hajiya Bunayya kuwa baki suka saki suna kallon Hajiya Ruƙayya da Mamaki aransu suka ce kaji shegiyar mata da iyayi uban wa takewa wannan addu’ar.

    Miƙewa Raudat tayi tare da riƙe hannun Hajiya Ruƙayya tace.

    “Aunty Ruƙayya ni zan biki gidanki, Inje in kwana dasu Salman tun da gobe babu makarata”.

    Da sauri Khausar ta kalli Raudat dake riƙe da hannun Aunty Ruƙayya tace.

    “Ayyah Raudat am baza mu kwana ba?”.

    Girgiza kai Raudat tayi tare da langwaɓar da kai kana tace.

    “ Ni dai Ina tsoro  ni bazan zauna ba”.

    Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.

    “Shikenan kibi Aunty Ruƙayya”.

    Murmushi Aunty Ruƙayya tayi tare da jan hannun Khausar dake cikin nata

     

    Har sun kai ƙofa Hajiya Bunayya ta ƙirƙiri murmushi tana kallon bayan Raudat tace.

    “Oohhh Raudat ba zaki bini mu tafi gida ba?”.

    Kafaɗa Raudat ta maƙale tace.

    “A’a ni zanbi Aunty Ruƙayya”.

    Aunyty Ruƙayya kuwa jan hannun Raudat tayi suka fice batare data sake jiran jin Abinda Hajiya Bunayya zata ceba.

     

    Bayan tafiyar Aunty Ruƙayya babu da ɗewa Hajiya Bunayya ta miƙe tare da kallon Mommy tace.

    “Toh ƙanwata  zamu wuce Allah yaƙara sauƙi”.

    Murmushi Mommy tayi da faɗin.

    “Nagode Yaya ahuta gajiya”.

    Hajiya Lami tace.

    “Babu Gajiya”.

    Sannan suka fice Khausar kuwa jinginar da kai tayi kamar mai bacci.

     

    Da daddare Khausar ta miƙe daga kan dogon kujeran asibitin da take kwance ta dubi Mommy da bacci ya fara fisgarta tace.

    “Mommy”.

    Buɗe idanu Mommy tayi tare da kallon Khausar tace.

    “Na’am Khausar ya akayi?”.

     

    Ajiyar zuciya Khausar ta saki tana wasa da yatsun hannunta tace.

    “Mommy baki zargi perpesoup ɗin nan da kika ci azubewar cikin nan ba!?”.

    Sosai Mommy ta tsira mata ido na second uku zuwa biyar sai kuma ta miƙe daga kwanciyar da take Atake fara’ar dake fuskanta ya gushe cikin ɗaure fuska cikin kakkausan Murya tace.

    “Khausar!, Khausar!!, Khausar!!!, Ki cigaba Nagode da abinda kike min Khausar, duk irin tarbiyyan da nake baki fatali kike dashi ko, kina ɗaukar rashin yarda kina ɗaurawa mutane ki sani Manzon Allah (S.A.W) Yace.

    :Azzana zambu walau kana haƙƙun”.

    Khausar kuwa ƙasa da kai tayi hawaye masu zafi suka cika Idanunta shin sai yaushe mahaifiyarta zata amince da gaskiyar da take so ta sani akan Hajiya Bunayya basa ƙaunarta cutar da ita suke sonyi.

    Cikin sanyi murya tare da rauni gami da ban haƙuri tace.

    “Shikenan Mommy kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyarki”.

    Mommy bata tanka taba ta juya ta gyara kwanciyar, ta itama Khausar juyawa tayi ta kwanta zuciyarta babu daɗi.

     

    Washe gari  Alhamis Da safe Dr ya shiga ya basu sallama dan jikinta yayi sauƙi Sosai Lamiɗo da kansa yaje ya maido su gida.

    Suna dawowa Hajiya Bunayya ta shigo hannunta riƙe da babban Warmers da tayi Perpesoup ɗin Kaji ta shigo dashi.

    Zama tayi akan 2sitter tace.

    “Sannu ƙanwata ya ƙarfin jikin?”.

    Mommy tayi yar dariya tare da faɗin.

    “Jiki yayi sauƙi Yaya sai faman hidima kike dani kamar wacce tayi haihuwar farko?”.

    Dariya Hajiya Bunayya tayi da faɗin.

    “Ai mai ɓari yafi son akula dashi fiye da mai haihuwa”.

    Khausar dake tsaye duk takaici ya gama cikita gashi babu dama ta faɗawa mahaifiyarta gaskiya sai ta hau kanta da faɗa bayan da ta iya daga ƙarshe ma Saboda takaici kawai sai ta koma Bedroom ɗin ta ta fara karatu.

     

    Wunin ranan haka Hajiya Bunayya ta yini tare da Mommy ta cigaba da kulawa da ita.

     

    Washe gari juma’a dai-dai lokacin da maza suka tafi Juma’a dai-dai lokacin da kowa ya tafi Sallar juma’a Akuma lokacin ne Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka tafi gidan Boka Kar’uzu.

     

    Khausar da Mommy ne zaune suna hira sosai jikin Mommy yayi ƙarfi abinka da mai juriya ga kuma kulawa da take samu.

    Sallamar Aunty Ruƙayya ya katse musu hirar da suke.

    Khausar ta faɗaɗa fara’ar fuskarta kana tace.

    “Aunty Ruƙayya sannu da zuwa ina Affan?”.

    Murmushi Aunty Ruƙayya tayi tana zama tace.

    “Affan yana lafiya bacci ma yake ya mai jikin”.

    Khausar tace.

    “Jiki da sauƙi”.

    Aunty Ruƙayya tace.

    “Masha Allah Ubangiji ya ƙara sauki”.

     

    Cikin sakin fuska Mommy ta gyara zaman hular dake kanta tace.

    “Hajiya Ruƙayya sannu da zuwa ya gajiyarki?”.

    “Hajiya Ruƙayya tayi murmushi da faɗin.

    “Babu gajiya ya jikin naki?”.

     

    “Jiki yayi sauƙi ya yara?”.

    Alhamdulillah ta bata amsa.

     

    Khausar kuwa miƙewa tayi cikin neman izinin tace.

    “Ayyah Mommy zanje gidan su Asma’u?”.

    Ido Mommy  ta zuma mata, na tsawon second bakwai tana kallonta kana tace.

    “Toh yayi kyau”.

     

    Khausar kuwa juyawa tayi ta shiga Bedroom Dogon rigar dake jikinta ta cire tare da ɗaura towel tashiga toilet,

    shawer ta ɓude ta sakarwa kanta ruwan ɗumi,

    ta ɗauki kusan minti shabiyar kafin ta fito ɗaure da towel da tsawon sa bai wuce gwiwar taba yayin da ƙarami ke kanta tana tsane ruwan kanta.

    Stool ta janyo ta zaune tare da goge ruwan jikinta ta ɗauki Vassiline lotion ta shafa kana ta ɗauki powder ta shafe sai kuma Kajol ta zizara a idanunta mascara ta ɗauka ta taje gashin Idonta da sukayi tsayi tamkar tasa Eyelashes golb mai sheƙi ta ɗauka ta shafa asaman pinch lips ɗin ta sai yayi kamar jan baki ta shafa kallon fuskarta tayi a mirrow sosai tayi kyau.

    Miƙewa tayi ta nufi jikin durowar ta buɗe uban kayan dake ciki ta zubawa ido ahankali Idanunta suka sauka akan wani Less Coffee da aka masa adon cycle da rastin Milk colour ta janyo ta sanya Masha Allah Sosai ɗinkin less ɗin ya mata kyau tare da fitar da shape din jikinta skirt ɗin ya zaune ɗass ajikinta tare da fitar mata da tsarerrenn ƙugunta haka ma rigar ta zauna ɗass ajikinta ɗan kwalin ta ɗauka tayi ɗauri mai kyau sai kuma ta ɗauki glaye medium size milk color kana ta feshe jikinta da turarukanta masu daɗin ƙamshi.

     

    Falon ta fita tun kan ta isa Aunty Ruƙayya ta ɗago kanta tare da tsira mata Idanunta jin ƙamshin daya ratsa hancinta ta saki murmushi kana tace.

    “Iyeee Masha Allah Khausar irin wannan kyau sai kace preety  ta ƙasar India”.

    Hannu Khausar ta sanya ta rufe fuskarta tana dariya sai kuma ta buɗe tace.

    “Kai Aunty Ruƙayya Ina Zan samu koda rabin kyawunta ne?”.

    Ware ido Aunty Ruƙayya tayi kana tace.

    “Allah kuna kama dan da zakije India ma cewa za’ayi ke ƙanwarta ce, har rawan kanki ma irin natane a Film ɗin Chori-Chori Cubke-Cubke ne”.

    Mommy Kam murmushi take musu batare da tace komai ba.

     

    Khausar kuwa Murmushin jin daɗi tayi tare da tsugunnawa ta ɗauki wayar Mommy tace.

    “Mommy zan tafi da wayarki”.

    Kai kawai Mommy ta gyaɗa mata sannan ta ɗauƙi wayar tare da faɗin.

    “Na tafi”.

    ta ida maganar tana gyara zaman Handbag din Hannunta tare da ciro earpiece aciki

    Suka haɗa baki wajen faɗin.

    “Adawo lafiya”.

    Kai ta jinjina tare da ficewa,

    Abokin gate ta haɗu da Haiydar riƙe da MP ɗin sa, cikin sauri tace.

    “Yauwa Haiydar dan Allah aramin MP ɗinka”.

    Cike da mamaki ya zuba mata ido tare da cewa.

    “Yau kuma to ke kuma da ba jin kiɗa ya dameki ba, me zakiyi dashi?”.

    Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.

    “Wallahi yau dai shauƙi nakeji zanje wurin Asma’u mu ɗan rausaya”.

    Murmushi yayi yana mamakin wai yau Khausar ce da cewa zata sha ƙiɗa, kawai miƙa mata yayi. Tare da cewa.

    “Kuma kikasa gyale ko?”.

    Cikin daɗi tace.

    “Ngd kai rabani kullum mutum liƙe da hijabi kamar maitakaba” na mgnar  tana fita  ta tari adaidaita sahu ta shiga.

     

    Acan ɓangaren Moddibo kuwa bayan an idar da Sallah juma’a ya kalli M Jameel dake Driving yace.

    “J yakamaya muje mu gaida Ummi kafin mu koma gida!”.

    Kai ya Jinjina  kana yace.

    “Dama abinda nake son faɗa kenan ka rigani”.

    Gyara zama Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa yana sauraron ƙira’ar dake tashi amotar kana ya shafa sajensa yace.

    “Muje toh”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da juya akalar motar zuwa unguwar su Ummi.

     

    Suna cikin tafiya wayar M Jameel ya hau ruri yana duba screen ɗin wayar yaga Bahrain ba suna sai Number Dariya M Jameel yayi still hankalinsa nakan Driving din yace.

    “Jalaludden! Wallahi Jalaludeen!!  nayi mana abinda ransa keso”.

    Moddibo da Idanunsa ke lumshe yayi ɗan guntun Murmushi ba tare daya buɗe idanun ba yace.

    “Toh ka ɗaga mana kar ya yanke”.

     

    Picking M Jameel yayi tare da Sallama.

    Amsawa Jalaludeen yayi  da faɗin.

    “Idan kun isa ku gaishe da Ummi”.

    M  Jameel yayi Murmushi kana yace.

    “Kana biye da mu ne?”.

     

    “A’a bana biye daku na dai rigaku zuwa na gaisheta”.

    Cewar Jalaluddeen

    Dariya M Jameel yayi sai kuma ya zare ido yace.

    “Wallahi Jalaludeen kada ka razana mana tsohuwa!”.

     

    Murmushi Jalaludeen yayi yace.

    “A’a bazata ra zanata ba sannan ba zata tsorata ba ai mun taɓa zuwa tare daku baku dai sani bane kuma na bayyana mata ta ganni”.

     

    “Wallahi Jalaludeen ka kiyaye mufa”.

     

    Dariya Jalaludeen yayi kana yace.

    “Tare dai mukayi sallama jumma’a a sahu daya.

    Yanzu kuma Na dai hango ku ahanya zakuje yanzu ina katakon nan?”.

    Da sauri M Jameel yace.

    “Wani katakon?”.

    Cike da tsokana Jalaludeen yace.

    “Katakon dake gefenka”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da kallon Moddibo yace.

    “A.J ɗin nawa ne katako?”.

     

    “Eh inba katako ba shi menene? ka faɗa masa cewa akwai furen dake ƙoƙarin tsiro a jikinsa tun daga ƙasa har ya isa zuciya ya gab da kanshi tuni ma ya ratsa zuciyarsa amma bai sani ba”.

    Murmushi M Jameel yayi  tare da kallon Moddibo da still Idanunsa ke lumshe kamar mai bacci kana yace.

    “Wai yace in faɗa maka akwai furen da zai fito tsakiyar kanka yama ratsa zuciyarka”.

    Sai asannan Moddibo ya buɗe idanunsa ya kalli M Jameel tare da faɗin.

    “Ka ganni karabu dani da kalaman Jalaludeen, shiya sani can yaje yata faman maganganunsa da baza ka gane kansu ba bare gindinsu ya riƙa yi mana maganar damu mutane zamu gane ba sai wanda sai sune masu ganewa ba”.

     

    Dariya Jalaludeen yayi yace.

    “Zaka gane ne ai lokaci ne yana zuwa”.

    Dariya M Jameel yayi tare da hong aƙofar gidan Ummi ganin shiru ba’a buɗe masu bane yasa, M Jameel fitowa ya buɗe, kana ya dawo yaja motar still kafaɗarsa saƙale da wayar

    Jalaludeen ne yace.

    “Ku gaishe da Ummi idan kun shiga”.

    Sannan ya katse wayar kana shi kuma ya kutsa kai cikin gidan.

     

    Dai-dai lokacin da a dai-dai-ta ya ajiye Khausar kudinsa ta basa tare da buɗe ƙaramin ƙofar dake maƙale da gate ɗin tashiga,

    Batama lura da babban gete ɗin dake ɗan buɗe ba,

    ganin mota a fake a harabar gidan yasa ta isa wajen kasancewar glass ɗin tink-tenk ne yasa bata fahimci da mutane aciki ba rawar kanta kuma ya hanata fahimtar alamun yanzu motar ta tsaya.

     

    Jikin gefen mai zaman banza ta nufi tare da kallon fuskarta ajikin mirrow sai kuma ta juya manyan Idanunta kalaman Aunty Ruƙayya suka dawo mata kunne tana kama da Preety matsa pinch lips ɗin ta tayi tare da lasa kadan sai kuma ta juya manyan Idanunta.

    M Jameel kuwa dake mazaunin Driver  murmushi ya saki domin  ya tabbata bata san da mutane aciki ba.

     

    Acan ɓangaren su Hajiya Bunayya kuwa zaune suke gaban boka Kar’uzu  cikin tsananin ɓacin rai da fushi Boka Kar’uzu ya buga musu wata razananniyar tsawa cikin sautin muryarsa mara daɗin sauti

    bayan ya gama sauraron Hajiya Bunayya yace.

    “Ai seda na faɗa muku aduk lokacin data fara aiki da maganin kada tayi alwala da sallah na tsawon wata ɗaya amma saboda taurin kai kuka bari tayi alwala tayi sallah shiyasa yake kallon fuskar ta kamar na ƙonennen Biri”.

    Atsorace Hajiya Bunayya ta juya ta kalli Hajiya Lami da itama ɗin Iran take kallo.

    Sun kasa hafimtar sharrin boka na wasa da hankali da ƙarya sun kasa tuna sam bai faɗa musu hakanba a lokacin, su kasa aminta mgnar boka dubune babu gsky ko ɗaya sai yaudara da taɓewa.

     

    Acan ɓangaren su Moddibo kuwa sake kallon madubi Khausar tayi tare dasa hannu ta gyara man lips ɗin ta sai kuma danna MP ɗin cikin Sa’a kuwa sautin waƙar BUGA ya fara tashi.

    A hankali ta gyara tsayuwar ta, tare da fara jujjuya ƙugunta a hankali tana mai rausaya jikinta.

    Zuwa tsakiyar waƙar kam fa da abu ya jiƙa, sai ga mayafinta bisa kafaɗarta gefe ɗaya, sosai take jujjuya mazaunenta tare da motsa dukkan jikinta, tana mai kallon kanta a madubi.

    Sai kuma ta kalli Glass ɗin tare da ɗaura bakinta akai ta saki zazzafan  kiss muahhhh.

    Shi kuwa Moddibo dake zaune idanu ya zuba mata tare da manna kumatunsa adai-dai glass ɗin sai kuma hakan yasa lips ɗinta sauƙa kan….!

     

     

    FREE page sun kusa ƙarewa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA ki biya 1k dinki ya isheki

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 18

    Sakayyah 18

     

    SAKAYAH

     

    18

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

    Spjt. Rungume juna sukayu tamkar zasu shige cikin jikin junansu, yayin da ruwan sama kuwa ke cigaba da sauƙa tamkar da bakin ƙwarya, kana ga walƙiya da tsawa dake cigaba da sauƙa.

    Moddibo shi kam baki ɗaya ya burkice ya rasa tunaninsa, na wushin gadi, gaba ɗaya jinshi yake a wata duniya ta da ban,

    ga wani matsanancin tsoro daya lulluɓe sa kana ga wani baƙon yanayi da yake ji yana yawo agaba ɗaya ilahirin ajikinsa, wani irin rawa lips ɗin sa keyi tamkar mai jin tsananin sanyi, ga kuma wani irin azabebben buguwan da zuciyarsa keyi da masifaffen ƙarfi yana bada sautin  dib-dab-dib-dab.

     

    Haka zalika Khausar dake rungume dashi, itama haka zuciyarta ke bugawa,

    sake ƙanƙamesa tayi da ƙarfi tana mai tura kanta afaffaɗan ƙirjinsa da bottle din gaban rigar suka buɗe, hakan ya bawa fuskarta damar mannewa farar afaffaɗan ƙirjinsa dake ƙawace da tattausan gashi baƙi mai sulɓi.

    Wani irin fusga numfashinta keyi saboda tsananin tsoro da firgici da tashin hankali, haka yasa idan taja numfashin sai ta ɗauki sekon talatin Kafin ya dawo.

    Ko kaɗan Moddibo bai da wani kataɓus sabida yanayin da suka kasance a ciki, sake rungumeta yayi tare da cusa kansa atsakanin wuyanta da kafaɗarta.

    Daga can bayansa yake jiyo sautin ƙaran mota tana danna masa ɗiyyyyttt-ɗiyyyytttt, yasan shi akeyiwa hon ɗin, amman sam baya jin zai iya koda kwakwaran motsine.

    Shi kuwa mai motar dake bayansa, ganin shiru bai motsa bane, yasa ya ɗan ratsa ta gefensu ya fuce yana dan leƙawa ganin ko lafiya kasancewar. Atsakiyar titin suke ganin babu wani alamun hatsari ko damuwa yasa ya wuce.

     

    Moddibo kuwa da ƙyar ya iya buɗe Idanunsa tare da ɗago kansa still ruwan ake sheƙawa zuwa yanzu harda  ƙanƙara yana jin yanda sautin ƙanƙarar ke sauka asaman motarsa fat-fat-fat ko kaɗan baya kallon komai duk da kuwa gashi idanunnasa abuɗe suke, amman ina ganinsa ya ɗauke makanta ta meye gurbin ganinsa, ya zama sam baya gani, kana ji yake jikinsa kamar shanyeyye.

    Daƙyar ya iya ɗaga hannunsa tare da dafe kansa da yake jin wani irin jiri na fizgarsa tare da sarawa, da sauri ya sake sunkuyar da kansa akan wuyanta kana ya sake rungumeta da ƙarfi baki ɗaya ya rasa wani irin yanayi yake ciki.

     

    Khausar kam sam batama san wani irin yanayi take ciki ba sam bata cikin hayyacinsa, hakan yasa ta sake rungume Moddibo da ƙarfi,

    Jin yadda take liƙewa a jikinsa ne, yasa shima ya saƙe yi mata wani irin amintaccen rugguma tare da fesar da wani irin raunataccen numfashin yana mai shaƙan ƙamshin jikinta.

    Itama sake rungumesa tayi cikin mawuyacin hali tana neman numfashi domin numfashinta na ƙoƙarin ɗauke wa gaba daya tsananin tsoro da tashin hankali ya bayyana asaman fuskarta, duk da sanyi garin da kuma yanda ake tsuga ruwa amma goshinta na na tsastsafo da zufa kana jikinta ya ɗauki ɗumi.

     

    Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa da ficewar hayyaci Moddibo ya sake rungumeta yana jin ɗumin jikinta kana yana mai furta.

    “Hasbullahu wani’imal wakin, Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n La’ilaha Illah anta subhanaka Inni ukuntu Minal Zhalimin, Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha”,Kana ya cigaba da karo to duk wata addu’a da tazo bakinsa cikin fitar hayyaci, Allah ya sani kuma shine shaidarsa ya rasa yanayin da yake ciki shin mutuwa zaiyi ne, koko kuma sumewa yake shirin yi,

    domin jinsa yakeyi  tamkar yana tafiya cikin sararin samaniya ne bisa gajumare,

    ji yake tamkar fuka-fuki garesa ya kasa tantance shin mafarki yake ko kuma azahirance ne kana yakasa tantance shin a sumen yake ko kuma amace yake, cikin rashin sanin madafa ya cigaba da karanto duk wata addu’a da tazo bakinsa.

    Yayin da numfashi Khausar ke cigaba da fusga,

    adduo’i ya cigaba dayi cikin ikon Allah Albarkanci Adduo’i da yake da kuma zuciyar namiji dake da dakiya yasa yafara dawowa hayyacinsa amma still Idanunsa basa gani mai kyau.

     

    Ganinta kwance ajikinsa tana fuzgar numfashi yasanya shi sa. Lallausan tafin hannunsa ya tallabo fuskarta tare buɗe manyan idanunsa da ƙyar dan har yanzu dishi-dushi yake gani, idanu ya tsirawa kan goshinta daya tsats-tsafo da zufa, sai kuma ya rumtse idanun da karfi kana ya buɗesu tare da zura ido na daƙiƙu bakwai sai kuma ya juya idanun zuwa kan wuyan hijabinta daya zame daga kanta zuwa kafaɗarta yalwataccen sumar kanta mai tsayi da ƙamshi ya zuba agadon bayanta, yayinda saura kuma ya zuba asaman fuskarta, kallonsa ya mayar kan fuskarta jin, yanda numfashinta ke fusga. Idanunsa ya mayar kan ƙirjinta da sauri ya lumshe idanun sai kuma ya buɗesu, ganin yanda numfashinta ke hawa da sauka alamun zata sume a ko wanne lokacin.

     

    Ganin tana gab da sumewane ya sanyashi sun kuyar da kansa kaɗan, zuwa kan fuskarta kana ya ɗaura lips ɗin da suke masifar  rawan sanyi akan karan hancinta, lumshe manyan idanunsa da suka sauya launi zuwa ja yayi, tare da fesa mata sanyayyan numfashinsa domin dai-dai ta mata nata numfashin, domin  duk da tsoron da kuma firgicin da yake ciki hakan, bai sanya numfashinsa ɗauke wa ba, kana yana kallon fuskarta wanda akowani lokaci zata iya suma, sai kuma ya sanya hannu ya toshe hancinta tare da ɗaura sanyayyan lips ɗin sa akan nata ya riƙa hura mata iskar bakinsa mai ɗumi da kamshi ceto rayuwa zuwa gareta,

    Wani irin dogon numfashi taja mai nauyi tare da fesar dashi da ƙarfi, cikin daƙiƙu kaɗan numfashinta ya soma dawowa dai-dai kana duk abinda ke faruwa idanunta na lumshe.

    Sannan har zuwa lokacin hannunta na kan mararsa, saman yatsarta na kan hudan cibiyarsa, sannu ahankali numfashinta ya dai-dai ta sai dai har zuwa lokacin bata dawo hayyacinta ba,  still kuma ruwan ake cigaba dayi tamkar da bakin ƙwarya ita ko sai wani irin sakewa tayi tare da lafewa a jikinsa tana shaƙar ƙamshinsa.

    Shi kuwa Moddibo sannu ahankali ya fara dawowa hayyacinsa da nitsuwarsa.

    Sake lafewa Khausar tayi ajikinsa tare da lumshe Idanunta domin ganin abun take kamar mafarki, ko kuma mutuwa tayi tsaban masifar tsoron rugugin da take.

     

    Shi kuwa Moddibo sannu ahankali cikin ikon Allah ya dawo hayyacinsa, kana har zuwa yanzu tsikar jikinsa na tashi yayin da kansa ke juyawa jiri na ɗibarsa.

    Ahankali ya sauƙe idanunsa akanta data manna a ƙirjinsa, yayinda  tattausan suman kanta ya baje aƙirjinsa, kallonta yakeyi kamar ya samu sabuwar halitta, kana aƙasan ransa ke mgnar zuci,

    Wai yaya haka ne? Mekw faruwa? Wai ma waye ni?

    Ya tambayi kansa da kansa,

    Kaine Moddibo, sannan wannan Khausar ce kwance ajikika tana rungume dakai cikin yanayin da ma’aurata ne kaɗai ya halatta su kasance ciki.

    Wani sashi na zuciyarsa ya bashi amsa.

    Lokaci ɗaya kuma jikinsa ya sake ɗaukar rawa far-far tamkar wanda ake sheƙa masa ruwan ƙanƙara lips inshi kuwa, wani irin masifeffen tsuma sukeyi,

    lumshe idanunsa yayi jin jikinsa babu kuzari kona misƙala zarratin, ji yake tamkar an zare masa lakar jikinsa cikin sanyi da rashin kuzari dake tare dashi.

    A hankali ya sake birkitota tare da ɗago kanta ya ɓanɓareta daga jikinsa gani yayi Idanunta alumshe.

     

    Ita kuwa Khausar ji take tamkar cikin bacci take, ko kuma suma ta kasa fahimtar kalar yanayin

    da dai take ciki,

    Shi kuwa Modibbo kanta ya tallabe da hannunsa ɗaya yayin da ɗaya hannu yake ɗan marin  fuskar yana faɗin.

    “Ke! Keh!!”.

    Shiru bata motsaba, hakan yasa ya sake ɗan fizgo muryasa tare da faɗin.

    “Khausar! Khausar!!”.

    har zuwa lokacin tana rungume jikinsa

    For the first time arayuwarsa da bakinsa yafara kiran sunanta.

     

    Fuskarta yake ɗan yiwa ƙananan maruka ahankali kana cikin wata Sanyayyar murya mai cike da tattausan lafazin yake fadin.

    “Khausar!, Khausar!! Khausaaaar!!!”.

    Lumshe idanunsa yayi shi kansa bai san yana da irin wannan raunataccen muryar ba, ya rasa taƙamemmen yana yin da yake ciki, yayin da aƙasan ransa so yake ya mata faɗa da tsawa da masifar ta sauƙa jikinsa, amma ya kasa kasancewar har zuwa lokacin bai gama dawowa cikin ainihin nutsuwarsa ba.

    Kumatunta ya cigaba  da ɗan mara yana faɗin.

    “Khausar!, Khausar!!”.

    A hankali kanta ya zame  daga hannunsa ya tafi gefe luuuh kamar sumammiya.

    Lokaci ɗaya zuciyarsa ta buga da ƙarfin gaske tare da jin tsinkewar zuciya ganin yanda Kanta yayi kamar ta mutu!.

     

    Cikin ɗaga sautin murya ya sake ɗan marin kuncinta tare da cewa.

    “Khausar, *Lelewal*”.

    Khausar kuwa still Idanunta na lumshe take Jin sautin muryar Moddibo na kiran sunanta kamar amafarki ko kuma daga can sama.

    Sai kuma ta sake jiyo sautin muryarsa da alamun kiɗima yake  cewa.

    “Ya salam Lelewal meya faru? me ya sameki?”.

     

    Ahankali ya sanya hannunsa tare da ture hijabinta kana ya sanya hannunsa aƙirjinta wanda har yana iya jin tudun caɓɓullen ta ahannunsa ji yayi ƙirjinta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi.

    Hannunsa ya cire tare da sunkuyar da kansa har suna shaƙar numfashi bakin juna, bakishin yakai kan kunnenta kamar meyu mata raɗa yake faɗin.

    “Lelewal tashi! Lelewal buɗe idonki!! Lelewal kalleni”.

    Lumshe Idanunsa yayi akaro na barkatai tare da kai bakinsa cikin kunnenta kana cikin Sanyayyar murya mai taushi yace.

    *“Fattanah!”.*

    Dogon numfashi taja tare da sauƙe nan-nauyan ajiyar zuciya tare da buɗe Idanunta sai kuma ta sake runtsesu da sauri gani take tamkar har yanzu rugugin akeyi kana walƙiyar zai iya kashe mata Idanu.

    Bayan kamar daƙiƙa ɗaya ta sake buɗe Idanunta still yana ronƙofe akanta yana shaƙar ƙamshin numfashin dana gashinta dake baje.

    Yayin da har zuwa yanzu hannunta ke cikin sa yatsunta guda uku nakan cibiyarsa tafin hannunta da sauran yatsu biyun nakan ainihin mararsa ta danne.

    Cikin wata sanyayyar murya ya tsira mata idanu tare da faɗin.

    “Lelewal”,Ya faɗa still yana tallafe da kanta.

    Buɗe Idanunta tayi sai kuma ta sake rufewa,

    Akuma dai-dai lokacin Moddibo da itan duk suka gama dawowa cikin hayyacinsu tare da nutsuwar.

    Cikin sauri tare da fushi

    Moddibo ya kalleta a tsawace yace.

    “Keee!!! Tafi can Mage uwar fitina tashi akaina ko in kakkaryaki”.

    Ya dire mgnar cike da tsawa tare da yarfa mata mari da bayan hannunsa.

    Shi kansa jin maganar yayi ta fito daga zuciyarsa kai tsaye kamar an fisgo a bakinsa.

     

    Azabure Khausar ta buɗe Idanunta dake lumshe tare da janye jikinta daga nasa amma still hannunta na kan cikinsa tana murza cibiyarsa.

    Wani mugun kallo mai cike tarin kufula, takaici, tsuyan zuciya, da tarin ƙunci ya watsa mata firgitaccen kallo. Ta da ɗaga hannunsa cikin wani irin masifeffen rawan jiki da gigitan yanayi yasanya tafin hannunsa ya finciko hannunta dake kan cikin sa da masifar ƙarfi ya yarfa hannun nata har saida ta saki ƙara, dan ji tayi kamar zai ɓalla mata hannun.

    Shi kuwa a take kuma tsikar jikinsa ta mimmiki ta tashi.

     

    Cikin tsananin tsoro da firgici Khausar ta janye jikinta kana ta koma ta mannu da jikin kujera tare da rungume kanta a can gefen jikin kujeran motar tana mai jin raɗaɗin marin.

    Moddibo kuwa da ƙarfi ya rumtse idanunsa sabida  wani irin masifaffen har bawa da yaji zuciysrsa nayi da masifar ƙarfi, lokaci ɗaya wani azabebben zufa ya wanke sa kana rawan da lips ɗinsa keyi ya tsananta karkarwa yayin da har hakoransa ke rawa har suna bugun juna saboda wani masifaffen abu da yaji yana yawo cikin kwanyar kansa, wani irin baƙon yanayi yaji ya taso masa da azaban ƙarfi, abinda bai taɓa jiba atsawon shekaru.

    Cike da dauriya da kuma fushi ya figi motar da gudu yayin da zuciyarsa ke wani irin azalzala idanunsa kuwa har yanzu dishi-dishi suke gani sanna, sai wani irin rawa jikinsa da lips inda keyi, cikin mintunan da basu gaza goma ba taji yayi Parking aƙofar gidansu.

     

    Cikin tsananin tsoro da ruɗu ta buɗe murfin motar, cikin sauri ta fice batare data lura da ɗan kwalinta da kuma hankief ɗin ta dake kan cinyar Moddibo ba.

    Da ƙarfi yafi gi motar cikin mintuna kaɗan ya isa gidan yana parking ya fito.

    Lokacin ɗaya ya jiƙe jikib saboda ruwan da ake cigaba dayi kamar da bakin ƙwarya.

    Cak ya tsaya Atsakiyar gidan nasu, ruwan na sauƙa atsakiyar kansa saboda masifeffiyar baƙon yanayi  da yake ji ga kuma suya da raɗaɗin da zuciyarsa keyi, na firgicin saɓawa Ubangiji da yayi, tsoron Allah da tarin damuwa ne ya sanya idanunsa fara zubda wasu irin zafafan hawaye masu ƙuna.

    Rumtse idanun da yayi tare da furta.

    “Astagfirullah wa,atubu ilaik, Ya Allah kaine mafi sanin zuciyata, Yah Allah ka gafarta min ya Allah ka shafe min wannan zunubi, ya rabbi kada ka sake bani damar sake saɓa maka Yah Allah ka sani ban taɓa aikata makamancin hakaba,”. Gaba ɗaya muryarshi rawa takeyi, yayinda idanunsa ke kwaranyar da hawaye.

    Duk da ruwan na dukansa amma ko kaɗan baiga alamar zaiji sauƙin abinda ke damunsa ba. ji yayi tamkar ya ɗora hannunsa a ka ya rinƙa ihu da kururuwa. Duk da dauriyarsa kuwa, bai san sanda kuka ya kubce masa, domin duk sauƙan ruwan akansa ji yake kamar ana  ƙara rurumashi wutar fitina a jikinsa,  ga kuma ƙuncin zaciya da yake ji,

    Har lau  haƙoran sake dukan juna suke nusa bada sautin Ƙat-ƙat-ƙat baki ɗaya jikinsa rawa yake tamkar mazari ahankali ya sunkuyar da kansa gani yayi yadda muhallin sa ya sake masifar nuna zalamarsa.

     

    Cikin mawuyacin hali ya dafe kansa da hannunsa na hagu murya narawa yace.

    “Wannan wace irin masiface? shin wannan wani irin abune mai wuyar jurewa me yake yafaru dani ne wai? Shegiyar yarinya mai fitintinun al’amura, ya Allah ka isarmin da cutar dani da tayi, Yah Allah kaga ita ta riskeni kaine shaida ni ban nufetaba, Allah ka isarmin kan wannan muguwar yarinya mai jikin zalumci Astagfurullah”.

    Ya ida maganar tare da fashewa da kuka, still dai yana tsaye acikin ruwan yana cigaba da dukansa, ganin sam kuma abin nasa yaƙi nitsuwa ne yasa ya nufi hanyar sashensa domin sakarwa da kansa ruwan ɗumi koda zaiji sauƙin abinda ke damunsa, abakin faradan Falon sa ya tsaya tare da zare rigar dake jikinsa kana ya zame wandon ya shanya ya rage daga shi sai boxer Kai tsaye toilet ɗin sa dake cikin Bedroom ɗinsa ya nufa yana shiga ya sakarwa da kansa ruwan ɗumi batare daya cire boxer ba yana tsaye ruwan ɗumin ya cigaba da zuba akansa amma babu abinda ke yawo a idanunsa kamar lokacin daya rungumi yarinyar ga wani masifaffen ƙamshinta da yake ji ajikinsa da ƙarfi ya matse jikinsa waje ɗaya kana cikin tsanananin tsoron Allah ya ci gaba istigfari.

    “Astagfurullah wa’atubu Ilaik ³ ya Allah na tuba kayafe min wannan abin da nayi. Ya Ubangijina na tuba”.

    Kai kawai yake girgiza wa cike da tashin hankali mara misaltuwa daya rufe idanunsa babu abinda yake hange face yanayin da suka kasance amota.

     

    Acan ɓangaren Khausar kuwa da gudu ta shiga gida tare da wucewa Falon su.

    Tsaye ta samu Mommyn ta cikin yanayin damuwa da tashin hankalin.

    Mommy na ganinta ta saki ajiyar zuciya mai nauyi tare da cewa.

    “Alhamdulillah Khausar kin dawo, gaba ɗaya hankalina ya tashi na kasa zaune na kasa tsaye, tunda Haiydar ya dawo ya faɗa min yanda ku kayi da Amina!”.

    Ida mgnar taba kallon yadda jikin Khausar ke ɗigar da ruwa ga wani rawa da jikinta keyi cikin  jin ƙai da tausayawa tace.

    “Amina bata kyauta min ba. Wallahi Allah Amina bata taɓa yimin abinda ya ɓata min rai irin na yau ba, ya za’a yi cikin wannan hadarin cikin wannan yanayin ta baro min ke a makaranta.

    Yanzu waya dawo dake?”.

    Cikin karkarwa na tsoro da sanyi  ga kuma zogin mari tace.

    “Uhhhmmm”.

    Ita kuwa Mommyn cikin sanyi tace.

    “Yanzun nan dama Abbanku nake jira? ya dawo dan baya nan na faɗa masa kina cikin makaranta. Yanzu yana dawowa ne akan zai ɗaukeni muje can ɗin”.

     

    Cikin sanyi da yanayin tsoro da kuma ruɗu Khausar ta dubi Mommy yayinda, jikinta ke rawa kamar zata faɗi.

    Kallonta Mommy tayi cike da tausayinta ta girgiza kai kana tace.

    “Gashi na sani Khausar yanda kike rikicewa idan kikaji rugugi kike fita hayyacinki idan kika ga walƙiya bare kuma kiji tsawa!.

    Gashi yau kuma ruwan yazo da wasu irin tswawwaki masu ban tsoro.

     

    Cikin rawan jiki ta sanya hannunta dake ta karkarwa ta janye Hijabinta kana ta kalli Mommyn Muryanta na rawa tace.

    “Yah Jameel ne ya kawo ni”.

    Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe kana tace.

    “Kai Ubangiji Allah yayi masa albarka. Allah ya saka masa da mafi kyawun sakamakon”.

    Kai Khausar ta gyaɗa still jikinta na tsuma tace.

    “Ameen Mommy bari in cire kayana”.

    Ta ida mgnar tare da wucewa Bedroom ɗin ta tana shiga ta kalli hannunta lokaci ɗaya ta sake shiga sabon tashin hankali, cike da damuwa ta yarfe hannunta kana tace.

    “Nashiga uku Ni Faɗimatuzzahara  ina nasanya hannu na! Ni Batula?”.

    Duk da cewa tana cikin tsoro amma tana sane da inda  ya zaro hannunta kai tsaye toilet ta Wuce tare da cire kayan jikinta ta sakarwa kanta ruwan ɗumi sabulu ta ɗauka ta mulke hannunta dashi kana ta shiga gogawa ajikin tiles dake jikin bangon tana Girgiza Kai kana tana mai Furta.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Astagfirullah wa’atubu ilaik Subhanallah ya Salam Allah na tuba”.

    Da ƙyar ta iya yin wankan ta fito bayan ta ɗaura alawalan tare da buɗe Siff ta ɗauki dogon riga na roba baƙi ta sanya har zuwa lokacin jikinta na ƙamshin tularensa Sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da Sallah kana ta riƙe carbi tana hawaye da Istigfari.

     

    Acan ɓangaren Moddibo kuwa bayan ya gama wanka al’wala ya ɗaura tare da fitowa har zuwa lokacin zuciyar sa na tsaye alamar zai samu nitsuwa Siff ya buɗe tare da ɗaukar Boxes ya sa sai kuma ya tsaya yana kallon kansa, ya tabbata idan yasa Jallabiya mutane zasu iya fahimtar halin da yake ciki wani dogon tsaki yaja.

    “Mitsssssssss!!! Yar iskar yarinya”.

    tare da sanya hannunsa ya matse muhallinsa da ƙarfi wai ko zai masa biyayya cikin yanayin tashin hankali ya kalli kuma sunkuyar da kansa tare da faɗin.

    “Wai wannan wacce iriyar Masifa ce!?”.

    Sake buɗe sabbin boxers ɗin sa dake cikin leda yayi ya ciro wani ƙarami wanda yake zaton zai masa kaɗan shiyasa ma bai taba sakasu ba,

    Cikin yamutsa fuska ya sanyashi,

    sosai ya matsesa sai dai har zuwa lokacin al’amarin  azimunne.

     

    Wani boyel baƙi mai kyau ya ɗauka ya sanya kana ya feshe jikinsa da turarukansa cikin sanyin jiki ya fita zuwa Masallaci ya gabatar da sallah Azahar.

    A wunin wannan ranan dai baki ɗaya haka yayita agigice.

     

    Acan gidan Lamiɗo kuwa Hajiya Bunayya ce zaune akan 3sitter yayin da Amina ke gefenta riƙe da kofin shayi yana tururi.

    Anutse Hajiya Bunayya ta juya tare da kallon Amina data kai kofin shayin bakinta kana tace.

    “Amina yanzu ya kuke da Malam Jameel ne? nifa nagaji da wannan al’amarin kullum sai munga Abu kamar yaci sai kuma kiga abu ya sake ta ɓarɓarewa!”.

    Gyara zama Amina tayi tare da ajiye Cup ɗin tea kana tace.

    “Hmmm ba gwara ma muba akan Samira Sani, sufa duk abinda suke kamar anshuka dusa shi Moddibo na nan kamar Waliyyi baya fahimtar karatunta shu’umanci bare ya ratsasa kamar kurma baya ma sauraronta bare kuma ya sake mata fuska”.

    Ta gumi Hajiya Bunayya tayi tana cigaba da sauraren Amina.

    Amina ta cigaba da cewa.

    “Amma kinga gwara Ni dama Malam Jameel Yana da sauƙin kai sannan yanzu ya daina shash-shareni idan na gaishesa yana Amsawa cikin sakin fuska da mutunci mun koma kamar da duk da dai dama haka halinsa yake ga kowa”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “Kawai dai abinda nake gani Ummah kawai Abbah ya masa magana idan Abba ya masa magana kan cewa Ina son sa bazai ƙini ba, saboda yana da kirki yana da mutunci da kawaici ko ba komai kuma gidan dala yake domin nifa kuɗin mahaifinsa nafiso, badon kuɗin da suke da shiba, nafi son miji irin Modibbo mishkili, ba sake fuska dan sunfi iya soyayya”.

     

    Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta sauke tare da gyara riƙon wayarta kana tace.

    “Anya Amina za’ayi hana kuwa? Ai gwara dai mujawo hankalinsa zaifi, kuma batun kuɗi yoh dama ai shi mukewa bauta domin duk abinda nake kashewa a wurin boka ina lissafawa kina shiga daga ciki zaku biyani”.

    Kwaɓe Fuska Amina tayi kana tace.

    “Kayya Ummah tun yaushe mukeyi amma abin baya wani kamasu  gwara ma Malam Jameel Idan munyi munga Abu ya kama kwana biyu sai kuma ya dawo baya kula har kata! anata ƙara lissafin kuɗin da zan biya”.

    Kai Ummah ta gyaɗa kana tace.

    “Gaskiya dai kam in dai hakan zaiyi sai in faɗawa Mafaifinku yafi min kwanciyar hankali ma amma ko. Abbanku baza mu fuskance sa kai tsaye haka ba dole sai anja hankalinsa akan maganar”.

    Ta gumi Amina tayi tare da cewa.

    “Toh Ummah acanza wani boka mana?”.

    Saurin Kallonta Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Wani boka muke dashi da yafi wannan?,Duk aikin sai yace ana wasa dashi sannan aikin kuɗi yake buƙata sosai kuma kinga Yanzu bani da kuɗi sosai Amina, kuma ai tunda muka canza boka Zurau wannan duk aikin da yake min yana ci”.

    Taɓe baki tayi tare da cewa.

    “Gaskiya Ummah asamu ayi aikin nan idan muka samu nashiga gidansu zamu fanshe duk kuɗin da muka kashe!”.

    Jinjina kai Ummah tayi kana tace.

    “Zanyi ƙoƙarin hakan in Allah ya yarda”.

     

    Acan ɓangaren su M Jameel kuwa bayan ya shiga gida ya sauya kayansa zuwa blue jeans da farin t-shirt mai dogon hannu kana ya gabatar da Sallah Azahar Yana idarwa ya nufi sashen Mahaifinsa zuwa lokacin ruwa ya tsaya bakinsa ɗauke da sallama ya shiga kana ya zauna kusa da Abbansa.

    Kallonsa Abba yayi bayan sun gaisa yayi gyaran murya tare da cewa.

    “Dama batun Company Adamawa ne acikin kayayyakin da aka kawo muga ya yanayin ingancinsu akwai atomfofi,

    Gyaleluwa da kuma sauran kayayyakin ya kamata kaje”.

    Jinjina kai M Jameel Yayi kana yace.

    “Toh shikenan Abba yaushe ne tafiyar”.

    Kallonsa Abbah yayi kana yace.

    “Insha Allah tafiyar zai kasance idan kun gama jarrabawar ɗaliban ku da zasu gama makarantar bana nasan zuwa lokacin hankalinka ya kwanta Asma’u da Bashir sun kammala Secondary School”.

    M Jameel kuwa jingina kansa da jikin kujeran yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.

    “Hakane kam Alhamdulillah yanzu kam na gama  sun gullarsu Asma’u”.

    Dai-dai lokacin da Hajiya Karima ta shigo falon Abba na cewa.

    “Kaga yanzu shikenan tun da kagama da wannan shungullan gaba ɗaya duk abinda ya shafi shungullana da kuma harƙoƙina, kasuwancina duk zan danƙasu ahannunka Babana.

    Domin ni girma ya fara zuwa Inason hutu”.

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Toh shikenan Abba babu damuwa duk abinda kace shi za ayi da izinin Ubangiji”.

    Murmushi Abba yayi har cikin ransa yake jin ƙaunar ɗan nasa saboda yanda yake masa biyayya ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.

    “Toh Nagode Allah yayi maka Albarka”.

    Duk abinda suka tattauna Hajiya Karima na rakuɓe tana jin tattaunawar su Amaryan Abban Jameel Hajia Turai ta shigo ganin Hajiya Karima atsaye yasa ta faɗin.

    “A’a Lafiya kike tsaye anan Hajiya Karima?”.

    Cikin sauri ta juya, sai asannan Abba da M Jameel suka juya suka ganta tsaye.

    Murmushin da bai wuce saman laɓɓabanta ba tayi kana tace.

    “Yanzu na iso ina gyara labule nai”.

    Ita dai Hajiya Turai batace komai ba ta ƙarasa shiga falon kana Hajiya Karima tabi yo bayan suka cigaba da hira.

     

    Washe gari.

    Cikin sanyin jiki da damuwa Khausar ta shirya cikin Uniform ɗin ta dake haska fatarta  baki daya ta kasa sakewa da zaran ta tuna inda ta sanya hannunta sai taji tashiga matsanancin tashin hankali.

    Cikin sanyin jiki ta fita tare da nufar inda motarsu ke fake Amina ce tafito hannunta riƙe da   lunchbox ɗin Aminu dai-dai lokacin da Lamiɗo ya fito daga sashen Gimbiya Dadu da  fuska a tsuke ya kalli Amina tare da cewa.

    “Banaso Amina kada ki sake yi min abinda kikayi jiya banaso haka ki kiyayeni! Ki kiyayeni!”.

    Ƙasa tayi da kanta kana tace.

    “Toh Abba kayi haƙuri”.

    Sannan ta juya ta  shiga, kana su Khausar ma suka shiga mota ko acikin mota Khausar jingina bayanta da jikin kujera tayi tare da damƙe hannunta ahaka har suka isa makarantar.

     

    Anutse ta fito ta tashiga hall da suke Exam kai tsaye bencin da number ta ke kai ta nufa tare da zama kana ta dafe kanta ba jimawa Malam Isa ya shigo ya fara raba musu Booklet da questions na Economics.

    Kallon Khausar data dafe kanta da hannu biyu yayi kana yace.

    “Lelewal meke damunki?”.

    Da sauri ta ɗago kanta ta kallesa sai kuma ta girgiza kanta cikin sanyin murya tace.

    “Ba komai Malam”.

    Question peper ya ajiye mata kana ya cigaba da rabawa sauran.

    Cikin mutuwar jiki Khausar ta riƙa yin amsarin Questions ɗin tun kafin a miƙa wa wasu Questions pepar tuni ta gama Amsawa kwantar da kanta akan deks ɗin tayi tana godewa Allah daya sa basu da Exam din Moddibo da batasan da idon da zata iya kallon sa ba.

     

    Moddibo kuwa tunda yashigo makarantar ya wuce office ɗin su ya zauna cikin zullumi da damuwa.

    Ahankali M Jameel ya fito daga class da yake teaching hannunsa riƙe da booklet ya nufi Office ɗinsu bakinsa ɗauke da Sallama yashiga zaune ya samu Moddibo idanunsa na rufe kana lips ɗin sa na rawan sanyi ahankali.

    Booklet ɗin ya ajiye tare da zama gefensa kana yace.

    “A.J meke damunka?”.

    A hankali Moddibon Ya jujjuya idanunsa dake lunshe yayi kana ya Girgiza masa kai tare da cewa.

    “Bakomai”.

    Kallonsa M Jameel Yayi kana yace.

    “Ya zaka ce min bakomai A.J ke faɗa min meke damunka ko dai baka da lafiya ne?”.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da gyaɗa masa kai.

     

    Cikin damuwa M Jameel yace.

    “Toh meke damunka?,Ka faɗa min abinda ke damunka mana”.

    Sai asannan Moddibo ya buɗe Idanunsa cikin raunin murya tamkar mai shirin fashewa da kuka yace.

    “I don’t know J I really don’t know what’s wrong with me WLH BAN SANIBA, BANSAN MEKE DAMUNA BA J”.

    Da Mamaki M Jameel ya kallesa kana yace.

    “How A.J kamar ya bakasan meke da munka ba”.

    Langwaɓar da kai Moddibo yayi cikin yanayin damuwa da tashin hankali ya kalli M Jameel daya tsaresa da ido ya sauƙe Idanunsa ƙasa kana yace.

    “Bansani ba J bansan meke damuna ba Na dai san bana jina dai-dai ina cikin ɗimuwa”.

    Ya ida maganar yana mai lumshe idanunsa sam ya rasa taya zai fara faɗawa M Jameel yanayin da yake ji ajikinsa.

     

    Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe kana yace.

    “To ko dai zazzaɓi ne?”.

    Girgiza kai Moddibo yayi still cikin raunin murya yace.

    “A’a”.

    Ahankali M Jameel ya sake cewa.

    “Toh ko Kanka ke ciwo?”.

    Still Kai Moddibo ya sake Girgiza masa alamar a’a.

    Numfashi M Jameel ya fesar kana yace.

    “Toh ko dai cikin kane?”.

    Nan ma kai Moddibo ya Girgiza kamar zai fashe da kuka.

    Tagumin M Jameel Yayi kana yace.

    “Toh meke damunka?”.

    Lumshe idanu Moddibo yayi cikin sanyin murya mai rauni ya buɗe idanunsa tare da kallon M Jameel daya tsaresa da Ido kana yace.

    “J bana jina dai-dai ina jin kamar akwai wani abu da nake buƙata amma bansan menene ba”.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “Toh me kake buƙata?”.

    Girgiza kai Moddibo yayi tare da buɗe hannunsa kana cikin sanyin murya yace.

    “Idont know J nima ban sani ba bansan me nake so ba amma inaji kamar akwai wani abu da ɗan Adam yake buƙata acikin rayuwarsa wanda nima nake buƙatarsa kusa sani, daga jiya zuwa yau amma bansan menene bane”.

     

    Kallonsa M Jameel Yayi tare da kallon yanda idanunsa suka sauya launi zuwa Ja tun safe da suka zo ya lura da hakan tamkar mai mayen bacci kana ya lura da yanda lips ɗin sa ke rawa sannan ya lura da yanda bini-bini yake matse ƙafafunsa.

    M Jameel na cikin Kallonsa. Moddibo yayi miƙa tare da matse ƙafafunsa kana lips ɗin sa suka shiga rawa sai kuma ya runtse Idanunsa.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “J kodai kana jin kana ɓuƙatar mace akusa da kai ne?”.

    Lokaci ɗaya Moddibo yaji zuciyarsa ya tsinke da masifar ƙarfi ajiyar zuciya ya saki tare da kallon M Jameel ji yake tamkar ya fashe da kuka ko zaiji sauƙin abinda ke damunsa  sunkuyar da kai ƙasa yayi cikin wata raunan’niyar murya mai sanyi yace.

    “Ban sani ba J”.

    M Jameel yace.

    “Toh mutafi gida mana tunda na gama abinda nake kai kuma naga kamar baka da komai”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana ya miƙe tare da yin miƙa da ayau ya zame masa jiki domin baya minti goma mai kyau sai yayi miƙa.

    Kallonsa M Jameel yayi dan yanda yaga Modibbonsa ya tashi ta saman rigar duk da kuwa boxes biyu ya saka duk dan ya suturta jikinsa ɗagowa M Jameel yayi tare da kallon fuskarsa yayi Murmushi.

    Fita Moddibo yayi M Jameel yabi bayansa dai-dai lokacin da aka kira sallar Azahar acikin masallacin dake makarantar.

    bayan sun Idar suka fito suka shiga mota M Jameel ke driving yayin da Moddibo ke gefen mai zaman banza idanunsa alumshe duk abin duniya ya Ishesa.

     

    Suna isa gida M Jameel yayi Parking ya fita kai tsaye sashen Innayi ya wuce ya karɓa musu abinci Moddibo kuwa cikin mutuwar jiki ya wuce sashen sa ya kwanta.

    Ba jimawa M Jameel ya dawo hannunsa riƙe da Warmers da kuma Plate kwance ya samu Moddibo akan 3sitter yayi rub da ciki idanunsa akan ƙofar falon.

    Ƙarasa shiga falon M Jameel Yayi tare da zama aƙasa kana ya kalli Moddibo da faɗin.

    “Saƙƙo muci abinci idan muka gama sai muje kaga Dr”.

    Girgiza kai Moddibo yayi cikin sanyayyar Murya yace.

    “Bana jin yunwa bana son cin komai”.

    Buɗe Warmer M Jameel Yayi tare da cewa.

    “Toh Meyesa haka J?”.

    Cike da raunin murya tamkar wanda ke shirin fashewa da kuka yace.

    “Ban saniba nima”.

    Dariya mara sauti M Jameel Yayi kana yace.

    “A.J Na fahimceka fa kamar *Mace* kake buƙata acikin rayuwarka!”.

    Cikin sauri Moddibo ya lumshe idanunsa jin suna tsats-tsafo wa da hawaye, miƙewa yayi tare da wucewa Bedroom ɗin sa yana shiga yasa key ya rufe.

     

    M Jameel kuwa jingina bayansa da jikin kujera yayi tare da fashewa da dariya harda riƙe ciki.

    Moddibo kuwa yana kulle ƙofar ya juya ya kwanta ruf da ciki tare da lumshe idanunsa yayin da ƙwaƙwalwar sa ta shiga tariyo masa moment da suka kasance acikin mota lokaci ɗaya Muhalinsa ya shiga harbawa da ƙarfi tamkar zai fisge ya fito, yayin da lips ɗin sa suka shiga rawa har haƙoransa na haɗuwa kar-kar-kar.

    Batare daya shirya ba yaji hawaye suna bin kuncinsa shi kansa baisan meyake so ba bai san meke faruwa dashi ba yakasa sanin yana yin da yake ciki ji yayi kawai yana kuka hawaye na bin kuncinsa yana sheshsheƙa.

    Miƙewa yayi cikin rashin sanin madafa shin ya zaiyi da wannan jarabar tun jiya yake fama da zaran ya rufe Idanunsa yanayin da suka kasance da yarinyar ne yake gani.

     

    M Jameel kuwa dambun shin kafa dayaji vegetables da soyayyen naman kaza dake tashin ƙamahi ya zuba a Plate ya fara ci yana cikin ci ne wayarsa dake gefensa ya hau ruri.

    Ahankali ya sanya hannunsa ya ɗauka Turkey Kawai ya gani babu Number.

    Picking yayi tare da kaiwa kunnensa yana dariya yace.

    “Yaushe kaje Turkey?”.

    Murmushi Jalaludeen yayi kana yace.

    “Na kusa kwana biyar acan ai”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.

    “Lallai dai kam yayi kyau ya gida”.

    Gyaran murya Jalaludeen yayi tare da cewa.

    “Lafiya wai meyasamu Aliyu ne”.

    M Jameel na ajiye cokalin hannunsa yace.

    “Nima kaina ban sani ba”.

    Dariya Jalaludeen yayi kana yace.

    “Mace ta fara shiga rayuwarsa kenan.

    Aure fa yake da buƙata yana da ƙaƙƙarfan sha’awar da tuntuni na kwantar masa da shi”.

    Zare Ido M Jameel Yayi kana yace.

    “Auuu Jalaludeen kenan kaine ka maida mu waliyan dole?”.

    Cikin sauri Jalaludeen yace.

    “A’a Ni ban mayar daku mata ba, amma dai kawai nasan Aliyu nada ƙarfin sha’awa na masifa idan har aka bar shi da wannan sha’awar zai iya zame masa masifa kana zai iya jefashi acikin damuwa gashi naga burinsa a lokacin yayi ilimi mai zurfi, kuma in ka tuna a lokacin yana yawan fama da ciwon ciki”.

    Dafe kunci M Jameel Yayi yana saurarensa.

    Murmushi Jalaludeen Yayi kana ya cigaba da cewa.

    “Tun haɗuwar mu na farko kafin ku fahimci wanene ni kafin ku fahimci komai akaina, kana tun kafin afahimci wanene ni asan komai akaina na bashi abinda yasha wanda ya karyar masa da ƙarfin sha’awarsa har yake ji kamar baya buƙatar mace acikin rayuwarsa”.

    M Jameel ya gyara zamansa tare da cewa.

    “Ikon Allah”.

     

    Jalaludeen kuwa cikin yanayin su na can yaci gaba da cewa.

    “Toh ajiya akwai abinda yafaru ko dai mace tashiga rayuwarsa ko dai akwai macen data kama jikinsa wannan dalili yasa gaba ɗaya takarya alƙadarin abinda ke jikinsa!”.

    Ajiyar zuciya M Jameel ya saki kana yace.

    “Toh fa”.

    Murmushi Jalaludeen yayi tare da faɗin.

    “Kai kuma kwaɗayin ka ne ya kaika dana bashi maganin yana cikin sha kawai ka amshi kofin kasha shiyasa kuka kasance atare haka amman ai kai naka ba kamar nashi bane ”.

     

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Amma dai gaskiya Jalaludeen baka da mutunci”.

    Dariya Jalaludeen yayi kana yace.

    “Nifa bance komai ba gaba ɗaya abinku lafiya lau yake kawai dai sha’awar ce na kwantar”.

    Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.

    “Toh yanzu shi kuma wannan ya za’ayi dashi dan yanzu wallahi ya tashi ya tafi ɗaki kamar zaiyi kuka”.

    Murmushi Jalaludeen yayi kana yace.

    “Kukan ma yakeyi yanzu”.

    Ware ido M Jameel Yayi kana yace.

    “Lallai dai kam maza sun gamu da aiki kenan”.

    Jinjina kai Jalaludeen yayi tare da cewa.

    “Gaskiya yanayin daya ke ciki ne awahale yake haka ya wuni jiya still haka ya kwana gashi kuma yau ma ya wuni haka”.

    Cike da tausayawa M Jameel yace.

    “Toh yanzu ya za’ayi ?”.

    Girgiza kai Jalaludeen yayi tare da cewa.

    “Gaskiya ban sani ba dan bani da yanda zan mishi kawai abune daya zo masa babu yanda za’ayi haka zaita rayuwa mafita ɗaya ne kawai yayi ƙoƙari yayi aure”.

     

    Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da cewa.

    “Ok zamu yi ƙoƙari muga mai ya dace tunda gashi dama duk abinda ya dace mun gama”.

    Jinjina kai Jalaludeen yayi kana yace.

    “Masha Allah amma yanzu ka samu ruwan ɗumi kasa masa laimun tsami yaji kana ka sanya zuma yaji sai ka bashi yasha zai ɗan ji sauƙi”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.

    “Toh shikenan ba matsala mun gode”.

    Sallama sukayi tare da katse kira.

    Miƙewa M Jameel Yayi yashiga cikin kichen dake falon ya buɗe Flaks dake ɗauke da ruwan tea ya zuba a Cup lemun tsami ya duba yaga babu rufe Cup ɗin yayi ya nufi cikin gadin ɗin gidan ya tsunko guda biyar sannan ya dawo ya wanke tare da matse su duka acikin shayin kana ya buɗe kofin roban zuma yasa.

    Fita yayi a kichen ɗin ya nufi Bedroom din Moddibo yayi Knowking ƙofar.

     

    Dai-dai lokacin da Moddibo ya cire kayan jikinsa ka ya zura Jallabiya kasancewar boxers ya takure masa jiki har yana jin mallakinsa na yimasa ciwo saboda yanda ya takuresa ya hanasa miƙewa cikin gajiyawa ya mike ya cire boxes ɗin tare da cewa.

    “Bari naga iya inda zaka tsaya uban ƴan zalamammu”.

    Yayi maganar yana kallon jikin nasa daya miƙe ya tsaya acikin Jallabiyar.

    Muryar M Jameel yaji yana cewa.

    “A.J ka buɗe min ƙofar mana in baka magani”.

    Daga ciki Moddibo ya buɗe masa ƙofar.

    Kallonsa M Jameel Yayi sai kuma ya kalli yanda  ya ɗaga rigar kawar da kai gefe yayi yana jin dariya na neman kufce masa.

    Kofin dake riƙe ahannunsu ya miƙa masa.

    Cikin Sanyayyar muryarsa yace.

    “J Me wannan?”.

    M Jameel ya Kalli kofin kana yace.

    “Kasha mana zaka ji sauƙin abinda ke damunka na fahimci meke damunka A.J”.

     

    Moddibo bai sake cewa komai ba ya amshi Cup ɗin ya koma bakin gado ya zauna tare da kafa kansa ya shanye tass kana ya ajiye kofin, cikin ikon Allah lokaci ɗaya yaji zufa ya fara sauƙa masa Atake yafara jin abinda ke damunsa na sauƙa kaɗan-kaɗan amma still jikinai ɗin na nan amiƙe ahankali yaji lips ɗin sa ya daina rawan zamewa yayi ya kwanta akan gadon yana sakin ajiyar zuciya akai-akai.

     

    Acan gidansu Khausar kuwa zaune suke afalon  Mommy suna cikin hira ka jiyo sallama.

    Cikin sauri Haiydar ya ɗago kansa tare da cewa.

    “Laaaaah….!

     

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki yar uwa 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, sai in saki a Group na ɗin da zanke posting. Ko kinga littafin SAKAYYAH a waje na satane*

     

     

     

     

     

    *By*

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 7

    Sakayyah 7

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 7_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE NE YAN UWA, BA WAI FREE BOOK BANE! INA GAMA SAKIN FREE PAGE, KO KINGA an fiddashi waje na satane. Na kuma Yaseen ne doguwa. Dan haka ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa biya ki karanta*

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace wanda bani da haufi kansa 7k ne kacal sai dai yar musilar robace., Kana masin Daɗi har Maɗigan yana da masigar kyau da tsatstsafo da ni’ima, wlh wasu in sunyi amfani dashi pan biyu sabida yadda zakiyi ta tsiyaya. 5k ne Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa 8k ne, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan wanda wlh koda sanyin cikin mahaifane fes yake wanke shi kuma ko mai ciki zata shashi baida illa, kama budurwa ko bazawara duk zasu iya sha harma da yara. Set ɗin da 10k ne innkuma za’a sa miki komai rabi-rabi ne 5k ne, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

     

    Moddibo ta hango zaune a gefen gabas yana fuskantar tata, bima’ana yana kallon yamma, zaune yake  akan wani dutse mai masifar sheƙi kana wasu mutane biyu na tsaye gefen hagu da damansa,

    Sannan da buta gabansa bisa alama  Al’wala yayi domin farin yashin daya mamaye wajen daga gabansa a jiƙe yake, kana yana mai fidda wani irin ni’imtaccen ƙamshi maisa ɗan Adam lumshe ido. Baki ɗaya haske ya mamaye ilahirin filin wajen hakan yasa itada Moddibo suna fuskantar juna yayin da M Jameel da Adda Adama matar Baffan Umaru  suma ke fuskantar juna.

    Kana lambu dake  can bayanta kuwa yake feso musu iskar yammaci dana lambun suka haɗu waje ɗaya daga sama kuma rana ne yayi Ja yana shirin faɗuwa.

    A hankali ta sauƙe numfashi mai nauyi tare da lumshe idanunta.

    Da sauri ta buɗe idanun nata, jin wani irin sassayan sautin dariya mai cike da shauƙi da Moddibo yakeyi.

    Cike da mamaki duk suka zuba mishi idanu.

    Yayinda Adda Adama ma tuni ta fara dariya mai sauti.

    Ita kuwa Khausar haka nan taji jikinta yana tsuma tare da sakewa, da sauri ta juya ta kalli  M Jameel ga mamakinta shima ita yake kallo, da idonshi ya nuna mata Moddibo yana mai yin lallausan Murmushi, da sauri ta maida kallonta kan Kekkyawar fuskar Moddibo, wacce tunda take a rayuwarta dashi bata taɓa ganin yayi dariyar da har haƙoransa na gaba zasu baiyana ba.

    “Fatabarakallahu fih hasanil khaliƙeen”.

    Ta furga a saman lips ɗinta, lokacin da ta sauƙe ƙwayar idanunta kan fuskar Moddibo, da sauri ta kuma lumshe manyan Idanunta sabida wani irin masifeffen sheƙi da ta hango sajenshi dake kwance lip-lip yanayi,

    Sautin dariyarsa da har yanzu yake ne yasata saurin buɗe idanun.

    “Subahanallah, tsarki ya tabbata ga Ubangiji da ya halicci wannan bawa ya kuma bashi waɗan nan haƙoran”.

    Ta faɗa a fili lokacin da taga ƙyellin da haƙoransa keyi har yana ɗauke mata idanunta,

    Lobgoɓar da kanta tayi bisa kafaɗarta.

    Wani irin sassayan numfashi ta fesar tare da tsaida idanunta a kanshi.

     

    Shi kuwa Moddibo dariya yakeyi mai sayyan sauti wanda yake da daɗin ji, har maƙolloton wuyanshi yana ɗan haurawa yayi sama kana ya dawo ƙasa.

    Yayinda ya ɗaura tafin hannunsa kan ƙirjinsa.

    Cikin tsananin dariyar ya samu ya ɗan tsagaita tare da furta.

    “Astagfurillah watubu ilaik”.

    Sai kuma ya ɗago ya kalli M Jameel lokaci ɗaya kuma ya sake sakin dariya mai sauti yana cewa.

    “Astagafitillah Wayyo cikina”.

     

    Cikin rage girman idanunta take kallon gashin girarsa dake kwance lip.

     

    Jameel kuwa sai Murmushi yakeyi tare da girgiza kansa.

    Yayinda Adda Adama ma dariyar takeyi harda riƙe ciki.

    Ita kuwa Khausar gaba ɗaya ta kasa ɗauke idonta daga kansa.

    A haka har rana tayi mudun kuyanƙi alamun yana gab da faɗuwa.

     

    amma kafin ya faɗi saiya rabu kashi biyu.

    Yayinda Khausar kuwa ke zaune tana fuskantar yamma hakan yasata ganin abin.

    Atake hankalin ta ya tashi ganin yanda ranan ya rabu kashi biyu.

     

    Ita kuwa Adda Adama hannu tasa ta dafe ƙirjinta tare da faɗin.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n yau mun shiga ukun mu ku dubi yanda ranar tayi fa!”.

    Tana faɗin haka duk dariya da murmushin da sukeyi ya tsaya.

     

    Moddibo kuwa daga inda yake zaune ya ɗaga kansa sama tare da juyawa bayanshi kana a hankali yace.

    “Ya Salam  ya ilahi ya mujabat da’awati meke Shirin faruwa”.

    Cikin tsananin gigita da tashin hankali da firgici Khausar ɗin ta saki kuka mai cike da rauni tare da cewa.

    “Innalillahi wa innailaihi raji’un, hasbunallahiwani’imanwakil, mun shiga uku”.

    Sai kuma ta juyo ta kalli Moddibo da ya gyara zamanshi kana a hankali yace.

    “Babu abinda zai faru wanda Allah bai sani ba, Insha Allah Ubangiji zai mana maganin duk kan abinda yayi tsanani”.

     

    M Jameel kuwa kasa furta komai yayi sai hawaye dake kwaranya daga idanunsa.

    ita kuwa Khausar ganin M Jameel na Hawaye kawai sai itama tashiga yin kuka amma ba mai sauti ba.

    Cikin wani irin yanayin da bazai misaltuba Moddibo ya dubesa kafin yace.

    “Haba J. Kamar ba namiji ba addu’a ya kamata muyi duk kan tsanani yana tare da sauƙi”.

    Still dai M Jameel baice komai ba.

    Shi kuwa Moddibo cikin sanyin jiki ya fuskanci Khausar cikin wata iriyar murya yace.

    “Khausar tausayi na kike ji ne?”.

    Cikin kwaranyar hawaye ta gyaɗa mishi kai tare da sakin raunataccen kuka mai cushe numfashi, lokaci ɗaya numfashin ta ya fara cushewa yana ɗauke wa, cikin yanayi wahalar neman numfashi taga Moddibo ya…!

    Dai-dai  lokacin kuwa ta farka daga baccin da takeyi ciki  razana tare da kaɗuwa ta dafe kanta da takeji yana jujjuyawa.

    Kana duk da sanyi da ake tsulawa a garin wani irin zufane ke tsastsafo mata ta ko ina.

    Cikin sauƙe ajiyar zuciya,  ta juya gefen hagunta ta karanta A’uziyya ƙafa uku kana ta canza hannun kwanciyar ta zuwa dama.

    Sai dai sam baccin yaƙi zuwa mata, sai ta kama karatun Alqur’ani cikin sassayan sauti,

    Cikin ikon Allah ta samu bacci ya kuma yin awon gaba da ita.

     

    Baki ɗaya Wunin wannan ranan akasalance tayi koda abinci ta kasa ci haka zalika koda yawan surutu sai ta rage sosai mafarkin ya tsaya mata arai da zaran ta tuna irin mafarkin da tayi sai taji zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske.

     

    Da daddare cikin ikon Allah data karanta Alkur’ani mai girma tare da bin haddarta da Malam Liman ya bata sai taji sauƙin abin aranta duk da kuwa bawai ta daina jin tsinkewar zuciyar bane amma ya ragu sosai.

    Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare Khausar suna zaune a farfajiya gidan Hajja Nana su uku ita Yaya Abba da kuma Dije suna hira jefi-jefi take sanya musu baki aciki daga ƙarshe ma ta miƙe tace zata je ta kwanta sai Dije ma ta miƙe ganin haka yasa Yaya Abba ya musu rakiya har gida.

     

    Washe gari:Da safe still haka Khausar ta tashi bata da wani ku zari koda abinci ne ta kasa ci iyakacinta tasha Tea ko ruwan kunu sannan ta kasa faɗawa kowa irin mafarkin da tayi domin jikinta ya mutu sosai da mafarkin.

    Da daddare ba kinta ɗauke da Sallama tashiga gidan Hajja Nana.

    Asaman laɓɓa Hajja Nana ta amsa mata Sallamar tana binta da harara dan tunda taƙi markaɗa mata wake take jin haushi ta.

    Ita kuwa khausar bata masan Hajja Nana nayi ba ta nemi waje ta zauna tare da kallon Hajja Nana tace.

    “Yunwa nakeji ki bani abinci zanci”.

    ta faɗa tana kallon ƙorenta dake jere guda goma sha Uku.

     

    Harara Hajja Nana ta wurga mata tace.

    “Gashi ki ɗauka ki ci”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da Matsawa jikin ƙoren tashiga buɗewa ɗaya bayan ɗaya tana dubawa saboda taga gidan Malam Liman anyanka kaji cikin Sa’a kuwa tana buɗe ɗayan taga Jan miyar dage-dage da kuma tuƙeƙƙen tuwon shinkafa.

    Ta gyara zamanta tare da wanke hannunta ta fara cin tuwon cikin Mintuna kaɗan ta cinye tass sannan ta kuma janyo wani Ƙoren dan sosai take jin yunwa sannan bata wasa da cikinta dan ita dai ko ciwo bai cika hanata cin abinciba karo na forko kenan a rayuwarta da abu ya tsaya mata a rai har ya hanata cin abinci na kwana biyu son ta Tara yunwar shiyasa.

    ta cinye ƙore  biyun tas dan dama tuwon ba wani mai yawa ake samata ba tunda akwai yawan kanukan.

     

    Hajja Nana kuwa juyawa tayi da mamaki ta kalleta kafin tace.

    “Yanzu har kin cinye tuwon nan”.

    Kai Khausar ta gyaɗa mata tace.

    “Na cinye mana kuma yanzu ma ƙarawa zanyi dan yunwa nakeji rabo na da abinci tun shekaran jiya da daddare fa sai dai in ta Shan abu mai ruwa-ruwa”.

     

    Taɓe baki Hajja Nana ta kuma yi tace.

    “Toh bubbuga rumbu ga shican ki ƙara ki cinye duka ma in Kinga dama”.

    Ta Faɗa tare da tura mata wani akoshin.

     

    Ɗauka Khausar tayi kamar wasa ta cinye dake abincin ba wani da yawa ake sawa aƙoron ba dake sun san cewa ƙorenta da yawa mafi yawan lokuta ma loma ɗaɗɗaya takeyi ako wani ƙoren idan tayi loma sha uku ya wadatar mata a dai cikin tsohuwa ta kuma tsinci nama ta cinye to shiyasa ba’asa mai yawa.

     

    Ita kuwa Hajja Nana ganin yanda Khausar ke cin abinci yasa tayi zaton gatse take mata ta harareta da faɗin.

    “Mutum kamar jaki wannan ci haka ki cinye wannan ƙoren ki cinye wancan”.

    Ta ida maganar tare da sake tura mata wani ƙoren.

     

    Ita kuwa khausar ta ƙoshi amma saboda ta ƙular da ita yasa ta janyo ta buɗe naman kan abincin ta cinye sannan ta gutsiri kamar loma biyar ta zuba akwanan dake empty.

    Wani kwanon Hajja Nana ta kuma tura mata still ta cinye naman ta kuma gutsura ta zuba a sauran kwanon.

     

    Hajja Nana ta dube ta cikin tsareta da ido tace.

    “Wai har yanzu baki ƙoshi ba?”.

     

    Khausar cikin yamutsa fuska ta gyaɗa kai kana tace.

    “Eyyy ban ƙoshi ba”.

    Wani akoshin Hajja Nana ta sake tura mata, Khausar kuwa laluma ta cigaba dayi idan taji da nama ta cinye ta gutsits-tsira tuwon ta bari.

     

    Ita kuwa Hajja Nana kamar wacce akace ta leƙa taga aika-aikan da Khausar keyi da tuwon ta miƙe cikin fushi tace.

    “Shegiyar yarinya gantalelliya  ni kike nunawa barikanci, ‘yar banza kinje kin zauna gidan Mayu kema kin koma kamar Mayya, sai cin nama kamar kura, wato ma duk naman kike lalubewa dan mayta ai dai na sani in dai ba cikin zanine da keba ai yaci ki ƙoshi”.

    Ya mutsa fuska Khausar tayi tare da riƙe ƙugunta tace.

    “Naci ɗin idan ni Mayya ce kinsan inda na samu maita, tunda nazo saboda shegen maƙo ko zabuwa ɗaya kin kasa yanka min gaki da Zabbi kamar zasu kashe ki ga shanu kuma aina Babana ne”.

     

    Salati Hajja Nana tayi tare da fashewa da kuka.

    Kasancewar duk dare aƙofar gidan ta suke zama yasa Baffa Umaru daya ji sautin kukan ta ya miƙe kasancewar Allah ya bashi kunne komai ƙanƙantar sautin abu ya kan iya ji.

     

    Ganin Hajja Nana na kuka yasa Baffa Umaru nufarta tare da cewa.

    “Addah Nana Meya faru?”.

    Nuna Khausar tayi  da hannu kana tace.

    “Wannan ‘yar Usmanu har zata min gori wai gadon Ubanta na riƙe kaji shegiyar gantalalla yarinya dan ma Allah yayi dan ke macece!”

     

    Ƙasa da murya Baffa Umaru yayi yace.

    “Dan Allah Addah Nana kiyi haƙuri kinsan yarinta ke damunta idan ta girma ba zatayi ba”.

    Ya ida maganar tare da jan hannun  Khausar suka fice waje.

     

    Bayan sun fita ya juya ya kalleta yace.

    “Haba Khausar kidena ki koyi yanda zaki zauna da manya kinga Addah Nana tsufa ya kamata tana buƙatar rarrashi da lallami, kinga duniyar nan ba matabbata bace idan yau kaine gobe ba kai bane ita rayuwar nan bata da tabbas, ki koyi magana mai daɗi ke idan Mahaifinki ina ita fa ɗan ta ne data haifa acikinta kuma ɗan ta mafi soyuwa agareta kada ki sake haka kinji Khausar am”.

     

    Ta gyaɗa masa kai da faɗin.

    “Toh shikenan Insha Allah bazan sake ba”.

    Ya shafa kanta yana murmushi yace.

    “Allah ya miki albarka kizo muje gidana mu kwana zansa ayanka miki Zabbi kici tun da mun gama cin abinci”.

     

    Kai ta gyaɗa tare da yin murmushi tace.

    “Toh”.

    Ya riƙe Hannunta suka tafi suna tafiya suna hira har suka isa gidan bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga gidan Adda Adama ta fito daga ɗaki tare da amsa musu sallamar.

     

    Kallon Adama Baffa Umaru yayi yace.

    “Akwai nama ne?”

    Adama tace.

    “Eh akwai Zabbin da aka yanka da yamma yanzu nake ƙarasa dahuwarsu”.

     

    Yace.

    “Toh shikenan ki ƙara sa gyarasu ki kawo ma wannan Kuran Birnin taci”.

    Dariya Khausar tayi tana zama akan taburman da Adama ta shimfiɗa musu, shi kuma Baffa Umaru ya zauna daga gefenta yayin da Adama taje taci gaba da aikinta kasancewar farin wata ya haska ilahirin garin.

     

    Anutse Baffa Umaru ya kira sunanta da faɗin.

    “Khausar”.

    Ta ɗago kanta tana kallon fuskarsa acikin farin watan kafin tace.

    “Na’am”.

    Idanunsa kanta yace.

    “Kinsan kamannin Babanki?”.

    Kai ta girgiza masa tare da faɗin.

    “A’a bansan kamanninsa ba”.

    A sanyaye yace.

    “Amma kin san akwai Baffanki ai yayan Babanki Hammadu Ɓadamaya ko?”.

     

    Tace.

    “Eh amma Ɓadamaya yake ko?”.

    Yace da ita.

    “Eh yana can Ɓadamaya dashi da Iyalansa da kuma ahalinsa gaba ɗaya.

    Insha Allah wataran Zakije shida Babanki Uwa ɗaya Uba ɗaya”.

    Kai ta jinjina da faɗin.

    “Eh Mommy na tafaɗa min cewa inada Baffa yana can Ɓadamaya dashi da matarsa da kuma ‘Ya‘yansa”.

     

    Murmushi yayi yace.

    “Toh idan kinje zaki ga mai kamannin Mahaifinki sak da sakin  sunan sa Aliyu shine yake kama da Mahaifinki ya gaji Babanki komai da komai kuma shine aka aurawa yayarki Nenne”.

    Kai ta gyaɗa tace.

    “Toh yaushe zanje in gansa?”

    Yace.

    “Kinga kamannin Mahaifinki kamar balarabe kinga ba yabon kai ba mutanen Rugar mu duka kyawawa ne amma kyawun mahaifin ki ya fita da ban farin Mutum ne kyakkyawa ga kuma gashin kansa mai tsawo da sheƙi wannan gashin naki ma shi kika ɗauka”.

     

    Idanunta ta lumshe cike da kewar mahaifinta sai kuma ta buɗe su tace.

    “Aikam nasan gashin sa na ɗauka ba Mamansa ba da kai agwagwiye”.

    Murmushinsa ya faɗaɗa da faɗin.

    “Ina Addar tawa kike yiwa ba’a itama tsufa ce yasa gashinta kaɗewa”.

    Murmushi tayi tace.

    “Ai lalle kam”.

     

    Sai kuma ta dai-dai-ta nutsuwarta tace.

    “Ku kuma dama nan ne asalin Rugarku?”.

    Kai ya gyaɗa mata yace.

    “Eh asali nan ne Rugar mu iyaye da kakanni”.

    Tace.

    “Toh Meyesa ita Hajja Nana ta dawo nan kuma ina ne asalin garinsu Babanmu?”

    Murmushi yayi yace.

    “Asalin garinsu Babanki yana da nisa lokacin da Addarmu tayi aure ta daɗe kafin tazo ta samu haihuwa to data haifi na farko sai Allah ya sake kawo wasu akan lokaci ta haifi yara uku sai Allah yayiwa kakanki daya haifi Babanki rasuwa,sai ta nemi zata dawo to data nemi zata dawo sai sukace tabarmu su yaran ita kuma tana son yaran sosai sai tace Inde akan dukiya ne tabar musu duka subarta ta taho da ‘Ya‘yanta”.

    Zama Khausar ta gyara tana sauransa da kyau.

    Shi ko a hankali ya cigaba da cewa.

    “Dake dangin Mahaifinki mutane ne masu karamci sai sukace su ba dukiyar su suke buƙatar ba kawai dai suna so suriƙa ganin ɗan uwansu ne sannan ita macece kada subar mata nauyi amma tunda tana son Zama da ‘ya’yanta baza su hanata ba sai suka bata duka gadon Mahaifinki da kuma na Baffanki da ƙannensa mata biyu hadda mai sunanki.

     

    A ranar da tashigo Rugar nan tashigo da aƙalla shanu sun kai ɗari biyu sannan harda raƙuma da tumakai duk gadon sune aka ɗauka aka basu suka dawo”.

    Sassayan ajiyar zuciya ta saki tana jinjinawa lamarin.

    Baffa Umaru ya cigaba da cewa.

    “Toh tun daga lokacin ne zamanta ya dawo nan daga baya Allah yayiwa mahaifan mu rasuwa da gida huɗu ne kacal anan mahaifinmu su suka fara kafata da duk nan dajine mahaifinmu ne ya sare bayan rasuwar mahaifinmu da kuma mahaifiyarmu,

    itace ta zame mana Uwa da uba tun muna yara itace ta renemu nida Mahaifinki mun taso tare atare mukayi wasan ƙasa ta raine mu tare ta zame mana kamar uwa Shiyasa mu awajen mu Adda Nana ba ya bace kaɗai uwa ace a garemu”.

     

    Ita kuwa khausar Ajiyar zuciya ta kuma saki tare da faɗin.

    “Ikon Allah Allah mai iko Mabuwayi Gagara misali”.

    Murmushi Baffa Umaru yayi yace.

    “Kin gane ko mu Addah Nana Uwace agaremu ba Ya ba sannan maganarta Umarni ne awajenmu muda ‘Ya’yanmu babu mai saɓa mata har jikokin mu kinga keda kika zo kina wannan abin sai akaga lallai ta samu karan tsaye”.

    Murmushi Khausar tayi tace.

    “Lallai dai kam,to amma ina ne asalin su Babanmu?”.

    Murmushi yayi yace.

    Gobe zan faɗa Miki Idan Allah yakaimu rai da Lafiya zan ƙara sa baki labarin insha Allahu”.

     

    “Toh Allah ya kaimu goben lafiya”. Cewar Khausar

     

    Cikin sauƙe numfashi yace.

    “Naji ma Addah Nana na cewa kafin ki koma Abbah zai kaiki Ɓadamaya kije kiga Baffanki da ‘Ya‘yansa”.

     

    “Toh ina kuma ance da nisa?”.

    Khausar ta tambaya

     

    “Eh danisa amma ai tafiyar wuni ɗaya ce zaku isa”.

    Ya bata amsa.

     

    Miƙe sawunta tayi bisa taburmar tare da cewa.

    “Toh shikenan ba matsala, Insha Allahu zamuje, nima ingansa sannan kodan inga mai kama da Babana”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Sannan kuma kafin ku tafi zakuje kiga Addarki ‘yar Baffanki da yake Ɓadamaya tana nan Rugar Fulani dake ma ƙobtanmu Adda Ikki aikin santa?”.

    Murmushi tayi tare da gyaɗa masa kai tace.

    “Eh na santa ai itakam tana zuwa har gidanmu ta dubani duk dangin Babana ma ita nafi sani”.

    Yace.

    “Toh shikenan Zakije wajenta kiyi kwana biyu”.

    Tace.

    “Tun kwanaki nake cewa Hajja Nana zanje in dubata, tace min ba yanzu ba, wai in bari ingama sanin mutanen garin nan”.

    Adama dake sauraron  hiransu ta miƙe hannunta riƙe da kwanan da ta gama gashin Zabbin dake ta tashin ƙamshi sannan ta haɗo musu da madara mai ɗumi.

    Akan tabarmu ta ajiye musu su duka ukun atare sukaci.

     

    Gyatsa mai sanyi Khausar kana tace.

    “Kai gaskiya naci naji daɗi Nagode”.

     

    Bayan sun kammala ne Khausar tashiga ɗakin Adama ta kwanta Adama kuwa ta nufi ɗakin mijinta suka kwanta tare.

     

    Can cikin dare kamar misalin ƙarfe biyu Baffa Umaru ya miƙe zaune, tare da kasa kunnensa sosai wanda hakan ya kasance ɗabi’arsa ne,

    domin shine Garkuwar Rugar tasu,  jin motsin tashin sa yasa Adama miƙewa ita ma ta zauna, kusa dashi tana faɗin.

    “Lafiya”.

     

    Ajiyar zuciya ya saki da faɗin.

    “Naji tsayuwar mota daga can nesa sannan naga haske yashigo har cikin garin nan kamar da akwai wani abu ko dai munyi baƙi ko kuma wani abu!”.

     

    Ahankali tace.

    “Toh yanzu fita zakayi kenan?”.

     

    “Dole in fita ai Adama idan ban fita ba ‘yan uwana zan bari wani abu yazo ya ritsa da mune ai bazan bari ba dole in fita inga ko menene”.

    Ya faɗa a hankali.

    Ita kuwa Adama  riƙe hannunsa tayi fuskarta na bayyanar da tashin hankali tace.

    “Nikam ina tsoro wallahi”.

    Da sauri yace.

    “Kada ki damu Insha Allah babu abinda zai faru wanda Ubangijin bai sani ba”.

     

    Kai ta girgiza kana tace.

    “Kai rashin network ɗin garin nan yana damun mu wallahi, kaga da akwai network tunda yawanci kowa yana da waya zaka kik kira su awaya kowa ya fito kaga idan yaso sai sufito ku haɗu Atsakiyar garin amma Ni ina tsoron fitarka kai kaɗai”.

    Suna cikin Maganar ne sukaji antura ƙofar gidansu anshigo Murfin ya fadi ƙasa Kifff kasancewar ba wani Murfin kirki bane gadon kara ne da gwafa aka haɗa.

    Cikin han zari ya mike ya tsaya.

     

    Itama miƙewa tayi da saurin ta riƙe hannunsa tace.

    “Fita zakayi dan Allah kada ka fita ka tsaya dan Allah kar ka fita”.

    Ya juya ya fuskanceta yace.

    “Ya kike so inyi idan ban fita ba kina jifa anshigo gidan nan”.

    Yana ida maganar ya fin cike hannunta dake cikin nasa ya fita.

    Cikin sauri ta shari gabansa ta fito ya zama na itace agaba shi yana bayanta.

     

    Suna fitowa idanunsu ya sauƙa akan mutanen uku dake sanye cikin baƙaƙen kaya hannunsu riƙe da bindigi da kuma toch ligh mai masifar haske.

    Arazane Adama tace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakin”.

    Ƙaran buɗe ƙofa da kuma sautin Muryan Adama ne ya fito da Khausar daga ɗaki wacce farkawanta babu daɗewa tana fitowa sukayi saurin kashe mata ido da hasken toch ligh dinsu ita da Adama.

     

    Cikin daga Murya suka ce da Adama

    “Ki matsa agabansa kada jini ya taɓa ki ki matsa kada mu illataki!”.

    Aruɗe tace.

    “In matsa agabansa!?Bazan matsa ba, ku suwaye ne? sannan me kuke nema? me kuka zo yimana acikin daren nan?”.

     

    Ɗaya daga cikin sune yace.

    “Kashe sa muka zo yi!”..

    Cikin tsananin tashin hankali tace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n hasbunallahiwani’imanwakil.

    dan Allah kada ku kashesa,me yayi muku zaku kashe sa?,Meyesa?”.

     

    Ɗaya daga cikinsu ba wanda yayi magana da farko ba yace.

    “Saboda yana hanamu rawan gaban hantsi zamu kashe sa muga takan tsiya bashi yace taurin kai ba”.

     

    Baffa Umaru kuwa murmushi yayi mai cike da Jarumtaka da kuma rashin tsoro yace.

    “Ni zaku kashe?,To idan kunga na mutu kwana nane ya ƙare,Kuma Ubangiji shi ya ɗauki raina.

    Amma ku baku isa ba babu mai rayawa babu mai kashewa sai ubangiji.

    Dan haka raina baya hannunku kuma ajalina baya hannunku idan kunga na mutu ma kada kusa aranku ku kuka kashe ni!”.

    Ya ida maganar tare da zabura zai shiga ɗaki dan ɗauko kwari da bakasan.

    Ita kuma Adam da saurin riƙesa dai-dai lokacin da suka harbesa  akafaɗarsa na dama.

     

    Ƙaran harbin ne ya tashi gaba ɗaya ilahirin mutanen garin Aɓangaren Hajja Nana kuwa tana tashi daga bacci sanadiyyar ƙaran harbin ta dafe kanta da faɗin.

    “Wayyo Umaru na Allah ka kare mana Umaru” domin shine mutum na farko daya faɗo mata arai cikin rawan jiki ta miƙe tare da ɗaukar zaninta ta ɗaura kana ta ɗauki mayani ta yana.

     

    Aɓangaren Baffa Jauro yana miƙewa yace.

    “Umaru”.

    Ya kira sunan sa cikin daga murya.

    Baki ɗaya ‘Yan uwansu da sauran jama’a babu wanda ya faɗo masu arai sai Baffa Umaru ko wannensu daya farka zai ce.

    “Wayyo! Umarunmu”.

     

    Shi kuwa Umaru juyawan da zai yi sai suka samu damar sake harbinsa ahaƙarƙarinsa na hagu.

    Cikin ƙarfin hali da ɗaga sautin Muryar sa yace.

    “La’ilah ha Illallahu Muhammad Rasulullahi(S.A.W) Adda Nana ki yafemin yau kam zasu kashe ni ki yafemin kece madadin Uwa awajena duk abinda nayi ki yafemin yau kam sun kasheni sun kashe ni,Yaya Jauro, Yaya Sadu, Yaya, GarGa, Yaya Liman, Yaya Garba,Yaya Sale yau kam sun kasheni sun cire muku ɗaya cikin goma kun zama ku tara!”.

     

    Adama kuwa Aruɗe ta riƙesa jikinta na kyarma taja numfashi amma ta gagara sakewa.

    Ita kuwa Khausar numfashin taja amma ta gagara sakewa saboda tsananin ruɗu da tashin hankali da tashiga kamar zata shiɗe!.

    Ihun da kiran sunan da yake yasa suka janye toch ligh ɗin su dake fuskar Khausar da Adama suka mai dashi sama wannan dalili ya bawa Khausar damar kallon fuskokinsu da kyau amma baki ɗaya jikinta ya sandare bata da wani kataɓus ɗin motsawa.

     

    Su kuwa ƙirjinsa suka saita suka sake harbinsa akwai wani ƙaton tukunya agefen  ya ratsa ya ɓula.

    Shi kuwa Baffa Umaru ƙirjinsa ya dafe da faɗin.

    “Laila Ha’illalhu Muhammad Rasulullahi (S.A.W)” Shikenan rai yayi halinsa.

     

    Su kuwa mutanen garin baki ɗaya gidan Baffa Umaru suka nufo ko wannensu na rataye da kwari da bakansa sukuwa jin hayaniyar mutanen yasa suka ɓulla ta bayan gidansa suka fice tare da zuwa inda suka bar motarsu suka shiga.

     

    Shi kuwa Baffa Umaru ta cikin tukunyar gefensa ya faɗa jini nata ɓulɓula.

    Hajja Nana ce farkon shigowa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa tana isa tsakiyar gidan,

    Ƙofar dakinsa ta nufa, tana isa inda yake ta janyo gawar ta rungume tana kuka tare da faɗin.

    “Umaru! Umaru!! Umaru!!! Yau kuma mai zan gani gawar Umaru zan riƙe ahannuna kamar yanda na riƙe gawar Usmanuna!”.Cikin kuka sosai take maganar.

     

    Su Baffa Jauro da sauran mutanen ne suka shigo sudai Allah Allah suke su ƙarasa cikin gidan suga abinda ya faru dashi sam basu yi tunanin bin bayan mutanen ba.

    Ita kuwa khausar hanyar da suka bi suka fita take nuna musu da yatsa ta kasa furta komai bare kuma ta taɓuka wani abun Yaya Abba ne da ya shigo yace.

    “Yayane Khausar!?”.

     

    Cikin matsananci kuka da tashin hankali tace.

    “Yaya Abba sun gudu sun kashe shi sun gudu sunbi ta nan na gansu sunbi tanan!”.

    Azabure Matasan suka bi wajen ina tuni sun shiga motarsu sun gudu sukuma su Baffa Jauro, Baffa, Sadu da sauran rungume gawar ƙaninsu sukayi suna kuka.

    Hajja Nana kuwa tattaɓa jikinsa tayi, Sadik yace.

    “Baba mu ɗaukesa mu kaisa asibiti”.

     

    Sake rungume gawarsa Hajja Nana tayi tace.

    “Saddiƙu wani asibiti zamu kaisa bayan sun kashe sa baya numfashi bashi da rai!?”.

    Jauro ne ya karɓesa ya duba shima ya rungumesa ganin ya rasu Baki ɗayan su akan Gawarsa suka kwana.

    Ita kuwa khausar gaba ɗaya ta rikice ta duburburce bata taɓa gani ankashe mutum agaban ta ba sai lokacin tayi kuka har ta godewa Allah manyan Idanunta sunyi luhu-luhu dasu ba abinda ke faɗo mata arai kamar yanda sukayi hira dashi.

     

    Washe gari  akaje aka kira

    Ƴan sanda acikin gari suka je sukayi bin cike tare da rubuce-rubucen su na banza da wofi sannan akayi masa sallah aka kaisa gidan sa na gaskiya.

    Kana akazo aka zauna zaman makoki, Addar Khausar Ikki da zata je wajenta a Rugar Fulani ce tazo da taji labarin rasuwar Baffa Umaru tana zuwa kai tsaye gidan Baffan Umaru ta nufa duk ‘yan uwan suna can suna karɓan gaisuwa.

     

    Khausar na ganinta ta tashi da gudu ta Rungumeta tana kuka tace.

    “Addah Ikki agaba na agabana fa suka kashe shi sun harbesa sun kashe sa ya rasu har lahira!”.

    Addah Ikki tace.

    Kiyi shiru Khausar duk mai rai mamacine addu’ar mu yake buƙata”.

    Kai Khausar ta gyaɗa amma ta gaza tsaida kukan ta Ganin haka yasa Addah Ikki taja hannunta suka fita zuwa gidan Hajja Nana.

     

    Suna Shiga Khausar ta tsaya cikin Muryanta daya dishe da kuka tace.

    “Ni ina tsoro bazan shiga ɗakinta ba akwai kuliya”.

    Addah Ikki tace to kitsaya na koreta sannan tashiga ɗakin ta fito da kuliyar tasa awani ɗaki ta rufe.

    Sai asannan Khausar ta yarda tashiga ɗakin bayan sun zauna Addah Ikki ta zauna ta riƙa yi mata nasiyya tare da kwantar mata da hankali.

     

    Yaya Abba ne ya ɗauki wayarsa ya tafi Bishiyar ƙare zancenka ya kira duk dangi na nesa ya riƙa sanar da su har ya kira Baffa Hammadu na Ɓadamaya ya sanar masa.

    Shima washe gari Baffa Hammadu ya ɗauko iyalansa baki ɗaya suka taho da yammaci gab maghariba motocinsi su guda biyu ajere suka shigo Rugar kai tsaye ƙofar Hajja Nana suka nufa sukayi parking motocinsu.

     

    Ita kuwa Khausar na cikin ɗakin Hajja Nana manne da jikin Addarta Ikki suka jiyo Sallama,

    Addah Ikki ce ta miƙe da faɗin.

    “Laaa Umma na sannan sai Baffanta yashigo daga bayansa kuma wani kyakkyawan matsakaici mutun ne fari ƙal kamar balarabe yayin da Yaya Abba ke biye dasu abaya.

     

    Durƙusawa Khausar tayi tare da fashewa da kuka kalaman Baffa Umaru ne kawai keyi mata suwwa akunne.

    Rarrashinta Addah Ikki ta shiga yi tana bata haƙuri da kyar ta tsaida kukan tace.

    “Addah Jiya da daddare Baffa Umaru kece min Baffana na Ɓadamaya yana da wani ɗan sa dake tsananin kama da Babana Addah Ikki wannan shine ke kama da Babana?”.

    Cikin matsanancin kuka ta ida maganar.

     

    Kai Addah Ikki ta gyaɗa mata alamar Eh.

    Ita kuwa khausar kanta ta kife acinyar Addah Ikki ta cigaba da rera kukanta.

    Baffan Hammadu  ne ya riƙe hannunta ya cewa.

    “Khausar kiyi shiru kada kiyi kukan rashin Uba nima Mahaifine agareki ni zan tsaya Miki madadin Uba ako ina dan dai Banason rabaki da mahaifiyar kice Shiyasa na barki kike zaune tare da ita muddin ina raye zan maye Miki gurbin Uba”.

    Cikin raunin murya tace.

    “ Baffa Allah hokke sabbugo”.

    Ameen thumma ameen suka amsa.k

    Kana suka tafi gida Baffa Umarun.

     

    Bayan angama zaman Makoki  Khausar tabi Addarta Ikki can Rugar Fulani tayi kwana biyu sannan suka dawo bayan sun dawo akayi addu’ar bakwai Baffanta na Ɓadamaya yafara shirin tafiya sai asannan Khausar taga sauran ‘ya‘yan sa daya zo dasu harda Mata bayan sun sake ganawa ne suka tafi.

     

    Akwana atashi ba wuya Khausar ta cika Makwanni uku Arugar Jauro yaya yayin da Baffa Umaru keda mako biyu da rasuwa kullum ‘Yan uwansa matarsa  kuma jama’ar gari cikin yi masa addu’a suke domin baza su taɓa mantawa dashi atarihin rayuwarsu ba da kuma irin gwagwarmayar da yayi adomin kare rayukansu.

     

    GEMBILA

     

    Acan ɓangare makarantarsu Khausar kuwa ayaune aka gama gyara ilahirin makarantar daga nesa idan ka hango ginin ba zakayi zaton cewa a Gembila makarantar take ba koda a ƙasashen turawa ne sai ’Ya’yan wane da  wane saboda yanda aka ƙawata ginin Makarantar fentin ya kasance Maroon and White haka zalika gate din Maroon anda white ne daga sama An rubuta

    *Al’ANSAR ACADEMIC SCHOOL* Rubutun ma Maroon and White ne.

     

    Acikin harabar makarantar kuwa Moddibo ne tsaye hannunsa harɗe aƙirji ya yinda manyan idanunsa ke lumshe yana kallon tsarin ginin Makarantar da akayi wani irin Up stair cycle daga cikin harabar makarantar zagaye yake flowers masu kyau da tsari.

    M Jameel ne yace.

    “Gaskiya Moddibo kayi ƙoƙari makarantar yayi masifan tsaruwa”.

     

    Murmushin gefen baki Moddibo yayi wanda ke ƙarawa fuskarsa kyau yace.

    “Masha Allah haka akeso”.

    Ya ida maganar tare da juyewa cikin nutsuwarsa yake tafiya har suka fita acikin harabar makarantar suka shiga motarsu dake gefe afake.

    Moddibo ke Driving yayin da M Jameel ke gefen mai zaman banza ƙira’an Sudai’s na tashi cikin suratul Nisi’i Moddibo kuwa jinjina kai yayi ayoyin na ratsa sa.

    M Jameel ya juya ya kalli Moddibo da bakinsa ke motsi alamar karatun yake bi yace.

    “Moddibo kamar akwai motar dake bin mu  fa”.

    Kai Moddibo ya girgiza yace.

    “A’a ba binmu akeyi ba”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa still yana kallon mirror bai dai ce komai.

    Daga nan suka ci gaba da tafiya ganin still kamar binsu akeyi yasa Moddibo ya tsaya.

     

    Ga mamakin su ganin su tsaya yasa wancan motar tayo kansu gadan-gadan…!

     

     

    *Wasan fa yanzu aka farashi. Bakin zaren labarin sun kai 12 dozi. Kenan. Akwai ababen dake a duhu fa. Saninsu sai kun bibiyu Al’ƙalamin Shatu yar Aliyu Garkuwa. Jikar Muhammad Babayo Maiturare. Kana kuma (BODDIN DEDDE)*

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 15

    Sakayyah 15

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 15_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

     

    *Saura ƙiris FREE PAGE dai yazo ƙarshe in sha Allah mun kusa gamawa. Yar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci domin littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP. 09097853276. Kana in saki a Groups ɗin da zamuci gaba da posting.*

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

     

    Anutse Moddibo da M Jameel suka fito daga motar dai-dai lokacin da Malam Ahmad ya fito daga harabar gidan ganinsu yasa ya faɗaɗa fara’ar fuskarsa tare da faɗin.

    “A’a Masha Allah tagwayen Ummi kunzo?”.

    Murmushi sukayi Atare kana suka ƙara sa kusa dashi.

    Kallonsu Malam Ahmad yayi fuskarsa ɗauke da murmushi kana yace.

    “Sannunku da zuwa ku isa daga ciki zan dawo mu gaisa”.

    Kai suka gyaɗa masa atare kana suka nufi haraban cikin gidan shi kuma ya fice.

    Bakin su ɗauke da Sallama suka shiga farfajiyar gidan,

    Kusan a tare suka juyo suka kalli juna lokacin da idanunsu, ya sauƙa akan shimfiɗar ƙaton taburma da Ummi ta shimfiɗe asaman baranda kana ga wani lallausan Chanis capet dake fitar da ƙamshi da wasu manyan tuntuna guda uku ɗaya na tsakiya biyu na gefe da gefe sai manyan tire guda huɗu akai tiren farko na kayan fruit ne kama daga,Tuffa, Inabi, Gwanda, Dabino, Abarba, Ayaba, Kankana, Lemo duk anyi slinzing ɗinsu.

    Ɗaya tiren kuma Flaks ɗin tea ne da ma dai-dai-tan kofina masu kyau sai gongomin madara da Bounvita.

    Sai kuma ɗayan dake ɗauke da Flaks din kunu agefe, sai kuma na ƙarshe wanda yafi su girma manyan kulo-line masu kyau kula na farko Perpesoup ɗin jan naman rago ne daya dahu ligif yana fitar da ƙamshi sai ɗaya kulan kuma soyeyyen dan kalin  ne da ƙwai gwanin ban sha’awa.

    Jin Sallamar sune yasa Ummi saurin fitowa daga falo tare da faɗaɗa fara’ar dake Samar fuskarta kana tace.

    “Lale marhaba sannunku da zuwa Babana”.

    Murmushin gefen baki Moddibo yayi wanda ke ƙara masa kyawun fuskarsa kana ya lumshe idanunsa tare da faɗin.

    “Barka dai Ummina”.

    M Jameel kuwa baki ya tura cike da Shagwaɓa kana ya langwaɓar da kai Idanunsa akan Umminsa sai kuma ya kalli Moddibo dake ƙoƙarin zama akan shimfiɗar da Ummi tayi kana yace.

    “Ni dai gaskiya na fara kishi Ummi mai yasa tun da har haka kike son Aliyun nan bakisa min sunan Babban naki  ba nima ki riƙa cemin Babana?”.

     

    Murmushi Ummi tayi Idanunta akansa ta zauna kana tace.

    “To ai kaima Babana ne ko ka manta Kai takwaran kakan kane Baban-Babanka.

    Dariya mai sauti yayi kana ya shafa sajensa tare da cewa.

    “Ƙwarai kuwa haka Abbana ke kirana da Babana munyi raba dai-dai Ummi ta kiraka da Babanta Ni kuma Abba na ya kira ni da Babana”.

     

    Gyaɗa kai Moddibo yayi cikin yanayin sanyin Muryansa ya Kalli M Jameel kana yace.

    “Oho dai amma nine na hannun daman Ummi”.

    Murmushi Ummi tayi cike da ƙaunarsu kana ta zauna daga gefensu Idanunta akan Moddibo dake motsa bakinsa idanunsa alumshe alamar tasbihi yake.

    Ganin haka sai ta miƙe dan kar ta takura masa ta ɗan ɗaga sautin Muryanta tare da cewa.

    “Bashir ga Yayanka sun zo baka zo kun gaisa ba”.

    Cike da ladabi Bashir ya fito kana yace.

    “Ummi kaya na nake gyarawa yanzu nake so in fito”.

    Ya Ida maganar tare da zama agefen Moddibo kana yace.

    “Yaya Moddibo ina wuni ya Ibada?”.

    Moddibo kuwa buɗe idanunsa dake lumshe ya buɗe tare da ɗaura hannunsa akan Bashir yana shafawa kana yace.

    “Lafiya lau Alhamdulillah ya karatu?”.

    Bashir ya amsa da.

    “Alhamdulillah”,Kana ya maida kallon sa kam M Jameel dake motsa baki da alama shima tasbihi yake ya kallesa tare da cewa.

    “Yaya Jameel Ina wuni ya ibada?”.

    M Jameel ya Amsa da.

    “Alhamdulillah”.

    Miƙewa Bashir yayi ya koma ya cigaba da aikin da yake.

     

    Moddibo kuwa bayan yayi tasbihi sai ya koma Azkharul masa ƙarfe shida da minti Ashirin da biyu aka kira Sallar maghariba Plate din Dabino da Ummi ta ajiye musu agabansu Anutse Moddibo ya miƙe tare da ɗaukan ruwa ya kuskure bakinsa kana ya dawo ya zauna.

    Shima M Jameel miƙewa yayi ya wanke bakinsa dabino Moddibo ya ɗauka ya buɗe sanan ya sanya abakinsa bayan ya furta.

    “Zahabazzaba’u Wabitallatil,Uruƙu wasu batul Ajri Insha Allah”.

    Anutse ya ke cin dabinon inda yaci sai ya sanya ƙwallon atafin hannunsa na hagu.

    Guda bakwai yaci kana ya dakata.

    M Jameel kuwa dabino Uku yaci kana ya janyo faranti kayan friut ɗin ya fara da Abarba.

     

    Lumshe idanu Moddibo yayi tare da ɗaukar Inabi ya kai bakinsa sai kuma ya buɗe Idanunsa akan Ummin data ƙara so wajen zama tayi tare da tsirawa M Jameel idanu baki ɗaya hankalinta da nutsuwar ta yana kansa.

     

    Iska Moddibo ya furzar daga bakinsa tare da jingina bayansa da jikin bangon ya lura da tun zuwansu wani irin kallon da Ummi ke bin M Jameel dashi kallone mai nuni da tsantsar so, da kuma ƙauna da shaƙuwa irin wanda uwa ke nunawa ƴaƴan ta.

    Ƙasa da kansa yayi yayin da yaji ruwan hawaye masu ɗumi na tsata-tsafo masa saboda ganin shi ya rasa wannan damar bazai samu irin wannan ba arayuwarsa ba still Kansa na ƙasa ba tare daya ɗago ba ya dai-dai-ta muryarsa tare da faɗin.

    “Ummi kiyi buɗa baki mana”.

     

    Sai asannan Ummi ta lura da kallon da take bin M Jameel dashi, Malam Ahmad ma murmushi yayi domin ya lura da kallon da Ummi kebin M Jameel dashi Shikuwa M Jameel sai alokacin ya ɗago kansa ya lura da irin kallon da Umminsa ke binsa dashi.

    Murmushi yayi mai cike da so da ƙauna.

    Kana yace.

    “Ya dai Ummina nayi kyaune ko muni kike ta kallona?”.

     

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta ɗan lumshe Idanunta tare da girgiza kai kana tace.

    “A’a kawai dai naga azumi ɗaya akayi ana biyu har ka rame”.

    Murmushi yayi tare da gyara zamansa kana yace.

    “Hmmm Ummi kenan ai kinga mu ba azumin ne kaɗai ba. akwai yawon zirga-zirga sannan abincinma bama nutsuwa mu cisa yanda ya kamata musamman ma idan na biyewa Babanki”.

     

    Jinjina kai Ummi tayi kana tace.

    “To yau kam anan sai kunci kuncika cikin ku sannan in dafa muku na Sahur ma ku tafi dashi”.

    Girgiza kai Moddibo yayi kana cikin sauri yace.

    “A’a Ummi ki zauna Innayi na mana sannan ga can Asma’u na taya ta yanzu idan mun koma sai mun rasa inda zamu sanya abincin a cikinmu”.

    Jinjina kai tayi kana tace.

    “Toh shikenan Babana”.

    Murmushi Moddibo yayi kana yace.

    “Ummi kici abinci mana”.

     

    Kai ta gyaɗa sannan ta janyo Plate ɗin dabinon ta ci guda uku Bayan tayi addu’ar buɗa baki.

    Malam Ahmad ma danino uku yaci sannan Ummi ta ɗauki Flaks da niyyar haɗa musu tea Moddibo dake cin friut yayi saurin cewa.

    “A’a Ummi bari sai munyi Sallah”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Toh shikenan sai kun dawo”.

     

    Miƙewa sukayi M Jameel da Moddibo suka ɗauki buta kana suka ɗaura alwala suka fice Malam Ahmad kuwa ya riga su fita.

    Kai tsaye masallacin ƙofar gidan su Ummi da Baban Asma’u ke limancin suka shiga. Suna idar da Sallar Maghariba bayan sun idar suka dawo cikin gida shigowarsu yayi dai-dai da rurin da wayar M Jameel keyi.

     

    Kallon Moddibo M Jameel yayi kana yace.

    “Innayi ce ke kira”.

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da cewa.

    “Uhm”.

    picking call din yayi ya kai kunnensa.

     

    Daga ɗaya ɓangaren Innayi tayi gyaran murya kana tace.

    “Jamilu lafiya baku dawo kunyi buɗa baki ba mai kuke yi har yanzu awaje?”.

    Sajensa ya shafa kana yace.

    “Innayi wallahi Ummi ce ta riƙe mu wai saidai muyi buɗa baki agidan ta”.

    Murmushi Innayi tayi kana tace.

    “Toh mu kuma na gidan mu ya zamu yi dashi”.

     

    Kallon Moddibo yayi sai kuma yayi Murmushi kana yace.

    “Innayi abawa Almajirai dai sai kibar mana na Sahur dan nasan kinyi miyarki mai daɗin nan miyar me kika mana ma tukunna?”.

     

    Dariya Innayi tayi kana tace.

    “Miyar roman da kake so na daddawa da ƙarago shi zanyi muku na Sahur”.

    murmushi ya saki tare da faɗin.

    “Yauwa ina son wannan miyar”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Toh shikenan sai kun dawo ka gaishe da Ummin”.

    Ta faɗa tare da katse kiran.

     

    Suna ida shiga gidan suka samu wajen suka zauna Ummi ta miƙe tare da ɗaukar Flaks da kofina ta haɗa musu tea mai kauri yana tururi kana ta zuba musu soyeyyen dankali da ƙwai.

    Anutse suka fara ci kaɗan Moddibo yaci ya janye hannunsa daga ciki.

    Kallonsa Ummi tayi kana tace.

    “Ya dai Babana kaci mana”.

    Murmushi Moddibo yayi tare da ɗaura hannunsa na dama akan shafefen cikinsa ya shafa kana yace.

    “Ummi na ƙoshi”.

    Girgiza kai Ummi tayi tare da cewa.

    “Kai Babana me ma kuka ci?”.

    Ɗan kwaɓe fuska yayi kana cikin sanyin murya mai kama da shagwaɓa ya lumshe idanunsa tare da cewa.

    “Ummi kar muje muna sallah abinci yan fitowa ta hancin mu”.

    Kallonsa Ummi tayi tare da murmushi kana tace.

    “A’a Babana me ma kuka ci da zai zazzago ta hancinku?”.

    Murmushi yayi tare da shafa sajensa zuwa gemunsa kana yace.

    “Allah Ummi mun ƙoshi ko ba haka ba J?”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da Hararan Moddibo ya cire hannunsa a Plate din dan kalin.

    Hira suka sake taɓawa kana Moddibo ya miƙe tare da kallon Ummi kana yace.

    “Ummi zamu tafi”.

     

    Jinjina kai Ummi tayi tare da cewa.

    “Idan kunyi sallah Isha’i zaku dawo ta nan?”.

    Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.

    “A’a Ummi sai wani lokaci”.

    Gyaɗa kai tayi tare da cewa.

    “Toh ku tafi da kunun nan”.

     

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da gyara tsayuwar sa kana yace.

    “Toh Ummi ina son kunun abamu zan tafi dashi”.

    M Jameel ya juya ya kalli Ummi tare da langwaɓar da kai kana yace.

    “Ummi Ni dai ba abani abinda nake so ba”.

    Cike da kulawa da kuma so ta juya ta kallesa kana tace.

    “Me kake so?”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Inabin za’a bani in tafi dashi”.

    Saurin Kallonsa Moddibo yayi sai kuma ya juya ya kalli Ummi tare da cewa.

    “Ummi kar ki basa yasha muna dashi agida”.

    Tura baki M Jameel Yayi kana yace.

    “Iyeee to na haƙura tunda ba aso ayimin kyautar”.

    Ummi Kam murmushi take Cike da ƙaunar su, ji takeyi tamkar su duka biyu a cikinta ta rainesu ta haifesu.

    Sallama suka mata kana suka fice suka shiga mota Moddibo ke mazaunin Driver yayin da M Jameel ke gefen mai zaman banza kai tsaye Masallacin da suke limancin na ƙofar gidan Sarki suka nufa sunyi tafiya mai ɗan tsayi kafin suka isa lokacin da suka isa ankira sallar Isha’i suka shiga Moddibo ne yayi limanci suka idar da Isha’i kana sukayi Asham bayan an watse kana suka fito suka shiga mota wannan karon M Jameel ke driving Kai tsaye gidan Innayi suka wuce.

     

    Ƙarfe takwas da rabi suka isa gidan bayan sunyi parking sun fito kai tsaye sashen Innayi suka shiga bakinsu ɗauke da sallama a farfajiyar gidan suka tarar da Innayi da Asma’u zaune Innayi dake gashin nama akan mangal da tarin gawayi agefenta ta daga kanta tare da Kallonsu kana ta amsa Sallamar su.

     

    Ƙara sawa kusa da ita sukayi M Jameel yaja kujera ya Zauna kana ya Kalli Innayi tare da cewa.

    “Innayi ya dai mai ake gasa wasa ne?”.

    Murmushi Innayi tayi kana tace.

    “Nama nake dan gasawa nasanku da cin nama kamar kuraye!”.

    Dariya M Jameel Yayi kana yace.

    “Aikam Innayi kin kyauta gashi asalin gashi na gargajiya kike yi”.

    Kai ta gyaɗa tana ɗaukar Plate tace.

    “Eh ai nasanku”.

    Ta ida maganar tare da miƙa musu naman data yayyanka ta zuba a Plate tare dasa musu yaji agefe sannan ta yaryara ɗa musu man shanu.

    Kallon Asma’u dake yi musu sannu da zuwa tayi kana tace.

    “Asms’u ɗauko musu capet su zauna”.

    Cikin murza kai gefen dama da hagu Modibbo yace.

    “Uhmm Innayi kin dai sanshi shi J ɗinki da son nama kamar kura”.

    Murmushi M Jameel yayi dan yasan tabbas Modibbo bai cika damuwa da namaba, asalima in dai gasheshene ko soyayya in dai yaci yanka huɗu zuwa biyar zaice muƙa-muƙinsa sun gaji da taunawa, in kuma dafaffene wani lokaci da haƙorin gaba zai ɗan tattauna in yaji ya gaji sai ya tura masa naman gabansa.

    Shi kuwa M Jameel Allah ya sani yana masifar son nama, shi kuwa Moddibo yafi bawa ƴaƴan itatuwa mahimmanci.

    Cikin murmushin yace.

    “Yoh in ban so namaba me zanso A.J Namafa shine maƙurar daɗi”.

    “A wurinka ba, gashi kuma kana son koyamin”.

    Cewar Moddibon,

    Asma’u kuwa ganin Innayi na kallonta cikin mamakin tace.

    “A’a Asma’u ɗauko musu abin zama mana”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa kana ta miƙe ta shiga falon ta ɗauko capet ɗin ta shimfiɗa musu awajen da yake agyare tass babu alamar ƙazanta.

    Zama sukayi akai, Innayi ta sake kallon Asma’u tare da cewa.

    “Haɗa musu Tea sannan kisa musu zuma yaji”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa kana ta miƙe ta zuba musu shayi tare da zuba wadataccen zuma aciki ta kawo musu.

     

    M Jameel kuwa Anutse ya kai yankan naman bakinsa lokaci ɗaya ya lumshe idanunsa tare da buɗe su akan Innayi kana yace.

    “Kai gaskiya gashin nan yayi daɗi sosai”.

    Murmushi Innayi tayi tare da kallon Moddibo dake cin naman kamar ko yaushe kamar dai dole, yana ɗan taunawa kaɗan-kaɗan cikin kula  tace.

    “Kai kuma fa Moddibo?”.

    Ɗago kansa yayi ya kalleta kana yace.

    “Uhm yayi”.

    Girgiza kai tayi kana tace.

    “Wato kai dai baza ka iya Yabawa ba kenan?”.

    Kansa ya sake ɗagowa tare da kallonta kana yace.

    “Ai gashinan J ya yaba kuma danɗanon harshen mu ɗaya ne ai”.

    Murmushi M Jameel da Asma’u sukayi.

     

    Innayi kuwa baki ta taɓe M Jameel da Moddibo suka cigaba daci Ahankali Moddibo ya ɗago hannunsa tare da kallon tsadedden agogonsa kana ya mayar da Kallonsa kan M Jameel tare da cewa.

    “Sai munyi sauri lokaci ya kusa J”.

     

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da cire hannunsa a Plate din kana yace.

    “Toh shikenan mu tafi”.

    Miƙewa Moddibo yayi tare da kallon Innayi kana yace.

    “Bari naje na canza kaya”.

    Daga haka ya juya ya nufi sashen sa, shima M Jameel bayansa yabi.

     

    Moddibo nashiga Bedroom ya sauya kayansa zuwa Jallabiya Coffee color tare da ɗaura farin hirami irin na samarin larabawa kana ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin ƙamshi.

    Anutse ya fito falo ya samu M Jameel da shima ya canza kayansa buɗe fridge M Jameel Yayi ya ɗauki goran faro mai sanyi sannan suka jera tare da Moddibo suka sauƙa.

     

    Kai tsaye sashen su Innayi suka koma batare da sun shiga farfajiyar gidan ba .

     

    “Toh Innayi mun tafi”.

    Cewar M Jameel

    Tana rufe roban yajin da suka ci nama dashi ta ajiye kana tace.

    “Toh Allah ya tsare muma yanzu muna bayanku”.

    M Jameel na gyara ɗaurin agogon dake tsintsiyar hannunsa ya kalleta kana yace.

    “Toh idan za kuje kuzo mu tafi mana sai mu sauƙe ku”.

     

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Ai akwai Napep zamu hau”.

    M Jameel kuwa kai ya Girgiza kana yace.

    “A’a ai abin baiyi ba bayan tanan muke tafiya kuma kuce zaki shiga Napep kawai kuzo mutafi”.

    Jinjina kai Innayi ta gyaɗa kana tace.

    “To bari mu tattara da sauri sai mu tafi”.

    “Toh”,M Jameel yace Shi kuwa Moddibo bai ce komai ba sai harɗe hannunsa da yayi aƙirji.

     

    Cikin sauri Innayi da Asma’u suka tattare wajen sannan suka sanya hijabansu kana suka rufe kichen da gidan suka fice abayan Mota suka zauna ita da Asma’u yayin da M Jameel da Moddibo ke gaba.

    Suna isa babban masallacin M Jameel yayi Parking Innayi da Asma’u suka fita suka nufi sashen mata su kuma suka shiga cikin masallacin daya cika sosai da al’umma.

     

    Bayan sun zauna Kamar ko yaushe M jameel ya buɗe musu da addu’o’in kana Moddibo ya gyara system ɗin sa tare da ƙara rage girms Idanunsa kana yasa lallausan tafin hannunsa ya gyara zaman microphone din dake gabansa tare dayin gyaran murya cikin sanyayyar sautin muryansa ya fara kamar haka:

    _“Auzubillahi Minal Shaiɗanir Rajim, Bismillahir Rahmanir Rahim.

    (10) Innalazina ya’akuluna, Amwalal yatama zhulman innama ya’akuluna fiy buɗunihim naraa,wasayaslauna sa’irah”._

    Jama’ar dake wajen masallacin cikin sassarfa suka ƙaraso cikin masallacin dan basa so koda harafi ɗaya ne su rasa daga cikin karatun Moddibo saboda baiwar muryarsa.

     

    Moddibo kuwa sanyayyar numfashi ya fesar tare da jingina bayansa da kujeran kana ya cigaba kamar haka:

    _“(11)Yusikumullahu fii auladikum,Lilzikri mislu hazzil unsaynan.Fa’in kunna Nisa’a fauƙasnatayni falahunna sulusa ma tarak,Wa’in kanat wahidatan falahannisf,Wali abwayhi likulli wahidin Minhumassudusu,Mimma taraka inkana lahuu waladun,Fa’in lam yakun lahu waladu wawarisahuuu abwahu fali ummihi sulus.Fa’in kana lahu Ikhwatun fali ummihi sudus min ba’adi wasiyyatin yusi biha audayn,abaukum wa’abna ukum latadruna ayyuhum aƙrabuna lakum naf’,a,Faridatan Minallah,Innalaha kana aliman hakima”._

    Ya dire ayar tare da jan numfashin sa da ya riƙe.

    Jinjina kai M Jameel Yayi yayinda ayoyin ke ratsa sa cikin yanayin sakewa ya lumshe idanu kana yace.

    “Aya ta gaba”.

     

    Jinjina kai Moddibo yayi kana cikin zazzaƙan muryansa mai sanyi da ratsa jiki kana da nutsuwa ya cigaba da jan ayoyin saida ya kai aya ta Ashirin kana ya tsaya.

    Shi kuwa M Jameel Cike da tsantsar ƙwarewa da nutsuwa kana da sanin makaman tafsir ya fara fassara ayoyin tare da cikekken kaddima da kowa amintattun haɗisai da suka da munasaba da ayoyin harma da sababul nuzur na ayoyi, lokacin ɗaya cikin masallacin ya sake samun nutsuwa tafsirin na ratsa su.

     

    Ƙarfe goma dai-dai suka tashi tafsir ɗin mata suka fara fita ta ɓangarensu kafin maza suka fita acikin mota Asma’u da Innayi suka jira M Jameel da Moddibo goma da kwata dai-dai suka fito suka tafi.

    Acan ɓangaren Khausar kuwa yauma kamar kullum taje tafsiri ita kaɗai ta dawo duk da masallacin a ƙofar gidansu yake bakinta ɗauke da Sallama tashiga cikin falonsu Anutse ta cire hijabinta tare da nufar kichen inda take jiyo motsin Mommyta kasancewar yau itace da girki yasa ko tafsir bata jeba.

     

    Juyiwa Mommy tayi jin motsi abayan ta ganin Khausar yasa ta maida hankalinta kan aikinta kana tace.

    “Kin dawo?”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tana kallon tuƙeƙken tuwon shinkafa da Mommy ke kwashe maran ƙarshe.

    Ahankali Khausar ta matsa kusa da Mommy kana tace.

    “Mommy ki bari zanyi miyar”.

    Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

    “Ok to Miyar zogala za kiyi”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da ɗaukar.

    Da fara aikin haɗa miyar zogalen.

    Cikin abinda bai gaza awa ɗaya da rabi ba, duk ta haɗa ta sanya komai na buƙata kana.

    Ta rufe nan danan kichen ɗin ya kaure da ƙamshin miyar sauran kayan da Mommy tayi amfani dasu ta haɗa ta wanke tare da sauƙe Miyar ganin tayi tik gwanin kyau.

     

    Bayan ta gama ta buɗe miyar da yayi mugun kyau a ido ta ɗauki kular wani sashe ta zuba miya kasancewar babban gidana yasa kowa kaina nasa akeyi, na buɗa baki kuwa ki wacce a side ɗinta takeyi, mai girki zata sawa Lamiɗo, da Dadu, haka tsarin nasu yake.

    Shigo wa Mommy tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli yanda kichen ɗin yayi fess ga ƙamshin miyar zogalan da yaki kifi da naman dariko, kallonta ta mayar kan Khausar kana tace.

    “Sannu da ƙoƙari ki ɗauki na sashen Hajiya Bunayya ki kai mata”.

    Kai Khausar ta gyaɗa sannan ta ɗauka kular Hajiya Bunayya ta wuce Haidar Mommy ta ƙwalawa kira bayan yazo tace ya ɗauki kular sashen Gimbiya Dadu ya kaimata dan Mommy tunda ta lura da Khausar batason zuwa yasa ta rage aikanta sashen shi kuwa Haiydar daga sashen Gimbiya Dadu ya wuce sashen Hajiya Bunayya.

     

    Hajiya Bunayya dake zaune akan kujera ta faɗaɗa fara’ar fuskarta ganin Haiydar ta tsira masa idanu kana tace.

    “Babana kaine dama yanzu nake niyyan zuwa in yi maka albishir”.

    Murmushi Haidar yayi tare da zama kana yace.

    “Daga sashen Gimbiya Dadu nake nace bari nazo na gaishe ki”.

    Murmushi tayi masu cike da Ma’anoni  tayi kana tace.

    “Insha Allah bayan sallah mashin ɗinka zai  zo kaga dama tun shekara biyu baya naso saya maka Abbanka yace saika ƙara girma kuma kaga yanzu aika girma”.

    Jinjina kai Haidar yayi cike da tsananin farin ciki mara mistuwa ya gyara zamansa kana yace.

    “Nagode Ummah Allah yarabaki da sharrin maƙiya”.

    Murmushin gefen baki tayi kana tace.

    “Bana son godiyar nan Babana”.

     

    Cike da farin ciki ya miƙe ya nufi sashen su fuskarsa ɗauke da murmushi ya shiga falon zaune ya samu Mommy da Khausar.

    Kallonsa Mommy tayi kana tace.

    “Ina ka tsaya?”.

    Zama yayi daga gefen Khausar still.

    Fuskarsa da murmushi da yakasa ɓoyewa ya numfasa tare da cewa.

    “Mommy Machine ɗina ya Kusa isowa fa, kinga tun shekara biyu baya Umma taso siya min shine Abba ya hanata yace saina ƙara girma ai yanzu kam dai na sake girma bazai hana ba ta saya min Machine sabo mai kyau bayan sallah zai iso”.

     

    Khausar kuwa tunda ya fara magana ta tsira masa idanu saida ya kai aya ta sauƙe ajiyar zuciya mai zafi tare da furzar da iska daga bakinta kana babu walwala afuskarta ta kawar da kanta gefe tare da cewa.

    “Kai kuma farin ciki kake ko?”.

    Juyawa Haiydar yayi tare da kallon ta kana yace.

    “Sosai ma kuwa kema kamata yayi kije kiyi mata godiya”.

    Harara Khausar ta ɓalla masa.

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Rabu da ita ai ni zanje.

    A yanzu kam aika girma yanda kake da tsawon ƙafan nan”.

     

    Murmushi yayi tare da kallon Khausar kana yace.

    “Sosai ma Mommy ai yanzu na girma yanzu fa shekara kusan sha shida nake nema gashi mai shekara sha takwas ɗinma na fita koda yake sha bakwai ne da yan watanni ne ko gareta”.

     

    Jinjina kai Mommy tayi kana tace.

    “Ai lallai dai kam kama cika sha shida kam  Allah yasa kafara hawa asa’a.

    Ubangiji ya tsareka da sharrin ƙarfe.

    Allah yatsare gabanka da bayanka!.

    Ubangiji ya makantar da idanun makiyan ka akanka!.

    Allah ya tsare ku ga duk kan abinda zai cutar da rayuwar ku! Allah ya muku katangan ƙarfe da dukkan abin da zai zama sharri acikin  rayuwarku!”.

    Cike da jin daɗin Addu’ar ta Haiydar yayi Murmushi tare da cewa.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum Mommy na”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da kallon Mommy kana tace.

    “Ameen ya Allah Mommy tunda kinyi addu’a magana ta ƙare baza’a ji tsoron komai ba babu bakin uwa akansu duk kan mai sharri zaiyi ya gama babu abinda zai sameshi da izinin Ubangiji”.

     

    Murmushi Haiydar yayi tare da kallon Khausar kana yace.

    “Aikam Addah Khausy babu bakin uwa akaina duk kan wani mai mugun nufi zai ƙare akansa”.

    Murmushi Mommy tayi cike da ƙaunar ƴaƴan nata,

    kallon ta ta mayar kansu tare da cewa.

    “Ku tashi kuje kuyi bacci dan mu samu mu farka da wuri mu kaiwa Ubangiji bukatun mu”.

    Miƙewa sukayi tare da yiwa juyawa sai da safe kana kowa ya wuce ɗakinsa ya kwantar.

     

    Misalin ƙarfe ɗaya na dare Mommy ta farka kallon Lamiɗo daya miƙe yashiga toilet tayi sai kuma ta miƙe ahankali ta tafi side ɗinta.

    ɗakin Khausar tashiga tare da kunna haske.

    Idanunta suka sauƙa akan Khausar dake sharan bacci ƙara sawa tayi tare da bubbuga ƙafarta kana tace.

    “Khausar ki tashi kiyi nafilla”.

    Ahankali Khausar ta buɗe Idanunta cikin Muryan bacci ta kalli Mommy kana ta yunƙura ta zaune bakinta ɗauke da addu’a tace.

    “Toh Mommy”,Sannan ta Sauƙa ta shiga toilet.

     

    Juyawa Mommy tayi ta koma ɗakin Lamiɗo lokacin data shiga har ya fara Sallah kai tsaye toilet ta shiga ta ɗaura Al’wala bayan tayi ta fito tare da shimfiɗa Sallaya ta tada Sallah cikin nutsuwa ta keyi bayan tayi sujja tayi Subhana Rabbiyal a’ala³ kana ɗaura da du’inta.

    “Ya Allah kayuwa ƴata zaɓin alkhairi,Ya Allah kashirya Khausar kasata ahanya madaidaiciya Ya hayyu ya ƙayyum  ka tsare mata imaninta, Ya Allah ka kare min Haiydar ɗina ya Allah katsaresa daga sharrin mai sharri ya Allah ka kare min ita ya Allah kabawa Ramadan da Raudat ilimi mai albarka da yayunsu dama dukkan ƴaƴan musulmai. Ya Allah katsare min ƴaƴana daga sharrin,Mutum, aljan da kuma ƙarfe, ya Allah katse min imanina Allah ka tsaremin zuciyoyinsu, ka tsaresu da sharrin hassada, ƙeta, munafurci, da ƙyashi ya Allah ka kare min mijina kabiya masa buƙatunsa na Alkhairi dama ɗauka cin al’ummar musulmai.

    Bayan ta idar da nafillah ta ɗauki Alkur’ani ta shiga Muraja’a.

     

    Khausar kuwa ƙarfe biyu da rabi bacci ya riƙa fisgarta akan Sallaya ta kwanta nan da nan bacci mai nauyi yayi nasarar  ɗauke ta.

    Can cikin baccinta ta fara wani mafarki mai cike da al’ajabi ganinta tayi.

    Gata nan tsaye a wani ƙaton fili.

    Baki ɗaya ilahirin filin ashare yake kuma , yashine malale a wurin iya ganinka sai wani irin haske mai masifar ƙyalli da ɗauke idon da ya cika wajen baki ɗaya, ahankali ta ɗaga kanta ta fuskanci gabas, da sauri ta rumtse idanunta gani wata ya fito ta gabar juyawa tayi taga yamma da sauri Still nan ya fito ta yamman sake juyawa kudu tayi still ta nan ma ya fito ahankali ta sake juyawa arewa, wani irin masifeffen karkarwa jikinta ya farayi, ganin tanan ma watan  yafito duk kusurwa huɗu wata ya fito sai asannan ta lura da haskensa ne yake ɗauke mata ido.

    Ahankali taga wani kyakkyawan.

    Yaro fari ƙal agabanta yayinda gashin kansa ke kwance lib-lib, daga bayansa ta hango wani kyakkyawan mutum sai dai fuskarsa na kallon gefe hannunsa na kan yaron yana shafawa cikin wata.

    Sanyayyar murya yake kallon yaron kana yace da ita.

    “Wannan shine jininmu mahaɗinmu, wannan shine sanadin haɗayyarmu bugun zuƙatanmuuuhh”.

    Ya ƙarasa jan kalmar cikin wata iriyar ƙasalalliyar murya mai cike da shauƙi.

    Ita kuwa ƙoƙari take taga fuskar mutumin sai dai ta kasa sai iya fuskan kyankyawan yaron take iya kallo.

    Dai-dai lokacin kuma ta buɗe Idanunta jin Muryan Mommy nacewa.

    “Khausar, Khausar ki tashi zaki makara fa ƙarfe huɗu tayi bakiyi Sahur ba anjima kaɗan zaki fara ce mana kin fara jin wahalar azumi”, Ta faɗa tana buga ƙafarta da saurin Khausar ta tashi zaune tare da sakin ajiyar zuciya kana tace.

    “Innslillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakin Astagfirullah wa’atubu ilaik”.

    Sai kuma tayi addu’a ta shafa.

    Mommy dake tsaye har yanzu kuwa sake taɓata tayu tare da cewa.

    “Khausar kada ki koma bacci fa kitaso”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Mommy na tashi bazan koma ba”.

    Juyawa Mommy tayi ta fice ita kuma Khausar toilet ta shiga.

    Brush tayi kana ta fito kai tsaye falon ta nufa.

     

    Samu tayi Mommy ta haɗa mata ɗumamen tuwon jiya da Tea mai kauri ahankali ta zauna tare da kai tuwon bakinta da ƙyar ta haɗiye baki ɗaya jikinta yayi mugun sanyi da mafarkin da tayi.

    Mommy dake zaune a kujeran falon ta juya ta kalleta ganin bata cin tuwon yasa ta girgiza kai tare da cewa.

    “Kici abinci fa Khausar kin sanki sarai da cin abinci anjima kaɗan zaki fara cewa yunwa kike ji”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da iskar bakinta kallon Mommy tayi kana cikin sanyin murya ta lumshe Idanunta tare da cewa.

    “Mommy wallahi tuwon ne nakeji kamar ba zai shiga ba babu wani abu ne?”.

    Kai Mommy data tsira mata Idanu ta gyaɗa kana tace.

    “Kije kichen akwai indomie dana ɗaura wa Haiydar shima yace ba zai ci tuwo ba to amma ke kam nasan indomie ba wani riƙe Miki ciki yake yi ba”.

     

    Lumshe Idanunta tayi kana ta buɗe su akan Mommy ahankali ta motsa laɓɓanta tare da cewa.

    “Bari in cisa yau ɗin kam amma Mommy da kifi ne koda nama”.

    Tayi tambayar ne domin bata fiye son kifi ba.

     

    Kawar da kai gefe Mommy tayi kana tace.

    “Da kifi ne idan zaki ci kici idan kuma baza kici ba ki bari”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da jan siririn tsaki kana tace.

    “Bari dai inci, tuwon ne naji kamar bazai ciwu ba  shi ɗin ma miyar aida kifi”.

    Mommy dai Bata sake cewa komai ba ahankali Khausar ta miƙe tashiga kichen ta ɗauki Plate ta ɗibi yanda zai isheta kana ta fito ta zauna tare da Bismillah ta fara ci bayan ta gama ta ɗauki tea da Mommy ta haɗa mata da bread taci.

    Haiydar ne ya shigo  da Sallama idanunsa akan Plate da Khausar ta gama cin indomie.

    Kallonsa Mommy tayi kana tace.

    “Jeka ɗebo indomie yayi sannan ka taho min da tuwo”.

    “Toh”,Ya amsa kana ya wuce kichen ɗin ya juye indomie sannan ya zubawa Mommy tuwon ya fito.

    Khausar dai na zaune tana lumshe Idanunta tare da tuna irin mafarkin da tayi wanda ya tuno mata wanda tayi shekaru biyu baya a Jauro Yayah.

     

    Ahankali ta saki ajiyar zuciya tare da juyawa ta kalli Haiydar da yagama Sahur ɗin ta gyara zamanta tare da cewa.

    “Haiydar  nikam yanzu wani surah kake?”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Ke ɗin wace surah kike?”.

     

    Zama ta gyara tare da cewa.

    “Hmmm aini nayi nisa ina Maryam kaga insha Allah zan samu sauƙa biyu”.

    Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

    “Toh ni ina Yasin  Insha Allah zan samu sauƙa uku insha Allah duk azumi goma zanyi sauƙa ɗaya”.

    Murmushi Mommy dake duba wani littafin addini tayi kana tace.

    “Masha Allah yayi kyau Khausar ya akayi kika tsaya wasa ya wuce ki”.

    Langwaɓar da kai tayi kana tace.

    “Mommy kinga ai shi baya taya ki yin aiki nice ke tayaki aiki kinga shi duk lokacin daya keso zaiyi karatu.

    Jinjina kai Mommy tayi kana tace.

    “Eh haka ne da wannan dan wannan amma dai ki dage kema”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Toh shikenan Mommy zan dage insha Allah amma Mommy ke izu nawa kikayi”.

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Insha Allah nima zan samu uku kaman na Haiydar”.

    Ware Ido Khausar tayi tare da tura madedecin bakinta kana tace.

    “Insha Allah nima zan dage duk azumi goma sai nayi sauƙa”.

    Jinjina kai Mommy tayi tare da faɗin.

    “Aikam da kin kyauta amma sai kin rage baccin safe”.

    Jinjina kai Khausar tayi kana tace.

    “Insha Allah zan rage”.

    Jin kiran assalatu yasa suka miƙe Haiydar ya tafi masallaci Mommy da Khausar suka shiga ɗaki suka ɗaura alwala kana suka gabatar da sallah bayan sun idar Khausar ta zauna tayi Azkharul sabah tana gamawa ta mike ta dawo falo ta gyara tare da sharewa kana ta fita zuwa kofar sashen nasu ta gama share ko ina sannan ta wuce Bedroom ta kwanta kasancewar akwai mai yi musu wanke-wanke tun kafin su shiga Sallah ta zo ta kwashe kayan ta wanke.

     

    Ahankali azumi ya cigaba da tafiya kwanaki suna tafiya lokaci yana ja  cikin ikon Allah har angama goman farko goma na marmari inji hausawa ko?. Har an  shiga goma na biyu,  goma na wuya ko? Yau an kai azumi na goma sha biyu.

     

    Yayin da Aɓangaren Moddibo da M Jameel sunyi nisa acikin tafsirin Suratul Nisa sun fassara har zuwa ayoyi na tamanin da tara zasu tashi akan aya na Casa’in

     

    Da daddare Misalin ƙarfe tara M Jameel da Moddibo ne zaune acikin masallaci gaban ko wannensu ɗauke da system da kuma roban Swan water mai sanyi Moddibo na cikin shigarsa as Usual kamar ko yaushe Jallabiya Neavy blue kansa ɗaure da Hirami M Jameel kuwa sanye yake cikin gezner blue da babbar riga.

    Cike da nutsuwa M Jameel Yayi gyaran murya tare da hura Microphone ɗin kana yace.

    Ya buɗe da addu’a kamar ko yaushe.

     

    Lokaci guda masallacin ya kaure da kabbara tamkar zasu tsaga masallacin saboda yanayin zafin jinjinsa da kwarjininsa cike da sakin fuska.

    Ya cigaba da cewa.

    “Anma ba’ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu”.

    Atare suka hada baki wajen cewa.

    “Wa’alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.

     

    A hankali ya numfasa tare da sauƙe nan-nauyan ajiyar zuciya kana ya dubi ɗumbin jama’ar dake zaune acikin masallacin cikin tsantsar nutsuwa ya juyo da system ɗin gabansa kana yace.

    “Acigaba da tafsirin Alkur’ani mai girma Amasallacin. Juma’a dake ƙofar gidan Mai martaba Sarki Gembulan Lamido Bashiru zamu cigaba da tafsirin Alkur’ani mai girma acikin Suratul Nisa’i zamu tashi a aya ta cassa’in”.

    Sai kuma ya juya ya Kalli Moddibo kana yace.

    “Aramma Bismillah”.

     

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da gyara zamansa kana ya ɗan jingina bayansa da jikin kujeran cikin Sanyayyar muryarsa mai cike da nutsuwa da zaƙi yayi basmala kaya ya fara karanta ayoyin kamar haka;

    _“(90)Illallazina Yasiluna Ilaƙaumim Bayna Kum wa Bayna hum misaƙun Auja,Ukum hasirat suduruhu an yuƙatalalukum.Walau sha Allahu lasallaɗhum Alaikum falaƙatalukum.Fa’in’itazalukum falam yuƙatilukum Wa’alƙau Ilaikumussalama fama ja’alallahu lakum Alaihim Sabila”._

     

    Moddibo ya ida kai Ayar yana mai lumshe idanunsa akuma take tsikar jikinsa suka tashi yayi saurin buɗe idanunsa tare da ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa kana ya cigaba da furta Aya ta gaba kamar haka.

    _“(91)Satajidunah Akharina Yuriduna Anyamanukum Wayamanu Ƙaumahum kullamaraduu Ilalfitnatin Urkisu fiha.Fa’in lam ya’atazilukum Wayulƙau Ilaikumussalama Wayakfuru Aydiyahum Fahuzuhum Waƙtuluhum haysu saƙiftumuhum.Wa Ula’ikum ja’alnalakum Alaihim sulɗanammubina”._

     

    Wani irin numfashi M Jameel ya saki tare da rintse idanunsa kana jikinsa ya ɗauki tsuma yana mai jin fassarar Ayar na yawo Atsakiyar kansa Atake kuma zuciyarsa ta cigaba da bugawa da kaso tamanin cikin ɗari.

    Yayinda gaba ɗaya al’ummar dake cikin masallacin dama wajensa sit kakeji kamar ba mai numfashi sabida tsananin yadda sautin karatun ke ratsa musu zuƙata da ƙoƙwale.

     

    Shi kuwa Moddibo ya kai minti ɗaya kafin ya saki gauron numfashi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi sabida sanin ma’anar ayoyin da zai kawo a gaba, cikin wani irin raunin tare da tsoron Allahu wahidun ƙahhar, gaba ɗaya muryarsa ta sake rauni cikin dakiya ya cigaba da Karanta Ayar Kamar haka.

    _“(92)Wama kana limu’uminun An yaƙtula Mu’uminan Illakhaɗa’a.Waman ƙatala Mu’uminan khaɗa’a fatahriru Raƙbatatin Mu’uminatin wadiyyatun Musallamatu Ila’ahlihee Illah An yassaddaƙun.Fa’in kana min ƙaumin Aduwwillakum Wahuwa Mu’uminun Fatahriru Raƙbatin Mu’uminatan.Wa’in kana min ƙaumim baynakum wa baynahum miysaƙun Fadiyyatun Musallamatun Ila Ahlihi watahriru raƙbatin mu’uminatin.Famallam yajidu fasiyamu shahraini mutatabi’ayni taubatan Minallah.Wakanallahu Aliman hakima”._

     

    Wani irin nutsuwa cikin masallacin yayi musamman ma wa’anda suka san fassarar ayoyin wa’anda basu san fassarar ba kuwa mu’ujiza ta Kur’ani ta dinga ratsasu tare da Sanyayyar sautin Muryar mai karatun.

    Moddibo kuwa idanunsa ya lumshe sakamakon wasu zafafan hawaye masu ɗumi da suka cika cikin ƙarfi ya furzar da iska mai zafin gaske Tabbas kashe ran mumini baƙaramin tashin hankali bane amma baki ɗaya awannan zamanin an maida rai ba abakin komai ba.

    Ya gyara zamansa tare da cigaba da karantar Ayar kamar haka.

    _“(93)Waman yaƙtul mu’uminan Muta’ammidan Fajaza’s’uhu Jahannama! halidan fiha wagadiballahu Alaihi wala’anahu! wa’aaddalahu Azaban! Azeeymah!!!!!”_.

     

    Awannan lokacin hawaye ne suka ciko idanun Moddibo jin irin tsananin azaban da Ubangiji ya tana darwa duk wanda ya kashe ran mumini batare da wani hakkiba.

    Walahabahu la’anar Ubangiji kana fajaza’ahun jahannamu  khaleedan fiha, fa ubangiji yace kana aka ɗaura da Azaban Azeeymah!!!, Duk wannan tanadinefa da Ubangiji yayiwa mai kashen ran mumini da gangan.

     

    Wani irin rawa jikin Moddibo keyi tamkar wanda aka konawa wuta a jikinsa cikin tsananin sheshsheƙan kukan da yake son dannewa ne ya bu ɗe baki a hankali dan kawo aya ta 94 sai kuma ya juyo cikin tsananin rauni ya kalli M Jameel da gaba ɗaya j….

     

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

     

     

    *By*

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 25

    Sakayyah 25

     

    SAKAYAH

     

    25

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

    *Al’bishirunku Ma’aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma’aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken  GARKUWAR MA’AURATA*

     

    NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.

    Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

     

    Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.

    Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?

    Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.

    Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?

    Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba’a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,

    Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.

    Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.

     

     

    Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*

    Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu’umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

     

    Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

     

    🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA

    *(GARKUWAR MA’AURATA)*

     

    Isrejy. Suna fita suka ga gari yayi shiru ga wani irin hadari daya haɗu baƙiƙƙirin, sanyayyar iska mai sanyi da ratsa jiki yana kaɗawa alamun wata ƙil hadarin ya watse ne ko kuma ya sako ruwa,  wani irin lumshe idanu Moddibo yayi tare da cije labɓansa na ƙasa cikin sauri ya shiga mota M Jameel yashiga maza mazaunin Driver yaja suka tafi suna isa gida aka fara yayyafi still yau ma ɗakin Moddibo M Jameel yashiga ya kwanta nan da nan bacci ya ɗauke sa.

    Moddibo kuwa tunda ya kwanta yake juyi ahankali ya miƙe ya zauna idanunsa cike da ruwan fitina da zaran ya lumshe Idanunsa kyakkyawar suranta daya gani amafarkine ke masa yawa kana idan ya buɗe lokacin da suka kasance amota ne yake masa gezo zama yayi Atsakiyar gadon D ɗinsa ya shiga harbawa da masifar ƙarfi tamkar zai tsinke lokaci ɗaya jikinsa ya ɗauki rawa yayin da lips ɗin sa suka shiga rawa har haƙoransa na haɗuwa suna bada sautin Ƙat-ƙat-ƙat kana Idanunsa sun kaɗa sunyi jawur tare da ƙanƙancewa kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin tsananin buƙatar kasancewa da.

    Mace da ƙyar ya miƙe yashiga toilet tare da sakarwa kansa ruwan sanyi duk da kuwa sanyin da ake agarin amma tamkar ƙarawa yake cikin mawuyacin hali da yanayin buƙatuwa ya fito tare da kwanciya rub da ciki cikin wahalallan hali bacci ya ɗaukesa.

     

    Bayan kwanaki biyar sosai kafar Ramadan yayi sauƙi har ya fara takawa ahankali  sosai Mommy da Khausar da kuma Lamiɗo sukayi farin ciki ganin babu wata matsala.

     

    Aɓangaren Uncle Naseer kuwa abubuwa suna tafiya kamar yanda ya tsara baki daya ya maida hankalinsa da nutsuwarsa kan Amina yana nuna mata zallar so tare da yimata duk wani abinda take so yayin da acan ƙasan ransa kuwa soyayyar Khausar na nan kamar yanda yake yana da burin ta kasance matar.

    Aurensa kana yana jin

    yana son ya haɗa shimfiɗa da ita yana so yaji shin ya ɗanɗanonta yake, domin itace mace ta farko daya fara so tare da ƙulafacin ɗanɗanar zumanta ita kaɗai duk da cewa yayi Sex da mata kala da ban da ban bai taɓa sanun cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali ba, yanaji  awajen Khausar ce kaɗai yake da ya ƙinin zai samu irin wannan nutsuwar da yake buƙata, duk wani tsarinsa yana yine dan ganin ya samu ya ɗanɗanin zumanta tare da kawar da ƙishinsa akanta.

     

    Aɓangaren su M Jameel kuwa sun sake samun malam Arɗo da batun barinsu makaranta amma fir malam Arɗo yaƙi amincewa sam baya so ma suzo masa da batun yayin da M Jameel da Moddibo suka rage zuwa makarantar domin sukanyi kwanaki uku ko  huɗu ba suje ba wani zubin ma har satin ya ƙare baza sujeba kasancewar sun riga da sun faɗa masa cewa sun ajiye aikin.

    Baki ɗaya sun mai da hankali da nutsuwar su akan abinda suka sa gaba na batun aikin da zasu fara a Company Abban M Jameel.

    Abba kuwa kasancewar yanzu damuna ne yasa ya maida baki ɗaya hankalinsa da ragowar kuɗin hannunsa akan noma musamman nomar Auduga da ake masa saboda yana amfani dashi a Companyn’,sa na Marrocco yana buga manyan zannuwan gadaje sallayoyi da jallabiyoyu na mata da maza riguna na alfama  da dai sauransu.

     

    Wata ranar Litinin tun safe garin Gembu suka tashi da ruwan sama tamkar da bakin ƙwarya sai daf Azahar ruwan ya tsaya gari yayi sanyi Sanyayyar iska na kaɗawa yayin da bishiyoyi ke rangaji tamkar zasu karye ko wanni magidanci yana farin ciki da kasancewar wannan Weather mai cike da Ni’imah da kuma sanya shauƙi.

    Acan ɓangaren Moddibo kuwa da yammaci misalin ƙarfe biyar M Jameel ne zaune aka 2sitter yayin da Moddibo ke kwance akan 3sitter yayi rub da ciki idanunsa alumshe.

    Anutse M Jameel ya ɗago kansa daga kan system tare da kallon Moddibo cikin yanayin shaƙuwa da ƙaunar junansu yace.

    “A.J muje gidan Ummi mana”.

    Cikin Yanayin buƙata da tsananin sha’awar dake addabarsa ya damƙe ƙasan mararsa waye wan garin yau yasha ruwan lipton da lemun tsami har ya godewa Allah amma ko kaɗan abinda yake ji bai raguba hakan yasa ya kasa furta komai.

    Jin kamar bai jiba yasa M Jameel sake maimaitawa.

    Ahankali Moddibo ya ɗago Idanunsa cikin raunin murya da yanayin harbawan da ɗin sa keyi kana muryarsa Asanyaye ya kalli M Jameel tare da cewa.

    “J bazan iya ba Wallahi bazan iya ba”.

    Ya faɗa yana lumshe Idanunsa ajikinsa yana jin tamkar idan ya miƙe  ɗin sa zai tsinke baki ɗaya ya rasa inda zai sanya ransa yaji daɗi ji yake tamkar ya ɗaura hannunsa akai yaita zunɗuma ihu koda zaiji sanyin Aransa baki ɗaya lips ɗin sa rawa suke idanunsa sun sauya launi zuwa ja jijiyoyin goshinsa sun tashi yayin da goshinsa ke tsata-tsafo da zufa.

     

    M Jameel kuwa lura da yanayin da yake ciki da yayi yasa ya miƙe tare da nufar kichen kamar ko yaushe ruwan Tea da lemun tsami da kuma zuma ya haɗa masa kana ya fito ya miƙa masa tare da cewa.

    “Gashi kasha”.

    Ba musu Moddibo ya sanya hannu ya karɓa domin baya cikin yanayin da zai iya musa masa ahankali yakai kofin bakinsa tare da kafa kai ya shanye saboda yanda yake ji ajikinsa.

    Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe kana cikin sanyin murya yace.

    “Tun da kasha ka kwanta Insha Allah zaka ji sauƙi bari zanje gidan Ummi anjima zan dawo bazan daɗe ba”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa masa still Idanunsa alumshe M Jameel kuwa key mota ya ɗauka tare da ficewa kai tsaye gidan Ummi ya nufa.

     

    Yana isa yayi Parking Cike da nutsuwa ya buɗe Murfin motar ya fita tare da duba agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa dake nuni da ƙarfe 5:15 lumshe idanunsa yayi kana ya buɗe tare da nufar cikin Falon bakinsa ɗauke da Sallama shiru falon ba kowa sai dai komai akimtse kana ga ƙamshin tularen wuta dana Room freshner dake tashi, Murmushi yayi Aransa yace.

    “Allah sarki Ummina ba dai tsafta ba”.

    Numfashi ya fesar tare da nufar kichen inda yake jiyo motsinta.

    Tsaye yasame ta a kichen ta tuƙa tuwo tana kwashewa aleda cike da so da ƙauna yace.

    “Ummina”.

    Juyawa Ummi tayi fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi ta kallesa kana tace.

    “A’a yaushe kashigo?”.

    Yana ƙara sa shiga kichen ɗin yace.

    “Yanzu Ummina”.

    Juyawa Ummi tayi tare da leƙa bayansa”.

    Dariya yayi kana yace.

    “Nasan wa kike nema ai”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Eh to ai ban gan shi bane naga Hussain banga Hassan ba”.

    Cikin sanyin murya yace.

    “Yana gida Ummi yau yana ɗan jin zazzaɓi ne shiyasa bamu zo tare ba”.

    Girgiza kai Ummi tayi cike da tausayawa tace.

    “Subhanallah Ubangiji ya bashi lafiya Allah ya sawwaƙa mishi”.

    Ahankali M Jameel yace.

    “Ameen”.

    Kana ya matsa jikin kular yana ƙoƙarin budewa yace.

    “Ummina yau me kika girka mana ne?”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Tuwo ne”.

    Wara ido yayi tare da cewa.

    “Miyar me za kiyi mana Ummi?”.

     

    Tana ƙoƙarin wanke nama ta kallesa kana tace.

    “Miyar taushe zanyi”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “A to asamana nama da yawa”.

    “Toh Babana za’a saka”.

    Ta ida maganar tare da ɗaura naman akan gas kana ta yanka albasa tare da sanya Maggi, citta kamafari ta rufe.

    M Jameel kuwa Attaruhu, Albasa,Tattasai ya haɗa ya wanke tare da gyarawa kana ya ɗauko blander ya zuba.

    Kallonsa Ummi tayi kana tace.

    “Ka bari fa da yaji kada yashiga Idon ka”.

    Kai ya girgiza tare da cewa.

    “A’a Ummi kibari in tayaki nima yau na samu ladan da Asma’u ke samu dana iyama ni zan miki girkin nan”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Ai dai kam hakan ma Nagode yayi Allah yayi albarka Ubangiji ya tsareka daga sharrin duk kan abinƙi kuma ai kafin Asma’u samun lada in sha Allah”.

    Kallonta yayi kana yace.

    “Ameen Ummina”.

    Ummi kuwa buɗe tukunyar tayi tare da zuba mai kana ta zuba jejjegen da M Jameel Yayi a blander.

    M Jameel dake gyara kifi banda ya juya ya kalli Ummi tare da cewa.

    “Ummi ya yau naji gidan Shiru ina Asma’u da Bashir”.

    Tana ɓare Maggi tace.

    “Sunje gidan Goggon su takwarar Asma’u”.

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Ayyah shiyasa yau naji gidan shiru sun barki ke kaɗai to Malam fa?”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Ai dai kam Malam kuma yaje wata rugar Fulani nan kusa amma sai gobe zai dawo acan zai kwana”.

     

    Kai ya jinjina tare da cewa.

    “Ashe dai yauma kam zan ta yaki ɗebe kewa gidan nan”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Ai dai kam ko zamu kwana ne?”.

    Ahankali ya juya ya kalleta tare da cewa.

    “Da nafi kowa farin ciki Ummina ace zan kwana gida ɗaya dake”.

    Murmushi Ummi tayi batare da tace komai ba.

    Ana kiran sallar maghariba suka gama dai-dai lokacin kuma Asma’u da Bashir suka dawo atare, alwala M Jameel Yayi kana Bashir ma yayi hannun Bashir ya riƙe suka tafi masallaci su kuma sukayi alwala tare da gabatar da Sallah.

    M Jameel kuwa koda suka idar da Sallah basu dawo ba saida sukayi Isha’i sannan suka fito.

    Asma’u kuwa Anutse ta fito daga Bedroom bayan ta idar da sallah kusa da Ummi ta zauna kana tace.

    “Ummina Ayyah yau aiki ke kaɗai”.

    Kallonta Ummi tayi kana tayi murmushi tare da cewa.

    “Ina kuwa nayi aiki Ni kaɗai Yayanku yazo ya tayani yau shiya mana miya ma”.

    Wara ido Asma’u tayi tare da sakin murmushi kana tace.

    “A lallai kai ashe yau zamu sha miyar Yaya kenan”.

    Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.

    “A sosai kam zaku sha miyar Yaya Jameel”.

    Atare M Jameel da Bashir suka shigo tare da zama.

     

    Gnin shigowarsu yasa ta miƙe tashiga kichen kular tuwon ta ɗauko kana ta koma ta ɗauko Plate-plate ta dawo Ummi ce ta karba ta sakawa M Jameel kana ta zuba masa miya agefe sannan ta zubawa Asma’u da Bashir.

    Ahankali M Jameel ya kalli Ummi kana ya kalli Asma’u da Bashir sai kuma ya kalli tuwon Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.

    “Toh Ummi muci tare mana musamu ladan cin abinci tare”.

    Ɗagowa Ummi tare da kallon sa kana tace.

    “Kuma dai”.

    Cikin wani irin yanayi ya gyaɗa mata kai kana yace.

    “Allah kuwa Ummi”.

    Kallonsa ya mayar kan Asma’u tare da cewa.

    “Asmeey jeki ɗauko Tray babba ki kawo mana”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa kana tace.

    “Toh Yaya Jameel”,.

    Sannan ta miƙe ta shiga kichen ɗin ta ɗauko Babban faranti ta fito dashi tana ƙoƙarin juyewa yace.

    “Kawo in zuba mana”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da faɗin.

    “Yah Jameel da kan ka kabari zan zuba mana”,

    Girgiza kai yayi kana yace.

    “A’a Asma’u kawo in zuba mana bana so ki wahalar da kanki”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Laaa Yah Jameel ka jika Allah zanyi mana”.

    Lumshe Idanunsa yayi tare da saurin dafe ƙirjinsa kana ya buɗe Idanunsa tare da Kallonsu ɗaya bayan ɗaya tare da cewa.

    “No Asmeey ki bari in zuba mana kaɗai”.

    Saurin Kallonsa tayi tare da miƙa masa Plate ɗin.

     

    Murmushi yayi tare ɗaukar Plate ɗin tuwon ya zuba musu akan babban farantin kana ya ɗauka ya ajiye musu Atsakiyar su tare da kallon Bashir yace.

    “Ɗauko Mana drinks”.

    Kai Bashir ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh”,Kana ya miƙe ya ɗauki Plate ya ɗebo drinks da swan water ya ajiye musu.

    Ya zauna sai ya zamana M Jameel da Ummi na facing juna Asma’u da Bashir ma na facing juna sai ya zama sunyi Cycle plate din na tsakiyar su.

     

    Ummi kuwa shiru tayi tare da zubawa M Jameel Ido Batare da tace komai ba kana tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa azuciyarta wanda takasa sanin na menene hakanan ta tsinci kanta da Kallonsa acikin kwanakin nan.

    Ahankali M Jameel ya janyo kular miyar tare da ƙara musu namar da bandan kifi kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Hayya kuci yau zakuci miyar da baku taɓa ciba irinta ba dan ni nayita ko Ummi?”.

    Ya faɗa tare da ɗago kai sai yaga baki ɗaya Idanun Ummi na kansa faɗaɗa Murmushin fuskarsa yayi tare da cewa.

    “Kai Ummina ya dai?,Ai gaskiya na faɗa”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “A gaskiya ka faɗa kam”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Toh Ummi kici mana”.

    Dariya Ummi tayi tare da girgiza kai kana tace.

    “A’a kai da kayi dai ka fara ci muga result ɗin da fuskarka zai bayar kafin mufara ci”.

    Wara ido yayi tare da kallon Asma’u da Bashir da suma Kallonsa suke,

    “Toh ɗan Auta fara ɗana mana muji”.

    Kai Bashir ya gyaɗa kana ya gutsiri loma ɗaya yakai bakin sa lumshe ido yayi tare da haɗa yatsunsa hannu biyu alamar jinjina kana yace.

    “Kai amma miyar tayi daɗi gaskiya Yah Jameel na baka Award”.

    Murmushi Ummi tayi tare da kallon M Jameel da Yayi wani irin kyau na ban mamaki tamkar wanda aka sanya shi a inji aka sake ƙenƙesashi ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

    “Uyummm toni nayi bashi ba”.

    Dariya M Jameel Yayi wanda ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana yace.

    “Toh na yarda Ummi mu duka biyu mukayi”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da kallon M Jameel kana tace.

    “Aikuwa Yaya Kayi ƙoƙari sosai amma muci kada yayi sanyi”.

    Kai suka gyaɗa atare kana lokaci ɗaya suka sanya hannunsu akan tuwon tare da kai tuwon bakinsu  lokaci ɗaya suka kalli juna tare da sakin murmushi.

    M Jameel kuwa murmushi ya saki tare da lumshe Idanunsa kana yace.

    “Ina ma ace zamu kasance ahaka ko yaushe mu riƙa zama tare nuna cin abinci atare da nafi kowa farin ciki”.

    Asma’u da takai nama bakinta ta kallesa kana tace.

    “Yah Jameel zamu kasance atare mana Insha Allah”.

    Kai ya Girgiza tare da cewa.

    “Dole wataran fa zan barku sai dai ku zauna ku uku kuci abinci ba tare dani ba”.

    Cikin sauri suka kallesa  Bashir yace.

    “A’a Yaya Jameel mai yasa zakace haka insha Allah zamu kasance atare”.

    Ummi kuwa Kallonsa kawai take.

    Murmushi M Jameel Yayi tare da kurɓan drinks kana yace.

    ”Dole wataran zan barku zanyi tafiya gari mai nisa wanda zan kasance Ni kaɗai acan batare da kuba nasan zanyi kewar ku kamar yanda zakuyi nawa tunda Abba ya dage dole zan koma Marrocco”.

    Kai suka gyaɗa tare da sauƙe ajiyar zuciya kana suka ci gaba da cin abinci batare da wanin su ya sake magana ba sai dai lokaci zuwa lokaci yakan kallesu tare da sakin murmushi.

     

    Wayar M Jameel ne ya karaɗe wajen da ruri ahankali ya ɗauka tare da sakin murmushi kana yayi Picking tare da Sallama.

    Daga ɗaya ɓangaren kuwa cikin sanyin murya Moddibo yace.

    “J ina ka tsaya na jika shiru ko abinci banci ba, sannan kasan bani da lafiya ko dai har yanzu kana gidan Ummi ne?”.

    Murmushi M Jameel Yayi tare da gyara zaman wayar akunnensa kana yace.

    “Ayyah sannu A.J Please kaci abinci sannan ka sake shan maganin dana haɗa maka Insha Allah ina hanya”.

    Lumshe idanu Moddibo yayi tare da sakin ajiyar zuciya kana.

    “Toh shikenan sai kazo kace ina Gaishe da Ummina”.

    Murmushi M Jameel Yayi tare da kallon Ummi dake sauraron duk abinda suke faɗa kana yace.

    “Zata ji”,daga haka ya katse kiran.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “Ohh ina ga dai wannan ko kunyi Aure gida ɗaya zaku zauna bakwa iya minti talatin batare da kunga juna ba ko kuma kunji muryan juna”.

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Ai dai kam dole watarana arabu”.

    Jinjina kai Ummi tayi,tana murmushi kana suka cigaba da cin abincin.

     

    Bayan sun cinye tuwon farantin M Jameel ya Kalli Ummi tare da cewa.

    “Ummi aƙara mana yau ina jin daɗin abinci ina so inci³ incika cikina dan ban sani ba sai kuma yaushe zan sake ci”.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “A’a to ai ko yaushe ma kakeso ai zaka zo kaci”.

    Lumshe Idanunsa yayi tare da buɗe su akan Ummi kana yace.

    “Toh Ummi kwanan nan zamu fara batun aikin nan kinga in dan na tafi Marocco ai bazan dinga samun ciba”.

    Kai ta jinjina tare da faɗin.

    “Ai in dai nan da ne ba nisa bane dashi idan ya kama sai inmaka miya da komai duk zan aika maka dasu idan yaso saika na sawa a fridge”.

    Murmushi Yayi tare da cewa.

    “Hmmyyym Ummina Allah ya ƙara miki nisan kwana mai amfani Allah ya barmu tare”.

    Jingjna kai tayi tare da faɗin.

    “Ameen Babana Allah ya ƙara maka nisan kwana inga har jikokin ka”.

    Murmushi yayi tare da kallonta kana yace.

    “Hmmm Ummina kenan.

    Kin ko san in sha Allah ƴata ta farko sunanki zan samata,

    Na kuwa tabbatar zata ga soyayya ko ƙuda bazan bari ya taɓa ta ba”.

    Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.

    “Jamiluuu na”.

    taja sunan tana murmushi haka nan take jin daɗin kiran sunan sa.

     

    Bayan sun kammala cin abincin Asma’u ta miƙe tare da tattare Plate ta Kai kichen M Jameel kuwa da kansa ya mike ya ɗauki kular abincin ya kai kichen Ummi kuwa Kallonsa ta riƙa yi cike da so.

    Bayan ya ajiye ya fito, woje ya nufa yana cewa

     

    “Bari in ɗauko abu a mota”.

    Toh Ummi tace kana ta meda hankali kan tv.

    Jim kaɗan da fitar da ya shigo riƙe da kwalayen waya masu kyau.

    Ƙirar Samson, kana ya  dawo ya zauna gefen Ummi Asma’u da Bashir suka zauna daga gefensa gyaran murya yayi tare da fuskantar Asma’u kana yace.

    “Ga woyoyinku nan Asma’u yau dai na cika alƙawarin ko”.

    Cikin tsananin jin dadi Bashir ya ruggumshi, yayinda Asma’u kuwa Ummu ta ruggume.

    Cikin son juna suka rinƙayi mishi godiya tare da fatan al’khairi.

    Murmushin jin dadi yayi tare da shafa kan Bashir kana yace.

    “Asma’u yanzu ke wani irin makaranta kike so?”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Yah Jameel duk makarantar da ka zaɓa min ina sonta ina farin ciki da ita”.

    Jinjina kai yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.

    “Zan kuwa zaɓa miki wanda ya dace dake  Insha Allah naga keda ƙawarki kusan ra’ayin ku ɗaya ko yaushe amman wannan karon an samu akasi ita Jenouelist take fata naga ke kuma likitanci kike son karanta”.

    Kallon Bashir yayi tare da cewa.

    “Kai kuma wani irin Makaranta kake so?”.

    Murmushi Bashir yayi kana yace.

    “Duk wanda ka zaɓa min Yaya”.

    Lumshe idanu M Jameel Yayi tare da cewa.

    “Insha Allah kuwa zan zaɓa maka ina ganin Law zaka karanta zaifi dacewa da kai”.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana ya tsira musu ido tare da cewa.

    “Asma’u”.

    Kanta ta ɗago tare da cewa.

    “Na’am Yaya”.

    Anutse ya kalleta cikin yanayin nutsuwarsa da alamun rashin wasa yace.

    “Kinga ke ƴa macece ita rayuwar duniyar nan duk i da ƴa mace ta tsinci kanta ta tsare mutuncinta da darajar ta shine abu mafi daraja ki kiyaye tarbiyyar da muka sha wahalar baki nida Ummi kada ki kunya tamu kada kisa ta baƙin ciki”.

    A hankali ya sauƙe numfashi tare da gyara zamansa kana yace.

    “Saboda ke ƴa macece ke mukafi taraddadi akan ki kinga yanzu ga Bashir amma bana ta raddadi akansa kamar ke mace”.

    Asma’u kuwa ƙasa ta sakeyi da kanta batare da tace komai ba sai wasa da yatsun hannunta da take yi.

     

    lumshe idanunsa yayi kana yace.

    “Burina da fatana inga mun kasance gida ɗaya muhalli ɗaya wallahi akanki da Bashir da kuma Ummin mu yasa nake so inyi Aure inga muna tare”.

    Sai kuma ya kalli Bashir da shima yayi ƙasa da kansa kana yace.

    “Ina so inga lokacin tafiyarku makarantar kana inga lokacin dawowan ku a idona sannan insan kalar mutanen da kuke mu’amala dasu”.

    Sai kuma ya juyo ya kalli Asma’u cikin yaƙini yace.

    “Na yarda da ƙawancen ku da Khausar saboda tana da tarbiyya duk da kuwa tana da rawan kai”.

    Numfasa yayi tare da kallon ta kana cikin raunin murya yace.

    “Asma’u ki kula da rayuwarki sannan kisan irin mutanen da zaki dinga alaƙa dasu idan kuma har Aure kike so Asma’u ki faɗa min idan yaso idan kikayi aure sai ki cigaba da karatun ki agidan mijinki kada ki ɓoye min ki faɗa min komai ki ɗaukeni tamkar ƴar Uwarki mace”.

     

    Cike da kunya Asma’u tayi ƙasa da kanta tare da girgiza kanta kana tace.

    “A’a Yah Jameel nikam karatu zanyi”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Kin tabbatar ba Aure kike so ba sannan babu wanda kike so?”.

    Cike da kunya ta girgiza masa kai tare da faɗin.

    “Yaya Jameel Ni kuma wazan so kuma babu wanda ke zuwa gurina”.

     

    Dariya M Jameel Yayi tare da kallonta kana yace.

    “Mun shiga uku Ummi kadde ƙanwar tawa baƙin jini take dashi?”.

    Murmushi Ummi dake aikin Kallonsu tayi tare da faɗin.

    “Ba wani baƙin jini kawai dai dake tana kiyaye kanta ne babu wanda ke kawo mata wargi”.

    Jinjina kai yayi tare da dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.

    “Toh shikenan Asma’u tun da dai kin bani tabbacin karatu kike so daga nan harki kai digir-gire ki gama har ki taka duk kan matakin da kike so nayi al’ƙawarin zan taimaka miki da duk kan ƙarfina da kuɗina muddin ina numfashi zan tsaya miki”.

     

    Kallon Bashir yayi tare da cewa.

    “Sannan kai kuma Bashir zaka karanci fannin Law tunda kana da ilimin addini ina da yaƙinin zaka tsaya akan gaskiya duk runtsi duk wuya kada Kabi bayan ƙarya ka kasance mai al’ƙawarin  da rikon amana aduk inda ka tsinci kan ka”.

    Jinjina kai Bashir yayi kana yace.

    “Yah Jameel Insha Allah Nayi alƙawari zan kasance ayanda kake fata”.

     

    Hira suka cigaba dayi sosai irin wanda suka ɗauki tsawon lokaci basuyi irin saba wanda har dare yaraba basu lura ba.

    Ahankali Ummi dake murmushi ta daga kanta Idanunta suka sauka akan agogon dake manne abango wanda ke nuni da ƙarfe sha biyu da minti goma,Cikin sauri ta kalli M Jameel tare da cewa.

    “Jamilu”.

    Anutse ya ɗago ya kalleta tare da cewa.

    “Na’am Ummina”.

    Ta sauƙe ajiyar zuciya tare da Kallonsa kana ta sake kallon agogon zuciyarta na bugawa tayi saurin dafe ƙirjinta kana tace.

    “Ka kalli time fa”.

    Cikin sauri M Jameel ya juya Kalli agogo tare da kallon Ummi kana…!

    Cikin sakin fuska yace.

    “Ummi yau anan zan kwana”.

    Cike da mamaki Ummi ta juya ta kallesa, domin tunda Allah yasa tayi aure agidan mahaifin Asma’u bai taɓa kwana ba, sai dai yakan zo aduk sanda yaga dama, a hankali ta sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Anan zaka kwana?”.

    Kai ya jinjina tare da faɗin.

    “Eh zan kwana Ummina”.

    Kallon Ummi Bashir yayi cike da farin ciki ya langwaɓar da kai kana yace.

    “Ayyah Ummi ki barshi kinga yanzu ma dare yayi ki gani fa sha biyu hadda kwata dare fa ya riga da yayi nisa”.

    Cikin sanyin murya me ɗauke da farin ciki Asma’u tace.

    “Gaskiya dai kam mu kwana kawai Yah Jameel, yau nayi matuƙar farin ciki zamu kwana agida ɗaya Allah ya nuna mana ranan Aurenka mu kasance atare na har abadan”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da shafa sajensa kana ya tsira musu ido tare da lumshe idanunsa, a hankali ya sauƙe ajiyar zuciya kana yace.

    “Asmeey zamu kasance atare in sha Allah zanyi Aure kana zaku kasance  gida me kyau da na al’farma da kwanciyar hankali, ni kaina bansan kamannin gidan ba amma na sani gida ne mai masifar kyau da ɗaukar hankali zan riska in sha Allah”,

    Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da lumshe idanunsa kana yaci gaba da cewa.

    “Wanda kowa ke burin samu, in Sha Allah zan sameshi, domin inaji ajikina na kusa isa wannan gidan kafin ku iso zan kasance cikin farin ciki amma idan ina tare daku zanfi farin ciki na zai fi nin kuwa”.

    Cikin yanayin sanyin jiki ya tsira musu ido su duka ukun.

    Ummi kuwa idanu ta zuba masa ko ƙyaftawa ba tayi wani irin yanayi takeji azuciyarta, wanda takasa tantance na menene.

    Asma’u kuwa murmushi tayi tare da Kallonsa kana tace.

    “Yaya Jameel Allah ya baka mace ta gari wacce zata kula da Ummin mu tamkar yanda kake kulawa da ita sannan ta ƙaunace mu tamkar yanda kake ƙaunar mu”.

    Murmushi yayi kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.

    “Insha Allah Asmeey matar da zan Aura, macece wacce ta fito daga babban gidane masu tarbiyya da kamala, wacce zata riƙe Ummina daku tamkar Iyayen ta da kuma ƙannenta”.

     

    Sai kuma ya numfasa tare da tsira mata ido.

     

    Kai Asma’u ta gyaɗa murya cike da jin daɗi tace.

    “Ni kuwa Yah Jameel Nayi maka al’ƙawarin zan kasance mata tamkar yar uwa Aminiya yadda kake fata har ma fiye da haka”.

    Sassayan numfashi ya fesar kana yace.

    “Alhamdulillah Asmeey idan kika min haka ko a ina na kasance zanyi al’fari dake sannan zanyi farin ciki”.

    Sai kuma ya maida kallonsa kan Bashir tare da cewa.

    “Yauwa kai kuma Bashir”.

    Anutse ya ɗago kansa tare da faɗin.

    “Na’am Yah Jameel”.

    cikin sanyin murya yace.

    “Bashir ka maida hankalin ka akan karatun ka, kada ka biyewa aboka nan banza kasan dawaye ya dace kayi abota kada ka biyewa matan banza da abokan baza kada kasa Ummi tayi Allah wadai da halayyar ka”.

    Ƙasa da kai Bashir yayi yayin da Ummi kuma shiru tai tana mai jin daɗin Nasiyyar da yake wa ƙannensa.

    A hankali ya numfasa kana yaci gaba cewa.

    “Bashir aikin Law aikine mai matuƙar daraja da muhimmanci sai dai wasu sun ɓata aikin da cin hanci da rashawa da tauye haƙƙin masu gaskiya, da tozartasu, ina so kamin alƙawari kai zaka kasance mutum mai adalci da karamci akan aikinsa wanda duniya za tayi al’fahari da kai sannan Ummina tayi farin ciki da rayuwarka”.

    Sai kuma ya ɗanyi shiru yana kallon yadda Bashir ke gyaɗa masa kai alamar nasihar na ratsashi, cikin yanayin lallashi da jan hankali yaci gaba.

    “Dan Allah Bashir kada ka bari adalilinka Al’umma su la’anci Ummina suyi Allah wadai da haihuwarka da tayi”.

    Cikin rawan murya Bashir yace.

    “In sha Allah zan zama yanda kake da buri har ma fiye da haka Yah Jameel”.

    Lumshe Idanu M Jameel Yayi tare da shafa sajensa kana cikin sanyin murya yace.

    “Nagode Bashir tabbas ko bayan ba nan Idan ka kasance mutumin kirki zanyi farin ciki, sannan ka kula min da Ummina da Asma’u kada ka bari hawayen baƙin ciki ya zubo daga idanunsu ni dai burina kayi min wannan al’ƙawarin”.

    Jinjina kai Bashir yayi tare da cewa.

    “Nayi maka alƙawari Yah Jameel Ummi da Asma’u baza su taɓa baƙin ciki dani ba, kullum zan saka su farin ciki sannan zan kasance mai riƙon alƙawari aduk inda na tsinci kaina”.

     

    Murmushi M Jameel Yayi Idanunsa alumshe yace.

    “Alhamdulillah³ Allah na gode maka”.

    Anutse ya juya ya kalli Ummi data tsira musu Ido kana cikin sanyin murya yace.

    “Yauwa Ummina faɗamin me kike buƙata ko kuma kike so arayuwar ki nayi miki?”.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tayi murmushi tare da cewa.

    “Toh ni kuma meya rage arayuwa wanda baka yimin ba Jamilu?

    Ai ni kam kayi min komai sai dai Ubangiji Allah ya maka albarka Allah yabaka ƴaƴan da zasu yi maka biyayya”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Ameen Ummina amma yanzu baki da wata damuwa ko buƙata?”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Bani da wani damuwa ko buƙata aduniya Jamilu, domin kafin na buƙaci komai ma kiyi min”.

    Hannunsa biyu ya ɗaga sama tare da faɗin.

    “Alhamdulillah Allah Nagode maka ya Ubangijin Allah ka bani damar da duk ɓuƙatar da mahaifiyata take dashi kafin ma ta buƙata nayi mata shi”.

     

    Murmushi tayi kana tace.

    “Ameen Ubangiji Allah ya maka albarka Allah ya rufa maka asiri duniya da lahira Allah yasa ƴaƴan ka su ramamaka abinda kayi mana”.

    Still Fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Ameen ya Allah”.

    Ummi kuwa ahankali ta daga kanta gani tayi har ƙarfe uku kallonta ta mayar kansu kana tace.

    “Yanzu yaranan baza ku tashi kuje ku kwanta ba ku dubi time fa”.

    Atare Asma’u da Bashir suka ce.

    “Toh Ummi am gaba ɗaya yau bama jin baccin ma”.

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Ai dai kam”,

    Ummi kuwa murmushi tayi kana suka cigaba da hira.

    Jin ankira Sallar ƙarfe huɗu yasa Ummi kallon su tare da faɗin.

    “Toh yanzu kam mutashi muyi alwala muyi nafillah mu rufe wannan daren da roƙon Ubangiji”.

     

    Bayan duk sunyi Al’wala ne suka dawo falo duk suka shimfida Sallaya sukayi nafila raka’a huɗu-hudu.

     

    M Jameel kuwa acikin sujjadar ta ƙarshene yace.

    “Ya Allah katsare min Mahaifiyata da ƙannena Ubangiji ka zama gatansu anan duniya da lahira ya Allah ka tsaresu daga sharrin abin ƙi Ubangiji ka inganta rayuwar Asma’u da Bashir ya Allah ka tabbatarwa da A.J na al’khairi a cikin samun mace tagari wacce zata kula da ɗawainiyarsa ya Allah kabiyawa duk musulmi ɓuƙatar su na Alkhairi”.

    Ko wannensu haka ya dinga addu’a saida aka kira Assalatu kafin suka miƙe Shida Bashir suka tafi masallaci Asma’u da Ummi kuwa anan suka Idar da Sallah.

     

    Bayan sun dawa daga masallaci M Jameel ya kwanta akan 3sitter Ummi Atake Bacci mai daɗi ya ɗaukesa.

    Ummi da Asma’u kuwa kichen suka shiga tare da soya musu soyayyen dankali da ƙwai kana suka tafasa ruwan tea da yaji citta da kanumfari sai kuma tayi musu ɗumamen tuwon jiya, ganin yadda yaketa zuba tururine yasa Asma’u tas hannun da nufin buɗe  murfin tukunya, zafin da taji ya ratsa ƴan yatsunta ne yasa ta saki karfin ya faɗi ƙasa tare da bada ƙara.

    Cikin sauri Ummi ta kalleta kana cikin ƙasa da murya tace.

    “Kai Asma’u kiyi a hankali mana kada ki tashi yayan ku, bakiga jiya bai samu bacci ba”.

    Murmushi Asma’u tare da gyaɗa mata kai kana tace.

    “Toh Ummi”.

     

    Har misalin ƙarfe tara M Jameel bai far kaba Ummi kuwa toilet tashiga tayi wanka bayan ta shirya ta fito falon har zuwa lokacin M Jameel na bacci ahankali ta zauna agefensa tare da tsira masa idanu tana kallon yanda yake baccin cikin kwanciyar hankali tamkar yana murmushi kyawun fuskarsa ya sake nunkuwa fiye da ko yaushe.

     

    Asma’u data fito daga kichen ta kalli Ummi kana ta saki murmushi tare da cewa.

    “Kayyy Ummi irin wannan kallon sai kace kin samu TV ”.

    Sai asannan Ummi ta ɗauke Idanunta daga kansa ta mayar kan Asma’u tare da yi mata daƙuwa.

    Murmushi Asma’u tayi kana tace.

    “Ai gaskiya ne”.

    Bashir daya shigo Bedroom din yayi dariya kana yace.

    “Gsky dai Ummi kwanan nan kina yawan kallon Yah Jameel ko dan yafi mu kyaune?”.

    Wara ido tayi tare da sakin murmushi kana tace.

    “Waya faɗa maka yafi ka kyau ai kafisa”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Ummina kin dai faɗa min inji daɗi ne kawai”.

    M Jameel kuwa cikin bacci yake jiyo hiransu sama-sana ahankali ya motsa.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da kallon sa kana tace.

    “Toh katashi kayi Breakfast. Idan yaso sai ka koma baccin”.

    Cikin sauri ya buɗe Idanunsa tare da Kallon Ummi kana yace.

    “Uhmmm Ummi sai anjima”.

    Kansa ta shafa kana tace.

    “A’a tashi kaci abinci, bana son bacci da yunwa Babana”.

    Hannunta ya riƙe kana yace.

    “Naji daɗina Ummina ta kirani da Babana Abbana ya kirani da Babana”.

    Miƙewa yayi ya zauna tare da cewa.

    “Ummina banyi wanka ba sannan banyi brush ba ba zan iya Breakfast ba”.

    Girgiza kai Ummi tayi tare da faɗin.

    “Aikam dai gashi tun ɗazu na bawa Bashir kuɗi ya sayo maka Brush kafin ka tashi ga Brush ga Maclean kayi”.

    Miƙewa yayi kana ya ɗauka, toilet dake falon yashiga ya wanke bakakinsa.

    Asma’u kuwa tun shigansa toilet ta Miƙe tankwaso musu kayan Breakfast ɗin yau ma kamar jiya haka atare sukayi Breakfast ɗin.

    A hankali ya kai kofin tea bakinsa sai kuma yayi sauri ajiye cup din jin wayarsa ta hau ruri Asma’u dake kusa da wayar ta miƙa masa karɓa yayi tare da sakin murmushi kana yayi Picking tare da cewa.

    “Assalamu Alaikum A.J”.

    Daga ɗaya ɓangaren Moddibo ne yace.

    “J yana jika shiru gashi Innayi ta haɗa mana Breakfast na kasa ci ni kaɗai”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da kallon Ummi, Asma’u,da Bashir kana yace.

    “A.J gani tare da Ummina da Asma’u da kuma Bashir muna Breakfast tray ɗaya kamar yanda mukayi jiya, ina jin farin ciki inaji kamar wani gurbi na cike wanda ban samu damar cike saba tsawon shekaru”.

    Lumshe idanu Moddibo yayi kana ya gyaɗa kansa tabbas ya fahimci farin cikin da M Jameel ke ciki ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.

    “Shikenan hakan yayi kyau bawa Ummina mu gaisa”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da miƙawa Ummi wayar.

    Cike da so Ummi tace.

    “Babana na ƙwace maka Amini ko?”.

    Murmushi Moddibo yayi wanda take iya jiyo sautin sa kana cike da ladabi yace.

    “Ayyah Ummina bakomai ai kawai ina kewar sa ne Ina kwana?”.

    Murmushi tayi tare da faɗin.

    “Lafiya Lau ya Innayi?”.

    Ahankali yace.

    “Tana lafiya tace agaishe  ki”.

    Daga haka sukayi sallama tare da katse kiran Bayan sun kammala Breakfast ɗin Asma’u ta tattare kwanikan kare da kaiwa kichen kana ta dawo ta gyara wajen.

    M Jameel kuwa jingina kansa da guiwar Ummi yayi kana suka cigaba da hira cike da tsananin ƙaunar junansu…!

     

     

     

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*