Author: Novels

  • Sakayyah 20

    Sakayyah 20

     

    SAKAYAH

     

    20

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

    Ujnr. Tana shiga ta sauƙe numfashi ganin babu. Gimbiya Dadu, falon shiru ba kowa sai Uncle Naseer dake zaune kan 3sitter yana riƙe da system akan cinyarsa da kuma wayarsa.

    Yana ganinta yayi saurin rufe system ɗin kana ya zira wayarsa acikin aljihu tare da tsira mata idanu afili ya furta.

    “Wowww Masha Allah kinsha kyau My Dear”.

    Batare da tace komai ba ta ƙara sa shiga falon tare da yiwa kanta masauƙi akan 1sitter.

    Tsuke fuska yayi tare da zuba mata idanu kana yace.

    “Meyesa ba zaki zauna akusa dani ba My Khausi?”.

    Kallonsa tayi da lumsassun idanunta kana da alamun bacci acikin Muryanta tace.

    “Unclr Naseer nan ma yayi”.

    ta ƙarasa maganar tana mai lumshe Idanunta.

    Ido ya tsira mata yana kallon yanda ta lumshe sexy Eyes ɗin ta miƙewa yayi tare da dawowa kusa da ita ya zauna a hannun kujeran, yana shaƙan daddaɗan ƙamshin turarenta, Khausar kuwa jin alamu sa akusa da ita yasa tayi saurin buɗe Idanunta dake lumshe kana ta miƙe da niyyan barin wajen.

     

    Cikin hanzari ya sanya tafin hannunsa dake ɗauke da zoben azurfa ya riƙe nata yana binta da wani mayataccen kallo.

    fuskarta ta yamutsa cikin ɗaure fuska kana da rashin walwala tace.

    “Me haka Uncle Naseer?”.

    Langwaɓar da kai yayi tare da tsaida idanunsa cikin nata kana ya karyar da murya tare da faɗin.

    “Guduna zakiyi?”.

    Kai ta girgiza masa tare da lumshe Idanunta jin bacci na fusgarta kana tace.

    “A’a ba gudunka nake ba kawai dai ai baidaceba”.

    Karyar da muryarsa yayi tare da yi mata kallon Up and down kana yace.

    “Toh ki zauna anan ni dodone, ko kuma cinye ki zanyi mai yasa kike min haka ne Khausar”.

    Kai ta girgiza tare da gyara hijabinta kana tace.

    “Bai dace bane Uncle Naseer haka baiyi ba ni ka sakar min hannu”.

    Wani kallo ya watsa mata kana yace.

    “Bazan sakar miki hannu ba”.

    Ya ida maganar yana latsa mata hannu tare da yi mata tafiyar tsutsa.

    Cikin fushi ta.

    Fisge hannunta tare da galla masa harara kana tace.

    “Ni gaskiya banason abinda kake min banaso sam”.

    Ta Faɗa tare da juyawa zata bar masa falon.

    Da sauri ya miƙe tare da shan gabanta kana ya durƙusa akan gwiwoyinsa tare dasa hannunsa duka biyu ya riƙe kunnensa cikin wata. Sanyayyar murya mai cike da lallashi ya zuba mata ido tare da cewa.

    “Na tuba dan Allah kiyi haƙuri, bazan ƙara ba Insha Allah, ki gafar ceni kinji My dear.

    Dan Allah Dan darajar Annabi Muhammad (S.A.W) kiyi haƙuri ki koma ki zauna naji Ni zan zauna a ƙasa”.

    Jin haka yasa ta saki ajiyar zuciya tare da komawa ta zauna.

    Murmushin gefen baki ya saki tare da miƙewa ya zauna aƙasan Capet mai taushi dake malale Atsakiyar falon tare da yin tagumi kana ya tsira mata Idanu, tare da saki ajiyar zuciya langwaɓar da kai yayi kana yace.

    “Khausar ina sonki, ya zanyi idan har kikayi fushi dani rayuwata ba zata yimin daɗi ba. Duniyar nan zata yimin duhu matuƙar dai kikayi fushi dani, hankalina ba zai kwanta ba.

    Kada ki mancefa na yarda nabi duk dokan da aka samin nacewa kada in sake inyi miki maganar soyayya har saikin kammala Secondary school, ni Kuma na kammala karatuna”.

    Ajiyar zuciya ya saki tare da fesar da numfashi kana yace.

    “Bisa wannan sharaɗin aka hanani koda jin Muryan kine Koda na Kira Mommy mun gaisa baza ta baki mu gaisa ba, haka nayi ta dakon soyayyarki azuciyata, duk tsawon shekarun nan da nayi a India ina ɗauke da dakon soyayyarki Khausar, Ina son ki³ kinsan tsawon shekara shida ba wasa ba I miss you, I really love you Matata, kece farin cikina kece sirrina kece duniya ta Khausar will you Marry me?”.

    Ahankali tayi ƙasa dan kanta har ga Allah batasan mai zata ce dashi ba.

    Kai ya jinjina tare da cewa.

    “Khausar zaki Aureni!?”.

    Lallausan tafin hannunta tasa ta rufe fuskarta batare data bashi amsa ba.

    Shi kuwa Naseer murmushi ya saki kana yace.

    “Nagode My Khausi”.

    Domin shi duk azatonsa kunyarsa da kuma rufe fuskar da tayi sonsa take.

     

    Cikin Sanyayyar murya mai taushi da kulawa ya kalleta kana yace.

    “Kece Sirrina duk abinda zanyi aduniya dole ke sirrina ce, dake zanyi shi abubuwa biyu ne suka dawo dani ƙasar nan Khausar,

    akwai mahaɗin abinda ya dawo dani ƙasar nan sai kuma burin mallakar ki da fatan  kasancewarki mallakina na har abada”.

     

    Cikin sanyin murya mai ratsa zuciyar duk wanda ya saurara tace.

    “Uncle Naseer kace Ubangiji ya mana zaɓi msfi al’khairi, duk abinda muke so aduniya mu barwa Ubangiji  zaɓi kaji ko Uncle Naseer”.

    Kai ya jinjina tare da cewa.

    “Naji Nagode amma ina da wata alfarma da nake so in nema awajenki shin zakiyi min shi?”.

    Cikin sanyi da alamun bacci a idanunta tace.

    “Eh Uncle Naseer in baifi ƙarfina ba zanyi maka shi”.

     

    Gyara zamansa yayi tare da cewa.

    “Kinyi alƙawari?”.

    A hankali ta buɗe Idanunta sosai akansa kana tace.

    “Toh  ai ban sani ba yafi ƙarfina ko baifi ba”.

    Langwaɓar da kai yayi tare da cewa.

    “Baima fi ƙarfin kiba Khausar. Insha Allah bai fi ƙarfin ki ba zaki iya ba abune na kokuwa ko dambeba sannan ba mugun abu da zai saɓawa Addinmu bane”.

    Ajiyar zuciya ta saki kana tayi murmushi tare da cewa.

    “Allah dagaske!?”.

    Ka ya jinjina mata kana yace.

    “Eh dagaske”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Toh shikenan Uncle Naseer”.

    Idanu ya tsira mata  tare da faɗin.

    “Kinyi alƙawari zakiyi min!?”.

    Wara manyan Idanunta tayi tare da cewa.

    “Bana so ina ɗauki al’ƙawari bansan kuma menene bane!”.

    Cike da manufa ya karyar da murya tare da cewa.

    “Ni dai nafi son kiyi min al’ƙawari, zaki te maki rayuwata, da kuma cigaban mu, da Kuma jin daɗin ki kinji ko Khausar, saboda jin daɗina da jin daɗin ki nakeso muyi wannan abin kuma wannan sirrin mu ne amatsayin ki na matata dan ko mahaifiyata bata san wannan sirrin ba!”.

     

    Nan-nauyan ajiyar zuciya Khausar ta saki Idanunta akansa tace.

    “Toh wannan wani irin sirrine ka faɗa min mana”.

    Kai ya Girgiza tare da cewa.

    “A’a har sai kinyi al’ƙawari zaki min abun zan faɗa miki”.

    Girgiza kai tayi kana tace.

    “Yaya Naseer bana so in maka al’ƙawarin da ban sani ba ko bazan iya ba”.

     

    fesar da iska mai sanyi yayi tare da kallonta kana yace.

    “Zama ki iya”.

    Kallonsa tayi ganin yanda ya marairaice yasa ta saki Ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Toh shikenan sai nayi shawara”.

    Da sauri ya kalleta tare da cewa.

    “Shawara kuma da waye zakiyi shawara? bana faɗa miki siririn mu bane! Sirrina ne dani dake kasancewar abu ɗaya zamu kasance, zaki kasance matata kuma uwar ƴaƴana kece zaki kasance ruwa mai kashe min ƙishina”.

    Sauƙe sanyayyar Ajiyar zuciya tayi tare da faɗin.

    “Toh shikenan sai nayi tunani”.

    Langwaɓar da kai yayi tare da cewa.

    “Zuwa yaushe?”.

    Shiru tayi alamar tunani sai kuma tace.

    “Zuwa gobe ko jibi”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh shikenan ba damuwa Allah ya kaimu muyi hira mana”.

    Marairaice fuska tayi kana tace.

    “Ayyah Uncle Naseer bacci nake ji”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Toh shikenan muje inda rakaki”.

    Batace komai ba tashige gaba yana biye da ita, tare da zubawa ƙugunta idanu saida ta shiga falo sannan ya koma ya shiga motarsa ya wuce gida.

     

    Acan ɓangaren Moddibo kuwa awannan dare haka ya kwana cikin mawuyacin hali saboda wani azabebben yanayi dake damunsa sai. Wajajen ƙarfe uku da rabi  wani irin bacci mai shegen daɗi ya ɗauke sa.

     

    Can cikin baccin nasa ya fara wani irin bahagon mafarki, ganinsa yayi tare da Khausar, suna kwance akan gado ɗaya cikin wani irin ni’imtaccen bargo fari ƙal mai masifar taushi, kana babu komai a jikinsu yana rungume da ita hannunsa na dama nakan yalwataccen sumar kanta mai ƙamshi da sheƙi yana shafawa, yayin da ɗaya hannun ke kan caɓullenta yana murzawa.

    Cikin Sanyayyar murya mai cike da shagwaɓa Khausar ta sakar masa wani irin narkekken kuka tare da cewa.

    “Tsoro nake ji nikam bazan iya ba Moddibo kabar ni bazan iya ba”.

    Shi kuwa Moddibo karyar da murya yayi cikin tattausan murya mai cike da salama yake lallashinta.

    Ƙarfe huɗu dai-dai ya farka sakamakon kiran sallar assalatu da akayi miƙa yayi tare da furta.

    _“Alhamdulillahi lazi ahyana bada amatana wa’ilaihin nushur”_.

    Kana ya tashi zaune yana kallin Boxes ɗinsa da ya bada damshi alamar yayi ta liking.

    Cikin sauri ya furta.

    “Ya Salam Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n nashiga Uku”.

    Da sauri ya miƙe tare da dafe kansa kana yace.

    “Innalillahi Wa’inna ilahi rajiu’n, shin wannan wace irin Masifa ce mai nacin tsiya da bibiyata, madadin abin nan yayi baya kullum sai gaba-gaba yake yi, yanzu abin har yakai matakin mafarkin yarinyar nan nakeyi wannan wace irin rayuwa ce? In banda ma rashin kunya da raini ya za’ayi yarinyar nan ta biyoni har cikin bacci na”.

    Sake kallon boxes sa yayi dan tabbatar wa still gani yayi zahiri ya jiƙe da yarinyar amafarki, cike da tafasan zuciya ya shafa Dk ɗin sa dake bayyana zalamarsa duk da cewa yayi liking.

    Amma bai nitsuba ba zama yayi abakin gado tare da dafe kansa da hannu biyu ji yake tamkar ya fashe da kukan takaici.

    “Tabbas da ace mafarki na zama gaskiya to da sai na sumar da yarinyar nan, ta yadda har abada bazata sake zuwan min ba”. yayi mgnar a sama lips inshi.

     

    Ahankali kuma sautin muryanta yashiga dawowa cikin kunnensa tana cewa.

    “Tsoro nakeji bazan iya ba Moddibo”.

    Wani dogon tsaki yaja kana cikin wani irin fushi ya miƙe tare da lumshe idanunsa tabbas badan amafarki bane da sai yayi maganin yarinyar.

    Toilet yashiga tare da wanka  kana ya ɗaura Al’wala duk zuciyarsa babu daɗi bayan ya shirya ya tafi masallaci.

     

    Bayan kwana biyu kamar ko yaushe Anutse Khausar ce ta fara miƙewa kana tayi submitting ɗin Booklet ɗin ta yayin da sauran ɗalibai ke cizon gindin biro sosai Exam ɗin Nahwun ya basu wahala ahankali. Khausar ta fita tana lumshe Idanunta duk da cewa ta saba answering questions kafin abasu amsa amma na yau ya wahalar da ita ajikin Up stair ta tsaya tare da ɗaura hannunta akan step ɗin sama kana ta zu bawa farfajiyar makarantar Ido, sanyayyan iska na kaɗata tsayuwar ta da kamar minti biyar wata baƙar mota tazo ta faka ta bada baya.

    Cikin sauri ta zare Ido tare da kallon number motar  cike da mamaki da al’ajabi ta mitsika Idanunta tare da sake kallon number motar cikin rawan murya tace.

    “Wannan Motar Again?”.

    Tabbas wannan shine motar da tagani a Jauro Yaya a lokacin da suka tafi Rafi dasu Dija still, kuma aranan aka kashe Baffa Umaru tabbas kamannin motar da kuma Number ba zasu taɓa ɓace mata ba to amma mai yazo yi amakarantarsu.

    Kallon motar ta sake yi still Yana tsaye cikin sauri ta fara taka step ɗin tana haɗawa bibbiyu har ta sauka kana ta nufi gate.

     

    Da sauri Baba Mai gadi ya miƙe tare da cewa.

    “Khausar ina Zakije?”.

    Kallonsa tayi tare da cewa.

    “Saƙo zan amsa awajen masu wancan motar”.

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Kinsan dokar makarantar nan bata bari idan anshiga afita amma kina amsa ki dawo”,

    Kai ta gyaɗa tare da ficewa shi kuma yabi bayanta.

     

    Ahankali ta tsirawa number motar Idanu kana cikin sanyin jiki ta nufi motar.

    Mutanen dake Cikin motar kuwa sam basu lura da ita ba saida taje gab dasu suka lura da kamar tana leƙa su ne, kana ga dukkan alamu Idanunta na kan Plate number motar cikin sauri suka ɗaga glass ɗin motar dake ƙasa.

    Khausar kuwa cikin sauri ta nufi gaban motar dan ganin fuskokin su waye ne, mutumin dake zaune a mazaunin Driver ne yayi saurin figar motar da mugun gudu suka tafi.

    Cike da mamaki Khausar ta dafe kuncinta tare da cewa.

    “Ha’a to meyesa haka?”.

    Anutse ta juya bayanta jin Muryan Baba mai gadi na cewa.

    “Toh ya kuma ba abinda suka baki suka ja mota da gudu haka suka tafi?”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kallon Baba mai gadi kana tace.

    “Agaskiya bansan suba fa, amma dai na taɓa ganin motar acan Rugar mu shiyasa yanzu na saƙƙo inga shin wannan motar ce ko kuma watace, kuma na gane motar ita ɗin ce, kuma awannan ranan ma dana gansu haka suka gudu”.

     

    Kai  Baba mai gadi ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh Allah yasa dai lafiya?”.

    Nan-nauyan ajiyar zuciya ta saki tare da furzar da iska mai zafi daga bakinta kana tace.

    “Ka kula gaskiya Baba mai gadi, ka kula duk sanda kasake ganin wannan motar ka faɗa min”.

    Kai ya jinjina tare da cewa.

    “Toh shikenan amma ai kalar motoci da yawa taya zan gane wannan?”.

    Sauƙe numfashi tayi tare da faɗin.

    “Aina riƙe number”.

    Bata jira cewarsa ba ta janyo biron dake kanta tare da yagar ƙasan Qautions paper ta rubuta masa number tare da miƙa masa kana tace.

    “Gashi ka riƙe duk sanda ka sake kallon tazo bakin makarantar nan, ka faɗa min ni ban yarda da motar nan ba, dan ko can Rugar da suje adaren ranan akwai abinda ya faru”.

    Ajiyar zuciya ta saki tare da rintse Idanunta kana ta cigaba da cewa.

    “Haka nan naji na tsargi motar duk da bani da tabbaci sannan still yauma. Kaga tazo ta tsaya mana abakin makaranta Indai tazo ka sake ganinta ka sanar min ko kuma ka sanarwa Malamai”.

    Jinjina kai Baba mai gadi yayi tare da cewa.

    “Toh shikenan insha Allah ”.

    Kai ta gyaɗa tare da buɗe ƙaramin gate ta koma cikin makaranta tana koma suka haɗu da M Jameel na ƙoƙarin zuwa office.

    Da Mamaki M Jameel ya kalleta kana yace.

    “Daga ina kike Khausar kaddai yanzu kika zo?”.

     

    Kallonsa tayi tare da girgiza kai tayi kana tace.

    “A’a tun ɗazu nazo na gama Peper nama shiyasa na fito”.

    Kai ya jinjina tare da cewa.

    “To mai kika je yi awaje?”

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Wani abu naje na ɗan duba?”.

    Gyara tsayuwarsa yayi kana yace.

    “Wani abu kika je dubawa bayan kinsan doka da ƙa’idar makarantar nan, in anshiga ba’a fita yanzu kiyi laifi idan ansaki kaɗe ɗankwali kice rayuwar bauta kike baki da cikekken ƴanci ko?”.

    Ƙasa tayi da kanta tare da cewa.

    “A’a wata mota ce muka gani nida Baba Mai gadi”. Dai-dai lokacin kuma ta hango Moddibo ya fito daga corridor da zai sada ka da office ɗin su zare ido tayi cikin sauri ta juya tare da hawa step ɗin class ɗinsu.

    Murmushi M Jameel Yayi tare da girgiza kai Dramer Moddibo da Khausar na sanyashi nishaɗi.

    Khausar kuwa na haurawa ta samu Asma’u ta fito tayi submitted Booklet din ta ba daɗewa kowa ya fito sannan suka tafi.

     

    Motar na parking Khausar ta fito dai-dai lokacin Mommy ta shigo tsayawa Khausar tayi har Mommy ta ƙaraso kusa da ita.

    Kallon ta Khausar tayi tare da cewa.

    “Mommy daga ina haka naga kamar kin fita Unguwa?”.

    Kai Mommy ta gyaɗa mata kana tace.

    “Eh Khausar na fita Unguwa naje gidan Aunty Asiya ce yau ta haihu Allah ya sauƙeta lafiya”.

    Wara Ido Khausar tayi cike da farin ciki tace.

    “Laaaa Mommy Aunty Asiya ta haihu? Mai ta haifa Mommy?”.

    Jinjina kai Mommy tayi tana tafiya tace.

    “Ta haifi ƴa mace”.

    Jinjina kai Khausar tayi tare da faɗin.

    “Masha Allah bari nayi wanka naje na duba Baby”.

    Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.

    “Ai dai kam ya kamata dama anats cewa wai yarinyar na kama dake”.

     

    “Dani kuma Mommy?”.

    Kai Mommy ta gyaɗa tare da zama akan 2sitter tana cire hijabinta tace.

    “Eh toh da Raudat take kama Raudat kuwa kinga dake take kama shiryasa kowa ke cewa Jaririyar kamar Khausar ²”.

     

    Murmushin fuskarta ta faɗaɗa kana tace.

    “Aikam bari nayi wanka Inje inga mai kama dani”.

    Ta ida maganar tare da wucewa Bedroom  akan beside drawer ta ajiye tarkacen hannunta kana ta cire Uniform ɗin ta ɗaura towel tashiga toilet.

    Tayi wanka tana fitowa ta zauna gaban Dressing mirrow tare da shafa Lotion ɗin ta, kana ta sanya dogon rigar material Sky blue ta yane Kanta da baƙin gyale, sannan ta feshe jikinta da turaruka masu daɗin ƙamshi ta fice.

    Mommy dake zaune a falo ta kalleta tare da cewa.

    “Khausar ko abinci fa baki ciba?”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “A’a Mommy sai na dawo”.

     

    “Adawo lafiya”.

     

    Anutse ta fita tafiya kaɗan tayi ta isa gidan mutum uku kawai ta samu aɗakin.

    Kusa da Aunty Asiya dake mata murmushin ta zauna tare da cewa.

    “Aunty Asiya ina baby?”.

     

    “Gata nan”.

    Ta faɗa tana nuna mata matar dake gefenta.

    “Masha Allah, wata tana kama da niko? Allah ya raya mana”.

    Murmushi Aunty Asiya tayi tare da faɗin.

    “Ameen Khausar ga Baby”.

    Da sauri Khausar ta karɓe ta tare da cewa.

    “Bari inga mai kama dani”.

    Ta faɗa tana zubawa Jaririyar Ido farace sol da ita ga wani yalwataccen gashi daya kwanta asaman goshinta kana girar tama da yelwataccen gashi bakinta yayi pich da dogon Eyelashes.

    Da sauri Khausar ta ɗago kanta da murmushi afuskarta tace.

    “Aunty Asiya wallahi kam Baby kam tayi kyau Masha Allah”.

    Jinjina kai Aunty Asiya tayi tare da cewa.

    “Aikam dake take kama, wai Gimbiya Dadu tace idan kinzo kitso ina yawan kallonki shiyasa na haifi me kama da ke”.

    Baki Khausar ta taɓe tare da cewa.

    “Uhm Ita kuma duk duniya akwai wanda yafi ta kallona ne?”.

    Murmushi Aunty Asiya tayi, Khausar kuwa Jaririyar ta miƙa mata tare da miƙewa kana tace.

    “Bari in tafi Aunty Asiya Allah ya raya”.

    Karɓar Jaririyar Aunty Asiya tayi kana tace.

    “Toh ki Gaishe da Mommy da gajiya”.

    Amsawa Khausar tayi da cewa.

    “Za taji” kana ta fice.

     

    Bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon zaune ta samu Mommy a inda ta tafi ta barta kusa da Mommy ta zauna da murmushi afuskarta tace.

    “Wallahi Mommy Jaririyar muna kama nima naga kamar mu”.

    Jinjina Kai Mommy tayi tare da ajiye wayarta kana tace.

    “Nima gaskiya naga kamar ku sai naga kamar lokacin kina Jaririya,  kuma haka Raudat ma take shiyasa ake ganin kamar dake take kama”.

    Veil dake kanta ta janye tare da cewa.

    “Ai dai kam”.

    Miƙewa tayi tare da cewa.

    “Mommy bari na ɗauko abincina”.

    Kai Mommy ta gyaɗa mata sannan ta wuce kichen ɗin.

     

    Bayan kwana shida; Alhamdulillah a yau ne su Khausar suka rubuta Final Exam ɗin su cike da tsananin farin ciki ko wanne ɗalibi ya fito daga hall da suka rubuta Exam ɗin, cikin tsanananin farin ciki Khausar ta nufi jikin tap ɗin ruwa tare da buɗe wa ta cika wani ƙaramin Bocket kana ta nufi kan Asma’u dake tsaye.

    Rungumeta tayi tare da sheƙa musu ruwan tace.

    “Thank God My Asmeey Alhamdulillah yau mun taka matsayi na farko  a fannin karatun mu”.

    Cike da farin ciki Asma’u da jikinta ke ɗigan ruwa ta kalleta kana tace.

    “Sosai kuwa Khausar mun godewa Allah”.

    Baki ɗaya ɗaliban haka suka ringa jiƙa jikinsu da ruwa cike da matsanancin farin ciki kasancewar an hanasu penday yasa suka shiga jiƙa jikinsu.

    Khausar kuwa kallon Samira sani da itama jikinta ke jiƙe tayi tare da miƙa mata hannu kana tace.

    “Assalamu Alaikum, Alhamdulillah yau kam abinda ya haɗa ya raba”.

    Hannunta Samira Sani ta riƙe tare da murmushin gefen baki sai kuma ta watsa mata Harara dama can ba wani haushin Khausar take jiba tunda Moddibo ba wani kulata yake ba sai dai yadda tafisu ƙwazone ke bata haushi.

     

    Acan ɓangaren Malamai kuwa baki ɗaya sun hallara a inda suka tanadar dan yin taro Moddibo ne kaɗai baya wajen bayan duk ɗalibai sun hallara.

    M Jameel ya miƙe tare da hura Microphone kana yace.

    “Assalamu Alaikum warahmatullah Wabarkatuhu”.

    Baki ɗaya Suka amsa da. “Wa’alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.

    Yayi gyaran murya tare da cewa.

    “Da farko amadadin dukkan malamai da shuwagabannin wannan Makaranta muna taya ɗaukakin Ɗaliban wannan makaranta murnan kammala jarrabawar su na gama makarantar.

    Allah ya bada sa’a Ubangiji ya baku ikon fitowa da sakamako mai kyau”.

    Baki ɗaya wajen suka amsa da.

    “Ameen”.

    Tsayuwarsa ya gyara tare da cewa.

    “Insha Allah shugaban makaranta zai bada Award da hannunsa ga dukkan ɗaliban da suka cancanta Malam Bismillahi”.

    Miƙewa Malam Arɗo yayi tare da karɓan Microphone ɗin kana yace.

    “Ina taya ɗaukakin Ɗaliban wannan makaranta ta *AL,ANSAR Academic School* murnan kammala karatun su na matakin farko Allah ya Albarkanci karatunki Ubangiji ya ɗauka ku aduk inda kuke”.

    Baki ɗaya suka amsa da.

    “Ameen”.

    Gyaran murya yayi tare da cewa.

    “Zamu miƙa award ga ɗilibar da tafi ko wacce ɗaliba.

    Hazaƙa da tsafta”.

    Baki ɗaya wajen sake nutsuwa yayi dan jin wacece wannan.

    “Khausar Usman Abubakar Lelewal itace ɗalibar da tafi ko wacce ɗaliba Hazaƙa da kuma tsafta”.

    Atake wajen ya kaure da kabarra masu taya ta murna irin su Asma’u da Aunty Ruƙayya nayi yayin da masu baƙin ciki irinsu Samira da sauransu keyi.

    Cike da nutsuwa Khausar ta miƙe tare da ƙara sawa ta amshi Award cike da tsananin farin ciki.

     

    Gyaran murya Malam Arɗo yayi  tare da cewa.

    “Ɗalibar da tafi ko wacce ɗalibai Nutsuwa da biyayya itace Asma’u Ahmad”.

    Cike da farin ciki Asma’u ta miƙe tare da ƙara sawa ta amshi Award ɗin ta haka aka kira sauran mutum uku aka basu Award .

    Cike da farin ciki Khausar ta koma gida kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar da cewa tana cikin farin ciki zaune take afalon hannunta riƙe da bowl na Fruit Salat.

    Haiydar ne yashigo falon bakinsa ɗauke da Sallama kallon Khausar yayi tare da cewa.

    “Addah Khausi Uncle Naseer yana kiranki afalon Abba”.

    Murmushi tayi tare da ajiye bowl din Fruit Salat ɗin kana tace.

    “A’a lallai kam ina zuwa”.

    Murmushi Mommy dake zaune gefenta tayi tare da cewa.

    “Yau kam Alhamdulillah gidan nan muna cike da farin ciki Khausar an gama Secondary school tare da samun Award”.

    Miƙewa tayi tare da cire hijabin Uniform da har zuwa lokacin yake jikinta wurgi tayi dashi tare da faɗin.

    “Yau kam nayi hannun riga da Uniform daga yau nayi bye bye da uniform, shiyasa ko aiki banason aikin da zai kasance min da Uniform,  daga yau na wurgar da Uniform aduniya shiyasa Insha Allah Jenouelist zan zama in dinga zaƙulo gaskiya aduk inda yake ”.

    Murmushi Mommy tayi tare da cewa.

    “Toh Allah ya taimaka Ubangiji ya cika miki burinki”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

    Ta faɗa tare da shigewa Bedroom kana ta cire Uniform ɗin ta tare da shiga toilet ta sakarwa kanta shawer bayan ta gama wankan ta fito Lotion ta shafa tare da sanya doguwar rigar atanfa mai golden kana tayi ɗaurin ture, ta feshe jikinta da turarukanta masu daɗin ƙamshi kana ta fice. Jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin kai tsaye falon Abba ta nufa bakinta ɗauke da Sallama.

     

    Lumshe Idanu  Naseer dake zaune kan 2sittee yayi tare da zuba mata idanu yana shaƙan daddaɗan ƙamshin turaren yace.

    “Congratulation My Khausi yau kin gama makarantar ki, nayi matukar farin ciki abubuwa na tafiya yanda ya kamata”.

    Murmushi Khausar tayi cike da farin ciki ta jinjina masa kai.

    Ahankali Naseer ya ɗauko Flowers dake jikin wata leda anyi wrapping ɗinsa tare da ɗauko kwalin waya iPhone  tare da tarin Choculate ya miƙa mata.

    “Ga gift ɗin Graudion ɗin ki”.

    Wara Ido Khausar tayi tare da kallon Uban gift ɗin cike da tsanananin farin ciki ta ɗago manyan Idanunta tare  da kallon sa kana tace.

    “duka wannan na wane?”.

    Kai ya jinjina mata tare da faɗin.

    “Yes My Wife duka naki ne”.

    Langwaɓar da kai tayi kana tace.

    “Mommy ta hanani riƙe waya tace sai na gama Secondary school duka ko lokacin da muke Ss duk abinda zanyi da waya tace sai dai in karɓi nata yanzu kuma kaga”.

    Saurin katseta yayi tare da cewa.

    “Ai me ai kun gama kin manta yau kukayi final Exam”.

    Jinjina kai tayi tare da cewa.

    “Eh haka ne fa Uncle Naseer”.

    Murmushi yayi tare da faɗin.

    “Kada kice komai kawai kice Allah yamin Albarka, ya mallaka min ke Insha daɗin zama dake”.

    Shiru tayi tare da ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta.

    Miƙewa yayi daga kan 2 sitter da yake zaune ya dawo gabanta ya zauna aƙasan rock ɗin daya mamaye ɗakin kana cikin narkar da murya yace.

    “Naga yau kina cikin farin ciki?”.

    Kai ta gyaɗa masa tare da cewa.

    “Sosai ma kuwa Uncle Naseer”.

     

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da narkar da murya kana yace.

    “Nima ki sani cikin farin ciki mana”.

    Tana wasa da yatsun hannunta ta ɗago kanta tare da cewa.

    “Toh me kake so in yimaka?”.

    Karyar da murya yayi tare da faɗin.

    “Ki cika min alƙawarin da kika ce zaki yimin, kince sai kinyi shawara nan da kwana biyu amma yau kusan kwana goma kenan da yin maganar mu kullum idan na tambayeki,  sai kice baki yi tunani Ba dan Allah yau dai kiyi min”.

    Cike da farin cikin kammala karatun ta da kuma nasaran data samu ta kallesa tare da cewa.

    “Nayi alƙawari Uncle Naseer duk abinda kake so zanyi maka matuƙar bai saɓawa addinin Musulunci ba”.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da gyara zamansa kana yace.

    “Naji daɗi My Khausi, Khausar ɗina ina sonki My life is nothing without you, you are my World”.

    Kallonsa kawai take Amma batace Komai ba.

    Ahankali ya sanya hannunsa acikin aljihu tare da ciro wani farin ƙyalle fari ƙal yana fitar da wani irin ƙamshi mai masifar hawa kai tare da birkita lissafi, ƙyallen ya miƙa mata ba tare da ta karɓa ba ta tsaida Idanunta akansa kana tace.

    “Wannan kuma na menene?”.

    Langwaɓar da kai yayi tare da cewa.

    “Ki karɓa mana”.

    Girgiza kai tayi tare da faɗin.

    “Toh ka faɗa min na menene sai na karba”.

    Marerece Murya yayi kana yace.

    “Ki karɓa mana zan faɗa miki ai ba dai kinyi al’ƙawari ba?”.

    Kai ta gyaɗa tare da karɓa..

    Murmushi yayi tare da shafa sajensa kana yace.

    “Ki shin shina ƙamshin mana”.

    Kai ta girgiza tare da jan siririn tsaki asaman laɓɓanta kana tace.

    “Haka ma yayi dan inajin ƙanshin yana hawa kai!”.

    Zama ya gyara tare da cewa.

    “Allah ko?”.

    Matsar da ƙyallen tayi daga jikinta saboda irin ƙamshin da yake fitarwa mai masifan hawa kai.

    Anutse ta ɗago manyan Idanunta dake lumshe ta kallesa tare da cewa.

    “Toh Uncle Naseer mai zan maka da wannan ƙyallen?”.

    Matsowa kusa da ita yayi har gwiwan ƙafarsa na taɓa yatsun ƙafa ta cikin wata siga ya karya murya tare da faɗin.

    “Khausar kinyi min al’ƙawari ko?”.

    Kai ta gyaɗa tare da cije lips ɗin ta kana tace.

    “Eh nayi al’ƙawari”.

     

    Ajiyar zuciya ya sauƙe  tare da kallon ƙofan falon kana yace.

    “Kuma na faɗa miki cewa sirrine tsakanin mu dake”.

    Kallon farin ƙyallen tayi tare da juyawa ta kallesa kana tace.

    “Eh nasani”.

    Sauƙe numfashi yayi tare da fesar da iska daga bakinsa kana yace.

    “Sannan kinsan na faɗa miki cewa ci gaban mu ne. Ni dake da kuma  ƴaƴan da zamu haifa?”.

     

    Jinjina kai tayi tare da cewa.

    “Eh nasani ka faɗa min mana”.

     

    Langwaɓar da kai yayi tare da narkar da murya kana yace.

    “Zan faɗa miki amma da farko ina so ki.

    Sirrinta min dan nasan duk duniya babu wanda zan roƙa ya min inba keba”.

     

    Aƙage ta kallesa tare da faɗin.

    “Toh ina jinka ka faɗa min menene?”..

    Kallon fuskarta yayi tare da sakin ajiyar zuciya kana ya sunkuyar da kansa.

    Idanu Khausar ta zuba masa tare da kallon yanda ya sunkuyar da kansa ƙasa sannan tace.

    “Ka faɗa kawai”.

    Ɗago kansa yayi cikin sigar rauni yace.

    “Kinyi al’ƙawari ba zaki faɗawa kowa ba ko?”.

    Jinjina kai tayi tare da cewa.

    “Nayi al’ƙawari bazan faɗa ba”.

    Sauƙe Ajiyar zuciya yayi tare da faɗin.

    “Kin tabbata?”.

    Aƙage ta gyaɗa masa kai batare da tace komai ba dan tagaji da wannan tambayar tasa.

    Iska ya furzar daga bakinsa kana yace.

    “Khausar nasan dai tuntuni kin daɗe da fara period ko?”.

     

    Cikin sauri tayi ƙasa da kanta cike da mamaki da kuma kunyar tambayarsa.

    Ya shafa ƙyeyarsa tare da karyar da murya kana yace.

    “Ya kikayi shiru?”.

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Babu komai”

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da tsira mata idanu kana yace.

    “Ki faɗa min gaskiya tsakanin ki da Allah nasan dai kin daɗe da farawa?”.

    Ƙin cewa komai tayi sai ƙasa data sake yi da kanta.

    “Ki faɗa min gaskiya kiyi haƙuri na haɗa ki da Allah”.

    Still Nan ma shiru tayi Zuciyarta na bugawa.

    Zama ya gyara tare da faɗin.

    “Nasan dai kin fara tabbas”.

    Ataƙaice ta gyaɗa masa kai.

     

    Zare Ido yayi tare da cewa.

    “Yauwa Alhamdulillah

    kin fara period din ko?”.

    Kai ta gyaɗa fuskarta babu walwala tace.

    “Eh”.

    Sajensa ya shafa tare da cewa.

    “Alfarma to nakeso kiyi min”.

    Gyara zamanta tayi tare da  ɗago kanta kana tace.

    “Toh wace iriyar alfarma ce zanyi maka?”.

     

    lumshe idanunsa yayi tare da buɗe su akanta kana yace.

    “Bance ki bani kuɗi ba, ban kuma ce kibani ranki, ko lafiyarki ba, kuma bance ki mallaka min kanki ba, kawai abinda nake so ki sammin Period ɗin ki”.

    Atsorace ta zare Idanunta tare da ɗago kanta kana cike da mamaki tace.

    “In san maka Period Kuma Uncle Naseer? Kamar yaya ban gane ba”.

    Tayi mgnar jikinta na rawa kana ta miƙe cike da tsoro tana ja da baya.

     

    Da sauri ya ɗaga mata hannunsa  cikin sassauta murya yace.

    “Karki manta fa kinyi al’ƙawari zaki sirranta min maganata, kuma shiyasa na faɗa miki dan nasan cewa zaki siririn ta min ki zauna mana kiji”.

    Ya ƙare mgnar yana kuma yin mgnar zuci.

    “Wannan yarinya sirri baya kamata da wuri, duk da ta shaƙi ƙamshin turaren nan amman ga yadda take min gardama”.

    Yayi mgnar cikin ƙoƙon zuciyarsa dan baiyi zaton zata iya musa mishiba.

    Ita kuwa Khsusar kallonsa tayi jikinta na rawa ta girgiza kai tare da faɗin.

    “Toh ai ban fahimci mai kake nufi bane! wannan wace iriyar magana ce?  me hakan yake nufi kenan?”.

    Marerece Murya yayi da alamun damuwa yace. “Dan Allah dan darajar Annabi Muhammad (S.A.W) kiyi shiru kar kuyi magana da ƙarfi kiyi magana ahankali zaki fahimceni”.

    Lokaci ɗaya tashin hankali ya bayyana afuskarta cike da tsoronsa tace.

    “Toh mai zanyi maka?.

    Kai ya langwaɓar tare da karyar da kai tamkar mai shirin fashewa da kuka yace.

    “Nasan kina Period”.

    Cikin fusata da yanayin tsoro tace.

    “Ni ka daina maimaita min wannan maganar”.

    Matsota yayi tare da cewa.

    “Dole in maimaita Miki wannan maganar tunda abinda nake sone kuma kikayi al’ƙawarin zaki yimin!”.

    Girgiza kai tayi still jikinta na rawa tace.

    “A’a ai ko al’ƙawari idan abu yafi ƙarfin ka ba zaka yiba zaka janye sa”.

    Cikin sauri ya kalleta tare da cewa.

    “No baifi ƙarfin kiba Khausar bafa cewa nayi kiyi min komai ba, idan Period ɗinki yazo kika fara kawai zaki ɗauki ƙyallen ne sai kisa shi agabanki madadin kisa Pad Idan yayi awa ɗaya sai ki cire kisa min aleda zanzo in karɓi abuna shine kawai abinda nake so Khausar abinda kaɗai nake sofa”.

    Ya ida maganar cikin yaudara murya tamkar zai fashe da kuka.

    Ya cigaba da cewa.

    “Kuma kada ki manta al’ƙawari kika yimin kuma baifi ƙarfin ki ba sannan ba kanki nace kibani ba”.

    Cike da mamaki take Kallonsa cikin yanayin damuwa da alamun tsoro ta zare Idanunta kana tace.

    “To me zakayi dashi Uncle mai zaka yi dashi wannan wani irin abune?, Wannan wace iriyar magana ce zaka ce min haka Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

    Cikin sauri ya riko tsintsiyar hannunta tare da Marerece fuska kana yace.

    “Ki yiwa Allah da Annabi ki nutsu Khausar kar ki manta cewa kinyi min al’ƙawari.

    Kuma wallahi idan kika faɗawa wani zan miki abinda ba kiyi tsammani ba!”.

     

    Cike da fushi da kuma tsoro tace.

    “Toh me zaka yimin tukunna?”.

    Karyar da murya yayi tare da saurin dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.

    “Zanyi fushi dake”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da sakin murmushi har tayi zaton ko wani mugun abu zai mata tura madaidaicin bakinta tayi tare da cewa.

    “Nidai gaskiya banyi al’ƙawari ba Uncle tsoro nakeji, amma tukunna mai zaka yi dashi?”.

    Ɗan hararanta yayi tare da cewa.

    “Ke dai me ruwanki? Maganin abu zanyi da shi maganine ance sai na samu Period ɗin zanyi maganin?”.

    Kallonsa tayi still zuciyarta na cigaba da tsinkewa tace.

    “Wani irin maganine wannan wanda saida period ɗin mace za’ayi shi?”.

    Wani irin kallo ya watsa mata kafin ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Magani ne kawai nace miki magani zan haɗa amma kamar baki yarda dani ba inada matsala ne ke dai in Zaki yimin in samu lafiya in kuma baza kiyi min ba shikenan dama can aikinsa inada ciwon kai ko?”.

     

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da jinjina kai kana tace.

    “Eh nasani toh shine ake cemin saina samu yanzu idan kika samin a farin ƙyalle, da daddare in zan kwanta ne zangoga shi asaman goshina ance insha Allah daga ranan na rabu da shi kenan”.

     

    Sanyayyar Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da lumshe Idanunta kana tace.

    “Tsakaninka da waye?”.

    Ahankali yace.

    “Tsakanina da Allah Wallahi dagaske na faɗa miki. My Khausi Magani zan haɗa kuma kinsan duk sanda ciwon kan nan ya tashi  kamar zan mutu”.

    Khausar kuwa jinjina kai tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana tace.

    “Toh shikenan  ba damuwa insha Allah zanyi maka”.

    Ta faɗa tare da juyewa ta fice bayan ta dauki ƙyallen.

     

    Tun da Khausar ta koma ɗaki ta rasa meke damunta baki ɗaya ƙamshin ƙyallen na damunta ahankali ta buɗe drawer ta ɗauki leda ta jefa ƙyallen aciki sannan tasake saka wani ledan saida ta ninka masa laida biyar sannan ta fita bakyard ta ajiye sai asannan ta samu nutsuwa baki ɗaya ƙamshin ɗaga mata hankali yake.

     

    Bayan kwana biyu Ya kama yau ne ake sunan Aunty Asiya misalin ƙarfe goma Mommy, Hajiya Bunayya, Amina, Raudat, Ramadan duk suka tafi sunan Aunty Asiya gidan ya rage saura Khausar ita kadai kasancewar. Mommy tace da ita dai idan ta dawo zata je dan kada abar gidan.

     

    Khausar dake zaune a Bedroom ɗin ta tayi saurin miƙewa jin muryan Asma’u afalo  atare Asma’u da Haiydar suka shigo falon da alama daga koyon Machine ya dawo saboda hannunsa dake riƙe da ƙaton L, kwanciya yayi akan 3sitter tare da kunna TV bayan sun gaisa da Asma’u, Khausar kuwa cike da farin ciki ta rungume Asma’u.

    Ahankali Asma’u ta janye jikinta daga na Khausar kana tace.

    “Ya naji gidan shiru kamar ba kowa?”.

    Kai Khausar ta jinjina cikin sanyin murya da alamun damuwa atare da ita tace.

    “Eh babu kowa sunje gidan Aunty Asiya yau sunanta, nima so nake inyi wanka sai Inje in duba su. Mommy nake jira baya ga haka ma jikina duk amace yake”.

    Ta ida maganar lokacin da suka shiga ɗakin ƙaramin fridge dake ɗakin Khausar ta buɗe tare da ciro Friut ta ɗauki Plate akai ta zuba mata kana ta ajiye mata agabanta.

     

    Cike da kulawa Asma’u tace.

    “Khausar ya dai na ganki Asanyaye kamar akwai abinda ke damunki?”.

    Girgiza kai Khausar tayi tare da cewa.

    “Babu komai Asma’u kici Fruit”.

    Kallonta Asma’u tayi tare da girgiza kai kana tace.

    “A’a Taya zan sha Friut baki faɗa min abinda ke damunki ba?”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da faɗin.

    “Wallahi Asma’u wani Abu ke damuna, yake kuma bani tsoro nasha faɗa miki al’amarin Uncle Naseer.

    Yana bani tsoro kince ba haka ba ko to kinji abinda ya faɗa min kwanaki”.

    Atake ta kwashe dukan yanda sukayi da Naseer ta faɗa mata“.

    Atsorace Asma’u ta dafe ƙirjinta tare da cewa.

    “Kai Khausar kada ki yarda ki sanya Period ɗinki akan wannan ƙyallen ki bashi muka san mai zaiyi dashi  ke har kin yarda dashi”.

    Girgiza kai Khausar tayi cike da damuwa ta langwaɓar da kai kana tace.

    “Nasan yana da ciwon kai, amma baki ɗaya ban yarda cewa maganin ciwon kai zaiyi dashi ba”.

    Ajiyar zuciya Asma’u ta sauƙe kana tace.

    “Gaskiya kar ki yarda ki kiyaye”.

    Cike da damuwa Khausar tace.

    “Toh yanzu ya zamuyi?”.

    Gyara zama Asma’u tayi tare da faɗin.

    “Gaskiya dai kam Khausar kada ki yarda kisa jininki akan wannan ƙyallen, hakan ma bazai yuba mukasan me yake nufi dashi, kika san me zaije ya aikata dashi ai haka baza ta yuba?”.

    Lumshe idanu Khausar tayi kana tace.

    “Toh shikenan ai dama bazan saba”.

    Mommy ce tashigo tare da ɗaga labulen bayan tayi sallama.

    Amsawa suka yi kana cike da ladabi Asma’u ta gaishe da Mommy.

    Cikin sakin fuska Mommy ta amsa tare da tambayarta yasu Umminta.

     

    Kallon Khausar Mommy tayi tare da cewa.

    “Khausar ki ɗauki Plate da Spoon ki Kai gidan Aunty Asiya”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da cewa.

    “Toh”,Juyawa Mommy tayi ta fice.

    Miƙewa Khausar tayi tare da cewa.

    “Asma’u muje ki rakani”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa tare da miƙewa direct kichen ta nufa ta tare da ɗaukar Plate da Spoon suka fita kai tsaye gidan Aunty Asiya suka nufa.

     

    Ahankali Asma’u ta zubawa raguna biyu dake rataye a coumpund ɗin ido, da alama na suna ne duk angama gyarasu  an cire kayan cikinsu ana jiran su tsantsame.

    Har suka shiga cikin gidan suka kai Plate ɗin baki ɗaya hankalin Asma’u na kan ragunan dake coumpund ɗin bayan sun fito Asma’u ta kalli ragunan cikin sanyin murya ta kalli Khausar tare da cewa.

    “Khausar ga dama ta samufa”.

    Da sauri Khausar tace.

    “Wacce damar”.

    Cikin yin ƙasa da murya Asma’u tace.

    “Dauko ƙyallen nan zamuyi muzo musaka jinin wuyan ragon nan”.

    Jinjina kai Khausar tayi cike da gamsuwa tace.

    “Ƙwarai kuwa Asma’u muje mu ɗauka”.

    Cikin sauri suka fice cikin sa’a koda suka shiga basu samu Mommy a falon ba tana toilet. Haiydar kuwa baya nan kai tsaye backyard suka nufa Khausar ta ɗauki ƙyallen a inda ta ajiye sannan ta since.

    Da sauri Asma’u ta kawar da kanta gefe jin yanda ƙamshin jiki ya bugeta.

    Cikin ya mutse fuska tace.

    “Kai Wannan wani irin ƙamshine mai tada hankali ba daɗin ji”.

    Baki Khausar ta taɓe kana tace.

    “Hmm nima dai haka naji”.

    Ahankali suka juya suka fita kai tsaye gidan sunan suka nufa Baba Mai gadi dake zaune yace da.

    “Hajiya Khausar ya gida?sai yanzu kika leƙo?.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “A’a ɗazu ma nazo bamu ganka bane”.

    Kai ya jinjina tare da cewa.

    “Ayyah wataƙil na zagaya ne”.

    Cikin sa’a babu kowa a coumpund ɗin kallon Khausar Asma’u tayi cikin ƙasa da murya tace.

    “Kinga mai gadi na kallonmu sai munje dai-dai wajen ragon zan durƙusa kamar takalmina ya tsinke ke kuma saikiyi saurin daddalan jinin ajiki”.

    Kai Khausar ya gyaɗa suna isa wajen Asma’u ta tsugunna tana taɓa ƙafarta.

    Khausar kuwa cikin sauri ta matsa jikin ragunan ta ciro ƙyallen cikin leda sannan ta manna ƙyallen ajikin wuyan ragon dake ɗigar da jini kaɗan-kaɗan sannan ta sake dan dala tayi haka har sau uku ajikin wuyan ragon cikin sauri tace.

    “Asamu’u nayi mu tafi”.

    Miƙewa Asma’u tayi suka nufi ƙofa,Baba mai gadi yace.

    “Ya dai Asma’u ta kalmin tsinkewa yayi ya kuka tafi baku shiga ba?”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da cewa.

    “A’a kawai dai na ɗan gurɗene naji ƙafar na yimin ciwo sannan mun manta ɗauko abinda Mommy ta aiko mu mukawo”.

    Daga haka suka fice daga gidan.

    Kai Baba ma gadin ya jinjina musu,

    Tare  da juyowa, cikin gidan,

    Wani irin zazzaro idanu waje yayi cike da tsanani tsoro da mamaki Baba Mai gadi ya buɗe baki da ido da hanci duka gani, cikin raguna biyu dake rataye ɗaya ya ɓace ɓat……!

     

     

     

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276,*

     

     

     

     

    *By*

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 30

    Sakayyah 30

     

    *Littafin SAKAYYAH dai na kuɗi ne ba free book bane 1k ne kacal ki biya ki karanta cikin Aminci kada ki karanta na sata na Allah ya isa. 0661110179 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 sai in saki a Group ɗina*

     

     

    Cappande. Acikin tafin hannunsa ya ɗebo sulallan Gwal ɗin da wasu yan guntu-guntun sanduna tare da birbiɗin yashin kana ya shiga jujjuyasu, ahankali ya maida kallonsa kan Innayi data gyaɗa masa kai alamar ya fito dasu hannunsa ya zura acikin tukunyar yashiga kalato salullan wanda na ainihin Gwalne aƙalla sun kai guda ashirin, karkaɗe yashin yayi tare da fitowa dasu kana ya ɗaura su akan rigarsa tare da gyara zaman sa abakin ramin ya tsura mata Ido Innayi ma ido ta zuba masa ganin yanda ya zauna yasa tashiga maida yashin ta rufe ramin kana ta sanya duwatsun ta rufe tare da tura fantekar kan ramin kallon Moddibo dake binta da kallo tayi kana tace.

    “Ɗaura min randan nan akai”.

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe still Idanunsa na Kanta cikin sanyin murya yace.

    “Innayi wannan kamar Gwal?”.

    Kai ta gyaɗa masa kana tace.

    “Eh Gwal ne”

    Still ba tare daya motsa ba ya sake kallon Gwal ɗin kana yace.

    “Ina kika same su Innayi?”.

    Girgiza masa kai tayi kana tace.

    “Wannan ba lokacin tambayar ina nasamu gwala-gwalai bane. Moddibo lokacine daya kamata ace ka lissafa su muga adadin su kana musan nawa za’a samu mu haɗa mu karɓo Jameelu yanzu tashi mubar wajen nan mushiga ɗaki kaga dare ya tsala”.

     

    Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

    “Toh”,Kana yabi bayanta tare da tsira mata idanu cike da ɗumbin mamaki tare da tarin tuhuma ahankali ya sake kallon sulallan Gwal ɗin dake haɗe da waɗanan sanduna guntaye aciki asaman laɓɓansa yayi sallama tare da shiga ɗaki.

    Wutan ɗakin Innayi ta kunna Atake haske ya zagaye ɗakin bayan Moddibo ta ratsa tare da rufe kofar ɗakin kana ta dawo kusa dashi ta tsaya  tare da sanya hannunta ta tsistsince ƴan guntulayen sandar ta shiga haɗawa kasancewar akwai wajen haɗawa ajiki Moddibo kuwa Idanu ya zuba mata cike da mamaki.

    tana cigaba da haɗawa ga mamakinsa sai yaga ya zama sanda irin wanda manyan Limamai ke riƙe wa suna tafiya dashi sanda ce mai masifar kyau da tsari wacce da ka gani kasan mai tsadace.

     

    Kallonsa Innayi tayi tare da cewa.

    “Wannan sanda ce samansa inda ake riƙewa ne kaɗai keda Gwal sai kuma ƙasan sa inda ake dogara wa amma wannan bazan baka shiba saboda ba zaiyi daraja sosai ba. Saboda ahaɗe yake da sanda kana sandar kuma bazan siyar ba, sulallan dai zaka haɗa ka duba sai dai sunzo mana alokacin da bashine ba saboda sulallan baki ɗaya sun ƙare”.

    Ido kawai Moddibo ya zuba mata still da shock atare dashi.

    Innayi ta cigaba da cewa.

    “Baki ɗaya nauyin karatunka.

    Cin mu, shan mu, suturar mu, tun kana ƙarami da duk wani abinda ya kama  su nake ɗauka in siyarwa Alhaji Hashim mai sayan gwala-gwalai shiyasan farashin sulallan duk yanda suke zan faɗa masa adadin da suke yazo ya siya muyi lissafi muga nawa za’a samu”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh shikenan”.Yayi mgnar tare da lumshe idanunsa, baki ɗaya damuwarsa asamu kuɗin bawai tunaninsa ya tambayi ina tasamu gwala-gwalan nan ba sannan bashida kuzarin da zai iya tambayar ta, sandar na menene, kana bashi da ƙarfin zuciyar jin mai yasa baza asayar da sandar ba, ayanzu burinsa bai wuce asamu ahaɗa kuɗaɗen akarɓo J ba.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kallon Innayi kana yace.

    “Toh zan tafi dasu ɗakina”.

    Kai ta gyaɗa masa kana ya miƙe ya fita yana jin confidence da farin ciki yasan Gwal nada daraja duk da cewa ƴan ƙananun sulallane amma yasan da izinin Ubangiji zasuyi daraja.

     

    Acan gidan Abba kuwa bayan tafiyar Moddibo Hajiya Karima ta kalli Abba daya zurfafa acikin tunani kana ta ɗan ya mutse Fuska tace.

    “Alhji wai yanzu baza ka sake ƙara neman ragi ba? yanzu sai ka ɗauki Million ɗari da hamsin ka basu mai kake tunanin zai faru gaba idan sunji daɗi za’a sake ɗaukan ƴaƴanka ne fa!”.

    Anutse Abba ya ɗago kansa tare da kallonta kana cikin sanyin Murya yace.

    “Karima to me kike tunani?”.

    Ba yabo ba fallasa tace.

    “Ka nemi ragi”.

    furzar da iska mai zafi yayi still Idanunsa na kanta kana yace.

    “Karima kamar baki ji me yace ba, cewa fa yayi muddin aka nemi ragi akan rayuwar Jameel”.

     

    Cikin sauri tace.

    “Bafa za’a kashe Jameel ba, kawai Alhj idan zaka nemi ragi ka nemi ragi, sai kace baka sha zafin neman kuɗin ba zaka ɗauka agabtale ka basu kamar ba kasan darajar suba, amma babu yanda zaka ɗauki wannan maƙudan kuɗin ka bayar akan Jameelu!”.

     

    Cike da mamaki Abba ya kalleta kana cikin ɗaga sautin murya yace.

    “Karima to idan ban bada kuɗi akan Jameelu ba akan wa kike so in bayar? Shin Karima anya Karima?”.

    Wani irin kallo ta masa kana cikin sauri tace.

    “Anya me?”.

    Dai-dai lokacin Hajiya Turai ta shigo baki ɗaya ta hargitse babu walwala afuskarta ta kalli Hajiya Karima kana tace.

    “Ai dai kam abin nata da mamaki, idan bai ɗauki kuɗi ya bayar akan Jameelu ba akan wa kike so ya bayar?”.

    Sai kuma ta maida kallonta kan Abba da idanunsa ke lumshe kana tace.

    “Aini Alhj naga ƙoƙarin ku ma da har kuka iya neman ragin da suka rage muku, kuma ai sunyi ƙoƙari ni dai anawa tunanin kada ku kuskura kada ku sake yin batun ragin wasu kuɗin, suje su kashe mana yaro abanza idan aka kashesa mai son sa keda asara wanda bai sonsa kuma bai damu ba”.

    Ta ida maganar hawaye na ciko kwarmin Idanunta.

     

    Hajiya Karima kuwa wani kallo ta watsa wa Hajiya Turai tare da cewa.

    “To mekike nufi?”.

    Taɓe baki Hajiya Turai tayi kana tace.

    “To ai gaskiya ne duk mai son Jameelu ba zai so ace za’a sake neman ragi ba”.

    Taɓe baki Hajiya Karima tayi tare da watsa mata kallon banza kana tace.

    “Kenan kina nufin Ni bana son Jameelu?”.

    Hannu Hajiya Turai ta buɗe kana tace.

    “A’a wannan ke ki kafaɗa da bakin ki amma dai shawaran da kika kawo ba shawara me kyau bace”.

    Hannu Abba ya ɗaga musu tare da kallon Hajiya Karima dake kumfar baki kana yace.

    “Bana son hayaniya ya isheku.

    Dan Allah kubarni inji da abinda ke damuna”.

    Kai Hajiya Turai ta gyaɗa tare da tsuke bakinta alamun itama ba hayaniyar take soba.

    Cikin sanyi ta kalli Abba tare da cewa.

    “Alhj ga Million biyu a Account ɗina zan bayar ahaɗa”.

    Wani shegen kallo Hajiya Karima tabi Hajiya Turai dashi kana cikin taɓe baki tace.

    “Hmmm munafurci dai da neman gindin zama haddasu kaza acikin cin danƙo”.

    Cikin sanyi Abba yace.

    “Nagode Turai Allah ya saka da alkhairi ayanzu kyauta koda na Naira biyar aka bani ita ina buƙatar ta, xansa acikin tumunin kudin da za’a karɓo Jameel”.

    Cikin sauri Hajiya Karima tace.

    “Nima Allah ya bani in bayar”.

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Ameen”.

    Juyawa tayi ta fice Hajiya Turai kuma ta zauna gefensa tana sake tausansa.

     

    Acikin kwanaki biyu Moddibo ya saida gwala-gwalan da kuma motocinsa dana M Jameel Yayi total ɗin  kuɗin sun kama Million ashirin da biyar ya turawa Abba cikin account ɗin sa Alhamdulillah yanzu akwai Million casa’in da biyar acikin account ɗin Abba Aɓangaren Abban ma yana cigaba da fafutuka ganin ya samu kuɗi.

    Acikin kwanakin baki ɗaya abubuwa sun kankama baki ɗaya sun sake maida hankalinsu kan neman kuɗin suga sun samu sun haɗa yau ya kama kwanan M Jameel goma kenan awajen Kidnappers din kana yau kwana biyu rabon Abba da Moddibo suyi waya da M Jameel Misalin huɗu na yamma Moddibo ya bar gidan Abba ya nufi gidansu bayan sun sake tattauna wa.

     

    Acan ɓangaren Boka Kar’uzu kuwa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce gurfane agabansa cikin wata sandararriyar murya Boka Kar’uzu ya kece da wata mahaukaciyar dariya tare da jujjuya gashin dake wangamemen tafi  hannunsa kana ya ɗago kansa tare da Kallon Hajiya Bunayya da jajayen Idanunsa da suka tara kwantsa yace.

    “Kin tabbatar gashin yaron ne dai ko?”.

    Cike da ƙwarin gwiwa Hajiya Bunayya ta jinjina masa kai tare da faɗin.

    “Tabbas na tabbatar Boka Kar’uzu Uban bokaye La’anannen Uban La’anannu Mugu Uban mugaye tsinanne Uban tsinannun wannan gashin kan Ramadan ne domin dana shafa  turare  na shafa kansa  bayan na fita naga gashi ya manne ahannu shine na tattare na kawo maka kamar yadda ka umarceni.

    Wata mahaukaciyar dariya. Boka Kar’uzu ya sheƙe dashi wanda yasa bukkan da suke ciki ya hau girgiza cike da jin daɗin kirarin data masa yace.

    “Hhhhh magana ta ƙare Ƙaramar la’ananniya me kafirar zuciya aiki ya riga yayi anwuce babinsa saura na Babban”.

     

    Girgiza kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

    “Agama da batun Ramadan ɗin kafin ayi na Haiydar to babu matsala wannan ba damuwa bace”.

    Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe kana tace.

    “Ni kuma Boka yanzu Abban Samira na nan amma nanda sati biyu masu zuwa zai tafi aikin Umrah, shiyasa nayi shiru da batun zuwan Samira nan  mu bari sai mahaifinta ya tafi  kaga ba kowa agida da banaso daga gidan Hajiya Bunayya arika zuwa ana daukan ta saboda sa idanawa. Amma Alhj na tafiya  idan ya kama ma ta dawo gidan ka idan kuma kaine ma zaka rinƙa kwana idan gari ya waye ka dawo to duk daya”.

    Wata dariya mai masifar ƙara Boka Kar’uzu ya kece dashi kana buga ƙafarsa na hagu wanda baki daya ƙura ta buke wajen kana yace.

    “Hhhhh saishi Boka Kar’uzu Uban bokaye La’anannen Uban La’anannu Mugu Uban mugaye tsinanne Uban tsinannun shaiɗani Uban shaiɗanu babu wata matsala da zaran ya tafi zan zo Ni da kaina dan zamu fi sakewa agidan naku acan ma zan tare in ragargaji sabon budurci”.

    Kai Hajiya Lami ta gyaɗa tana murmushi kana tace.

    “Yanda kake so haka za’ayi”.

    Daga nan suka miƙe suka fita ta baya kamar yanda suka shigo suka nufi gida ransu fari soll musamman Hajiya Bunayya.

     

    Acan ɓangaren Khausar kuwa sanye ta fito cikin hijabi maroon mai facemaks kafadarta rataye da jaka fari sol jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin turaren Oud Ma’aruf cikin yanayin sanyin ta da tun ɓatan M Jameel bata dawo dai-dai ba ta kalli Mommy dake zaune kan 2sitter kana tace.

    “Mommy zan tafi”.

    Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

    “To kice ina gaida Ummi”.

    Kai Khausar ta gyaɗa cike da nutsuwa ta fita tare da sanya Platshoe fari Anutse ta nufi coumpund ɗin dai-dai lokacin da Amina da Uncle Naseer suka shigo hannunsu sarƙafe da juna kallo ɗaya Khausar ta musu ta kawar da kanta gefe kana ta lumshe Idanunta.

     

    Ido Uncle Naseer ya zuba mata tare da shafa kansa kana cikin sakin fuska yace.

    “A’a Khausi ina zuwa da yamma nan?”.

    Batare data sake kallon inda suke ba kana cikin sanyin murya tace.

    “Zanje gidan su Asma’u ne”.

    Langwaɓar da kai yayi kana yace.

    “Ai haka dai maganar bata haɗa muba Khausar, ashe wai Malam Jameel aka sace Agaskiya garin nan ya fara bada tsoro bari muje na kaiki in jajantawa Ummi”.

     

    Girgiza kai Khausar tayi kana tace.

    “A’a kabari kawai”.

    Cikin sauri Amina ta watsawa Khausar harara kana ta maida kallonta kan Uncle Naseer Shima ta hararesa.

    Uncle Naseer kuwa ganin kallon da Amina ke jifansu dashi yasa ya ware idonsa tare da sakar mata da lallausan murmushi kana yace.

    “Ohh Baby Colm down mu nayin Auren mu zan ɗauke ki mu gudu mubar ƙasar nan, kafin muma Akinnafemu tunda kinga anfara tsincr ƴaƴan masu kuɗi an ɗauke Malam Jameel next target ɗin su ni za’a ce za’a saɓe ko ke, kafin ma su ankara zamu gudu abinmu.

    Dariya Amina ta ƙyalƙyale dashi tare da manna kanta ajikin damtsen hannunsa.

    Khausar kuwa cikin sauri ta kawar da kanta gefe tare da lumshe Idanunta.

    Ahankali Uncle Naseer ya ɗago kansa tare da tsura wa Khausar Ido tabbas soyayyanta acikin jininsa yake har yau har gobe zuciyarsa na muradin Khausar, itace burinsa Kawai zai Auri Amina ne domin cikar Burinsa amma Khausar itace muradinsa.

     

    fesar da iska mai sanyi yayi yana jin wani irin yanayi agame da ita kana yace.

    “Khausi jirani in ɗauko sakon Uwaniyona inzo in kaiki?”.

    Da sauri Amina ta janye kanta dake manne adantsensa kana tace.

    “Ka kaita kuma?”.

    Kai ya gyaɗa tare da yimata raɗa akunne yace.

    “Yes My dear wife ai jaje ne”.

    Ashagwaɓe ta girgiza kai tare da cewa.

    “Gaskiya Ni dai Uncle Naseer bana so ka tafi ka barni”.

    Shafa fuskarta yayi kana yace.

    “Bafa daɗewa zanyi ba”.

    Khausar kuwa cike da takaicin abinda sukeyi tace.

    “A’a Uncle Naseer ka bari ganan Haiydar ma zai kaini da mashin ɗinsa”.

    Kai ya gyaɗa still Idanunsa na kanta yace.

    “Ok”.

    Dai-dai lokacin Haiydar ya fito daga sashen Abbansu hannunsa riƙe da key mashin dinsa.

    Kallon Uncle Naseer da Haiydar yayi da murmushi afuskarsa yace.

    “Uncle Naseer yau dai Addah Khausy ta yarda in jata amashin ɗina”.

    Cikin alamun so Naseer yace.

    “To ayi a hankali dai banda fifita”.

    Dariya Haiydar yayi tare da cewa.

    “Uhmm aikam zata sha fifita”.

    Murmushi Uncle Naseer yayi tare da cewa.

    “Dan Allah ka jata ahankali kada kayi mana asara”.

    lumshe Idanunta tayi baki ɗaya bata da wani kuzari ɓatan M Jameel yayi masifar ratsata hakan yasa ko magana bata fiye yiba daga Um-sai Um-um.

    Haiydar kuwa mashin ya ɗauko tare da ɗaukar ta suka fice kana Amina da Uncle Naseer suka shiga ciki.

     

    Haiydar na isa kofar gidan Ummi yayi Parking ahankali Khausar ta sauƙa tana gyara zaman hijabinta kana atare suka shiga cikin Falon Ummi bakinsu ɗauke da Sallama.

    Ummi dake zaune riƙe da carbi ahannunta Asma’u da Bashir na zaune gefenta suka Amsa Sallamar.

    Cike da ladabi Haiydar ya gaisheta tare da sake yi mata jaje kana suka gaisa da Bashir tukunna suka fice atare.

    Khausar kuwa cike da sanyin tace.

    “Ummi ki kwantar da hankalin ki insha Allah yaya Jameel zai bayyana babu abinda zai sameshi da izinin Ubangiji addu’a mu bazai tafi abanza ba”.

    Jinjina kai Ummi tayi cikin yanayinta kamar mara lafiya tace.

    “Ameen ya Allah”.

    Cikin sanyin murya Asma’u da Muryanta ya dishe da kuka tace.

    “Babbar matsalar mu yau kwana biyu kenan Basu sake kira ba gashi baki ɗaya kuɗin Million Casa’in da biyar aka samu aka haɗa”.

    Kallonta Khausar tayi tana cire hijabinta tace.

    “Haka dai kika cemin jiya har yanzu kuɗin basu haɗuba”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa mata kana tace.

    “Basu haɗu ba Khausar damuwar dake damunmu kenan wlh, baki ɗaya hankalinmu ya kasa kwanciya sai dai Yah Modibbo yace Abba ya nemi bashin banki amman sunce yau ko gobe zai samu kuɗin”.

    Cikin sanyin murya Khausar tace.

    “Insha Allah kuɗin zasu haɗu da izinin Ubangiji Allah ya karesa ya tsare lafiyarsa”.

    Atare suka amsa da Ameen.

    Shiru Khausar tayi tare da tallafe kuncinta kana ta kalli Ummi da Asma’u sai kuma ta fesar da numfashi kana buɗe jakarta tare da kwaso ƴan kunnaye da sarƙa da kuma zobe kala biyu da alamun nata dana Mommy ne,  hannun Ummi ta kama tasasu a ciki kana ta rufe hannun Ummin tare da cewa.

    “Gashi inji Mommy na, tace Dan girman Allah da Manzonsa kada ki ƙi karba Ummi dan Allah kada kice komai a saidashi a haɗa kuɗin.

    Cikin tsananin jin dadi Ummi ta kalli girman Gwal ɗin musamman na Mommy wanda a ƙalla shi kadai zai iya kai one Million da yan ɗori.

    Hawaye na tsiyayo mata tace.

    “Bazan ƙiba Khausar kicewa Mommynki ngd matuƙa ubanji yayi mata sakayya da gidan al’janna mai girma”.

    Cikin sanyi duk suka amsa da Amin.

    Cikin sanyi Khausar ta fesar da numfashin kana a hankali tace.

    “Amma Ummi Meyesa ba asa Police acikin maganar ba?”.

    Cikin raunin murya Ummi tace.

    “Sunce muddin Akasa police acikin maganar to abakin ransa”.

    Cikin sauri ta dafe ƙirjinta tare da cewa.

    “Innalillahi  akan ransa kuma?”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa Tare da cewa.

    “Kuma batun kuɗi ma da suka ce da farko Million ɗari biyu sukace yanzu ya zama Million ɗari da hamsin saboda ragin da aka nema to yanzu sunce muddin aka sake neman ragi akan ransa”.

    Aruɗe Khausar ta rintse Idanunta tare da cewa.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

    Sai kuma ta juya tare da kallon Ummi cikin sanyin murya tace.

    “Ummi kinsan wani abu?”.

    Kai Ummi ta girgiza kana tace.

    “A’a”.

    Lumshe idanu Khausar tayi tare da cewa.

    “Ummi ranan da Yah Jameel ya mai dani gida da muna tafiya munga wata mota tana ta binmu abaya”.

    Sai kuma tayi shiru alamar tunani ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “Ummi shine fa dama nace da za’a faɗawa hukuma zan iya bada number Motar saboda na zargi motar duk inda mukayi motar na biye damu wataƙil da hukuma zasu shiga za’a iya kama wa anda suka sace Yah Jameel, domin tun fitar mu motar ke bibiyanmu har saida muka kusa gidanmu suka daina binmu”.

    Cike da mamaki Asma’u tace.

    “Kai Khausar?”.

    Kallonta Khausar tayi tare da gyaɗa mata kai kana tace.

    “Wallahi kuwa Asma’u amma lokacin bamu kawo komai aranmu ba shima kuma Malam Jameel Bai kawo komai ransa ba”.

    Girgiza kai Ummi tayi kana tace.

    “Toh ya zamuyi idan an faɗa zai zama matsala zasu kashesa tunda sunce basu yarda afaɗa wa hukuma ba shiyasa dole muyi hakuri”.

    Jinjina kai Khausar tayi kana cikin sanyin murya tace.

    “Toh shikenan Ummi Insha Allah zamu cigaba da yiwa Yah Jameel Addu’o’i Allah ya bayyana shi”.

    Jingina kai Ummu tayi tare da cewa.

    “Yawwa shine abinda ya dace Allah yabamu Sa’a”.

     

    Wunin wannan ranan haka Khausar tayi ta rarrashin Asma’u da Ummi kana tana sake basu ƙwarin gwiwa kan cewa da izinin Ubangiji M Jameel zai dawo bayan Sallar sala’sar ta koma gida tana isa gida daga bakin.

    Barandarsu ta jiyo sautin kukan Ramadan cikin sauri ta cire takalminta tare da shiga falon bakinta ɗauke da Sallama.

    Cike da damuwa ta sauƙe Idanunta akan Ramadan daya kifa kansa kan cinyar Mommy cikin rauni da raɗaɗin ciwo yake jujjuya kansa akan cinyar Mommy kana yana cewa.

    “Mommy Kaina ciwo!,Mommy Kaina zai fashe!”.

    Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe Cike da damuwa tace.

    “Subhanallah Ramadan yau tun safe kake ta cemin kanka na ciwo to meke faruwa ne na baka magani kasha abanza ko dai in kira Abbanka ne akai ka asibiti?”.

    Cikin tsanananin ciwo ya Girgiza mata kai yayi kana cikin Muryan kuka yace.

    “Mommy ni dai Banason allura aƙara min magani kar kaina ya fashe”.

    Khausar kuwa cikin sauri ta cire hijabinta kana ta ƙara sa kusa dashi tare da ɗaura tafin hannunta akan goshinsa lokaci ɗaya zafi ya ratsa tafin hannunta har ƙananan jijiyoyin kansa sun tashi suna harbawa cikin sauri ta kalli idanunsa gani tayi sun kaɗa suyi jawur dasu kana yanayin su ya koma kamar ajuye.

     

    Saurin kallon Mommy dake jera masa sannu tayi kana tace.

    “Subhanallah gaskiya Mommy akaishi Asibiti”.

    Cikin sanyin murya Mommy ta kalli Ramadan dake ta juyi kana ta kalli Khausar dake cikin damuwa ta fesar da numfashi tare da cewa.

    “Nima nace aikai shi asibiti amma yace baya Son allura da zaran nace akaisa saiya sa kuka”.

    Girgiza kai Khausar tayi kana ta sake shafa goshinsa da yayi masifar zafi cike da damuwa tace.

    “Mommy yaushe za’a biye masa jifa yanda kansa yayi zafi kamar wuta”.

    Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

    “Bari akwai maganin da Abbanku yace zai sayo masa yanzu bari idan ya kawo za’a bashi idan Allah yasa ya samu sauƙi shikenan idan kuma abin be lafa ba dole sai mutafi asibitin”.

    Jinjina kai Khausar tayi tare da cewa.

    “Toh shikenan Allah ya bashi lafiya Allah kuma ya dawo da Abba lafiya”.

    Mommy na shafa kan Ramadan tace.

    “Ameen”.

     

    Acan ɓangaren Abban Jameel kuwa ahankali ya miƙe tare da kallon wayarsa kana ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da nufar toilet domin ya watsa ruwa baki daya baya jin daɗin jikinsa bakinsa ɗauke da addu’a ya shiga toilet din kana ya fara wanka.

    Hajiya Karima dake zaune afalon kasancewar itace da girki tayi saurin kallon wayar Abba dake ruri miƙewa tayi tare da isa kan 3sitter ganin number babu suna yasa tayi saurin picking tare da kaiwa kunnenta tace.

    “Assalamu Alaikum”.

    Ba tare da mutumin ya amsa Sallamar taba yace.

    “Ina Mahaifin Jameelu?”.

    Da sauri ta gyara zaman wayar akunnenta tare da cewa.

    “Me kuke so ku faɗa min nice mahaifiyarsa”.

    Cike da gadara Mutumin  yayi gyaran murya kana yace.

    “Dashi muke son magana, muna son muji shin kuɗin mu sun haɗu ne?.

    Zamu faɗa masa inda za’a ajiye kuɗin sannan kuma da inda za’a zo akarɓi Jameel”.

    Hajiya Karima kuwa cikin ƙasa da murya tace.

    “Haba bayin Allah kuji tsoron Allah mana.

    Yanzu fisabilillah ina zamu samu Million ɗari da hamsin wannan aiba rayuwa bane duk da cewa Mahaifinsa mai kuɗi ne ina zai samu wannan uban kuɗin acikin ƙaramin lokaci kawai dai ku temaka ku rage idan ku akayi wa haka ya zakuji? Gwara dai ana rage mugunta”.

    Dai-dai lokacin da Abba ya fito daga wankan batare daya gama ba jin alamar muryan Hajiya Karima na magana ƙasa².

    Yana fitowa ya Fisge wayar ahannunta tare da mannawa akunnensa dai-dai lokacin da mutumin ke magana cikin tsanananin fushi da gadara yace.

    “Ok haka ma kuka ce. Wato wasa da mu ku keyi kun maida mu bamusan abinda muke ba, toh Insha Allah daga yau har gaban Abadan baza mu sake kiran kuba. Alhj Bashir ya maka kyau duk irin halarcin da gargaɗin da muka maka baka jiba har kuna sake neman ragi”.

     

    Cikin tsanananin kaɗuwa, ruɗu, da tashin hankali. Abba ya girgiza kai kana cikin raunin murya yace.

    “Dan Allah da m…”.

    Kafin ya ƙarasa yaji ɗit-ɗit-ɗit alamar sun kashe kiran.

    Cikin wani irin yanayi ya zauna tare da sake kiran layin yaji akashe Aruɗe ya shiga fito da sauran numbers din su yana kira amma baki ɗaya Switch off.

    Kansa ya dafe da hannunsa na dama yayin da hannunsa na hagu ke riƙe da wayar.

    Cikin wani irin fushi ya miƙe tare da kallon Hajiya Karima dake tsaye azabure ya ɗaga hannunsa tare da kife ta da mari kana ya sake watsa mata wani gigitaccen marin da saida taga gilmawar taurari cikin wani irin fushi ya cigaba da yarfa mata maruka gefen hagunta da damanta.

    Muryarsa na rawa yace.

    “Karima na saki acikin wannan maganar tunda aka fara. Meyesa zaki ɗauka min waya. Karima kin cuceni. Wallahi Karima duk wani abinda ya faru da Jameelu kece sanadi kece kika ja ke kika cutar min da rayuwar ɗana”.

    Da sauri ya dafe ƙirjinsa dake wani irin zafi kana ya ɗago ya kalleta da idanunsa da suka sauya launi zuwa tsantsar tashin hankali kana yace.

    “Karima haka nayi dake kina gani ɗazu akan idonki na dawo daga Taraba naje na karamo kuɗi na sake karɓan bashin banki 50 millons yanzu ruwan kuɗi ahannuna Million Ɗari da arba’in da biyar ne Million biyar  ne kaɗai ya rage kuma nasan da izinin Ubangiji ba zasu gagara ba zan nemosu amman shine zaki nema min ragi”.

    Hajiya Karima kuwa kuncinta ta dafe tare da sun kuyar da kanta ƙasa tana mai cike da taraddadi.

     

    Cikin rauni da fusata Abba ya cigaba da cewa.

    “Saboda bake kika haifi min Jameelu ba shine zaki salwantar da rayuwarsa, yanzu da ɗan da kika haifa a cikin kine zaki masa irin wannan abin? Karima kin cutar da rayuwata cuta mafi muni, muddin wani mummunan abu ya faru da Jameelu na bazan taɓa yafe miki ba”.

    Cikin zubda hawaye Hajiya Karima tace.

    “Haba Alhj wallahi ni ba haka nake nufi ba, kafahimceni tunda naga wancan karon ma da aka nemi ragin ai sun rage shiyasa nace barin ne mamaka sauƙi”.

    Dai-dai lokacin Moddibo ya shigo falon idanunsa suka sauƙa akan Abba da jikinsa ke rawa idanunsa sunyi Jawur tamkar zai tsats-tsafo da hawayen jini yayin da numfashinsa ke seizing.

     

    Cikin sauri Moddibo ya ƙara sa tare da riƙe Abba kana ya zaunar dashi akan kujera cikin sanyin murya yace.

    “Abba mai ya faru?”.

    Kasa cewa komai Abba yayi baki ɗaya baya cikin hayyacinsa numfashinsa sai kai koma yake cikin rauni da ficewar hayyaci yace.

    “Karima kin cuceni Meyesa zaki min haka. Meyesa zaki ƙuntata min ta wannan hanyar!?”.

    Cikin sauri Hajiya Turai ta shigo ganin halin da Abba ke ciki yasa kai tsaye ta wuce Bedroom ɗinsa tare da ɗauko masa magani kana ta kira Dr Muktar ya ɗagawa tace.

    “Dan Allah Dr maza kazo jikin Alhj ya tashi gaba ɗaya ma numfashinsa sama yake yi”.

    Da Ok Dr ya Amsa kana ta katse kiran tare da fitowa da magani ta ɓare tare da miƙa masa.

    Cikin azabebben rawan da jikinsa keyi ya ture hannunta tare da cewa.

    “Ba zan shaba Karima kin cuceni kin cutar da rayuwata, kin datse min farin cikina. Meyesa haka Karima duk abinda ya samu Jameelu Karima kece sanadi idan wani abu ya samu Jameelu Karima kece sanadi!”.

     

    Ganin alamar baya cikin nutsuwarsa yasa Moddibo cewa.

    “Dan Allah Abba ka kwantar da hankalin ka”.

    Girgiza kai Abba keyi yana cewa.

    “Karima kin cuceni kin cutar da rayuwata kin katse min farin cikina”.

    Zama Moddibo yayi kana cikin sanyin murya ya shiga Furta.

    _“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakil Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha La’ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin la haula Wala ƙuwwata Illah billahil aliyul Azhim”_.

    Ahankali Abbah yafara bin bakinsa yana karato adduo’in tun yani yi Aransa har yafara afili.

     

    Hajiya Turai kuwa number Dr Muktar ta sake Kira yana ɗagawa tace.

    “Dr kayi sauri dan Allah ina katsaya har yanzu baka zoba kuma na faɗa maka jikin Alhj ya tashi gashi mun basa magani yaƙi sha”.

    Cikin sauri Dr Muktar yace.

    “Gani nan na fito dama yanzu zan wuce asibiti amma yanzu na kusa gidanku ma ina ƙara so wa”.

    Cike da damuwa tace.

    “Toh shikenan sai kazo dan Allah kayi sauri”.

    Ta ida maganar tare da katse kiran kana ta juya ta fice.

    Moddibo kuwa ciki sanyi ya riƙe hannun Abba tare da cewa.

    “Abba dan Allah kayi haƙuri ka cigaba da Addu’a”.

    Kai Abba ya gyaɗa kana ya cigaba da maimaita adduo’in but still ɓarin da jikinsa keyi bai dai naba saima ƙaruwa da yake.

    Dai-dai lokacin da Dr Muktar yayi hong mai gadi ya buɗe masa kana cikin sauri ya fito daga motar hannunsa riƙe da fest aid box Hajiya Turai dake Safa da marwa a coumpund ɗin ta masa jagora zuwa ɗakin suna shiga Dr Muktar ya zauna kan 1sitter kana ya buɗe Aidbox ɗin sa tare da gwada Bp Abba.

    Cikin sauri ya kalli Abba tare da cewa.

    “Subhanallah jinin Alhj ya hau sosai na faɗa muku ku daina kawo duk wani abu da kuka san zai ɓata masa rai, ko kuma tayar masa da hankali”.

    Ya faɗa tare da ciro sirinji kana yace.

    “Alhj bari nayi maka allura baki ɗaya damuwa yayi masa yawa”.

    Ajiye sirinji Dr Muktar yayi kana ya balli magunguna ya miƙa masa tare da cewa.

    “Alhj gashi kasha”.

    Girgiza kai Abba yayi cike da rauni yace.

    “A’a bazan shaba”.

    Asanyaye Dr Muktar yace.

    “Ayyah Alhj dan Allah kasha mana”.

    Girgiza kai Abba yayi tare da cewa.

    “A’a bazan shaba menene amfanin rayuwata matuƙar dai bazan iya temakon Jameelu na ba.

    Meye riban cigaba da rayuwata matukar Jameelu na baya tare dani?”.

     

    Cikin sauri Moddibo ya Girgiza kai tare da cewa.

    “Subhanallah Abba kada kace haka kada zafin damuwa yasa mu kaucewa lissafin hankali da na Musulunci Abba kayi addu’a dan Allah ka karɓi maganin kasha Abba. shin yakakeso nayi idan har kaima ka faɗi   ciwo ya kwantar da kai”.

    Cikin tausayawa ya kalli Abba idanunsa cike da ruwan hawaye kana yace.

    “Abba na tabbatar ko da J na nan bazai yi farin ciki da haka ba Abba dan Allah kayi haƙuri kasha maganinka, ganinka cikin dauriya shike bani ƙarfin gwiwa Abba bazan so ganin wani mugun abu yasa Meka ba. Idan har wani abu ya sameka  Abba ya zanyi da rayuwata!?”.

    Ya ida Maganar tare da miƙawa Abba maganin karɓa Abba yayi tare da kaiwa bakinsa ya haɗiye miƙewa Dr Muktar yayi kana yace.

    “Alhj bari a maka Allura”.

    Kai Abba ya gyaɗa kana Dr Muktar ya masa bayan ya masa ya juya ya fice.

    Sannu Ahankali Abba ya fara maida numfashi kana ya jingina bayansa da jikin kujera ahankali numfashinsa ya fara dai-dai-ta Atake zufa ya shiga tsats-tsafo masa agabaki ɗaya ilahirin jikinsa.

    Moddibo kuwa ganin haka yasa ya miƙe ahankali tare da ɗaukan remote ɗin AC ya kunna kana ya dawo ya zauna agefensa.

     

    Matsawa kusa da Abba Hajiya Turai tayi kana ta ɗauki hankief ta shiga goge masa zufa,

    cikin sanyin murya tace.

    “Sannu Alhj Ubangiji ya sawwaƙa maka, ka kwantar da hankalin ka insha Allah babu abinda zai samu Jameelu sai al’khairi”.

    Kallonta yayi amma baice komai ba.

    Moddibo ma ahankali ya dawo kusa dashi ya zauna kana cikin sanyin murya yace.

    “Abba ka kwantar da hankalin ka insha Allah babu abinda zai samu J Abba yanzu fa abinda ya kawoni da mukayi waya kace ansamu kudin kwata kwata Abba yanzu fa Million biyar ne ya rage akan kuɗin da muke nema ai abu yazo ƙarshe insha Allah babu abinda zai samu J,

    Kuma ma kafin inzo nayi waya da Ummi tace akwai wasu gwala-gwalai guda biyu gobe zata kaisu Taraba, da akan yau zata kaisuma to dare yayi, ta kuma cemin in sha Allah zasu iya kai two million.

    Kajifa alamomin nasara Abba meye zai tayar maka da hankali!?”.

     

    Ahankali Abba ya ɗago jajayen Idanunsa tare da kallon Moddibo kana ya kalli Hajiya Turai sai kuma ya maida kallonsa kan Hajiya Karima dake tsaye cikin rauni ya nuna ta da yatsa kana yace.

    “Karima ce nashiga wanka suka kira.

    Karima ta ɗauka wai tana musu maganan ragin kuɗin nace ta nema min ragi ne?

    Tabarni mana Jameelu ba ɗana bane ai zan fashi ɗana amma Meyesa Karima zata min haka!?”.

    Moddibo kuwa cikin wani azabebben tsinkewar zuciya ya riƙe kansa tare da cewa.

    “Innalilahi wa’inna ilahi rajiu’n.

    kika nemi ragin kuɗi kuma Aunty Karima amma gaskiya baki kyauta mana ba”.

    Cikin tsananin tsoro da fargabar abinda hakan zai haifar yaci gaba da cewa.

    “Amma gaskiya baki kyauta manaba, ai wannan mugunta ne an saki ne ko kuma annemi wani temako awajenki  fisabilillahi? wallahi kin cutar damu wannan shine cuta mafi muni da kika mana bayan kinji gargaɗin da sukayi”.

    Ya ƙarashe mgnar cikin raunin murya yana jin zuciyarsa na wani irin zafi da karaya.

     

    Cikin sauri Hajiya Turai ta kalli Hajiya Karima tare da Girgiza kai cike da takaicin halayyar ta tace.

    “Idan har ba tayi haka ba ai bata cika Yadukko ba, ai dama baka sanin mai sonka da gaskiya sai kashiga wani hali, wasu kuma burinsu su samu hanyar da zasu musguna wa rayuwarka suke nema”.

    Kallon Hajiya Turai Hajiya Karima tayi kana ta kalli Abba da Moddibo cikin Muryan kuka tace.

    “Agaskiya ni anyi min bahaguwar fahimta nima Ina son Jameelu tamkar ɗa yake awajena fa, ke Hajiya Turai da kike wannan maganar nida ke waya fara zama da Jameelu ne?”.

    Banza Hajiya Turai tayi da ita tana jin wani irin takaicin abinda ta aikata aranta.

    Sannu Ahankali bacci ya fara fisgar Abba saboda magani da Alluran da aka masa nan take Bacci ya ɗauke sa kwanciya Moddibo ya gyara masa akan kujeran kana ya miƙe tare da ɗaukar key ɗin motarsa zuciyarsa cike da rauni damuwa da tashin hankali duk sun bayyana afuskarsa.

    Yana fita yashiga motarsa tare da yimasa key yayin da hawaye suka cika kwarmin Idanunsa Driving yake yana sake try numbers din da suke kira kasancewar duk lokacin da suka kira saiya yi copy amma baki ɗaya Swich off.

    Ahankali ya fito da Number M Jameel kana Yayi dearling cikin ikon Allah yaji wayar tashiga tana ringing lokaci ɗaya ya shiga cikin matsanancin farin ciki afili ya furta.

    “Yau kuma wayar J tana shiga”.

    Cikin sauri ya juya akalar motarsa zuwa gidan Ummi kana ya Parking awaje tare da buɗe gate ya shiga coumpund ɗin yana cewa.

    “Ummi! Ummi!! Ummi!!!”.

    Ummi dake tsaye Atsakiyar falo tayi saurin fitowa tare da cewa.

    “Na’am Babana me yafaru?”.

    Cike da walwala yace.

    “Ummi wayar J ɗina yana shiga yau”.

    Cike da farin ciki Ummi ta ware ido kana tace.

    “Wayar Jameelu yana shiga?”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa still da murmushi afuskarsa ya gyaɗa mata kai kana yace.

    “Wallahi yana shiga Ummi bari ma kiji”.

    Ya faɗa tare da dearling number M Jameel aikuwa ya shiga ya fara ɗut-ɗut-dut cikin Sauri ya samata akunne da sauri Asma’u da Bashir dake Bedroom suka fito jiyo sautin su Ummi cikin farin ciki.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “Bari in Kira nima”.

    Ta ida maganar tare da dearling number kasancewar wayar na hannunta still ya shiga yana ringing.

     

    Cikin sanyi ta juya ta kalli Moddibo tare da cewa.

    “Babana to ya baya ɗauka kuma?”.

    Cikin wani masifaffen tsinkewar zuciya da tsoro Moddibo ya kalleta cikin ƙoƙarin ɓoye tsoronsa yayi Murmushi tare da cewa.

    “A’a Ummi Insha Allah tunda har wayarsa tana shiga zai ɗaga mu cigaba da kira da izinin Ubangiji zai ɗaga Agaskiya Ummi yau naji sanyi”.

    Murmushi Ummi haram Asma’u, da  Bashir.

     

    “Har naji hankali na ya dan kwanta wayar J ɗina ya shiga, kinga farko kafin mu rasa shi kiran wayarsa muka fara rasawa Ummi, yanzu kuma Insha Allah mun samu kiran wayarsa shi zamu ƙara samu next da izinin Ubangiji”.

    Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.

    “Ameen”.

    Cikin jin sanyi Asma’u tayi murmushi kana tace.

    “Alhamdulillah wayar Yah Jameel ya shiga gaskiya munyi farin ciki”.

    Malam Ahmad daya fito daga wanka ya fito coumpund ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi kana yace.

    “Alhamdulillah Asma’u maza kawo musu abinci suci tunda mun samu wayar Jameelu ya shiga maza kawo musu abinci”.

    Moddibo kuwa kallon Malam Ahmad yayi kana yace.

    “Nikam ma Malam baki ɗaya cikina ya cushe baki ɗaya farin ciki ya cika min cikana”.

    Murmushi Ummi tayi kana tace.

    “Nima cikina ya cika baki ɗaya farin ciki nake ji”.

    Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.

    “Dan Allah ku zauna kuci abinci wayarsa muka fara rasawa yanzu kuma wayarsa muka faru samu insha Allah shi ma zamu sameshi nan kusa ”.

    Dai-dai lokacin Asma’u tazo ta ajiye musu abincin.

    Tun ɓatan M Jameel sai yau Ummi da Moddibo sukaci abinci mai nauyi acikinsu duk da ba dayawa suka ciba.

    Miƙewa Moddibo yayi kana yace.

    “Ummi bari naje in faɗawa Innayi ta tayamu farin ciki”.

    Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.

    “Aikam dai gwara kaje”.

    Ficewa yayi tare da tafiya Driving yake Cike da farin ciki har ya isa gida yana zuwa ya shiga sashen Innayi.

    Innayi dake ki shimfiɗe ta miƙe kana tace.

    “Alhamdulillah Moddibo naga kana cikin farin ciki da alama akwai labari mai daɗi?”.

    Kai ya gyaɗa still Fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Innayi wayar J ɗina ya shiga yau”.

    Kai Innayi ta gyaɗa tare da cewa.

    “Alhamdulillah gaskiya munyi farin ciki. Allah ya bayyanar mana dashi”.

    Ameen ya amsa tare da wucewa sashen sa cike da farin ciki yana shiga ɗaki ya kira layin Malam Arɗo.

    Malam Arɗo na dagawa yace.

    “Malam Alhamdulillah yau wayar J ɗina yashiga a cigaba da taya mu da addu’a a masallacai da makarantu”.

    Cike da farin ciki malam Arɗo yace.

    “Masha Allah da izinin Ubangiji zai fito Insha Allah zamu cigaba da addu’a”.

     

    Awannan daren haka Moddibo Ummi, Asma’u Bashir malam Ahmad da Innayi suka kwana cike da farin cikin shigar wayar M Jameel.

     

    Yayin da Aɓangaren Abba ya kwana cikin taraddadi da tashin hankali koda ya farka tsakiyar dare kuka yayi ta yi yayin da Hajiya Karima ke kuka tana basa haƙuri kana tana cewa bada niyya tayi ba.

     

    Aɓangaren gidan Lamiɗo ma haka Khausar da Mommy suka kwana azaune da Ramadan da kansa ke masifar ciwo da zaran an bashi maganin da Lamiɗo ya kawo yasha ciwon zai ɗan lafa jimawa kaɗan kuma zai sake tashi tsakiyar dare ya farka ya riƙa kuka dole Ummi ta kira Abba ya kawo masa magani cikin ikon Allah yana sha ciwon kan ya lafa.

     

    Washe gari; Moddibo, Malam Arɗo, Ummi Innayi duk wani makusancin M Jameel na cikin farin ciki kana duk wanda ya kira wayarsa zai shiga sai dai ba aɗagawa Wunin wannan ranan haka Moddibo yayi yana kiran layin M Jameel still ba amsa.

    Zuwa yamma jikin Moddibo ya fara sanyi da lamarin ganin yana kiran wayar M Jameel baya shiga lokaci ɗaya tsoro ya fara kamashi hankalinsa ya tashi Misalin ƙarfe goma na dare yana gidan Abba zaune sun kira Jameel kuma sama da sau ashirin kuma duk  kiran yana shiga, sau dai ba’a ɗagawa, su kuma masatan basu kiraba.

    Yayin da idanun Abba ke kumbure alamar har yanzu jinjinsa bai sauƙa sosai ba.

    Cikin mutuwar jiki Moddibo ya koma gida kai tsaye sashen Innayi ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama ya shiga.

    Innayi dake zaune riƙe da carbi ta amsa masa cikin raunin Murya yace.

    “Innayi”.

    Kallonsa tayi cike da kulawa kana tace.

    “Na’am”.

     

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana cikin sanyin murya yace.

    “ Innayi hankalina ya soma tashi wayar J yana shiga ba’a ɗauka sannan mutanen nan basu sake kira ba”.

    Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe tare da cewa.

    “Ba komai Moddibo Insha Allah ka kwantar da hankalin ka”.

    Girgiza kai yayi kana yace.

    “Anya kuwa Innayi?”.

    Cikin bashi ƙwarin gwiwa tace.

    “Ba komai Insha Allah ka cigaba dayi masa addu’a da izinin Ubangiji zai fito yanzu idan sun sake kira kuce musu an samu kuɗin Insha Allah Million biyar  bazai gagara ba koda a masallatai anemi temako za’a samu  su  haɗu”.

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Toh Innayi Allah yasa su kira ɗin dan yanzu kam ma cikon Million ukune”.

    Cikin jin daɗi Innayi tace.

    “Alhamdulillah Allah ya bamu sa’a”.

    Amin yace

    Sanna ya miƙe ya koma sashen sa cike da damuwa. Washe gari jin sauran kuɗin da ake buƙata, Lamido ya bawa Mommy da kanta ta kaiwa Ummi su sau dai sam basu kuma kiraba.

     

    Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya yau kusan kwana ki shida kenan duk lokacin da aka kira wayar M Jameel zai shiga sai dai ba’a ɗauka.

     

    Yayinda Ramadan kuwa ke kwana da azabebben ciwon kai idan aka bashi magani yasha ciwo ya lafa anjina kaɗan kuma ya sake dawowa.

    Ga ɗaya Mommy da kwausar sun shiga damuwa, sun kai asibiti har cikin Taraba anyi hoton kan da duk wani gwaje-gwaje amman babu wani ciwo dake kansa, dan da farima likitocin sunyi zaton brain cancer ne.

    baki ɗaya yaron ya fita hayyacinsa saboda tsananin ciwon kai.

    Yau kimanin kwana shida  kenan da aka fara samun wayar M Jameel na shiga.

    Washe garin rana ta bakwai.

    Da safe bayan an idar da Sallar Asbah Moddibo na fita a masallaci ya kira wayar M Jameel.

    Cike da mmki tsoro ya janye wayar a kunnenshi sabida jin ance masa Switch off.

    cikin mutuwar jiki ya nufi gidan Ummi yana shiga ya samu Ummi zaune akan Sallaya hannunta riƙe da Carbi.

    Cike da ladabi ya gaisheta kana cikin sanyin murya yace.

    “Ummi”.

    Kallonsa tayi tare da cewa.

    “Na’am Babana”.

    Cikin raunin murya yace.

    “Ummi na kira wayar J ɗina baya shiga”.

    Ahankali Ummi ta jingina kanta da jikin kujeran falon kana tace.

    “Nima na kira wayan Jameelu na baya shiga bansan Meyesa ba Allah yasa al’khairi ne”.

    Cike da sanyi Middibo yace.

    “Amin ya Allah in sha Allah ba komai Ummi”.

    Cikin raunin murya Ummi ta lumshe Idanunta tare da cewa.

    “Hmmm,Hmmm Ubangiji Allah yabamu ikon cinye jarrabawar da zai jarabce mu”.

    Cikin sanyi Moddibo yace.

    “Ameen”.

    Miƙewa Moddibo yayi kana yace.

    “Ummi bari naje gidan Abba naji koshi ya kira ya shiga”.

    Kai Ummi ta gyaɗa Muryanta cike da rauni tace.

    “Toh”.

    Cikin sanyin jiki zuciya cike da karaya Moddibo ya nufi gidan Abba yana shiga coumpund ya ga Abba na ƙoƙarin shiga falo dawowansa daga masallaci kenan.

    Ƙara sawa Moddibo yayi tare da miƙa masa hannu sukayi musabaha kana cikin sanyin murya Moddibo yace.

    “Abba wayar J ɗina baya shiga”.

    Ahankali Abba ya sunkuyar da kansa hawaye masu zafi suka shiga bin kuncinsa Shar-shar-shar kamar ƙaramin yaro baki ɗaya ya rame cikin raunin murya yace.

    “Aliyu dama wayar Jameelu da kira yake shiga. Wani sanyi ne dama hankalina ya tashi tun jiya nake kiran wayar baya shiga, dama ni banyi farin ciki da shigan wayar Jameelu ba. Aliyu inaji Ajikina kamar akwai wani abu da bamu san menene ba jikina na bani ko ina Jameelu na yaje baya cikin walwala na rasa tudun dafawa”.

    Cikin sauri Moddibo ya runtse Idanunsa zuciyarsa na bugawa da masifaffen ƙarfi kana cikin raunin murya yace.

    “Abba insha Allah J yana cikin ƙoshin lafiya mu cigaba da masa addu’a amma nima baki ɗaya hankalina yayi masifar tashi”.

    Cikin rauni da tsanananin tashin hankali suka ci-gaba da tattaunawa.

     

    Acan gidan Lamiɗo kuwa  Mommy, Khausar da Lamiɗo basu rintsaba a wannan daren.

    A kan Ramadan suka kwana yanata kuka baiyi bacci ba.

    Washe gari Bayan an idar da sallan Asbah Hajiya Bunayya ta shigo falon Mommy ahankali Ramadan dake kuka ya miƙa mata hannu kana cikin wata raunan’niyar murya mai cike da wahala yace.

    “Ummah! Ummah! Kaina zai fashe kaina zai faɗi Wayyo Allah na Kaina! kaina”.

    Baki daya jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu dasu yayinda idanunsa sukayi ja.

    Cike da tausayawa Khausar ta ɗaura tafin hannunta na dama akan goshinsa Idanunta cike da ruwan hawaye kasa riƙe hawayen ta tayi jin yanda kan ke harbawa da masifar ƙarfi.

    Kuka sosai Ramadan keyi kana cikin tsananin radaɗin ciwo ya riƙo hannun Mommy kana yace.

    “Wayyo Mommy Kaina zai fashe. Mommy Kaina Wayyo zan mutu Mommy Zan mutufa”.

    Wani irin miƙa Ramadan yayi tare da cewa.

    “Momyyyyy zan mutuuuu”.

    Cikin sauri Lamiɗo da yanzu ya shigo ya karɓesa ganin yanda idanun yaron suka juya da sauri ya fara ɗan bubbuga kumatunsa yana cewa.

    “Ramadan! Ramadan!”.

    Wani irin juyawa Idanun yaron yayi tare da wulƙitawa kana yaja dogon numfashi….!

     

     

     

    *Zuwa yanzu dai mun gama ratsa tsakiyar labari babi-babi na zaren na dab da fara warware wa.*

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 24

    Sakayyah 24

     

    SAKAYAH

     

    24

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta, cikin Aminci domin ko kin gashi a wasu wuraren toh na satane na Allah ya isane, Yaseen kuwa wlh na Allah ya isan ne duk ƙanƙatar haƙƙina ban yafeba, yake yar uwa mai tsoron Allah da kikaye haƙin wani ki biya 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, sai in saki a Group ɗin, ku kuma masu fitar da littafina ki da Allah, Allahu Rabbi ya isarmin wahalata da nasha kusan tsawon shekara ina rubutu. Dan ki biya 1k kudin karatu kike fitarwa mutun sama da ɗari, toh yadda kika tozarta min kasuwanci ne kema Allah ya haɗaki da mai miki fiye da abinda kikayi min, kuma ki sani wlh ban yafeba*

     

    Isrnett. Gaban motar ne ya bugi Ramadan, kamar gilmawar walƙiya ya faɗi agefen kwaltan.

    Akuma dai-dai lokacin motar Moddibo da M Jameel ya tsaya awajen cikin sauri M Jameel ya buɗe motar tare da fita yana cewa.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”. kana ya nufi inda Ramadan ke kwance.

    Moddibo kuwa kansa ya dafe tare da rintse idanunsa.

    Akuma dai-dai lokacin Malam Isa,Malam Ahmad da malam Sa’id suka ƙara so  Kasancewar lokacin ne Malamai suka fara zuwa wasu ma ko Parking basuyi ba.

    Motar daya bige Ramadan kuwa ko tsayawa bai yiba ya ɗiba aguje.

    Aminu kuwa cikin tsoro da tashin hankali ya juya tare da kallon Ramadan dake kwance yayin da M Jameel ke tsugunne kansa zuwa lokacin tuni Ramadan ya suma ɗagosa M Jameel yayi tare da ɗan buga kuncinsa yana cewa.

    “Ramadan! Ramadan!!”.

    Amma ko motsa wa baiyi ba alamar babu nunfashi atare dashi.

    Cikin sauri Malam Arɗo ya fito daga cikin makaranta kasancewar ɗaya daga cikin Malaman yashiga ya sanar masa an samu hatsari awaje.

    Moddibo kuwa cikin sauri yayi wa motar key tare da ƙoƙarin bin bayansu ganin basu da niyyar tsayawa yana ƙoƙarin gilmawa M Jameel ya ɗaga masa hannu tare da faɗin.

    “A.J ka tsaya mu ɗauke sa mu kaisa asibiti”.

    Jin haka yasa Moddibo fasa bin bayan motar kana ya tsirawa bayan motar Ido ya tsaida ganinsa kan number burki ya taka.

    M Jameel kuwa cikin sauri ya ɗauko Ramadan ya sanya shi cikin motar ya tada suka nufi asibiti, Malam Arɗo kuma motar Malam Isa suka shiga tare da kallon sauran Malaman dake tsaye kana yace.

    “Malam Isma’il ku shiga ciki”.

    Kana Malam Isa yaja motar suka tafi.

     

    Haiydar kuwa har zuwa yanzu ya kasa buɗe Idanunsa saboda tsananin tsoro da tashin hankali ji yake yana buɗe idanunsa zai ga ƙwaƙwalwar Ramadan abaje akan kwalta hakan yasa ya runtse Idanunsa kana ya sanya hannunsa duka biyu ya dafe kansa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.

    Raudat kuwa kuka take tamkar ranta zai fita yayin da take yarfe hannunta tare da bubbuga ƙafarta  tana cewa.

    “Wayyo Ramadan ina za ku kaisa Meyesa mesa Wayyo Ramadan ɗina!”.

    Malam Isma’il ne ya ƙara so kusa da Haiydar tare da riƙe hannunsa ganin yanda jikinsa ke rawa kana yace.

    “Haiydar buɗe idon ka”.

    Girgiza kai Haiydar yayi still cikin Muryan kuka yace.

    “A’a tsoro nakeji in buɗe ido na inga ƙwaƙwalwan Ramadan akan kwalta”.

    Girgiza kai Malam Isma’il yayi tare da cewa.

    “Babu komai babu abinda ya sameshi beji ciwo ba motar ce ta bigesa ya koma gefe amma bata bi ta kansa ba!”.

     

    A hankali ya buɗe Idanunsa da sauri kuma ya sake ware su ganin babu kowa sannan Ramadan ma baya nan cikin rawan murya ya kalli malam Isma’il tare da cewa.

    “Ina Ramadan ɗin?”.

    Kallon titin Malam Isma’il yayi tare da faɗin.

    “Malam Jameel da Moddibo sun tafi kaishi asibiti sannan Malam Arɗo yabi bayansu yanzu kutafi cikin makaranta ka kwantar da hankalinka kaji?”.

     

    Girgiza kai Haiydar yayi yace.

    “Ya za’ayi kace in kwantar da hankalina kansa yafashe ko?

    ya karye ko? Ko dai ya mutu ne?.

    Cikin sa ya fashe ko? Kan kare sa akayi akwalta ko!?”.

    Duk alokaci ɗaya ya jero masa tambayar.

     

    Girgiza kai Malam Isma’il yayi kana yace.

    “Wallahi babu abinda ya sameshi kawai dai tsoro ne idan mutum bai taɓa accident ba dole tsoro zai sa ya suma kaje kashiga cikin makarantar maza kushiga ciki”.

    Dai-dai lokacin kuma ɗalibai suka fara zuwa cikin rarrashi Malam Isma’il yace.

    “Ku shiga ciki”.

    Raudat kuwa kuka ta riƙa yi tana yarfe hannu tsugunna wa Malam Isma’il yayi ya ɗauketa suka shiga cikin makarantar kana ya shiga bawa Haiydar ƙarfin guiwa.

     

    Acan ɓangaren su M Jameel kuwa suna isa Hospital ɗin aka karɓi Ramadan tare da kaisa Emergency Room.

    Atake aka fara bashi temakon Gaggawa kasancewar akwai ƙwararrun Likitoci cikin ikon Allah beji wani rauni ba sai karaya daya samu aƙafarsa na hagu.

    Cikin mintunan da baza su gaza talatin ba ya farfaɗo tare da fashewa da kuka kana ya buɗe Idanunsa tare da cewa.

    “Wayyo ƙafata Addah Khausi Ƙafata, Wayyo Addah Khausi Ƙafata”.

    Ahankali Moddibo dake gefensa ya matsa tare da riƙe hannunsa kana yace.

    “Sorry Ramadan kayi haƙuri kayi shiru kaji”.

    Cikin kuka sosai Ramadan ya kallesa tare da cewa.

    “Mommy na Malam akaini wajen Addah Khausi.

    Ina Addah Khausi na Ƙafata ciwo yake min zafi?”.

    Ya ida maganar yana jujjuya kai yayin da gaba ɗaya zufa ya wanke masa ilahirin jikinsa Musamman saman goshin sa amma babu hawaye a Idanunsa yayinda ƙafansa ya sake kamar roba ya langwaɓe.

    Cike da rarrashi da kuma tausayawa Moddibo yace.

    “Kayi haƙuri zai daina insha Allah”.

    M Jameel kuwa magunguna da abubuwan da za’ayi ɗauri Dr ya rubuta masa kana ya ya fice tsaye ya samu malam Arɗo maƙale da waya akunnen da alama da Lamiɗo yake magana.

     

    Cikin yanayin jimami ya gyara zaman wayar akunnensa tare da cewa.

    “Wallahi kuwa akwai yaron wajenka da mota ta ɗan kuskuresa yanzu haka ma muna asibiti”.

    M Jameel ne ya gyara tsayuwar sa  tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya lumshe idanunsa.

    Cikin sauri Malam Arɗo yace.

    “A’a ka kwantar da hankalin ka Mai Martaba baiji wani ciwo ba.

    Dan Allah dan Annabi ka kwantar da hankalin ka”.

    Ganin Malam Arɗo ya katse kiran yasa M Jameel cewa.

    “Malam wai batun ɗauri ne ƙafarsa ta karye to yanzu ance za’a yi masa ɗauri”.

    Jinjina kai Malam Arɗo yayi kana suka fita da M Jameel.

     

    A can Gidan Lamiɗo kuwa tun bayan tafiyarsu Ramadan Makaranta Mommy ta kasa miƙewa taje ta gyara ɗakin mijin nata.

    Duk da kuwa cewa itace da girki baki ɗaya jikinta Asanyaye yake bata da wani kuzarin kirki  yayin da Khausar ke kwance gefenta har zuwa lokacin hannunta na dafe da maranta.

    Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe tare da furzar da iska mai zafi daga bakinta kana ta yunƙura da niyyar miƙewa dai-dai lokacin Lamiɗo ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.

     

    Yana shiga idanunsa akan Mommy tare da cewa.

    “Aysha!, Aysha”.

    Cikin sanyin murya da mutuwar jiki Mommy tace.

    “Na’am”.

    Sai da yayi ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa tare da cewa.

    “Zo muje ki rakani?”.

    Kallon Mamaki Mommy tayi masa tare da faɗin.

    “Ina zamu je?”.

    ƙasa yayi da kansa kana yace.

    “Ke kam zoki rakani wani waje mana”.

     

    Atake  zuciyarta ya tsinke ƙirjinta ya buga da masifar ƙarfi kana tace.

    “Rakiya kuma ina kuma zamuje. Mai Martaba ka faɗa min?”.

    Ta ƙara sa maganar tare da kallon ƙwayar idanunsa da take iya hango tsantsar tashin hankali da damuwa.

    Cikin rawan murya tace.

    “Meyesa mu Ramadan”.

    Jin abinda tace yasa Khausar dake kwance tayi saurin miƙewa Atake Idanunta suka cika da ruwan hawaye lokaci ɗaya tsoro ya rufeta!.

     

    Cikin dakiya Lamiɗo yace.

    “Babu Abinda Ya samu Ramadan ke kam zoki rakani”.

    Cikin yanayin sadaukar wa Mommy ta kallesa kana tace.

    “Dan Allah ka faɗa min Meya samu Ramadan ɗina!”.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.

    “Kizo mu tafi mana”.

    Miƙewa Khausar tayi cikin rawan murya dan tuni hawaye suka wanke mata fuska kana tace.

    “Dan Allah Abba inzo mu tafi”.

    Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

    “Eh”.

    Cikin sauri ta sanya dogon hijabinta dake fitar da sanyayyan ƙamshin ta fita, shima Lamiɗo fita yayi sashen Hajiya Bunayya ya nufa yana kirata kasancewar shi kansa be san waya samu hatsari acikin ƴaƴan nasa ba Haiydar, Aminu, ko Ramadan.

     

    Mota suka shiga Khausar na gaba Lamiɗo Gimbiya Bunayya da Mommy suna baya.

    Lokaci ɗaya hankalin Mommy ya sake tashi ganin sun nufi hanyar asibiti cikin tsanananin tashin hankali tace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n dan Allah Mai Martaba ka faɗa min me yasamu Ramadan ɗina?”.

    Girgiza kai yayi tare da kallonta kana yace.

    “Nima kaina ban sani ba Aysha babu yanda muka iya da hukuncin Ubangiji”.

    Hajiya Bunayya kuwa ƙasa tayi da kanta cikin tsananin farin ciki da jin daɗi ta saki murmushi aranta tace Alhamdulillah burina ya cika in. Allah ya yarda yau ankawar min da Haiydar da Ramadan na huta dole inƙara musu kuɗi me tsoka yanda  zasuji farin ciki na kawar min da ƴaƴa biyu maza ɗin nan shikenan Mai martaba bashida wani ɗa Namiji sai Aminu dole Aminuna shi zai gaji sarauta.

     

    Ahankali ta ɗago kanta Idanunta cike taf da ruwan hawaye ta kalli Lamiɗo tare da cewa.

    “Innalillahi Wa’inna ilahi rajiu’n. Mai martaba mai yafaru?”.

    Cikin yanayin damuwa yace.

    “Ni kaina ban sani ba ance min dai ɗana Namiji ne amma ban sani ba Aminu ne…”.

    Aruɗe Hajiya Bunayya tasa hannu ta dafe ƙirjinta tare da cewa.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n ɗaya-ɗayan nawa”.

    A hankali ya fesar da iska daga bakinsa kana yace.

    “Kuma ban sani ba ko Haiydar, ko Ramadan ne ban sani ba sai mun shiga”.

    Mommy kuwa lumshe Idanunta tayi tare da faɗin.

    _“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan min ha”_.

    Suna isa suka fito bayan Driver Yayi parking Malam Arɗo na ganin Lamiɗo yayi saurin miƙewa tare da isa inda suke kana yace.

    “Sannunku da zuwa Mai Martaba”.

    Khausar kuwa tun da suka fito take kuka baki ɗaya jikinta ya gama bata Ramadan ne kuma ya rasune.

     

    Batare da Lamiɗo ya amsa Barka da zuwan da yake masa ba yace.

    “Acikin ƴaƴana waye ne yasamu hatsarin?”.

    Malam Arɗo ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.

    “Ƙaramin ne”.

    Ƙasa daure wa Khausar tayi kuka ta fashe dashi tare da faɗin.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Mommy Ramadan ne,

    sai da yace kada yaje makaranta yau kawai abarshi kada yaje kamar yasan me zai faru dashi na nace dole na muka turashi”.

    Mommy kuwa kasa daure wa tayi hawaye masu zafi suka shiga zubo mata.

     

    Dai dai lokacin M Jameel ya dawo daga sayo magungunan a Pharmacy dake cikin Hospital ɗin.

    Kallon Malam Arɗo Lamiɗo yayi kana yace.

    “Ku kaimu ciki”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare dayi musu Jagora kasancewar Mai matarba ne da iyalansa yasa aka barsu suka shiga.

     

    Suna Shiga idanun Khausar ya sauƙa akan Moddibo dake Rungumeta da Ramadan yana lallashinsa.

    Ramadan na kallonta ya fashe da sabon kuka tare da cewa.

    “Adda Khausi ƙafata Addah Khausi zoki riƙe min ƙafata”.

    Kallonsa ya mayar kan Mommy tare da cewa.

    “Mommy ancire min ƙafata ko? Bana jinta a jikina”.

    Sai kuma ya kalli Lamiɗo daya zuba masa Idanu cikin matsanancin kuka yace.

    “Abbah Ƙafata, Ƙafata”.

    Kallonsa ya mayar kan Hajiya Bunayya ya langwaɓar da kai amma baice komai ba.

     

    Hajiya Bunayya kuwa kallon Moddibo tayi jikinta na tsuma tace.

    “Ina Haiydar kadde shi yana mutuware?, Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

    Ido Moddibo ya zuba mata tare da tsaida idanunsa acikin nata abinda ba ɗabi’arsa bace ba kuma al’adarsa bace haɗa ido da mutum amma haka nan ya tsinci kansa da tsaida idanunsa akan matar yana kuma nazartan ta.

    Cikin yanayin ɓacin rai M Jameel ya juya ya kalleta tare da cewa.

    “Haba Hajiya wannan wani irin kalma ne ya za ayi kice yana mutuware?”.

    Hannu tasa tare da share hawayen fuskarta kana tace.

    “To ina yake? Ina Haiydar Allah sarki babban ɗan mu wanda zai gaji Mahaifinsa a sarauta Wayyo Haiydar”.

     

    Malam Arɗo da shigowarsa kenan ya kalleta tare da cewa.

    “Haiydar na nan lafiya yana makaranta yana karatu kana suna cikin kulawa!”.

    Da sauri Ta haɗiye wani abu mai masifar ɗaci tare da cewa.

    “Toh Ina Aminuna?”.

    Cike da kulawa malam Arɗo yace.

    “Shima yana cikin ƙoshin lafiya wannan ne kaɗai Accident ɗin ya faru dashi”.

    Lokaci ɗaya wani masifaffen ɓacin rai da baƙin ciki ya mamaye zuciyarta cikin ranta tace Haiydar bai mutu ba sannan shima wannan karayane ka ɗai?”.

    Tsaban zancen zuci dake cinta saida kalmar Karaye ne kaɗai ya fito fili.

     

    Atare Khausar da Moddibo suka kalleta jin abinda tace wannan ɗin ma Karaye ne kaɗai Moddibo ya maimaita kalmar Aransa.

    Khausar kuwa kwallon ta tayi tare da tsareta da ido tana sake maimaita kalmar aranta.

    Malam Arɗo ya kalli Lamiɗo tare da cewa.

    “Mai Martaba karaya yasamu dama akan za’a yi masa ɗauri ne saboda Andu basa gaba ɗaya baiji wani ciwo ba Karayane da Allah ya ƙadarta toh insha Allah yanzu za’a yi masa ɗauri”.

     

    Jinjina Kai Lamiɗo yayi tare da cewa.

    “Mun gode Allah ya saka da alkhairi”.

    Cike da damuwa Malam Arɗo yace.

    “Dan Allah kayi haƙuri akasani ne, tsautsayi aka samu wanda baya wuce ranan sa mai motar kamar da gayya yayi ko tsayawa bai yiba ya gudu baki ɗaya abin yazo da akasani ne bamu taɓa samun irin wannan akasin abakin makarantar ba”.

    Girgiza kai Lamiɗo yayi tare da cewa.

    “Bakomai Malam Arɗo ai babu yanda muka iya da ƙaddara ko agadon Mahaifiyarsa yake idan Allah ya ƙadarta zai karye dole ya karye Waman Ƙadarallahu Haƙƙa ƙadrihi”.

    Kai Malam Arɗo ya gyaɗa tare da cewa.

    “Haka ne kam”.

    Ajiyar zuciya Lamiɗo ya sauƙe tare da faɗin.

    “Amma bana son ɗaurin asibiti zamu koma dashi gida ayi masa na Gargajiya”.

    Jingina kai Malam Arɗo yayi tare da cewa.

    “Toh shikenan Babu matsala”.

    M Jameel ya Kalli Ramadan cike da tausayawa kana yace.

    “Toh Mai Martaba Allah ya ƙara sauƙi”.

    Kana ya miƙa masa ledan maganin daya sayo yace.

    “Gashi magunguna ne na rage zugi da zafin ciwo koda ɗaurin gidan za’ayi masa za ayi amfani dasu”.

    Karɓa Lamiɗo yayi tare da faɗin.

    “Toh angode”.

    Kana ya sanya hannu acikin aljihu ya ciro wayarsa tare da kiran number Malam Bala mai ɗauri.

    Katse wayar yayi bayan sun gama mga, juyawa yayi ya kalli Hajiya Bunayya da Mommy kana yace.

    “Mutafi to”.

    Sai kuma ya juya ya kalli Khausar dake kuka hadda sheshsheƙa yace.

    “Haba Addah Khausi kiyi haƙuri mana ai sai ki ƙara tayar masa da hankali shi yana kuka yana kiran ki sannan kema kina kuka ki bashi ƙarfin gwiwa mana”.

     

    Kai ta gyaɗa tare da Matsawa kusa dashi still Moddibo na riƙe dashi bakin gadon ta ƙara sa Moddibo kuwa saurin lumshe idanunsa yayi.

    Ita ko Khausar cikin kuka ta kalli Ramadan tare da cewa.

    “Kayi haƙuri Ramadan da mun sani da baka je makarantar nan ba tun jiya kake cewa baza kaje ba kana ta roƙon Mommy kada kaje”.

    Kallonta ta mayar kan Mommy tare da faɗin.

    “Dan Allah Mommy duk sanda yaron nan ya sake cewa ba zaije makaranta ba kada abarshi yaje tun jiya yake ta roƙo yau ɗaya abarshi ya huta kamar yasan abinda zai faru dashi”.

    Kasa cewa komai Mommy tayi ɗan ita kaɗai tasan yanda zuciyar ta ke mata.

     

    Khausar kuwa ahankali ta tsugunna akan Ramadan ganin yanda goshinsa ke tsats-tsafo da zufa ta ɗago lallausan tafin hannunta tare da mannawa agoshin sa ta yarfe masa zufan.

    Ahankali Moddibo ya tsirawa tafin hannunta Idanu cikin wani irin yanayi sannu Ahankali tsikar jikinsa ya fara tashi lumshe idanunsa yayi kana ya tuna lokacin da Amafarki ta sanya Lallausan tafin hannunta tana shafa Sajensa, ɗan juya hannunta ya buɗe Idanunsa da suka sauya launi tare da kallon hannunta yanda take shafa goshin Ramadan ɗin cikin nutsuwa yasa yaji wani abu mai masifar ƙarfi ya tsirga masa tun daga kan yatsan ƙafansa har zuwa ƙwaƙwalwar kansa lokaci ɗaya… ɗin sa ya harba da ƙarfin gaske cikin sauri ya cije lips ɗin sa tare da lumshe idanunsa yana kiran Sunan Allah Aransa.

     

    M Jameel ya juya ya Kalli Moddibo da Idanunsa ke lumshe kana yace.

    “Mu tafi ko?”.

    Kai ya gyaɗa tare da yunƙurawa ya ɗauki Ramadan dake ta faman kuka Khausar ta kauce gefe tana sakin ajiyar zuciya.

     

    Anutse Moddibo ya juya ya fita kana suma suka fice daga ɗakin zuwa harabar asibitin yana isa jikin motar ya samu har Lamiɗo yashiga gaba kana Mommy tashiga baya cikin sauri Hajiya Bunayya tace.

    “Kawo shi nan in riƙe shi”.

    Banza Moddibo yayi tamkar baiji me tace ba haka nan zuciyarsa ke raya masa Mommy ce mahaifiyarsu saboda kammani kana ga yanda Khausar ke kiran sunan Mommy akai-akai haka ma Ramadan yasa ya fahimci itace Mahaifiyarsu.

    Buɗe bayan motar yayi tare da kallon Mommy da hankalinta ke tashe ahankali ya ɗago Ramadan tare da ɗaura mata shi akan cinyarta.

     

    Cikin sanyayyar muryarsa mai cike da kamala nutsuwa da ladabi da kuma ƙwarjini yace.

    “Mommy dan Allah kada ki tada hankalin ki. Insha Allah zai samu lafiya ki cigaba dayi masa addu’a”.

    Jinjina kai tayi tare da cewa.

    “Nagode Allah ya saka maka da alkhairi Ubangiji ya Albarkanci rayuwar ka nagode”.

    Kansa a ƙasa ya amsa da.

    “Ameen Allah ya sawwaƙa”.

    Sannan ya rufe musu mota.

    Driver yaja suka tafi kana Moddibo da M Jameel suka shiga motarsu suka tafi.

    Sannan Malam Arɗo da Malam Isa suka shiga mota suka tafi.

     

    Ahankali Moddibo ke Driving yayin daya tsirawa titin Idanu,M Jameel dake gefe ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Kai Allah ya gyara wannan al’amarin Ubangiji Allah ya ƙara tsarewa ya kare gaba!”.

    Anutse M Jameel ya juya ya kalli Moddibo jin bai amsa addu’ar tasa ba cike da kulawa yace.

    “Ya dai? A.J meyafaru ne kayi shiru? Ina ta magana ba reply?”.

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da furzar da iska mai zafi  da kallon M Jameel kamar wanda aka fisgo maganar daga bakinsa yace.

    “Wannan Accident ɗin  shiryeyyene!”.

    Zare ido M Jameel Yayi tare da cewa.

    “Kamar ya shiryeyyene?”.

    Ƙaramin tsaki Moddibo yaja kana yace.

    “Akwai abinda ban gamsu dashi ba amma babu komai insha Allah zamuyi bin cike saboda na ɗauki number Motar Allah dai yabawa yaron nan Lafiya”.

    Sauƙe numfashi yayi tare da fesar da iska daga bakinsa kana yace.

    “Kaga yanda mahaifiyarsa tashiga tashin hankali amma matar nan da suka zo da ita hmmmm”.

    Sai kuma yayi shiru tare da faɗin.

    _“Astagfirullah Wa’atubu Ilaik ³_”.

    A hankali ya numfasa tare da cewa.

    _“Azzanna zambu walau kana haƙƙun,_

    Allah kagafar ta min Allah kaya femin munana zato dana yi mata”.

    Kallon M Jameel Yayi kana yace.

    “J bangamsu da yanayinta ba”.

    Jinjina kai M Jameel yayi tare da cewa.

    “Sosai ma nima na lura da wani yanayi atare da ita amma dai Astagfirullah Allah mun tuba”.

    Har suka shiga makarantar ba wanda ya sake magana Moddibo na Parking ya fita.

     

    Acan gidan Lamiɗo kuwa bayan sun isa Lamiɗo ya riko Ramadan aka kafadarsa Already mai ɗaurin yazo kai tsaye sashen sa ya nufa dashi cikin sauri Mommy ta tsaya daga gefensa cikin raunin murya tace.

    “Mai Martaba akaishi wurina kawai aje amasa acan”.

    Kallon ta Lamiɗo yayi kana yace.

    “Aysha aje amasa awaje na kawai ni yakamata inyi jinyarsa tunda yaro na miji ne”.

    Girgiza kai tayi kana cikin sanyin murya tace.

    “Zaka bar uzurorin kane ai ƙaramine zan iya yi masa komai yanzu da Haiydar ne zaka iya cewa zai fi ƙarfin indinga ɗaga sa ko kuma yi masa wani abu”.

    ta faɗa Idanunta na zubar da hawaye

    Jinjina kai Lamiɗo yayi tare da cewa.

    “In dai har kina so in Samu ƙarfin gwiwa kidena zubar da hawaye kin san Banason ganin hawayen ki”.

    Khausar kuwa tuni ta bar wajen.

    Bayan sun shiga falon Mommy Malam Bala ya ɗaura ƙafar cikin tsanananin azaba Ramadan ke kuka saboda zafi da raɗaɗi daya ke ji miƙewa Mommy tayi tashiga Bedroom ɗin tana hawaye cike da tausayinsa Khausar ma miƙewa tayi ta shige Bedroom ɗin ta yana sheshsheƙa ba zata iya juran Kallonsa cikin ciwo ba Lamiɗo kuwa riƙe sa yana rarrashin sa bayan angama ɗaurin Malam Bala ya basu magunguna da za’a shafa ledan da M Jameel ya bashi ya ɗauko tare da ɓalla masa maganin ya bashi sannun ahankali Ramadan ya fara sakin Ajiyar zuciya nan da nan bacci ya ɗauke sa miƙewa Lamiɗo yayi ya kwantar dashi akan 3sitter kana ya nufi Bedroom ɗin Mommy.

     

    Hajiya Bunayya kuwa ganin ba kowa afalo yasa ta sanya hannunta abakin zaninta tare da ciro wayarta kana tayi dearling wani Number tana Jin anyi picking tayi ƙasa da murya tare da cewa.

    “Ya haka? Shima wanda kuka buge ɗin karaya ne fa kaɗai!?”.

    A kuma dai-dai lokacin Khausar ta fito daga Bedroom ɗin ta jin falon yayi shiru ta ɗago manyan Idanunta da sukayi ja ta kelleta.

    Cikin basarwa Hajiya Bunayya tace.

    “Wallahi Allah ya taƙaita karaya ce kaɗai toh Nagode”.

    sannan ta katse wayar.

    Jinjina kai Khausar tayi tare da Kallon ta babu walwala atare da ita tace.

    “Hmmm Mai rabon ganin baɗi dai zai gani koda ana kamawa ana sawa aturmi ana kirɓawa, kana zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana ga muzuru ga shaho sai yayi”.

    Hararan ta Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

    “Ni tsiyata  dake kin cika habaici da zaurance gaki Bafulatana amma kamar ba haushiya”.

    A kuma dai-dai lokacin Mommy da Lamiɗo suka fito daga Bedroom ɗin suna murmushi Mommy na Kallon Hajiya Bunayya tace.

    “Yaya keda Khausar dai”.

    Murmushin yaƙe Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

    “Ai lallai dai kam”.

    Kallon Lamiɗo Mommy tayi kana tace.

    “Yayi bacci”.

    Jinjina kai yayi tare da cewa.

    “Eh kafin ya tashi ya kamata adafa masa kaji ahaɗa da maganin da Bala ya bada yana tashi sai abashi yaci”.

    Kai Mommy ta gyaɗa tare da karɓa, Khausar ta kalli Mommy tare da faɗin.

    “Mommy kawo inje in dafa masa ainaga kamar akwai sauran kaji a fridge kana ta wuce kichen ɗin”,

    Jinjina kai Mommy tayi tare da miƙa mata.

     

    Acan Makaranta kuwa Haiydar na ganin Moddibo da M Jameel sun shigo ya miƙe da sauri tare da riƙe hannun Raudat da har zuwa lokacin take kuka kana ya nufi wajensu.

    Cikin sanyun muryan yace.

    “Malam ya jikin Ramadan?”.

    Cike da kulawa Moddibo ya kallesa cike da tausayi ya riƙe hannun Haiydar acikin nasa tare da cewa.

    “Bakomai fa ya samu lafiya karaya ne kaɗai Abbanku yaje ya ɗauke sa ankoma dashi gida za ayi masa ɗaurin gida ka kwantar da hankalin ka Haiydar ba komai insha Allah”.

    M Jameel kuwa Raudat ya ɗauka tare da kallon Moddibo kana yace.

    “Ita wannan kam Malaman su sunce ba tayi karatu ba sai kuka”.

    Ahankali Moddibo ya juya ya kalleta baki ɗaya fuskarta yayi ja Idanunta sun kumbura kana jikinta ya ɗauki zafi cikin sanyin murya yace.

    “Kiyi haƙuri Hassan ɗinki yana lafiya babu abinda ya sameshi zaki koma ki same shi agida cikin ƙoshin lafiya Insha Allah”.

    Kallonsa tayi tare da cewa.

    “Da gaske!?”.

    Kai ya gyaɗa mata.

    “Toh zamu koma gida yanzu”.

    Ta faɗa tare da fashewa da kuma hadda sheshsheƙa.

    Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da kallon Moddibo kana yace.

    “Ina ganin ya kamata abarsu su koma gida dan yau ɗin nan ko sun zauna bawani karatu zasuyi ba ga Haiydar dake Babba ma baki ɗaya agigice yake bare ita yarinyar sai kuka take duk jikinta yayi zafi”.

    Jinjina kai Moddibo yayi idanunsa akan Raudat yace.

    “Eh hakan yayi sai su koma gida kawai”.

    M Jameel na Kallon Haiydar yace.

    “Bari akira gida sai aturo Driver yazo ya ɗauke ku”.

    Kai Haiydar ya gyaɗa kana ya nufi Office ɗin Malam Arɗo ya sanar masa  nan Malam Arɗo ya kira Lamiɗo babu daɗewa Driver yazo ya ɗauke su.

     

    Suna isa gida Raudat ta fice da gudu tare da shiga falon Idanunta ya saƙa akan Khausar dake zaune gefen Ramadan tana bashi kazar da already ta gama dafawa shi kuwa yana amsa yana ci Zugin ƙafar yayi sauƙi Sosai sai abinda ba arasa ba da gudu Raudat ta shiga tare da ƙara sawa ta rungume kan Ramadan cikin sauri ya ɗaga mata hannunsa na hagu tare da nuna mata ƙafar sake sa tayi tare da komawa gefensa ta zauna kana tace.

    “Ya ƙafan ka?”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Da sauƙi”, Langwaɓar da kai tayi kana tace.

    “Allah ya ƙara sauƙi sannu³”.

    Haiydar kuwa zama yayi agefensa tare da rintse idanunsa hawaye masu zafi suka zubo masa ahankali ya buɗe Idanunsa tare da sauƙe su akan Mommy kana yace.

    “Mommy tamkar gimmawar walƙiya haka naga motar nan tazo ta bugi Ramadan sanda yayi sama kafin ya faɗo Mommy banyi tsammanin kansa ba zai fashe ba”.

    Khausar dake cirewa Ramadan ƙasusuwa ajikin kazar ta ɗago kanta tare da miƙawa Ramadan tsokar kana ta mayar da kallon ta kan Haiydar tace.

    “Allah ne ya kare Haiydar saboda addu’ar mahaifiyarmu saboda haka Ubangiji zai ci gaba da kare mu yana mana katangar ƙarfe da magauta!”.

     

    Da sauri Mommy dake cirewa Raudat Uniform ta ɗago ta kalleta kana tace.

    “Khausar wasu magautan kuma wannan ai ƙaddara ce wacce ta riga fata”.

    Murmushi mai ciwo Khausar tayi kana tace.

    “Hmmm Mommy kenan”.

     

    Acan ɓangaren Hajiya Bunayya kuwa bayan tashiga ɗaki zaune ta samu Amina hannunta riƙe da Tuffa tana ci,

    Amina na kallonta tace.

    “Mommy ba abinda ya sameshi ko?”.

    Ƙwaffa Hajiya Bunayya tayi tare da zama kana cike da takaici tace.

    “Ai shi Haiydar ba abinda ya sameshi ko ƙwarzani bai yiba. Ramadan ne kaɗai ya bugu ba wani na arziƙi ba Karayane kaɗai”.

    A kufule ta ajiye Mayafinta tare da kallon Amina data tsareta da ido kana tace.

    “Na kirasu munyi magana dasu sannan na nuna musu ɓacin raina sai suka ce wai abinda yasa haka saboda lokacin Malamai sun fara zuwa idan suka tsaya za’a iya kama su”.

    Ya mutse fuska Amina tayi kana tace.

    “Ai dai kam sai ahankali”.

     

    Hannu tasa tare da ɗaukar Ayaba a Plate dake gaban Amina kana tace.

    “Ɗazu bayan kin dawo ina kika tsaya dana shigo ban ganki bane?”.

    Murmushi Amina tayi tare da cewa.

    “Ina side ɗin Gimbiya Dadu nida Uncle Naseer”.

    Wara Ido tayi kana tace.

    “Allah ko?,Ni dai Amina da zaki yarda sannan badan Masifar Son da yake yiwa wannan shegiyar Khausar mai kama da sadaka Yallanba yanda yaron nan ya samu cigaba da arziƙi ga kuma arziƙin da Iyayensa suke dashi da kin haƙura da Jameel din Nan duk da kuwa arziƙin da Mahaifin sa yake dashi”.

     

    Ƙwaffa Amina tayi tare da cewa.

    “Nifa Mommy Ina son Uncle Naseer kuma Ina son Malam Jameel saboda gaba ɗayan su suna da kuɗi kuma dama Ni ko Malam Jameel saboda kuɗin sa nake son sa”.

    Sai kuma tayi saurin cewa.

    “Yawwa Ummah ni kuwa Akwai Aure atsakanin mu  Uncle Naseer?”.

    Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da ajiye ɓawon Ayaba kana tace.

    “Sosai ma kuwa Akwai Aure atsakanin ku ko a musulunci ya halatta”.

    Kai Amina ta gyaɗa tare da faɗin.

    “Ummah kiga yanda yake kashewa yarinyar nan kuɗi kinga wayar daya siya mata kuwa wayar kusan dubu ɗari huɗu da hamsin kinga siye-siye tunda kinga Malam Jameel Anyi anyi aka mashi awajen Boka an kasa tunda shi wannan yana da riƙo da Ibada shi kuma wannan shgirigirbaune za’ayi saurin kamashi”.

    Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

    “Hakane fa Amina nima na fara wannan tunanin ga abu mai sauƙi sawa zamuyi asa ya tsani Khausar ɗin ya soki shidama in anyi auren bazaku wuce wata uku ba anan zaku tafi india”.

     

    Murmushi Amina tayi kana tace.

    “Eh kuma wannan abu mai sauƙi ne duk da masifar son da yake yiwa Khausar tun tana ƙarama amma yau ɗin nan tun da muka zauna tsawon zaman mu ya sake min fuska kamar zai iya maraba da duk abinda naje masa dashi”.

    Cikin jin dadi ta saki wani murmushi tare da cewa.

    “Tun da muka zauna yau ko yawan kiran sunan Khausar da yake yau be yawaita ba Ummah”.

    Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta sauƙe kana tace.

    “Bari zamu duba mu gani sannan zamuyi magana akai ai ɗazun muka rabu da Jameel da wannan ɗan banzan Moddibon ko yaushe ka gansa da Jallabiya kamar ɗan Larabawa”.

    Dariya Amina ta fashe dashi kana tace.

    “Aini shiyasa Samira Sani ke bani mamaki da take son Moddibo me yake dashi meya mallaka komai fa idan kika ganshi dashi sai dai idan Malam Jameel ne ya bashi kullum yana nan acikin Jallabiya bashi da kayan daya wuce Jallabiya ko motar da yake hawa daga kin gani kinsan mahaifin Malam Jameel ne ya saya mishi”.

     

    Ta gumi Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Ikon Allah shi kuma haka yake ashe se Uban faɗin rai kamar ɗan ƙaruna saboda arziƙi yana abu kamar mai rawani gashi da uban kwarjini”.

    Tsaki Amina taja kana tace.

    “Ko sutura kika gansa dashi sai dai in Malam Jameel ne yasaya mishi saboda duk yawanci kayansu iri ɗaya ne na rasa Meyesa Samira Sani take son shi koda yake inaga tsabar kyansa da ƙwarjinsa take so”,

    Sai kuma ta gyara zamanta tare da taɓe baki kana tace.

    “Inba hakaba me abin so ajikin talaka faƙiri komai sai aboki ya masa, arayuwa gashi ba kuɗiba  se shegen jijji da kai da taƙamar banza da ɗan karen ƙasaita”.

    Dariya Hajiya Bunayya tayi tare da kallon Amina kana tace.

    “Nima kaina abin ya ban dariya Amina da Hajiya Lami tazo tana ta haukan bin bokaye akansa yaron da ko wa’azin sa kake kallo yana cikin Jallabiya da Hirami kamar rainon Saudi”.

    Dariya Amina tayi kana ta taɓe baki tare da faɗin.

    “Ai dai kam ni dai mai ruwana su suka sani mu dai yanzu mun canza shekarar mu daga kan Malam Jameel zuwa Uncle Naseer”,

    murmushi ta saki tare da kallon Hajiya Bunayya kana  tace.

    “Idan kuma za’a tayi akansu su biyun muna raba ƙafa da duk wanda yazo tun da duka Iyayen su nada arziki kuma suma suna dashi duk kansu babu wanda yayi karatu aƙasar nan ko wannensu mijin nunawa sa’a ne da zaran na auri ɗaya daga cikinsu zan zama big Girl acikin garin nan”.

     

    Acan ɓangaren Gimbiya Dadu kuwa Uncle Naseer ne zaune akan 2sitter hannunsa riƙe da wayarsa yana latsawa Gimbiya Dadu na zaune kan Sallaya tunda ta idar da maghariba bata motsa ba suna taɓa hira jefi-jefi.

    Cike da nutsuwa Lamiɗo yayi sallama ya shiga, tare da miƙawa Uncle Naseer hannu sukayi Musabaha kana ya gaishe da Gimbiya Dadu.

    Cikin sanyin Murya Lamido ya kalli Gimbiya Dadu kana yace.

    “Ɗazu fa Ramadan ya gamu da hatsari ya karye”.

    Da sauri Uncle Naseer ya ɗago kansa kana yace.

    “Subhanallah³ ikon Allah”.

    Gimbiya Dadu ma cikin sauri ta ɗago kanta tare da kallon Lamiɗo cikin yana yin damuwa tace.

    “Subhanallahi bari idan na idar da Sallar Isha’i zanje in duba sa”.

    Miƙewa Uncle Naseer yayi tare da cewa.

    “Bari naje na dubasa”.

    Ya faɗa tare da ficewa.

     

    Kai tsaye sashen Mommy ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama Ahankali Idanunsa suka sauka akan Khausar dake zaune gaban Ramadan kallon falon yayi yaga ba kowa sai su kadai.

    Ahankali Khausar data ji Sallamar sa ta juya ta kallesa.

     

    Cike da duniyan ci ya sakar mata da mayaudariyar murmushi kana ya kashe mata ido ya wani langwaɓar da kai tare da Shagwaɓe fuska kana yace.

    “Ya dai Matas?”.

    Shiru Khausar tayi tare da yin ƙasa da kanta cike da mamakinsa aranta tace Uhmmm Uncle Naseer da tsaurin Ido duk abinda ya aikata ashe zai iya zuwa inda nake.

     

    Cikin rashin damuwa ya matsa kusa da ita idanunsa akan Ramadan yace.

    “Ayyah Ramadan sorry Allah ya sawwaƙa³”.

    Kai Ramadan ya gyaɗa kana yace.

    “Ameen Uncle Naseer”.

    Hannun Ramadan ya riƙe tare da cewa.

    “Me kakeso in kawo maka”.

    Kallonsa Ramadan yayi tare da cewa.

    “Komai ma ka siya min ina so Uncle Naseer ”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh Autan Mommy”.

     

    Ahankali Naseer ya juya ya kalli Khausar da Idanunta ke kan Ramadan ya narkar da murya tare da faɗin.

    “Mommy fa?”.

    Kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace.

    “Ta shiga ciki tana Sallah Isha’i ne”.

    Jinjina kai yayi kana yace.

    “Ayyah Allah ya bashi lafiya”.

    Ta lumshe Idanunta tare da cewa.

    “Ameen ya Allah”.

    Ahankali ya juya gareta tare da gyara zamansa akan rock ɗin kamar yatsun hannunsa zasu taɓa yatsun Ƙafarta.

     

    Ya karyar da kai tare da sanyaya muryarsa kana yace.

    “My dear yau kusan kwana uku kenan koda naki ra wayar ki bata shiga idan wani laifi na miki sai ki faɗa min laifina in baki haƙuri duk da cewa ina da yaƙinin bani nayi miki laifa kece kikayi min laifin, gashi ke kuma baki iya bada haƙuri bako”.

    Saurin Kallonsa Khausar tayi tare da maimaita bani nayi miki laifi ba aranta.

    Kamar yasan tunanin da take ya jinjina kai tare da narkar da murya kana yace.

    “Yes My Khausi Kece kika yi min laifi amma baza kiban haƙuriba to naji na amshi laifina.

    Ni zan baki haƙuri duk da cewa kin ɓata mana aiki”.

    Sai kuma ahankali ya juya ya kalli ƙofar Bedroom ɗin Mommy kana ya kalleta duk ya koma kalar tausayi kana yace.

    “Kin ɓata mana aiki My Khausi baki damu da rayuwata ba ke baki damu da in mutu ko ina rayu ba abinda na faɗa miki ai ba jini kawai ake buƙata ba tunda ba Jinin mutum kawai ba jinin ma na Period ɗin mace magani za’a haɗa min”.

    Ta gefen ido ya saci kallonta tare da fesar da numfashi kana yace.

    “Amma kika je kikayi min abinda bashi bane, Wallahi kin yimin muguwar fahimta wallahi ba wani abu bane saboda yanda kika ɓata kikasa na dabba shiyasa aka samu akasin da aka samu”.

     

    Anutse Khausar ta ɗago manyan Idanunta dake cike da mamaki ta tsaida su akan sa.

    Ganin kallon data ke jifansa dashi yasa ya dake tare da langwaɓar da kai kana ya marairaice murya tare da cewa.

    “Wallahi na rantse miki da Allah My Khausi gaskiya nake faɗa miki ki yarda dani”.

    Still Ido Khausar ta zuba masa aranta tace Ohhh lalle Uncle Naseer baya tsoron Allah ya aikata abu sannan yazo yana rantsewa da girman Allah saboda baisan girman Allah ba.

     

    Hannun Ramadan ya riƙe acikin nasa tare da sake Matsawa gabanta kana yace.

    “Na rantse miki da Allah My Khausi ban aikata abinda kike zargina ba wallahi tallahi ai babu wani abu sama da Allah?”.

    Wani irin kallo ta watsa masa tare da Kallonsa kana tace.

    “Ni dai awajena da duk wani Muminin duniya babu wani abu sama da Allah.

    Amma awajen matsafi yana da abu da yake ganin zai bashi abu sama da Allah yana da dodon tsafi! Kuma dama yawan rantsuwa a mgn ai masiface”.

     

    Zare Ido Uncle Naseer yayi cikin yanayin ruɗewa  ya kalleta tare da cewa.

    “Innalillahi wa’inna Ilahi rajiu’n Khausar!, Khausar!!, Khausar!!! Nine matsafi?, Hasbunallahu wani’imal wakil, ya Salam Khausar Ashe dama kallon da kike min kenan?. Kai cona da wannan zargi da matar aurena take min”.

     

    Lokaci ɗaya jikin Khausar yayi masifsr sanyi kallon fuskarsa  tayi taga duk yanda ya wani susuce aranta tace To Uncle Naseer ko dai dan naji tsoron abin ne amma kayi haƙuri na zarge ka akan abinda baka aikata ba.

    Uncle Naseer kuwa jin bata ce komai ba yasa ya sake narkar da murya tare da cewa.

    “Sam ban taɓa zaton zaki yimin irin wannan mummunar fahimtar ba, My dear koda ace ina tsafi tasirin soyayyarki ba zaisa inyi tsafi dake ba shin idan nayi tsafi dake dawa zan rayu? kece rayuwata My life is nothing without you Khausi”.

     

    Dai-dai lokacin Mommy ta fito daga Bedroom.Jin motsin fitowarta yasa Uncle Naseer ya juya tare da dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.

    “Mommy ya mai jiki ashe abinda yafaru Allah ya sawwaƙa”.

    Ba yabo ba fallasa Mommy tace.

    “Ameen mun gode”.

    Kana ta nufi kichen tare da cewa.

    “Khausar zo muje mu ƙara sa aiki”.

    Ahankali Khausar ta kalleta tare da cewa.

    “Toh”.

    Mommy kana ta miƙe idanu ya zuba mata har ta ɓacewa Kallonsa.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da miƙewa ya fita.

     

    Acan ɓangaren Moddibo kuwa Anutse suka fito daga masallaci bayan sun idar da Sallar Isha’i suka nufi gida suna shiga coumpund ɗin M Jameel ya tsaya.

    Anutse Moddibo ya juya ya kallesa tare da cewa.

    “Ya dai J”.

    Lumshe idanu M Jameel Yayi kana cikin sanyin Murya yace.

    “A.J muje wajen Ummi mana nayi missing ɗin ta”.

    Kallonsa Moddibo yayi kana yace.

    “Kai J ina yau da safe ma kafin muje makaranta sai da muka biya?”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.

    “A.J Ina son ganinta ne wallahi A.J inajin zanyin Aure kwanan nan”.

    Cike da Mamaki Moddibo ya juya ya kallesa kana yace.

    “Aure J?”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.

    “Eh zanyi Aure”.

     

    Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.

    “Toh babban magana J wannan magana ce mai girma ai mushiga daga ciki muyi ta”.

    Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.

    “A’a mushiga mota dai muje muyi ta agidan Ummi”.

    Wara Ido Moddibo yayi tare da saurin kallon M Jameel kana yace.

    “J baka da kunya agaban Ummi?”.

    Murmushi M Jameel Yayi tare da faɗin.

    “A.J ni kake cewa bani da kunya ba gwara niba cewa nayi inason Aure, kaifa jikinka ne ya nuna kana son Aure na riga dana fadawa Innayi na faɗa mata komai na kuma zaɓa maka matar da zaka aura ma”.

    Cike da mamaki Moddibo ya juya ya kallesa tare da sakar masa da murmushi kana ya shafa sajensa tare da cewa.

    “Iyeee sannu Babana”.

    Dariya M Jameel Yayi kana yace.

    “Ayaaa kana wasa ne?, Wallahi da gaske nayi maka zaɓin mata kuma na faɗawa Innayi sannan ta aminta da hakan kana na shaida mata cewa A.J ɗina yana ɓuƙatar Aure”.

     

    Juyawa Moddibo yayi ya kallesa tare da Matsawa kusa dashi kana ya ɗan mari fuskarsa.

    M Jameel kuwa dariya ya fashe dashi wanda ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana ya shiga tsinkar fulawar dake wajen yana sunsunawa tare da watsa su sama ga hasken farin wata da da gloves ɗin ya haska wajen.

    Moddibo kuwa idanu ya zubawa M Jameel yana sakin murmushi akai-akai wani irin amintaccen kyau M Jameel ya masa fuskarsa kuwa sheƙi da ƙyalli takeyi more especially gishinsa, lumshe idanu Modibbo yayi kana Aransa yace.

    “Masha Allah J kayi kyau sosai baka taɓa yin kyau irin na yau ba”.

    M Jameel kuwa still dariyar ya cigaba dayi yana mai buɗe hannayensa tare da cewa.

    “Allah ko A.J nayi kyau, kace inje amaryata ta ganni”.

    Ahankali Moddibo ya sauke Ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Au ashe mgnar ta fito fili.”

    Cikin sakin yalwataccen murmushin da yasa kyawawan haƙoransa bayyana ya gyaɗa mishi kai.

    Shi kuwa Modibbo a hankali yace.

    “Sosai ma kuwa J kayi kyau,  fara’a nayi maka kyau idan kana dariya kana kyau sosai”.

    Ahankali M Jameel ya ɗago ya kallesa still Yana cigaba da dariyar yace.

    “Ai kaima in zaka yi fara’a haka yana maka kyau A.J”.

    Girgiza kai Moddibo yayi har zuwa lokacin da murmushi afuskarsa yace.

    “Bazan iya dariya yanda kake yi haka ba J”.

    Wara Ido M Jameel Yayi kana cikin dariyar yace.

    “Zaka iya A.J”.

    Harɗe hannunsa yayi a ƙirjinsa tare da ɗan jingina da jikin mota, kana ya zubawa M Jameel ɗin idanu yana kallon yadda yaketa dariya har maƙolloton wuyanshi yana ɗan haurawa sama kana ya yi ƙasa, sannan haƙoransa nata sheƙi.

    Innayi ce ta fito daga sashen ta tare da kallon M Jameel kana tace.

    “A’a Jamilu yau mai ya maka daɗi haka?”.

    Cikin dariya sosai ya kalli Moddibo kana ya nuna masa saitin Dick ɗin sa da ido.

    Da sauri Moddibo ya sunkuyar da kansa tare da kallon inda M Jameel ya nuna da sauri ya lumshe Idanunsa ganin yanda Dick ɗinsa ke miƙe tun ranan da abin ya faru tsakanin sa da Khausar har yau Dick ɗin sa bai sake kwanciya ba koda na second ɗaya sam yaƙi kwanciya ya koma Normal yanda yake cikin dabara ya sanya ƙafarsa ɗaya agaba ɗaya abaya ya matse cinyarsa kana ya cije lips ɗin sa.

     

    Wani sabon dariya M Jameel ya fashe dashi tare da riƙe cikinsa kana ya kalli Innayi tare da cewa.

    “Wayyo Allah cikina hahahaha khhykhy Innayi wai dan nace masa na zaɓa masa mata shine yake cewa, nine Babansa kuma na faɗa masa akan na faɗa miki cewa wallahi Aure yakeso ya girma yanzu shine yake wata magana Innayi ki faɗa masa bana zaɓa masa mata ba?”.

     

    Murmushi Innayi tayi kana tace.

    “Sosai ma”.

    Moddibo kuwa sajensa ya shafa tare da kallon su kana yace.

    “Iyeee kune ma masu tsara min rayuwata toni nace muku ina bukatar aure ne?”.

    Still cikin ƙyelƙyala dariya sosai M Jameel yace.

    “Ai bai sai kafaɗa da bakin ka ba A.J dama ai body language ɗabi’ar kace to ganganar jikinka ta faɗa min kana son Aure”.

    Moddibo kuwa cikin sauri ya juya tare da nufar mota jin M Jameel na Shirin tona masa asiri batare daya juya ba yace.

    Toh kazo mu tafi Innayi bari muje gidan Ummi”.

    Kai Innayi ta gyaɗa da murmushi afuskarta tace.

    “Toh Allah ya tsare”.

    Bayansa M Jameel yabi tare da buɗe motar yashiga har suka isa gidan da zaran M Jameel ya Kalli Moddibo zaiyi dariya shi kuwa Moddibo sai ya sakar masa da murmushi.

    Suna isa Moddibo yayi Parking suka fita akan baranda suka hango Ummi hannunta riƙe da kayan shanya da alama akan igiya ta ɗebosu, ƙara sawa Moddibo yayi kana yace.

    “Ummi kawo in karɓa miki”.

    Miƙa masa yayi.

    Cike da so M Jameel yace.

    “Umminaaa”.

    Kallonsa Ummi tayi tare da ƙara sa shiga falon ya suka biyo bayan ta atare.

     

    Akan capet Ummi ta zauna tare da jingina bayanta da jikin kushin kana ta miƙe ƙafafunta ahankali Moddibo ya zauna daga gefenta tare da ajiye kayan wankin ganin kayanta ne yasa ya fara ninkewa.

    M Jameel kuwa ahankali ya kwanta tare da ɗaura kansa akan cinyar Ummi kana ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya kana ya lumshe Idanunsa tare da cewa.

    “Ummina kenan”.

     

    Ahankali Ummi ta juya ta kalli Moddibo kana ta mayar da kallonta kan M Jameel sai kuma ta ɗaga kanta ta kalli haɗeɗɗen agogon dake manne abango kana ta sauƙe Idanunta ƙasa tare da cewa.

    “Ayana yin garin nan da yake ga alamun yau akwai hadari sannan baku zo da wuri ba dubi time fa har kusan 8:30 kodai zamu kwana ne?”.

     

    Murmushi M Jameel Yayi tare da ɗago kai ya kalleta kana ya langwaɓar da kai tare da cewa.

    “Ummi dana fi kowa farin ciki ace yau gani gaki muna kwana gida ɗaya”.

    Juyawa yayi ya kalli Moddibo kana yace.

    “Shiyasa ma nake faɗawa A.J nifa Aure zanyi”.

     

    Cikin sauri Ummi ta juya ta kallesa kana cike da Mamaki wannan shine karo na biyu da yake faɗa mata Kalmar yana son Aure Girgiza kai tayi kana tace,

    “Jamiluuuu”,Ta faɗa kai tsaye ta rasa Meyesa acikin kwanakin take kiran sunan sa kai tsaye.

     

    Dariya M Jameel ya fashe dashi sosai yake ƙyalƙyala dariya harda kaɗa ƙafa.

    Asma’u da Bashir kuwa jiyo sautin dariyar sa yasa suka fito daga Bedroom tare da zama daga gefensu cike da girmamawa suka gaishesu atare.

    Ahankali ya kalle tare da sakar musu da murmushi kana yace.

    “Ƴan ƙanne na”.

    Sai kuma ya juya ya kalli Ummi dake murmushi kana yace.

    “Wallahi Ummi dagaske aure nake so”.

     

    Wara Ido Asma’u tayi cike da farin ciki ta kalli M Jameel kana tace.

    “Kai Alhamdulillah gaskiya munji daɗi”.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “Aikam dai Asma’u munji daɗin mu zan ginawa Ummina da Malam side ɗin su na musamman in saka su acikin”.

    Sai kuma ya numfasa tare da lumshe idanunsa kana yace.

    “Sannan ingina miki ɗakin ki in zuba miki kayan masu kyau sannan Bashir ma ingina mishi side dinsa da ban da daddare kafin inyi bacci inzo inyi hira da Ummina inganta ta ganni kana kullum idan gari ya waye daga na dawo daga masallaci in biya inga Ummina ta ganni kana ta bani shayinta mai daɗi Insha”.

     

    Cike da jin daɗi Asma’u ta kallesa kana tace.

    “Allah yasa Yah Jameel”.

    Lumshe Idanunsa yayi kana yace.

    “Hmmmm!”.

    Kansa Ummi tashafa cike da ƙaunarsa tace.

    “Ameen”.

    Moddibo kuwa ahankali ya zuba musu Idanu yana kallon su cike da burgewa.

     

    Ummi kuwa ahankali take shafa kan M Jameel kana tace.

    “Kai ko kunya baka ji ƙato da kai kazo ka kwanta min akan cinya na!?”.

    Ta ƙarashe maganar tana shafa yalwataccen sumar kansa.

     

    Murmushi yayi kana yace.

    “Uhmmm Ummina idan ban ɗaura kaina akan kiba to akan wa zan ɗaura? Abinda ma ya kusa ƙare wa hmm”.

    cikin sauri tace.

    “Ya kusa ƙare wa kamar ya!?”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Idan nayi Aure mana ai shikenan na samu sabon cinya”.

    Girgiza kai Moddibo yayi tare da kallon M Jameel kana yace.

    “Mtssss J Allah ya shiryeka”.

    Miƙewa M Jameel Yayi tare da kallon Ummi kana yace.

    “Ummi nida A.J rana ɗaya za muyi Aure, nida Innayi mun zaɓa mishi mata, amma sai idan nazo ni kaɗai zan faɗa miki sai mugama magana tsakanina dake”.

     

    Wara ido Ummi tayi tare da kallon Moddibo kana tace.

    “Allah ko”.

    Kai ya gyaɗa mata yana dariya ganin hararar da Moddibo ke wurga masa kana yace.

    “Eh”.

     

    Sha ɗaya saura suka yiwa Ummi Sallama kana suka tafi suna isa gida suka shiga falon M Jameel har ya juya da niyyar shiga ɗakinsa da yake kwana ya fasa yabi bayan Moddibo.

    Ahankali Moddibo ya juya ya kallesa tare da cewa.

    “Ya dai J?”.

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Yau tare zamu kwana”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana ya wuce ciki.

    Tunda Moddibo ya fito daga toilet ya zauna agefen gado tare da dafe kansa da hannu biyu har yanzu bai janye yayinda Jameel kuwa ke ciki.

    Ahankali M Jameel ya fito daga toilet ɗin.

    Yana mai tsane suman kanshi da mini towel Idanunsa suka sauƙa akan Moddibo daya dafe kansa da hannu biyu.

    Cike da kulawa yace.

    “A.J ya dai?”.

    Ahankali Moddibo ya ɗago kansa.

    M Jameel kuwa kallon yanda Idanunsa suka kaɗa suka jawur yayi kana lips ɗin sa na rawa yayin da jikinsa ke ɓari kamar mai jin sanyi.

    Cikin sauri M Jameel ya matsa kusa dashi kana yace.

    “A.J ya dai?”.

    Cikin yanayin damuwa da raunin murya Moddibo ya kallesa kana ya miƙe tare da yin wani irin fitinenne miƙa Atake A ɗin sa ya Miƙe tsaye baki ɗaya jikinsa rawa yake idanunsa sun kaɗa sunyi jawur tuni lips ɗin sa ke rawa tamkar mai jin zazzaɓi.

    Wani irin tausayinsa ne ya kama M Jameel Cike da tausayawa yace.

    “A.J ya dai?”.

    Cikin yanayin tashin hankali Moddibo ya Girgiza masa kai kana cikin raunin murya yace.

    “J ga halin danake c….!

     

     

     

    *Littafin SAKAYYAH dai na kuɗine 1k ne kacal ki biya ki karanta cikin aminci 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA.*

     

     

     

    *By*

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 32

    Sakayyah 32

    SAKAYAH

     

    32

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

    Spndeɗɗ. Baya Moddibo ya koma. Suuuuuu ya faɗi a sume, cikin sauri Lamiɗo ya tarosa, ya faɗa jikinsa cike da tashin hankali Lamiɗo yace.

    “Innalillahi ya suma fa Subhanallah!”.

    Cikin sauri Malam Arɗo ya ƙara sa kusa da Lamiɗo idanunsa akan Moddibo ya shiga kiran sunan sa yana faɗin.

    “Moddibo!, Moddibo!!, Moddibo!!!”.

    Ina tuni Moddibo ya sume babu alamar numfashi atare dashi.

    Abba kuwa kansa ya ɗaga tare da kallon fuskar skeleton M Jameel kana ya maida Idanunsa ƙasa kan takalmin dake sanye aƙafarsa ahankali ya leƙa bayan idanunsa suka sauƙa akan guntun rigarsa da bai gama sauƙa daga jikin skeleton ba jinjina kansa yayi cikin wata dakakkiyar murya ya juya ya kalli Moddibo dake sume kai ya girgiza tare da sakin murmushin da yafi kuka ciwo murmushi da yafi ihu zafi, murmushin da yafi ciwo, Ciwo murmushin da yafi raɗaɗi zafi, ya saki kana ya juya ya kalli sauran mutanen dake tsaye sai ya kuma kalli fuskar skeleton tare da maida kallonsa kan yatsun hannunsa.

    Cikin wata dakakkiyar murya me ɗauke da tarin raɗaɗi da ƙuna yace.

    “Uhmmm Jameelu na ne”.

    Kallonsa ya mayar kan Moddibo da har zuwa lokacin yake. Rungume a jikin Lamiɗo taune lips ɗinsa yayi tare da cewa.

    “Kai kam Aliyu kahuta, inama ace nima zan sume ko kuma in mace ma gaba ɗaya da hakan yafi min sauƙi”.

    Cikin sauri ɗaya police ɗin  ya juya tare da isa gefen Abba ya riƙe sa cike da alhini da tarin tausayawa yace.

    “Alhj Bashir kayi addu’a kaji”.

    Kai Abba ya gyaɗa cikin wata dakakkiyar murya yace.

    _“Innalillahi wa’inna Ilahi rajiu’n lahaula wala ƙuwwata Illah billahil aliyul Azhim Hasbunallahu wani’imal wakil Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha La’ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal Zhalimin”_ sune Adduo’in da yake iya maimaitawa afili da kuma ransa.

     

    Ori dake tsaye ciki ruɗu da tausayawa yayi saurin ƙarasawa gaban skeleton gawar M Jameel ya ɗauko goran ruwan kana ya dawo tare da miƙawa Lamiɗo yana mai cewa.

    “Lamiɗo gashi ayayyafa masa”.

    Karɓa Lamiɗo yayi kana ya buɗe tare da yayyafawa Moddibo dake kwance jikinsa amma ko kaɗan Moddibo bai motsa ba.

    Kallon Buba Lamiɗo yayi kana yace.

    “Ori taimaka min mu saka shi cikin Mota”.

    Kai Buba ya gyaɗa.

    Ɗaya daga cikin Folisawan ne yace.

    “Ranka shi daɗe bari mu saka shi”.

    Ya faɗa tare da kallon ɗan gidansa da Ido ya masa alamar yazo su kama Moddibo ƙarasawa yayi sannan suka ɗauki Moddibo suka sauƙa kasan dutsen, tare da sanya shi abayan Motar Malam Arɗo.

     

    Folisawan kuwa ƙara sawa sukayi suka shiga ɗaukar hoton gawar skeleton M Jameel.

    Bayan sun gama ɗauka tare yan dube-dubensu, da Babbansu da sauran suka saka handglove suka ƙarasa gaban gawar da niyyar sunjanye gawar Babbansun  najan Igiyar da aka ɗauɗaureshi  ƙasusuwan suka kakkarye tare da zubewa a ƙasa babu ta yanda zasu iya daukarsa Babban su ya umarci Coustable yaje ya ɗauko musu kwali abayan mota kana suka tattara gawar suka zuba acikin kwalin kana suka kwashe takalmansa da wayoyinsa suka saka awata leda.

    Abba kuwa cikin wani irin yanayi ya nufi cikin jejin  yana tafiya ba tare da shi kansa yasan inda ya nufaba.

    Cikin sauri Lamiɗo ya nufesa tare da riƙe hannunsa cike da tausayawa yace.

    “Alhj banan zamu bi ba can baya ne, hanyar kazo innu na maka hanyar da zamu bi”.

    Kai Abba ya gyaɗa tare da bin bayan Lamiɗo baki ɗaya baya cikin nutsuwarsa ya kasa gane shin mafarki yake ko kuma azahirance komai ke faruwa.

    Bayan sun isa Lamiɗo da kansa ya buɗe masa mota yashiga sannan shima yashiga.

    Folisawan kuwa kwalin da gawar M Jameel ke ciki suka ɗauka tare da sawa abayan motarsu suka tafi gida.

    Abba kuwa kallon hanya kawai yake baki ɗaya baya cikin hayyacinsa ganin yanayin da yake ciki ne yasa Malam Arɗo ya fara yi masa Adduo’i yana tofa masa kana yana faɗa afili.

    Ahankali Abba ya fara sakin Ajiyar zuciya kana yashiga maimaita Adduo’in sannu Ahankali ya fara jin hankalinsa ya fara dawowa jikinsa.

    Motar da Moddibo ke ciki Ori da police ɗaya ne aciki direct Asibiti suka nufa dashi.

     

    Yayin da Motar dasu Abba da kuma gawar M Jameel ke ciki kai tsaye gida suka wuce, suna isa kai tsaye falonsa suka wuce police ɗin ne ya ɗauko kwalin Gawar M Jameel ya shigo dashi kana ya ajiye agabansu.

    Hajiya Turai dake sashenta tana jin tsayuwar motoci ta fito zuwa falon Abba.

    Ganin Abba zaune tare dasu Lamiɗo yasa ta nufi gefen Abba cikin yanayin damuwa tace.

    “Alhj lafiya ya ake ciki Gawar waye kuka samu?”.

    Ahankali ya ɗago Idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur ya kalleta kana yayi ƙasa da kansa cikin raunin murya yace.

    “Gawar Jameelu na ne!”.

    Arazane Hajiya Turai ta kallesa zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi Idanunta akansa tace.

    “Gawar Jameelu kuma!?”.

    Kai ya gyaɗa mata Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu ta fashe da kuka me tsuma zuciya tana furta.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n ina gawar yake?”.

    Da hannu ya nuna mata kwalin dake gabansa.

    Da kallo tabi kwalin cikin sauri ta sake Kallonsa Idanunta cike da ruwan hawaye tace.

    “Gawar Jameelu ne acikin kwali haka?”.

    Kai ya gyaɗa batare daya ɗago kaiba yace.

    “Shine”.

    Wani sabon kuka ta fashe dashi tana Girgiza kai Kukanta ne ya fito da Hajiya Karima itama ganin abinda ke faruwa yasa ta fashe da kuka.

     

    Acan Asibiti kuwa ana kai Moddibo likitoci suka shiga bashi temakon Gaggawa saidai koda wasa bai farfaɗo ba ganin haka yasa suka dauƙo wani na’ura mai kama da Iron akafara danna masa aƙirji.

    Amman ina babu alamun zai motsa, sosai likitocin suka dugufa wurin ganin sun cetoshi, a karo na biyu suka kuma danna mishi a ƙirjunshi, amman ina, Dr Lukman ne ya karɓi aikin tare da goggoga jikin na’urar ya manna masa a kirjinsa da ƙarfi.

    Cikin ikon Allah yaja wani dogon numfashin sake dannawa yayi da karfi wani irin maraitaccen numfashi ya sake ja amma still bai farfaɗo ba sake dannawa sukayi akaro na biyar ne yaja wani dogon numfashi tare da buɗe idanunsa kana yace.

    “Jyyyyyyy”.

    Malam Arɗo da bai daɗe da dawowa daga gidan Abba bane,  yayi saurin riƙe hannunsa tare da cewa.

    “Moddibo kayi addu’a”.

    Duk da cewa baya Cikin nutsuwarsa hakan bai hanashi maimaita duk wata addu’a da tazo bakinsa ba ahankali ya ɗago kansa tare da kallon Malam Arɗo yace.

    “Malam J ɗina nefa!”.

    Jinjina kai Malam Arɗo yayi cike da tausayawa yace.

    “Eh shine Moddibo Allah ya karɓi Jameelu muyi masa addu’a Allah ya karɓi shahadarsa”.

    Girgiza kai Moddibo yayi tare da cije lips ɗin sa duka biyu, kana ya runtse Idanunsa cikin wani irin yanayi mai wuya yace.

    “Malam Arɗo mutuwar azaba suka masafa, ɗaure sa sukayi suka ajiye masa goran ruwan agabansa ta yanda yana ji yana gani bashi da damar sha sun barshi da azabar ƙishi”.

    Kallonsa Malam Arɗo keyi cike da tausayawa yana ganin yanda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.

    Cikin wata raunan’niyar murya Moddibo ya cigaba da cewa.

    “Malam ɗaure sa sukayi suka ajiye masa wayoyinsa agabansa ta yanda yana kallon muna kiransa bashi da damar ɗauka bare yace mukawo masa ɗauki”.

    Sai kuma ya rintse idanunsa da masifan ƙarfi zuciyarsa na cigaba da buguwa da masifaffen ƙarfi kana yace.

    “Ɗaure sa sukayi ta yanda yana ganin ga hanyar tsira sai dai bashi da damar kiran wani ya kawo masa ɗauki ɗaure sa fa sukayi ta yanda yana ganin kiran mu amma bashi da damar ɗauka”.

    Jujjuya kansa ya farayi kamar zautacce hawaye na bin gefe da gefen idanunsa har suna shiga kunnensa cikin Muryan kuka yace.

    “Ɗauresa fa sukayi ta yanda yana ganin kiran Abbansa bashi da damar ɗauka,Mutuwar azaba da raɗaɗi suka masa da ƙishi fa suka kasheshi”.

    Kasa ƙarasa maganar yayi kawai ya fashe da matsanancin kuka mai tafiya da numfashi Atake numfashinsa ya ɗauke ya sake sumewa!.

     

    Cikin sauri Malam Arɗo ya miƙe tare da kiran likitoci kana ya sanar dasu ya sake suma taruwa likitocin sukayi akansa kana suka shiga bashi temakon Gaggawa da kyar da temakon Allah suka samu ya farfaɗo ganin ya farfaɗo yasa Dr ya masa Alluran bacci Atake baccin wahala ya ɗauke sa.

    Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da miƙewa ya fita kana yayi dearling number Lamiɗo yana ɗauka yace.

    “Ranka shi daɗe yaron nan fa gashi agigice yake baki ɗaya da zaran ya farfaɗo sunan Marigayi Jameelu yake kira, yana kiran sunan kuma zai sake suma!”.

     

    Acan gidan Abba kuwa zaune yake afalonsa hannunsa riƙe da waya tunda suka dawo yake zaune awajen ya kasa koda motsawa se kwalin Gawar Jameelu daya zubawa Ido yana jujjuya wayar hannunsa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kiran number Ummi Yana Jin tayi picking ya fesar da numfashi kana yace.

    “Fatima”.

    Cike da mamaki Ummi tace.

    “Abban Jameel”. Jin muryansa.

    Cikin raunin murya ya sake cewa.

    “Fatima”.

    Anutse Ummi ta amsa da.

    “Na’am”.

    Runtse Idanunsa yayi kana yasake cewa.

    “Fatima”.

    Cikin dakiya Ummi da taji zuciyarta ya tsinke da Masifar ƙarfi tace.

    “Na’am Abban Jameel ka faɗa min me yasamu Jameelu na sun kira ne ko kuma yaya!?”.

    Cikin rauni yace.

    “Hmmm”.

    ya faɗa tare da katse kiran kana ya fito da Number Malam Ahmad.

     

    Malam Ahmad na ɗagawa Abba yace.

    “Malam kazo da Fatima da yaranta!?”.

    Cikin tsinkewar zuciya Malam Ahmad dake Bedroom ɗinsa ya miƙe tare da cewa.

    “Meya faru Alhj Bashir ka faɗa min”.

    Girgiza kai Abba yayi tare da taune lips ɗinsa kana yace.

    “Ga gawar Jameelu na agabana”.

    Cikin tsanananin tashin hankali Malam Ahmad ya dafe bango tare da faɗin.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha”.

    Katse kiran Abba yayi cikin sauri ya fito falon tsaye ya samu Ummi riƙe da waya a hannunta cikin ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin sa yace.

    “Fatima Lafiya!?”.

    Ahankali Ummi ta juya ta kallesa tare da cewa.

    “Yan zun nan Abban Jameel ya kirani, to kuma ya yanke gashi kuma ina ta sake kira naji line Busy”.

    Da ƙyar ya haɗiye wani abu mai masifar ɗaci  kana cikin ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yace.

    “Toh kada ki damu kizo muje muji meke faruwa”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Toh”.

    Sannan ta nufi hanyar fita.

    Kallon Bashir da Asma’u dake tsaye yayi kana yace.

    “Kuma kuzo mu tafi”.

    Kai suka gyaɗa kana suka bi bayansa suka fita.

     

    Suna isa falon suka samu Hajiya Turai da Hajiya Karima da ƴaƴan Hajiya Karima na kuka cikin sauri Ummi ta ƙara sa shiga falon tare da tsayawa agaban Abba kana tace.

    “Abban Jameel meye faru?”.

    Ahankali ya ɗago ido ya kalleta, sai alokacin yaji kuka ya kufce masa ganin Ummi agabansa baki ɗaya ta gigice jikinta na rawa.

    Cikin rawan murya tace.

    “Abban Jameel meyafaru!?”.

    Kasa cewa komai Abba yayi sai kuka da yake tamkar ƙaramin yaro.

    Da sauri Ummi ta juya tare da kallon yanda su Hajiya Turai ke kuka cikin rawan murya da yanayin tashin hankali tace.

    “Ku faɗa min mana meke faruwa!?”.

    Tayi tambayar baki ɗaya ilahirin jikinta na rawa.

    Asma’u da Bashir dake tsaye Atare suka fashe da matsanancin kuka ganin yanda ƙannen M Jameel ke kuka.

    Ahankali Malam Ahmad ya matso kusa da Ummi tare da cewa.

    “Fatima ki zauna”.

    Girgiza kai tayi kana tace.

    “Ni bazan zauna ba kafaɗa min abinda ke faruwa”.

    Cikin sanyin murya Lamiɗo yace.

    “Maman Jameel kiyi haƙuri ki zauna”.

    Kallon sa tayi tare da cewa.

    “In zauna?”.

    Kai ya gyaɗa mata kana yace.

    “Eh”.

    Cike da tausayawa Malam Ahmad ya janyo hannunta tare da zaunar da ita.

     

    Abba kuwa kallonta yayi cikin tsanananin fargaba da tashin hankali yace.

    “Fatima”.

    Cikin rawan murya da raunin zuciya tace.

    “Na’am Alhj Bashir”.

    Cikin sauri Abba ya kalleta wannan shine karo na farko arayuwar sa da yaji ta kira sunan shi kai tsaye.

    Jinjina kai tayi Idanunta tsaye akansa tace.

    “Eh Alhj Bashir ka faɗa min menene? kafaɗa meke faruwa”.

    Rintse idanunsa yayi yana jin kansa na sarawa Araunane yace.

    “Fatima Jameelun mu”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Eh nasani akan Jameelu ne to Menene ya faru?”.

     

    Kasa cewa komai Abba yayi kawai sai ya fashe da matsanancin kuka yayin da hawaye ke bin kuncinsa Shar-shar-shar.

    Cikin raunin murya yace.

    “Fatima ga Gawar Jameelun mu”.

    Atake maganar ya daki dodon kunnenta kana ya ratsa ƙwaƙwalwar ta zuwa zuciyarta saurin kallon Abba tayi tare da sakin Murmushi kana ta juya tare da kallon su Hajiya Karima dake kuka cikin wata dakakkiyar murya mai cike da ƙuna tace.

    “Toh kukan me kukeyi!?,

    Juyawa tayi tare da kallon Abban M Jameel kana tace.

    “Har kaima kuka kakeyi!?Haba Alhj Bashir Addu’a ya kamata ka masa amma ba kuka ba!, Su mata suyi kuka kaina kayi Yanzu ina yake?”.

    Cikin sheshsheƙan Kuka Abba ya nuna mata kwalin da ya tsarsa kana yace.

    “Gashi can”.

    Saurin Kallon wajen tayi Zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi still Muryanta adake da wani irin bushewa da hurawar zuciya tace.

    “Gawar ne kuma acikin kwali”.

    Cikin wata raunan’niyar murya ya Girgiza kai kana yace.

    “Kiyi haƙuri kiyi ta maimaita Addu’a”.

     

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da rintse Idanunta kana tace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakin La’ilaha Illah anta subhanaka inni kuntu Minal Zhalimin Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha³”.

    Ahankali ta gyara zamanta tare da naɗe ƙafafunta  tare da sakin murmushi kana ta fuskanci gabas yayin da Idanunta suka kaɗa sukayi jawur jikinta na wani irin tsuma na tsananin tashin hankali cikin raunin murya tace.

    “Ya Allah kaine ka bani Jameelu, kai kasa ya zamemini Garkuwa, ya Allah kajiƙan sa da rahma, ya Allah kasa ya huta Alfarman Annabi da Alkur’ani, Allah kayi mana SAKAYYAH akan dukkan waɗanda suka cutar damu ya Allah kayi mana SAKAYYAH”.

    Kusan a haɗe baki daya mutanen falon suka amsa da Ameen.

    Wani irin kuka mai tsuma zuciya ne ya kufcewa Asma’u da Bashir musamman Asma’u numfashinta har fisga yake baki ɗaya Falon kaurewa yayi da koke cikin rawan murya Ummi tace.

    “Ina gawar yanzu Jameelu na ne haka acikin kwali?”.

    Jinjina mata kai Abba yayi tare da cewa.

    “Eh shine”.

    Still Muryanta adake tace.

    “Wani irin mutuwa yayi da har gawarsa zata ƙankace ya zauma acikin kwali”.

     

    Asp dake tsaye ya kalli Ummi cike da tausayawa yace.

    “Hajiya kiyi haƙuri ya riga daya bushe, shiyasa ana taɓa shi ya kakkarye!”.

    Ahankali ta juya ta kalli Asp kana tace.

    “Toh ya akayi kuka tabbatar Jameelu na ne?”.

    Cike da tausayawa Asp ya ƙara sa gaban Kwalin kana ya buɗe mata ahankali Ummi ta tsirawa jerarrun gabɓan gawar dake cikin kwalin ido ahankali ta sauƙe Idanunta akan zara-zaran yatsun, hannunsa da suka bushe kana ta tsirawa zoben hannunsa ido.

    Cikin wani irin yanayi na ƙunan zuciya da sadaukarwa tace.

    “Hmmm!”.

     

    Ahankali Asp ya sake nuna mata takalmin M Jameel dake cikin leda da kuma wayoyinsa cikin sanyin murya yace.

    “Ga takalmansa da kuma wayoyinsa duk agabansa muka samu sun ajiye masa da goran ruwa.

     

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana tace.

    “Tabbas Jameelu na ne”.

    Ahankali ta matsa jikin kwalin sosai tare da sanya tafin hannunta ta rufe kana ta sunkuyar da kanta akan kwalin cikin Muryan ta daya fara karaya tace.

    “Babana bazan yi maka kuka ba, sannan baza zubar maka da hawaye ba, kana bazan yi maka Ihu da kururuwa ba, amma zan ƙarashe baki ɗaya sauran rayuwata ina maka addu’a, zan ƙare rayuwata da ƙunan rashinka zan ƙare rayuwata babban giɓin rashinka”.

     

    Wani irin tausayinta ya ratsa baki ɗaya jama’ar dake falon ahankali Malam Ahmad da Lamiɗo suka sanya hannu tare da share hawayen da suka saƙƙo musu.

    Cike da rauni Ummi ta cigaba da cewa.

    “Babana zan ƙare baki ɗaya sauran rayuwata ina maka addu’ar Ubangiji ya karbi shahadarka Allah ya maka SAKAYYAH tun daga nan duniya akan wa anda suka zalince ka har zuwa ranar tashin Alkiyama. Allah Ubangiji yajiƙan ka da rahma Allah ya gafarta maka yasa kahuta”.

    Cikin sauri Hajiya Turai ta ƙarasa kusa da ita tare da Rungumeta ajikinta kana cikin Muryan kuka tace.

    “Kiyi haƙuri Hajiya Fatima kiyi shiru”.

    Kallonta Ummi tayi still Muryanta adake tace.

    “Idan banyi haƙuri ba Hajiya Turai ya zanyi. Ubangijin daya ɗauke Jameelu shi yabani shi kuma shi ya ɗauke sa kana ya fini sanin wanene Jameelu agareni, sannan ya fini sanin Jameelu Allah ya masa rahma”.

    Ta ida maganar tare da janye Jikinta daga na Hajiya Turai tare da juyawa ta kalli Abba kana tace.

    “Ina Moddibo!?”.

    Tana gama fadar haka tayi baya tare da sumewa.

     

    Cikin sauri Hajiya Karima ta mike tare da ɗauko ruwa ta yayyafa mata dogon numfashi Ummi taja tare da buɗe Idanunta kana tace.

    “Ina Moddibo yake?”.

    Cike da tausayawa Abba yace.

    “Moddibo yana asibiti asume tunda abin ya faru daya farfaɗo idan ya kira sunan Jameel zai sake sumewa, yanzu ne da aka samu ya farfaɗo aka masa Alluran bacci”.

    Araunane tace.

    “Ku kaini inga Moddibo sannan kada aje abinne Jameelu abari sai Moddibo ya farfaɗo yaga J ɗinsa na ƙarshe ya tabbatar cewa J dinsa tafi ya barsa bari na har abada, idan yaga haka zai dangana ya sawa ransa haƙuri amma yanzu dan Allah ku kaini wajen Moddibo”.

    Abba ne yace.

    “Yanzu zaki tafi can?”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Eh ku kaini wajensa”.

    Ahankali Malam Ahmad ya miƙe tare da riƙe hannunta suka tafi.

     

    Asma’u da Bashir kuwa kuka suka sake fashewa dashi har muryarsu baya fita saboda tsananin tashin hankali.

    Rintse Idanu Abba yayi cike da tausayawa ya kallesu kana yace.

    “Ku daina kukan nan kuyi masa addu’a babu abinda Jameelu ke buƙata awajenmu yanzu kamar addu’a.

     

    Acan asibiti kuwa Ummi da Malam Ahmad na isa  a reception suka samu Malam Arɗo tsaye ganinsu yasa ya ƙara sa kusa dasu kana yace.

    “Maman Jameelu kiyi haƙuri. Ubangiji Allah ya jikansa da rahma Allah ya gafarta masa Ubangiji ya amshi shahadarsa”.

    Cikin sanyin murya tace.

    “Ameen Malam Arɗo ina Moddibo?”.

    Ahankali ya gyara tsayuwar sa kana yace.

    “Gashi can yana ciki”.Ya faɗa tare da shiga gaba Ummi da Malam Ahmad na biye dashi.

    Suna shiga ɗakin Ummi ta zubawa Moddibo idanu dake kwance plat Fuskarsa tayi fayau duk da bacci yake amma tashin hankali da fargaba ne kwance asaman fuskarsa.

    Ahankali ta riƙe hannunsa acikin nata kana tace.

    “Moddibo munyi rashi, rashin da baza mu maimaita gurbinsa ba, munyi rashi rashin da har abada ba zamu mance shiba, munyi rashi rashin da saidai namu mutuwar ne zai mantar mana dashi”.

    Moddibo kuwa duk da Alluran baccin dake jikinsa hakan bai hana shi jiyo sautin muryan Ummi ba. So yake ya farka domin kunnuwansa na sauraronta haka zalika yana iya motsa gaɓɓansa sai dai koda ya buɗe idanunsa baya ganin komai cikin wani irin yanayi ya damƙe hannun Ummi acikin nasa, yayinda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da masifar ƙarfi.

    Kallon Malam Ahmad Malam Arɗo yayi kana yace.

    “Toh tunda kunzo bari na wuce na faɗawa Kakarsa halin da ake ciki”.

    Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.

    “Ya kamata kam aje afaɗa mata sannan itama ataho da ita”.

     

    Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana ya juya ya fita kai tsaye gidan su Moddibo ya nufa yana isa yayi Parking ɗin motarsa kana ya shiga gate din farko ya daga sautin muryarsa tare da yin sallama.

    Cikin sauri Innayi ta fito ganinsa yasa ta saki Ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Alhamdulillah dama yanzu nake tunanin in kira ka dan. Moddibo tun safe daya fita bai dawo ba, duk da cewa dama yanzu bai cika dawowa da wuri ba”.

    Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe kana yace.

    “Ki zo mutafi”.

    Saurin Kallonsa tayi kana tace.

    “Ina zamuje”.

    Cikin sanyin Murya Malam Arɗo yace.

    “Wajen Moddibo zamuje yana asibiti”.

    Da sauri ta dafe ƙirjinta sai kuma ta juya ta nufi cikin gida hijabinta ta ɗauko ta sanya kana ta rurrufe kofofin gidan kafin ta fita.

    Bayan sun fara tafiya acikin motar Malam Arɗo ya kalli Innayi kana yace.

    “An samo gawar Jameelu fa!”.

    Cikin tsanananin ruɗu da tashin hankali ta dafe ƙirjinta tare da faɗin.

    “Gawar Jameelu kuma?”.

    Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana yace.

    “Eh gawar Jameelu aka samu sun kashe sa”.

    Atake hawaye suka shiga zubowa Innayi cikin tashin hankali da jimami ta saki sassayan kuka tare da addu’o’i.

     

    A dai daren wannan ranar haka kowa ya kwana cikin ƙunci da raɗaɗi azuciya.

    Asp da tawagarsa sun koma gida bayan sun gama dukkan abinda ya dace na bincikensu, haka zalika  Lamiɗo ma ya koma gida Abba kuwa kwana yayi da gawar Jameelun sa agabansa batare daya rintsa ba.

     

    Asma’u kuwa Hajiya Turai ta jata zuwa ɗakinta Anan ta kwana duk da cewa ba tayi bacci ba.

    Bashir kuwa aɗakin ƙannen M Jameel ya kwana tare dasu Aɓangaren Moddibo kuwa haka ya kwana cikin wani irin yanayi shi ba bacci ba kuma kuma shiba Ido biyu ba ba kuma a sumeba.

    Ana kiran Assalatun Farko acikin kunnen Moddibo sannu Ahankali ya fara bude idanunsa da yaji sunyi masifar nauyi har ya sauƙesu akan Ummi dake riƙe da hannunsa Idanunta abushe alamar ko rintsawa ba tayi ba bare kuma bacci.

    Cikin wata murya mai cike da karaya da kuma rauni yace.

    “Ummi”.

    Kallonsa Ummi tayi tare da faɗin.

    “Na’am Aliyu”.

    Girgiza kai yayi yayinda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da masifar ƙarfi yace.

    “Ummi J ɗina”.

    Cike da tausayawa ta rintse Idanunta kana tace.

    “Aliyu kayi haƙuri”.

    Cije Lips ɗinsa yayi tare da damƙe hannunta acikin nasa kana yace.

    “Ummi J ɗina”.

    Jinjina kai tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya tace.

    “Kayi haƙuri kaje kayi sallah duk abinda kake ji Aranka kana so ka faɗa min ka faɗawa Ubangiji”.

     

    Cikin sauri Malam Ahmad dake tsaye ya ƙara so bakin gadon tare da riƙe hannun Moddibo cikin sanyin murya yace.

    “Kayi haƙuri kaje kayi alwala”.

    Kallon Malam Ahmad Ummi tayi kana tace.

    “Toh ni yanzu zan tafi gida”.

    Girgiza kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.

    “A’a ki bari mu tafi gidan Alhj Bashir yanzu”.

    Girgiza kai tayi kana tace.

    “A’a mu tafi gidanmu dai”.

    Girgiza mata kai yayi kana yace.

    “A’a gidan Alhj Bashir zamu je acan fa za ayi jana’izar mu tafi can ɗin!”.

     

    Shiru kawai Ummi tayi ahankali.

    Moddibo da har yanzu hannunsa ke cikin nata yace.

    “A’a Ummi dan Allah muje gidan Abba”.

    Kai ta gyaɗa masa cikin sanyi tace.

    “Toh shikenan”.

    Batare da an sallamesu ba suka fita Moddibo da Malam Ahmad suka shiga gaba Ummi tashiga baya Anutse Malam Ahmad yayiwa motar key kana yaja suka bar Asibitin kai tsaye gidan Abba suka nufa suna isa Malam Ahmad ya danna hong ta cikin ƙaramin ɓulin. Mai gadi ya leƙa jin ana ta danna hong ganin motar da tazo jiya da safe ne yasa ya koma cikin gida tare da sanarwar Abba yaga motar da jiya tazo yauma ta dawo.

    Kai Abba ya gyaɗa kana yace.

    “Eh kaje ka buɗe musu Maman Jameel ne yanzu aka sallame su daga asibiti kaje ka buɗe musu”.

    Kai ya gyaɗa sannan ya buɗe musu gate din suka shiga bayan Malam Ahmad yayi Parking suka fito kai tsaye falon Abba suka shiga.

    Zaune suka samesa shi kaɗai a falon hannunsa riƙe da Carbi ya tsirawa kwalin Gawar Jameel Ido.

    Ahankali Ummi ta ƙarasa tare da zama agefen kwalin shima Moddibo zama yayi agefen kwalin Malam Ahmad ma ya zauna agefen kwalin sai ya zamana sun saka kwalin Atsakiyar su.

    Moddibo kuwa kallon kwalin yayi kana ya kalli Ummi cikin raunin murya yace.

    “Ummi yanzu J ɗinane aciki?.

    Ummi da gaske J ɗina ne ya rasu!?”.

    Kai Ummi ta jinjina kana tace.

    “Da gaskene Moddibo, tabbas Jameelu ne yarasu Jameelu ya tafi yabar mu bari na har abada, ba zamu sake ganinsa ko jin sautin muryarsa ba sai dai ahoto”.

    Girgiza kai Moddibo yayi tare da ɗaura kansa akan kwalin ya fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya cikin sheshsheƙan Kuka yace.

    “Yanzu shikenan J ɗina mun rabu har abada bayan yana burin yin Aure ya zauna gida ɗaya da Ummi da ƙannensa yanzu shikenan wannan burin ya tafi”.

    Ya sake Rungume Kwalin tare da cewa.

    “Yanzu shikenan J ya tafi ya barni shin dawa zan rayu duk wani farin ciki ne da walwala na J ɗina ne shin waye zai fahimcini a duniya? J ɗina ne kaɗai yake iya fuskarta halin da nake ciki shikenan sun rabani da aminina kuma farin cikina!”.

    Wani irin tausayinsa ne ke ratsasu Abba kam kasa daure wa yayi ya sunkuyar da kansa ƙasa hawaye na zuba.

     

    Cikin sheshsheƙa Moddibo ya ɗago kansa tare da kallon Ummi idanunsa cike da ruwan hawaye yace.

    “Shikenan Ummu sunyi mai kisan gillah, sun hanashi shan ruwa, ya mutu da kishi da begenmu, yana ganin muna kiransa amma bashida damar ɗauka, Ummi ashe duk kiran da mukewa J yana kallon kiran mu!”.

    Sai kuma ya kife kansa akan kwalin hawayen sa na sauka akai yace.

    “Ummi J yana ganin kiran mu amma bazai iya ɗagawa ba Ummi sun azabtar da J ya mutu da tsananin begenmu da muradin son kasancewa damu Ummi sun cutar da J mutumin da koda ƙwaro baya iya cutarwa bare bil adam shin wani irin zunubi suka aikata!”.

     

    Jin ankira assalatu yasa Malam Ahmad sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Moddibo kayi haƙuri ku tashi muyi alwala mu tafi masallaci”.

    Ahankali Moddibo ya ɗago kansa akan kwalin daya jiƙe da hawayensa cikin ransa yace shikenan J ya tafi yabarni bari na har abada shikenan ni kaɗai zan rayu.

    Hajiya Turai ce ta shigo falon tare da jan Ummi suka tafi ɗakinta Anan sukayi sallah.

     

    Dole Gawar M Jameel yanda ya kasance a kakkarye ahaka aka yayyafa masa ruwa madadin wonkan kana aka kaisa makwancinsa na gaskiya.

    Jana’izar data samu halarta ɗumbin jama’ar domin kafin gari ya waye mutuwar ta zagaye cikin Gembulan da kewayenta har Taraba Yola da dai sauransu.

     

    Rayuwa tayiwa duk wani makusancin M Jameel ƙunci da zafi musamman Ummi, Abba, Moddibo, Asma’u, Bashir daga Jiya zuwa yau sunyi wani masifaffen ramewa kallo ɗaya zaka musu kasan cewa suna cikin tsananin ƙuncin rayuwa musamman Moddibo baki daya ya fita cikin hayyacinsa duk ya gigice ya sake zama wani shiru.

     

    Misalin ƙarfe biyu na rana bayan andawo daga sallar jana’izar M Jameel Lamiɗo ya koma gidansa kai tsaye falon Mommy ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama.

    Anutse Mommy da Khausar dake zaune suka amsa masa Sallamar.

    Cike da kulawa Mommy tace.

    “Sannu da zuwa yinin yau duk baka nan sau biyu ina zuwa sashenka”.

    Zama yayi akan 3sitter tare da sauƙe ajiyar zuciya kana ya jingina bayansa da jikin kushin ɗin tare da lumshe idanunsa kana yace.

    “Eh yanzu na dawo daga jana’iza”.

    Cikin sauri ta kallesa tare da cewa.

    “Jana’iza kuma?”.

    Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

    “Eh”.

    Gyara zama tayi tare da faɗin.

    “Janaizar waye!?”.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da dafe kansa kana yace.

    “Janaizar Jameelu”.

    Cikin sauri Khausar ta dafe ƙirjinta tare da kallon Lamiɗo kana tace.

    “Abbah waye”.

    Kallonta Lamiɗo yayi kana yace.

    “Malam Jameelu”.

    Cikin tashin hankali Mommy tace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Jameelu Yayan Asma’u”.

    Kai Lamiɗo ya gyaɗa kana yace.

    “Eh shi ɗin dai Allah ya masa rasuwa”.

    Cike da kaɗuwa tace.

    “Innalillahi Ayyah Ummin Asma’u Allahu Akbar duniya yanzu yaron nan kashesa sukayi”.

     

    Khausar kuwa tunda ta dafe hannunta aƙirji ta kasa koda ƙokƙwaran motsi ne wani irin bugawa da masifaffen ƙarfi zuciyarta keyi.

    Atake wani irin kuka mai tsuma zuciya ya kufce mata cikin sheshsheƙan kuka mai cike da tausayi da tashin hankali tace.

    “Abba Yaya Jameel ya rasu!? Abba kashe Yah Jameel sukayi? Abba me yayi musu da zasu kashesa, suka rabasa da rayuwarsa”.

    Kai ya gyaɗa mata kana yace.

    “Eh Khausar sun kashesa kisa mafi ciwo”.

    Sau kuma ya zayyane musu yanda suka samu labarin har suka je wajen da kuma yanda suka samu gawar.

    Cike da tausayawa Khausar ke jujjuya kai tana cigaba da kuka yayinda numfashinta ke sarƙewa.

     

    Kallon Mommy da hawaye ke kwaranya daga idanunta Lamiɗo yayi kana yace.

    “Tun jiya ne, ai muka samu gasar, ban dai faɗa muku bane, dan kada in hanaku bacci.

    Yanzu ku shirya anjima idan anyi Sallar La’asar zan kaiku gidan kuyi musu ta’aziyya”.

    Cikin muryan kuka Mommy ta gyaɗa masa kai cike da rauni tace.

    “Ayyah Ummin Jameel ta ɗandani mutuwa me raɗaɗi da ƙunan zuciya”.

    Ta faɗa tana tuno Ramadan domin ko Rasuwar Ramadan bata samu tayi kuka haka ba bayan Lamiɗo ya sake rarrashin sune ya miƙe ya nufi sashen Hajiya Bunayya ya sanar mata.

    Khausar kuwa Kuka takeyi tamkar zata mace.

     

    Bayan anyi sallar La’asar Lamiɗo ya ɗebe su suka tafi gidan Abba.

     

    Suna zuwa falon Hajiya Turai suka nufa Cikin gidan da falon cike yake da mutane ƴan ta’aziyya duk wanda yaji rasuwar M Jameel da kuma yanda aka samu gawarsa saiya zubda hawaye tare da la’antar wa anda suka aikata masa haka.

     

    Asma’u dake gefen Ummi zaune Idanunta cike da hawaye tana ganin Khausar ta fashe da sabon kuka kana ta miƙa mata hannu cikin sauri Khausar ta kamo hannunta tare da zama gefenta ta.

    Rungume juna sukay tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya.

    Mommy da Hajiya Bunayya kuwa kusa da Ummi suka zauna.

    Mommy na Kallon Ummi taji wasu sabbin hawaye sun zubo mata cike da tausayawa Mommy tace.

    “Ummi Sannu”.

    Sunkuyar da kai Ummi tayi cike da dauriya tace.

    “Toh ya zamuyi Aysha ya zamuyi da hukuncin Ubangiji.

    Jameelu ya riga mu gidan gaskiya ya tafi ya barni da gurbin da bansan ya zai cikeminba”.

    Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.

    “Kiyi haƙuri Ummi”.

    Kasa ƙara sawa tayi sabida kuka yaci ƙarfin ta kawai saita kife kanta gefen Ummi ta shiga rera kuka.

    Ajiyar zuciyar Ummi ta sauƙe cikin sanyin murya me ɗauke da ƙuna tace.

    “Kiyi haƙuri Aysha haka Ubangiji ya tsara bamu isa muja da lamarinsa ba addu’ar mu suke buƙata muyi musu addu’a Allah ya gafarta musu”.

    Cikin sheshsheƙa Mommy tace.

    “Ameen”.

    Ahankali Mommy ta juya suka gaisa da Hajiya Turai da Hajiya Karima sannan da ƙannen Abban Jameel Hajiya Maryam da Hajiya Fa’iza suka yi musu ta’aziyya.

     

    Khausar dake Rungume da Asma’u cikin Muryan kuka tace.

    “Asma’u yanzu da gaske Yah Jameel ya rasu shikenan ya tafi ya barmu!”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa tare da cewa.

    “Da gaske Khausar Yah Jameel ya rasu shikenan gatanmu ya rasu rufin asirin mu ya tafi garkuwan mu ya barmu Inuwarmu wajen fakewar mu ya gushe, bangon da muke jingina muji daɗi ya fadi ƙasa”.

    Kasa ƙara sawa tayi kawai ta fashe da kuka me tsuma zuciya.

    Cikin sauri Ummi ta girgiza mata kai Araunane tace.

    “Kul Asma’u!,Kada ki faɗi haka kada kiyi butulci ga Ubangiji domin shi ya bamu Jameelu kuma shi ya ɗauke mana shi kuma zai jibanci laluranmu muddin mukayi tawakkali”.

    Innayi dake gefe ta matso kusa da Asma’u da Khausar ta janyosu jikinta tare da ɗaura kansu akan cinyarta cikin Muryan rarrashi tace.

    “Kuyi haƙuri kuyi masa addu’a”.

    Ahankali Khausar ta ɗago tare da kallon Innayi kana tace.

    “Innayi yanzu shikenan Yah Jameel ya tafi ya barmu har abada baza ku sake ganinsa ba!? Bazai sakeyi mana nasihaba, bazai sake neman al’farma a wajenaba ashe Yah Jameel Wasiyya yayi ta barmin a wancar ranar”.

    Shafa kanta Innayi tayi kana tace.

    “Khausar kada kiyi kuka muyi masa addu’a shine abinda yake buƙata awajenmu kana mu cika masa dukkan wasiyar daya bar mana”.

    Kai Khausar ta gyaɗa kana ta cigaba da kuka mai ciwo har Idanunta suka kumbura.

    Sai Bayan sun idar da Sallar Maghariba kafin Lamiɗo ya ɗebe su suka tafi

    A wannan daren ranar baki ɗaya haka suka kwana cikin ƙunci zuciya da alhini Moddibo kuwa baya um bare Um-um ko awajen zaman makoki idan akace masa sannu baya magana saidai kallo sai ance Allah ya jikansa kafin yace.

    “Ameen ya Allah Nagode”. Iya abinda yake iya faɗi kenan.

     

    Haka rayuwa tayi musu ƙunci da ɗaci haka aka ɗauki tsawon kwanaki bakwai ana zaman makoki har awannan kwanaki kullum cikin gida da waje a cike yake da masu zuwa ta’aziyya.

    Washe garin rana ta takwas da safe Moddibo na fita bai nufi ko ina ba sai gidan Ummi bakinsa ɗauke da Sallama yashiga falon zaune ya sameta hannunta riƙe da carbi ta zubawa waje ɗaya ido.

    Jin Sallamar sane yasa ta ɗago kanta tare da tsira masa Ido agefenta ya zauna.

    Cikin sanyi tace.

    “Babana”.

    Ahankali yace.

    “Na’am Ummi”.

    Cike da tausayawa Ummi tace.

    “Babana kalli yanda ka sake dawowa fa yaushe zaka sawa ranka dangana ne? Kadafa muyi abinda Allah bayaso”.

    Batare da yace Uffan ba yayi ƙasa da kansa yana jin wani irin zafi azuciyarsa.

    Jin muryarsa yasa Asma’u dake Bedroom ta fito tare da zama agefensa kana ta gaishesa.

     

    Ahankali Moddibo ya juya ya kalli Ummi kana yace.

    “Ummi yanzu a Duniya babu abinda nake buri daya wuce ingano su waye suka sace J sannan suka yi masa kisan gillah ina so insani. Ummi inaso inyi bincike akai ina so inga lallai a hukunta su kwatankwacin zalinci da suka mana”.

    Ajiyar zuciya Asma’u ta sauƙe tare da cewa.

    “Aikuwa Yah Moddibo Khausar tana da dan abinda ta sani.

    Domin ranan da muka rabu da Yah Jameel na karshe aranan ne ya maida Khausar gida kuma tace mana.

    Taga wata mota na binsu.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tace.

    “Amma Babana Meye amfanin bincike bayan sun kashesa!?”.

    Cikin sauri yace.

    “To ai Ummi nan nema yake da amfani tunda suka kashesa dama mun biye musu ne saboda munji tsoron kada su kashesa shiyasa mukabi tsarinsu!”.

    Girgiza kai Ummi tayi kana tace.

    “Toh amma dai ni inaganin barin shi yafi A’ala kada kai ɗinma da ka rage mana su cutar mana da kai”.

    Sam Ummi ta rigada ta saki komai na duniya shiyasa duk yadda yaso ayi mgnar a sake buɗe file din binciken taki.

    Fahimtarsa bazata yardabane yasa ya nuna mata ya hakura.

    Kallon Asma’u yayi tare da miƙewa kana yace.

    “Asma’u zamuyi magana”.

    Kai ta gyaɗa sannan ya fice.

     

    Yau ya kama sati biyu da rasuwar Ramadan wanda yayi daidai da kwanaki sha biyu da jana’izar M Jameel.

    Acan gidan Lamiɗo kuwa da misalin karfe sha biyu na rana Hajiya Ruƙayya da Mommy da kuma Khausar na zaune afalo suna hira kamar daga sama suka jiyo Sallamar Hajja Nana da faɗin.

    “Assalamu Alaikum”…!

     

    *Kada kyiwa labarin bahagon fahimta. Wasu abubuwa na cikin Labarin gaba ɗaya gaskiyane ya faru da gaske. Ina mai roƙonku da Allah kuyiwa Jameel Addu’o’i Allah ya jiƙamsa da rahama ya kuma toni asirin waɗanda sunka saceshi suka kasheshi kisa mai muni. Ku sashi a addu’o’i ku, domin Wallahi tallahi rasuwar Jameel gsky ne kuma ya faru, da gaske wanda nasan mafi akasarin mazauna Adamawa zasu san labarin rasuwar Jamilu matashi mai Kekkyawan ɗabi’un sun kashewa sun bar mahaifiyarsa da ƙunshin a zuciya, sun sa mahaifinshi a rauni mai ciwo. Yah Allah ka jiƙan Jamilu kayi masa rahama da gafara, ka tausashi zuciyar iyayensa ka ƙara zamewa mahaifiyarsa Gatan*

     

     

    🤝🏻KADA KUMA KU DAMU ZAKUSHA MAMAKIN YADDA LABARIN ZAI SAKU FARINCI DA SHAUƘI ZAKUSHA MMKIN YADDA LAMARIN ZAI BADA CITTA, KU DAI KU BIYONI KUSHA LABARI, WACCE BATA BIYA TA BIYA.

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 10

    Sakayyah 10

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page10_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *NA DAI FA KUSA GAMA FREE PAGE, SAURA KAƊAN. Yar uwa baki makara ba ki biya ki karanta cikin Aminci, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Kana in saki a Groups ɗin dana buɗe na littafin SAKAYYAH wanda in dai ba a cikinsa kikeba toh yar uwa na sata kike gani. Amman na yanzu dai Free page ne*

     

     

    Ita kuwa Khausar Jinjina kanta tayi, yayin da idanunta ya cika da ruwan hawaye aranta tace.

    “Ta Allah bata ku ba amma kam yardan da Mommy na tayi miki ya ƙazanta ta gaza gane cewa ke ɗin kara da kiyashi ne ɗaukar rashin sani.

    Sai kuma ta juya cikin mutuwar jiki ta juya ta koma falon nasu bakinta ɗauke da Sallama.

    Zaune ta samu Mommy afalo Idanunta alumshe yayin da ta jingina bayanta da jikin kujeran.

    Ƙara sawa kusa da ita Khausar tayi tare da zama tace.

    “Mommy yadai baki shiga kichen ɗin ba?”.

     

    Ahankali Mommy ta ɓude Idanunta dake lumshe kana tace.

    “Wallahi Khausar bacci nake ji duk jikina babu ƙarfi!”.

    Jinjina Kai Khausar tayi cikin sanyu tace.

    “To kiyi baccin Mommy bari nashiga kichen nayi girkin”.

    Kai Mommy ta gyaɗa still Idanunta alumshe tace.

    “Toh”.

    Juyawa Khausar tayi ta shiga kichen ajikin sink din ta jingina asaman laɓɓanta tace.

    “Kenan yawan baccin da Mommy na keyi kwanan nan, ciki ne da ita wanda Hajiya Bunayya ke ƙoƙarin zubarwa”.

    A hankali ta saki Ajiyar zuciya da faɗin.

    “Allah mai iko”.

    Sai kuma ta juya ta ɗauki tukunya tasa ruwa ta ɗauraye cikin sannan ta tari ruwa da yawa aciki tarufe Sannan ta juya ta kunna Gas ta ɗaura ruwa,

    Jiki a mace ta buɗe drower Na’a na’a ta ɗiba tare da citta, kanamfari, da masoro kaɗan, gyara su tayi kana ta ɗaureyesu sannan ta saka cikin tukunyar.

     

    Doya ta ɗauko manya guda huɗu, ta fara ferewa.

    Hummmm taja sassayan numfashi lokacin da taji tea ɗin data ɗaura yanata baza ƙamshi alamun ya dafu, da sauri ta ƙarasa free doyan, kana ta wonkesu fes bayan ta rarraba su.

    Hannunta ta ɗauraye bayan ta stabtace wurin da ta feren.

    Flacks ta ɗauko guda huɗu cikasu tayi baki ɗaya, kana ta maidasu wurin zamansu.

    Wannan  tukunyar ta kuma ɗaurayewa kana tasa ruwa ɗan madaidaici.

     

    Doyan ta ƙara sassarewa tayisu yan ma dai-dai-ta dai’dai sawa a baki, kana ta kuma wankewa ta tsanesu, kana ta juyeshi a tukunyar, gishiri ta ɗan tarfa a kai, sannan ta rufe tukunyar tare da ɗan dai-dai-ta wutan.

     

    Drower gefen dama ta ta kuma buɗe wa, wani farin roba ta jawo mai cike da ƙuli-ƙuli irin dogayen nan plate ta ɗauka saida ta cikashi kana ta maida ta rufe.

    Sannan ta ɗebi borkono dai-dai misali.

    Tasa a turmi kana ta sa kanamfari tare da Maggi star,  Noo, Tera, Rayco, da dai sauransu, dakasu tayi , sannan tasa ƙaragon duk ta haɗa su ta dake su luƙui.

    Kana ta kwashesa a wasu ƴan robobi masu masifar kyau da yan marafensu guda huɗu.

     

    Fridge ɗin dake gefenta ta bude ta dauko goran ma shanu, ɗan wani tukunyan ƙasa ta ɗauka tare da tsulala manshanun,

    Daya gefen ta kunna gas ɗin, kana ta ɗaura, sai kuma ta ɗauki manyan albasa har guda huɗu, gyarasu tayi kana ta yayyankasu.

    Tukunyar da doyan ke ciki ta buɗe,

    Kai ta jinjina ganin ya kusa dafuwa, da sauri ta watsa rabin albasan da ta yanka ɗin a kai.

    Kana ta maida marfin ta rufe, tare da rage wutan.

     

    Ɗan ludayi, tasa cikin man shanun jin ya daina bada sauti alamun ruwan ciki ya ƙare, sake raba albasan biyu tayi ta watsashi cikin man shanun.

    Hhummmmmm taja wani dogon numfashi sabida wani irin masifeffen ƙamshi mai tsinka yawun mutun daya buɗe illahirin gidan.

    Kashe wutan babbar tukunyar tayi dan ya dafu albasar, ta razanu.

     

    Kana ta ɗauko kulli ta kwashe na sashin Hajia Bunayya tare dana Gimbiya Dadu.

    Sai kuma na Abbansu,

    Sannan na side dinsu.

    Sauƙe man tayi kana ta cire wannan albasan daya fara ƙonewa, sai kuma ta juye wannan sauran, shuyuuuu ya bada sautin soyuwa da zafin man.

     

    ɗaya daga cikin manyan ƙullin naman dake cikin fridge ta ɗauka mai sokoki zalla anyi ta kansu dogo-dogo.

    Ɗaurayewa tayi tasa a yar madaidaicin tukunya ta zuba naman,

    dama already ta jajjaga ɗanyen citta da tafarnuwa ta buɗe ta zuba aciki sannan ta Marmasa Maggi da time kana ta jajjaga attaruhu da albasa ta zuba tare da diban man shanun data soya ta watsa a ciki da duk sauran spices,Cikin Mintuna kaɗan kichen ɗin ya ɗauki mayataccen ƙamshin girkin dana man shanu daya wadata aciki zazzafan gashin da takeyiwa Abban.

     

    Mommy kuwa ahankali ta miƙe tashiga kichen ɗin Idanunta akan Khausar dake wanke yan kwanunkan data ɓata, cikin alamun bacci tace.

    “Ƙamshin girkin ki ne ya tasheni da gaba baccin.

    nazo in tayaki gashi kuma naga kamar ma kin gama”.

    Murmushi Khausar tayi tana motsa gashin naman mai romon da takeyi wanda tuni yanata ɓararraka kai ta jinjina kana tace.

    “Mommy kije ki huta nama gama fa”.

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “A’a kada ki damu ai baccin ya sakeni”.

    Kai kawai Khausar ta gyaɗa sannan ta cigaba da aikinta tana sauƙe gashin Mommy ta taimaka mata suka  juye kulan Abba da kuma na Dadu, saura kuma suka sawa Hajia Bunayya saura kuma suka barwa kansu.

    “Yauwa ɗauki na Ummanki ki kai mata”.

    cewar Mommy, cikin sauƙe numfashi Khausar ta ɗauka bayan ta sa jera yan robobin man shanun da yajin ƙuli-ƙulin, sai yar kulan gashin naman.

    Kana ta nufi sashen bakinta ɗauke da sallama tashiga.

    Amina dake zaune riƙe da waya ahannu ta watsa mata kallon tsana batare data amsa sallamar taba tace.

    “Agola kin zo kina wani tunƙaho kamar gidan tsohonki ne Masarautar very soon zaki bar gidan nan dan nafi ƙarfin nayi shearing abinda nake so dake”.

    Ya mutsa fuska Khausar tayi tare da jan siririn tsaki tace.

    “Iska na wahalar dame kayan kara wannan ƴar masarautar kike mgn a kai har wata siyace”.

    tana ida maganar ta fice batare data jira jin abinda Amina zata ceba.

     

    Kai tsaye kichen ta nufa tsaye ta samu Mommy tana ɗauraye tukwanen da Khausar tayi amfani dashi kallon ta tayi tace.

    “Ki ɗauki kular Gimbiya Dadu ki kai mata”.

    Langwaɓar da kai Khausar tayi tace.

    “Ayyah Mommy Haiydar ya Kai mana”.

    Juyawa Mommy tayi ta kalleta da faɗin.

    “Wai Khausar Meyesa idan na aike ki sashen Gimbiya Dadu sai kice in aiki  Haiydar bana jin daɗin abinda kike min fa wato kina nuna min cewa ke ba jikarta bace?”.

    Girgiza kai Khausar tayi tace.

    “Wallahi Mommy Ina tsoron zuwa wajenta bana shiri da ita”.

    Kallon Mamaki Mommy tayi mata kafin ta watsa mata harara da faɗin.

    “Rufe min baki zakiji tsoronta ita ɗin kurace? wato kinje kakar ki tasa Miki ra’ayi da batun cewa ita Mayya ce da sauransu ko?”.

     

    Girgiza kai Khausar tayi Idanunta cike da ruwan hawaye aranta tace. har yanzu Mommy ba zata gane ba taya zan ganar da ita cewa ni kaina na gamsu da cewa matar nan Mayya ce.

    Amma nasan kona faɗa ba zata yarda ba dan yanda take haƙiƙan cewa akan ba Mayya bace ko ‘ya‘yan cikinta basa haƙiƙan cewa akan hakan, ita babu dama ace Gimbiya Dadu Mayya ce bayan ni da kaina naga alamomin hakan kuma ya fito da bakinta ta faɗa min ita Mayyace kawai ya rage amma sam Mommy taƙi yarda idan taji mutum ya fadawa Gimbiya Dadu Mayya aita bala’i da ita se kace Uwarta aka kira Mayya.

     

    Ita kuwa Mommy ganin yanda Khausar ta tsirawa waje ɗaya idanu yasa aɗan fusace tace.

    “Khausar ba magana nake Miki ba ko baza kije bane Inje da kaina?!”.

    Asanyaye tace.

    “Ayyah Mommy kiyi haƙuri zanje”.

    Ta Faɗa tare da ɗaukar kulan ta fice tana furta.

    ”اعذبكلمتلله تممت منشررم حلق“.

    Bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon akan darduma taga Gimbiya Dadu na sallar maghariba cikin sauri ta ajiye kular.

    Ita kuwa Gimbiya jin Muryan Khausar yasa cikin hanzari tayi sallama batare data idar ba ta juya ta zuba mata Na mujiya.

    Ita kuwa Khausar cikin sauri ta juya ta fice daga sashen ta nufi sashen su tana sakin Ajiyar zuciya sai kuma ta furta.

    “Alhamdulillah”.

    Sosai tayi farin cikin tarar da Gimbiya Dadu tana Sallah.

    Koda ta shiga Falon nasu bata samu Mommy ba da alama tana ciki tana sallah kai tsaye Bedroom ɗin su ta wuce tare da shiga toilet bayan tayi addu’a.

    Anutse tayi alwala tare da fitowa da ƙafar dama.

     

    Darduma mai taushi dake fitar da sanyayyan ƙamshi ta shimfiɗa kana ta sanya dogon hijabinta ta fuskanci alƙibla cikin nutsuwa tare da maida komai zuwa ga mahalicci ta gabatar da sallah bayan ta idar ta ɗaga hannunta biyu sama tare da lumshe Idanunta cikin tsantsar nutsuwa tare da ladabi alokacin neman wani buƙata ga Ubangiji mabuwayi gagara Misali ta ɗaga hannunta biyu tace.

    “Ya waduud,Ya zul’arshil Majeed,Ya fa’alil lima yureed As’aluka bi izzatil lati la yura wa mulki kallazi la yurad wa nuru wajihikallazi mala alkana arshik najjini min hazal mujrimin  ya Allah ka tsare min mahaifiyata da abinda ke cikinta daga sharrin Mai sharri”.

    ta faɗa tare da shafawa Alkur’ani ta ɗauka ta fara Muraja’a tun daga Kahf sai data je Hajj kafin ta tsaya ta miƙe ta ida da Isha’i awajen ta kishingiɗa da haka bacci ya ɗauke ta.

     

    Washe gari juma’a Khausar na zauna afalon Mommy akan Lallausan Capet yayin da Mommy ke saman kujera Khausar na matsa mata ƙafafunta ahankali Khausar ta ɗago kai tare da kallon Mommy da Idanunta ke lumshe tace.

    “Mommy wallahi nayi missing Hajja Nana, Baffa Jauro Sadik, Dije duka mutanen Rugar ma nayi kewarsu gashi babu network bare nakira naji Muryansa”.

     

    Murmushi Mommy tayi tare da jan numfashi kana ta buɗe Idanunta dake lumshe tace.

    “Lalle kam Khausar yau kece ke faɗin Kinyi kewar Hajja Nana da bakin ki?”.

     

    Murmushi Khausar tayi wanda ya lotsar da dimple ɗin ta kana tana cigaba da yiwa Mommy massaging ƙafafunta tace.

    “Allah tana da daɗin zama kawai dai faɗanta da kuma mulkin mallaka da take nunawa yasa bamu jituwa amma tanason Babana da yawa sannan tana masa addu’a ni kuwa kinga duk mai yiwa Babana addu’a ina ƙaunarsa”.

    Ta ƙarashe tare da buɗe Idanunta dake lumshe wanda ruwan hawaye ya cika su.

    Shafa kanta Mommy tayi tare tace.

    “Ubangiji Allah yajiƙan sa da rahma Allah ya gafarta masa Ubangiji ya jiƙan dukkan musulman da suka rigamu gidan gaskiya”.

    Sanyayyar Ajiyar zuciya me haɗe da kyewa Khausar ta saki kana ahankali ta furta.

    “Ameen”.

    Mommy tace.

    “Sai ki shirya idan kunyi wani hutun kije ki gansu”.

    Wara ido Khausar tayi tare da gyara zamanta kana fuskarta ɗauke da murmushi tace.

    “Ai lalle kam”.

    Sai kuma tayi saurin juyawa jin Muryan Asma’u na sallama.

     

    Ƙarasawa Falon Asma’u tayi tare da zama daga gefen hagun Khausar ta ajiye Handbag dake hannunta ta shiga Matsawa Mommy ƙafanta na hagu da faɗin.

    “Mommy ina kwana yasu Raudat?”.

    Hannu Mommy ta sanya ta shafa kanta da faɗin.

    “Lafiya lau Asma’u ya gida yasu Umminki?”.

    Asma’u na cigaba da Matsawa Mommy ƙafanta tace.

    “Tana lafiya tace na gaisheki”.

    Mommy tace.

    “Ina amsawa”.

     

    Ita kuwa khausar kallon Asma’u tayi tace.

    “Sannu da zuwa taso mu shiga ciki”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa sannan ta miƙe ta ɗauki Handbag ɗin ta suka shiga.

    Zama tayi agefen gadon Idanunta akan Khausar data buɗe ƙaramin fridge ta ɗebo mata kayan marmari tace.

    “Anbani saƙon gaisuwa in kawo miki”.

     

    Ajiye ƙaramin Plate ɗin Khausar tayi tare da zama tace.

    “Toh ina Amsawa wani bawan Allah ne?”.

    Da sauri Asma’u ta ƙumshe dariyar dake cikinta kana tace.

    “Moddibo ne yace agaisheki da hannu”.

    Zare idanu Khausar tayi lokaci ɗaya ta ƙware da Inabi dake bakinta da dugu ta miƙe ta nufi fridge ta ɓude Goran Swan water ta ɓude ta kafa abakinta saida tasha fiye da rabi kafin ta janye roban daga bakinta tana maida numfashi.

     

    Asma’u kuwa kasa riƙe dariyar ta tayi cikin dariya sosai tace.

    “Me haka Khausar daga jin sunan Moddibo zaki wani ruɗe haka?,sai kace wani abin tsoro!?”.

    Zama Khausar tayi tana maida numfashi tace.

    “Wallahi mutumin nan ya wuce inda kike tunani yanda kika san bashida zuciya aƙirjinsa baya jin bada haƙuri fa”.

    Ta ida maganar tare da jan siririn tsaki tana tuno fuskar Moddibo lokacin da take bashi haƙuri.

     

    Asma’u ta katse shirun  tare da buɗe Handbag ɗin ta ta ciro takardan Economics da Mi’atu Hadith da sauran darasin da sukayi ta miƙa mata tace.

    “Gashi ki kwafa sannan kiyi karatu akai”.

    Amsa Khausar tayi tare da budewa tace.

    “Toh shikenan ba matsala zan duba”.

    Bayan sun sake taɓa hira Asma’u tace.

    “Zan tafi”.

    Khausar tace.

    “Tun yanzu?”.

    Hararanta Asma’u tayi tayi tace.

    “Eyyyyy lalle kam aigwara ni dakeke sai ki kusan shekara bakije gidanmu ba”.

    Tana gama Fadar haka ta Miƙe ta fita.

    Dariya Khausar tayi tare da sanya Blue Black ɗin hijabinta ta fice afalon ta samu Asma’u nayiwa Mommy Sallama bayanta tabi suka fice.

     

    Washe gari ta kama ranar.

    Asabar Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce acikin mota, suka nufi unguwar shamaƙi, yayin da Hajiya Bunayya ke tuƙi suna sauraron wakar Nazeer Sarkin Waƙa mai taken Bamu babu ku,kuma baku babu mu.

    Cike da nishaɗi Hajiya Lami tace.

    “Hajiya Bunayya Matsalar mu tazo ƙarshe da zaran munje wajen wannan mutumin komai yazo ƙarshe dan ina da tabbacin aikinsa”.

    Dariya Hajiya Bunayya ta sheƙe dashi tare da buga stairing motar tace.

    “Kedai bari nayi al’ƙawari saina tarwatsa wannan matar”.

    Da wannan hiran suka isa unguwar daga can bakin hanya sukayi parking motarsu.

     

    Kana suka ɗanyi tafiyar ƙafa kaɗan suka tsallaka titin, suka nufi wani ƙaton  kango mai zagaye da dogon katanga da duhuwar bishiyoyi,

    da baya-baya suka fara shiga cikin wajen da manyan bishiyoyin Tsamiya dana kuka suka masa ƙawanya sai kuma wasu manyan bishiyoyi irin na Ceɗiya masu masifar tsawo da duhu kana sai wani ƙaramin bukka daya kasance Atsakiyar bishiyoyin,

    jikin bukkar ke waye yake da jajayen ƙyalle da wasu irin ƙwarya masu masifar munin gani ajikin ƙwaryan akwai kuratandu sai kuma wasu baƙaƙen ƙaho masu siffar fuskan bil Adam.

    Daga nesa suka ajiye takalmansu kana suka cigaba da tafiya da baya har suka shiga cikin gidan da ƙafar hagu yayinda wani masifaffen ɗoyi ya cika gidan baki daya ya mamaye ilahirin gidan.

     

    Cikin ɗaga sautin murya suka haɗa baki wajen faɗin”.

    “An gaida Boka Kar’uzu uban bokaye angaida la’anannen Uban la’anannu mugu uban mugaye

    Hatsabibi uban hatsabibai”.

    Daga ciki kuwa wata daskararriyar murya mai firgitarwa mara daɗin saurara yace.

    “Kushigo da baya-baya kana ku tabbata ƙafar hagu zaku riƙa takawa har ku iso gareni”.

     

    Cikin tsinkewar zuciya da matsanancin tsoron kada su saɓa masa doka cike da biyayya suka gyaɗa masa kai tare da ƙara sawa kusa dashi suka zauna suna maida numfashi.

    Cikin daskararriyar muryarsa mara daɗin sauraro yace.

    “Ku tashi anan suna zaune zaku danne ɗan ƙundalo mai ido agoshi! Maza ku koma ta gefen hagu bana ƙaunar ganin ku.

    A dama saboda ba aikin dama zamu yiba”.

     

    Tsaban tsoro saidai Hajiya Bunayya ta dungura tare da kurje hannunta kana jikinsu na rawa suka koma gefen hagunsa.

    Kallon Hajiya Bunayya yayi ya kece da wata mahaukaciyar dariya me tsananin razanarwa, ya nunata da wani mummunan yatsansa da farce yayi tsawo kana yace.

    “Kin makara cikinta har ya kusa wata uku amma zamu jijjigesa da ƙarfin ikon mu zamu fito dashi!”.

    Ita kuwa Hajiya Bunayya Atake taji tsoron ta ya tafi ta washe baki da faɗin.

    “Laaa Malam kasan abinda ke tafe dani?”.

     

    Cikin fushi yace.

    “Sunana ba Malam ba Kur’ani kika gani agabana ko hadisai da za ki kirani da Malam ki kirani da Boka Kar’uzu uban bokaye La’anannen uban la’anannu Mugu Uban Mugaye”.

     

    Ƙasa da kai tayi tana cewa.

    “Tuba nake Boka Kar’uzu bazan sake ba”.

    Kai ya gyaɗa mata yace.

    “Sai kuma batun Jameel da ’yarki Amina”

    Cikin rawan jiki tace.

    “Eh boka Kar’uzu”.

     

    Ya kece da wata mahaukaciyar dariya yace.

    “Ai ƙaddarar abai-bai take,Ai ƙaddarar abai-bai take, ƙaddarar abai-bai take!”.

    Ita kuwa Hajiya Lami cikin zaƙuwa take gyaɗa kai.

    Hajiya Bunayya tace.

    “Boka kamar ya ƙaddara abai-bai take ban fahimta ba”.

    Yace.

    “Babu damuwa za’ayi Miki aiki”.

    Hajiya Lami ta gyara zama sosai tace.

    “Toh Boka Kar’uzu ni ya batun ‘yata?”.

     

    Ya sake kecewa da wata mahaukaciyar dariya yace.

    “Aike batun ki mai sauƙi ne shi wannan babu wata Aransa shi wannan dakike gani yana nan kamar Waliyi ne, koko ince katako, sai dai fa akwai ganye bishiya da yake tsirowa ajikinsa har ta fara jijiya ajikinsa tana gab da zuba rassuna”.

     

    Hajiya Lami tace.

    “Boka koma wani irin ganye ne Indai bana Samira bace atun ɓukesa”.

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Angama angama”.

    Cikin jin dadi ta juya ta kalli Hajiya Bunayya tana sakar mata da murmushi alamar da akwai Nasara.

    Sai kuma ta juya ta kalli Boka Kar’uzu tace.

    “Ya batun abubuwan aiki?”.

     

    A tsawace boka Kar’uzu yace.

    “Zaku kawo Fararen Bunsuraye guda uku, Da baƙaken karnuka guda biyu da baƙar kaza mai bungi-bungi guda ɗaya na batun aikin zubar da ciki.

    Batun Jameel kuwa zaki kawo gurguwar jaka mace sannan ki samu makauniyar tinkiya me watanni bakwai sai kuma  agwagwa fara mai ƙafa ɗaya”.

    Zare Idanu sukayi Atsorace jin abubuwan da ake buƙata.

    Ya cigaba da cewa.

    “Batun aikin Moddibo kuwa zaku kawo Gurguwar shanu ja mai Ido ɗaya da kuma namijin doki fari soll wanda aka haifesa acikin gida sai kuma ku samo Alade guda biyu mace dana miji”.

     

    Cikin tashin hankali da damuwa Hajiya Lami tace.

    “Boka a ina zamu iya samo wa’annan abubuwan aise kai saidai mu bayar asamo”.

    Yace.

    “Toh ku ajiye kuɗin masu tarin yawa”.

    Cikin rawan jiki Hajiya Bunayya tasa hannu a jakarta ta ciro kuɗi wanda batasan adadin suba ta ajiye masa”.

    Kallon kuɗin yayi yace.

    “Kuje bayan sati biyu kuzo ku karɓi kayan aikinku sha yanzu magani yanzu”.

    Godiya suka masa kana suka  tashi suka fita kamar yanda suka shigo.

     

    Acan ɓangaren su Khausar kuwa karatu suke sosai babu kama ƙafar yaro sabbin Malamai da aka kawo musu sun zage damtse wajen koyar da ɗalibai ga kuma sabbin ɗalibai da ake shigowa dasu saboda yanda aka tsara Makarantar sosai makarantar ya sake samun ɗaukaka fiye da farko ga kuma shirye-shiryen musabaƙa da akeyi na Jahar Taraba baki ɗaya Khausar da Asma’u sun sake dagewa.

     

    Bayan sati biyu Hajiya Bunayya da Hajiya Lami ce zaune agaban Boka Kar’uzu.

    Wani ƙullin magani ya ɗauka tare da kallon Hajiya Bunayya ya miƙa mata kana yace.

    “Wannan ki dafa shi da farfesun kayan ciki ki bawa Hajiya Aysha tana ciki, sunan cikinta anyi angama saide wani cikin bashi ba!.

    Sannan idan kin shirya kizo za’a zazzage mata mahaifa asa mata ajiya yanda baza ta sake ɗaukar wani cikin ba, sannan kuma mijinta zai tsaneta ba zai sake sha’awar kusantar taba!”.

    Murmushin samun nasara Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Boka Indai cikin nan ya zube zan dawo akan aikin amma yanzu burina cikin ya zube sannan ajawo hankalin Jameel kan Amina”.

     

    Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar’uzu ya sheƙe dashi yace.

    “Ga wannan”.

    Hannu bibbiyu Hajiya Bunayya tasa amshi ƙullin maganin tana jujjuyawa yace.

    “Ki bawa ‘Yarki Amina tayi wanka dashi sannan tayi hayaƙi idan zatayi hayaƙin ta ɗago kaskon ta kawo bakinta ta riƙa kiran Jameel!, Jameel!!, Jameel!!! na tsawon kwanaki uku sannan ta tsallake kwana uku ta sake na kwana uku na sannan ta sake kwana uku ta tsallake kwana uku sannan ta sake kwana uku kuma ko wanne idan tazo hayaƙin sai takai kaskon bakinta ta kira sunansa kada ku yarda asamu kuskure dan in an fa samu kuskure abun bazaiyi kyau ba”.

     

    Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi tare da jinjina mata hannu tana murmushi cikin ƙasa da murya tace.

    “Alhamdulillah nakusa ganin ƙarshen wannan matsiyatan”.

    Martanin Murmushin Hajiya Lami ta mata itama ranta fess burinsu ya kusa cika.

    Tunda Boka Kar’uzu yace.

    “Muddin tayi na tsawon wannan kwanakin shida kansa zai kawo kansa gareta idan kuma wannan baiyi ba akwai wanda zamu sakeyi saidai shi wannan kankat ne amma shi sai farkon damuna tukunna zamu samu ayishi”.

    Cike da farin ciki Hajiya Bunayya tace.

    “Boka Kar’uzu Uban bokaye Insha Allahu ma nasan wannan aikin zaici”.

    Cikin wata razananniyar tsawa yace.

    “Oho Ni dai nace kada ki sake kiramin sunan Allah anan domin da kina jin tsoronsa ba zaki zo nanba bare har kinemi aikata mugun abu akan wani idan kuma kina son aikin ki ya ɓaci ki sake kiran Allah anan”.

     

    Cikin rawan baki da tsoron kada aikinta yaƙi ci tace.

    “Tuba nake Boka Kar’uzu Uban bokaye La’anannen Uban La’anannu Mugu Uban mugaye da ikon ka wannan aiki zaici”.

     

    Ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya mai kama da sautin ƙaran lalataccen Injin Markaɗe yace.

    “Yanzu ne aikin ki zaiyi yanzu ne kika yi magana mai ma’ana”.

    Ta saki ajiyar zuciya cike da farin ciki.

     

    Hajiya Lami ta matso kusa tare da gyara zama sosai tana fuskantar Boka tace.

    “Ni kuma ya maganar ’yata?”.

    Wani irin kallo ya mata kana yace.

    “Na ‘yarki sai anyi babban shiri domin wannan da kike gani shida saƙago basu da banbanci baya kallon mace ako wani irin mataki daya wuce ɗaliba ya karantar da ita ya kuma bata ilimi da tarbiyya shi koda mace zata wuce tsirara agabansa babu abinda zai damesa da ita tamkar zuciyar dutse ne aƙirjinsa!”.

     

    Ta gumi Hajiya Lami tayi tare da faɗin.

    “Ikon Allah aƙasan ranta”.

    Boka Kar’uzu ya cigaba da cewa.

    “Sai munyi mata shiri sosai yanda lokaci ɗaya zata jawo hankalin sa gareta sai bayan wata biyu zaki zo ki karɓi haɗin da muke tsuma shi sannan tayi kokari ta bashi yaci daya ci aiki ya gama”.

    Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta saki tace.

    “Da ƙarfin ikon ka zamuyi hakan boka”.

    Ya kece da wata mahaukaciyar dare yace.

    “Na gama daku zaku iya tafiya”.

    Miƙewa sukayi suka ce. “Godiya muke Boka Kar’uzu Uban bokaye La’anannen Uban La’anannu Mugu Uban mugaye”.

    Shikuwa Dariya ya kece dashi yana jin daɗin kirarin da ake masa kamar yanda suka saba shiga haka suka fita da baya.

     

    Cikin tsananin farin ciki Amina ke kallon Hajiya Bunayya dake mata bayani karɓan maganin tayi tare da rungume Hajiya Bunayya tace.

    “Nagode Umma”.

    Ƙullin maganin ta karɓa sannan ta shiga ban ɗaki tayi wanka dashi tana fitowa Hajiya Bunayya ta kawo mata wuta akasko ta bata zama Amina tayi tare da kai saitin kaskon bakinta tace.

    “Jameel!, Jameel!!, Jameel!!!”.

    Ta faɗa da ƙarfi yayin da hayaƙin ke bin ilahirin jikinta kallon Hajiya Bunayya tayi cikin jin daɗi tace.

    “Umma M Jameel ya Kusa zama mallakina?”.

    Dariya Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Ƙwarai kuwa?”.

    Asiya ce tashigo falon da Sallama da sauri ta toshe hancinta jin wani masifaffen wari da ƙauri tayi saurin kallon ƙofar Bedroom ɗin Hajiya Bunayya inda nan take jin wari da ƙaurin ke fita.

    Tana ƙoƙarin shiga Hajiya Bunayya ta fito Kallonta Asiya tayi tace.

    “Ummah warin meke fita daga ɗakinki?”.

     

    Harara Hajiya Bunayya ta watsa mata tace.

    “Warin lafiya ko kuma ke ki kafi kowa hanci?”.

    Girgiza kai Asiya tayi tace.

    “Wallahi Ummah da gaske akwai..”.

    Tsawa Hajiya Bunayya ta buga mata da faɗin.

    “Ki wuce kibani waje sakaryar banza mara tunani”.

    Ahankali Asiya tace.

    “Allah yabaki haƙuri Ummah”.

    Kana ta juya cikin mutuwar jiki ta nufi ɗakinta.

     

    Bayan wata ɗaya:

    Amina ta gama amfani da duk maganin da Hajiya Bunayya ta karɓo mata awajen Boka Kar’uzu cike da farin ciki ta dubi Hajiya Bunayya asanda take sanya uniform ɗinta tace.

    “Ummah na matsu na isa Makaranta inga irin tarban da Jameel zai min!”.

    Murmushi Hajiya Bunayya tayi da faɗin.

    “Kede ki kama kanki karki bari ya gane kina sonshi ya rainaki dan yanzu sai yanda mukayi dashi”.

    Asiya data fito daga  kichen hannunta riƙe da Cup ɗin tea dake tururi ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon Idanunta akan Amina tace.

    “Amina ki maida hankali akan karatunki kada kice zakiyi wasa da damarki komai da kika gani arayuwa muƙaddari ne daga Ubangiji”.

    Cikin tsawa Hajiya Bunayya tace.

    “Asiya zanci Ubanki fa idan baki fita sabgar Amina ba shegiyar yarinya me baƙin halin tsiya.

    Niko anya ma  ba canza min ke akayi ba, dan wallahi badan kamannin dake tsakanin mu ba sai ince sauya min ke akayi”.

     

    Miƙewa Asiya tayi tace.

    “Allah ya baki haƙuri Umma amma ita gaskiya ɗaya ce”.

    Harara Amina ta watsa mata tace.

    “Ke har wani gaskiya ce dake to ki riƙe gaskiyar ki bama bukata”.

    tana gama fadar haka ta fice.

     

    Atare suka fito da Khausar dake riƙe da hannun Raudat kallo ɗaya Khausar ta mata ta kawar da kanta gefe,

    Ita kuwa Amina murmushi mai cike da ma’anoni ta sakarwa Khausar sannan tashiga motar yayin da Khausar tabi bayan ta suka shiga sannan driver yaja motar suka tafi.

     

    Motar na tsayawa kowa ya nufi ajinsu kamar kullum saida Khausar takai Raudat ajinsu kafin ta wuce ajinsu.

    Aɓangaren Amina kuwa kai tsaye ajinsu ta nufa tare da zama tana sakin murmushi duk da Amina da Khausar

     

    Shigansu baa daɗewa M Jameel ya shigo ajin cikin wata farar gezner me kyau yayin da kansa ke sanye da baƙin hula gashinsa ya fito ta ƙeya ƙafarsa sanye da sau ciki baƙi jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi Amina kuwa ta gumi tayi tare da zu bawa  sajensa zuwa gemunsa idanu tana mai furta.

    “Wowww”.

    Shi kuwa M Jameel hankalinsa ya mayar kan Black Board.

    Cikin karya murya tare da lanƙwasa harshe Amina tace.

    “Malam Barka da safiya”.

    Anutse M Jameel ya juya ya kalleta cikin sauri ya runtse Idanunsa da ƙarfin gaske.

    Sai kuma ya sake buɗewa akan fuskarta still da sauri ya sake runtse Idanunsa yana mai furta.

    “Hasbunallahu wani’imal wakil.

    Astagfirullah wa’atubu ilaik”.

    Ita kuwa Amina cike da ƙissa ta sake karya harshe tana juya Idanunta tace.

    “Malam ina kwana”.

     

    Shi kuwa M Jameel Batare daya juya ya kalleta ba ya ɗaga mata hannu, domin tun sanda ya kalli fuskarta sau ɗaya yaga kamar an ƙona fuskar Biri, sosai ta masa muni tunda yake kallon fuskar yarinyar bai taɓa ganin tayi masa muni irin na yau ba, baki ɗaya fuskarta babu haske bare annuri Kawar da kansa yayi ya cigaba da koyar wansa batare daya yarda ya sake kollon inda take ba har yagama ya fita.

    Ita kuwa Amina bata kawo komai aranta ba domin atunaninta maganin ne ya fara aiki.

     

    Acan ajinsu Khausar kuwa Moddibo ne tsaye jikin Black Board Ya rubuta Geography ajiki,

    Da alama shine subject ɗin da zai riƙa ɗaukansu.

    Jikinsa sanye da Jallabiya Coffee color yayin da kansa ke naɗe da hirami siririn sajensa zuwa gemunsa yasha gyara sai sheƙi yake jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi tularen Oud.

    Cikin nutsuwa da kuma sanyin Muryansa ya gyara tsayuwar sa tare da harɗe hannayensa aƙirji kana ya ɗan lumshe idanunsa kafin yace.

    “Class What is Geogry?”.

    ya ƙare tambayar cikin tsananin tsuke fuska da tsare hirar samata ƙasa, sabida yanayin dariasin in yayi garaje yara zasu rainasa, Allah ya sani ba ƙaunar darasin yakeba sabida yanayin abubuwan dake ƙunshe a ciki masu cin karo da addini.

    Shiru class din yayi ba wanda yayi magana sabida yadda baya kallon idonsu haka suna kan suke shayin koda motsi bare Kallonsa.

    Khausar da Idanunta ke lumshe ta buɗe tare da zaro harshe ta ɗan lashi lips ɗin ta sai kuma ahankali ta ɗaga siririn hannunta dake maƙale da zoben azurfa da kuma Gold.

    Shi kuwa Moddibo ahankali ya maida da idanunsa zuwa ta inda take.

    Kana tsare sashin da taken yayi da ido amman ba fuskantar yake kalloba, ƙara tsuke fuska yayi tare da sa hannunsa ya shafa  yalwataccen sajen dake fuskarsa kana ya mata alamun ta tashi.

    Cikin nutsuwa tare da taka tsan-tsan akan gudun lefin da zatayi ta motsa lips ɗin ta da yayi pich saboda man baki data shafa kana ta lumshe Idanunta tace.

    “Geography can be defined as the discription of the Earth”.

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da faɗin.

    “Dayyit, sit-down”.

    Kai ta gyaɗa tare da zama.

     

    Ahankali ya motsa lips ɗinsa da faɗin.

    “Yah Salam”. Yayi mgnar yadda ba mai jinshi.

    gajeren tsaki, Samira Sani taja dan ji tayi kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda baƙin ciki taso ace itace zatayi wannan karatun

    Shikuwa Moddibo kallon Khausar yayi tare da yimata alamar tazo cikin sauri ta miƙe ta isa gabansa, ba tare da yace mata komai baya miƙa mata hannunsa.

     

    Kallon tattausan farin tafin hannunsa dake ɗauke da zara-zaran yatsu da ga wasu zoben azurfa fari da baki daya ƙawata yatsun.

    Cikin rawan murya tace.

    “Malam mai zanyi?”.

    Ya mutsa fuska yayi tare da watsa mata harara daya sa ‘ya‘yan hanjinta kaɗawa da ido ya nuna mata zobunan hannunta.

    Cikin rawan jiki ta cire ta basa lokaci ɗaya Idanunta suka sauya launi sosai take masifar son zoben ɗaya Mommy tace ta bata ɗaya kuma  Hajja Nana ce ta bata ta kuma shaida mata tun na babantane na azurfan.

    Saida ta koma ta zauna yace.

    “Nasha faɗa muku cewa nan ba wajen ado bane idan kowa yace zaiyi ado yazo ai wasu ma baza agansu ba”.

    Ya ida maganar tare da juyawa ya cigaba da koyar musu cike da ƙwarewa tare da kare ƙa’idar musulunci gudun dulmuyar tunanin ɗalibai.

     

    Bayan kwana uku baki daya Amina tashiga damuwa da tashin hankali koda ta gaida M Jameel baya Amsawa sai dai ya ɗaga mata hannu, gwara ma da yana kallonta Sannan wataran yakan mata murmushi amma yanzu koda kallonta baya ƙaunar yi.

    Bayan antashi tana komawa gida.

     

    Kai tsaye Bedroom din Hajiya Bunayya ta nufa.

    Zaune ta samu Hajiya Bunayya riƙe da kofin tea mai ɗumi ahannunta.

    Zama tayi agefen Hajiya Bunayya cikin raunin murya tace.

    “Ummah tunda fa nagama aiki da maganin M Jameel Koda kallona ne baya ƙaunaryi, ko gaishesa nayi saidai ya ɗaga min hannun!”.

    Da Mamaki Hajiya Bunayya tace.

    “Ikon Allah to ya zama dole inshirya na koma gidan Boka Kar’uzu inji me yesa”.

    Gyaɗa kai Amina tayi tace.

    “Gaskiya ya kamata dai Ummah”.

     

    Hajiya Bunayya tace.

    “Gashi nima yau nakeso in fara na wannan matsiyaciyar matar dan nafi so dama sai kin gama naki sai in dafa in bata”.

    Amina tace.

    “Ya kamata dai kam yazo tana ta cika mana gida da yara”.

    Ita kuwa Hajiya Bunayya miƙewa tayi da kanta ta shiga kichen ta buɗe fridge  ta ɗauko kayan ciki ta haɗa masa kayan ƙamshi da kayan hadi Sosai sai tashin ƙamshi yake.

    Warmers ta ɗauka ta juye kana ta dauko ƙullin maganin da boka Kar’uzu ya bata ta barbaɗa akai sannan ta ɗauka ta nufi sashen Hajiya Aysha dashi.

    Mommy na zaune afalo ta miƙe ƙafafunta ta jiyo Sallamar Hajiya Bunayya murmushi tayi tare da tace.

    “Yaya kece da kanki sannu da zuwa”.

     

    Murmushi Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Wallahi kuwa kinga Perpesoup nayi na kayan ciki, nasan kuma kina so, shiyasa nace nari na kawo miki, idan kinsha da dan ruwan Tea  mai ɗumi zakaji daɗi asanyin da ake”.

    Murmushi Mommy tayi tace.

    “Aikuwa Nagode yanzu nake tunanin tashi in dafa ko indomie ne naci dan na gagara cin tuwon”.

    Murmushi Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Ayyah ƙanwata to ga wannan sai kisha ai zakiji daɗinsa”.

     

    Acan ɗaki kuwa Khausar ce tsaye jikin wodurobe tana gyara kayansu da Raudat ta burkitasu.

     

    Siririn tsaki ta saki tare da kallon tulin kayansu dake burkice kamar basu taɓa ganin ninkiba bare guga stool taja ta zauna tana ninke kayan.

     

    Acan falo kuwa yunƙurawa Mommy tayi da faɗin.

    “Bari na ɗauko Plate”.

    Da sauri Hajiya Bunayya ta mike tare da cewa.

    “A’a bari na ɗauko Miki”.

    Ta Faɗa tare da shiga kichen ɗin.

    Ita kuwa Mommy murmushi tayi aranta tana jinjinawa ƙaunar da Hajiya Bunayya ke nuna mata tabbas samun irinta acikin kishiyoyi sai antona.

    Hajiya Bunayya kuwa nashiga kichen ta fashe da dariya mai ɗan sauti tace.

    “Shegiyar mata zaki ci Ubanki atunaninki har ƙasan raina nake sonki”.

    Sai kuma ta sake tun tsirewa da wata dariya mai sauti can ƙasa, kana ta ɗauki cup ta zuba mata Tea kana ta ɗauki Plate da spoon ta fita.

    Miƙa wa Mommy plate ɗin tayi tare sa faɗin.

    “Naga kamar kwana biyu bakyajin daɗi”.

    Ya mutse fuska Mommy  tayi kana tace.

    “Wallahi kuwa gaba ɗaya bana jin daɗin jikina wannan karon kuma da laulayi sosai yazo min”.

    Cike da tausayawa Hajiya Bunayya tace.

    “Ayyah sannu Ubangiji Allah ya inganta”.

    Aranta kuwa cewa tayi Allah ya tarwatsa matsiyaciya.

    Ita ko Mommy tace.

    “Ameen ya Allah”.

     

    Miƙewa Hajiya Bunayya tayi tare da ɗaukan Plate din ta ɓude perpesoup ɗin dake tururi yana tashin ƙamshi ta zubawa Mommy tare da miƙa mata da kofin shayin.

    Lumshe idanu tayi sosai ƙamshin ya bugeta, a take yawunta ya tsinke abinka da mai cike lokaci ɗaya taji ranta yabiya da Perpesoup ɗin hannu tasa ta amsa tare da ajiye plate ɗin bisa cinyarta kana tasa spoon ɗin  da sauri ta ɗebo sokar hanta da rokon ta perpesoup ɗin takai bakinta…..!

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

     

    _By_

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 29

    Sakayyah 29

     

    *LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE KO KIN GANSHI A WASU WURAREN DA BA CIKIN GROUPS NA DANA BUƊE NA SAKAYYAH BAto na satane, 1k ne kacal kuɗin littafin SAKAYYAH yar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, kiyiwa Allah da Manzonsa ku dena fidda min littafina, in dai kin san kin sayane dan ki turawa wasu, dan Allah ki gaya min in mayar miki da kuɗinki🙏🏻🙏🏻Dan Allah nace ba dan niba*

     

    Isrnejny. Moddibo kuwa cike da mamaki da tsoro ya maimaita 200 Millions asaman laɓɓansa, he can’t believe or imagine zasu iya tambayar wannan maƙudan kuɗin how cames kidnapper zasu tambayi kuɗin fansa kamar sun sace ɗan shugaban ƙasa.

    Rintse idanunsa yayi tare da cije labɓansa na ƙasa lokaci ɗaya jijiyoyin kansa suka tashi sukayi ruɗu-ruɗu dasu.

    Dafe kuncin Hajiya Karima tayi da hannunta duka biyu kana ta kyale baki tare da cewa.

    “Ohh Allah ya kawo mu wani zamani ka haifi ɗa sannan wasu ƙartin banza da wofi su saka kasa ke sayan sa bafa Millions biyu ba, Ba ashirin ba, Ba hamshin ba, Ba ɗari ba,  har Millions ɗari biyu sai kace abin Masifa ko dan sunyi zaton Jameel ɗan Aliko ɗan Gwate ne, shi, ka haifi ɗa kasha wahalar ciyar dashi shayar dashi tufatar dashi biya masa makaranta sannan ace ka sake siyan sa”.

    Dafe kai Abba yayi da duka hannunsa biyu baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake kar-kar-kar tamkar mazari  yayin da idanunsa suka kaɗa sukayi jawur tamkar garwashi.

    Dai-dai lokacin Hajiya Turai tashigo baki ɗaya tayi zuru-zuru da ita. Idanunta sun kaɗa sunyi jawur dasu ganin halin da Abba ke ciki yasa tace.

    “A’a Alhj Lafiya Subhanallah”.

    ta faɗa tare da nufar Bedroom ɗin sa ta da buɗe drawer ta ɗauko naganinsa ganin alamar hawan jinjinsa ne ya tashi tare da manna waya akunnenta bayan kamar second uku tace.

    “Hello Dr Muktar dan Allah kazo yanzu ina ganin kamar hawan jinin Alhj ne ya tashi”.

    Cikin raunin murya Abba ya ɗago kai ya kalleta tare da cewa.

    “A’a ki bari ba sai Dr yazoba, ki bani maganin kawai”.

    Kai ta gyaɗa kana cikin sauri ta zuba masa ruwa a glass cup ta miƙa masa tare da bara masa maganin karɓa yayi ya afasu  abakinsa ya haɗiye.

    Sannu a hankali ya fara maida numfashi sama-sama yana jin bugun zuciyarsa tare da sarawan da kansa keyi ya fara raguwa amma still hannunsa na dafe da kansa.

     

    Ɗago Idanunsa yayi tare da kallon Moddibo daya zuba masa Idanu kana ya kalli gefen damansa Hajiya Turai ce durƙushe Idanunta cike da hawaye  lumshe idanunsa yayi kana ya shiga tunani kwata-kwata kuɗin dake cikin account ɗinsa tsuran kuɗi, gaba da baya Million Sha biyu ne wanda yake tunanin da sun cika Ashirin zai bawa M Jameel saboda ya habɓaka Company daya bashi, da ƙarfi ya sake rintse idanunsa tare da dafe kansa tuno wa da yayi acikin Million Sha biyu ma akwai cikon kudin hajji nashi da na matansa da zai cika ta, baki ɗaya tunaninsa ya tushe ina yasan zai fara kai kadaransa asiya masa su cikin gaggawa kuma da daraja sannan abashi kuɗin cikin tsanananin tashin hankali yace.

    _“Ya Ilahi ya lillahi ya mujibud da’awati ya hayyu ya ƙayyum bi rahma tika astaghisu lahaula wala ƙuwwata illa billahil aliyul azim”_.

    Abin da yake maimaitawa kenan asaman laɓɓansa.

    A hankali Moddibo ya matsa kusa dashi cike da tausayawa yace.

    “Colm down Abba ka nutsu ka kwantar da hankalin ka everything will be fine by the grace of Allah”.

    Cikin sauri Abba ya riƙo tsintsiyar hannun Moddibo tare da cewa.

    “Aliyu Why should I find 2 hundred Millions?”.

    Aliyu mai zan fitar in sayar dashi cikin gaggawa in Samu kuɗi?.

    Aliyu bani da ko Million ashirin acikin account ɗina,kaji kuɗin da suka kira fa”.

    Kallonsa kawai Moddibo keyi cike da tausayinsa Cikin raunin murya Abba ya cigaba da cewa.

    “Aliyu kwanan nan na cire kuɗi na siya filin nan kuma shima gaba ɗaya filin dana siyeshi 25 Million ne da ace suna nan kaga kuɗin akwai ɗan gwaɓi ahannu na”.

    Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da sake damƙe hannun Moddibo acikin nasa kana yace.

    “Ina da kadaran da zan iya sayarwa amma ta yaya awani lokaci zan samu ace ansiya se anbani kuɗina sannan na wane”.

    Kasa ƙara sa maganar yayi kawai saiya janye hannunsa dake cikin na Moddibo ya rufe fuskarsa yana mai furta.

    _“Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha Hasbunallahu wani’imal wakin La’ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu Minal zhalimin”_.

     

    Hajiya Karima dake dafe da kuncinta ta ɗago kai tare da kallon Abba kana tace.

    “Alhj ai dole dama za ayi ciniki dasu idan yaso sai anemi ragi”.

    Moddibo kuwa kai ya girgiza tare da kallon ta kana yace.

    “Idan da ace sunzo mana da sauƙi da kuma Imani acikin zancen zamu iya hakan amma fa kiga yanda idan sunyi magana sai su yanke mana kiran baza su tsaya suji ta bakin muba sai sun kwana ɗaya ko biyu kafin su sake kiran mu”.

    Da ƙarfi ya runtse Idanunsa tare da cije labɓansa na ƙasa kana ya cigaba da cewa.

    “Basa tunanin shin wani irin yanayi ko hali zamu kasance aciki ba yaya zamuyi, da wannan kuɗin da suka kira”.

    Ya ida maganar cikin raunin murya.

    Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.

    “Nima abinda nake tunani kenan idan nace musu babu zasu iya yiwa Jameel Illah”.

    Girgiza kai Moddibo yayi tare da cewa.

    “Abba kar ma kace musu babu sai muyi ƙoƙari duk yanda zamuyi mu haɗa kuɗin nan muyi ƙoƙari mu basu”.

    Ahankali Abba ya furta.

    “Ya Salam”.

    Hajiya Turai kuwa cikin matsanancin kuka ta kalli Moddibo kana ta maida kallonta kan Abba tare da cewa.

    “Ai abayar ɗin yafi Alhj duk wani abinda kake dashi ka sashi akasuwa kawai asamu asayar akarɓo Jameel meye fi maka Jameel aduniyar nan Alhj, kawai asayar da komai akai musu kuɗin akarɓo shi”.

    Cikin sauri Hajiya Karima ta kalli Hajiya Turai kana tace.

    “Kamar ya asaida komai Hajiya Turai kifayi tunani akan abinda kike faɗa idan aka sayar da komai muku mu murayu aya kenan?”.

    Sai kuma ta maida kallonta kan Abba kana ta cigaba da cewa.

    “Alhj ya za ayi ɗauki irin wannan maƙudan kuɗin amulmula abasu kaga idan wa’annan ƴan Kidnapping din da suka kinnafe Jameelu sunji dadi an basu abinda suke so to wasu kuma ai sauran ƴaƴan zasu zo su kwashe”.

    Ta ida mgnar tare da sauke numfashi kana ta cigaba da cewa.

    “Suma sauran ƴaƴan sai aje a kinnafesu su kuma idan kuɗin da za’a fanshe su bai rage ba ya za ayi kenan.

    A gaskiya wannan ba shawara bace ace za aɗauki wannan maƙudan kuɗin abasu sai kace ba asha wahala wajen ne mansu ba”.

    Ahankali Moddibo ya ɗago kumburarrun Idanun sa ya kalli Hajiya Turai dake dafe da ƙafaɗan Abba tana sharɓan kuka kana ya maida kallonsa kan Hajiya Karima data zabga tagumi.

    Girgiza kansa yayi.

    Sosai hankalin Abba yayi masifar tashi yama rasa wani irin tunani zaiyi Aransa ya gaza tantance abin cewa.

    Sannu a hankali idanunsa suka fara lumshewa jikinsa ya saki  baya yaja tare da gyara kwanciyarsa akan 3sitter tare da lumshe idanunsa  Atake Bacci ya ɗauke sa sabida magungunansa da Hajia Turai ta bashi yasha sun jiƙa sunbi jininsa.

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da miƙewa kana yai musu sai da safe tare da ficewa yashiga motarsa kai tsaye gidan Ummi ya nufa.

    Awaje yayi Parking motarsa kana ya fita iska na kaɗa ko wani sashe na jikinsa ahankali ya murɗa handle din ƙofar ya tura bakinsa ɗauke da sallama ya shiga.

     

    Idanunsa suka sauƙa akan Ummi dake zaune kan Sallaya hannunta riƙe da Carbi yayin da Malam Ahmad ke zaune gefenta yana rarrashin ta.

    Ganinsa yasa Ummi ta ajiye carbin dake hannunta kana ta maida hankalinta kansa,Anutse Moddibo ya ƙara sa tare da miƙawa malam Ahmad hannu sukayi musabaha kana ya koma ya zana agaban Ummi.

    Jin Sallamar sa yasa Asma’u da Bashir suka fito daga Bedroom tare da zama gefe da gefen Ummi ya zamana sun sashi a tsakiya kana cikin raunin murya suka gaishesa atare zuwa lokacin shima Bashir kuka yake sosai duk yayi zuru-zuru.

     

    Ahankali Ummi ta zubawa Moddibo Idanu kana cikin sanyin murya tace.

    “Babana ya akayi sun sake kira?”.

    Kai ya gyaɗa tare da sun kuyar da kansa ƙasa kana yace.

    “Eh”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

    “Me suke buƙata?”.

    Still Kansa na ƙasa yace.

    “Ummi kuɗi suke so”.

    Numfashi ta fesar kana tace.

    “Kuɗi suke so?”.

    Kai ya gyaɗa amma bai ce komai ba.

    Cikin tsira masa ido tace.

    “Kuɗi kamar nawa suke so?”.

    Cikin rauni ya kalleta kana ya kalli malam Ahmad, Asma’u da Bashir ya fesar da numfashi tare da cewa.

    “Ummi kuɗin suna da yawa kuɗin da suke buƙata sun wuce zatonmu”.

    Gyara zama tayi kana tace.

    “Toh Meye amfanin kuɗin mahaifinsa?, Meye amfanin kuɗin Babansa?,Menene amfanin duk tattalin da yake yi!?”.

    Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.

    “Ummi kuɗin sun wuce tunanin mai tunani!?”.

    Ɗa gowa Ummi tayi tare da tsira masa ido kana tace.

    “Kamar nawa suke buƙata Babana?”.

     

    Cikin raunin murya da alamar sarewa Moddibo yace.

    “Ummi har Million ɗari biyu suke buƙata”.

    Cikin wani irin yanayi mai cike da rauni, tsoro, mmki Ummi taja ajiyar zuciya kana ta maida kanta ta jingina da jikin kujeran da Malam Ahmad ke zaune tare da lumshe Idanunta kana Muryanta na rawa tace.

    “Ƙarya sukeyi ba kuɗin suke so ba so suke su kashe min Jameelu lallai Mahaifinsa mai arziƙi ne amma be kai matakin da za’a matsesa lokaci ɗaya ace ya fito da Million ɗari biyuba, kawai dai yaudarace suke mana anya ma Jameelu yana raye kuwa?”.

    Cikin sauri Moddibo ya girgiza mata kai kana yace.

    “Yana raye Ummi ina ji ajikina J yana raye kuma na faɗa miki munyi magana dashi”.

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Yau da suka kira kunyi magana dashi?”.

    Shiru yayi yana kallonta amma baice komai ba.

     

    Kallonsa Ummi tayi cikin muryan kuka tace.

    “Babana ka faɗa min gaskiya tsakanin ka da Allah yau kunyi magana dashi?”.

    Girgiza mata kai Moddibo yayi tare da faɗin.

    “Ummi ba muyi magana dashi ba, amma naji muryan J ƙasa-ƙasa yana cewa Abba abasu duk abinda suke so”.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da rintse idanunsa kana tace.

    “Babana ka tabbatar gaskiya kake faɗa min?”

    Jinjina kai Moddibo yayi kana cikin sanyin murya yace.

    “Wallahi Wa rabbul Khaba Ummi naji muryan J ƙasa. yana magana bawai sun bashi bane amma naji yana magana”.

    Kuka Asma’u da Bashir suka fashe da shi atare kana lokaci ɗaya suka haɗa baki wajen cewa.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n ya Allah ka kuɓutar da Yah Jameel Ubangiji kada ka basu ikon cutar dashi ya Allah kaine gatanmu Yah Jameel shine ka wakilta da isar mana gatanmu ya Allah ka karesa da karewaka”.

     

    Numfashi Malam Ahmad ya fesar kana cike da tausayawa yace.

    “Asma’u ba kuka ya kamata kuyi ba addu’ar mu Jameelu ke buƙata idan kuna kuka ya kuke so Ummin ku tayi?”.

    Cikin sheshsheƙan Kuka Asma’u tace.

    “Abba Yah Jameel fa Yah Jameel yana cikin mawuyacin hali Abba kaji  fa maƙudan kuɗin da suke buƙata Abba ya za’ayi mu samu irin wannan kuɗin mu karɓo Yah Jameel Abba Ina tsoron kada su cutar mana dashi”.

     

    Girgiza kai Malam Ahmad yayi cikin sanyin murya yace.

    “Insha Allah da izinin Ubangiji babu abinda zai samu Jameelu, ko wani bawa da kalar tashi ƙaddaran tun kafin a haifi Jameelu Ubangiji ya zana masa ƙaddaransa muyi masa addu’ar Allah ya sauƙaƙa mana zafin ƙaddararsa”.

    Jinjina kai Moddibo yayi yana jin wani irin azabebben zafi aƙirjinsa.

    Kallon Moddibo Malam Ahmad yayi kana yace.

    “Moddibo mai Yakamata ayi acikin wannan al’amarin!?”.

    Moddibo da kansa ke ƙasa ya ɗago ya kallon Malam Ahmad a hankali yace.

    “Malam abinda yakamata kawai afara cuku-cukun neman kuɗin nan sai muga abinda zai kasance”.

     

    Girgiza kai Ummi tayi still tana jingine da jikin kujera tace.

    “Babana ina zamu samu kuɗin nan Million ɗari biyu fa da ace Million biyu suka ce koni kaina ma zan bada su”.

    Ta faɗa tare da ɗaukar wayarta tayi checking balance kana tace.

    “Gashi yanzu anan ina da Million ɗaya da dubu ɗari huɗu da hamsin da ɗaya sannan kuma ba matsala gobe in Allah ya kaimu zan tafi cikin.

    Taraba zan kai gwala-gwalaina”.

    Sai kuma ta ɗan tsaya, jin numfashin ta na yankewa, da ƙarfi ta fizgo numfashin tare da cije labɓanta na ƙasa hawaye cike da Idanunta murya na cike da rauni ta cigaba da cewa.

    “Zan saida su inga nawa zan samu ajikinsu zan haɗa harda na Asma’u sannan, motata itama zan saidawa muga nawa zan samu awurina”.

    Jingina kai Malam Ahmad yayi kana cikin sanyin Murya yace.

    “Har gidan nan ma asashi a. Kasuwa asayar dashi”.

    Kallonsa Moddibo yayi tare da girgiza kai kana yace.

    “A Malam ayi haka”.

     

    Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.

    “Asiyar Moddibo menene Jameelu baiyi mana ba aduniyar na, kasancewar sa atare damu shiyafi mana komai”.

    Ahankali Ummi ta ɗago kanta tare da tsira masa ido hawaye na bin kuncinta ta sani fili dai filinsa ne halalinsa mallakinsa, amma baki ɗaya ginin dake ciki Jameel ne ya musu bayan yasa an buge tsohon ginin taɓon.

    Girgiza kai tayi cikin rauni tace.

    “A’a ba sai anyi haka ba bari muga abinda Mahaifinsa zai samu”.

    Girgiza kai Malam Ahmad yayi tare da kallon Asma’u da Bashir da har zuwa lokacin suke kuka a hankali ya fesar da numfashi tare da cewa.

    “Ni dai na sadaukar da wannan gida ga.

    Jameelu wallahi na yafe masa shi duniya da lahira na amince asa shi akasuwa muddin za a samu masu siya, to asa shi akasuwa  mu samu muga aƙalla dai awajen mu ace an samu Million goma kuɗin zaifi gwaɓi”.

    Sun kuyar da kai ƙasa Ummi tayi hawaye masu masifar zafi suka zubo mata.

    Hannunta Moddibo ya riƙe cikin sanyin murya yace.

    “Ummi dan Allah ki daina wannan kukan idan kina kuka muku ma ya zamuyi Ummi babu abinda J ke buƙata awajen mu face addu’a ganin ki awannan yanayin naya sake raunatamana zuciya”.

    Kai Malam Ahmad ya gyaɗa kana yace.

    “Sosai ma wannan kukan da kike Fatima saidai ya haddasa miki wani ciwon amma babu amfanin da zaiyi dan Allah ki daina ki cigaba da yi masa addu’a. shi kansa ba zaiso ace kina masa kuka ba”.

    Kai ta gyaɗa tare da share hawayen ta kamar yarinya kana tace.

    “Na daina Insha Allah zan cigaba da yimasa addu’a Ako da yaushe”.

     

    Saida Moddibo ya tabbata ta daina kukan kafin ya mata sallama ya fice cike da tausayinsu Driving yake ahankali har ya isa gida yayi Parking kana ya fito ya rufe gate din tare da wucewa sashen Innayi bakinsa ɗauke da sallama.

    Kwance ya samu Innayi cikin Yanayin damuwa gefenta da Radio tana sauraro wanda ɓatan M Jameel ake sanarwa.

    Miƙewa tayi ta zauna tare da amsa Sallamar sa kana tace.

    “Moddibo ya labarin Jameelu?”.

    Cikin sanyin murya yace.

    “Innayi sun sake kira ɗazu”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

    “Toh kunyi magana dashi yana cikin ƙoshin lafiya?”.

    Girgiza mata kai yayi  kana yace.

    “A’a Innayi bamuyi waya dashi ba amma bisa duk kan Alamu J baya jin daɗin zaman wajen can”.

    Ahankali Innayi ta jingina bayanta da jikin bango kana ta matsar da Radio gefe tare da cewa.

    “Dama Moddibo ya za ayi yaji daɗin zaman wannan wajen. kasan yanayin da yake ciki ai dole bazai ji daɗin zaman wannan wajen ba amma me suke buƙata?”.

     

    “Innayi kuɗi suka nema”.

     

    “Kuɗi suka nema to aisai abasu aje a karɓe shi”.

     

    “Innayi kuɗin da suka nema na fitar hayyacine!”.

     

    “Kuɗi har nawa suka nema? Da zai zama na fitar hankali”.

    Dafe goshinsa yayi kana yace.

    “Innayi Million ɗari biyu suka nema kuma cikin ƙanƙanin lokacin fa”.

    Ita kam Innayi baki ɗaya lissafin ta sincewa yayi jin maƙudan kuɗin tama rasa nawane, kallon Moddibo tayi tare da cewa.

    “Dubu ɗari biyu?”.

    Kai Moddibo ya Girgiza tare da cewa.

    “A’a ba dubu ɗari biyu bafa Million fa Million ɗari biyu”.

    Daga kanta sama tayi alamar tunani sai kuma ta kallesa tare da cewa.

    “Million biyu?”.

    Still girgiza mata kai Moddibo yayi kana yace.

    “A’a Million ɗin goma, ashirin, hamsin, ɗari, ɗari da hamshin har ɗari biyu”.

    Dafe kirji tayi kana tace.

    “Million ɗari biyu?”.

    Jinjina mata kai Moddibo yayi.

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Ban gane lissafin ba Aliyu”.

     

    Lips ɗinsa duka biyu ya cije a lokaci guda kana yace.

    “Ba zaki gane lissafin ba Innayi kuɗi ne masu tarin yawa suke nema”.

    Cikin sanyin murya Innayi ta jujjuya kanta kana tace.

    _“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakin Layukalliful nafsi illa wusɗaha_

    Toh yanzu mai Baban nasa yace?”.

     

    “Innayi Abbansa bashi da wannan kuɗin a ƙasa kwanan nan dama ya gama yi mana ƙorafi bashi da kuɗi”.

    Lumshe idanu Innayi tayi kana tace.

    “Ya Salam ya Ubangiji Allah ka dube mu da idon rahama, ya Allah ka yayemana ya Allah ka sauƙaƙa mana ya Allah ka tsare Jameel ka kare mana shi, Allah ka tseratar da wannan bawan naka”.

    Cikin sanyin murya Moddibo yace.

    “Ameen”.

     

    Kallon second biyar zuwa bakwai Innayi ta yiwa Moddibo kana tace.

    “To amma kai Moddibo mai kake ganin zakayi akai?”.

    Still hannunsa na dafe akansa yace.

    “Innayi akwai kuɗi awajena zan tattara su in haɗa su muga nawa za’a samu awajena”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Yafi kam”.

    Bayan sun sake tattauna ne Moddibo ya miƙe tare da  yi mata Sallama kana ya nufi Sashen sa ahankali ya tura Murfin Kofar shiga tare da mayarwa ya rufe.

     

    Kana ya jingina bayansa da jikin da kofar tare da rintse idanunsa sautin murya M Jameel ya farayi masa kai-komo AJ bansan idan nakeba,

    Lumshe danunsa yayu zuciyarsa na bugawa da masifar ƙarfi yana bada sautin dif-dif-dif cikin sauri ya buɗe Idanunsa jin muryan M Jameel na yawo a kansa yana cewa A.J A.J Kallon kan 3sitrer kurui ji yake kamar zaiga J dinsa a wurin, cikin raunin murya yace.

    “J Why are you?, Zuciyata zata fashe ya Allah kaji ƙaina ya rabbil Izzati ka dawo da J garemu cikin aminci da salama ya Allah kada ka bawa waɗɗanan azzaluman daman cutar dashi”.

    Ya kai 15 minutes yana mai jero Addu’o’in cike da rauni, kafin ya miƙe kamar wanda aka mitsina ya nufi Bedroom ɗin sa kai tsaye toilet ya shiga ya watsa ruwa kana ya ɗaura alwala ya fito ya kwanta bisa gadonsa yayi rigingine  duk da yasan cewa da wuya bacci ya ɗauke sa amman ya lumshe idonsa domin yau kwana uku rabon da ya samu wani wadataccen bacci sai wani irin azabebben ciwon kai da yakeji tamkar kansa zai rabe da ga wani irin sarawa da yakeyi yana bada wani irin sauti mara daɗi gau-gau-gau!.

    A hankali ya bude idon sai kuma yayi saurin

    Lumshe Idanun sabida sarawa da kan yayi masa.

    Cikin zazzaƙan muryansa mai cike da rauni ya fara raira ƙira’ar Suratul Yusuf hawaye masu ɗumi suka riƙa fita daga idanunsa suna shiga kunnensa cikin wannan yanayin da cikar Sa’adatu da  karatun Alqur’ani mai girma ya samar masa, wani irin kiɗimemmen baccin da bai shirya masa ba ya sace sa.

     

    Acan cikin baccin sa kuwa zaune ya hangosa akan wata.

    Tattausan shimfiɗa cikin wani masha’hurin falo mai masifar kyau da ƙawa.

    Sai dai kima yana ta dariya hartada karketawa, yayinda idanunsa kuma sunyi jawur jikinsa na rawa jin.

    A hankali ya fara jujjuya kansa yana mai ci gaba da dariyar ya juyo kansa gabansa, jin alamar tafiya tare da wani ƙamshi daya ratsa hancinsa yasa ya ɗaga manyan idanunsa da sukayi luhu-luhu ya  sauƙe ganinsa akan Khausar dake zuwa garesa cikin wata iriyar ƙasaitacciyar shiga, ido ya zira mata ko ƙebtawa bayayi har ta isa garesa, a hankali ta zauna gefensa.

    Tare da tsira masa manyan Idanunta masu haske wanda ke ciki da ruwan hawaye kana ta miƙa masa wani hankief fari ƙall mai masifar ƙamshin turare.

    Ƙin karba yayi saima lumshe idanunsa da yayi wanda sai lokacin ya samu wasu irin tafasassun hawaye suka samu damar kwaranyowa, hakan yasake kawar da kansa gefe tare da sakin sheshsheƙa.

    Ahankali Khausar ta matsa gabansa har suna shaƙan nunfashin juna kana ta sanya hankief ɗin ta shiga share masa hawayen cikin wata Sanyayyar murya mai cike da nutsuwa da kuma rauni tace.

    “Yah Jameel Addu’ar mu yake buƙata ba kuka ba idan kai kana kuka.

    Toh Ni kuma ya zanyi addu’a za muyi masa kaji ko Abu J”.

    Ta ida mgnar da kiransa da sunan da ta raɗa masa, tare da faɗawa jikinsa ta fashe da sassayan kuka dai-dai lokacin kuma ya farka.

    Kansa ya dafe tare da miƙewa ya shiga toilet ya ɗaura al,wala kana ya dawo ya shimfiɗa Sallaya ya fara nafillah yana cigaba da yiwa M Jameel addu’a.

    Ba tare da yabi ta kan mafarkinba, domin yanzu kam idan da sabo ai yaci ace ya saba da yawan ziyarar kutse da nacin da Khaisar keyi masa cikin rayuwar baccinsa.

     

    Washe gari Ummi ta tattara baki ɗaya Sarkoƙi, ta da ɗan kunnen zobe da awarwon Gwal nata dana Asma’u ta shirya ta tafi Tarata.

    Tana isa kai tsaye babbar kasuwar su ta wuce kana tashiga shagon saida gwala-gwalai ta bayar aka gwada cikin sa’a ta samu sunyi farashi sosai kasancewar Manyan Sarƙoƙine nata dana Asma’u wasu nata tun tana gidan Abban Jameel ne, suka haɗa mata kuɗin ta Naira Million biyu da dubu ɗari huɗu da hamsin sukayi mata transfer dinsu.

     

    Daga nan gidan kai tsaye gidan Ƙawarta Hajiya Salma Wanda mijinta ke saida Motoci yawanci awajensa M Jameel ke siyan mota ko kuma can zawa.

     

    Mai A dai-dai-tan na sauƙeta ta miƙa masa kudinsa kana ta shiga cikin tangamenen coumpund ɗin daya tsaru kai tsaye ciki ta nufa tare da Knowking ɗin ƙofar kana ta murɗa handle ɗin tashiga bakinta ɗauke da sallama.

    Hajiya Salma dake zaune akan kujera ta miƙe cikin sauri kana tace.

    “Hajiya Fatima sannu da zuwa ga wajen zama”.

    Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.

    “Yawwa Nagode”.

    Sannan ta zauna tare da sakin Ajiyar zuciya.

    Bayan sun gaisane.

    Cikin sanyin murya Hajiya Salma tace.

    “Ayyah Hajiya ashe ga abinda ya faru da ɗana Jameel kuwa?”.

    Cikin yanayin sanyin ɗaya zamewa Ummu jiki, ta gyaɗa mata kai tare da cewa.

    “Ummm bari ke dai Hajia Salma duniya tayi min zafi”.

    Cikin tausayawa Hajia Salma tace.

    “Ba komai in sha Allah, kada ki damu Hajia Fatima.

    Ubangiji Allah ya bayyanar da Jameel aduk inda yake Ubangiji ya karesa daga sharrin mai sharri”.

    Cikin sanyin Murya Ummi tace.

    “Ameen ya Allah ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

    Cike da tausayawa Hajiya Salma tace.

    “Wallahi Koda wasa banji ba sai ɗazu da safe Alhj na duba jarida ya gani shine yake sanar min”.

    Kai Ummi ta gyaɗa kana tace.

    “Allah sarki ai yanzu anshiga kwana na huɗu kenan.

    Uhmmm dama nazo kiyiwa Alhj Abdallah magana ne akan ya duba motata ya siya”.

    Ajiyar zuciya Hajiya Salma ta sauƙe kana tace.

    “Ubangiji Allah ya tsare Malam Jameel aduk inda yake”.

    ta faɗa tare da shigewa ciki tsaye ta samu mijin nata yana ƙoƙarin fita Kallonsa tayi kana tace.

    “Alhj Hajiya Fatima ce ta zo mahaifiyar Malam Jameel”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Ikon Allah muna shirin zuwa kuma sai gata”.

    Ya faɗa tare fitowa a tare, a inda Hajiya Salma ta barta anan suka sameta tayi ta gumi.

    Ahankali Ummi ta ɗago jai tare da cewa.

    “Alhj Abdallah ina kwana ya gida”.

    Zama yayi kana yace.

    “Lafiya lau Hajiya ashe kuma ga abinda ya faru da Malam Jameel”.

    Kai Ummi ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.

    “Eh”.

    Ajiyar zuciya Alh Abdallah ya sauƙe kana yace.

    “Wallahi bamu da labari sai ɗazu ina karanta Jarida na gani nake faɗawa Salma tace itama bata da labari dake akwai wani fitar gaggawa daya kamani nace idan nadawo zan kaita da yamma ta gaishe ki”.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da gyada kai kana tace.

    “Allah sarki dama Motata ce nazo ka tura adauƙa maka ka ga lafiyarta zan saidata in zaka siya”.

    Ɗagowa yayi tare da kallonta kana yace.

    “Motar da Malam Jameel ya siya miki nan?”.

    Kai ta gyaɗa masa tare da cewa.

    “Eh shi”.

    Zaman hular kansa ya dan gyara kana yace.

    “Amma ai motar bata daɗe ba Hajiya Fatima”.

    Kai ta gyaɗa Muryanta na rawa tace.

    “Eh bata daɗe ba Uzurin gaggawa ne ya kama Ni shiyasa zan siyar”.

    Jinjina kai yayi tare da cewa.

    “Aikam dama mota ce mai kyau sannan bai daɗe da sayanta ba za tura yaro yaje ya ɗaukota kuma yanzu mugama magana tunda abu na gaggawa ne”.

    Cikin sanyin murya tace.

    “Tun baka gani ba”.

    Girgiza kai yayi tare da faɗin.

    “Baki da matsala Indai wannan ne zan baki Million shida”.

    Cikin sauri Ummi tace.

    “Alhj har Million Shida kuma dama motar yana da tsada kenan?”.

    Kai ya gyaɗa mata tare da zaro wayarsa acikin aljihu kana yace.

    “Eh dama Million biyar ne haka ya siyeta toh nasiyeta biyar ɗin kamar yanda ya siya sannan Million ɗayan kuma na bada nawa gudunmawar Ubangiji Allah ya bayyana Malam Jameel”.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.

    “Ameen ya rabbil izzati, ngd Matuƙa”.

    Da sauri ta kalleshi jin yana cewa.

    “Ki bani account number ki zan miki transfer”.

    Kai Ummi ta gyaɗa tare da kiramasa number’s ɗin.

    Atake ya mata transfer.

    Miƙewa tayi tare da yi masa godiya sosai kana ta fito, har ƙofa Hajiya Salma ta rakata kana ta Wuce.

     

    Kai tsaye tashar motar Gembila ta nufa, tana zuwa kuwa tayi sa’a mutun ɗaya ya rage, haka yasa ta shiga motar ta tashi.

     

    Alhamdulillah sun isa Gembila lfy.

     

    A hankali Ummi ke tafiya tana jin wani irin sanyi a ranta tare da Comfedance ga Million ɗaya da dubu ɗari huɗu da  dake account ɗinta ga kuma Million biyu da dubu ɗari huɗu da hamsin na Sarkoƙi kana ga Million Shida na mota ya zama tana da tsuran kuɗi ahannunta har Naira Million tara da dubu ɗari takwas kenan.

    A hankali ta sauƙe wani zazzafafar ajiyar zuciya kana ta nufi gida.

    Acan ɓangaren Moddibo kuwa ya haɗa duk wasu kuɗaɗe dake hannunsa ya samu Million huɗu da dubu ɗari biyu da hamshin kai tsaye gidan Ummi ya nufa yana Parking ɗin motarsa mai A dai-dai-tan sahu na ajiyeta atare suka shiga falonta.

    Suna shiga Bayan sun gaisa Ummi tashiga Alart massage tare da miƙawa Moddibo wayarta tare da cewa.

    “Babana ka kalli kuɗi sunyi gwaɓi”.

    Amsar wayar yayi tare da Kallon Alart massage ɗin kuɗin kana ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Masha Allah kuɗi sunyi gwaɓi bari na haɗa  dana wajena”.

     

    Kallonsa Ummi tayi haka nan taji hawaye na ciko mata kwarmin Idanunta.

    Cikin sanyin murya Moddibo yace.

    “Ummi na wurina na bashi da yawa Million huɗu da dubu ɗari biyu da hamsin ne”.

    Cike da tausayinsa tace.

    “Toh Allah ya biya. Babana Allah yabamu yanda zamuyi Ubangiji ya saka maka amma ka rage wani abu aciki ka samu na kashewa”.

    Girgiza kai yayi cikin raunin murya yace.

    “Ummi wani abu zan rage idan ina da abinda yafi wannan zan ɗauka in bayar akarɓo J naje. nayi magana da dillalai gidan mu na sashi akasuwa in dai za’a samu siyansa akan lokaci.

    Cikin sauri Ummi ta kallesa tare da cewa.

    “Gidan ku kuma Babana!?”.

    Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

    “Ummi Meye amfanin gidan mai zamuyi da gidan babu wani farin ciki acikisa.

    Muddin J baya nan fa wanne farin ciki zamuyi. kuma komai da muka rasa zamu iya samu idan J ya dawo gare mu”.

    Jinjina kai Ummi tayi, Account number dake wayarsa ya fito dashi ya mata transfer kuɗin tare da miƙa mata wayar karɓa tayi ta duba Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kallon kuɗin Naira Million goma sha huɗu kenan cib.

    Numfashi ta fesar tare da kallon Moddibo kana tace.

    “Alhamdulillah Babana kuɗi sun cika Million goma sha huɗu bari muje gidan Abban sa tare”.

     

    A hankali yace.

    “Amma Ummi ki bari sai gobe muje wataƙil yau ba zasu kira ba sai goben, amma ni yanzu idan nafi ta zanje wajen Abba muji nawa aka samu awajensa”.

    Kai ta gyaɗa cikin sanyi tace.

    “Toh shikenan Babana Allah yasa muji al’khairi”.

    Kai ya gyaɗa tare da miƙewa kana yace.

    “Amin.

    Toh shikenan bari naje yanzu”.

    Ya faɗa tare da ficewa.

     

    Kai tsaye gidan Abba ya nufa bayan yayi Parking ya fito tare da shiga Falon bakinsa ɗauke da Sallama.

    Abba dake zaune kan 2 sitter ya jingina bayansa da jikin kujera ya amsa masa Sallamar cike da tausayinsa ya zuba masa yana ganin yadda yake tafiya duk ya faɗa acikin kwanaki huɗu ya rame yayi shafal.

     

    Ƙara sawa Moddibo yayi tare da zama gefensa kana yace.

    “Abba ina yini ya kuma haƙurin rayuwa?”.

    Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da cewa.

    “Alhamdulillah Aliyu ya wajen su Innayi?”.

    Kansa a ƙasa yace.

    “Lafiya lau Abba basu sake kira ba ko?”.

    Girgiza kai Abba yayi tare da fesar da numfashi kana ya runtse Idanunsa cikin sanyin murya yace.

    “Basu sake kira ba Aliyu”.

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da cewa.

    “Toh yanzu Abba kuɗi kimanin nawa aka samu awajenka?”.

    Abba kuwa ahankali ya zame daga kan kushin ɗin ya zauna akan capet tare da fuskantar Moddibo kana yace.

    “Aliyu na tattara duk abinda yake wajena kana duk wanda nake binsu bashi na tattarasu sannan na nemi temakon bashi duk wanda zan nemi temakonsu sunban bashi baki ɗaya kuɗin dana samu awajena Million hamsin da shida ne, iya adadin kudin dake hannu na kenan, duk ta inda zan buga na buga Aminaina ƴan uwana duk na nemi temako awajen su wasu sun bani kyauta wasu kuma aro na buga shine Million hamsin da shida”.

     

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da cewa.

    “Toh Abba kuɗi dai sun ɗanyi gwaɓi gashi awurin Ummi an samu Million Sha uku yanzu kenan muna da Million Saba’in dai-dai a ƙasa.

    Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana yace.

    “Alhamdulilah kuɗi sun fara taruwa Amma ɗari biyu fa suka ce gashi ko ɗari cikekke bamu samu ba”.

    Cikin raunin murya Moddibo yace.

    “Abba bari mugani idan sun sake kira sai mu rokesu su rage mana idan sun tallafa sun tausaya mana ko bashin banki ne zamu ci sai mu ƙara akai kuɗin ya cikata”.

    Kallon sa Abba yayi tare da jinjina kai kana yace.

    “Toh shikenan ba laifi Allah yasa mu dace”.

    Ameen Moddibo ya amsa kana suka cigaba da hira har Misalin ƙarfe goma.

    Abba najin ringing din wayarsa Yayi saurin zabura tare da picking kana yayi Sallama.

    Daga ɗaya ɓangaren cikin bauɗaɗɗiyar murya mutumin yace.

    “Alhj Bashiru ka haɗa kuɗin?”.

    Cikin raunin Murya Abba ya gyaɗa kansa kana yace.

    “Kuyi haƙuri bawan Allah dan Allah kuyi haƙuri wallahi kuɗin nan da kuka faɗa babu su awajena kwata kwata babu”.

    Daga ɗaya ɓangaren mutumin ya juya  tare da kallon M Jameel dake zaune a ƙasa kana cikin wata dakakkiyar murya mutumin yace.

    “Da alama dai mahaifinka baya sonka”.

    Jin muryan mutumin agefe yasa Abba saurin cewa.

    “Don Allah ku bani inji muryarsa”.

    Cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya Mutumin ya wurga wa M Jameel wayar kana yace.

    “Gashi kaji muryan sa”.

    Cikin sauri M Jameel ya cafke wayar tare da kaiwa Kunnensa kana cikin sanyin mai cike da rauni mai tada hankalin ɗan Adam cikin murya mai cike da galabaita yace.

    “Abbana”.

     

    Cikin sauri Moddibo ya karɓi wayar a hannun Abba kana yasa a handsfree tare da danna record.

    Cikin raunin Murya M Jameel yace.

    “Abba kabasu kuɗin Abba dan Allah ka basu abinda suke so ka fitar dani awannan wajen mana Abbana”.

    Runtse Idanu Abba yayi kana yace.

    “Babana zan fitar da kai ina nan ina har haɗawa kuɗin insha Allah zan fitar da kai amma Jameelu duka-duka kuɗin da muka haɗa anan Million Saba’in ne su kuma sunce Million ɗari biyu suke so”.

    Cikin wata raunan’niyar murya mai cike da masifaffiyar galabaita da neman jin ƙai M Jameel yace.

    “Abba a saida motocina duka sannan aduba ɗakina akwai kuɗi amma bai cika Million biyu bama dan Allah ahaɗa Abba abasu azo a karɓe ni”.

    Cikin rauni ya runtse Idanunsa da hawaye suka cika kana yace.

    “Abba bana son zaman nan babu daɗi ba Ummina ba A.J sannan kaima ba kai wuri ba daɗi dan Allah Abba ka basu duk abinda suke so kazo ka karɓe ni ku saida komai nawa a haɗo kuɗin”.

    Kai Abba ya gyaɗa tare da ƙoƙarin hana hawayen sa zubowa kana yace.

    “Babana Insha Allah zan zo in karɓe ka koda raina suke so zan basu amadadin ranka”.

    Modibbo kuwa tuni wasu irin hawaye masu masifar zafi ke kwaranyo mishi tamkar mace.

     

    Fisge wayar sukayi daga hannun M Jameel kana cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya Mutumin yace.

    “Toh kaji dai abinda ɗan ka ya faɗa zamu baka dama ta karshe”.

    Cikin sauri Moddibo da idanunsa ke rintse ya buɗe tare da cewa.

    “Dan Allah! Dan Allah!! Dan girman Allah!!! dan darajar Annabi Muhammad (S.A.W) badan  muba kamar yanda kuka ce J nada mutunci da kamala toh dan Allah saboda wannan kamalar tasa ku rage mana kuɗin zamu yi muku duk kan biyayya amma ku faɗa mana abinda zamu iya kawo wa”.

    Daga ɗaya ɓangaren shiru mutumin yayi  ba tare da yace komai ba kana bai katse kiran ba.

    Cikin raunin murya Moddibo yace.

    “Dan Allah kuyi haƙuri ku rage mana Insha Allah ba zamuyi gardama ba, amma kuɗin hannun mu munyi munyi sun kasa kai adadin da kuke buƙata mu samu su kai adadin da kuke buƙata wannan shine matsalar mu ku temaka ku ragar mana”.

    Ajiyar zuciya mutumin ya sauƙe tare da cewa.

    “Wannan Moddibo ne ke magana ko?”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana cikin sanyin murya yace.

    “Eh”

    Cike da gadara Mutumin yace.

    “Toh shikenan ku bada Million ɗari da hamsin”.

    Cikin raunin murya Moddibo yace.

    “Mungode amma dan Allah ba zaku ƙara rage mana ba?”.

    Cikin wata razananniyar tsawa Mutumin yace.

    “Dan ubanka dan ka samu na zabge Million hamshin.

    Atake to wallahi acikin Million ɗari da hamsin Naira biyar ba zamu rage ba kuma wallahi idan ku ka yarda kuka sake yi mana batun ragi kuɗi to wallahi akan ran Jameel domin kuɗi ne dai mu ki ya rayu ko ya mutu zamu samesu”.

    Cikin tsanananin tsoro da kaɗuwa Moddibo ya dafe ƙirjinsa yayin da kansa ya sara da masifan ƙarfi.

    Cikin tsawa Mutumin ya cigaba da cewa.

    “Yanzu Moddibo gashi kayi magana dashi na ƙarshe wanda ko bacci yake yana kiran sunan ka gashi kayi magana dashi dan wataƙil shine maganarka na ƙarshe kenan dashi matukar dai baku haɗa kuɗin nan ba ku kasake yi mana batun ragin kuɗin to kayi magana dashi na ƙarshe kenan”.

    ya faɗa tare da wurgawa M Jameel wayar.

     

    Cikin sauri M Jameel ya cafke wayar tare da maƙalawa akunnensa kana cikin raunin murya yace.

    “A.J”.

    Cikin sauri da zaƙuwa Moddibo yace.

    “J ina kake?”.

    Girgiza kai M Jameel Yayi tare da cewa.

    “A.J ban san inda nake ba ina Ummina!?”.

    Runtse Idanu Moddibo yayi tare da taune lips ɗinsa kana yace.

    “Tana lafiya J?”.

    Cikin sanyin Murya M Jameel yace.

    “J ka tabbata?”.

    Cikin raunatacciyar murya yace.

    “Na’am”.

    jin haka yasa yaci gaba da cewa.

    “Kace mata kada tayi kuka tayi ta min. Addu’a A.J ina sonka Ina son Ummina Ina son Abbana Ina Son Asma’u Ina son Bashir”.

    Da sauri Moddibo ya dafe ƙirjinsa dake harbawa da masifan ƙarfi  cikin raunin murya M Jameel ya cigaba da cewa.

    “A.J Ina son Khausar tashigo rayuwar mu”.

    Cikin tsanananin rauni Moddibo yace.

    “Na sani J nasan kana son mu muma muna sonka, kuma in sha Allah duk zamu kasance a tare, zata shiga rayuwarka J zan mutunta abinda kakeso J”.

     

    Girgiza kai M Jameel Yayi still cikin raunin murya yace.

    “Ngd A.J in kayi haka kayi min komai, kayiwa Ummina magana idan akwai wani abu a hannunta ta bayar ahaɗa azo a karɓeni awajen nan dan Allah katemaka min”.

    Araunane Moddibo yace.

    “Insha Allah J zan taimaka da duk kan iyawa ta da kuma duk kan damata J koda ace da raina ne zan fanshi ranka da rayuwarka Insha Allah zamu fito da kai”.

    Jinjina kai M Jameel yayi tare da faɗin.

    “Nagode Nagode A.J ina maka fatan al’khairi acikin rayuwarka ga Amanar Ummina, Asma’u, Bashir,Abba da…. ka kula dasu kafin in dawo sannan kada ka mance batun Kh”…

    Fisge wayar akayi daga kunnensa tare da katsewa.

     

    Dafe kai Moddibo yayi cikin wani irin azabebben rauni ya fashe da matsanancin kuka tare da miƙewa batare da yace komai da Abba ba ya fice yana fita ya shiga motarsa tare dayi  mata key.

    Kana ya ciro wayarsa tare da dearling number Ummi tana ɗagawa  murya a raunace yace.

    “Ummi”.

    Cikin sanyin murya tace.

    “Na’am”.

    Cikin ƙoƙarin hana kansa kuka yace.

    “Ummi munyi waya da J yanzu”.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tace.

    “Dagaske Babana?”.

    Kai ya gyaɗa kamar tana gabansa.

    Cike da tsoro Ummi tace.

    “Babana to Meyesa kake kuka?”.

     

    Fashewa yayi da kuka kana cikin sheshsheƙa yace.

    “Ummi ina kukan rashin J akusa dani ne Ummi wanda suka sai motarki Alhj Abdallah kice ya tura Azo aɗauki motocina da na J  duka azo asiya ahaɗa kudin duka”.

    Numfashi Ummi ta fesar tare da rintse idanunta kana tace.

    “Sunƙi ragewa ko?”.

    Girgiza kai yayi tare da cewa.

    “A’a Ummi sun rage mana Million hamsin akai yanzu ya zama Million ɗari da hamsin suke buƙata”.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.

    “Toh Alhamdulillah wataƙila zamu iya cin nasara”.

    Cike da rauni Moddibo yace.

    “Insha Allah Ummi da izinin Ubangiji”.

    Ya faɗa tare da katse kiran jin wani kuka na neman kufce masa.

     

    Kai tsaye hanyar gida ya nufa ba abinda ke yawo acikin kunnensa face sautin Muryar J ɗinsa yana isa gida yayi Parking tare da rufe musu gate.

    Kai tsaye sashen Innayi ya nufa yana isa ya zauna abakin baranda tare da riƙe kansa da hannu duka biyu,

    Kana ya fashe da wani irin kuka mai masifar ciwo a zuciya.

    Wani irin azaban zogi yaji zuciyarsa na masa hadi da zafi da raɗaɗi yayin da wani masifaffen rauni ya lulluɓesa.

    Innayi da bacci ya fara fisgarta ne, ta miƙe da sauri jin kamar sheshsheƙan Kukan Moddibo kana ta fito tare da Kallonsa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ya ɗauki rawa cikin sanyin murya tace.

    “Ya dai Moddibo lafiya kuwa mai ya faru da Jameelu?”.

    Cikin matsanancin kuka yace.

    “Innayi ya zamuyi taya zanyi in.

    Samu in taimaki J duk kan tattalina ya ƙare babu abinda zan samu in saida cikin gaggawa.

    Zan saida tsohuwar motar  da kika siya min da wannan sabuwar da kuma na J duka za’a siyar sannan Innayi nasan koda an siyar dasu duka, kuɗin ba zasu ciki Million ɗari ba”.

    Sai kuma ya kife kansa bisa guiwowinsa ya sake fashewa da sabon kuka kana yace.

    “Innayi sunce idan muka sake neman ragi akan kuɗin kamar mun nemi akashe J ne”,.

    Jingina kansa yayi jikin fillan dake gefenta tare da fashewa da matsanancin kuka hadda sheshsheƙa.

     

    Cikin Sanyin jiki Innayi ta zauna kusa dashi batare da tace yayi shiri ko kuma ya daina kukan ba, domin  ta tabbata duk abinda yasa Moddibo kuka ba ƙaramin abu bane, kana idan har bai yiwa wannan abin kuka ba to mai zai yiwa kuka arayuwarsa.

    Moddibo kuwa kuka ya cigaba da yi tamkar ransa zai fita har shidewa yake.

    A ƙalla ya ɗauki Mintuna masu tsawo yana kuka kafin ahankali ya ɗago kansa tare da kallon Innayi kana yace.

    “Innayi”.

    Cikin sanyin murya tace.

    “Na’am Moddibo”.

     

    Cikin Muryansa daya dishe da kuka yace.

    “Innayi ta wace hanya ce wace damace  wane daliline kike samu kike mana duk kan buƙatun rayuwarmu?

    Innayi in dai har adana kuɗi kikayi in dai har basu ƙare ba Innayi ki fito mana dasu ki  taimakeni aceci J dashi”.

    Jinjina kai tayi kana tace.

    “Moddibo gaba ɗaya tattalin da mukayi na zaman rayuwar mu awannan yanki awannan gari a wannan ƙasar anje matakin da gaba ɗaya tattalin namu yazo ƙarshe sabida lokacin komawa muhalli ya kusan cimmmana”.

    Sai kuma ta kalli Moddibo da har zuwa  lokacin hawaye ke bin Fuskarsa kana tace.

    “Na tanadi komai ne domin sanin cewa muna da bukatar su kama daga karuntaka, ci, sha, Jinya, sutura.

    Da dai sauransu to yanzu kuma lokaci ya tafi rayuwa ta juya abubuwa sun tafi baki ɗaya tattalin namu yayi ƙasa tsadan rayuwa ya cinye kaso mafi tsoka”.

    Numfashi Moddibo ya fesar kana yace.

    “Innayi koma wani irin tattaline shin babu ragowa ne ko kaɗan ne?”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Akwai ragowa”.

    Cikin kuka yace.

    “Menene amfanin ragowan duk tattalin arzikin da kike dashi matukar dai ba zai fito atemaki J ɗina da shiba Jamelunki fa ya fito daga inda yake fa”.

    Ya ƙare mgnar cikin ƙunan rai, domin gani yake kamar ma duk duniya ba’a damu da J ɗinsa ba.

    Ita kuwa Innayi cikin tafiya wani sashi  nazarin Jinjina kai tayi tare da cewa.

    “Bashi da amfani Indai bazan fito dashi ba, amma bari na fito dashi amma yanzu ka fara yin shiru tukunna kana kayi min al’ƙawarin cewa bazaka tambayeni komaiba akan duk abinda zaka gani”.

    Kai ya gyaɗa mata kana yace.

    “Innayi muga abinda zan fara samu awajenki tu kunna zanfi jin sanyi, ni yanzu a duniya babu tambayar da ke bakina daya wuce ina J yake , wanne hali yake ciki”.

    Sai kuma ya fesar da zazzafan numfashi tare da cewa.

    “Wallahi Allah ji nakeyi  tamkar naje na zauna abakin masallacai inyita bara asamu ahaɗa kudi in cikata in karɓo J Innayi ya zanyi”.

    Cike da rauni Innayi tace.

    “Ba zakayi bara ba Moddibo Bari muga abinda Allah zai mana”.

    Kai ta gyaɗa tare da jan hannunsa suka nufi bayan ɗakinta inda randunan ƙasa ke ajiye.

    Kallon Moddibo da har zuwa lokacin hawaye ke zuba a idanunsa tayi kana tace ɗaga min randan nan”.

    Sauri kallonta yayi kana ya Kalli randan ƙasan tare da cewa.

    “In ɗaga miki randa kuma?”.

    Ba tare data kallesa ba tace.

    “Kada kayi min musu idan na baka Umarni kabi”.

    Kai ya gyaɗa cikin sanyin yace.

    “Toh”.

    Tare da ɗaga randan ya matsar gefe.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “Toh ɗaga  fantekar”.

    Kai ya ɗaga tare da matsar da fantekar dake cike da ƙasa gefe.

    Yana janye fantekar yaga ƙasan wajen alailaye.

    Ahankali Innayi ta zauna agaban wajen Moddibo kuwa cikin sanyi jiki ya durƙusa agefenta.

    Itako Innayi hannunta ta sanya ta fara tono ƙasan dake wajen ganin duhu agarin yasa Moddibo sanya hannunsa acikin aljihu ya ciro wayarsa tare da kunna tochligt ya haska mata inda take tonawan.

    Innayi kuwa ahankali ta cigaba da tono ƙasan bayan ta gama kwashe ƙasan ya rage sauran wasu manyan duwatsu ahankali ta ciresu duka.

    Cike da mmki Moddibo ya tsaida idanunsa akan  fafakekken rami an lailayeshi da siminti yana rufe da murfin tukunya kamar na lamba uku, da ɗan ƙarfi ta ɗago Murfin tukunya.

    Cikin sauri  Moddibo yayi saurin rintse idanunsa da karfu sakamakon wani  haskene mai masifar sheƙi daya ɗauke masa idanu daya kashe  masa idanu,

    A hankali ya kuma saƙe buɗe inadunsa, da sauri ya mitso ganin yadda cikin ramin ke sheƙi da ƙelƙeli mai ɗauke ido yake fitowa daga cikin ramin, acan ƙasan ramin kuwa cike yake da ƴan ƙananan sulallan gwala-gwalai wanda basu fiye yawa ba  sosai hasken ya ɗauke masa idanu saboda hasken wayarsa daya haske cike da tsanananin mamakin ya sunkuyo tare haska cikin ramin da kyau kana ya sanya tafin hannunsa acikin ramin ya ɗebo guda huɗu tabbas sulallan Gwalne…!

     

     

    Littafin SAKAYYAH na kuɗine ko kin ganshi a wani wurin na satane. Ki biya ki karanta cikin Aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA.

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 27

    Sakayyah 27

    SAKAYAH

     

    27

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

    *Al’bishirunku Ma’aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma’aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken  GARKUWAR MA’AURATA*

     

    NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.

    Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

     

    Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.

    Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?

    Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.

    Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?

    Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba’a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,

    Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.

    Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.

     

     

    Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*

    Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu’umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

     

    Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

     

    🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA

    *(GARKUWAR MA’AURATA)*

     

    Isrehjɗɗ. Acan Falon Moddibo kuwa zaune yake akan 2sitter hannunsa riƙe da Kofin Tea yana sha time to time zai ɗaga kansa tare da kallon agogon dake manne abango ahankali ya gyara zamansa tare da kurɓan tea dake tiriri ya lumshe idanunsa tare da buɗe su akan agogon  cinyarsa ya matse da ƙarfi har saida yaji jikinsa na rawa, ƙara matse jikinsa yayi sabida yadda yake jin M ɗinsa na miƙewa yana harbawa cike da zalama, ɗan gajeren tsakiya yaja, cikin sanyin murya a fili yace.

    “J har yanzu baka dawo ba”.

    Yayi mgnar kamar Jameel ɗin na gabansa.

    Sai kuma ahankali yasa hannunsa tare da laluɓar wayarsa a aljihun sa na hagu da dama jin babu yasa yaja siririn tsaki tare da miƙewa cikin wani irin masifeffen kasala da sanyin jiki mai kashe ilahirin gaɓɓai ya nufi bedroom ɗinsa a kuma lokaci ɗaya zuciyarsa ta buga tare da tsinkewa da masifaffen ƙarfi, da ƙyar ya iya ɗaga ƙafarsa na dama kana ya taka ya shiga Bedroom tare da furta.

    “Hasbunallahu wani’imal wakin”.

    Jin yanda zuciyarsa ke cigaba da bugawa cikin yanayin tsinkewar zuciya da sanyin jiki ya ɗauki ƙaramar wayar tasa,  kana ya dawo falon ya zauna tare da shiga Call log zai kira M Jameel sai kuma kiran Malam Arɗo yashigo wayar sa.

    Zubawa screen ɗin wayar ido yayi tare da jan siririn tsaki kamar ba zai ɗaga ba sai wata zuciyar tace ka ɗaga mana kasan menene Uzirinsa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da picking.

     

    Acan ɓangaren Ummi kuwa zaune take a falonta kan kujera 3sitter tayi ta tagumi da duka hannunta biyu, kana ta tsirawa waje ɗaya Idanu yayin da ƙirjinta ke bugawa da masifar ƙarfi  zuciyarta na tsinkewa yana bada sautin dif-dif-dif lokaci ɗaya taji wata muguwar kasala na rufe mata jiki haka nan take jin zuciyarta na tsinkewa.

    Jiki a mace Asma’u ta fito daga kichen hannunta riƙe da Plate ƙara sawa falon tayi Idanunta akan Ummi data zabga tagumi ta zauna akan 1sitter tare da cewa.

    “Ummi har yanzu baki kwanta ba?”.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana ta gyaɗa mata kai tare da cewa.

    “Eh Asma’u ban kwanta ba”.

    Cike da kulawa Asma’u ta ɗaga kanta tare da kalli agogo, tare da cewa.

    “Ummi kalli fa har sha ɗaya ta wuce me kikeyi afalo ke kaɗai shiru ga Abban mu yashiga tun ɗazu”.

    Lumshe Idanu Ummi tayi still zuciyarta na tsinkewa kana tace.

    “Babu”.

    Numfashi Asma’u ta fesar tare da ajiye cokalin dake hannunta tace.

    “Toh Ummi ko dai baki da lafiya ne?”.

    Kallonta Ummi tayi tare da girgiza kai.

    “Lafiyata ƙalau Asma’u”.

     

    “Ayyah Ummi am to mai yasa baki kwanta ba kin zauna shiru ke kaɗai dubi yanda kika yi tagumi da hannu duka bibbiyu”.

    Cewar Asma’u.

     

    “Ban sani ba Asma’u ba wai bani da lafiya ba amma ina jin jikina wani iri bai min daɗi ba ina jin zuciyata na tsinkewa sannan ga wata kasala data rufe ni”.

    Ido Asma’u ta zuba mata kamar mai son gane wani abu sai kuma tace.

    “Toh Ummi ki riƙa maimaita Hasbunallahu wani’imal wakin mana kuma may be rashin bacci ne kinga jiya kwana mukayi muna hira ba kisamu kinyi wadataccen bacci ba, sannan yau da safe ma baki samu kinyi wani ishesshen bacci ba”.

    Gyara riƙon da taiwa plate ɗin tayi kana taci gaba da cewa.

    “Har yanzu ma baki samu kinyi Ummi, kiyi ƙoƙari kije ki kwanta Insha Allah zakiji dama dama”.

    Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.

    “Toh ki maida Plate ɗin kichen idan kin gama sannan ki rufe ƙofar kichen ɗin kana kizo ki rufe mana ƙofan falon”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa tare da cewa.

    “Toh”.

    Ta mike tare da ajiye Plate din ta kife Sauran abincin sannan ta rufe ƙofar tare da murza mukulli ta dawo.

    Still zaune ta samu Ummi tayi tagumi.

    Cike da kulawa tace.

    “Ummi kije ki kwanta dan Allah kiyi baccin”.

    Ahankali Ummi ta ɗago ta kalleta tare da sauƙe ajiyar zuciya kana tace.

    “Toh kije Insha Allah yanzu zan kwanta”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa kana ta wuce Bedroom ɗin ta Ummi kuwa kasa tashi tayi ahankali ta lumshe Idanunta tare da komawa ta kwanta akan kujeran still zuciyarta na cigaba da tsinkewa tana mai  maimaita kalmar Hasbunallahu wani’imal wakin aƙasan ranta.

     

    Acan ɓangaren Moddibo kuwa yana Picking call ɗin yakai kunnensa tare da cewa.

    “Assalamu Alaikum”. cikin sanyin murya M Arɗo ya gyara zaman wayar akunnensa tare da cewa.

    “Wai yanzu yaran nan tsakanin ku da Allah kun bar batun karantarwa Amakarantar nan kenan?”.

    Anutse Moddibo ya lumshe Idanunsa kana ya buɗe su cikin yanayin kasala da tsinkewar zuciyar da yake ji ya gyara zamansa tare da cije lips ɗinsa na ƙasa  yace.

    “Toh ka asamsa Sallamar da nayi maka mana Before ka fara ƙorafi da zakayi”.

    Girgiza kai Malam Arɗo yayi tare da cewa.

    “Toh Wa’ailaikum salam kune ai baki ɗaya kuke son caza min kai, baki ɗaya satin nan yashiga har ya fita amma baku zoba toh gashi yau jumma’a gobe Asabar za akoma shiyasa nace bari na kira ku kada ace baku zoba”.

    Iska mai zafi Moddibo ya fesar daga bakinsa tare da shafa sajensa kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.

    “Gaskiya baza mu zoba”.

    Asanyaye Malam Arɗo yace.

    “Toh meyesa”.

    Muskutawa Moddibo yayi tare da gyara zaman wayar akunnensa kana yace.

    “Ai mun riga da mun gama yi maka magana kayi haƙuri kawai ”.

     

    “Amma kunsan ina son koyar wanku Amakarantar nan ina jin dadin zama daku sannan ɗaliban ma suna jin daɗin koyarwanku, makaranta na ya cigaba adalilin kune  kada kuyi min haka”.

     

    “Malam kayi haƙuri da akwai Uzurin da yake gaban mu, wanda yafi wannan na tabbata badan wannan Uzurin ba babu dalilin da zaisa mubar koyar wa Amakarantar”.

    Cikin sanyi murya Malam Arɗo ya sauƙe Ajiyar zuciya kana yace.

    “Toh shikenan tunda abin ya zama haka dole in sawa zuciyata haƙuri amma kusa marmin wasu Malamai masu Hazaƙa, duk da nasan da wuya asamu kamar ku tabbas nasan nayi rashin zaƙaƙuran Malamai kamar ku”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana cikin sanyin murya yace.

    “Toh ba matsala zamu yi kokarin hakan”.

    Cikin sanyi Malam Arɗo yace.

    “Toh Nagode saida safe”.

    kana ya katse wayar.

    Moddibo kuwa cikin sauri zuciyarsa ya cigaba da bugawa yana bada sautin dif-dab-dif-daf ahankali ya ɗago wayar da niyyar kiran M Jameel cikin wani Irin yanayi ya dafe saitin ƙahon zuciyarsa jin yanda yake bugawa da azabebben ƙarfi yana cigaba da bada sautin dif-dif-dif rintse idanunsa yayi still hannunsa na dafe da saitin ƙahon zuciyarsa.

     

    Acan ɓangaren Gimbiya Bunayya kuwa har Misalin ƙarfe sha biyu da minti biyu na dare Uncle Naseer da Amina na zaune akan 2sitter suna hira.

    Yayin da ita kuma ke kwance a Bedroom ɗin ta kunneta maƙale da waya tana Magana da Hajiya Lami.

    Murmushi Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

    “Hajiya Lami ni dai yanzu Alhamdulillah buƙata ta biya hankalina ya kwanta, yanzu batun soyayyar Amina da Naseer ya kankama yayi zurfi”.

    Atake fara’ar dake fuskanta ya gushe ta mike ta zauna tare da cewa.

    “Yanzu kuma hankalina ya koma kan ƴaƴan wannan shegiyar matar mai kama da Mayyar wannan yaro mai ƙwala-ƙwalan ido daya karye nake son kawar dashi tun da shi wancan mai kama da Brolas ɗin Uwarsa ta shayar dashi saɓani, tunda kinga wannan hatsarin ma shi na shiryawa abi takansa amma, ba’a samu babban ba akabi takan ƙaramin”.

    Sai kuma ta sauƙe numfashi tare da jan dogon tsaki kana tace.

    “Dole saina koma na samu boka Kar’uzu da maganar ayi duk abinda za ayi nikam Haiydar shine babban matsala ta tunda shi Ramadan shine ƙarami akan Aminu, babu yanda za ayi Aminu na raye aɗauki Sarauta abawa Ramadan dole dai sai ɗana ɗin dai”.

    Cikin sauri Hajiya Lami ta katseta tare da cewa.

    “Kul-Kul Hajiya Bunayya  kada kiyi la’akari da wannan ƙaramin tunanin naki, ba kiji Malam Bahaushe na cewa ɗan hakin daka raina shike tsole maka Ido ba?.

    To ki rufa wa kanki asiri ki kawar dasu duka biyun hankalinki ya kwanta ki samu nutsuwa da salama aranki”.

    Kana ta saki wani murmushi tare da cewa.

    “Kinga idan kika gama dasu ɗaya ce zaki samu nutsuwa akanta itace Raudat da kuma Khausar.

    Kinga Khausar kuwa ba ƴar gidan bace babu yanda za ayi agola tavi gadon Sarauta koda na mijine bare kuma mace. Raudat kuwa ƙarama ce kuma mace.

    Amman Haiydar da Ramadan dai kaudasu, da kike batun Ramadan shine ƙarami a kan sulaiman, sau nawa manyan Yayu ke zaune ake bawa ƙannen su Sarautar, ni dai shawarar da zan baki yanda zaki gama da Haiydar haka zaki gama da Ramadan”.

    Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da gyara zaman wayar akunnenta kana tace.

    “Haka ne fa kuma aini duk wannan tunanin bai zo min ba, atunanina idan na kawar da Haiydar shikenan”.

    Girgiza kai Hajiya Lami tayi tare da faɗin.

    “A’a tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa, har kina wani batun shine ƙaramin akan Aminu ai ba’a wannan zancen kima rufawa kanki asiri, kigama dasu gaba ɗaya to asannan hankalin zai kwanta, ki samu nutsuwa  anan ne zaki tabbatar sarauta ahannun Aminu take, ke kuma kin zama Gimbiyar Gembulan Matar sarki Uwar sarki amma muddin ƴaƴan wancan koɗaɗɗiyar matar na nan keda Saurauta saidai hange daga naisa”.

    Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi cike da gamsuwa kana tace.

    “Aikuwa hakane Nifa duk wannan tunanin bai zomin ba shiyasa nake alfahari dake ƙawata.

    Insha Allah zanje muyi magana da boka Kar’uzu asan yanda za’a ɓullowa lamarin”.

    Kai Hajiya Lami ta gyaɗa tare da cewa.

    “Eh nima Insha Allah gobe idan muka je zan faɗa masa ya tsaida rana da Samira zata fara zuwa  wajensa suyi satin, tunda dai yace idan ya kusance tama zai mayar mata da budurcinta ai shikenan”.

    Atare suka sheƙe da dariyamai cike da farin ciki da annushawa kana Hajiya Bunayya tace.

    “Ai dai haka yafi shiyasa na yarda da aikin Boka Kar’uzu kamar yankan wuƙa dan sha yanzu magani yanzu ne tun yaushe muke bin boka bursunu tsawon shekaru ba biyan buƙata sai asaran kuɗi”.

    Jinjina kai Hajiya Lami tayi kana tayi mata Sallama suka katse wayar.

     

    Aɓangaren Abban M Jameel kuwa tsaye yake ajikin window falonsa ya tsirawa harabar gidan Ido tun bayan fitar Motar M Jameel ya kasa motsa wa daga wajen.

    Hajiya Karima data fito daga Bedroom ɗin sa ta dubesa cike da kulawa tace.

    “Ya dai Alhj tun tuni kana tsaye ana ka gaza motsa sama da awa biyu kenan tun bayan fitar motar  Jameel kake tsaye lafiya kuwa?”.

    Cikin wani irin yanayi ya lumshe idonsa.

    Haka nan yaji ruwan hawaye na tsats-tsafo masa a hankali ya sauƙe ajiyar zuciya tare da furzar da iska kana yace.

    “Haka nan dai narasa me nake tunawa awajen nan”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da dafa bayansa kana tace.

    “Toh kazo ka zauna mana”.

    Girgiza kai yayi tare da fesar da numfashi kana cikin sanyi murya yace.

    “Ina ga ko dan garin dana gani da alamun hadari ne ko yaya ne ban sani ba”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Toh kadawo ka zauna dan Allah tsayuwar tayi yawa”.

    Kai ya gyaɗa lokaci ɗaya yaji wani irin masifaffen rauni mai haɗe da bugun zuciya ya rufe sa Atake yaji Idanunsa na tsats-tsafo da ruwan hawaye masu ɗumi yayin da zuciyarsa ya cigaba da tsinkewa jikinsa na mutuwa tamkar ana zare masa laka cikin sanyi jiki yaja ƙafafunsa da yaji sunyi masa mugun nauyi ya zauna akan kujera tare da kwanciya akan 3sitter kana ya lumshe Idanunsa.

    Cike da kulawa tace.

    “Ya dai lafiya kuwa kashiga ciki mana?”.

    Girgiza kai yayi still zuciyarsa na cigaba da bugawa yayinda muryarsa ke ɗauke da rauni yace.

    “Please Karima ki barni in kwanta inaji kamar kaina na ciwo”.

    Cikin sauri tace.

    “Alhj kad dai BP kane?”.

    Girgiza kai yayi still Idanunsa na lumshe yace.

    “A’a ba BP na bane bari dai mu gani”.

    Zama tayi daga hannun kujeran kana tace.

    “Toh kasha maganin ka kuwa?”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Eh sosai ma yan zun nan kafin Jameelu ya fita ya bani nasha”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Eh ƙwarai kuwa hakane toh Allah ya sawwaƙa”.

    Ahankali yace.

    “Ameen”, Miƙewa tayi tare da shiga Bedroom ɗin sa ta kwanta.

     

    Ɓangaren Moddibo kuwa har Misalin sha biyu da kwata yana zaune dafe da ƙirjinsa dake cigaba da bugawa ahankali ya ɗago kansa tare da shafa gefen wayarsa  haske ya bayyana tare da nuna masa ƙarfe 12:15 afili ya furta.

    “Har yanzu J bai zoba”.

    Yayi mgnar tare da shiga Call log yayi dearling number M Jameel amma ga mamakinsa sai yaji Swich off.

    Cikin yanayin damuwa ya dafe kansa tare da cewa.

    “Ikon Allah lafiya kuwa wayar J arufe?”.

    Kallonsa ya mayar kan babbar wayarsa tare da ɗauka kana ya fito da ɗaya number M Jameel ya kira Shima still Swich off.

    Miƙewa tsaye yayi  ido a lumshe yace.

    “Ha’a ya wayar J akashe kuma dai J baya kashe wayarsa, to amma mai yafaru yau wayarsa akashe toh me yake faruwa bayan ya faɗa min yau zai dawo!?”,l.

    Yayi maganar cikin zulumi

    “Ya ilahi ya mujabat da’awati, to kuma ko kafin J  ya fito sai da ya kirni yace zaije wajen Abba ya sallame sa sannan yazo amma kuma har yanzu bai zoba”.

     

    Atake wata zuciyar tace kasani ko yazo suna tare da Innayi suna can suna ƙus-ƙus atake ya amince da abinda zuciyarsa ya raya masa cikin mutuwar jiki ya nufi ƙofan falonsa tare da buɗewa.

    Wani sanyayyan iska ya hurasa ahankali ya ɗaga kansa sama gani yayi hadari ya fara haduwa sai walƙiya dake  haskawa  can ƙasa alamun yanzu hadarin ya fara, garin ya danyu duhu sakamakon rashin wuta ga kuma hadarin,

    ahankali yabi sararin samaniyar da kallo ganin yanda hadarin yayiwa garin zobe kana aƙasan ransa yace to kodai wannan hadarin ne ya hana J zuwa sai kuma yace to kodai yana ɗakin Innayi ya faɗa yana taka step ɗin ahankali.

    Cikin sauri Innayi ta haske masa ido da touch light mai masifar haske cikin han zari ya Janye hannuunsa dake danne da J ɗinsa ya tare Idanunsa dashi saboda hasken touchlight daya haska masa ido.

    Cike da kulawa Innayi tace.

    “Moddibo ya dai lafiya ina zuwa Atsakiyar adaren nan?”.

    Ahankali ya sake sakƙowa daga kan step ɗin tare da jingina bayansa da jikin filan barandarsa, kana hannunsa na dama na kan flowes dake gefe yace.

    “Kece fa kike ganinsa tsakiyar dare ne, dudu shabiyu da rabi ne fa yanzu”.

    Kallonsa tayi tare da cewa.

    “Tsakiyar dare ne mana Moddibo yanzu fa ƙarfe shabiyu harda rabi ai tsakiyar dare ne, to amma me kafito yi lafiya dai ko?”.

    Cikin sanyin murya yace.

    “J ne har yanzu bai zo ba kuma ya fito akan zai zo ma ya kirani awaya kan cewa yanzu zai shiga wajen Abbansa ya masa saida safe ya fito, kuma har yanzu bai iso ba sannan nata kiran layukan sa basa shiga”.

    Ya ida maganar akasalance.

    Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe tare da cewa.

    “Toh dan bai zoba Moddibo ai ba abin tashin hankali bane, kaga yanayin wannan hadarin daya haɗu zai iya hanasa zuwa wataƙil daya shiga wajen Abban nasa zaice dare yayi kuma ga hadari ya bari sai gobe”.

    Da sauri ya katseta da cewa.

    “To ai Innayi wayarsa bata shiga fa”.

    Saurin Kallonsa Innayi tayi tare da cewa.

    “Ka kira layinsa duka?”.

    Kai ya jinjina mata.

    “Eh na kira layukansa duka fa basa shiga”.

    Cikin yanayin bacci ta kalli Moddibo tare da sakin hamma kana ta aro Jarumtaka tare da cewa.

    “To ko dai network ne?”.

    Lumshe Idanunsa yayi tare da Girgiza mata kai kana yace.

    “A’a ba network bane cemin akeyi akashe kuma fa Innayi J baya kashe wayarsa, ko zai kwanta komai yaya kuma nasan wayar J baya rasa caji”.

    A hankali Innayi ta rufe idonta jin kamar tsinkewar zuciya ya ziyarci ta.

    Amma sai ta daure kana tace.

    “To amma kaga jiya ma kace min wajen Umminsa ya kwana to ko dai yauma yaje  canne ne ya kashe wayarsa dan kada kayi ta kiransa?”.

     

    Jinjina kai yayi tare da faɗin.

    “Ok ba mamaki fa bari na kira Ummi”.

    Cikin sauri Innayi ta kallesa tare da cewa.

    “Aƙarfe ɗaya saura zaka kirasu?”

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Eh Innayi in dai har wurin Ummi yake nasan yanzu zasu ganshi kamar takwas na dare ne, saboda nasan yanzu suna hira ba suyi bacci ba.

    Kai Innayi ta gyaɗa tare da gyara tsayuwar ta kana tace.

    “Toh shikenan ka kira”.

     

    Dearling number Ummi yayu.

    Acan ɓangaren Ummi kuwa kwance take yayin da idanunta ke lumshe cikin tsananin tsinkewar zuciya da kasala jin rurin wayarta yasa ta miƙe firgice cikin yanayi sanyi  sanya hannunta na dama ta janyo wayar tare da ƙurawa screen ɗin Ido sunan Moddibo ke yawo.

     

    Cikin sauri tare da rawan jiki tayi Picking call ɗin tare da kaiwa Kunnenta batare data amsa Sallamar daya mata ba tace.

    “Babana Lafiya?”.

    Cikin ƙoƙarin danne damuwarsa yace.

    “Ummi lafiya ya naji kamar kin razana?”.

    Ahankali ta koma ta jingina bayanta da jikin kushin ɗin tare da lumshe idanunta kana cikin wata raunan’niyar murya mai cike da kasala da tsoro ta fesar da numfashi tare da cewa.

    “Gaba ɗaya ma ai. Arazanen nake Babana”.

    Moddibo kuwa cikin kasala da mutuwar jiki ya yaja numfashi tare da fesar wa kana yace.

    “To Ummi me yafaru?”.

    Buɗe Idanunta dake lumshe tayi tare da dafe ƙirjinta da still yake bugawa kana tace.

    “Ban saniba amma gaba ɗaya ina jina wani irin gani nan dai kamar mara lfy, kuma ba zance ga abinda yake damuna kai tsaye ba”.

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.

    “Toh amma Ummi lafiyar ki lau?”.

    Kai ta gyaɗa masa kamar yana gabanta kana tace.

    “Lafiya ta ƙalau,Amma Babana lafiya ka kira yanzu?”.

    Numfashi ya sauke tare da lumshe idanunsa kana ya sake jingina bayansa da jikin step ɗin tare da cewa.

    “Eh lafiya lau babu komai dama zan tambayeki ne ko dai J yazo yana wurinki ne munyi dashi tun ɗazu akan zai zo har yace min gashi ya fito amma zai sallami Abbansa ne kawai ya taho”.

    Sai kuma ya lumshe idanunsa tare da cijan lip ɗin sa na ƙasa kana yace.

    “Amma har yanzu be taho ba, inata jiran sa ko ƙofar gida bamu rufe ba, shiyasa nace bari na kira koya biya wajenki, da yake jiya ma nan ya kwana!?”.

    Rumtse ida nunta tayi da masifar ƙarfi k cikin wani azabebben tsinkewar zuciya da faɗuwar gaba ta buga hannunta na dama aƙirji tare da cewa.

    _“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n. Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan min_

    bai zo ba kuma yace maka zai zo?

    Abbansa kaɗai zai Sallama?”.

    Gyaɗa kai Moddibo yayi tamkar yana gabanta kana cikin raunan’niyar murya mai cike da sanyi yace.

    “Eh Ummi”.

     

    Cikin wani irin yanayi na taraddadin zuciya da rauni Ummi tace.

    “Ya Ubangiji Allah ka dubeni da Idon Rahma. Ya Allah ka tsare wannan bawan naka, aduk inda yake Alfarman Annabi da Alkur’ani”.

    Jin salatin da kuma yanayin da Ummi tayi Magana cikin firgici ya farkar da Asma’u, Bashir da Malam Ahmad Aruɗe Asma’u ta miƙe tare da dafe kanta da taji yayi masifar sarawa ta sauƙa daga kan gadon.

     

    Acan ɗakin  Bashir kuwa Hasbunallahu wani’imal wakin ya furta tare da sauƙa ƙasa kusan atare suka fito falon ko wannensu zuciyarsa na bugawa da kaso tamanin cikin ɗari.

    Moddibo kuwa cikin sanyu da ruɗu yace.

    “Ameen ya Allah Ummi ameen ya rabbil Izzati”.

     

    Cikin zulumi Ummi ta runtse Idanunta kana tace.

    “Amma Babana ka kira Abbansa mana”.

    Numfashi Moddibo ya fesar tare da kallon Innayi data tsaresa da ido cikin yanayin razani yace.

    “Eh Ummi nayi tunanin kiran Abbansa amma sai nace bari na fara kiranki tunda jiya yazo na, sannan Ummi nasan J baya kashe wayarsa rashin shigar wayarsa nema yafi damuna!”.

    Girgiza kai Ummi tayi yayinda ruwan hawaye masu masifar ɗumi suka cika kwarmin Idanunta kana cikin raunan’niyar murya tace.

    “Tabbas baya kashewa ka kira Abbansa kaji”.

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Eh dama zan kirasa amma Innayi tace ko Abbansa ne ya hanasa zuwa ganin hadari”.

     

    A hankali tace.

    “Anya?,Ka kira sa dai”.

     

    “Amma yanzu dare baiyi ba Ummi”.

     

    Cikin sauri tace.

    “A’a ka kira Babana ka kira Abbansa ɗin duk yanda kukayi ka kirani ka sanar min”.

    “Toh”.

    Moddibo yace kana ya katse kiran.

     

    Asma’u da Bashir kuwa zuru-zuru sukayi da ido domin suna iya jiyo sautin muryar Modibbo.

    Durƙusa wa Asma’u tayi tare da toshe bakinta kana tashiga.

    Girgiza kanta tare da cewa.

    “Ya Allah kada ka jarabcemu da abinda baza mu iyaba ɗaukaba Allah ka tsare Yaya Jameel aduk inda yake ya Allah kada ka bari wani abu na cutarwa ya sameshi”.

    Cikin raunin murya Ummi ta kalleta Atake  taji wasu hawaye masu masifar ɗumi sun zubo kuncinta.

    Ahankali Malam Ahmad da jikinsa yayi masifar sanyi ya ƙarasa kusa da Ummi.

     

    Moddibo kuwa yana katse kiran ya shiga contact tare da fito da Number Abban M Jameel.

    Kana ya Kalli Innayi cikin sanyin murya mai cike da tashin hankali yace.

    “Kin gani ko Innayi baya can. J baije gidan Ummi ba. Innayi ina J ya tafi bayan yasanar dani cewa zai taho”.

    Lokaci ɗaya wani masifaffen tsoro da tashin hankali ya ziyarci Innayi wanda ta kasa ɓoyewa har hakan ya bayyana asaman fuskarta dake nuni da tsantsar ruɗu.

    Cikin dakiya da kuma nuna masa babu komai insha Allah ta gyara tochligt dake hannunta kana tace.

    “Ka dai kira Abbansa muji wataƙil yana can tare dashi hadarin ne ya hanasa fitowa”.

    Kai ya gyaɗa mata tare da dearling number Abban M Jameel yana jin yanda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da masifar ƙarfi yana bada sautin dif-dumm-dif dumm.

    Abba dake kwance kan 3sitter Idanunsa arufe bacci ya fara fusgarsa yaji suwwan wayarsa Atsakiyar kansa afirgice ya miƙe tare da zama kana ya duba screen ɗin wayar nan yaga sunan Moddibo na yawo cikin rawan jiki yayi Picking.

    Atare Abba da Moddibo sukayi Sallama.

    Ahankali Moddibo ya sauƙe numfashin  tare da ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.

    “Wa’alaikum Salam Abba”.

    Cikin yanayin firgici da ruɗu Abba ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Na’am Aliyu ya akayi?”.

    Numfashi Moddibo ya fesar kana yace.

    “Lafiya Abba”.

    Kai Abba ya gyaɗa tare da jingina bayansa da jikin kushin kana yace.

    “Ya gida kowa lafiya dai?

    Jameelun yaƙara so yana lafiya ko?”.

    Lokaci ɗaya zuciyar Moddibo ya buga da masifar ƙarfi kana yayi saurin dafe ƙirjinsa tare da cewa.

    “Abba baya gidane”.

    Wani irin azabebben bugawa zuciyar Abba yayi kana yace.

    “A’a bakwa tare ne tun 10:15 ai ya sallameni yace min zai taho wurinka”.

    Moddibo kuwa da sauri ya rumtse idanunsa tare da dafe jikin step ɗin yana mai jin kansa na masifar sarawa tamkar zai rabe gida biyu cikin raunin murya yace.

    “Abba tun ƙarfe 10:15  ya fita kuma yace wajena zai zo? Abba tun ɗazu fa nake jiransa ko ƙofar gida bamu rufe ba har yanzu J bai zoba sannan fa nata kiran layukan basa shiga”.

     

    Cikin tsananin razani da tsinkewar zuciya Abba ya miƙe tsaye kana yace.

    “Aliyu mai kace?”.

    Araunane Moddibo da Idanunsa ke juyawa ya dafe kansa kana cikin sanyin murya yace.

    “Abba na yita kiran layinsa baya shiga”.

     

    A ruɗe Abba ya miƙa tsaye tare da cewa.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n to lafiya Aliyu?”.

    Girgiza kai Moddibo yayi tare da gyara tsayuwar sa kana yace.

    “Toh Abba kuma yace waje na ɗin zai taho?Abba J bai zoba bafa”.

    ya ida maganar cikin raunin murya mai cike da tsantsar tashin hankali.

     

    Atake zufa ya wanke wa Abba jiki duk da iskar dake kaɗawa d ƙarfi ya haɗiye wani abu mai ɗaci kana yace.

    “Ko dai gidan Ummin sa yaje”.

    Da sauri Moddibo ya girgiza kansa muryarsa na rawa yace.

    “Um-um Abba baya can yanzu nayi waya da Ummi itace ma tace in Kira ka Dan ni Ina tunanin dare ma yayi bazan kira ba”.

     

    Cikin tsinkewar zuciya Abba ya nufi ƙofar falon Hajiya Karima da sautin muryansa ya farkar da ita tayi saurin fitowa daga Bedroom ɗin Aruɗe ta kallesa kana tace.

    “Lafiya Alhj?”.

    Girgiza kai Abba yayi tare da cewa.

    “Jameelu ba agansa ba wai baije  wajen Moddibo ba sannan baije wajen Umminsa ba”.

    Da sauri ta dafe ƙirjinta kana tace.

    “Ba agansa ba kuma gashi yanzu ƙarfe ɗaya”.

    Kasa cewa komai Abba yayi ya nufi ƙofa da sauri.

    Tare da cewa.

    “Miƙo min key mota”.

    Cikin sauru tabi bayansa tare da Kallonsa ganin Gajeren wando da single ne kaɗai ajikinsa yasa tace.

    “Toh yanzu ina zaka je adaren nan??”.

    Cikin raunin murya yace.

    “Karima ina zanje kike tambaya ta?  Jameelu na fa baya gidansu Aliyu sannan baya gidan Umminsa to ina Jameelu yaje kinsan waye Jameelu da in dai baya nan yana gidansu Aliyu ko gidan Umminsa tabbas da akwai abinda yake faruwa”.

    Cikin sauri ta juya tare da komawa Bedroom ta dauƙa Masa Jallabiya da key mota kana ta sanya hijabinta ta fito tare da miƙa masa.

     

    Karba yayi yana tafiya yana saka jallabiyar kana ya nufi inda Motarsa yake ya shiga cikin sassarfa tabi bayansa yana shiga mazaunin Driver itama tayi saurin buɗe gefen mai zaman banza ta Zauna.

    Kallonta yayi tare da cewa.

    “A’a ki koma”.

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “A’a Alh ya za’ayi in barka ka tafi kai kaɗai muje dai”.

    Kai ya gyaɗa batare da yace komai ba ya figi motar.

    Suka tafi bayan mai gadi ya buɗe masa ahankali ya fara bin hanyar Yana dudduba gefen titin kana cikin sanyin murya yace.

    “To ko dai motarsa ta samu matsale ne?”.

    Girgiza kai Hajiya Karima tayi kana tace.

    “Idan ma motarsa ta samu matsala Alh ai saidai ya kira akawo masa wata”.

    Kai ya jinjina still Yana cigaba da Driving ɗin yayin da zuciyarsa ke cigaba da bugawa da kaso Cassa’in cikin ɗari suna cikin tafiya har suka isa gidan su Moddibo.

     

    Moddibo dake tsaye coumpund ɗin har zuwa lokacin ya gagara koda ƙoƙƙwaran motsi yayi saurin kallon gate ɗin ganin hasken mota Itama Innayi dake tsaye tayi saurin bin wajen da kallo zuciyarta na cigaba da bugawa.

    Cikin sauri tare da rauni yace.

    “Toh waye wannan ko dai motar J ne?”.

    Ya faɗa tare da nufar gate ɗin Innayi kuwa ido ta zuba masa har ya buɗe gate.

    Moddibo kuwa yana buɗe gate din idanunsa suka sauƙa akan motar Abba.

    Cikin sauri ya ƙarasa jikin motar tare da cewa.

    “Abba kaine?”.

    Jinjina kai Abba yayi asanda ya ƙarasa fita daga motar kana cikin raunin murya yace.

    “Eh Nine Aliyu ina tsammanin Jameelu yana nan to idan ba nan ba ina Jameelu zai je adaren nan.

    Amma anya ka bin cika baya gidan Umminsa ba wasa take mana ba?”.

     

    Girgiza kai Moddibo yayi cikin mutuwar da jiki da rauni yace.

    “A’a Abba baya can tunda nayi magana da Ummi kuma yanzu da muka gama waya da kai ma na kirata nace baya can itama kuka fa takeyi”.

    Cikin ruɗu da rashin sanin madafa Abba yace.

    “Toh kazo muje can ɗin mu duba may be ko motarsa ta ɓaci ahanya can ya nufa”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa tare da faɗin.

    “To bari in ɗauki motata dan nasan Innayi ma bazata zauna ita kaɗai agida ba”.

    Ya faɗa tare da shigewa cikin gida kai tsaye falonsa ya nufa ya ɗauki key sannan suka fito da Innayi acikin motar.

    Motar Modibbo ce ta shiga gaba na Abba na biye da ita tuƙi kawai Moddibo yake amma baki ɗaya baya cikin nutsuwarsa.

     

    Acan gidan Ummi kuwa tunda Moddibo ya sanar mata M Jameel baya gidan Abba hankalinta yayi masifar tashi ta fito coumpund ta tsaya tana kuka yayinda Asma’u da Bashir ke taya ta cikin tsanananin kaɗuwa.

     

    Cikin rarrashi da nasiyya Malam Ahmad ke tausanta dasu Asma’u.

    Cikin sauri Ummi ta ɗaga kanta ganin hasken motoci abakin gate ɗin gidan su.

    Aruɗe ta kallesa tare da cewa.

    “Ka kalli hasken mota Malam ko dai Jameelu ne?”.

    Cikin sanyin murya yace.

    “Ki kwantar da hankalin ki Fatima dan Allah ki nutsu Insha Allah babu komai, ba abinda zai samu Jameelu”.

    Kai ta girgiza kana tace.

    “A’a to ai naga hasken mota ne”.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da riƙe hannunta ganin yanda ta firgice kana yace.

    “Toh bari naje na duba naga ko waye ne”.

    Kai ta girgiza kana cikin raunin murya tace.

    “A’a to muje dai”.

    Kai ya gyaɗa tare da yin gaba kana tabi bayansa Malam Ahmad na buɗe ƙaramar ƙofa yaga motar Moddibo daf da bakin gate Dai-dai lokacin Moddibo ya buɗe Murfin motar ya fito.

    Cikin sauri Ummi ta kallesa tare da leƙa motar dake bayansa kana tace.

    “Babana”.

    Cikin sanyin murya yace.

    “Na’am Ummi J bai zo nan ba dagaske?”.

    Cikin muryan kuka ta girgiza kai kana tace.

    “A’a bai zo bafa Babana idan yazo ya za ayi in ɓoye muku”.

     

    Cikin mutuwar jiki Abba ya buɗe Murfin motar tare da fita kana ya kalli Ummi da hawaye ke bin kuncinta yace.

    “Fatima”.

    Saurin Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.

    “Abban Jameel”.

    Cikin yanayin tashin hankali yace.

    “Da gaske Jameelu bai zoba?”.

    Kai ta gyaɗa Masa still Hawaye na bin kun cinta tace.

    “Bai zoba kuma nata kiran wayoyinsa basa shiga”.

    Cikintashin hankali da ruɗu suka haɗa baki wajen furta.

    _“Innalillahi Wa’inna Ilahi rajiu’n Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha”_.

    Cikin sanyi Moddibo ya kalli Abba da idanunsa suka sauya launi saboda tashin hankali kana yace.

    “Abba mu koma ta hanyar gidaku mu duba ko dai motarsa ta samu matsala ne ko kuma yayi hatsari ne?”.

    Kai suka gyaɗa cikin sauri Ummi ta juya tare da kallon Moddibo kana tace.

    “Bari na ɗauko hijabina muje tare”.

    Bata jira jin abinda zasu ce ba ta juya da sauri ta koma tare da ɗaukan hijabinta ta fito coumpund ɗin kallon Asma’u da Bashir tayi wanda har zuwa lokacin suna cikin ruɗani, cikin Muryan kuka tace.

    “Asma’u ku  kula da kanku zamu duba hanya ko Allah zaisa mu gansa”.

    Cikin sauri Asma’u tace.

    “Ummi zamu biku”.

    Girgiza kai Ummi tayi tana tafiya tace.

    “A’a ku zauna kada ku fito”.

    Daga haka ta fice Malam Ahmad na ƙoƙarin ɗauko mota Moddibo yace.

    “Ummi kuzo ku shiga motata kawai”,

     

    Kai ta gyaɗa kana tashiga bayan motar kusa da  Innayi.

    Malam Ahmad kuwa a gaba, kana suka fara tafiya koda da irin tunanin da yake Aransa duk wani inda suke tunanin mota zai iya maƙalewa ko kuma hatsari sun duba amma babu M Jameel da motarsa babu dalilinsa har unguwar su Abba suka koma amma still Babu shi babu dalilinsa.

     

    Cikin yanayin gajiyawa da ɗimuwa Abba ya buɗe Murfin motar ya fito kana Moddibo da sauran ma duk suka fito.

    Cikin raunin murya me nuni da razani Abba yace.

    “Gashi mun biyo har nan ma amma baya nan, to mu gwada zuwa asibiti mu duba ko dai yayi hatsari ne ko yaya”.

    Cikin raunin murya Moddibo ya Girgiza kai kana yace.

    “Abba hatsari kuma? Ai da hatsari ne da munga mota kuma da ankira mu”.

    Kafin Abba yace wani abu Innayi ta kalli Moddibo tare da cewa.

    “Eh muje dai asibitin saboda Kore shakku”.

    Jinjina kai sukayi tare da shiga motar kana suka nufi Asibitin.

    Ahankali Moddibo ya kalli Innayi kana yace.

    “Toh wani asibitin zamuje kin san dai bawasu manyan asibiti muke dasu ba”.

    Cikin sanyi malam Ahmad yace.

    “Mu fara zuwa babban asibitin idan yaso sai mu duba sauran daga baya”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa tare da nufar babban asibitin Abba na biye dasu.

    Suna isa suka tarar da gate din asibitin arufe kasancewar har biyu tayi,sauran asibitin suka shiga zagayawa amma ko wanne arufe in sun buga an buɗe musuma in sun shiga bashi ba lbrinsa.

    Cikin han zari Abba ya cewa Moddibo su nufi Private hospital ɗin Abba haka kuwa akayi.

    Suna isa Moddibo ya sauƙa tare da nufar cikin Hospital kana ya tambayi Norse dake aiki ko M Jameel yazo suka ce a’a juyawa yayi ya shiga motar kana suka ci-gaba da nemansa.

    Wasa gaske fa babu Jameel ba dililinsa ba motarsa, gaba ɗaya sun shiga ruɗu  da zulumi gamida tsoro.

     

    Misalin ƙarfe uku hankalin su ya kai ƙololuwa wajen tashi baki ɗaya sun cika da damuwa zuwa wannan lokacin sun tabbatar ba lafiya domin M Jameel baya yawo sannan Gembulan ba wani babban gari ne da keda charking point ba bare su kai report.

    Moddibo kuwa banda tasbihi da kiran sunan Allah babu abinda yake Aransa yayin da kasala da mutuwar jikinsa ke ƙaruwa fiye da farko kana ga hadarin da zuwa yanzu yayi gangami asama da alamar ruwa na gab da sakƙowa, dan tuni aka fara yayyafi.

     

    Abba kuwa tunda suka fito a asibiti ya kifa kansa ajikin motar zuciyarsa na bugawa da masifaffen ƙarfi cikin raunin murya yace.

    “Acikin wannan daren ga hadari na kira layukan Jameeluna duka basa shiga a wannan yanayin ina Jamilu na ya shiga”.

     

    Cikin  raunin murya mai cike da karaya Modibbo ya fesar da numfashi mai zafi kana yace.

    “Yanzu acikin daren nan ina J yake?.

    Wani hali yake ciki?.

    Wani irin yanayi yake cikin a wannan daren da kuma hadarin da yake tasowa ina J ɗina yake!?”.

     

    Cikin ƙarfin hali Malam Ahmad ya numfasa kana yace.

    “Insha Allah ba komai mu bari muga zuwa safiya abinda Ubangiji zai yi”.

     

    Cikin tsanananin rauni Ummi ta kife kanta da jikin kujeran Motar  kana ta fashe da wani Marayan kuka mai gunji”.

     

    Cikin damuwa da kuma tausayawa Abba ya juya tare da kallon Malam Ahmad kana yace.

    “Malam ku tafi gida kaima Moddibo ku koma gida da Innayi kada ruwan nan ya saƙƙo muna nan duk inda ya kamata mu duba mun duba baya nan bari mu gani zuwa safiya”.

     

    Girgiza kai Moddibo yayi  Araunane yace.

    “Abba ya za ayi mu koma mu shiga cikin gida mu samu mafaka bayan bamu san halin da J yake ciki ba. Abba ina kake tunanin zamu koma mu samu nutsuwa acikin wannan yanayin bayan bamu san ina J yake ba!?”.

     

    Kallonsa Abba yayi cike da rauni yace.

    “Toh Aliyu ina zamuje mu duba?, Duk inda ya kamata mu duba mun duba sannan wayoyinsa basa shiga wannan shine babban tashin hankalina mu koma gida muyi alwala mu sanar wa Ubangiji halin da muke ciki Aliyu”.

    Jinjina kai sukayi atare cike da gamsuwa da abinda yace sam tashin hankali da ruɗanin da suke ciki yasa sun kasa samun nutsuwar da zasuyi addu’a.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.

    “Toh Abba”.

    Sannan suka shiga mota Abba yaja ya nufi gidansu cikin tashin hankali da ɗimuwa yayin da Hajiya Karima ke kuka Abba kuwa ko da kallonta ya gagara yi bare kuma ya iya lallashin ta.

    Ya yinda Moddibo ya nufi gidan Ummi babu abinda ke tashi acikin motar banda sheshsheƙan Kukan Ummi ta rasa shin wani irin tunani zata yi shin ina Jameelunta yake awannan tsohon daren Akuma irin wannan lokacin.

    Moddibo kuwa cikin tsananin damuwa da zulumi da macewar jiki ya cigaba da Driving har ya isa kofar gidan yayi Parking.

    Fita Malam Ahmad yayi Ummi ma ta sauƙa suka nufi cikin gidan.

    Ganin hasken mota yasa Bashir miƙewa da sauri tare da buɗe ƙaramin gate ɗin.

    Cikin sauri Asma’u da har zuwa lokacin take zaune ta ɗago kanta tare da miƙewa ta riƙe hannun Ummi kana tace.

    “Ummi Ina Yaya Jameel Ummi kunga Yah Jameel?”.

    Cikin sanyi Ummu ke jujjuya mata kai.

    Ita kuwa a ɗimauce tace. “Ummi to ina yashiga awannan daren dubi hadari fa wani hali yake ciki?”.

    Girgiza kai Ummi tayi tare da fashewa da kuka kana tace.

    “Ban saniba Asma’u Bansan inda Jameelu na yake ba, bansan halin da yake ciki ba Asma’u zuciyata zafi take jinake tamkar kaina zai rabe gida biyu!”.

    Aruɗe Asma’u tace.

    _“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha_, nashiga uku Yah Jameel”.

    Cikin sauri Malam Ahmad ya riƙe hannun Asma’u ganin kamar bata hayyacinta kana yace.

    “Subhanallah Asma’u da iliminki kike kirawa kanki shiga uku kada ki sake haka Addu’a ya kamata mu masa kunji ko?”.

    Kallonsa ya mayar kan Bashir kana yace.

    “Kuzo mushiga muyi masa addu’a ayanzu ba kuka Jameelu yake da buƙata daga wajen muba face adduoi”.

    Kai suka gyaɗa sannan ya sake hannun Asma’u ya riƙe na Ummi Bashir kuma yarike hannun Asma’u suka shiga ciki kai tsaye ko wannensu toilet yashiga ya ɗaura Al’wala kana ya fito suka shimfiɗa Sallaya tare da fara jera nafillah suna roƙon Allah daya fitar da M Jameel aduk halin da yake ciki.

     

    Moddibo kuwa suna isa gida yayi Parking tare da rufe ƙofar kana ya wuce falonsa yayin da Innayi ma tashige sashen ta yana shiga kai tsaye toilet dake falon ya shiga ya ɗaura alwala kana ya fito ya shimfida Sallaya cike da nutsuwa ya fara Sallah kana duk sujjadar da zaiyi sai ya roƙi Ubangiji ya kare J ɗin sa aduk inda yake”.

    Baki ɗaya su haka suka raya wannan daren cike da bautar Ubangiji tare kuma da rokon Allah daya bayyanar da M Jameel kana Allah yaraba sa da duk kan sharrin Mutum da Aljan.

     

    Bayan an kira Assalatu Moddibo ya fito ya nufi masallaci ana idar da sallah kai tsaye gidan Abba ya nufa.

    Yana isa kiran Ummi na shiga wayarsa ciki. Sanyin jiki  ya ɗaga wayar tare da kaiwa kunnensa kana yayi Sallama.

    Cikin dashashshiyar murya Ummi ta amsa Sallamar sa kana tace.

    “Babana ya labarin Jameelu na?”.

    Cikin sanyin murya yace.

    “Ummi nima gashi yanzu nazo wajen Abba naji ko ya dawo gida”.

    Dai-dai lokacin Abba ya buɗe gate ya fito ganin Moddibo tsaye yasa ya isa wajensa ahankali Moddibo ya zare wayar daga kunnensa bayan yace anjina zai kirata.

     

    “Aliyu dama yanzu zanje wajenka”.

    A hankali Modibbo yace.

    “Abba to yanzu ya zamuyi”.

    Numfashi Abba ya fesar tare da cewa.

    “To mu tafi police station  Jiya Baki ɗaya ba muyi tunanin zuwa can ba”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana suka shiga motarsa yaja Abba kuwa jingina da jikin kujera yayi baki ɗaya zuciyarsa ta tushe ya rasa wani irin tunani zaiyi yayin da Idanunsa suka tsats-tsafo da ruwan hawaye.

    Moddibo kuwa Driving yake amma baki ɗaya baya fahimtar komai ko gilmawar mutum ya gani sai yaga kamar J ɗin sane.

    Suna isa yayi Parking atare suka fito daga motar tare da shiga station din Dpo dake ƙoƙarin fita yayi Murmushi tare da cewa.

    “Alh Bashiru maidala Barka da zuwa kaine da kan ka?”.

    Jinjina kai Abba yayi kana cikin sanyin murya yace.

    “Na kawo report ne ɗana Jameelu ne bamu ganiba”.

    Cike da mamaki da kuma  al’ajabi Dpo da sauran folisawan suka ce.

    “Ɗan ka Jameelu kuma?”.

    Kai Abba ya gyaɗa kana yace.

    “Eh tun jiya ba agansa ba kuma babu motarsa sannan akira layukan sa basa shiga”.

    Cike da jimami Dpo yace.

    “Subhanallah Alhj mai yasa baku kawo report tun dare ba!?”.

    Numfashi Abba ya fesar kana yace.

    “Yanayin hadari ne sannan baki daya hankalin mu baya Jikin mu sai mukayi tunanin bari muyi addu’a mu kaiwa Ubangiji kukan mu”.

    Daga nan yayi miki bayanin dukkan abinda ke tafiya.

    Kai Dpo ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh shikenan Alhj insha Allah yanzu zamu kira hedquater mu na cikin Taraba afaɗa musu halin da ake ciki”.

    Kai Abba ya gyaɗa kana yace.

    “Toh shikenan mun gode”.

    Moddibo kuwa tun da suka shiga ya jingina da jikin bango Ya Lumshe Idanunsa yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi bai ce komai.

     

    Wunin wannan ranan baki ɗaya haka gidaje uku sukayi sa cikin zullumi,fargaba da kuma tsantsar tashin hankali Moddibo kuwa duk bayan minti biyu sai ya kira Number M Jameel aƙalla daga Jiya da daddare zuwa yau ya kira wayarsa yafi sau ɗari.

    Acan ɓangaren Ummi ma haka yakasance bini-bini zata kira layin sa amma amsar ɗaya ake basu shine Switch off.

    Haka zalika Abba time to time zaiyi try number M Jameel amma akashe Wunin wannan ranan baki ɗaya sunyi zuru-zuru dasu kallo ɗaya zaka musu kasancewa suna cikin tsananin tashin hankali da ɗimuwa duk inda ya kamata su nema ko su bincika duk sun nema sun bincika amman ba lbri.

    Abba kuwa zama yayi afalonsa tare da kira duk wani danginsa ko kuma abokin arziki ko zaiji Jameelu yaje amma kowa amsa ɗaya yake basa baije ba.

    Haka zalika Ummi baki ɗaya ta kira danginta ko M Jameel yaje amma suma dai amsar ɗaya ce baije ba.

     

    Wunin wannan ranan har dare babu M Jameel babu labarin sa zuwa wannan lokacin tsananin tashin hankali da ruɗun da suke ciki ba zai misaltuba.

     

    Da daddare Misalin ƙarfe goma Moddibo ne zaune a falon Abba kansa aƙasa yayinda idanunsa suka kaɗa sukayi ja jawur kana jijiyoyin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu rabonsa da bacci tun daren shekaran jiya haka zalika yauma koda runtsawa ne yakasa kana ya sanya duka hannunsa biyu ya dafe kansa dashi zuwa lokacin baki ɗaya ya kasa control ɗin kansa kife kansa yayi ajikin kujera tare da fashewa da kuka mai gunji.

    Cikin wata raunan’niyar murya mai cike da karkarwa yace.

    “Abba ina J yake? Abba ina J ya tafi ya barni Abba wani hali J yake ciki?”.

    Hajiya Karima ce  tashigo falon bakinta ɗauke da Sallama tare da kallon Moddibo dake kuka tamkar ƙaramin yaro lumshe Idanunta tayi tare da cewa.

    “Haba Aliyu kuka kuma kai da ya kamata ka tausashi Mahaifinsa sannan kuma ka zauna zakuyi ta kuka atare kenan?”.

    Karo na farko kenan arayuwar data yi masa magana cikin taushin lafazi.

    Ahankali Moddibo ya ɗago kai ya kalleta still yana kuka yace.

    “Aunty Karima ina J yake Ina J ɗina yashiga ya barni?”.

    Cikin rauni Abba ya ɗago idanunsa da hawaye ke zuba Akuma dai-dai lokacin wayar Abba ta ɗauki ruri yana ɗagawa yaga number ce ba suna sai ya mayar ya ajiye.

    Kallonsa Moddibo yayi tare da faɗin.

    “Abba waye ne?”.

    Ciki Sanyin Abba ya kalli wayar kana yace.

    “Numbar ce ba suna”.

    Cikin muryan kuka Moddibo yace.

    “Toh Abba ka ɗaga mana ko za’a faɗa mana anga J ne”.

    Cikin sauri Abba yayi Picking call ɗin tare da cewa.

    “Assalamu Alaikum”.

    Daga ɗaya ɓangaren cikin wata bauɗaɗɗiyar murya aka amsa da.

    “Wa’alaikum Salam kaine Alhaji Bashiru Maidala mahaifin Malam Jameelu?”.

    Cikin sauri Abba ya gyaɗa kai tare da miƙewa tsaye kana yace.

    “Eh nine mahaifin Jameelu”.

    Cikin sauri Moddibo ya miƙe tsaye,

    itama Hajiya Karima cikin sauri ta miƙe tsaye.

    Gyaran murya yayi kana yace.

    “Toh Jameelu yana wajen mu”.

    Cikin rawan baki Abba yace.

    “Jameelu yana wajen ku yana cikin halin lafiya? To a ina kuke?”.

    Kai tsaye yace.

    “Eh gashi ma kaji muryarsa”.

    Ya faɗa tare da miƙawa M Jameel wayar.

    Cikin sauri Abba yace.

    “Jameelu”.

    M Jameel kuwa cikin wata raunan’niyar murya me cike da galabaita da tashin hankali kamar wanda yayi kuka yana sauƙe ajiyar zuciya yace.

    “Abbana”.

    Cikin rawan jiki da rauni Abba yace.

    “Na’am Jameelu Meye sameka?,Aina kake?”.

    Ajiyar zuciya mai nauyi M Jameel ya sauƙe cikin rauni da yanayi wahala yace.

    “Abba nima ban sani ba  bansan inda nake ba Abba ina A.J”.

    Cikin muryan kuka Abba ya kalli Moddibo da jikinsa ke rawa kana yace.

    “Gashinan”.

    Ahankali M Jameel dake sakin ajiyar zuciya yace.

    “Abba ka bashi wayar”.

    Miƙawa Moddibo wayar Abba yayi cikin sauri Moddibo ya amsa tare da mannawa akunnensa kana Yace.

    “Jyyyyyy”,yaja sunan cike da taraddadi.

    Fesar da numfashi M Jameel Yayi tare da cewa.

    “AJ”.

    Cikin yanayin rauni da tausayawa ya lumshe idanunsa tare da cewa.

    “J ina kake?”.

    Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.

    “AJ ban sani ba bansan inda nake ba, ban san ida suka kawoni ba”.

    Cikin sauri aka Fisge wayar daga hannun M Jameel kana cikin wannan bauɗaɗɗiyar murya akace.

    “Ka bawa mahaifinsa waya”.

    Ahankali kuma cikin sanyi Moddibo yace.

    “Waye kai ina J yake?”.

    Cikin wata razananniyar tsawa yace.

    “Kabawa mahaifinsa waya ba da kai muke son magana ba?”.

    Moddibo kuwa Girgiza kai yayi kana yace.

    “Toh me kuke so ku faɗa min ko mameye”.

    Cikin sauri Abba ya janye wayar daga kunnensa tare da sa wayar a handsfree kana yace.

    “Gani mahaifin Jameelu”.

    Daga ɗaya ɓangaren mutumin yace.

    “Jameelu yana hannunmu bawai mun sace sa dan mu kashe sa ko wani abu bane amma idan kuka yi mana taurin kai zamu iya kash”…

     

     

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa 1k ne kacal ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

     

     

     

    *By*

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 9

    Sakayyah 9

     

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 9_

     

    NA

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE NE ƴar uwa ki biya ki karanta abinki cikin Salamah, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Kana in saki a Groups da na buɗe ba SAKAYYAH in da zaki karanta abinki salamun ƙaulum min rabbil rahim. Nama lfy fata lfy. Ba ruwan ki da jiran na sata na Allah ya isa*

     

     

    Cikin nitsuwa yake tafiya, tare da taka steps ɗin a hankali, yana  sauƙa ƙasa, yayinda hankalishi baki ɗaya ke bisa system nashi dayake kan hannunsa na dama yana daddanashi da hannun hagunsa, bisa dukkan alamu.

    Abu mai mahimmanci ne yakeyi.

     

    A dai-dai lokacin kuma Khausar ta iso bakin steps ɗin, cikin sauri take tafiya, da alamun tsoron kada malami ya rigata  shiga aji ne.

    Da sauri take tattaka steps ɗin tanayi sama.

    Steps biyu ta taka ana uku, taji juyo da kanta da sauri dan jiyo muryar M Jameel na ce mata.

    “Khausar sai yanzu?”.

    Ba tare da ta tsaya ba, kana bata kuma juyo kanta ba taci gaba da tafiya a haka, hannunta na kan da ƙarfe dake gefen steps ɗin cikin yanayin sakewarta da M Jameel ɗin tace.

    “Wallahi tun ɗazu muka iso fa Malam”.

    Yana mai binta da ido yace.

    “To kuma meya hanaki shiga class?”.

    Still bata janye kanta daga kallonsa ba, kana bata tsaya daga haurawa saman da takeyi ba tace.

    “Raudat ce ta tsaidani a side ɗin su”.

    Da sauri yace.

    “Da me ta tsaida ki?”.

    Ɗan guntun murmushi tayi tare da cewa.

    “Wai ƙwarone ya shiga idonta, shinefa tai ta ihu taƙi sakina dole saida aka cire matashi Allah sai kaga yadda idonta yayi jazir”.

    Kanshi ya sunkuyar yana ɗan murza zaɓen azurfan dake yatsar  yace.

    “Ayya kwaro bai kyauta ba ya shiga idon Gimbiya Raudat”.

    “Ai dai kam fa”.

    Ta faɗina tana mai ƙoƙarin juyo kanta.

    Cikin tsokana yace.

    “Gashi kuwa har Malam Moddibo ya shiga ajinku”.

    Cikin sauri ta kuma juyo kanta da dama bata gama juyashi ba cike da kaɗuwa tace.

    “Da gaske?”.

    Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

    “Tun ɗazuma kuwa”

    Cikin yanayin tsoro ta ɗan zaro manyan udanunta tare da cewa.

    “Na shiga ukuna”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.

    “Ato kiyi sauri ki hau, in kinyi sa’a ya barki ki shiga”.

    Jin haka yasa ta juyo da sauri tare da taka step ɗin gaba kana tayi kwanan haurawa kam steps ɗin da zai sadata da sama.

    Wanda kuma dai-dai lokacin Moddibo ma ya taka step na ƙarshen kwanan.

    Unexpected taji tayi karo da mutu.

    Shi ma Moddibo ba zato ba tsammani yaji kanta ya bugi ƙirjinsa yayinda hannunta ya bugi System ɗin dake hannunsa ya subce ya tafi ƙasa da sauri ya sunkuyo ya cafe system ɗin da kana ya miƙe tsaye,

     

    Ita kuwa Khausar cikin sauri ta ɗago kanta dai dai lokacin kuwa ya ɗago kansa shima ido cikon ido suka kalli juna kamar a fuzge ya furta.

    “Again?”. a lokacin guda kuma, cikin tsananin takaici da zafin rai ya ɗaga tafin hannunsa na hagu ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari mai masifar zafi gami da raɗaɗi.

     

    M Jameel kuwa jin sautin sauƙan marin ne yashi ɗago kansa da sauri.

     

    Ita kuwa Khausar wani irin gigitaccen ihu mai cike da rauni tare raɗaɗi ta saki, tare da dafe kuncinta kana ta rumtse idonta wanda duhu mai tarin yawa ya mamaye mata gani, kana tayi taga-taga ta koma baya zata faɗi, jin ta tafi suuuuu ƙafarta ta sule yasa takuma sakin wani ƙaran tare da buɗe idanunta, sai kuma tayi sauri ta medasu ta rufe sabida ganin wasu irin taurarin masu wutsiya da tartsatsi suna gilmawa ganinta sabida zafin marin da yasa suka mamayewa ganinta.

     

    Gaba ɗaya ta sadakar domin tasan muddin ta faɗo nan to ita da karaya sun zama aminan juna.

     

    M Jameel kuwa kanshi ya riƙe da hannu bibbiyu tare da faɗin.

    “Innalillahi!!”.

    Wanda faɗin hakane ya jawo hankalin Malam isa da yazo wucewa ta gefensa.

    Shima ma Malam isa idonsa ya rumtse da ƙarfi tare da cewa.

    “Yah Salam”.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin takaici yayi sauri miƙa hannunsa da nufin kamo hannunta amman ina tuni tayi nisa.

    Sai yatsunta biyu ya samu ya riƙe da masifan ƙarfi.

    Wanda saida suka bada sautin ƙas-ƙas.

    Cikin zafin nama ya fincikota da ƙarfi wanda hakan yasa ta afka jikinsa.

     

    Ita kuwa Khausar jinta a jikin mutum ne yasa tayi masa wani irin sahihin rugguma mai cike da razani dan gani take kamar dai har yanzu bata tsira ba.

    Kanta ta cusa cikin ƙirjinsa tana mai shaƙan turarensa mai masifar ƙamshi.

    Wanda a take nitsuwarta ta fara dawowa.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin tsoro da wani irin masifeffen abu da yaji ya soƙi tsakiyar kansa har zuwa cikin ƙahon zuciyarsa kana ya harba masa wasu irin masifaffun baƙin al’amuran a cikin jijiyoyin jikinsa da suka sa jikinsa sakin wani irin masifeffen karkarwa da sabauta aniyarsa, ya ware hannunsa tare da rumtse idanunsa da masifan ƙarfi.

     

    M Jameel kuwa ajiyan zuciya mai ƙarfi ya sake tare da jingina bayansa da jikin ƙarfen.

    a hankali ya kuma sakin numfashi tare da kallon yadda Moddibo ya buɗa hannayensa duka biyu kana ita kuma Khausar tana kwance bisa ƙirjinsa tayi lip tana ruggume dashi da masifan ƙarfi.

     

    Wani irin shu’umin dariya mai sauti M Jameel ya sake.

    Wanda hakan yasa Moddibo buɗe idanunsa kana dai-dai lokacin yaji gaba ɗaya tsikar jikinsa na tashi.

     

    Malam isa kuwa sunkuyar da kansa yayi yana murmushi.

     

    M Jameel kuwa dariya yake tare da nuna Modibbo da Khausar ɗin wacce tuni fuskarta tayi jazir shatin yatsun hannunsa sunyi ruɗu-ruɗu a farar fatarta.

    Cikin sauri Moddibo ya ɓalle hannunta daga jikinsa tare da matsawa gefe da sauri.

    Wani irin tsuke fuskarsa yayi tare da watsa mata kallon da yasa hantar cikinta kaɗawa.

    Wanda cikin rawan jiki da rawan murya cike da rauni tace.

    “Ana Aspet ya Mu’allim Allah mi larai ma on! Please! Kayi haƙuri”.

    Ta ƙare mgnar cikin tsoro tare da gwamusa yaruka hudu duk a wuri ɗaya dan neman afuwa.

    Shi kuwa Moddibo juyawa yayi tare da ratsa gefenta ya wuce kana cikin wata fusatacciyar murya mai matuƙar firgitarwa yace.

    “Biyoni!”.

    Cikin ɓarin jiki tace.

    “Toh”.

    Sannan ta miƙe tabi bayansa.

     

    M Jameel dake riƙe da System ɗin yana juyawa yayi saurin bin bayansa da faɗin.

    “Alhamdulillah kamar babu abinda ya samu System ɗin”.

    Shi dai Moddibo ko juyawa baiyi ba bare kuma ya tankawa M Jameel.

     

    Malam Isa kuwa dake ƙasa ido ya zirawa Khausar dake sauƙwa dafe kuncinta da kunne ya da tun da tasha marin ya bada sautin kauwww har yanzu ƙaran takeji, kana ga idanunta da suka kaɗa sukayi jawur asanda ta saƙƙo yace.

    Fattanah sam bakya yin abinda ya dace a rayuwarki”.

     

    Cikin zafin raɗaɗin marin da fuskarta keyi ta ɗago Idanunta da suke sake girma da ja ta kalli Malam Isa sai kuma tace.

    “Wallahi bansa niba ne na juya ina kallon Malam Jameel ne dake yimin magana ne mukayi karo”.

    Bata jira jin abinda zai ce ba tabi bayan M Jameel dake biye da Moddibo.

     

    Cak Khausar ta tsaya daga bakin Office ɗin, karo na farko kenan arayuwarta da zata fara shiga Office ɗinsa, duk da cewa da basu da office da yawa, amma yanzu gyaran da akayi an haɗa Malamai biyu akan Office  ɗaya Office din ba wasu masu girma bane, haka zalika ba ƙanana bane, sannan duk kusan ajere suke.

    Ahankali Khausar ta maida Idanunta bakin office ɗin da akasa wasu irin flowes masu launi mai kyau da ɗaukar hankali aka jera suna fitar da wani irin sanyayyan ƙamshi.

    Cikin Office ɗin kuwa Madaidaitan deks ne da kujeru ɗaya na fuskantar gabar ɗaya na fuskantar yamma daga gaban ko wanne kuma akwai kujeru guda biyu daga kan deks ɗin daga gefen damar sa akwai wani Cubet kamar kanta dake ɗauke da tarin littattafai na addini da kuma na boko cikin wajen kamar dai Library haka wurin yake.

    Daga gefen hagunsa kuma flowes ne masu  kyau da tsari daga jikin bangon kuma Room hitane ne maƙale abango yana fitar da ɗumi mai daɗi a jiki,

    Sai kuma labulayen window da suka kasance farare sol Sanyayyan iska na kaɗawa daga bangon kudu dake kallon yamma TV ne maƙale abango daga tsakiya kuwa wani irin dakekken turkey carpet mai yawan gashi fari sai ratsin maroon kaɗan. sosai Office ɗin yayi kyau.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin nutsuwa da kuma zafin da zuciyarsa keyi masa ya zauna akan kujeran dake gabar yana fuskantar yamma yayin da M Jameel ya zauna akan kujeran dake yamma yana fuskantar gabar kana da sunan ko wannensu ajiki kujerarsa.

     

    Ita kuwa khausar cikin tsananin tsoro ta ƙarasa shiga office ɗin tare da tsugunnawa agaban table ɗin da Moddibo ke zaune.

    Ta riƙe kunnenta Muryanta Araunane wanda ke nuni da tsantsar tsoro da tashin hankali tace.

    “Malam kayi haƙuri bansan kana tahowa ba”.

    Shi kuwa Moddibo ko kallonta baiyi ba saboda yanda zuciyarsa ke tsananin ta farfasa ya tabbata idan yace zai daketa to zai iya karyata ko kuma ya sumar da ita hakan yasa ya janyo kujeran dake kusa dashi ya ɗaura ƙafafunsa akai kana ya lumshe idanunsa tare dasa hannu ya janyo Hiramin dake kansa ya rufe saman Idanunsa.

     

    Cikin tsantsar nutsuwa da kuma sanyayyan sautin muryarsa mai zaƙi ya fara rara Ƙira’a acikin suratul Rahman yasan hakan shine kaɗai zai sanyaya masa ransa da zuciyarsa yasan muddin yace zai daketa ayanzu zai iya sumar da ita ko kuma karyata.

    Saboda abubuwan da yarinyar ke masa yayi yawa.

    Sabida tsabar raini da rashin kunya fa har gidansu ta bisa tayi masa rashin kunya sannan ta jima sa ciwo ayatsun ƙafansa wanda ya ɗauki tsawon kwanaki yana fama da ciwo.

    Kana  yaje ƙauyen su nan ma bata barshi ba saida ta bisa tayi masa rashin kunya ta nemi jefa shi acikin ruwa da wannan masifeffen sanyin garin nasu,

    kana amakaranta ma bata barsa ba shin tsaranta ta mayar dashi kome?.

     

    Ita kuwa khausar cikin Sanyayyar Muryanta me cike da tsoro tace.

    “Ayyah malam na tuba kayi haƙuri wallahi bansani bane”.

    Ƙin tanka mata Moddibo yayi ya cigaba da rera karatunsa cikin zazzaƙan muryansa.

    Shi kuwa M Jameel Gyaran murya yayi hakan yasa Khausar tayi saurin Kallonsa da manyan Idanunta da suka kaɗa sukayi jawur.

    Da ido yanuna mata Moddibo alamar ta cigaba da basa haƙuri.

    Kai ta gyaɗa sannan ta cigaba da cewa.

    “Ayyah Malam na roƙeka kayi haƙuri bazan sake ba”.

     

    Acan sama ajinsu Khausar kuwa wani irin tsarin gini ne mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali wasu irin windon Glass ne tsala-tsala masu tsayi da kyan tsari sannan ga flowes masu fitar da sanyayyan ƙamshi kana ga Room hita  guda biyu gaba da baya daga farkon shiga class ɗin kuwa wani irin Black Board ne mai tsari irin wanda ake amfani dasu a manyan makarantu, kana ga wasu irin kujeru na zaman ɗalibai masu taushi da kyau, agaban ko wani kujeran ɗalibi akwai sunan sa ajiki, hakan yasa duk ɗalibar data shiga baza tasha wahala neman wajen zamanta ba wanda kuma manna sunan ake bisa alamu in an tashi kawai ɓarewa za’ayi a saka sunayen sabbin waɗanda zasu shigo ajin, kujeran Khausar shine na farko acikin jerin kujerun dake gaba da sunanta manne kamar haka _Khausar Usman Abubukar Lelewal._

    Samira Sani ce ta ɗan juya Idanunta kan kujerar dake gefenta.

    Wanda sunan Khausar dake manne kujerar afarkon.

     

    Wani irin ya mutsa fuska tayi tamkar wacce taga wani abin ƙi cikin taɓe baki da tsanar mamallakiyar sunan tace.

    “Ikon Allah wannan shine suna mai buƙatar hadda sunaye huɗu duk masu tsawo!”.

    Ta Ida maganar tare da bankawa kujeran harara tamkar Khausar ɗin na kai, kana ta zauna daga baya inda sunan ta ke kai.

     

    Asma’u dake gefe azaune tace.

    “Ha’a sunane de ai ba wani abu ba kuma duk sunayene masu inganci da Kekkyawar nasaba naga dai sunanta sunane na ɗiya ga Annabi  Muhammad (S.A.W) sannan sunan mahaifinta sune na sahabin Manzon Allah (S.A.W) haka zalika sunan kakanta sune na sahabin Manzon Allah (S.A.W).

    Lelewal kuwa naga suna ne da kowa ke fatansa”.

     

    Abeeda Sule ne ta watsa wa Asma’u harara tare da faɗin.

    “Ke kuma wayasa bakin ki?”.

    Taɓe baki Asma’u tayi kana tace.

    “Ai gaskiyane daga kallon sunan baiwar Allah zata fara ƙanan magana”.

    Ɗaya daga cikinsu manyan matan ajin nasu ne wacce bata fiye magana Hajia Khadija tace.

    “Da wannan hatsaniyar da kukeyi tunda Moddibo ya fita tun ɗazu akan zaije ya dawo bai dawo ba aigwara kuje ku duba ko lafiya mai ya tsaida shi aji ba kowa kuma shine muke da First period?”.

     

    Cikin zumuɗi Samira Sani tace.

    “Gaskiya ne kam bari naje na kirasa”.

    ta ida maganar tare da ficewa ta sauƙa ƙasa.

    Cikin yauƙi ta nufi Office

     

    Tana isa idanunta suka sauƙa akan Khausar dake riƙe da kunnenta, ga kuma Idanunta da suka sauya,

    yayin da shi kuwa Moddibo idanunsa ke lumshe yana rera karatun Alkur’ani cikin Sanyayyar sautin muryansa daya haɗu da ɗumin room hita ga ƙamshin daddaɗan tularensa.

    Numfashi mai nauyi ta fesar  tare da tsirawa yalwataccen sajensa daya ƙawata kyawun fuskarsa idanu sai kuma ta maida kallonta kan zara-zaran yatsun hannunsa dake kan table yana ɗan bubbugasu ahankali cike da shauƙi tace.

    “Wowww”.Faɗar hakan da tayi shi ya janyo hankalin M Jameel yayi saurin juyawa ganinta tsaye acikin Office din yasa shi faɗin.

    “Lafiya?”.

     

    Sai asannan ta dawo cikin nutsuwarta still Idanunta na kan Moddibo tace.

    “Malam Barka da safiya”.

     

    “Barka dai”.

     

    Still idanunta na akan Moddibo tace.

    “Malam dama munzo kiran Malam Moddibo ne, shine muke dashi tun ɗazu ya sauƙa, akan cewa zai zo ya ɗauki wani abu sannan kuma bai koma ba”.

     

    Da ido M Jameel ya nuna mata Moddibo da har zuwa lokacin idanunsa ke lumshe yana karatu sai dai ya rage sautin muryansa ya koma fita asaman laɓɓansa.

     

    Shi kuwa Moddibo jin Muryanta yasa ya janye Hiramin dake fuskarsa kana ya buɗe idanunsa da har zuwa yanzu akwai alamun ɓacin rai acikinsu, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kansa gefe.

    Ita kuwa Samira gefe ta koma ta tsaya.

    Khausar kuwa lumshe Idanunta da suka kaɗa sukayi jawur tayi sai kuma ta buɗe su still Hannunta nakan kunnenta tace.

    “Ayyah Malam kayi haƙuri”.

    Shi kuwa Moddibo juyawa yayi tare da kallon M Jameel yace.

    “J ka da keta”.

    Da sauri M Jameel ya juya tare da nuna kansa da babban yatsa kana yace.

    “Ni!?”.

     

    Cike da tsuke fuska Moddibo ya gyaɗa masa kai kana yace.

    “Eh ka daketa!”.

    Zare Ido M Jameel yayi tare da cewa

    “Meyesa?”.

    A kufule Moddibo yace.

    “J kadaketa nace!”.

    Kallon mamaki M Jameel yake masa tare da cewa.

    “Akan me zan daketa?”.

    Cike da ɓacin rai Moddibo yace.

    “Idan fa ka bari nace ni zan daketa zan sumar da ita fa!, zan karyata fa!!”.

    Cikin tsananin fusata ya ida maganar.

     

    Ita kuwa Khausar tuni jikinta ya hau rawa Allah ya sani bata son duka, sannan mari ɗaya daya mata ya mugun gigita mata ƙwaƙwalwa wanda har zuwa yanzu take jin raɗaɗin sa asaman fuskarta.

     

    Fuskarsa babu walwala yace.

    “Idan har nace zan daketa zan sumar da ita”.

    Ita kuwa Khausar jin azaban mari ɗaya daya mata, aranta tace Ashe Allah ya rufa min asiri da yasa duk lokacin da nayiwa Moddibo laifi baya duka na yake sa Malam Adam display master ke dukana na tabbata dashi yake dukana kullum da tuni ya kasheni!.

     

    Cikin hanzari ta juya tare da kallon M Jameel ta miƙa masa hannu Muryanta na rawa tace.

    “Malam ka dakeni!”.

    Girgiza kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.

    “Ni dai kam bazan iya ba bazan iya dukanta ba Moddibo, ka dubi fuskarta fa mari ɗaya da ka mata kalli fuskarta fa ai ya wadatar wani hukunci ya rage bayan wannan?”.

    Ya kare mgnar a hankali

    Moddibo kuwa cikin fushi yace.

    “Kada keta in kuma baza ka daketa ba zan daketa da kaina fa”.

    Cikin sauri M Jameel ya fara girgiza kai  yayi cikin wata Sanyayyar murya me cike da zallar jin ƙai tare da tarin tausayi gami da rauni yace.

    “La! La!! La!!! A.J  bazan iya ba! Wlh Bazan iyaba ba wannan ba hurumina bane hurumin taɓa ta awajenka yake bani da karsashi ko ƙwarin gwiwar da zan iya taɓa ta!”.

    Ya ida maganar cikin wani irin salo na daban, kana dai-dai lokacin  Amina tazo Office ɗin domin kiran M Jameel ya shiga ajinsu wani irin sarawa kanta yayi jin yanda yake cewa bazai iya ba.

    Da sauri ta dafe ƙofar office ɗin jin jiri na ɗibarta kadde ace dokon soyayyarsa za tayi abanza, kadde Khausar yake so yanda ya ƙarashe maganar na nuni tamkar itace rayuwar sa.

     

    Da sauri Moddibo ya juya ya kalli M Jameel jin yanda yayi magana da kuma yanda ya lanƙwasa harshensa abun ya bashi mamaki.

    Azuciye Moddibo yace.

    “In daketa kenan?”.

     

    Langwaɓar da kai M Jameel yayi cikin sanyin murya yace.

    “Kayi haƙuri ina mai bada haƙuri amada dinta ka nemi wani punishment ɗin ka bata amadadin wannan, amma nikam bazan iya dukan taba sannan kaima banaso ka daketa!”.

    Baki ɗayan su kallon Mamaki suka bi M Jameel dashi ganin yanda yake lanƙwasar da murya tare da nemawa Khausar ya fiya, ita kuwa Amina wasu hawaye ne masu zafin gaske ne na tsananin kishi da baƙin ciki, suka zubo mata  saurin ta sanya hannu ta share.

    Kwantar da Murya M Jameel ya kuma sakeyi ya cigaba da cewa.

    “Kallifa A.J mari ɗayan nan da kamata kalli fuskarta fa ka daketa awaje mafi daraja”.

     

    Moddibo kuwa  lumshe idanunsa yayi kana ya buɗesu akan M Jameel tare da cewa.

    “J kadaketa ni idan nace zan daketa bazai mata daɗi bafa”.

    Sake Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana yace.

    “Kayi haƙuri Moddibo ni bazan iya dukanta ba!”.

     

    Ita kuwa Samari Sani na tsaye agefe ta harɗe hannayenta aƙirji yayin da ta zubawa Moddibo ƙananun Idanunta ko ƙyaftawa ba tayi.

    Ita kuwa Amina Idanun ta nakan M Jameel da idanunsa ke kan Khausar zuciyarta nayi mata zafi.

     

    Khausar kuwa kallon M Jameel ta sakeyi akaro na barkatai tace.

    “Malam Jameel ni dai ka dakeni”.

    Kai ya girgiza mata tare da faɗin.

    “Bazan iya dukan ki ba Khausar!”.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin tsananin ɓacin rai ya juya ya kalleta a kufule yace.

    “Toh inda keta da kaina!?”.

    Girgiza kai M Jameel yayi sai kuma yace.

    “A’a asassauta mana dan Allah”.

    Ƙwafa Moddibo yayi da faɗin.

    “Shikenan kije ki kaɗe ɗan kwali sau ashirin”.

     

    Cike da tsoro ta zaro ido domin kaɗe ɗan kwallon da yace  yana nufin ta cire ɗan kwalinta tasa abokitin ruwa ta matse kana ta kaɗe har sai ya bushe,

    sannan ta sake sakawa cikin ruwa ta matse kana tayi ta kadewa har sai ya bushe.

    Tofa jin haka ne yasa a tsorace ta zare Ido Jin hukuncin daya yanke mata ba zata manta lokacin daya sata kaɗewa sau goma ba awannan lokacin ma saida tayi sati biyu gaɓɓanta na ciwo ko abu zata ɗauka da ƙyar take iyawa.

     

    Cikin yanayin neman alfarma M Jameel ya sake langwaɓar da kai kana yace.

    “Dan Allah ka sassauta mata karage mata”.

    Jin Muryan M Jameel yasa ita ma ta kalli Moddibo cikin wata raunatacciyar murya tace.

    “Dan girman Allah Malam kayi haƙuri karage min”.

     

    Shi kuwa Moddibo wani kallo ya watsa mata cikin haɗe girar sama dana ƙasa yace.

    “Kada ki sake haɗa ni da girman Allah da kinsan darajar girman Allah da zaki mutunta Malama ki,

    kije kiyi shabiyar kinci darajar girman Allah.

    idan kika sake cemin dan Allah in rage miki kuwa nida ke bibbiyu!”.

    Gyaɗa kai tayi kana tace.

    “Toh shikenan”.

    Shi kuwa M Jameel kallon Moddibo yayi cikin jujjuya  ido  yace.

    “Ina neman alfarma abarta tashiga aji tayi karatu idan antashi Break sai tayi”.

     

    Shi kuwa Moddibo Ɓata fuska yayi yace.

    “Bana son ganinta a aji Idan naganta a aji zan kakkaryata in wurgar ta window”.

    Ita kuwa Samira Sani cikin lanƙawasa harshe tace.

    “Malam Moddibo mu tafi”.

    Sake tamke fuska yayi tare da juyawa ya watsa mata wani bayyane  harara sai kuma ya nuna mata ƙofa alamar ta ɓace masa da gani.

     

    Sum sum ta  juya da sauri  ta fice.

    Da harara yabi bayanta Aransa yace.

    Shegiyar yarinya mai kama da Mayya,

    sai shegen kallon jaraba tasani gaba zakiyi dan rashin kunya.

     

    Samira Sani kuwa tana shiga ajinsu ta lumshe Idanunta tare da kallon gefen ko wannen kujera dake ɗauke da flowes ta saki murmushi mai cike da jin daɗi,

    tasan wannan aikin Moddibo ne domin kaf cikin Malaman shike son flowers.

    Hajia Ruƙayya ce ta dubi Samira data shigo kana tace.

    “Ni kam ya banga Khausar ta shigo ba har yanzu kuma ɗazu na hangota kafin na haura”.

    Juye Ido Samira tayi tare da faɗin.

    “Tana can tayiwa Moddibo rashin kunya yana cin Ubanta, shegiyar yarinya fitsararriya ‘yar marasa tarbiyya!”.

     

    Asma’u ce ta juya ta kalleta rai a haɗe tace.

    “Haba Samira meyesa zaki zagi iyayenta ai bai kamata ki zagi iyayenta komai yaya iyaye nada daraja”.

    Harara Samira ta wurga was Asma’u kana ta buɗe baki da niyyar magana ta fasa sakamakon shigowar Moddibo.

     

    Ganin shigowar Moddibo yasa ta tsuke bakinta tare da neman waje ta zauna cike.

    Cike da ladabi suka gaishesa cikin harshen larabci tare da faɗin.

    ”صبحل خير ىاعثتذ“

    Ya Amsa da.

    “صبحل نور كىفل قراء“.

    Suka amsa da.

    ”الحمد الله“

    Kasancewar Tafseer zasuyi dake yanzu lokacin Islamiyya ne yasa yace.

    “Kuyi muraja”.

    Cikin bawa ko wanne harafi hukuncinsa suka shiga karanta suratul Muhammad har zuwa karshe.

    Bayan sun gama kawo haddan ya jinjina kai tare da faɗin.

    “Sai gobe Insha Allah zamu fara tafsirin sa”.

     

    Aɓangaren M Jameel kuwa tare suka jera da Amina suka nufi ajinsu yayin da azuciyar Amina yayi baƙiƙƙirin data tuna yanda M Jameel ke karyar da murya akan Khausar har suka isa ajin tunanin da take aranta kenan yanayin yanda tsarin ajinsu Khausar yake haka ko wanne aji yake cike da ƙwarewa M Jameel ya shiga yi musu ƙarin Mi’atu Hadith daga na Arba’in bayan sun karanta masa.

    Ko wanne aji da Malami aciki suna darasi.

     

    Ita kuwa Khausar ita kaɗai ce tsaye aharabar Makarantar cikin gajiyawa ta ɗaga boket ɗin ruwan ta koma rana wai ko zata samu yafi bushewa da wuri, tsoma ɗan kwalin tayi aciki kana ta matse sannan ta fara kaɗewa.

    Nannauyan ajiyar zuciya ta saki tun akaɗewa na uku taji hannunta ya sage aranta tace.

    “Insha Allah Ina komawa gida zan nemi ɗankwali mai shara-shara mara nauyi wanda kodan irin rana ta yau ta faru zaimin sauƙi.

    Cike da gajiya ta miƙe  ta riƙe ƙugunta da hannu ɗaya ta lumshe idanunta sosai ta gaji.

     

    Shi kuwa Moddibo daga can sama acikin ajinsu Khausar yake kallonta tana kaɗe-kaɗen ganin ta tsaye ta riƙe ƙugu gaban ƙirjinta duk ya jiƙe da fuskanta, ganin ta tsayanne yasa ya buɗe glass ɗin window dake saitin ta tare da ziro hannunsa ya ƙyasta yatsunsa da ƙarfi wanda hakab yaja hankalin Khausar da saurin ta ɗaga kanta.

    Ganin abinda yayi yasa da sauri ta cigaba da kaɗewa tana mai rintse Idanunta.

     

    Har Moddibo ya gama teaching ɗinsa ya fita Khausar nakan punishment Koda ya saƙƙo ya ganta Harara ya watsa mata kana a kufule yace.

    “Ba zaki shiga ajiba yau har sai kin gama abinda nasaki”.

    Fuska ta Shagwaɓe  tare da langwaɓar da kai tace.

    “Ayyah Malam dan Allah kayafemin duk ɗan Adam ajizine!”.

    Harara ya watsa mata ya wuce batare daya bata amsa ba,

    bayansa tabi da kallo tana tura ƙaramin bakinta, to har wani malami ya sake shiga yayi darasi Khausar bata gama ba sai sha biyu dai-dai lokacin tashin matan Aure sannan Yara da ‘Yan mata suyi suci abinci su koma ajin boko.

     

    Hajiya Ruƙayya ce da Aunty Khadija ne suka  fito tare da ƙarasawa kusa da Khausar dai-dai lokacin da Khausar ke faɗin.

    “Wayyo hannuna”.

    Ta faɗa tana matsa yatsunta dake raɗaɗi.

     

    Dafata Hajiya Ruƙayya tayi kana tace.

    “Ayyah sannu Khausar kece bakyaji me kika yiwa Moddibo!?”.

    Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da marairaice murya tace.

    “Allah babu abinda na masa kawai ina tahowa ne mukayi karo dashi har System ɗinsa ya faɗi kuma ma naji malam Jameel yace System ɗin beyi komai ba amma sai da ya sani wannan kaɗe-kaɗen sabida in baici zalina ba baya jin daɗi rayuwarsa ta duniya”.

    Ta ida maganar da faɗin.

    “Affan zo”,tare da miƙa masa hannu.

    Murmushi Aunty Khadija tana mai jujjuya kai.

    Ita kuwa Hajia  Rukayya

    Miƙa mata yaron dake ta faman ƙyalƙyala mata Dariya Aunty Ruƙayya tayi Sai kuma tayi saurin janye hannunta tana cewa.

    “Wayyo Aunty Ruƙayya hannu na ya gaji yaukam bazan iya riƙe sa ba”.

    Ta ƙare mgnar tana ƙara matsowa  kusa da Aunty Ruƙayya kan kumatunsa ta sumbata tana faɗin.

    “Affan gaye”.

    Shi kuwa yaron sai dariya yake ƙyalƙyala mata tare da miƙa mata hannu alamar yana so ta ɗauke sa dan sosai yaron ya saba da ita saboda Aunty Ruƙayya na zumunci da Mommy Khausar sannan Khausar na shiga lokaci zuwa lokaci.

     

    Samira Sani da Abeeda Sule ne suka ƙaraso wajen Kallon Abeeda Sule Samira tayi da faɗin.

    “Ai Moddibo shike maganin tantirai marasa mutunci ’ya’yan Fitsararru awannan makarantar yana min dai-dai!”.

     

    Sake hannun Affan Khausar tayi ta juya ta kalli Samira da kyau tace.

    “Waye ‘Yar marasa mutuncin?

    Akwai ‘Yar marasa mutunci daya wucike ne ‘Yar magulmata Munafuka kawai! Inbanda munafurci da gulma da biye-biyen bokaye Me kuka iya!?”.

    Afusace tace.

    “Ke Khausar zanci Ubanki fa!”.

    Wara ido Khausar tayi kana tace.

    “Ubana kuma, uhmm saide Kici naki uban domin ni kam nawa Ubana tuni Ubangiji ya daɗe da yimasa sutura sai dai kije kici naki ‘Yar matsiyata?”.

    Ta ida mgnar cikin tsiwa,.

     

    Abeeda Sule ne tace.

    “Ke akwai ma ƴar matsiyata irinki, kina tsammanin bamu san cewa munsan ke Agwola bace acikin gidan sarki da kike nunawa kamar gidan ku ne?”.

     

    Dariya Khausar tayi kana tace.

    “Dan Allah rufe mana baki ‘Yar Alhaji sule baka layya kibari tukunna in Babanki ya fara layya saiki faɗa wa mutane Magana?”.

     

    Zare ido Abeeda tayi tare da hayayya ƙowa tace.

    “ ‘Yar iska ni zaki cewa Ubana baya layya”.

    Taɓe baki Khausar tayi tare da faɗin.

    “Ke rufe min baki ai bani na faɗa ba Inkiyarsa ce hakan, ko ba sunan sa bane? Alhaji Sule baka layya!! ko kuma ni nasa masa ko kuma dan tsoronki sai inki kiransa da sunan da aka sa mishi”.

     

    Hajiya Ruƙayya ce tace.

    “Khausar rabu dasu”.

    Gyaɗa kai tayi.

    Ita kuwa Samira cikin takaici tace.

    “ ‘Yar banza kawai agola”.

    Dariyar rainin hankalin Khausar tayi sannan tace.

    “Eh koma menene inma ni Agolace inada daraja sannan ina da tushe dama ni ban ɓoyewa cewa Agola bace Ni saboda idan kinga sunan su Amina da sunana kin san ba yar gidan bane,

    Ni sunana Khausar Usman Abubukar Lelewal sukuwa kinga ba haka sunan su yake ba daga nan ma mutum yasan Ni Agola ce ko dama anɓoye miki ne?”.

     

    Hannunta Hajiya Ruƙayya taja suka bar wajen zuwa gefe tace.

    “Khausar kifita har ƙansu  kiyi abinda ke gabanki kinga duk yau baki samu karatu ba”.

    Kai Khausar ta gyaɗa mata sannan tayi mata Sallama ta tafi.

    Asma’u ce ta ƙaraso wajen Idanunta akan Samira da Abeeda dake zagin Khausar cikin yanayin sanyin muryanta tace.

    “Khausar kifita sabgar wa’annan yaran dan Allah keda su ba ɗaya bane kada ki ringa biye musu muta nen da ƙwaƙwalensu basa ja, kinga fa yanzu da ya kamata suna SS 3 nefa daƙiƙancinsa kesa kullum basa gaba sunan a jaɓe har muka isosu”.

    Yamutse fuska Khausar tayi kana tana matsa yatsun hannunta tace.

    “Kinsan Allah Asma’u Indai basu fita sabgata ba zan basu mamaki zan nuna musu Khausar Usman Abubakar Lelewal ba kanwar lasa bace”.

     

    Hannunta Asma’u ta riƙe tace.

    “Ni dai dan Allah ki fita sangarsu ai ko kare bai haushi shi kaɗai tukunna wai me kika yiwa Moddibo ya saki Punishment?”.

     

    Rau-rau da ido Khausar tayi sai kuma ta ya mutse fuska tare da jan tsaki kana tace.

    “Mutum yana nan kamar wani sabon boss sam fuskarsa babu fara’a yana nan sai baƙin mugunta.

    Kuma wallahi Wuta bal-bal ban yafe masa ba, ai bani kaɗai nayi kuskuren ba shima yayi yana tafiya kamar makaho, kuma yaseen saƙo na baki ki faɗa masa ehe”.

    Ta ida mgnar cike da tsiwa da murguɗa baki

    Asma’u kuwa  dariyar  dake cinta ta danne kana tace.

    “Aikuwa gashi nan abayanki yana ma jinki ba sai na faɗa masa ba”.

    Arazane Khausar ta saki ihu  tare da rintse Idanunta cikin tsananin tsoro da rawan jiki ta juya tana mai faɗin.

    “Dan Allah! Dan Allah!! Dan Allah!!! kayi haƙuri Allah bada kai nake ba kuskuren harshene ni da kainama nakeyi”,

    Ta ida maganar tana buɗe Idanunta jin be tanka taba ga mamakinta bata gansa ba.

    Kallon Asma’u tayi wacce zuwa lokacin ta saki dariyar ta tace.

    “Fattanah sarkin tsiwa dama gwada ki nayi inga da gaske saƙon kika bani”.

     

    Harara Khausar ta zabga wa Asma’u amma batace Komai ba.

    Murmushi Asma’u tayi tare da jan hannunta zuwa resting chair dake cikin harabar makarantar suka zauna Asma’u ta fito da kula da ɗauke da pride rice da yaji kayan hadi da namar kaza suka ci.

    Bayan sun gama cin wannan Khausar ta buɗe bata kukan.

    Peper checking ne guzurin zabbin data dawo dasu.

    Sunaci suna ɗan hirarsu dai har suka gama,  suka mike tare da zagaya classes din makarantar suna kallon yanda aka tsara makarantar kamar ba shiba.

    12:10  suka koma aji.

    Bayan komawar su Malam Isa dake ɗaukar su Economist ya shiga ya koyar musu sosai Khausar da Asma’u ke fahimtar karatun 1:15 dai-dai suka fita sallah.

     

    Bayan sun fita Al’wala sukaje wajen da aka tanada dan alwala sukayi gefen maza da ban na mata da ban Amma masallacin guda daya ne saidai anraba daga tsakiya anyi katanga mata zasu shiga ta gefen dama maza tagefen hagu.

    Bayan sun idar da Sallah ƙarfe 1:30 suka koma aji wasu Malaman suka sake shiga.

    Sosai Malaman suka dage wajen koyar dasu domin anƙara musu Salarie sannan ankawo sabbin Malamai hakan yasa babu period din dake wucewa ba tare da anshiga ba  5:00 dai-dai suka tashi motar su Khausar tazo ta ɗauke su.

     

    Washe gari.

    Ma haka suka gudanar da karatunsu kamar na jiya.

    Acikin satin karatu suke gadan gadan babu kama ƙafar yaro saboda suna son dai-dai-ta komai na lokacin daya wuce ahutu koda wasa Khausar bata sake yin ganganci wani abu ya haɗa ta da Moddibo ba bare tayi masa laifi da zaran ya shiga ajinsu zata tattara duk kan nutsuwarta akansa tana sauraron abinda yake koyar musu kuma sosai take fahimta yayin da ita kuma Samira Sani zata tsaya aikin Kallonsa aduk sanda ya shiga musu shikuwa Moddibo duk yana lura da yanayin ko wannensu.

     

    Yau Alhamis ya kasance babu makaranta suna hutu.

    Khausar ce zaune a falon Mommy ta tana duba Mi’atu Hadith,Mommy dake Bedroom ta ƙwala mata kira Amsawa tayi tare da ajiye Hadith ta fita.

    Bakinta ɗauke da Sallama tashiga Bedroom din Kallonta Mommy tayi tace.

    “Khausar ɗibi wannan kayan ki kaiwa Hajiya Bunayya kala ɗaya nasiya mana”.

    Kallon mamaki Khausar ta yiwa Mommy anma wannan basabon abu bane ko yaushe Mommy na zaune zuciya ɗaya da ita tana kyautata mata, amma ita Hajiya Bunayya ba da zuciya ɗaya take zaune dasu ba.

    Gyaran Murya Mommy tayi tace.

    “Khausar tunanin me kike?”

    Murmushi Khausar tayi tare da ɗiban kayan tace.

    “Toh”,Mommy sannan ta fice.

     

    Bakinta ɗauke da Sallama ta shiga falon Hajiya Bunayya kana ta nemi waje ta zauna aɗaya daga cikin kujerun dake falon tace.

    “Ummah gashi Mommy na ta siya musu iri daya”.

    Washe baki Hajiya Bunayya tayi tare da kallon turamen Zannuwa da tsadaddun less ɗin tace.

    “Aaaa lalle kam Khausar Nagode Allah yayiwa ƙanwata al’barka muje inyi mata godiya”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa dai-dai lokacin Hajiya Lami mahaifiyar Samira Sani tayi sallama suka shigo atare.

    Kallon Khausar Hajiya tayi tace.

    “Khausar jeki nayi baƙi kice mata Nagode zan shigo anjima”.

     

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da ficewa yayin da Samira ta bita da mugun kallo.

    Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi kana ta mika mata hannu suka tafa Dariyar ƙeta Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Kalli Sokuwarki wai kaya ta saya mana iri ɗaya”.

     

    Dariya Hajiya Lami ta fashe dashi tare da cewa

    “Aaaa Ikon Allah sokuwa ta ƙarshen zamani kuwa wato hadda siya muku anko”.

    Tsaki Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Bar ‘yar banza mai kama da ‘ya‘yan mayu tazo ta liƙewa mijina”.

     

    Hajiya Lami tace.

    “Aikam wa’annan mutanen sai Allah aike kika sake kika basu dama, kika bar mijinki ya ƙara aure ni yanzu Baban Samira ya isa yace zai ƙara aure ne, sannan bayan kin bari yayi auren ma kika barta tahaifi santalelen yaro me jikin girma bayan shi hadda ‘yan biyu da kawunansu kamar ‘Ya‘yan ruwa ga shegen gashi kamar ‘ya‘yan Aljanu”.

     

    Ƙwafa Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Ai wallahi nayi sake amma daga ‘yan tagwayen babu ita ba sake haihuwa ina lura da ita kwannan kamar cikine da ita to bazan bari ta haife sa ba zanje wajen boka Kar’uzu azubar dama duk cikin ta uku kafin ’yan biyu ni nake sawa azubar  shegiya ai bazan barta ba kenan yanzu ma inada  niyya zanje wajenki jibi muje wajen Malami”.

     

    Gyara zama Hajiya Lami tayi tare  da faɗin.

    “Aini ma abinda ya kawoni kenan Hajiya Bunayya in sanar miki”.

    Kallonta Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Toh Meye faru?”.

    Ajiyar zuciya Hajiya Lami ta sauƙe tace.

    “Akwai wani Malami ne amakarantar su Samira take sonshi”.

    Cikin don jin ƙarshen zancen Hajiya Bunayya tace.

    “Toh wani Malami?”.

     

    “Wai shi malam Moddibo tana masifar sonshi shi kuma yana nan kamar Waliyi ko ta kanta bayayi”.

     

    “Ikon Allah”.

    Cewar Hajia Bunayya

     

    “Toh fa shine nake son zamu kai sunansa wajen Malami ya jawo mana hankalinsa da tunaninsa”.

    Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Eh hakan ma yayi shine dai-dai, gwara ajashi ya dawo yana binta, nima dama abinda zai kaini kenan harda batun Amina itama wani Malamin su take so”.

     

    Cikin mamaki Hajia Kamu tace.

    “Ita kuma wani Malamin take so?”.

    Da sauri Hajiya Bunayya tace.

    “Eh wani Malami take so wai shi M Jameel shi kuma baki ɗaya hankalinsa nakan wannan ‘yar matsiyatan!”.

     

    Cikin zato ido Hajiya Lami tace.

    “Wa kenan?”.

     

    “Khausar mana”.

     

    Hajiya Lami kam baki ta saki  tare da riƙe haɓa kana ta saki salati tace.

    “Ikon Allah Uwarta ta hanaki rawan gaban hantsi, sannan itama Khausar tun yanzu zata hana ‘yarki rawan gaban hantsi, ta hana ta samun abinda take so, to ko lallai kinada aiki ja a gabanki

    Yakamata muyi aggawan zuwa mu ɗauki mataki dan bata isa ba amma shi Jameel din ɗan gidan waye!?”.

     

    Murmushi Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Ɗan gidan Alh Bashir Mafindi.

    Ko da yake yanzu anfi saninshi da  Maidala ne”.

    Kai Hajiya Lami ta jinjina tace.

    “Kai-kai lallai kice babban kamu ne ina zamu yarda muyi wasa dashi waye bai san Alhaji Bashir Maidala ba”

    .

    “Ai dai kam  ɗan masu kuɗi ina zamu bari muyi wasa da wannan damar tamu.

    Ai wlh koda zan tafi tsirara bazan taɓa bari ya auri Khausar ba, sannan Insha Allah zanyi kokarin ganin anja mana hankalinsa yaji ya tsaneta ya riƙa cin Ubanta kamar yanda Moddibo keyi mata amakaranta shine abinda yafi mana a’ala da kwanciyar hankali”.

     

    Acan waje kuwa Khausar ce tsaye aƙarshen Barandar Hajiya Bunayya cikin tarin al’ajabi da mamaki ta jinjina kanta bayan ta gama sauraron abinda suka faɗa…..!

     

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki Ka mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nane🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 26

    Sakayyah 26

     

    SAKAYAH

     

    26

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

     

    Isrnejg. Acan ɓangaren gidan Lamiɗo kuwa Ramadan ya fito daga Bedroom da gudu kai tsaye Bedroom din Mommy ya nufa afalo suka ci karo da Hajiya Bunayya wani irin kallo tabisa dashi dai-dai lokacin da Khausar ta fito sanye cikin riga da skirt na less ɗinkin ya zauna ɗas ajikinta kana ta sanya Blue Black hijabi mai Facemaks jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin turaren Oud Ma’aruf fuskarta ɗauke da simple Make-up.

    Cak ta tsaya tare da kallon Hajiya Bunayya data tsirawa Ramadan idanu ganin tsayuwar Khausar yasa Hajiya Bunayya sakin murmushi tare da cewa.

    “Ikon Allah Ramadan ƙafa tayi sauki sosai”.

    Sai kuma ta juya tana cewa.

    “Ki cewa Aysha ankawo kayan tazo ta gani ta zaɓa mana”.

    Girgiza kai Khausar tayi tare da kallon Ramadan dake cewa.

    “Addah Khausi ƙafana tayi sauƙi”.

    Murmushi tayi tare da shafa kansa kana tace.

    “Alhamdulillah Ramadan amma ka daina wannan gudun har yanzu ƙafanka baiyi ƙwari ba”.

    Kai ya gyaɗa mata kana yabi bayanta zuwa Bedroom ɗin Mommy bakinsu ɗauke da sallama.

     

    Ƙara sawa Ramadan yayi tare da faɗawa jikin Mommy kana yace.

    “Mommy ƙafana yayi sauƙi badan Addah Khausi tace kar inyi gudu ba da nayi kin gani”.

    Murmushi Mommy tayi tare da shafa kansa kana tace.

    “Masha Allah mun godewa Allah, ka riƙa bi ahankali insha Allah zaiyi sauki”.

    Khausar na murmushi tace.

    “Mommy zanje gidan su Asma’u”.

    Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

    “Toh Allah ya kiyaye ki gaishe su amma kada ki daɗe Allah ya tsare”.

    Kai ta gyaɗa kana ta fice.

     

    Tare da Sallama ta ɗan tura ƙofar Falon.

    Tana shiga Idanunta ya sauka akan M Jameel dake zaune kan 2 sitter murmushi ta sakar masa kana tace.

    “Laa Yah Jameel”.

    Murmushin ya maidamata tare da faɗin.

    “A’a Lelewal kece yau agidanmu?”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Eh mana Yah Jameel na kawowa Ummi ziyara ne kuma nayi kewar Asmeey”.

    Wara ido yayi tare da cewa.

    “Iyeee Lelewal wato wariya zaki nuna min ni bakiya kewata ba? Rabona dake tun randa kuka karkare makaranta fa”.

    Rufe fuska tayi tare da cewa.

    “Kai Yah Jameel nayi mana, duk makarantar ma nayi missing ɗinta da kowa nata”.

    Murmushi yayi kana cikin yanayin fara’arsa yace.

    “Yanzu naji bayani amman harda Modibbo kinyi kewarsa?”.

    Da sauri ta tura baki tare da cewa.

    “Kewar masu sona nayi banda maƙiyana”.

    Dariya mai sauti yayi tare da cewa.

    “Maƙiyi kuma, kai a’a kam Lelewal”.

    Ita dai Khausar juyawa tayi ta kalli Ummi

    kana tace.

    “Ummi ina yini?”.

    Cike da kulawa Ummi tace.

    “Lafiya lau ya Ramadan da ƙafa?”.

    Gyara zama Khausar tayi kana tace.

    “Yaji sauƙi Ummi yanzu yana takawa ko ina”.

    Atare suka ce Masha Allah Ubangiji Allah ya ƙara sauƙi”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Ameen”.

    Kana suka ci-gaba da hira wanda duk mafi yawan hiran nasiyya M Jameel yake musu kan sukula da rayuwar duniya kana suka sance masu riƙe al’ƙawari tare da kare mutuncin su.

    Ganin rana ya fara yasa Asma’u ta kalli Khausar tare da cewa.

    “Khausy mushiga kichen muyi girki”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da miƙewa ta cire hijabinta tabi bayan Asma’u abakin ƙofar ta tsaya tare da juyawa falon kana cike da kulawa tace.

    “Yah Jameel mai za’a dafa maka?”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Duk abinda kika dafa min Khausar ina so zanci”.

     

    Jinjina kai tayi tare da sakar masa da murmushi kana tace.

    “Toh shikenan Yah Jameel Insha Allah zanyi maka abinda zaka so da izinin Ubangiji”.

    Khausar na shiga kichen suka fara aikin cikin nutsuwa da ƙwarewa Dambun shinkafa da yaji Vegetables suka Atake kichen ɗin ya gauraye da ƙamshi Warmers me kyau ta ɗauka ta zuba masa kana ta ɗauki Bowl ta haɗa masa Fruit Salat mai sanyi sannan ta ɗaura Ababban faranti ta fito.

     

    Kallon M Jameel dake hira da Ummi tayi kana tace.

    “Yah Jameel gashi na kawo maka”.

    Wara ido yayi kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Wai Lelewal duka Ni kaɗai?”.

    Kai ta gyaɗa masa kana tace.

    “Eh aina Malamina ne yanzu ma zan gasa maka nama gashin tukunya”.

    Jinjina kai yayi tare da cewa.

    “Lallai Khausisi naji daɗina na dafa tudu biyu ga Malami sannan kuma yaya saura cikon tudun dafawa na uku”.

    Murmushi tayi tare da zama gefensa kana tace.

    “in sha Allah in akwai na huɗuma duk zaka taka Yaya Jameel”.

    Yana sa Fruit Salat abakinsa ya lumshe Idanunsa kana ya kalli Khausar tare da cewa.

    “Uhm Yummmy na daɗe bansha Fruit salat mai daɗi irin wannan ba Lelewal da alama dai na musamman ne”.

    Asma’u data fito daga kichen ta wara ido kana tace.

    “Kai Yah Jameel har nawa?”.

    Kai ya jinjina mata tare da sanya dariya kana yace.

    “Iyee sosai ma Asmeey nifa yau komai jinsa nake na daban, girkinma tun tuni yake cika min hanci da ƙamshi”.

    Kallon yanda yake dariya Khausar tayi wanda har ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana idanunsa alumshe haskensa ya sake bayyana kana sajensa sunyi luf-luf suna sheƙi.

     

    Ajiyar zuciya ta sauƙe still Fuskarta ɗauke da murmushi tace.

    “Yah Jameel kaima yau na da banne kyawunka ya sake nunkuwa tamkar Balarabe”.

    Bashir da Asma’u kuwa  haɗa baki sukayi wajen cewa.

    “Wallahi kuwa Muma duk akwanakin nan haka muke kallonsa”.

    Wara ido yayi still Yana Shan Fruit Salat ɗin yace.

    “Uhm ko dai dan na kusa Aure ne yasa kuke kallon kyawuna”.

    Saurin Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.

    “Sai kace gobene auren.

    Murmushi yayi tare da faɗin.

    “Uyumm Ummina”.

     

    Sai kuma ya maida Kallonsa kan Khausar tare da cewa.

    “Lelewal zaman gida ya kusa ƙarewa ko?”.

    Kai ta jinjina tare da cewa.

    “Eh Yah Jameel Insha Allah result ɗin mu na fitowa za’a samomin Admission”.

    Jinjina kai yayi tare da cewa.

    “Masha Allah, haka muke fata, ku dai kiyaye ku tsare mutuncinku a duk inda kuka riski kanku”.

     

    “Insha Allah Yah Jameel na maka alƙawari zan kasance fiye da hakan ma”.

     

    Kallon Asma’u Ummi tayi tare da cewa.

    “Kawo mana abincin muci”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa tare da miƙewa ta zuba musu ababban faranti Khausar kuwa drinks ta kwaso musu.

    Kana suka zauna kallon Ummi M Jameel yayi tare da langwaɓar da kai kana yace.

    “Ummi ya aka cire ni adangi gaskiya nima ajuye muci tare”.

    Murmushi Khausar tayi tare da cewa.

    “Toh Yah Jameel bari na zuba mana”.

    Ta faɗa tare da juye nasa akan faranti kana suka zauna tare da sanya farantin Atsakiyarsu Ummi da Khausar na facin juna Asma’u da M Jameel na facing juna haka suka gama cin abincin cike da nishaɗi.

     

    Suna gamawa ana kiran sallar Azahar M Jameel ya Miƙe tare da shiga toilet ya ɗaura alawala kana ya nufi masallaci Asma’u da Khausar kuwa wajen suka gyara tare da kwashe kwanukan suka kai kichen kana suka wuce Bedroom ɗin Asma’u suka ɗaura alwala tare da gabatar da sallah bayan sun idar suka fito zuwa falo.

     

    Bayan an isar da salla.

    M Jameel yana shigowa ya kalli Ummi dake zaune kan 2sitter kana yace.

    “Toh Ummi zan tafi ina jin jikina aɗaɗɗaure tun jiya da daddare fa rabona da wanka ji nake kamar nayi wata banyi wanka ba”.

    Cikin sauri Khausar ta miƙe tare da cewa.

    “Yawwa Yah Jameel dan Allah ka sauƙeni agida Mommy tace kar in daɗe”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh Lelewal muje mana”.

    Kai ta gyaɗa tare da riƙe hannun Asma’u kana suka fita.

     

    Ummi kuwa haka nan ta tsinci kanta da ɗago kai ta zuba masa Ido batare da tace komai ba.

    Ahankali ya kalli Ummi ganin shi take kallo yace.

    “Ya dai Ummina?”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da girgiza masa kai kana tace.

    “Bakomai ba zaka bari sai anjima ba?”

    Girgiza kai yayi tare da cewa.

    “Um-um Ummi ina so in tafi sauri nake”.

    Cikin sanyin murya tace.

    “Toh saurin me kake?”.

    Langwaɓar da kai yayi kana yace.

    “Toh Ummi banyi wanka bafa ba kuji na fara tsami ba?”.

    Wara ido Asma’u tayi tare da sanya dariya kana tace.

    “Ƙamshi dai kake Yah Jameel”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Gwara dai Inje inyi wanka”.

     

    Dai-dai lokacin wayarsa ta hau ruri yana cirowa yaga Moddibo murmushi yayi tare da kallon Ummi kana yace.

    “Kinga fa Moddibo na kira na yanzu zaice ko Breakfast baiyi ba yana jirana, haka yake dake cin abinci bai damesa ba idan bana nan sai yace yana jirana, yaita takura min da kira idan kuma ina nan yaƙi ci”.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “Toh yanzu tafiya zaka yi?”.

    Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

    “Eh Ummi”.

    Cikin sanyin murya tace.

    “Toh ka kira Baban nawa yazo nan kuci abincin”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Ummi zan tafi Insha Allah da yamma zan zo musha hiran mu”.

    Sai kuma ya matsa kusa da ita tare da ranƙwafawa kanta ya kai bakinsa dai-dai kunnenta kana yace.

    “Ummi sai anjima da daddare zanzo insha Allah musha hiran mu sannan in faɗa miki matar da zan Aura da kuma matar da na zaɓawa A.J na”.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “Toh shikenan Babana Allah ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya Ubangiji Allah yama SAKAYYAH da mafificin Aljanna”.

    Murmushi yayi tare da durƙusawa agabanta cike da jin daɗin Addu’ar ta yace.

    “Ameen Ummina Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

    Ummi kuwa hannu ta sanya acikin sumar kansa tana shafawa kana tace.

    “Allah ya rufa maka asiri duniya da lahira Allah yasa kagama da duniya lafiya Allah yasa Aljanna ce makomarka Allah ya tsareka da dukkan sharrin abinƙi Ubangiji ya raba ka da sharrin mai sharri”.

    Tafin hannunta ya riƙe kana yace.

    “Allah ya amsa addu’o’in ki Ummina, shiyasa nake da yaƙinin cewa duk abinda ya sameni, na tabbata ƙaddarar ce da  Ubangiji ya rubuta minne amma addu’ar ki ba zai taɓa bari wani mummunan abu yasame niba Nagode sai dai in daga Allah ne”.

    Bashir daya shigo kuwa Ido ya zuba musu yana kallon yanda Ummi ke sanya masa albarka tare da adduo’i shi kuma yana Amsawa da Ameen.

    Da sauri ya isa ya durƙusa gefen yayan nashi tare da cewa.

    “Ayi addu’o’in damu”.

    Murmushin Ummi tayi tare da shafa kansu,l.

    Asma’u da Khausar kuwa tuni suka fita suna jira ganin shiru bai fito bane yasa Khausar leƙawa Falon kana tace.

    “Yah Jameel baza mutafi ba. Mommyna fa tace kada in wuce Azahar”.

    Kai ya gyaɗa tare da faɗin.

    “Gani nan zuwa Lelewal”.

    Kai Khausar ta gyaɗa kana suka cigaba da hira da Asma’u.

    M Jameel kuwa fita yayi har ya isa baranda sai kuma yayi baya tare da leƙawa falon kana yace.

    “Ummi yau ba rakiya ne ko dan bamu zo da Babanki bane?”.

    Ummi kuwata

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da Kallonsa kana tace.

    “Na’am Jamilu”.

    Langwaɓar da kai yayi kana yace.

    “Ummi yau dai dan ban zo da Babanki ba ba rakiya”.

    Murmushi tayi tare da faɗin.

    “Toh muje in rakaka Babana”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh Nagode”.

    Sannan suka fita afalon kai tsaye jikin motarsa ta nufa ta buɗe masa.

    Murmushi yayi tare da shiga kana ya maida kallonsa kan Bashir tare da cewa.

    “Bashir yau dai na ƙwace maka fadar ka”.

    Murmushi Bashir yayi tare da kallon M Jameel kana yace.

    “Ba komai Yah Jameel na bar maka lokacin kane ai”.

     

    Ahankali Ummi ta tura Murfin motar tare da rufewa.

    M Jameel kuwa Ido ya zubawa Ummi ta ɗan tsakanin glass din Motar batare daya jaba Itama Ummi Idanu ta zuba masa tare da juya masa hannun alamar ya dai?.

    Sauƙe glass ɗin motar yayi tare da sanya babban yatsan sa acikin bakinsa yana ɗan ciza farcen a hankali.

    Cikin tsare sa da ido tace.

    “Ya dai?”.

    Sauke glass ɗin motar yayi tare da zuba mata Ido.

    Girgiza mata kai yayi still baice komai ba.

    Matsawa jikin Glass din tayi kana tace.

    “A’a wai meye haka?”.

    Ƙasa cewa komai yayi still Idanunsa na kanta.

    Sunkuyawa jikin Glass din Motar tayi kana tace.

    “Ya dai?”.

    Ahankali ya lumshe idanunsa tare da jan dogon numfashi kana ya fesar cikin rawan murya yace.

    “Ban sani ba Ummi”.

    Da mamaki tace.

    “Baka sani ba kuma?”.

    Kai ya gyaɗa mata still ya tsansa na bakinsa.

    Cike da kulawa tace.

    “Toh me kake so?”.

    Juyawa yayi ya kalli faɗin ilahirin gidan nasu kana ya kalli Asma’u da Bashir  sai kuma ya dawo da Kallonsa kan Ummi kana yace.

    “Ummi ku nake so”.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “Kai ko Jameelu ba’a rabaka da zolaya”.

    Ta faɗa tare da kallonsa tsakiyar idanunsa ga mmkinta sai taga still baiyi murmushi ba kamar yanda ya saba ba.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “To ko dai ka manta wayar kane?”.

    Hannu ya sanya tare da shafa aljihun gaban rigarsa still yatsansa na cikin bakinsa yana gyatsawa a hankali kana yace.

    “Um-um Ummi ban manta wayata ba gashi a aljihuna”.

    Cikin yanayin damuwa da jinƙai irin na mahaifa tace.

    “Toh Meye ne?”.

    Kanshi ya ɗaura a kan hannunta dake kan glass ɗin motar, tare da lumshe idanunsa kana ya janyo tafin hannunta ɗaya ya kife akan goshinsa tare da buɗe lumsassun idanunsa da suke sheƙi, shiru yayi kamar mai nazari.

    Sai ya kuma lumshe idanu.

    Khausar dake gefe tayi dariya tare da cewa.

    “Kai Yah Jameel bisa dukkam alamu dai yau kam Shagwaɓa kake ji dashi?”.

    Ahankali ya buɗe idanunsa dake lumshe batare daya juya ba kana cikin raunin murya yace.

    “Uhm Lelewal baza ki gane ba”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Yah Jameel zan gane mana gashi yau Shagwaɓa kake yiwa Ummi”.

    Ummi kuwa sun kuyowa kansa tayi sai taga ya kuma lumshe idanunsa yayi shiru Kamar mai tunani hannunta dake goshinsa ta ɗago tare da cewa.

    “Menene? Shin wai meke damunka? Me kake son faɗa min mana?”.

    Cikin sanyin murya yace.

    “Ummi”.

    Sai kuma yayi shiru.

     

    Ahankali ya buɗe Murfin motar ya fito tare da jan hannunta suka nufi cikin falon kana ya kalli su Asma’u tare da cewa.

    “Ku jirani”.

    Da kallo Khausar, Asma’u da kuma Bashir suka bisu, amma babu wanda yace komai kowa da tunanin da yake Aransa.

    Suna shiga falon ya zaunar da Ummi kan 1sitter kana ya durƙusa agabanta cikin raunin murya yace.

    “Ummi ba abinda kikeso in miki?”.

    Cikin raunin murya tace.

    “Meyesa kake hakane, shin wai idan ina da ɓuƙatar abu, bani da kaina nake kiran ka in faɗa maka ba Jameelu?”.

    Araunane ya kalleta tare da cewa.

    “Ummi ki tuna dai! ba abinda kike so in miki kada damar ta wuceni fa Ummi? Ki tuna dai”.

    Ya ƙare mgnar yana murza tafin hannunsa kan rumfa sawunta

    Saurin Kallonsa tayi kana tace.

    “Kamar ya damar ya wuce ka Jameelu?

    Na faɗa maka bana ɓuƙatar komai”.

    Cikin raunin murya yace.

    “Toh bani wayar ki Ummi”.

    Ahankali ta miƙa masa wayarta dake hannun kujeran karɓa yayi tare da shiga text messages ɗin ta, ya duba Alart gani yayi duka-dudu  kudin dake ciki baifi dubu ɗari biyu da hamsin da biyar ba.

    Kallonta yayi kana yace.

    “Ummi kina da buƙatar kuɗi”.

     

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Ga kuɗi kuma mai zanyi dasu?.

    Me zanyi da kuɗi komai fa kai kakeyi min Jamilu”.

    Girgiza kai yayi tare da zaro wayarsa acikin al’jihunsa Atake yayi charking balance tare da cewa.

    “Nima bani ba kuɗi da yawa acikin account ɗina”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

    “Ta yaya kuɗi zai zauna acikin account ɗin ka Jamilu nasan ka haka Allah yayi ka kana da yawan kyauta zaka bawa wannan ka bawa wancan”.

     

    Girgiza kai yayi tare da cewa.

    “Allah yabamu mu bayar Ummi”.

    Jinjina kai tayi tare da cewa.

    “Ameen”.

    Atake ya Mata transfer million ɗaya zuwa account dinta.

    Kana yace Ummi ga Million ɗaya na miki transfer”.

     

    Cikin sauri ta kallesa kana tace.

    “Me zanyi dasu Jameelu?”.

    Hannunta ya damƙe acikin nasa kana yace.

    “Ummi duk abinda kike so kiyi dashi, tunda kin ƙi ki faɗa min abinda kike buƙata ina ji kamar akwai nauyin da ban gama sauƙewa ba gani nake kamar kinada wata buƙatar”.

    Ya ida maganar muryarsa na rawa sosai sai kuma ya kama gwiwoyinta da hannu kana ya kife kansa akan cinyarta.

     

    Cikin sanyayyar murya mai cike da rauni yace.

    “Ummi”.

    Ummi kuwa cikin sanyin murya tace.

    “Na’am”.

    Still muryarsa na rawa yace.

    “Idan akwai abinda na miki kiya femin”.

    Cikin sauri ta kallesa kana tace.

    “Wai Jameelu Meyesa kake yin haka ne?.

    Wai meyesa?”.

    Girgiza kai yayi tare da faɗin.

    “Ai ɗa baya rasa laifin da yake yiwa Mahaifiyar sa, ko babu abinda na miki a yanzu, ai kin ɗauki nauyin cikina tsawon wata tara da kwanaki tara, kin sha wahalar naƙuda kafin ki haifeni, kinsha jidalin rainona, nayi miki kashi nayi miki fitsari na miki tumɓuɗi da amai, na hanaki bacci  a lokacin da kowa ke bacci

    Ummi kiya femin domin wannan ma shine babban  abin neman yafiya ga iyaye, idan kuna akwai abinda na miki yayin kuruciya da girma da kuma yayin rarrafe wata ƙil har cizonki nayi yayin shayarwa dan Allah da Manzonsa duk ki yafe min, kiyi min aikin gafara”.

    Ya ƙare mgnar cikin wani irin raunataccen muryar mai rawa.

    Kai ta girgiza kana cikin raunin murya tace.

    “Ba kayi min komai ba kuma na yafe maka duniya da lahira na yafe maka komai na raunin cewa ko da haihu da rainonka bayan haihuwa, duk na yafe maka shi tun kafin yau”.

    Wasu irin tagwayen numfarfashi masu nauyi ya rinƙa sauƙe tare da cewa.

    “Alhmadulillah Ummina ngd matuƙa.”

    Ita kuwa Ummu cikin sarƙewan murya taci ga da cewa..

    “Meyesa kake min irin wa’annan abubuwan bana sofa”.

     

    Dariya yayi kana yace.

    “Toh Ummi dan ɗa yanemi yafiyar Uwarsa sai yazama laifi?”.

    Girgiza kai tayi tare da Kallonsa kana tace.

    “Toh ni babu abinda ka min ka tashi mu tafi Allah yayi ma sakayya da mafifiyaciyar Al’jannah mai cike da ƙololuwa  ni’ima tashi muje in rakaka”.

    Ta faɗa tare da miƙewa kana ta riƙe hannunsa kamar yaro haka suka fito kana ta buɗe masa murfin motar tace.

    “Toh kashiga Allah yayi maka al’barka”.

    Kai ya gyaɗa tare da shiga.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “Toh kaje Ubangiji Allah ya maka albarka Allah ya tsareka Allah ya rufa maka asiri Ubangiji ya maka sakayya da mafi kyawun abin sakamako Allah yatsare min kai Allah Ubangiji ya Albarkanci rayuwar ka Allah ya azurtaka da arziki mai albarka da yara na gari”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum Ummina”.

    Ya ida maganar tare da zuba mata Ido.

    Asma’u kuwa ita ma shiru tayi tare da zuba masa Idanu tana kallon yanda yake kallon Ummi.

     

    Khausar kuwa Kallonsa tayi kana tace.

    “Yah Jameel gaskiya zan tafi idan kai ba zaka tafi ba”.

    Kallonta yayi kana yace.

    “Toh mutafi Lelewal baki sani bane duk saurin da kikeyi nafi ki sauri fa bakisan inda zanje bane fa shiyasa”.

    Tura baki tayi kana tace.

    “Yah Jameel Ina zaka je”.

    Murmushi yayi tare da kallon Asma’u da Bashir kana yace.

    “Ku kula da kanku sannan ku riƙe kada ku manta da alƙawarin da kuka min ga amanar Ummi na kafin na dawo”.

    Murmushi sukayi tare da gyaɗa masa kai kana suka ce.

    “Insha Allah Yah Jameel Allah yatsare sai kadawo.

    Murmushi kawai yayi tare da jan motar suka fita saida Ummi taga motar ya ɓacewa kallonta kafin ta sauƙe ajiyar zuciya ta koma cikin gida Asma’u da Bashir na biye da ita.

     

    Acan mota kuwa Anutse M Jameel ke Driving kana ahankali ya juya ya kalli Khausar data tsirawa tiri idanu kana ya sauƙe numfashi daga zuciyarsa ya fara tunanin Maganar da zai mats kana cikin sanyin murya yace.

    “Lelewal”.

    Juyawa tayi ta kallesa tare da cewa.

    “Na’am Yah Jameel”.

    A hankali ya furzar da iska kana a hankali cikin tattausan lafazin yace.

    “Inne mi alfarma awajen ki mana?”.

    Anutse ta kallesa kana tace.

    “Toh Malam Jameel Allah yabani ikon yin duk al’farman daka ke so awajena”.

    Cikin jin daɗi ya buɗe idanunsa dake lumshe ya kalleta kana yace.

    “Kinyi alƙawarin duk abinda nake nemi al’farmar zaki yimin?”.

    Kai ta gyaɗa masa kana tana wasa da yatsun hannunta tace.

    “Na sani malam Jameel baza ka sani yin haramtaccen abu ba sannan baza ka sani yin abinda yafi ƙarfi naba kuma kafi ƙarfin neman alfarma ko wani abu awajena ina hana ka saidai ka bani Umarni Yah Jameel faɗa min me kake so inyi maka? Kai tsaye bani umarnin kawai ni kuwa in cika maka umarninka da sauri”.

    Jinjina kansa yayi still Yana driving Cike da nutsuwa kana yace.

    “Alhamdulillah naji daɗin Lelewal Thanks”.

    sai kuma yayi gyaran murya tare da juyowa ya kalleta, itama shi take kallo ganin yadda fuskarsa ta koma alamun daga can cikin ƙahon zuciyarsa abinda zai faɗa ɗin zai fito cikin yanayin neman al’farma cikin iyawa da ƙwarewa ya juya harshe zuwa sahihin Larabci mai cike da Kekkyawan lugga ya fara mgn da larabci yayinda itama Khausar ta  juya harshen zuwa larabcin.

     

    Aƙalla sunyi magana daya ɗauki tsawon minti goma sha biyar, kafin suka koma magana da yaren Hausa Inda M Jameel ya ƙare maganar da cewa.

    “Nagode Khausar Nagode Nagode Lelewal Ubangiji Allah ya miki albarka”.

     

    Khausar kuwa cikin wata raunan’niyar murya tayi ƙasa da kanta yayin da ruwan hawaye suka cika kwarmin Idanunta kana tace.

    “Ameen”.

    Ahankali M Jameel ya cigaba da Driving kana Yana cigaba da yi mata nasiyya akan rayuwa.

    Ahankali Khausar da Idanunta ke kan madubin side ɗin da take ta juya tare da kallon M Jameel kana tace.

    “Yah Jameel kamar wannan motar binmu fa take”.

    Kai ya gyaɗa mata kana cikin sanyin murya yace.

    “Eh nima na lura da haka Khausar tun ɗazu ma”.

    Jinjina kai tayi tare da cewa.

    “Toh Yah Jameel ka rage gudu mugani mana muga kodai mudin suke bi”.

    Kai ya gyaɗa tare da rage gudun still sai motar dake bayansu itama ta rage gudun.

    Ahankali M Jameel ya cigaba da Driving yayin da still motar ke bin bayansu.

    Suna isa wani babban super market M Jameel ya kalli Khausar da hankalinta ke kan motar kana yace.

    “Bari mushiga cikin Super Market ɗin nan mugani idan ma mu suke bi ai zasu tsaya”.

    Suna Parking suka fita tare da shiga cikin Super Market din M Jameel  ya ɗiba mata turaruka tare da Choculate da sweet da kuma Biscuits yana tsinta yana faɗa mata wasu kalamai da larabci, duk da dai ba ji nake amman yadda fuskarta ke nuna kalaman masu nauyi ne yake sanarmata.

    Kana kamar kimanin minti talatin da shigarsu suka fito ga mamakinsu sai suka ga wannan motar ta faka agefen nasu kai tsaye suka shiga motar M Jameel ya mata key ita ma wannan motar sai akamata key aka tayar sunbi ta bayan motar idanun Khausar ya sauƙa akan  Motar tana kallon fuskar mutanen ciki, duk da nesa ne ta gane cewa mutanen ne da  ta gani Arugar Jauro Yaya sannan itace abakin makarantar su kana taga still Motar ta cigaba da binsu.

     

    Lokaci ɗaya tsoro da damuwa ya shigeta cikin yanayin tsoro ta kalli M Jameel tare da cewa.

    “Yah Jameel Motar nan mu take bi”.

    Jinjina kai yayi tare da faɗin.

    “Nima naga alama amma watakila arashi ake samu sunyi”.

    Kai ta gyaɗa still zuciyarta na cigaba da bugawa da masifar ƙarfi suna cikin tafiya motar ta ɓacewa kallon su.

     

    Anutse M Jameel ya Kalli Khausar kana yace.

    “Kin gani kawai arashi ake samu may be suma zasu shiga Super Market ne sannan hanyar mu ɗaya shiyasa haka”.

    Murmushin yaƙe Khausar tayi kana tace.

    “Haka ne kam”.

    Aranta kuwa cewa tayi to kodai mutanen sun gane ta ganeta ne shiyasa suke bibiyar rayuwarta wata ƙil ita suke son su kasheta kana ta raya dole idan ta koma dole ta faɗawa Mommy.

     

    Anutse M Jameel ya juya tare da kallon Khausar data zurfafa cikin tunani kana yace.

    “Lelewal muje mu gidan su Moddibo ki gaishe da Kakarmu”.

    Da sauri ta dafe ƙirjinta tare da cewa.

    “Gidansu Moddibo kuma?”.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “Babu abinda zai miki Khausar”.

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Nikam ina tsoro Yah Jameel. Abu kaɗan ya fara masifa ko agidan mu ma faɗa yake min bare kuma naje gidansu”.

    Cikin sanyin murya M Jameel yace.

    “Nayi miki alƙawari ko hararanki ba zai yiba, Insha Allah bare kuma ya miki faɗa zai miki maraba, ki yarda dani”.

    Kai ta gyaɗa kana cikin sanyin murya tace.

    “Toh shikenan”.

     

    Suna isa gidan yayi Parking a coumpund din farkon kana ya fita cike da nutsuwa yake tafiya tana biye dashi a baya, a kuma dai-dai lokacin da Moddibo ke kokarin fitowa daga falonsa,  cikin sassarfa ya nufeshi.

    Shi kuwa Modibbo wani irin sassayan numfashi ya fesar tare da tsaida idanunsa kan J ɗinsa.

    Shi kuwa M Jameel murmushi mai cike da farin ciki yayi tare ƙara sawa wurin Modibbo rungume shi yayi da ƙarfi.

    Wanda haka yasa shima Modibbo yayi masa wani irin amintaccen

    runguma mai cike da son juna a tare suka sauƙe ajiyan zuciya cikin sanyin sauti  Modibbo yace.

    “J nayi fushi da kai”.

    Cikin sanyin Muryan M Jameel yace.

    “Kada kayi fushi dani A.J idan kayi fushi da J ɗin ka dawa zaka sulhunta”.

    Cikin sanyin Murya Moddibo yace.

    “J ka tafi gidan Ummi ka barmu mu kadai agidan, sam gidan nan ba daɗi idan baka nan shiru baki ɗaya gidan bai mana daɗi ba”.

     

    Murmushi M Jameel yayi kana a hankali yace.

    “A.J Rungumeka da nayi alfarma nake nema awajenka.

    Saboda muyi maganar sirri akwai baƙuwar da nazo da ita dan Allah dan darajar Annabi A.J ko hararanta kada kayi”.

    Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da cewa.

    “Ayyah A.J ka tayani cika al’ƙawarin dana ɗauka dan Allah kada ka tozar tamu ka tuna ba haushe yace baƙonka Annabin ka sannan Annabi Muhammad (S.A.W) yace duk wanda yayi imani da Allah da rana ta ƙarshe to ya girmama baƙon”.

    Kai Moddibo ya jinjina kana yace.

    “Toh J naji dama ya za’ayi na tozarta matar da J na zai aura har abada bazanyi hakaba?”.

    Hararansa M Jameel yayi tare da faɗin.

    “Kai dai kayi min al’ƙawari koma wacece ai zaka ganta”.

    Kai kawai Moddibo ya gyaɗa.

    Tare da cewa.

    “Nayi al’ƙawari”.

    Ahankali M Jameel ya sakeshi tare da matsawa.

    Da sauri Moddibo ya ɗan yi gefe da kansa lokacin da idanunsa suka sauka akan Khausar da Idanunta ke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

     

    Khausar kuwa cikin wata Sanyayyar murya mai cike da rauni ta kawar da kanta gefe tare da cewa.

    “Ina yini”.

    Kamar yanda ta kawar da kai gefe haka shima ya kawar tare da faɗin.

    “Lafiya”.

    Daga nan ya juya yayi gaba.

    Khausar da M Jameel suka jera atare zuwa sashen Innayi bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga.

     

    M Jameel kuwa cikin yanayin sa yace.

    “Innayi ga baƙuwa na kawo miki ku gaisa”.

    Daga cikin Innayi tayi murmushi tare da cewa.

    “Sannun ku da zuwa ko dai matar ce ka kawo Min?”.

    Murmushi mai sauti yayi kana yace.

    “Ehahea lallai Innayi kenan ke dai ga tanan ku gaisa dama zan wuce da ita gida ne.

    Kuma A.J nata kirana shiyasa nace bari na fara zuwa nasan idan bai ganni ba wataƙil hankalin sa bazai kwanta ba”.

     

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauke kana yace.

    “Hmmm Yayi maka kyau da kazo a gaggauce ai da sai ka ajiyeta kafin kazo”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.

    “Ai kawota nayi ta gaida Innayi kuma bamu gama tattaunawa da itaba”.

    Taɓe baki Moddibo yayi ba tare da yace komai ba.

     

    Khausar kuwa ahankali ta tsugunna tare da Gaishe da Innayi.

    Kallonta Innayi tayi kana tace.

    “A’a wannan ai kamar na ganeki kamar ƙawar Asma’u ko?”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da sakin murmushi kana tace.

    “Eh nice Innayi”.

    Jinjina kai Innayi tayi tare da cewa.

    “Yasu mamanki?”.

    Cike da nutsuwa Khausar tace.

    “Duk suna lafiya”.

    Ƙoƙarin miƙewa Innayi tayi kana tace.

    “Bari akawo miki abin taɓawa”.

    Cikin sauri Khausar ta girgiza kai tare da cewa.

    “Nagode Innayi yanzu daga gidan Ummi nake ta cika min cika na da abinci”.

     

    Saurin kallonta Moddibo yayi jin yanda take magana Anutse kamar ba ita ba baki ya taɓe tare da mgnar zuci.

    “Ganta kamar gaske haka take da nitsuwa”.

    M Jameel kuwa kallon Innayi yayi kana ya juyi ya kalli Khausar yace.

    “Mu tafi ko”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Toh”.

    kana tayi gaba M Jameel da Moddibo suka fito atare a hankali suke tafiya, a hankali lips ɗin M Jameel na motsawa alamun mgn yakeyiwa Modibbo, shi kuwa Modibbo kai kawai yake jinjina mishi tare da tsaresa da ido, a haka har suka isa bakin motar Moddibo da kanshi ya buɗe masa gaban motar ya shiga kana yace.

    “Dan Allah kazo kada ka barni. Ni kaɗai sam bana jin daɗin gidan”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da yiwa motar key kana yace.

    “A.J ka jika randa akace babu nifa?”.

    Cikin sauri Moddibo ya rumtse idanunsa da karfi, sai kuma ya buɗe su da sauri ya kallesa tare da cewa.

    “Jhhhh”.

    Ya ja sunan a cikin maƙoshinsa.

    Murmushi M Jameel yayi tare da jan motar,

    Shi kuwa Modibbo hannunsa ya harɗe a ƙirji yana kallonsa har  suka tafi.

     

    Kai tsaye unguwar su Khausar suka nufa suna tafe yana tsokanarta, a haka har suka isa yana isa yayi Parking ta fita tare da yi masa godiya kana tayi cikin gida.

     

    M Jameel kuwa Anutse ya juya akalar motarsa kai tsaye gidansu ya nufa yana isa yayi Parking tare da fita kai tsaye sashen Abban sa ya nufa yan shiga sukayi ta hira har La’asar tayi, atare suka je masallaci suka gabatar da sallah kana bayan su. Idar ya fito ya nufi Sashen sa yashiga bai sake fita ba sai da akayi Maghariba kana ya nufi masallaci bai fito ba sai da aka Idar da Isha’i sannan yana dawowa ya nufi sashen Abbansa lokacin shima Abbah bai dade da dawowa daga masallaci ba.

    Cikin lumshe ido yace.

    “Abba zanje wajen Moddibo za muyi magana”.

    Jinjina kai Abba yayi tare da cewa.

    “Allah ya tsare amma idan dare yayi ka kwana a can bana son tafiyar daren nan, kasan duniyar nan babu gaskiya”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana ya fice yana murmushi.

    Motarsa ya shiga da addu’a kana yayi Hong mai gadi ya buɗe masa ya hau kan titi yana maiyin murmushin, wayarsa ya zaro, whatsApp ya shiga kan number’n Moddibon ya kusa kai.

    Cikin sakin murmushin yayi mishi voice ɗin 1 mitune And 33 second

    Ba zato ba tsammani yaji an sako hannu daga bayansa an ɗaura masa bindiga akai kana cikin wata magautacciyar murya akace kana juyawa zan fasa maka ƙwaƙwalwar kai da sauri ya saki wayar tasa ta faɗa kan cinyarsa garin ta sule ɗin ne kuma yatsarsa ma nuniya tayi sending din voise ɗin nasa da sauri ya ƙara taka motar jin mutumin ya ɗana kunaman bindigar yana cewa.

    “Maza mu tafi kada kayi min gardama dan ko motsi kayi zan fasa kanka…!

     

     

     

     

    Dan-dan yanzufa aka fara labarin ku biyuni, da kekkyawar yaƙini da ƙarfin zuciya.

     

    *By*

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 17

    Sakayyah 17

     

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 17_

    *LAST FREE PAGE*

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *DAGA WANNAN PAGE ƊIN FREE PAGES SUN ƘARE, IN MA KIN SAKE GANIN LITTAFIN SAKAYYAH A WAJE TO. NA SATANE NA ALLAH YA ISA ne, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal yar ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 kiyiwa da Annabi in dai kin san kin sayane don ki fitarmin da littafin na kiyi min mgn in mayar miki da kuɗinki. In kuma kin san zaki sayane dan ki fidda min littafina, wasu Groups ɗin, kiyiwa Allah da Manzonsa ki bar kuɗinki na yafe cinikin bana buƙatar sa*

     

     

    Alhamdulillah su Moddibo sun sauƙa lfy a ƙasa Mai Tsarki cikin ikon Allah Mabuwayi gagara Misali sunyi Umarah sun samu goma shabiyar na watan acan cike da ɗumbin farin ciki.

    Yau yakasance ranace ta Sallah angama azumi lfya. Al’ummar Musulmai na duniya sun cika da farin ciki kowa kagani fuskarsa ɗauke da yalwataccen farin ciki, kana kowa yayi shiga ta haiba da kamala.

    Alhamdulillah bayan an saƙƙo daga sallar  idi ko wani gida kashiga zaka samesu cikin farin ciki da shiga ta kamala kana da Lafiyayyan abinci.

    Kamar yanda ko ina na faɗin duniya ya cika da farin cikin wannan ranan haka yakasance Agidan Lamiɗo.

    Acan falon Mommy kuwa hallare suka gaba ɗayan su Khausar ce tsaye riƙe da waya ahanununta cikin shiga ta alfarma da kamala wani rantsatstsen less ne Blue da ratsin fari ne ajikinta ɗinkin riga da skirt yayin da skirt ɗin ya fitar mata da shape din  ƙugunta rigan kuwa tayi ɗass ajikinta ma dai-dai-tan dukiyar fulaninta sun cika fam yayin da tayi ɗaurin ƴar Minister ta zubo yalwataccen sumar kanta zuwa baya daga gaban goshin kuwa ya kwanta luf-luf wuyanta maƙale da sarƙan Gwal da ɗan kunnensa kana fuskarta ɗauke da simple make up daya sake ƙawata kyawun fuskarta.

    Yayin da Raudat ma ke sanye cikin irin shigar dake jikin Khausar sai dai nata ɗinkin dogon riga ne.

    Haiydar kuwa sanye yake cikin wata Bugaggiyar shadda Sky blue anyi masa ɗinkin samarin zamani rigar ta tsaya iya gwiwarsa, kansa sanye da hula yalwataccen sumar irin na fulanin Usul yana kwance lib aƙeyarsa haka ma Ramadan sanye yake cikin irin shigar Haiydar Yayin da Mommy ke sanye cikin Atanfa mai Golden mai masifar kyau anyi mata ɗinkin riga da zani fuskarta ɗauke da simple make da Khausar tayi mata.

    Baki ɗaya falon wani sanyayyan ƙamshi yake fitarwa wanda ya haɗu da ƙamshin jikinsu.

    Cike da tsantsar farin ciki Khausar dake ɗaukar su hoto ta juya ta kalli Mommy kana tace .

    “Kuce Chesss”.

    Dariya suka fashe dashi kana suka ce.

    “Cheeessss”, Akuma dai-dai lokacin ta ɗauki hoton.

    Sosai hoton yayi kyau kallo ɗaya zaka musu ka tabbatar da cewa suna cikin tsantsar farin ciki da annushawa tare da nutsuwa.

     

    Suna cikin hoton Hajiya Bunayya tashigo cikin shiga ta alfarma da kamala sosai tayi kyau.

    Zama tayi bayan tayi Sallama Idanun ta akan Mommy tace.

    “Barka da Sallah ƙanwata fatan anyi Sallah lafiya?”.

    Murmushi Mommy tayi kana ta zauna kusa da ita tare da cewa.

    “Ayyah Yaya ina shirin zuwa wajenki ma”.

    Murmushi Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Ayyah babu komai nima cewa nayi bari na rigaki zuwa in samu ladan gaisuwar. Fatan munyi Sallah lafiya?”.

     

    Jinjina Kai Mommy tayi kana tace.

    “Lafiya Lau Alhamdulillah Yaya Ubangiji Allah ya amshi ibadun da ayyukanmu na Al’khairai Allah ya nuna mana na baɗin baɗaɗa da rai da lafiya”.

    Kai Hajiya Bunayya ta gyaɗa kana tace.

    “Ameen ya Allah Ƙanwata”.

     

    Khausar kuwa kallo ɗaya tayi mata ta kawar da kai gefe.

    Hajiya Bunayya kuwa kallonta ta mayar kan Khausar dake ɗaukar Haiydar, Ramadan, da Raudat hoto, cike da makirci tayi wani murmushi kana tace.

    “Khausar Barka da Sallah”.

    Anutse Khausar ta juya ta kalleta babu walwala afuskarta muryarta ta saisaita kana tace.

    “Yawwa Barka dai Ummah”.

     

    Hajiya Bunayya ta mayar da kallonta kan Haiydar dake tsaye gefenta hannunsa ta kama tare da damƙa masa key da murmushi afuskarta tace.

    “Ga Barka da Sallah ka Babana”.

    Zare ido Haiydar yayi tare da buɗe hannunsa ya kalli sabon key ɗin mashin dake cikin tafin hannunsa,

    cike da tsananim farin ciki mara misaltuwa ya faɗa jikin Hajiya Bunayya tare da rungumeta cike happy ya saƙi ƙara kana yace.

    “Wayyo Ummah na Nagode. Allah ya saka da al’khairi. Allah yaƙara miki nisan kwana mai amfani. Allah yarabaki da sharrin Mutum da Aljan, gaskiya nayi farin ciki kinyi surprise ɗina da kince sai bayan Sallah da kwana biyu.

    Cike da farin ciki tayi murmushin gefen baki kana tace.

    “Ameen,Ameen Babana, Eyyyy dama sunce sai bayan Sallah da kwana biyu sai kuma suka kawo jiya da daddare”.

     

    Khausar kuwa cike da takaicin halayyar matar ta riƙa watsa mata harara wani irin haushin ta takeji, aƙasan ranta kam cewa take shegiya muguwa aniyar ki ta biki da izinin Allah babu abinda zai samesa.

     

    Mommy kuwa kallon Khausar dake bin Hajiya Bunayya da harara tayi kai ta girgiza tare da cewa.

    “Khausar jeki ɗauko mana abinci a kichen ki kawo kin tsaya kin tsare mutane da ido baza ki iya taya ɗan uwanki samun abin farin cikin da yayi ba”.

    Zumɓura baki Khausar tayi  tare da miƙewa batare da tace Komai ba tashiga kichen.

     

    Haiydar kam Kallon Mommy Yayi kana yace.

    “Mommy Ummah ku tashi nayi muku hoto”.

    Miƙewa sukayi da murmushi afuskarsu Haiydar yashiga ɗaukar su.

    Khausar kuwa fitowa tayi hannunta riƙe da Warmers dake ɗauke da soyayyun kaji ta ajiye a dining kana ta koma ta sake ɗauko wasu Warmers ta ajiye.

    Dai-dai lokacin da Mommy ke cewa.

    “Yaya mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi Agaskiya nayi farin ciki”.

    Fuskar Khausar ta ɓata kana tace.

    “Haba Mommy irin wannan godiyar sai kace wacce aka biyawa Kujeran Hajji”.

    Kallonta Mommy tayi kana tace.

    “Ai kujeran hajjin ne Khausar, mutumin daya so ɗan ka arayuwa har yayi masa alkhairi ai babu kamarsa ”.

    Kai Khausar ta girgiza kawai aranta tace Mommy har yanzu baki san wacece wannan makirar matarba, shiyasa kike yabonta wannan matar da kike gani tafi kwalba sharri afili kuwa cewa tayi.

    “Hmmmm Allah ya kyauta”.

     

    Murmushin da be wuce saman laɓɓaba Hajiya Bunayya tayi kana ta miƙe tare da cewa.

    “Nikam zan wuce”.

    Miƙewa Mommy tayi tare da cewa toh mungode Yaya Allah yaƙara girma da ɗaukaka”.

    Ita kuwa Hajiya Bunayya ficewa tayi Yayin da Haiydar yabi bayanta zuwa sashen Lamiɗo.

    yana shiga yace.

    “Abba gashi Ummah ta siya min Mashin zan hau?”.

    Kai Lamiɗo ya gyaɗa kana yace.

    “Babu damuwa tun da kana son hakan, amma kafin nan sai an sake koya maka mashin ɗin na tsawon wata biyu kafin ka fara hawa kai ɗaya kaga ai ka sake koya”.

    Jinjina kai Haiydar yayi kana yace.

    “Toh shikenan Abba babu Matsala ”.

     

    Bayan sallah da kwana biyu jirginsu Moddibo ya sauƙa a Nigeria cike da farin ciki Moddibo, Innayi da M Jameel Ummi suka dawo gida yayin da Hajja Nana ma ta sauƙa ta Ɓadamaye cike da farin ciki da kuma murna.

     

    **********

     

    Ahaka rayuwa ta cigaba da tafiya komai yana tafiya dai-dai cikin ikon Allah Akwana atashi asaran mai rai, sekonni na juyawa izuwa Mintuna, Mintuna na tafiya izuwa awanni.

    Yayin da awanni ke juyawa izuwa kwanaki, kwanaki na tafiya izuwa Makonni.

    Yayin da Mokonni ke juyawa izuwa Watanni. A hankali kuma  watanni ke tafiya Izuwa shakara ko shekaru…

     

    Alhamdulillah su Khausar sunyi nisa kiwo aski yazo gaban goshi, yanzu suna shirye shiryen zana jarabawar Ƙarshe na kammala secondary School WEAC and NECO baki ɗaya kansu ya ɗauki zafi basu da wani lokaci saina karatu sosai suka maida hankalin su suna karatu tuƙuru domin fitowa da kyakkyawan sakamako Inda yanzu ya rage saura Exam biyar ya rage su kammala Neco.

     

    Khausar ce tsaye gaban Dressing mirror jikinta ɗaure da towel da tsawon sa ya kai gwiwarta,

    Zuwa yanzu ko ina na jikinta ya cika fam, dukkan ƙirar girma maƙerin budurci ya ƙenƙesa matashi, musamman Dukiyar fulaninta da kuma hips dinta da suka cika ƙugunta, yalwataccen sumar kanta irin na Fulanin Usul ya sake tsawo da sansti.

    Manyan Idanunta sun sake girma tare da lumshewa siririn dogon hancinta ya sake tsawo yayin da madaidaicin bakinta ya sake tattarewa izuwa pich collor, yana yin ƙiranta kamar kolbar Coca cola Yayin da Tsananin kamanninta da Kajol ya sake bayyana ayanzu tana da shekara goma sha tara a duniya.

    Cikin sauri ta shafa Lotion ɗin ta tare da shafa powder sama-sama sai kuma ta shafa kwalli amanyan Idanunta lipstick kaɗan ta shafa asaman laɓɓannta cikin sauri sauri ta sanya Uniform ɗin ta daya sha guga tulin sumar kanta tayi acuci dashi kana ta feshe jikinta da turarukanta masu masifar daɗin ƙamshi da sanya nutsuwa.

    Cikin Sassarfa ta fito falo harara Mommy ta maka mata kana tace.

    “Ke dai Khausar ba zaki canza ba kin girma amma kullum shiririta kike ƙarawa tun yaushe Ake jiranki, ga Amina ma can tanata jira amma sai ɓata musu lokaci kike”.

    Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da riƙe kunnenta kana tace.

    “Sorry Mommy”.

    Fuska ta tsuke tare da ce wa. “Kin dai san Amina in ta gaji da jiran ki”.

    Cikin ɗan sauƙe numfashi tace.

    “Uhumm ai yaseen in ta gaya min mgn ramawa zanyi in banda asarama tun tuni yaci ace ta gama, amman kullum taba cikin dakon aji har wai sai yanzu zamu gama tare”.

    Mommy na juya zata fita tace.

    “A’a ni bana son fitina”.

    Ta ida mgnar tana fita,

     

    Haka yasa ta biyo bayan Mommy da ɗan sauri yayin da ko wanni gaɓa na jikinta ke motsa wa baki ɗaya alamun Budurci sun bayyana ajikinta ta ko wanni fanni ta zama cikakkiyar budurwa ƴar gayu First class.

    Bayan motar ta buɗe ta shiga bayan ta ƙarasa wajen gani tayi duk Amina ta wani babbaje.

    Kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace.

    “Ɗan matsamin in zauna”.

    Kallon banza Amina ta watsa mata cikin ya mutse Fuska ta kalli Khausar kana tace.

    “Keɗin har nawa kike da wannan wajen ba zai ishe ki ba?”.

    Cikin juya ido tace.

    “Kinsa cikakkiyar sura ta ƙasaitattun mata Allah ya min dole wurin bazai isheni ba tunda ba irin baki bane”.

    Cike da fusata Amina tace.

    “Eh lallai yarinyar nan wuyanki ya kai yanka, amman dadin ta dai bada ɗuwawunki nake zamaba kuma bada ƙugunki nake ɗaura zabi ba”.

    Taɓeki tayi tare da juyawa ta kalleta.

    Har kamar zata yi magana sai kuma ta fasa ganin yanda lokaci ke tafiya sannan ya Exam na Geography zasuyi tasan muddin aka fara Moddibo na iya hukuntata baya ga haka ga kuma alamun yau akwai  hadari a garin wanda yau kimanin kwana tara kenan ba’ayin musu ruwan saman ba.

    Gefen Haiydar ne ya matsa mata ta shiga kana Driver yaja suka tafi.

    Suna Isa Khausar tayi saurin ficewa tare da nufar Hall da zasu zana Exam ta nufi Hall ɗin yayin da Iska mai sanyi ya soma kaɗawa gari ya fara duhu suna cikin rubuta Exam ɗin hadari ya fara haɗa gangami sosai a hankali gari ya fara duhu.

    Basu wani ja lokaci ba suka kammala rubuta Exam ɗin atare Khausar da Asma’u suka fito.

    Asma’u ma ta zama cikakkiyar budurwa komai na Budurci ya bayyana ajikinta.

     

    Juyowa Khausar tayi  ta kalleta ƙirjinta rungume da Questions da suka gama rubutawa,  murmushi ta ɗan yi kana tace.

    “Asmeey ki gaida min Ummi dan Allah, wallahi nayi missing ɗinta, rabo na da ita fa ya kai wata biyu”.

     

    Hararanta Asma’u liƙa mata kana tace.

    “Ai baki da kirkine sannan babu saƙon  ki da zan fada mata in da gaskene kizo”.

    Ta ƙare mgnar tana mai ɗaga kanta ta kalli sama, ganin yadda gaba ɗaya garin ya rufa yayi duhu.

    Da sauri Khausar ma ta fara juye-juye tana cewa.

    “Yah Salam wannan hadari haka, ina Haiydar suzo mu tafi, kar ruwa nan ya rutsamu a nan.”

    Murmushi Asma’u tayi tare da cewa.

    “Allah yasa ya rutsa kin dai muga ta tsoro”.

    Ta ida mgnar tare da yin murmushin mugunta dan tasan yadda Khausar ke masifar tsoron walƙiya da tsawa.

    “Ba Amin ba”.

    Khausar ta faɗa tare da tura baki.

    Ita kuwa Asma’u dariya tayi tare da jan hannun Bashir sukayi gaba saboda yanda hadarin ke sake gangami ko ina yayi ɗib.

    Murmushi Khausar tayi kana tace.

    “Bashir dan Allah kagaida Ummi, dan naga yau mutuniyar Black Stomach take ji dashi”.

    Asma’u na ƙoƙarin shiga mota tayi murmushi kana tace.

    “Oho dai ance zuwa da kai ai yafi saƙo”.

    Khausar kuwa murmushi tayi tare da bin bayansu ganin Haiydar yayi gaba.

    Da ɗa  sassarfa ta  tashiga bayan motar ta zauna kusa da Haiydar tana ɗan kallon harabar makarantar da duk aka watse sai mutane ɗaɗɗaya har malamai da alamun sun tattafi da sauri ta juya ta kalli Haiydar kana tace.

    “Ina Amina kuma?”.

    hannu ya buɗe mata alamar bai sani ba, bata sake cewa komai ba,

    ta lumshe idanunta tare da jingina bayanta da jikin Kujeran sassayan iskan  hadarin dake bugawa na ratsata.

     

    Acan harabar makarantar kuwa Amina ce da Samira Sani ke tafiya.

    Cikin taɓe baki Samira ta kalli Amina kana tace.

    “Ni wallahi tunda nake ban taɓa kallon mutum Irin Moddibo ba ace mutum kamar dutse sam baya fahimtar komai”.

    Murmushi Amina tayi kana tace.

    “Hmmm ke dai Samira bari M Jameel ɗin ma meyene, duk tsawon lokacin da muka ɗauka muna aiki da maganin fa yanda yake wani shan min Ƙamshi”.

    Harara Samira ta watsa mata cike da takaici tace.

    “Amma Wallahi Amina baki da godiyar Allah ki dubi yanda mutumin nan ya fara sake miki, yana amsa gaisuwar ki da fara’a, yana kula ki da ace nice nasamu wannan damar, awajen Moddibo ai dana godewa Allah”.

    Jinjina kai Amina tayi kana tace.

    “Haka ne kuma amma gaskiya har yanzu sai mun sake sabon shiri akansu domin har yanzu Malam Jameel yafi ji da wannan shegiyar yarinyar akaina”.

    Da wannan hira suka isa jikin motar wani matsiyacin kallo Amina ta watsawa Khausar dake bayan mota Idanunta alumshe cike da gadara da kuma Izzah ta ya mutse fuska kana tace.

    “Iyeee ƙarfin hali yau naji Agola da ƙarfin hali, motar na gidan Ubankine da zaki shiga baya kiyi kane-kane aciki, to ni kuma a ina zan zauna ji yanda kika tara ƙannenki kuka lafe abaya ku gaku ramukan kura ko daga ke sai ƙannen ki, wai ma tukunna ni akanki zan zauna ne!? Da kika wani baza masaka-masakan duwaiwaka”.

     

    Ahankali Khausar ta buɗe Idanunta dake lumshe ta zuba mata su tana kallonta cike da mmki, amma ba tace komai ba sai gyara zamanta da tayi tare da buɗa mata inda zata zauna.

     

    Ya mutse fuska Amina tayi cike da jaraba da kuma gadara ta dubi inda Khausar ta matsa mata kana tace.

    “Wannan wani irin iskanci ne da raini ne ko kuma ni sa’ar kice ke badan kinyi sa’ar Babanki ya mutu ya bar uwarki tayi zawarci babana ya kwasa ba ai koda hanyar da nabi baki isa ki biba. Agola kawai mara galihu ƴar matsiyata”.

     

    Cike da ɓacin rai Khausar ta ɗago kanta babu walwala afuskarta ta kalli Amina tare da cewa.

    “Wai Meyesa kike son zagina ne? Baga shi na gyara niki ba wannan ɗan ɗuwawun da kamar an ɗaurawa kare zani me zai hana filin isarki, baki shigo  kin zauna kinga wurin bai ishi tsamurarrun mauzanki da suke kamar an matse lemon tsamiba kawai saboda kin saba da Akuyanci da kuma karnukan ci sai kin tsaya anta masifa dake da raba hali, saboda ke Jaka ce baki san darajar mutane ba,  zaki tsaya kina ta goranta min akan wani Akwalar mota! To ki sani ni dai bazan zagi iyayenku ba musamman mahaifinki da yake mumini uwarki kuwa zaginta ma asarane don ko zagi akan mai tsarki yake fatan a aikeshi”.

    Harara Amina ta watsa mata kana Afusace tace.

    “Eh koda Akwalar ce aiba Ubanki bane ya saya idan kuma Ubankine ya saya sai inji? koda yake nasan har matsiyacin Ubannaki ya mutu bai taɓa mallakar irin wannan na kansa ba!”.

    Cike da matsanancin ɓacin rai Khausar ke kallonta idan akwai abinda tafi tsana aduniya kana yake saurin fusata ta shine zagin mahaifinta.

    Azuciye ta sauƙa daga motar yayinda Haiydar da su Ramadan ma suka sauƙo,

    cikin nuna Amina da yatsa tare da ƙanƙantar da idanunta kana tace.

    “Kada ki sake zagin Ubana domin Ubana yafi ki daraja koda Agaban Ubangiji”.

     

    A yatsine Amina ta watsa mata mugun kallo kana tace.

    “An zage sa ƴar iskan yarinya mai hana ruwa gudu ƴar matsiyata”.

    Cikin wani irin fushi Khausar ta ɗaga hannunta tare da kife Amina da wani irin azabebben mari hagu da dama cikin nunuta da yatsa tace.

    “Ki sake zagar min  Uba kiga abinda zan gwada miki”.

    Dafe kuncin Amina tayi cike da Mamaki take kallon Khausar kana tace.

    “Ni kika mara Khausar?”.

    Harara Khausar ta watsa mata da manyan Idanunta kana tace.

    “An mare ki”.

    Ahankali Habu Driver ya leƙo kansa tare da faɗin.

    “Khausar kiyi haƙuri”.

    Sai kuma ya kalli Amina dake huci kana yace.

    “Amina kema sam baki kyauta ba taya zaki zagi Ubanta ai duk Abinda zakuyi tsakaninku ne”.

    Wani shegen kallo ta watsa masa Afusace tace.

    “Habu ka rufe min baki ka fita Idona na zagi Uban nata idan taji haushi tabar mana gidan mu ta tafi gidan Ubanta ƴar matsiyata ƴar jarababbu Angola ta bar nan garin ta koma can dajin nasu mana”.

    Ta ida maganar tare da shiga motar taja murfin ta rufe da ƙarfi.

    Sai kuma ta sauƙe glass ɗin motar  tare da cewa “Haiydar, Ramadan, da Raudat ku shigo motar tunda ku dai ta  Ubanmu ne”.

    Cikin takaici Haiydar ya girgiza kai alamar a’a su tafi.

    Ita kuwa Khausar ciki takaici ta ɗaga Raudat da Ramadan ta sakasu cikin motar tare da nunawa Haiydar ƙofar motar alamun ya shiga.

    Murya a cushe yace.

    “Toh kefa Adda Khausy”.

    Cikin danne fushinta tace.

    “Kada ka damu zan shiga Napep”.

    Zai yi mgn tayi tayi saurin cewa.

    “Dan Allah kada kace komai shiga kuje”.

    Ta ƙare mgnar tana turashi ciki, dole ya shiga.  Ita kuwa Amina tsaki taja tare da cewa.

    “Dole su kam shiga ke kuma sai kije can kishiga naki na Uban”.

     

    Kallon Habu tayi kana tace.

    “Haba kaja motar mu tafi”.

    Da mamaki Habu drive ya kalleta kana yace.

    “Haba Amina taya zamu tafi mu barta anan dubi hadarin daya taso sannan babu kowa a haraban makarantar ya za’ayi mutafi ne”.

    Harara ta galla masa kana tace.

    “Mu tafi kuma wallahi idan ka ƙi na rantse da Allah saina sa Ummah tasa akoreka”.

    Ahankali Haiydar ya juya ya kalli Amina wanda tun da suka fara magana bai sa baki ba yace.

    “Haba Addah Amina Meyesa haka Fisabilillah ai koma menene bai kamata ki hanata shiga mota ba dubi hadari fa kuma kin san yadda take tsoron yanayin ruwan sama”.

    Harara ta watsa masa kana tace.

    “Rufe min baki an hanata ɗin rufe min baki ɗan Iskan yaro zaka nuna min ƴan Ubanci kenan ruwan ya cinyata, ta mutuma kawai kowa ya huta”.

    Da ɓacin rai Afuskarsa ya kalleta kana yace.

    “Ni dai bazan nuna miki ƴan Ubanci ba, saboda bamu tashi da shiba, kuma wallahi idan na koma gida na faɗawa Ummah ma ke kanki kinsan sai tayi miki faɗa”.

    Dogon tsaki taja tare da cewa.

    “Kayi sauri kada ƙuda ya rigaka”.

    Jin haka yasa Haiydar yin shiru sai kuma ya kalli Amina tare da cewa. “Matsa min In ɗauki jakata bazan iya tafiya in barta anan ba”.

    Girgiza kai Khausar tayi kana tace.

    “A’a Haidar kada ka ɗauka ka shiga dasu Ramadan ku tafi nima yanzu zan biyo bayanku”.

    Amina kuwa kallon Habu Driver tayi kana tace.

    “Mu tafi”.

    Jin haka yasa Khausar jan marfin motar tare da rufewa kana tace.

    “Pless dan Allah Haiydar zauna ku tafi, in Sha Allah babu abinda zai sameni”.

    Dole ya zauba ba don ya soba,

    Shi kuwa Habu ba yanda ya iya haka yaja motar ya tafi.

     

    *Yar uwa littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan page ɗin na gama Free page, in dai kin ganshi a waje to na satane, a Groups ɗina na sakayya ne ɗai ya halatta, 1k ne biya ki karanta cikin Salamah 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA ban yafe ba a karanta min littafi ba’a biya ba in kin tura kuɗin ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

     

    Khausar kuwa shiru tayi tare da bin motar da kallo har ya fice aharabar makarantar,  ahankali ta juya ta kalli cikin makantar babu ɗalibi ko ɗaya duk sun watse haka zalika ma Malamai duk sun watse shiru tayi sai kuma ta ɗaga kanta sama ganin yanda hadari ya taso ga iska dake kaɗawa da ƙarfi.

    Tamkar kazar da ƙwai ya fashewa aciki haka ta fara jan ƙafanta har ta fice acikin Makarantar tsayawa tayi abakin titin koda zata samu Napep amma takai minti biyar babu abin hawan da yazo ya gifta sakamakon hadari daya taso sosai a garin yasa dukkan ababe hawa tsagaita zirga-zirga tana nan tsaye har aka fara ɗan yayyafi hakan yasa ta fara tafiya ahankali a gefen titin.

    Ba tayi nisa da makarantar ba taji an buɗe gate ɗin makarantar da ɗan sauri ta juya, akan motar Moddibo Idanunta suka sauƙa da sauri ta kawar da kanta gefe kana ta cigaba da tafiya.

    Acikin mota kuwa Moddibo ne da M Jameel yayin da Moddibo ke  Driving M Jameel na gefen me zaman banza.

    Kallo ɗaya Moddibo yayiwa bayanta ya ganeta, baki ya taɓe Aransa yace yau kuma wannan wani sabon rashin kunya tayi musu suka sauƙeta, sai kuma ya ɗage kafarɗarsa alamun ita ta jiyo.

    M Jameel kuwa sam bai ganeta ba saida suka gifta wajenta sannan yaga fuskarta.

    Da mamaki ya furta.

    “A’a Lelewal”.

    Cikin sauri ya ɗaura hannunsa kan Moddibo tare da cewa.

    “A.J tsaya Please dubi duk ɗalibai sun watse amma sai ita kaɗai mai ya tsayar da ita anan kuma ga hadari baƙiƙƙirin dubi fa yanda garin yayi duhu ko Babba hadarin na bashi tsoro yakeyi!”.

    Juyawa Moddibo yayi tare da Kallonsa cikin yanayin nutsuwarsa yace.

    “To ina ruwanka da ita!?”.

    Wara Ido M Jameel yayi kana yace.

    “Ban gane ina ruwana da ita ba? ɗalibarmu cefa! sannan kullum a mota ake kawo su sannan zuwa ake aɗauke su, kana mun ganta ba’a tafi da ita ba sannan ka duba ita kaɗai ce a layin nan dubi fa yanda layin babu kowa”.

    Kallon gefen Ido Moddibo yayi masa kana ya taɓe baki.

    Da sauri M Jameel ya cigaba da cewa.

    “Haba A.J ya za’ayi kace haka?”.

    Moddibo kuwa juya idanunsa yayi kana yace.

    “Toh Meye haɗin mu da ita? kasan Meye Uzurin daya tsayar da ita?

    Sannan kasan Meye dalilin tsayuwarta! Wata ƙil ma wani bishiyoyin anguwar takeson hawa”.

     

    Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.

    “Ai koma mene sai mu tsaya mu tambayeta ko?”.

    Kallonsa Moddibo yayi kana yace.

    “Nifa bazan tsaya ba”.

    Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana cikin sanyin murya yace.

    “Dan Allah A.J da darajar Annabi Muhammad (S.A.W) mu taimaki yarinyar nan.

    Yanzu idan Asma’u ce zaka iya barin ta awajen nan ne?”.

    Da sauri Moddibo ya kallesa kana yace.

    “Asma’u kuma mai ma zai tsayar da ita anan mai zai haɗa ta faɗa da wasu har tayi musu rashin kunya su sauƙeta amota, ai Asma’u baza ta kasance haka bama!”.

    Sake Langwaɓar da kai M Jameel yayi kana yace.

    “Amma kayi tunani ƴa mace ce ita ko addininmu ya koyar mana da kula dasu da kuma kula da al’amuran daya shafesu A.J bai kamata ba na roƙe ka dan Allah ba danni ba kuma badan ita ba dan Allah da kuma darajar Manzon mu kayi haƙuri ka tsaya! In ma bazaka ɗauketa ba, ni ka sauƙin bazan iya tafiya in bar Khausy cikin wannan yanayin A.J bazan iya barin ta ananba”.

    Ya ƙarashe mgnar cikin wata iriyar raunatacciyar murya mai fito da sirrin dake binne cikin zuciyarsa.

    Hannu Moddibo ya sanya tare da dafe goshinsa alamar ya gaji da damuwar M Jameel ahankali yasanya lallausan tafin hannunsa ya shafa sajensa ba tare da yace komai ba ya taka burki ya tsaya.

    Yana mai kallon yadda M Jameel ya sauƙe numfashi.

    Ganin ya tsaya ya sanya M Jameel sakin murmushi tare da buɗe motar ya fita cikin sassarfa da ɗan gudu ya nufi inda Khausar take dan sun ɗanyi mata nisa kana ga yayyafin da aka fara da ƙarfi da kuma rugugi alamar ana gaba da kecewa da ruwa mai ƙarfi.

    Moddibo kuwa da kallo yabi M Jameel ta mirror motarsa.

    Aransa yace Ohhh J ji yanda yake gudu kamar wani yaro ko ya gani a wannan ƴar nan har yake jinta cikin zuciyarsa.

    Khausar kuwa tana ganin M Jameel ta saki nannauyan Ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Yaya Jameel”.

    Cike da kulawa ya kalleta tare da cewa.

    “Lelewal mai yafaru yana ganki anan ke kaɗai, bayan baki ɗaya student’s sun watse”.

    Ahankali ta kallesa sai kuma tayi saurin lumshe Idanunta tare da cewa.

    “Wallahi Yaya Jameel Amina ce ta hanani shiga motarsu yau kam masifa take ji dashi”.

    Girgiza kai yayi tare da faɗin.

    “Subhanallah gaskiya bata kyauta ba, maza zo ki shigo mota mutafi”.

    “Toh”,tace tare da bin bayansa cikin sassarfa yayinda ko wanne gaɓa na jikinta ke motsawa.

    Ɗan guntun tsaki Modibbo yaja, tare da kauda kansa daga kan madubin, ganin yadda suka wani jero da J ɗinsa.

    Suna isa wajen motar M Jameel ya buɗe mata bayan gefen da Modibbo yake tashiga, sannan shi kuma ya zagaya  ya shiga a hankali Khausar ta ɗaga kanta tare da kallon gaban motar ai kuwa idanunta suka sauƙa akan Moddibo da batasan yana cikin motar Ba gashi ta zauna asaitin bayansa.

    A kuma dai-dai lokaci  ruwa ya kece tamkar da bakin ƙorya, key Moddibo yayi wa motar tare da figarta a dan guje suka fara tafiya.

     

    Kallon Moddibo M Jameel yayi kana yace.

    “A.J kasan zamu biya ta gida ka sauƙe ni tun safe Abba ke kirana wai Inje Yana son magana dani muje ka sauƙe ni”.

    Kallon sa Moddibo yayi tare da cewa.

    “Baza ka bari sai anjima ba?”.

    Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.

    “A’a muje dan Allah ka sauƙe ni saboda bansan me yake sona dashi ba yanata ne mana tun tuntuni”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.

    “Toh naji”.

    Yayi mgnar tare da haharan M Jameel ɗin,

    Sannan ya cigaba da Driving ɗin sa.

    Shi kuwa M Jameel murmushin yayi tare da ɗan mishi alamun zunɗe.

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan page ɗin na gama Free page, daga gobe in dai kinga littafin SAKAYYAH a wani wuri to na satane, yar uwa ki biya 1k ne kacal ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin kowa a kanki littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa kada ki karanta in baki biyaba 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

     

    Khausar dake zaune abayan motar kuwa ƙanƙame jikinta tayi saboda yanda ɗumin motar ke ratsata sam cikin motar babu sanyi da yawa ba kamar waje da iska ke kaɗawa ba.

     

    Sanyayyar Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da gyara Questions peper dake hannunta ta sake rungumesu aƙirji sai kuma ta gyara zaman wuyan hijabinta wanda har tattausan gashin gaban goshinta mai sansti ya bayyana.

     

    Baki ɗaya cikin motar a wadace yake da wani irin ni’imtaccen sanyayyan ƙamshi mai daɗin shaƙa yakeyi, Ahankali Khausar ta maida kallon kan bayan Moddibo da take fuskanta sanye yake  cikin ɗanyen Boyel fari ƙal yasha guga sosai yayin da kansa ke sanye da hula zanna bukar wadataccen sumar ƙeyansa ya kwanto lib-lib gwanin kyau sai sheƙi da ƙyalli yake zubawa.

    Ƙeyar tasa ta zubawa ido sai kuma ta gallawa ƙeyar tasa harara  tare da murguɗa masa baki.

     

    Tana ɗago Idanunta suka sauƙa akan Idanun Moddibo ta madubin jikin motar yana kallonta cikin mugun sauri tayi ƙasa da kanta zuciyar ta na mai bugawa da ƙarfin tsiya.

    Moddibo kuwa Ƙoffa yayi tare da haɗa harshensa da hoƙorinsa ya fitar da wani sauti kana yace.

    “Hmmmm!”.

    Kallon sa M Jameel da Idanunsa ke lumshe yayi kana cike da kulawa yace.

    “Ya dai A.J?”.

    Shiru Moddibo ya masa tare da watsa masa Harara!.

    Ware Ido M Jameel yayi tare da shafa sajensa kana yace.

    “Ya dai kake ta harare-harare acikin mota!”.

    Ƙin tanka masa Moddibo yayi ya cigaba da Driving ɗinsa tare da ƙara tsuke fuska.

    Khausar kuwa shiru tayi sai kuma ta sake ɗago kanta ahankali ta kalli madubin ganin ya kawar da kansa gefe yasa ta sake liƙawa ƙeyansa harara tamkar  idanunta zasu manne bisa ƙeyar tasa, kana ta ɗago hannunta na dama ta ɗan haɗe kan yatsun tare da buɗe su ta watsa masa alamar Jarabebbe! Mayatacce!! Masifeffe!!! Fitinenne!!!! sai kuma ta sake watsa masa Harara tare da kai hannunta ƙeyarsa kamar zata kai masa ronƙwashi.

    A kuma dai-dai lokacin ya ɗago ya kalleta ta madubin.

    Azabure taja baya tare da jinginar da bayanta da jikin kujeran zuciyarta na bugawa.

    Cikin fushi Moddibo ya watsa mata mugun kallo tare da cewa.

    “Anh zan karyaki wallahi kakkarya ki zanyi in watsar dake atiti inyi tafiyata, ƴar rashin kunya fitsararriya”.

    Ita dai Khausar rumtse Idanunta tayi da masifan ƙarfi tare da sake rungume question peper ta aƙirji gam-gam.

    M Jameel kuwa daya ta kure jikinsa waje ɗaya idanunsa alumshe saboda sanyi da ake yayi saurin buɗe idanunsa yayi tare da kallon Moddibo dake Driving tamkar bashi yayi maganar ba cikin tsaresa da Ido yace.

    “Ha’a wai mai yake faruwa a motar nan ne kake abubuwa iri-iri daga Harara, Ƙoffa, tsaki, tsuke fuska,  yanzu kuma sai cewa zaka kakkarya!,To waima wa zaka karya ne kam?”.

     

    Cikin fushi Moddibo ya juya ya kallesa kana yace.

    “Ai duk wanda zan karya ya sani!

    Karya yarinyar nan zanyi fitsararriyar banza mara kunya idan kina sake kuskuren kallon min ƙeyata saina gutsitsi-tsiraki na ƙwaƙule miki manyan mayatattun idonun ki masu kama da na yan maye na jefar! A titi ko na samu salama”.

    Lokaci ɗaya tsoro ya dirarwa Khausar jin wai zai Kakkarya ta ya ƙwaƙule mata ido cike da tsoro ta kuma ƙara rumtse Idanunta tare da ta kure jikinta ajikin kujera ita kanta batasan dalilin da yasa yake mata haka ba ita dai tasan da zata samu dama itama karyashin zatayi ta kuna tsitstsige gemunshi.

    Akuma dai-dai lokacin suka isa ƙofar gidan su M Jameel Moddibo yayi Parking.

    Ɓude Murfin motar M Jameel yayi tare da fita duk da ruwan da ake tsugawa bai hana sa saka kansa ta cikin glass ɗin side da Khausar take ba, cikin ƙasa da murya yace.

    “Lelewal be careful don’t Misbehaving kinga bana nan yaseen kika mishi ba dai-dai a titi zai wurgaki ya tafiyarsa”.

    Kai ta gyaɗa masa cike da alamun tsoro sai taji kamar ta fita ta bisa.

     

    Shikuwa M Jameel kallon Moddibo yayi tare da cewa.

    “Toh Allah ya tsare Allah ya kaiku lafiya A.J Amana ce, dan amana A.J ka kularmin da ita”.

    Daga haka ya juya da gudu ya nufi cikin gida zuwa lokacin duk ya jiƙe saboda yanda ruwan ke sauƙa da ƙarfi.

     

    Acikin motar kuwa lumshe idanu Moddibo yayi ba tare da yaja motar ba.

    Khausar kam ƙasa da kanta tayi aranta tace wannan dai akwai bahagon mutum, fisabilillah yana kallon yanda ake tsuga ruwa kamar da bakin ƙwarya amma yaja ya tsaya jifa yanda ruwan ke sauƙa.

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine daga wannan na gama Free page, 1k ne kuɗin samun damar karantawa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, biya ki karanta cikin Aminci*

     

    Sun kai kusan minti biyar ahaka ita batace komai ba, haka zalika shima baice komai ba banda sautin ƙaran ruwa babu abinda ke sauƙa ɗago Idanunsa yayi dai-dai lokacin da itama Khausar ta ɗago Idanunta ta kalli madubin cikin motar,

    idanunsu ne suka sarƙafe cikin na juna.

    Harara ya watsa mata kana cikin wata razananniyar murya da shi kansa  bai san yana da ita ba yace.

    “Uban me kike abayan mota koni.

    Driver kine harda wani hakimcewar ki abaya a dole kega Sarauniya kin samu Driver!

    Kifita idona fa, nifa ba J bane zan karya kifa”.

    Cikin sauri ta buɗe bayan motar ta fita aranta tace Gwanda inyi yanda yake so dan yanda yake kiran zai karya nin nan inda yazo da tsautsayi sai yajawa Mommy asarata, gaban motar ta buɗe ta shiga amma duk da haka saida ta ɗan jiƙe sabida ruwan da ya fara ƙarfi, tana zama yaja motar suka tafi.

    Akuma dai-dai lokacin ruwan ya sake kecewa da ƙarfin gaske tamkar da bakin ƙwarya ake tsuga ruwan.

     

    Khausar kam lumshe Idanunta tayi aranta tace ya Allah ka kaimu gida lafiya ka rabani da wannan bawa naka lafiya,

    domin akwai rata tsakaninsu da gida sosai ahankali ta buɗe Idanunta ta kalli titin da yayi shiru babu hayaniyar sai ƙugin motarsu da kuma yanda tayun ke fesar da Iska da ruwan kan kwalta fuuuu kana har zuwa yanzu garin ɓakiƙƙirin yake duk da kuwa yadda ake sheƙa ruwan alamar har yanzu ruwan bashi da niyyar ɗauke wa.

     

    Suna cikin tafiya akayi wani irin walƙiya mai haske.

    Da sauri Khausar ta rumtse idonta tare da furta.

    “Bismillahi”.

    A lokacin guda kuma ta sake buɗesu da sauri sabida

    jin wani irin rugugi da akayi mai bada sautin rududuuu-duuuuhhh kana ga walƙiya daya haska da wani irin sauri Khausar ta rungume jikinta waje ɗaya aranta tace.

    _“Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakil Subhanal Lazi yusabbihul ra’adu bi handihi  wal Mala’ikatu min hiyfatin”._

     

    Cikin tsananin tsoro tayi addu’ar domin arayuwarta babu abinda take masifar tsoro a damuna kamar tsawa da walƙiya  sam bata yarda ta haɗa ido da walƙiya da zaran taga za’a yi walƙiya zata rufe Idanunta ta sunkuyar da kanta.

    Shi kuwa Moddibo tafiya ya cigaba dayi yayin da titin yayi shiru babu hayaniyar komai sai bishiyoyi dake rangaji ruwa na sauƙa akansu Sanyayyar iska mai cike da Ni’imah na kaɗasu baki ɗaya shaguna dake gefen titin arufe suke baki daya garin babu hayaniya sai jefi-jefi suke hango Mutane.

     

    Suna cikin tafiyar aka sake wani walƙiya mai masifar haske ja, alamun yanzu za’a ƙara kecewa da ruwa.

    Atsorace cikin ɗaga sautin murya tace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”.

    Ta ida addu’ar tare da kife kanta akan gwiwarta yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa A ɗan juya kai Moddibo yayi kalleta, domin shi kansa zuciyarsa ta harba sabida walƙiyar saida ta ɗauke masa ido saboda yanda walƙiyar tazo da haske mai ƙarfin gaske sosai yaji tsoron walƙiyar amma sai yayi addu’a aransa kana yana cigaba da tafiya bai tsaya ba.

    Bayan walƙiyar ba daɗewa aka saki wata tsawa mai sautin rututuuuu alokaci ɗaya zuciyarsu ta buga domin ji sukayi tamkar ƙasa zai tsage.

    Atake wani matsananci tsoro ya sake lulluɓe Khausar yayin da jikinta yashiga rawa tamkar mazari kanta ta kife acinyarta zuciyarta na cigaba da bugawa da masifan ƙarfi kana har zuwa lokacin kanta na sunkuye akan ƙafafunta tun daga wannan rugugin.

    Yayinda gaba ɗaya mazauna garin Gembu Mebila suke cike da taraddadi sabida bisa dukkan alamu yau da tsawa da rugugin ruwan yake sauƙa.

     

    Acikin haka ne aka sake walƙiya mai masifar haske irin walkiyar nan mai zuwa tamkar an watsa dogon bulala koko tafiyar maciji,

    Da masifar haske da tarsatsi yazo tamkar an watsa bulala Sharrrrrr sai kuma a take aka saki wata iriyar tsawa mai masifar ƙarfi yabi yo bayansa wanda ke fitar da sautin felelelelelelelen  da masifar karaji da gigita dukkan bani adam

     

    Cikin wani irin tsananin tsoro da gigita Khausar ta saki ƙara mai masifar  sauti tare da furta. _“Hasbunallahu wani’imal wakil. Subhanal Lazi yusabbihul ra’adu bi hamdihi wal Mala’ikatu min hiyfatihi”._

    Atake aka sake sakin wani walƙiyar haɗe da wata iriyar firgitacciyar tsawa mai masifar kara mai razana dan adam dasa hanjin mutum kaɗawa.

    Cikin tsananin tsoro da masifar gigita ta dari ta ɗago kanta a kiɗime ta afkawa jikin Moddibo yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa shi kansa Moddibo wani irin tsoro ne ya kamasa saboda hasken walƙiyar saida ya tsaga glass ɗin gaban motarsa tare da bada sautin ƙarararassss!!!.

    Wani irin bugawa zuciyarsa keyi da masifar ƙarfe yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinsa ya ɗauki rawa ƙoƙarin taka burki yake amma ya gagara saboda yanda ta takure jikinta ajikinsa ta kanainayeshi, bashida wani kataɓus ɗin motsa wa, sabida yadda ta kife kanta afaffaɗan ƙirjinsa hannunta ɗaya na zagaye da bayansa yayin da ta cusa hannunta na dama akan maransa.

     

    Moddibo kuwa wani irin masifaffen rawa jikinsa ya farayi tamkar mazari yana wani irin tsuma ji yake tamkar ana tsikara masa allurai ne agaba ɗaya ilahirin jikinsa lokaci ɗaya wani irin baƙon yanayi ya ziyarcesa ga fargaban tsawar da har zuwa lokacin bai gama tsayawa ba.

    Tsawan na tsayawa wani mai masifar rugugi ya sake sauƙa.

    Wani irin masifaffen tsuma jikin Khausar keyi yayin da numfashinta ke fusga saboda tsananin tsoro Allah ya sani tana masifar tsoton tsawa hakan yasa ta sake ƙanƙamesa tamkar zata tsaga jikinsa ta shige ciki.

     

    Shi kuwa Moddibo baki ɗaya jikinsa tsuma ya shiga yi saboda yanda ta kanainayesa kar-kar-kar haka jikinsa ke rawa  yayin da baki ɗaya tsikar jikinsa ya miƙe daga tsakiyar kansa har zuwa babban yatsan ƙafarsa yaji wani irin yanayi wanda bai taɓa jiba a iya tsawon rayuwarsa, sai  yau kuma yanzu ya jishi.

     

    Wani irin harba zuyarsa da sashi mafi daraja a jikinsa sukayi a tare da wani irin azaban ƙarfi.

    Akuma lokacin aka sake sakin tsawa da walƙiya.

     

    Ita kam Khausar cikin tsananin gigita da tsananin tsoro kana da ficewar hayyaci ta sake rungumesu tare da sake tura hannunta ka maransa yayin da yatsun hannunta suka sauƙa akan cibiyar sa.

    Tsawar da aka sake yine ya razana illahirin wani abu mai rai dake yankin Gembu,

    yayinda hakan take a wurin Modibbo ma wani  cikin rashin sanin makaman kamawa ya ya buɗe hannayensa ya rungumeta da azaban karfi tare da taka burkin motar da ƙarfi wani irin sautin ƙuuuuuuu motar tayi tare da cigaba da tafiya sabida tsantsin kwaltan da yayi sabida ruwan sama da kuma tsantsin sabbin tayoyin da ƙyar ya samu motar ta tsaya a tsakiyar titin, sake Rungumeta yayi da masifar ƙarfe kana ya cusa kansa atsakanin kafaɗarta da wuyanta.

    Lokacin da aka kuma sakin wani irin rugugin nan da zakaji kamar ƙasa na amsawa.

    Atake zuciyarsu ya buga da mugun ƙarfi tare da bada sautin dib-dab-dib-dab-difffh yayin da yake jin wani irin masifaffen abu na tsirgar masa lokaci ɗaya lafiyarsa sa ta shaida mushi  kasantuwarsa cikekken Namiji.

    Ita kuwa khausar tana jin yatsarta cikin ɗan hudan cibiyarsa amma tsananin tsoron da take ciki yasa ta kasa fahimtar menene sai cusa kanta da ta kumayi a kirjinsa.

    Shi kam Moddibo wani irin rungumeta yayi da masifar ƙarfi yana mai sakin wani irin amintaccen nish….!

     

    *Free page sun ƙare daga wannan, ko kin ga littafin a wani wuri na satane, littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ɗin da nan kadai zanke posting*

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

    *By*

    *GARKUWAN MARUBUTA*