Author: Novels

  • Sakayyah 19

    Sakayyah 19

    SAKAYAH

     

    19

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

    Spjnyh.  Miƙewa Haiydar yayi kana ya nufi ƙofar falon fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Oyoyo Uncle Naseer”.

    Khausar dake zaune kan 1sitter sanye cikin riga da baƙin wando Pencil da riga pinch color mai gajeren hannu gaban rigar an rubuta Never Give Up manyan boobs ɗin ta sun cika gaban rigar yayin da bajejjen ƙugunta ya baje acikin wandon, kanta sanye da hular Net baƙi gashinta ya zubo ta gefen wuya, a hankali ta juyo ta kallesa tare da faɗaɗa fara’ar dake saman fuskarta kana tace.

    “Laaa Uncle Naseer”.

    Shi kuwa Naseer ido ya zuba mata yana sakar mata da wani irin shu’umin murmushi yayin da yashiga bin ilahirin jikinta da kallo wani irin kallon Up and Down yake mata yana jin komai nata na kars burgesa soyayyar ta na kuma ninkuwa a ransa.

    Cikin wani irin salo kana still Idanunsa na kanta ya wani lumshe ido afili ya furta.

    “Masha Allah Matata ta girma”.

    Mommy dake zaune kan 3sitter tayi murmushi tare da cewa.

    “Masha Allah Naseer mutanen India kwanan nan mukayi magana da Aunty Jameela kece min ka kusa dawowa Ashe-ashe dawowa yazo ma”.

    Murmushi yayi kana cikin yanayin zumuɗinsa yace.

    “Aidai kam suma Surprised ɗin su nayi babu wanda yasan dawowana akwanan nan kawai sai ganina sukayi”.

     

    Cike da kulawa Mommy tace.

    “Masha Allah sannu da zuwa ka iso”.

    Raudat da Ramadan dake zaune suka mike tare da zuwa suka riƙe hannunsa,hannun Raudat ya riƙe tare da ɗagata sama kana yace.

    “Iyeee Baby Raudat Masha Allah an girma anyi kyau. Amma dai duk da haka Matas tayi miki wayau ta fiki kyau”.

    Murmushi Mommy dake zaune tayi kana tace.

    “Haka dai kace”.

    Ware ido yayi kana idanunsa akan Khausar yace.

    “Allah kuwa Mommy dubi fa Khausi na tafita kyau”.

     

    Khausar kuwa lallausan tafin hannunta tasa ta rufe fuskarta.

    Sai kuma ta miƙe ta nufi kichen ta ɗauko drinks da Snacks sai kayan Friut tafi to masa dashi.

    Har zuwa lokacin batayi magana ba sai dai da zaran sun haɗa ido zata sakar masa da ɗan guntun murmushi kamar yanda shima yake sakar mata.

    Haiydar kuwa da sauri ya saki hannun Naseer kana ya nufi sashen Hajiya Bunayya yana faɗin.

    “Ummah,Ummah ga Uncle Naseer kizo ku gaisa”.

    Miƙewa Ummah tayi fuskarta ɗauke da murmushi Amina ma miƙewa tayi tana murmushi tabiyo bayansu.

     

    Cike da farin ciki Amina tace.

    “Uncle Naseer mutanen India”.

    Washe baki Naseer yayi domin shi mutum ne mai fara’a da son nuna shi wani ne, kana ga fafa da iyayi baya ga haka yana da budeɗɗen ido da son holewa.

    Ita kuwa Hajiya Bunayya  kallonsa takeyi da murmushi afuskarta tace.

    “Naseer sai ganinka mukayi babu sanarwar anyi karatu angama ka dawo Nigeria kenan?”.

    Sha fa sumar kansa yayi yana shan Fruit da Khausar ta kawo masa yace.

    “Wallahi kuwa Ummah nazo ganin Matata ce muyi aure in ɗauke ta mutafi.

    Amma Ziyara nazo yi muku zan koma da matata, dan bazan iya zaman Nigeria ba”.

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Ayyah Naseer ai nan ma muna da waja-je masu kyau kodai India sunfi mu Weather mai kyau ne?”.

    Girgiza Kai yayi tare da cewa.

    “No Mommy bawai Weather mai daɗi ba kawai dai can ɗin zan samu aiki ne sannan gaskiya ni yanzu bazan iya rayuwar Nigeria ba”.

    Ya ida maganar yana ya mutse fuska cike da Iyayi.

    Murmushin da bai wuce saman laɓɓaba Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Aikam dai kam yayi kyau Allah ya taimaka bari na koma ina aiki”.

    Ta ida maganar tare da miƙewa dan Allah ya sani ya ƙona mata rai da batun ya aure Khausar su koma India.

    Amina kuwa siririn tsaki taja cike da jin haushin yanda Naseer ke Shish-shigewa Khausar ta miƙe tabi bayan Hajiya Bunayya suka fice.

     

    Bayan fitarsu Mommy ta miƙe tashiga Kichen Haiydar ma miƙewa yayi tare da ɗaukar Ramadan da Raudat suka fita danmai yi musu lesson yazo.

    Falon ya rage daga Khausar sai Naseer, Ahankali Khausar ta miƙe da niyyan barin falon cikin sauri Naseer yace.

    “Ohh My dear Wife Why are you going?”.

    Murmushi Khausar tayi aranta tace Ohh Uncle Naseer sam bazai canza ba, wannan kalma ya riƙe ta tun yarinta alokacin batasan ma’anarsa ba amma yanzu da zaran ya faɗa kunya take ji wai matarsa ko kunya faɗa agaban su Mommy baya ji.

    Anutse ta dawo ta zauna a inda ta tashi, cikin tsareta da Ido yace.

    “Tunda baki gaisheni ba bari in gaishe ki”.

    Cikin sauri tayi ƙasa da kanta kana tace.

    “A’a Uncle Naseer ina yini ya karatu fatan ka dawo Lafiya?”.

    Sumar kansa ya shafa kana yace.

    “Karatu Alhamdulillah ya naki karatun??”.

    Murmushi Khausar tayi kana tace.

    “Alhamdulillah Uncle Naseer nan da kwana goma zamu gama Secondary school Insha Allah”.

    Washe baki yayi yana binta da wani irin  kallon yace.

    “A’a Masha Allah Abu yayi kyau kenan abu zai tafi dai-dai yanda aka tsara”.

    Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

     

    Ɗago kansa yayi tare da miƙewa ya koma kusa da ita.

    Cikin wata narkakkiyar murya ya kalleta tare da cewa.

    “Khausar ina fatan baki manta da maganar mu bako?”.

    Murmushi tayi still ba tace komai ba sai ƙasa da tayi da kanta tana cigaba da wasa da yatsun hannunta”.

    Shi kuwa Naseer sake narkar da muryarsa yayi tare da faɗin.

    “My Khausi kinsan dai ina sonki, ke tawa ce inaji Ajikina Ubangiji ya halicce ki ne domin ni kaɗai kinsan ina matuƙar ƙaunarki ina burin ki kasance matata ke ta dabance ina miki sahihiyar ƙauna bani da burin daya wuce mu zamto ma’aurata in mori ni’imar da Allah ya halitta miki”.

    Batare data ɗago kanta ba tace.

    “Uhm”.

    Shi kuwa wani narkar da fuska yayi tare da lanƙwasar da harshe kana yace.

    “Meyesa ne komai nace sai kice Uhm?. Yanzu ke kanki bakya jin kina so kiyi Aure ne? aike kanki kin girma kin kai matakin da akan kanki zaki buƙaci na miji atare dake musamman ma na miji irina wanda zai iya gamsar dake tare da biya Miki duk kan buƙatunki ko ba haka bane?”.

     

    Lokaci ɗaya Khausar ta kwaɓe fuska cikin yanayin rashin jin daɗi da kuma rashin tsammanin abinda ya faɗa ta ɗago kanta tare da Kallonsa sai kuma ta kawar da kanta gefe fuska a tsuke.

    Shiko sake narkar da murya yayi tare da tsira mata Idanu kana yace.

    “Shifa rayuwar nan baya tafiya dai-dai dole sai ansamu dai-dai-to atsakanin halittar Namiji da mace, rayuwar nan bata da wani daɗi idan har babu mace akusa da namiji, haka itama mace rayuwar bata mata daɗi idan har babu Namiji akusa da ita, musamman idan anfara tafiya irin matakin shekarun kin nan daga Sha tara, Ashirin, Ashirin da ɗaya,Asirin da biyar, Talatin,har zuwa talatin da biyar dole tana buƙatar Namiji”.

    Ya sake narkar da murya yana binta da wani shu’umin kallo yace.

    “Muyi Aurenmu Khausar zaki ci gaba da karatunki a India sai kije kiyi karatunki acan”.

     

    Ƙasa ta sake yi da kanta kana cikin yanayin ɓacin rai ta ɗago batare data yarda sun haɗa ido ba tace.

    “Ni bana sha’awar zuwa India nafiso in zauna an ƙasata kusa da Mommy na bana buƙatar duk wani abu da zai nesanta ni da ita da kuma ƙasata domin duk abinda India take dashi ai muma muna da shi harma fiye da nasun”.

    Cikin sauri ya sake Matsawa kusa da ita tare da sanya hannunsa zai kamata.

    Da mugun sauri ta kauce ranta babu daɗi ta kallesa kana tace.

    “Ya haka Uncle Naseer mai yasa zaka kama min hannu?”.

    Ido ya lumshe yana jin sautin muryarta na ratsa shi sai kuma ya buɗesu akanta tare da cewa.

    “Ohh My God wai Khausar har yanzu baki waye bane?  me haka kamar ba ƴar zamani ba!? Dan na taɓa ki ai bawani abu bane kada ki manta tun kina ƙarama ko su Abba sun sani ke mallaki nace idan Ubangiji ya nufa”.

     

    Fuska ta sake ɗaurewa kana cikin sauri tace.

    “Toh kabari sai Ubangijin ya nufa kasamu. Shaidu sai inzama mallakin naka”.

    Ta ida magarta tare da miƙewa tabar wajen.

    Binta yayi da kallo bajejjen ƙugunta wanda duk takun da tayi sai sun motsa tamkar da gangan take juyasu.

    Dai-dai lokacin kuma Mommy ta fito daga kichen yana ganin ta ya miƙe tare da cewa.

    “Mommy bari in isa wajen Yafendo Dadu”.

    Shi ɗin ɗan ƙanwar Gimbiya Dadu ce,

    Ya ida maganar tare da ficewa kai tsaye sashen Gimbiya Dadu ya nufa bakinsa ɗauke da Sallama ya shiga falon.

     

    Gimbiya Dadu dake zaune tana shan Fruit ta Washe baki kana tace.

    “Nasiru lallai mutanen India masha Allah sannu da zuwa”.

    Zama yayi daga gefenta yana murmushi kana yace.

    “Yafendo fatan mun sameku lafiya?”.

    Cike da farin ciki tace.

    “Lafiya lau Nasiru ina ƴar Uwata ƴar Autanmu”.

    Zamansa ya gyara tare da cewa.

    “Tana lafiya tace in gaisheki”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Ayyah Ina Amsawa”.

     

    Gyaran murya yayi tare da fuskantar Gimbiya Dadu kana yace.

    “Yafendo na gama karatuna yanzu na dawo sannan na dawo da burin yin Aure. Ya maganar mu da khausar tana nan dai ko?”.

    Ajiyar zuciya mai nauyi Gimbiya Dadu ta sauke tare da lumshe Idanunta kana ta saki wani shu’umin murmushi tare da kallonsa kana tace.

    “Sosai ma kuwa maganar ku tana nan mai zai hanata da izinin Ubangiji maganar ku tana nan baka da matar data wuce Khausar yau ɗin nan zan yiwa Abbansu maganar”.

    Cike da farin ciki ya saki sanyayyar ajiyar zuciya kana yace.

    “Kai Alhamdulillah Yafendo na naji daɗi”.

    Murmushi kawai tayi shi kuwa miƙewa yayi bayan sun sake taɓa hira ya tafi.

     

    Bayan kwana uku.

    Ahankali Khausar ta sauƙa daga motar dake kaisu makaranta hannun riƙe da Raudat ta nufi ajinsu ta kaita kana ta dawo tashiga ajinsu Lokacin har an fara raba booklet kallonta Malam Isma’il dake raba Booklet ɗin yayi kana yace.

    “Lelewal mai yasa kike son zuwa letti ne Exam ɗin ma baza ki fito da wuri ba?”.

    Langwaɓar da kai Khausar tayi tare da cewa.

    “Ayyah Malam ayimin afuwa”.

    Harara Samira Sani dake bayan ta ta watsa mata cike da tsanar ta Asma’u dake gefen ta ta girgiza kai domin ita dai ta rasa me. Khausar ta tsare musu suka tsaneta.

    Khausar kuwa zama tayi Malam Isma’il ya bata Booklet da kuma Quatons peper Na Arabic da zasuyi yau ma kamar kullum tun kafin a gama rabawa Khausar tashiga answering Questions ɗin cikin mintunan da baza su gaza ashirin ba ta kammala.

     

    Acan office ɗin Moddibo kuwa zaune yake ya jingina bayansa da jikin kujera yayin da ya ɗaura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya akan deks ɗin Idanunsa na lumshe.

    Cikin sauri ya buɗe Idanunsa tare da jan dogon tsaki.

    Domin da zaran ya rufe idanunsa babu abinda yake gani sai moment da suka kasance da yarinyar cike da damuwa ya sauƙe numfashi kana aƙasan ransa yace.

    “Na godewa Allah da yasa karatun yaran nan yazo ƙarshe kana naji daɗi da cewa sun gama Exam ɗina, bazan sake shiga ajinsu ba”.

    Da sauri ya runtse Idanunsa haka nan yake jin kunyar kansa da kansa ya rasa ta yanda zai fassara al’amarin yasan tun farko yarinyar bata da kunya bare kuma wannan abu ya faru shin taya zai iya haɗa ido da ita?.

     

    Anan sashin su kuwa.

    Atare Khausar da Asma’u suka fito daga Area class ɗinsu har zasu wuce suka hango M Jameel tsaye.

    Abakin Office ɗin su Moddibo.

    M Jameel ne tsaye ya jingina bayansa da jikin ƙofar yayin da Amina ke tsaye gefensa cikin iyayi da yauƙi ta kashe murya tare da cewa.

    “Malam sai gobe idan Allah ya kaimu zan dawo ko Principal ya dawo na amshi result ɗina”.

    Anutse M Jameel ya juya ya kalleta tare da cewa.

    “Ok Allah ya kaimu ki gaida gida”.

    Sake karya murya tayi cikin tsaresa da ido tace.

    “Toh gida zaiji Malam kaima ka gaida gida”.

    Jinjina kai yayi batare daya sake kallonta ba yace.

    “Gida zaiji”,Juyawa tayi tabar wajen.

    Dai-dai lokacin da Asma’u da Khausar suka iso a tare Kallonsa Khausar tayi tare da cewa.

    “Barka da rana Yah Jameel”.

    Murmushi ya sakar mata kana yace.

    “Yawwa Khausi bar ka dai yanzu kam an zama manyan ƴan mata ankusa agama Secondary school a huta  a shiga babin girma ko?”.

    Jinjina kai tayi cikin jin daɗi ta kalli Asma’u kana tace

    “Ai lallai dai kam bari kawai Yah Jameel jinmu nake tamkar ansaki tsuntsuwa daga sheƙarta.

    Wani irin daɗi mukeji mun kusa mu rabu da rayuwar bauta rayuwar duka cin zali, kaɗe ɗan kwali, harara, tsawa, hantara,”.

    Kallon ta M Jameel Yayi tare da juya idanunsa zuwa office ɗin ya mata alamar Moddibo na ciki.

    Cikin sauri ta sanya hannunta ta rufe bakinta tare da barin wajen bayanta Asma’u tabi tana ƙyalƙyala dariya tare da cewa.

    “Khausar ga Moddibo na miki magana wai kije”.

    Dariya M Jameel yayi ganin

    Cikin sassarfa Khausar ta fice daga wajen batare data yadda ta juya ba.

     

    Moddibo kuwa na zaune a office duk Maganar da sukayi akunnensa da zaran sautin muryanta ya ratsa kunnensa zaiji tsikar jikinsa ya tashi tamkar ana stikaresa da allura hakan yasa ya runtse Idanunsa da ƙarfi kana yayi shiru.

    Allah ne kaɗai yasan yana yin da yake ciki.

     

    Khausar kuwa na fita wajen motarsu ta nufa ta samu duk su Amina su shiga ita kadai ake jira tana zama Driver yaja suka tafi.

    Asma’u kuwa na fita ita da Bashir mai Napep ɗin su ya iso ya ɗauke su suka tafi.

     

    Washe gari da yamma bayan Khausar sun dawo makaranta misalin ƙarfe Uku ta fito cikin wata Bugaggiyar shadda milk color anyi masa ɗinkin dogon riga da kuma zubi da akayi sa da Coffee zare fuskarta ɗauke da light Make-up yayin da tayi ɗaurin Aysha Buhari ta zuba  jelar gashinta ta gefen dama dake fitar da sanyayyan ƙamshi kana ta yafa milk colour gyale akafaɗarta Hannunta riƙe da jaka Coffee haka ma takalmin Half cover coffee color jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin tularen Balila da  kuma Sedection.

    Kai tsaye Bedroom din Mommy ta nufa bakinta ɗauke da sallama tashiga ganin Mommy Bata ciki yasa ta fito tare da nufar kichen.

     

    Tsaye ta samu Mommy tana yanka albasa.

    Mommy na ganinta tace.

    “Har kin gama shiryawa?”

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Eh Mommy na gama shiryawa”.

    Jinjina kai Mommy tayi tana cigaba da yanka albarsar tace.

    “Idan kinje ki Gaishe da Ummin Asma’u”.

    Kai ta gyaɗa tare da gyara rikon Handbag din ta kana tace.

    “Insha Allah zata ji Mommy”.

    Dai-dai nan suka jiyo Sallamar Naseer afalo, cikin sauri ta kalli Mommy sai kuma ta ɓata fuska lokaci ɗaya ta nemi fara’ar dake fuskanta ta rasa.

    Kallon mamaki Mommy tayi mata kana tace.

    “Ya dai haka daga jin muryan sa kin wani tsuke fuska sai kace wanda yazo miki da wani mugun abu”.

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Babu komai Mommy”.

    Girgiza kai Mommy tayi tare da fita tana cewa.

    “A’a wa nakeji kamar Naseer mutan India”.

    Yana zaune kan kujera ya gyaɗa kai tare da cewa.

    “Eh Mommy nine”.

    Dai-dai lokacin da Khausar ta fito miƙewa yayi idanunsa akanta yace.

    “Wooow Masha Allah”.

    Sam ya mance da Mommy dake tsaye a wurin.

    Gaba ɗaya imaninsa ya tafi gareta cike da zalama ya nufi Khausar tamkar zai rungumeta yana faɗin.

    “Wowww my dear Wife you look so georoures, Fantastic, beautiful  you look so Pretty”.

    Khausar kuwa ganin yanda yake matsota zai Rungumeta yasa taja baya da sauri tare da cewa.

    “Nagode.

    Mommy kuwa kallon ikon Allah take ganin yanda baki ɗaya hankalinsa ya tafi kan Khausar da alama ya mance da tana wajen.

    Gyaran murya tayi tare da cewa.

    “A’a Naseer ka zauna mana akawo maka abin taɓawa mana”.

    Girgiza kai yayi da faɗin.

    “A’a Mommy Nagode”.

     

    Itako Khausar ɓata fuska tayi babu walwala atare da ita tace.

    “Mommy na tafi”.

    Cikin sauri ya mike tare da bin bayanta kana yace.

    “My dear Wife Ina Zakije?”.

    Ataƙaice tace.

    “Unguwa”,

    Cikin yanayin zumuɗinsa yace.

    “Bari in sauƙe ki”.

    Mommy kuwa ita kanta rawan kansa ya bata tsoro ganin yanda yake nuna zalamarsa afili kamar kura yaga ɗanyen Nama!”.

    Da sauri Mommy ta kallesa tare da cewa.

    “A’a Naseer ka bari basai ka kaita ba ai zata shiga Napep”.

    Zare ido yayi tare da cewa.

    “A’a Mommy na isa kamar ni  ace Matata tashiga Napep no, impossible kamar Matar Naseer Ibrahim ɗancanji amma ace Matata na hawa Napep Ina bai yiba bai yiba”.

     

    Ita kuwa Mommy aranta tace Ohhh wannan yaro dai Allah yamasa kurari bawai basu da arziƙinba mahaifinsa nadashi amman kurarinsa yafi kuɗin nasu yawa bashi da aiki sai cika baki.

    Khausar kuwa tuni ta fice cike da takaicin zumuɗinsa.

    Da sauri yabi bayanta yana cewa.

    “My dear Wife ki tsaya mana let me drop you”.

    Banza Khausar tayi masa tayi ficewar ta.

    Kashe murya yayi tare da cewa.

    “Dan Allah ki tsaya mai yasa kike yin haka?”.

    Ba tare data juya ba kana cikin ɗaure fuska tace.

    “A’a Uncle Naseer ka bari kawai zanje da kaina gidansu Asma’u nefa Napep ma zan shiga”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Yawwa muje kinga nima sai ingaishe da Umminta kinga dama na daɗe banga Asma’u ba yau ya kamata mu gaisa”.

    Khausar kam sake ɗaure fuska tayi tare da cewa.

    “Yaya Naseer Allah da kabari kada in saka wahala nasan baza ka rasa abinyi ba”.

    Langwaɓar da kai yayi tare da marairaice fuska kana ya karyar da murya tare da cewa.

    “Please My dear Wife allow me to escort you kinsan dai Ina ƙaunarki sannan ina son kasancewa da ke banaso kidinga nesanta kanki daga gareni”.

    Siririn tsaki taja aranta kana tayi gaba abinta domin har ga Allah zalamarsa na bata tsoro.

    Shi kuwa da sauri ya nufi Parking space tare da ɗaukar motarsa yazo ta gefenta tare da buɗe mata kana ya karyar da murya tare da cewa.

    “Please Wife to be kishigo mana”.

    Dai dai lokacin da gate man ya buɗewa Lamiɗo da Gimbiya Dadu suka shigo bisa duk kan alamu daga asibiti suke anje duba lafiyar Idonta dan bayan ta fito hannunta na riƙe da ledan magunguna da kuma tambarin asibiti.

     

    Gimbiya Dadu kuwa tun da ta sauƙa daga mota Idanunta nakan Khausar ta wani kafeta da Ido tare da sake laɓenta na ƙasa.

    Khausar kuwa cikin rawan jiki da tsinkewar zuciya tayi saurin koma wa bayan Naseer zuciyarta na bugawa da mugun ƙarfi cike da tsoro take karanta duk wata addu’a da tazo bakinta.

    Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.

    “A’a Nasiru ya dai ina zakuje kaida Mutuniyar taka?”.

    Cikin yanayin zumuɗinsa da rawan kai ya shafa ƙeyarsa tare da cewa.

    “Abbah zan kaita gidansu Asma’u ne dan banaso ta hau Napep”.

    Jinjina kai Abba yayi kana yace.

    “Yayi kyau Allah ya kiyaye hanya, Khausar sai kun dawo”.

    Kasa cewa komai Khausar tayi still tana tsaye bayan Naseer zuciyarta na cigaba da tsinkewa ganin har zuwa lokacin Gimbiya Dadu na Binta da ido burinta su haɗa Ido.

    Gyaran Murya Lamiɗo yayi kana yace.

    “Khausar shiga mota ku tafi”.

    Cikin sauri tace.

    “Toh Abba”.

    Kana ta fito daga bayan Naseer tashiga gaban motar.

    Kallon Gimbiya Dadu Naseer yayi kana yace.

    “Yafendo sai mun dawo”.

    Ya ida maganar tare da buɗe mazaunin Driver ya shiga kana yaja motar suka fice ahankali ya dai-dai ta hancin motarsa suka hau kwalta.

     

    Sai asannan ya juya ya kalli Khausar da fuskarta babu annuri kona misƙala zarratin zaman blutooth dake kunnensa ya gyara ajiyar zuciya ya saki yana bin ilahirin jikinta da kallo hannunsa ya kai tare da ranƙwafawa kanta zai riƙe yalwataccen sumar dake gefen wuyanta zai shinshina.

    Cikin sauri Khausar ta kauce tare da watsa masa wani kallo.

    Tsuke fuska yayi tare da marairaice murya kana yace.

    “Haba My Wife mai yasa zaki min haka kibari mana in sinsina gashinki naji wannan Sanyayyar ƙamshin da yake fita”.

    Sake tsuke fuska Khausar tayi tare da tura ƙaramin bakinta kana tace.

    “A’a nidai Yaya Naseer ka bari bana so”.

    Langwaɓar da kai yayi kana cikin wata murya mai ɗauke da zallan shauƙi da sha’awa yace.

    “Toh na bari ai yanda kike so haka za ayi hope dai kina sona?”.

    Ƙasa tayi da kanta tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta amma ba tace komai”.

    Sake narkar da muryarsa  mai ɗauke da zallan sha’awa kana yace.

    “Dan Allah kice kina ƙaunata ko zanji daɗi kinsan na daɗe ina dakon soyayyarki azuciyata, Khausar kece rayuwata bazan iya rayuwa idan babu keba kece muradin raina, kece fitilar dake haskaka rayuwata ina miki sahihiyar ƙauna wanda bana yiwa kaina”.

    Lumshe idanunsa yayi tare da kallon fuskarta zuwa ƙirjinta kana yace.

    “Kece wacce zuciyata keda burin kasancewa da   ita, kece farin cikina muddin ban mallakeki amatsayin matata ba bazan taɓa samun nutsuwa ba, My Khausi saboda ke nadawo Nigeria ba dan keba wlh bazan dawo ba.

    Duk yawan kyakkyawawan matan dake India babu wacce ta burgeni ta kuma kwanta min arai sai ke duk kyawunsu kallon maza nake musu!”.

     

    Ita dai Khausar batace komai ba sai wasa da take da yatsun hannunta.

    Naseer kuwa karyar da murya yayi tare da lashe lips ɗin sa kana yana binta da wani shu’umin kallo ya lumshe Idanunsa tare da cewa.

    “Khausar inada burin mallakar ki ke kaɗai ce zaki iya sarrafani, akan shimfiɗata sannan ke kaɗai ce zaki iya bani farin ciki akan shimfiɗa ta”.

    Lokaci ɗaya Khausar ta sake haɗe fuska cike da takaici tarasa Meyesa Naseer yake mata wasu irin maganganu marasa kan gado.

    Al’amarin Naseer yafi kama da irin mayaudaran mazan nan na zamani.

    Shirune ya ratsa motar har suka isa ƙofar gidansu Ummi yayi Parking daga waje, Ahankali Khausar ta ziro ƙafanta da suka sha jan lalle.

    Dai-dai lokacin Asma’u ta iso.

    Ganin Khausar yasa ta faɗaɗa fara’ar fuskarta kana tace.

    “A’a Khausisi, Lelewal tawa”.

    Murmushi Khausar ta sakar mata tare da gyara zaman gyalenta kana tace.

    “A’a ina kika je?”.

    Asma’u na gyara wuyan hijabinta ta kalli Khausar tare da cewa.

    “Wallahi kitso naje”.

    Jinjina kai Khausar tayi kana tace.

    “A lallai dai kam”.

    Juyawa tayi ɓangaren da Naseer ke tsaye ya zuba mata ido ɗauke kanta daga garesa tayi kana ta mayar da kanta kan Asma’u tare da cewa.

    “Asmeey ga Uncle Naseer”.

    Sai alokacin Asma’u ta ganesa da murmushi afuskarta tace.

    “Laa Uncle Naseer Mutanen India fatan kazo lafiya. Khausar tace min kadawo toh Allah yatemaka”.

    Kai ya jinjina cike da Iyayi kana yace.

    “Wallahi na dawo amma fa saboda My Khausi nazo, ana ɗaura mana aure kuma zan ɗauki abata mukoma can”.

     

    Murmushi Asma’u tayi tare da kallon Khausar da ta tsuke fuska kana tace.

    “Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairi”.

    Da sauri ya amsa da.

    “Ameen”.

    Khausar kuwa hannun Asma’u ta riƙe zasu shiga gida.

    Da sauri yace.

    “Ya dai haka My Khausar ba zaki tsaya mu ɗanyi hira ba?”.

    Ataƙaice ta girgiza masa kai tare da cewa.

    “A’a”.

     

    Shafa kansa yayi tare da lumshe idanunsa kana  yace.

    “Toh ƙarfe nawa zaki koma gida sai inzo in ɗauke ki”.

    Babu walwala atare da ita tace.

    “A’a ba sai kazo ba Uncle Naseer zan koma”.

    Wani irin zare ido yayi tare da girgiza kai kana yace.

    “A’a My Khausi kar ki min haka.

    Ni dai ki faɗa min ƙarfe nawa zanzo ɗaukarki”.

    Ƙaramin tsaki taja aranta tare da cewa wannan mutumin ya fiye naci afili kuma juyawa tayi ta kallesa tare da cewa.

    “Toh ka dawo ƙarfe shida na Yamma”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh shikenan My Wife sai nazo”.

    Ya ida maganar tare da shigewa motarsa yaja.

     

    Bayan sun shiga cikin gida Khausar ta juya tare da kallon Asma’u kana tace.

    “Ya dai naga kamar Ummi bata nan?”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa tare da cewa.

    “Eh Ummi ta tafi gidan Innayi. Ni kaɗai ce sai Bashir dana bari yana mana gadin gidan shiyasa ma ana gama min kitson na dawo.

    Jinjina kai Khausar tayi kana tace.

    “Ayyah yayi kyau”.

    Kai tsaye Bedroom din Asmau suka shiga fridge Asma’u ta buɗe ta kawo mata drinks da Fruit.

    Kallon Friut ɗin Khausar tayi tare da zabga ta gumi.

    Zama Asma’u tayi daga gefenta cike da kulawa tace.

    “Ya dai Khausar tunanin me kike?”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare cire gyalenta ta ajiye kana ta kalli Asma’u tare da cewa.

    “Ni wallahi lamarin Uncle Naseer ya fara damuna”.

    Asma’u na ninke hijabin data cire ta kalli Khausar tare da faɗin.

    “Mai yafaru?”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare da lumshe Idanunta kana tashiga zayyanewa Asma’u abubuwan daya yima tun daga zuwansa har yanzu daya kawota kana ta ɗaura da cewa.

    “Asma’u Uncle Naseer yana bani tsoro abubuwan da yake gwada min sun fi kama dana mayaudara idan yana wani abun tamkar yana da wani nufi akaina, sannan yana yawan nuna zalamarsa akaina, ya rinƙa wani abu kamar maye!”.

     

    Dariya Asma’u tayi tare da cewa.

    “Wataƙil tsanananin son da yake miki ne kike ganin kamar haka, kinga tun kina ƙarama kamar da wasa ya fara ce Miki matarsa har gashi girma yazo wataƙil tsananin soyayya ne sannan kinga ya zauna a ƙasar da al’adun mu ba ɗaya dana suba  kinga ƙasashen India wannan sai ahankali runguma da sumbata basu ɗauke shi abakin komai ba may be shiyasa kike ganin yake miki haka kuma kinga ai ya riƙa dole zaiso mace”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da furzar da iska mai zafi kana tace.

    “Anya kuwa Asma’u abin nasa is too hight ɗazun fa agaban Mommy saura kaɗan ya rungumeni saida na kauce”.

    Dafe kunci Asma’u tayi tare da kallon Khausar da fuskarta ke ɗauke da alamun damuwa kana tace.

    “Toh tunda har haka ne ki kiyaye al’amarin sa”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta saki tare da lumshe Idanunta kana tace.

    “Zan kiyaye insha Allah amma gaskiya ya fara bani tsoro baki ɗaya al’amarin sa azalamance yake”.

    Jinjina kai Asma’u tayi tare da cewa.

    “Amma duk da haka yana sonki”.

    Kai Khausar ta gyaɗa kana ta buɗe Idanunta dake lumshe tace.

    “Na sani Uncle Naseer na ƙaunata, amma kuma wani lokaci soyayyar tafi kama da Sha’awa”.

    Girgiza kai Asma’u tayi tare da cewa.

    “No Khausar kada ki fassara shi da haka, sannan kinga yanzu lokaci yayi da zaki bawa Uncle Naseer dama kinga dama ga Maganar da Hajja Nana tazo da ita cewa kina gama Secondary school za ayi batun Aurenki kinga yanzu munzo gangara koma ince mungama kawai”.

    Shiru Khausar tayi tare da lumshe Idanunta tana jin wani iri azuciyar ta.

     

    Asma’u ta cigaba da cewa.

    “Sannan kin gani tayi miki maganar Yayanki Aliyu idan har baki amince da Naseer ba kika fitar dashi amatsayin wanda kike soba dole Yaya Aliyu za’a liƙa miki, kuma kinga Yaya Naseer tunda ansan Asalin sa sannan ansan komai nasa, kuma ke kanki kinsan yana masifar sonki”.

    Ƙaramin tsaki Khausar taja tare da kallon Asma’u kana tace.

    “Kayya Asma’u Asalin nasa har wani kyau gareshi!?

    Mahaifiyarsa fa ƙanwar Gimbiya Dadu ce Uwar su ɗaya ubansa ɗaya, kuma duk ɗabi’u da hallayar Gimbiya Dadu babu wanda mahaifiyarsa ta bari, sannan kuma shine ɗan Auta wajenta Ni Wallahi tsoron su na nake ji wallahi nama fi tsoron mahaifiyarsan”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe  kana ta cigaba da cewa.

    “Amma shi Uncle Naseer bashi da matsala Saboda zuciya nason mai kyautata mata, shi kuma tun ina ƙara ma yake nunawa kowa cewa. Ni ta da bance ni ta musamman ce awajensa, na ɗaukesa ne tamkar wani sashina amma banjin Uncle Naseer awani mataki na daban sannan batun Yaya Aliyu kuwa gaskiya saidai Hajja Nana tayi duk abinda zatayi, amma ni bazan Aure shiba babu ta yanda zanyi na aureshi”.

    A hankali ta furzar da iska mai zafi daga bakinta kana ta kalli Asma’u da itama ita take kallo.

    Idanunta ta lumshe cikin sanyi murya tace.

    “Ni inaji azuciya ta ina da muradin da nake da ita na, musamman da nake buƙata inada muradin da nake so Asma’u ina da wani abun da nake so,  wanda ni kaina bansan menene ba.

    Amma Uncle Naseer ba irin Nature da nakeso ajikin namiji yake dashi ba dama yanada ilimi Addini kamar Yah Jameel ne to da ya tsarkaka, dama ace ɗabu’unsa irin na Yah Jameel ne da ya cikemib ko wanne gurbi”.

    Ajiyar zuciya Asma’u ta sauƙe kana tace.

    “Allah ko?”.

    Tayi mgnar a fili yayinda zuciyarta ke saƙa wasu zantukan, ita kuwa Khausar kai kawai ta gyaɗa mata.

    Cikin sauƙe numfashin Asma’u tace.

    “Allah ya mana zaɓi mafi alkhairi dai”.

    Cikin lumshe ida Khausar tace.

    “Amin”.

    Hira suka cigaba dayi, ƙarfe biyar dai-dai Khausar ta miƙe tare da ɗaukan gyalenta ta yafa kana ta kalli Asma’u tare da cewa.

    “Asma’u Ni zan tafi”.

    Saurin Kallonta Asma’u tayi tare da cewa.

    “Toh ba kince sai ƙarfe shida zaki tafi ba?,Kuma ina Uncle Naseer zai zo ya ɗauke ki!?”.

     

    Baki Khausar ta taɓe kana tace.

    “Guduwa zanyi kafin yazo ɗin dai, ai shiyasa nace masa shida kinga yanzu biyar zan tafi”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da cewa.

    “Toh idan yazo fa?”.

    Ka faɗa Khausar ta ɗage tare da taɓe baki kana tace.

    “Sai kice masa na tafi”.

    Ta ida maganar tana ficewa da sauri.

    Asma’u tabi bayanta dan yi mata rakiya.

     

    Misalin ƙarfe shida saura kwata Naseer yayi Parking aƙofar gidansu Asma’u tare da danna Hong.

    Asma’u dake sauraran zuwansa ta sanya hijabi ta fita zaune ta samesa acikin mota kana tace.

    “Bata daɗe da tafiya da taga iska ya taso”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Nagode”.

    Kana ya figi motarsa yabar layin kai tsaye gidansu Khausar ya nufa lokacin daya isa ankira maghariba direct masallaci ya wuce ya gabatar da sallah kana ya wuce gidan kai tsaye sashen Gimbiya Dadu ya shiga.

    Shigarsa ba daɗewa Haiydar ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama kana ya gaishesu tare da ajiye kulan abincin Gimbiya Dadu.

    Har ya juya zai fita.

    Naseer ya kallesa tare da cewa.

    “Please Haiydar kace da Khausi tazo zamuyi hira”.

    Kai Haiydar ya gyaɗa kana yace.

    “Toh Uncle Naseer sannan ya fita”.

    Kai tsaye masallaci ya wuce sai Misalin takwas saura kwata ya koma sashen su bakinsa ɗauke da Sallama.

     

    Khausar dake zaune kan 1sitter sanye cikin Neavy blue riga da wando na bacci mai santsi wanda ya sauƙa har ƙasa rigar kuma mai hannun Spaghetti ne kanta sanye da hular Net jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshin tularen ta yayin da hannunta ke riƙe da wayar Mommy tana latsawa.

    Da sauri Haiydar ya kalleta tare da cewa.

    “Addah Khausar na manta ban faɗa miki ba, ɗazu kafin na wuce Masallaci Uncle Naseer yace. In faɗa miki kije ki same shi a sashen Gimbiya Dadu yana son ganinki”.

    Nanda nan Khausar ta canza fuska tare da cewa.

    “A falon Gimbiya Dadu kuma!?”.

    Harara Mommy ta watsa mata kana tace.

    “Toh cin yeki Gimbiya Dadu za tayi ko kuma me Ni nalura wani shan ƙamshi kike yiwa Naseer fa, idan kinsan bakya sonshi ki fito fili ki faɗa, sannan ki fito da wanda kike so, tun kafin kakar ki tazo ta buwayemu da batun Aurenki.

    Kinga dama ta ajiye target ne kina gama Secondary school magana ya ƙare za azo ayi miki aure”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙa kana ta cigaba da cewa.

    “Idan kuma kinƙi baki da hujjar da zaki ƙi Auren Aliyu, dole kibi zaɓin ta dan haka ma gwara ki tsaida zuciyarki kisan me kike ciki don in duniya duk zasu taru babu mahluƙin da zai hana batun wai kin gama secondary School za’ayi miki aure, tunda har Hajja Nana ta rantse, dan haka gwara kawai ma ki tsaida zuciyarki, ki fidda mijin da zai iya barinki kici gaba koda kinyi aure, kuma da fidda wanda kike sone, zamu samu hujjar nuna mata kinada wanda kike son”.

     

    A hankali Khausar ta janye idonta daga kallon Mommy kana tace.

    “To amma ni gaskiya ba zanje.

    Falon Gimbiya Dadu ba”.

    Ɓata fuska Mommy tayi babu walwala atare da ita tace.

    “Maza ki wuce kije idan ita kura ce to ta cinye ki”.

    Miƙewa Khausar tayi badan ranta yaso ba sai dan ganin yanda Mommy ta ɓata rai yasa ta ɗauki hijabinta dake fitar da ƙamshi sanya kana ta fice.

     

    Acan ɓangaren su Moddibo kuwa zaune suke aɗakin Innayi shi da M Jameel bayan sun kammala cin abinci Anutse ya miƙe tare da kallon Innayi da suke magana da M Jameel ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.

    “Innayi saida safe”.

    Kallon sa M Jameel da mamaki afuskarsa yace.

    “Zaka je ka kwanta fa kace?”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa tare da lumshe idanunsa kana yace.

    “Eh”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da faɗin.

    “Ok nima zan tafi gida”.

    Ahankali Moddibo ya buɗe Idanunsa dake lunshe kana yace.

    “Mu kwana anan mana tunda har ƙarfe takwas tayi”.

    Girgiza kai M Jameel yayi tare da miƙewa kana yace.

    “A’a ina so Inje gida”.

    Kallon yanayin fuskarsa Moddibo yayi tare da cewa.

    “Dan Allah mu kwana mana”.

    Ataƙaice M Jameel yace.

    “A’a tafiya zanyi”.

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauke tare da cewa.

    “Toh shikenan ni zanje in kwanta”.

    Ya Ida maganar tare da ficewa.

    Da kallo Innayi da M Jameel suka bisa har ya ɓacewa Kallonsu.

    Moddibo kuwa yana shiga falonsa yayi saurin yarfe hannunsa tare da jan tsaki  tare da jan numfashi kamar wanda yaci yaji lokaci ɗaya lips ɗin sa suka kama rawa cikin yanayin damuwa ya dafe kansa tare da cewa.

    “Ya salam³,Wannan wani irin al’amari ne meke mai wuyar ɗauka haka?”.

    Cikin mutuwar jiki ya wuce kichen tare da ɗaukan Cup ya ɗauraye ya zuba ruwan Tea kana ya yanka lemun tsami ya matse sannan ya zuba zuma ya kafa kansa ya shanye tass, ajiye Cup ɗin yayi ya fita zuwa Bedroom ɗin sa yana shiga ya kwanta ko minti ɗaya baiyi da kwanciya ba yayi saurin miƙewa ya zauna cikin sauri ya sake komawa ya kwanta tare dayin ruf da ciki cikin wani irin yanayi yasanya hannunsa duka biyu ya danne mararsa saboda wani masifaffen harbawa da yakeyi.

     

    Acan ɓangaren Gimbiya Dadu kuwa cikin sanyi jiki Khausar ta buɗe ƙofar falon tare da Sallama tana shiga ta…!

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki littafin 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, kana in saki a Group ɗin da zanke posting nashi, yar uwa koda kinga LITTAFIN SAKAYYAH A WAJE TO na satane, in dai kin san baki biya kadama ki karanta.*

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

    *By*

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 13

    Sakayyah 13

     

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 13_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama, ba haƙƙin kowa akanki. Littafin 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ɗin littafin inda zan rinƙa posting.

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

     

    Khausar kuwa cikin tsare Hajja Nana da ido ta riƙe ƙugu tare da cewa.

    “Gaskiya nikam bana son irin wannan mulkin mallakar naki”.

    Da sauri Mommy ta ɗaga mata hannu fuskarta babu walwala ta kalli Khausar kana tace.

    “Kifita, daga nan Khausar!”.

    Lokaci daya fara’ar data shigo da shi ya gushe  ɓacin rai ya mamaye mata zuciya juyawa tayi ta fice daga Bedroom ɗin Mommy ta nufi nata tana shiga Bedroom ɗin ta jiyo  Muryan Asma’u afalo.

    Kai tsaye Bedroom ɗin Khausar Asma’u ta shiga tare da cewa.

    “Assalamu Alaikum”.

    Atare Dije da Khausar suka amsa da.

    “Wa’alaikum Salam”.

    Asma’u naganin fuskar Khausar ta ware Ido kana tace.

    “Ya dai mutuniyar naga fuskarki haka?”.

    Wani abu mai masifar ɗaci Khausar ta haɗiye Idanunta akan Asma’u dake tsaye ta gyara zamanta tare da faɗin.

    “Babu komai ƙara so ki zauna”.

     

    Zama Asma’u tayi tare da tsare Khausar da ido ganin yanayin damuwa atare da ita.

    Kallon Dije Khausar tayi sai kuma ta juya ta kalli Asma’u tare da faɗin.

    “Wannan Itace Dije”.

    Murmushi Asma’u tayi Idanunta akan Dije ta ajiye Handbag din dake hannunta kana tace.

    “Sannunki”.

    Murmushi Dije tayi tare da faɗin.

    “Yawwa”.

     

    Juyawa Asma’u tayi tare da kallon Khausar kana tace.

    “Khausar wacece ban ganeta ba”.

    Muskutawa Khausar tayi tare da gyara zamanta kana tace.

    “Dije ce wacce nake baki labarin ta a Jauro Yaya”.

    Jinjina kai Asma’u tayi tare da faɗin.

    “Ohh Ayyah na tuna ta itace tazo ita da Hajja Nana suka zone?”.

     

    Khausar kuwa kai ta gyaɗa mata kana tace.

    “Eh”

    Murmushi tayi tare da faɗin.

    “Ai lallai dai kam kice muna da manyan baƙi Dije amma zamu daɗe ko?”.

    Kai ta girgiza tare da yin murmushi kana tace.

    “A’a yau zamu koma ”.

    Ware ido Asma’u tayi tare da faɗin.

    “A’a yau zaku koma kuma?”.

    Sai kuma Asma’u ta juya ta kalli Dije kana tace.

    “Shaf-shaf haka?”.

    Ita dai Khausar na gefe ta jingina bayanta da jikin gado Idanunta alumshe tana tunanin maganar Hajja Nana.

    Kai Dije ta gyaɗa tare da faɗin.

    “Eh ai da Yaya Aliyu muka zo”.

    Murmushi Asma’u tayi kana tace.

    “Ayyah ai kam munji daɗin ganinki”.

     

    Asma’u kuwa juyawa tayi tare da kallon Khausar wacce ta tsirawa waje ɗaya Idanu cike da kulawa Asma’u ta dafa kafaɗar ta kana tace.

    “Wai Meye ne kike ta haɗa rai!?”.

    Iska mai zafi ta furzar tare da kallon Asma’u fuskarta babu walwala ta saki Ajiyar zuciya kana tace.

    “Kina ji wata magana da wannan tsohuwar tazo dashi wai batun Aurena!kuji min tsohuwar nan da wani iyayi ta bari Iyayena suyi magana akai na mana ita kuma kaka wake maganarta!?”.

     

    Asma’u kuwa Dariya mai sauti tayi tare da cewa.

    “Iyeeee kice zamu sha bidiri!”.

    Dije tayi murmushi kana tace.

    “Barta dai kuma ma kinga mijin data samun ne kyakkyawa fa?”.

    Baki Khausar ta kuma taɓewa tare da wurga musu Harara kana tace.

    “Toni ina ruwana dashi?,

    Ni bana so kada ma ayimin wannan maganar tsakani da Allah shi yafara Auren yayata fa Asma’u”.

    Da sauri Asma’u ta ɗago kanta tare da cewa.

    “Addarki kuma?, Dama ba kece ƴar farin Mommy ba?”.

    Jinjina mata kai Dije tayi tare da cewa.

    “Eh ba ita bace ƴar fari Akwai Addarta Nenne Amma ta rasu kuma itama Yayanta Aliyu aka aura mata sunyi aure da shekara biyu ta samu ciki tazo wajen haihuwa ta rasu!”.

    Asma’u ta jinjina kai tare da cewa.

    “Allah sarki Allah ya gafarta mata,.

    Ohh Ashe shiyasa Mommy bata kunyar kiran sunanki nida duk atunanina kece ƴar fari har nace Mommy ƴar zamani ce bata ɓoye sunan ki”.

     

    Kai Khausar ta girgiza kana tace.

    “A’a ba nice ƴar fari ba ni ta biyu ce”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da faɗin.

    “Ohhh lalle kam kice zamu sha biki”.

    Khausar kuwa fuska ta tsuke kana tace.

    “Zaku sha bikin waye?”.

    Dariya Asma’u tayi tare da cewa.

    “Bikin ki mana”.

    Cikin haɗe rai Khausar  kai ta girgiza tare da faɗin.

    “Asma’u kiyi min fatan alkhairi mana, kina jin tsohuwar nan da shiririta da shirme wai ko bayan sallah za ayi ko menene oho?”.

    Dije kam kai ta girgiza tare da cewa.

    “Bafa cewa tayi bayan sallah ba ita dai alissafinta ki gama karatunki sai anyi idan yaso in kinaso kici gaba da karatunki sai Yaya Ali ya saki ki cigaba dayi a Adamawa bayan sallan baɗi take nufi”.

     

    Fuska Khausar ta ya mutse kana tace.

    “Aima Allah ya kiyaye abar mutum yayi karatunsa mai zurfi mana sannan ai mutum nada tsarin rayuwarsu da kuma yanda yake so ya kasance haka kawai sai atakura min”.

    Dariya Asma’u tayi tare da cewa.

    “Mu dai kar ki mana baƙin ciki ki hana mu shan biki”.

    Harara Khausar ta maka mata kana tace.

    “Ai sai kuyi shagalin ku kuka ɗai”.

    Dije na dariya ta dubi Khausar kana tace.

    “Yo ina zamuyi shagali ba Amarya ai dan ke za’ayi”.

    Baki Khausar ta taɓe kana tace.

    “Ai lalle dai kam”.

     

    Mommy ce tashiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama kallon Asma’u tayi kana tace.

    “A’a Asma’u kece yaushe kika zo”.

    Asma’u kuwa zamewa tayi daga kan gadon tare da cewa.

    “Ban daɗe da zuwa ba Mommy Ina yini?”.

    Mommy ta amsa da.

    “Lafiya lau alhamdulillah yasu Umminki?”.

    Miƙewa Asma’u tayi tare da zama agefen gadon kana tace.

    “Tace agaisheki”.

    Masha Allah Mommy ta faɗa tare da maida kallonta kan Dije kana tace.

    “Dije kizo Hajja Nana na kiranki wai zaki rakata gidan Aminiyarta”.

    Ta ida maganar tare da juyawa ta fice.

    Miƙewa Dije tayi tare da kallon Khausar kana tace.

    “Khausar mu tafi mana”.

    Fuska Khausar taya mutse kana tace.

    “A’a kuje kawai Allah ya kiyaye hanya ni bazan jeba, muyita faɗa da ita a gidan  mutane muna raba hali agidan mutane duk inda mukaje sai ansan mu”.

    Murmushi Dije tayi tare da faɗin.

    “Toh shikenan mun tafi”.

    Sannan ta fice kai tsaye ɗakin Mommy ta wuce sannan ta samu Hajja Nana atsaye.

    Hajja Nana na kallonta tace.

    “Wuce ki kira su Aliyu mu tafi”.

    Kai Dije ta gyaɗa sannan ta fice.

    Mommy kuwa Jakar data haɗa wa Hajja Nana tsaraba ta ɗauka sannan ta fice.

    A coumpund ɗin ta samu Yaya Aliyu da Yaya Abba tsaye jikin mota cike da girmamawa da kuma ladabi Ya Aliyu ya kalli Mommy tare da cewa.

    “Toh Mommy mun gode Allah ya saka da alkhairi Allah yabar zumunci”.

    Murmushi Mommy tayi tare da cewa.

    “Amin, Allah ya tsare muku hanya”.

    Hajja Nana ta amsa da.

    “Ameen”.

    Tare da buɗe bayan motar tashiga Dije ta zauna agefenta Yaya Aliyu na gefen mai zaman banza Yah Abba kuwa shike Driving suka fice daga gidan.

    Sai da Mommy taga fitar su sannan ta koma cikin gida.

     

    Yaya Abba kuwa kai tsaye gidan su Moddibo ya nufa.

    Hajja Nana nayi masa kwatance har suka isa gida suna shiga gidan.

    Cikin sauri Yaya Ali ya lumshe Idanunsa kana yace.

    “Masha Allah wlh Ina son garin Gembulan nan saboda yana da kyawun tsari dan yafi Adamawa kyawun tsari da komai akwai yanayin sanyi da daɗi”.

    Jinjina kai Yaya Abba yayi yace.

    “Aikam sosai ma”.

    Yaya Ali ya juya tare da kallon Hajja Nana kana yace.

    “Hajja Nana wannan kuma gidan  wacece ɗinkin ne?”.

     

    Murmushi Hajja Nana tayi alokacin da take sauƙa amotar ta kalli Ali kana tace.

    “Ƙawata ce tare mukaje da ita aikin hajji na farko na biyu ma tare muka je sannan ko daga baya muna yawan zuwa   Umarah tare da ita”.

    Murmushi Yaya Ali yayi tare da cewa.

    “Ai dai lalle kam kice gidan Aminiyar kice?”.

     

    Dariya Hajja Nana tayi tare da cewa.

    “A’a sosai ma kam”.

    Dai-dai lokacin da suka isa ƙaramin gate ɗin da zai sadaka da farfajiyar tsakar gidan Innayi.

    Innayi dake zaune ta hango Hajja Nana da baƙi abayanta,

    Cike da fara’a ta miƙe da sauri fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi mai cike da jin daɗi ta matso kusa da Hajja Nana kana tace.

    “Aaaa Lalle marhaba Hajjaju Makkatun Masha Allah Hajiya Nana mutanen Makka lale marhaba ku iso”.

    Ta faɗa tare da juyawa ta shiga ɗaki tare da ɗaukan lallausan Chanis capet ta shimfiɗa musu.

     

    Sai kuma ta fito cike da farin cikin daya kasa ɓoyuwa afuskarta kallon Yaya Ali tayi tare da cewa.

    “Wannan shine  Mijin namu na Adamawa da kike bamu labarin?”.

    Kai Hajja Nana ta gyaɗa tana murmushi kana tace.

    “Eh”.

    Innayi ta juya ta kalli Hajja Nana kana tace.

    “Ku shiga”.

    Sannan ta kalli Yaya Abba da Yaya Ali kana tace.

    “Ku ƙara so”.

    Ta faɗa tare da ficewa Innayi ta nufi sashen Moddibo tare da cewa.

    “Moddibo, Moddibo ga baƙi munyi”

    Shi kuwa Moddibo atare suka miƙe da M Jameel suka fito.

    Ɗan sake fuska Moddibo yayi kana yace.

    “Sannunku da zuwa ku iso”.

    ya faɗa tare da matsa musu.

     

    M Jameel na ganin Yaya Abba ya miƙa masa hannu fuskarsa ɗauke da murmushi kana yace.

    “Ha’a Abba kaine?”.

    Murmushi Yaya Abba yayi kana yace.

    “Ni ne dai”.

    M Jameel yayi dariya kana yace.

    “Sannu ku da zuwa”.

     

    Yaya Abba na bin bayansu yace.

    “Laaa Jameel nan gidan kune?”.

    M Jameel yayi Murmushi tare da shafa sajensa ya kalli Yaya Abba tare da faɗin.

    “Eh gidan mune!”

    Murmushi Yaya Abba yayi da faɗin.

    “Masha Allah”.

    sannan suka shiga falon din wanda tuni Ya Ali da Moddibo suka shiga.

     

    Innayi dake tsaye ta juya tare da cewa.

    “Moddibo zoka kawo musu abin taɓa wa”.

    Daga ciki Moddibo ya miƙe kana yace.

    “Toh Innayi”.

    Sannan ya fice tare da bin bayanta.

    Juyawa Innayi tayi tare da kallon Moddibo dake biye da ita kana tace.

    “Kashiga daga ciki ka gaida ƙawata Hajja Nana dana ke ce maka munje aikin Hajji na farko dana  biyu kuma yawanci Umarah ma tare muke zuwa ɗakin mu ɗaya tun da take zuwa gidan nan bata taɓa samunkaba,

    Kai ya gyaɗa da faɗin.

    “Na’am”.Ya ida maganar tare da shiga ɗakin bakinsa ɗauke da sallama Idanunsa ya sauƙa akan tsohuwar da yaje ya yamata ta’aziyya a Jauro Yaya.

    Cike da nutsuwa da kuma ladabi ya zauna daga gefenta kana yasa hannu ya shafa sajensa cikin yanayin rashin walwalarsa yayi ƙasa da kansa tare da cewa.

    “Sannun da zuwa”,Ya gaisheta batare daya nuna ya ganeta ba.

     

    Hajja Nana kuwa Kallonsa tayi kana tace.

    “A’a kamar nasan wannan fuskarta fa, kwanaki kamar kunje da wani abokin Malam Liman mai suna Malam Arɗo ko?”.

    Kai Moddibo ya jinjina still Kansa a ƙasa kana yace.

    “Eh”.

    Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.

    “Ayyah sannun ka ashe dai Jikana ne Allah yayiwa rayuwarka albarka Allah yabaka zuri’a ɗayyiban”.

    Still Kansa A ƙasa ya shafa kwantaccen sumar  kansa mai sheƙi da yalƙi kana yace.

    “Ameen Ngd”.

    Ya ida maganar  a taƙaice tare da miƙewa ya fice.

    Tiren da Innayi ta haɗa Gasassun Zabbi da  M jameel yasa ta gasa musu, shinkafa da miyar dage-dage da yaji naman kaza sai Akwashi dake ɗauke da ƴaƴan itatuwa ta miƙawa Moddibo amsa yayi kana ya nufi sashen sa dashi.

     

    Bakinsa ɗauke da Sallama yashiga tare da ajiye Tiren akan center table dake tsakiyar falon kana ya maida kallonsa kan M Jameel dake ta hiran Yaushe gamo da Yaya Abba kai ya girgiza tare da cewa.

    “J miƙo musu ruwa acikin fridge ka barsu haka gashi har na dawo baka kawo musu komai ba”.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “Wallahi muna ta hiran yaushe gamo da Abba nasan sa mun taɓa haɗuwa dashi a Adamawa”.

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da jingina bayansa da jikin kushin kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.

    “Ayyah ashe kunsan juna”.

    Kai Yaya Abba ya gyaɗa alamar Eh.

    Ya Ali kuwa hankalin sa ya mayar kan wayarsa yana latsawa.

     

    Acan ɗakin Innayi kuwa zama Innayi tayu tare da kallon Hajja Nana kana tace.

    “Yanzu ma kinzo wajen jikar tamu ce?”.

    Kai Hajja Nana ta gyaɗa kana tace.

    “Eh wallahi”.

    Murmushi Innayi tayi tare da cewa.

    “Shine baki zomin da ita ba”.

    Baki Hajja Nana ta taɓe tare da faɗin.

    “Barta ba shiri muke da ita ba fitsararriya ce yanzu ma nazo ne akan batun aurenta da yayan ta amma na lura ma kamar batason abin ko yayane ohon mata kinsan ƴaƴan yanzu da tsaurin ido su suke zaɓawa kansu maza yanzu ma na barta tana can tana kumbure kumburen baki”.

    Murmushi Dije da ke kurɓan tes tayi aranta tace Dramer Hajja Nana da Khausar bai ƙarewa.

     

    Innayi kuwa murmushi tayi kana tace.

    “Ayyah ai da tazo na ganta kice mu shirya akwai shan biki?”.

    Dariya Hajja Nana tayi kana tace.

    “Ai dai kam Insha Allah akwai shan biki dan biki yana nan yana tafe”.

    Innayi kuwa kai ta gyaɗa kana tace.

    “Lallai abu yayi kyau amma dai zamu kwana”.

    Girgiza kai Hajja Nana tayi kana tace.

    “A’a yanzu ma zamu tafi dan mun sallami can kam da zan tafi da jikar tawa ma to sai mahaifiyata take ce min bata da lafiya don haka na barta saboda tana taimakawa mahaifiyar tan da ɗan aikace-aikacen yau da kullum”.

     

    Kai Innayi ta jinjina tare da faɗin.

    “Ayyah Allah yabata lafiya.

    Yaushe zamu koma Umarah bana zaki je na Ramadan?”.

    Hajja Nana kuwa kai ta jinjina kana tace.

    “Eh Insha Allahu zanje in Allah ya yarda amman ta Adamawa zan tashi kefa zakije kuwa?”.

    Murmushi Innayi tayi tare da cewa.

    “Nima zanje in Allah ya yarda amman kin san ni ta nan Jaligo zan tashi”.

    Kai Hajja Nana ta gyaɗa tare da faɗin.

    “Abu yayi kyau Ubangiji Allah yasanya alkhairi Allah ya bamu sa’a”.

     

    Innayi ta amsa da.

    “Ameen”,kana ta cigaba da cewa.

    “Nima zamu tafi da jikina da kuma abokinsa tare za muje”.

    Dariya Hajja Nana tayi kana tace.

    “A’a abu yayi kyau to sai mun haɗu acan ɗin”.

    Hiran yaushe gamu suka cigaba dayi yayin da Dije ke gefe tana yagar Gashesh-shen Zabbi da nonon shanu mai ɗumi.

     

    Acan falon Moddibo kuwa bayan sun gama gaisawa Yaya Abba da Yaya Ali suka sha fruit din kana suka ci gashshen Naman  dake fitar da ƙamshi tare da ruwan Tea mai zafi.

    M Jameel ya kalli Yaya Abba daya koma ya zauna tare da rufe Warmers din Cike da kulawa ya sake Kallonsa kana yace.

    “Abba ya bakuci abincin ba”.

    Murmushi Yaya Abba yayi kana yace.

    “Wallahi aƙoshe muke yanzu ma dan kar kuce munƙi cin komai ne amma Alhamdulillah”.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “Toh shikenan”.

    Miƙewa sukayi Atare jin Innayi na cewa.

    “Moddibo kufita Hajja Nana zasu wuce”.

    Da to Moddibo ya amsa kana suka fita cike da kulawa M Jameel da Moddibo suka kalli yaya Abba da yaya Ali atare suka haɗa baki wajen faɗin.

    “Toh mun gode da ziyara Allah yabar zumunci”.

    Yaya Ali ya amsa da.

    “Ameen”.

    Sannan Yaya Abba yashiga mazaunin Driver Yaya Ali kuma ya zauna gefen mai zaman Banza yayin da Hajja Nana da Dije suka zauna abaya M Jameel ya miƙa kansa ta window tare da ajiye wa Hajja Nana kuɗi akan cinyarta tare da cewa.

    “Allah ya tsare”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Allah ya muku albarka nagode”.

    Motar Yaya Abba yaja suka fice saida motar ta fita layinsu kafin Innayi, Moddibo,da kuma M Jameel suka koma cikin gida.

     

    Cikin awa biyu Hajja Nana suka isa Jauro Yaya Washe gari Da safe yaya Ali ya koma Adamawa dashi da Abba suka tafi.

     

    A ɓangaren Khausar kuwa tunda daga ranan da Hajja Nana tayi mata maganar aure ta watsar da maganar kasancewar Momynta bata sake yi mata maganar ba ita ma bata sake tada maganar ba hakan yasa bata ɗauki maganar da muhimmanci ba ita kuwa Mommy tasa aranta tun daga Ramadan ya kawo kai ta samu dama ta yanda zata roƙowa ƴar ta al’khairi idan har Aliyu al’khairi ne agareta Allah ya tabbatar mata da al’khairi idan kuma ba al’khairi bane Allah ya zaɓa mata mafi al’khairi shima kuma Allah ya musanya masa da mafi al’khairi.

     

    Yau ya rage azumi saura kwana biyu da hantsi Mommy na zaune afalo taji Sallamar sabon mai gadinsu da aka kawo kallon Khausar dake riƙe da hisnul Muslim tana Azkhar tayi sai kuma ta maida kallonta ga Haiydar dake danna wayarta ta gyara zamanta tare da cewa.

    “Haidar jeka duba lafiya Namadi ke Sallama”.

    Kai Haiydar ya gyaɗa kana yace.

    “Toh Mommy”.

    Sannan ya miƙe ya fita.

    Kallon Namadi dake tsaye yayi kana yace.

    “Lafiya kuwa”.

    Kai Namadi ya gyaɗa tare da faɗin.

    “Kayane Alhaji ya aiko dasu Azo ashiga dashi ciki”.

    “Ok kashigo dasu”. Ya faɗa tare da juyawa ya koma ciki.

     

    Kallon Mommy Haiydar yayi kana yace.

    “Kayan azumine Abbah ya aiko dasu shine Namadi zai shigo dasu”.

    Jinjina kai Mommy tayi tare da cewa.

    “Ok”.

    Da Sallama Namadi yashigo kansa ɗauke da buhun shin kafa ya ajiye a store kana ya koma ya ɗauko na ɗanyen shinka yakai, sannan ya kuma kimawa ya rinƙa shigo da catton ɗin indomie, Catoon ɗin Spaghetti, Cotton ɗin Macoroni, Couscous, Buhun fulawa, Buhun niƙeƙƙen garin gero na kunu, buhun wake, buhun sugar Corn Flakes, Madara, Patoto, Doya Crate din ƙwoyi Jarkan mai Jarkan man ja haka ya riƙa shigowa da tarkacen kayan buƙata na Ramadan.

     

    Kamar yanda ya kawo sashen su Khausar haka ya kai sashen Hajiya Bunayya.

     

    Yayinda hakan take a kowani gida haka magidanta suka riƙa shiga da kayan azumi domin shiryawa wannan wata mai falala.

     

    Acan ɓangaren gidansu Moddibo kuwa shida M Jameel amota Moddibo ke driving yayin da M Jameel ke gefen mai zaman banza sai kuma wani yaro daga baya mai suna Iro wanda ke musu aika hong sukayi aƙofar gidansu Moddibo kana suka shiga cikin gidan bayan Iro ya fita ya buɗe musu.

    Innayi na zaune atsakar gida akan kujera ƴar tsugunno taji ƙaran mota na shiga cikin harabar gidan aranta tace yau lafiya Moddibo ke shigowa da mota har cikin gidan.

    Moddibo kuwa  kusa da Innayi yayi Parking motar tare da buɗe Murfin motar ya zira ƙafarsa ɗaya awaje ɗaya kuma na ciki M Jameel da Sadik kuma suka fita kusa da Innayi M Jameel ya zauna shi kuwa Sadik Boot ɗin motar ya buɗe tare da fito da buhun far n gero,  Buhun wake, Buhun shinkafa ɗanye da gumi, Catoon ɗin indomie, Catoon, Spaghetti, Bushesh-shen kifi crate ɗin ƙwoyi, Gongwanaye mayen madara da Vournvita buhun, Sugar kwalin Lipton sai kuma naman rago da aka gyara gaba ɗaya ga kuma na shanu ga kifaye duk Sadik yasa su a fridge

     

    Kallon Moddibo Innayi tayi sai kuma ta maida kallonta kan M Jameel dake kusa da ita tayi tare da cewa.

    “Lalle kayan Azumi sun saƙƙo ga Azumi sai ƙaratowa yake yau saura kwana biyu ko uku”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.

    “Ai dai kam Innayi azumi yazo”.

    Ya ida maganar tare dasa hannu acikin aljihunsa ya ciro Bandir ɗin kuɗi kimanin dubu ɗari ya miƙawa Innayi tare da faɗin.

    “Innayi gashi babu yanda banyi da Moddibo ba yabarni in saya miki kayan Azumi amma dake ɗan baƙin haline baya so in samu lada yaƙi furrr yace komai shi zai siya gashi wannan ki riƙe kiyi yadda kika ga dama dasu”.

     

    Kallon kuɗin Innayi tare da Girgiza kai kana tace.

    “Ayyah Jameel am bana son wannan shungullan yanzu ni kuma me zanyi da wannan kuɗin kabar su Jameel am ni ba ɓuƙatar su nake ba”.

     

    M Jameel kuwa zama ya gyara tare da fuskantar Innayi da kyau kana cikin wata raunan’niyar Murya ya lumshe idanunsa tare da cewa.

    “Tunda muke tare daku tsawon shekaru Innayi daga ke har Moddibo ban taɓa ɗaukar abu in baku ku karɓa ba, duk abinda na baku sai kun mayar min dashi baya, ban sani ba wataƙil shi Moddibo yana ɗaukar Maganar Aunty Karima keyi amatsayin matakin ƙin karɓan abu awajena”.

    Lumshe idanu Moddibo yayi tare da jingina kansa da Murfin motar yana sauraron abinda aminsa ke faɗa.

    Ita kuwa Innayi idanu ta zuba masa tana nazarin kalamansa.

     

    M Jameel ya cigaba da cewa.

    “Abinda Moddibo bai saniba koya karɓi abu awajena ko karya karɓa ita gani take komai na rayuwarsa Ni nake masa dan haka gwara ma ya karɓa idan yaso ta tuhumesa da tushe”.

    Ya furzar da iska mai zafi kana ya cigaba da cewa.

    “Kema kuma Innayi ina ganin maganar mutane kike ɗauka da suke cewa Babana ke daukar ɗawainiyar ku amma ni nasan ba haka bane. Allah ne kaɗai ya barwa kansa sanin yanda kuke rayuwarku duk da aminantakar dake tsakani na da Moddibo har yau ɗin nan bansan taya kuke mu’amala da rayuwarku ba bansan ta yanda kuke samun abinda kuke biyan buƙatar rayuwarku ba kama daga karatun Moddibo kab babu aƙaramar makaranta zuwa hidimar fitanmu Makarantar waje ina sane ina kuma tunawa Naira biyar kun ƙi karɓan tallafi awajen Babana ku keyin komai abinda yasa mutanen gari suke ɗaukar haka suna lura da Moddibo ba wani sana’a yake ba sannan ana mamakin irin buƙatun da kuke yafi ƙarfin samun ku ko kuma tattalin ku Innayi!”.

     

    Dariya mara sauti Innayi tayi tare da jinjina kai kana ta tsaida idanunta akan Moddibo daya dafe kansa sai kuma ta kalli M Jameel daya dafe kansa tayi murmushi tare da cewa.

    “Abun aduhu ne Jamilu barshi kawai babu ɓuƙatar sai ansani,  shi kansa Moddibo bai san komai akan al’amuran rayuwar nan ba bare ya gaya maka”.

    Moddibo kuwa Sanyayyar Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da kallon M Jameel ya buɗe masa hannunsa alamar kaji dai  nima bansan komai ba a cikin abubuwan da kake son sani.

    Sai kuma Moddibo ya numfasa tare da lumshe Idanunsa kana cikin sanyin murya mai cike da rauni ya kalli Innayi tare da cewa.

    “Kagani ni kaina ban san komai  ba kama daga lokacin dana ke karatu.

    Ni dai nasan tana min komai idan nayi magana sai tace gadon Iyayena da suka bar min ne, bansan inda ta ɓoye kuɗin ba na girma ma yanzu ta bani gadona ahannuna taƙi ko gani take har yanzu ban kai ba oho.

    Kai kuma kana tuhumata kamar acikin aminantakar mu akwai abinda nake ɓoye maka, bayan kuma J ka sani babu wani shamaƙi tsakaninmu”.

    Ya ƙarisa mgnar tare da

    runtse idanunsa a take kuma ya  buɗe su akan M Jameel da shima shi yake kallo, a hankali ya furzar da iska mai sanyi tare da cewa.

    “J ba’ayi wani abu na duniya da ni Aliyu zan iya ɓoye maka ba, aminantakar mu ta wuce babin in ɓoye maka wani abu”.

    Jinjina kai M Jameel yayi yana kallon amininsa cike da tausayawa.

     

    Innayi kuwa murmushi tayi tare da jinjina kai amma ba tace komaiba ba.

    Moddibo kuwa kallon Innayi yayi kana yace.

    “Yanzu kuma hidimar da nake kai kan ka kasan inda nake samu tunda muna aiki kuma ana biyan mu sannan kuma. Ni kaina wataran saidai inga tayi min abu misali yanzu mota dai ni bansa araina ba kafin in ankara har ta saya anyi komai kafin ma mu dawo”.

    Numfashi ya sauke  kana ya cigaba da cewa.

    “Babu yanda banyi da ita ta faɗa min ba idan ma a kuɗin gado nane tunda na girma ta bani abuna zan iya sarrafawa”.

    Hararansa Innayi tayi kana tace.

    “Anƙi abaka”.

    Shiru M Jameel da Moddibo kai ya jinjina ba tare da tace komai ba sai tsirawa Innayi ido da sukayi.

    Miƙewa M Jameel yayi yace.

    “Bari mu tafi Innayi”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Allah ya tsare”

    Suka amsa da.

    Amin

    Shi kuwa Moddibo Kallon Innayi  yayi kana yace.

    “Innayi har yanzu yarinyar nan bata zoba?”

    Jinjina kai Innayi tayi tare da cewa.

    “Dama wannan shekarar Ummin Asma’u tace in bari zata turo min Asma’u dan ƴaƴan ƙabilun in sun zo gaba ɗaya lalata sukeyi sannan basajin magana to Asma’u zata zo ta tayani”.

    Cikin kula ya kalli  Innayi  kana yace.

    “Innayi anya Asma’u zata iya ayyukan da suna da yawa fa kinga akwai abincin da za’a dinga fitarwa na masallaci”.

    Jinjina kai Innayi tayi kana tace.

    “Zamu iya ai naga Asma’u tana da kuzari kuma nima da kuzarina da kuma lafiyata zan iya”.

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Toh Allah ya temaka”.

    Ta amsa da.

    “Ameen”,Kana tace.

    “Ai girkin ma na iya tsawon kwana goma sha biyar ne zamuyi”.

    Kai M Jameel ya Jinjina kana yace.

    ”Eh haka ne Innayi”.

    Sallama suka mata sannan M Jameel ya Miƙe.

    Dama already Moddibo na cikin motar yaja suka tafi.

     

    Kai tsaye kasuwa Moddibo ya sake nufa Kallonsa M Jameel yayi kana yace.

    “Mai zamu kuma yi a kasuwa?”.

    Ba tare da Moddibo ya juya ya kallesa ba ya lumshe idanunsa kana yace.

    “Idan muka je za kaga ni”.

    Shiru M Jameel yayi har suka isa kasuwar kamar yanda Moddibo yayiwa Innayi siyayya haka ya sake sayan wasu Kallonsa M Jameel yayi tare da cewa.

    “Wannan kayan na waye haka?”.

    Anutse Moddibo yace.

    “Ina ruwanka”.

    Daga haka yaja motar suka fita kai tsaye hanyar gidan Ummi ya nufa.

    Da sauri M Jameel ya juya ya kallesa kana yace.

    “Ai baka isa ba Ummi ba zata karba ba ai kai ma idan zan kaiwa Innayi abu hana wa kakeyi”.

    Moddibo kuwa baki ya taɓe kana yace.

    “Ai ba Umminka kai ka ɗai bane harda ni dan haka kabarni in  samu lada”.

    Murmushi M Jameel yayi Amma baice komaiba.

     

     

    Koda suka isa aka shigar da kaya, M Jameel yayi wa Ummu bayanin yadda sukayi.

    Ita kam Ummi sai ta riƙa sakin murmushi bayan ta gama jin jawabin M Jameel sai kuma ta kalli uban kayan da aka shigo dasu ta juya ta kalli Moddibo daya tanƙwashe ƙafafunsa tare da sunkuyar da kansa ƙasa tayi murmushi fuskarta ɗauke da murmushi cike da ƙaunarsu ta saki ajiyar zuciya kana tace.

    “Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwar ku Ubangiji Allah ya baku ƴaƴan da zasuyi muku biyayya fiye da yanda kuke mana”.

    Atare suka amsa da.

    “Ameen”, Bayan sun sake taɓa hira suka miƙe tare da yimata sallama suka tafi…!

     

     

     

     

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 11

    Sakayyah 11

     

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 11_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE fa ya kusa ƙarewa*

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine wannan Free page ne ƴar uwa 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ɗin.*

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

    Cikin lumshe Ido Mommy ke cin perpesoup ɗin yayin da daɗinsa ke ratsa ilahirin jikinta,

    kallonta Hajiya Bunayya dake murmushi tayi tare da ɗiban romon da cokali takai bakinta kana ta buɗe Idanunta dake lumshe.

    Tace.

    “Gaskiya Yaya Nagode wallahi bakiji yanda naji daɗin Perpesoup ɗin nan ba, dama sai tunanin a binda zanci nake tuntuni sai kuma gashi Allah ya kawo ki”.

    Murmushi mai cike da Ma’anoni Hajiya Bunayya tayi kana ta muskuta tare da gyara zamanta tace.

    “Lallai de kam aidama sanyin nan saida abu mai ɗumi da ɗan yaji-yaji”.

    Yayin da aƙasan ranta wani irin farin cikine mara misaltuwa wanda har yakasa ɓoyuwa asaman fuskanta.

    Ita kuwa Mommy Sosai take cin perpesoup ɗin tana mai lumshe Idanunta yayin da daɗin sa ke ratsa har ƙwaƙwalwar kanta tace.

    “Yaya perpesoup ɗin nan yaji kayan yaji”.

    Dariya Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Dama Alhaji nayiwa nace bari na zubo miki dan nasan zaki ji daɗin sa”.

    Kai Mommy ta gyaɗa da faɗin.

    “Aikam gashi yamin daɗi sosai”.

     

    Acan ɗaki kuwa miƙewa tsaye Khausar tayi daga kan stool tare da riƙe ƙugunta ta bayan ta gama nin ke kayan asaman laɓɓannta ta furta.

    “Wash Allah!, Gashi yanzu na gama gyara kayan nan, amma Raudat na zuwa ɗaukan abu ɗaya zata wargaza shi kab, ya zama kamar ba’a taɓa gyarashi,  amma Insha Allah next time, Idan ta ƙara har gitsashi, sama Zan mayar dan kayanta, ta yanda idan tazo baza ta iya ɗauka ba sai ta kirani in bata yafiye min sauƙi”.

    Ta Ida maganar tare da fitowa falon tana riƙe da ƙugunta da hannu ɗaya yayin da ɗaya hannun ke dafe asaman wuyanta.

    Cike da mamaki take kallon Hajiya Bunayya dake zaune yayin da Mommy ta ke shan perpesoup ɗin da kaɗan ya rage asaman Plate ɗin.

     

    Cikin yanayin tashin hankali da razana Khausar ta ɗaga Muryanta tace.

    “Mommy me kike ci?”.

    Anitse Mommy ta ɗago kanta dan sam batasan ta fito ba sai da taji muryanta, gyara rikon Plate din Mommy tayi kafin tace.

    “Perpersoup ne ko zaki cine?”.

    Ita kuwa Khausar kai ta girgiza cikin rawan murya tace.

    “A’a nikam bazan ciba Mommy kekam Komai kika samu sai kinci, ba zaki tsaya ki duba ingancin sa da kuma rashin ingancin saba”.

    Baki Mommy ta sake tana kallon Khausar da Mamaki.

     

    Ita kuwa Hajiya Bunayya wani mugun Harara ta galla mata cike da tsanarta tace.

    “Komai ta samu saita ci ke kin isa ki hanata cine?, Khausar!, Khausar!!, Khausar!!! ki kiyayeni fa”.

    Ta Ida maganar tana dariya irin abin awasa takeyin sa, yayin da kuwa azuciyarta ba haka bane.

    Ita kuwa Mommy taɓe Baki tayi tace.

    “Yaya rabu da ita itama kanta kwaɗayin ya kawota ƙilan so take in bata”.

     

    Fuska Khausar ta ɓata cike da damuwa tace.

    “Wallahi nikam ba zanci ba Mommy kema Meyesa zakici, kema daga ganin abu saiki hau ci, batare da kin duba ingancin sa ba Allah ma dai yasa kinyi Bismillah”.

    Dafe kai Mommy tayi tace.

    “Aikuwa de Wallahi kwaɗayin sa yasa na shafa banyi Bismillah ba, Anma bari nayi.

    Bismillahi feh Auwalihi Wa’ahirihi”.

    Ta faɗa tare da cigaba da shan perpesoup ɗin.

    Wani banzan kallo me cike da tsana Hajiya Bunayya ta watsa wa Khausar aranta tace, shegiyar yarinya, wannan yarinyar saina bi takan ta tukunna zata gane kurenta, bari dai ingama da matsalolin dake gabana”.

    Ita kuwa Khausar kallon mahaifiyarta da har zuwa yanzu take shan perpesoup ɗin tayi tace.

    “Wai Mommy ba zaki haƙura dasha haka ba?”.

    Girgiza Kai Mommy tayi kana tace.

    “Kema Idan zaki ci ga shican akula Khausar ban hana kiba, amma wannan tambayoyin naki sun fara isata”.

     

    Ƙwafa Hajiya Bunayya tayi tace.

    “Ƙyaleta bare ma ni bazan bar mata ba ina kedai ya isheki?”.

    Cikin sakin fuska Mommy ta gyaɗa kai tare da faɗin.

    “Eh Alhamdulillah ya isheni”.

     

    “Aiko buƙatar maje haji salla, ba zan bar matashi ba, tunda dai ke kinsha ai hikenan, idan tanaso ta biyoni ɗakina”.

    Ta ida maganar tare da ɗaukan kularta ta fice bayan ta yiwa Mommy sai anjima.

     

    Zama Khausar tayi agaban mahaifiyarta cikin raunin murya da yanayin damuwa tace.

    “Mommy meyesa!?, Rayuwar nan fa ba yanda kika ɗauke ta da yanda zuciyarki take ace haka na kowa yake  da munji daɗin duniyar nan fa, amma Mommy meyesa daga kawo miki abu zaki ɗauka kici yanzu kuma idan abin cutarwa ne fa?”.

     

    Kallonta Mommy tayi cikin tsukr fuska kana cikin fushi tace.

    “Khausar ki kiyayeni fa, bana son wannan baƙin halin da kike ɗaurawa rayuwarki fa. Ni bakiga ina nunawa matar nan baƙin hali ba haka zalika itama da zuciya ɗaya take zaune damu,  zaman lafiya mukeyi babu kishi bare tsangoma ko hassada, amma meyesa zaki sawa ranki rashin yarda akan n

    Me kike zaton zata cutar dani, babu abinda zata yimin dan haka ki kiyaye”.

    Ita kuwa khausar hawaye da ya cika mata Idanunta  tashiga ƙoƙarin mayarwa  sabida takaici, mahaifiyarta ta ɗauki duk kan yarda da amana ta basu, amma sukuma da wannan damar suke amfani ganin sun cutar da rayuwarta.

    Ƙasa Tayi da kanta kana tace.

    “Shikenan Mommy Komai na faɗa miki ba zaki yarda dani ba, amma babu komai Ubangiji Allah yatsareki ya kuma kareki”.

    “Ameen”Mommy ta amsa a kufule.

    Ita kuwa Khausar cikin mutuwar jiki ta miƙe tare da wucewa Bedroom ɗinta tana maijin wani irin zafi azuciyarta.

    Da kallo Mommy tabi bayanta tana ayyana abubuwa da yawa akanta, tarasa ina Khausar ta ɗauko wannan halin baki ɗaya bata da yarda muddin Hajiya Bunayya zata kawo mata abu ko Haiydar saita tsaya tana musu tambayoyi akai, da faɗin kada suci kada suyi kaza da kaza.

    Jin ƙiran sallah magriba yasa ta miƙe tashiga Bedroom ɗin ta dan gabatar da Sallah.

     

    Aɓangaren Khausar kuwa tana shiga ɗaki ta lumshe Idanunta tare da manna bayanta da jikin ƙofa.

    Hawaye masu ɗumi suka zubo mata jikinta na bata da wani makircin da Hajiya Bunayya ta shiryawa mahaifiyarta sam bata yarda da wannan perpesoup ɗin da takowo mata ba,

    shin wai ma ta wani hanya zatabi ta fahimtar da mahaifiyar?.

    Sosai ta zurfafa acikin tunanin da take har aka shiga Masallaci sai, asannan ta sauƙe gauron numfashi tare da nufar toilet cikin nutsuwa ta ɗaura alwala kana ta fito,   tare da shimfiɗa darduma duk da yanayin zullumi da take ciki bai hanata tattara nutsuwarta zuwa ga Ubangiji mabuwayi gagara Misali ba,

    bayan ta sallame ta ɗaga hannayenta biyu zuwa sama kana tace.

    “Ya Allah baka zalinci sannan kai ka hana zalunci atsakaninmu ya Allah baka gyan-gyaɗi bare bacci ya Allah kada ka bawa wannan baiwar taka daman cutar damu ya Allah ka  kare  mahaifiyata al’farma Annabi da al’ƙur’ani”.

    Kana ta shafa addu’ar tana mai zubar da hawaye har aka idar da Isha’i bata fita ba saima miƙewa da tayi ta kwanta agado lamo cike da tunanin rayuwa da haka bacci mara daɗi ya ɗauke ta.

     

    Cikin ikon Allah haka Mommy ta kwana lafiya lau batare da wani mugun abu ba, tun Khausar na jira taji Mommy tace wani wajen nayi mata ciwo ko kuma taga zubewan cikin Mommy kamar yanda Hajiya Bunayya ta faɗa taji shiru,

    hakan yasa ta watsar da abin aranta yayin da Aɓangaren Hajiya Bunayya baki ɗaya kunnenta ke sauraron jin wani labari daga bakin Mommy sai dai shiru amma tace bari ta kara jira kaɗan ta gani.

     

    Yau kwanan Mommy uku da cin perpesoup ɗin da Hajiya Bunayya ta kawo mata tana zaune a Bedroom ɗin ta cike da kasala.

    Cikin rumtse idonta ta zabura tare da dafe ƙasan maranta da yayi wani masifan murɗawa ahankali ta furta.

    “Wash! Allah na”.

    Sai kuma ta koma ta zauna tare da lumshe Idanunta yayin da hannunta na dama ke dafe asaman maranta sai ka ta miƙe  tare da fitowa falon tana takawa ahankali.

    Khausar dake zaune a asaman 3sitter Jikinta sanye da half gownt na bacci  yayin da ta tura tulin sumar kanta acikin hular Net Idanunta na kan takardan Geography dake riƙe ahannunta yayin da Nahawu ke ajiye gefe ta ɗago manyan Idanunta ta zubasu akan Mommy dake ya mutse fuska alamar bata jin daɗin jikinta, zama tayi akan 1 sitter kana a hankali tace.

    “Khausar har yanzu baki shiga ba?”.

    ta ida mgnar tana mai cije lips ɗinta.

     

    Ita kuwa Khausar kai ta gyaɗa mata tace.

    “Eh Mommy karatu nakeyi,  gobe Idan Allah ya kaimu zamu fara Exam ɗin First term, lokacin ai ya tafi amma Mommy lafiya na ganki haka?”.

    Ta ƙare mgnar tana kafe mata ido.

    Ya mutse fuska Mommy tayi tare da lumshe Idanunta still cikin na damƙarta tace.

    “Wallahi cikina ke ɗan min ciwo Khausar”.

     

    Cike da tausayawa Khausar tace.

    “Cikin ki kuma Mommy?”.

    Kai Mommy ta gyaɗa tace”.

    “Eh”.

    Ita kuwa Khausar ajiye takardan hannunta tayi tare da tsirawa mahaifiyarta ta Ido cikin tausayawa tace.

    “Mommy kodai in faɗawa Abba Azo atafi Asibiti ne?”.

    Kai Mommy ta girgiza kana tace.

    “A’a ai beyi tsanani har haka ba”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da sauƙe numfashi tace.

    “Toh Allah ya sawwaƙe”.

    Mommy da hannunta ke dafe asaman cikinta still Idanunta na lumshe tace.

    “Ameen”

    Miƙewa Mommy tayi ta koma kan 3sitter ta kwanta kamar minti biyu da kwanciyarta ta sai kuma sake miƙewa ta zauna tana yamutse fuska.

     

    Ita kuwa khausar cikin yanayin damuwa tace.

    “Sannu Mommy kode in Kira Abba ne?”.

    Girgiza kai Mommy ta kumayi sannan tace.

    “A’a tashi ki koma ɗaki nima yanzu zan shiga na kwanta”.

    Girgiza kai Khausar tayi tace.

    “A’a Mommy Zan zauna dake”.

    Lumshe idanu tayi tare da cije laɓɓanta na ƙasa tace.

    “Kada ki damu kije ki kwanta na faɗa miki naji sauƙi kuma nima yanzu zan shiga na kwanta”.

     

    Cikin sanyin jiki ta mike kana tace.

    “Saida safe Allah yaƙara sauki”.

    Mommy ta amsa da “Ameen”.

     

    Ita kuwa Khausar tana shiga ɗaki ta zube akan gadonta tare da faɗa wa duniyar tunanu, a haka bacci ya ɗauke ta kasancewar dare yaja batayi bacci ba ga kuma gajiya.

     

    A ɓangaren Mommy kuwa haka ta kwana cikin mawuyacin hali tare da murƙusoso cikin matsanancin ciwon ciki.

    Washe gari.

    Da safe bayan Khausar na idar da Sallah tayi Azkhar ta nufi ɗakin Mommy bakinta ɗauke da sallama.

    Mommy dake kishingiɗe kan darduma ta ɗago kanta tare da amsa sallamar Khausar.

     

    Kusa da ita Khausar ta tsugunna tare da riƙe hannunta tace.

    “Mommy ina kwana ya cikin naki?”.

    “Murmushin Ƙarfin hali Mommy tayi kana tace.

    “Naji sauƙi Khausar kije ki haɗa muku abin Breakfast kada lokaci ya ƙure”.

    Kai Khausar ta gyaɗa kana tace.

    “Amma da sauki Mommy kodai daurewa kike yi?”.

    Murmushi Mommy tayi tace.

    “Eh jeki shirya muku”.

    Kai ta gyaɗa sannan ta fice kai tsaye kichen ta nufa.

     

    Tana shiga tasa ruwa kadan atukunya yanda zai wadatar mata bayan ya tafasa ta ɗan zuba mai kana ta zuba Couscous kamar minti goma ta buɗe taga ya dahu yayi sar gwanin kyau, amfanin ɗiga man kenan.

    Sauƙewa tayi sannan ta buɗe fridge ta ɗauko miyan stwe da yaji naman kaza ta ɗumama sai kuma ta dauko lunch box din Raudat, Ramadan da Haiydar da kuma nata ta zuba musu, sai kuma ta koma ɗaki tashiga toilet tayi wanka Agurguje ta fito ɗaure da towel mai ɗan girma sannan ta cirewa Raudat kayanta tayi mata wanka bayan sun fito tashafa mata mai kana ta sanya mata Uniform sannan itama ta shirya cikin Uniform da yayi matukar amsar jikinta hannu Raudat taja suka fita dai-dai lokacin da Haiydar suka fito da Ramadan cikin shiri ko wannensu ya nufi inda lunch box ɗin da yake ya ɗauka kana suka fice harabar gidan suka shiga mota.

     

    Kamar ko yaushe motar na parking Khausar ta fito riƙe da hannun Raudat,

    Sai da ta kaita ajinsu sannan cikin sauri ta juya ta kama hanyar koma ajinsu daga baya taji ankira sunan ta da faɗin.

    “Lelewal ke kullum sai kowa ya riga ki shiga cikin aji ko?”.

    Ahankali ta juya tare da sauƙe manyan Idanunta akan Malam Isa dake tsayi  murmushi tayi da faɗin.

    “Ba haka bane Malam na tsaya kai Raudat ajinsu ne shiyasa”.

    Kai ya gyaɗa still Idanunsa akanta hakanan yarinyar ke burgesa ahankali yace.

    “To ki tafi kar araba musu questions paper ba kyanan”.

    Kai ta gyaɗa tare da juyawa cikin sassarfa da sanin darajar kanta take tafiya har ta isa cikin ajin.

     

    Aɓangaren Amina kuwa koda M Jameel yashiga class da niyyar raba musu questions paper ƙasa tayi da kanta ta amsa batare data kalli fuskarsa ba domin koda gaishesa ne ta dena tunda ta lura da baya buƙata kallon fuskanta, to shima M Jameel Sosai yaji daɗi da yarinyar ta daina gaishesa, dan ko kaɗan baya ƙaunar kallon fuskarta, bare kuma wata magana ta haɗa su.

     

    Acan gida kuwa tun bayan tafiyar su Khausar Makaranta cikin Mommy ya tsananta da ciwo da ƙyar ta yunƙura ta miƙe tana mai rintse Idanunta jini taga yana bin ƙafafunta da sauri ta dafe cikinta da ƙyar ta iya furta.

    “Ya Allah wannan ciwon cikin kuma na menene?”.

    Da ƙyar taja ƙafanta zuwa jikin beside drawer ta ɗaga wayarta tare da kiran number Hajiya Bunayya, kafin ya katse Hajiya Bunayya tayi picking tare da Sallama.

     

    Mommy kuwa cikin azaban ciwon da cikinta ke mata ta rintse Idanunta kana tace.

    “Yaya”.

    Da sauri Hajiya Bunayya ta katseta da faɗin.

    “Ƙanwata lafiya naji muryanki haka?”.

    cike da yarda  ta rintse Idanunta cikin yanayin azaban ciwon da cikinta keyi tace.

    “Wallahi Yaya cikina ciwo yake tun daren jiya, haka na kwana banyi bacci ba yanzu kuma gashi jini ya ɓalle min!

    Dan Allah ki faɗawa Alhj mutafi asibiti”.

     

    Hajiya Bunayya kuwa da damuwa amuryanta tace.

    “Subhanallahi! bari na faɗa masa yanzu ma kuwa”.

    Sannan ta katse wayar ta nufi ɗakin Lamiɗo ranta fari Sol burinta ya cika abakin ƙofa suka haɗu yana shirin fita.

    A take ta wani marairaice fuska kana cikin yanayin damuwa tace.

    “Yanzu Mommyn Khausar ta kirani.

    Wai jiya da ciwon ciki ta kwana yanzu kuma jini ya ɓalle mata”.

    Ai bai ma gama sauraron abinda zata faɗa ba ya ratsa ta ya wuce sashen Mommy cike da damuwa.

    Hajiya Bunayya kuwa da harara tabi bayansa kafin taja siririn tsaki ta mara masa baya.

    Tana shiga Bedroom ɗin ta samu Lamiɗo tsugunne akan Mommy da sauri ta tsugunna daga gefensa ta riƙo hannun Mommy.

     

    Cike da tausayawa kamar za tayi kuka tace.

    “Sannu Aysha ciwon ciki amma baki yi magana ba, gashi har ya tsananta jini na zuba”.

    Ta ida maganar zufa na karyo mata wanda in kagani zakayi zaton na tsananin damuwa ce, nan kuwa na tsananin farin cikin burinta ya cika ne.

     

    Lamiɗo kuwa miƙewa yayi tare da naɗe hannun rigarsa zai ɗauke ta Ganin haka ne yasa Hajiya Bunayya tayi saurin miƙewa tare da tallafo Mommy jikinta suka fita,

    agidan baya suka zauna Lamiɗo kuma ya shiga gefen mai zaman banza Driver yaja suka tafi Hajiya Bunayya sai faman sannu take yiwa Mommy.

     

    Suna isa asibitin aka karɓe su kai tsaye emergency aka nufa da ita ganin cikin ya riga ya zube yasa likitoci suka nufi wani ɗaki da ita tare da yi mata wankin ciki kana suka yi mata allurai nanda nan bacci wahala ya ɗauke ta Lamiɗo kuwa kasa Matsawa daga kusa da ita yayi ya cike da kulawa ya zauna a bakin gadon tare da riƙe tafin hannunta cike da tausayinta.

     

    Hajiya Bunayya data shaƙa ta cika kuwa.

    Wani lalataccen harara ta watsawa ƙeyansa cikin ranta tace, tabbas sai tayi wani abu akan wannan rawan jikin da yake mata.

    A zahiri kuwa dafa kafaɗar sa tayi,  ahankali ya ɗago kansa ya kalleta da idanunsa dake cike da damuwa amma baice komai ba.

    Cike da kirsa ta ƙirƙiri murmushin da bai kai zuciba kana tace.

    “Dan Allah ka rage damuwar nan, babu yanda zamuyi da ƙaddara haka Ubangiji ya tsara wannan ɗin ma ba rabo bane, ayanzu addu’ar lafiya take da buƙata awajenmu”.

    A hankali ya sauƙe nannuyar Ajiyar zuciya tare da mayar da Kallonsa ga Mommy dake bacci tamkar babu abinda ke damunta.

    Lumshe idanunsa yayi yace.

    “Ina matuƙar tausayawa Aysha tun bayan haihuwar Haiydar take fama da wannan matsalar sannan ko wanne cikin sai ya wahalar da ita kafin ya fita”.

    Da sauri Hajiya Bunayya ta katsesa da faɗin.

    “Ya zamuyi da rubutacciyar ƙaddara, ai kaga da Ubangiji yaga dama ai cikin Raudat da Ramadan ya zauna”.

    Kai ya jinjina amma baice komai ba.

    Ita kuwa cikin ɓoye farin cikinta ta sauƙe ajiyar zuciya da faɗin.

    “Zan koma gida kafin ‘yan makaranta su dawo, naga lokaci yaja amma Insha Allah anjima zan dawo”.

    Kai ya gyaɗa ba tare da yace komai ba still Idanunsa na kan Mommy.

    Hajiya Bunayya kuwa ficewa tayi ranta fari fess kana tasa Driver ya maida ta.

     

    Acan Makarantar su Khausar kuwa koda suka gama Exam ba abasu damar tafiya ba bayan sunyi sallar la’asar suka shiga haddar Alkur’ani sai ƙarfe biyar aka tashe su, kana suka shigo mota suka nufi gida, motar na parking Raudat ta fice da gudu ta nufi sashen su

    Tana shiga falo ta fara  kiran.

    “Mommy! Mommy!! na mun dawo”.

    Jin shiru yasa ta nufi Bedroom ɗinta da gudu ta buɗe ta shiga tana kiran.

    “Mommy!, Mommy!!, Ina kika shiga”.

    Still Bata ganta ba da gudu ta juya ta fito falon dai-dai lokacin Khausar kuma ta shigo ƙara sawa kusa da Khausar tayi ta riƙe hannunta kana tace.

    “Addah Khausy Ina Mommy?”.

    Kallonta Khausar tayi kafin tace.

    “Bata ɗaki ne?”.

     

    Kai Raudat ta gyaɗa mata alamar Eh,

    Sake hannunta Khausar tayi kana ta nufi kichen ta buɗe wayam tagani alamar bata nan komawa tayi ta shiga Bedroom din ta ɓude still ba tanan jikin toilet ta nufa ta manna kunnenta ajiki tare da faɗin.

    “Mommy Mommy kina ciki kuwa?”.

    Jin shiru yasa ta tura ƙofar toilet din still bata nan fitowa tsakiyar falon Khausar tayi tare dasa hannun damanta ta riƙe ƙugunta tana tunanin ina Mommy ta shiga haka, bayan tasan bata fiye fitar yamma ba kuma koda zata fita tun safe kafin su tafi makaranta zata faɗa musu bare kuma yau da suka barta bata jin daɗi.

     

    Da sauri ta kalli Raudat sai kuma tace.

    “Jirani anan ina zuwa”.

    ta faɗa tare da ficewa kai tsaye sashen Hajiya Bunayya ta nufa bakinta ɗauke da sallama tana faɗin.

    “Ummah”.

    Shigar ta yayi dai-dai da lokacin da Hajiya Bunayya ke riƙe da waya tana cewa.

    “Kedai Hajiya Lami bari buƙata ɗaya ta biya saura ɗaya, tana can kwance a asibiti cikin ya zube yabi makwarari, saura ɗayan daman  jira nake inga ya zata kaya ne ki shirya jibi zamu koma”.

    Komai Hajiya Lami ta faɗa ohon musu, ita dai Hajiya Bunayya  cikin jin dadi ta kece da wata mahaukaciyar dariya mai nuni da tsantsar farin ciki.

    Lokaci ɗaya kuma dariyar nata ya tsaya ganin Khausar tsaye, sai kuma ta katse kiran tare da kallon Khausar.

    Kafin tace wani abu Khausar tayi saurin cewa.

    “Ummah ina Mommy mu?”.

     

    Hajiya Bunayya ta wani langwaɓar da kai kana tace.

    “Ayyah Khausar am Mommy ku tana asibiti bata da lafiya wallahi cikinta ya zube”.

     

    Da sauri Khausar da kanta ke ƙasa ta ɗago ta kalli Hajiya Bunayya tana sake maimaita kalmar cikinta ya zube akasan ranta lokacin ɗaya hawaye masu zafin gaske suka cika kwarmin Idanunta.

    Sai kuma tayi saurin maida hawayen ta kafin tace.

    “Shikenan ɓuƙatar magauta tabiya hankali ya kwanta. Allah ya raya mata wa anda ta haifa. Ubangiji ya tsaresu daga sharrin mai sharrin”.

    Ta ida maganar tana ƙoƙarin fita.

    Da sauri Hajiya Bunayya tace.

    “Ke Khausar zo nan Me kike nufi?”.

     

    Anutse Khausar ta juya tare da sauƙe manyan Idanunta da suka sauya launi zuwa ja ta zubawa Hajiya Bunayya kana tace.

    “A’a Ummah babu abinda nake nufi, kawai dai addu’a ce nayi”.

    Cikin tsuke fuska Hajiya Bunayya ta watsa mata Harara da faɗin.

    “Sannan su waye ne Magautan?”.

     

    Ware hannu Khausar tayi tare  da faɗin.

    “Nikam ban sansu ba,  amma dai nasan Allah Mabuwayi gagara Misali ya sansu kuma zaiyi maganin su, domin ai bahaushe yace rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya,  suji tsoron ranan da Ubangiji zai musu kamun talala!”.

     

    Cike da Mamaki Hajiya Bunayya tace.

    “Wai Khausar me kike magana kamar habaici kike min ko kuma hannunka mai sanda!?.”

     

    Ware ido Khausar tayi tace.

    “Haba Ummah in Miki habaici kuma ayanda kike ƙaunar Mommyn mu kinfi ƙarfin habaici ko hannunka mai sanda kin wuce haka sai dai mgnar ce tazo kamar zaurance”.

     

    Ɓoyeyyen Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta saki domin tayi zaton yarinyar ta gano lagonta ne.

    Khausar kuwa murmushi tayi tare da faɗin.

    “Bari na tafi asibitin kar dare yayi”.

    Da sauri Hajiya Bunayya ta gyara zamanta Idanunta akan Khausar tace.

    “Toh kibari in ƙara sa abinci mana sai ki tafi dashi”.

    Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.

    “Toh amma bari na shiga gidan Aunty Ruƙayya kafin ki ƙarasa”.

    Kai Hajia Bunayya ta gyaɗa tare da faɗin.

    “Toh ki gaisheta”.

    Kai kawai Khausar ta gyaɗa Sannan ta wuce sashen su.

     

    Tana shiga Bedroom direct toilet ta wuce ta cire Uniform ɗin ta sannan ta watsa ruwa bayan ta fito ta dauki dogon rigar material pinch colour ta sanya, kana ta nufi kichen Agurguje ta dafawa su Haiydar jollof ɗin shin kafa da yaji bushesh-shen kifi da kayan ƙamshi nan da nan kichen ɗin ya ɗauki ƙamshi Warmers ta ɗauka ta juye sannan ta tafasa musu tea kana ta ɗura musushi, sannan ta fita falon dai-dai lokacin da Haiydar ya shigo.

     

    Kallonsa Khausar tayi tare da kiran sunansa tace.

    “Haiydar”.

    Ya amsa da.

    “Na’am”.

    Cikin sanyi tayi ƙasa da muryanta tare da faɗin.

    “Dan Allah Haiydar ka kwana anan kai da Ramadan, Raudat kuma zamu tafi da ita asibiti sai mu kwana da Mommy”.

     

    Kai ya gyaɗa mata sai kuma yace.

    “Nima ai inaso naje na dubata”.

    Jinjina kai Khausar tayi tace.

    “Ba damuwa kazo mutafi dukan mu amma yanzu zan fara shiga gidan Aunty Ruƙayya in sanar mata, idan yaso kai da Ramadan ku taho tare da Ummah,

    In yaso sai ku dawo tare amma kubar min Raudat dan zamu kwana tare”.

     

    “Toh shikenan Allah ya bata lafiya”.

     

    “Ameen”,

    Tace kana ta juya ta tafi har ta kusa fita ta sake juyawa ta kalli Haiydar dake tsaye Ahankali tace.

    “Dan Allah Haiydar ka kula, bakomai za’a baka kaci ba, akwai abinci na dafa muku sannan duk wani abu da zaku buƙata akwai”.

    Da sauri ya dafe kansa tare da faɗin.

    “Ke dai jeki da rashin yardan ki kedai haka Allah ya halicce ki baki da yarda”.

    Cikin sanyi ta girgiza kai kana tace.

    “Shikenan ni dai ban san sai yaushe zaku yarda dani ba”.

    Ta ida maganar tare da ficewa”.

     

    Kai tsaye gidan Aunty Ruƙayya ta nufa.

     

    Tare da Sallama tashiga Babban falon da yaji kayan alfarma kujerun set biyu aciki Black and Ash sai kuma babban tv plasma dake Manne abango daga ƙasansa kuma horm teater ne ƙasan falon kuma shimfiɗe yake da chanis capet.

     

    Aunty Ruƙayya dake bedroom ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tace.

    “Khausar kece sannu da zuwa, shigo ciki”.

    Da sauri tace.

    “A’a Aunty sauri nakeyi ai”.

    Cikin kulawa tace.

    “Yo yasu Mommy ki?”.

    Murmushi Khausar tayi tace.

    “Wallahi Aunty Ruƙayya Mommy ce ke asibiti bata da lafiya, shine nace bari nazo na faɗa miki, Ni yanzu ma zan wuce ko za muje tare?”.

     

    Cike da tausayawa Aunty Ruƙayya tace.

    “Ayyah Allah ya bata lafiya zanje bari ina zuwa mu tafi tare”.

    Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.

    “Toh”.

    Aunty Ruƙayya kuwa bedroom ta shiga tare kiran mijinta a waya, bayan ya bata izinine, ta ɗauko key mota da mayafinta suka fita,

    suka shiga mota,

    jingina kai Khausar tayi da jikin motar kalaman Hajiya Bunayya nayi mata suwwa akunne.

    Juyawa Aunty Ruƙayya tayi ganin yanda Khausar ta zurfafa cikin tunani yasa tace.

    “Ki riƙa yi mata addu’a”.

    Kai kawai Khausar ta iya gyaɗa mata.

    Cikin Mintuna kaɗan suka isa Asibitin bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga ɗakin da aka kwantar da Mommy saboda Hajiya Bunayya ta faɗa mata.

     

    Kwance akan gado suka tarar da ita yayin da Lamiɗo ke gefenta akan kujera hannunsa riƙe da kofin tea yana miƙa mata da faɗin.

    “Ki tashi kisha”.

    Yana jin Sallamar Khausar ya juya yana kallonta har ta isa kusa dashi.

    Cike da kulawa yace.

    “Khausar har kun dawo?”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Eh Abba ya jikin Mommy!?”.

    Sai da ya ɗan kalli Mommy dake jingine da pillow sai kuma ya mayar da Kallonsa kan Khausar yace.

    “Da sauƙi”.

    Sai asannan ya lura da Hajiya Rukayya ya ɗan yi murmushi da faɗin.

    “Hajiya Ruƙayya sannu da zuwa”.

     

    Zama tayi akujeran dake kusa da ita tana cewa.

    “Yawwa ya Hajiya Aysha da jikin kuma?”.

    Ɗan Murmushi yayi kana yace.

    “Da sauƙi”.

    Tana kallon Mommy tace.

    “Ubangiji Allah ya ƙara sauki”.

    Ya amsa da.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

     

    Khausar kuwa bakin gadon ta ƙarasa ta riƙe hannun Mommy acikin nata.

    Cikin raunin murya tare da tausayawa mahaifiyar tata tace.

    “Sannu Mommy ya Jikin?”.

    Lumshe idanu Mommy tayi kana ta buɗe su a hankali tace.

    “Da sauƙi Khausar bana jin komai in dan ta nice ma, da su sallame ni in koma gida mu kwana tare, dan bana jin ciwon cikin yayi sauƙi babu inda yake min ciwo!”.

     

    Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da faɗin.

    “Masha Allah Mommy Allah yaƙara sauƙi Ubangiji ya ƙara tsarewa ya kare”.

    A ranta kuwa cewa tace.

    Ayyah da ace duk addu’o’in da takeyiwa Mommynta tun randa taci ferfesun da ace tana haɗa addu’ar da yaron cikin wata ƙil da bai zube ba.

     

    Shafa kanta Mommy tayi cike da ƙaunar ta tace.

    “Ameen Khausar ki kwantar da hankalin ki ba najin Komai”.

    Ta faɗi hakan ganin yanda Khausar tayi zuru-zuru da ita.

    Hajiya Ruƙayyance ta kalli Mommy kana tace.

    “Hajiya Aysha ya ƙarfin jikin!?”

     

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Dasauƙi Hajiya Ruƙayya ya ‘Yar taki ya kuma rigima a makaranta!?”.

    Kallon Khausar Hajiya Ruƙayya tayi kana tace.

    “A’a yanzu ai ta daina ta fara girma!”.

    Jin haka yasa Khausar tayi murmushi.

     

    Lamiɗo kuwa miƙewa yayi idanunsa akan Mommy yace.

    “Toh shikenan bari na tafi dama ganin babu kowa ne yasa nake zaune bari na samu naje nayi wanka dan tunda muka zo ban samu na koma gida ba”.

     

    Hajiya Ruƙayya tace.

    “Ayyah ai babu komai Alhaji kaje”.

    Jinjina kai Mommy tayi tace.

    “Allah ya tsare”.

    Ya Amsa da.

    “Ameen”sannan ya juya ya fice.

    Tafiyar Lamiɗo babu daɗewa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka zo Raudat na riƙe da hannunta.

     

    Suna shiga Hajiya Bunayya ta zauna daga gefen gadon tare da kallon Mommy tace.

    “Sannu ƙanwata ya ƙarfin jikin?”.

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Ai naji sauki Yaya”.

    Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi cikin yanayin tausayawa tace.

    “Allah ya baki lafiya”.

    Hajiya Ruƙayya kuwa kallo ɗaya tayi wa Hajiya Bunayya da Hajiya Lami taji sam basu kwanta mata arai ba musanman ma Hajiya Bunayya dake wani shish-shugewa Mommy.

    Ta dai daure tace.

    “Sannunku da zuwa”.

    Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka haɗa baki wajen cewa.

    “Yawwa ya mai jikin”.

    Ataƙaice Hajiya Ruƙayya tace.

    “Da sauƙi”.

     

    Hajiya Lami kuwa jikin gadon ta matasa Idanunta akan Mommy tace.

    “Ayyah Sannu Hajiya Aysha Ashe ga abinda ya faru kuma? Amma wannan abu yayi  yawa ai gwara Alhj yayi ƙoƙari ya fitar dake waje wannan matsalar ko yaushe da ansamu ciki ya zube ai babu daɗi!”.

     

    Kafin Mommy tayi magana Hajiya Bunayya tayi saurin cewa.

    “Kede bari Hajiya Lami abin nan yana damun mu, gaba ɗaya mun kasa gane menene ainihin matsalar, amma hankalinmu na tashi kullum cikin yanayin nan, abin babu daɗi yanzu ciki takwas kenan yana zubewa abin ai babu daɗi!”.

    Taɓe baki Khausar da Hajiya Rukayya sukayi alokaci ɗaya.

     

    Ahankali Mommy ta gyara matashin data kishingiɗa akai kana tace.

    “Uyummm ya za’ayi da abinda Allah ya tsara, amma ni inaga nin ba wani matsala bane, tun da gashi na haihu bayan haihuwar Haiydar ma haka nata fama da ɓare-ɓaren nan, kuma daga baya da Allah ya kawo Ramadan da Raudat an haifesu ba komai ai”.

     

    Cike da kirsa Hajiya Bunayya tayi yaƙe kana tace.

    “Hakane kam, toh Allah ya kawo masu albarka”.

    Hajiya Lami kuwa harara ta gallawa Mommy tare da taɓe baki aranta tace shegiya me iyayin jaraba keda haihuwa sai dai kiga anayi.

     

    Idanun Hajiya Ruƙayya da Khausar na kan Hajiya Lami alokacin data taɓe baki ta harari Mommy,

    Juyawa Hajiya Ruƙayya tayi ta kalli Khausar tare da jinjina kai itama Khausar kai ta jinjina.

     

    Miƙewa Hajiya Ruƙayya tayi tare da kallon Mommy tace.

    “Toh Hajiya Aysha Ubangiji Allah ya ƙara sauki sannan Allah ya tsareki daga sharrin abin ƙi ni zan wuce!”.

    A hankali Mommy ta ɗan yunƙura tare da lumshe Idanunta kana tace.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum Hajiya Ruƙayya Nagode”.

     

    Hajiya Lami da Hajiya Bunayya kuwa baki suka saki suna kallon Hajiya Ruƙayya da Mamaki aransu suka ce kaji shegiyar mata da iyayi uban wa takewa wannan addu’ar.

    Miƙewa Raudat tayi tare da riƙe hannun Hajiya Ruƙayya tace.

    “Aunty Ruƙayya ni zan biki gidanki, Inje in kwana dasu Salman tun da gobe babu makarata”.

    Da sauri Khausar ta kalli Raudat dake riƙe da hannun Aunty Ruƙayya tace.

    “Ayyah Raudat am baza mu kwana ba?”.

    Girgiza kai Raudat tayi tare da langwaɓar da kai kana tace.

    “ Ni dai Ina tsoro  ni bazan zauna ba”.

    Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.

    “Shikenan kibi Aunty Ruƙayya”.

    Murmushi Aunty Ruƙayya tayi tare da jan hannun Khausar dake cikin nata

     

    Har sun kai ƙofa Hajiya Bunayya ta ƙirƙiri murmushi tana kallon bayan Raudat tace.

    “Oohhh Raudat ba zaki bini mu tafi gida ba?”.

    Kafaɗa Raudat ta maƙale tace.

    “A’a ni zanbi Aunty Ruƙayya”.

    Aunyty Ruƙayya kuwa jan hannun Raudat tayi suka fice batare data sake jiran jin Abinda Hajiya Bunayya zata ceba.

     

    Bayan tafiyar Aunty Ruƙayya babu da ɗewa Hajiya Bunayya ta miƙe tare da kallon Mommy tace.

    “Toh ƙanwata  zamu wuce Allah yaƙara sauƙi”.

    Murmushi Mommy tayi da faɗin.

    “Nagode Yaya ahuta gajiya”.

    Hajiya Lami tace.

    “Babu Gajiya”.

    Sannan suka fice Khausar kuwa jinginar da kai tayi kamar mai bacci.

     

    Da daddare Khausar ta miƙe daga kan dogon kujeran asibitin da take kwance ta dubi Mommy da bacci ya fara fisgarta tace.

    “Mommy”.

    Buɗe idanu Mommy tayi tare da kallon Khausar tace.

    “Na’am Khausar ya akayi?”.

     

    Ajiyar zuciya Khausar ta saki tana wasa da yatsun hannunta tace.

    “Mommy baki zargi perpesoup ɗin nan da kika ci azubewar cikin nan ba!?”.

    Sosai Mommy ta tsira mata ido na second uku zuwa biyar sai kuma ta miƙe daga kwanciyar da take Atake fara’ar dake fuskanta ya gushe cikin ɗaure fuska cikin kakkausan Murya tace.

    “Khausar!, Khausar!!, Khausar!!!, Ki cigaba Nagode da abinda kike min Khausar, duk irin tarbiyyan da nake baki fatali kike dashi ko, kina ɗaukar rashin yarda kina ɗaurawa mutane ki sani Manzon Allah (S.A.W) Yace.

    :Azzana zambu walau kana haƙƙun”.

    Khausar kuwa ƙasa da kai tayi hawaye masu zafi suka cika Idanunta shin sai yaushe mahaifiyarta zata amince da gaskiyar da take so ta sani akan Hajiya Bunayya basa ƙaunarta cutar da ita suke sonyi.

    Cikin sanyi murya tare da rauni gami da ban haƙuri tace.

    “Shikenan Mommy kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyarki”.

    Mommy bata tanka taba ta juya ta gyara kwanciyar, ta itama Khausar juyawa tayi ta kwanta zuciyarta babu daɗi.

     

    Washe gari  Alhamis Da safe Dr ya shiga ya basu sallama dan jikinta yayi sauƙi Sosai Lamiɗo da kansa yaje ya maido su gida.

    Suna dawowa Hajiya Bunayya ta shigo hannunta riƙe da babban Warmers da tayi Perpesoup ɗin Kaji ta shigo dashi.

    Zama tayi akan 2sitter tace.

    “Sannu ƙanwata ya ƙarfin jikin?”.

    Mommy tayi yar dariya tare da faɗin.

    “Jiki yayi sauƙi Yaya sai faman hidima kike dani kamar wacce tayi haihuwar farko?”.

    Dariya Hajiya Bunayya tayi da faɗin.

    “Ai mai ɓari yafi son akula dashi fiye da mai haihuwa”.

    Khausar dake tsaye duk takaici ya gama cikita gashi babu dama ta faɗawa mahaifiyarta gaskiya sai ta hau kanta da faɗa bayan da ta iya daga ƙarshe ma Saboda takaici kawai sai ta koma Bedroom ɗin ta ta fara karatu.

     

    Wunin ranan haka Hajiya Bunayya ta yini tare da Mommy ta cigaba da kulawa da ita.

     

    Washe gari juma’a dai-dai lokacin da maza suka tafi Juma’a dai-dai lokacin da kowa ya tafi Sallar juma’a Akuma lokacin ne Hajiya Bunayya da Hajiya Lami suka tafi gidan Boka Kar’uzu.

     

    Khausar da Mommy ne zaune suna hira sosai jikin Mommy yayi ƙarfi abinka da mai juriya ga kuma kulawa da take samu.

    Sallamar Aunty Ruƙayya ya katse musu hirar da suke.

    Khausar ta faɗaɗa fara’ar fuskarta kana tace.

    “Aunty Ruƙayya sannu da zuwa ina Affan?”.

    Murmushi Aunty Ruƙayya tayi tana zama tace.

    “Affan yana lafiya bacci ma yake ya mai jikin”.

    Khausar tace.

    “Jiki da sauƙi”.

    Aunty Ruƙayya tace.

    “Masha Allah Ubangiji ya ƙara sauki”.

     

    Cikin sakin fuska Mommy ta gyara zaman hular dake kanta tace.

    “Hajiya Ruƙayya sannu da zuwa ya gajiyarki?”.

    “Hajiya Ruƙayya tayi murmushi da faɗin.

    “Babu gajiya ya jikin naki?”.

     

    “Jiki yayi sauƙi ya yara?”.

    Alhamdulillah ta bata amsa.

     

    Khausar kuwa miƙewa tayi cikin neman izinin tace.

    “Ayyah Mommy zanje gidan su Asma’u?”.

    Ido Mommy  ta zuma mata, na tsawon second bakwai tana kallonta kana tace.

    “Toh yayi kyau”.

     

    Khausar kuwa juyawa tayi ta shiga Bedroom Dogon rigar dake jikinta ta cire tare da ɗaura towel tashiga toilet,

    shawer ta ɓude ta sakarwa kanta ruwan ɗumi,

    ta ɗauki kusan minti shabiyar kafin ta fito ɗaure da towel da tsawon sa bai wuce gwiwar taba yayin da ƙarami ke kanta tana tsane ruwan kanta.

    Stool ta janyo ta zaune tare da goge ruwan jikinta ta ɗauki Vassiline lotion ta shafa kana ta ɗauki powder ta shafe sai kuma Kajol ta zizara a idanunta mascara ta ɗauka ta taje gashin Idonta da sukayi tsayi tamkar tasa Eyelashes golb mai sheƙi ta ɗauka ta shafa asaman pinch lips ɗin ta sai yayi kamar jan baki ta shafa kallon fuskarta tayi a mirrow sosai tayi kyau.

    Miƙewa tayi ta nufi jikin durowar ta buɗe uban kayan dake ciki ta zubawa ido ahankali Idanunta suka sauka akan wani Less Coffee da aka masa adon cycle da rastin Milk colour ta janyo ta sanya Masha Allah Sosai ɗinkin less ɗin ya mata kyau tare da fitar da shape din jikinta skirt ɗin ya zaune ɗass ajikinta tare da fitar mata da tsarerrenn ƙugunta haka ma rigar ta zauna ɗass ajikinta ɗan kwalin ta ɗauka tayi ɗauri mai kyau sai kuma ta ɗauki glaye medium size milk color kana ta feshe jikinta da turarukanta masu daɗin ƙamshi.

     

    Falon ta fita tun kan ta isa Aunty Ruƙayya ta ɗago kanta tare da tsira mata Idanunta jin ƙamshin daya ratsa hancinta ta saki murmushi kana tace.

    “Iyeee Masha Allah Khausar irin wannan kyau sai kace preety  ta ƙasar India”.

    Hannu Khausar ta sanya ta rufe fuskarta tana dariya sai kuma ta buɗe tace.

    “Kai Aunty Ruƙayya Ina Zan samu koda rabin kyawunta ne?”.

    Ware ido Aunty Ruƙayya tayi kana tace.

    “Allah kuna kama dan da zakije India ma cewa za’ayi ke ƙanwarta ce, har rawan kanki ma irin natane a Film ɗin Chori-Chori Cubke-Cubke ne”.

    Mommy Kam murmushi take musu batare da tace komai ba.

     

    Khausar kuwa Murmushin jin daɗi tayi tare da tsugunnawa ta ɗauki wayar Mommy tace.

    “Mommy zan tafi da wayarki”.

    Kai kawai Mommy ta gyaɗa mata sannan ta ɗauƙi wayar tare da faɗin.

    “Na tafi”.

    ta ida maganar tana gyara zaman Handbag din Hannunta tare da ciro earpiece aciki

    Suka haɗa baki wajen faɗin.

    “Adawo lafiya”.

    Kai ta jinjina tare da ficewa,

    Abokin gate ta haɗu da Haiydar riƙe da MP ɗin sa, cikin sauri tace.

    “Yauwa Haiydar dan Allah aramin MP ɗinka”.

    Cike da mamaki ya zuba mata ido tare da cewa.

    “Yau kuma to ke kuma da ba jin kiɗa ya dameki ba, me zakiyi dashi?”.

    Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.

    “Wallahi yau dai shauƙi nakeji zanje wurin Asma’u mu ɗan rausaya”.

    Murmushi yayi yana mamakin wai yau Khausar ce da cewa zata sha ƙiɗa, kawai miƙa mata yayi. Tare da cewa.

    “Kuma kikasa gyale ko?”.

    Cikin daɗi tace.

    “Ngd kai rabani kullum mutum liƙe da hijabi kamar maitakaba” na mgnar  tana fita  ta tari adaidaita sahu ta shiga.

     

    Acan ɓangaren Moddibo kuwa bayan an idar da Sallah juma’a ya kalli M Jameel dake Driving yace.

    “J yakamaya muje mu gaida Ummi kafin mu koma gida!”.

    Kai ya Jinjina  kana yace.

    “Dama abinda nake son faɗa kenan ka rigani”.

    Gyara zama Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa yana sauraron ƙira’ar dake tashi amotar kana ya shafa sajensa yace.

    “Muje toh”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da juya akalar motar zuwa unguwar su Ummi.

     

    Suna cikin tafiya wayar M Jameel ya hau ruri yana duba screen ɗin wayar yaga Bahrain ba suna sai Number Dariya M Jameel yayi still hankalinsa nakan Driving din yace.

    “Jalaludden! Wallahi Jalaludeen!!  nayi mana abinda ransa keso”.

    Moddibo da Idanunsa ke lumshe yayi ɗan guntun Murmushi ba tare daya buɗe idanun ba yace.

    “Toh ka ɗaga mana kar ya yanke”.

     

    Picking M Jameel yayi tare da Sallama.

    Amsawa Jalaludeen yayi  da faɗin.

    “Idan kun isa ku gaishe da Ummi”.

    M  Jameel yayi Murmushi kana yace.

    “Kana biye da mu ne?”.

     

    “A’a bana biye daku na dai rigaku zuwa na gaisheta”.

    Cewar Jalaluddeen

    Dariya M Jameel yayi sai kuma ya zare ido yace.

    “Wallahi Jalaludeen kada ka razana mana tsohuwa!”.

     

    Murmushi Jalaludeen yayi yace.

    “A’a bazata ra zanata ba sannan ba zata tsorata ba ai mun taɓa zuwa tare daku baku dai sani bane kuma na bayyana mata ta ganni”.

     

    “Wallahi Jalaludeen ka kiyaye mufa”.

     

    Dariya Jalaludeen yayi kana yace.

    “Tare dai mukayi sallama jumma’a a sahu daya.

    Yanzu kuma Na dai hango ku ahanya zakuje yanzu ina katakon nan?”.

    Da sauri M Jameel yace.

    “Wani katakon?”.

    Cike da tsokana Jalaludeen yace.

    “Katakon dake gefenka”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da kallon Moddibo yace.

    “A.J ɗin nawa ne katako?”.

     

    “Eh inba katako ba shi menene? ka faɗa masa cewa akwai furen dake ƙoƙarin tsiro a jikinsa tun daga ƙasa har ya isa zuciya ya gab da kanshi tuni ma ya ratsa zuciyarsa amma bai sani ba”.

    Murmushi M Jameel yayi  tare da kallon Moddibo da still Idanunsa ke lumshe kamar mai bacci kana yace.

    “Wai yace in faɗa maka akwai furen da zai fito tsakiyar kanka yama ratsa zuciyarka”.

    Sai asannan Moddibo ya buɗe idanunsa ya kalli M Jameel tare da faɗin.

    “Ka ganni karabu dani da kalaman Jalaludeen, shiya sani can yaje yata faman maganganunsa da baza ka gane kansu ba bare gindinsu ya riƙa yi mana maganar damu mutane zamu gane ba sai wanda sai sune masu ganewa ba”.

     

    Dariya Jalaludeen yayi yace.

    “Zaka gane ne ai lokaci ne yana zuwa”.

    Dariya M Jameel yayi tare da hong aƙofar gidan Ummi ganin shiru ba’a buɗe masu bane yasa, M Jameel fitowa ya buɗe, kana ya dawo yaja motar still kafaɗarsa saƙale da wayar

    Jalaludeen ne yace.

    “Ku gaishe da Ummi idan kun shiga”.

    Sannan ya katse wayar kana shi kuma ya kutsa kai cikin gidan.

     

    Dai-dai lokacin da a dai-dai-ta ya ajiye Khausar kudinsa ta basa tare da buɗe ƙaramin ƙofar dake maƙale da gate ɗin tashiga,

    Batama lura da babban gete ɗin dake ɗan buɗe ba,

    ganin mota a fake a harabar gidan yasa ta isa wajen kasancewar glass ɗin tink-tenk ne yasa bata fahimci da mutane aciki ba rawar kanta kuma ya hanata fahimtar alamun yanzu motar ta tsaya.

     

    Jikin gefen mai zaman banza ta nufi tare da kallon fuskarta ajikin mirrow sai kuma ta juya manyan Idanunta kalaman Aunty Ruƙayya suka dawo mata kunne tana kama da Preety matsa pinch lips ɗin ta tayi tare da lasa kadan sai kuma ta juya manyan Idanunta.

    M Jameel kuwa dake mazaunin Driver  murmushi ya saki domin  ya tabbata bata san da mutane aciki ba.

     

    Acan ɓangaren su Hajiya Bunayya kuwa zaune suke gaban boka Kar’uzu  cikin tsananin ɓacin rai da fushi Boka Kar’uzu ya buga musu wata razananniyar tsawa cikin sautin muryarsa mara daɗin sauti

    bayan ya gama sauraron Hajiya Bunayya yace.

    “Ai seda na faɗa muku aduk lokacin data fara aiki da maganin kada tayi alwala da sallah na tsawon wata ɗaya amma saboda taurin kai kuka bari tayi alwala tayi sallah shiyasa yake kallon fuskar ta kamar na ƙonennen Biri”.

    Atsorace Hajiya Bunayya ta juya ta kalli Hajiya Lami da itama ɗin Iran take kallo.

    Sun kasa hafimtar sharrin boka na wasa da hankali da ƙarya sun kasa tuna sam bai faɗa musu hakanba a lokacin, su kasa aminta mgnar boka dubune babu gsky ko ɗaya sai yaudara da taɓewa.

     

    Acan ɓangaren su Moddibo kuwa sake kallon madubi Khausar tayi tare dasa hannu ta gyara man lips ɗin ta sai kuma danna MP ɗin cikin Sa’a kuwa sautin waƙar BUGA ya fara tashi.

    A hankali ta gyara tsayuwar ta, tare da fara jujjuya ƙugunta a hankali tana mai rausaya jikinta.

    Zuwa tsakiyar waƙar kam fa da abu ya jiƙa, sai ga mayafinta bisa kafaɗarta gefe ɗaya, sosai take jujjuya mazaunenta tare da motsa dukkan jikinta, tana mai kallon kanta a madubi.

    Sai kuma ta kalli Glass ɗin tare da ɗaura bakinta akai ta saki zazzafan  kiss muahhhh.

    Shi kuwa Moddibo dake zaune idanu ya zuba mata tare da manna kumatunsa adai-dai glass ɗin sai kuma hakan yasa lips ɗinta sauƙa kan….!

     

     

    FREE page sun kusa ƙarewa 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA ki biya 1k dinki ya isheki

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 18

    Sakayyah 18

     

    SAKAYAH

     

    18

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

    Spjt. Rungume juna sukayu tamkar zasu shige cikin jikin junansu, yayin da ruwan sama kuwa ke cigaba da sauƙa tamkar da bakin ƙwarya, kana ga walƙiya da tsawa dake cigaba da sauƙa.

    Moddibo shi kam baki ɗaya ya burkice ya rasa tunaninsa, na wushin gadi, gaba ɗaya jinshi yake a wata duniya ta da ban,

    ga wani matsanancin tsoro daya lulluɓe sa kana ga wani baƙon yanayi da yake ji yana yawo agaba ɗaya ilahirin ajikinsa, wani irin rawa lips ɗin sa keyi tamkar mai jin tsananin sanyi, ga kuma wani irin azabebben buguwan da zuciyarsa keyi da masifaffen ƙarfi yana bada sautin  dib-dab-dib-dab.

     

    Haka zalika Khausar dake rungume dashi, itama haka zuciyarta ke bugawa,

    sake ƙanƙamesa tayi da ƙarfi tana mai tura kanta afaffaɗan ƙirjinsa da bottle din gaban rigar suka buɗe, hakan ya bawa fuskarta damar mannewa farar afaffaɗan ƙirjinsa dake ƙawace da tattausan gashi baƙi mai sulɓi.

    Wani irin fusga numfashinta keyi saboda tsananin tsoro da firgici da tashin hankali, haka yasa idan taja numfashin sai ta ɗauki sekon talatin Kafin ya dawo.

    Ko kaɗan Moddibo bai da wani kataɓus sabida yanayin da suka kasance a ciki, sake rungumeta yayi tare da cusa kansa atsakanin wuyanta da kafaɗarta.

    Daga can bayansa yake jiyo sautin ƙaran mota tana danna masa ɗiyyyyttt-ɗiyyyytttt, yasan shi akeyiwa hon ɗin, amman sam baya jin zai iya koda kwakwaran motsine.

    Shi kuwa mai motar dake bayansa, ganin shiru bai motsa bane, yasa ya ɗan ratsa ta gefensu ya fuce yana dan leƙawa ganin ko lafiya kasancewar. Atsakiyar titin suke ganin babu wani alamun hatsari ko damuwa yasa ya wuce.

     

    Moddibo kuwa da ƙyar ya iya buɗe Idanunsa tare da ɗago kansa still ruwan ake sheƙawa zuwa yanzu harda  ƙanƙara yana jin yanda sautin ƙanƙarar ke sauka asaman motarsa fat-fat-fat ko kaɗan baya kallon komai duk da kuwa gashi idanunnasa abuɗe suke, amman ina ganinsa ya ɗauke makanta ta meye gurbin ganinsa, ya zama sam baya gani, kana ji yake jikinsa kamar shanyeyye.

    Daƙyar ya iya ɗaga hannunsa tare da dafe kansa da yake jin wani irin jiri na fizgarsa tare da sarawa, da sauri ya sake sunkuyar da kansa akan wuyanta kana ya sake rungumeta da ƙarfi baki ɗaya ya rasa wani irin yanayi yake ciki.

     

    Khausar kam sam batama san wani irin yanayi take ciki ba sam bata cikin hayyacinsa, hakan yasa ta sake rungume Moddibo da ƙarfi,

    Jin yadda take liƙewa a jikinsa ne, yasa shima ya saƙe yi mata wani irin amintaccen rugguma tare da fesar da wani irin raunataccen numfashin yana mai shaƙan ƙamshin jikinta.

    Itama sake rungumesa tayi cikin mawuyacin hali tana neman numfashi domin numfashinta na ƙoƙarin ɗauke wa gaba daya tsananin tsoro da tashin hankali ya bayyana asaman fuskarta, duk da sanyi garin da kuma yanda ake tsuga ruwa amma goshinta na na tsastsafo da zufa kana jikinta ya ɗauki ɗumi.

     

    Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa da ficewar hayyaci Moddibo ya sake rungumeta yana jin ɗumin jikinta kana yana mai furta.

    “Hasbullahu wani’imal wakin, Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n La’ilaha Illah anta subhanaka Inni ukuntu Minal Zhalimin, Allahumma Ajirni fii musibati wa’ahlifli khairan minha”,Kana ya cigaba da karo to duk wata addu’a da tazo bakinsa cikin fitar hayyaci, Allah ya sani kuma shine shaidarsa ya rasa yanayin da yake ciki shin mutuwa zaiyi ne, koko kuma sumewa yake shirin yi,

    domin jinsa yakeyi  tamkar yana tafiya cikin sararin samaniya ne bisa gajumare,

    ji yake tamkar fuka-fuki garesa ya kasa tantance shin mafarki yake ko kuma azahirance ne kana yakasa tantance shin a sumen yake ko kuma amace yake, cikin rashin sanin madafa ya cigaba da karanto duk wata addu’a da tazo bakinsa.

    Yayin da numfashi Khausar ke cigaba da fusga,

    adduo’i ya cigaba dayi cikin ikon Allah Albarkanci Adduo’i da yake da kuma zuciyar namiji dake da dakiya yasa yafara dawowa hayyacinsa amma still Idanunsa basa gani mai kyau.

     

    Ganinta kwance ajikinsa tana fuzgar numfashi yasanya shi sa. Lallausan tafin hannunsa ya tallabo fuskarta tare buɗe manyan idanunsa da ƙyar dan har yanzu dishi-dushi yake gani, idanu ya tsirawa kan goshinta daya tsats-tsafo da zufa, sai kuma ya rumtse idanun da karfi kana ya buɗesu tare da zura ido na daƙiƙu bakwai sai kuma ya juya idanun zuwa kan wuyan hijabinta daya zame daga kanta zuwa kafaɗarta yalwataccen sumar kanta mai tsayi da ƙamshi ya zuba agadon bayanta, yayinda saura kuma ya zuba asaman fuskarta, kallonsa ya mayar kan fuskarta jin, yanda numfashinta ke fusga. Idanunsa ya mayar kan ƙirjinta da sauri ya lumshe idanun sai kuma ya buɗesu, ganin yanda numfashinta ke hawa da sauka alamun zata sume a ko wanne lokacin.

     

    Ganin tana gab da sumewane ya sanyashi sun kuyar da kansa kaɗan, zuwa kan fuskarta kana ya ɗaura lips ɗin da suke masifar  rawan sanyi akan karan hancinta, lumshe manyan idanunsa da suka sauya launi zuwa ja yayi, tare da fesa mata sanyayyan numfashinsa domin dai-dai ta mata nata numfashin, domin  duk da tsoron da kuma firgicin da yake ciki hakan, bai sanya numfashinsa ɗauke wa ba, kana yana kallon fuskarta wanda akowani lokaci zata iya suma, sai kuma ya sanya hannu ya toshe hancinta tare da ɗaura sanyayyan lips ɗin sa akan nata ya riƙa hura mata iskar bakinsa mai ɗumi da kamshi ceto rayuwa zuwa gareta,

    Wani irin dogon numfashi taja mai nauyi tare da fesar dashi da ƙarfi, cikin daƙiƙu kaɗan numfashinta ya soma dawowa dai-dai kana duk abinda ke faruwa idanunta na lumshe.

    Sannan har zuwa lokacin hannunta na kan mararsa, saman yatsarta na kan hudan cibiyarsa, sannu ahankali numfashinta ya dai-dai ta sai dai har zuwa lokacin bata dawo hayyacinta ba,  still kuma ruwan ake cigaba dayi tamkar da bakin ƙwarya ita ko sai wani irin sakewa tayi tare da lafewa a jikinsa tana shaƙar ƙamshinsa.

    Shi kuwa Moddibo sannu ahankali ya fara dawowa hayyacinsa da nitsuwarsa.

    Sake lafewa Khausar tayi ajikinsa tare da lumshe Idanunta domin ganin abun take kamar mafarki, ko kuma mutuwa tayi tsaban masifar tsoron rugugin da take.

     

    Shi kuwa Moddibo sannu ahankali cikin ikon Allah ya dawo hayyacinsa, kana har zuwa yanzu tsikar jikinsa na tashi yayin da kansa ke juyawa jiri na ɗibarsa.

    Ahankali ya sauƙe idanunsa akanta data manna a ƙirjinsa, yayinda  tattausan suman kanta ya baje aƙirjinsa, kallonta yakeyi kamar ya samu sabuwar halitta, kana aƙasan ransa ke mgnar zuci,

    Wai yaya haka ne? Mekw faruwa? Wai ma waye ni?

    Ya tambayi kansa da kansa,

    Kaine Moddibo, sannan wannan Khausar ce kwance ajikika tana rungume dakai cikin yanayin da ma’aurata ne kaɗai ya halatta su kasance ciki.

    Wani sashi na zuciyarsa ya bashi amsa.

    Lokaci ɗaya kuma jikinsa ya sake ɗaukar rawa far-far tamkar wanda ake sheƙa masa ruwan ƙanƙara lips inshi kuwa, wani irin masifeffen tsuma sukeyi,

    lumshe idanunsa yayi jin jikinsa babu kuzari kona misƙala zarratin, ji yake tamkar an zare masa lakar jikinsa cikin sanyi da rashin kuzari dake tare dashi.

    A hankali ya sake birkitota tare da ɗago kanta ya ɓanɓareta daga jikinsa gani yayi Idanunta alumshe.

     

    Ita kuwa Khausar ji take tamkar cikin bacci take, ko kuma suma ta kasa fahimtar kalar yanayin

    da dai take ciki,

    Shi kuwa Modibbo kanta ya tallabe da hannunsa ɗaya yayin da ɗaya hannu yake ɗan marin  fuskar yana faɗin.

    “Ke! Keh!!”.

    Shiru bata motsaba, hakan yasa ya sake ɗan fizgo muryasa tare da faɗin.

    “Khausar! Khausar!!”.

    har zuwa lokacin tana rungume jikinsa

    For the first time arayuwarsa da bakinsa yafara kiran sunanta.

     

    Fuskarta yake ɗan yiwa ƙananan maruka ahankali kana cikin wata Sanyayyar murya mai cike da tattausan lafazin yake fadin.

    “Khausar!, Khausar!! Khausaaaar!!!”.

    Lumshe idanunsa yayi shi kansa bai san yana da irin wannan raunataccen muryar ba, ya rasa taƙamemmen yana yin da yake ciki, yayin da aƙasan ransa so yake ya mata faɗa da tsawa da masifar ta sauƙa jikinsa, amma ya kasa kasancewar har zuwa lokacin bai gama dawowa cikin ainihin nutsuwarsa ba.

    Kumatunta ya cigaba  da ɗan mara yana faɗin.

    “Khausar!, Khausar!!”.

    A hankali kanta ya zame  daga hannunsa ya tafi gefe luuuh kamar sumammiya.

    Lokaci ɗaya zuciyarsa ta buga da ƙarfin gaske tare da jin tsinkewar zuciya ganin yanda Kanta yayi kamar ta mutu!.

     

    Cikin ɗaga sautin murya ya sake ɗan marin kuncinta tare da cewa.

    “Khausar, *Lelewal*”.

    Khausar kuwa still Idanunta na lumshe take Jin sautin muryar Moddibo na kiran sunanta kamar amafarki ko kuma daga can sama.

    Sai kuma ta sake jiyo sautin muryarsa da alamun kiɗima yake  cewa.

    “Ya salam Lelewal meya faru? me ya sameki?”.

     

    Ahankali ya sanya hannunsa tare da ture hijabinta kana ya sanya hannunsa aƙirjinta wanda har yana iya jin tudun caɓɓullen ta ahannunsa ji yayi ƙirjinta na bugawa da ƙarfi-ƙarfi.

    Hannunsa ya cire tare da sunkuyar da kansa har suna shaƙar numfashi bakin juna, bakishin yakai kan kunnenta kamar meyu mata raɗa yake faɗin.

    “Lelewal tashi! Lelewal buɗe idonki!! Lelewal kalleni”.

    Lumshe Idanunsa yayi akaro na barkatai tare da kai bakinsa cikin kunnenta kana cikin Sanyayyar murya mai taushi yace.

    *“Fattanah!”.*

    Dogon numfashi taja tare da sauƙe nan-nauyan ajiyar zuciya tare da buɗe Idanunta sai kuma ta sake runtsesu da sauri gani take tamkar har yanzu rugugin akeyi kana walƙiyar zai iya kashe mata Idanu.

    Bayan kamar daƙiƙa ɗaya ta sake buɗe Idanunta still yana ronƙofe akanta yana shaƙar ƙamshin numfashin dana gashinta dake baje.

    Yayin da har zuwa yanzu hannunta ke cikin sa yatsunta guda uku nakan cibiyarsa tafin hannunta da sauran yatsu biyun nakan ainihin mararsa ta danne.

    Cikin wata sanyayyar murya ya tsira mata idanu tare da faɗin.

    “Lelewal”,Ya faɗa still yana tallafe da kanta.

    Buɗe Idanunta tayi sai kuma ta sake rufewa,

    Akuma dai-dai lokacin Moddibo da itan duk suka gama dawowa cikin hayyacinsu tare da nutsuwar.

    Cikin sauri tare da fushi

    Moddibo ya kalleta a tsawace yace.

    “Keee!!! Tafi can Mage uwar fitina tashi akaina ko in kakkaryaki”.

    Ya dire mgnar cike da tsawa tare da yarfa mata mari da bayan hannunsa.

    Shi kansa jin maganar yayi ta fito daga zuciyarsa kai tsaye kamar an fisgo a bakinsa.

     

    Azabure Khausar ta buɗe Idanunta dake lumshe tare da janye jikinta daga nasa amma still hannunta na kan cikinsa tana murza cibiyarsa.

    Wani mugun kallo mai cike tarin kufula, takaici, tsuyan zuciya, da tarin ƙunci ya watsa mata firgitaccen kallo. Ta da ɗaga hannunsa cikin wani irin masifeffen rawan jiki da gigitan yanayi yasanya tafin hannunsa ya finciko hannunta dake kan cikin sa da masifar ƙarfi ya yarfa hannun nata har saida ta saki ƙara, dan ji tayi kamar zai ɓalla mata hannun.

    Shi kuwa a take kuma tsikar jikinsa ta mimmiki ta tashi.

     

    Cikin tsananin tsoro da firgici Khausar ta janye jikinta kana ta koma ta mannu da jikin kujera tare da rungume kanta a can gefen jikin kujeran motar tana mai jin raɗaɗin marin.

    Moddibo kuwa da ƙarfi ya rumtse idanunsa sabida  wani irin masifaffen har bawa da yaji zuciysrsa nayi da masifar ƙarfi, lokaci ɗaya wani azabebben zufa ya wanke sa kana rawan da lips ɗinsa keyi ya tsananta karkarwa yayin da har hakoransa ke rawa har suna bugun juna saboda wani masifaffen abu da yaji yana yawo cikin kwanyar kansa, wani irin baƙon yanayi yaji ya taso masa da azaban ƙarfi, abinda bai taɓa jiba atsawon shekaru.

    Cike da dauriya da kuma fushi ya figi motar da gudu yayin da zuciyarsa ke wani irin azalzala idanunsa kuwa har yanzu dishi-dishi suke gani sanna, sai wani irin rawa jikinsa da lips inda keyi, cikin mintunan da basu gaza goma ba taji yayi Parking aƙofar gidansu.

     

    Cikin tsananin tsoro da ruɗu ta buɗe murfin motar, cikin sauri ta fice batare data lura da ɗan kwalinta da kuma hankief ɗin ta dake kan cinyar Moddibo ba.

    Da ƙarfi yafi gi motar cikin mintuna kaɗan ya isa gidan yana parking ya fito.

    Lokacin ɗaya ya jiƙe jikib saboda ruwan da ake cigaba dayi kamar da bakin ƙwarya.

    Cak ya tsaya Atsakiyar gidan nasu, ruwan na sauƙa atsakiyar kansa saboda masifeffiyar baƙon yanayi  da yake ji ga kuma suya da raɗaɗin da zuciyarsa keyi, na firgicin saɓawa Ubangiji da yayi, tsoron Allah da tarin damuwa ne ya sanya idanunsa fara zubda wasu irin zafafan hawaye masu ƙuna.

    Rumtse idanun da yayi tare da furta.

    “Astagfirullah wa,atubu ilaik, Ya Allah kaine mafi sanin zuciyata, Yah Allah ka gafarta min ya Allah ka shafe min wannan zunubi, ya rabbi kada ka sake bani damar sake saɓa maka Yah Allah ka sani ban taɓa aikata makamancin hakaba,”. Gaba ɗaya muryarshi rawa takeyi, yayinda idanunsa ke kwaranyar da hawaye.

    Duk da ruwan na dukansa amma ko kaɗan baiga alamar zaiji sauƙin abinda ke damunsa ba. ji yayi tamkar ya ɗora hannunsa a ka ya rinƙa ihu da kururuwa. Duk da dauriyarsa kuwa, bai san sanda kuka ya kubce masa, domin duk sauƙan ruwan akansa ji yake kamar ana  ƙara rurumashi wutar fitina a jikinsa,  ga kuma ƙuncin zaciya da yake ji,

    Har lau  haƙoran sake dukan juna suke nusa bada sautin Ƙat-ƙat-ƙat baki ɗaya jikinsa rawa yake tamkar mazari ahankali ya sunkuyar da kansa gani yayi yadda muhallin sa ya sake masifar nuna zalamarsa.

     

    Cikin mawuyacin hali ya dafe kansa da hannunsa na hagu murya narawa yace.

    “Wannan wace irin masiface? shin wannan wani irin abune mai wuyar jurewa me yake yafaru dani ne wai? Shegiyar yarinya mai fitintinun al’amura, ya Allah ka isarmin da cutar dani da tayi, Yah Allah kaga ita ta riskeni kaine shaida ni ban nufetaba, Allah ka isarmin kan wannan muguwar yarinya mai jikin zalumci Astagfurullah”.

    Ya ida maganar tare da fashewa da kuka, still dai yana tsaye acikin ruwan yana cigaba da dukansa, ganin sam kuma abin nasa yaƙi nitsuwa ne yasa ya nufi hanyar sashensa domin sakarwa da kansa ruwan ɗumi koda zaiji sauƙin abinda ke damunsa, abakin faradan Falon sa ya tsaya tare da zare rigar dake jikinsa kana ya zame wandon ya shanya ya rage daga shi sai boxer Kai tsaye toilet ɗin sa dake cikin Bedroom ɗinsa ya nufa yana shiga ya sakarwa da kansa ruwan ɗumi batare daya cire boxer ba yana tsaye ruwan ɗumin ya cigaba da zuba akansa amma babu abinda ke yawo a idanunsa kamar lokacin daya rungumi yarinyar ga wani masifaffen ƙamshinta da yake ji ajikinsa da ƙarfi ya matse jikinsa waje ɗaya kana cikin tsanananin tsoron Allah ya ci gaba istigfari.

    “Astagfurullah wa’atubu Ilaik ³ ya Allah na tuba kayafe min wannan abin da nayi. Ya Ubangijina na tuba”.

    Kai kawai yake girgiza wa cike da tashin hankali mara misaltuwa daya rufe idanunsa babu abinda yake hange face yanayin da suka kasance amota.

     

    Acan ɓangaren Khausar kuwa da gudu ta shiga gida tare da wucewa Falon su.

    Tsaye ta samu Mommyn ta cikin yanayin damuwa da tashin hankalin.

    Mommy na ganinta ta saki ajiyar zuciya mai nauyi tare da cewa.

    “Alhamdulillah Khausar kin dawo, gaba ɗaya hankalina ya tashi na kasa zaune na kasa tsaye, tunda Haiydar ya dawo ya faɗa min yanda ku kayi da Amina!”.

    Ida mgnar taba kallon yadda jikin Khausar ke ɗigar da ruwa ga wani rawa da jikinta keyi cikin  jin ƙai da tausayawa tace.

    “Amina bata kyauta min ba. Wallahi Allah Amina bata taɓa yimin abinda ya ɓata min rai irin na yau ba, ya za’a yi cikin wannan hadarin cikin wannan yanayin ta baro min ke a makaranta.

    Yanzu waya dawo dake?”.

    Cikin karkarwa na tsoro da sanyi  ga kuma zogin mari tace.

    “Uhhhmmm”.

    Ita kuwa Mommyn cikin sanyi tace.

    “Yanzun nan dama Abbanku nake jira? ya dawo dan baya nan na faɗa masa kina cikin makaranta. Yanzu yana dawowa ne akan zai ɗaukeni muje can ɗin”.

     

    Cikin sanyi da yanayin tsoro da kuma ruɗu Khausar ta dubi Mommy yayinda, jikinta ke rawa kamar zata faɗi.

    Kallonta Mommy tayi cike da tausayinta ta girgiza kai kana tace.

    “Gashi na sani Khausar yanda kike rikicewa idan kikaji rugugi kike fita hayyacinki idan kika ga walƙiya bare kuma kiji tsawa!.

    Gashi yau kuma ruwan yazo da wasu irin tswawwaki masu ban tsoro.

     

    Cikin rawan jiki ta sanya hannunta dake ta karkarwa ta janye Hijabinta kana ta kalli Mommyn Muryanta na rawa tace.

    “Yah Jameel ne ya kawo ni”.

    Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe kana tace.

    “Kai Ubangiji Allah yayi masa albarka. Allah ya saka masa da mafi kyawun sakamakon”.

    Kai Khausar ta gyaɗa still jikinta na tsuma tace.

    “Ameen Mommy bari in cire kayana”.

    Ta ida mgnar tare da wucewa Bedroom ɗin ta tana shiga ta kalli hannunta lokaci ɗaya ta sake shiga sabon tashin hankali, cike da damuwa ta yarfe hannunta kana tace.

    “Nashiga uku Ni Faɗimatuzzahara  ina nasanya hannu na! Ni Batula?”.

    Duk da cewa tana cikin tsoro amma tana sane da inda  ya zaro hannunta kai tsaye toilet ta Wuce tare da cire kayan jikinta ta sakarwa kanta ruwan ɗumi sabulu ta ɗauka ta mulke hannunta dashi kana ta shiga gogawa ajikin tiles dake jikin bangon tana Girgiza Kai kana tana mai Furta.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Astagfirullah wa’atubu ilaik Subhanallah ya Salam Allah na tuba”.

    Da ƙyar ta iya yin wankan ta fito bayan ta ɗaura alawalan tare da buɗe Siff ta ɗauki dogon riga na roba baƙi ta sanya har zuwa lokacin jikinta na ƙamshin tularensa Sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da Sallah kana ta riƙe carbi tana hawaye da Istigfari.

     

    Acan ɓangaren Moddibo kuwa bayan ya gama wanka al’wala ya ɗaura tare da fitowa har zuwa lokacin zuciyar sa na tsaye alamar zai samu nitsuwa Siff ya buɗe tare da ɗaukar Boxes ya sa sai kuma ya tsaya yana kallon kansa, ya tabbata idan yasa Jallabiya mutane zasu iya fahimtar halin da yake ciki wani dogon tsaki yaja.

    “Mitsssssssss!!! Yar iskar yarinya”.

    tare da sanya hannunsa ya matse muhallinsa da ƙarfi wai ko zai masa biyayya cikin yanayin tashin hankali ya kalli kuma sunkuyar da kansa tare da faɗin.

    “Wai wannan wacce iriyar Masifa ce!?”.

    Sake buɗe sabbin boxers ɗin sa dake cikin leda yayi ya ciro wani ƙarami wanda yake zaton zai masa kaɗan shiyasa ma bai taba sakasu ba,

    Cikin yamutsa fuska ya sanyashi,

    sosai ya matsesa sai dai har zuwa lokacin al’amarin  azimunne.

     

    Wani boyel baƙi mai kyau ya ɗauka ya sanya kana ya feshe jikinsa da turarukansa cikin sanyin jiki ya fita zuwa Masallaci ya gabatar da sallah Azahar.

    A wunin wannan ranan dai baki ɗaya haka yayita agigice.

     

    Acan gidan Lamiɗo kuwa Hajiya Bunayya ce zaune akan 3sitter yayin da Amina ke gefenta riƙe da kofin shayi yana tururi.

    Anutse Hajiya Bunayya ta juya tare da kallon Amina data kai kofin shayin bakinta kana tace.

    “Amina yanzu ya kuke da Malam Jameel ne? nifa nagaji da wannan al’amarin kullum sai munga Abu kamar yaci sai kuma kiga abu ya sake ta ɓarɓarewa!”.

    Gyara zama Amina tayi tare da ajiye Cup ɗin tea kana tace.

    “Hmmm ba gwara ma muba akan Samira Sani, sufa duk abinda suke kamar anshuka dusa shi Moddibo na nan kamar Waliyyi baya fahimtar karatunta shu’umanci bare ya ratsasa kamar kurma baya ma sauraronta bare kuma ya sake mata fuska”.

    Ta gumi Hajiya Bunayya tayi tana cigaba da sauraren Amina.

    Amina ta cigaba da cewa.

    “Amma kinga gwara Ni dama Malam Jameel Yana da sauƙin kai sannan yanzu ya daina shash-shareni idan na gaishesa yana Amsawa cikin sakin fuska da mutunci mun koma kamar da duk da dai dama haka halinsa yake ga kowa”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “Kawai dai abinda nake gani Ummah kawai Abbah ya masa magana idan Abba ya masa magana kan cewa Ina son sa bazai ƙini ba, saboda yana da kirki yana da mutunci da kawaici ko ba komai kuma gidan dala yake domin nifa kuɗin mahaifinsa nafiso, badon kuɗin da suke da shiba, nafi son miji irin Modibbo mishkili, ba sake fuska dan sunfi iya soyayya”.

     

    Ajiyar zuciya Hajiya Bunayya ta sauke tare da gyara riƙon wayarta kana tace.

    “Anya Amina za’ayi hana kuwa? Ai gwara dai mujawo hankalinsa zaifi, kuma batun kuɗi yoh dama ai shi mukewa bauta domin duk abinda nake kashewa a wurin boka ina lissafawa kina shiga daga ciki zaku biyani”.

    Kwaɓe Fuska Amina tayi kana tace.

    “Kayya Ummah tun yaushe mukeyi amma abin baya wani kamasu  gwara ma Malam Jameel Idan munyi munga Abu ya kama kwana biyu sai kuma ya dawo baya kula har kata! anata ƙara lissafin kuɗin da zan biya”.

    Kai Ummah ta gyaɗa kana tace.

    “Gaskiya dai kam in dai hakan zaiyi sai in faɗawa Mafaifinku yafi min kwanciyar hankali ma amma ko. Abbanku baza mu fuskance sa kai tsaye haka ba dole sai anja hankalinsa akan maganar”.

    Ta gumi Amina tayi tare da cewa.

    “Toh Ummah acanza wani boka mana?”.

    Saurin Kallonta Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Wani boka muke dashi da yafi wannan?,Duk aikin sai yace ana wasa dashi sannan aikin kuɗi yake buƙata sosai kuma kinga Yanzu bani da kuɗi sosai Amina, kuma ai tunda muka canza boka Zurau wannan duk aikin da yake min yana ci”.

    Taɓe baki tayi tare da cewa.

    “Gaskiya Ummah asamu ayi aikin nan idan muka samu nashiga gidansu zamu fanshe duk kuɗin da muka kashe!”.

    Jinjina kai Ummah tayi kana tace.

    “Zanyi ƙoƙarin hakan in Allah ya yarda”.

     

    Acan ɓangaren su M Jameel kuwa bayan ya shiga gida ya sauya kayansa zuwa blue jeans da farin t-shirt mai dogon hannu kana ya gabatar da Sallah Azahar Yana idarwa ya nufi sashen Mahaifinsa zuwa lokacin ruwa ya tsaya bakinsa ɗauke da sallama ya shiga kana ya zauna kusa da Abbansa.

    Kallonsa Abba yayi bayan sun gaisa yayi gyaran murya tare da cewa.

    “Dama batun Company Adamawa ne acikin kayayyakin da aka kawo muga ya yanayin ingancinsu akwai atomfofi,

    Gyaleluwa da kuma sauran kayayyakin ya kamata kaje”.

    Jinjina kai M Jameel Yayi kana yace.

    “Toh shikenan Abba yaushe ne tafiyar”.

    Kallonsa Abbah yayi kana yace.

    “Insha Allah tafiyar zai kasance idan kun gama jarrabawar ɗaliban ku da zasu gama makarantar bana nasan zuwa lokacin hankalinka ya kwanta Asma’u da Bashir sun kammala Secondary School”.

    M Jameel kuwa jingina kansa da jikin kujeran yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.

    “Hakane kam Alhamdulillah yanzu kam na gama  sun gullarsu Asma’u”.

    Dai-dai lokacin da Hajiya Karima ta shigo falon Abba na cewa.

    “Kaga yanzu shikenan tun da kagama da wannan shungullan gaba ɗaya duk abinda ya shafi shungullana da kuma harƙoƙina, kasuwancina duk zan danƙasu ahannunka Babana.

    Domin ni girma ya fara zuwa Inason hutu”.

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Toh shikenan Abba babu damuwa duk abinda kace shi za ayi da izinin Ubangiji”.

    Murmushi Abba yayi har cikin ransa yake jin ƙaunar ɗan nasa saboda yanda yake masa biyayya ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.

    “Toh Nagode Allah yayi maka Albarka”.

    Duk abinda suka tattauna Hajiya Karima na rakuɓe tana jin tattaunawar su Amaryan Abban Jameel Hajia Turai ta shigo ganin Hajiya Karima atsaye yasa ta faɗin.

    “A’a Lafiya kike tsaye anan Hajiya Karima?”.

    Cikin sauri ta juya, sai asannan Abba da M Jameel suka juya suka ganta tsaye.

    Murmushin da bai wuce saman laɓɓabanta ba tayi kana tace.

    “Yanzu na iso ina gyara labule nai”.

    Ita dai Hajiya Turai batace komai ba ta ƙarasa shiga falon kana Hajiya Karima tabi yo bayan suka cigaba da hira.

     

    Washe gari.

    Cikin sanyin jiki da damuwa Khausar ta shirya cikin Uniform ɗin ta dake haska fatarta  baki daya ta kasa sakewa da zaran ta tuna inda ta sanya hannunta sai taji tashiga matsanancin tashin hankali.

    Cikin sanyin jiki ta fita tare da nufar inda motarsu ke fake Amina ce tafito hannunta riƙe da   lunchbox ɗin Aminu dai-dai lokacin da Lamiɗo ya fito daga sashen Gimbiya Dadu da  fuska a tsuke ya kalli Amina tare da cewa.

    “Banaso Amina kada ki sake yi min abinda kikayi jiya banaso haka ki kiyayeni! Ki kiyayeni!”.

    Ƙasa tayi da kanta kana tace.

    “Toh Abba kayi haƙuri”.

    Sannan ta juya ta  shiga, kana su Khausar ma suka shiga mota ko acikin mota Khausar jingina bayanta da jikin kujera tayi tare da damƙe hannunta ahaka har suka isa makarantar.

     

    Anutse ta fito ta tashiga hall da suke Exam kai tsaye bencin da number ta ke kai ta nufa tare da zama kana ta dafe kanta ba jimawa Malam Isa ya shigo ya fara raba musu Booklet da questions na Economics.

    Kallon Khausar data dafe kanta da hannu biyu yayi kana yace.

    “Lelewal meke damunki?”.

    Da sauri ta ɗago kanta ta kallesa sai kuma ta girgiza kanta cikin sanyin murya tace.

    “Ba komai Malam”.

    Question peper ya ajiye mata kana ya cigaba da rabawa sauran.

    Cikin mutuwar jiki Khausar ta riƙa yin amsarin Questions ɗin tun kafin a miƙa wa wasu Questions pepar tuni ta gama Amsawa kwantar da kanta akan deks ɗin tayi tana godewa Allah daya sa basu da Exam din Moddibo da batasan da idon da zata iya kallon sa ba.

     

    Moddibo kuwa tunda yashigo makarantar ya wuce office ɗin su ya zauna cikin zullumi da damuwa.

    Ahankali M Jameel ya fito daga class da yake teaching hannunsa riƙe da booklet ya nufi Office ɗinsu bakinsa ɗauke da Sallama yashiga zaune ya samu Moddibo idanunsa na rufe kana lips ɗin sa na rawan sanyi ahankali.

    Booklet ɗin ya ajiye tare da zama gefensa kana yace.

    “A.J meke damunka?”.

    A hankali Moddibon Ya jujjuya idanunsa dake lunshe yayi kana ya Girgiza masa kai tare da cewa.

    “Bakomai”.

    Kallonsa M Jameel Yayi kana yace.

    “Ya zaka ce min bakomai A.J ke faɗa min meke damunka ko dai baka da lafiya ne?”.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da gyaɗa masa kai.

     

    Cikin damuwa M Jameel yace.

    “Toh meke damunka?,Ka faɗa min abinda ke damunka mana”.

    Sai asannan Moddibo ya buɗe Idanunsa cikin raunin murya tamkar mai shirin fashewa da kuka yace.

    “I don’t know J I really don’t know what’s wrong with me WLH BAN SANIBA, BANSAN MEKE DAMUNA BA J”.

    Da Mamaki M Jameel ya kallesa kana yace.

    “How A.J kamar ya bakasan meke da munka ba”.

    Langwaɓar da kai Moddibo yayi cikin yanayin damuwa da tashin hankali ya kalli M Jameel daya tsaresa da ido ya sauƙe Idanunsa ƙasa kana yace.

    “Bansani ba J bansan meke damuna ba Na dai san bana jina dai-dai ina cikin ɗimuwa”.

    Ya ida maganar yana mai lumshe idanunsa sam ya rasa taya zai fara faɗawa M Jameel yanayin da yake ji ajikinsa.

     

    Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe kana yace.

    “To ko dai zazzaɓi ne?”.

    Girgiza kai Moddibo yayi still cikin raunin murya yace.

    “A’a”.

    Ahankali M Jameel ya sake cewa.

    “Toh ko Kanka ke ciwo?”.

    Still Kai Moddibo ya sake Girgiza masa alamar a’a.

    Numfashi M Jameel ya fesar kana yace.

    “Toh ko dai cikin kane?”.

    Nan ma kai Moddibo ya Girgiza kamar zai fashe da kuka.

    Tagumin M Jameel Yayi kana yace.

    “Toh meke damunka?”.

    Lumshe idanu Moddibo yayi cikin sanyin murya mai rauni ya buɗe idanunsa tare da kallon M Jameel daya tsaresa da Ido kana yace.

    “J bana jina dai-dai ina jin kamar akwai wani abu da nake buƙata amma bansan menene ba”.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “Toh me kake buƙata?”.

    Girgiza kai Moddibo yayi tare da buɗe hannunsa kana cikin sanyin murya yace.

    “Idont know J nima ban sani ba bansan me nake so ba amma inaji kamar akwai wani abu da ɗan Adam yake buƙata acikin rayuwarsa wanda nima nake buƙatarsa kusa sani, daga jiya zuwa yau amma bansan menene bane”.

     

    Kallonsa M Jameel Yayi tare da kallon yanda idanunsa suka sauya launi zuwa Ja tun safe da suka zo ya lura da hakan tamkar mai mayen bacci kana ya lura da yanda lips ɗin sa ke rawa sannan ya lura da yanda bini-bini yake matse ƙafafunsa.

    M Jameel na cikin Kallonsa. Moddibo yayi miƙa tare da matse ƙafafunsa kana lips ɗin sa suka shiga rawa sai kuma ya runtse Idanunsa.

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “J kodai kana jin kana ɓuƙatar mace akusa da kai ne?”.

    Lokaci ɗaya Moddibo yaji zuciyarsa ya tsinke da masifar ƙarfi ajiyar zuciya ya saki tare da kallon M Jameel ji yake tamkar ya fashe da kuka ko zaiji sauƙin abinda ke damunsa  sunkuyar da kai ƙasa yayi cikin wata raunan’niyar murya mai sanyi yace.

    “Ban sani ba J”.

    M Jameel yace.

    “Toh mutafi gida mana tunda na gama abinda nake kai kuma naga kamar baka da komai”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana ya miƙe tare da yin miƙa da ayau ya zame masa jiki domin baya minti goma mai kyau sai yayi miƙa.

    Kallonsa M Jameel yayi dan yanda yaga Modibbonsa ya tashi ta saman rigar duk da kuwa boxes biyu ya saka duk dan ya suturta jikinsa ɗagowa M Jameel yayi tare da kallon fuskarsa yayi Murmushi.

    Fita Moddibo yayi M Jameel yabi bayansa dai-dai lokacin da aka kira sallar Azahar acikin masallacin dake makarantar.

    bayan sun Idar suka fito suka shiga mota M Jameel ke driving yayin da Moddibo ke gefen mai zaman banza idanunsa alumshe duk abin duniya ya Ishesa.

     

    Suna isa gida M Jameel yayi Parking ya fita kai tsaye sashen Innayi ya wuce ya karɓa musu abinci Moddibo kuwa cikin mutuwar jiki ya wuce sashen sa ya kwanta.

    Ba jimawa M Jameel ya dawo hannunsa riƙe da Warmers da kuma Plate kwance ya samu Moddibo akan 3sitter yayi rub da ciki idanunsa akan ƙofar falon.

    Ƙarasa shiga falon M Jameel Yayi tare da zama aƙasa kana ya kalli Moddibo da faɗin.

    “Saƙƙo muci abinci idan muka gama sai muje kaga Dr”.

    Girgiza kai Moddibo yayi cikin sanyayyar Murya yace.

    “Bana jin yunwa bana son cin komai”.

    Buɗe Warmer M Jameel Yayi tare da cewa.

    “Toh Meyesa haka J?”.

    Cike da raunin murya tamkar wanda ke shirin fashewa da kuka yace.

    “Ban saniba nima”.

    Dariya mara sauti M Jameel Yayi kana yace.

    “A.J Na fahimceka fa kamar *Mace* kake buƙata acikin rayuwarka!”.

    Cikin sauri Moddibo ya lumshe idanunsa jin suna tsats-tsafo wa da hawaye, miƙewa yayi tare da wucewa Bedroom ɗin sa yana shiga yasa key ya rufe.

     

    M Jameel kuwa jingina bayansa da jikin kujera yayi tare da fashewa da dariya harda riƙe ciki.

    Moddibo kuwa yana kulle ƙofar ya juya ya kwanta ruf da ciki tare da lumshe idanunsa yayin da ƙwaƙwalwar sa ta shiga tariyo masa moment da suka kasance acikin mota lokaci ɗaya Muhalinsa ya shiga harbawa da ƙarfi tamkar zai fisge ya fito, yayin da lips ɗin sa suka shiga rawa har haƙoransa na haɗuwa kar-kar-kar.

    Batare daya shirya ba yaji hawaye suna bin kuncinsa shi kansa baisan meyake so ba bai san meke faruwa dashi ba yakasa sanin yana yin da yake ciki ji yayi kawai yana kuka hawaye na bin kuncinsa yana sheshsheƙa.

    Miƙewa yayi cikin rashin sanin madafa shin ya zaiyi da wannan jarabar tun jiya yake fama da zaran ya rufe Idanunsa yanayin da suka kasance da yarinyar ne yake gani.

     

    M Jameel kuwa dambun shin kafa dayaji vegetables da soyayyen naman kaza dake tashin ƙamahi ya zuba a Plate ya fara ci yana cikin ci ne wayarsa dake gefensa ya hau ruri.

    Ahankali ya sanya hannunsa ya ɗauka Turkey Kawai ya gani babu Number.

    Picking yayi tare da kaiwa kunnensa yana dariya yace.

    “Yaushe kaje Turkey?”.

    Murmushi Jalaludeen yayi kana yace.

    “Na kusa kwana biyar acan ai”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.

    “Lallai dai kam yayi kyau ya gida”.

    Gyaran murya Jalaludeen yayi tare da cewa.

    “Lafiya wai meyasamu Aliyu ne”.

    M Jameel na ajiye cokalin hannunsa yace.

    “Nima kaina ban sani ba”.

    Dariya Jalaludeen yayi kana yace.

    “Mace ta fara shiga rayuwarsa kenan.

    Aure fa yake da buƙata yana da ƙaƙƙarfan sha’awar da tuntuni na kwantar masa da shi”.

    Zare Ido M Jameel Yayi kana yace.

    “Auuu Jalaludeen kenan kaine ka maida mu waliyan dole?”.

    Cikin sauri Jalaludeen yace.

    “A’a Ni ban mayar daku mata ba, amma dai kawai nasan Aliyu nada ƙarfin sha’awa na masifa idan har aka bar shi da wannan sha’awar zai iya zame masa masifa kana zai iya jefashi acikin damuwa gashi naga burinsa a lokacin yayi ilimi mai zurfi, kuma in ka tuna a lokacin yana yawan fama da ciwon ciki”.

    Dafe kunci M Jameel Yayi yana saurarensa.

    Murmushi Jalaludeen Yayi kana ya cigaba da cewa.

    “Tun haɗuwar mu na farko kafin ku fahimci wanene ni kafin ku fahimci komai akaina, kana tun kafin afahimci wanene ni asan komai akaina na bashi abinda yasha wanda ya karyar masa da ƙarfin sha’awarsa har yake ji kamar baya buƙatar mace acikin rayuwarsa”.

    M Jameel ya gyara zamansa tare da cewa.

    “Ikon Allah”.

     

    Jalaludeen kuwa cikin yanayin su na can yaci gaba da cewa.

    “Toh ajiya akwai abinda yafaru ko dai mace tashiga rayuwarsa ko dai akwai macen data kama jikinsa wannan dalili yasa gaba ɗaya takarya alƙadarin abinda ke jikinsa!”.

    Ajiyar zuciya M Jameel ya saki kana yace.

    “Toh fa”.

    Murmushi Jalaludeen yayi tare da faɗin.

    “Kai kuma kwaɗayin ka ne ya kaika dana bashi maganin yana cikin sha kawai ka amshi kofin kasha shiyasa kuka kasance atare haka amman ai kai naka ba kamar nashi bane ”.

     

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Amma dai gaskiya Jalaludeen baka da mutunci”.

    Dariya Jalaludeen yayi kana yace.

    “Nifa bance komai ba gaba ɗaya abinku lafiya lau yake kawai dai sha’awar ce na kwantar”.

    Girgiza kai M Jameel Yayi kana yace.

    “Toh yanzu shi kuma wannan ya za’ayi dashi dan yanzu wallahi ya tashi ya tafi ɗaki kamar zaiyi kuka”.

    Murmushi Jalaludeen yayi kana yace.

    “Kukan ma yakeyi yanzu”.

    Ware ido M Jameel Yayi kana yace.

    “Lallai dai kam maza sun gamu da aiki kenan”.

    Jinjina kai Jalaludeen yayi tare da cewa.

    “Gaskiya yanayin daya ke ciki ne awahale yake haka ya wuni jiya still haka ya kwana gashi kuma yau ma ya wuni haka”.

    Cike da tausayawa M Jameel yace.

    “Toh yanzu ya za’ayi ?”.

    Girgiza kai Jalaludeen yayi tare da cewa.

    “Gaskiya ban sani ba dan bani da yanda zan mishi kawai abune daya zo masa babu yanda za’ayi haka zaita rayuwa mafita ɗaya ne kawai yayi ƙoƙari yayi aure”.

     

    Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da cewa.

    “Ok zamu yi ƙoƙari muga mai ya dace tunda gashi dama duk abinda ya dace mun gama”.

    Jinjina kai Jalaludeen yayi kana yace.

    “Masha Allah amma yanzu ka samu ruwan ɗumi kasa masa laimun tsami yaji kana ka sanya zuma yaji sai ka bashi yasha zai ɗan ji sauƙi”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana yace.

    “Toh shikenan ba matsala mun gode”.

    Sallama sukayi tare da katse kira.

    Miƙewa M Jameel Yayi yashiga cikin kichen dake falon ya buɗe Flaks dake ɗauke da ruwan tea ya zuba a Cup lemun tsami ya duba yaga babu rufe Cup ɗin yayi ya nufi cikin gadin ɗin gidan ya tsunko guda biyar sannan ya dawo ya wanke tare da matse su duka acikin shayin kana ya buɗe kofin roban zuma yasa.

    Fita yayi a kichen ɗin ya nufi Bedroom din Moddibo yayi Knowking ƙofar.

     

    Dai-dai lokacin da Moddibo ya cire kayan jikinsa ka ya zura Jallabiya kasancewar boxers ya takure masa jiki har yana jin mallakinsa na yimasa ciwo saboda yanda ya takuresa ya hanasa miƙewa cikin gajiyawa ya mike ya cire boxes ɗin tare da cewa.

    “Bari naga iya inda zaka tsaya uban ƴan zalamammu”.

    Yayi maganar yana kallon jikin nasa daya miƙe ya tsaya acikin Jallabiyar.

    Muryar M Jameel yaji yana cewa.

    “A.J ka buɗe min ƙofar mana in baka magani”.

    Daga ciki Moddibo ya buɗe masa ƙofar.

    Kallonsa M Jameel Yayi sai kuma ya kalli yanda  ya ɗaga rigar kawar da kai gefe yayi yana jin dariya na neman kufce masa.

    Kofin dake riƙe ahannunsu ya miƙa masa.

    Cikin Sanyayyar muryarsa yace.

    “J Me wannan?”.

    M Jameel ya Kalli kofin kana yace.

    “Kasha mana zaka ji sauƙin abinda ke damunka na fahimci meke damunka A.J”.

     

    Moddibo bai sake cewa komai ba ya amshi Cup ɗin ya koma bakin gado ya zauna tare da kafa kansa ya shanye tass kana ya ajiye kofin, cikin ikon Allah lokaci ɗaya yaji zufa ya fara sauƙa masa Atake yafara jin abinda ke damunsa na sauƙa kaɗan-kaɗan amma still jikinai ɗin na nan amiƙe ahankali yaji lips ɗin sa ya daina rawan zamewa yayi ya kwanta akan gadon yana sakin ajiyar zuciya akai-akai.

     

    Acan gidansu Khausar kuwa zaune suke afalon  Mommy suna cikin hira ka jiyo sallama.

    Cikin sauri Haiydar ya ɗago kansa tare da cewa.

    “Laaaaah….!

     

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin kowa a kanki yar uwa 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276, sai in saki a Group na ɗin da zanke posting. Ko kinga littafin SAKAYYAH a waje na satane*

     

     

     

     

     

    *By*

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 7

    Sakayyah 7

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 7_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE NE YAN UWA, BA WAI FREE BOOK BANE! INA GAMA SAKIN FREE PAGE, KO KINGA an fiddashi waje na satane. Na kuma Yaseen ne doguwa. Dan haka ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa biya ki karanta*

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace wanda bani da haufi kansa 7k ne kacal sai dai yar musilar robace., Kana masin Daɗi har Maɗigan yana da masigar kyau da tsatstsafo da ni’ima, wlh wasu in sunyi amfani dashi pan biyu sabida yadda zakiyi ta tsiyaya. 5k ne Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa 8k ne, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan wanda wlh koda sanyin cikin mahaifane fes yake wanke shi kuma ko mai ciki zata shashi baida illa, kama budurwa ko bazawara duk zasu iya sha harma da yara. Set ɗin da 10k ne innkuma za’a sa miki komai rabi-rabi ne 5k ne, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

     

    Moddibo ta hango zaune a gefen gabas yana fuskantar tata, bima’ana yana kallon yamma, zaune yake  akan wani dutse mai masifar sheƙi kana wasu mutane biyu na tsaye gefen hagu da damansa,

    Sannan da buta gabansa bisa alama  Al’wala yayi domin farin yashin daya mamaye wajen daga gabansa a jiƙe yake, kana yana mai fidda wani irin ni’imtaccen ƙamshi maisa ɗan Adam lumshe ido. Baki ɗaya haske ya mamaye ilahirin filin wajen hakan yasa itada Moddibo suna fuskantar juna yayin da M Jameel da Adda Adama matar Baffan Umaru  suma ke fuskantar juna.

    Kana lambu dake  can bayanta kuwa yake feso musu iskar yammaci dana lambun suka haɗu waje ɗaya daga sama kuma rana ne yayi Ja yana shirin faɗuwa.

    A hankali ta sauƙe numfashi mai nauyi tare da lumshe idanunta.

    Da sauri ta buɗe idanun nata, jin wani irin sassayan sautin dariya mai cike da shauƙi da Moddibo yakeyi.

    Cike da mamaki duk suka zuba mishi idanu.

    Yayinda Adda Adama ma tuni ta fara dariya mai sauti.

    Ita kuwa Khausar haka nan taji jikinta yana tsuma tare da sakewa, da sauri ta juya ta kalli  M Jameel ga mamakinta shima ita yake kallo, da idonshi ya nuna mata Moddibo yana mai yin lallausan Murmushi, da sauri ta maida kallonta kan Kekkyawar fuskar Moddibo, wacce tunda take a rayuwarta dashi bata taɓa ganin yayi dariyar da har haƙoransa na gaba zasu baiyana ba.

    “Fatabarakallahu fih hasanil khaliƙeen”.

    Ta furga a saman lips ɗinta, lokacin da ta sauƙe ƙwayar idanunta kan fuskar Moddibo, da sauri ta kuma lumshe manyan Idanunta sabida wani irin masifeffen sheƙi da ta hango sajenshi dake kwance lip-lip yanayi,

    Sautin dariyarsa da har yanzu yake ne yasata saurin buɗe idanun.

    “Subahanallah, tsarki ya tabbata ga Ubangiji da ya halicci wannan bawa ya kuma bashi waɗan nan haƙoran”.

    Ta faɗa a fili lokacin da taga ƙyellin da haƙoransa keyi har yana ɗauke mata idanunta,

    Lobgoɓar da kanta tayi bisa kafaɗarta.

    Wani irin sassayan numfashi ta fesar tare da tsaida idanunta a kanshi.

     

    Shi kuwa Moddibo dariya yakeyi mai sayyan sauti wanda yake da daɗin ji, har maƙolloton wuyanshi yana ɗan haurawa yayi sama kana ya dawo ƙasa.

    Yayinda ya ɗaura tafin hannunsa kan ƙirjinsa.

    Cikin tsananin dariyar ya samu ya ɗan tsagaita tare da furta.

    “Astagfurillah watubu ilaik”.

    Sai kuma ya ɗago ya kalli M Jameel lokaci ɗaya kuma ya sake sakin dariya mai sauti yana cewa.

    “Astagafitillah Wayyo cikina”.

     

    Cikin rage girman idanunta take kallon gashin girarsa dake kwance lip.

     

    Jameel kuwa sai Murmushi yakeyi tare da girgiza kansa.

    Yayinda Adda Adama ma dariyar takeyi harda riƙe ciki.

    Ita kuwa Khausar gaba ɗaya ta kasa ɗauke idonta daga kansa.

    A haka har rana tayi mudun kuyanƙi alamun yana gab da faɗuwa.

     

    amma kafin ya faɗi saiya rabu kashi biyu.

    Yayinda Khausar kuwa ke zaune tana fuskantar yamma hakan yasata ganin abin.

    Atake hankalin ta ya tashi ganin yanda ranan ya rabu kashi biyu.

     

    Ita kuwa Adda Adama hannu tasa ta dafe ƙirjinta tare da faɗin.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n yau mun shiga ukun mu ku dubi yanda ranar tayi fa!”.

    Tana faɗin haka duk dariya da murmushin da sukeyi ya tsaya.

     

    Moddibo kuwa daga inda yake zaune ya ɗaga kansa sama tare da juyawa bayanshi kana a hankali yace.

    “Ya Salam  ya ilahi ya mujabat da’awati meke Shirin faruwa”.

    Cikin tsananin gigita da tashin hankali da firgici Khausar ɗin ta saki kuka mai cike da rauni tare da cewa.

    “Innalillahi wa innailaihi raji’un, hasbunallahiwani’imanwakil, mun shiga uku”.

    Sai kuma ta juyo ta kalli Moddibo da ya gyara zamanshi kana a hankali yace.

    “Babu abinda zai faru wanda Allah bai sani ba, Insha Allah Ubangiji zai mana maganin duk kan abinda yayi tsanani”.

     

    M Jameel kuwa kasa furta komai yayi sai hawaye dake kwaranya daga idanunsa.

    ita kuwa Khausar ganin M Jameel na Hawaye kawai sai itama tashiga yin kuka amma ba mai sauti ba.

    Cikin wani irin yanayin da bazai misaltuba Moddibo ya dubesa kafin yace.

    “Haba J. Kamar ba namiji ba addu’a ya kamata muyi duk kan tsanani yana tare da sauƙi”.

    Still dai M Jameel baice komai ba.

    Shi kuwa Moddibo cikin sanyin jiki ya fuskanci Khausar cikin wata iriyar murya yace.

    “Khausar tausayi na kike ji ne?”.

    Cikin kwaranyar hawaye ta gyaɗa mishi kai tare da sakin raunataccen kuka mai cushe numfashi, lokaci ɗaya numfashin ta ya fara cushewa yana ɗauke wa, cikin yanayi wahalar neman numfashi taga Moddibo ya…!

    Dai-dai  lokacin kuwa ta farka daga baccin da takeyi ciki  razana tare da kaɗuwa ta dafe kanta da takeji yana jujjuyawa.

    Kana duk da sanyi da ake tsulawa a garin wani irin zufane ke tsastsafo mata ta ko ina.

    Cikin sauƙe ajiyar zuciya,  ta juya gefen hagunta ta karanta A’uziyya ƙafa uku kana ta canza hannun kwanciyar ta zuwa dama.

    Sai dai sam baccin yaƙi zuwa mata, sai ta kama karatun Alqur’ani cikin sassayan sauti,

    Cikin ikon Allah ta samu bacci ya kuma yin awon gaba da ita.

     

    Baki ɗaya Wunin wannan ranan akasalance tayi koda abinci ta kasa ci haka zalika koda yawan surutu sai ta rage sosai mafarkin ya tsaya mata arai da zaran ta tuna irin mafarkin da tayi sai taji zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske.

     

    Da daddare cikin ikon Allah data karanta Alkur’ani mai girma tare da bin haddarta da Malam Liman ya bata sai taji sauƙin abin aranta duk da kuwa bawai ta daina jin tsinkewar zuciyar bane amma ya ragu sosai.

    Da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare Khausar suna zaune a farfajiya gidan Hajja Nana su uku ita Yaya Abba da kuma Dije suna hira jefi-jefi take sanya musu baki aciki daga ƙarshe ma ta miƙe tace zata je ta kwanta sai Dije ma ta miƙe ganin haka yasa Yaya Abba ya musu rakiya har gida.

     

    Washe gari:Da safe still haka Khausar ta tashi bata da wani ku zari koda abinci ne ta kasa ci iyakacinta tasha Tea ko ruwan kunu sannan ta kasa faɗawa kowa irin mafarkin da tayi domin jikinta ya mutu sosai da mafarkin.

    Da daddare ba kinta ɗauke da Sallama tashiga gidan Hajja Nana.

    Asaman laɓɓa Hajja Nana ta amsa mata Sallamar tana binta da harara dan tunda taƙi markaɗa mata wake take jin haushi ta.

    Ita kuwa khausar bata masan Hajja Nana nayi ba ta nemi waje ta zauna tare da kallon Hajja Nana tace.

    “Yunwa nakeji ki bani abinci zanci”.

    ta faɗa tana kallon ƙorenta dake jere guda goma sha Uku.

     

    Harara Hajja Nana ta wurga mata tace.

    “Gashi ki ɗauka ki ci”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da Matsawa jikin ƙoren tashiga buɗewa ɗaya bayan ɗaya tana dubawa saboda taga gidan Malam Liman anyanka kaji cikin Sa’a kuwa tana buɗe ɗayan taga Jan miyar dage-dage da kuma tuƙeƙƙen tuwon shinkafa.

    Ta gyara zamanta tare da wanke hannunta ta fara cin tuwon cikin Mintuna kaɗan ta cinye tass sannan ta kuma janyo wani Ƙoren dan sosai take jin yunwa sannan bata wasa da cikinta dan ita dai ko ciwo bai cika hanata cin abinciba karo na forko kenan a rayuwarta da abu ya tsaya mata a rai har ya hanata cin abinci na kwana biyu son ta Tara yunwar shiyasa.

    ta cinye ƙore  biyun tas dan dama tuwon ba wani mai yawa ake samata ba tunda akwai yawan kanukan.

     

    Hajja Nana kuwa juyawa tayi da mamaki ta kalleta kafin tace.

    “Yanzu har kin cinye tuwon nan”.

    Kai Khausar ta gyaɗa mata tace.

    “Na cinye mana kuma yanzu ma ƙarawa zanyi dan yunwa nakeji rabo na da abinci tun shekaran jiya da daddare fa sai dai in ta Shan abu mai ruwa-ruwa”.

     

    Taɓe baki Hajja Nana ta kuma yi tace.

    “Toh bubbuga rumbu ga shican ki ƙara ki cinye duka ma in Kinga dama”.

    Ta Faɗa tare da tura mata wani akoshin.

     

    Ɗauka Khausar tayi kamar wasa ta cinye dake abincin ba wani da yawa ake sawa aƙoron ba dake sun san cewa ƙorenta da yawa mafi yawan lokuta ma loma ɗaɗɗaya takeyi ako wani ƙoren idan tayi loma sha uku ya wadatar mata a dai cikin tsohuwa ta kuma tsinci nama ta cinye to shiyasa ba’asa mai yawa.

     

    Ita kuwa Hajja Nana ganin yanda Khausar ke cin abinci yasa tayi zaton gatse take mata ta harareta da faɗin.

    “Mutum kamar jaki wannan ci haka ki cinye wannan ƙoren ki cinye wancan”.

    Ta ida maganar tare da sake tura mata wani ƙoren.

     

    Ita kuwa khausar ta ƙoshi amma saboda ta ƙular da ita yasa ta janyo ta buɗe naman kan abincin ta cinye sannan ta gutsiri kamar loma biyar ta zuba akwanan dake empty.

    Wani kwanon Hajja Nana ta kuma tura mata still ta cinye naman ta kuma gutsura ta zuba a sauran kwanon.

     

    Hajja Nana ta dube ta cikin tsareta da ido tace.

    “Wai har yanzu baki ƙoshi ba?”.

     

    Khausar cikin yamutsa fuska ta gyaɗa kai kana tace.

    “Eyyy ban ƙoshi ba”.

    Wani akoshin Hajja Nana ta sake tura mata, Khausar kuwa laluma ta cigaba dayi idan taji da nama ta cinye ta gutsits-tsira tuwon ta bari.

     

    Ita kuwa Hajja Nana kamar wacce akace ta leƙa taga aika-aikan da Khausar keyi da tuwon ta miƙe cikin fushi tace.

    “Shegiyar yarinya gantalelliya  ni kike nunawa barikanci, ‘yar banza kinje kin zauna gidan Mayu kema kin koma kamar Mayya, sai cin nama kamar kura, wato ma duk naman kike lalubewa dan mayta ai dai na sani in dai ba cikin zanine da keba ai yaci ki ƙoshi”.

    Ya mutsa fuska Khausar tayi tare da riƙe ƙugunta tace.

    “Naci ɗin idan ni Mayya ce kinsan inda na samu maita, tunda nazo saboda shegen maƙo ko zabuwa ɗaya kin kasa yanka min gaki da Zabbi kamar zasu kashe ki ga shanu kuma aina Babana ne”.

     

    Salati Hajja Nana tayi tare da fashewa da kuka.

    Kasancewar duk dare aƙofar gidan ta suke zama yasa Baffa Umaru daya ji sautin kukan ta ya miƙe kasancewar Allah ya bashi kunne komai ƙanƙantar sautin abu ya kan iya ji.

     

    Ganin Hajja Nana na kuka yasa Baffa Umaru nufarta tare da cewa.

    “Addah Nana Meya faru?”.

    Nuna Khausar tayi  da hannu kana tace.

    “Wannan ‘yar Usmanu har zata min gori wai gadon Ubanta na riƙe kaji shegiyar gantalalla yarinya dan ma Allah yayi dan ke macece!”

     

    Ƙasa da murya Baffa Umaru yayi yace.

    “Dan Allah Addah Nana kiyi haƙuri kinsan yarinta ke damunta idan ta girma ba zatayi ba”.

    Ya ida maganar tare da jan hannun  Khausar suka fice waje.

     

    Bayan sun fita ya juya ya kalleta yace.

    “Haba Khausar kidena ki koyi yanda zaki zauna da manya kinga Addah Nana tsufa ya kamata tana buƙatar rarrashi da lallami, kinga duniyar nan ba matabbata bace idan yau kaine gobe ba kai bane ita rayuwar nan bata da tabbas, ki koyi magana mai daɗi ke idan Mahaifinki ina ita fa ɗan ta ne data haifa acikinta kuma ɗan ta mafi soyuwa agareta kada ki sake haka kinji Khausar am”.

     

    Ta gyaɗa masa kai da faɗin.

    “Toh shikenan Insha Allah bazan sake ba”.

    Ya shafa kanta yana murmushi yace.

    “Allah ya miki albarka kizo muje gidana mu kwana zansa ayanka miki Zabbi kici tun da mun gama cin abinci”.

     

    Kai ta gyaɗa tare da yin murmushi tace.

    “Toh”.

    Ya riƙe Hannunta suka tafi suna tafiya suna hira har suka isa gidan bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga gidan Adda Adama ta fito daga ɗaki tare da amsa musu sallamar.

     

    Kallon Adama Baffa Umaru yayi yace.

    “Akwai nama ne?”

    Adama tace.

    “Eh akwai Zabbin da aka yanka da yamma yanzu nake ƙarasa dahuwarsu”.

     

    Yace.

    “Toh shikenan ki ƙara sa gyarasu ki kawo ma wannan Kuran Birnin taci”.

    Dariya Khausar tayi tana zama akan taburman da Adama ta shimfiɗa musu, shi kuma Baffa Umaru ya zauna daga gefenta yayin da Adama taje taci gaba da aikinta kasancewar farin wata ya haska ilahirin garin.

     

    Anutse Baffa Umaru ya kira sunanta da faɗin.

    “Khausar”.

    Ta ɗago kanta tana kallon fuskarsa acikin farin watan kafin tace.

    “Na’am”.

    Idanunsa kanta yace.

    “Kinsan kamannin Babanki?”.

    Kai ta girgiza masa tare da faɗin.

    “A’a bansan kamanninsa ba”.

    A sanyaye yace.

    “Amma kin san akwai Baffanki ai yayan Babanki Hammadu Ɓadamaya ko?”.

     

    Tace.

    “Eh amma Ɓadamaya yake ko?”.

    Yace da ita.

    “Eh yana can Ɓadamaya dashi da Iyalansa da kuma ahalinsa gaba ɗaya.

    Insha Allah wataran Zakije shida Babanki Uwa ɗaya Uba ɗaya”.

    Kai ta jinjina da faɗin.

    “Eh Mommy na tafaɗa min cewa inada Baffa yana can Ɓadamaya dashi da matarsa da kuma ‘Ya‘yansa”.

     

    Murmushi yayi yace.

    “Toh idan kinje zaki ga mai kamannin Mahaifinki sak da sakin  sunan sa Aliyu shine yake kama da Mahaifinki ya gaji Babanki komai da komai kuma shine aka aurawa yayarki Nenne”.

    Kai ta gyaɗa tace.

    “Toh yaushe zanje in gansa?”

    Yace.

    “Kinga kamannin Mahaifinki kamar balarabe kinga ba yabon kai ba mutanen Rugar mu duka kyawawa ne amma kyawun mahaifin ki ya fita da ban farin Mutum ne kyakkyawa ga kuma gashin kansa mai tsawo da sheƙi wannan gashin naki ma shi kika ɗauka”.

     

    Idanunta ta lumshe cike da kewar mahaifinta sai kuma ta buɗe su tace.

    “Aikam nasan gashin sa na ɗauka ba Mamansa ba da kai agwagwiye”.

    Murmushinsa ya faɗaɗa da faɗin.

    “Ina Addar tawa kike yiwa ba’a itama tsufa ce yasa gashinta kaɗewa”.

    Murmushi tayi tace.

    “Ai lalle kam”.

     

    Sai kuma ta dai-dai-ta nutsuwarta tace.

    “Ku kuma dama nan ne asalin Rugarku?”.

    Kai ya gyaɗa mata yace.

    “Eh asali nan ne Rugar mu iyaye da kakanni”.

    Tace.

    “Toh Meyesa ita Hajja Nana ta dawo nan kuma ina ne asalin garinsu Babanmu?”

    Murmushi yayi yace.

    “Asalin garinsu Babanki yana da nisa lokacin da Addarmu tayi aure ta daɗe kafin tazo ta samu haihuwa to data haifi na farko sai Allah ya sake kawo wasu akan lokaci ta haifi yara uku sai Allah yayiwa kakanki daya haifi Babanki rasuwa,sai ta nemi zata dawo to data nemi zata dawo sai sukace tabarmu su yaran ita kuma tana son yaran sosai sai tace Inde akan dukiya ne tabar musu duka subarta ta taho da ‘Ya‘yanta”.

    Zama Khausar ta gyara tana sauransa da kyau.

    Shi ko a hankali ya cigaba da cewa.

    “Dake dangin Mahaifinki mutane ne masu karamci sai sukace su ba dukiyar su suke buƙatar ba kawai dai suna so suriƙa ganin ɗan uwansu ne sannan ita macece kada subar mata nauyi amma tunda tana son Zama da ‘ya’yanta baza su hanata ba sai suka bata duka gadon Mahaifinki da kuma na Baffanki da ƙannensa mata biyu hadda mai sunanki.

     

    A ranar da tashigo Rugar nan tashigo da aƙalla shanu sun kai ɗari biyu sannan harda raƙuma da tumakai duk gadon sune aka ɗauka aka basu suka dawo”.

    Sassayan ajiyar zuciya ta saki tana jinjinawa lamarin.

    Baffa Umaru ya cigaba da cewa.

    “Toh tun daga lokacin ne zamanta ya dawo nan daga baya Allah yayiwa mahaifan mu rasuwa da gida huɗu ne kacal anan mahaifinmu su suka fara kafata da duk nan dajine mahaifinmu ne ya sare bayan rasuwar mahaifinmu da kuma mahaifiyarmu,

    itace ta zame mana Uwa da uba tun muna yara itace ta renemu nida Mahaifinki mun taso tare atare mukayi wasan ƙasa ta raine mu tare ta zame mana kamar uwa Shiyasa mu awajen mu Adda Nana ba ya bace kaɗai uwa ace a garemu”.

     

    Ita kuwa khausar Ajiyar zuciya ta kuma saki tare da faɗin.

    “Ikon Allah Allah mai iko Mabuwayi Gagara misali”.

    Murmushi Baffa Umaru yayi yace.

    “Kin gane ko mu Addah Nana Uwace agaremu ba Ya ba sannan maganarta Umarni ne awajenmu muda ‘Ya’yanmu babu mai saɓa mata har jikokin mu kinga keda kika zo kina wannan abin sai akaga lallai ta samu karan tsaye”.

    Murmushi Khausar tayi tace.

    “Lallai dai kam,to amma ina ne asalin su Babanmu?”.

    Murmushi yayi yace.

    Gobe zan faɗa Miki Idan Allah yakaimu rai da Lafiya zan ƙara sa baki labarin insha Allahu”.

     

    “Toh Allah ya kaimu goben lafiya”. Cewar Khausar

     

    Cikin sauƙe numfashi yace.

    “Naji ma Addah Nana na cewa kafin ki koma Abbah zai kaiki Ɓadamaya kije kiga Baffanki da ‘Ya‘yansa”.

     

    “Toh ina kuma ance da nisa?”.

    Khausar ta tambaya

     

    “Eh danisa amma ai tafiyar wuni ɗaya ce zaku isa”.

    Ya bata amsa.

     

    Miƙe sawunta tayi bisa taburmar tare da cewa.

    “Toh shikenan ba matsala, Insha Allahu zamuje, nima ingansa sannan kodan inga mai kama da Babana”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Sannan kuma kafin ku tafi zakuje kiga Addarki ‘yar Baffanki da yake Ɓadamaya tana nan Rugar Fulani dake ma ƙobtanmu Adda Ikki aikin santa?”.

    Murmushi tayi tare da gyaɗa masa kai tace.

    “Eh na santa ai itakam tana zuwa har gidanmu ta dubani duk dangin Babana ma ita nafi sani”.

    Yace.

    “Toh shikenan Zakije wajenta kiyi kwana biyu”.

    Tace.

    “Tun kwanaki nake cewa Hajja Nana zanje in dubata, tace min ba yanzu ba, wai in bari ingama sanin mutanen garin nan”.

    Adama dake sauraron  hiransu ta miƙe hannunta riƙe da kwanan da ta gama gashin Zabbin dake ta tashin ƙamshi sannan ta haɗo musu da madara mai ɗumi.

    Akan tabarmu ta ajiye musu su duka ukun atare sukaci.

     

    Gyatsa mai sanyi Khausar kana tace.

    “Kai gaskiya naci naji daɗi Nagode”.

     

    Bayan sun kammala ne Khausar tashiga ɗakin Adama ta kwanta Adama kuwa ta nufi ɗakin mijinta suka kwanta tare.

     

    Can cikin dare kamar misalin ƙarfe biyu Baffa Umaru ya miƙe zaune, tare da kasa kunnensa sosai wanda hakan ya kasance ɗabi’arsa ne,

    domin shine Garkuwar Rugar tasu,  jin motsin tashin sa yasa Adama miƙewa ita ma ta zauna, kusa dashi tana faɗin.

    “Lafiya”.

     

    Ajiyar zuciya ya saki da faɗin.

    “Naji tsayuwar mota daga can nesa sannan naga haske yashigo har cikin garin nan kamar da akwai wani abu ko dai munyi baƙi ko kuma wani abu!”.

     

    Ahankali tace.

    “Toh yanzu fita zakayi kenan?”.

     

    “Dole in fita ai Adama idan ban fita ba ‘yan uwana zan bari wani abu yazo ya ritsa da mune ai bazan bari ba dole in fita inga ko menene”.

    Ya faɗa a hankali.

    Ita kuwa Adama  riƙe hannunsa tayi fuskarta na bayyanar da tashin hankali tace.

    “Nikam ina tsoro wallahi”.

    Da sauri yace.

    “Kada ki damu Insha Allah babu abinda zai faru wanda Ubangijin bai sani ba”.

     

    Kai ta girgiza kana tace.

    “Kai rashin network ɗin garin nan yana damun mu wallahi, kaga da akwai network tunda yawanci kowa yana da waya zaka kik kira su awaya kowa ya fito kaga idan yaso sai sufito ku haɗu Atsakiyar garin amma Ni ina tsoron fitarka kai kaɗai”.

    Suna cikin Maganar ne sukaji antura ƙofar gidansu anshigo Murfin ya fadi ƙasa Kifff kasancewar ba wani Murfin kirki bane gadon kara ne da gwafa aka haɗa.

    Cikin han zari ya mike ya tsaya.

     

    Itama miƙewa tayi da saurin ta riƙe hannunsa tace.

    “Fita zakayi dan Allah kada ka fita ka tsaya dan Allah kar ka fita”.

    Ya juya ya fuskanceta yace.

    “Ya kike so inyi idan ban fita ba kina jifa anshigo gidan nan”.

    Yana ida maganar ya fin cike hannunta dake cikin nasa ya fita.

    Cikin sauri ta shari gabansa ta fito ya zama na itace agaba shi yana bayanta.

     

    Suna fitowa idanunsu ya sauƙa akan mutanen uku dake sanye cikin baƙaƙen kaya hannunsu riƙe da bindigi da kuma toch ligh mai masifar haske.

    Arazane Adama tace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakin”.

    Ƙaran buɗe ƙofa da kuma sautin Muryan Adama ne ya fito da Khausar daga ɗaki wacce farkawanta babu daɗewa tana fitowa sukayi saurin kashe mata ido da hasken toch ligh dinsu ita da Adama.

     

    Cikin daga Murya suka ce da Adama

    “Ki matsa agabansa kada jini ya taɓa ki ki matsa kada mu illataki!”.

    Aruɗe tace.

    “In matsa agabansa!?Bazan matsa ba, ku suwaye ne? sannan me kuke nema? me kuka zo yimana acikin daren nan?”.

     

    Ɗaya daga cikin sune yace.

    “Kashe sa muka zo yi!”..

    Cikin tsananin tashin hankali tace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n hasbunallahiwani’imanwakil.

    dan Allah kada ku kashesa,me yayi muku zaku kashe sa?,Meyesa?”.

     

    Ɗaya daga cikinsu ba wanda yayi magana da farko ba yace.

    “Saboda yana hanamu rawan gaban hantsi zamu kashe sa muga takan tsiya bashi yace taurin kai ba”.

     

    Baffa Umaru kuwa murmushi yayi mai cike da Jarumtaka da kuma rashin tsoro yace.

    “Ni zaku kashe?,To idan kunga na mutu kwana nane ya ƙare,Kuma Ubangiji shi ya ɗauki raina.

    Amma ku baku isa ba babu mai rayawa babu mai kashewa sai ubangiji.

    Dan haka raina baya hannunku kuma ajalina baya hannunku idan kunga na mutu ma kada kusa aranku ku kuka kashe ni!”.

    Ya ida maganar tare da zabura zai shiga ɗaki dan ɗauko kwari da bakasan.

    Ita kuma Adam da saurin riƙesa dai-dai lokacin da suka harbesa  akafaɗarsa na dama.

     

    Ƙaran harbin ne ya tashi gaba ɗaya ilahirin mutanen garin Aɓangaren Hajja Nana kuwa tana tashi daga bacci sanadiyyar ƙaran harbin ta dafe kanta da faɗin.

    “Wayyo Umaru na Allah ka kare mana Umaru” domin shine mutum na farko daya faɗo mata arai cikin rawan jiki ta miƙe tare da ɗaukar zaninta ta ɗaura kana ta ɗauki mayani ta yana.

     

    Aɓangaren Baffa Jauro yana miƙewa yace.

    “Umaru”.

    Ya kira sunan sa cikin daga murya.

    Baki ɗaya ‘Yan uwansu da sauran jama’a babu wanda ya faɗo masu arai sai Baffa Umaru ko wannensu daya farka zai ce.

    “Wayyo! Umarunmu”.

     

    Shi kuwa Umaru juyawan da zai yi sai suka samu damar sake harbinsa ahaƙarƙarinsa na hagu.

    Cikin ƙarfin hali da ɗaga sautin Muryar sa yace.

    “La’ilah ha Illallahu Muhammad Rasulullahi(S.A.W) Adda Nana ki yafemin yau kam zasu kashe ni ki yafemin kece madadin Uwa awajena duk abinda nayi ki yafemin yau kam sun kasheni sun kashe ni,Yaya Jauro, Yaya Sadu, Yaya, GarGa, Yaya Liman, Yaya Garba,Yaya Sale yau kam sun kasheni sun cire muku ɗaya cikin goma kun zama ku tara!”.

     

    Adama kuwa Aruɗe ta riƙesa jikinta na kyarma taja numfashi amma ta gagara sakewa.

    Ita kuwa Khausar numfashin taja amma ta gagara sakewa saboda tsananin ruɗu da tashin hankali da tashiga kamar zata shiɗe!.

    Ihun da kiran sunan da yake yasa suka janye toch ligh ɗin su dake fuskar Khausar da Adama suka mai dashi sama wannan dalili ya bawa Khausar damar kallon fuskokinsu da kyau amma baki ɗaya jikinta ya sandare bata da wani kataɓus ɗin motsawa.

     

    Su kuwa ƙirjinsa suka saita suka sake harbinsa akwai wani ƙaton tukunya agefen  ya ratsa ya ɓula.

    Shi kuwa Baffa Umaru ƙirjinsa ya dafe da faɗin.

    “Laila Ha’illalhu Muhammad Rasulullahi (S.A.W)” Shikenan rai yayi halinsa.

     

    Su kuwa mutanen garin baki ɗaya gidan Baffa Umaru suka nufo ko wannensu na rataye da kwari da bakansa sukuwa jin hayaniyar mutanen yasa suka ɓulla ta bayan gidansa suka fice tare da zuwa inda suka bar motarsu suka shiga.

     

    Shi kuwa Baffa Umaru ta cikin tukunyar gefensa ya faɗa jini nata ɓulɓula.

    Hajja Nana ce farkon shigowa yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa tana isa tsakiyar gidan,

    Ƙofar dakinsa ta nufa, tana isa inda yake ta janyo gawar ta rungume tana kuka tare da faɗin.

    “Umaru! Umaru!! Umaru!!! Yau kuma mai zan gani gawar Umaru zan riƙe ahannuna kamar yanda na riƙe gawar Usmanuna!”.Cikin kuka sosai take maganar.

     

    Su Baffa Jauro da sauran mutanen ne suka shigo sudai Allah Allah suke su ƙarasa cikin gidan suga abinda ya faru dashi sam basu yi tunanin bin bayan mutanen ba.

    Ita kuwa khausar hanyar da suka bi suka fita take nuna musu da yatsa ta kasa furta komai bare kuma ta taɓuka wani abun Yaya Abba ne da ya shigo yace.

    “Yayane Khausar!?”.

     

    Cikin matsananci kuka da tashin hankali tace.

    “Yaya Abba sun gudu sun kashe shi sun gudu sunbi ta nan na gansu sunbi tanan!”.

    Azabure Matasan suka bi wajen ina tuni sun shiga motarsu sun gudu sukuma su Baffa Jauro, Baffa, Sadu da sauran rungume gawar ƙaninsu sukayi suna kuka.

    Hajja Nana kuwa tattaɓa jikinsa tayi, Sadik yace.

    “Baba mu ɗaukesa mu kaisa asibiti”.

     

    Sake rungume gawarsa Hajja Nana tayi tace.

    “Saddiƙu wani asibiti zamu kaisa bayan sun kashe sa baya numfashi bashi da rai!?”.

    Jauro ne ya karɓesa ya duba shima ya rungumesa ganin ya rasu Baki ɗayan su akan Gawarsa suka kwana.

    Ita kuwa khausar gaba ɗaya ta rikice ta duburburce bata taɓa gani ankashe mutum agaban ta ba sai lokacin tayi kuka har ta godewa Allah manyan Idanunta sunyi luhu-luhu dasu ba abinda ke faɗo mata arai kamar yanda sukayi hira dashi.

     

    Washe gari  akaje aka kira

    Ƴan sanda acikin gari suka je sukayi bin cike tare da rubuce-rubucen su na banza da wofi sannan akayi masa sallah aka kaisa gidan sa na gaskiya.

    Kana akazo aka zauna zaman makoki, Addar Khausar Ikki da zata je wajenta a Rugar Fulani ce tazo da taji labarin rasuwar Baffa Umaru tana zuwa kai tsaye gidan Baffan Umaru ta nufa duk ‘yan uwan suna can suna karɓan gaisuwa.

     

    Khausar na ganinta ta tashi da gudu ta Rungumeta tana kuka tace.

    “Addah Ikki agaba na agabana fa suka kashe shi sun harbesa sun kashe sa ya rasu har lahira!”.

    Addah Ikki tace.

    Kiyi shiru Khausar duk mai rai mamacine addu’ar mu yake buƙata”.

    Kai Khausar ta gyaɗa amma ta gaza tsaida kukan ta Ganin haka yasa Addah Ikki taja hannunta suka fita zuwa gidan Hajja Nana.

     

    Suna Shiga Khausar ta tsaya cikin Muryanta daya dishe da kuka tace.

    “Ni ina tsoro bazan shiga ɗakinta ba akwai kuliya”.

    Addah Ikki tace to kitsaya na koreta sannan tashiga ɗakin ta fito da kuliyar tasa awani ɗaki ta rufe.

    Sai asannan Khausar ta yarda tashiga ɗakin bayan sun zauna Addah Ikki ta zauna ta riƙa yi mata nasiyya tare da kwantar mata da hankali.

     

    Yaya Abba ne ya ɗauki wayarsa ya tafi Bishiyar ƙare zancenka ya kira duk dangi na nesa ya riƙa sanar da su har ya kira Baffa Hammadu na Ɓadamaya ya sanar masa.

    Shima washe gari Baffa Hammadu ya ɗauko iyalansa baki ɗaya suka taho da yammaci gab maghariba motocinsi su guda biyu ajere suka shigo Rugar kai tsaye ƙofar Hajja Nana suka nufa sukayi parking motocinsu.

     

    Ita kuwa Khausar na cikin ɗakin Hajja Nana manne da jikin Addarta Ikki suka jiyo Sallama,

    Addah Ikki ce ta miƙe da faɗin.

    “Laaa Umma na sannan sai Baffanta yashigo daga bayansa kuma wani kyakkyawan matsakaici mutun ne fari ƙal kamar balarabe yayin da Yaya Abba ke biye dasu abaya.

     

    Durƙusawa Khausar tayi tare da fashewa da kuka kalaman Baffa Umaru ne kawai keyi mata suwwa akunne.

    Rarrashinta Addah Ikki ta shiga yi tana bata haƙuri da kyar ta tsaida kukan tace.

    “Addah Jiya da daddare Baffa Umaru kece min Baffana na Ɓadamaya yana da wani ɗan sa dake tsananin kama da Babana Addah Ikki wannan shine ke kama da Babana?”.

    Cikin matsanancin kuka ta ida maganar.

     

    Kai Addah Ikki ta gyaɗa mata alamar Eh.

    Ita kuwa khausar kanta ta kife acinyar Addah Ikki ta cigaba da rera kukanta.

    Baffan Hammadu  ne ya riƙe hannunta ya cewa.

    “Khausar kiyi shiru kada kiyi kukan rashin Uba nima Mahaifine agareki ni zan tsaya Miki madadin Uba ako ina dan dai Banason rabaki da mahaifiyar kice Shiyasa na barki kike zaune tare da ita muddin ina raye zan maye Miki gurbin Uba”.

    Cikin raunin murya tace.

    “ Baffa Allah hokke sabbugo”.

    Ameen thumma ameen suka amsa.k

    Kana suka tafi gida Baffa Umarun.

     

    Bayan angama zaman Makoki  Khausar tabi Addarta Ikki can Rugar Fulani tayi kwana biyu sannan suka dawo bayan sun dawo akayi addu’ar bakwai Baffanta na Ɓadamaya yafara shirin tafiya sai asannan Khausar taga sauran ‘ya‘yan sa daya zo dasu harda Mata bayan sun sake ganawa ne suka tafi.

     

    Akwana atashi ba wuya Khausar ta cika Makwanni uku Arugar Jauro yaya yayin da Baffa Umaru keda mako biyu da rasuwa kullum ‘Yan uwansa matarsa  kuma jama’ar gari cikin yi masa addu’a suke domin baza su taɓa mantawa dashi atarihin rayuwarsu ba da kuma irin gwagwarmayar da yayi adomin kare rayukansu.

     

    GEMBILA

     

    Acan ɓangare makarantarsu Khausar kuwa ayaune aka gama gyara ilahirin makarantar daga nesa idan ka hango ginin ba zakayi zaton cewa a Gembila makarantar take ba koda a ƙasashen turawa ne sai ’Ya’yan wane da  wane saboda yanda aka ƙawata ginin Makarantar fentin ya kasance Maroon and White haka zalika gate din Maroon anda white ne daga sama An rubuta

    *Al’ANSAR ACADEMIC SCHOOL* Rubutun ma Maroon and White ne.

     

    Acikin harabar makarantar kuwa Moddibo ne tsaye hannunsa harɗe aƙirji ya yinda manyan idanunsa ke lumshe yana kallon tsarin ginin Makarantar da akayi wani irin Up stair cycle daga cikin harabar makarantar zagaye yake flowers masu kyau da tsari.

    M Jameel ne yace.

    “Gaskiya Moddibo kayi ƙoƙari makarantar yayi masifan tsaruwa”.

     

    Murmushin gefen baki Moddibo yayi wanda ke ƙarawa fuskarsa kyau yace.

    “Masha Allah haka akeso”.

    Ya ida maganar tare da juyewa cikin nutsuwarsa yake tafiya har suka fita acikin harabar makarantar suka shiga motarsu dake gefe afake.

    Moddibo ke Driving yayin da M Jameel ke gefen mai zaman banza ƙira’an Sudai’s na tashi cikin suratul Nisi’i Moddibo kuwa jinjina kai yayi ayoyin na ratsa sa.

    M Jameel ya juya ya kalli Moddibo da bakinsa ke motsi alamar karatun yake bi yace.

    “Moddibo kamar akwai motar dake bin mu  fa”.

    Kai Moddibo ya girgiza yace.

    “A’a ba binmu akeyi ba”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa still yana kallon mirror bai dai ce komai.

    Daga nan suka ci gaba da tafiya ganin still kamar binsu akeyi yasa Moddibo ya tsaya.

     

    Ga mamakin su ganin su tsaya yasa wancan motar tayo kansu gadan-gadan…!

     

     

    *Wasan fa yanzu aka farashi. Bakin zaren labarin sun kai 12 dozi. Kenan. Akwai ababen dake a duhu fa. Saninsu sai kun bibiyu Al’ƙalamin Shatu yar Aliyu Garkuwa. Jikar Muhammad Babayo Maiturare. Kana kuma (BODDIN DEDDE)*

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 15

    Sakayyah 15

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 15_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

     

    *Saura ƙiris FREE PAGE dai yazo ƙarshe in sha Allah mun kusa gamawa. Yar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci domin littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP. 09097853276. Kana in saki a Groups ɗin da zamuci gaba da posting.*

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

     

    Anutse Moddibo da M Jameel suka fito daga motar dai-dai lokacin da Malam Ahmad ya fito daga harabar gidan ganinsu yasa ya faɗaɗa fara’ar fuskarsa tare da faɗin.

    “A’a Masha Allah tagwayen Ummi kunzo?”.

    Murmushi sukayi Atare kana suka ƙara sa kusa dashi.

    Kallonsu Malam Ahmad yayi fuskarsa ɗauke da murmushi kana yace.

    “Sannunku da zuwa ku isa daga ciki zan dawo mu gaisa”.

    Kai suka gyaɗa masa atare kana suka nufi haraban cikin gidan shi kuma ya fice.

    Bakin su ɗauke da Sallama suka shiga farfajiyar gidan,

    Kusan a tare suka juyo suka kalli juna lokacin da idanunsu, ya sauƙa akan shimfiɗar ƙaton taburma da Ummi ta shimfiɗe asaman baranda kana ga wani lallausan Chanis capet dake fitar da ƙamshi da wasu manyan tuntuna guda uku ɗaya na tsakiya biyu na gefe da gefe sai manyan tire guda huɗu akai tiren farko na kayan fruit ne kama daga,Tuffa, Inabi, Gwanda, Dabino, Abarba, Ayaba, Kankana, Lemo duk anyi slinzing ɗinsu.

    Ɗaya tiren kuma Flaks ɗin tea ne da ma dai-dai-tan kofina masu kyau sai gongomin madara da Bounvita.

    Sai kuma ɗayan dake ɗauke da Flaks din kunu agefe, sai kuma na ƙarshe wanda yafi su girma manyan kulo-line masu kyau kula na farko Perpesoup ɗin jan naman rago ne daya dahu ligif yana fitar da ƙamshi sai ɗaya kulan kuma soyeyyen dan kalin  ne da ƙwai gwanin ban sha’awa.

    Jin Sallamar sune yasa Ummi saurin fitowa daga falo tare da faɗaɗa fara’ar dake Samar fuskarta kana tace.

    “Lale marhaba sannunku da zuwa Babana”.

    Murmushin gefen baki Moddibo yayi wanda ke ƙara masa kyawun fuskarsa kana ya lumshe idanunsa tare da faɗin.

    “Barka dai Ummina”.

    M Jameel kuwa baki ya tura cike da Shagwaɓa kana ya langwaɓar da kai Idanunsa akan Umminsa sai kuma ya kalli Moddibo dake ƙoƙarin zama akan shimfiɗar da Ummi tayi kana yace.

    “Ni dai gaskiya na fara kishi Ummi mai yasa tun da har haka kike son Aliyun nan bakisa min sunan Babban naki  ba nima ki riƙa cemin Babana?”.

     

    Murmushi Ummi tayi Idanunta akansa ta zauna kana tace.

    “To ai kaima Babana ne ko ka manta Kai takwaran kakan kane Baban-Babanka.

    Dariya mai sauti yayi kana ya shafa sajensa tare da cewa.

    “Ƙwarai kuwa haka Abbana ke kirana da Babana munyi raba dai-dai Ummi ta kiraka da Babanta Ni kuma Abba na ya kira ni da Babana”.

     

    Gyaɗa kai Moddibo yayi cikin yanayin sanyin Muryansa ya Kalli M Jameel kana yace.

    “Oho dai amma nine na hannun daman Ummi”.

    Murmushi Ummi tayi cike da ƙaunarsu kana ta zauna daga gefensu Idanunta akan Moddibo dake motsa bakinsa idanunsa alumshe alamar tasbihi yake.

    Ganin haka sai ta miƙe dan kar ta takura masa ta ɗan ɗaga sautin Muryanta tare da cewa.

    “Bashir ga Yayanka sun zo baka zo kun gaisa ba”.

    Cike da ladabi Bashir ya fito kana yace.

    “Ummi kaya na nake gyarawa yanzu nake so in fito”.

    Ya Ida maganar tare da zama agefen Moddibo kana yace.

    “Yaya Moddibo ina wuni ya Ibada?”.

    Moddibo kuwa buɗe idanunsa dake lumshe ya buɗe tare da ɗaura hannunsa akan Bashir yana shafawa kana yace.

    “Lafiya lau Alhamdulillah ya karatu?”.

    Bashir ya amsa da.

    “Alhamdulillah”,Kana ya maida kallon sa kam M Jameel dake motsa baki da alama shima tasbihi yake ya kallesa tare da cewa.

    “Yaya Jameel Ina wuni ya ibada?”.

    M Jameel ya Amsa da.

    “Alhamdulillah”.

    Miƙewa Bashir yayi ya koma ya cigaba da aikin da yake.

     

    Moddibo kuwa bayan yayi tasbihi sai ya koma Azkharul masa ƙarfe shida da minti Ashirin da biyu aka kira Sallar maghariba Plate din Dabino da Ummi ta ajiye musu agabansu Anutse Moddibo ya miƙe tare da ɗaukan ruwa ya kuskure bakinsa kana ya dawo ya zauna.

    Shima M Jameel miƙewa yayi ya wanke bakinsa dabino Moddibo ya ɗauka ya buɗe sanan ya sanya abakinsa bayan ya furta.

    “Zahabazzaba’u Wabitallatil,Uruƙu wasu batul Ajri Insha Allah”.

    Anutse ya ke cin dabinon inda yaci sai ya sanya ƙwallon atafin hannunsa na hagu.

    Guda bakwai yaci kana ya dakata.

    M Jameel kuwa dabino Uku yaci kana ya janyo faranti kayan friut ɗin ya fara da Abarba.

     

    Lumshe idanu Moddibo yayi tare da ɗaukar Inabi ya kai bakinsa sai kuma ya buɗe Idanunsa akan Ummin data ƙara so wajen zama tayi tare da tsirawa M Jameel idanu baki ɗaya hankalinta da nutsuwar ta yana kansa.

     

    Iska Moddibo ya furzar daga bakinsa tare da jingina bayansa da jikin bangon ya lura da tun zuwansu wani irin kallon da Ummi ke bin M Jameel dashi kallone mai nuni da tsantsar so, da kuma ƙauna da shaƙuwa irin wanda uwa ke nunawa ƴaƴan ta.

    Ƙasa da kansa yayi yayin da yaji ruwan hawaye masu ɗumi na tsata-tsafo masa saboda ganin shi ya rasa wannan damar bazai samu irin wannan ba arayuwarsa ba still Kansa na ƙasa ba tare daya ɗago ba ya dai-dai-ta muryarsa tare da faɗin.

    “Ummi kiyi buɗa baki mana”.

     

    Sai asannan Ummi ta lura da kallon da take bin M Jameel dashi, Malam Ahmad ma murmushi yayi domin ya lura da kallon da Ummi kebin M Jameel dashi Shikuwa M Jameel sai alokacin ya ɗago kansa ya lura da irin kallon da Umminsa ke binsa dashi.

    Murmushi yayi mai cike da so da ƙauna.

    Kana yace.

    “Ya dai Ummina nayi kyaune ko muni kike ta kallona?”.

     

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta ɗan lumshe Idanunta tare da girgiza kai kana tace.

    “A’a kawai dai naga azumi ɗaya akayi ana biyu har ka rame”.

    Murmushi yayi tare da gyara zamansa kana yace.

    “Hmmm Ummi kenan ai kinga mu ba azumin ne kaɗai ba. akwai yawon zirga-zirga sannan abincinma bama nutsuwa mu cisa yanda ya kamata musamman ma idan na biyewa Babanki”.

     

    Jinjina kai Ummi tayi kana tace.

    “To yau kam anan sai kunci kuncika cikin ku sannan in dafa muku na Sahur ma ku tafi dashi”.

    Girgiza kai Moddibo yayi kana cikin sauri yace.

    “A’a Ummi ki zauna Innayi na mana sannan ga can Asma’u na taya ta yanzu idan mun koma sai mun rasa inda zamu sanya abincin a cikinmu”.

    Jinjina kai tayi kana tace.

    “Toh shikenan Babana”.

    Murmushi Moddibo yayi kana yace.

    “Ummi kici abinci mana”.

     

    Kai ta gyaɗa sannan ta janyo Plate ɗin dabinon ta ci guda uku Bayan tayi addu’ar buɗa baki.

    Malam Ahmad ma danino uku yaci sannan Ummi ta ɗauki Flaks da niyyar haɗa musu tea Moddibo dake cin friut yayi saurin cewa.

    “A’a Ummi bari sai munyi Sallah”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Toh shikenan sai kun dawo”.

     

    Miƙewa sukayi M Jameel da Moddibo suka ɗauki buta kana suka ɗaura alwala suka fice Malam Ahmad kuwa ya riga su fita.

    Kai tsaye masallacin ƙofar gidan su Ummi da Baban Asma’u ke limancin suka shiga. Suna idar da Sallar Maghariba bayan sun idar suka dawo cikin gida shigowarsu yayi dai-dai da rurin da wayar M Jameel keyi.

     

    Kallon Moddibo M Jameel yayi kana yace.

    “Innayi ce ke kira”.

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da cewa.

    “Uhm”.

    picking call din yayi ya kai kunnensa.

     

    Daga ɗaya ɓangaren Innayi tayi gyaran murya kana tace.

    “Jamilu lafiya baku dawo kunyi buɗa baki ba mai kuke yi har yanzu awaje?”.

    Sajensa ya shafa kana yace.

    “Innayi wallahi Ummi ce ta riƙe mu wai saidai muyi buɗa baki agidan ta”.

    Murmushi Innayi tayi kana tace.

    “Toh mu kuma na gidan mu ya zamu yi dashi”.

     

    Kallon Moddibo yayi sai kuma yayi Murmushi kana yace.

    “Innayi abawa Almajirai dai sai kibar mana na Sahur dan nasan kinyi miyarki mai daɗin nan miyar me kika mana ma tukunna?”.

     

    Dariya Innayi tayi kana tace.

    “Miyar roman da kake so na daddawa da ƙarago shi zanyi muku na Sahur”.

    murmushi ya saki tare da faɗin.

    “Yauwa ina son wannan miyar”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Toh shikenan sai kun dawo ka gaishe da Ummin”.

    Ta faɗa tare da katse kiran.

     

    Suna ida shiga gidan suka samu wajen suka zauna Ummi ta miƙe tare da ɗaukar Flaks da kofina ta haɗa musu tea mai kauri yana tururi kana ta zuba musu soyeyyen dankali da ƙwai.

    Anutse suka fara ci kaɗan Moddibo yaci ya janye hannunsa daga ciki.

    Kallonsa Ummi tayi kana tace.

    “Ya dai Babana kaci mana”.

    Murmushi Moddibo yayi tare da ɗaura hannunsa na dama akan shafefen cikinsa ya shafa kana yace.

    “Ummi na ƙoshi”.

    Girgiza kai Ummi tayi tare da cewa.

    “Kai Babana me ma kuka ci?”.

    Ɗan kwaɓe fuska yayi kana cikin sanyin murya mai kama da shagwaɓa ya lumshe idanunsa tare da cewa.

    “Ummi kar muje muna sallah abinci yan fitowa ta hancin mu”.

    Kallonsa Ummi tayi tare da murmushi kana tace.

    “A’a Babana me ma kuka ci da zai zazzago ta hancinku?”.

    Murmushi yayi tare da shafa sajensa zuwa gemunsa kana yace.

    “Allah Ummi mun ƙoshi ko ba haka ba J?”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da Hararan Moddibo ya cire hannunsa a Plate din dan kalin.

    Hira suka sake taɓawa kana Moddibo ya miƙe tare da kallon Ummi kana yace.

    “Ummi zamu tafi”.

     

    Jinjina kai Ummi tayi tare da cewa.

    “Idan kunyi sallah Isha’i zaku dawo ta nan?”.

    Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.

    “A’a Ummi sai wani lokaci”.

    Gyaɗa kai tayi tare da cewa.

    “Toh ku tafi da kunun nan”.

     

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da gyara tsayuwar sa kana yace.

    “Toh Ummi ina son kunun abamu zan tafi dashi”.

    M Jameel ya juya ya kalli Ummi tare da langwaɓar da kai kana yace.

    “Ummi Ni dai ba abani abinda nake so ba”.

    Cike da kulawa da kuma so ta juya ta kallesa kana tace.

    “Me kake so?”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Inabin za’a bani in tafi dashi”.

    Saurin Kallonsa Moddibo yayi sai kuma ya juya ya kalli Ummi tare da cewa.

    “Ummi kar ki basa yasha muna dashi agida”.

    Tura baki M Jameel Yayi kana yace.

    “Iyeee to na haƙura tunda ba aso ayimin kyautar”.

    Ummi Kam murmushi take Cike da ƙaunar su, ji takeyi tamkar su duka biyu a cikinta ta rainesu ta haifesu.

    Sallama suka mata kana suka fice suka shiga mota Moddibo ke mazaunin Driver yayin da M Jameel ke gefen mai zaman banza kai tsaye Masallacin da suke limancin na ƙofar gidan Sarki suka nufa sunyi tafiya mai ɗan tsayi kafin suka isa lokacin da suka isa ankira sallar Isha’i suka shiga Moddibo ne yayi limanci suka idar da Isha’i kana sukayi Asham bayan an watse kana suka fito suka shiga mota wannan karon M Jameel ke driving Kai tsaye gidan Innayi suka wuce.

     

    Ƙarfe takwas da rabi suka isa gidan bayan sunyi parking sun fito kai tsaye sashen Innayi suka shiga bakinsu ɗauke da sallama a farfajiyar gidan suka tarar da Innayi da Asma’u zaune Innayi dake gashin nama akan mangal da tarin gawayi agefenta ta daga kanta tare da Kallonsu kana ta amsa Sallamar su.

     

    Ƙara sawa kusa da ita sukayi M Jameel yaja kujera ya Zauna kana ya Kalli Innayi tare da cewa.

    “Innayi ya dai mai ake gasa wasa ne?”.

    Murmushi Innayi tayi kana tace.

    “Nama nake dan gasawa nasanku da cin nama kamar kuraye!”.

    Dariya M Jameel Yayi kana yace.

    “Aikam Innayi kin kyauta gashi asalin gashi na gargajiya kike yi”.

    Kai ta gyaɗa tana ɗaukar Plate tace.

    “Eh ai nasanku”.

    Ta ida maganar tare da miƙa musu naman data yayyanka ta zuba a Plate tare dasa musu yaji agefe sannan ta yaryara ɗa musu man shanu.

    Kallon Asma’u dake yi musu sannu da zuwa tayi kana tace.

    “Asms’u ɗauko musu capet su zauna”.

    Cikin murza kai gefen dama da hagu Modibbo yace.

    “Uhmm Innayi kin dai sanshi shi J ɗinki da son nama kamar kura”.

    Murmushi M Jameel yayi dan yasan tabbas Modibbo bai cika damuwa da namaba, asalima in dai gasheshene ko soyayya in dai yaci yanka huɗu zuwa biyar zaice muƙa-muƙinsa sun gaji da taunawa, in kuma dafaffene wani lokaci da haƙorin gaba zai ɗan tattauna in yaji ya gaji sai ya tura masa naman gabansa.

    Shi kuwa M Jameel Allah ya sani yana masifar son nama, shi kuwa Moddibo yafi bawa ƴaƴan itatuwa mahimmanci.

    Cikin murmushin yace.

    “Yoh in ban so namaba me zanso A.J Namafa shine maƙurar daɗi”.

    “A wurinka ba, gashi kuma kana son koyamin”.

    Cewar Moddibon,

    Asma’u kuwa ganin Innayi na kallonta cikin mamakin tace.

    “A’a Asma’u ɗauko musu abin zama mana”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa kana ta miƙe ta shiga falon ta ɗauko capet ɗin ta shimfiɗa musu awajen da yake agyare tass babu alamar ƙazanta.

    Zama sukayi akai, Innayi ta sake kallon Asma’u tare da cewa.

    “Haɗa musu Tea sannan kisa musu zuma yaji”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa kana ta miƙe ta zuba musu shayi tare da zuba wadataccen zuma aciki ta kawo musu.

     

    M Jameel kuwa Anutse ya kai yankan naman bakinsa lokaci ɗaya ya lumshe idanunsa tare da buɗe su akan Innayi kana yace.

    “Kai gaskiya gashin nan yayi daɗi sosai”.

    Murmushi Innayi tayi tare da kallon Moddibo dake cin naman kamar ko yaushe kamar dai dole, yana ɗan taunawa kaɗan-kaɗan cikin kula  tace.

    “Kai kuma fa Moddibo?”.

    Ɗago kansa yayi ya kalleta kana yace.

    “Uhm yayi”.

    Girgiza kai tayi kana tace.

    “Wato kai dai baza ka iya Yabawa ba kenan?”.

    Kansa ya sake ɗagowa tare da kallonta kana yace.

    “Ai gashinan J ya yaba kuma danɗanon harshen mu ɗaya ne ai”.

    Murmushi M Jameel da Asma’u sukayi.

     

    Innayi kuwa baki ta taɓe M Jameel da Moddibo suka cigaba daci Ahankali Moddibo ya ɗago hannunsa tare da kallon tsadedden agogonsa kana ya mayar da Kallonsa kan M Jameel tare da cewa.

    “Sai munyi sauri lokaci ya kusa J”.

     

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da cire hannunsa a Plate din kana yace.

    “Toh shikenan mu tafi”.

    Miƙewa Moddibo yayi tare da kallon Innayi kana yace.

    “Bari naje na canza kaya”.

    Daga haka ya juya ya nufi sashen sa, shima M Jameel bayansa yabi.

     

    Moddibo nashiga Bedroom ya sauya kayansa zuwa Jallabiya Coffee color tare da ɗaura farin hirami irin na samarin larabawa kana ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin ƙamshi.

    Anutse ya fito falo ya samu M Jameel da shima ya canza kayansa buɗe fridge M Jameel Yayi ya ɗauki goran faro mai sanyi sannan suka jera tare da Moddibo suka sauƙa.

     

    Kai tsaye sashen su Innayi suka koma batare da sun shiga farfajiyar gidan ba .

     

    “Toh Innayi mun tafi”.

    Cewar M Jameel

    Tana rufe roban yajin da suka ci nama dashi ta ajiye kana tace.

    “Toh Allah ya tsare muma yanzu muna bayanku”.

    M Jameel na gyara ɗaurin agogon dake tsintsiyar hannunsa ya kalleta kana yace.

    “Toh idan za kuje kuzo mu tafi mana sai mu sauƙe ku”.

     

    Girgiza kai tayi tare da cewa.

    “Ai akwai Napep zamu hau”.

    M Jameel kuwa kai ya Girgiza kana yace.

    “A’a ai abin baiyi ba bayan tanan muke tafiya kuma kuce zaki shiga Napep kawai kuzo mutafi”.

    Jinjina kai Innayi ta gyaɗa kana tace.

    “To bari mu tattara da sauri sai mu tafi”.

    “Toh”,M Jameel yace Shi kuwa Moddibo bai ce komai ba sai harɗe hannunsa da yayi aƙirji.

     

    Cikin sauri Innayi da Asma’u suka tattare wajen sannan suka sanya hijabansu kana suka rufe kichen da gidan suka fice abayan Mota suka zauna ita da Asma’u yayin da M Jameel da Moddibo ke gaba.

    Suna isa babban masallacin M Jameel yayi Parking Innayi da Asma’u suka fita suka nufi sashen mata su kuma suka shiga cikin masallacin daya cika sosai da al’umma.

     

    Bayan sun zauna Kamar ko yaushe M jameel ya buɗe musu da addu’o’in kana Moddibo ya gyara system ɗin sa tare da ƙara rage girms Idanunsa kana yasa lallausan tafin hannunsa ya gyara zaman microphone din dake gabansa tare dayin gyaran murya cikin sanyayyar sautin muryansa ya fara kamar haka:

    _“Auzubillahi Minal Shaiɗanir Rajim, Bismillahir Rahmanir Rahim.

    (10) Innalazina ya’akuluna, Amwalal yatama zhulman innama ya’akuluna fiy buɗunihim naraa,wasayaslauna sa’irah”._

    Jama’ar dake wajen masallacin cikin sassarfa suka ƙaraso cikin masallacin dan basa so koda harafi ɗaya ne su rasa daga cikin karatun Moddibo saboda baiwar muryarsa.

     

    Moddibo kuwa sanyayyar numfashi ya fesar tare da jingina bayansa da kujeran kana ya cigaba kamar haka:

    _“(11)Yusikumullahu fii auladikum,Lilzikri mislu hazzil unsaynan.Fa’in kunna Nisa’a fauƙasnatayni falahunna sulusa ma tarak,Wa’in kanat wahidatan falahannisf,Wali abwayhi likulli wahidin Minhumassudusu,Mimma taraka inkana lahuu waladun,Fa’in lam yakun lahu waladu wawarisahuuu abwahu fali ummihi sulus.Fa’in kana lahu Ikhwatun fali ummihi sudus min ba’adi wasiyyatin yusi biha audayn,abaukum wa’abna ukum latadruna ayyuhum aƙrabuna lakum naf’,a,Faridatan Minallah,Innalaha kana aliman hakima”._

    Ya dire ayar tare da jan numfashin sa da ya riƙe.

    Jinjina kai M Jameel Yayi yayinda ayoyin ke ratsa sa cikin yanayin sakewa ya lumshe idanu kana yace.

    “Aya ta gaba”.

     

    Jinjina kai Moddibo yayi kana cikin zazzaƙan muryansa mai sanyi da ratsa jiki kana da nutsuwa ya cigaba da jan ayoyin saida ya kai aya ta Ashirin kana ya tsaya.

    Shi kuwa M Jameel Cike da tsantsar ƙwarewa da nutsuwa kana da sanin makaman tafsir ya fara fassara ayoyin tare da cikekken kaddima da kowa amintattun haɗisai da suka da munasaba da ayoyin harma da sababul nuzur na ayoyi, lokacin ɗaya cikin masallacin ya sake samun nutsuwa tafsirin na ratsa su.

     

    Ƙarfe goma dai-dai suka tashi tafsir ɗin mata suka fara fita ta ɓangarensu kafin maza suka fita acikin mota Asma’u da Innayi suka jira M Jameel da Moddibo goma da kwata dai-dai suka fito suka tafi.

    Acan ɓangaren Khausar kuwa yauma kamar kullum taje tafsiri ita kaɗai ta dawo duk da masallacin a ƙofar gidansu yake bakinta ɗauke da Sallama tashiga cikin falonsu Anutse ta cire hijabinta tare da nufar kichen inda take jiyo motsin Mommyta kasancewar yau itace da girki yasa ko tafsir bata jeba.

     

    Juyiwa Mommy tayi jin motsi abayan ta ganin Khausar yasa ta maida hankalinta kan aikinta kana tace.

    “Kin dawo?”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tana kallon tuƙeƙken tuwon shinkafa da Mommy ke kwashe maran ƙarshe.

    Ahankali Khausar ta matsa kusa da Mommy kana tace.

    “Mommy ki bari zanyi miyar”.

    Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

    “Ok to Miyar zogala za kiyi”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da ɗaukar.

    Da fara aikin haɗa miyar zogalen.

    Cikin abinda bai gaza awa ɗaya da rabi ba, duk ta haɗa ta sanya komai na buƙata kana.

    Ta rufe nan danan kichen ɗin ya kaure da ƙamshin miyar sauran kayan da Mommy tayi amfani dasu ta haɗa ta wanke tare da sauƙe Miyar ganin tayi tik gwanin kyau.

     

    Bayan ta gama ta buɗe miyar da yayi mugun kyau a ido ta ɗauki kular wani sashe ta zuba miya kasancewar babban gidana yasa kowa kaina nasa akeyi, na buɗa baki kuwa ki wacce a side ɗinta takeyi, mai girki zata sawa Lamiɗo, da Dadu, haka tsarin nasu yake.

    Shigo wa Mommy tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta kalli yanda kichen ɗin yayi fess ga ƙamshin miyar zogalan da yaki kifi da naman dariko, kallonta ta mayar kan Khausar kana tace.

    “Sannu da ƙoƙari ki ɗauki na sashen Hajiya Bunayya ki kai mata”.

    Kai Khausar ta gyaɗa sannan ta ɗauka kular Hajiya Bunayya ta wuce Haidar Mommy ta ƙwalawa kira bayan yazo tace ya ɗauki kular sashen Gimbiya Dadu ya kaimata dan Mommy tunda ta lura da Khausar batason zuwa yasa ta rage aikanta sashen shi kuwa Haiydar daga sashen Gimbiya Dadu ya wuce sashen Hajiya Bunayya.

     

    Hajiya Bunayya dake zaune akan kujera ta faɗaɗa fara’ar fuskarta ganin Haiydar ta tsira masa idanu kana tace.

    “Babana kaine dama yanzu nake niyyan zuwa in yi maka albishir”.

    Murmushi Haidar yayi tare da zama kana yace.

    “Daga sashen Gimbiya Dadu nake nace bari nazo na gaishe ki”.

    Murmushi tayi masu cike da Ma’anoni  tayi kana tace.

    “Insha Allah bayan sallah mashin ɗinka zai  zo kaga dama tun shekara biyu baya naso saya maka Abbanka yace saika ƙara girma kuma kaga yanzu aika girma”.

    Jinjina kai Haidar yayi cike da tsananin farin ciki mara mistuwa ya gyara zamansa kana yace.

    “Nagode Ummah Allah yarabaki da sharrin maƙiya”.

    Murmushin gefen baki tayi kana tace.

    “Bana son godiyar nan Babana”.

     

    Cike da farin ciki ya miƙe ya nufi sashen su fuskarsa ɗauke da murmushi ya shiga falon zaune ya samu Mommy da Khausar.

    Kallonsa Mommy tayi kana tace.

    “Ina ka tsaya?”.

    Zama yayi daga gefen Khausar still.

    Fuskarsa da murmushi da yakasa ɓoyewa ya numfasa tare da cewa.

    “Mommy Machine ɗina ya Kusa isowa fa, kinga tun shekara biyu baya Umma taso siya min shine Abba ya hanata yace saina ƙara girma ai yanzu kam dai na sake girma bazai hana ba ta saya min Machine sabo mai kyau bayan sallah zai iso”.

     

    Khausar kuwa tunda ya fara magana ta tsira masa idanu saida ya kai aya ta sauƙe ajiyar zuciya mai zafi tare da furzar da iska daga bakinta kana babu walwala afuskarta ta kawar da kanta gefe tare da cewa.

    “Kai kuma farin ciki kake ko?”.

    Juyawa Haiydar yayi tare da kallon ta kana yace.

    “Sosai ma kuwa kema kamata yayi kije kiyi mata godiya”.

    Harara Khausar ta ɓalla masa.

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Rabu da ita ai ni zanje.

    A yanzu kam aika girma yanda kake da tsawon ƙafan nan”.

     

    Murmushi yayi tare da kallon Khausar kana yace.

    “Sosai ma Mommy ai yanzu na girma yanzu fa shekara kusan sha shida nake nema gashi mai shekara sha takwas ɗinma na fita koda yake sha bakwai ne da yan watanni ne ko gareta”.

     

    Jinjina kai Mommy tayi kana tace.

    “Ai lallai dai kam kama cika sha shida kam  Allah yasa kafara hawa asa’a.

    Ubangiji ya tsareka da sharrin ƙarfe.

    Allah yatsare gabanka da bayanka!.

    Ubangiji ya makantar da idanun makiyan ka akanka!.

    Allah ya tsare ku ga duk kan abinda zai cutar da rayuwar ku! Allah ya muku katangan ƙarfe da dukkan abin da zai zama sharri acikin  rayuwarku!”.

    Cike da jin daɗin Addu’ar ta Haiydar yayi Murmushi tare da cewa.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum Mommy na”.

    Ajiyar zuciya Khausar ta sauƙe tare da kallon Mommy kana tace.

    “Ameen ya Allah Mommy tunda kinyi addu’a magana ta ƙare baza’a ji tsoron komai ba babu bakin uwa akansu duk kan mai sharri zaiyi ya gama babu abinda zai sameshi da izinin Ubangiji”.

     

    Murmushi Haiydar yayi tare da kallon Khausar kana yace.

    “Aikam Addah Khausy babu bakin uwa akaina duk kan wani mai mugun nufi zai ƙare akansa”.

    Murmushi Mommy tayi cike da ƙaunar ƴaƴan nata,

    kallon ta ta mayar kansu tare da cewa.

    “Ku tashi kuje kuyi bacci dan mu samu mu farka da wuri mu kaiwa Ubangiji bukatun mu”.

    Miƙewa sukayi tare da yiwa juyawa sai da safe kana kowa ya wuce ɗakinsa ya kwantar.

     

    Misalin ƙarfe ɗaya na dare Mommy ta farka kallon Lamiɗo daya miƙe yashiga toilet tayi sai kuma ta miƙe ahankali ta tafi side ɗinta.

    ɗakin Khausar tashiga tare da kunna haske.

    Idanunta suka sauƙa akan Khausar dake sharan bacci ƙara sawa tayi tare da bubbuga ƙafarta kana tace.

    “Khausar ki tashi kiyi nafilla”.

    Ahankali Khausar ta buɗe Idanunta cikin Muryan bacci ta kalli Mommy kana ta yunƙura ta zaune bakinta ɗauke da addu’a tace.

    “Toh Mommy”,Sannan ta Sauƙa ta shiga toilet.

     

    Juyawa Mommy tayi ta koma ɗakin Lamiɗo lokacin data shiga har ya fara Sallah kai tsaye toilet ta shiga ta ɗaura Al’wala bayan tayi ta fito tare da shimfiɗa Sallaya ta tada Sallah cikin nutsuwa ta keyi bayan tayi sujja tayi Subhana Rabbiyal a’ala³ kana ɗaura da du’inta.

    “Ya Allah kayuwa ƴata zaɓin alkhairi,Ya Allah kashirya Khausar kasata ahanya madaidaiciya Ya hayyu ya ƙayyum  ka tsare mata imaninta, Ya Allah ka kare min Haiydar ɗina ya Allah katsaresa daga sharrin mai sharri ya Allah ka kare min ita ya Allah kabawa Ramadan da Raudat ilimi mai albarka da yayunsu dama dukkan ƴaƴan musulmai. Ya Allah katsare min ƴaƴana daga sharrin,Mutum, aljan da kuma ƙarfe, ya Allah katse min imanina Allah ka tsaremin zuciyoyinsu, ka tsaresu da sharrin hassada, ƙeta, munafurci, da ƙyashi ya Allah ka kare min mijina kabiya masa buƙatunsa na Alkhairi dama ɗauka cin al’ummar musulmai.

    Bayan ta idar da nafillah ta ɗauki Alkur’ani ta shiga Muraja’a.

     

    Khausar kuwa ƙarfe biyu da rabi bacci ya riƙa fisgarta akan Sallaya ta kwanta nan da nan bacci mai nauyi yayi nasarar  ɗauke ta.

    Can cikin baccinta ta fara wani mafarki mai cike da al’ajabi ganinta tayi.

    Gata nan tsaye a wani ƙaton fili.

    Baki ɗaya ilahirin filin ashare yake kuma , yashine malale a wurin iya ganinka sai wani irin haske mai masifar ƙyalli da ɗauke idon da ya cika wajen baki ɗaya, ahankali ta ɗaga kanta ta fuskanci gabas, da sauri ta rumtse idanunta gani wata ya fito ta gabar juyawa tayi taga yamma da sauri Still nan ya fito ta yamman sake juyawa kudu tayi still ta nan ma ya fito ahankali ta sake juyawa arewa, wani irin masifeffen karkarwa jikinta ya farayi, ganin tanan ma watan  yafito duk kusurwa huɗu wata ya fito sai asannan ta lura da haskensa ne yake ɗauke mata ido.

    Ahankali taga wani kyakkyawan.

    Yaro fari ƙal agabanta yayinda gashin kansa ke kwance lib-lib, daga bayansa ta hango wani kyakkyawan mutum sai dai fuskarsa na kallon gefe hannunsa na kan yaron yana shafawa cikin wata.

    Sanyayyar murya yake kallon yaron kana yace da ita.

    “Wannan shine jininmu mahaɗinmu, wannan shine sanadin haɗayyarmu bugun zuƙatanmuuuhh”.

    Ya ƙarasa jan kalmar cikin wata iriyar ƙasalalliyar murya mai cike da shauƙi.

    Ita kuwa ƙoƙari take taga fuskar mutumin sai dai ta kasa sai iya fuskan kyankyawan yaron take iya kallo.

    Dai-dai lokacin kuma ta buɗe Idanunta jin Muryan Mommy nacewa.

    “Khausar, Khausar ki tashi zaki makara fa ƙarfe huɗu tayi bakiyi Sahur ba anjima kaɗan zaki fara ce mana kin fara jin wahalar azumi”, Ta faɗa tana buga ƙafarta da saurin Khausar ta tashi zaune tare da sakin ajiyar zuciya kana tace.

    “Innslillahi wa’inna ilahi rajiu’n Hasbunallahu wani’imal wakin Astagfirullah wa’atubu ilaik”.

    Sai kuma tayi addu’a ta shafa.

    Mommy dake tsaye har yanzu kuwa sake taɓata tayu tare da cewa.

    “Khausar kada ki koma bacci fa kitaso”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Mommy na tashi bazan koma ba”.

    Juyawa Mommy tayi ta fice ita kuma Khausar toilet ta shiga.

    Brush tayi kana ta fito kai tsaye falon ta nufa.

     

    Samu tayi Mommy ta haɗa mata ɗumamen tuwon jiya da Tea mai kauri ahankali ta zauna tare da kai tuwon bakinta da ƙyar ta haɗiye baki ɗaya jikinta yayi mugun sanyi da mafarkin da tayi.

    Mommy dake zaune a kujeran falon ta juya ta kalleta ganin bata cin tuwon yasa ta girgiza kai tare da cewa.

    “Kici abinci fa Khausar kin sanki sarai da cin abinci anjima kaɗan zaki fara cewa yunwa kike ji”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da iskar bakinta kallon Mommy tayi kana cikin sanyin murya ta lumshe Idanunta tare da cewa.

    “Mommy wallahi tuwon ne nakeji kamar ba zai shiga ba babu wani abu ne?”.

    Kai Mommy data tsira mata Idanu ta gyaɗa kana tace.

    “Kije kichen akwai indomie dana ɗaura wa Haiydar shima yace ba zai ci tuwo ba to amma ke kam nasan indomie ba wani riƙe Miki ciki yake yi ba”.

     

    Lumshe Idanunta tayi kana ta buɗe su akan Mommy ahankali ta motsa laɓɓanta tare da cewa.

    “Bari in cisa yau ɗin kam amma Mommy da kifi ne koda nama”.

    Tayi tambayar ne domin bata fiye son kifi ba.

     

    Kawar da kai gefe Mommy tayi kana tace.

    “Da kifi ne idan zaki ci kici idan kuma baza kici ba ki bari”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da jan siririn tsaki kana tace.

    “Bari dai inci, tuwon ne naji kamar bazai ciwu ba  shi ɗin ma miyar aida kifi”.

    Mommy dai Bata sake cewa komai ba ahankali Khausar ta miƙe tashiga kichen ta ɗauki Plate ta ɗibi yanda zai isheta kana ta fito ta zauna tare da Bismillah ta fara ci bayan ta gama ta ɗauki tea da Mommy ta haɗa mata da bread taci.

    Haiydar ne ya shigo  da Sallama idanunsa akan Plate da Khausar ta gama cin indomie.

    Kallonsa Mommy tayi kana tace.

    “Jeka ɗebo indomie yayi sannan ka taho min da tuwo”.

    “Toh”,Ya amsa kana ya wuce kichen ɗin ya juye indomie sannan ya zubawa Mommy tuwon ya fito.

    Khausar dai na zaune tana lumshe Idanunta tare da tuna irin mafarkin da tayi wanda ya tuno mata wanda tayi shekaru biyu baya a Jauro Yayah.

     

    Ahankali ta saki ajiyar zuciya tare da juyawa ta kalli Haiydar da yagama Sahur ɗin ta gyara zamanta tare da cewa.

    “Haiydar  nikam yanzu wani surah kake?”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Ke ɗin wace surah kike?”.

     

    Zama ta gyara tare da cewa.

    “Hmmm aini nayi nisa ina Maryam kaga insha Allah zan samu sauƙa biyu”.

    Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.

    “Toh ni ina Yasin  Insha Allah zan samu sauƙa uku insha Allah duk azumi goma zanyi sauƙa ɗaya”.

    Murmushi Mommy dake duba wani littafin addini tayi kana tace.

    “Masha Allah yayi kyau Khausar ya akayi kika tsaya wasa ya wuce ki”.

    Langwaɓar da kai tayi kana tace.

    “Mommy kinga ai shi baya taya ki yin aiki nice ke tayaki aiki kinga shi duk lokacin daya keso zaiyi karatu.

    Jinjina kai Mommy tayi kana tace.

    “Eh haka ne da wannan dan wannan amma dai ki dage kema”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Toh shikenan Mommy zan dage insha Allah amma Mommy ke izu nawa kikayi”.

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Insha Allah nima zan samu uku kaman na Haiydar”.

    Ware Ido Khausar tayi tare da tura madedecin bakinta kana tace.

    “Insha Allah nima zan dage duk azumi goma sai nayi sauƙa”.

    Jinjina kai Mommy tayi tare da faɗin.

    “Aikam da kin kyauta amma sai kin rage baccin safe”.

    Jinjina kai Khausar tayi kana tace.

    “Insha Allah zan rage”.

    Jin kiran assalatu yasa suka miƙe Haiydar ya tafi masallaci Mommy da Khausar suka shiga ɗaki suka ɗaura alwala kana suka gabatar da sallah bayan sun idar Khausar ta zauna tayi Azkharul sabah tana gamawa ta mike ta dawo falo ta gyara tare da sharewa kana ta fita zuwa kofar sashen nasu ta gama share ko ina sannan ta wuce Bedroom ta kwanta kasancewar akwai mai yi musu wanke-wanke tun kafin su shiga Sallah ta zo ta kwashe kayan ta wanke.

     

    Ahankali azumi ya cigaba da tafiya kwanaki suna tafiya lokaci yana ja  cikin ikon Allah har angama goman farko goma na marmari inji hausawa ko?. Har an  shiga goma na biyu,  goma na wuya ko? Yau an kai azumi na goma sha biyu.

     

    Yayin da Aɓangaren Moddibo da M Jameel sunyi nisa acikin tafsirin Suratul Nisa sun fassara har zuwa ayoyi na tamanin da tara zasu tashi akan aya na Casa’in

     

    Da daddare Misalin ƙarfe tara M Jameel da Moddibo ne zaune acikin masallaci gaban ko wannensu ɗauke da system da kuma roban Swan water mai sanyi Moddibo na cikin shigarsa as Usual kamar ko yaushe Jallabiya Neavy blue kansa ɗaure da Hirami M Jameel kuwa sanye yake cikin gezner blue da babbar riga.

    Cike da nutsuwa M Jameel Yayi gyaran murya tare da hura Microphone ɗin kana yace.

    Ya buɗe da addu’a kamar ko yaushe.

     

    Lokaci guda masallacin ya kaure da kabbara tamkar zasu tsaga masallacin saboda yanayin zafin jinjinsa da kwarjininsa cike da sakin fuska.

    Ya cigaba da cewa.

    “Anma ba’ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu”.

    Atare suka hada baki wajen cewa.

    “Wa’alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.

     

    A hankali ya numfasa tare da sauƙe nan-nauyan ajiyar zuciya kana ya dubi ɗumbin jama’ar dake zaune acikin masallacin cikin tsantsar nutsuwa ya juyo da system ɗin gabansa kana yace.

    “Acigaba da tafsirin Alkur’ani mai girma Amasallacin. Juma’a dake ƙofar gidan Mai martaba Sarki Gembulan Lamido Bashiru zamu cigaba da tafsirin Alkur’ani mai girma acikin Suratul Nisa’i zamu tashi a aya ta cassa’in”.

    Sai kuma ya juya ya Kalli Moddibo kana yace.

    “Aramma Bismillah”.

     

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da gyara zamansa kana ya ɗan jingina bayansa da jikin kujeran cikin Sanyayyar muryarsa mai cike da nutsuwa da zaƙi yayi basmala kaya ya fara karanta ayoyin kamar haka;

    _“(90)Illallazina Yasiluna Ilaƙaumim Bayna Kum wa Bayna hum misaƙun Auja,Ukum hasirat suduruhu an yuƙatalalukum.Walau sha Allahu lasallaɗhum Alaikum falaƙatalukum.Fa’in’itazalukum falam yuƙatilukum Wa’alƙau Ilaikumussalama fama ja’alallahu lakum Alaihim Sabila”._

     

    Moddibo ya ida kai Ayar yana mai lumshe idanunsa akuma take tsikar jikinsa suka tashi yayi saurin buɗe idanunsa tare da ƙoƙarin dai-dai-ta nutsuwarsa kana ya cigaba da furta Aya ta gaba kamar haka.

    _“(91)Satajidunah Akharina Yuriduna Anyamanukum Wayamanu Ƙaumahum kullamaraduu Ilalfitnatin Urkisu fiha.Fa’in lam ya’atazilukum Wayulƙau Ilaikumussalama Wayakfuru Aydiyahum Fahuzuhum Waƙtuluhum haysu saƙiftumuhum.Wa Ula’ikum ja’alnalakum Alaihim sulɗanammubina”._

     

    Wani irin numfashi M Jameel ya saki tare da rintse idanunsa kana jikinsa ya ɗauki tsuma yana mai jin fassarar Ayar na yawo Atsakiyar kansa Atake kuma zuciyarsa ta cigaba da bugawa da kaso tamanin cikin ɗari.

    Yayinda gaba ɗaya al’ummar dake cikin masallacin dama wajensa sit kakeji kamar ba mai numfashi sabida tsananin yadda sautin karatun ke ratsa musu zuƙata da ƙoƙwale.

     

    Shi kuwa Moddibo ya kai minti ɗaya kafin ya saki gauron numfashi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi sabida sanin ma’anar ayoyin da zai kawo a gaba, cikin wani irin raunin tare da tsoron Allahu wahidun ƙahhar, gaba ɗaya muryarsa ta sake rauni cikin dakiya ya cigaba da Karanta Ayar Kamar haka.

    _“(92)Wama kana limu’uminun An yaƙtula Mu’uminan Illakhaɗa’a.Waman ƙatala Mu’uminan khaɗa’a fatahriru Raƙbatatin Mu’uminatin wadiyyatun Musallamatu Ila’ahlihee Illah An yassaddaƙun.Fa’in kana min ƙaumin Aduwwillakum Wahuwa Mu’uminun Fatahriru Raƙbatin Mu’uminatan.Wa’in kana min ƙaumim baynakum wa baynahum miysaƙun Fadiyyatun Musallamatun Ila Ahlihi watahriru raƙbatin mu’uminatin.Famallam yajidu fasiyamu shahraini mutatabi’ayni taubatan Minallah.Wakanallahu Aliman hakima”._

     

    Wani irin nutsuwa cikin masallacin yayi musamman ma wa’anda suka san fassarar ayoyin wa’anda basu san fassarar ba kuwa mu’ujiza ta Kur’ani ta dinga ratsasu tare da Sanyayyar sautin Muryar mai karatun.

    Moddibo kuwa idanunsa ya lumshe sakamakon wasu zafafan hawaye masu ɗumi da suka cika cikin ƙarfi ya furzar da iska mai zafin gaske Tabbas kashe ran mumini baƙaramin tashin hankali bane amma baki ɗaya awannan zamanin an maida rai ba abakin komai ba.

    Ya gyara zamansa tare da cigaba da karantar Ayar kamar haka.

    _“(93)Waman yaƙtul mu’uminan Muta’ammidan Fajaza’s’uhu Jahannama! halidan fiha wagadiballahu Alaihi wala’anahu! wa’aaddalahu Azaban! Azeeymah!!!!!”_.

     

    Awannan lokacin hawaye ne suka ciko idanun Moddibo jin irin tsananin azaban da Ubangiji ya tana darwa duk wanda ya kashe ran mumini batare da wani hakkiba.

    Walahabahu la’anar Ubangiji kana fajaza’ahun jahannamu  khaleedan fiha, fa ubangiji yace kana aka ɗaura da Azaban Azeeymah!!!, Duk wannan tanadinefa da Ubangiji yayiwa mai kashen ran mumini da gangan.

     

    Wani irin rawa jikin Moddibo keyi tamkar wanda aka konawa wuta a jikinsa cikin tsananin sheshsheƙan kukan da yake son dannewa ne ya bu ɗe baki a hankali dan kawo aya ta 94 sai kuma ya juyo cikin tsananin rauni ya kalli M Jameel da gaba ɗaya j….

     

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

     

     

    *By*

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 25

    Sakayyah 25

     

    SAKAYAH

     

    25

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

    *Al’bishirunku Ma’aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma’aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken  GARKUWAR MA’AURATA*

     

    NI DAI AYSHA ALIYU GARKUWA.

    Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaice, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

     

    Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.

    Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?

    Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.

    Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?

    Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba’a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,

    Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ki zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan.

    Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.

     

     

    Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*

    Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu’umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

     

    Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

     

    🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA

    *(GARKUWAR MA’AURATA)*

     

    Isrejy. Suna fita suka ga gari yayi shiru ga wani irin hadari daya haɗu baƙiƙƙirin, sanyayyar iska mai sanyi da ratsa jiki yana kaɗawa alamun wata ƙil hadarin ya watse ne ko kuma ya sako ruwa,  wani irin lumshe idanu Moddibo yayi tare da cije labɓansa na ƙasa cikin sauri ya shiga mota M Jameel yashiga maza mazaunin Driver yaja suka tafi suna isa gida aka fara yayyafi still yau ma ɗakin Moddibo M Jameel yashiga ya kwanta nan da nan bacci ya ɗauke sa.

    Moddibo kuwa tunda ya kwanta yake juyi ahankali ya miƙe ya zauna idanunsa cike da ruwan fitina da zaran ya lumshe Idanunsa kyakkyawar suranta daya gani amafarkine ke masa yawa kana idan ya buɗe lokacin da suka kasance amota ne yake masa gezo zama yayi Atsakiyar gadon D ɗinsa ya shiga harbawa da masifar ƙarfi tamkar zai tsinke lokaci ɗaya jikinsa ya ɗauki rawa yayin da lips ɗin sa suka shiga rawa har haƙoransa na haɗuwa suna bada sautin Ƙat-ƙat-ƙat kana Idanunsa sun kaɗa sunyi jawur tare da ƙanƙancewa kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin tsananin buƙatar kasancewa da.

    Mace da ƙyar ya miƙe yashiga toilet tare da sakarwa kansa ruwan sanyi duk da kuwa sanyin da ake agarin amma tamkar ƙarawa yake cikin mawuyacin hali da yanayin buƙatuwa ya fito tare da kwanciya rub da ciki cikin wahalallan hali bacci ya ɗaukesa.

     

    Bayan kwanaki biyar sosai kafar Ramadan yayi sauƙi har ya fara takawa ahankali  sosai Mommy da Khausar da kuma Lamiɗo sukayi farin ciki ganin babu wata matsala.

     

    Aɓangaren Uncle Naseer kuwa abubuwa suna tafiya kamar yanda ya tsara baki daya ya maida hankalinsa da nutsuwarsa kan Amina yana nuna mata zallar so tare da yimata duk wani abinda take so yayin da acan ƙasan ransa kuwa soyayyar Khausar na nan kamar yanda yake yana da burin ta kasance matar.

    Aurensa kana yana jin

    yana son ya haɗa shimfiɗa da ita yana so yaji shin ya ɗanɗanonta yake, domin itace mace ta farko daya fara so tare da ƙulafacin ɗanɗanar zumanta ita kaɗai duk da cewa yayi Sex da mata kala da ban da ban bai taɓa sanun cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali ba, yanaji  awajen Khausar ce kaɗai yake da ya ƙinin zai samu irin wannan nutsuwar da yake buƙata, duk wani tsarinsa yana yine dan ganin ya samu ya ɗanɗanin zumanta tare da kawar da ƙishinsa akanta.

     

    Aɓangaren su M Jameel kuwa sun sake samun malam Arɗo da batun barinsu makaranta amma fir malam Arɗo yaƙi amincewa sam baya so ma suzo masa da batun yayin da M Jameel da Moddibo suka rage zuwa makarantar domin sukanyi kwanaki uku ko  huɗu ba suje ba wani zubin ma har satin ya ƙare baza sujeba kasancewar sun riga da sun faɗa masa cewa sun ajiye aikin.

    Baki ɗaya sun mai da hankali da nutsuwar su akan abinda suka sa gaba na batun aikin da zasu fara a Company Abban M Jameel.

    Abba kuwa kasancewar yanzu damuna ne yasa ya maida baki ɗaya hankalinsa da ragowar kuɗin hannunsa akan noma musamman nomar Auduga da ake masa saboda yana amfani dashi a Companyn’,sa na Marrocco yana buga manyan zannuwan gadaje sallayoyi da jallabiyoyu na mata da maza riguna na alfama  da dai sauransu.

     

    Wata ranar Litinin tun safe garin Gembu suka tashi da ruwan sama tamkar da bakin ƙwarya sai daf Azahar ruwan ya tsaya gari yayi sanyi Sanyayyar iska na kaɗawa yayin da bishiyoyi ke rangaji tamkar zasu karye ko wanni magidanci yana farin ciki da kasancewar wannan Weather mai cike da Ni’imah da kuma sanya shauƙi.

    Acan ɓangaren Moddibo kuwa da yammaci misalin ƙarfe biyar M Jameel ne zaune aka 2sitter yayin da Moddibo ke kwance akan 3sitter yayi rub da ciki idanunsa alumshe.

    Anutse M Jameel ya ɗago kansa daga kan system tare da kallon Moddibo cikin yanayin shaƙuwa da ƙaunar junansu yace.

    “A.J muje gidan Ummi mana”.

    Cikin Yanayin buƙata da tsananin sha’awar dake addabarsa ya damƙe ƙasan mararsa waye wan garin yau yasha ruwan lipton da lemun tsami har ya godewa Allah amma ko kaɗan abinda yake ji bai raguba hakan yasa ya kasa furta komai.

    Jin kamar bai jiba yasa M Jameel sake maimaitawa.

    Ahankali Moddibo ya ɗago Idanunsa cikin raunin murya da yanayin harbawan da ɗin sa keyi kana muryarsa Asanyaye ya kalli M Jameel tare da cewa.

    “J bazan iya ba Wallahi bazan iya ba”.

    Ya faɗa yana lumshe Idanunsa ajikinsa yana jin tamkar idan ya miƙe  ɗin sa zai tsinke baki ɗaya ya rasa inda zai sanya ransa yaji daɗi ji yake tamkar ya ɗaura hannunsa akai yaita zunɗuma ihu koda zaiji sanyin Aransa baki ɗaya lips ɗin sa rawa suke idanunsa sun sauya launi zuwa ja jijiyoyin goshinsa sun tashi yayin da goshinsa ke tsata-tsafo da zufa.

     

    M Jameel kuwa lura da yanayin da yake ciki da yayi yasa ya miƙe tare da nufar kichen kamar ko yaushe ruwan Tea da lemun tsami da kuma zuma ya haɗa masa kana ya fito ya miƙa masa tare da cewa.

    “Gashi kasha”.

    Ba musu Moddibo ya sanya hannu ya karɓa domin baya cikin yanayin da zai iya musa masa ahankali yakai kofin bakinsa tare da kafa kai ya shanye saboda yanda yake ji ajikinsa.

    Ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe kana cikin sanyin murya yace.

    “Tun da kasha ka kwanta Insha Allah zaka ji sauƙi bari zanje gidan Ummi anjima zan dawo bazan daɗe ba”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa masa still Idanunsa alumshe M Jameel kuwa key mota ya ɗauka tare da ficewa kai tsaye gidan Ummi ya nufa.

     

    Yana isa yayi Parking Cike da nutsuwa ya buɗe Murfin motar ya fita tare da duba agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa dake nuni da ƙarfe 5:15 lumshe idanunsa yayi kana ya buɗe tare da nufar cikin Falon bakinsa ɗauke da Sallama shiru falon ba kowa sai dai komai akimtse kana ga ƙamshin tularen wuta dana Room freshner dake tashi, Murmushi yayi Aransa yace.

    “Allah sarki Ummina ba dai tsafta ba”.

    Numfashi ya fesar tare da nufar kichen inda yake jiyo motsinta.

    Tsaye yasame ta a kichen ta tuƙa tuwo tana kwashewa aleda cike da so da ƙauna yace.

    “Ummina”.

    Juyawa Ummi tayi fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi ta kallesa kana tace.

    “A’a yaushe kashigo?”.

    Yana ƙara sa shiga kichen ɗin yace.

    “Yanzu Ummina”.

    Juyawa Ummi tayi tare da leƙa bayansa”.

    Dariya yayi kana yace.

    “Nasan wa kike nema ai”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Eh to ai ban gan shi bane naga Hussain banga Hassan ba”.

    Cikin sanyin murya yace.

    “Yana gida Ummi yau yana ɗan jin zazzaɓi ne shiyasa bamu zo tare ba”.

    Girgiza kai Ummi tayi cike da tausayawa tace.

    “Subhanallah Ubangiji ya bashi lafiya Allah ya sawwaƙa mishi”.

    Ahankali M Jameel yace.

    “Ameen”.

    Kana ya matsa jikin kular yana ƙoƙarin budewa yace.

    “Ummina yau me kika girka mana ne?”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Tuwo ne”.

    Wara ido yayi tare da cewa.

    “Miyar me za kiyi mana Ummi?”.

     

    Tana ƙoƙarin wanke nama ta kallesa kana tace.

    “Miyar taushe zanyi”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “A to asamana nama da yawa”.

    “Toh Babana za’a saka”.

    Ta ida maganar tare da ɗaura naman akan gas kana ta yanka albasa tare da sanya Maggi, citta kamafari ta rufe.

    M Jameel kuwa Attaruhu, Albasa,Tattasai ya haɗa ya wanke tare da gyarawa kana ya ɗauko blander ya zuba.

    Kallonsa Ummi tayi kana tace.

    “Ka bari fa da yaji kada yashiga Idon ka”.

    Kai ya girgiza tare da cewa.

    “A’a Ummi kibari in tayaki nima yau na samu ladan da Asma’u ke samu dana iyama ni zan miki girkin nan”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Ai dai kam hakan ma Nagode yayi Allah yayi albarka Ubangiji ya tsareka daga sharrin duk kan abinƙi kuma ai kafin Asma’u samun lada in sha Allah”.

    Kallonta yayi kana yace.

    “Ameen Ummina”.

    Ummi kuwa buɗe tukunyar tayi tare da zuba mai kana ta zuba jejjegen da M Jameel Yayi a blander.

    M Jameel dake gyara kifi banda ya juya ya kalli Ummi tare da cewa.

    “Ummi ya yau naji gidan Shiru ina Asma’u da Bashir”.

    Tana ɓare Maggi tace.

    “Sunje gidan Goggon su takwarar Asma’u”.

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Ayyah shiyasa yau naji gidan shiru sun barki ke kaɗai to Malam fa?”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Ai dai kam Malam kuma yaje wata rugar Fulani nan kusa amma sai gobe zai dawo acan zai kwana”.

     

    Kai ya jinjina tare da cewa.

    “Ashe dai yauma kam zan ta yaki ɗebe kewa gidan nan”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Ai dai kam ko zamu kwana ne?”.

    Ahankali ya juya ya kalleta tare da cewa.

    “Da nafi kowa farin ciki Ummina ace zan kwana gida ɗaya dake”.

    Murmushi Ummi tayi batare da tace komai ba.

    Ana kiran sallar maghariba suka gama dai-dai lokacin kuma Asma’u da Bashir suka dawo atare, alwala M Jameel Yayi kana Bashir ma yayi hannun Bashir ya riƙe suka tafi masallaci su kuma sukayi alwala tare da gabatar da Sallah.

    M Jameel kuwa koda suka idar da Sallah basu dawo ba saida sukayi Isha’i sannan suka fito.

    Asma’u kuwa Anutse ta fito daga Bedroom bayan ta idar da sallah kusa da Ummi ta zauna kana tace.

    “Ummina Ayyah yau aiki ke kaɗai”.

    Kallonta Ummi tayi kana tayi murmushi tare da cewa.

    “Ina kuwa nayi aiki Ni kaɗai Yayanku yazo ya tayani yau shiya mana miya ma”.

    Wara ido Asma’u tayi tare da sakin murmushi kana tace.

    “A lallai kai ashe yau zamu sha miyar Yaya kenan”.

    Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.

    “A sosai kam zaku sha miyar Yaya Jameel”.

    Atare M Jameel da Bashir suka shigo tare da zama.

     

    Gnin shigowarsu yasa ta miƙe tashiga kichen kular tuwon ta ɗauko kana ta koma ta ɗauko Plate-plate ta dawo Ummi ce ta karba ta sakawa M Jameel kana ta zuba masa miya agefe sannan ta zubawa Asma’u da Bashir.

    Ahankali M Jameel ya kalli Ummi kana ya kalli Asma’u da Bashir sai kuma ya kalli tuwon Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.

    “Toh Ummi muci tare mana musamu ladan cin abinci tare”.

    Ɗagowa Ummi tare da kallon sa kana tace.

    “Kuma dai”.

    Cikin wani irin yanayi ya gyaɗa mata kai kana yace.

    “Allah kuwa Ummi”.

    Kallonsa ya mayar kan Asma’u tare da cewa.

    “Asmeey jeki ɗauko Tray babba ki kawo mana”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa kana tace.

    “Toh Yaya Jameel”,.

    Sannan ta miƙe ta shiga kichen ɗin ta ɗauko Babban faranti ta fito dashi tana ƙoƙarin juyewa yace.

    “Kawo in zuba mana”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da faɗin.

    “Yah Jameel da kan ka kabari zan zuba mana”,

    Girgiza kai yayi kana yace.

    “A’a Asma’u kawo in zuba mana bana so ki wahalar da kanki”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Laaa Yah Jameel ka jika Allah zanyi mana”.

    Lumshe Idanunsa yayi tare da saurin dafe ƙirjinsa kana ya buɗe Idanunsa tare da Kallonsu ɗaya bayan ɗaya tare da cewa.

    “No Asmeey ki bari in zuba mana kaɗai”.

    Saurin Kallonsa tayi tare da miƙa masa Plate ɗin.

     

    Murmushi yayi tare ɗaukar Plate ɗin tuwon ya zuba musu akan babban farantin kana ya ɗauka ya ajiye musu Atsakiyar su tare da kallon Bashir yace.

    “Ɗauko Mana drinks”.

    Kai Bashir ya gyaɗa tare da cewa.

    “Toh”,Kana ya miƙe ya ɗauki Plate ya ɗebo drinks da swan water ya ajiye musu.

    Ya zauna sai ya zamana M Jameel da Ummi na facing juna Asma’u da Bashir ma na facing juna sai ya zama sunyi Cycle plate din na tsakiyar su.

     

    Ummi kuwa shiru tayi tare da zubawa M Jameel Ido Batare da tace komai ba kana tana jin wani irin yanayi mara misaltuwa azuciyarta wanda takasa sanin na menene hakanan ta tsinci kanta da Kallonsa acikin kwanakin nan.

    Ahankali M Jameel ya janyo kular miyar tare da ƙara musu namar da bandan kifi kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Hayya kuci yau zakuci miyar da baku taɓa ciba irinta ba dan ni nayita ko Ummi?”.

    Ya faɗa tare da ɗago kai sai yaga baki ɗaya Idanun Ummi na kansa faɗaɗa Murmushin fuskarsa yayi tare da cewa.

    “Kai Ummina ya dai?,Ai gaskiya na faɗa”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “A gaskiya ka faɗa kam”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Toh Ummi kici mana”.

    Dariya Ummi tayi tare da girgiza kai kana tace.

    “A’a kai da kayi dai ka fara ci muga result ɗin da fuskarka zai bayar kafin mufara ci”.

    Wara ido yayi tare da kallon Asma’u da Bashir da suma Kallonsa suke,

    “Toh ɗan Auta fara ɗana mana muji”.

    Kai Bashir ya gyaɗa kana ya gutsiri loma ɗaya yakai bakin sa lumshe ido yayi tare da haɗa yatsunsa hannu biyu alamar jinjina kana yace.

    “Kai amma miyar tayi daɗi gaskiya Yah Jameel na baka Award”.

    Murmushi Ummi tayi tare da kallon M Jameel da Yayi wani irin kyau na ban mamaki tamkar wanda aka sanya shi a inji aka sake ƙenƙesashi ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

    “Uyummm toni nayi bashi ba”.

    Dariya M Jameel Yayi wanda ya bayyanar da Fararen haƙoransa kana yace.

    “Toh na yarda Ummi mu duka biyu mukayi”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da kallon M Jameel kana tace.

    “Aikuwa Yaya Kayi ƙoƙari sosai amma muci kada yayi sanyi”.

    Kai suka gyaɗa atare kana lokaci ɗaya suka sanya hannunsu akan tuwon tare da kai tuwon bakinsu  lokaci ɗaya suka kalli juna tare da sakin murmushi.

    M Jameel kuwa murmushi ya saki tare da lumshe Idanunsa kana yace.

    “Ina ma ace zamu kasance ahaka ko yaushe mu riƙa zama tare nuna cin abinci atare da nafi kowa farin ciki”.

    Asma’u da takai nama bakinta ta kallesa kana tace.

    “Yah Jameel zamu kasance atare mana Insha Allah”.

    Kai ya Girgiza tare da cewa.

    “Dole wataran fa zan barku sai dai ku zauna ku uku kuci abinci ba tare dani ba”.

    Cikin sauri suka kallesa  Bashir yace.

    “A’a Yaya Jameel mai yasa zakace haka insha Allah zamu kasance atare”.

    Ummi kuwa Kallonsa kawai take.

    Murmushi M Jameel Yayi tare da kurɓan drinks kana yace.

    ”Dole wataran zan barku zanyi tafiya gari mai nisa wanda zan kasance Ni kaɗai acan batare da kuba nasan zanyi kewar ku kamar yanda zakuyi nawa tunda Abba ya dage dole zan koma Marrocco”.

    Kai suka gyaɗa tare da sauƙe ajiyar zuciya kana suka ci gaba da cin abinci batare da wanin su ya sake magana ba sai dai lokaci zuwa lokaci yakan kallesu tare da sakin murmushi.

     

    Wayar M Jameel ne ya karaɗe wajen da ruri ahankali ya ɗauka tare da sakin murmushi kana yayi Picking tare da Sallama.

    Daga ɗaya ɓangaren kuwa cikin sanyin murya Moddibo yace.

    “J ina ka tsaya na jika shiru ko abinci banci ba, sannan kasan bani da lafiya ko dai har yanzu kana gidan Ummi ne?”.

    Murmushi M Jameel Yayi tare da gyara zaman wayar akunnensa kana yace.

    “Ayyah sannu A.J Please kaci abinci sannan ka sake shan maganin dana haɗa maka Insha Allah ina hanya”.

    Lumshe idanu Moddibo yayi tare da sakin ajiyar zuciya kana.

    “Toh shikenan sai kazo kace ina Gaishe da Ummina”.

    Murmushi M Jameel Yayi tare da kallon Ummi dake sauraron duk abinda suke faɗa kana yace.

    “Zata ji”,daga haka ya katse kiran.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “Ohh ina ga dai wannan ko kunyi Aure gida ɗaya zaku zauna bakwa iya minti talatin batare da kunga juna ba ko kuma kunji muryan juna”.

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Ai dai kam dole watarana arabu”.

    Jinjina kai Ummi tayi,tana murmushi kana suka cigaba da cin abincin.

     

    Bayan sun cinye tuwon farantin M Jameel ya Kalli Ummi tare da cewa.

    “Ummi aƙara mana yau ina jin daɗin abinci ina so inci³ incika cikina dan ban sani ba sai kuma yaushe zan sake ci”.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “A’a to ai ko yaushe ma kakeso ai zaka zo kaci”.

    Lumshe Idanunsa yayi tare da buɗe su akan Ummi kana yace.

    “Toh Ummi kwanan nan zamu fara batun aikin nan kinga in dan na tafi Marocco ai bazan dinga samun ciba”.

    Kai ta jinjina tare da faɗin.

    “Ai in dai nan da ne ba nisa bane dashi idan ya kama sai inmaka miya da komai duk zan aika maka dasu idan yaso saika na sawa a fridge”.

    Murmushi Yayi tare da cewa.

    “Hmmyyym Ummina Allah ya ƙara miki nisan kwana mai amfani Allah ya barmu tare”.

    Jingjna kai tayi tare da faɗin.

    “Ameen Babana Allah ya ƙara maka nisan kwana inga har jikokin ka”.

    Murmushi yayi tare da kallonta kana yace.

    “Hmmm Ummina kenan.

    Kin ko san in sha Allah ƴata ta farko sunanki zan samata,

    Na kuwa tabbatar zata ga soyayya ko ƙuda bazan bari ya taɓa ta ba”.

    Kallonsa Ummi tayi tare da cewa.

    “Jamiluuu na”.

    taja sunan tana murmushi haka nan take jin daɗin kiran sunan sa.

     

    Bayan sun kammala cin abincin Asma’u ta miƙe tare da tattare Plate ta Kai kichen M Jameel kuwa da kansa ya mike ya ɗauki kular abincin ya kai kichen Ummi kuwa Kallonsa ta riƙa yi cike da so.

    Bayan ya ajiye ya fito, woje ya nufa yana cewa

     

    “Bari in ɗauko abu a mota”.

    Toh Ummi tace kana ta meda hankali kan tv.

    Jim kaɗan da fitar da ya shigo riƙe da kwalayen waya masu kyau.

    Ƙirar Samson, kana ya  dawo ya zauna gefen Ummi Asma’u da Bashir suka zauna daga gefensa gyaran murya yayi tare da fuskantar Asma’u kana yace.

    “Ga woyoyinku nan Asma’u yau dai na cika alƙawarin ko”.

    Cikin tsananin jin dadi Bashir ya ruggumshi, yayinda Asma’u kuwa Ummu ta ruggume.

    Cikin son juna suka rinƙayi mishi godiya tare da fatan al’khairi.

    Murmushin jin dadi yayi tare da shafa kan Bashir kana yace.

    “Asma’u yanzu ke wani irin makaranta kike so?”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Yah Jameel duk makarantar da ka zaɓa min ina sonta ina farin ciki da ita”.

    Jinjina kai yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya kana yace.

    “Zan kuwa zaɓa miki wanda ya dace dake  Insha Allah naga keda ƙawarki kusan ra’ayin ku ɗaya ko yaushe amman wannan karon an samu akasi ita Jenouelist take fata naga ke kuma likitanci kike son karanta”.

    Kallon Bashir yayi tare da cewa.

    “Kai kuma wani irin Makaranta kake so?”.

    Murmushi Bashir yayi kana yace.

    “Duk wanda ka zaɓa min Yaya”.

    Lumshe idanu M Jameel Yayi tare da cewa.

    “Insha Allah kuwa zan zaɓa maka ina ganin Law zaka karanta zaifi dacewa da kai”.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kana ya tsira musu ido tare da cewa.

    “Asma’u”.

    Kanta ta ɗago tare da cewa.

    “Na’am Yaya”.

    Anutse ya kalleta cikin yanayin nutsuwarsa da alamun rashin wasa yace.

    “Kinga ke ƴa macece ita rayuwar duniyar nan duk i da ƴa mace ta tsinci kanta ta tsare mutuncinta da darajar ta shine abu mafi daraja ki kiyaye tarbiyyar da muka sha wahalar baki nida Ummi kada ki kunya tamu kada kisa ta baƙin ciki”.

    A hankali ya sauƙe numfashi tare da gyara zamansa kana yace.

    “Saboda ke ƴa macece ke mukafi taraddadi akan ki kinga yanzu ga Bashir amma bana ta raddadi akansa kamar ke mace”.

    Asma’u kuwa ƙasa ta sakeyi da kanta batare da tace komai ba sai wasa da yatsun hannunta da take yi.

     

    lumshe idanunsa yayi kana yace.

    “Burina da fatana inga mun kasance gida ɗaya muhalli ɗaya wallahi akanki da Bashir da kuma Ummin mu yasa nake so inyi Aure inga muna tare”.

    Sai kuma ya kalli Bashir da shima yayi ƙasa da kansa kana yace.

    “Ina so inga lokacin tafiyarku makarantar kana inga lokacin dawowan ku a idona sannan insan kalar mutanen da kuke mu’amala dasu”.

    Sai kuma ya juyo ya kalli Asma’u cikin yaƙini yace.

    “Na yarda da ƙawancen ku da Khausar saboda tana da tarbiyya duk da kuwa tana da rawan kai”.

    Numfasa yayi tare da kallon ta kana cikin raunin murya yace.

    “Asma’u ki kula da rayuwarki sannan kisan irin mutanen da zaki dinga alaƙa dasu idan kuma har Aure kike so Asma’u ki faɗa min idan yaso idan kikayi aure sai ki cigaba da karatun ki agidan mijinki kada ki ɓoye min ki faɗa min komai ki ɗaukeni tamkar ƴar Uwarki mace”.

     

    Cike da kunya Asma’u tayi ƙasa da kanta tare da girgiza kanta kana tace.

    “A’a Yah Jameel nikam karatu zanyi”.

    Kai ya gyaɗa tare da cewa.

    “Kin tabbatar ba Aure kike so ba sannan babu wanda kike so?”.

    Cike da kunya ta girgiza masa kai tare da faɗin.

    “Yaya Jameel Ni kuma wazan so kuma babu wanda ke zuwa gurina”.

     

    Dariya M Jameel Yayi tare da kallonta kana yace.

    “Mun shiga uku Ummi kadde ƙanwar tawa baƙin jini take dashi?”.

    Murmushi Ummi dake aikin Kallonsu tayi tare da faɗin.

    “Ba wani baƙin jini kawai dai dake tana kiyaye kanta ne babu wanda ke kawo mata wargi”.

    Jinjina kai yayi tare da dai-dai-ta nutsuwarsa kana yace.

    “Toh shikenan Asma’u tun da dai kin bani tabbacin karatu kike so daga nan harki kai digir-gire ki gama har ki taka duk kan matakin da kike so nayi al’ƙawarin zan taimaka miki da duk kan ƙarfina da kuɗina muddin ina numfashi zan tsaya miki”.

     

    Kallon Bashir yayi tare da cewa.

    “Sannan kai kuma Bashir zaka karanci fannin Law tunda kana da ilimin addini ina da yaƙinin zaka tsaya akan gaskiya duk runtsi duk wuya kada Kabi bayan ƙarya ka kasance mai al’ƙawarin  da rikon amana aduk inda ka tsinci kan ka”.

    Jinjina kai Bashir yayi kana yace.

    “Yah Jameel Insha Allah Nayi alƙawari zan kasance ayanda kake fata”.

     

    Hira suka cigaba dayi sosai irin wanda suka ɗauki tsawon lokaci basuyi irin saba wanda har dare yaraba basu lura ba.

    Ahankali Ummi dake murmushi ta daga kanta Idanunta suka sauka akan agogon dake manne abango wanda ke nuni da ƙarfe sha biyu da minti goma,Cikin sauri ta kalli M Jameel tare da cewa.

    “Jamilu”.

    Anutse ya ɗago ya kalleta tare da cewa.

    “Na’am Ummina”.

    Ta sauƙe ajiyar zuciya tare da Kallonsa kana ta sake kallon agogon zuciyarta na bugawa tayi saurin dafe ƙirjinta kana tace.

    “Ka kalli time fa”.

    Cikin sauri M Jameel ya juya Kalli agogo tare da kallon Ummi kana…!

    Cikin sakin fuska yace.

    “Ummi yau anan zan kwana”.

    Cike da mamaki Ummi ta juya ta kallesa, domin tunda Allah yasa tayi aure agidan mahaifin Asma’u bai taɓa kwana ba, sai dai yakan zo aduk sanda yaga dama, a hankali ta sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Anan zaka kwana?”.

    Kai ya jinjina tare da faɗin.

    “Eh zan kwana Ummina”.

    Kallon Ummi Bashir yayi cike da farin ciki ya langwaɓar da kai kana yace.

    “Ayyah Ummi ki barshi kinga yanzu ma dare yayi ki gani fa sha biyu hadda kwata dare fa ya riga da yayi nisa”.

    Cikin sanyin murya me ɗauke da farin ciki Asma’u tace.

    “Gaskiya dai kam mu kwana kawai Yah Jameel, yau nayi matuƙar farin ciki zamu kwana agida ɗaya Allah ya nuna mana ranan Aurenka mu kasance atare na har abadan”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da shafa sajensa kana ya tsira musu ido tare da lumshe idanunsa, a hankali ya sauƙe ajiyar zuciya kana yace.

    “Asmeey zamu kasance atare in sha Allah zanyi Aure kana zaku kasance  gida me kyau da na al’farma da kwanciyar hankali, ni kaina bansan kamannin gidan ba amma na sani gida ne mai masifar kyau da ɗaukar hankali zan riska in sha Allah”,

    Sai kuma ya sauƙe numfashi tare da lumshe idanunsa kana yaci gaba da cewa.

    “Wanda kowa ke burin samu, in Sha Allah zan sameshi, domin inaji ajikina na kusa isa wannan gidan kafin ku iso zan kasance cikin farin ciki amma idan ina tare daku zanfi farin ciki na zai fi nin kuwa”.

    Cikin yanayin sanyin jiki ya tsira musu ido su duka ukun.

    Ummi kuwa idanu ta zuba masa ko ƙyaftawa ba tayi wani irin yanayi takeji azuciyarta, wanda takasa tantance na menene.

    Asma’u kuwa murmushi tayi tare da Kallonsa kana tace.

    “Yaya Jameel Allah ya baka mace ta gari wacce zata kula da Ummin mu tamkar yanda kake kulawa da ita sannan ta ƙaunace mu tamkar yanda kake ƙaunar mu”.

    Murmushi yayi kana ya lumshe idanunsa tare da cewa.

    “Insha Allah Asmeey matar da zan Aura, macece wacce ta fito daga babban gidane masu tarbiyya da kamala, wacce zata riƙe Ummina daku tamkar Iyayen ta da kuma ƙannenta”.

     

    Sai kuma ya numfasa tare da tsira mata ido.

     

    Kai Asma’u ta gyaɗa murya cike da jin daɗi tace.

    “Ni kuwa Yah Jameel Nayi maka al’ƙawarin zan kasance mata tamkar yar uwa Aminiya yadda kake fata har ma fiye da haka”.

    Sassayan numfashi ya fesar kana yace.

    “Alhamdulillah Asmeey idan kika min haka ko a ina na kasance zanyi al’fari dake sannan zanyi farin ciki”.

    Sai kuma ya maida kallonsa kan Bashir tare da cewa.

    “Yauwa kai kuma Bashir”.

    Anutse ya ɗago kansa tare da faɗin.

    “Na’am Yah Jameel”.

    cikin sanyin murya yace.

    “Bashir ka maida hankalin ka akan karatun ka, kada ka biyewa aboka nan banza kasan dawaye ya dace kayi abota kada ka biyewa matan banza da abokan baza kada kasa Ummi tayi Allah wadai da halayyar ka”.

    Ƙasa da kai Bashir yayi yayin da Ummi kuma shiru tai tana mai jin daɗin Nasiyyar da yake wa ƙannensa.

    A hankali ya numfasa kana yaci gaba cewa.

    “Bashir aikin Law aikine mai matuƙar daraja da muhimmanci sai dai wasu sun ɓata aikin da cin hanci da rashawa da tauye haƙƙin masu gaskiya, da tozartasu, ina so kamin alƙawari kai zaka kasance mutum mai adalci da karamci akan aikinsa wanda duniya za tayi al’fahari da kai sannan Ummina tayi farin ciki da rayuwarka”.

    Sai kuma ya ɗanyi shiru yana kallon yadda Bashir ke gyaɗa masa kai alamar nasihar na ratsashi, cikin yanayin lallashi da jan hankali yaci gaba.

    “Dan Allah Bashir kada ka bari adalilinka Al’umma su la’anci Ummina suyi Allah wadai da haihuwarka da tayi”.

    Cikin rawan murya Bashir yace.

    “In sha Allah zan zama yanda kake da buri har ma fiye da haka Yah Jameel”.

    Lumshe Idanu M Jameel Yayi tare da shafa sajensa kana cikin sanyin murya yace.

    “Nagode Bashir tabbas ko bayan ba nan Idan ka kasance mutumin kirki zanyi farin ciki, sannan ka kula min da Ummina da Asma’u kada ka bari hawayen baƙin ciki ya zubo daga idanunsu ni dai burina kayi min wannan al’ƙawarin”.

    Jinjina kai Bashir yayi tare da cewa.

    “Nayi maka alƙawari Yah Jameel Ummi da Asma’u baza su taɓa baƙin ciki dani ba, kullum zan saka su farin ciki sannan zan kasance mai riƙon alƙawari aduk inda na tsinci kaina”.

     

    Murmushi M Jameel Yayi Idanunsa alumshe yace.

    “Alhamdulillah³ Allah na gode maka”.

    Anutse ya juya ya kalli Ummi data tsira musu Ido kana cikin sanyin murya yace.

    “Yauwa Ummina faɗamin me kike buƙata ko kuma kike so arayuwar ki nayi miki?”.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tayi murmushi tare da cewa.

    “Toh ni kuma meya rage arayuwa wanda baka yimin ba Jamilu?

    Ai ni kam kayi min komai sai dai Ubangiji Allah ya maka albarka Allah yabaka ƴaƴan da zasu yi maka biyayya”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “Ameen Ummina amma yanzu baki da wata damuwa ko buƙata?”.

    Murmushi tayi tare da cewa.

    “Bani da wani damuwa ko buƙata aduniya Jamilu, domin kafin na buƙaci komai ma kiyi min”.

    Hannunsa biyu ya ɗaga sama tare da faɗin.

    “Alhamdulillah Allah Nagode maka ya Ubangijin Allah ka bani damar da duk ɓuƙatar da mahaifiyata take dashi kafin ma ta buƙata nayi mata shi”.

     

    Murmushi tayi kana tace.

    “Ameen Ubangiji Allah ya maka albarka Allah ya rufa maka asiri duniya da lahira Allah yasa ƴaƴan ka su ramamaka abinda kayi mana”.

    Still Fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Ameen ya Allah”.

    Ummi kuwa ahankali ta daga kanta gani tayi har ƙarfe uku kallonta ta mayar kansu kana tace.

    “Yanzu yaranan baza ku tashi kuje ku kwanta ba ku dubi time fa”.

    Atare Asma’u da Bashir suka ce.

    “Toh Ummi am gaba ɗaya yau bama jin baccin ma”.

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Ai dai kam”,

    Ummi kuwa murmushi tayi kana suka cigaba da hira.

    Jin ankira Sallar ƙarfe huɗu yasa Ummi kallon su tare da faɗin.

    “Toh yanzu kam mutashi muyi alwala muyi nafillah mu rufe wannan daren da roƙon Ubangiji”.

     

    Bayan duk sunyi Al’wala ne suka dawo falo duk suka shimfida Sallaya sukayi nafila raka’a huɗu-hudu.

     

    M Jameel kuwa acikin sujjadar ta ƙarshene yace.

    “Ya Allah katsare min Mahaifiyata da ƙannena Ubangiji ka zama gatansu anan duniya da lahira ya Allah ka tsaresu daga sharrin abin ƙi Ubangiji ka inganta rayuwar Asma’u da Bashir ya Allah ka tabbatarwa da A.J na al’khairi a cikin samun mace tagari wacce zata kula da ɗawainiyarsa ya Allah kabiyawa duk musulmi ɓuƙatar su na Alkhairi”.

    Ko wannensu haka ya dinga addu’a saida aka kira Assalatu kafin suka miƙe Shida Bashir suka tafi masallaci Asma’u da Ummi kuwa anan suka Idar da Sallah.

     

    Bayan sun dawa daga masallaci M Jameel ya kwanta akan 3sitter Ummi Atake Bacci mai daɗi ya ɗaukesa.

    Ummi da Asma’u kuwa kichen suka shiga tare da soya musu soyayyen dankali da ƙwai kana suka tafasa ruwan tea da yaji citta da kanumfari sai kuma tayi musu ɗumamen tuwon jiya, ganin yadda yaketa zuba tururine yasa Asma’u tas hannun da nufin buɗe  murfin tukunya, zafin da taji ya ratsa ƴan yatsunta ne yasa ta saki karfin ya faɗi ƙasa tare da bada ƙara.

    Cikin sauri Ummi ta kalleta kana cikin ƙasa da murya tace.

    “Kai Asma’u kiyi a hankali mana kada ki tashi yayan ku, bakiga jiya bai samu bacci ba”.

    Murmushi Asma’u tare da gyaɗa mata kai kana tace.

    “Toh Ummi”.

     

    Har misalin ƙarfe tara M Jameel bai far kaba Ummi kuwa toilet tashiga tayi wanka bayan ta shirya ta fito falon har zuwa lokacin M Jameel na bacci ahankali ta zauna agefensa tare da tsira masa idanu tana kallon yanda yake baccin cikin kwanciyar hankali tamkar yana murmushi kyawun fuskarsa ya sake nunkuwa fiye da ko yaushe.

     

    Asma’u data fito daga kichen ta kalli Ummi kana ta saki murmushi tare da cewa.

    “Kayyy Ummi irin wannan kallon sai kace kin samu TV ”.

    Sai asannan Ummi ta ɗauke Idanunta daga kansa ta mayar kan Asma’u tare da yi mata daƙuwa.

    Murmushi Asma’u tayi kana tace.

    “Ai gaskiya ne”.

    Bashir daya shigo Bedroom din yayi dariya kana yace.

    “Gsky dai Ummi kwanan nan kina yawan kallon Yah Jameel ko dan yafi mu kyaune?”.

    Wara ido tayi tare da sakin murmushi kana tace.

    “Waya faɗa maka yafi ka kyau ai kafisa”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Ummina kin dai faɗa min inji daɗi ne kawai”.

    M Jameel kuwa cikin bacci yake jiyo hiransu sama-sana ahankali ya motsa.

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da kallon sa kana tace.

    “Toh katashi kayi Breakfast. Idan yaso sai ka koma baccin”.

    Cikin sauri ya buɗe Idanunsa tare da Kallon Ummi kana yace.

    “Uhmmm Ummi sai anjima”.

    Kansa ta shafa kana tace.

    “A’a tashi kaci abinci, bana son bacci da yunwa Babana”.

    Hannunta ya riƙe kana yace.

    “Naji daɗina Ummina ta kirani da Babana Abbana ya kirani da Babana”.

    Miƙewa yayi ya zauna tare da cewa.

    “Ummina banyi wanka ba sannan banyi brush ba ba zan iya Breakfast ba”.

    Girgiza kai Ummi tayi tare da faɗin.

    “Aikam dai gashi tun ɗazu na bawa Bashir kuɗi ya sayo maka Brush kafin ka tashi ga Brush ga Maclean kayi”.

    Miƙewa yayi kana ya ɗauka, toilet dake falon yashiga ya wanke bakakinsa.

    Asma’u kuwa tun shigansa toilet ta Miƙe tankwaso musu kayan Breakfast ɗin yau ma kamar jiya haka atare sukayi Breakfast ɗin.

    A hankali ya kai kofin tea bakinsa sai kuma yayi sauri ajiye cup din jin wayarsa ta hau ruri Asma’u dake kusa da wayar ta miƙa masa karɓa yayi tare da sakin murmushi kana yayi Picking tare da cewa.

    “Assalamu Alaikum A.J”.

    Daga ɗaya ɓangaren Moddibo ne yace.

    “J yana jika shiru gashi Innayi ta haɗa mana Breakfast na kasa ci ni kaɗai”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da kallon Ummi, Asma’u,da Bashir kana yace.

    “A.J gani tare da Ummina da Asma’u da kuma Bashir muna Breakfast tray ɗaya kamar yanda mukayi jiya, ina jin farin ciki inaji kamar wani gurbi na cike wanda ban samu damar cike saba tsawon shekaru”.

    Lumshe idanu Moddibo yayi kana ya gyaɗa kansa tabbas ya fahimci farin cikin da M Jameel ke ciki ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.

    “Shikenan hakan yayi kyau bawa Ummina mu gaisa”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da miƙawa Ummi wayar.

    Cike da so Ummi tace.

    “Babana na ƙwace maka Amini ko?”.

    Murmushi Moddibo yayi wanda take iya jiyo sautin sa kana cike da ladabi yace.

    “Ayyah Ummina bakomai ai kawai ina kewar sa ne Ina kwana?”.

    Murmushi tayi tare da faɗin.

    “Lafiya Lau ya Innayi?”.

    Ahankali yace.

    “Tana lafiya tace agaishe  ki”.

    Daga haka sukayi sallama tare da katse kiran Bayan sun kammala Breakfast ɗin Asma’u ta tattare kwanikan kare da kaiwa kichen kana ta dawo ta gyara wajen.

    M Jameel kuwa jingina kansa da guiwar Ummi yayi kana suka cigaba da hira cike da tsananin ƙaunar junansu…!

     

     

     

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 4

    Sakayyah 4

     

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 4_

     

    *NA*

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

    *Free page*

     

    *KADA DAI KU MANTA WANNAN FREE PAGE NE, KI KI BIYA KI KARANTA CIKIB AMINCI BA HAƘƘIN WANI GABA GAREKI SAKAYYAH 1k ne kacal ƴar uwa. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

     

     

    *Al’bishirunku Ma’aurata, GA GARKUWAR KU nan tafe muku da tsarabobi na musamman gareku ma’aurata daga cibiyar mgnin mata mai taken  GARKUWAR MA’AURATA*

     

    NI DAI AYSHA Ɗiyar ALIYU GARKUWA.

    Ina matukar mamakin wani irin lokaci da ya riske mu mai wahalallan fassara. Kullum dai magana daya ce, akan ma’aurata, fada, rashin jituwa, mutuwar aure, akan kuskure kalilan, rashin kula, rashin yi wa juna uziri. Toh wai duk me ya janyo hakan? Na zurfafa a tsananin tunani hakan ya tilasta min bincike mai tarin yawa wanda ya kai ni ga gano inda matsalar take? Shin yar’uwa ke macece amma kin san wacece mace ku? Kin san me ake kira mace kuwa? Mace ita ce matar da take zama iyali a wajan namiji ta zame masa bango, sanyin idaniyarsa, ta zame masa gata da farin cikin rayuwarsa ta zame masa ruwa abar kore ƙishinsa ta zame masa mayafi mai karesa daga gigitar kadaici, ta kuma dorar da mijinta kan turbar gaskiya, ta kashe masa jiki da salonta ta rikita shi da baiwa da ni’imar da Allah ya bata idan har ta san hanyar mayar da kanta sabuwa dal awajanta, wato kullun takasance masa tamkar amarya har ya kasa tantance daren amarcinsu da sauran dararen rakun rayuwar su.

     

    Wannan ita ce mace. Ina da wata saukakkar hanyar da zaki zama abar so da kulawa da soyayya a wajan mijinki ta hanya mafi sauki, 09097853276 hanyar ita ce ki gwada amfani da kayana na gyara ki gani, ina mai tabbatar miki da in sha Allahu sai kin dara da murna sai kuma kin gode min. Kayana kaya ne da aka yi shi da zallan itacanmu na gado marasa illa a cikin jikin dan adam musamman mace, kaya ne da suke taimakawa (sex hormones 😍) dinki.

    Misali kina kallon India😘, hollywood, Asian film🥰 kina ganin yanda mazansu ke nunawa matansu tsananin soyayya kamar su ba su kyautar ransu!?

    Saboda me hakan? Saboda suna sadaukar da lokacinsu wajan gyara jikinsu da kayan da ke tsattsafo da ni’ima cike da tsukewa, kayan nan kuma ana yinsu ne zallar magungunan gargajiya wanda ba su da illa domin haɗine na ingantattun itatuwa da yayansu.

    Ina baiwar Allahn da miji ke daure mata fuska babu hirar arziki?

    Zo ki ji yar’uwa zan baki gumbata da zallar gari wanda aka yi su da nagartattun itacen da ke da matukar amfani a jikin mace. Gubar ciko, gumbar tsalle dole, gubar da ba’a baiwa mai kishiya, garin maɗi, garin mallaka, tsumin goron tula, tsumin tsartai, tsumin maratsi, pala-pala butar sirri, kwanon k’asaitacciyar mace, furar mata madararta gareki Hajia takenta sha yanzu mgni yanzu,

    Ina mata masu fama da sanyi? Sanyin mara ji zo na hadaki da magani na na sanyi wanda yake wanke mara ya fitar da duk wata cuta da ke samun mazauni a wajan set ɗin 10k ne kacal wlh koda sanyin mahaifane in sha Allah zakiji saukin.

    Ina da ciccibi mai kyau. Ina da hadin amare mai kyau wanda zai gyara yarinya ya kankaro mata kimarta akwai hadin mai jego wanda muke yinsa na asali inada kekkyawan Hadi maida tsohuwa yarinya.

     

    Akwai ɗaya bangaren wato *KAMSHI*

    Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu’umar humra, kana da kulaccar sirri sayan na gari maida kuɗi gida, banda harkar karanta yayin gyara Hajia.

     

    Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

     

    🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA

    *(GARKUWAR MA’AURATA)*

     

     

    Tana dirowa hannunta dake dungule da Appel  suka sauƙa kan ƙafarsa.

    Yayinda yatsun hannunta dake ɗauke da zoban azurfa na kusa da da ƙaramin yatsa da kuma ƙaramin suka sauƙa akan  faratun yatsun sa,

    atake yatsun hannunta suka bada sautin ƙash! yayin da shi ma Moddibo yatsun ƙafansa suka bada sautin ƙas-ƙas!, Idanshi ya rumtse da sauri, sabida wani irin masifaffen zogi da yaji ya ratsa sa cikin sauri ya tsugunna da niyyan matsasu tuni ɗanƙwalin ta ya zame yalwataccen sumar kanta baƙi daya sauƙa zuwa kafarɗarta ya zubo yana fitar da wani sihirtaccen ƙamshi…

     

    Khausar kuwa jin zafin daya ratsa ƙafarta data malkoɗe ne  yasa ta furta.

    “Wayyyo Allah ƙafata!”. ta faɗa da ƙarfi  tare da ɗago kanta yayin da yalwataccen sumar kanta ya rufe mata fuska da sauri tasa hannu ta janye ta ɗago kanta.

    Idanunta ne suka sauƙa akan Moddibo dake durƙushe, cikin ruɗewa da tsanananin tsoronsa ta  ɗauki ɗan kwalinta kana ta miƙe da gudu tana cewa.

     

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n dan Allah kayi haƙuri wallahi Allah bansani ba”.

    Ta faɗa tana ƙoƙarin fita daga gate ɗin.

     

    Asma’u kuwa fitowarta daga gate ɗin da zai sadaka da cikin farfajiyar  Innayi kenan ta hango Khausar na shirin fita babu ɗan kwali akanta.

    Cikin Sassarfa tabi bayanta tana faɗin.

    “Khausar! Khausar!! Khausar!!!”.

    ta kira sunanta har sau uku Kafin ta sake cewa.

    “Dan Allah kada ki fita ahaka Khausar ki tsaya”.

     

    Moddibo kuwa cikin yanayin nutsuwarsa da kuma sanyinsa ya kira sunanta da faɗin.

    “Asma’u”.

    Saidai akwai alamun ɓacin rai acikin sautin Muryansa.

     

    Atsorace Asma’u ta juya Idanunta cike da tsoro tace.

    “Na’am Yah Moddibo”.

    Tsayuwarsa ya gyara  tare da lumshe idanunsa masu ƙwarjini da haiba kana ya buɗe su ya dubi Asma’u da har yanzu take tsaye da tsoro a idanunta yace.

    “Meyesa zaki ɗauko Biri ki kawo mana gida!?”.

    Ya ƙare mgnar da bin Khausar da ido wacce tuni ta kai bakin gate.

     

    Asma’u kuwa saurin ɗagowa tayi ta dubesa jin ya kira Khausar da Biri saidai bata yarda sun haɗa ido ba.

    Shi kuwa cike da takaici

    ya cigaba da cewa.

    “Koda wasa kada ki sake zuwa da wannan yarinyar gidan nan, tunda ita bata da hankali da kuma nutsuwa da kamun kai”.

    Ya ƙarashe mgnar yana mai lumshe idanunsa dake cike da ƙwarjini har zuwa sannan yatsun ƙafar na masa rawa tamkar alokacin ta buga masa yatsunsa.

     

    Ajiyar zuciya Asma’u ta sauƙe ganin tuni Khausar ta fice kanta a ƙasa tace.

    “Dan Allah kayi haƙuri Insha Allah hakan bazai sake faruwa ba”.

    Moddibo kuwa baice da ita Komai ba saima lumshe idanunsa da yayi yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yaci gaba da yi.

     

    Ita kuwa Asma’u jin baice komai ba yasa ta juya cikin sassarfa ta nufi gate dan bin bayan Khausar…

     

    M Jameel dake zaune cikin falon Moddibo kuwa wanda ya tsirawa window idanu yana ganin duk abinda ya faru ya saki lallausan murmushi tare da miƙewa yana gyara zaman Farin t-shirt da blue jeans dake jikinsa kana ya sanya hannu ya buɗe ƙofan falon ya fito fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi cikin yanayin sa na ƙaunar Amininsa  yace.

    “Ba sa ido ba?,ka fita sabgar yarinya ka ƙi yanzu inba sa’a ba kasa taji ciwo dan naga lokacin da take gudu tana ɗin gishi”.

    Moddibo kuwa buɗe idanunsa dake lumshe yayi tare da zab gawa M Jameel Harara cikin yanayin nutsuwarsa daya zame masa jiki yace.

    “Dama karyewa tayi da shi yafi yarinya bataji bata da hankali ko kaɗan”.

     

    Da gudu Asma’u ke bin Khausar tana cewa.

    “Khausar ki jira ni mana”.

    Ƙin tanka mata Khausar tayi tana cigaba da sassarfa yayin da ko wani gaɓa na jikinta ke rawa kana tana cigaba da ɗaure gashinta daya baje kasancewar unguwa ce da babu hayaniyar mutane yayin da take yarfe hannunta dake masifar zugi kana tana me ɗingisa ƙafarta.

    Ganin da gaske Khausar ba zata tsaya ba yasa Asma’u ta ƙara gudunta har ta isa inda take tana sauƙe numfashi saboda gudun da tayi tace.

    “Ayyah Khausar ki tsaya mana ga hijabinki saka”.

    Hannunta tasa ta amshi hijabin nata tare da zirashi a jikinta kana taci gaba da tafi.

    “Ayyah Khausar ki tsaya mana”.

    Asma’u ta kuma faɗa tare da shan gabanta,

    a raunane  tace.

     

    “Bazan tsaya ba Asma’u meyesa zaki min haka Asma’u? banyi tsammanin zaki yimin haka ba gidansu Moddibo kika kawoni mutumin da kin san baya ko son ganina.

    Gashi yanzu kinsa na buga masa yatsuna masu zobe aƙafa naji masa ciwo,yanzu bansan  wani irin hukunci zai ɗauka akaina ba”.

     

    Tsoron Khausar ɗaya kada Moddibo yace zai zaneta duk irin rashin ji da ƙiriniyarta tana matuƙar tsoron bulala kana tasan duk hukuncin da Moddibo zai ɗauka bazai wuce yasa Malam Bello ya zaneta idan taje Hadda.

     

    Cikin sanyin murya Asma’u tace.

    “Ayyah Khausar kiyi haƙuri, amman kuma ai da kinji mgnata da haka bai faruba. kece bakya ji sannan ba kyaso ataɓa lafiyar jikinki”.

    Kallonta Khausar tayi da Idanunta dake cike da tsoro da kuma fargaba tace.

    “Meyesa zaki ce haka Asma’u kawai naga Appel da inabin ne ya ban sha’awa shiyasa na cira”.

     

    Kai Asma’u ta girgiza tace.

    “Inabi Khausar? na tabbata duk wannan abubuwan da kika gani akwai su a gidanku ku fiye ma da hakan”.

     

    Sake Marerece fuska Khausar tayi tace.

    “Na ganine ya bani sha’awa laifi ne dan na cire!?”.

    Murmushi Asma’u tayi ganin har zuwa lokacin Atsorace Khausar take sai kuma tace.

    “Kema dai baki jira kanki ba daga zuwa gidan mutane sai ki fara cire musu abu batare da neman izini ba”.

     

    Ita kuwa khausar jin abinda Asma’u tace yasa ta watsa mata Harara cike da tsiwa tace

    “Tun da kinsan gidan masu baƙin hali zaki je Meyesa zaki ɗaukeni ki kaini?, Kisa aranki daga yau babu inda zan sake rakaki tunda haka kikayi min”.

     

    Wara ido Asma’u tayi sai kuma ta langwaɓar da kai tace.

    “Kiyi haƙuri Khausar bansan haka zai faru ba ni kawai da niyyar mu gaida Innayi nace ki raka ni amma kada kice baza ki sake raka niba na tuba”.

     

    Kallonta kawai Khausar tayi amma ba tace komai ba, sake langwaɓar da kai Asma’u tayi cike da tausayinta tace.

    “Ki zauna awancan dakalin se inja miki ƙafar!”

     

    Kai Khausar ta girgiza tana rintse Idanunta tace.

    “Basai kin ja minba kawai sama mana adedeta mu hau”.

    Kai Asma’u ta jinjina tare da riƙe hannunta suka ɗan tsaya bakin titi cikin sa’a tsayuwar su babu daɗewa suka samu adedeta hawa sukayi tare da yimasa kwatancen inda ze kaisu…

     

    Aƙofar gida me Adedeta ya sauƙe su bayan sun isa Asma’u ce ta ciro kuɗi ta basa kana ta riƙe hannun Khausar suka nufi gate Khausar ce tasa hannu ta tura gate ɗin cikin rashin sani suka buge juna da Samira Sani wacce ke ƙoƙarin fita Amina na biye da ita.

     

    Saurin ɗago kai Khausar tayi jin Samira Sani na cewa.

    Ke ‘yar uban waye da zaki haɗa kafaɗa dani shin dame kike taƙama!?”.

    Kamar Khausar za tace wani abu sai kuma ta fasa taja siririn tsaki tare da jan hannu Asma’u suka bar wajen tana me cigaba da ɗingisa ƙafarta.

    Ƙwafa Samira Sani tayi cikin kumfar baki tare da tsanan Khausar aranta tace da Amina.

    “Wallahi na tsani wannan shegiyar yarinyar me kama da sadaka yalla Idan ban sabautata ba bazan taɓa samun nutsuwa ba!”.

    Tsaki Amina taja tana kallon Samira tace.

    “Allah ne kaɗai yasan irin abinda zan mata”.

     

    Kafin su ƙarasa shiga falon Khausar ta janye hannunta dake cikin na Asma’u kana ta gyara tsayuwar tare da dai-dai ta tafiyarta tana me rintse Idanunta sam bataso Momy ta fahimci abinda ya sameta.

    Asma’u kuwa kallon ta tayi cike da tausayinta amma batace komai ba Ƙofan falon suka tura

    suka shiga tare da haɗa baki wajen cewa.

     

    “Assalamu Alaikum”.

    Momy dake zaune kan kujera ta ɗaura ɗaya kan ɗaya ce ta faɗaɗa Murmushin fuskarta tace.

    “Wa’alaikum salam har kun dawo?”.

    Zama suka yi daga gefen ƙafarta aƙasan chanis capet Asma’u tace.

    “Eh Momy”.

     

    “Masha Allah ya jikin Innayin?”.

    Cewar Mommy.

    Khausar na ƙoƙarin miƙewa tace.

    “Da sauƙi Momy” Sannan ta nufi Bedroom ɗin ta da sauri Asma’u ta miƙe tabi bayanta.

     

    Bakinta ɗauke da sallama tashiga ɗakin nata kana tayi saurin ɗin gisa ƙafarta se kuma ta kwanta agefen  gadonta dake shimfiɗe da white bedsheet tana sakin ajiyar zuciya akai-akai alamar har yanzu akwai tsoro atare da ita.

    Zama Asma’u tayi agefenta ganin yanda ƙafan Khausar ke rawa yasa tace.

    “Bari na ɗebo ruwan ɗumi na matsa miki”.

    Kai Khausar ta girgiza da faɗin.

    “A’a ga can man zafi agaban mirrow ki ɗauka min na shafa”.

     

    Kai Asma’u ta gyaɗa kana ta miƙe ta ɗauko man zafin ta ɓude kana ta kama ƙafar Khausar tana mulka mata.

    Khausar kuwa rintse Idanunta tayi tanajin zafin man na ratsa jikinta  yayin da aƙasan zuciyarta tsakanin tsoro da firgicin hukuncin da Moddibo ze ɗauka akan tane.

    Asma’u kuwa hira ta riƙa yiwa  Khausar na ɗebe kewa kana daga bisani ta miƙe ganin yamma tayi seda ta biya ta kichen ta sake yiwa Momy Sallama kana ta tafi.

     

    Khausar kuwa yanayin zogin da ƙafarta da kuma hannunta ke mata yasa bayan  tafiyar Asma’u ba jimawa bacci ya ɗauke ta…

     

    Ita kuwa Momy ganin har maghariba tayi bata jiyo motsin Khausar kuma bata nemi Raudat suyi salla ba  se abin ya bata mamaki bayan ta idar da Sallah ta fito daga Bedroom ɗinta Kai tsaye Bedroom ɗin Khausar ta nufa,

    bakinta ɗauke da sallama ganin Khausar na bacci yasa ta ƙarasa bakin gadon tare da taɓa fuskarta da hannunta dake da damshin ruwa ruwa tana kiran sunanta da faɗin.

     

    “Khausar! Khausar!! Khausar tashi kiyi Sallah maghariba tayi”.

    Momy ke faɗa tana me sake shafa fuskarta da hannunta dake da damshin ruwa.

    jin muryan Momy da kuma damshin hannunta da take shafa fuskarta yasa ta buɗe Idanunta ahankali tace.

    “Na tashi Momy”.

    Juyawa Momy tayi ta fita ita kuwa khausar miƙewa tayi tare da furta.

    “Alhamdulillah”,Jin babu ciwo da Zugin da ƙafar ke mata se kuma hannun data ji ya sake baki ɗaya tamkar ba ajikinta yake ba.

     

    Ta lumshe lumsassun idanunta kana ta miƙe ta nufi toilet tana me furta.

    “Allahumma Inni Auzubika Minal khubsi wal khaba’is”.

    Kana tashiga cikin toilet ɗin da komai ke akimtse yana fitar da wani irin ƙamshi Anutse tashiga yin alwalan har ta ida kana ta fito bayan ta furta.

    “Gufra naka”.

    Bayan ta gabatar da Salla tayi adduo’i ta miƙe tare da naɗe darduman se kuma ta juya ta fice tana me buɗe hannunta da rufewa koda ze dawo dai-dai…

     

    Zaune ta samu Momy kan kujera hannunta riƙe da hisnul Muslim tana Azkharul Masa,Yayin da Raudat ke gefenta daga ƙasa tana bin bakinta zama Khausar tayi daga gefen Raudat kanta aƙasa tace.

    “Momy gobe zan tafi JAURO YAYAH”.

    Da mamaki Momy ta zuba mata ido jin mgnar a bakatatam cike da mmki tace.

    “Zaki tafi Jauro yaya kuma Khausar?”.

    Ataƙaice Khausar tace.

    “Eh”.

    tana mai cigaba da jan yatsun hannunta.

     

    Momy ta sake duban ta da mamaki akaro na biyu tace.

    “Anma babu yanda banyi dake ba jiya kan cewa kishirya yau kutafi tunda mutanen garinsu na zuwa sallan jumma’a sosai ku tafi tare, kika ce ba zaki tafi dasu ba kuna hadda, sannan kun kusa zuwa ƙarshen surar idan kika tafi karatun ki ze koma baya sannan na yarda na barki kan cewa se sati me zuwa yanzu kuma kice zaki tafi gobe”.

     

    Murmushi ta ƙaƙalo tare  da faɗin.

    “A’a Momy babu damuwa munyi magana da Asma’u tace koda awaya zan iya ƙarawa da kaina batare da anwuce Ni ba”.

    Dubanta Momy tayi tare da cewa.

    “Kin tabbata Khausar har cikin ranki kikeson zuwa Jauro Yaya!?”.

     

    Kai ta gyaɗa tace.

    “Eh”.

    Aranta kuwa cewa tayi ba gwara masifar wancan tsohuwar ba dan ko yaya bazan tsaya ta dake niba amma wannan mutumin ya riƙa tsareka da firgitattun idanunsa masu saka tsoro da fargaba, baya ga haka in banyi sa’a ba duka na zai sa ayi banyi masa lefi bama idan yasamu sarari sawa yake  aci zalina  bare kuma nayi masa laifi…

     

    Muryan Momy dake cewa.

    “Toh shikenan nima nafi so ki tafi Kinga idan hutun ku ya ƙare sannan anƙarasa muku gyaran makaranta seki dawo”.

    Ya dawo da ita daga duniyar data lula.

     

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Shikenan Momy”, Sannan ta miƙe ta shiga Bedroom ɗin ta.

    Momy kuwa Hisnul Muslim ta ɗauka ta cigaba da Azkhar yayin da Raudat ta miƙe tabi bayan Khausar.

     

    Ita kuwa khausar na shiga ɗaki ta hau kan stoll ta janyo trolley ɗin ta sannan tashiga haɗa kaya Raudat dake kallonta tace.

    ”Dani Zaki tafi Addah Khausi?”.

    Girgiza mata kai Khausar tayi alamar a’a.

     

    Kuka Raudat ta fashe dashi tana cewa.

    “Ni zan biki”.

    Zama Khausar tayi ta riƙe hannunta tare da langwaɓar da kai tace.

    “Raudat garin bashi da daɗi fa, ga tsohuwar garin ta fiye masifa, kana yi mata kuskure kaɗan zata  zane Mutum”.

    Jin haka yasa Raudat ta girgiza kai tace.

    “Nide ba zanje ba idan haka ne”.

     

    Aɓangaren Momy kuwa bayan tashiga turakar Lamiɗo sunyi shirin kwanciya ta dubesa fuskarta ɗauke da murmushi me sanyi tace.

    “Uhum wai ɗazu Khausar ke cemin idan Allah yakaimu gobe tana son zuwa Rugar Jauro Yaya”.

    Zamanshi ya gyara tare da  faɗaɗa Murmushin dake fuskarsa kana yace.

    “Allah ya kaimu hakan nada kyau idan yaso tunda gobe weekend ne zamuje dukan mu kema sai ku gaisa tunda kinyi shekaru baki jeba”.

    Kai ta jinjina kafin tace.

    “Kai naji dadi Allah ya kaimu”.

    Amin yace kana sukaci gaba da hirarsu.

     

    Washe gari Ya kama asabar da wuri Khausar ta tashi ta gyara ɗakinta  sannan ta nufi ɗakin Momy ta gyara kana ta share har zuwa falo da kuma duk sashen saida ta gyara ko wani lungu da saƙo.

    Bayan ta gama ta dawo ta shiga kichen ta zuba musu Breakfast soyayyan cheaps da tea  ita da Raudat ke ciki.

    Bayan sun kammala ta miƙe tana ƙoƙarin tattare wajen Momy tashigo Idanunta akan Khausar.

     

    fuska ta ɗan tsuke tare da faɗin.

    “Maza kije yanzu Aunty Jamila tayi Miki kitso”.

    Aunty Jamila matar ƙani Lamiɗo ne sannan Momy tasan inba tayiwa Khausar dagaske to baza taje ba domin bata ƙaunar kitso.

     

    Ganin fuskar Momy babu walwala yasa Khausar gyaɗa kai tare da shiga Bedroom ta ɗauko dogon hijabinta fari Nevy blue daya sha ninkin guga ta ɗaura akan riga da wandon dake jikinta kana ta fice ta nufi gidan Aunty Jamila tana zumɓura baki da kuma kifiya da kum a hannunta.

     

    Bakinta ɗauke da sallama tashiga gidan, Aunty Jamila dake zaune ta amsa Sallamar tana faɗaɗa fara’ar dake fuskarta tace.

    “A’a Khausar kece?, sannu da zuwa”.

    Sake fuska Khausar ta ɗanyi tace.

    “Eh nice Aunty wai kitso nazo kiyi min zanje Jauro Yaya”.

    Murmushi Aunty Jamila tayi tare da cewa

    “Masha Allah kice zakije ziyara?”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tana murmushi.

    Cikin sakin fuska Aunty Jamila tace.

    “Allah Ya kaiku lafiya”.

     

    “Amin ya rabbil izzati”.

    Cewar Khausar.

    “Kinga kuwa kinyi sa’a duk na gama aiyuka na”.

    Da sauri tace.

    “Aunty Jamila manya fa zakiyi shida ko takwas”.

    Murmushi Aunty Jamila tayi.

    Kana ta miƙe ta shiga ɗaƙi tare da kwantar da yaronta kana ta fito,

    Akan kujeran roba Khausar ta zauna ita kuma ta tsaya ta fara yi mata kitson suna cikin kitson ne suka jiyo Sallamar Gimbiya Dadu.

    Anutse Aunty Jamila ta ɗago kanta fuskarta ɗauke da murmushi tace.

    “Sannu da zuwa Mama”.

    Asaman laɓɓa Gimbiya Dadu ta Amsawa Aunty Jamila baki ɗaya nutsuwarta da hankalinta suna kan Khausar.

    Miƙewa Aunty Jamila tayi tashiga ɗaki dan ɗaukowa Gimbiya Dadu Darduman zama.

     

    Ita kuwa khausar ahankali ta ɗago kanta caraf Idanunta suka sauƙa akan Gimbiya Dadu data tsareta da ido ita kuwa khausar cikin hanzari tayi ƙasa da idanunta tana mai karanto duk wata addu’ar da tazo bakinta kamar minti ɗaya Khausar ta sake ɗago kanta akaro na uku still Idanun Gimbiya Dadu na kanta.

     

    Ita kuwa khausar kasa jurewa tayi ta tsayar da Idanunta akan Gimbiya Dadu  cikin dakiya tace.

    “Wai dan Allah Gimbiya Dadu Meyesa kike kallona haka?”.

    Wani murmushi mai cike da ma’anoni Gimbiya Dadu tayi tare da cewa.

    “Uhum yaro man kaza,

    ai tunda kika bar cikin Awaki ‘yan uwanki kika dawo cikin Kuraye ai dole akalleki! In kalleki in kuma”.

    jin abinda Gimbiya Dadu tace yasa ta miƙe cikin rawan jiki da alamar tsoro aƙwayar Idanunta ta sanya hijabinta ta fita batare data jira Aunty Jamila ta fito ta ƙarasa yi mata kitson ba…

     

    Sauri-sauri gudu-gudu take tafiya har ta isa  bakin gate dinsu da sassarfa ta shigo coumpund ɗin su har yanzu jikinta be daina ɓari ba tana gyara zaman hijabin kanta Momy ta fito,Kallonta Momy tayi tare da cewa.

    “Har angama kitson ne”.

    Ka ta gyaɗa mata ba tare da tace komai ba.

    “Dama yanzu zan aika Haiydar ya kira ki kizo mu tafi”.

    Murmushin karfin hali ts ƙirƙira kana tace.

    “Eh mun gama”.

     

    Wuce ta Momy tayi taje tashiga gaban mota Ita kuwa khausar kallon Raudat, Ramadan, da kuma Haiydar dake tsaye tayi tare da ɗaga musu hannu suma hannu suka ɗaga mata ahankali ta juya ta nufi wajen motar tana isa tasa hannu ta buɗe tashiga gidan baya Haiydar da Ramadan na cigaba da ɗaga mata hannun.

    Babban gate mai gadin ya buɗe musu kana Lamiɗo  ya cilla hancin motarsa.

    Khausar kuwa jingina bayanta ajikin motar tayi tare da lumshe Idanunta zuciyarta na bugawa da mugun sauri abu biyu ne suka yiwa zuciyarta ƙawanya na farko hukuncin da Moddibo zai ɗauka akanta na biyu kalaman Gimbiya Dadu wanda suke ƙara tabbatar mata da zantuka dake yawo a gari cewa matar nan mayyace…

     

    Anutse Momy ta dubi Moddibo dake sharara gudu akan Lafiyayyan titin nasu tace.

    “Abban Haiydar gudun nan baiyi yawa ba”.

    Kanshi ya ɗan jujjuya mata,

    Ita kuwa cikin sanyi tace.

    “Gsky dai ka rage gudun kamar yayi yawa”.

    Juyowa yayi ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace.

    “Lokaci na tafiya kinga yanzu goma tayi gwara mu isa da wuri kada rana tayi mana mu samu mu juyo da wuri”.

    Kai ta gyaɗa  kafin tace.

    “Amma duk da haka arage gudun”.

     

    Tattausan murmushin ya sakar mata  tare da gyaɗa kai…

     

    Sunyi tafiya mai tsawo kafin suka fara hango garin Atake suka fara tabbatar da sanyin da ake acikin Gembila wasa ne.

    Domin tun kafin su shiga garin suka hango tamkar hayaƙi ke tashi saboda masifaffen sanyin da ake tsugawa acikin Jauro yaya suna shiga cikin garin suka fara ratsa  bishiyoyi masu korayen ganye suna rangaji tare da fitar da sanyayyan Iska kasancewar hantsi ne duk makiyaya sun tafi  se kuma,

    ‘yan dalo da aka ɗaɗɗaure masu kyan launi ga kuma kukan tsuntsaye dana zabbi da ke tashi suna ajiye ƙwai.

     

    Suna shiga tsakiyar Rugar Jauro,

    kai tsaye ƙofar gidan dake kusa da babbar fadan Rugar suka nufa anan sukayi parking motar tare da fitowa.

     

    Wasu dattawa dake zaune aƙofan masallacin dake kusa da babbar fadan suka taso baki ɗaya idanun su akan Khausar data fito daga mota tana gyara zaman hijabinta suna faɗin.

    “Audiii Barka da zuwa kece?”.

    ɗaya daga cikin dattijon ne ya taso wanda ya kasance shine Jauron garin ya riƙe hannun Khausar.

    Fuskarsa ɗauke da murmushi yake faɗin.

    ”Addah, Addah, Addah, kizo ga Khausar”.

    sauran ma bin bayansu sukayi zuwa cikin gidan suna masuyiwa Momy da Lamido Barka da zuwa.

     

    Biyu daga cikine suka ce da Momy da kuma Lamiɗo.

    “Sannunku da zuwa ya kuka tsaya ku shigo daga ciki”.

    Kai Momy ta gyaɗa kana suka yi musu godiya bisa jagoranci suka nufi cikin gidan.

    Jauro kuwa yana riƙe da hannun Khausar yana mata wasa da faɗin.

    “Iyeee girman falo ji jiki kamar auduga,

    bakisan riƙe sandar kiwo ba sannan baki san ta tsar nono ba girman burodi wayon shayi kawai”.

     

    Ita kuwa khausar hannu ta wara da faɗin.

    “Ban iya ba kam”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Zamu koya muki ai”.

    maƙale kafaɗa tayi tace.

    “Bana so ba kace min girman bread wayon tea ba”.

    Murmushi yay i tare da cewa.

    “To girman fura da nono”.

    Akuma dai-dai lokacin suka shiga ɗakin tsohuwar wanda yake ginin gargajiya shatin kobo.

     

    Suna shiga Jauro yace. “Addah ga ‘yar Usman tazo”.

    Ya mutse fuska Hajja Nana tayi tare da kallon Khausar tace.

    “Shegiyar kaya me wuyar ɗauka se yau kika ga damar zuwa??”.

    Murmushi Jauro yayi still hannunsa na cikin na Khausar yace.

    “Tazo da mahaifiyarta da kuma Mahaifinta”.

    Wani kallo Hajja Nana ta masa tare da cewa.

    “Kai Jauro ka gyara kalamanka,

    badai mahaifinta ba mahaifin riƙo  dai ko?  ka manta mahaifinta da kai aka binnesa shekaru goma sha biyar da suka wuce?”.

    Kai ya jinjina alamar hakane amma bece komai ba ita kuwa miƙewa tayi ta ɗauko taburma ta shimfida tare da ɗauko darduman kilisa ta shimfiɗa.

     

    A kuma lokacin Momy da Lamiɗo suka shigo cikin sakin fuska tashiga yi musu lale marhaba.

    zama Momy da Lamiɗo sukayi akan shimfiɗar data musu kana ita kuma ta zauna awajen zamanta na farko yayin da duka ƙannenta maza suka zauna daga bayanta se ta zamto tamkar sarauniya acikinsu ko wannensu fuskarsa ɗauke da murmushi yake faɗin.

    “Addah yau kam ga Khausar tazo”.

    Haka yasa ta juyu.

    Ta dubi Khausar da alamun farin cikin ganinta afuskarta saidai yanayin zafinta bazai sa ka fahimta ba.

    Ta dubi Khausar da tayi kicin-kicin da fuska tace.

    “Menene kike wani kumbura fuska? gwara ma ki saki ranki fa”.

     

    Zumɓura baki Khausar tayi saidai ba tace komaiba.

    Hajja Nana kuwa sake kallon Khausar tayi akaro na barkatai tace.

    “Ki tashi ki kawo ma baƙi abin taɓawa”.

     

    Lumshe idanu tayi kafin tace.

    “Nice zan kawo abin taɓa wa?,Nima ai baƙuwa ce akawo mana dai”.

     

    “Ina magana kina magana!?”.

    Hajja Nana ta fadi a faɗace.

    Cikin tura baki tace.

    “Ai gaskiyane”.

    Danƙolo Momy ta yiwa Khausar hakan yasa ta tsuke bakinta.

    Ɗaya daga cikin ƙannen Hajja Nana wanda ya kasance shine ƙaramin su (Autah)ya miƙe da faɗin.

    “To bari na kawo musu”.

    Sannan ya shige uwar ɗakan Hajja Nana ba daɗewa ya fito hannunsa riƙe da Akwashi ya ajiye agabansu sannan ya koma ya ɗauko goran zuma kana ya koma ya sake ɗauko wani Akwashin.

     

    Hajja Nana ta dubi Momy tare da cewa.

    “Ayyah wallahi ban san da zuwanku ba”.

    Kai Momy ta gyaɗa tare da cewa.

    “Ai inata gwada kiran layin ki baya shiga”.

    Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.

    “Kinsan Rugar tamu bamu da network se kaje bishiyar ƙare zancenka  in kaje bishiyar ma seka hau sama ni kuma ban cika son zuwa ba da girmana Inje in hau bishiya na faɗo”.

     

    Khausar kuwa taɓe baki tayi tace.

    “Hmmm ba network kuma har sai anje wani bishiya?”.

    Harara Hajja Nana ta watsa mata ta cigaba da cewa.

    “Wallahi bansan da zuwan kuba dana shirya muku abin taɓa wa”.

    Murmushi Momy tayi batace Komai ba.

    Akwashin da aka shigo dashi ne Autansu Hajja Nana ta buɗe Nono ne me zafi yana tururi ga kuma goran zuma dake gefe ɗayan kuma daya buɗe ɗumamen danɗerun zabbi ne suna tururi.

    Sauran mazan dake kewaye da Hajja Nana ce suka shiga Gaisawa dasu Lamiɗo.

     

    Muskutawa Hajja Nana tayi tare da gyara zamanta ta kalli Lamiɗo dake zaune ya tanƙwashe ƙafafunsa tace.

    Wa’annan daka ke kallo duka ƙannena ne mu goma ne acikin mahaifiyarmu gaba ɗayansu Mazane ni Kaɗai ce mace kuma nice ‘yar Fari.

     

    Jinjina kai Lamiɗo yayi yana sauraronta da duka nutsuwarsa duk da yasa abinda take faɗa kishin. tunda ba yaune zuwansa na firkoba.

    Ita ko Hajja Nana nuna wanda ke gefenta tayi tare da cewa.

    “Ga mai bina Jauro, Sannan kuma sai Sadu, Sannan se Abubakar, Sai kuma Garga, sannan sai Aliyu liman, Sannan kuma sai Dumau ,Sai Salmanu, Sannan kuma Isa sai kuma Umaru”.

    Lamiɗo kuwa kallon su yake yana sake tabbatar da abinda ta faɗa saboda kamannin dake tsakanin su.

     

    Hajja Nana tayi murmushi tace.

    “Duk ƙanne nane sannan kuma duk da matansu”.

    Ta nuna Jauro tace.

    “Matan sa biyu,Garga ma Matansa biyu, Sannan Sadu ma matansa biyu, sai kuma Liman shima Matansa biyu”.

    Ta sake nuna Jauro, Sadu, Garga, da kuma Liman tace.

    Jauro da Sadu ‘ya’yansu maza biyu sunyi aure kuma ‘ya’yan Liman da Garga suka Aura ma’ana Auran dangi sukayi”.

    Lamiɗo kuwa murmushi yayi alamar yana fahimtar abinda take faɗa masa.

     

    Ita kuwa Hajja Nana  cigaba tayi da  cewa.

    “Duk garinmu babu bare mu ya mune, sannan kuma babu maye mu garinmu atsarkake yake kushigo hankalin ku kwance ku fita lafiya,

    Salamun Ƙaulan Min rabbil Raheem”.

     

    Momy kuwa sunkuyar da kai ƙasa tayi Saboda tasan ana zargin Mahaifiyar Lamiɗo da Maita.

    Shima Lamiɗo sun kuyar da kansa ƙasa yayi dan yasan zargin da ake yiwa Mahaifiyar sa kenan kasancewar sa mutum me haƙuri da kuma dattako saiya ɗago kansa fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Masha Allah yayi kyau zuri’a tayi albarka Allah yaƙara rufa asiri”.

    Murmushi Hajja Nana tayi tace.

    “Ameen ya Allah”.

     

    Domin Hajja Nana ‘yar takife ce bata tsoro inma tsoron wani abu ake itace ke isar dashi.

    Miƙewa Sauran sukayi suna kallon Lamiɗo suka ce bari mu barku kuci abinci sannan suka fice.

     

    Itama Hajja Nana miƙewa tayi tace.

    “Khausar zo mu shiga ciki kici naki”.

    Girgizi kai Khausar tayi tace.

    “A’a zanci anan”.

    Ta juyi ta dubi Khausar da kyau tace.

    “Kizo mu tafi nace”.

     

    Shi kuwa Lamiɗo cike da ladabi yace.

    “Da kin barta munci anan ɗin babu matsala”.

    Juyawa Hajja Nana tayi kafin tace.

    “Toh shikenan”.

     

    Miƙewa Khausar tayi tabi bayanta ta karɓo ƙananan akwashi aka zuba mata sannan suma suka zuba,Yanayin sanyin da ake tsugawa agarin yasa mazauna garin ke bukatar abu me ɗumi,Suna cin zabbin suna ɗaurawa da Nono me ɗumi bayan sun gama Khausar ta miƙe ta tattara akushin ta mayar.

    Ganin ta mayar ne yasa Hajja Nana fitowa suka zauna.

    Atake sega yara suna ta shigowa a jere a jere angama abincin rana suna kawowa duk gida Jen garin Hajja Nana tana da kwanonta acan suna kawo mata abinci domin ita bata girki abinci safe ne kawai bata Yarda akawo mata ita take dafa wanda zata ci,Duk ƙannenta taran nan sai ankawo kwanuka tara an ajiye mata ga kuma na ‘ya’yansu da sukayi Aure tana da ƙore goma sha uku.

    Ga yaran garin ƙanana kyawawa dasu farare soll kamar irin yaran ƙauyen larabawa.

    Lamiɗo da kansa da yaga yaran na shigowa sun basa sha’awa,Ko wacce idan tashigo zata ce.

    “Goggo Hajja! Goggo Hajja!! Aɗonna”.

    Ƙannenta da Addah Nana suke kiranta ‘Ya’yan  ƙannenta kuma Goggo Goggo Hajja idan kuma jikoki zasuce mata Hajja Nana.

    Duk Wacce ta kawo mata abinci zata ce nice,daga gidan Sadu,Nice daga gidan Garga,saboda yawansu kowa ke gabatar da kansa.

    Duk wanda yazo ya ajiye zata ce.

    “Angode masu nomawa Allah ya basu ƙarfi da lafiyar nomawa masu girkawa ma Allah yabasu ƙarfin girkawa”.

     

    Sannan ga yanayin tsarin yaran garin babu alamar ƙazanta ajikinsu ko wanne tsaf dashi ga kuma tarbiyya duk wanda suka zo sai sun tsugunna sun gaida Lamiɗo da Momy da fulatanci kasancewar basu iya Hausa Sosai ba.

     

    Ɗaya daga ciki data zone ta ajiye kwanon Idanunta akan Khausar tace.

    “Goggo Hajja Khausar naa” .

    Murmushi Hajja Nana tayi tace.

    “Eh”.

    Murmushi yarinyar tayi ta matso kusa da Khausar tace.

    “Sunana Dija”.

    Murmushi Khausar tayi tace.

    “Yayi kyau Dija”.

    Dija ta kuma murmushi tace.

    “Kullum Goggo Hajja na bamu labarin ki rabonki da nan tun kina ƙarama yanzu ya kai shekara shidafa ake cewa”.

    Kai Khausar ta jinjina da faɗin.

    “Eh”.

    Hannunta Dija ta riƙe tace.

    “Kizo muje gidanmu ku gaisa da Mamana”.

    Ta ƙare mgnar tare da jan hannu Khausar suka fice…

     

    Kiran sallan Azahar yasa Lamiɗo ya miƙe ya tafi masallaci tare da Ƙannen Hajja Nana ita kuma Momy tayi alwala tare da gabatar da sallah bayan sun idar da Sallah Hajiya Aysha ta ɓude jakan da tazo dashi ta fito da turaman zannuwa da Sabulai ta miƙawa Hajja Nana.

    Murmushi Hajja Nana tayi tace.

    “Hadda ɗawainiya haka?,To angode Allah yayi albarka”.

     

    “Ameen”, Momy ta amsa kafin tace.

    “Hajja ga Khausar nan na kawo tayi hutu amma mako uku  ne hutun nasu”.

    Murmushi Hajja Nana tayi tace.

    “Toh Nagode”.

    Ita ko Momy tana gyara mayafinta tace.

    “Sati uku  ne hutun nasu”.

     

    Faska Hajja Nana ta tsuke tare da cewa.

    “Sai kin sake Jaddada min ne?”.

    Da sauri Momy ta girgiza mata kai.

    Cikin isa tace.

    “Toh sai sanda naga dama zata dawo kinyi naki saura nawa”.

    Ƙasa da kai Momy tayi tare da faɗin.

    “Shikenan Hajja duk yanda kikace yayi mukan zamu tafi”.

     

    Miƙewa Hajja Nana tayi tace.

    “Bari akira muku Khausar kuyi sallama”.

    Cike da ladabi Momy tace.

    “A’a Hajja base ankira taba”.

    Dan tasan muddin aka kirata sai tayi kuka kafin su rabu.

    Sallama suka sake yi musu kafin suka fice suka tafi…

     

    Acan Gembila kuwa Washe gari.

    Asabar Moddibo ya shirya kamar ko yaushe cikin Jallabiya Sky blue Kansa sanye da hula da kuma hirami cikin nutsuwarsa kamar ko yaushe ya shiga cikin makarantar yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi da hannu kawai yake amsa gaisuwar da ɗaliban haddar ke masa kai tsaye Ajin haddarsu Khausar ya nufa yayin da Aransa yayi ƙudurin sawa Malam Bello ya casa masa ita saboda gaba ta kiyaye domin ya lura ganganci da sakalci ke damunta.

    Cikin rashin sa’a yana shiga ajin ya samu bata nan.

    Asma’u ya kira.

    Cike da ladabi ta fito tare da tsugunnawa agabansa tace.

    “Gani Yah Moddibo”.

     

    Tsayuwar sa ya gyara cikin yanayin sanyin Muryansa yace.

    “Ina wannan Birin?”.

    Asma’u kuwa kanta aƙasa tace.

    “Nima yau da nazo ban ganta ba sai nake tambayar Amina ina take shine tace wai taje garin Kakanninta”.

    Ƙwafa yayi yace.

    “Shikenan yayi kyau”.

    Kana ya juya ya bar waje….

     

    Acan mota kuwa Momy ta dubi mijinta tace.

    “Kayi hakuri da Hajja Nana yanayin tsufa ne”.

    Murmushi yayi still Idanunsa ahanya yace.

    “Ai bakomai ba gamu da Gimbiya Dadu ba ai haka take”.

     

    Acan Rugar Jauro yaya kuwa bayan Khausar ta dawo gida ta tar da Momy ta sun tafi ta tsare Hajja Nana da ido tace.

    “Meyesa ba ki kirani ba kafin su tafi?”.

     

    Salati Hajja Nana ta sanya tace.

    “Tuhuma ta kikeyi? Ko kuma me?”.

    baki ta cinna sama tare da cewa.

    “Ai gaskiyane abinda ya dace na faɗa”.

    Salati Hajja Nana ta sanya tare da faɗin.

    “Ohhh ni Shatu Allah ya nuna min ‘yar Usmanu yarinya kamar ruwan aski sai rashin ta ido”.

    Ta ƙare mgnar tana kallon Khausar dake tsaye fuska akumbure cikin tsawa tace.

    “Bari kiji in faɗa miki ni agarin nan idan nayi magana kamar yankan wuƙa yake babu me bani Amsa ko musu ko jayayya dani!”.

    Ita kuwa Khausar wani irin juya Ido sama tayi tare kana tace.

    “Uhummm to gwara ma ki sani.

    Idan maganarki yankan wuƙa ne to kin samu me yankan rez”……!

     

     

     

    Littafin SAKAYYAH na kuɗine biya ki karanta 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 14

    Sakayyah 14

     

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Pape 14_

     

    NA

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *Free page ne ƴar uwa saura uku kacal mu gama free page, har yanzu baki makaraba ki biya*

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci da salama babu haƙƙin wani kanki. SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Kana sai in saki a Group, ɗin da zan rinƙa posting.*

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

     

    Washe garin washe gari.

    Da daddare  watan Ramadan ya bayyana.

     

    Haka yasa dukkan ɗauka cin Musliman duniya suka cika da farin ciki tare da yin niyan ɗaukar azumin watan Ramadan ɗin, kana kowa yana shirya bukatunsa dan miƙa su ga Ubangiji Mabuwayi gagara Misali.

     

    Washe gari Ranar Litinin gaba ɗaya al’ummar Musulman duniya sun tashi da azumin watan Ramadan abakinsu gaba ɗaya ɗaukan farko ɗauka ɗaya akayi duk duniya abinda aka daɗe ba’a yiba tsawon lokaci mai yawa wannan shekarar ansamu  kowa na cike da farin cikin wannan al’amari azuciyar musulmai.

     

    Da daddare Misalin ƙarfe 9:00 pm Babban masallacin juma’a dake ƙofar gidan Sarki cike yake da.

    Al’ummar Musulmi maza da mata wanda duk shekara idan aka shigo Ramadan bayan an idar da sallar isha’i M Jameel da Moddibo ke gabatar da Tafseer Alkur’ani mai girma duk shekara Moddibo ke jan baƙi yayin da M Jameel keyin Tafseer yana fassarawa.

     

    Masha Allah kamar yanda suka gabatar ashekarar Bara ayau ma hakane Cikin Masallacin Maƙil yake da dubban jama’a yayin da Moddibo ke zaune akan wani ƙayatenccen kujera gabansu babban table ne dake ɗauke da system jikinsa sanye da Jallabiya Armygreen mai yauƙi da sansti kana gaba ɗaya ilahirin jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi tularensa, idanunsa alumshe yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yake.

    Yayin da M Jameel ke zaune gefensa cikin shiga na alfarma Bugaggiyar shadda ce fara sol anyi masa ɗin kin ƴar ciki da gariya sai hula baƙa sosai yayi kyau gaban jikin rigarsa maƙale da microphone.

     

    Cikin tsantsar nutsuwa da kamala M Jameel ya hura microphone ɗin tare da gyara zamansa kana yace.

    _“A’uzubillahi Minal Shaiɗanir rajeem Bismillahir Rahmanir Rahim. Innal hamdillah Nahmud wanastainuhu wanastaghfiru, wa’nazubillahi min shuriri anfusna, wamin sayyi ati a’amalina, manyah dillahu fala mudillah waman yudil fala hadiyala, Wa’ash hadu Allah ilahalillahu wahdahu lasharika lahu Wa’ash hadu Anna Muhammad Abduhu warasuluhu._

    Ya ɗan sauƙe numfashi tare da sauƙe numfashi kana ya sakin ajiyar zuciya sannan ya cigaba da cewa.

    _“Ya ayyuhallazina amanut taƙullaha haƙƙu tuƙatihi wala ta mutunna illah wa’antum Muslimun ya ayyuhan nabiyu taƙu rabbakummalazi wahida wakalaƙa minha zaujuha wabassa min huma rijalan kasiran wani sa’a wattaƙullahal lazi tasa aluna bihi wal arhama innalaha bikum kana alaikum raƙibaaa_

     

    Baki ɗaya ciki da wajen masallacin ya kacame da sowa da sassarfan waɗanda ke harabar masallacin da suke shigowa da sassarfa.

     

    M Jameel kuwa idanu ya lumshe tare da buɗesu kana yace.

    “Amma ba’ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum Warahmatullah Wabarkatuhu”.

     

    Gaba ɗaya cikin masallacin da harabarsa suka amsa da faɗin. “Wa’alaikum Salam Warahmatullah wabarkatuhu”.

    Gyara zama M Jameel ya yi tare da kallon ɗumbin jama’ar dake masallacin kana a hankali ya numfasa sannan yace.

    “Insha Allahu zamu cigaba da Tafsirin Alkur’ani mai girma kamar yadda muka saba, zamu kuma ɗaura daga inda muka tsaya bara. A cikin suratul Nisi’i awancan shekarar mun tsaya akan aya na ɗaya wanda ya zamana shi muka karanta Ramadan ya ƙare cikin ikon Allah gashi ya sake sada mu acikin watan wanda da yawa wasu daga cikin wanda mukayi tafsiri dasu wancan shekarar yanzu basa nan kana da yawa wanda muka fara ayau da ƙyar zamu ga ƙarshen amma muna roƙon Allah daya nuna mana ƙarshen wannan wata mai falala da kuma al’barka  lfy”.

     

    Baki ɗaya wajen suka amsa da faɗin.

    “Ameen”.

    Domin wasu daga cikin masu sauraron karatun suna zuwa ne saboda yanda M Jameel ya ƙware awajen Tafseer gashi kuma yana da zafi nama da kwarjinin tafsir.

    Juyawa M Jameel yayi tare da kallon Moddibo da kansa ke ƙasa ya tsirawa System ɗin sa idanu ya gyara zamansa tare da cewa.

    “Bismillaha Alaramma  jeka cikin Suratul Nisa’i ka karanto mana muji abinda Allah ma ɗauka kin sarki yake faɗa”.

     

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da gyara zamansa kana ya jingina bayansa da jikin kujera sannan ya lumshe idanunsa cike da nutsuwa ya motsa laɓɓansa kana yayi gyaran Murya cikin Sanyayyar muryarsa mai daɗin saura da sanya nutsuwa  da ratsa zuciyar bani adam ya fara kamar haka;

    “Bismillahir Rahmanir.

     

    Gaba ɗaya illahirin yaƙin da sautin muryarsa ya ratsa kunnuwansa, sit sukayi babu abinda wani sauti ko hayaniya, wurin yayi sit kai kace babu mai rai a wurin bare numfashi, gaba ɗaya an nitsu, wanda hakan kuma a jinin Modibbo yake, duk hayaniyar wuri muddin yayi basmalla a take kab za’a nutsu.

     

    Idanunsa ya ɗan lumshe kana ya buɗe su a hankali yana kallon taron al’ummar Annabi dake tare maƙil, cike da nitsuwa ya fara karatu cikin zaƙin murya ya kawo aya ta biyu cikin suratul Nisa.

    .2-Wa’atul ystamaa amwalahum,Wala tatabaddalul khabisa biɗɗayyir,Wala ta’akuluu Amwalahum Ila amwalikum,Innahu kana huban kabira”._

    Atake mutanen da masallacin suka shiga lumshe idanunsa yayin da wasu suka shiga sakin ajiyar zuciya Moddibo mutum ne mai ƙwarjini duk yanda waje keda hayaniya da zaran sautin muryarsa ya fita zakaji wajen yayi stit.

    M Jameel kuwa ya Jinjina kai yayi yana mai jin ayan na ratsa sa cikin yanayin faram-faram ɗinsa yace.

    “Gabaaa jeka aya ta gaba Aramma muji mai Allah yace”.

    Sanyayyar iska mai sanyi Moddibo ya furzar tare da gyara zamansa kana ya cigaba da jan Ayar kamar haka;

    _3-Wa’in hiftum Allah tuƙsiɗu fil yatama fankihu ma ɗabala lakum Minal Nisa Masna wasulasa waruba ,Fa’in hiftum Allah ta’adilu fawahidatan Auma malakat aymanukum,Zhalika adnaa Allah ta’aluun_.

     

    Cikin jin daɗin sauraron muryarsa mafi yawan Ƴan matan dake sauraron karatun suka lumshe idanunsu suna burin Allah ya mallaka musu shi amatsayin mijin Aure.Yayin da magidanta suke burin ƴaƴan su suzama kamar Moddibo.

    Cikin ɗaga sauti M Jameel ke gyaɗa kansa kana yace.

    ”Je gaba Aramma muje gaba muji me Ubangiji yace”

     

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da jingina bayansa ajikin kujera kana ya lumshe Idanunsa tare da gyara system dake gabansa ya cigaba.

    _“4-Wa’atunnisa’a saduƙatihinnah Nihylah,Fa’in ɗibna lakum anshay’in minhu nafsa fakuluhu hani’am mariyya.5-Wala tu’utussahafa’u Amwa lakumallati ja’alallahu lakum ƙiyama warzuƙuhum fihaa warkusuhum waƙulu lahum ƙaulan ma’arufah”_.

    Ya ƙarashe jan ayar cikin zazzaƙar muryarsa.

    Shiko M Jameel  gyara zaman Microphone dake gabansa yayi kana yace.

    “Masha Allah Aramma”.

    Atake masallacin ya kaure da kabbara wasu na buri da fatan Allah ya azurtasu da baiwan murya irin na Moddibo da yawa daga masu zuwa Tafseer ɗin suna zuwa ne Saboda zaƙin muryan ƙira’ar Moddibo da kuma nutsuwarsa musamman yanda Laudspeaker ke fitar da zazzaƙan murya Moddibo tare da sanya nutsuwa,

    M Jameel da Moddibo sun iya Tafseer domin shi M Jameel mutum nai mai zafin jini Moddibo kuma ya kasance mutum mai sanyi komai nasa cikin nutsuwa yake hakan yasa mutane ke matukar ƙaunar Tafseer ɗin su mutane kan tsallake unguwar su suzo  su saurari nasu.

     

    M Jameel kuwa cike da tsantsar ƙwarewa da kuma sanin abinda yake yi ya fara tafsirin ayoyin bayan yayi muƙaddima ya fara fassarar kamar haka :

    _”Aya ta(2) Allah madaukakin sarki nacewa

    (Kuma ku baiwa marayu dukiyoyinsu kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau.kuma kada kuci dukiyoyinsu zuwa ga duniyoyin ku, Lalle shiya kasance zunubi ne mai girma”_

    Mafiya yawan mutanen dake wajen jikinsu ne yayi sanyi domin ji sukayi Ayar tamkar dasu take magana cike da nutsuwa suke sauraren.

    M Jameel ya numfasa kana ya cigaba da cewa.

    _“Aya ta (3) Allah yana cewa.

    _Kuma idan kunji tsoron ba za kuyi adalci ba acikin marayu to(akwai yadda za’a yi)ku auri abinda yayi muku dai-dai daga mata biyu-biyu,Uku-uku ko huɗu-huɗu sa annan idan kunji tsoron baza kuyi adalci ba to ku auri guda ɗaya ko kuwa abinda hannayenku na dama suka mallaka.wannan shine mafi kusantar zama baku wuce haddi ba”._

    Numfashi wasu daga cikin mata masu kishi suka saki jin Allah da kansa ya bawa maza ikon su ƙara aure yi shin to wai menene abin kishin hauka duk da cewa dole ne ayi kishi amma ya kamata su rika sassauta.

     

    M Jameel kuwa juyawa yayi tare da kallon Moddibo daya zubawa system ɗin sa idanu numfashi ya sauƙe cikin yanayin zafin jinjinsa ya cigaba da cewa.

    _“Acikin aya ta (4). Allah Mabuwayi gagara Misali cewa yayi.

    Kuma ku baiwa mata sadakin su sauƙin bayarwa sannan idan suka yafe muku wani abu daga gareshi a daɗin rai to kuci shi da jin daɗi da saukar da hadiya”._

    Ya ɗago kansa tare da kallon jama’ar dake masallacin cikin ɗaga sautin murya ya gyara zaman hular dake kansa kana yace.

    “Kai Kuce Allahu Akbar”.

    Atake masallacin ya ɗauki kabbara da faɗin Allahu Akbar Allah ya ƙara maka nisan kwana.

    Murmushi yayi tare dasa hankie ya goge gaban goshinsa kana ya cigaba da cewa.

     

    _“Kada ku baiwa wawaye  dukiyar ku Wanda Allah ya sanya ta agareku kuna tsayuwa (ga gyaranta)kuma ku ciyar dasu cikinta,kuma ku tufar dasu kuma ku gaya musu magana sanyayya ta alkhairi”_.

    Atake masallacin ya jure da kabbara cike da jin daɗin tafsirin.

     

    Agefen ɓangaren mata Asma’u ce zauna tare da Innayi sai Khausar dake can gabansu Matsawa Asma’u tayi tare da taɓa bayan Khausar,juyawa Khausar tayi ganin Asma’u yasa tayi murmushi tare da miƙewa daga inda take ta dawo kusa da Asma’u.

    Tana murmushi ta gyara zamanta tare da cewa.

    “Asma’u ya Ummi amma ɗazun da mukayi waya baki ce min zaki zo Tafseer ba”.

    Murmushi Asma’u tayi kana tace.

    “Ai nadawo gidan Innayi da zama zan riƙa taya ta aiki sai Azumi ya ƙare zan koma gida”.

    Bata jira jin Abinda Khausar zata ceba ta juya tare da kallon Innayi data tattara nutsuwarta zuwa ga tafsirin da  jikokin ta keyi hannunta Asma’u ta riƙe kana tace.

    “Innayi ga Khausar ƙawata”.

     

    Murmushi Innayi tayi tare da kallon Khausar,Ita kuwa khausar ƙasa tayi da kanta cike da nutsuwa  ta gyara zaman hijabinta kana tace.

    “In wuni ya ibada?”.

    Murmushi Innayi tayi tare da cewa.

    “Lafiya lau Alhamdulillah”.

    Haka nan Khausar taji tsohuwar ta burgeta Kallon Asma’u tayi cikin ƙasa da murya ta kalli Asma’u tare da cewa.

    “Wacece?”.

    Asma’u na murmushi ta juya ta kalli Khausar kana tace.

    “Kakar Moddibo ce”.

    Taɓe baki Khausar tayi kana tace.

    “Itakam tana da kyawawan hali ba iri jikanta ba ko ina ya gado baƙin zuciya ohon mishi mugu”.

    Dariya Asma’u tayi amma batace Komai ba.

     

    Bayan M Jameel yayi tafsirin Ayoyi guda goma,ya duba lokaci ganin ƙarfe goma saura minti takwas ya numfasa tare da faɗin.

    “Wasubhanakal Lahumma wabi hamdi Nash’hadu Allah’ila ha Illah anta nastagfirka wanstubu Ilaik”.

    Ya rufe system ɗin sa tare da cewa.

    “Dan Allah kamar yanda aka saba maza suyi haƙuri mata su fara fita”.

     

    Sai da duk matan suka gama fita kafin maza acan mota Innayi da Asma’u suka jira M Jameel da Moddibo har gida aka kaisu bayan sun isa gidansu Moddibo kasancewar duk Ramadan agidansu Moddibo M Jameel keyi saboda yawan hidimarsu.

    Suna isa kai tsaye sashen Moddibo M Jameel suka nufa Asma’u da Innayi kuwa sashen ta suka nufa suna shiga ciki Innayi ta cire dogon hijabin dake jikinta tare da kallon Asma’u tana ajiye hijabin ta sauƙe ajiyar zuciya da faɗin.

    “Asma’u ɗauki abinci ki kaiwa Yayunki tun da akayi buɗa baki ƴaƴan itatuwa da kunu kaɗai suka sha basu ci wani abu ba”.

    Jinjina kai Asma’u tayi kana tace.

    “Toh”,Sannan ta ɗauki Faranti Perpesoup ɗin kaza,da Couscous da miyan ƙwai sai perper cheking sai juice ɗin Abarba da kwakwa sai kuma fruit salad.

    Bakinta ɗauke da Sallama tashiga zaune ta same su M Jameel na kan 2sitter yayin da Moddibo ke kan 3sitter Idanunsa alumshe ajiye wa tayi tare da juyawa zata fita.

     

    M Jameel ya ɗago kansa tare da kallon Asma’u dake shirin fita yace.

    “Asma’u zo ki zuba mana yunwa nakeji wallahi kinsan Magana ba wasa ne dashi ba”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Hakane”.

    Kam sannan ta tsugunna ta buɗe Warmers din Atake ƙamshi ya bugi hancinsu da sauri M Jameel ya Kalli Asma’u tare da cewa.

    “Asmeey wayayi wannan girkin?”.

    Tana zuba musu miyar ƙwoyin akan Couscous ɗin ta ta ajiye kana tace.

    “Ya Jameel nice Nayi”.

     

    Ware ido M Jameel yayi.

    “Kai Asmeey ki faɗi gaskiya dai”.

    Murmushi tayi da faɗin.

    “Allah da gaske ni nayi yaya Jameel”.

    Abincin ya ɗiba ya kai bakinsa tare da lumshe idanunsa kana yace.

    “Waya koya Miki wanna girkin?”.

    Dariya tayi kana tace.

    “Khausar ce ta koya min Allah yaya Jameel yawanci idan naje gidan take koya min”.

    Moddibo dake kwance ya harareta kana yace.

    “Ke dai Arayuwarki komai baki iya ba sai dai wata ce ta koya miki, ki bari mana akoya mikin kawai akayi ba magana ta ƙare ba ba sai kince ga wacce ta koya miki ba”.

    Ya ƙare maganar kamar bashi yayi ba.

    Murmushi Asma’u tayi kana tace.

    “Allah Yaya Moddibo Khausar ta iya girki sosai saboda kullum tare suke shiga kichen da Mommy ta”.

    Baki ya taɓe da faɗin.

    “Naji jeki ki gaida Innayi”.

     

    Kai ta gyaɗa tare da yin murmushi har ta kai ƙofa zata fita sai ta kuma ta sake juyawa tare da komawa ciki kana tace.

    “Yaya Jameel ƙofan Innayi babu wata gashi kuma naga nan akwai wuta”.

    Moddibo dake kwance ya shafa sajensa kana yace.

    “Itace tace bata so gashi har cikin kicin ɗinta taƙi a kaishi ɗakinta”.

     

    Baki Asma’u ta tura tare da Marerece fuska kana tace.

    “Nikam gaskiya zama ba wutan nan baimin ba”.

    M Jameel dake cin Chicken Peper ya kalleta tare da cewa.

    “Toh kije ki faɗa mata wata ƙil wala Allah idan ke kin faɗa ta yarda asa mata”.

     

    Kai Asma’u ta jinjina kana ta miƙe tare da faɗin.

    “Toh”,Sannan ta fice ta nufi sashen Innayi.

    Bakinta ɗauke da Sallama tashiga ɗakin Innayi zaune ta samu Innayi da lantarta azaune hannunta riƙe da carbi tana ja.

    Zama tayi daga gefen Innayi kana tace.

    “Innayi naga an kawo wuta a sashen su Yaya Moddibo Nan kuma babu wallahi rashin wutar nan beyi ba”.

    Anutse Innayi ta juya ta kalleta kana tace.

    “Ayyah Asma’u am ni tsoron wutan nan nake ji bana son irin wannan abubuwan ke kuma kina so ko?”.

    Jinjina Kai Asma’u tayi tare da faɗin.

    “Allah Ni dai inaso”.

    Innayi ta kalleta kana tace.

    “Zafi kike jine?”.

     

    Girgiza kai Asma’u tayi tare da cewa.

    “Ba zafi ba haske dai Innayi ɗan tv nan dai idan alasa zamu riƙa kallon sunna Tv”.

    Jinjina kai Innayi tare kana tace.

    “Shikenan sai asaka tunda haka kike so insha Allah gobe zan faɗa musu asaka mana”.

    Da sauri Asma’u ta miƙe kana tace.

    “Bari Inje in faɗa musu yanzu”,Ta ida maganar tare da ficewa.

     

    Kai tsaye sashen ta koma bakinta ɗauke da Sallama tashiga Idanunta akan Moddibo dake kurɓan Juice ɗin fuskarta ɗauke da murmushi kana tace.

    “Yaya Moddibo Wallahi Innayi ta yarda aja mata wuta kuma dan Allah asamar mana Tv zamu riƙa kallon Tafseer kaga ita yanzu sai dai tayi ta rungumar Radio komai sai dai taji ta Radio”.

     

    Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.

    “Toh shikenan Allah ya kaimu goben”.

    M Jameel kuwa kallon Asma’u yayi fuskarsa ɗauke da murmushi ya ajiye Plate ɗin hannunsa kana yace.

    “Tafff lallai Asma’u ke ta musamman ce kinyi babban sa’a babu yanda ba muyi da ita ba muja mata wuta taƙi”.

    Murmushi Moddibo yayi kana yace.

    “Ai Asma’u ta hannun daman Innayi ce”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da ficewa ta koma falon Innayi suka kwana Misalin biyu da rabi Innayi ta farka kana ta tashi Asma’u suka fita alwala sukayi suka gabatar da nafilla tare da adduo’i ƙarfe uku dai-dai Innayi da Asma’u suka shiga kichen Innayi tayi musu ɗumanen tuwan jiya tare da tafasa ruwan shayi daya ji kayan ƙamshi sai kuma ta ɗumama perpesoup ɗin kazan ita kuwa Asma’u attaruhu da albasa ta jajjaga tare da ɗauraye tukunya ta sanya akan gas wanda zuwan Asma’u ne Moddibo suka kawo mai ta zuba kana ta zuba jajjegen tare da zuba spices da Maggi da kuma Curry ta zuba kana ta zuba sanwa Bushesh-shen kifi dake gyare ta zuba sannan ta ɗauƙi carrots,da grean beans,da kuma cabbage ta shiga gyarawa jin ruwan na tafasa ta tsaya ta zuba Spaghetti leda ɗaya sannan ta cigaba da gyarawa sai daya kusa tsotsewa sannan ta zuba cabbage,grean beans,Carrot,aciki Nan da nan gidan ya kaure da ƙamshi Warmers ta ɗauka ta juye sannan ta zuba sauran a plate ta haɗa kayan duka a babban faranti ta ɗauka bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon.

     

    Moddibo dake zaune riƙe da Alkur’ani ya ɗago kansa tare da amsa Sallamar bayan ya kai ƙarshen ayan Moddibo kuwa idanunsa ya ɗauke daga kan system ɗin tare da kallon Warmers din sai kuma ya Kalli Asma’u dake ajiyewa akan center table ya shafa sajensa tare da cewa.

    “Asmeey ya naga kuloli da yawa haka?”.

    Murmushi tayi kana tace.

    “Wannan ɗumame ne Innayi tayi muku ɗayan kuma ɗumamen perpesoup ɗin jiya ne wannan kuma jollof nayi muku na Spaghetti”.

    Jinjina kai M Jameel yayi kana yace.

    “Ni dai kamar nafi son ɗumamen Amma bari naga jollof ɗin naki”.

    Ya ida maganar tare da buɗe Kulan cikin sauri ya lumshe idanunsa jin ƙamshin daya ratsa hancinsa.

    Kallonta yayi kana yace.

    “A’a bazan ci ɗumame ba”.

    Juyawa Moddibo yayi tare da kallon M Jameel kana yace.

    “Ai kuwa baka Isa ba ɗumame zaka ci, Asma’u Allah ya miki albarka”.

    Sai kuma ya sake kallon M Jameel dake murmushi kana yace.

    “Ai dolenka ɗumame zaka ci dan kaine Innayi ke yin ɗumame ko wani shekara sai ka ishemu da ɗumame saboda kai ake liƙa mana”.

     

    Murmushi M Jameel yayi kana yace.

    “Ai ɗumamenta yana da daɗi kai kan ka in faɗa maka zakayi missing ɗumanenta idan baka kusa yanzu ma dan kana tare dashi ne”.

    Murmushin gefen baki Moddibo yayi kana yace.

    “Um naji amma dai yau shi zaka ci”.

    Dariya M Jameel yayi tare da cewa.

    “Ba matsala ai ɗumamen Innayi nace”.

    Miƙewa Asma’u tayi tare da ficewa Moddibo da M Jameel kuwa Matsawa sukayi tare da fara cin ɗumamen kaɗan suka ci sannan suka ci jollof ɗin taliya suka sha tea perpesoup din kazar kuwa ko buɗewa basuyi ba bayan sun gama suka miƙe suka tafi masallaci tare da idar da sallah saida sukayi Azkhar kafin suka dawo gida suka kwanta bacci kafin wani lokaci su tashi su tafi Tafseer acikin makarantar su.

     

    Ƙarfe Goma da rabi dai-dai suka farka atare Moddibo ya miƙe bakinsa ɗauke da addu’a kana yashiga toilet yayi wanka tare da daura al’wala zama yayi tare da shafa lotion mai ƙamshi sannan ya sanya Jallabiya Marron colour tare da ɗaura baƙin Alkyabba akai kana ya naɗa hirami akansa sosai yayi kyau tamkar balarabe kana ya feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin ƙamshi sallah walha ya gabatar tare da zama ya fara ƙira’a cikin Suratul Maryam.

    Sha daya da rabi dai-dai M Jameel ya fito daga ɗaya Bedroom din cikin shiri da alama ya gabatar da sallar walhar shima kallon hadaɗɗen agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yayi kana ya maida kallonsa kan Moddibo tare da cewa.

    “A.J sha biyu ta kusa fa mutafi kasan ana jiranmu”.

    Dai-dai lokacin da wayar Moddibo yayi ruri kallon screen ɗin yayi tare da kallon M Jameel kana yace.

    “Gashi ma malam Arɗo ke kirana da alama zai ce mu ake jira masallaci ya cika”.

    Jinjina kai M Jameel yayi kana yace.

    “Mu tafi”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa tare da ɗaukar mukullin motar suka fice.

     

    Kai tsaye masallacin dake cikin makarantarsu suka nufa wanda yake cike da maza da mata ko wanne na ɓangaren su sai dai mata sunfi yawa ƙarfe 12:00 ya musu acikin masallacin.

    Gyaran Murya M Jameel yayi cikin nutsuwa da kuma yanayin zafin jinjinsa ya gyara zamansa tare da cewa.

    _“Innalhamdulillah Nahmaduhu Wanastainuhu wanastaghfiru wa’nazubillahi billahi min shuriri anfusna wamin sayyi ati a’amalina manyah dillahu fala hadiyala waman mudillah fala hadiyala Wa’ash hadu Allah ilahalillahu Wa’ash hadu anna Muhammadu Abduhu warasulu amma ba’ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu”_.

     

    Suka amsa da.

    “Wa’alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.

    Ya numfasa tare da kallon Moddibo da idanunsa ke lumshe sai kuma ya gyara zamansa kana yace.

    “Duk kan yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanahu wata’ala mai kowa mai komai daya sake nuna mana wannan wata mai cike da falala da kuma rahma Allah ya nuna mana ƙarshen sa lafiya kamar yanda ya nuna mana farkon sa Awancan shekarar mun tsaya aƙarshen Suratul Jinni insha Allah yau zamu ɗaura acikin Suratul Muzammil Aramma jeka cikin suran muji mai Allah yace”.

     

    Gyaɗa kai Moddibo yayi tare da gyara zamansa cikin nutsuwa da sanyin Muryansa tare da kamala kana yayi A’uziyya tare da basmala ya fara kamar haka;.

    _“1-Ya Ayyuhal Muzammil,2-Ƙumullaila illa ƙaliliah 3-Nisfshu awinƙus minhu ƙalila”_

    Atake masallacin yayi tsit tamkar babu mahalukin dake numfashi yayin da karatun ke ratsasu.

     

    Shikuwa M Jameel Kai ya gyaɗa da faɗin.

    “Yawwa Aramma ci gaba mai Allah yake cewa acikin aya ta gaba”.

    Jinjina kai Moddibo yayi tare da manna bayansa da jikin kujera ya cigaba da cewa.

    _“4-Auzidhu alaihi warartilill ƙur’ana tartila5-Inna sanulƙi alaika ƙaulan sakila”_.

     

    Numfashi M Jameel yayi kana yace.

    “Suratul Muzammil Makiyya ce tana da ayoyi guda ashirin.

    Ya numfasa tare da lumshe idanunsa kana ya cigaba da cewa.

    “Suratul Muzammil tana karantar da tarbiya da juriya ga Muslimi,domin susami damar tsayuwar da umarnin Allah”.

    Still wajen yayi tamkar babu mahalukin dake numfashi jama’ar dake wajen su tattara duk kan nutsuwarsu suna sauraron abinda Allah yace Moddibo kuwa System ɗin gabansa ya zubawa Idanu tare da lumshe idanunsa.

    M Jameel ya numfasa tare da cewa.

    _“Ya Ayyuhal Muzammil,Ma’ana ya kai wanda ka lulluɓa da mayafi”_

    Atake masallacin ya kaure da kabbara suna faɗin.

    “Allahu akbar, Allahu akbar Allah yakareka Malam”.

    Zama M Jameel ya gyara tare da kallon jama’ar bayan sunyi shiru ya ɗaura da cewa.

    _“ƙumillayla illa ƙalila,katsaya domin yin Sallah acikin dare(suka) face kaɗan”._

    Nanma kabbara suka sake kaurewa dashi.

    Shi kuwa M Jameel numfashi ya sauƙe kana ya cigaba da fadin.

    _“Nisfshu awin minƙushu ƙalila,Rabinsa ,ko ka rage Abu kaɗan daga gareshi._

    Haka suka cigaba da tafsirin ayoyin.

    Ƙarfe ɗaya dai-dai suka tashi ɗaya da kwata sukayi Sallar azahar zama sukayi acikin masallacin suka fara Muraja’a tun daga suratul tauba zuwa Nahal jin kiran la’asar yasa suka dakata kana suka tashi Moddibo ne yaja Sallar M Jameel kuwa shi yayi ladanci bayan sun idar ne suka fita kai tsaye masallacin dake Unguwar su Moddibo suka nufa ƙarfe biyar suka fara gabatar da tafsirin acikin suratul hujurat wannan kuma na maza ne zalla ƙarfe shida dai-dai suka tashi.

     

    Bayan sun tashi M Jameel yashiga mazaunin Driver Moddibo kuwa gefen mai zaman banza ya zauna tare da lumshe idanunsa yana sakin numfashi Kallonsa M Jameel yayi tare da murmushi kana yayiwa motar key.

    Wayar Moddibo ne ya hau ruri Anutse ya sanya hannu ya ɗauka ganin sunan Ummi yasa ya gyara zamansa cike da nutsuwa yayi Picking tare da Sallama kana yace.

    “Ummi ina yini”.

    Daga ɗaya ɓangare cike da so da kulawa Ummi tayi murmushi kana tace.

    “Babana”.

    Moddibo ya amsa da.

    “Na’am Ummina”.

    Murmushi Ummi tayi tare da cewa.

    “Babana sannuku da ƙoƙari nasan yanzu baki da hutu Ramadan ya shigo”.

    Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.

    “Ga munan dai kam Ummi muna fama”.

    Cike da kulawa da kuma ƙaunar su tace.

    “Allah sarki Allah ya biya ku Allah yaƙara rufa asiri”.

    Ya amsa da.

    “Ameen”.

    Ummi ta gyara wayar akunnenta kana tace.

    “Babana nashirya muku abin buɗa baki kuzo kusha ruwa”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.

    “Toh Ummi mun gode muna nan tafe yanzu ma Insha Allah zamu zo”.

     

    Kasancewar M Jameel na Jin Komai saboda wayar a handsfree yake yasa ya juya akalar motar zuwa hanyar gidan Ummi adai-dai ƙofar gidan Ummi M Jameel yayi hong mai gadi ya buɗe musu suka shiga…!

     

    Yau dai ba editing. Dan muna cikin hidiman bikine

     

     

    By

    *GARKUWAN MARUBUTA*

  • Sakayyah 2

    Sakayyah 2

     

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    Page 2

     

    NA

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE*

     

    *LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE, WANNAN FREE PAGE NE, ƳAR UWA KI BIYA KI KARANTA CIKIB AMINCI BA HAƘƘIN WANI GABA GAREKI 1k ne kacal kuɗin littafin duk da yawa shi. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, ta nan zaku biya, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In kuma baki da account ko matsalar Network ZAKI IYA SAYAN KATIN MTN sai ki copy number’s ɗin katin ki turo min ta WHATSAPP. 09097853276. Kada ki kirani in kin san ba kayan Ɗa’a kike soba. In dai littafine kiyi min mgn a whatsapp ɗin.*

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun da zuƙatan mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida, kai har ma da tan kaɗen gida Shararru kuma ƙasaitattun magungunan matan dans saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata daga hannun. *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Ma’aurats ayau ma na dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki, ko ƙanwarki, ko ƴarki, ko a miniyarli, damake kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Dukansu ƙananan robobin akan dubu uku uku ne kacal Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, koriyar gumba, gumbar madara, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, dukansu a kan dubu uku uku ne ƙananan robobin, sai ta kwalli da ridi da Uku al’khairi da 3 in 1 su dubu biyar biyar ne. Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ta dawo da sabon budurci shi ƴar mitsilar robar 7k ne kana ga masin Daɗi har Maɗigan 5k ne kacal Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, 8k ne  Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, su duka dubu uku uku ne, haɗin Cida kaza, kala biyu ne akwai na 18k shi yanada su tsumi da kwai da rubutu, sai kuma ɗaya haɗin shi 13k ne Ciccibi Abodi, shi 19k ne Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, duk 3k ne kana akwai maganin sanyi sadidan, wanda bani da haufi a kansu set ɗin 10k ne, rabinshi kuma 5k. Ko mai ciki zata shashi baida matsala, infection ko na cikin mahaifane yana magninsa da uzin Allah. Sai su butar sirri, audugar babbar mace,  da dai sauransu…

    Sai kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276.  muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci idan kuna ga account no da zaku tura kuɗinku ta ciki masu son kayan Ɗa’an 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

     

    Cikin fesa sassayyan numfashi, Modibbo ya ci gaba da faɗin.

    “Kuji falalar Allahu rabbil samawati garemu, ubangiji yana sonmu yana tausayin mu,  yana kuma jinkanmu.”

    Ya dire mgnar yana ɗan sauƙe wani numfashi dan Allah ya sani ya fara jin bakinshi ya gaji da mgna. Cikin tattausan muryarsa yaci gaba da cewa.

    Daga Abdullahi ibn Busr, Allah ya yarda dashi, yace:

    (Ya ma’akin Allah! Shari’o’in Musulunci sunyi yawa a gareni,  saboda haka ka nuna mini wani abu da zanyi riƙon da shi.

    Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa.

    (Kar harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambaton Allah.

    Kuma mai tsira da amincin Allah yace:

    (Wanda  ya karanta harafi ɗaya daga littafin Allah yana da ladan kekkyawan aiki ɗaya,  shi kuma kekkyawan aiki ɗaya yana da ladan  misalin goma.

    Ba ina nufin Alif lam Mim harafi bane,

    A’a.  Alif harafi ne, Lam harafi ne, kana shima Mim harafi ne.”.

     

    Wani irin mayataccen kallo Samira ke bin lips ɗin Moddibo dashi, tana mai kallon dukkan yadda yake motsasu, da yadda tattausan sajensa ke zuba ƙyalli ƙawarta Ikilima Ibrahim ce ta ɗan taɓata da kafa alamun wannan wanne irin kallo ne.

    Yayinda gefen damansu kuwa, wata madaidaciyar macece, Hadiza Muhammad Yahaya, wacce take cikin sabbin dalibai.

    Kallon da Samira Sani keyiwa Moddibo ne ke bata mamaki.

    Shi kuwa Moddibo a hankali yaci gaba da cewa.

    Kuma daga Ukbatu Ibn Amir Allah ya yarda dashi yace:

    Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

    Ya fito alhalin muna cikin rumfa sai yace:

    (Wannene daga cikinku zai so ya fita kullum da safe zuwa ƙoramar Buɗhan ko Aƙiƙ ya  dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna ba tare da yayi wani laifi ba ko yanke zumunta ba?

    Mukace masa muna son haka.

    Yace:

    (Ɗayanku yaje Masallaci ya nemi sani, ko ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin littafin Allah, mabuwayi mai ɗaukana, yafi masa taguwa  uku ayoyi huɗu sun fi masa taguwa huɗu da kwatankwacin adadinsu na raƙuma.)

    Kunga ashe muna ɓarar da damarmakinmu riƙe da waya ba tare da mun samu mun ribaci ilimin da iyayenmu da malanmu suka bamu ba.

    Kuma mai tsira da Amincin Allah yace:

    (Wanda ya zauna a wani waje, bai ambaci Allah a wajenba, wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah, wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajenba shima zai zamanto masa abin bibiya a wajen ALLAH.

    Kuma mai tsira da amincin Allah yace:

    (Babu wasu mutane  da zasu zauna a majalisi da basu ambaci Allah a cikinsa  ba, kuma basu yi salati ga annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya, in Allah yaso yayi musu azaba, in yaso kuma sai ya gafarta musu.”

    Jujjuya idanunsa yayi fuskarsa cike da shauƙin son Mahaikin Allah Muhammadu Rasulullah, da sahabbansa,

    Wani irin sassayan numfashi ya fesar tare da lumshe idanunsa, wanda yakan shiga wannan yanayi a duk lokacin da yakeyiwa ɗalibansa nuni da al’khairan dake cikin ammaton Allah da bin sunnar manzonmu abinkoyinmu abinsonmu da sahabbansa masu daraja.

    Ita kuwa Khausar ƙasa tai da idanunta.

    Sai kuma ta ɗan ɗago ta kalleshi jin tattausar muryarsa yaci gaba da cewa.

     

    “Kuma mai tsira da amincin Allah yace:

    Babu wasu mutane da zasu tashi daga wani majalisi da basu ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan *mushen jaki ne* kuma zai zamanto musu abin dana sani)”….

    Ya ƙare mgnar da haɗe kan yatsunsa duka, kana sai ya buɗasu a tare da ware tafin hannunsa kamar ya sake abu,

    alamun ya dasa babbab ɗamba, ya gama da wannan yankin.

     

    Gaba ɗaya hankalinsu tunaninsu duk yana kansa, domin suna matuƙar jin dadin yadda wasu lokutan idan ya shiga aji  yake tunasar dasu mahimman abubuwan da suka cancanci musulmi ya lizamcesu.

    Yayinda wasu kuwa da sam baya shiga ajujuwansu cike da son salon sa suke sauraronsa, kasan cewar makarantar nada yalwar malamai kuma shi aiyuka sun mai yawa shisa ba dukkan class da suke dashi yake shigaba.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin alamun gajiya da yawan motsa lips nasa da yayi yaci gaba da cewa a gaggauce.

    “Mu farka mu ribaci wannan shekarar dukanta kada muce dan wannan wata na Ramadan daya shuɗe, zamu bar wasu ayyukan ibada, mu jure mu zamo dasu ɗabi’armu a kullum domin shi ubangiji ka gafartawa bayinsa, a duk sanda yaso ya ainta wasu daga azaba zuwa rahmarsa madaumiya,  mu wasar da wayoyin nan mu ruggumi Alqur’ani mai girma da tasbihai ya zama dai ita wayar nan sai time to time zamu riƙe ya ke mai karatu dake nake.”

    Ya faɗi hakan yana nuna gefensu Samira dake buɗe da littafi a gabansu.

    Sai kuma ya ɗan gyara saƙale Lapel Microphone din a wuyar jallabiyar jikinsa dan yaji muryarsa tana ƙasa sosai alum yadan zame kaɗan, da ɗan sauri yace.

     

    “Zaku iya duba Muslim (1/554) Abu Dawud (4/264) da waninsa duba Sahihul Jam’i, (5/342). Tirmizi duba Sahihul Tirmizi (3/140) Abu Dawud (4/264) da Ahmad (2/389) duba Sahihul Jami (5/176) Allah shine mafi sani… Abinda nace dai-dai Allah ya haɗamu a mizanin ladan abinda nai kuskure Allah ya gafartamin.”

     

    Ya rufe mgnar da addu’a tare da juyawa ya fita.

    Sukuwa gaba ɗaya numfashi suka sassauƙe, yana fitowa Malam Jamil na isowa wurin, dan shi zai shiga ya shaida musu kwanakin da aka ƙara.

     

    Kai Modibbo ya kauda gefe, jin Aminin nashi na cewa.

    “Fattanah maza yi gudu ki shiga aji kada in rigagi, shiga, dan in na rigaki nima yau gadin aji zansa kiyi mana”.

    Da sauri Khausar din ta juyo tare da kallon shi cikin alamun yanai musu barkwanci tace.

    “Malam ko ta window ma zan shiga”.

    Murmushin yayi tare da cewa.

    “Har yanzu baki girmi shiga ta window ba FATTANAH”.

    Da sauri tace.

    “Toh ai banyi jikiba, ka gani”.

    Kawai sai ta kama jikin window alamun zata zauna ta wajen sai ta juya ta ciki.

    Cikin yamutsa fuska Moddibo yace.

    “Ke bar nan,”.

    Ai da sauri ta diro tare, da nufar ƙofa, tana tura baki.

    Shi kuwa Malam Jamil cikin tsananin son yarinyar sabida ƙwazonta da jan da kwanyarta keyi kana da ƙawancenta da ƙanwarsa Asma’u Ahmad ya bita da ido.

    Rungume Moddibo yayi tare da yin mgn murya can ƙasa.

    “Tuba mukeyi Moddibo ai mana tsawan a hankali ka mance baka cire Lapel Microphone ɗinba, har nima tsawar ta razanani”.

    Wani irin nannauyan numfashin Moddibo ya sauƙe tare lumshe idanunsa.

    Shi kuwa M Jamil murmushin yayi kana kuma ya sake shi yace.

    “Lokaci na tafiya sai na fito na sallami maza kam”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa tare da sauƙa ƙasa.

     

    Goma  dai-dai aka tashi islamiyan gaba ɗaya duk ɗaliban suka koma gida bayan M Jamil ya musu bayanin dalilin ƙarin hutun, wanda kuma suma sunga hakan.

     

    Ƙarfe ɗaya dai-dai suka tashi daga taron tattaunawa da malaman nasu baki ɗaya.

     

    Bayan sunyi sallan azahar ne, kana duk suka tafi, ma’aikata sukaci gaba da aikinsu.

     

    A gidansu Khausar kuwa.

     

    Khausar ce kwance bisa 3 str daga ita sai yar doguwar rigar material mai taushi a jikinta, Pink collor, sai hular sanyi data sa a kanta, yayinda himilin gashinta yayi tub-tub a ciki.

    Da alamun bacci take sonyi.

    Cikin sanyi ta buɗe ido ta tare da juyowa ta kalli Momynta dake fitowa daga kitchen ɗinta, hannunta riƙe da plate da  yankakkun fruits  a ciki masu sanyi, gefen ta ta zauna bisa 1 str ta ɗaura plate ɗin kan cinyarta tare kallon Khausar ɗin  data miƙa mata hannu alamun ta bata.

    “Tashi kije ki ɗebo Uniform ɗin ku, nasan yanzu ya bushe kizo ki goge muku kafin a kira magriba”.

    Numfashi mai ɗan sanyi Khausar ɗin ta fesar tare da miƙewa zaune, ita kuwa Momy tafin sawun ɗiyar Tata take kallo cike da ganin kamannin sawunta dana ahlinta.

    Hannu tasa ta ɗauki inabi guda uku. Kana ta  miƙe tsaye tare da juyawa ta fita.

    Ita kuwa Momy da idanu ta rakata.

     

    Tana fita a barandar ta tsaya tare da ɗan sa hannunta na dama ta riƙe ƙugunta.

    Amina  ce ta fito daga side din Gimbiya Bunayya, mahaifiyarsu kenan, uwar gidan Lamido,

    Wacce daga itana sai Maman su Khausar wacce itace amaryarsa.

     

    Wani irin  kallo Amina tayiwa Khausar tare da cewa.

    “Hamshaƙiya, cin abu a tsaye ba koyarwar musulunci bane”.

    Fuska Khausar ɗin ta ɗan yamutsa tare da cewa.

    “Ngd”.  Sai kuma ta miƙawa Aminu ƙanin Amina wanda yake gefenta.

    Da sauri Amina ta kwaɓe hannun yaron da bazai gaza shekara goma sha ɗaya  ba tare da cewa.

    “Makwaɗaicin baza, in zakaci akwai a fridge kaje a baka”.

    Ido Khausar ɗin ta zuba mata, sai kuma ta sauƙe numfashi dan batayi mmkin hakanba, cikin alamun kasalan da baccin da takeji ya sakar mata, ta nufi wurin shanyan nasu, a hankali take tafiya, dan ganin shanyan nasu yana can  har bayan Part ɗin Hajia Bunayya Umma.

    “Wannan daga gani ma aikin Ramadan ne, shine zai zo yayi mana shanya har nan, zaice waɗan can igiyoyin tsawonsa bazai kaiba”.

    Ta ƙare mgnar tana nufar can.

    A hankali ta fara janye shanyan, har ta isa dai-dai window Hajia Bunayya, cikin mamaki ta ɗan tsaya jin yadda Umman ke mgn da faɗa-faɗa.

    “Kada in damufa kake cewa.

    Kasan kuwa irin tashin hankali da nake ciki duk sanda na buɗi idanuna na kalli Haiydar a matsayin ɗan Lamido Yariman Gembila kuwa, ko ka mance shine ɗan sa na miji babba, shin baka ganin iyakata da mulki sai dai gani sai hange tunda shine ɗa babba akan Aminu na.

    Kai bakaga yadda komai zai juye min ba a gaba, ina gani sarauta zata koma ɗakin Aysha ƴaƴanta ne zasu mulki masarautarmun”.

    Sai kuma tayi shiru alamun tana sauraron abin da ake cewa a ɗaya sashin.

     

    Ita kuwa Khausar cike da tsoron halin irin na Umma, gashi dai abinda taji, amman koda zata kwana gayawa mahaifiyarsu bazata taɓa yardaba, domin Umma bata taɓa nuna kishinta a kanta, shiyasa ta ɗauki dukkan yarda ta bata.

     

    Cikin tsananin tsoro Khausar ɗin ta zaro ido ta tare dasa tafin hannunta ta dafe ƙahon zuciyarta, jin Hajia Bunayya na cewa.

    “Wallahi tallahi billahil azeem zanyi komai dan ganin bayan Aysha da yaranta, zanyi duk abinda ya kama domin in kauda Haiydar a matsayin yarima mai jiran gado, dan wlh Allah zan iya kasheshi kowama ya huta!…”.

    Cikin tsananin kaɗuwa Khausar ta juya da sassarfa ta koma sade ɗin Maminta, tana isa kawai sai ta watsar da kayan bisa kujera.

     

    Da sauri ta kamo hannun mahaifiyar tata tare da cewa.

    “Momy! Momy dan Allah ki biyoni zo kiji wani abu”.

    Ta ƙare mgnar a matuƙar kiɗime, wanda hakan yasa dole Hajia Aysha ta bita a baya.

     

    Ita kuwa da sauri take jenta, har zuwa bayan window Hajia Bunayya.

    Cirko-cirko suka tsaya,

    Ita kam Khausar cike da firfito da ido waje take sauraron abinda Hajia Bunayya ke faɗi.

     

    Momy kuwa wani irin…!

     

     

    A hankali M Jamil yayi parking  a bakin gate ɗin gidansu Moddibo juyowa yayi ya kalli Moddibo dake gefensa yana lallatsa system nasa.

    “Toh wazai fita ya buɗe mana gate ne kam?”.

    Ba tare da ya ɗago ya kalleshiba ya ɗaga kafaɗarsa ɗaya tare  buɗe tafin hannunsa alamun

    Oho.

    Kai M Jamil ya jujjuya tare da cewa,

    “To bari ni buɗe”.

    Kai ya kuma gyaɗa masa alamun.

    “Toh”.

    Murmushin M Jamil yayi tare da fita ya buɗe gate ɗin, kana ya dawo yaja motar suka shiga ciki.

     

    Parking yayi kana suka fito suka nufi cikin gidan,

     

    Kai tsaye sashin Innayin suka wuce.

     

    Wani irin yalwataccen murmushin M Jamil yayi tare dayin saurin ya haura kan barandar zama yayi daɓas bisa tattausan carpert ɗin dake shimfiɗe a barandar.

    Innayi na kwance yayinda  Ummin Jamil kuwa ke gefenta tana ɓare mata banana.

    Itama yalwataccen murmushin tayi tare da miƙawa Moddibo ayaban data ɓaren.

    Amsa yayi tare da juyowa ya ɗan kalli M Jamil da ya zame ya kwanta bisa carpet ɗin tare da ɗaura kansa bisa cinyarta, cike da so, ƙauna, shaƙuwa, tausayawa, yace.

    “Ummina kin san irin farin cikin da nakeji a raina kuwa in na ganki?”.

    Murmushin kawai tayi dan ita bazata iya cewa komaiba a gaban Innayi sabida Jamil shine ɗan ta na fari, kuma su nan Gembila sashine na cikakkun Fulani.

     

    Kawai dai abinda ta sani a baɗini tasan ta fishi farin ciki.

    Shi kuwa Moddibo gefen Innayi dake kwance da alamun har yanzu nitsuwarta bai ida dawowa jikintaba, hannunta ya riƙe tare da kallon M Jamil.

    “Kai dan Allah ɗagata kada ka karya mana cinyarta da katon kankan nan”.

    Ya ƙare mgnar yana gutsuran banana.

    Shi kuwa Jamil da sauri ya tashi zaune jin Umminshi na ture kanshi tana cewa.

    “Ai kam gskyarka Moddibo”.

    Tashin nasa ne, yasa ta miƙe ta nufi kitchen, trayn data shirya kulolin abincinsu ta kawo musu.

    Ta ajiye a tsakiyar su,

    Shi kuwa Modibbo a hankali ya kamo hannun Innayin tare da tallabota alamun so yake ya ganta a zaune.

    Sai kuma duk suka kalli Innayi data buɗe kwayar idanunta jin yana tallabota.

    Zaunar da ita yayi cikin kulawa yace.

    “Yanzu me yake miki ciwo?”.

    Cikin sanyi tace.

    “Nima kaina ban saniba, kawai dai zuciyata ke a tsinke tsoro nakeji Moddibo”.

    Da sauri Jamil yace.

    “Toh Innayi tsoron me kuma kikeji?”.

    Cikin sanyi tace.

    “Tsoron kada mutuwa tai mini zuwan ba zata”.

    Wani irin masifeffen tsinkewan zuciya ne ya riski Moddibo jin Jamil ya ɗan yi yar dariya tare da cewa.

    “Kada ki damu Innayi ki dena jin tsoron mutuwa, domin ita wajibinmu ne ita.

    Kuma tsufa ba shine hanyar mutuwaba, ba abin mamaki bane ki rayu ni nan Jamilu in mutu in barki, in bar Ummina da rashina, in bar Aminina Moddibo da rashin Aboki kamata, tabbas a al’amarin ubangiji zan mutu in barku a raye da kuma ƙunar rashina”.

    Da sauri Moddibo yace.

    “Yah Salam wai kai J meyasa ne wasu lokutan kalamanka a baibaisuke? Dan Allah kasan abinda zakana cewa”.

    Murmushin mai sauti Jamil yayi tare da cewa.

    “Zanfa mutu kam, dole zan mutu to kai dama a gani kake a haka zamu tabbata ne?”.

     

    Da hannu Moddibo ya nuna masa Umminsa da haka kawai taji wasu irin zafafan hawaye sun zubo mata.

    Da sauri Jamil yasa tafin hannunsa ya sharce mata hawayen tare da cewa.

    “Kada kiyimin kuka kodama na mutu kada ki damu Ummina kinga aminina Aliyu ko to shi zai zame miki madadina”.

    Da sauri tayi mishi dakuwa.

    Sai kuma yayi dariya mai sauti tare dace.

    “Oh su Ummi ana son ɗan fari wato irin bakya son Jamilunki ya mutun nan ko”. Ya ƙare mgnar cikin tsigar wasa kamar dai kakarsa ce,

    Hakanne yasasu yin murmushin ganin zata kai mishi duka ya ɗan zille yana cewa.

    “Haka kawai wai kunya wai ni ɗan fari bazakice kina sonaba, toh ni kam ina sonki ina sonki ina sonki Ummina”.

    Ƙeyarsa ta ɗan buge, kana ta  tura musu plate ɗin dake cike da fruits sai kuma ta mimmiƙa musu fork,

     

    Innayi kuma yar wannan hirar da sukayi yasa ta ɗan sake kaɗan, duk da har yanzu in ta rufe idanunta tana ganin abinda Allah ya nuna mata daren jiya.

     

    Jamil ne ya kalli Innayin tare da cewa.

    “Dr  Jamila tazo ta dubaki ko, dan da safe kafin mu wuce makaranta na kirata tazo”.

    Kai Ummi ta gyaɗa alamun eh tazo.

     

    Frutis ɗin kawai suka ci kana suka miƙe suka nufu part ɗin Moddibo.

    Suna shiga falon,

    Cikin sanyi Jamil ya zauna bisa kujera tare da riƙo yatsar Moddibo manuniya, cikin wata iriyar sassayar muryar yace.

    “Moddibo kasan ina jin farin ciki na musamman in naga Ummina ko?”.

    Sunkuyar da kai Moddibo yayi tare da zuwa aminin nasa idanu cikin sanyi yace.

    “J nasani! Na sani dan farin cikin baya ɓuya a fuskarka”.

    Cikin Muryar da tafi ta ɗazu rauni ido na ciko da hawaye yace.

    “Amman kuma fa farin cikina raggene, duk daɗin da nakeji in na tuna cewa Ummina ba a gidan Dadyna takeba, inajin ciwo mai yawa a raina, inajin takaicin Kasan cewar mahaifiyata bata gidan mahaifina tana can a wani gidan.

    Bayan ita tasha wahalar zama dashi cikin talauci,  saida yayi kuɗi dai-dai sanda zataji dadin rayuwa ya saketa, gashi yan uwanta ba masu haliba, mijin da Allah ya ƙaddara ta aura shima rayuwar ba daɗi sabida baida ƙarfi”.

    A hankali Moddibo ya zauna kusa dashi cikin ƙarfafa mishi guiwa yace.

    “J wanne dadine na kuɗi ya rage wanda bakayiwa Ummi ka tunafa, duk abinda kace kanaso Daddy yana baka, duk kuɗin da zaka nema zai baka, a haka har Makka ka kai Ummi yaranta ka sasu a makaranta mai kyau sanadin su kaƙi kayi aiki a ko ina kace zakayi karantarwa a makarantarsu dan ka tayata basu tarbiyya. Kana kuma yi tunda gashi yanzu sun kusa gamawa, tunda ko Asma’u nanda shekara uku dai zasu gama,  secondary School, kace kuma suna gamawa zaka aurar da Asma’u kana ka ɗauki nauyin karatunta, ta na gaba tana gidan mijinta, shi kuwa Bashir na mijine kuma kace in ya gama so kake ya samu jami’atul Madina, in ya tafi can sannan kayi aure kace kuma kana aure zaka ɗauke Ummi da ita da mijinta Malam Ahmad zaka riƙe su, Jamil to meya rage na jin daɗi da baka samawa Ummi ba, ka gyara mata gidan da take, ka gyara mata ɗakinta”.

    Wani murmushin mai sanyi yayi tare da cewa.

    “To wai Moddibo da kake cewa haka, rainafa mallakin ubangijine a duk sanda yaga dama zai ɗaukeni daga  wannan duniyar, ko ban gama cikace burukana ba, in babuni a raye wa zai maiye musu gurbina?”.

    Cikin tsuke fuska Moddibo yace.

    “To dama wa yake da tabbacin rayuwa, yanzu ni in dai naci zan lizanci irin tunaninka Innayi fa bata da kowa a duniya saini.

    J ni zaka gayawa mutuwa? Ni Aliyu zaka gayawa mutuwa?”.

    Sai kuma duk sukayi shiru suka zubawa juna ido.

    Numfashi mai nauyi Moddibo ya fesar kana a hankali yace.

     

    “J ka kalleni mana! In zame maka madubi, gwara kaifa,

    kasan su Ummi kana ganin ta gafa Daddy”.

    Da sauri M Jamil ya ri ƙa gyaɗa mishi kai tare da tuno maraicin aminin nasa.

    Shi bai san iyayensu ba ranar da mahaifisa ya rasu, firgicin abin ne ya tadawa mahaifiyarsa naƙudansa, ta haifeshi kana itama tabi bayansa kamar yadda Innayi ke basu labari.

    Da sauri M Jamil ya kalleshi jin yana mgn a hankali.

     

    “Ba uwa ba uba ba wa ba ƙani ko ƙanwa ba Baffa ba kawu ba goggo ba Yafendo, yanzu ashe bazaka dubi maraicina ba, sai kai ka godewa Allah ba J kaga ni kuwa idan na tuna duk rashin da nayi in naji ƙunci da ciwo sai in tuna.

    Allah ya azurtani da rayuwa da lafiya kana yayi min ni’imar kasan cewa Musulmi, ya bani hankali ya ƙara min da haddar izu settin, da littattafai masu tarin yawa wanda masu iyaye da dama basu samuba, ya bani sa’a a dukkan karatuna mukayi digire har master’s har zuwa P.H.D a makaranta mafi daraja a duniya Jami’atul Madina, kana muka samu gurɓin aiki kuma a can.

    Wanda ko yau muka koma can da aikinmu a hannu, amman kai ga uzurin daya tsareka, nima kuma da uzurin daya tsareni”.

    Da sauri M Jamil yace.

    “Astagfurullah! Astagfurullah!! Astagfurullah!!! Alhamdulillah aboki na gari rahama ne, ai kam ni ga uzurin daya tsareni  to amman kaifa Moddibo uzurin menene ya tsareka duk da bana son mu rabu Amman zaso kaje can kayi aikinka da al’bashinka mai daraja”.

    Kai Moddibo ya kauda tare da cewa.

    “Uzurina ai a fili yake J Innayi na tana son kulawata”.

    Da sauri M Jamil yace.

    “Ba gsky bane Moddibo karo na forko kenan a rayuwarmu daka ɓoye min abinda ke ranka kaƙi ka gaya min me dalilin ka na zama a ƙasar nan bayan saudia na buƙatar ka, kuma harda daman zama da iyalanmu fa muke dashi a can”.

    Kai ya jujjuya tare da cewa.

    “J yaushe na zama makaryacin da har mgnata bazata samu karɓuwa a wurinka ba?”.

    Da sauri M Jamil yace.

    “No wlh ni mai shaidar ka ne har gaban abadan kai ba makaryaci bane, kawai dai ban gamsu da hujjar bane”.

    Kanshi ya jujjuya kana ya nufi bedroom ɗinsa,

    Shi kuwa M Jamil ɗayan ya shiga.

     

    A can cikin masarautar Gembila kuwa,

    Cike da kaɗuwa Khausar ta…

     

    Ta juyo ta kalli mahaifiyarta sabida jin kalaman da Hajia Bunayya ke faɗi.

    “Eh Sulaiman a kawo min mashin ɗin lipan mai kyau wanda zaiyi dai-dai da Haiydar,

    A kawo fari dan yafi son komai nasa fari”.

    Sai kuma ta ɗan yi jim, alamun tana sauraran abinda ake faɗi a ɗaya sashi,

    dariya mai cike da sakewar zuciya tayi tare da cewa.

    “Ai kaima kasan shi na musamman ne, Yarima ne fa, mai jiran gado, kuma gashi sunan Babanmu gareshi, in banji dashi ba da waye zanji”.

     

    Ita kam Khausar cike da mmki take kallon yadda mahaifiyar ke sakin wani murmushi mai cike da yarda da jin daɗin kawaici da ihsanin uwar gidan tata,

    Yayinda ita kuwa Khausar take kallon abun da idanun basira, tana tuna kalaman da taji ɗazu da wanda Umman keyi a yanzu, a sanyaye tace.

    “Marching kuma?”.

    Daga ciki kuwa sai suka tsinkayo muryar Asiya na cewa.

    “Ehye Haiydar ɗan gatan Umma da Lamido, yaron nan kunaji dashi,”.

    Murmushin mai cike da manufa tayi tare da kallon inuwar Khausar da Mami  ta jikin window nata, cikin ɗan daga sauti tace.

    “Kema ai ɗan lelenki ne,”.

    Miƙewa tsaye Asiya tayi tare da cewa.

    “Yauwa dan Allah Umma ni zanyi masa albishir”.

    Kai ta gyaɗa tare da cewa.

    “Amman ba yauba sai marching ɗin ya iso”.

     

    Numfashi mai sanyi Momy ta fesar tare da kamo hannun Khausar suka juya suka tafi.

     

    Ganin tafiyar sune yasa Hajia Bunayya yin kwaffa tare da cewa.

    “Uhum zanyi mgnin kine, shegiyar yarinya mai masifar wayon tsiya da  sa ido, tama fi mahaifiyar tata wayo da fahimtar manufar mutum”.

     

    Su kuwa, suna shiga falon Khausar ta juyo a hankali tace.

    “Dan Allah Momy kada ku bari Haiydar yaja marching yayi ƙarami dudu du fa shekarunsa sha 13 ne kawai dan yanada saurin girma”.

    Da sauri ta juyo ta kalli Haiydar da yanzu shigowarsa, kanshi ya nuna da yatsarsa manuniya tare da cewa.

    “Ni ne ma yaron? To da shekaru nawa kika fini dabino uwar tsufa,  ba shekara ɗaya rak kike bani”.

    Yes tabbas kam shekarunsa 13 ne, amman in ka ganshi zakayi zaton yaje 16, domin yanada girman jiki, kuma irin masu wayo da halin girman nanne shiyasa sam bazaka tantance shekarunsa ba, ya fita jiki da tsawo sosai.

    Dan in ka gansu zakayi zaton shine babban irin ya bata shekara ukun nannan ne”.

    Kai ta jujjuya tare da rumtse tafin hannunta, kana cikin sanyi tace.

    “Dan Allah  Momy kada ki bari dan Allah a wannan karon dai ki yarda dani”.

    Kai Hajia Aysha ta gyaɗa mata tare da cewa.

    “Zan duba.”

    Cikin kwaɓe fuska Haiydar ya turo baki gaba tare da cewa.

    “Plesse Momy kada kibi ta kan mgnar ta”.

    Still kai ta gyaɗa masa shima tare da cewa.

    “Toh zan duba”.

    Cirko-cirko sukayi a gabanta.

    Dan dama da haka take yanke musu taƙaddama.

    Idanu ta ɗan lumshe jin an kira sallan magrib cikin fesar da sassayan numfashi tace.

    “Lokacin salla yayi, maza muje muyi salla”.

    Ba musu duk suka juya, shi Haiydar waje ya fita yana cewa.

    “Ramadan zomu tafi masallaci”.

    Ita kuwa Khausar ɗakinsu ta nufa tana cewa.

    “Raudat zomuje muyi salla.”

    Da sauri kuwa sukabi bayansu.

     

     

    A can gidansu Moddibo kuwa,

    M Jamil ne, ya kalli dun-duniyar sawun Moddibo lokacin da suka fito kan barandar da alamun al’wala sukayi.

    A hankali yake taku cikin nitsuwa, yayinda yake motsa laɓɓan bakinsa yana taibihi.

     

    Sai kuma ya maida kallonsa kan sumar ƙeyarsa dake kwance lip-lip tayi irin naɗin nan mai kamar taburma.

    Kusan a tare suka sauƙo,

    Hango Ummi da Innayi zaune bisa sallayunsu, da kaskon rushi a tsakiyar su ne, ya sasu juyawa suka nufi waje, sabida tafiya masallaci.

     

    A hankali Moddibo ya zira tafukan hannunsa cikin aljuhun jallabiyar jikinsa, sabida wani irin masifeffen sanyi dake fesowa, duk da rigunan sanyin da suka ɗaura kan jallabiyoyin bai tsare musu sanyi irin na garin Gembila ba, musamman ma, a lokacin da magrib ta ƙarato, wanda lokacin sanire ke sauƙa.

     

    Kasan cewar masallaci babu nisa da gidan ne, yasa suka, tafi da sawu.

     

    A hankali M Jamil ya lumshe idanunsa sabida yadda yake jiyo sautin muryar Moddibo can ƙasa yana zikirin tafiya masallaci.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin yanayin sanyin da yakeji yake motsa laɓɓan sa a hankali cikin dadɗan  sauti can ƙasa-ƙasa yake cewa.

    اللَّهُـمَّ اجْعَـلْ فِي قَلْبِـي نُوراً، وَفِي لِسَـانِي نُوراً، وَفِي سَمْعِي نُوراً، وَفِي بَصَرِيِ نُورًا، وَمِنْ فََوْقِي نُوراً، وَ مِنْ تَحْتِي نُوراً، وَ عَنْ يَمِينِي نُوراَ، وعَنْ شِمَالِي نُوراً، وَمِنْ أَماَمِي نُوراً،,وَمِنْ خَلْفِي نُوراً، وَاجْعَلْ فِي نَفْسِي نُوراً، وأََعْظِمْ لِي نُوراً، وَعَظِِّمْ لِي نُوراً، وَاجْعَلْ لِي نُوراً، واجْعَلْنِي نُوراً، ألَلَّهُمَّ أَعْطِنِي نُوراً، وَاجْعَلْ فِي عَصَبِي نُوراً، وَفِي لَحْمِي نُوراً، وَفِي دَمِي نُوراً، وَفِي شَعْرِي نُوراً، وفِي بَشَرِي نُوراً، أَللَّهُمَّ اجِعَلْ لِي نُوراً فِي قَّبْرِي… وَ نُوراَ فِي عِظاَمِي، وَزِدْنِي نُوراً، وَزِدْنِي نُوراَ، وَزِدْنِي نُوراً، وَهَبْ لِي نُوراً عَلَى نُوراً

    Dai-dai lokacin da yazo ƙarshen addu’ar suka isa bakin masallacin.

    Kusan a tare suka haɗa baki wurin yin addu’ar shiga Masallaci.

    ”أَعوذُ بِاللّهِ العَظِيـمِ، وَبِوَجْهِـهِ الكَرِيـمِ وَسُلْطـَانِه القَدِيـمِ، مِنَ الشَّيْـطَانِ الرَّجِـيمِ، بِسْـمِ اللّهِ وَالصَّلَاةُ وَالسَّلامُ عَلَى رَسُولِ اللّهِ، اَللَّهُـمَّ افْتَـحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتـِكَ“

    Kana a nitse suka shiga cikin masallacin.

    Shi Moddibo gefen daman sahun forko ya zauna, yayinda shi kuma M Jamil ya nufi wurin kiran salla…

     

    Kasan cewar M Jamil ke ladancin masallacin Moddibo kuma limancin…

     

    Bayan an idar da sallane, Khausar ta juyo ta kalli Raudat tare, da miƙa mata littafin  Dua azkar, amsa tayi kana ta buɗe daga shafin forko ta fara cikin sassayan sautin yarinta.

     

    Ita kuwa Khausar Alqur’anin ta, ta ɗauka tare da fara, rero karatun Alqur’ani cikin zazzaƙar muryarta take biya suratul Nisa’i.

     

    A haka har aka kira isha sukayi kana, suka fito.

    A falon suka zauna baki ɗayansu suna cin abinci.

     

    Misalin ƙarfe tara da rabi, Ummi ce zaune gefen Innayi da hijabi  a hannunta alamun ta gama shirin tafiya.

    Cikin kulawa da martabawa tace.

    “Toh Innayi Allah Ubangijin talikai ya baki lfy yasa zakkan jikine, in Sha Allah gobe koda dare zan zo in kuma dubaki da jiki”.

    Kai ta gyaɗa cike da jin daɗin kulawar Ummin Jamil cikin ƙarfin guiwar da ta ɗan samu tace.

    “Amin ya rabbil izzati Fatima ngd matuƙa Allah ya raya miki ahlinki yasa suyi miki fiye da abinda kikeyi min”.

    Cike da jin daɗin addu’ar tace.

    “Amin ya Allah”.

    Moddibo kuwa, kai ya tankwara gefe yana kallon kakartasa, sosai ta rame a dare ɗaya da wuni ɗaya.

     

    Haka dai sukayi sallama Jamil ya ɗauke ta suka tafi.

     

    Har bakin gate Modibbo ya rakasu.

    Kai ya ɗan juya ya kalli wata motar dake gefen damansa ƙirar BMW irin dai wacca M Jamil yaja sukaje makaranta, sai dai wacce baƙace wannan kuma farace ƙal  mai masifar kyau.

    Murmushin M Jamil yayi sabida ya fahimci kallon da yayiwa motar ma magana ce.

    kanshi ya juya tare da cewa.

    “Lafiyarta ƙalau kawai na barta a nanne sabida nan ya dace da ita, tunda ba gida ɗaya mukeba, Allah ya kiyaye wani uzurin zai iya tashi da dare, kaga kamar jiya da kasan Innayi ba lafiya kawai ɗaukarta zakayi ku tafi hospital ko Ummi?”.

    Ya dire ayar mgnar yana kallon Umminsa da shima Moddibo ita yake kallon.

    Cikin gamsuwa Ummin tace.

    “Sosai ma kuwa”.

    Cikin yin ƙasa da kai Moddibo yace.

    “Ummi har kema haka zakice, kamar baki san me ake faɗi a cikin gariba, ba cikin gari, bama har cikin gidansu fa, ganin kaskas akemin wasuma ɗaukar abotarmu ta tun yarinta sukeyi a matsayin na maida J saniyar tatsa.”

    Cikin sanyi Ummin tace.

    “To Moddibo ai shi ɗan adam ba’a biye masa”.

    Da sauri Jamil yace.

    “Yauwa Ummi gaya masa dai kam”.

    Cikin tsare M Jamil din da ido yace.

    “Motace dai ta hannunka ta ishemu, kuma ga waccar ma, kasan in bawai baka nanba always muna tare”.

    Da sauri Jamil ya jujjuya mishi kai tare da jan motar ya tafi.

     

    Sashin  Innayin ya nufa, cike da zurfin nazari.

    Tv ya kunnamata tashar Sunna, inda aka sa sautin karatun Alqur’ani mai girma.

    Ido Innayi ta lumshe jin nitsuwa da salama na diro mata,

    Saida safe yayi mata kana juya ya fita zuwa Part ɗin sa.

     

    Washe gari ranar Alhamis ne, yau babu makaranta ko yan haddan bazasu jeba, shiyasa su Khausar suna gida,

    Bayan sallan la’asar Asma’u Ahmad ta shigo falon Momy cikin sakin fuska tayi sallama.

    Da sauri Khausar ta fito daga ɗakin Momy tana cewa.

    “Wa alaikissalam Giɗaɗo”.

    Murmushin Asma’u Ahmad Giɗaɗo  tayi, ƙanwar M Jamil kenan da suka haɗa uwa.

    Cikin sakin fuska tace.

    “Jauro”.

    Fuska Khausar ta kwaɓe tare da cewa.

    “Wai jauro gsky ni an cuceni”.

    Murmushin sukayi baki ɗaya sabida daƙuwar da Mamy tayi musu.

    Cikin kunya Asma’u ta ɗan rusuna, tare da cewa.

    “Barka da yamma Mamy”.

     

    “Barka dai Asma’u ya Umminki?”.

     

    “Tana lfy tace in gaidaki”.

     

    “Masha Allah Ina amsawa”.

     

    Da sauri ta miƙe tsaye jin Khausar ta kamo hannunta.

    Ɗakinta suka nufa, suna shiga suka zauna bisa gado.

    Raudat dake kwance kan gadon riƙe da wayan Mamy tana game ne ta miƙe da sauri ta faɗa kan Asma’u.

    Ruggumi yarinyar tayi tare da cewa.

    “Autan Mamy tsifa ake yi ne”.

    Kai ta gyaɗa mata tare da cewa.

    “Eh kuma gashi har yanzu Adda Khausi bata gama minba, tsifanta zafi”.

    Hararanta kausar ta ɗanyi tare da cewa.

    “Da Allah tashi daga nan, nawama da yaya nake tsifan,  kin samu ma inayi miki”.

    Ta ƙare mgnar tana fita daga ɗakin.

    Jim kaɗan ta shigo riƙe da filas da kofuna guda biyu bisa tray da kuma kayan tea, kan bed side drower ta ajiye tiran kana ta haɗa musu tea mai zafi, sabida rage sanyin da suke rayuwa cikinsa, yasa tea ya zame musu tamkar ruwa, madadin in kaje baƙunta a baka abin sha mai ɗan sanyi, sai a tarbeka da zazzafan shayi.

     

    “Gidado bar tsifan nan ga tea”.

    Khausar ta faɗa  tana zama gefenta tare da miƙa mata, kofin.

    Amsa tayi tare da kallon Raudat da ta fice da gudu sabida jin Abbansu ya shigo yana kiranta.

     

    Riƙe cup ɗin tayi ba tare da tasha ba,

    Ido Khausar ta ɗan zuba mata kana tace.

    “Ya dai Giɗaɗo lfy kuwa?”.

    Numfashi mai nauyi Asma’u ta fesar kana cikin sanyi tace.

    “Kamar zan biya ɗazu ki rakani”.

    Ajiye cup ɗin hannunta tayi tare da cewa.

    “Ina?”.

    Murmushin Asma’u tayi tare da cewa.

    “Gidan su Moddibo”.

    Fuska ta kwaɓe tare da cewa.

    “Allah ya kiyasheni, me zai kaini gidansu wannan mugun, mutumin da duk duniya bana da maƙiyi sama dashi, duk abin da nai laifine, ni zanje gidansu yace na kai musu fitsara ya dakani a banza”.

    Murmushin Asma’u tayi tare da cewa.

    “Yoh ai shiyasa ma ban biyaba dan nasan bazaki taɓa yarda kijeba, kuma dai don shine sarkin masifa da mugunta kawai daga zuwa gidansu sai ya kama dukanki”.

    Baki ta taɓe tare da cewa.

    “Yoh ai bazanma jeba ma”.

    Kai Asma’u ta jinjina a ranta tana raya wata rana zatayiwa Khausar tsiya, ta kwasheta ta kaita.

     

    Ajiye kofin tea  ɗin tayi tare da cewa.

    “A’a  dubiyar mara lfy cefa Innayinsa ce ba”.

    “Can musu”.

    Ta faɗa tana kwaɓe fuska

    Murmushin Asma’u tayi tare da cewa.

    “Toh naji”.

     

    Daga nan sukaci gaba da hira.

     

    Washe gari ranar jumma’a, misalin ƙarfe biyar dai-dai Khausar da ta shigo cikin gidan riƙe da hannun Raudat da alamun kitso ta kaita.

    A bakin mashigar gidan nasu tayi kiciɓis da Amina da Samira sani,

     

    Sun iso bakin ƙofar a tare, dole sai ɗaya ya kaucewa ɗaya kafin a samu wurin wuce.

    Wani  masiyacin kallo Samira ta cillawa Khausar tare da jan tsaki.

    Ita kuwa Khausar tsuke fuska tayi cikin rashin shakka ko tsoro ta goga kafaɗarta da na Samira duk da kuwa Samira ta girmeta ainun.

    Cikin izza Samira tace.

    “Ke karere ki nitsu kisan da waye kikeyi”.

    Ba tare da ta cire idanunta cikin nataba tace.

    “Toh  dodon gori”.

    Cikin fahimtar caguben baƙar mgnar da Khausar ɗin ta yaɓa mata wanda yafi abinda ta gaya mata ciwo, tace.

    “Ke nifa uwarki zanci”.

    Wani bauɗeɗɗen harara da dogon tsaki Khausar taja tare da cewa.

    “Raudat mu tafi, kada mu tsaya muji, kukan tsuntsaye marasa tushe da gurbatacciyar tarbiya”.

    Daga nan, ta juya tayi gaba.

     

    Samira sani kuwa wani irin masifeffen kallo mai cike da tsana take Binta dashi.

    Cikin takaici tace.

    “Wallahi na tsani wannan yarinyar sam bana son ganinta, domin ta zame min madakatar nasarata”.

    Kwaffa Amina tayi tare da cewa.

    “Bar shegiyar yarinya zanyi mgninta”.

     

    Cikin tarin tsana Samira tace.

    “Kune ma kuka bata dama ai, tana agola sai iyayi take muku, an wani dai-dai ta komai naku da nata, wai hatta makarantarku ɗaya da ita, ni wlh da nice ke sai na zuga Umma ta zuga Lamido tasa an cireta a wannan makarantar, shegiyar yarinya mai kama da ƴan ruwa.”

    Kwaffa Amina tayi tare da cewa.

    “Bar hegiyar yarinya, zanyi maganinta”.

     

    Ita kuwa Khausar a falo suka samu Mamynsu kishingiɗe bisa carpet saƙale da wayarta a kunne, da alamu waya takeyi, ido ta zuba mata jin tana cewa.

    “Eh Hajja Nana in Sha Allah, zata zo, don dama cikin azumi suna hutu to kuma rashin lfyar ne ya hanata zuwa, amman yau suka koma makaranta, kuma an ƙara musu hutun mako uku guda, sabida gyaran da akeyi a makarantar in Sha Allah zata zo, a satin nan,”.

    Sai kuma ta ɗan yi shiru, na wasu ƴan daƙiƙu, cikin sanyi da girmamawa tace.

    “Eh gata nan ma”.

    Tayi mgnar tana miƙawa Khausar wayar, cikin kwaɓe fuska kamar zatayi kuka ta amshi wayar tare da karawa a kunne murya ciki-ciki tace.

    “Njam ɓanɗu.

    Ina yini?”.

    Daga can kuwa cikin irin isa da kasaita ta tsofi masu iko Hajia Nana tace.

    “Lafiyata lau, ki shirya kuna gama jarrabawar jarabar taku ta bokoko a wutan zakizo nan Jauro yaya inada buƙatar ganinki”.

    Cikin sauri da alamun akwai zaunanniyar tsama a tsakaninsu tace.

    “Toh ai muna da hadda yanzuma da aka ƙara mana hutun, kuma zamuna zuwa leson”.

    A faɗace tace.

    “Leso mato nace leso mato, ita haddar mu nan ɗin ce miki akayi garin kafuraine, kizo liman Sadu zai baki duk ilimin da kikeso in dai na addinine, na kafurcine dai bamu dashi”.

    Cikin takaici tace.

    “Nifa ki dena kafurta mana ilimin mu”.

    Cike da mamaki da al’ajabi Hajja Nana tayi wani dogon salati, tare da sanar da Ubangiji wai itace tana mgn ana bata amsa, ita da mgnar ta take tamkar wahayi a cikin rugarsu kasancewarta itace babba.

    Da sauri ta katse kiran tare dasa wayar a Airplane mode,  ta kifeta gefenta sabida kada Mamynta ta gane.

     

    Cikin yin rau-rau da ido tace.

    “Mamy dan Allah kice mata tayi haƙuri sai ran babban sallah zanje muyi kwana biyu kafin a koma makaranta”.

     

    Da sauri Momy ta fara jujjuya mata kai tare da cewa.

    “Ban isaba Khausar ni dai kam bani da bakin yin taƙaddama da umarni Hajja Nana, ki kwana da sanin can zakije kiyi hutun nan, da kika samu ma bakije kinyi azumi a canba, tun tsawon shekaru takebi tana son hakan kuma bai samuba sabida uzurin da ita kanta ke fadarsa na zuwan ta Umara, bana kuma tace, saboda ke, bazata je Umrar ba, saboda tana so kije ki daɗe kisan yan uwanki su sanki.”

    Cikin jan dogon numfashi tace.

    “Mamy ni dai kin san ba shiri nakeyi da ita ba, ko zuwa nan tayi a wuni ɗaya sai tayi min masifa da sharri sama da sau biyar”.

    Cikin haɗe fuska Mamy tace.

    “Kuma dole kan umarnin ta da izininta mizanin muhallin zamanki  yake, ki fara shiri kawai ma in Allah ya kaimu gobe zan gayawa Abbanku, zuwa ranar jumma’a mai zuwa sai ki bisu in sunzo cin kasuwa kije RUGAR JAURO YAYAH tabbas d….!

     

     

     

    Littafin SAKAYYAH na kuɗine biya ki karanta cikin Salamah yar uwa.

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*