Author: Novels

  • Sakayyah 3

    Sakayyah 3

     

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 3_

     

    _NA_

    _AYSHA ALIYU GARKUWA_

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE*

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne kacal ƴar ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276*

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran su dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk jihar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida. Set ɗina akwai manya akwai ƙananan set akwai kuma na tsakiya, ƙananan set ɗin daga 40k 35k 30k 25k 20k 15k 10k shine ƙara ɗan cukulan haɗiba bana haɗin kasa da 10k sai kuma haɗin kwanon ƙasaitacciyar mace shi 8k set ɗin tsakiyan su da 50k 60k 70k 80k 90k ne manyan kuma daga 100k ne zuwa yadda zaki iya Hajia ta*

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

     

    Cikin sanyin jiki Khausar ta miƙe tsaye tare da juyawa a hankali ta bar falon Mommy ta wuce ɗakinsu.

     

    Ɗakin mai girmane wanda  ke ɗauke da matsakaici gado ƙiran Italian bed sai durowarsa dake gefe wanda ke ɗauke da ƙofa shida, daga kusurwan gabas babban TV plasma ne da DStv sai tattausan canis carpet pinch color dake shimfiɗe Atsakiyar ɗakin wanda shi ke ɗan rage musu masifeffen sayin tayis ɗin,

    komai na ɗakin pinch colour ne sai ɗan ratsin fari.

     

    Cikin jagulewar zuciya ta kwanta bisa gadon tare da lumshe manyan Idanunta dake cike da ruwan hawaye.

    Allah ya sani sam bata ƙaunar zuwa Jauro Yaya ko kaɗan, ya zame mata dole ta newa kanta mafita.

    Ɗan gajeren tsaki taja tare da mirginawa ta juya  tsakiyar gadon, kana ta lumshe idanunta, da wannan tunani bacci ya ɗauke ta…

     

    Cikin nutsuwarsa da kuma sanyinsa kamar koda yaushe yake tuƙa motar,  yayin da M Jameel ke gefen hagunsa kamar wanda akace ya dubi madubin dake gefensa se kuma yayi saurin kallon Moddibo dake Driving cike da mamaki  yace.

    “Kai A.J kaga kamar binmu akeyi fa ko?”.

    Kai Moddibo ya jinjina tare da ɗan yamutsa fuska anitse yace.

    “Eh binmu akeyi sai munje gidan Ummi zan tsaya”.

    Cikin sauri M Jameel ya juyo gareshi tare da ɗan ware idonsa yace.

    “Kama san ana binmu kuma shine ka ƙi tsayawa? Idan kuma wanda zasu cutar da mune fa A.J?”.

    Kai Moddibo ya girgiza yana mai cigaba da tuƙinsa tare da buɗe lips inshi a sanyaye yace.

    “Ai nasan wanda ke binmu fa Alhaji Bashir ne”.

    Da sauri M Jameel yace. “Waye Alh Bashir?”.

    Ɗan juyow Moddibo yayi tare da ɗan kallonshi  kafin yace.

    “Babban yaron Malam Arɗo ne”.

    Cikin sauƙe Numfashi M Jameel yace.

    “Ok to Meyesa ba zaka tsaya ba?”.

    Ba tare da ya juyo ba yace.

    “Nasan magana ce  mai yawa yazo dashi, koda na tsaya ma, ba zamu gama ba kuma kaga agefen titi muke baya ga hakama na masa signal ya fahimta”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare  da faɗin.

    “Ok shikenan”.

    Daga nan sukaci gaba da tafi.

     

    Suna isa ƙofar gidan Ummi M Jameel ya buɗe ƙofa ya fita dai-dai lokacin da Alh Bashir ya ƙara so fuskarsa ɗauke da murmushi ya miƙa wa Alh Bashir hannu sukayi musabaha cikin sakin fuska Alh Bashir yace.

    “M Jameel Ko?”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa mishi tare da cewa.

    “Ya gida ya iyalai ya kuma Baba Arɗo?”.

    Cikkn sakin fuska Alhj Bashi yace.

    “Duk Suna lafiya”.

    Murfin motar M Jameel ya buɗewa Alh Bashir tare da cewa.

    “Bismillah kashiga”,

     

    Sannan ya zagaya gefen da moddibo yake wanda har zuwa lokacin bai fito ba yace.

    “Bari nashiga ciki sai ka shigo”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa cikin yanayin sanyin magarsa yace.

    “Nima Ina Shigowa yanzu”.

    “To sai ka shigo”.

    Ya fadi tare da juyawa ya nufi cikin gida yashiga bakinsa ɗauke da sallama.

    Ba lefi madedecin gida ne mai kyau daga farkon gidan ze iya ɗaukan motoci biyu se tank na ruwa dake can gefe tsakar gidan shimfiɗe yake da interlock sai babban sashe guda ɗaya cikin gidan zagaye yake da fulawa wi masu kyau wanda keda alaƙa da Moddibo dan duk inda yake da dama sai ya ƙawatasa da fulawowi, sabida suna samishi farin ciki.

    Tsarin ginin yayi matuƙar kyau duk da cewa ba babba bane amma komai fess dashi haka zalika madedecin falon nasu da befiye girma ba yayi matuƙar kyau falon na ɗauke da manyan setin kujeru kalar ash da baƙi cai Centre table dake tsakiya da kuma ƙaton TV dake maƙale abango daga gabar da TV akwai ƙaton fanka bayan AC dake maƙale da bango daga yamma da TV zagaye yake da wasu flowes masu kyau da ɗaukar hankali sai tattausan carpet mai ɗan kare kyau dake malale a tsakiyar falon…

     

    Cike da so kulawa ƙauna irin ta uwa Ummi ta kalli Jameel dake shigowa tare da sakar masa da murmushin da bata san ya subce mata ba,

    bayan ta amsa sallama.

     

    Cike da farin ciki Asma’u ta miƙe tare da gyara wuyan abaya ɗan baby himar dake zage da  fuskarta da ɗauke da murmushi cike da jin daɗi ta rungume M Jameel da faɗin.

    “Oyoyo Yaya Jameel na Ina yini”.

    Kanta ya shafa cike da son yar uwar tasa yace.

    “Lafiya lau my blood ya karatu?”.

    Cikin murmushin ta amsa da.

    “Alhamdulillah”.

    kana ta zauna daga ƙasa kusa da ƙafafunsa,

    Ummu kuwa miƙewa tayi tana ɗan leƙan bayansa.

    Murmushi M Jameel yayi domin ya fahimci Moddibo take leƙawa ganin basu shigo tare ba.

    Cikin yanayin fara’arsa yace.

    “Kai Ummina ki bari mugaisa kafin ki tambayi ‘yan biyun nawa??”.

    Ka ta girgiza  tare da cewa.

    “A’a gwara in tambaya naji, domin shi yace na muku dambun couscous shiya keso kaga kuwa ai bazan ji daɗi ba in ban ganshi ba”.

    Murmushi M Jameel yayi yana mai jin daɗin yadda mahaifiyarsa ke nunawa amininsa ƙauna tamkar ita ta haifeshi, yana murmushi jin dadi yace.

    “To yana mota”.

    Da sauri ta sake dubansa tare da cewa.

    “To me yakeyi amota da bai shigo ba?”.

    Ashagwaɓe yace.

    “To Ummina mu gaisa mana”.

    Dawowa tayi ta zauna bisa kujera 2 str,

    shi kuwa M Jameel  zamewa ƙasa yayi zauna daɓas bisa carpet kana ya ɗaura kansa acinyarta murya a sanyaye yace.

    “Ummina daga shigowa ko gaisawa ba muyiba sannan baki samin albarka ba kika tsareni da tambayar Moddibo”.

    Hannunta ta ɗauka bisa tsakiyar kasan tare da  shafa kansa tana mai cewa.

    “Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwarku! Allah ya dafa muku acikin dukkan lamuranku!!

    Ubangiji ya tsareku daga sharrin abinƙi tsakanin mutum da aljan!!!

    Allah ya baku ‘ya’ya masu biyayya tamkar yadda kuke mana kaida Amininka”.

    Cike da tsananin jin dadi da sassayan salama yace.

    “Ameen thumma Ameen Yah Ummi”.

    Hannunta ta ɗan janye daga kansa tare da sake tambayar sa.

    “Ina Moddibo?”.

    Ƴar dariya mai sauti yayi tare da miƙewa ya zauna akusa da ita kasancewa kujeran 2sitter ne.

    gyara zamansa yayi yana fuskantar ta yace.

    “Moddibo zai shigo amma ba yanzu ba”.

    Da sauri tace.

    “Meyasa?”.

    Cikin saurin shima yace.

    “Bari dai in miki bayani hankalinki ya kwanta.

    Muna tahowa ne  Alh Bashir babban yaron Malam Arɗo ya biyo mu to suna mota suna tattaunawa.

    Nasan bazai wuce ƙorafi ya kawo akan mahaifinsu ba”.

    Tsaresa da ido Ummi tayi kana tace.

    “ƙorafi akan Babansu kuma?”.

    Kai ya jinjina tare da cewa.

    “Eh Ummi saboda Malam Arɗo wani irin mutum ne wanda zamuce  mai dukiyar lukudi gashi dai Allah ya bashi dukiya na ban mamaki amma babu wanda ya isa yaci wannan kuɗin kamar abin masifa”.

    Gyara zama Ummin tayi tare da cewa.

    “Ikon Allah to sabi da me?”.

    Numfashin M Jameel ya ɗan fesar tare da cewa.

    “Tun bayan rasuwar mahaifinsa abubuwan suka ƙazanta.

    Domin baya sauraron shawarar kowa koda kuwa ƙannensa ne domin shine babba acikinsu dan haka babu mai tanƙwarashi.

    To fa saidai Allah ya ɗaura masa son Moddibo a zuciyarsa duk abinda Moddibo yace ko kuma ya kawo shawara akai to zaiyi koda kuwa ransa baya so.

    Duk da wani lokaci zakiji yana yiwa Moddibon ma faɗa akan cewa zaisa shi kashe kuɗi amma koda ya gama surutun daga baya zakiga yayi abin da ya fadan.”

    Gyara zama M Jameel yayu tare daci gaba da cewa.

    “To fa wannan dalilin ne yasa muddin ‘ya’yansa suna buƙatar wani abu saidai su biyo ta hannunsa Moddibo”.

     

    Ka saƙe Ummi tayi tana kallon Jameel din kana cikin sanyin murya tace.

    “To kada fa hakan yasa yayi baƙin jini awajen ‘ya’yansa kasan ɗan adam”.

    Dariya M Jameel yayi kana yace.

    “Ummi me Moddibo zai buƙata awajen Malam Arɗo me zeyi da dukiyarsu? Mutumin da baiwa yayansa Bama me zai bawa Moddibo wanda baida shi”.

    Kai Ummi ta gyaɗa tare fesar da numfashi a sanyaye tace.

    “Hakane kam al’amarin Moddibo da Innayi akwai al’ajabi, domin ko nasan baza su taɓa  buƙatar wani abu awajensa ba, duk da kuwa anayi musu kallon basu da wani cikekken jigo acikin rayuwarsu.

    Amma kuma yanda suke tafiyar da rayuwarsu cikin tsari da hikima da wadata yana bani makaki”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da cewa.

    “Kinga Koda motar da Malam Arɗo ke hawa tsohuwa ce aƙalla zata kai shekaru ashirin da biyar ko ashirin da takwas amma har zuwa yau ya kasa can zawa, anyi-anyi dashi yaƙi duk yanda akayi dashi ya sauya wata yaƙi kuma kullum ciki bashi ciwon kai takeyi.

    har kyautar Mota ɗansa Alh Bashir ya bashi amma yaƙi amsa domin atunaninsa daga baya zai fanshe kuɗin sa.

    Ko gidansa da kike gani yanzu ga gini dai yayi mai kyau amma ɗakunan matansa kamar zauren haka suke babu kujeru bare wani abu shi Tv.

    Yanzu haka kwanan ake gyaran makarantarsa wanda da taimakon Moddibo akeyinsa kuma adalilinsa ne yake biyan Malamai albashi mai tsoka inba haka ba baki ɗaya makarantar ta koɗe sannan babu albashin kirki saboda Moddibo yanzu aka rushe makarantar ake gyarawa yanzu hutun da aka kara ma gani yake kamar za’a yi masa asara shiryasa yace adawo ko ba’a gama gininba to bayan an dawo yanzu dole aka sake komawa hutu saboda ba’a gama gyaranba yanzu ma cewa yayi dole kada a wuce wata ɗaya da ƙyar Moddibo ya lallaɓasa aka tafi hutun kafin adawo angama gini da kuma tsare tsare sa duk ya buwaye mu da cewa Moddibo na sashi kashe kudinsa”.

     

    Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da cewa.

    “Masha Allah shiko wannan wani irin mutum ne?”.

    Murmushi M Jameel yayi tare da cewa.

    “Ummi haka ‘ya’yansa ke fama dashi, kin san ku  fulani”.

    Murmushi Ummi  tayi tare dayi masa daƙuwa.

     

    Aɓangaren Moddibo kuwa.

    Zaune suke da Alh Bashir bayan sun gama gaisawa shiru na wasu daƙiƙu ya wanzu atsakaninsu kafin.

    Cikin kulawa Moddibo ya ɗan juyo ya kalli Alh Bashir cikin kulawa yace.

    “Alh ya akayi?”.

    Numfashin mai nauyi Alh Bashir ya sauƙe kana a hankali yace.

    “Mitsss  Moddibo Agaskiya al’amarin Babanmu  yana matuƙar ɗaure mana kai?”.

    Lumshe idanunsa yayi  kafin yace.

    “Meya faru!?”.

    Kai ya girgiza cikin yanayin damuwa yace.

    “Modobbo wallahi Mahaifiyata bata da lafiya, ance sai anfitar da ita waje, gashi duk cikin mu babu wanda yake da halin biya afita da itan.

    Kasan halin Babanmu kuma, duk iyakar iyawata yaƙi amincewa.

    Ni kuma bani dashi”.

    Cikin sanyi Moddibo yace.

    “Alh baka dashi kuma”.

    Kwaffa Alh Bashir yayi tare da cewa.

    “Wallahi Allah Moddibo wasu lokuta idan akace min Alh Bashir  ba ƙaramin ɓaci raina yake ba domin bafa mahaifina ne yabiya min Makka ba.

    Sannan ba nine na biyawa kaina ba dukiyata bace yasa naje ba.

    Dalilin Surukina naje wato mahaifin Matata fa ya biya min na samu naje duk wani abu da nake buƙata sai dai Inje wajensa wanda kuma hakan da kunya da kuma zubar da girma.

    amma mahaifina Allah ya hore masa fiye dana surkina amman bazai taimaka manaba ayanzu ga jinyar mahaifiyarmu dole sai anfitar da ita waje an mata dashen ƙoda.

    shi kansa yana ɓuƙatar canjin mota lokuta da dama yana tafiya Atsakiyar titi zakaga ta lalace, idan shi baya damuwa da zaginsa da akeyi a gari da rayuwarsa to mu muna buƙatarsa ba mason wani abu ya sameshi kuma bama jin dadin habaice-habaicen da akeyi mana.

    Shiyasa nazo wajen ka.

    Dan Allah da Manzonsa kayi masa magana ya kai mahaifiyarmu asibiti. Sannan ya canza motarsa bayan wannan akwai kannen mu mata da suka gama secondary akwai buƙatar su tafi jami’a amma yaƙi sasu domin aganinsa za’a cajesa kuɗi masu yawo dan Allah katemaka kayi masa magana akan waɗan nan abuvuwan”.

    Ya dire ayar mgnar da haɗe tafin hannunsa alamun roƙo da neman al’farma.

    Moddibo kuwa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da  buɗe idanunsa dake lumshe kana a hankali yace.

    “Insha Allah zanyi masa magana, amma ayanzu da ƙyar zai amince domin da mun zauna zance ɗaya yake nanata min wai na sashi kashe kuɗi amakaranta wai zan talautashi”.

    Murmushi mai ciwo Alh Bashir yayi tare da cewa.

    “Muma ko agida haka muke shan complain Koda kudin cefene da sauran abubuwa aka tambayesa zaice Ni bani da kudi  wannan yaron Moddibo duk yasa na kashe kuɗaɗenna aginin makaranta”.

    Murmushin gefen baki Moddibo yayi wanda ke ƙara fitar da ainihin kyawunsa cikin sanyi yace.

    “Uhufm Malam Arɗo kenan.

    Ba matsala Insha Allah zanyi magana dashi duk yadda mukayi dashi zakaji”.

    Ya kare mgnar yana shafa tattausan sajensa.

     

    Godiya Alh Bashir ya masa sannan su kayi sallama Moddibo yashiga cikin gida.

     

    Shi kuma ya juya ya tafi.

     

    Tattausan murmushi Ummi tayi ganin Moddibo cikin kulawa tace.

    “Babana na kaina sannu da zuwa”.

    Kasancewar sunan mahaifinta garesa.

    Cike da ladabi ya zauna yana cewa.

    “Ummi fatan mun same ku lafiya ya yara?”.

    Da murmushi afuskarta tace.

    “Duk muna lafiya ya jikin Innayi?”.

    “Alhamdulillah Ummi jiki kam da sauƙi  sosai ma”.

    Ya kare mgnar yana  mayar da kallonsa ga Asma’u data fito daga Bedroom da alama muryarsa taji ta fito, har ƙasa ta tsugunna tare da cewa.

    “Yah Moddibo ina yini”.

     

    “Lafiya Asma’u ya karatu da hadda?”.

     

    “Alhamdulillah”.

    Kai Ya jinjina tare da faɗin.

    “Meyesa yau bakije hadda ba?”.

    Kanta aƙasa tace.

    “Yah Moddibo bani da lafiya ne zazzaɓi ke damuna”.

    Kallonta yayi na daƙiƙu uku, kana yace.

    “Asmau kadafa ki biyewa wannan mashiririciyar ƙawar taki, ki dena harƙa da ita sam banason alaƙarta dake tsakaninku.

    Domin yarinyar bata ji kona misƙala zarratin, bana son ganinki tare da ita dan gaba ɗaya sunanta ya zagaye makarantar saboda rashinjinta sam bata da nutsuwar da za’ayi abota da ita.”

    Ita dai Asma’u kai take jinjina mishi.

    M Jameel kuwa ido ya zuba mishi yayinda Ummu kuwa ke murmushi.

    Shi kuwa Moddibo gyara zamansa yayi tare daci gaba da cewa.

    “Domin shin abota anaso ayi da na gari, bi ma’ana idan za kayi  abota kayi da mutum na gari domin kamar dai misalin:

    meyin abota da me saida turarene koda ba azata masa ƙamshi ba to baza azata masa wari ba, sannan misalin: mai abota dame zuga-zugi koda yana da haske to ba za’ayi masa zaton haske ba”.

    Ɗan kishingiɗan  M Jameel yayu tare da lumshe idanunsa.

    Shi kuwa Moddibo cikin nitsuwa yaci gaba da cewa.

    “Manzon Allah (S.A.W) ya kwaɗaitar damu da yin abota da mutanen ƙwarai domin abokin ƙwarai yana daga cikin wanda Allah yayi alƙawarin zai sasu acikin inuwar alarshinsa ranar tashin ƙiyama, amma kuma duk abotar da ba’agina sa saboda Allah da manzo ba to ƙarshensa nadama ce sam wannan FATTANAH bata dace da zama abokiya a garekiba”.

    Itade Asma’u kanta na ƙasa batare data ɗago ba tace.

    “Toh Yah Moddibo”.

     

    M Jameel dake kishin giɗe  idanunsa lumshe kuwa a hankali ya miƙe tare da buɗe idanunsa akan Moddibo dake cigaba da yiwa Asma’u nasiyya akan tarabu da Khausar cikin tsareshi da ido yace.

    “Wai dan Allah A.S meye haka?  kana tayiwa Asma’u huɗubar watsar da aminiyarta shin ita Khausar ɗin sheɗan ka ɗauketa  ko kuwa dujjal?”.

    Ɗago kai Moddibo yayi tare da tsuke fuska yana kallon M Jameel yace.

    “Kusan haka domin sam yarinyar bata da ɗabi’un kirki”.

    Kai M Jameel ya girgizi kana yace.

    “Haba Moddibo yarinyar nan tana fahimtar karatu duk wasu abubuwa da ake koyarwa tana ganewa fiye da duk yan ajinka,

    kawai rawan kai da ƙuruciya ke damunta, da zaran ta mallaki hankalinta zata dena, amma ka zauna kana ƙoƙarin cusa ƙiyayyarta azuciyar Aminiyarta sam hakan ba dai-dai bane yoh ba ita cema ke taimakawa ƙanwar taka da kake zugawarba ita me take ganewa ma tana nan kai kamar na kifi”.

    Itade Asma’u kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

     

    Wani kallo mai cike da manufofi Moddibo yayiwa M Jameel  tare da taɓe baki kana yace.

    “Ina ruwanka? bansa bakinka ba da Asma’u ƙanwata nake magana”

    Kana ya juyo ya kalli Asma’u da har zuwa lokacin kanta ke sunkuye yace.

    “Maganata kika ɗauka zakiyi amfani dashi ko nasa?”.

    Da sauri tace.

    “Naka Yah Moddibo”.

    Murmushi yayi da faɗin.

    “Ɗayyit Allah ya miki albarka”.

    Ɗago kai M Jameel yayi dai-dai lokacin Asma’u ta ɗago kanta,

    ido yakashe mata ita kuma murmushi ta sakar masa.

    Ummi dake sauraronsu kuwa sai yanzu tace.

    “Yawwa Moddibo ka cigaba da samun Ido akan yaran nan dan yaran saida sa ido”.

    Moddibo kuwa ido ya lumshe tare da gyaɗa kai kana yace.

    “Insha Allah Ummi na lura J da wannan fitinanniyar yarinyar kusan halinsu ɗaya shima kullum fama  nake dashi ya nutsu yaƙi nitsuwa”.

    Wara ido M Jameel yayi tare da cewa.

    “Nine bani da nutsuwar A.S?”.

    duk dariya suka sanya banda Moddibo da yayi murmushi.

     

    Abinci Ummi ta bawa Asma’u umarnin ta kawo musu fita tayi ba daɗewa ta dawo hannunta ɗauke da warmers ta ajiye musu M Jameel ne ya buɗe murmushi Moddibo ya saki yana kallon yanda dambun yayi kyau sai tashin ƙamshi albasa da kuma ƙamshin man shanu.

    Ummi da kanta ta zuba musu tare da mimmiƙa musu plate ɗin.

     

    Bismillah sukaui kafin suka fara ci suna kammala ci sukayi wa Ummi sallama sannan suka tafi.

     

    Washe gari. Tun wuri Khausar ta tashi amma taƙi shiryawa da wuri seda kowa ya gama shiri ya rage saura ita kaɗai, dan Allah ya sani ita ta tsani ta gama shiri ta tsaya jiran wasu.

    Ahankali take shan comflakes dake hannunta kamar ba jiranta akeyi ba yayin da Raudat ke zaune gefenta, Cikin fushi Amina ta banko labulen ɗakin cikin kumfar baki tace.

    “Wallahi Khausar zamu tafi in banda raini da samun waje tuntuni muke jiranki amma kin tsaya feleƙe dan kin san in mun tafi mun barki Abba zaiyi faɗa”.

    Anutse ta ɗago manyan Idanunta dake lumshe ta watsawa Amina wani kallo kafin ta taɓe bakinta kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa ta miƙe ta riƙo hannu Raudat suka fita bayan ta gama shanye Comflakes ɗin.

    Ajiyar zuciya Amina ta sauƙe cike da takaici tabi bayan Khausar da haramta, duk sanda tazo da niyyan ciwa yarinyar mutunci da zaran sun haɗa ido zata nemi duk wani karsashinta ta rasa koda suka shiga motar Amina bata tanka taba ita da Raudat keta faman surutu har suka isa cikin sa’a Moddibo beshiga ba zamansu ba daɗewa yashigo as usual cikin shigar jallabiya Onion color da yasha guga kansa sanye da hula malam taɓani kaji ruwan hadith yayin da ya naɗe da hirami jikinsa na fitar da ƙamashin daddaɗan tularensa,

    cike da ladabi suka shiga gaishesa Amsawa yayi kamar ko yaushe a saman laɓɓan sa.

     

    Taɓe baki Khausar tayi aranta tace.

    “Akwi madaran ƙasaita ana mutun kamar sarki”.

    Batare daya kallesu ba yace.

    “Su kawo hadda wiƙiƙi da ido Amina tashiga yi kasancewar itace afarko kuma bata iya ba ya dubi Samira sani yace ta karanta hadda still itama bata iyaba kallon Abeeda Sa’idu yayi yace ta karanta wacce ƙawar Samira Sani ce da ƙyar ta karanta aya biyar aciki sumunin da zasu karanta koda yazo kan Khausar cikin nutsuwa da ƙwarewa ta karato sumuni ɗaya na farkon Suratul Taubah.

    Kanshi ya jinjina tare da juyowa ya kalli Asma’u Ahmad.

    Cikin yanayin tsoro ta kawo suminin amman yayi mata gyara biyu.

     

    Da ɓacin rai Moddibo ya fitar da wanda basu karanta ba ya basu punishment.

    Khausar kuwa tasa su gaba ta riƙa dariya baƙin ciki ya cika musu zuciya kamar su mutu ahaka Malam Ahmad dake malamin Tajweed ne shima ya zuwa wurin addar.

    Har yayi ya gama basu dawo ba seda aka tashi kafin aka ƙyalesu akan punishment ɗin…

     

    Da dare.

    Mamy ce tsaye cikin ƙasaitacciyar shiga, tana zuwa wani irin ƙamshin kulaccar sirri da ta saya wurin Aysha Aliyu Garkuwa.

    Baki ta ɗan taɓe tana kallon yada Khausar ke shishita sabida uban yajin da ta zambadawa indomei wanda yaji nama da.

    Kai kawai ta jijjiga sannan tayi musu sallama ta wuce turakar mijinta.

    Tanaci tana kurɓar ruwan sanyi, tana bawa Raudat har suka gama ɗaukar Raudat tayi suka shiga ɗaki kai tsaye toilet suka wuce brush tayi sannan tayiwa Raudat kana suka ɗaura alwala suka fito.

    Jikin window Khausar ta nufa da niyyan rufewa Idanunta suka sauka akan Haiydar dake ɗauke da Ramadan zasu shiga sashen Hajiya Bunayya,

    fasa rufe window tayi cikin ɗan ɗaga murya tace.

    “Haiydar ina zakuje?”. shima cikin ɗaga murya yanda zataji yace.

    “inda kika aikemu”.

    Cikin takaici ta rumtse idonta kafin tace.

    “Wai Haiydar meyesa karai nani ba dama in maka magana, ko in baka umarni saika riƙa bani amsa kai tsaye”.

     

    Bakinshi ya taɓe tare sa fadin.

    “Acikin gida ma saiki riƙa tambayar ina zanje! Me zanyi? Me zanci? fisabilillah ni bani da ikon da zanyi abu da kaina koda Mamy bata Matsamin irin yanda kike min gsky na gaji”.

    Bai jira jin amsartaba ya wuce yashiga sashen Hajiya Bunayya,

    Aseeya yayar Amina na ganinsa ta saki murmushi tace.

    “Umma ga babanki yazo”.

    Cikin sauri Hajiya Bunayya ta fito hannunta ɗauke da glass cup na madara tana jujjugawa fuskarta da murmushi tace.

    “Gashi babana madaran shanu ne mai ɗumi”.

    Amsa yayi yana murmushi saboda yanayin sanyin dake garin yace.

    “Nagode Umma”.

    Jujjuya Glass Cup ɗin yayi kafin ya kai bakinsa da faɗin

    “Bismillahi”.

     

    Khausar  kuwa jingina bayanta da jikin bango tayi kafin ta ɗaga hannunta sama cikin raunin murya tace.

    “(Ya wadud³,Ya zul’arshil makin,ya fa’alillima yurid,As’aluka bi izzatil lati la yura,wa mulki kallazi la yuda)ya Allah katsare min ɗan uwana kada Hajiya Bunayya taci galaba wajen cutar dashi”.

    Kafin ta shafa ta kwanta lamo agado….

     

    A can side din kuma cikin mugun sauri Hajiya Bunayya ta riƙe hannunsa domin bokan daya basu maganin ya tabbatar musu da zaran anyi Bismillah laƙanin maganin ya karye,ta anshi Glass Cup ɗin da faɗin.

    “Bari mugani kode da zafi ne kada ka ƙone bakinka”.

    Kai ya girgizi tare da faɗin.

    “Ba zafi Umma”.

    miƙa masa ta sake yi amsa yayi ya sake kaiwa bakinsa da faɗin.

    “Bismillah”, saurin karɓa ta kuma yi tare da cewa.

    “Mugani kode sugar bai jibane”.

    Kai ya girgizi yace.

    “Kin san ba damu da zaƙiba Umma”.

    yaƙe tayi da faɗin.

    “bari dai na ƙaro maka sugar”.

    Ta faɗa tare da shigewa Bedroom duk aƙoƙarinta na ganin ta mantar dashi Bismillah ba jimawa ta fito ta sake miƙa masa tana jujjuyawa aranta tana addu’ar Allah yasa ya manta da Bismillah. Aseeya kuwa ikon Allah kawai take gani wajen mahaifiyarta ita kuwa Amina tasan komai domin ita ta karɓo maganin wurin boka Karƙuzu.

    Karɓan Glass Cup ɗin yayi yakai bakinsa kana yayi Bismillah yasha kallon Ramadan yayi yace.

    “Zaka sha?”.

    Kai Ramadan ya girgiza alamar a’a…

    Hajiya Bunayya kam ji tayi kamar ta haɗiye zuciya ta mutu ganin maganin data kashe maƙudan kuɗi wajen amsarsu aranta tace.

    “Shegen yaro mai ta ammalli da addu’a duk uwarsu ta koya musu yin addu’a akan ko wani irin abu afili kuwa murmushi tayi tace.

    “Babana sugan yayi?”.

    Kai ya gyaɗa mata sannan ya shanye bayan sun sake taɓa hirane ya mata seda safe ya fice…

     

    Washe gari da safe Ummi ta nufi gidansu Moddibo domin duba jikin Innayi bakinta ɗauke da sallama tashiga cikin gidan atsakar gida taci karo da Innayi dake faman gasa nama irin wanda ake yiwa masu jegon.

    Cikin sakin fuska Innayi ta mata sannu da zuwa, Murmushi Ummi tayi tare da zama ta gaisheta cike da ladabi tare da tambayarta ya jiki kana ta kama mata aikin suka gama.

    Bayan sun gama ne Moddibo da M Jameel suka dawo zama sukayi tare da gaisawa Ashagwaɓe M Jameel ya dubi Ummi yace.

    “Ummi bacci nakeji”.

    bai jira cewarta ba ya zame ya kwanta tare da ɗaura akansa a cinyarta

    Moddibo kuwa Hararansa yayi yace.

    “Kaidai ba zaka taɓa girma”.

    Tura baki M Jameel yayi  amma baice komaiba saboda baccin dake cinsa kwanciyarsa ba jimawa bacci ya ɗaukesa ganin lokaci na tafiya yasa Ummi tace. “Moddibo bani filo ka gani”.

    miƙewa yayi ba daɗewa ya fito hannunsa riƙe da pillow Ummi ta karɓa ta ɗaura kan M Jameel akai sannan ta yiwa innayi Sallama.

    Moddibo ya tafi mai data bayan sun hau kwalta Moddibo ya dubi Ummi cikin sanyin murya yace.

    “Dan Allah Ummi ki riƙa yiwa Asma’u faɗa ta daina ƙawance da wannan yarinyar sam bata da nutsuwa zata ɓata Asma’u da halayyarta na rashin nutsuwa yarinya nada naci in ba da gaske mukayi ba bazamu ci nasara ba da na lura ta shiga ranta koda na yiwa Asma’u magana kan tarabu da ita.

    Kuma naga kamar ba zata yiba anma idan ya zamana mu biyune muke mata faɗa zata ɗauka”.

    Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.

    “Insha Allahu zan riƙa yi mata”.

    Ahaka suka isa gida ya ajiyeta sannan ya koma…

     

     

    Washe gari. Ya kama Juma’a misalin ƙarfe uku Khausar na zune kan 2sitter Raudat na gefenta tana yanke mata ƙumba yayin da Mamy ke riƙe da hisnul Muslim tana Azkhar Asma’u tashigo bakinta ɗauke da sallama miƙewa Khausar tayi tare da rungumeta tace.

    “Oyoyo Ƙawar arziƙi”, Murmushi Asma’u tayi cikin sigar zolaya tace.

    “Fattanah kina son karya ni ko?”.

    Saketa Khausar tayi tare da tura ƙaramin bakinta tace.

    “Kina so mu ɓata ko?”, Murmushi Asma’u tayi tare da tsugunnawa har ƙasa ta gaisheda Momy cikin sakin fuska Momy ta amsa tana tambayarta Umminta ta bata amsa da.

    “Tana lafiya, Momy tace ma in gaidaki”.

    Cikin sakin fuska Momy tace.

    “Ina amsawa”.

    Ita kuwa  Asma’u cikin girmamawa tace.

    “Ayyah Momy in ba  abinda  Khausar zatayi miki ta rakani mana Ummi ta aikeni kuma banason zuwa ni kaɗai”.

    Sanin Asma’u yarinya ce me tarbiya da nutsuwa uwa uba kamun kai yasa Momy amincewa.

    Kai ta gyada mata tare da cewa.

    “Toh kada dai ku daɗe ku kuma kula da kanku banda kula maza”.

    Cikin jin dadi Asma’u tace.

    “In sha Allah kuwa Momy”.

    Ita kuwa Khausar murmushi tayi tare da cewa.

    “To ni baki nemi izinina ba”.

    Ta ƙare mgnar tana

    Shiga Bedroom ɗin ta, murmushin Asma’u tayi tare da bin bayanta kana ta langwaɓar da kai tace.

    “Ayimin afuwa ƙawar arziƙi”.

    Hira suka ɗan fara taɓa sannan Asma’u ke sanarwa mata zata raka unguwar Teku ta kai saƙo Ummi ta aiko cikin zumuɗi da son fita ta  miƙe tare da ɗaukan dogon hijab maroon colour tasa akan riga da wondon dake jikinta ba tare data tambayi inda zata jeba tace su tafi dan kawai tana masifar son unguwar Teku…

     

    Aɓangaren Moddibo kuwa bayan ya dawo daga sallar la”asar,

    Side ɗinsa ya wuce,

    Ruwa ya watsa tare da sauya kayan jikinsa, wani tattausan riga da wondo nevy blue  mai taushi ya zira,  tare da fesa turarensa oud jannah mai masifar ƙamshi,

    System ɗinsa da wayarsa ya ɗauka kana ya fito, a hankali ya lumshe idanunsa jin yadda sassanyar iskar ke ratsa cikin tattausan sumar kansa da yana iya kwana biyu bai cire hulaba.

    A hankali yake taka steps din yana sauƙowa ƙasa  wani irin masifeffen kyau yayi collor kayan jikinsa yayi matuƙar amsarsa farar fatarsa ta ƙara bayyana, yayinda tattausan sajensa yayi lib-lib gwanin burgewa jajayen lips ɗinsa dake cikin zagayen sajensa da kota million ɗinsa sai sheƙi sukeyi, a hankali yake taka tattausan silifas dake sawunsa.

    ya nufi can gefen yamma inda wasu kyawawan bukoki na zamani da yake wajen hutuwansa,

    Wurine mai kyau da ban sha’awa a hankali ya zauna bisa ɗaya daga kujerin dake cikin bukkar da tafi sauran ƙawayuwa da flawers.

    A hankali yake motsa lips ɗinsa alamun  yana tasbihi   yalwataccen sumar kansa kamar na larabawa na sheƙi da ɗaukar ido idanunsa na lumshe yana motsa bakinsa a hankali.

     

     

    Cikin nutsuwa Asma’u da Khausar suka fito duk da rawan kai irin na Khausar komai nata anitse takeyi cikin nutsuwa suke tafiya yayinda hijabansu yarufe har takalmansu adedeta suka tara tare da sanar dasu inda ze kaisu.

    Tafiyar Mintuna ashirin da biyar sukayi suka isa aƙofar gidan.

    A gaban gate ɗin adedeta ya ajiyesu.

     

    Asma’u ce agaba tasa hannunta da babu komai ta tura ƙofan gate ɗin yayin da ɗaya hannu ke riƙe da Kula wanda Ummi ta yiwa Innayi dambun naman kaza.

    Cikin wani irin shauƙi Khausar ke bin ilahirin gidan da kallo ganin yanda flowes da shuke shuken kayan marmari suka zagaye gidan tamkar garden,

    Da sauri  ta juyo da kallonta kan Asma’u tare da cewa.

    “Wooow masha Allah.

    Kai Asma’u wannan gidan waye haka? gaskiya yayi kyau sosai”.

    ta ƙare mgnar tana lumshe idanunta tare da shaƙar sassayan iskar dake haɗe da ƙamshi flawers da kuma turare jikin Moddibo.

    Kana ta riƙa bin fulawowin tana shafa duk wanda hannunta ya sauƙa akai saita tsinke takai hancinta kana taja dogon numfashi tare da lumshe ido.

     

    Shi kuwa Moddibo tun ƙarar buɗe gate ɗin da yayi ya ɗago kansa yana kallon wajen.

    Cikin mamaki yace

    “Khausar Usman Lelelwal a gidan nan”.

    Hannunsa yasa ya tallabe habarsa tare tsuke fuskarsa.

    Ita kuwa Khausar cike da shauki ta buɗe hannunta tare da jujjuyawa har hijabinta na buɗuwa cikin ɗan ɗaga sauti tace.

     

    “Agaski Asma’u gidan nan ya min komai na ciki sun burgeni gawani irin ƙamshi da suke, ji yanda ilahirin gidan ke fitar da wani ni’imantaccen ƙamshi.

    Gaskiya gidan nan shine aljannar duniya da alamu kuma mutanen ciki maƙurane wajen tsabta ina son komai na gidan nan”.

    Asma’u Kam dariyar dake cinta take ƙunshewa ta tabbata da Khausar tasan cewa gidansu Moddibo ne babu dalilin dazai kawota sannan ta tabbata yau juma’a ya irin wannan lokacin Moddibo na gida babu inda zeje.

     

    Ita kuwa Khausar juyi ta cigaba da yi tare da sauri ta nufi side din Moddibo steps din ta fara tattaunawa tana shafa furannin dake jere a kan.

    Saida ta hau har tsakiyar barandar kana ta juyo ta fuskanci yama.

    “Wooww Masha Allah Asma’u zo ki hau ki gani wlh ina hango bakin Teku kinga yadda ruwa da tsuntsaye keyi!”.

     

    Ita dai Asma’u hannunta tasa ta rufe bakinta  tana murmushi.

    Yayinda tun shigowarsu Moddibo ya zuba musu idanu saidai sam su basu lura dashi ba,da gudu Khausar ta juya ta fara taka steps din tana sauƙa ta nufi sashen da Moddibo ke zaune tana faɗin.

    “Wowww gaskiya wannan gidan yayi mugun yimin kyau da ace zan rayu a ciki da wanda raina zaiso zan meda mishi gidan tamkar dausayin farin cikin duniya”.

    Cikin danne dariya Asmau tace.

    “Khausar zomu tafi mana”.

    kai Khausar ta girgiza tace.

    “A’a ki tafi ni wlh saina cire inabin can da Appel  kije kawai”.

    Ahankali Asma’u tace.

    “Kizo muje mugaida Innayi sai mu gaya mata kafin ki cire”.

    dan tasan a irin wannan lokacin tabbas Moddibo na nan shiyasa take mgn a hankali wai dan kar ya jisu.

    Kai Asma’u ta dafe tare da cewa.

    “Idan masu gidan kuma suka zo suka sameki fa?”.

    Taɓe baki Khausar tayi tace.

    “Gida kamar wannan masushi bazasuyi rowa ba, kuma ai nan kamar  babu kowa babu wanda zaizo”.

    ta faɗa tana komawa inda inabi yake tasa hannu ta fara tsinka tana tsalle jin hijabinta zai takurata ne yasa ta zare hijabin tare da ajiyeshi kan kujerar dake ƙasan bishiyar.

    Middibo kuwa dafe kunci yayi yana ganin ikon Allah Aransa yace.

    “Yarinya kamar ba mace ba dubi yanda take tsalle kamar biri wannan ba budurciba abinda yafi budurcima zata watsar domin yasan illar hawa bishiya yakan buɗa mace duk da cewa ita ba hawan tayi ba.

    Tunaninsa ne yakatse asanda ta nufi bishiyar Appel tsalle tayi da niyyar tsinkowa dan bishiyar Appel irin yan masaƙaitan nanne,

    tsalle ta kuma yi amman ta kasa ga dai  hannunta na taɓawa sede baza ta iya tsinka ba.

    tattare gashinta tayi tare da dan mai dashi bayan wuyanta kana ta nannaɗe ƙafar wandonta,

    tsalle tayi tare da kamo rashen da yafi kusa,

    sai kuma ta hango wasu a can sama haka yasa ta fara taka jikin bishiyar har ta hau bisa rashen duk da ba wani tsowone da shiba,

    Cal sai gata akan bishiyar.

     

    Cikin tsananin takaici da sassarfa ya mike tare da nufar wajen, yasan koda yace zeyi mata tsawa muryarsa baze fita ba saboda bashida da amo mai karfi sannan yasan dai baya cikin tarbiyya mai.kyau ƴa mace tai ta hawe-haween bishi yana isa bakin bishiyar ya tsaya tare da harɗe hannayensa aƙirji kafin yayi magana ta juyo da niyyar kai hannu zata tsinki appel sukayi ido huɗu dashi ido cikin ido sukayi kamar yadda damisa kan iya tsare kenwa da ido haka yayi mata.

     

    Cikin tsananin firgici da tsoro da kaduwa tace.

    “Hasbunallahu wani’imal wakin,

    Aizubillahi Minal shaiɗanirrajim, innahu min sulaimanu wa innahu Bismillahir rahmanir rahim”.

    Cikin tsananin tsoro take jera addu’o’in domin gani take shin fatalwane ko kuma aljan yazo mata asuffarsa cikin kiɗima da firgici ta rikito tayi ƙasa ta faɗo gababsa yayin da hannayenta suka sauƙa akan…..!

     

     

     

     

    Kada dai ku shagala wannan duk garaɓasar FREE PAGE. Labarin sashi-sashi gareshi. Ko wacce kusufa da darasin dake ƙunshe a ciki. Al’amarin babbane fa babu abinda babu cikin lbrin

     

    Inada lbri na musamman

    Wanda nake son in rubuta in Allah yaso ya yarda ya bani aron rai da lfy da dama.

    In na gama TUBALI.

    Zafin labarin kan sani inji Tamkar in aje TUBALI na fara wancan ɗin

    *SAKAYYAH*

     

    lbri ne mai cike da abubuwa na musamman masu tarin rikitarwa al’ajami matsalar kasarmu kalubale masautu.

    Taraddadin rayuwa, tsaka mai wuya, tsubucewar dama da samunta,

    Nesanta da kusanta, tausayi, kuka, dariya, barkwamci, iko, isa, mallaka, kasaita, kekkyawan ilimin addini, da aiki dashi, fasadi, zalumci, shirka da sakamonta, kalubalen dalibai ga Malami, matsalar , yadda ya kamata gomnati da jami’an tsaro da masarautun gargajiya su juyo kam lamarin bindiga Dadi Zazzafar soyayya mai kekkyawan tubalin raino a ɓoye!!!.

    Ya Salam Labarin ya rusa min tunanin da nake cewa bazan sake wani littafi Mai kamar GARKUWA ba sai gashi  in second’s Allah ya buda min tunanin na harhaɗo Labarin *SAKAYYAH. FATTANAH kenan.*

     

    Amman sai dai kuwa kusan wani Abu!??!

    In kuna son sani ku biya 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In kin biya kikuma bibiyeni zakusha al’ajab.

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 6

    Sakayyah 6

     

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 6_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE*

     

     

    *LITTAFIN SAKAYYAH na kuɗine, wannan Free page ne, ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA. Sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP

    09097853276.

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

    Akwai daya bangaren wato *KAMSHI*

    Kimarki gyaranki da kamshinki. Matan da suka gane suka san yanda za su kankaro da mutunci su ne masu amfani da kayan gyara da kuma sanyaya jikinsu da kamshi, ina da turaren wanka da na bandaki na daki na jiki da na kaya dana tsuguno kamshin turarena na dabam ne mai sanyaya zuciyar wanda ya shaka ina da kayan kamshi na amarya da na maijego da na uwargida da dukkan macen da take kokarin mayar da kanta mai daraja a idon kowa ta zamo sarauni a idon mijinta, akwai shu’umar humra, sayan na gari maida kuɗi gida, banda karanta yayin gyara Hajia.

     

    Zaku iya samun kayyakina a duk garin da kike, zakiyi min mgn ta whatsApp number na 09097853276 domin yin zaɓinki, ko karin bayani, zaki tura kuɗin ta account na 0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU in mun gama mgna zan sa miki kaya a mota yazo duk garin da kike, in baki shirya saya yanzuba Please kada mu wahal da juna ki bari sai kin shirya kafin kiyi min mgn.

     

    🤝🏻🥰😘 Daga taku AYSHA ALIYU GARKUWA

    *(GARKUWAR MA’AURATA)*

     

     

    Cike da mamaki Sadik ke kallon yanda take ta tsar Nonon cike da tsantsar ƙwarewa da rashin tsoro.

    Fuskarsa ɗauke da murmushi ya juya ya kalli Baffa Jauro kafin yace.

    “Ikon Allah Baffa kalli yanda  take tatsan”.

    Murmushi Baffa Jauro yayi yace.

    “Ai ‘yar na gadana tafi ‘yar na koya gadonta ne fa abune da ajinin mu yake in Bata iya ba ai sai muce ba tsatson mu bace”.

     

    Ita kuwa khausar murmushi tayi ita da kanta tana mamakin yanda ta riƙe bakin Nonon shanun tana tatsa Shar-shar kawai Nono mai ɗumi yana zubowa.

    Ƙwayar dake cinyarta ne ya cika Dije ta janye ta sake sanya mata wani cike da shauƙi da kuma jin daɗi take cigaba da ta tsar Nonon kamar wacce tunda canma ta iya.

    Baffa Jauro na murmushi ya janye ƙwarya ta biyu ya sake saka mata wani yana murmushi yace.

    “Zan kaiwa Addah Hajja Nonon da kika tatsa da hannunki”.

    Murmushi kawai tayi yayin da Sadik da Dije ke cigaba da mamakin ƙwarewarta.

    Bayan ta tatso na ƙarshe ne Baffa Jauro yace.

    “Kusha toh”.

     

    Ita kuwa khausar ɗaga ƙwaryan tayi ta kai bakinta sai kuma ta cire kana ta mayar da kallonta kan Baffa Jauro tace.

    “Nikam bazan iya sha ba suga ba”.

    Murmushi Baffa Jauro yayi tare da buɗe tandu duma dake hannunsa wanda ke ɗauke da zuma ya zuba mata aciki kana yace.

    “Toh kusha”.

     

    Kai Khausar ta gyaɗa masa sannan takai ƙwaryar ɗanyen madaran mai ɗumi bakinta tasha sosai tana lumshe Idanunta kafin ta miƙawa Sadik yasha kana ya bawa Dije sauran.

    Bayan sun shanye suka ɗauko hanyar komawa gida.

     

    Khausar ta ɗaga Kaita kalli gefen damanta inda taji muryar Yaya Abba, ta hango Yaya Abba da Sule yayan Dije da take bi zaune acikin shagon caji da kuma  kati wanda duk lokacin da Yaya Abba ya koma makaranta Sule ke zama ashagon kallon Sadik da Dije Khausar tayi tace.

    “Ayyah mu biya ta wajen Yaya Abba mu gaisa”.

    “Toh”

    Suka ce sannan suka nufi shagon kana suka gaisa.

     

    Kallon Khausar Yaya Abba yayi yace.

    “Khausar kisan yanda zaki zauna da Goggon mu kar kinayi mata gautsin baki ba daɗi gsky”.

     

    Khausar kuwa jin abinda Yaya Abba yace yasa ta taɓe baki kafin tace.

    “Ni gaba ɗaya haushin matar nan nakeji idan ita bata sani ba ita tasa na tsani zuwa Rugar nan ba abinda yake ban haushi da Rugar nan kamar rashin wuta,Jiya duhu kamar zai kashe mutane sannan gashi ta ajiye Kuliya aɗakinta baki ɗaya garin ba daɗi wallahi”.

    Ta ƙarashe tana mai ya mutse fuska.

     

    Murmushi Abba yayi yace.

    “Shine kenan matsalar duhu na damunki!?”.

    Kai ta gyaɗa masa kai da faɗin.

    “Eh”.

    Yace.

    “Shikenan toh za’a haɗa wutan Gen.ɗin nan dana ɗakinta shikenan ko?, Saboda kar kuna samun matsala atsakaninku bakisan yanda take son Babanki ba kema kullum zakiji tana maganarki amma ta shedeki cewa kina da gautsin baki ke ba irin Nanne data raina bace kinga su suna mata biyayya duk abinda take so”.

     

    Kallon sa Khausar tayi kafin tace.

    “Toh sude sunga zasu iya ne wannan ai mulkin mallaka takeyi mutum bashi da ‘yancin yin abu saida izininta, kuma batun wuta nifa ba kwana zanyi a gidanta ba tunda naga kuliyoyi take kiwatawa”.

    Kusan a tare Sadik da Dije suka haɗa baki wajen cewa.

    “Ki daure ki riƙa yin abinda takeso zaku shirya”.

     

    Shiru kawai ta musu amma bata tunanin yin haka hira suka sake taɓawa kana daga bisani sukayi wa Yaya Abba sallama sannan suka shiga cikin gida…

     

    Akwana atashi ba wuya yau kwanakin Khausar Biyar acikin Rugar Jauro Yaya ta fara sabawa da mutanen garin Sosai Musamman ma Dije ta sun zama ƙawaye dan agidansu take kwana ita da zuwa gidan Hajja Nana sai da safe take zuwa tayi mata shara sannan duk lokacin da sukaje sukayi tatsa zasu kai mata Nono.

    Kasancewar duk gidajen ƙannenta taran ne ko yaushe sukayi tatsa zasu kai mata madara Shiyasa koda duk Rugar za’a rasa Madara da zuma ba’a rasawa a wurinta.

     

    Kullum da rana gidan Hajja Nana Khausar ke zuwa cin abinci saboda anan ne zata zaɓi wanda ranta keso duk sanda ta zata buɗe kwanikan ta zaɓi wanda ranta keso Hajja Nana za tace ba tasa son ƙaƙale duk wanda ta fara buɗewa shi zata ci ita kuwa khausar tace bataji abunta haka ba domin Hajja Nana ta kasance irin tsofi nan masu sa ido bata gani sai ta tanka to kullum cikin faɗa suke  ko yaushe Dije na maƙale da Khausar sosai Shaƙuwa ya sake shiga tsakaninsu sai kuma Ma’u yar bappa Garga sai dai ita bata karisasu girmaba,

    sannan sosai take walwala domin garin ya mata daɗi sai dai kullum cikin kewar Mahaifiyarta da kuma ƙannenta take .

     

    Washe gari, da safe Khausar na zaune gefen Hajja Nana tana matsa mata ƙafa.

    Hajja Nana tayi saurin janye ƙafarta azabure tana watsawa Khausar kallon banza azafafe tace.

    “Idan ba zaki matsa min ƙafarba aise ki bari bawai kizo kina min mugunta ba”.

     

    Sheƙeƙe Khausar ke Kallonta da mamaki.

    Ta janye hannunta daga kan ƙafar Hajja Nana tace.

    “Ashe abin arziƙi yana zama na tsiya daga temako sai kiyi min ƙazafi”.

    Kallon Banza Hajja Nana ta warsa mata kafin tace.

    “Saboda baki da kunya nice zanyi miki ƙazafin?”.

     

    Khausar data buɗe baki da niyyar magana ta fasa jin Sallamar Yaya Abba zama yayi tare da gaishe da Hajja Nana cike da ladabi Amsawa tayi tana sanya masa albarka.

    Kallonsa Khausar tayi tace.

    “Good Morning Yaya Abba”.

    Da murmushi afuskarsa yace.

    “Morning Khausar how was your night?”.

    “Fine”. Tace tana ɗan murmushin tsokana tasan kwanan zance,

    Ai kuwa taɓe baki Hajja Nana tayi tace.

    “Wato Abba ƙafara koyon munafurci irin na baƙaƙen kafuran nan ko kazo har gaba kana zagina?”.

     

    Kai Yaya Abba ya girgiza yace.

    “Wallahi ba munafurci ko zagi muke ba Goggo Hajja kawai gaisawa muke”.

    Ta gyaɗa kai tace.

    “Toh adai dinga magana da yaren da zanji dan Manzon Allah (S.A.W)Yayi Hani da idan mutane na zaune wasu daga ciki su sauya harshe zuwa wanda sauran basaji koda ba zaginsu zasuyi ba amma wanda baijin Yaren zai tsargu dan haka ku kula hegiya gantalelliya mai kaɗifiri”.

     

    Kai Yaya Abba ya gyaɗa cike da ladabi yace.

    “Insha Allah zamu kiyaye”.

    Ita kuwa khausar baki ta taɓe aranta tace wannan tsohuwa ta fiye mita da takalan magana. Ta fara da fadin Manzon Allah a karshe kuma ta buge da masifa da cemin gantalelliya.

     

    Azahiri kuwa sai ta saki fursakarta ta matsa kusa da yaya Abba tace.

    “Ayyah Yaya Abba ka sammin wayarka zan kira Mommy na mugaisa”.

    Juyowa yayi ya kalleta tare da cewa.

    “Ok ba matsala anjima zan baki sai Khadijah ta rakaki bishiyar ƙare zancen ka kuyi magana”.

    Cikin jin dadi tace.

    “Toh shikenan Nagode”.

    Sallama yayi musu kana ya tafi.

     

    Da yammaci Khausar na zaune adakali Dije kuma na shara suna hira sai da ta kammala sharan Khausar ta dube tace.

    “Dije muje ki rakini wajen Yaya Abba in karɓi wayarsa”.

    Kai Dije ta gyaɗa da faɗin.

    “Toh”,sannan suka fice suna hira har suka isa.

     

    Yaya Abba kuwa yana ganinsu ya miƙe tare da zuwa kusa dasu Idanunsa akan Khausar yace.

    “Kinzo”.

    Kai ta gyaɗa alamar eh.

    Yace.

    “Ok mutafi nima zanje taya ƙanina Ibrahim ɗiban ƙwai”.

    Ɗan murmushi tayi tare da faɗin.

    “Yaya Abba kaima kana aikin?”.

    “Sosai ma aikin gado ne ai duk da cewa ina shirin kammala degree na acikin Ɓadamaya bazai hana nayi aikin gadona ba”.

    Cewar Abba

    Kai ta jinjina kana tace.

    “Allah yataimaka”.

    Ya amsa da.

    “Ameen”.

    Suna isa Gindin bishiyar Khausar ta juya ta kalli Dije tace.

    “Dole sai na hau bishiyar network zai zo”.

    Dije ta girgiza kai tace.

    “A’a ko kan duwatsun nan  kika zauna zaki samu network inde ba’a cika ba abinda yasa wasu ke hawa bishiyar saboda kafin su zo duk an cika saman duwatsun idan kasamu ancika dole sai kan bishiyar”.

     

    Kai ta gyaɗa kafin ta ƙarasa ainihin inda ƙarƙashin bishiyar yake Sadik ta gani zaune yana waya.

    Murmushi ta sakar masa tare da zama gefensa sannan ta sanya number Mommy. ringing ɗaya ana biyu Mommy tayi picking.

     

    Ita kuwa khausar cike da zumuɗin jin Mommy tayi picking call ɗin tace.

    “Mommy na”.

    Aɓangaren Mommy kuwa jin Muryar Khausar yasa ta saki murmushi mai sanyi kafin tace.

    “Khausar”.

    Murmushi mai nuni da zallan farin ciki Khausar tayi tace.

    “Na’am Mommy na nayi missing ɗinki”.

     

    “Nima nayi missing ɗinki Mamana”.

    Dariya Khausar tayi tace.

    ”Mommy Ina Raudat?,Ina Haiydar?, Ina Ramadan??”.

    Murmushi Mommy tayi tace.

    “Duk suna lafiya”.

    Haiydar dake gefen Mommy yace.

    “Gani nan Maman Fitina nayi missing ɗinki tunda kika tafi babu mai min faɗa babu wanda zai ce na renasa sannan babu mai nuna min iko da mulkin mallaka”.

     

    Dariya Khausar tayi tace.

    “Hmmm ai nagane ɗan uwa ko ina nuna maka iko da mulkin mallaka gada nayi in faɗa maka na samu wacce ta cuna Ni komai da ƙa’ida akeyi ko kallo zakayi sai an maka tsarin kallon da zaka yiwa mutum shi”.

     

    Murmushi Haiydar yayi yace.

    “Allah Hajja Nana ko?”.

    Dariya tayi tace.

    “Ita dai fitinanniyar tsohuwa, tsohuwa sai Bala’i ba’a zaman lafiya da ita”.

     

    Mommy dake gefe ta amshi wayar da faɗin.

    “Um,Um Khausar karfa ta jiki”.

    Murmushi Khausar tayi tace.

    “Toh idan ta jini ma ya ta iya dani bare ma tana can gida mun barta tana gyaɗa kai muku ma munzo wajen bishiyar ƙare zancenka ne ko surutunka ne ohon musu!”.

     

    Haiydar ne yayi Dariya kasancewar wayar a speaker yake yana jin komai yace.

    “Wani irin bishiya ne kuma ƙare zencen ka”.

     

    Ita kuwa khausar cewa tayi.

    “Hmm garin fa basu da network sai wajen bishiya ɗaya suke zuwa yanzu ma haka wurin bishiyar nake”.

     

    Dariya Haiydar yayi yace.

    “Ai dama kin iya ɗale-ɗalen bishiya kina nan kamar Biri”.

    Murmushi tayi sai kuma ta ɓata fuska tace.

    Ni sa’arkace za kace ina tsalle kamar Biri??”.

     

    Murmushi tare da faɗin.

    “Addah Khausar Sarkin son girma kiyi haƙuri to yar uwa”.

    sakin murmushi tayi kafin tace.

    “Bawa Ramadan”.

    Miƙa masa Haiydar yayi.

    Ramadan yace.

    “Addah Khausi nayi kewarki”.

    Cike da ƙaunar ƙannen nata tace.

    “Nima nayi kewarka ɗan ƙanina Insha Allah na kusa dawowa”.

    Amsar wayar Mommy tayi tace.

    “Kin Kusa dawowa haka kukayi da Hajja Nana nan?”.

     

    fuska ta ya mutsa kana tace.

    “Sai munyi da ita Mommy yau kwanana biyarfa ana shida nake idan nayi sati biyu zan dawo ai”.

    Mommy tayi murmushi tace.

    “Tsakaninku de ni yanzu ba ruwana nima ba bari na tayi ba”.

    Dariya Khausar tayi tace.

    “Ina Raudat? Su Ramadan na zuwa hadda ko?”.

     

    Kai Mommy ta gyaɗa tace.

    “Ai Asma’u ma tazo tace malamai nata tambayarki sunce taya zakiyi tafiya baki sanar musu ba kodan ba boko ne sai hadda ne kawai wato?”.

     

    Girarta ta ɗan shafa da yatsarta manuniya kana tace.

    “Hmmm ai kuwa na faɗawa Asma’u ta sanar musu wataƙil ta manta ne”

    “To ai yanzu kam sai in kin dawo.

    Ki dai bi tsohuwar ahankali saboda ki samu tabarki ki dawo akan lokaci”.

    Cewar Mommy.

    Itako Khausar kai ta gyaɗa  kafin tace.

    “Toh shikenan Mommy na zanyi duk yanda kika ce. Yawwa Mommy ki turo min Number Ummin Asma’u”.

    ”Toh”Mommy tace sannan ta katse kiran.

    Ita kuwa Khausar juyawa tayi tare da kallon yaya Abba dake tsaye ta langwaɓar da kai kafin tace.

    “Ayyah Yaya Abba in ƙara Kiran wata ƙawata?”.

    Kai ya gyaɗa kana yace.

    “Ki kira ba matsala”.

    “Toh”,

    tace tare da maida kallonta kan wayar da text ɗin Number ya shigo copy tayi tare da dearling.

     

    Tana kira ringing ɗaya Ummi ta ɗauka.

    Khausar tace.

    “Ummina”.

    Murmushi Ummi tayi tace.

    “A’a Khausar kece? Ya mutanen Ruga fatan kun same su lafiya?”.

     

    “Lafiya lau Ummi. Ina Asma’u”. Cewar Khausar

     

    “Gata nan tana tsifa”. Ummi ta faɗa tare da miƙa wa Asma’u wayar.

     

    Asma’u na amsar wayar ta maƙala akunnenta tare da ƙyalƙyalewa da dariya tace.

    “Na sani”.

    Ita kuwa Khausar hararan wayar tayi jin Dariyar da Asma’u keyi tace.

    “Kinsan me?”.

    Asma’u tace.

    “Na sani tsoron Yah Moddibo kike yasa kika gudu kika tafi Rugar nan inba haka ba keda baki ƙaunar tafiyar nan amma daga arba dashi kika tafi Ruga”.

     

    Ƙwafa Khausar tayi tace.

    “Ba dole in tafiba tunda kika kaini kafin in dawo wala Allah ya huce”.

    Cike da zolaya Asma’u tace.

    “Wai ai Yah Moddibo baya mantuwa duk abinda aka masa”.

    Wara ido Khausar tayi sai kuma tace.

    “Asma’u duk kece kika janyo min da baki kaini gidansu ba da haka bai faru ba wlh”.

     

    Asma’u kuwa murmushi ya subce mata  kafin tace.

    “Calm down wasa nake Miki shi idan abu ya wuce kwana uku ma wata ƙil mancewa”.

    Ita kuwa khausar jin haka yasa ta saki ajiyar zuciya da faɗin.

    “Alhamdulillah”. Sai kuma ta harari wayar tare da cewa.

    “Au wata ƙil nema kenan”.

    Dariya Asma’u tayi kana tace.

    “Yaushe zaki dawo?”

    Taɓe baki Khausar tayi tace.

    “Waya sanma wannan tsohuwar wataƙila nan da sati biyu ko kuma sati ɗaya idan nayi sa’a tabarni in dawo anata wuceni ahadda ko?”.

     

    Da sauri Asma’u  tace.

    “Eh ana wuce ki kam”.

    Ita kuwa Khausar ɗan jim taui kafin tace.

    “Insha Allah nima dai na kusa dawowa”.

    “Toh Allah yasa”. Asma’u ta faɗa kana sukayi Sallama tare da katse kiran.

     

    Kallon Khausar yaya Abba yayi yace.

    “Koda kuna hutun ana baku hadda ne?”.

    Kai ta gyaɗa da faɗin.

    “Eh Yaya Abba muna zuwa hadda”.

     

    “To ai babu matsala inde hadda ne ki riƙa zuwa wajen Babanmu yana ƙara miki ai zai baki hadda ki cigaba kada awuceki”.

    Cewar Abba.

    Khausar kuwa cike da farin ciki tace.

    “Toh shikenan Yaya Abba insha Allah kuwa”.

    Daga haka suka miƙe suka taho kai tsaye gidansu Abba suka nufa bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga.

     

    Kallon Dije da Ibrahim Yaya Abba yayi yace.

    “Bari na rakata wajen Liman”.

    Kai suka gyaɗa sannan yayiwa Khausar jagora zuwa ɗakin Mahaifinsa bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga ɗakin.

    Ɗaki ne irin na bukka mai shatin kwabo baki ɗaya ɗakin kewaye yake  da littattafan Addini kana da qura’anai bugu da ban bugun misira da warash.

    Cike da ladibi Khausar ta gaishesa Amsawa yayi cikin sakin fuska kafin ya kalleta da murmushi yace.

    “Matso mana”.

    Kai ta gyaɗa tare da Matsawa kusa dashi ta zauna akan buzunsa.

    Yana murmushi yace.

    “Lafiya? ko dai ƙaran Addata kika kawo?”.

     

    Murmushi tayi tace.

    “Ni Meye ruwana da ita da zan kawo ƙaranta, dama karatune muna hadda Acan toh kuma na tsaya za’a iya wuceni”.

     

    Kai Ya jinjina kana yace.

    “Wacce surah kuke?”.

    Anutse tace.

    “Suratul Taubah muke munyi shafi huɗu zan tashi ashafi na biyar”.

    Cikin gamsuwa ya gyaɗa kai tare da faɗin.

    “Karanta inda kukayi naji”.

    Gyara zamanta tayi tare da  gyaɗa kai kana taja sassayan numfashi cikin zazzaƙan Muryanta tayi basmala kana ta fara rerewa karatun cike da jan Tajwidan Tartilan.

    Kai Malam Liman ya jinjina da faɗin.

    “Masha Allah”.

    Yaya Abba kuwa lumshe Idanunsa tun lokacin data fara karatu kana ya buɗe su alokacin da takai ƙarshen ayan yace.

    “Masha Allah Allah ya baki zaƙin murya Hafiza”.

    Jin abinda yace.

    Yasa Khausar sakin sakin ɗan guntun murmushi

     

    Malam Liman ne yace.

    “Masha Allah, yanzu dai kullum ki ringa zuwa irin wannan lokacin kina ɗauka darasin saboda maza basu fara zuwa ba, dalibai yara kuma sun tashi. kullum zan dinga baki awa ɗaya sai ki dinga zuwa ina ƙara miki sannan da wasu littattafan ma idan kunayi  ki faɗa zan dinga ƙara miki”.

     

    Cikin daɗi tace.

    “Toh ba matsala Insha Allah sannan munayin littafin Tajweed, Tauheed, Urasatul Nurul yaƙin, Nahwu, da kuma Mi’atu Hadith da dai sauransu”.

    Gyara zaman babbar rigarsa yayi tare da faɗin.

    “Insha Allah zaku riƙa zuwa ina ƙara miki keda Dija da Ma’u tunda dama sunyi sauƙa”.

    Sannan ya buɗe kur’ani ya miƙa mata shi kuma ya shiga karanta mata akai yayin da yake bin ko wanne harafi yana basa haƙƙinsa saida yakai har ƙarshen shafin kafin ya dubeta yace.

    “In mai-maita Miki?”.

    Kai ta girgiza alamar a’a tana jinjina baiwar ilimi da zaƙin murya da Allah ya masa.

    Anutse yace.

    “Ki hadda ce su kafin gobe sannan ki kawo min”.

    Khausar kuwa kai ta gyaɗa tace.

    “Insha Allah zan dage Malam amman dai goben ma zan biya sai jibi a ƙara min ko?”.

    Murmushi yayi tare da cewa.

    “La ba’as”.

    Miƙewa tayi Sannan tace.

    “Zan tafi da Kur’anin”.

     

    “Toh” ya cemata

    Sannan suka fice bayan fitansu ta dubi Dije tace.

    “Muje gidan garkuwan rugan ki”.

    Murmushi Dije tayi tace.

    “Gidan Baffa Umaru”.

    Kai Khausar ta gyaɗa sannan suka nufi gidan Baffa Umaru.

    Aƙofar gida suka samesa yana tare da baƙi,

    Juyawa yayi ya kallesu kafin yace.

    “Kushiga ciki ina zuwa”.

     

    Kai suka gyaɗa sannan suka shiga cikin gidan bakinsu ɗauke da Sallama,kallon cikin gidan Khausar tayi ko ina ashere fes-fes babu alamar datti ko ƙazanta.

    Adama kuwa murmushi fuskarta ta faɗaɗa tace.

    “Su Khausar ne sannun ku da zuwa”.

    Dije tace.

    “Yawwa Goggo Adama ya gida”.

    Ta amsa da lafiya lau sannan ta miƙe ta kawo musu faten doya da ruwa arandan ƙasa mai sanyi.

    Ita kuwa khausar murmushi tayi tana jinjina mutunci da karancin Goggo Adama atare sukaci kana suka gabatar da sallan Azahar sannan sukayi mata har zuwa lokacin Baffa Umaru bai shigo ba.

     

    Bayan fitarsu agidan Baffa Umaru Khausar ta juya ta kalli Dije tace.

    “Muje gidan Hajja Nana in ɗauki kayana”.

    Dije tace.

    “Toh”.

    Sannan suka nufi gidan Hajja Nana ba suyi wani tafiya mai tsawo ba suka isa gidan, Atsakar gida suka tarar da Hajja Nana.

     

    Harara Hajja Nana ta watsa mata tace.

    “Ke kam Uwar gantali kina nan kina ta yawo bazan ganki ba bare in Zauna dake”.

    Fuska Khausar ta ɓata da faɗin.

    “Wani irin gantali duk ba gidan ƙannenki da ‘ya‘yanki nake zuwa ba kuma ɗazun nan ina anan na tashi zaki ce amma yanzu zaki ce min gantali na tafi to nide gaskiya ba gantalalliya bace yawwa zaki wani cemin gantali ba gidan ƙannenki na tafi ba kuma saida na faɗa miki zamuje Bishiyar ƙare zancenka in kira Mommy na sannan yanzu ki wani cemin gantalalliya to nide wallahi ba gantalalliya bace”.

     

    Hajja Nana tace.

    “Ke kam wace gantalalliya ce ma ta fiki?,In banda gantali me kika iya?”.

    Ita kuwa khausar  juya manyan Idanunta dake lumshe kafin tace.

    “Wallahi da abinda na iya”.

    Hajja Nana kuwa kai ta gyaɗa tace.

    “ƙwarai da abinda kika iya fitsara ba gashi ma yanzu kina yi bayan shi babu wani abu da kika iya”.

     

    Khausar za tayi magana Dije tayi saurin riƙe hannunta cikin ƙasa da murya tace.

    “Dan Allah kiyi shiru ki ƙyaleta”.

    Kai ta gyaɗawa Dije tare da tsuke bakinta.

     

    Hajja Nana kuwa fuska ta tsuke Idanunta akan Khausar tace.

    “Bari in samiki doka gidan Jauro da kike zuwa ki kwana bazan hanaki ba tunda kince kinfi farar kura tsoro.

    Amma gobe ana sallar asuba na ganki anan dan zaki riƙa tayani aiki.

     

    Baki Khausar ta taɓe da faɗin.

    “Allah ya kaimu sannan bawai ana idar da Sallah bane zanzo saina yi Azkharul sabah da kuma karatuna”.

    Harara Hajja Nana ta watsa mata tace.

    “Toh Al-huda-huda sarkin karatu”.

     

    Khausar kuwa baki ta taɓe tace.

    “Koma de menene”. Sannan ta juya ta shiga ɗaki ta dauko kayanta tana fitowa ne taji Hajja Nana na cewa Dije.

    “Kar kice zaki koyi rashin kunyar wannan yarinyar”.

    Dije kam murmushi tayi ita kuwa khausar batare data tanka taba ta fice Dije tabi bayanta…

     

    GEMBILA

     

    Acan ɓangare Moddibo kuwa kwance yake akan makeken gadonsa daya sha shimfiɗa na Alfarma yayin da hannunsa biyu ke haɗa yana addu’ar bacci ya ɗauki kimanin minti goma kafin yasha fa addu’ar ya gyara kwanciyarsa yana mai lumshe idanunsa da haka bacci ya ɗauke sa can cikin baccinsa yaji wayarsa na ruri ya buɗe idanunsa kasancewar sa ba mutum ne mai nauyin bacci ba yasa hannu ya janyo wayar yana kallon screen ɗin Bahrain shine sunan dake ƙasan screen ɗin.

     

    Picking Yayi tare da kai wayar kunnensa tare da sallama.

    Amsawa Jalaludeen yayi da faɗin.

    “Ya yatsun ƙafar naka sun warke ne!?”.

    Moddibo kuwa gyara kwanciyarsa yayi da faɗin.

    “Jameel ya faɗa maka kenan?”.

    Jalaludeen yace.

    “Kamar dai baka sanni ba sai Jameel ya faɗa min zan sani?”.

     

    Moddibo kuwa kwanciyar sa ya gyara kana yace.

    “Eh ainaga kunyi waya ne bayan abin ya faru”.

    Jalaludeen yace.

    “Wallahi Jameel bai faɗa min ba lokacin da abin yafaru ma ai ina nan”.

     

    Shi kuwa Moddibo   kwanciyarsa ya gyada tare da faɗin.

    “Hmmm yayi kyau ka kawo mana ziyara kenan”.

     

    “Eh nakawo muku ziyara Barka da jumma’a ai tare mukayi jam’in sallan jumma’a ma”.

     

    Sassayan numfashi Moddibo ya fesar kana yace.

    “Mungode amma aiba mu gaisa ba”.

     

    Murmushi Jalaludeen yayi yace.

    “Ai zamu gaisa sai kuma na samu abin kallo ana dramer Shiyasa ba mugaisa ba, na tafi shi Kam Jameel baima  San nazo ba Dan  ban faɗa masa ba”.

    Kai Moddibo ya jinjina kafin yace.

    “Toh yayi kyau ya labarin mutanen England”.

    Jalaludeen yace.

    “Duk suna nan lafiya”.

    Kana sukayi Sallama.

    Kallon screen ɗin wayar Moddibo yayi Aransa yace Allah mai kyauta shi Jalaludeen jinsinsa da ban amma haka yake jin daɗin Mu’amala damu sannan babu cutarwa atsakaninmu da wannan tunani bacci ya ɗauke sa.

     

    Acan Rugar Jauro yaya kuwa Washe gari da Asubah bayan Khausar ta idar da Sallah tayi Azkharul sabah da tagama ta juya tare da kollon Dije tace.

    “Muje gidan Hajja Nana”.

    Dije tace.

    “A’a kije Ni zan dafa mana abinda zamu ci  kinga Goggo Nanne bata jin daɗi”.

    Kai Khausar ta gyaɗa sannan ta miƙe ta fita  atsakar gida ta samu Hajja Nana ta jiƙa wankekkdn wakenta ya jiƙa,

    Zama Khausar tayi tace.

    “Ina kwana Hajja Nana”.

    Ba yabo ba falassa Hajja Nana tace.

    “Lafiya”.

    Sannan ta ɗaura da cewa.

    “Ga can wake ki ɗauka ki markaɗamin acan”.

    Ta ida maganar tana nunawa Khausar inda ta kafa dutse irin na mutan da saboda basu da inji agarin”.

     

    Ita kuwa khausar inda Hajja Nana ta nuna mata da faɗin zatayi markaɗe ta riƙa bi da kallo kafin ta mayar da kallonta kan Hajja Nana tace.

    “Wai in markaɗa Miki me?”.

     

    Hajja Nana tace.

    “Waken ƙosai kinga kwana biyu banyi ba tunda kika zo Mai nane ya ƙare sai jiya na samu da Sadik ya shiga Gembila ya sayo min”.

     

    Ita kuwa khausar da Mamaki tace.

    “Kamar ya in miki markaɗe?”.

    Kallonta Hajja Nana tayi tace.

    “Kiyi min markaɗe nace”.

    Ita kuwa Khausar ƙugu ta riƙe tace.

    “Ni wallahi ban taɓa ganin yanda akeyi ba ban sani ba kuma ban iya ba”.

     

    Hajja Nana kuwa sheƙeƙe ta dubi Khausar tace.

    “Insaki aiki kice baki iya ba?”.

    Baki Khausar ta tura tare da riƙe ƙugu tace.

    “To ban iya ba ya za’ayi na iya ni Wallahi ba zanyi ba taya ma nasan zan iya riƙe dutsen nan nace zanyi markaɗe kije ki kirɓasa aturmi mana kawai”.

     

    Haɓa Hajja Nana ta riƙe cike da mamaki tace.

    “Ni kike cewa Inje in kirɓa aturmi Meye amfaninki Kai Allah wadaran naka ya lalace ke kam ba irin Addarki ba sam”.

     

    Ita kuwa khausar hannunta ta harɗe aƙirji Idanunta tsaye akan Hajja Nana tace.

    “Toh yanzu tunda kinsan Ni ba irin Addah bace sai kiyi min hakuri Addah na agabanki ta girma  duk wani horonki ta iya Ni Kuma ba agaban ki na girma ba, kuma ban iya ba ya za’ayi kice min haka wata ƙil ma bakya tuna ta kiyi mata addu’a sai in magana irin haka aya tashi kike tunata”.

     

    Dafe ƙirji Hajja Nana tayi da faɗin.

    “La’ilah ha ilallahu Muhammadu Rasulullah (S.A.W) Khausar ni zaki nunawa son Nanne?”.

    Ita dai Khausar na riƙe da ƙugu sannan tace baza tayi markaɗe akan dutse ba.

     

    Suna nan atsaye haka Baffa Umaru ya shigo ganinsu tsaye ahaka yasa yace da Khausar.

    “Lafiya kuwa”.

    Fuskarta babu walwala tace.

    “Wai Hajja Nana ce saina yi mata markaɗe akan dutse Ni kuma ban iya ba”.

    Baffa Umaru kuwa juyawa yayi ya sake kallon Hajja Nana yaga sai wurgawa Khausar Harara take Kallonsa ya mayar kan Khausar yace.

    “Ayyah Khausar ki gwada mana ba aikin mata bane”.

    Da sauri tace.

    “Toh ban iya ba Baffa Umaru taya zan gwada”.

     

    Hannunta ya riƙe tare da faɗin.

    “Zo in koya miki”.

    Ba musu ta matsa kusa dashi ɗan dutsen ya ɗauka ya kafa sannan ya matso da roban waken ya ɗibi wake cikin hannunsa yace.

    “Ki markaɗa”.

    Ta gyaɗa masa kai sannan ta fara Markaɗawa ga mamakinta sai taga yana markakaɗuwa har tayi niyyan zagewa ta markaɗa sai ta fasa ta fara jefar da ɗaɗɗaya tasan muddin tayi mai kyau Hajja Nana zata mayar dashi aikinta baya ga haka kuma daga riƙe dutsen yatsun hannunta sun sage tun lokacin data faɗo daga bishiya agidansu Moddibo hannunta bai dawo dai-dai ba.

     

    Ganin tana jefer da waken da guda-guda yasa Hajja Nana cewa.

    “Hegiya gantalelliya kibar min abuna”.

    Ta ƙarashe maganar tare da amsar dutsen tashiga markaɗawa.

    Miƙewa Khausar tayi tare da kaɗe hannunta tace.

    “Yafi Nono fari”.

    Shi dai Baffa Umaru murmushi yayi tare da yiwa Hajja Nana sallama ya tafi,

    Ita kuwa Khausar  saurin bin bayansa tayi suka tafi adai-dai ƙofar gidan Malam Liman suka tsaya tagaishesa cike da ladabi.

    Sannan suka cigaba da tafiya suna taɓa hira har suka isa gidansa.

    Adda Adama na ganinta ta sakar mata murmushi tare da faɗin.

    “Khausar sannu da zuwa ya gida ya gajiyarku na jiya?”.

     

    Murmushi tayi da faɗin.

    “Ba gajiya Adda Adama ya Aiki”.

    Ta amsa da.

    “Alhamdulillah.

    Kana tace.

    “Ke kam tunda kika zo baki taɓa zuwa kin kwana mana ba”.

     

    Khausar na gyara zama tace.

    “Insha Allah yau zan zo mukwana”.

    Murmushi Adda Adam tayi da faɗin.

    “Aikam Nagode”.

    Khausar ta juya tare da kallon Baffa Umaru dake sakin murmushi tace.

    “Amma fa ki faɗawa jarumin mijinki ya kawo min abu mai daɗi”.

    Murmushi kana tace.

    “Inde wannan ne baki da matsala”.

    Bayan sun gama hira tayi musu sallama ta tafi.

     

    Da daddare bayan sun idar da Sallah Isha’i Khausar tace da Dije.

    “Muje gidan Garkuwan Rugarku mu kwana”.

    Dije tace.

    “Toh muje”.

    Sannan ta miƙe suka shiga ɗaki sukayi wa Goggo Nanne sallama.

    Adda Amada dake ɗaki tana jin Sallamar su ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tana cewa.

    “Ai yanzu nake cewa zanbi sawunku”.

     

    Khausar tayi murmushi tace.

    “To aigamu ina Jarumin mijin naki?”.

     

    “Yana nan mai zaki bashi?”.

     

    “Babu abinda zan bashi abin daɗi da yace zai ajiye min zai bani idan kuma babu in tattara in tafi”.

    Ta Ida maganar tana murmushi.

     

    Miƙewa Adda Adama tayi tace.

    “Toh ki kwantar da hankali ga abin daɗi”.

    Tayi maganar tana ajiye musu karamin kwandon kaba dake ɗauke da Inabi, Tuffa, Mangoro, Ruman, da sauran kayan itatuwa sai kuma kwanon farfesun kifi yana tururi.

     

    Murmushi mai sauti Khausar tayi tace.

    “Lallai yana yina ashe wannan gara haka”.

    Ita dai Dije murmushi kawai take musu.

    Duka suka haɗu suka ci sannan suka kwanta ɗaki ɗaya da Adama.

     

    Shiko Baffa Umaru  yana can aɗakinsa ya kwana.

     

    Misalin ƙarfe biyu na dare Khausar ta farka aɗan firgice sakamakon hayaniya da take jiyowa.

     

    Dije ta gani itama zaune tana zazzare idanu ganin sukayi Adda Adama ta fice aɗakin da mugun sauri suma cikin sauri suka bi bayanta.

    Da gudu Adam ta nufi ɗakin mijinta dai-dai lokacin daya fito.

     

    Hannunsa ta riƙe cikin raunin murya tace.

    “Dan Allah kada ka fita da alama suna da yawa kaji hayaniyar su”.

     

    Da sauri ya juya ya kalleta tare da faɗin.

    “Idan ban fita ba wa zai dakatar da su wannan daga ji mutanen Ƙauyen Garinga ne bamusan mai suka zo dashi ba dare dare zasu zo mana haka babu yanda za’ayi dole in fita”.

     

    Ta girgiza kai tare da riƙe sa kana tace.

    “Dan Allah kada ka fita”.

    Tureta yayi daga jikinsa ya fita yana fita ya hango Arnan mutanen Garinga ne wanda yawansu zai kai kimanin mutum ɗari da sauri ya nufi hanyar jejin yayin da bayansa ke rataye da kwari da baka hannunsa na riƙe da touch light mai masifar haske.

    Cikin fushi da tsawa ya haskasu da touch light ɗin hannunsa mai masifar kashe ido yace.

    “Menene wai ma tukun ina kuka nufa!?”.

     

    Ɗaya daga cikinsu wanda ya kasance babban su yace.

    “Ƴar mu muke nema ta ɓata”.

    Duk da acikin duhu ne hakan bai hana shi watsa musu kallon banza ba yace.

    “Ƴarku ta ɓata shine dare-dare haka zaku zo wajenmu nemanta?”.

    Biyu Daga cikin su suka ce.

    “Ai kidnapping ɗinta akayi”.

     

    Afusace yace.

    “Kuma in kidnapping ɗinta akayi sai akace muku tana nan Rugarnu?”.

    Babban cikinsu yace.

    “Tana nan Rugarku dama Fulanin ku ai sune suka sace ta suka kawota dan haka an saceta tana nan mu nan muke zargi”.

     

    Cikin tsananin fushi da zuciya Baffa Umaru yace.

    “Baku isa ba babu yanda za’ayi haka ya faru!”.

    Babban cikinsu yace.

    “Dole sai mun shiga garinku gida-gida ɗaki-ɗaki mun bincika”.

     

    Cikin tsananin fusata Baffa Umaru yace.

    “Wallahi in dai ina raye baku isa ba babu wanda ya isa yashiga garinmu yace yayi bin cike indai haka kuke so kuje kuzo da rana muyi magana”.

     

    Babban su yace.

    “Mu adaren nan muke so muyi magana”.

    Baffa Umaru yace.

    “Toh baku isa ba”.

    Dumfaro sa sukayi da niyyar shiga Rugar gadan-gadan.

    Shi kuwa baya yaja tare da jan kwari da baka yace.

    “Duk wanda yake jin shi Jarumi ne kuma ya kai to ya kuskura ya shiga mana cikin Ruga yaga abinda zai faru”.

    Tsayawa su kayi akuma dai-dai lokacin ne sauran mazan cikin Rugar suka fiffito mafi yawa ma sautin Baffa Umaru ne ya tashe su dan shi mutum ne mai zafin gaske musamman ma idan ransa ya ɓaci.

    Acan bakin ƙofar gida kuwa sosai Khausar ta shiga mamaki sai asannan ta tabbatar da maganar Adama da tace mijinta Jarumi ne kuma Garkuwan Rugar.

     

    Malam Liman ne yayi gyaran murya bayan isan su wajen yace.

    “Tun da kunce haka yanzu ku koma da safe sai kuzo aje wajen Mai gari sai ayi magana”.

     

    “Toh”, Babban su yace sannan suka juya suka tafi badan ransu ya soba.

     

    Washe gari da safe bayan sunyi ta tsansu sun daddawo da hantsi Arnan garin Garinga suka zo suka haɗu aƙofar gidan Jauro.

    Bayan sun gama gaisawa Jauro ya dubesu Anutse cike da kamala irin na shugaba yace.

    “Mai yafaru muna sauraron ku”.

    Babban su yayi gyaran murya yace.

    “Ƴar muce buke ce akayi kidnapping sannan muna zargin tana cikin wannan Rugar”.

    Cikin danne takaicin ƙazafin da arnan ke son yi musu Jauro ya jinjina kai kana yace.

    “Kun tabbatar tana cikin wannan Rugar?”.

    Kai Babban su ya jinjina yace.

    “Ƙwarai mun tabbatar sannan mun zo zamu shiga Umaru ya hana mu sannan Umaru shi yake sa mana Ido komai akayi bamu isa muyi magana ba  sam Bama ƙaunar abinda Umaru yake mana yayi rayuwarsa muyi rayuwar mu!”.

     

    Wani banzan kallo Baffa Umaru ya watsa musu cikin yanayin zafinsa yace.

    “Ba zanyi rayuwata kuyi rayuwarku ba muddin kuna so nayi rayuwata kuyi naku to ku fita sabgarmu banga wanda ya isa ya shigo cikin Rugar mu yace zai taka mu inbar saba”.

    Da sauri Jauro ya ɗaga masa hannu hakan yasa Baffa Umaru yayi shiru.

     

    Baffa Jauro kuwa  maida kallonsa garesu yayi kan yace.

    “Munji mun yarda an sace muku yarinya anyi Kidnapping ɗinta”.

    Sai kuma ya maida kallonsa kan Malam Liman yace.

    “Ɗauko mana Bible agidanka”.

     

    Kallon Yaya Abba Malam Liman yayi yace.

    “Jeka ɗauko min asalin Bible na da acikin littatafai na”.

    Miƙewa Yaya Abba yayi babu daɗewa ya dawo hannunsa riƙe da Bible ɗin ya mikawa Jauro.

    Karɓa Jauro yayi  tare da miƙawa Babban su yace.

    “Gashi ku rantse da littafin ku tunda kuce ƴarku ta ɓata kuma tana garin nan”.

    Ƙin amsa Babban su yayi.

    Cikin sanyi Jauro yace.

    “Inde ka tabbata ƴarku ta nan to ka karba ka rantse Inde ka rantse.

    To mukuma zamu baku damar shiga sannan muma zamu rantse da Alkur’anin mu mai girma cewa ‘yarku bata nan amma duk da haka idan kun rantse zamu baku damar shiga cikin gida-gida ɗaki-ɗaki kuyi bin cike”.

     

    Shi dai babban nasu kin rantse wa yayi sai wuƙi-wuƙi yakeyi da ido.

    Ganin haka yasa Jauro ya kalli sauran na bayansa yace.

    “To ɗaya daga cikin ku ya karɓa ya rantse”.

    Still suma ƙin karɓa sukayi.

    Afusace Baffa Umaru yace.

    “Ba gashi ba basu da gaskiya Arnan nan neman fitina suke damu sam babu gaskiya alamarin su bayan sace-sacen dabbobi da kuke mana sai kun nemi fitina damu”.

     

    Babban su ya juya ya kalli Baffa Umaru yace.

    “Wani irin sace-sace kuma?”.

    Harara Baffa Umaru ya watsa masa yace.

    “kana tunanin bamusan kune kuke sace mana dabbobin muba to yanzu ga Bible ka karɓa ka rantse da littafin ku cewa ƴarku ta ɓata duk alamun rashin gaskiya ya bayyana atare da ku kawai ku taru dare-dare kuzo mana da mugun nufi”.

     

    Anutse Jauro yace.

    “Umaru kayi haƙuri kaki”.

    Yasan idan ransa ya ɓaci babu wanda zai iya shawo kansa.

    Malam Liman ya dubesu yace.

    “Tunda har baku rantse da littafin kuba kenan ƴarku bata ɓata ba in kuma ta ɓata to baku da tabbacin tana garinmu”.

    Babban su yace.

    “Shikenan babu matsala tunda zaku iya rantse wa da littafin ku munsan bata Rugarku yanzu magana ya ƙare.

    Amma Jauro da malam Liman ku jawo Umaru kunne ya fita sabgarmu”.

     

    Miƙewa Baffa Umaru yayi tare da nuna kansa da hannu yace.

    “Ni ɗin nan ka ganni nan Babu wanda nake tsoro sai Allah daya hallicceni”.

    Ƙwafa Babban su yayi yace.

    “Tun da haka kace shikenan amma zaka ga abinda kake tsoro”.

    Da sauri Jauro ya juya ya kalli Babbansu yace.

    “Mu ba mason fitina me kake nufi da zaiga abinda yake tsoro?”.

    Babban su yace.

    “Indai zai shiga sabgarmu to zaiga abu da yawa”.

    Jauro yace.

    “Toh bama son fitina tunda kuda kanku kun tabbatar da ‘Yarku bata cikin Garinmu sannan kuda kanku kunsan baku da gaskiya kun ƙi ku rantse, karku sake shigo mana Rugar mu haka ba maso idan kuma kuka sake to zamu haɗa ku da Sarkin cikin Gembila”.

    Jin Jauro yace zai haɗa su da Sarkin Gembila yasa suka ce.

    “To ayi hakuri ba zasu sake ba”.

    Sannan suka juya suka tafi cike da baƙi ciki badan Umar daya hana su shiga ba adaren da sun samu damar kwasan dabbobi damar saboda haka suka ce ansace musu ‘yarsu.

     

    Bayan kwana biyu Komai ya lafa ba fitina da hantsi Khausar da Dije da Ma’u sun ɗebo kayan marmari arafi suna fitowa  daga cikin rafin suka hango wata mota fake agefen Rugar tasu sai kuma hango wasu mutane biyu ɗaya ya fito daga gefen dama ɗaya kuma daga gefen hagu da gudu suka shiga motar kafin su Dije su ƙara so sun figi motar.

    Khausar kuwa sosai tsura  fuskokin su ido kafin su shiga motar, sosai ta riƙe kamanninsu. sannan tabi motar da kallo lokaci ɗaya ta riƙe Number motar Dije da sauran ‘yan matan kuwa mamaki suka shiga yi shin mai ya kawo masu motar garin sannan mai yasa da suka gansu suka gudu bayan sun san a irin wannan lokacin, duk mazan garin basa nan makiyaya sun tafi kiwo saura kuma su tafi jeji wa’anda ke rafi kuma sun tafi lambu jiki Asanyaye suka tafi.

     

    Bayan kwana biyu da daddare Khausar na bacci, yayi da take ta takurewa wuri ɗaya sabida wani irin masifeffen sayin da ake tsula musu.

    A hankali taja dogon numfashi kana ta fesar a hankali tayi lib.

    Can cikin baccinta kuwa  cikin wani ƙaton fili mai yalce da yashi fari ƙal-ƙal tana zaune bisa wani dutse tana fuskantar yamma kana daga bayanta  kuma wani garden ne mai masifar kyau da girma babu kalan bishiya da sirran da baya ciki, wani irin ni’imtaccen iskane mai cike da ƙamshi furanni ke buso masu wata irin iska mai ɗan karen sanyi.

    Gefen damanta ta juya ga mamakinta M Jameel ne zaune bisa wani dutse   yana murmushi, da sauri ta juya gefen hagunta kuma, Adda Adama ce ta gani zaune bisa dutse tanata murmushi.

    A can gabanta kuwa Mod….!  *NO EDITING*

     

    *Kuyi haƙuri sai yanzu na samu caji gashi ba editing. KUNSHA TYPING ERRORS*

     

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 16

    Sakayyah 16

     

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

    *SAKAYYAH*

    _page 16_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *In sha Allah daga gobe zan gama free page, ƴar uwa baki makara ba ki biya ki karanta cikin Aminci littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 daga wannan page ɗin sai na gobe mun gama free page, ki biya yafi sauƙi tsira ba haƙƙin kowa kanki.*

     

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

    Shiko M Jameel Wani irin tsuma ilahirin jikinsa keyi sakamakon tuni da ayoyin sukayi mishi na jin azabar da Ubangiji ya tanadar wa  da duk wanda ya kashe ran mumini da gangan ba tare da wani haƙiba.

    Cikin raunin murya me cike da tsananin tsoron Ubangiji  M jameel ɗin ya kawo fassarar aya na 90 da kuma 91, tsit gaba ɗaya masallacin yayi babu abinda ke tashi sai sautin kukan M Jameel daya kasa ci gaba, yayinda kukansa yasa da dama cikin mutanen yin kuka.

    Middibo kuwa kife tafukan hannunsa yayi kan fuskarsa yana maiyin wani irin sassayan kuka mai masifar sa rawan jiki, gaba ɗaya fuskarsa tayi jazir.

    Cikin ƙarfin hali M Jameel ya fara mgn cikin rawan murya  yace.

    “A cikin suratul Nisa, Aya ta 92 Allah ma ɗaukakin sarki na cewa, 92:

    -:Baya  halasta ga mutum da ya kashe ran mumini, sai dai idan ya kasance kuskure ne.”.

    Sai kuma ya tsagaita tare da sayan tafin hannunsa ya share hawyen daketa kwaranyowa da idanunsa, cikin rawan murya yaci gaba da cewa.

    “Duk wanda kuma ya kashe! Mumini da kuskure toh, zai ƴanta wuyan Muminin, sannan ya bada Diyya ga iyalan wanda ya kashe”.

    Sai kuma ya dire ayar mgnar tare da rushewa da zazzafan kuka mai cike da tashin hankalin da raunata zukata aya ta 93.

    Cikin rauni yasa hannu ya karɓi hankicif ɗin da ɗan agajin dake bayansa ya miƙa masa, sharce hawayensa yayi tare da juyowa ya kalli Moddibo da gaba ɗaya jikinsa rawa yake sai sheshsheƙan kuka mai fuzge numfashin da yakeyi, bazai iya hana kansa kuka ba, bare ya samu iko da damar hana aminin nasa.

    Cikin sheshsheƙan kuka M Jameel ya gyara zamanshi tare da cewa.

    “Huymmmm, a kuma cikin suratul Nisa ɗin ayata 93, Allah madaukakin sarki nacewa-:

    (Duk wanda ya kashe Mumini bisa ganganci, ko Mugunta da zalumci. Toh Sakamakonsa shine wutar Jahannama”.

    Sai kuma ya sake sakin wani irin raunataccen kuka mai cike da tsoro kana yaci gaba da cewa.

    “Allah madaukakin sarki cewa yayi-:

    Duk wanda ya kashe ran mumini zai dawwamane cikin jahannama, kuma Allah yayi fushi dashi, sannan kuma ya tsine masa”.

    Kawai sai ya kife kansa bisa Table ɗin dake gabansa, shar-shar haka hawayensa ke kwaranyar babu ƙaƙƙautawa.

    Modibbo kuwa cire tafukan hannunsa yayi bisa fuskarsa tare da dafa kafaɗar M Jameel ɗin kawai saka sufashe da kuka a tare, cikin kukan murya na rawa M Jameel ya buɗe baki da nufin zaiyi mgn amman ina ya kasa.

    Haka yasa Moddibo rumtse idanunsa kana murya na rawa yace.

    “Bayan fushi da tsinuwar ubangiji Allah Mabuwayi da komai baya ɓuyar masa yace.

    -:Wa ahdalahun Azaban Azeeymah).

    Ma’ana ya tandarwa duk wanda ya kashe ran mumini da ganganci Azaba mai girma!!!!.”

    Zuwa lokacin  wasu daga mutanen cikin masallacin kuka sukeyi da sheshsheƙan mafi akasari kuma duk jikinsu yayi sanyi.

    Shi kuwa Moddibo cikin rauni da sanyi  yace.

    “Duk waɗannan ugubobin sun ta’allaƙane ga wanda ya kashe ran mumini da ganganci, sakamakonshi Jahannama, kuma a cikinta zai tabbata, sannan Allah yayi fushi dashi, kana ya tsine masa, kuma ya ƙara masa da azaba mai girma.

    Wannan masifa har ina ɗan adam zai kaishi koda iyayenka ne sukayi fushi da kai taɓewa kakeyi bare Ubangijin talikai, koda iyayenka ne suka tsine maka lalacewa kakeyi bare tsinuwar Allah,  sannan azaba koda ta tururin tea ne tsoronsa muke bare kuma tabbata ta jahannama sannan da tanadin azaba mai girma”.

    Kawai sai lips inshi suka fara rawa kar-kar shima ɗin ya kasa ci gaba.

    Ganin hakane yasa M Jameel sharce hawayensa tare da cewa.

    “Aramma kawo mana dukkan wata Ayar Al,qura’ani da Ubangiji yayi magana akan duk wanda ya kashe ran mumini”.

    Cikin tsumar jiki tare da wata raunatacciyar murya mai cike da tsananin tsoron Ubangiji da kuma sanin hukuncin wanda ya saɓa masa Moddibo yayi gyaran murya dai-dai zai fara karanta Ayar manyan Malaman dake wajen suka nuna musu agogon dake liƙe a can bayansu a jikin gini.

    Wanda hakan ke musu nuni da alamar lokaci yayi.

     

    Nan-nauyan ajiyar zuciya M Jameel ya sauƙe tare da share ƙwallan da suka zuba masa kana cikin raunin murya yace.

    “Lokaci yayi sai dai idan Allah ya kaimu gobe zamu ɗaura daga inda muka tsaya”.

    Ya sauƙe nannuyar Ajiyar zuciya tare da cewa.

    “Ya Allah Ubangiji yabamu zaman lafiya ya Allah karabamu da sharrin ƴan bindiga daɗi Ubangiji ya tsare mu da sharrin kidnappers Ubangiji ya bamu zaman lafiya Allah yajiƙan iyayen mu da duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya.

    Wa subhanakallahumma wabi hamdika ash shahadula’ilahu. nastagfirka wanatuubu Ilaik”.

    Tunda ya fara addu’ar suke Amsawa da Ameeen har aka shafa.

    Mata ne suka fara fita kafin maza.

     

    Acan ɓangaren Khausar kuwa, bayan ta koma gida kai tsaye Bedroom ɗinta ta wuce batare data shiga wajen Mommy ba, tana shiga ta kwanta lamo akan gado hawaye na tsiyaya daga kyawawan Idanunta sosai.

    Tafseer ɗin da M Jameel Yayi ya riƙa ratsa jikinta har ƙwaƙwalwar kanta Muryar Modibbo kuwa har yanzu yana ratsa kunnuwanta, da haka bacci ya ɗauketa batare data shirya ba.

    Washe gari Da safe still haka Khausar ta tashi cikin mutuwar jiki Anutse ta fito daga Bedroom ɗin ta zauna agefen Mommy dake falo.

    Lumshe Idanunta tayi kana cikin sanyin murya tace.

    “Mommy ina kwana”.

    Anutse Mommy ta maida kallonta gareta tare da na zartan yanayin ta batare data amsa gaisuwar data mata ba ta jefo mata tambya tare da cewa.

    “Meke damunki Khausar na lura tun jiya jikin ki Asanyaye”.

    Ɗago Kai Khausar tayi Idanunta cike da ruwan hawaye kana cikin sanyi murya tace.

    “Wallahi Mommy tun jiya da muka je wajen tafsir ɗin da Malam M Jameel yayi jikina ya mutu hankalina ya tashi gaba ɗaya na rasa mai yasa tsoro ya kamani”.

    Miƙewa Mommy tayi tare da matsowa kusa da Khausar ta shafa kanta kana tace.

    “Babu komai wannan masiface-masiface ne da Allah ya jarabci Al’umma wannan ƙarnin saidai mu dage da addu’a Allah ya yaye mana ya kuma tsaremu da faɗa wa mummunar ƙaddara Allah ya rufa mana asiri ya karemu da zamewa sanadin mutuwar koda kadagare ne”.

    Jinjina kai Khausar tayi tare da cewa.

    “Ameen”.

     

    Acan gidansu Moddibo kuwa Innayi ce zaune atsakar gida ta zabga tagumin tunda taji tafsirin da M Jameel sukayi jikinta yayi masifar sanyi wani irin tsoron Allah mara misaltuwa tashiga hakan fargaba ya rufeta.

    Washe gari.

    Da hantsi A hankali Moddibo da M Jameel suka fito, Moddibo na sanye cikin Shigarsa as Usual Jallabiya Sky blue mai yauƙi da santsi kansa ɗaure da farin Hirami  kana takalmamsa farare jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi turaren Oud Khareem na tashi.

    Shima M Jameel  sanye yake cikin irin shigar Modibbo jikinsa na fitar da sanyayyan ƙamshi kai tsaye sashen Innayi suka nufa,Innayi dake zaune gaban barandar akan kujera ƴar tsugunno ta ɗago kai ta kalli Moddibo da M Jameel kawai sai taji Idanunta na tsats-tsafowa da ruwan hawaye.

    Tsayuwa Moddibo ya gyara kana yace.

    “Ya dai Innayi”.

    Idanu ta zuba masa batare data iya furta komaiba kawai sai hawaye suka shiga kwaranya daga idanunta.

     

    Cikin yanayin tashin hankali Moddibo ya tsugunna agefenta na dama yayin da M Jameel ya durƙusa  agefenta na hagu kana suka haɗa baki tare da cewa.

    “Innayi ya dai me yasame ki?”.

    Kallonsu tayi hawaye na cigaba da kwaranya daga idanunta ta sauƙe numfashi kana tace.

    “Wa’azinku na jiya ya ratsa jikin mutane wa’azin yasa mutane acikin ɗimuwa wa’azinku na jiya ya tunatar sannan yasa tashin hankali kuma wannan zamanin muna fama da Masifa Allah dai ya yaye mana jiya hankalina atashe yake domin ire-iren abubuwan akeyi!”.

    Jinjina kai M Jameel yayi tare da sauƙe numfashi kana yace.

    “Hakane sosai ma Innayi amma mu cigaba da addu’a babu abinda ya gagari Ubangiji ga dama yazo watan Ramadan muyita addu’a Allah ya yaye ya taƙaita ya sauƙaƙa mana”.

    Atare Modibbo da Innayi suka amsa da.

    “Ameeen”.

    Miƙewa M Jameel da Moddibo suka atare kana M Jameel ya Kalli Innayi tare da cewa.

    “Toh Innayi zamu tafi Tafseer A masallacin makarantar mu”.

    Jinjina kai Innayi tayi kana tace.

    “Ubangiji Allah ya tsare ku ya kuma sake ɗaukaku”.

    Ameeen suka amsa tare da juyawa zasu fita har sun kai ƙofa Innayi ta ɗan ɗaga sautin Muryanta tare da cewa.

    “Yauwa wai niko ya batun tafiyar mu ne?”.

    M Jameel ya juya tare da cewa.

    “Komai ya kammala na tafiyar mu Insha Allah ranan sha biyar ga wata zamu tashi misalin sha biyu da rabi na dare jirginmu zai tashi jibi kenan ba in sha Allah, kuma sai munyi tafsir ɗin ranan ma zamu tafi Taraba”.

     

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Allah ya nuna mana Ubangiji Allah ya kaimu lokacin lafiya amman kuma kace sai kunyi tafsirin ranar?”.

    Kai ya jinjina tare da cewa.

    “Eh kinga Tara na dare zamu fara, goma zamu tashi, dama kuma kafin mu tafi zamu gama shirin mu duka, tsananin mu Gembulan da taraba kuma tafiyar awa ɗaya da rabine, kinga kenan sha ɗaya da rabi zamu isa, zamu samu awa ɗaya ma acan kafin mu tafi, Abba na kuma su gobe nema zasu tashi”.

    Cike da gamsuwa Innayi ta jinjina kai tare da amsawa.

    “Allah ya kaimu lfy”.

    Ameeen suka amsa a tare kana suka fice mota suka shiga M Jameel ke Driving cikin nutsuwa har suka isa masallacin.

     

    Suna shiga suka fars gabatar da tafsirin kamar yanda suka saba ƙarfe ɗaya da rabi dai-dai suka gabatar da sallah Moddibo yayi limanci bayan sun idar suka cigaba kiran sallar La’asar yasa suka dakata da karatun tare da miƙewa suka gabatar da sallah bayan sun idar suka fito suka shiga mota awannan lokacin ma M Jameel ke Driving har suka iso gida.

    Hong M Jameel Yayi Modibbo ne ya fita ya buɗe  musu.

    Anutse suka fito tare da furta Bismillahi,

    Ahankali Moddibo ya gyara tsayuwarsa tare da fesar da sassayan numfashi.

    Ido ya tsirawa bishiyar Ayaba da iska ke kaɗawa  har na tsawon sakonni goma, sai kuma ya maida kallonsa kan Bishiyar mangoro Idanunsa ya lumshe domin Allah ya sani ganin sirrai ya fiye mishi ganin komai daɗi. sannu ahankali ya riƙa tuna lokacin da yarinyar tashigo gidan har tayi nasaran hawa reshen bishiyar mangoro mai girma da tsawo, da kuma sanda ta faɗo akan yatsun ƙafarsa.

    Da sauri ya buɗe idanunsa

    Tare da jan dogon tsaki mai cike da tsanar lamuran yarinyar. Idanunsa ya juya jin M Jameel na cewa.

    “A.J tunanin mai kakeyi haka ka tsiwara Bishiya ido?”.

    Sanyayyar Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe tare da furzar da iska mai sanyi daga bakinsa kana yasa hannu ya shafa kwantaccen Sajen fuskarsa ya maida kallonsa kan M Jameel da har zuwa lokacin shiyake kallo,Ya mutse fuska yayi kana yace.

    “Babu komai”.

    Daga haka ya wuce gaba Kai M Jameel ya Girgiza tare da bin bayansa suka shiga Babban falon Moddibo da komai ke kimtse sai tashin ƙamshi yake.

     

    Zama M Jameel Yayi akan 3sitter tare da faɗin.

    “Wash’ Allah!”.

    Kallonsa Moddibo yayi amma bai ce komai ba Bedroom ya nufa tare da janye Hiramin kansa kana ya cire jallabiyar dake jikinsa ya buɗe ƙofar toilet da addu’a

    Kana yashiga  shawer ya sakarwa kansa  yashiga cuɗe jikinsa ya ɗauki kusan minti ashirin kafin ya fito zama yayi agaban Dressing mirrow ya shafa Mai sama-sama kana ya miƙe ya sanya Jallabiya Maroon colour da farin hirami. Feshe jikin sa da turarukansa masu daɗin ƙamshi yayi. shima M Jameel wanka yayi tare da sauya kan jikinsa zuwa Jallabiya fari kana ya ɗaure kansa da Maroon Hirami Sosai sukayi kyau    atare suka fito zuwa farfajiyar gidan anan suka samu Innayi da Asma’u na aikin abin buɗa baki kallon Innayi dake soya ƙosai yayi sai kuma ya maida kallonsa kan Asma’u dake dama kunun sadaka na masallaci har ta gama ta rufe sai kuma suka bita da ido.

    Kallon Asma’u dake kwaɓa fulawa, kuka, da kanwa M Jameel Yayi  yace.

    “Yau kuma ɗan wake ake mana ne Asmeey?”.

    Kai ta jinjina kana tace.

    “Eh dan naji jiya Yaya Moddibo nacewa ɗan wake mukayi ne shiyasa yau nace bari ayi”.

    Murmushi Moddibo yayi ya mai binta da wani irin amintaccen  yace.

    “Kai kin kyauta mun kuwa, kwana biyu bamuci ba inaga tunda azumi ya kama kamar baku yimana shiba”.

     

    Kallonsa Asma’u tare da ce wa.

    “A’a munyi amma ranan baka ciba agidan Ummi kuka sha ruwa ranan”.

    Jinjina kai yayi  yace.

    “Toh yau kam Insha Allah zamu dawo muci ɗanwaken nan”.

    Murmushi tayi ta na jefa ɗan waken da cokali tace.

    “Allah ya dawo daku lafiya”.

    Ameeen suka amsa kana suka mayar da Kallonsu kan Innayi dake musu gashin Zabbi sai tashin ƙamshi yake.

    Idanu M Jameel ya lumshe yace.

    “Innayi zamu wuce”.

    Da murmushi afuskarta ta kallesu  tace.

    “Ubangiji Allah ya tsare”.

    “Ameen”,Suka amsa sannan suka fice atare kai tsaye masallacin Juma’ar da suke limancin suka nufa cike da nutsuwa da kuma kamala suka gabatar da tafsirin Alkur’ani acikin Suratul Zariyat yayin da Moddibo ke jan baƙi M Jameel na tafsiri ƙarfe shida dai-dai suka tashi.

     

    Anutse suka fito daga cikin masallacin suka shiga mota akuma dai-dai lokacin wayar M Jameel ya hau ruri cike da nutsuwa ya gyara zamansa tare da ciro wayar daga aljihun sa Sunan Abban sa ke yawo a screen ɗin kallon Moddibo da idanunsa ke lumshe yayi yace.

    “Kaga Abba ke kira”.

    Ya ƙara sa maganar tare da Amsa kiran yakai kunnensa tare da cewa.

    “Assalamu Alaikum”.

    Daga ɓangare Abba yace.

    “Wa’alaikum Salam Babana”.

    M Jameel Yayi murmushi tare da cewa.

    “Na’am Abba na”.

    Gyaran murya Abba yayi kana yace.

    “Nikam laifin me mukayu mukune da kai da Moddibo da baza kuzo mu samu ladan baku buɗa baki agidan nan ba”.

    Murmushi M Jameel Yayi yace.

    “Ayyah Abba na laifin me zaku mana mukam a duniyar nan gama A.J ɗin yana jinka”.

    Ɗan Matsawa kusa da  M Jameel ɗin Moddibo yayi kana yace.

    “Abbah mai zaku mana  A duniya ko kun yi mana abu baza muyi fushi da kuba waye zaiyi fushi da iyayensa?”.

     

    Murmushi Abba yayi  yace.

    “Toh tun da akayi azumi baku zo kunsha ruwa a gidan nan bafa, abin yana damuna yau fa  kwana goma sha uku  kenan da baku zo kunsha ruwa agidan nan ba fa”.

     

    Dariya M Jameel Yayi yace.

    “Abba ka dai manta mun zo ranan da akayi azumi biyar agidan muka sha ruwa fa”.

    Gyara zaman wayar Abba yayi akunnensa kana yace.

    “To ai bana nan ba asha ruwan dani ba yau dai so nake kuzo musha ruwa tare”.

     

    Gyara zama Moddibo yayi  yace.

    “Abba baza mu bari sai gobe ba?”.

    “A’a yau nakeson ganinku kuzo musha ruwa anan”.

    Cewar Abba.

    Jingina kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.

    “Toh shikenan Abba zamu zo insha Allah amma bari mu fara zuwa gida”.

    Cikin sauri Abba ya Girgiza kai tare da cewa.

    “A’a karfa ku makara kuzo komai ya kammala ku kawai ake jira ga kun lokacin ya ƙarato”.

    Atare suka haɗa baki wajen cewa.

    “Toh shikenan Abba ga munan zuwa”.

    Kallon Moddibo M Jameel dake Driving Yayi kana yace.

    “Muje?”.

    Moddibo kuwa Idanunsa dake lunshe ya buɗe yace.

    “Eh muje mana J”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa kana ya juya akalar motar zuwa Unguwar su Abba ba abinda ke tashi acikin motar face ƙira’ar Alkur’ani acikin Suratu Yusuf tare da Sanyayyar ƙamshin tularensu, Wayar Moddibo dake gaban aljihu ne ya hau ruri Anutse yasanya lallausan tafin hannunsa mai zagaye da gashi ya ciro wayar tare da kallon sunan mai Kiran Malam Arɗo amsa kiran yayi tare da kai wa kunnensa.

    Daga ɗaya ɓangaren Malam Arɗo yayi gyaran murya kana yace.

    “Wai kai baza kazo kasha ruwa agidana ba ko sau ɗaya ne Moddibo?”.

    Murmushin gefen baki Moddibo yayi tare da shafa kwantaccen Sajensa kana yace.

    “To Malam ka gayyace mune ai baka gayyace mu shan ruwa ba”.

    Da sauri Malam Arɗo yace.

    “To na gayyace ku xo yanzu”.

    Girgiza kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa kana yace.

    “Toh ba yau ba dai sai gobe”.

    Da sauri Malam Arɗo ya zare Ido tare da cewa.

    “To duk abubuwan da nasa aka dafa muku kuma fa?”.

    Murmushin gefen baki Moddibo ya kuma yana imagine fuskarta malam Arɗo kana yace.

    “Ka bawa mutanen gida suci ba rabon mu bane

    gobe kuma Idan Allah ya kaimu kama na namu kuma ayi da mutanen gida duka”.

    Cikin sauri Malam Arɗo yace.

    “Wato dai kai ko yaushe sai ka kawo min sabon tsari acikin al’amari na ko”.

    Murmushi M Jameel yayi shaƙuwar dake tsakanin Moddibo da malam Arɗo ya wuce zaton mutane.

    Moddibo kuwa ɗan Murmushin dake ƙarawa fuskarsa kyau yayi kana yace.

    “Ai dole dai kam”.

    Dariya Malam Arɗo yayi  yace.

    “Dama gobe ka tabbatar lokacin shan ruwa yana yi na ganka, ba sai na kira ba ka gaishe da Jamilu kar ku cinye min kati na”.

    Ya ida maganar tare da katse kiran.

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Malam Arɗo ko?”.

    Murmushi kawai Moddibo yayi yana motsa laɓɓansa alamar tasbihi yake.

     

    Cikin mintunan da baza su gaza biyar ba suka isa ƙofar katafaren gidan Hong M Jameel Yayi mai gadi ya buɗe musu Anutse M Jameel ya cinna hancin motarsa gidan tare da yin parking a inda aka tana da danyi Parking ɗin motoci.

    Cike da nutsuwa suka nufi sashen Abban M Jameel, bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga tamfatsetsen Falon nasa daya gaji da tsawuwa yana fitar da sanyayyan ƙamshi.

    Tsaye suka hangosa yana gyara ɗaurin agogon hannunsa fuskarsa da damshi da alama Al,wala yayi.

     

    Kallonsu yayi tare da sakar musu da murmushi kana yace.

    “Ku shiga kuyi al,wala kunga muna shan ruwa sai mutafi masallaci”.

    Kai suka gyaɗa sannan M Jameel ya nufi toilet dake Falon kana ya kalli Moddibo da faɗin.

    “A.J kashi ga toilet ɗin ciki kayi al,wala”.

    Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.

    “A’a kashiga na ciki ni zan shiga wannan”.

    Kallon Moddibo Abba yayi kana yace.

    “Wato shi yashiga ɗaki na kai ba zaka shiga ba ko? To ai kaima ɗana ne kashiga babu komai Moddibo”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana yace.

    “Toh shikenan Abba”.

    Sannan ya wuce Bedroom ɗin Abba ahankali ya saki murmushi ganin komai na Bedroom din tsaf-tsaf akimtse Aransa yace ashe de J gadon tsafta yayi awajen Abba shima komai nashi tsaf-tsaf ajiyar zuciya ya sauƙe tare da shiga toilet ɗin nan ma komai atsaftace Al’wala ya ɗaura kana ya fito atsaye ya samu M Jameel da Abba Kallonsu Abba yayi kana yace.

    “Ku ƙaraso mu isa dining”.

    Kai suka gyaɗa tare da nufar dindin ɗin da aka ƙawata da kayan ciye-ciye na alfarma wani irin kwando ne na kayan marmari ne kama daga, Inabi, Abarba, Ayaba, Kankana, Lemo, Ruman, Tuffa, Mangoro.

    Sai kuma wasu Warmers masu kyau dake ɗauke da pride rice da yaji kayan lambu,sai daga ɗaya gefen kuma wasu jug ne masu kyau ɗaya kindirmo ne mai sanyi adame ɗayan kuma kunun shinkafa  ne sai Flaks dake ɗauke da ruwan tea da kuma kofina daga gefensa kuma gongomin madara ne dana Bounvita sai kulan ƙosai sosai dining din ya ƙawatu.

    Anutse suka zauna akan kujeran Abba ya zauna daga ɓarin kudu Moddibo ya zauna daga ɓarin yamma yana fuskantar gabar M Jameel kuwa daga ɓarin gabas ya zauna yana fuskantar yamma.

    Anutse Moddibo ya ɗauki dabino guda bakwai ahannunsu idan yaci sai ya sanya ƙwallon ahannunsu na hagu bayan yaci sai ya ɗauki inabi yaci M Jameel kuwa dabino uku yaci tare da apple haka ma Abba.

    Sai.kuma suka sha kankana da inabi kana suka ɗan ɗaura da ayaba.

    Kallon su Abba yayi cike da so da ƙaunarsu kana yace.

    “Toh kuci abinci”.

    Girgiza masa kai sukayi kana atare suka ce.

    “A’a Abba sai mun dawo daga masallaci”.

    Kai ya gyaɗa musu kana suka miƙe atare suka tafi masallaci suka idar da sallah bayan sun dawo M Jameek ya ɗebi Pride rice Kaɗan da tsokokin kaza. Modibbo kuwa kindirmon da aka dama ya ɗiba a Cup Abba kuwa chicken peper da pride rice shima ya ɗebi yana ci.

    Fara cinsu babu daɗewa aka turo ƙofar aka shigo Idanun Hajiya Karima bai sauƙa ko ina ba sai kan Moddibo dake  riƙe da kofin kindirmon kana da plate ɗin da Abba ya sa mishi pepper chicken and vegetables da fork a samansu.

     

    Cike da tsanarsa ta watsa masa wani wulaƙantaccen kallo kana tace.

    “Toh acire tsatsan haƙori anan, kaska raɓi mai jini wato ko zuwa shi kaɗai ya samu ya keɓe da mahaifinsa ba za’a bari ya samu damar hakan ba ko?

    Oh ni Kareeme tunda nake a duniya ni dai ban taɓa ganin mutum mai shegen nacin tsiya irin kaba, sam baka da godiyar Allah ba zaka tsaya amatsayin ka ba shin kai wani irin Jarabebben mutum ne Aliyu?!”.

    Cikin wani irin fushi da ɓacin rai Abba ya mike ahasale ya dubeta kana yace.

    “Hajiya Karima mai kikeyi haka ne?

    Wai meyasa ne ke baki da hankali ne? kinsan abinda kike faɗa kuwa!”.

     

    Fuska ta ɓata kana tace.

    “Toh Alhaji gaskiyane ya barka kaida ɗan ka kuhuta mana kuyi shawara acikin sirri”.

    Afusace Abba ya katseta tare da faɗin.

    “Me kike nufi shiɗin ba Uwa da Ubane suka haifeshi ba shima ɗana ne”.

    Sheƙeƙe Hajiya Karima ke Kallonsa kafin cike da Isgilanci ta kallesa kana tace.

    “Yaushe  ka haifesa bamu da labari?,yaushe ka auri uwarsa har ka haifesa bamu sani ba?”.

    Cikin tsananin fushi Abba yace.

    “Kifita anan ki fita Karima bana son ganinki tun da ke kince baki da ɗa’a baki iya Mu’amala da mutane  arayuwarki ta duniya ba, bana son haka, Bana son haka kar ki sake yin haka na yi miki kashedi na ƙarshe wannan shine last warning Hajiya Karima!, Kada ki sake yimin haka.

    Domin kuwa koda Mahaukaci Jameel ya ɗauko ya kawo wannan gidan wallahi yafi min ke daraja, saboda nasan koda mahaukacine Jameel zai nuna masa cewa ni mahaifinsa ne kuma na tabbata zai mutunta ni”.

    Cikin fushi ya sauƙe ajiyar zuciya tare da furzar da Iska kana ya cigaba da cewa.

    “Na tabbata ko  Mahaukaci Jameel ya kawo gidan nan zai mutuntani, kuma zai ɗauke ni da daraja fiye da yanda ke ki ɗaukeni ban isa da keba, misali ga yadda idan na baki umarni kike fatali dashi, ba zakiyi amfani dashi ba.

    Dan haka ko kin san Jameel ya fimin komai.

    Jameel da kike gani shine Komai nawa a Duniya akan farin cikin Jameel ina iya yin komai dan haka tun wurima ki kiyayeni!

    Kifita idona in rufe Hajiya Karima!!.

    Ki kiyayeni kada inci miki mutunci!!!”.

    Ya ida mgnar tare da buga jikin kujerar dining ɗin kana yaci gaba da cewa.

    “Na tabbata kare idan Jameel zai kawo gidan nan sai yamin biyayya fiye da yanda ke kike min biyayya. Kare dai nasan idan Jameel zai kawo min gidan nan bazai tsaya yamin irin haushin da kike min ba!”.

    Sai kuma ya watsa mata Kallon mai cike da fushi  kana yace.

    “Kare idan Jameel zai kawo gidan nan kare mai ɗa’a da biyayya zai kawo min ba karen da zai kunya ta min baƙi na ba amma ke kullum baki da hankali. idan Jameel ɗan kine da kika haifa acikin ki zaki yi masa haka ne?”.

    Kasa cewa komai Hajiya Karima tayi sai huci da take tamkar zakanya.

     

    M Jameel kuwa ƙasa yayi da kansa cike da jin daɗi karo na farko kenan da mahaifinsa ya burgesa a kanta daya buɗewa Hajiya Karima wuta akan abinda ta keyiwa Moddibo domin kullum idan ta wulaƙanta Moddibo sai sunbar gidan kafin yake mata faɗa akan ta daina, amma yau yaji daɗin faɗan da Abba yayi mata agaban Idon Moddibo saboda Moddibo zaiji daɗi sannan zai san cewa yana da daraja da kuma kima awajensu.

    Moddibo kuwa kansa ya sunkuyar ƙasa da cike kunya sam baiji daɗin  ɓatawan mata da Miji adalilinsa ba, yayi dana sanin zuwa gidan, yasan cewa duk lokacin da yazo gidan sai yayi sanadin da za’a samu hatsaniya, sannan ya riga daya sani tun yana yaro matar nan bata sonshi bata ƙaunar ganinsa da Jameel sai dai ya fahimci ba wai shi ta tsana ba tana fakewa da guzma ne ta harbi karsana.

    Cikin sanyi murya ya ɗago kansa tare da furzar da iska mai zafi kana yace.

    “Abba kayi haƙuri dan Allah dan darajar Annabi”.

    Juyawa Abba yayi ya kallesa kana ya ɗaga masa hannu da faɗin.

    “Yi shiru ba maganar ka Aliyu barni da ita haka take yimin, ba kai kaɗai ba, duk baƙon da Jameel zai kawo gidan nan sai taci masa zarafi, duk mutumin da zata gansa da Jameel saita nuna min ba mutumin kirki bane!”.

    Sai kuma ya juyo Afusace tare da kallonta har zuwa lokacin tana tsaye cike da ɓacin rai ya tsira mata idanu kana yace.

    “Mai Jameel ya tsare miki?, Jameel tun tasowar yana ƙarami biyayya yake miki bai taba Musa Miki ba duk da kinzo kin samu yana da shekara goma sha huɗu na tabbata baki yiwa Jameel wahala ba amma yana karramaki sannan yana mutuntaki kamar yanda yake mutunta mahaifiyarsa”.

    Zazzafan iska ya furzar  kana still muryarsa cike da ɓacin rai yace.

    “Amma ke kullum baki da buri daya wuce kici masa zarafi, Idan kin zauna ki riƙa faɗa mun magana kinyi zaton cewa bana son Jameel ne?.

    Shin inada wani ɗa aduniya daya wuce Jameel ne?”.

     

    Cikin tsananin fushi da ɓacin rai Hajiya Karima ta nuna kanta kana tace.

    “Ni ka ciwa zarafi akan yaro ɗan maƙota dan yana abokin ɗan ka, sannan dan na faɗa maka gaskiya, kai baka ga yadda yake liƙewa ɗan nakaba duk ya hana sa tattalin arziki sannan ya hanasa ya tara abin kansa”.

    Cikin wata fusatacciyar tsawa daya amsa ilahirin falon yace.

    “Ki fice min anan Karima bana son ganinki”.

    Afusace ta juya kamar zata tashi sama tana wani irin huci tare da jin tsanar Moddibo da M Jameel fiye da komai arayuwarta!.

     

    Anutse Abba ya juya ya kalli Moddibo kana cikin sanyi murya yace.

    “Dan Allah Aliyu kayi haƙuri kada ka damu da abinda tayi maka, sannan bance ka ɗauki wannan amatsayin wani mataki da zai hana ka zuwa gidan nan ba, aduk sanda kaga dama zaka zo”.

    Murmushi yayi kana yace.

    “Babu komai Abba ai ita mahaifiya ce agurin mu dan tayi mana haka ba zai zama wani aibu ba”.

    Jinjina kai Abba yayi tare da cewa Ubangiji Allah ya al’barkaci rayuwarku”.

    Atare suka amsa da.

    “Ameen”.

    Juyawa M Jameel yayi tare da kallon Moddibo Cikin sanyin murya mai cike da so da shaƙuwa ya numfasa kana yace.

    “Dan Allah A.J kayi haƙuri”.

    Murmushi Moddibo yayi kana yace.

    “Laa babu Komai J. Yanzu dai tashi muje mu bata haƙuri”.

     

    Da sauri Abba ya kalli Moddibo kana yace.

    “Baza ku bata haƙuri ba ku zauna kuci abinci”.

    Kai suka gyaɗa sannan suka zauna baki ɗayansu, basu wani ci abincin kirki ba, domin ko kowa da irin damuwar dake ransa, bayan sun kammala suka miƙe tare da yiwa Abba Sallama haƙuri Abba ya sake bawa Moddibo.

    Murmushi Moddibo yayi kansa aƙasa yace.

    “Ayyah Abba Allah babu komai”.

    Sannan suka juya har sun kai ƙofa Abba ya ɗan ɗaga sautin muryansa tare da cewa.

    “Yau kam ba zamu kwana anan bane?”.

    Girgiza kai Moddibo yayi kana yace.

    “A’a Abba idan mun kwana anan Innayi ita kaɗai zamu bari acan”.

    Jinjina kai Abba yayi kana yace.

    “Eh kam ya kamata gida babu namiji ba gida bane kuje”.

    Godiya suka masa kana suka fice.

    Suna cikin mota aka kira Isha’i kai tsaye masallacin da suke limancin suka nufa kamar ko yaushe Moddibo ne yaja Sallar bayan sun idar sukayi Asham kana suka wuce gida.

     

    Suna shiga gida kai tsaye sashen Innayi suka nufa zaune suka sameta riƙe da carbi ahannun Asma’u kuma tana riƙe da Alkur’ani mai girma tana karatu.

    Batare da sun ƙarasa shiga ba Moddibo yace.

    “Innayi Barka da shan ruwa”.

    Anutse ta kallesa kana tace.

    “Yawwa yau ina kuka tsaya ne baku dawo da wuri ba, nace Asma’u ta kira min ku inji kuma ashe wayar ba kati”.

    Murmushi M Jameel Yayi kana yace.

    “Ayya Innayi Abba ne ya kiramu wai muje mu sha ruwa acan shiyasa kika jimu shiru”.

    Kai ta jinjina tare da kallon Moddibo tace.

    “Fatan duk suna lafiya?”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa mata  kana ya sake labulen tare da faɗin.

    “Innayi akawo mana abinci”.

    Ya ida mgnar tare da zama akan shimfiɗar dake barandar Asma’u Innayi ta ƙalla kana tace.

    “Ɗauki abincin ki kai musu”.

    Kai Asma’u ta gyaɗa sannan ta ɗauki lemun tsani ta yanka ta matsa kaɗan akai  kana tayi slinzing ɗin ƙwoyi kana ta zuba musu wadataccen man gyaɗa da kuma dakekken yajin barkono sai Cucumber da Cabbage ta Kai musu.

    Sosai suka Moddibo da M Jameel suka ci ɗan waken tare da 5alive, bayan sun kammala kai tsaye ɗakinsu suka wuce tare da watsa ruwa, kana suka sake shiryawa tare da feshe jikinsu da turaraku masu daɗin ƙamshi.

    Cikin nutsuwa suka fito aharabar gidan suka samu Innayi da Asma’u sun fito buɗe bayan motor sukayi suka shiga sannan Moddibo ya shiga mazaunin Driver yayin da M Jameel yashiga gefen mai zaman banza, kai tsaye masallacin suka nufa har suka isa ƙira’a na tashi amotar suna parking Innayi da Asma’u suka shiga sashen mata suka ma suka ƙara sa sashen su.

     

    Yau ma kamar kullum gaba ɗaya cikin masallacin da harabar sa cike yake da ɗumbin jama’a cikin tsantsar nutsuwar daya zame musu jiki suka nufi wajen zamansu cikin sanyi mai cike da kamala da kuma kamun kai Moddibo ya ajiye System ɗin sa kana ya zauna tare da ɗan jingina bayansa da  jikin kujeran ya lumshe Idanunsa tare da motsa laɓɓansa alamar tasbihi Shikuwa M Jameel zaman microphone da aka dasa masa  ya gyara tare da buɗe System ɗin sa Lokaci ɗaya cikin masallacin ya gauraye da  ƙamshin sanyayyan turaren su yayin da hasken Fararen glob ɗin ya haskaka hasken farin fuskarsu na fitar da sheƙin annuri yayin da baƙin sajensu ya kwanta luf-luf komai nasu kusan ɗaya yake tamkar tagwaye.

     

    Cikin nutsuwa M Jameel ya lumshe Idanunsa tare da gyara zaman Microphone kana Yayi gyaran murya cikin Sanyayyar muryarsa mai cike da kamala yayi gyaran murya kana yace.

    _“Innalhamdulillah Nahmaduhu Wanastainuhu wanastaghfiru wa’nazubillahi billahi min shuriri anfusna wamin sayyi ati a’amalina manyah dillahu fala hadiyala waman yudil fala mudillalah Wa’ash hadu Allah ilahalillahu wahdahu lasharika Wa’ash hadu anna Muhammadu Abduhu warasulu Ya Ayyuhal lazina amanut taƙullaha haƙƙu tuƙatihi wala tamu tunna illah wa’antum muslimun Ya ayyuhan nasu taƙu rabbakummalazi halaƙakum min nafsi wahida wahalaƙa minha zaujuha wabassa min huma rijalan kasiran wa Nisa’a wattaƙullahal lazi tasa aluna bihi wal arhama innalaha kana bikum raƙiba, Amma ba’ad faya Ikhwatul musulmi Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu”_.

     

    A tare jama’ar dake cikin masallacin suka amsa da.

    “Wa’alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.

    A hankali M Jameel ya fesar da sassayan numfashi tare da lumshe idanunsa kana a hankali yace.

    “A yau muna sha huɗu ga watan Ramadan a cigaba da tafsirin Alkur’ani mai girma da muke acikin masallacin mai Martaba sarki Bashiru acikin Suratu An-Nisa’i ayau zamu tashi akan aya ta Cassa’in da huɗu wala Allah kuma bazai wuce da biyar zamu tsaya ba, sai kuma shekara mai zuwa idan Allah ya bamu aron rai da lfyar”.

    Sai kuma ya sauƙe numfashi kana ya cigaba da cewa.

    “Tun daga kan aya na cassa’in da biyu muka shiga babi akan kashe ran mumini, da kuma hakkin ran Muminai,  ayau Insha Allah zamu cigaba, amman kafin nan zamuyi duba i zuwa kan dukkan ayoyin Alkur’ani dake mgna kan ran muminai”.

    A hankali ya buɗe kwayar idanunsa, sabida jin yadda masallacin ya cika da kabbara.

    Gyara system ɗinshi yayi kana yace.

    “Insha Allah ayau Aramma zai zaƙulo mana Ayoyin da Ubangiji yayi magana akan hakkin kashe ran mumini, domin tunatar wa da kuma jan hankali da kuma fito da darajar ran ɗan Adam Dan kiyaye lalacewar zamani da kuma tunatar da hakkin ran musulmi amatsayin ba komai ba”.

    Cikin yanayin kamala ya juya tare da maida kallonsa kan Modibbo  da idanunsa ke lumshe ajiyar zuciya sauƙe  kana yace.

    “Aramma bamu ayoyin da Ubangiji yayi magana akan kashe ran mumini”.

    Anutse Moddibo ya gyara zamansa tare da ɗan ture system ɗin sa gefe kana yayi gyaran murya cikin sanyayyar sautin muryarsa ya fara kamar haka.

    Surah Al-ma’idah Aya 32

    مِنْ أَجْلِ ذَٰلِكَ كَتَبْنَا عَلَىٰ بَنِي إِسْرَائِيلَ أَنَّهُ مَن قَتَلَ نَفْسًا بِغَيْرِ نَفْسٍ أَوْ فَسَادٍ فِي الْأَرْضِ فَكَأَنَّمَا قَتَلَ النَّاسَ جَمِيعًا

    Ya ƙare jan karshen ayar da fesar numfashinsa da ya riƙe domin fidda cikekken haƙin ko wanne harafi,

    Yayin da Al’ummar Annabi dake cike a masallacin kuwa, sukayi sit suna masu samun cikekkiyar nitsuwa ta mu’ijizan jin karatun Alqur’ani mai girma kenan.

    M Jameel kuwa cike da raunin murya ya fara fassara ayar Allah madaukakin sarki nacewa-:

    “Sakamakon haka ne muka wajabta akan ‘ya’yan Isara’ila cewa, duk wanda ya kashe wata Rai ba tare da ita Rai ɗin ta kashe wata ba, ko kuma yayi ɓarna a kan ƙasa (ta’addanci, Fashi da makami etc) toh kamar ya kashe mutane ne gaba ɗaya na Duniya kuma ubangiji zai hukunta shi dai-dai da laifinsa”.

    Shiru masallacin yayi baki ɗaya, kowa jiki nai a mace, yayinda manyan dottaɓai dake ciki kuwa, suka zuba M Jameel da Modibbo ido suna nazartan yadda akayi akalar tasirin ya sauya daga kan Suratu An-Nisa’i ya koma kan duk ayar da ke mgn kan kisan kai.

    Shi kuwa M Jameel juyowa yayi ya kalli Modibbo tare  cewa.

    Aramma koma cikin suratul Al-ma’idah akwai ayar da Allah ke mgn kan rayuka”.

    Cike da ƙwarewa da cikekkiyar hadda mai ɗauke da kaifin basira, Modibbo ya lumshe idanunsa da yakeji suna cika da rauni cike da zaƙin murya ƙira’a mai sa nitsuwa ya kawo ayar

    Surah Al-ma’idah Aya 33 إِنَّمَا جَزَاءُ الَّذِينَ يُحَارِبُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ وَيَسْعَوْنَ فِي الْأَرْضِ فَسَادًا أَن يُقَتَّلُوا أَوْ يُصَلَّبُوا أَوْ تُقَطَّعَ أَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُم مِّنْ خِلَافٍ أَوْ يُنفَوْا مِنَ الْأَرْضِ.

    Cike da nitsuwa ya dire ƙarshen ayar,

    M Jameel kuwa gyara zamansa yayi tare da fara fashin baƙin.

    “Allah madaukakin sarki nacewa-:

    Lallai sakamakon waɗanda suke yaƙar Allah da Manzo nai, kuma suke yaɗa ɓarna a doron ƙasa (ta’addanci, Fashi, ƙwamushe Garkuwa Da mutane etc), shine a kashe su, ko a giciye su”.

    Sai kuma ya fesar da sassayan numfashi tare da lumshe idanunsa wanda tuni suke sheƙin ruwan hawaye, murya cike da rauni yaci gaba da cewa.

    “Ko a yanke Hannayen su da Ƙafafuwan su a saɓani (hannun hagu da ƙafar dama, ko kuma Hannun dama da ƙafar Hagu), ko kuma a kore su daga Garin.”.

    Zuwa yanzu shar-shar hawayensa ke kwaranya yayinda tuni muryarsa ke rawa, haka yasa da yawa mutanen suke zubda hawaye.

    Haka dai Modibbo ya rinƙa zaƙulo dukkan ayoyin Alkur’ani dake mgna kan ran mumini, M Jameel na fassarawa, yayinda gaba ɗaya zuƙata  jama’ar masallacin ya cika da rauni.

    Kasan cewar gobe ne, Modibbo da M Jameel ɗin zasu wuce ƙasa mai tsarki, damin yin Umrah Ramadan, yasa dole a ranar aka rufe tafsir ɗin. Bayan jero Addu’o’in wa al’ummar musulmi dama kasa baki ɗaya.

     

    Washe gari ranar 15 ga watan Ramadan misalin ƙarfe tara na dara dai jirgi su Modibbo ya tashi daga cikin Taraba zuwa ƙasa mai tsarki…!

     

     

     

    Daga yauwa ɗin nan Laraba mun gama free page, in kina son ci gaban littafin SAKAYYAH to ki biya ki karanta cikin aminci. Littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Ki biya ki karanta ba haƙƙin kowa a kanki.

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 1

    Sakayyah 1

     

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️

     

    بسم لله الر حمن الر حيم…

    2:03 Pm.

    Friday 4 February 2022.

     

    *SAKAYYAH*

    *GARKUWA SABON SALO*

    Book One, page 1

    NA

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE*

     

    *Komai na rayuwa sai Allah ya nufa, kugafa  Time and Date din da na fara rubata littafin nan amman sai Allah ya bani ikon fara sakinshi.*

     

     

    Wannan littafin nawa mai suna FATTANAH kirkirerren labarine, Amman akwai wasu abubuwan dama da sun faru da gasken gaske, banyi da wata ko waniba, Hakkin mallakarsa nawane AYSHA ALIYU GARKUWA, ban aminceba! ban lamunceba!! ban yardaba!!! ayimin amfani da labarin littafina tako wacce sigaba, har sai in an nemi izinina an samu sahalewata, sabida haka ga number ta 09097853276 kafin ayi komai a nemi sahalewata, komai yafi daɗi cikin mutuntaka zama lfy yafi zama ɗan Sarki!!!..

     

    *Yah Allah ka bani ikon rubuta al’khairai da abinda zai amfani al’ummar fiyeyyen halinta, Ya Allah kayi riƙo da hannayena, tunanina, idona, yatsuna, nazarina, ka hanani samun damar rubuta duk wani abin ƙi da zai zamewa al’ummar musulman masifa ko ƙazanta ko bata tarbiyya, ya Allah ka bani ikon tunasarwa da jan kunne da jan hankali ih zuwa ga nasarar mai tawakkali da imani da riƙo da ibada, Ya Allah ka nuna min ƙarshen littafin nan lfy kamar yadda ka nuna min forkonsa Lfy dani da iyayena ƴaƴana, yayuna, ƙannena, da maƙota makaranta na masu biyana kafin su karanta da masu karanta na sata da dukkan musulmai ya Allah ka nuna mana forkonsa da ƙarshensa lfy kayiwa rayuwarmu data ƴaƴan mu al’barka ka shirya mana ahlinmu ka bawa yayanmu mata maza na gari, mazan ka basu mata na gari, aurarru ka basu zaman lfy da zuri’a ta gari ka tsare mana tarbiyar yaranmu bisa tafarkin dai-dai.  Ya Allah kayi mana rufin asiri duniya da ƙiyama, ya rabbil izzati ka dubi bayinka masu buƙatan haihuwa da aure da idanunka masu rahama ka basu masu albarka, marasa lfy Allah ka basu lfy masu juna biyu Rabbi ka sauƙesu lfy masu fama da matsar babu da bashi ya Allah ka yalwata masu ka basu arziƙi mai albarka la basu ikon biyan bashi, Ya Allah ƴaƴan musulmai da tatbiyarsu ke a gurɓace Allah ka shiryesu. Ya Allah ka kawo mana sauƙin wannan zadar rayuwar, ka magance mana fitintinun dake damun ƙasarmu, mahajjatsnmu kasa sunyi hajji Mabruk. al’farmar Annabi da al’ƙur’ani, ya Ubangijin talikai ka jiƙanmu ka yafe mana kurarenmu kayi mana Kekkyawar ƙarshe kasa mucika da kalmar shahada yayin barinmu duniya ka sadamu da mala’ikun rahama masu zaran rai salamun salaman. Yah hayyu ya ƙayyum birahamatika astaƙisu ka jiƙan mahaifiyata Fatima (Deddena) ka sanyaya mata makwanci ta ka haskaka mata ƙabarinta ka yelwata matashi  ya Allah kasa tana cikin dausayin jannatul firdausi ya ubangijin kasa can yafi mata nan, ya Allah ka bamu haƙurin da juriyan rashinta. Ya Allah kai mata rahama al’farmar Annabi da al’ƙur’ani🙏🏻😭😭😭*

     

    ~Aisha Alto, Mom Bobo, kune wanɗa nake ganin kamar kunsan ciwon da nakeji a raina a duk sanda na tuna banda mahaifiya, domin kusan lokaci daya muka rasa iyayenmu. Allah yayi musu rahama yasa sun huta, ina tunawa a lokacin nafi son yin mgn daku fiye da kowa a social media, domin gani nake kun san yadda nakeji a zuciyata, Aisha Alto addu’o’in da kikeyi min dani da mahaifiyata yasa nakejin ke ta dabance mom bobo kuwa munsha kokawa tare, mu rasa mai lallashi wani tsakaninmu~

     

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine 1k ne kacal wannan Free page, yar uwata ki biya ki karanta abinki cikin Salamah 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. In baki da account zaki iya bada a P.O.S ki Basu 100 na su turo 900 wasuma 50 suke amsa, ko kuma ki sayi katin Mtn sai ki copy number’s ɗin katin ki turo min ta WHATSAPP. Banda V.T.U. dan Allah.*

     

     

    A hankali ta turo ƙofar ɗakin nata, cike da jin nitsuwa da salamar, sanin ta yanke baccinta ne ta tashi cikin talatainin daren, domin neman aminci da yardar ubangijinta daya halincceta ya bata rai da lfy, cikin rashin tsoron da ko yaushe in ta tashi tsakiyar dare, Allah ke yaye matashi, duk da kasancewar makaken gidane bila haddin wanda ke kewaye da tsirrai, kana ga wutsiyar kogin Gembulan na jihar Taraba da yayiwa gidan zanen harafi C, yayinda kuwa su biyu ne rak suke rayuwa a cikin ƙaton gidan.

    Koda yake tazarar dake tsakanin ɗakinta da sade ɗin jikanta Modibbo tazarace mai yawan gaske, sai dai suna raya gidan da Ambaton Allah a koda yaushe, shiyasa ubangiji yake saukar musu da cikekkiyar nitsuwa salama.

     

    Numfashin ta fesar a hankali tare da gyara ɗaurin zaninta,  kana ta gyara riƙon da tayiwa yar butar dake hannunta.

     

    Ido ta lumshe tare da buɗe su a hankali, sabida wani irin sassayan iska mai masifar daɗi da ratsa jiki da taji yana ratsata da sakar mata wani irin nitsuwa, salama, da farin ciki.

    Juyowa tayi ta kalli yamma sabida ganin wata ta faɗi alamun dare ya tsala, domin watan tayi kwana goma sha ɗaya ne, faɗawanta ke nuni da biyun dare ko ɗaya da rabine.

    Kai ta ɗan juyo gabas ta kalli ƙofar safe ɗin Moddibo wanda yake can nesa da ita sosai, yayinda wasu sassayan fulawowi yayiwa ko ina na gidan ƙawanya.

     

    Tsarin ginin gidan tsarine, wanda ko a ƙasashen turawa na musamman ne,

    Ƙaton gidane mai yalwar fili.

    Daga can bakin gate ɗin gidan filine mai girma wanda zai iya ɗaukar motoci shida ba tare da wata ta gogi wata ba, ko matsi wataba, ɗakine mai ɗan girma a bakin gate ɗin wanda ke haɗe da bayi a ciki, da yar baranda alamun ɗakin mai gadi, saidai babu kowa a ciki.

    Daga gefe kuwa watsu tsala-tsalan bishiyoyin na mijin gwanɗa ne masu masifar tsawo da ganye mai duhu a can sama sune suke jere reras a jikin katangar gidan baki ɗaya, daga ƙasansu kuma, wasu tsirran fulawowi ne masu masifar kyau da sanyi masu collor’s blue,  red, and yellow.

    Tsakanin farfajiyar gidan da can cikin gidan kuma, akwai wani katanga a tsakiyar da kuma ɗan madaidacin gate shima ɗin mota zai iya wucewa ta nan,

    Cikin katangar shima zagaye yake da bishiyoyin dabino ta wajen ta cikin kuma in bishiyoyin mangoro ne guda biyu sai daya gefen kuma na goiba,  ne da kuma cabɓulle (Tsada) akwai fili ta gefen hagu, inda motoci biyu zasu iya tsayawa a wurin.

    Sai gefen dama kuma, wani ɗan siririn hanya ne, wanda fulawowi ne yazama kamar katangar wurin, tafiya kaɗan zakayi ka riski part din Moddibo, irin ginin nanne mai tudu, duk da bawai bene bane amman ginin a sama sosai yake, forko daga wurin baranɗace mai girma, da tudu wacce ke malale da tayis mai masifar sheƙi, a  bakin barandar anyi wasu steps guda bakwai masu faɗi, kafin hawa barandar,

    A gefen dama da hagunsa kuwa wasu fararen ƙarafun silver ne masu kyau sukayiwa barandar garkuwa, a ƙasansu kuwa, wasu. Tukwanen ƙasane masu tsirran fulawowi masu masifar kyau da ƙamshi, kana a kan ko wanne step akwai tukanen a gefen hagu da daman a jere, guda bakwai-bakwai kenan.

     

    In ka gama haurawa saman barandar kuwa ka juyo ka kalli bayanka ras zaka hango tekun Gembilan kwance a can, da tsirran bakin Kogin.

    A can bayan Part ɗin nashi kuwa wani tamfatsetsen garding ne mai masifar kyau da ƙamshi, sai wani tabkin wanka mai kyau kujeru guda bibbiyu a kusurwowin alƙibila, sai kuma gado a gefen dama da hagunsa,

    Cikin Part ɗin nasa kuwa, wani tamfatsetsen parlour ne mai kyan tsarin ƙasaitattun kujeru da labulaye da kayan wuta, komai na ciki farine tas,

    tambarin shaidar tsananin  tsabtar ma-mallakin wurin kenan, sai ɗan ratsin sky blue, wanda hakan yasa in ka shiga falo sai kayi zaton a sararin samaniya kake shawagi.

    Sai dinning area, da kuma kitchen, sai wani yalwataccen corridor’n wanda ke gefen dama da hagu ko wanne bedroom ɗaya ne a ciki, sai can mashigar falon nanma akwai wani ɗan madaidaicin bedroom.

     

    Hatta cikin falon kuwa kewaye yake da fulawowi, shaidar ma-mallakin wurin masoyin sirraine da sanyi da kamshi window palon irin manyan nanne har kusan ƙasa, haka yasa yana iya hango bakin tekun daga cikin palonshi.

     

    Daga Part ɗin nashi kuwa gefen hagu akwai wata hanyar mai kewaye da tsirrai, wacce ke sadashi da can cikin gidan.

    inda ɗaki ɗaya ne rak, na kakarsa Innayi wacce tace ya isheta rayuwar duniya.

    Sai kuma kitchen nata a gefe mai tsarin gargajiya, kana da bayan gidanta can gefe, domin sam taƙi yarda ayi mata bathroom a cikin ɗaki, acewarta kada santsin tayis ya ƙaryata, dole haka Modibbo ya haƙura da tsarinta komai na gargajiya, hatta gadonta taƙi a sauya mata.

    Sai dai ta amince da tsarinsa na zageyesu da tsirran shuke-shukensa da zuba mata tattausan Turkey carpet mai masifar taushi, tsarin dakin nata komai ya fito kamar na gidan sarakai shuke-shiku kuwa ba dama.

    Daga can gefen hagun side nashi, wani wurine mai ɗan tudu wanda akayiwa rumfa irin ta gargajiya rumfar bunu, gefenta zagaye, da tsirran, cikinta kuwa wasu tsala-tsalan kujerune masu masifar kyau guda hudu da table a tsakiyar su, sai ɗan dandamali na al’adar mutanen Gembilan wanda suke hura wuta a ciki sabida rage tsananin sanyin da ake tsula musu.

     

    ALLAH kuma ya yelwata hannunsa da al’barka duk abinda ya shuka sai ya tsiro a yalwace.

    (Moddibo kenan)

     

    Numfashi Innayin ta sauƙe lokacin da ta gama ƙarewa farfajiyar gidan da lukkunan gidan kallo,

    duk da ba hasken farin wata, babu kuma na taurari sosai, sakamakon hadarin gajumaren da yayiwa sararin samaniya ƙawanya.

     

    Juyawa tayi ta nufi, ɗan bayan gidanta dake, nan gefenta kaɗan, tana maiyin taku cikin yanayin tsufar da ya cinmata, tare kuma da taka tsantsan gudun kada santsin simintin dake malale a farfajiyar sashin nata ya kadata.

     

     

    A bakin ƙofar bayin ta ɗan tsaya tare da yin, addu’a shiga bayin.

    “Allahumma inni’aauzubika minal kuɓsi wal kaba ihsi”.

    Kamar yadda Moddibo ke nusar da ita mahimmancin addu’a ako wanne lokacin.

     

    Bayan ta fito ne, da addu’a a bakinta, ta zauna bisa, wani dutse mai kyau dake bakin barandar ɗakinta, ta fuskanci gabas.

    Tare da fara al’wala.

     

    A can side ɗin Moddibo kuwa, kwance yake, harshensa jiƙe da ambaton Allah, duk da cikin bacci yake.

    Saidai baccin, ba baccine kamar na kowa ba, domin bacci yake cikin wani irin yanayin daya gaza tantancewa, shi ba bacci ba, kuma ba ido biyu ba, ba kuma mafarkiba ba kuma zahiri ba, ba kuma a sumeba wasu abubuwan da lokuta da dama yana riskarsu cikin bancinsa yake fuskantar su.

     

    Ita kuwa Innayi a hankali ta gyara zamanta, tare da juyowa ta kalli bayanta, da sauri sabida wani irin haske da taga ya gilmawa ganinta, sai kuma tayi saurin juyowa gabanta ta, kalli gabas saitin ɗakin Moddibo domin a zatonta ko an dawo da wutar nepa ne.

    Ga mamakinta kuwa, babu alamun hasken wutan nefan sai wani irin sanyi mai ratsa jiki.

    Haka nan taji wani yanayi na rufeta,

    wanda yafi kama da tsoro abinda bata taɓa fuskarta sa acikin gidanba duk duhun dare.

     

    Hakan yasa tayi saurin sunkuyar da kanta taci, gaba da yin al’wa’ar, hannunta ta wonken, kana ta ciko tafin hannunta na dama da ruwa, zata kai bakinta domin kuskuran baki kenan.

    Wani irin saurin ɗago kanta tayi ta kalli gabanta, sabida ganin wani irin masifeffen haske mai firgitarwa da taga ya haska illahirin duniyar har hasken yana haska cikin ruwan dake tafin hannunta.

    Cike da tsoro ta zubda ruwan tare, da juyawa ta kalli.

    Gabas da yamma Kudu da Arewa.

    Babu mutun ba dalilinsa, babu kuma alamun ta inda hasken ke fitowa.

    Kana kuma ga kuma hasken dake tsananta.

     

    Da wata sassayan iska mai ratsa jiki da sanyaya zuciya.

    Wacce tasa Moddibo gyara kwanciyarsa tare da ci gaba da wani irin bacci mai mayataccen daɗi da yaji ya dannesa da kuma shigo masa da wasu sabbin ababen gani a idanniyansa, yayinda harshensa kuwa ke nanata addu’o’in masu tarin yawa.

     

    Yayinda ita kuwa Innayi, wani irin tsuma jikinta ya farayi lokacin da taga gaba ɗaya duniyar ta ɗauki wani irin mashahurin haske mai kyan gani.

    Wanda ta rasa ta ina yake fitowa.

    “Innalillahi wa innailaihi raji’un hasbunallahiwani’imanwakil”.

    Ta fara maimaita cikin firgici lokacin da ta ɗago kanta, ta kalli sararin samaniya.

    Wani irin kerma da makerketa  mai cike da tsananin tashin hankali, firgici, tsoro, da karkarwa jikinta ya farayi, sabida yadda taga ubangijin talikai, yana wanzar da ikonsa da buwayarsa a sararin samaniya.

    Wasu irin masifaffun hawaye masu zafi wanda irinsu kan tsinkowa ɗan Adam lokacin da yaga tsananin abin tsoro da shiga firgici da ƙudurar Allah.

    Kar-kar haka jikinta yake rawa, ganin yadda taurari.

    Suke fizgowa sunayin wani irin haske mai kashe idanun ɗan adam, wanda sune take ganin duk sun cika sararin samaniya da haske tamkar rana.

    “Ya hayyu ya ƙayyum birahamatika astaƙisu, ya Salam, innalillahi wa innailaihi raji’un, la haulawa ƙuwta illabillahil aliyul azeem”.

    Sune tasbihai da furucan da ubangijin ya bata ikon furtawa, lokacin da ta fara ganin taurarin sunayin ƙasa tamkar zasu faɗo, ƙasa domin gani take kamar sai sunzo har ƙasa sosai kamar zasu taɓo rufin kwanon ɗakin Modibbo, sai kuma taga ubangijin ya janyesu sun koma sama da azaban sauri tare da tartsatsin haske mai kyan gani.

     

    Fadin halin tsoro ko tashin hankali ko firgici da ɗimuwar da take ciki ya zarta zaton mai zato, ya wuce tunanin mai tunani ya shallake nazarin mai nazari, wasu irin wahaye ne ke kwaranyo mata.

    Yayinda ta koma baya ta jingina bayanta da jikin filan barandar ɗakinta dake bayanta, ta jingina kanta tana kallon sama.

    Tare da fara nanata kalmar shahada.

    Domin ta gama sallamarwa cewa, lokacin ta yayi, ma’ana mutuwa zatayi.

    “La hailahaillahu Muhammadu Rasulullahi sallahu alaihi Wasallama”.

    Shi ta fara maimaitawa can ƙasan maƙoshinta domin.

    Komai na jikinta ya fara tsayawa, sabida azabebben tsoron daya rufeta da cikekken imanin kaɗaita rabbissamawati wal ardi zuwa yanzu tama fara ɗimautan shin anyama kuwa a raye take?.

     

    A ƙalla 30 minute ubangijin talikai na wanzar da ikonsa! Da kuma, buwayarsa!! Can kuma sai ta fara ganin gaba ɗaya duhu na meye hasken.

    Duhu mai cike da sassayan iska.

    Wani irin tsorone ya kuma rufeta wanda ya diro mata da zazzafan zazzaɓi mai haɗe da masifeffen ciwon kai.

    Wanda ya tilasta mata kife kanta bisa guiwowinta tare da rumtse idanunta tamkar zata liƙesu da juna.

     

    A can cikin masarautar Gembilan   kuwa, Gimbiya Dadu ce, ke kwance bisa tsakiyar gadon ta, wani irin masifeffen mafarki mai tada hankali takeyi.

    Wanda yasata ihun neman ceto, wanda bata saninba har ya fito fili.

    Fitarsan ne, yasa hadimarta saurin shigowa tare, da tadata. Ai kuwa cikin tsananin firgici da tsoro ta farka tana mai karkarwa, lokaci guda kuma zazzafan zazzaɓi ya rufeta.

     

    A nan gidansu Moddibo kuwa.

    A hankali ya fara buɗe idanunsa tare da ambaton Allah.

    Hannunsa yasa bisa  bed side drawer ya jawo wayarsa.

    Gefen wayar ya ɗan taɓa da yatsarsa manuniya, wanda hakan yasata kawo haske har ya haska Kekkyawar fuskarsa mai cike da yalwataccen saje mai sulɓi da ɗan madaidaicin gemun da bazai uwace kamu ɗaya ba yayiwa siraran jajjayen leɓɓansa masu sheƙi ƙawanya.

     

    A hankali ya ziro ƙafafunsa ƙasa, sabida ganin, ƙarfe huɗu saura kwata.

    Bathroom ɗinsa ya nufa.

     

    Yana shiga yayi brush da wonka tare da yin al’wala, kana ya fito.

    Durowarsa ya buɗe yayinda yake amfani da wayar hannunsa wurin haska abin nemansa domin har yanzu babu wuta kasan cewar yanayin garin Gembilan garin mai masifar sanyi mai daɗi, yasa basu cika damuwa da rashin wutar da ƙasartamu ke fama dashi ba.

    Wata tattausar jallabiya fara ya zira kan ƙananan kayan dake cikinsa, tare da jawo farin hula taɓa kaji hadis a kansa, turaren Oud bakhur mai masifar ƙamshi ya fesa, tare da sa hannunsa na dama, ya zaro carbinsa kana ya fito, falonsa, tare da sassarfa ya buɗe ƙofar falon ya fito.

     

    Can cikin gidan ya nufa kamar kullum domin tabbatar da cewa kakartasa ta tashi daga bacci duda yasan kullum bisa sallaya zai sameta to amman hakan baya hanasa zuwa.

     

    Ɗan tsayawa yayi tare da kallon inda Innayi ke zaune har yanzu, yadda kanta ke kife bisa guiwarta sai yayi kamar tana sunkuyene irin zata wonke fuskartan nan.

    Da ɗan sauri ya juya ya nufi bakin gate nasu yana mai tasbihi.

     

     

    Ƙarami ƙofar dake manne jikin gate ɗin ya tura ya fita asalin farfajiyar babban gate din nasu,

    A hankali yake motsa laɓɓan bakinsa, yana taibihai, tare da shaƙar sassayar iskar,

    A hankali ya kuma buɗe ƙaramar kafar  kana ya nufi masallacin jumma’a dake layin nasu wanda yana kallo tamfatsetsen gate din gidan tsohon gidan Alhaji Abubakar Mafindi mahaifi ga Amininsa M Jamil kenan.

     

    Ita kuwa Innayi ƙamshin turarensa ne, da kuma motsinsa ya tabbatar mata shine, so take ta ɗago kanta amman ta gaza, sabida wani irin sarawa da kanta yakeyi.

    Har yanzu sunan Allah take kira, a ƙalla mintuna 20 da fitarsan kafin Allah ya bata ikon motsawa,

    Cikin ƙarfin hali ta ɗago kan nata, lokacin da taji sautin murya Jamil yana kiran assalatu.

     

    Wasu irin zafafan hawaye ne suka tsilalo mata wanda tsananin ciwon kan ne  ya jaza mata su,

    Cikin ƙarfin hali tayi, al’wala tare da yunƙurawa ta mike tsaye tana mai dafe kanta, ta koma, cikin ɗakinta, dai-dai lokacin kuma aka dawo da wuta, yayinda ko ina ya gauraye da haske, sallaya ta shimfiɗa kana ta zira hijabinta, ta fara nafila, jiki na rawan zazzaɓi da kyarman tsoro tanayi tana mamakin shin wai ashe a raye take?…

     

    Ƙarfe bakwai dai-dai na safe.

    Ya shigo gidan, maida ƙofar yayi ya rufe, tare da ɗan tsayawa, tsakiyar gidan, yana mai kallon ƙofar kitchen ɗin, Innayi yana mai nufar cikin gidan.

    Agogon hannunsa ya kalla, tare da ɗan jinjina kai sai kuma ya juya, ya nufi, side ɗinsa, yana shiga bathroom ya wuce, ƙofar ya maida, ya rufe, tare dasa hannunsa ya jawo, tattausan towel, ya ɗaurasa a ƙugunsa bayan ya zare, jallabiyar, da vest, yana ɗauke da towel, sassayan numfashin ya fesar kana ya shiga cikin jaccuzie ɗin.

     

    Cikin nitsuwa yayi wonka fes, ya fito.

    Yana wani irin masifeffen ƙamshi yayinda gargasan jikinsa ya kwanta lib a tattausar farar fatarsa da damshin ruwa,

     

    Wani towel ɗin ya jawo ya ɗaura, kana ya zare na ƙasan, matseshi yayi tare da shanyasa.

    Sannan ya fito yana mai tsane tattausan sumar kansa da ƙaramin towel ɗin.

     

    Gaban dreesin meeror’nsa ya tsaya, ya fara kimtsawa, cikin yanayin nitsuwarsa da rashin yin abu da gaggawa…

     

    Bayan ya gamane ya fito fes yana baza ƙamshi mai masifar daɗin shaƙa, sai wani irin kyalli sajensa keyi, yayinda jajayen lips ɗinsa suke wani irin sheƙi tamkar dai irin yadda lips ɗin jarirai yake sheƙi in sun ɗan laso lips ɗin.

    Wata tattausar jallabiya blue color mai ɗan karen taushi da kyau ne, a jikinsa, tayi cib-cib da ɗan madaidaicin jikinsa, sai kuma fararen takalma half cover masu taushi da ya zira tattausan sawayensa da suke farare ƙal, yayinda dun-duniyar sawun nasa ke sarari.

    Farin hirami ya naɗa a kansa, irin naɗin nan na zamani wanda matasan larabawa keyi,

    Sai wayarshi daya zira a ajihun gaban jallabiyar tasa, wani irin sassayan ƙamshi mai ɗan karen daɗin shaƙa yake zubawa,

    Taku yakeyi cike da kamala, yayinda hannunsa na dama ke riƙe da jakar system nasa.

     

    Cikin yanayinsa na nitsuwa ya ƙara so bakin kitchen ɗin.

    Siraran Idanunsa ya ɗan jujjuya ya kalli tsakiyar gidan baki ɗaya, sai ya kuma ɗan leƙa cikin kitchen din, nan ma babu alamun Innayi.

    Cikin nitsuwa ya kuma juyowa ya nufi ɗakin nata, ganin takalmanta a bakin ƙofar.

    “Assalamu alaikum”. Yayi sallama cikin wata iriyar sassayar muryar mai cike da haiba nitsuwa da kamala.

    Sai kuma yayi saurin shigowa cikin ɗakin.

     

    Ganin Innayi na kwance bisa sallaya babu ko pillown ga kuma karkarwa da jikinta keyi.

    A hankali ya rusuna tare da takwara ƙafarsa ta dama ya zauna kanta ta hagu kuma ya tsaidata, cikin kulawa da tarin so tausayi, ya motsa lips ɗinshi a hankali yace.

    “Yah Salam.

    Innayi! Innayi!! Innayi!!!”. Ya kirata sau uku, ganin bata amsa bane, yasashi manna  tafin hannunsa kan goshinta, wanda hakan ne yasata buɗe kwayar idanunta da sukayi ja.

    Sai kuma ta medasu ta rufesu, sai ga wasu hawayen masu zafi sun kwaranyo mata.

    Jiki na rawa tasa hannunta, ta kamo hannunsa, murya a raunace tace.

    “Aliyu”. Da sauri ya zuba mata idanun tare da tsareta dasu, domin zai iya cewa, wannan shine karo na biyu a rayuwarsa da yaji ta kirasa da asalin sunansa na yanka.

    A hankali yace.

    “Na’am Innayi meke damunki? Meyasa baki kirani kin gaya min baki da lfy ba? Tashi mu tafi asibiti”.

    Ya ƙare mgnar yana mai tallabota ya zaunar da ita.

    Wani dogon numfashi Innayin taja cikin rawan murya tace.

    “Aliyu ka zauna, kaji abinda zan gaya maka”.

    cikin yanayin kulawa a sanyaye yace.

    “A’a muje asibiti tukuna, sai mun dawo”.

    Cikin ɗan ɗaga murya tace.

    “Aliyu ka bari kaji abinda baka saniba.

    Bana son in mutu in barka a nahiyar maraici, bana son in mutu da abinda ni kaɗaice na sani kuma nakeda dama da ikon sanar da kai, idan na mutu a haka ban sanar da kai abinda ke bibiye da muba, nayi maka cuta mafi muni a rayuwarka.

    Aliyu ka bari in sanar da kai abinda Allah ya nuna min a daren jiya”.

    A hankali ya fesar da nannauyan numfashi, sai kuma ya juyo ya kalli ƙofar ɗakin, jiyo Muryar Amininsa mafi ɗan uwa, wato M Jamil yanayin sallama, a hankali yace.

    “Wa alaikassalam J”.

    Ya ƙira Aminin nasa da sunan da duk duniya shi kadai ke kiransa da hakan,

    Ido ya zubawa M Jamil ɗin a hankali tare dayi masa alamun ya shigo da kwayar idanunsa,

    Cikin yanayin sauƙin kai sakin fuska faram-faram Jamil ya sako kansa cikin ɗakin yana mai cewa.

    “Iya innare yau me kika dafa mana ne, dan tun jiya da na dawo ƙasar nan banci komai ba, nace sai abincinki zanci ko na Ummina”.

    Sai kuma yayi shiru tare da matsowa kusa da ita…

     

    Cikin Masarautar Gembilan kuwa.

    Wata Kekkyawar matace yar duma-duma mai kyan shiga da haiba, ke zaune bisa kujera, yayinda System ke gabanta bisa ɗan madaidaicin stool yayinda fuskarta ke manne da wani ɗan farin glass siriri.

    Da alamu typing takeyi.

     

    Kai ta ɗan jinjina tare da juyowa ta kalli dinning area inda hayaniyar yaranta ke tashi.

    Kai ta ɗan jinjina tare da kallon wata yar narkekkiyar matashiya da bazata wuce 14 year’s ba.

    Ido ta zuba mata ganin ta nufota da sauri.

    Hannunta ɗaya.

    Riƙe da school bag da  takalmin sinika da kuma ɗan madaidacin hijabin Uniform ɗin ta.

     

    Da sauri ta rusuna gaban Matar tare da juya mata baya tana cewa.

    “Ayya Momy tubke min kaina, nayi-nayi yaƙi sai na ƙulleshi sai ya sule”.

    Kwaffa tayi tare da cewa.

    “To wai ke kam Khausar yaushe ne zaki iya, tubke gashin kanki”.

    Ta ƙare mgnar tana tattaro suman Khausar din yana mai zamewa,

    Sai kuma ta ɗago kanta ta kalli Ɗan matashin yaron da yanzu ya fito cikin Uniform ɗinsa. Wanda yake iri ɗaya dana jikin wacce aka kira da Khausar.

    Da alamun ya gama shirinsa tsab.

    Cikin tsuke fuska ya watsawa Khausar din harara tare da cewa.

    “Gsky ni zan tafi Ramadan Raudat zomu tafi, kullum ita ke jaza mana yin letting muje aita zanemu kamar bayi.

    Ni wlh da zan samu a rabamun hanya da ita inaso, muna shiga school kamar wasu shaidanu zakaji an fara cewa.

    FATTANAH kuka biyewa ko, duk sai an gama shiga aji  kafin ku iso.”

    Cikin yanayin tsiwa da son girma ta miƙe tsaye tana ɗaure ɗan kwalinta harara ta watsa mishi tare da cewa.

    “Wallahi ka shiga hankalinka dani Haydar in baka dena cemin FATTANAH ba zan fasa maka baki”.

    Dogon tsaki yaja tare da juyawa ya nufi ƙofar falon, yana gyara zaman  net ɗin sa. Tare da cewa.

    “Sai ki gayawa wanda yasa miki sunan, ko kuma ki nitsu ki dena rashin kunya da rawan kai”.

    Cikin ɗan ɗaga murya Momyn nasu tace.

    “Gsky Babana bana son wannan sunan da aka liƙawa Mamana sam bafana son sunan”.

    Da sauri yace.

    “Toh Momy ai ita ta jawa kanta fitinenneyar ce ta gasken gaske,  in dai kinji faɗa to da ita a ciki, in kuma babu ita to zakiji ance ai gulma akayi ta maidawa maishi, wai ita ba’a gulma da ita, itafa tana iya zuwa zuwa ta samu ana faɗa ta shiga tayi kane-kane sai an gama tace wai me dalilin faɗan”.

    Ya ƙare mgnar yana fita.

    Ita kuwa Khausar zama tayi gefen Momynsu tana sa takalmanta da ɗan sassarfa domin yau din ranace ta musamman a wurinta tana cike da ɗokin zuwa makaranta kasancewar yau suka dawo hutu, kuma hutune na canjaza aji da JSS zata tafi SS 1 wanda takega matakin samun encinta ne kenan zata taka, tunda yanzu zata koma aji da matan aure, a islamiyar safe, sai kuma na bokone tacan anan ne babu enci sai randa ta gama sa takalmin ta saka, tana sakin yelwataccen murmushi.

    Yayinda Ramadan da Raudat suke tsaye gefenta.

    Hannu tasa ta kama hannun Raudat tare da cewa.

    “Mu tafi”.

    Da sauri ta juyo ta kalli Momyn nasu tare da kwaɓe fuska jin tana cewa.

    “Ku biya sashin Gimbiya Dadu ku gaidata, bata da lfy”.

    Cikin kwaɓe fuska tace.

    “Momy zamuyi letti muje wannan mai sunan baban naki ya samu damar sawa a azabtar dani”.

    Ta ƙare mgnar cikin son zillewa zuwa sashin Gimbiya Duda, ita kuwa Momy tsuke fuska tayi tare da cewa.

    “Ku biya ku gaisheta da jiki nace ko”.

    Cikin bin umarnin mahaifiyar tata badon tasowa tace.

    “Toh Momy”.

    Daga nan ta kada kan ƙannen nata Duk suka fito.

    Sai kuma tayi sauri ta juyo tare da cewa.

    “Momy mun tafi”.

    Murmushi tayi sanin manufar ta yasa cikin lumshe idanu tace.

    “Allah ya kaiku lfy ya baku Sa’a Allah yasa ki shiga SS 1 da ƙafar dama, Allah ya shirya min ku”.

    Cike da jin daɗi tace.

    “Amin Ya Allah”.

    Kana suka fita.

    Suna fitowa suka samu duk sauran yaran gidanma sun fito.

     

    Kamar haɗin baki kab ɗin su sashin Gimbiya Dadu suka nufa.

    Kai tsaye suka wuce har bedroom ɗin ta domin bata falon.

     

    Su Asiya ce, a gaba ita da sauran ƙannenta,  sai kuma su Khausar din.

     

    Zaune suka sameta bisa tsakiyar gadon mulkinta, mai martaba Lamido Gembilan yana zaune ƙasa bisa carpet, yana haɗa mata tea,

    Cikin tarin biyayya, da sauri suka rusuna baki ɗayansu, kusa haɗa baki sukayi wurin cewa.

    (“Allah saine Abba, noi nɓanɗu Dadu?) Allah ya faranta maka Abba ya jikin Dadu?”.

    Cikin son ahlin nasa ya jinjina masu kai tare da cewa.

    (“Yettore Allah nwodi dama) an godewa Allah da sauƙi”.

    “Allah ntokkin dama”.

    Suka faɗa a tare, cikin tankwashe sawunsa yace.

    “Allah jabu”.

    Amin suka faɗi  baki ɗayansu,

    Yayinda Khausar kuma taketa jan hijabinta, tana mai sunkuyar da kanta ƙasa,

    Allah ya sani bata ƙaunar abinda zai kawo ta gaban Gimbiya Dadu,

    Domin jikinta da nitsuwarta duk rasasu takeyi, sabida wani irin mayataccen kallo mai bada tsoro da tsohuwar ke Binta dashi.

    Kamar koda yaushe kuma hakane, duk da bata da lafiya, amman wani irin masifeffen kallo ta tsare Khausar ɗin dashi har bata jin gaisuwar da jikokin nata keyi mata,

    Cikin taɓe baki Asiya tace.

    “Dadu wannan wanne irin kallo ne? muna gaidaki kinyi shiru?”.

    Jin hakanne yasa  Khausar ɗan ɗago kanta,

    Ai kuwa ido cikin ido sukayi da Dadu.

    Da sauri ta motsa lips ɗin ta a hankali tare da cewa.

    “Innalillahi wa innailaihi raji’un”.

    Sabida wani irin tashi da tsikar jikinta ya farayi, yam-yam.

    Ita kuwa Dadu har lau bata cire idanunta a kantaba,

    Haydar ne ya ɗan miƙa tsaye tare da kamo hannun Ramadan da Raudat yace.

    “Dadu Allah ya sauwaƙa, zamu tafi school kada muyi letti Raudat muje”.

    Abin mamaki har lau Dadu batama san anayi mata mgna ba, bare ta amsa musu, gaba ɗaya nitsuwarta da kallonta yana kan Khausar….!

     

    Lamido kuwa ido ya zubawa maifiyar tasa, cike da mamakin lamarinta, ya zama  ana kallon kalo, ita tana kallon Khausar data kasa koda ƙwaƙƙwaran motsi shi kuwa yana kallonta.

    Asiya kuwa itama miƙeqa tayi tare da kaɗa kan ƙannenta tayi gaba Amina ce ƙanwar Asiya mai binta ta ɗan miƙa tare da cewa,

    “Uhum”. ta fice

    Ya zama daga Dadu sai Lamido sai Khausar.

     

    Cikin wani irin yanayi da Khausar din keji ta kuma kallon Dadu, wacce zuwa yanzu ta saki laɓen bakinta na ƙasa, wani irin  yawu mai cike da mayataccen kwaɗayi ne ya tsinko mata, har yana ɗan sauƙowa kan lips ɗin ta.

    Cikin sauri Khausar ta miƙe jin Lamido yana cewa.

    “Mamana tashi ku tafi”.

    Ai kafin ma ya rufe bakinsa, tuni ta fita tana mai cewa.

    “Toh Abba”.

    Ita kuwa Dadu wani nannauyan numfashin ta sauƙe tare da juyowa takalli ɗan nata, dake miƙa mata cup ɗin tea.

    Cikin diriricewa tace.

    “A’a bana buƙatar abin zaƙi, a kawo min abu mai yaji-yaji”.

    Cike da biyayya yace.

    “Toh”.

    Kana ya miƙe ya  fita.

     

    Tuni su Khausar kuwa sun shiga school bos ɗinsu,

    Amina ce ƙanwar Asiya mai binta ta kalli Ramadan dake cewa.

    “Kalli fa 8:13 na tabbatar yauma zamu zanu”.

    Cikin sanyi tace.

    “Mu dai Allah ya rufa mana asiri daga SS 2 akwai matan aure da yawa a ciki, so ba batun duka a side ɗin mu.

    Kuma ma duk bama saɓa doka cikin nitsuwa da tarbiyyar mu muke, ko nayi litting nasan za’ayi min uzuri.

    Cike da jin daɗi, Khausar tace.

    “Nima dai Allah ya yaye min masifa da cin zalin su Moddibo tunda yau dai  zan tafi Ss 1 ɗin, da ba duka ba zagi, wlh inci karena babu babbaka”.

    Taɓe baki Haydar yayi tare da cewa.

    “Mu gefen maza, babu manya, duk yarane, manyan da dare suke zuwa, shiyasa babu roggomi”.

    Asiya ce ta kalli Khausar cikin yanayin son yarinyar tare da cewa.

    “Ai wlh ke dai in baki nitsuwa ba ko jami’a kikaje in dai Moddibo na cikin malamanku, na tabbatar zai san matakin da zai ɗauka a kanki.

    Sannan ma da kike batun  kin tafi Ss1 akwai matan aure, kin mance cewa, na safene, na islami.

    Akwai na rana zuwa biyar bokone, kuma kuna tare da moddibo.”

    Kwaffa tayi tare da cewa.

    “Kai na shiga ukuna wlh”..

     

    Anan gefen su Modibbo ku, fir innayi taki aje asibitin. Su kuna su kasa fahimtar ta, gani suke zafin zazzaɓin maleria ne yake son sata surutai shiyasa suke hanata mgn sukayi ta mata addu’o’i hardai ta ɗan fara samun nitsuwa har bacci ya ɗan sureta.

    Gani  ta ɗan rumtsane yasa suka tafi wurin Ummin M Jameel suka ɗauko Ummin dan tazo ta ɗan kula da ita.

     

    Suna isa bakin gate, ba tare da sun shigaba, Ummin ta kalli M Jamil da yayi saurin fitowa bayan yayi parking marfin motar ya buɗe, mata cikin tsananin son mahaifiyar tasa, yace.

    “Bismillah Ummi fito ki shiga  wurin Innayinki, domin mu dai yau mun gaza gane kanta, da alamun Ita dai dare ɗaya gigin tsufa ya sauƙo mata”.

    Ɗan buge ƙeyarsa tayi tare da ciwa.

    “Tsufa kan zai cimma taka uwar mafa, kawai dai inaga zafin zazzaɓine kusan wasu lokutan yanasa yara surutai, to ita kuma girma yazo dole in ciwon yayi zafi zatayi kamar na yara”.

     

    Juyowa tayi ta kalli Moddibo daya jingina kansa jikin kujerar gaban motar gefen mai zaman banza,

    Cikin sanyin murya yace.

    “Uhmmmm Ummi waifa cewa tai taga taurari suna sauƙowa ƙasa har kamar zasu taɓa rufin side nan, anya kuwa Ummi wannan zazzaɓi ne?”.

    Sai kuma ya ɗan fesar da numfashi tare da lumshe idanunsa cikin alamun nazari yace.

    “Ina tsoron kada fa matsalar ƙwaƙwalwa ce, nayi nayi muje asibiti kuma taƙi.”

    Ya dire mgn tare haɗa kan yatsun hannunsa.

    Jamil ne yaci gaba da cewa.

    “Saida fa Moddibo yayi ta mata tofi kafin muka samu tayi bacci har muka fito ɗin.”

    Cikin kulawa Ummi tace.

    “In sha Allah babu komai, bari in shiga, ku kuje”.

    To Jamil yace kana ya shiga mota, ita kuma tayi cikin gidan.

     

    A hankali ya miƙa dalleliyar motarsa ƙirar BMW kan shimfiɗeɗen titin,

    Yana tafiyar hawainiya, murmushin yayi ganin kallon da Moddibo yake masa.

    “Sanin yau za’a dawo makaranta ne, yasa nayi ƙoƙarin dawowa baro Marrocco, duk da akwai ayyukan da ban gama dasu a company’nba,”.

    Cewar M Jamil shi kuwa Moddibo kai ya jinjina alamun yana jinsa, shi kuwa M Jamil gudu ya ɗan ƙara tare da ci gaba da mgn dan yasan ba lallai ne Moddibo ya amsa mishi da bakiba, inda sabo ya saba, kuma shi yasan cewa body language al’adane ko ɗabi’a koma yace halittar Moddibo ne.

    Juyowa yayi ya kalleshi tare da cewa.

    “Na zaƙu muje makarantar nan, dan nasan zaiyi kyau sosai a tsarin gyarashi da akayi”.

    Cikin ɗan ƙwaɓe fuska yace.

    “In an gama gyaran ba”.

    Da sauri M Jamil yace.

    “Kamar yaya za’a gama mana”.

    Juyowa yayi ya ɗan kalli M Jamil ta gefen ido kana a takaice yace.

    “Toh ba’a gaman ba”.

    Cikin sauri M Jamil yace.

    “A.S da gaske ba’a gama ba?”.

    A.S shine sunan da yake kiran Moddibo dashi kuma su biyu kaɗai suka san ma’anar sai kuma abokan karatunsu.

    Shi kuwa Modibbo littafin dake gaban motar ya ɗauka tare da buɗe wa kana yace.

    “Dama tun lokacin da za’a bada hutun na faɗa bazai isa a gama gyaran school ɗin ba, musamman da ya zama an ƙara yawan class, kana ga gina hall din da akace za’ayi, kuma dole aikin bazaiyi guduba sabida Ramadan, tun lokacin nace a ƙara kwanakin hutun, sabida samun isasshen lokacin, wannan  Ba fulatanin yaƙi”.

    Murmushin M Jamil yayi tare da cewa.

    “Toh kai meyasa baka ƙara hutunba, ai da sai ka sanar”.

    Juyowa yayi ya kalleshi bayan hannunsa yasa ya shafa tattausan sajensa tare da cewa.

    “Uhmmmm”.

    Ya san me wannan Uhmmm ɗin take nufi, kai ya jinjina tare da cewa, “Mu dai yan kallone,”.

    Da sauri yace.

    “Nima haka, dan na gaji ko yaushe sai ya kwaɓa abu yazo yana cemin ina mafita”.

    Dai-dai lokacin aka buɗe musu gate din makarantar, Ya Salam.

    Wani irin tsarine da zubi makarantar yake dashi, tsari mai burgewa, yayinda shima makarantar Moddibo ya ƙawatata da tsirrai na kyautata muhalli.

    Tabbas gyara kam da saura ba’a gama shi ba.

    Domin daga woje dai kam an kammala komai amman daga ciki, duk cikin ajujuwan a hargitse yake.

    M Jamil nayin parking, wani kekkyawan dattijo bafulatani ya nufo matar tasu da sauri, bisa alamu dai shine shugaban makarantar domin duk malaman na miƙa gaisuwar garesa cikin mutuntawa.

    “Moddibo! Moddibo!! Moddibo!!!.”

    Jamil ne ya fito yana murmushin tare da cewa.

    “Allah rene,”.

    Da sauri yace.

    “Ina Moddibo”.

    Cikin motar Jamil ya nuna masa, da sauri ya sunkuyo,

    Yayinda shi kuwa Moddibo meda bayansa yayi ya jingina tare da lumshe idanunsa, murmushi Dattijon yayi tare da cewa.

    “Ga ɗalibai duk sun dawo makaranta ta cika maƙil ga sabbin ɗauka, kuma aiki baifi rabi ba, ya zamuyi?”.

    Cikin taɓe baki yace.

    “Allahu a’lamu!”.

    Jamil ne ya juyo ya kalli Malam Ahmad da Malam  Habibullah da suma fitowar su kenan daga can cikin makarantar.

    Shi kuwa Malam Arɗo Umaru mamallakin makarantar kuma .

    Kai ya ɗan dafe tare da cewa.

    “Dan Allah ka fito Moddibo kasan bayanin da zakayi musu, kana ka kara musu kwanakin hutun, tsawon lokacin da kakega za’a iya gama gyaran”.

    Yadda ya dire mgnar da karya wuyane yasa Moddibo fitowa.

    Murmushin sauran malaman sukayi, domin sosai tsufa ya fara cimma Mala Arɗo, zuwa yanzu ya kamata ragamar makarantar ya zama a hannun yara, domin badon Allah yasa Moddibo ke tsara komai na jadawalin abubuwan ciki da wajen makarantar ba, da tuni ta durƙushe, to amman sabida shi da sauran haziƙan malamai da suke da tsananin kula da tarbiyyar yara da sukeyi yasa har yau makarantar bata da na biyu a faɗin birnin Gembila.

    Kusan a tare suka rakaya cikin makarantar.

     

    Yayinda hayanin ɗalibai manya da yara maza da mata, ke tashi.

     

    Juyowa yayi ya kalli Jamil tare da cewa.

    “J kaje masallaci kayi mgn duk mu su haɗu a tsohon halla ɗin mu na sama.”.

    To Jamil yace yana tunanin to me zaice musu,

    Masallacin ya wuce tare da yin sanarwan.

    Nan take kuwa, duk ɗaliban suka haura sama, suka shiga cikin babban hall ɗin nasu wanda yake ƙato sai dai duk da haka yanzu ya musu ƙaramin,.

     

    A gafen mazama suma duk sun haɗu a halla nasu.

     

    Shi kuwa Moddibo office nasa ya wuce.

    Jim kaɗan ya fito, da Lapel Microphone a hannunsa yana saƙalasa a wuyan tattausan jallabiyar jikinsa Malam Ahmad ne ya matso kusa dashi tare da cewa.

    “Zamu jirane ko an ƙara mana hutu”.

    Ɗan murmushin gefen baki yayi tare da cewa.

    “Hutu kuwa sosai ma har na tsawon mako uku za’a ƙara”.

    Cike da murmushi yace.

    “Mu tafi kenan”.

    Kai ya gyaɗa masa tare da cewa.

    “Suma duk yanzu zan kaɗa kansu ko wacce tai gida sai dai muma muna da zama na musamman”.

    Ai kuwa jin haka yasa duk malam suka zauna jiran.

     

    Shi kuwa ya haura saman yana mgn da M Jamil a waya.

     

    “Su maza basu da hayaniya, kawai J ka ɗanyi musu nasiha, kana kace sai bayan  mako uku zasu dawo kafin nan an gama gyara,

    Sai dai masu zuwa hadda suci gaba da zuwa.”

    Cike da gamsuwa M Jamil yace to.

    Kana sukayi sallama.

     

    Dai-dai lokacin kuma  su Khausar suka shiga cikin makarantar,

    Da in ka gani kace a ƙasashen ƙetarene, domin makaranta ce mai zaman kanta, mai cike da haziƙan malamai, duk da sunyi makarar mintuna 20, an bar motarsu ta shiga ne, sabida magiyar da sukayi tayi da kuma girman gidan da suka fito, da bada uzurin motar ta ɗan lalacemusu a hanyane kana da kuma ganin ma yau ba karatun za’ayi ba, hutun za’a kuma ruɓanyawa.

     

    Suna shiga kuwa, ga mamaki su  aka barsu suka shige ba hukuncin komai.

     

    Kana ko wa ya nufi sashin da ajinsa yake.

     

    Da sauri duk suka tsaya jin Malam Habibullah na cewa.

    “Fattanah uwar yan letti yau makarar har ta 20 minute duk da yau aka dawo, duk kuyi sama ana taro a hall”.

    Cikin ɗan tura baki tace.

    “Toh Malam”.

    Yayinda tuni su Asiya kam sun haura har sun shiga hall ɗin.

     

    Da ɗan sassarfa ta fara take steps ɗin da zai sasanta, da hall da yake a sama ganin ita kaɗai ta rage.

     

    Daga corridor’n steps ɗin, ta ɗan lumshe idanu ta, tare da gyara saƙala school bag ɗinta a kafaɗar dama.

    Sabida ƙamshin turarensa ya shaida mata, tabbas tuni ya shiga hall ɗin.

     

    A hankali ta sauƙe numfashin ta tare, da nemo dukkan nitsuwarta.

    Lokacin da ta gama haurowa, sama, da sauri ta tsaya, jikin window dake gab da bakin ƙofar shiga, ido ta lumshe tare da buɗewa a hankali kana ta kutsa kai cikin hall din da a kalla mutane ciki sun kai ɗari da hamsin, duk da tasan bai taɓa barinta, ta shiga ajiba, muddin ya rigata shiga, to amman kullum sai ta gwada sa’anta musamman yau da yake a hall ne.

    Taku ɗaya tayi ana biyu, ta tsaya, sabida, ganin ya ɗaga mata, tafin hannunsa.

    Cikin yin mui-mui da bakinta tace.

    “Afwan ya mu’allim sayyara…”.

    Da sauri ta ɗan ja da baya ta koma jikin window ganin ya juya baya tare, da gyara ɗan masaƙalin Lapel Microphone dayake saƙale a wuyan jallabiyar jikinsa, sabida tsananin sanyin sautin muryarsa yasa dole sai dashi yake amfani a cikin class, domin ɗalibansa su samu damar jinsa sautinsa ras domin sam baya iya kware muryarsa yayi mgna da ƙarfi haka Allah ya haliccesa da nitsestsiyar sauti to bare a irin taron maƙil da hall ɗin yayi yau.

    Cikin tattausar muryar sa mai cike da sanyi yace.

    “Makfut?”. Cike da  jin daɗin nasihar da yakeyi musu suka amsa da “Na’am”.

    Kai ya jinjina tare da cewa.

    “Ɗeyib!”.

    Sai kuma ya ɗan juyo ya fuskancesu, hakan ya zama, ya ɗan bawa Khausar baya, tattausan sumar ƙeyansa dake kwance lib-lib ta zubawa harara.

    Numfashi mai sanyi taja tare da shaƙa daddaɗan ƙamshin turarensa mai sawa ɗan adam salama.

    Sai kuma tayi ƙasa da kwayar idanunta dugadigin sawunsa, ta zubawa idanu tana ganin yadda sukeyin ja in ya taka sawun, in kuma ya ɗaga sai suyi fari, baki ta ɗan tura sama ta da liƙa ƙeyarshi wani sabon hararan.

     

    Shi kuwa Moddibo a hankali yake taku a gaban ɗaliban nasa, masu biyayya da girmamawa a garesa, cikin tattausan lafazi yace.

    “Falalar zikirai da karatun Alqur’ani , nakeso son in tunasar mana, sabida kididdigar manazarta, ta nuna mana Al’ummar wannan ƙarnin sun samu naƙasun zikiri da   karatun Alqur’ani mai girma, sun maida hankali akan sashin yanar Gizo-gizo fiye da yadda ya kamata,  mu maida hankali kan Al’ƙurani littafin Allah da hadisan Manzon Allah,  mu samman a wannan taki da muke ciki, na shuɗewar Ramadan wanda zaka samu da yawa mutane sun fuskanci aikin al’khairai da bautar ubangiji a cikin watan, da zaran watan ta gabata sai a koma gidan jiya aita sharholiyar duniya.”

    Sai kuma yayi shiru, tare da fesar da numfashi a hankali, kana ya juyo a hankali yace.

    “Mutane da yawa sun mance koma ince wasu basu san me Allah maɗaukakin sarki yace ba  A cikin Suratul Baqara, ayata 152.

    Allah maɗaukakin sarki yace.

    فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُوا لِي وَلَا تَكْفُرُونِ.

    Ma’ana:

    Ku  ambaceni zan ambaceku, ku godemin kada ku butulcemin.”.

    Ya ƙare mgnar da rumtse tafin hannunsa alamun ƙarfafa mgnar, wanda kuma wannan ɗabi’arsace ko ace halittar sace.

    Duk mgnar da yakeyi yana kamantata ko suffantata da tafukan hannunsa like dai yadda manyan sarakuna keyin mgn turawa kuma suka cewa hakan body language, Wanda mafi akasari ɗabi’ar yan jarida ne, in suna mgn.

    Shiru hall ɗin yayi alamun suna fahimta sosai.

    Shi kuwa Moddibo cikin girmama zancen Allah madaukakin sarki yaci gaba da cewa.

    “A dai wannan ƙarni da muke ciki da yawa, suna butulcewa faɗin Allah madaukakin sarki, daga barin ambatonsa, gaba ɗaya shagala tayiwa al’ummar mu ƙawanya, shafukan sada zumunta na yanar Gizo-gizo ya maiye gurbin da yake muhallin Qura’ani ne a wurin wasu musul manmu, sai a wuni a kwana musulmi bai ɗauki Qura’an ya karanta ya duba kyan baƙin da yake haɗawaba,  amman sai ka sameshi awa 14 na awannin 24 na rana yana rungume da wayarsa, ana charting, a  Facebook a koma whatsApp, daga nan a tafi Instagram, sai kuma a murgina a koma twitter sai kuma a rarrafawa zuwa wannan lalataccen kuma kazamin dandalin Tiktok, ayi ta raye-raye da waƙe-waƙe, anaiwa juna cin zarafi, wasu su koma yiwa malamai isgilanci ana yaɗa fasadi da fajirci ana meda ashariya kamar ruwan sha.”

    Ya dire ayar mgnar tare da haɗe kan yatsun hannunsa gaba ɗayansu wuri ɗaya alamun ya dunƙule mgnar kenan bawai ya gamata bane zai tafi sashi mafi muhimmanci ne.

     

    A jikin window a waje kuwa, cikin jujjuya ido Khausar ta raɓa jikin window tare da maida hankalinta baki daya cikin.

    Shi kuwa Moddibo a hankali ya ɗan juyo gefen damansa, jin inda sautin surutu yake ɗan tashi kaɗan.

    Ganin yana kallon sune kuwa yasa,

    Samira Sani yin shiru.

    Cikin nitsu ya kuma cewa.

    “A wata ayar kuwa a cikin suratul Ahzab ayata 41, me Allah maɗaukakin sarki yace mana!???”.

    Ya ƙare mgnar da alamun ayar tambaya, hakan na nufin su ja mishi baƙi yake so, sanin mafiya akasarinsu yan haddansa ne,

    Ji kakeyi, hall din sit kowacce tayi ƙasa da kai, gudun kada ya nuna ta kaɗan daga cikinsu kuma bawai basu sani bane diricewa ne da kwarjininsa ke sasu yin ƙasa da kai.

    Cikin sanyi yace.

    “Na’am Samira Sani”. Da sauri tace.

    “Malam ni?”. Fuskarsa ya  tsuke tare da juyowa ya kalli Asma’u Ahmad dayi mata alama da hannu, tsilli-tsilli tayi da idanu.

    Samira Sani kuwa ganin ya cire ido a kanta ne yasa tayi saurin buɗe Qura’an ɗin ta.

    Dan dubo ayar,

    sai kuma duk suka ɗago kansu suka zuwa Khausar dake jikin  window  idanu,

    jin ta uzi shaitan tare da yin basmalla kana  taja numfashinta tare da lumshe idanu murya cike da tajwed ta fara jan ayar.

    Surah Al-Ahzab aya ta 41:

    يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْرًا كَثِيرًا

    Murmushin mai cike da jin dadin Asma’u Ahmad tayi tare da sauƙe numfashin, FATTANAH ta ɗauki belinsu kamar yadda aka saba, domin in dai batun jane na ƙwaƙwalwa to kwanyar Khausar ta musamman ce.

    Mata da yawa kuma cikin manyan mata kallonta sukeyi cike da sha’awa da jin daɗin zazzaƙar muryarta na kuma ratsa musu kunnuwa.

     

    Shi kuwa Moddibo ba tare da ya juyo ya kalle taba.

    Ya fara kawo musu fassarar ayar.

    “Allah madaukakin sarki yana cewa:

    Yaku waɗanda suka yi imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa.

    Ammato kuma na haƙiƙa bawai kawai kije kiyi karatun Qura’an kara zube ko gatsa-gatsa ba, kuyi karatu kwatankwacin yadda tayi inma kunce juyawa ih zuwa irin nawa da wuya.”

    Cikin sanyi Asma’u Ahmad tace.

    “Malam ai karatun Khausar irin nakane, ba banbanci kawai dai, ita muryar mata kai muryar maza muna son mu koya irin ƙira’ar sosai.”

    Kai ya ɗan juya ya ɗan basu baya tare cewa.

    “In sha Allah zaku iya”.

     

    Samira Sani kuwa, tattausar sajensa ta zubawa idanu cikin wani irin salo dake cikin jiki da zuciyarta.

    Shi kuwa Moddibo a hankali ya kuma yin gyaran murya tare da  cewa.

    “A wata ayar kuwa cikin suratul A’araf aya ta 205. Allah maɗaukakin sarki na cewa…

    Sai kuma yayi musu alamun suja ƙira’arar.

    Cikin kauda kai Khausar ta lumshe idanu ganin wani irin masifeffen kallon daya watsa mata, wanda saida taji hantar cikinta ta kaɗa.

    Cike da dagiya a fagen neman ilinta dan bata wasa kuma bata barin tsoronsa ya hanata fahimta, cikin nitsuwar da take samu in zatayi karatu  tayi bismilla tare da fara jan ayar.

    “Surah Al-Araf, aya ta 205:

    وَاذْكُر رَّبَّكَ فِي نَفْسِكَ تَضَرُّعًا وَخِيفَةً وَدُونَ الْجَهْرِ مِنَ الْقَوْلِ بِالْغُدُوِّ وَالْآصَالِ وَلَا تَكُن مِّنَ الْغَافِلِينَ

    Ta dire ayar da sauƙe nannauyan numfashi  sabida tagib da taja, wanda dole ta ɗan riƙe numfashinta na kusan second 32.

     

    Samira kuwa, wani irin malolon bakin cikine, ya tokare mata maƙoshi, sabida masifar kishi da takaicin yadda ko yaushe Khausar ke gaba dasu.

    Asma’u kuwa sai murmushi takeyi,

    Yayinda da yawa suke fatan Allah ya buɗa musu kwakwalensu kamar na Khausar.

     

    Shi kuwa Moddibo a hankali ya fara fassara musu ayar.

    “Abinda Allah madaukakin sarki yake cewa.

    (Kuma ka ambaci Ubangijinka, a cikin zuciyarka, kana mai ƙanƙan da kai,  da tsoro, ba da ɗaukaka murya a, tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa da safe da kuma maraici, kuma kada ka zamo cikin falaki,.

    A wata ayar kuwa, Allah madaukakin sarki na cewa.

    (Da masu ambaton Allah,  maza,  da masu ambaton sa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai  girma)”.

    Sai ya kuma ɗan tsagaita wa tare da kallonsu yana cewa.

    “Makfut?”.

     

    “Na’am”. Suka amsa baki ɗaya,

    “Ɗayyit”. Yace tare da kallon agogon hannunsa, ganin saura 9 minute lokacin da ya kamata ya sallamesu yacika ne, yasashi ci gaba da cewa

    “Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:

    (Misalin wanda yake ambaton Allah da wanda baya ambaton Ubangijinsa kamar misalin rayayya ne da matacce.

    A wani wurin kuma yace.

    (Shin bana baku labarin mafi al’khairin ayyuka ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakarku,  kuma mafi ɗaukakarsu, ga darajojinku,  kuma mafi al’khairi gareku daga ciyar da  zinariya da azurfa, kuma mafi al’khairi gareku daku haɗu da  abokan gabanku ku riƙe dukkan wuyoyinsu kuna dukan wuyoyin suba?)

     

    Duba Sahihul Bukhari, tare da sharhinsa Fathul Bari (11/208)  Muslim ya ruwaito da lafazin:

    Misalin gidan da ake ambaton Allah a cikinsa da wanda ba’a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayya ne da matacce, (1/539)

    Sai Sahabbai Sukace ka bamu labari.

    Sai yace musu.

    (Ambaton Allah madaukaki sarki)

    Kuma yace:

    Allah madaukaki yana cewa:

    (Ni ina tare da zaton bawana dani,

    Kuma ina tare dashi idan ya ambaceni, cikin ransa, zan ambaceshi a cikin raina,

    Idan kuma ya ambaceni a cikin jama’a zan ambaceshi a cikin jama’ar da ta fisu al’khairi, in ya kusanceni taƙi ɗaya, zan kusancesa kamu guda, in ya kusanceni kamu guda, zan kusancesa  tsawon gaɓa guda, in yazo min yana tafiya zan zo masa ina gaggawa)”.

    Sai kuma ya fesar da sassayan numfashi a hankali tare dasa tafin hannunsa ya shafa tattausan sajensa, yana mai lumshe idanunsa alamun cikekkiyar nitsuwarsa buɗe idanun yayi a hankali tare da cewa.

    Tirmizi (5/459). da Ibn Majah, (2/1245). duba Sahih Ibn Majah (2/316). da kuma Sahihul Tirmizi  (3/139). Bukhari (8/171). Da Muslim (4/2061) lafazin riwayar na Bukhari ne.

    Cikin nitsuwa ya kuma juyowa ya fuskacesu, murya cike da kamala, da tashin lafazi yace….!

     

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma na dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi Gumbar Ukku al’khairi, Dukansu  garukan da gumbunan akan  dubu uku uku ne sai gumbar Riɗi da uku khairi su dubu biyar biyar ne ! Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace ta koma tamkar budurwa 7k, kana masin Daɗi har Maɗigan mai masifar kyau da kwaranyo da ni’ina 5k

    Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa 8k, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi duka a dubu uku-uku ne ƙananan robobinfa, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, set dinsa dubu goma in kuma komai rabi-razi zan sa miki 5k ne butar sirri da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai duba littafin (Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci ga kuma account no 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, kina iya tura kuɗinki kafin ma ke min mgn duk abinda na irga akwaisu Available…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 12

    Sakayyah 12

     

    📝✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 12_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *Littafin SAKAYYAH na kuɗine wannan Free page ne ƴar uwa ki biya ki karanta cikin Aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276 saura shafi huɗune kacal ana biyar na gama Free page*

     

     

     

    Da sauri Modibbo ya rintse idanunsa, tare da shafa sajensa domin, badan glass dake tsakani ba da akan tattausan sajensa  sumbatar zata sauƙa.

    Shi kuwa M Jameel cikin sauri ya lumshe idanunsa tare da gyara zamansa yana fuskantar  ta da kyau.

    Ita kuwa Khausar hannu tasa tare da gyara zaman ɗaurin ɗan kwalinta, sai kuma ta canza Baitin da take ji zuwa.

    Waƙar Lamba tana marming tamkar zabia kai kace itace ta raira waƙar, bin baitukan takeyi tana jujjuya manyan idanunta, tana mai girgiza jikinta zuwa  ƙugunta.

    lumshe manyan Idanunta kumayi tare da fitar da sautin zazzaƙar muryanta a fili ta tace.

    “Kai zan yiwa kalamaina.

    Kai zan baiwa muƙamai na. Ungo makullaina ka riƙe.

    Ta ida bautin tare da nuna saitin fuskar Moddibo da yar yatsarta ma nuniya.

    Wani irin shu’umin murmushi M Jameel ya sake tare da sa hannunsa ya riƙon hannun Moddibo da ya yunƙura zai ɓalle karfin motar.

     

    Ita kuwa Khausar, cikin azama taci gaba da bin waƙar cike da zazzafan shauƙi tace.

    “Ni ban furta da wasa ba, samari dukka basu kai ba, kana nan banganin kowa da ido, dan  basu isheni kalloba”.

    Tayi mgnar bisa alamu daga ainihin cikin ranta take bin waƙar, M Jameel kam murmushi yakeyi cike da shauƙi.

    Modibbo kuwa ya cika yayi fam dan har ransa yakeji yarinyar ta tarainashi gani yake kai tsaye ma dashi takeyi, gashi kuwa M Jameel ya riƙe masa hannunsa ƙam-ƙam.

     

    Ita kuwa Khausar mazari uwar rawa, ƙugunta da ƙirjinta take motsawa a slowly tana mai ci gaba da cewa.

    “Kai zaka zauna adamana, kuma ka bani gurin kwana, wannan shine fassarar mafarkin da nake kullum cikin baccina”.

    Wani irin yar-yar Moddibo yaji tsikar jikinsa na tashi domin suna jinta ras kasan cewar Glass ɗin bayan motar a suna ƙasa kaɗan.

    Ita kuwa Khausar

    ida baitin tayi tana mai nuna Moddibo dake kwance jikin kujeran Idanunsa alumshe da yatsan hannunta tana murmushin dake ƙarawa fuskarta kyau.

     

    Shi kuwa Moddibo Cikin fushi ya fuzge hannunsa daga riƙon da M Jameel yayi masa tare da sanya tattauaan tafin hannunsa da niyyan buɗe motar.

    Shi kuwa M Jameel cikin sauri ya riƙe tafukan hannunsa da ƙarfi tare da girgiza masa kai alamar ya bari suga iya gudun ruwanta.

     

    Ƙwafa Moddibo yayi tare da jingina bayansa da jikin kujeran ya cigaba da kallonta.

    Ita kuwa rawanta ta cigaba dayi tana Girgiza jikinta ganin abin nata ba mai ƙare wa bane yasa Moddibo buɗe motar cike da tsananin  fusata.

     

    Kamar walƙiya ko wanda ya diro daga sama haka taga Moddibo a gabanta,

    Cikin tsoro, mamaki, da kiɗima  kalli fuskarsa cikin zare ido ta tayi ƙasa da kanta,

    domin bata tsammaci  da mutum aciki ba.

     

    Shikuwa Moddibo cikin nutsuwarsa da kuma kamala ya fito daga motar tare da tsaida idanunsa akanta yana mai ƙara tsananta suƙe fuskarta da ya ƙara razanata.

     

    Ita kuwa cikin tsananin ruɗu da tashin hankali mara misaltuwa ta ɗaura hannunta akai.

    tare da zubewa akan gwiwoyinta tana mai girgiza kanta gaba ɗaya ta gaza cewa komai.

     

    M Jameel kuwa gefen Driver ya buɗe tare da fitowa yana dariya mai sassayan sauti,

    dai-dai lokacin da Ummi da Asma’u suka fito  daga cikin gidan zuwa harabar gidan.

    Idanu Ummi ne suka sauƙa akan Moddibo da M Jameel kafin kuma ta maida ganinta kan Khausar dake durƙushe ta kama kai da hannunta duka biyu,

    cike  da mamaki asaman fuskarta Ummu  tace.

    “A’a ikon Allah Khausar lafiya ya dai haka!?”.

    Kasa cewa komai Khausar tayi, still hannunta na kanta haka zalika ta kasa ɗago kanta banda bugawa da ƙarfi babu abinda zuciyarta keyi da ƙarfi.

     

    Ganin Ummi da tambayar da take yiwa Khausar yasa Moddibo basarwa kamar baisan da ruwan ɗigon Khausar dake tsugunne gabansa ba,

    cike da nutsuwa da kuma takun ƙasaita ya janye ƙafarsa da ya ɗaga da niyar zaiyi wasan ƙollo da Khausar ɗin yana mai maida fushinsa ya haɗiye ya juya ya nufi gaban Ummi.

     

    Murmushi Ummi tayi Idanunta akan Moddibo tace.

    “Sannun ku da zuwa  Babana, dama yanzu nake shirin zuwa unguwa  zanje duba jikin Maman Khausar”.

    Ta ida mgnar ta maida kallonta kan Khausar da har zuwa yanzu take durƙushe sai dib dab dib dab da sautin zuciyarta ke badawa,  cikin kula tace.

    “A’a Khausar yaushe kika zo? ya jikin Mommyn ki?”

    Ita dai Khausar bata ɗago ba bare kuma ta motsa, gani take aduk lokacin da tayi kuskuren ɗaga kanta Moddibo zai iya kifeta da azabebben marinsan nan mai sa mutum ganin taurari masu wutsiya.

    Cikin kula Ummi ta juya ta kalli Moddibo dake tsaye hannunsa na acikin aljihu  murmushi tayi kana tace.

    “Allah yayi zaku zo ku sameni, kuzo mushiga daga ciki”.

    Kai suka jinjina tare da wuceta, ita kuwa Ummi juyawa  tayi zuwa gaban Khausar ɗan tsugunna tayi tare da riƙo hannun Khausar tace.

    “Duk cikin gaishe da Malama ne har haka Khausar? to taso mu tafi”.

    Sai asannan Khausar ta ɗago kanta tare da sakin wani  nan-nauyan ajiyar zuciya, ganin Moddibo bai nan cikin mutuwar jiki tabi Ummi falon.

    Suna shiga Khausar tayi saurin janye hannunta daga cikin na Ummi, kana ta kama na Asma’u suka nufi Bedroom ɗinta”.

     

    Suna shiga Bedroom ɗin Khausar ta janye hannunta daga na Asma’u ta zauna agefen gadon Idanunta cike da ruwan hawaye ta dafe ƙirjinta tare da cewa.

    “Asma’u nashiga ukuna!nikam yau naga ta kaina, Allah yana jarabtana ta hanyar haɗani da Moddibo a bauɗaɗɗen yanayi,

    zuwa na kenan naji wata waƙa tamin daɗi na tsaya ina bi uwa zabiya.

    Kuma kin sanima fa ni ban fiye jin waƙa ba, sannan bai dameni ba amma kawai ɗazu naji wata waƙa MP din Haiydar Wai ita Buga da Lamba kuma wallahi nasan Haiydar ne ya haxa min da bai bani aron MP ɗinsa ba ai da banjita ba bare inji yamin daɗi,  kawai na kama rawa tamkar yar gala,

    ashe Moddibo na kallona nikam bansan irin hukuncin da zai minba gobe amakaranta, ƙilan ma ya sake sakani kaɗe ɗan kwali nikam nashiga Ukuna! Laifi kan laifi gashi gyale na yafa ga uban turaren dana zumbuɗa ga rawa dajin waƙa Wayyo ni Batula Faɗimatuzzahara naga ta kaina!”.

     

    Ta gumi Asma’u tayi tare da kallon, Khausar da tayi narai-narai da ido kana tace.

    “Ke kam dai Khausar kamar saɓani Allah yake haɗaki dashi”.

    Narai-narai tayi da ido tare da dafe kuncinta da hannun biyu kana tace.

    “Mummunan saɓani ma kuwa, na sharri ma ya Allah kashiga tsakanin na gari da mugu, Allah kara bani dashi ya Allah kada ka bashi ikon zalunta na, tun da dai arashin sani nayi kuma babu wanda yafi ƙarfin kuskure ai seya min uzuri ko?”.

     

    Janye mata tagumin Asma’u tayi tana dariya tace.

    “Kece Khausar wani zubin sai ahankali, kawai daga zuwa saiki hau rawa kamar mazari da anyi magana ki wani ce Allah yashiga tsakanin na gari da mugu sannan da kike maganar uzuri a’a ba’asi za amiki ba uzuri ba kuma waye mugun waye na garin”.

     

    Sheƙeƙe Khausar ta ɗago kai tare da tsirawa Asma’u Idanu kana tace.

    “Nifa na lura dake tun ba yanzu ba, kinfi ƙaunar Moddibo dani wato har kina goyon bayan sa akan ni kin zaɓe sa kin barni? Yoh shine mugu mana ni ta gari”.

    Ware idanu Asma’u tayi tare da langwaɓar da kai tana dariya tace.

    “Haba ƙawar arziƙi matsayinki yafi haka, dan Allah kada ki sake faɗan hakan aise kisa ayimina dariya”.

     

    Taɓe baki Khausar tayi tare da faɗin.

    “Kinsan gwara in gane matsayina ai tun wurima,

    idan kinfi ƙaunar Moddibo insan matsayina”.

    Dariya mai sauti Asma’u tayi da faɗin.

    “Maida wuƙar ranki shi daɗe Fattanah”.

    Murmushi Khausar tayi tare da kishingiɗa akan gadon.

     

    Acan falo kuwa bayan Moddibo da M Jameel sun sake gaisawa da Ummi ta miƙe tashiga kichen ba daɗewa ta fito hannunta riƙe da babban tray dake ɗauke da Warmers ta ajiye musu.

    Murmushi Moddibo yayi yace.

    “Sannu da gajiya Ummi”.

    Murmushi tayi tace.

    “Yawwa Babana”.

    M Jameel kuwa miƙewa yayi yashiga kichen ya dauko musu Plate da cups guda biyu kana ya dawo ya zauna.

    Kulan ya buɗe, da sauri ya gyara zamansa jin wani ƙamshi mai daɗin ya ratsa hancinsu.

    M Jameel ya lumshe ido tare da zuba musu akan Plate.

    Moddibo ya matso tare da tsirawa Pride rice ɗin da yaji vegetables da naman kaza amsar spoon ɗin da M Jameel ke miƙa masa yayi, cikin fesar da numfashi Moddibo ya ɗibi abincin ya kai bakinsa, lokaci ɗaya yaji daɗi ya mamaye masa baki, kallon Ummi yayi tare da faɗin.

    “Ummi wannan girkin yayi daɗi”.

    murmushi tayi tare da tsiyaya musu tea mai ɗumi.

     

    Bayan sun gama ci.

    M Jameel ya goge bakinsa da tissue kana yace.

    “Ummi ɗazun ina zakije dama?”.

    Tana matsar da Flaks ɗin tea tace.

    “Wallahi Maman Khausar zanje dubawa, bata da lafiya shekaran jiya a asibiti suka kwana jiya ne aka sallame su da safe”.

     

    Girgiza kai yayu kana yace.

    “Ayyah Subhanallah Allah yabata lafiya Allah yasa zakkan jikine”.

    Amin Ummu tace.

    Yayinda  shi kuwa Moddibo Aransa yace. “Uhhhm yarinyar kamar aljana ita da mahaifiyar ta babu lafiya har ankwantar da ita a asibiti jiya-jiya aka sallame su, amma yau har ta gararo yawo, har tana rawa agidan mutane kamar wacce aka yiwa bushara da Aljanna, ita kuwa wannan daɗin me takeji”. sai kuma ya taɓe baki takaicin halayyar yarinya yasa bece musu komai amaganar ba.

    Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.

    “Toh Ummi mu zamu tafi”.

    Ummi ta juya ta kallesa da murmushi afuskarta tace.

    “Da wuri haka Babana?”.

    M Jameel ne yace.

    “Ai dama a gaggauce muka zo Ummi, dan kwana biyun nan naga ya maida hankalinsa akan rubutun da yake inagama ya kusan gamawa”.

     

    Ummi kuwa kallonta ta mayar kan Moddibo kana tace.

    “Masha Allah Ubangiji Allah ya taimaka, ya kuma baku sa’a ka kusa gama wa kenan?”.

    Cike da nitsuwa Moddibo ya amsa da.

    “Ameen”,Kana yace.

    “Eh Ummi na kusa gamawa, amma waɗan da na tura ƙasar Ɓadamaya ma tukunna wanda na turawa, Sheykh Jabeer ya duba min su har yau basu dawo ba, to inaso kawai na haɗa wa’annan ma dake wancan bugun Hafs ne wannan kuma Warash ne”.

    Yai da mgnar tare  sauƙe numfashi kana ya cigaba da cewa.

    Warash ne nake rubuta wa to inaso idan nagama rubuta wannan ɗin na tura masa, wala Allah ya tuna mishi da duba wancan ɗin.

    Nasani abubuwa ne suka masa yawa da yake ya wanci yakin arewacin nan duk wanda ya rubuta Kur’ani shi ya ake turawa sai ya duba yagani toh zanyi ƙoƙari na gama rubuta wannan ɗin sai ahaɗa akai gaba ɗaya ko zan samu ya haɗa min su lokaci ɗaya idan ya duba ingancin su”.

     

    Jinjina kai Ummu tayi cike da yabawa jajurcewarsa da kuma ƙoƙarin sa tace.

    “Masha Allah Allah yatemaka  Allah ya bada sa’a abu yayi kyau Allah yabar mana irinku Moddibo Allah yayi jagora”.

     

    Moddibo kuwa cikin jin daɗin addu’ar ta yace.

    “Ameen Ummi Allah ya amsa Nagode”.

    Miƙewa M Jameel yayi idanunsa akan Ummin sa yace.

    “Ummi zamu tafi”.

    Tana ƙoƙarin kwashe Plate da sukayi amfani dashi tace.

    “Toh Nagode Allah ya muku albarka”.

    Suka haɗa baki wajen faɗin.

    “Ameen”.

    kana suka fice.

     

    Bayan sun ɗauki hanya M Jameel ya dubi Moddibo wanda shike Driving ɗin yanzu yace.

    “Ni ka sauƙe ni agida”.

    Moddibo da still hankalin sa ke kan Driving yace.

    “Ba zamu tafi tare ba?”.

    Girgiza kai M Jameel yayi kana yace.

    “A’a nasan rubuta zaka je kayi sannan Abba ya kirani akan batun yana so naje Ɓadamaye batun Company sa akwai sabbin Injina da aka kawo, za’a saka kaga na daɗe ban jeba, amma wannan karon ko naje baze wuce kwana biyu zanyi in dawo ba”.

     

    Moddibo kuwa jinjina kai yayi kana yace.

    “Toh yaushene tafiyar?”.

    Kai M Jameel ya Girgiza tare da faɗin.

    “Toh dai ban sani ba tukun”.

    Moddibo dake ƙoƙarin shan kwana yace.

    “Yawwa zanyi ƙoƙari inga na gama rubutunan idan zaka tafi sai ka tafi min dashi”.

     

    Shi kuwa M Jameel Kai ya gyaɗa cike da gamsuwa da maganarsa yace.

    “Toh shikenan hakan ma yayi Allah yatemaka”.

    Moddibo ya amsa da.

    “Ameen”,tare da parking motar bayan ya isa ƙofar gidan su M Jameel.

    Sauƙa M Jameel yayi tare da yi masa sai anjima, kai Moddibo ya gyaɗa kana yaja motar ya tafi.

     

    Yana isa gida bayan yayi Parking motarsa ya wuce Bedroom ɗinsa kasancewar yana da alwala yasa ya ɗauko abubuwan buƙatar sa na rubun Alkur’ani da yakeyu kana yaciigaba da rubutu, saida aka kira sallar La’asar sannan ya tashi yaje masallaci ya gabatar da sallan la’asar, bayan ya dawo kuma, yazo ya cigaba da rubutun, yana yi yana karantar Suratul Kahfi  kasancewar yammacin jumma’a ne, sai misalin ƙarfe biyar kafin ya ajiye Kur’ani.

     

    Acan ɓangaren Innayi kuwa zaune take akan kujera ’yar tsugunno acikin kichen tana juya miyar zogala wanda yaji namar Rago da kuma wadataccen man Shanu da wake yana tashin ƙamshi bayan ta sauƙe miyar ta ɗaura Ruwan shayi daya ji na’ana, kaninfari da kuma ɗanyan citta yana tafasowa yana ƙamashi mai daɗin shaka.

    Flaks guda biyu ta ɗauka ta juye sannan ta ɗauki ɗaya ta nufi sashen Moddibo dashi.

     

    Acan gidansu Asma’u kuwa bayan tafiyar Moddibo da M Jameel Khausar ta miƙe tare da fitowa falon Idanunta akan Ummi tace.

    “Toh Ummi mu tafi ba dama kince gidan mu zaki jeba”.

    Jinjina kai Ummi tayi tace.

    “Eh Khausar inaso naje na duba jikin Mommyn ki”.

    Ba tare data zauna ba tace.

    “Toh Ummi mu tafi”.

    Kai Ummi ta jinjina kana ta miƙe suka fita su ukun Bashir ƙanin Asma’u ne kaɗai suka bari agida Ummi da kanta take Driving Khausar da Asma’u na baya suna hira.

     

    Acan ɓangaren su Hajiya Bunayya kuwa Kallonsu Boka Kar’uzu yayi cikin wata razananniyar tsawa yace.

    “Wannan maganin ya riga daya ɓaci, ta lalata komai yanzu sai anyi aikin dai-dai-ta fuskarta ma tukunna kafin azo ayi aikin jawo hankalinsa, yaran nan biyu da kuka gani kuke magana akansu yarane dasu na tsaye da sunan Allah da riƙo da Ibada, musamman ma Moddibo  da kuke magana akansa kwata-kwata baya rabuwa da alwala ajikinsa ka masa zaiyi wuya”.

    Cikin tashin hankali Hajiya Bunayya ta juya ta kalli Hajiya Lami da duk tagama shiga ruɗu.

     

    Boka Kar’uzu kuwa cigaba yayi  da cewa.

    “Yanzu sai munyi aikin wata uku kafin fuskarta ya dawo dai-dai sannan sai tabar Sallah na tsawon watanni shida kafin mu samu mu fara aiki shiko aikin za’ayi na tsawon watanni shida kafin ta fara nuna masa muradanta”.

    Kana ya maida kallonsa ga Hajiya Lami data zabga uban tagumin tana kallon sa cikin Muryansa Mara daɗin Amo yace.

    “Kema naki hakanne sai tayi wannan watannin”.

    Dafe ƙirji Hajiya Lami tayi tare da zare Ido kana tace.

    “Har Watanni shida shida Boka kafin wannan lokacin fa har sun kusa gama Ss 2 ma zasu tafi 3 awannan lokacin daka ɗiba mana”.

    Cikin tsawa da hargagi yace.

    “Dole sai anbi wannan ƙa’ida idan ba haka ba babu abinda zaku samu ya tafi dai-dai!”.

     

    Ta gumi Hajiya Lami ta rafka kana tace.

    “Shikenan Babu damuwa Indai burinmu zai cika tunda ai makarantar basu gama ba zamu bi ahankali”.

    Ya yamutse fuska tare da watsa musu wani kallo da jajayen Idanunsa cikin wata murya mara daɗin Amo yace.

    “Ƙa’idah ne yanzu zata je tayi ta aiki da wannan maganin na tsawon watanni ukku fuskarta zai koma dai-dai a Idanunsa sannan bayan wannan kuma tsawon watanni kar kuyi sallah daga nan kuma zan fara haɗa magani na tsawon watanni shida kafin su tun kare su daga magana”.

     

    Murmushin Hajiya Bunayya tayi tare da gyara zamanta tana fuskantar Boka Kar’uzu da kyau tace.

    “Toh shikenan ba matsala.

    Amma fa ciki ya zube aiki yayi kyau!”.

    Wani irin mahaukaciyar dariya mai matuƙar razanarwa Boka Kar’uzu ya saki da faɗin.

    “Ai dama dole aiki zaiyi kyau idan kun bishi da ƙa’ida wannan ma ku kuka je kuka ɓatashi!”.

     

    Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

    “Godiya muke Boka ana gaba zamu kiyaye”.

    Kai ta gyaɗa kana yace.

    “Toh ya batun aikin toshe mahaifar!?”.

    Kai Hajiya Bunayya ta Girgiza tare da faɗin.

    “Boka muga ma da batun aikin Amina tukunna, kaga ga yayar ta ma tana zaune ba tayi aure ba, sannan ga itama Aminan ta girma shiru, amma ita kace rabonta ne yayi nisa abin ya ɗaure mana kai mun rasa yanda zamuyi har wajen ƙan wata na tura ta Aƙasar Khautal ko zata samu rabonta acan amma acan ɗin ma shiru kuma kaga ta dade da gama karatu amma  har yau Auren bai samu ba zamu jona mata wani makarantar ta fara zuwa jami’a kawai, tunda itama kanta Amina dan wasa da karatun take da tayi shekaru biyu da gamawa amman sai aikin maimaita aji gashi har shegiyar yarinyar nan ta kusan cimmata”.

     

     

    Kai Boka Kar’uzu ya ɗago daga bugun ƙasar da yake tare da cewa.

    “Babu matsala ita Aseeya rabonta yana nan tafe”.

    Cike da jin daɗi Hajiya Bunayya tace.

    “Godiya muke Boka Uban bokaye La’anannen Uban La’anannu Mugu Uban mugaye Hatsabibi Uban Hatsabibai!”.

     

    Wata mahaukaciyar dariya Boka Kar’uzu ya kece dashi cikin jin daɗin kirarin da ta masa yace.

    “Aikin ki zai tabbata ƙaramar la’ananniya  Aljani ɗan ƙundalu mai ido Atsakiyar kai zai cika miki burinki ku fita da ƙafar hagu ta baya!”.

    Miƙewa sukayi suka fice kamar yanda ya faɗa ransu fesss suna tsalle da kafar hagu kamar kutaren agwagi…

     

    Acan ɓangaren su Ummi kuwa bayan sun isa gidan su Khausar sun gama gaisawa da Mommy da kuma Hajiya Ruƙayya da har zuwa lokacin suke tare.

    Mommy tana murmushin tace.

    “Ummi ya fama rigimar Khausar, ɗazun nan tace zata je ta duba ki ashe kina hanya”.

    Dariya Ummi tayi tace.

    “Ai lalle dai kam Hajiya Aysha babu ruwan Khausar ai”.

    Murmushi Mommy tayi tace.

    “Kina dai karate ta Amma Khausar ba dai rigima ba?”.

    Aunty Ruƙayya tayi Dariya kana tace.

    “Ai Khausar bata da rigima ita dai baza’ayi gulma agaban Idanunta bane, sannan ba za’a cakake ta ta haƙura ba, kunga kuwa ai da gaskiyar ta”.

    Dariya Ummi tayi tace.

    “Aikam de lalle da gaskiyar ta”.

    Ita kuwa Mommy Dariya tayi kana suka cigaba da hira.

     

    Washe gari Asabar suka koma makaranta Khausar kuwa cikin tsoro da fargaban abinda Moddibo zai mata ta zuciyarta ya riƙa bugawa da ƙarfi lokacin da yashigo raba musu questions pepar  tayi zaton zai mata hukunci sai taga baima kalli inda take ba.

    Shikuwa Moddibo kawai ya fita sabgarta ne ganin alamar bata da cikikakkiyar nutsuwa in ya biyata zata zarar dashi.

     

    Akwana atashi haka al’amura suka cigaba da tafiya komai yana wakana Moddibo ya kammala rubutun Kur’aninsa ya bawa M Jameel ya tafi wa da Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Joɗa na Adamawa.

    Satin M Jameel biyu ya dawo tare da shedawa Moddibo ya karɓa harma ya fara dubuwa Insha Allah nan kusa zai turo masa.

    Karatun su Khausar na tafiya komai na tafiya dai-dai yanda ake buƙata Anyi gasar musabaƙa jihar Taraba Makarantarsu Khausar Al’ansar Academic school_ shine yazo na farko Khausar ce tazo na ɗaya a haddar Izu arba’in yayin da Asma’u tazo na biyu Aishatu Abdullahi tazo na uku ,A haddar Izu biyar Raudat ce tazo na ɗaya kyaututtuka masu yawa suka samu kana suka dawo cike da nasarori.

     

    Yanzu karatu na tafiya akwana atashi babu wuya wasa gaske yanzu Khausar suna Ss2

    thirth term suna shirye shiryen fara Exam gashi kuma Ramadan ya kawo kai yayin da ake ta shirye shiryen shiga Ramadan tuni Gwamnatin Jaha ta rarraba malamai zuwa inda ko wanne zaiyi Tafseer kamar yanda aka saba Moddibo da M Jameel antura su Babban Masallacin juma’a dake ƙofar sarki Gembu anan zasuyi Tafseer ɗin su na Ramadan.

    Lokaci natafiya karatun su Khausar na sake tafiya yanda ake buƙata tsakanin Amina da Khausar babu wani jituwa hasalima gaba ce domin har gobe M Jameel na sake nuna kulawa ta musamman akan Khausar yayinda Moddibo kuwa kwata-kwata baya lura da al’amuran Khausar hasalima idan tayi laifi zai yanke mata hukunci fiye dana kowa wannan dalili yasa basa shiri kana babu wata jituwa atsakaninsu.

     

    Alhamdulillah ayaune Khausar suka rubuta exam na ƙarshe kuma da Geography suka rufe.

    Taro Moddibo yasa aka haɗa kamar yanda aka saba a kowani ƙarshen hutu ko baki ɗaya Malaman sun haɗu awajen zamansu haka ma ɗalibai Khausar da Asma’u na zaune awaje ɗaya.

     

    Shi kuwa Moddibo cikin nutsuwarsa da kuma kamala ya nufo wajen as usual cikin shigar sa kaman ko yaushe sanye yake cikin Jallabiya fari kansa naɗe da hirami idanunsa sanye da ɗan siririn farin glass daya ƙawata kyawun fuskarsa yalwataccen sajensa  zuwa gemunsa ya kwanta luf-luf yana sheƙi.

    Cikin tsantsar nutsuwa da sanin darajar kansa ya gyara zaman microphone ɗin tare da hura iska kaɗan kana yayi gyaran murya yace.

    _“Bismillahir Rahmanir Rahim, Innalhamdulillah nahmaduhu wanasta’inuhu wanastaghfiru wa’nazubillahi min shururi anfusna wamin sayyi ati a’amalina, man yahdillahu fala mudillahlah waman yudlil fala hadiyala, Wa’ash hadu Allah ilahalillahu,  Wa’ash hadu anna Muhammadu Abduhu wa Rasulullah (S.A.W)”._

     

    Sai kuma ya ɗan lumshe idanunsa tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana ya cigaba da cewa.

    “Duk kan yabo da godiya su tabbata ga Allah subhanahu wata’ala mai kowa mai komai, da yakawo mu wannan lokaci da muke shirin karɓan hutu saboda gabatowan wannan wata mai falala, haƙiƙa watan Ramadan wata ne mai falala da rahma wanda duk kan musulmi yake da burin ganinsa.

     

    Baki ɗaya wajen shiru yayi kowa ya maida nutsuwarsa zuwa garesa yayin da Samira kejin aduk lokacin data mallakesa babu macen da takaita sa’a a faɗin wannan duniya tamu ta bani adam.

    Malam Arɗo kuwa Aransa yake jin Moddibo ne Garkuwa kuma ginshiƙin makarantarsa.

    Moddibo kuwa cikin yanayin sanyin Muryar sa mai cike da nutsuwa ya cigaba da cewa.

    “An abu Huraira ta radiyallahu anhu,

    _Manƙama Ramada Imanan Wahtisaban gufra lahu mata ƙaddama min zambi muttafaƙun Alaik”_

     

    Ma’ana ankarbo daga Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda, yana cewa Duk wanda watan Ramadana ya kama yana mai Imani da kyautatawa ana kankare masa zunubansa da suka gabata”.

     

    Ya sauƙe sanyayyar Ajiyar zuciya mai sanyi kana ya cigaba cewa.

    “Wannan kaɗai zai iya nuna maka muhimmanci da kuma darajar wannan wata hakika wannan watar ba wata bane na wasa watane daya kamata mu tsaya mu miƙa lamuranmu ga Ubangiji Mabuwayi gagara Misali, sannan mukasance masu yawan Karatun Alkur’ani, Istigfari, hailala da kuma tasbihi, ba sai na tsawaita ba ko naja duk abinda zance kun sani”.

    Sai kuma ya maida kallonsa ga sauran Malaman yace.

    “Koda akwai mai magana?”.

     

    Duk suka girgiza kai alamar babu Moddibo kuwa M Jameel ya miƙawa microphone ɗin kana ya koma ya zauna shi kuwa M Jameel bayanai ya ƙara akan na Moddibo kana ya sanar dasu Bayan Sallah da sati ɗaya zasu dawo.

    Yana gama Maganar ya juya tare da kallon Khausar da ita adai-dai lokacin Idanunta na kasansa cikin Sanyayyar Murya yace.

    “Lelewal zoki rufe mana  da addu’a!”.

    Anutse Khausar ta gyaɗa kai tare da miƙewa.

    Shikuwa Moddibo kallon mamaki yabin M Jameel dashi amma baice komai ba.

    Amina kuwa jitayi tamkar zuciyarta zai buga saboda baƙin ciki da kishi.

    Ita kuwa Khausar cike da tsoron Modibbo dake sa ta nemo nutsuwa ta amshi microphone ɗin cikin zazzaƙan Muryanta tayi addu’a kana aka tashi kowa ya watse dalibai nata murnan hutu kowa ya koma gidansu cike da farin ciki.

     

    Da daddare Khausar na zaune akan 1sitter hannunta riƙe da wayar Mommy yayin da Mommy kekan 3sitter ta miƙe ƙafafunta Hannunta riƙe da kofin tea.

    Anutse Mommy ta ɗago kanta tare da sauƙe Idanunta dake kan Khausar Wacce baki ɗaya hankalinta ke kan wayar da take dannawa ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

    “Khausar tunda an baku hutu ko dai za kije Jauro Yaya kuyi azumi tare”.

    Da sauri Khausar  ta ajiye wayarta tare dasa hannu ta dafe ƙirjinta tace.

    “Nashiga Ukuna! Dan Allah dan darajar Annabi Mommy Kar kiyi Wannan maganar, kibar tsohuwar nan tunda dai bata ne maba”.

     

    Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

    “Toh shikenan yanzu azumi saura sati amma nasan zaiyi wuya acikin satin nan idan bata neme kiba”.

    Marerece fuska Khausar tayi kana tace.

    “Allah yasa karma ta nemeni duk da garin yamin daɗi Mommy amma inaso in tayaki aiki”.

    Murmushi Mommy tayi kana tace.

    “Toh shikenan ba matsala hakan ma Allah ya zaɓa Mana abinda yafi zama alkhairi”.

     

    Acan ɓangaren su Hajiya Lami kuwa zaune take afalon Hajiya Bunayya tare da Samira Sani da kuma Amina.

    Kallon Hajiya Lami Hajiya Bunayya tayi kana tace.

    “Yanzu dai saura mana watanni biyu mu gama cika Umarnin Boka Kar’uzu na watanni shida daya ɗiba mana kada muyi Sallah, kafin na ƙarshe da zamuyi muje mu karɓi maganin su zo suyi aiki dashi”.

    Murmushi Hajiya Lami tayi tare da jinjina kai tace.

    “Eh haka ne bayan Sallah da sati Uku zamu gama”.

    Jinjina kai Hajiya Bunayya tayi tare da cewa.

    “Gashi kuma azumi ya gabato amma acikin wannan azumin ma ace ba zamuyi sallah ba kuma watan falala da ibada!?”.

     

    Wani kallo Hajiya Lami tayi mata kana tace.

    “Idan ke zakiyi sallah ki ɓata aikin da kikayi to kinyi na wancan watannin shida da kika samo fuskar ’yar ki ya dawo dai-dai a idanunsa, sannan yanzu wata ɗaya da rabi daya rage ne zaki ɓata ba zaki iya jira ba. Agaskiya nikam zan cika ƙa’idata domin in samu cikar burin ‘yata”.

     

    Samira kuwa zama ta gyara tana fuskantar Hajiya Bunayya da kyau tace.

    “Agaskiya Ummah kar muyi wasa da wannan damar da muka samu idan yaso idan muka gama sai mu rama bashin sallah dake kan mu!”.

     

    Ita kuwa Amina Kallon mahaifiyarta tayi tare da ƙanƙance Idanu kana tace.

    “Yanzu ke Ummah wasa zakiyi da wannan damar da muka sha wahala tsawon watanni muna yi!?”.

    Zare ido Hajiya Bunayya tayi tare da nuna kanta da yatsa tace.

    “Ina waya faɗa miki ko an faɗa miki daɗi nake ji ga yayarki azaune gaki kuma kema azaune”.

    Ta ida maganar dai-dai lokacin da Asiya ta fito daga Bedroom bayan ta gama sauraron duk abinda suke faɗa zama tayi akan 1 sitter dake fuskantar Hajiya Bunayya cikin sanyin murya tace.

    “Gaskiya Ummah!, Gaskiya Ummah!! Kada neman duniya yasa mu rasa ƙiyama tare da rahamar Ubangiji, Ummah sallah da arayuwar duniya itace farkon abinda za’a bin ciki mutum dashi aranan gobe hisabi idan tayi kyau abin cika sauran abubuwa idan kuma ba tayi kyauba, baza ma aje ga sauran abubuwan ba”.

    Tayi ƙasa da Idanunta ganin shegen kallonda Umman take bin ta dashi bata damu ba ta cigaba da cewa.

    “Ummah aduniya Allah ya Umarceki da kiyi sallah da Azumi amma Boka La’anannen yace kada kiyi, sannan ki biye masa har ki yarda sannan ki riƙa ɗaura ‘yarki akan gurɓatacciyar hanya nikam wannan al’amari yana tayar min da hankali, wannan al’amarin sam bai yi ba yanzu dama akan wannan turban kuke tafiya?”.

    Ta saki Ajiyar zuciya tare da gyara zamanta kana tana ƙoƙarin maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata cikin dauriya ta cigaba da cewa.

    “Shiyasa tun da na dawo sati biyu banga kinyi alwala ko Sallah ba?, Ni nayi zaton ma al’ada kike yi,Itama Amina naga bata sallah dana tambayeta saita kama yimin rashin kunya”.

     

    Amina dake jifanta da mugun hararane tayi saurin katseta tare da cewa.

    “Anyi miki rashin kunyar keda ba kyabin Ƙa’ida da Umarnin Bokan baga ki har yanzu baki auru ba!sai shegen iyayi da kwainane!”.

     

    Asiya da Idanunta suka ciko da ruwan hawaye ta kalli ƙanwar nata cike da mamaki sai kuma tayi murmushi mai ciwo tace.

    “Wannan Allah ne bai nufaba, idan Allah ya saƙƙo da lokaci zanyi shi domin Aure da mutuwa lokacine”.

    Atsawace Hajiya Bunayya tace.

    “Rufe min baki, keda ma can ba’a haɗa shiri dake ya tafi dai-dai, dama ke da magautana kike tare kina nan kamar wancan matar ce ta haifeki”.

     

    Asiya ta danne kukan dake neman kufce mata tace.

    “Ba haka bane Ummah zanso mu gudu tare mu tsira tare ne, bazan so ganin ku cikin halaka ba Umma kuyi tunani akan wannan rayuwar da kuka jefa kanku”.

     

    Hajiya Lami kuwa cikin fushi tace.

    “Wannan dai akwai gantalelliyar yarinya shegiya mai shegen mugun halin jaraba, duk yanda akayi wancan gafalalliyar kishiyar Uwar taki ta baki nononta kinsha”.

    Kallonsu kawai Asiya keyi cike da mamaki.

     

    Hajiya Bunayya kuwa Afusace tace.

    “Bana son gaskiyar taki ki riƙe abarki.

    ki gudu ke kaɗai mu ma mu gudu mu kaɗai kiga wanda zai riga isa tsakanin mu da ke”.

    Cikin tsananin tashin hankali Asiya tace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n.

    Allahumma Ajirni fi musibati wa’ahlif khairan minha”.

    Ta ida addu’ar tare da miƙewa ta shiga Bedroom ɗin su akan gado ta faɗa tare da dafe kanta tace wannan wani irin Masifa ce Ummah ta jefa kanta.

     

    Acan falo kuwa Ummah suka cigaba da tattaunawa tare da tsaida matsaya akan idan sun kammala aiki zasu biya Sallolin da ake binsu.

     

    Washe gari.

    Da hantsi misalin 12:00 Khausar na kwance A Bedroom kamar daga sama tajiyo Sallamar Hajja Nana da sauri ta miƙe tare da zama Atsakiyar gadon ta kasa kunnenta dan tabbatar wa shin ita ɗin ce ko kuwa.

    Aikuwa Muryan Mommyn ta taji tana cewa.

    “A’a Hajjar Allah Maraba sannu da zuwa Allah raine Jaɓɓama,Jaɓɓama Yottu,yottu”.

    Ita kuwa Khausar wani irin zare ido tayi sai kuma ta miƙe da sauri ta fito abakin Bedroom din ta tsaya Idanunta akan Hajja Nana da Dije dake tsaye agefenta.

     

    Jan zuciya Khausar tayi tare da tsaida idanunta akan Hajja Nana tace.

    “Kece?”.

    Harara Hajja Nana ta watsa mata da faɗin.

    “Toh ki koreni wato ba kyason ganina!?”.

    Tura baki Khausar tayi tace.

    “A’a”.

    Sai kuma ta juya tare da kallon Dije dake tsaye tana kallon falon da dugu ta nufi Dije tana cewa.

    “Oyoyoo Dije nayi kewarki ya gida ya Goggo Nanne?,Ya Yaya Abba?,Ina Sadik?, Yasu Baffa Jauro?, Baffa Sadu?,Baffa Liman?, Baffa Garga? Ina Bishiyar Ƙare zencen ka ina Rafi?”.

     

    Murmushi Dije tayi kana tace.

    “Duk suna lafiya kuma sunce agaisheki da kyau da kyau”.

    Tayi murmushi tace.

    “Allah sarki nima nayi kewarsu sosai”.

     

    Cikin sakin fuska Mommy ta fito daga kichen hannunta riƙe da Flaks da kuma kofi biyu ajiyew tayi, kana ta koma ta ɗauko fruits duk ta ajiye agaban Hajja Nana data hakimce akan kujera sannan ta zauna still fuskarta da Murmushin daya kasa ɓoyuwa tace.

    “Sannu Hajja kunsha hanya ya mutanen gida?”

    Ta ida maganar tana tsiyaya mata Tea a kofi.

    Amsa Hajja Nana tayi ta kai bakinta.

    Mommy kuwa miƙewa tayi ta shiga kichen dan haɗa mata abinci.

     

    Hajja Nana kuwa juyawa tayi tare da kallon Khausar dake maƙale da Dije kana tace.

    “Wato ba zaki gaisheni ba, Dije ce kikayi farin cikin  ganinta ni bakiyi farin ciki da ganina bako!?”.

     

    Ya mutse fuska Khausar tayi tace.

    “Tun ɗazu nake ta gaisheki kina fama da ciye-ciye baki jini ba”.

    Sake baki Hajja Nana tayi tare da riƙe haɓa sai kuma tace.

    “Ubanki nake baciye-ciye ba”

    Hannu Khausar ta buɗe da faɗin.

    “Ɗanki kika zaga dama kin barsa ya kwanta cikin kabarinsa acikin salama da yafi”.

    Ta ida mgnar idonta na ciko da hawaye dan Allah ya sani bata son a zagar mata mahaifi.

    Hajja Nana ta ajiye Kofin shayin dake hannunta ta nuna Khausar da hannu tace.

    “Ki kiyaye nifa,Ki kiyayeni fa Khausar”.

    Tura baki Khausar tayi kana tace.

    “To ai gaskiya na faɗa”.

     

    Ita kuwa Hajja Nana na ɗaukar kofin shayinta tace.

    “To ya miki kyau koma mene ki ƙarata can, yanzu kishirya ki haɗa kayanki tare zamu tafi zamu je muyi azumi acan”.

    Kallonta Khausar tayi kana tace.

    “Mu tafi ina?”.

    Hajja Nana tace.

    “Eh mana Khausar mu tafi Jauro Yaya”.

     

    Da sauri Khausar ta maida kallonta gareta kana tace.

    “To ai muna zuwa hadda”.

    Hajja Nana tace.

    “To ai wannan ba abin damuwa bane idan muka je sai Malam Liman ya riƙa ƙara miki”.

     

    Kai Khausar ta girgiza kana tace.

    “Baza ki gane bane, inada abubuwan da zanyiwa Mamana ɗin nan da kike gani ina taya ta aiki”.

     

    Hararanta Hajja Nana tayi da faɗin.

    “Dama kece mai taya ta aikin ina masu taya ta aikin?”.

    Zare ido Khausar tayi kana tace.

    “Tayi cikin shege ankoreta ta koma ƙauyensu.

    Mai gadin muma ana canza shi saboda shi ya mata ciki”.

    Da mamaki Hajja Nana tace.

    “Ash’sha Subhanallahi ashe gidan naku babu tsaro kenan, ashe ku gidan bayan maita hadda rashin tsaro a’a maza-maza shirya mu tafi”.

    Dai-dai lokacin da Mommy ta fito girgiza kai tayi tace.

    “Kai Khausar bakyajin magana maza ki ɗauka wa Dije abinci ku wuce ɗakin ki”.

     

    Kai Khausar ta gyaɗa tare da wucewa kichen ta daukawa Dije abincin sannan suka wuce Bedroom ɗin.

    Mommy kuwa zama tayi agefen Hajja Nana tare da ajiye mata tiren abinci cikin sanyin murya tace.

    “Hajja Nana kiyi haƙuri da halin Khausar zaku tafi idan hakan kike so”.

    Kai Hajja Nana ta gyaɗa kana tace.

    “Toh babu damuwa amma tace min baki da lafiya da gaske ne?”.

     

    Kai Mommy ta Jinjina kana tace.

    “Eh wallahi kwanakin nan duka ban cika jin daɗi ba bansan meke damuna ba!”.

    Jinjina kai Hajja Nana tayi kana tace.

    “Subhanallah Allah ya sawwaƙa Allah ya yaye.

    Kuma da gaske ne mai aikin ku ta haihu cikin shege?”.

     

    Dai-dai lokacin Hajiya Bunayya da Amina suka shigo falon.

    Ɗaga kai Mommy tayi tare da kallon Hajiya Bunayya data zauna tace.

    “Hajiya ga Kakar Khausar”.

    Murmushi Hajiya Bunayya tayi Idanunta akan Khausar tace.

    “Ai na ganeta Hajja Nana sannu da zuwa ina yini ya gajiya kunzo lafiya?”.

     

    Ita kuwa Amina batare data ƙarasa shiga falon ba ta ɗaga sautin Muryanta da faɗin.

    “Khausar!, Khausar!! Khausar!!!,”.

    Daga ciki Khausar tace.

    “Me?”.

    Afusace Amina tace.

    “Bana son rashin kunya ni zaki yiwa rashin kunya? ina kiranki kina jina ba zaki fito ba aikin san dai tunda na kira ki ina da ɓuƙatar ki!”.

    Jin surutan da take yasa Khausar ta fito tare da tsayawa daga bakin ƙofa ta riƙe ƙugunta kana tace.

    “To ai tunda ke kike da ɓuƙatata kinsan inda dakina yake sai ki shiga ki sameni”.

     

    Cike da kirsa Hajiya Bunayya tayi dariya tana kallon Khausar tace.

    “Kudai in Kun hadu bakwa rabuwa da faɗa kamar wasu ƙananun yara Allah dai ya kawo muku sauƙi kuna na  kamar wuta da Auduga”.

    Juyawa Hajja Nana tayi ta kalli Khausar da Amina kana ta taɓe baki tare da cewa.

    “To ai kinsan haka al’amarin yake, mu zuriyarmu  bama gani mu ƙyale sannan bama ji muyi shiru, sannan su kuma mayu haka suke basason mai baki shiyasa baza’ayi shiri ba”.

    Hajiya Bunayya tayi saurin cewa.

    “Hmmm Hajiya ai tsatsonne na mayu su basu tsotsaba dan mu atsarkake muke”.

    Kallon mamaki Mommy tayi mata kana tace.

    “Hajiya har ke kin yarda da kalmar kenan?”.

    Hajiya Bunayya ta taɓe baki kana tace.

    “Ha’a abinda ake faɗa musu acikin gari mun isa mu hana ne?”.

    Atake fara’ar dake fuskar Mommy ya gushe cikin rashin jin daɗin abinda Hajiya Bunayya ta faɗa tace.

    “Wallahi sukam ba Mayu bane har dake ki yarda kefa komin yaya, ita Uwa ce agareki kuma kakar ’ya’yanki kuma Inde har za’ace suna ciki to mijinki ma yana ciki”.

     

    Hajiya Bunayya kuwa cikin sauri tace.

    “A’a mijina atsarkake yake.

    Uwarsa kuwa ba zan musan ta mata ba yawwa a duniya idan kaji an cewa mutum maye ba zaka musanta masa ba kawai dai abinda na sani mijina ba yayi nima banayi kuma ‘ya’yana na basayi.

    Hajja Nana gaskiya kika faɗa taje can ta ƙarata da baƙin halinta inma tanayi can mata inma ba tayi can mata amma abinda gari dai ake faɗa tana yi, kuma mutum bashida hujjar da zaiyi musu akan hakan, gwara ma hujjar da mutum zai ɗabbaga tunda ga alamu ke yanzu ko cikin ki dake yawa zubewa bakya ta Allah ƙashi da ita!?”.

     

    Cikin sauri tare da ɗaure fuska Mommy tace.

    “A’a nikam Allah ne ya ƙaddara min zubewar ciki babu wani wanda ya zubar min da ciki”.

    Murmushi Hajiya Bunayya tayi aƙasan ranta tace can miki ƙidahuma.

     

    Khausar kuwa kallon mamaki tabi Hajiya Bunayya dashi kana aƙasan ranta tace lalle Hausawa sunyi gaskiya da suka ce iya ruwa fidda kai”.

    Amina dake tsaye ta watsa Khausar Harara kana tace.

    “Abbah ke kiranki kizo kakar taki tazo da wasu maza suna waje sai kije ku gaisa”.

    Ta ida maganar tare da juyawa ta fice.

     

    Ita kuwa khausar cike da farin ciki ta juya ta fice ta nufi coumpund kasa ɓoye fara’ar fuskarta tayi ganin Yaya Aliyu tsaye yaron Baffanta na Adamawa tare da Yaya Abba cikin jin dadi ta ware manyan Idanunta cike da farin ciki tace.

    “Yaya Aliyu sannu da zuwa ku ƙara so”.

    Ta faɗa tana yin gaba zuwa Falon Lamiɗo dake saukan baki.

    Bayan sun shiga falon sun zauna ta dubi Aliyu still Fuskarta da murmushi tace.

    “Yaya Aliyu yaushe kazo?”.

    Gyara zamansa yayi yana fuskantar ta kana fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

    “Baffanki ne ya tasoni wai sai na kawowa tsohuwar sa kayan azumi shine kuma yanzu Hajja Nana tace sai munzo”.

    Khausar kuwa murmushi tayi kana tace.

    “Hajja Nana rigima”

    Sai kuma ta maida kallonta kan Yaya Abba dake latsa waya tace.

    “Yaya Abba ya karatu?”.

    Ahankali ya ɗago kansa da murmushi afuskarsa yace.

    “Karatu ya ƙare yanzu wannan karon tare zamu tafi da Aliyu can Adamawa idan Allah ya nufa idan munje zan samu aiki Insha Allah tunda kinga Baffan Jimeta yana da hanya da manyan mutane Insha Allah za’a samu”.

     

    aSaki murmushi tayi kana tace.

    “Masha Allah abu yayi kyau”.

    Lamiɗo ya shigo suka gaisa bayan sun gama gaisawa ya fita, Khausar kuwa Anutse ta miƙe tace.

    “Ina zuwa”.

    sannan ta fice.

    Kai tsaye kichen ɗin su ta nufa ta ɗauko Babban Warmers da faranti ta fita.

    Hajja Nana ta bita da kallo baki sake ganin Uban kula me kyau da tsari da tafita dashi.

    Ba daɗewa Khausar ta dawo ta sake ɗaukan Flaks da kofuna.

     

    Har takai ƙofa Hajja Nana data kasa haƙuri tace.

    “Kede akwai Jaira mara kirki tunda nazo kike wani shan ƙamshi kamar baki so zuwa na ba, ko arzikin gaisuwa ban samu ba bare insa rai da ruwan sha, amma wa’annan saboda ‘yan uwanki ne jiki na rawa kin wani kinkimi Uban kula kin fita yanzu kin dawo kin ɗauki Flaks”.

    Kallonta Khausar tayi tare da taɓe baki tace.

    “Kinga sai anjima Ni sauri nake”.

    Tana gama fadar haka ta fice bakinta ɗauke da Sallama tashiga falon.

    Amsawa sukayi tare da kallonta.

    Zama tayi tare da buɗe Warmers din ta ɗauki babban Plate ta zuba musu shin kafa da miyar  da yaji naman kaza sai kuma haɗin coslow kana ta zuba musu shayi dake tururi.

    Yaya Abba yayi Murmushi yace.

    “Da’alama wannan girkin kine saboda wannan ƙamshi”.

    Murmushi tayi amma batace Komai ba.

     

    Acan ɗaki kuwa bayan ankira sallan Azahar Mommy takai Hajja Nana har toilet ɗin ta tayi alwala kana ta fito ta gabatar da Sallah bayan ta idar tayi adduo’i.

    Ta juya ta kalli Mommy dake riƙe da carbi ahannunta tace.

    “Aisha”.

    Cike da girmamawa Mommy tayi ƙasa da kanta kana tace.

    “Na’am”

    Hajja Nana kuwa gyara zamanta tayi tare da tattara duk kan nutsuwarta zuwa kan Mommy tare da cewa.

    “Magana ce mai muhimmanci ta kawoni”.

    Cikin girmamawa Mommy da kanta ke ƙasa tace.

    “Toh ina sauraronki Hajja Nana”.

     

    Hajja Nana kuwa Ajiyar zuciya ta sauƙe kana tace.

    “Magana ce akan Khausar da kuma ɗan Baffanta wato Aliyu”.

     

    Jinjina kai Mommy tayi cike da ladabi tace.

    “Toh Hajja Nana ina jinki”.

    Hajja Nana ta gyara zamanta tare da cewa.

    “Toh zuwa yanzu dai inaga Khausar ta girma, sannan inaga ta gama karatun ta yanzu idan ma bata gama ba to ta kusa”.

    Jinjina kai Mommy tayi kana tace.

    “Eh ta kusa Insha Allah yanzu kam Shekara ɗaya yarage bayan sallah Insha Allah zata tafi ajin ƙarshe na gama makarantar gaba da primary”.

     

    Cikin jinjina kai Hajja Nana tace.

    “Masha Allah Ubangiji ya taimaka”.

    Mommy ta amsa da.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

    Hajja Nana kuwa duk kan nutsuwarta ta tattara tare da cewa.

    “To ai yanzu dai ta samu ta kori jahilci ta yaƙesa, yanzu batun aurenta za’ayi.

    Ga kuma Yayanta kuma ɗan Uwanta za’a aura Matashi magana ya ƙare sannan kuma idan karatun take so ta cigaba idan sunyi aure zata yi acan jahar Adamawa tunda suna da makarantu manya-manya acan dan haka yanzu batun aure ne ya kawo mu nazo dashi za’a haɗa bayan sallah in Allah ya yarda”.

    Akuma dai-dai lokacin Khausar ta shigo ɗakin, cike ka ɗuwa Idanunta na kan Hajja Nana cikin sauri tace.

    “Wai me naji kina cewa?”.

    Cikin isa, gadara, Hajja Nana ta wurga mata Harara kana tace.

    “Batun Aurenki nakeyi”.

    Arazane Khausar ta zare ido kana tace.

    “Wa…..!

     

     

     

     

    *GARKUWAR* taku ce dai MA’AURATA, da masu shirin aure, da masu jego, da yan gayu masu son k’amshi kece raini, da gyaran da zaike  maimaita muku dararen forkon kuruciya*

     

    Ko kunsan Jikinmu na da sinadaran hormones da suke taimakawa dan’adam akan komai musamman lokacin da mace take mu’amalar aure da mijinta. Mafi akasari wannan hormones din ne ke samun matsala ko su yi sanyi koma su daina aiki kwata-kwata shi ne dalilin da zai sa mace tace bata jin sha’awa ko bata san dadin aure ba. Albishirinku ina da kayan da ke taimakawa wannan sinadaran du dawo aiki tukuru don karkato miki da kimarki wajan mai gida sannan su taimakawa wannan sinadaran hormones dinki su dinka secreting din ni’ima wadatacciya da zata taimaka miki ki gamsu mijinki ya gamsu fiye da tunaninki. Note: Kayana ba sa tsinka ruwan ni’ima suna dai taimakawa hormones dinki ne su tsattsafo da ni’imar musamman wacca cutar sanyi ko dattin mahaifa ya dankarar da su ya hana su yin aikinsu yanda ya kamata. Haka zalika idan kina da kyau ki kara da wanka. Zaki iya amfani da magani na na gargajiya wanda zai gyara miki sex hormones din kullum ki kasance cikin humidify wato cikin damshi mai albarka kamar yanda ake son mace. Yana gyara miki mara.

     

    Sai kamshi. Hajiyata daure ki fara amfani da turarena ki ji irin salon kamshin sa salo ne da zai daidaita ki da mijinki ya kankaro miki da kimarki a wajansa. Siyan na gari mayar da kudi gida.

     

    Ga masu buƙata ga number’ wayata wanda nake whatsApp dashi 09097853276 kimin mgn ta whatsApp in har kin tabbatar kin shirya saya mu dai-dai ta, kayana ba ƙanana bane, shiyasa bana harkan karanta, muddin kinsan baki shirya sayaba Please kada kiyi min mgn ki bari sai kin shirya kuɗinki a hannu,  ba ina nufin kayana bana talaka bane, no akwai ƙananan set na masu karamin karfi, banson aimin mgn a ɓatamin lokacin aiyukana a shirme baki shiryaba. Shine karantan da bana so.

    0005388578 Jaiz bank AISHA GARKUWA ALIYU. In kin shirya ga number ta ga kuma account number ta wanda in mun gama mgn zaki turo kudin ki, kana insa miki kaya a mota, duk ƙasar da kike kayana zaije gareki, amman fa in kinada dalilin zuwan nasune🤝🏻sayan na gari meda kudi  gida.

     

     

    GARKUWAR MA’AURATA

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 8

    Sakayyah 8

     

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 8_

     

    _NA_

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

     

    *Free page ne ƴar uwa in sun ƙare ko kinga littafin SAKAYYAH a a waje ba a cikin Groups na na SAKAYYAH ɗin da nabuɗeba, toh na satane kuma na Allah ya isane, kana na Yaseen doguwane😂 bulluƙutu kuma baƙar mutuwa… Dan haka biya ki karanta cikin Salamah yar uwa ba haƙƙin kowa kanki, littafin SAKAYYAH 1k ne kacal 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276. Sai in saki a Group ki karanta abinki Nana lfy fata lfy*

     

    Masu son kayan Ɗa’a akwaisu Available.

     

    Motar tayo kansu gadan-gadan.

    Aruɗe M Jameel yace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n!Hasbunallahu wani’imal wakin!! A’a su waye wannan suna da hankali kuwa!?”.

    Cike da al’ajabi Moddibo ya zuba musu ido tare da ƙoƙarin yiwa motar key sai kuma ya gaza yin komai ya zubawa motar ido ganin gada-gadan fa ta nufi kansu haiƙan ƙadaran.

     

    Sai da motar tazo gab dasu sai kuma ta kauce ta hau titi ta wuce.

    Wani irin nannauyan ajinyan zuciya mai masifan ƙarfin M Jameel ya dire tare da meda kansa ya jingina da kujerar.

     

    Shi kuwa Moddibo Idonu ya tsirawa motar cike da mamaki sai kuma ya motsa laɓɓansa a saman lips ɗinshi ya furta.

    “Wannan wani irin tuƙi ne?.

    Tuƙin ganganci ne ko kuwa dai da nufi ne?”.

    Dalilin da yasa ya tsaya ma atunanin sa ko ɗaya daga cikin ‘Ya‘yan Malam Arɗo ne sai kuma yaga saɓanin haka.

    Key yayiwa motar tare da kallon M Jameel dake lumshe da ido a hankali yace.

    “J nayi zaton ɗaya daga cikin ‘Ya‘yan Malam Arɗo ne ya biyo mu shiyasa na tsaya, amma inaga basu bane wata ƙil ɗan koyon tuƙi ne”.

    Ya ida Maganar batare daya ɗauki abin da muhimmanci ba.

     

    Kai M Jameel ya gyaɗa da faɗin.

    “Allah ya kyauta amma na tsorata da ganin yanda sukayo kanmu kamar da gayya suka yi sun tsinka min zuciya saura kaɗan fa su hau kanmu”.

    Girgiza Kai Moddibo yayi kana yace.

    “Da alama dai ‘yan koyo ne!”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da gyara zamansa, kana suka cigaba da tafiya.

    Kai tsaye masallaci suka nufa kasancewar lokacin sallar Azahar yayi, bayan sunyi parking ne suka fito suka nufi cikin masallacin, aƙofar masallacin suka tsaya kusan tare sukay addu’ar shiga masallacin.

    _“Auzubillahil Azim,Wabiwajhihil Kareem,Wasulɗanihil Ƙadiym,Minal Bismillahi Wassatu Wassalamu Ala Rasulullah.Allahummaftahliy Abwabal Rahmatik”_.

    kana suka shiga.

     

    Bayan sun idar sun fito daga masallacin M Jameel ya juya ya kalli Moddibo yace.

    “Muje gida muci abinci”.

    Da gefen ido

    Moddibo ya kalleshi tare damotsa lips enshi  zaiyi magana.

    M Jameel yayi saurin ɓata fuska tare da cewa.

    “Ba zakaje ba ko?”.

    Murmushi Moddibo yayi tare da juyawa akalar motar zuwa gidansu M Jameel.

    Yanzu ƙira’ar Sheykh Jabeer suke saurara har suka isa.

     

    Bayan sunyi parking suka shiga Babban falon gida Adining suka zauna sukaci abincin shikam Moddibo kaɗan yaci ya bari.

     

    Miƙewa sukayi suka fita Fitowarsu daga falon yayi dai-dai da ƙarasowar Hajiya Karima wajen M Jameel yace.

    “Aunty Karima ina yini”.

    Ba tare data amsa ba ta watsawa Moddibo kallon tsana tace.

    “Maƙale anzo kenan?”.

    Cikin ɗan sakin fuska yace.

    “Ehh”.

    Cike da mamakin halayensa da ƙarfin halinsa tace.

    “To wai kai dan Allah ka rabu da bawan Allah nan da dukiyar mahaifinsa mana ko zai samu yayi abin kansa!”.

     

    Cikin takaici M Jameel yace.

    “Dan Allah Aunty ki ƙyale Moddibo da irin wa’annan kalaman mana, na sha faɗa miki shi ba irin mutunen da kike zato bane, ta ya zan fahimtar da ke?”.

    Baki ta taɓe tare da juyawa tabar wajen kamar zata tashi sama.

    Shi kuwa Moddibo lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓaɓɓansa na ƙasa tare da kiran sunan Allah aransa.

    Araunane M Jameel yace.

    “Dan Allah Moddibo kayi haƙuri da abinda Aunty Karima keyi maka”.

     

    Cikin kula Moddibo ya dubesa cikin yanayin nutsuwarsa da kuma ƙasaitarsa yace.

    “J.kada ka damu inda sabo ai yaci ace na saba da halin Aunty abinda tun tasowar mu a haka nake da ita abinda tun bamu wuce shekaru shida-shida a duniya ba take min, har yanzu da muka bawa talatin baya, ai ya zama man shafawa kawai dai abu biyu ke sawa ban taɓa yi mata wonkin babban borgoba”.

    Ya ƙare mgn tare da nufar ɗakin M Jameel.

     

    Cikin jinjina kai M Jameel ya bi bayansa  yana mai al’ajabi abinda Modiyke ɓoyewa tsawon shekaru da yake cewa dalilin dake hanasa taka mata birki, yayi ya gaya masa kuma sam yaƙi.

    A ha dai suka isa, suna shiga ɗakin Moddibo ya kwanta bisa kujera tare da lumshe idanunsa alamun bacci zaiyi.

     

    Acan gidansu Lamiɗo kuwa Mommy ce zaune yayin da Asma’u ke zaune daga ƙasa gefen ƙafafunta ta ɗago kanta tace.

    Mommy asatin nan zamu koma makaranta gashi har yanzu Khausar bata dawo ba”.

     

    “Wallahi kuwa gashi duk kwana biyun nan ba muyi waya ba, dan munfi sati da yin mgn”.

     

    “Ayyah Allah Andi Meyesa”.

    Cewar Asma’u

    Kai Mommy ta jinjina tare da cewa.

    “Kuma Idan ka kiransu ba zai shiga ba sai dai idan su suka kira ka”.

     

    Gyara zama Asma’u tayi tare da cewa.

    “Gaskiya Mommy Idan ta kira kice ta dawo tasan ana komawa za’a fara karatu gadan-gadan”.

    Mommy tace.

    “Inasha Allah zan faɗa mata”.

    Daga nan sai suka ɗan ci gaba da hida, daga bisani sukayi

    Sallama sannan ta tafi.

     

    Acan Rugar Jauro Yaya kuwa yau sati da rasuwar Baffa Umaru baki ɗaya basu da cikakkiyar walwala duk da cewa sun dawo da sabgoginsu kamar da sai dai ciwon na nan aransu.

     

    Khausar kuwa sosai tayi sanyi tun da akayi rasuwar bata cikin hayyacinta shiyasa bata samu ta kira Mommy ta ba.

    Kasancewar jiya akayi adduo’ar bakwai Baffanta da yaransa duk sun koma bayan sunyi exchange na number ita dai ta Mommy ta basu. tare da yiwa Khausar al’ƙawarin kai mata ziyara wataran…

     

    Anutse Khausar ta juya ta kalli Yaya Abba cikin sanyin murya tace.

    “Ayyah yaya Abba dan Allah ka bani wayarka zan kira Mommy na”.

    Kallonta Yaya Abba yayi cike da tausayi duk tayi wata iri yace.

    “Toh shikenan amma ki bari sai gobe ki kirasu dan yau network bashi da kyau koda kin hau kan Bishiyar ma ba zaki ji magana ba”.

    Kai ta gyaɗa masa kana tace.

    “Toh Allah ya kaimu”.

    “Amin”.

    Ya amsa tare da miƙewa ya fita.

     

    *GEMBILA*

    Washe gari da safe tunda gari ya waye Malam Arɗo ke ta kiran wayar Moddibo awaya amma ba’a ɗagawa.

    Shi kuwa Moddibo Anutse ya farka daga baccin daya koma tare da furta.

    _“Alhamdulillahil Lazi ahyana bada amatana wa’ilaihil nushur”_

    Wayarsa dake gefe ya janyo ganin Miss call ɗin malam Arɗo bar katai da yayi ne ya sashi ajiye wayar.

    Kana ya miƙe ya shiga toilet.

    Tare da addu’a a baki nai

     

    Wanka yayi wanda ya ɗauke sa kimanin minti talatin kana ya fito yana mai faɗin.

    _“Gufranaka”_

    Suman kansa yake tsanewa da baby pink towel mai taushi.

    Yayinda yake sanye da jibgegiyar bathrobe pink color mai masifar taushi wacce ya saƙale igiyoyinta a ƙugunsa.

    A hankali ya zauna agaban dressing mirrow tare da,

    Jona handdryer kana ya kunna tare da gyara zamansa da kyau bisa kujerar, dressing mirror ɗin tare da fara busar da sumar kansa mai ɗan karen sulɓi.

    56 seconds yayi zuwa 1 minute yayi yana jujjuya kan handdryer ɗin tare da sa hannunsa ɗaya dake riƙe da madaidaicin Kum.

    A hankali ya ajiye dryer din tare, da buɗe wani gora mai haɗe da man gashi na musamman, wanda Ummi ce ke haɗa musu, ɗan tsiyaya yayi kana ya murza tafin hannunsa tare da shafa.

    Wani irin sheƙi da ƙyalli mai ɗaukan ido suman nasa ya farayi tare da fidda wani ni’imtaccen ƙamshi.

    wani ƙum mai laushi wanda yafi na farin ya ɗauka tare da bin gashin nasa ya mishi tafiyar tsutsa,

    Wow masha Allah, kamar saƙan taburma haka gashin ya kwanta da salo mai burgewa.

    Goge tafin hannunsa yayi da towel ɗin dake bisa ƙafaɗarsa, kanaya

    lakato lotion ɗin sa mai daɗin ƙamshi ya shafa jikinsa baki ɗaya.

    idonsa ya lumshe tare da kauda kansa lokacin da yake shafawa cinyoyinsa mayin,

    fuskarsa ya ɗan shafawa, mai ɗin tare da sa yatsarsa babba ya kwantar da gashin giransa na gefen dama, kana yasa babbar yatsar na hagu ya kwantar da na gefen hagun. sannan ya ɗan tsiyayi man kanshin ya shafawa tattausan sajensa dake kwance lip-lip ya shafa, wani irin sheƙi sajen keyi yana fitar da sanyayyan ƙamshi.

    Anutse ya Miƙe ya buɗe durowarsa ya ɗauki jallabiyarsa mai masifar tsada da taushi Kalar Army green, kana ya zaro tattausan boxer and singlet farare ƙal-ƙal,

    ɗan sunkuyawa yayi ya sanya boxer ɗin ba tare da kalli surarsa ba.

    Kana ya miƙa tare da dai-dai ta zaman robor a gugunsa,

    Bathrobe din ya kwance, kana ya saƙalashi bisa wata yar Kekkyawar masaƙali dake gefen drowersa, singlet ɗin ya saka, kana ya zira tattausar jallabiyar dake zuba sheƙi da ƙyalli wacce kai da ka gani kasan taja kuɗi.

    baƙin hirami ya jawo, sanya kana ya naɗe kansa da hirami tare da sako jelar ɗaurin ta gefensa na hagu tsayawa yayi agaban Dressing mirrow tare da ɗaukar kwalbar turaren mai masifar ƙamshi ya feshe ilahirin jikinsa dashi wayarsa ya ɗauka tare da sanya wa a aljihun gaban rigarsa  kana ya fice.

     

    A motarsa ya shiga bayan ya buɗe gate sannan ya fice kana ya sake fitowa ya rufe gate ɗin.

     

    Aƙofar gate ɗin gidan Malam Arɗo yayi Hong mai gadi ya buɗe masa yashiga Babban gida ne sosai sai dai kallo ɗaya zaka yiwa gidan kasan mamallakin gidan mutum nai mugun maƙo da kirta babu wani fentin arziƙi ajikin ginin gidan haka zalika ginin ɗakunan single rooms ne cikin haraban gidan kuwa koda flow babu daga can kusan ƙaramin ƙofar da zai sadaka da cikin gidan rijiya ce babba anyi masa murfin ƙarfe fitowa Malam Arɗo yayi yana murmushi.

     

    Ɗan guntun  Murmushin gefen baki  Moddibo ya mayar masa tare da cewa.

    “Ina kwana Malam ɗazu ka kira ina bacci”.

    Ya ida maganar yana shiga ɗakin ɗaya daga cikin matan Malam Arɗo mai suna Hajiya Zainabu domin Malam Arɗo ya ɗauki Moddibo tamkar jika.

     

    Wara ido Moddibo yayi yana kallon Hajiya Zainabu yace.

    “Hajiya ina kujerun ɗakin?

    Indai ba kujera Ni gaskiya bazan zauna ba”.

    Sai kuma ya juya tare da kallon Malam Arɗo yace.

    “Malam dan Allah asamu kujeru saboda idan sukayi baƙi su samu inda zasu zauna”.

     

    Hararansa Malam Arɗo yayi tare da cewa.

    “Ba kai bane kake lissafin duk abinda zai cin yemin aljihu kasan yanda gyaran makarantar nan ya cinye min kuɗi kuwa?.

    Yanzu ma abu biyune yasa na kira ka na farko motata ta ɓaci zaka kaini Rugar Jauro yaya sannan kuma  muyi magana akan ƙara kudin school fees ɗin yara dan gaskiya saina fanshe kuɗin dana kashe a school fees ɗin forko Aradun Allah.

     

    Kai Moddibo ya jujjuya tare da yar kwaffa hana yace.

    “Toh ba matsala ai ka’ida iyayen yara.

    Yau kuma mai yasami motar ta lalace ne? Ko kuma sa maine bazaka iya ba”.

    Yana mai laluben aljihunsa yace.

    “Duka biyu, ta lalacen kuma yau du-du-du  da naira ashirin da biyar na tashi”.

    Kai Moddibo ya sunkuyar yana mai kallon wayarshi yace.

    “Kuma har ina Rugar Jauro Yaya yake da nisa ne!?”.

     

    Da sauri Malam Arɗo Yace.

    “Koma da nisa  kai zaka kaini dan badan ka matsa min akan gyaran makarantar nan ba da wataƙil in canza mota kuma da ko ban canza a ai bazan rasa kuɗin da mai ba”.

     

    Murmushi Moddibo yayi kana yace.

    “Dama wataƙil ne Malam koba ayi gyaran makaranta ba da wuya ka canza wannan motar.

     

    Dariya Hajiya Zainabu tayi tace.

    “Aikam Moddibo ka faɗi gaskiya”.

    Anutse Moddibo yace.

    “Koma dai menene dan Allah Malam ayi ƙoƙari asa musu kujeru dubi fa ba laida ba Capet ba kujere ba tiles sai siminti kawai dan Allah ka daure kasamu tiles da kujeru”.

     

    Murmushi Hajiya Zainabu tayi tare da yiwa Moddibo alamar jinjina da hannu kana tace.

    “Allah ya maka albarka”.

    Tayi maganar yanda Malam Arɗo ba zai jiba.

     

    Kai Malam Arɗo ya gyaɗa da faɗin.

    “Naji wuce muje”.

    Taɓe baki Moddibo yayi kana suka fita.

    Ɗakin Uwar gidan Malam Arɗo suka shiga mai suna Hajiya Ramatu,

    Kwance suka same ta akan faranda ta shimfiɗa ta burma.

    Gefenta Moddibo ya ɗan zauna bisa dakalin dake mazaunin Mlma Arɗo cikin mutuntaka yace.

    “Ina kwana Hajiya ya jikin?”.

     

    “Da sauƙi Moddibo ya ƙoƙari?”.

    Tace tana mai kallonsa, kauda kansa yayi tare da cewa.

     

    “Alhamdulillah”. yana miƙewa.

    Yace.

    “Ai dole ma sanyi yata kamaku ba Capet ba kujeru asanyin garin nan kam dan Allah Malam asamu kujeru inba haka ba zasu ta cutuwa sanyi zaita kamasu sannan ya batun fitar da ita wajen?”.

     

    Tsaresa da Ido Malam Arɗo yayi kafin yace.

    “Moddibo! Moddibo!! Moddibo Kafita idona baka iya lissafin komai ba sai lissafin yanda za’a cinye min kuɗina ko”.

     

    Shi kuwa Moddibo kai ya karya kana cikin sanyi yace.

    “Ai gaskiya ne Malam ita lafiyar nan dole aneme ta”.

    Harara ya galla masa tare da faɗin.

    “Ai mun gama magana da Basiru na basa kuɗin da zai isa”.

     

    Shi kuwa Moddibo kai ya jinjina yace.

    Malam munyi magana da Basheer kuɗin ba zai isa ba Malam fita waje fa ba abune mai sauƙi ba”.

    Saurin Kallonsa Malam Arɗo yayi yace.

    “Na fahimta wato har ƙarana suke kaiwa wajenka to kaiɗin Ubana ne da zaka sani inyi!?”.

     

    Murmushin gefen baki Moddibo yayi wanda ke ƙarawa fuskarsa kyau yace.

    “A’a Malam niba Babanka bane ai shawara ce dai”.

     

    Shi kuwa Malam Arɗo kai ya gyaɗa yace.

    “Toh shikenan naji zanyi”.

    Sallama Moddibo yayi wa Hajiya Ramatu sannan suka wuce ɗakin Malam Arɗo.

    Kallon Moddibo Malam Arɗo yayi yace.

    “Ya batun ƙara school fees ɗin yaran nan?”.

    Shi ma Moddibo Kallonsa yayi kafin yace.

    “Malam duk gyaran makarantar nan da akayi a asusun makaranta akayi school fees ɗin yaran yayi dan angyara makaranta baya nufin sai anƙarawa ɗalibai school fees zaka kashe makarantar ida kuɗin yayi yawa”.

     

    Baki Malam Arɗo ya cuna har Moddibo ya ida magana sai kuma yace.

    “In kashe makaranta fa kace?

    Bayan na gyara makaranta sannan kuma ga lafiyayyun malamai masu ilimi yara suna samun wadataccen ilimi ko za’a samu  ilimi abanza ne? zan ƙara school fees Tabbas zan ƙara”.

     

    Murmushi Moddibo yayi yace.

    “Toh shikenan kamar nawa za’a ƙara?”.

    Sai asannan Malam Arɗo yayi Murmushi yace.

    “Za’a ƙarawa ko wani ɗalibi dubu Ashirin”.

    Wara ido Moddibo yayi yace.

    “Innalillahi gaskiya Malam yayi yawa inma za’a ƙara ya kama dole to bazai wuce aƙara dubu biyar biyar za’a ƙara shima saboda za’a ƙara sabbin malamai ne da kuma sabbin tsare-tsare”.

    Kai Malam Arɗo ya jinjina yace.

    “Toh shikenan tunda ka matsa zan barshi ahaka”.

    Zama Moddibo ya gyara yace.

    “Akwai kuma maganar tafiya musabaƙa na gasar hadda da za’ayi za’aje Noka”.

    Kai Malam Arɗo ya gyaɗa da faɗin.

    “Wannan ba matsala ashirya komai”.

     

    Murmushin gefen baki Moddibo ya kumayi idanunsa akan Malam Arɗo yace.

    “Eh badamuwa Malam wato tunda kasan wannan iyayen yarane zasu biya kuɗin motar da sungulla da komai”.

     

    Dariya Malam Arɗo yayi yace.

    “Atoh ainima dai ina ƙoƙari tunda motoci makarantar nanne ake tafiya dasu ko”.

    Kai Moddibo ya jinjina yace.

    “Ai Malam, Ƙarfe nawa zamu tafi can jauro yayan sannan mai zakaje yi?”.

     

    Cikin sanyi yace.

    “Wata Rugar Fulani ce amma gaskiya akwai tafiya zamu tafi da yanzu tun da kaga ƙarfe tara zuwa sha ɗaya zamu isa Insha Allah,Yawanci ina zuwa karatu can wajen wani Malam Aliyu limamin Rugar tasu sannan kuma anyi masa rasuwa shine nakeso Inje inyi masa ta’aziyya to kaga motata ta samu matsala”.

     

    Jinjina kai Moddibo yayi da faɗin.

    “Allah yajiƙan musulmi toh ba matsala  muje tunda dama yanzu babu abinda nake yi, amma dai zamu dawo da wuri ko tunda kasan akwai ‘yan hadda?”.

    Kai Malam Arɗo ya gyaɗa yace.

    Toh ba matsala Allah dai ya kaimu lafiya”.

    “Amin”. Yace

    Sannan ya miƙe suka shiga mota suka fice kasancewar Ashirye suke.

     

    Moddibo kuwa ƙira’ar Sheykh Jabeer ya kunna suna tafiya yana saurara tare da bin bakinsa tafiya mai ɗan nisa sukayi a haka.

     

    Malam Arɗo ne ya katse shirun da faɗin.

    “Gaskiya wannan tsarin ginin Makarantar yayi kyau Moddibo kayi ƙoƙari”.

    Murmushi Moddibo yayi yace.

    “Uhum Masha Allah”.

    Haka suka cigaba da tafiya suna taɓa hira jefi-jefi wanda mafi yawan hiran Malam Arɗo keyi shi dai Moddibo daga Uhm sai um-um. Koko yace Masha Allah ko Alhamdulillah.

     

    Suna dosan Rugar  Moddibo yaga wajen kamar Rafi hayaƙi na tasowa lokaci ɗaya wani irin sanyi mai ratsa jiki ya ratsa gaba ɗaya ilahirin jikinsa Atake ya lumshe idanunsa tare da cije laɓɓansa na ƙasa.

    Ahankali ya juya ya kalli malam Arɗo yace.

    “Kai Malam garin nan akwai sanyi”.

    Murmushi malam Arɗo yayi yace.

    “Sosai ma kuwa garin akwai sanyi”.

     

    Kai ya jinjina tare da jan numfashi kana ya fesar da huci mai ɗan karen ɗumi.

    Dai-dai lokacin yayi parking a ƙofar gidan malam liman kana  yana motsa laɓɓansa alamar Tasbihi yake.

    “Subahanallahi”. Ya furta a hankali sabida tsarin garin yayi matuƙar ratsa shi.

     

    Yaya Abba da shigowarsa kenan ya isa garesu tare da miƙawa Moddibo hannu sukayi musabaha kana yace.

    “Sannun ku da zuwa fatan kunzo lafiya?”

     

    Kai Moddibo ya gyaɗa da faɗin.

    “Alhamdulillah”.

    Kallon Malam Arɗo Yaya Abba yayi yace.

    “Tsoho mai ran ƙarfe”.

    Murmushi Malam Arɗo yayi da faɗin.

    “Ya akayi ɗan saurayi”.

    Cikin alamun sanayya yayi musu jagora, har cikin ɗakin Malam Liman.

    Cike da mutuntaka daddataku Malam Liman yake musu marhabin da zuwa.

    “A’a Malam Arɗo kaine tafe, sannu da zuwa, on laleko mon njabɓa ma mon laleko bagare”.

    Sai kuma ya juyo ya kalli

    Yaya Abba kana yace.

    “Jeka kawo musu abin taɓa wa”.

    Kai yaya Abba ya gyaɗa sannan ya miƙe ya shiga cikin gida.

    Ba jimawa ya dawo hannunsa riƙe da Akwashi guda biyu akan faranti sannan ya koma ya sake ɗauko kofi guda biyu ya buɗe akwashin daya fi girma Gashesh-shen naman ragone da aka masa gashin ruwa ruwa yayin da ɗaya akwashin ke ɗauke da madaran shanu mai ɗumi Yaya Abba yace.

    “Bismilla kuci”.

    Bai jira jin mai zasu ceba ya miƙe yabar wajen.

     

    Shi kuwa Moddibo lumshe idanunsa yayi sakamakon ƙamahin naman daya ratsa hancinsa da kuma yanda gashin yayi kyau a ido da farko baiyi niyyan ciba amma ganin yanda gidan yake atsaftace da kuma masu gidan ga wani irin ƙamshi dake tashi yasa ya fara cin naman cikin nutsuwa tare da zuba madaran sosai yaci dan baƙaramin daɗi naman yayi ba, gashi dama baiyi breakfast ba.

    Malam Arɗo ma sosai yaci sannan yasha madaran wanda shi kuwa kirtansa ke hamada ci sai yazo nan yake kashe tsatsan haƙoransa shiyasa ba cika fashin zuwa duk wata yana zuwa sai biyu.

     

    Bayan sun kammala ne Malam Liman yashigo ya zauna daga gefen Malam Arɗo ya bashi hannu sukayi musabaha.

    Malam Arɗo yace.

    “Fatan mun same ku lafiya ya kuma muka ji da ƙarin haƙuri?”.

     

    Kai Malam Liman  gyaɗa tare da faɗin.

    “Hakuri mungode Allah”.

    Malam Arɗo yace.

    “Allah ya jiƙansa da rahma da kuma dukkan musulman da suka rigamu gidan gaskiya”.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum”.

    ya amsa.

     

    Shima Moddibo cike da girmamawa yace.

    “Malam ya mukaji da haƙuri Ubangiji Allah ya jikansa da Rahman Allah ya haskaka makwancinsa”.

    Malam Liman ya amsa da.

    “Ameen”.

     

    Baffa Liman ya kalli Malam Arɗo yace.

    “Muje ka gaida Babbar Addarmu wacce take madadin mahaifiyarmu”.

    Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana yace.

    “Toh ba matsala muje”.

    Ya ida Maganar suna miƙewa.

    Baffa Liman da malam Arɗo na gaba yayin da Moddibo da yaya Abba ke bayansu Moddibo na ƙarewa yanayin garin kallon sosai garin ya burgesa ko ina ka duba tsaf-tsaf babu alamar ƙazanta ko datti.

     

    Bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga gidan Hajja Nana lokacin tana zaune atsakar gidan kan ta burma.

    Baffa Liman ya kalli Hajja Nana yace.

    “Ga Yayana kuma ɗalibina yazo zai gaisheki”.

     

    Tace.

    “Ayyah sannunku da zuwa”.

    Sannan ta miƙe ta shimfiɗa musu darduma dake tsaf dashi babu alamar datti ajiki komai na gidanta tsaf babu datti duk da stufanta amma komai nata tsaf yake.

    Sosai garin da mutanen garin suka burge Moddibo komai na garin akimtse.

    Gaisawa sukayi da Hajja Nana sannan suka yi mata ta’aziyya madara mai ɗumi tasa aka kawo musu. Koda sukace Alhamdulillah fir tace dolefa susha ita baƙo baya zuwa wurinta ya fita baici komaiba.

    Madarar kawai Moddibo yasha kasancewar ya ƙoshi agidan malam Liman Aransa kuwa sai yaba karamci da dattakon mutanen yake.

     

     

    Aɓangaren Khausar kuwa tana can rafi tare da Dije da Sadik sunje ɗiban ƙwan Zabbi da kuma kayan lambu dake hannun Khausar bayan sun gama suka fito kallon Sadik da Dije Khausar tayi tace.

    “Tunda wayar yaya Abba na hannu na zanje Bishiyar ƙare zancenka in Kira Mommy na”.

    Kai suka gyaɗa mata da faɗin.

    “Muje toh”.

     

    Bayan fitowarsu daga gidan Hajja Nana Moddibo ya ciro wayarsa da niyyar kira sai yaga ba network kallon Yaya Abba yayi yace.

    “Baku  da network ne?”.

    Kai Yaya Abba ya gyaɗa yace.

    “Eh bamu dashi amma akwai inda zaka samu idan kana da buƙata sai muje in kaika wajen akwai service ta nan nede babu”.

     

    Kai Moddibo ya gyaɗa yace.

    “Eh inada buƙata gaskiya muje”.

    Sai kuma ya juya ya kalli Malam Arɗo da Baffa Liman yace.

    “Bari zamuje ya rakani in sami network ina so zanyi kira”.

     

    Baffa Liman yayi Murmushi yace.

    “Yau ka shigo Rugar Fulanin da basu da network sai anje annema ko?”.

    Dan murmushin Moddibo yayi tare da shafa sajensa zuwa gyamunsa daya ƙawata kyawun fuskarsa.

    Malam Liman ne yace.

    “Abba in kunje  ku karasa  cikin Rafi Modibbo  yayiwa Jauron garin nan ta’aziyya sannan kuce yazo munada boƙo ne”.

    Jinjina kai Abba yayi sannan suka fita shi kuma Malam Arɗo da Baffa Liman suka wuce can gida domin ƙara karatu.

     

    Suna fita Moddibo ya kalli Yaya Abba yace.

    “Kai sanyin garin kun nan yayi yawa bari na ɗauki Jacket nasa”.

    Ya faɗa tare da nufar motar ya buɗe ya ɗauki farin Jacket ya ɗaura akan Army green ɗin jallabiyarsa da yayi masifar yi masa kyau.

     

    Murmushi Yaya Abba yayi Aransa yana yaba baiwar kyawunsa da kuma iya Dressing ɗin sa.

    Ta cikin wata siririyar hanya dake ɗauke da korayen ciyayi masu kyau da ƙamshi suka ratsa.

    Sai wani  lumshe  ido Moddibo keyi yana jin kamar ya tabbata awajen saboda yanda garin ya tsaru komai nasu mai kyaune.

    Ta Cikin wannan Hanyar suka ɓulla har Rafi Yaya Abba nata yi masa hira shi dai daga Uhm sai Um-um saiko Masha Allah.

    kasancewar sa ba mutum nai me surutu ba.

     

    Suna shiga cikin Rafin Moddibo ya dunƙule hannunsa waje ɗaya jin sanyin wajen yafi na cikin garin juyawa yayi ya kalli Yaya Abba kana yace.

    “Muma muna da sanyi amma sanyin ku yafi namu sosai”.

     

    Kai Yaya Abba ya gyaɗa yace.

    “Sosai ma ai tanan kam munfi sanyi”.

    Jinjina kai Moddibo yayi yace.

    “To ku riƙa rage Bishiyoyi mana sanyin be damun ku?”.

     

    Yaya Abba yace.

    “Aikuwa mu munajin daɗin sanyin”.

    Moddibo yace.

    “Masha Allah”.

    Acan cikin rafi kuwa Sadik riƙe yake da ƙwan Zabbi mai yawa yayin da Khausar ke riƙe da ma daidaicin kwando ahannunta wanda ke ɗauke da,Inabi,Tuffa, Mangoro,Abarba,Kwakwa, Lemo,da sauran kayan itatuwa yayin da ɗaya hannunta ke riƙe da wayar Yaya Abba tana dannawa Sadik ya juya ya kalleta yace.

    “Khausar da kin haƙura da danna wayar nan sai mun tsallake wannan ruwan dake gudu kinga akwai duwatsu aciki”.

    Still hankalinta na kan wayar tace.

    “Kada ka damu ai ina kallo”.

    Kai ya gyaɗa mata  sannan suka cigaba da tafiya.

     

    Yaya Abba kuwa yana ƙoƙarin karya kwanar da zai sadasu da Bishiyar ƙare zancenka ya hango Baffa Jauro acikin Rafi juyawa yayi ya kalli Moddibo yace.

    Gacan Baffa na Jauron garin nan da Malam yace mubiya kamasa ta’aziyya”.

     

    Kai Moddibo ya gyaɗa yace.

    “Toh mu ƙara sa”.

    Kai Yaya Abba ya gyaɗa sannan suka nufi wajen Moddibo kuwa wayarsa ya ciro a aljihu yana duba ko akwai network ata wajen Dai-dai lokacin da Khausar ta iso wajen baki ɗaya hankalinta da nutsuwar ta nakan wayar tana saka number Mommy.

     

    Kallon Dije Yaya Abba yayi wacce tuni ta tsallake ƙoramar ruwan yace.

    “Dije har kun ɗebo ƙwoyin?”.

    Kai Dije ta gyaɗa masa kana tace.

    “Eh Ya Abba”.

    Moddibo kuwa sam bai lura da mutum agabansa ba, ya ɗago ƙafarsa na dama zai tsallaka yashiga rafin kenan, ita kuma Khausar ta ɗago ƙafarta na hagu zata tsallaka tafita a rafin ji kake gub  suka bugi juna da ƙafafunsu.

    Tagal-tagal Khausar tayi baya zata fadi yayin da shikuma Moddibo da ƙyar ya tsaida kansa daga faduwar da zai yi.

    Ita kuwa khausar Atsorace ta saki kwandon kayan Marmarin dake hannunta  tare da kai hannu ta riƙe rigarsa da hannu ɗaya yayin da ɗaya hannun ke riƙe gam da wayar Yaya Abba.

    A kuma lokaci guda ta rumtse idanunta tare da sakin kara.

    Shi kuwa Moddibo cikin hanzari yakai hannu ya riƙota sai alokacin idanunsa suka sauƙa akan fuskarta ita.

    Ita kuwa Khausar sassayan numfashi ta fesar jin an riƙeta bata faɗiba yasa ta ɗago kan  Idanunta ne suka sauƙa akan fuskar  Moddibo.

     

    Lokaci ɗaya jikinta ya ɗauki rawa na tsananin tsoro da firgicin ganinsa kawai sai ta sake hannunsa tare da rintse Idanunta tayi baya zata faɗa cikin ruwan,Cikin zafin nama yasanya Lallausan tafin hannunsa ya riƙo hannunta tare da fisgota ta tsallaka sai yayi wucewarsa batare daya juya ya kalleta ba.

    Ita kuwa khausar banda rawa babu abinda jikinta keyi cikin rawan murya tace.

    Ka-ka-kayi ha-ƙuri ban gankaba shiyasa, shi kuwa Moddibo ko juyawa baiyi ba bare yaji abinda take faɗa yabar wajen.

    Sai alokacin Yaya Abba ya lura da yayan itatuwan ta data zubar yace.

    “Ya haka Khausar mai yasa bakya kallon gabanki in kina tafiya?”.

    Cikin rawan murya tace.

    “Tsautsayine”.

    Tafaɗa tare da barin wajen aranta kuwa tunani take yau kuna Moddibo Arugar mu me ya kawo sa? kuma mai ya haɗa sa da yaya Abba? to me ya zoyi? da wannan tunanin ta isa Bishiyar ƙare zancenka tana isa ta hau kan dutse. dake farko ta zauna tare da sa hannunta ta riƙe reshen, kana ta kiran number Mommy.

     

    Shi kuwa Moddibo bayan sun karasa wajen Baffa Jauro.

    yace.

    “Ina yini Baffa fatan mun same ku lafiya ya kuma ƙarin haƙuri?”.

    Baffa Jauro kuwa cikin yanayin sauƙin kansa da kuma dattako ya amsa da.

    “Haƙuri Alhamdulillah fatan kunzo lafiya?”.

    Moddibo ya amsa da. “Lafiya Ubangij Allah yajiƙan sa da rahma idan kuma tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani”.

     

    Baffa Jauro ya amsa da.

    “Ameen”.

     

    Yaya Abba ya kalli Baffa Jauro da faɗin.

    “Bari muje na rakasa Bishiyar ƙare zencen ka kuma Baba Yace kaje tare suke da Malam Arɗo”.

    Kai Baffa Jauro ya gyaɗa kana yace.

    “Adawo lafiya”.

    Miƙewa sukayi suka nufi Bishiyar ƙare zancenka tun kafin su isa Moddibo ke jiyo suturatai da dariyar mutane Aransa yace to lafiya dai.

     

    Suna ƙarasawa yaga tsoffi,Matasa,maza,da mata kowa maƙale da waya akunnensa ahankali kunnuwansu ke jiyo masa kamar sautin Muryan Khausar da mamaki ya ɗaga kansa gefen yamma idanunsa suka sauƙa akanta saman dutse kana kanta na bisa reshen Bishiyar.

    Aransa yace to ashe ga inda ta samo ɗabi’ar hawa bishiya wato garin ne dole sai akan bishiya ake waya wannan shine gado.

     

    Ya juya tare da kallon yaya Abba yace.

    “Dole sai na hau kan Bishiya zanyi wayar?”.

    Girgiza kai Yaya Abba yayi yace.

    “A’a ko akan dutsen ma zaka samu network”.

     

    Jinjina kai Moddibo yayi yace.

    “To ku maida ƙa’ida mana mata su hau kan duwatsu maza su hau kan Bishiya idan ya kama dole ne sai an hau kan Bishiya ko kuma ku maida lokacin yin wayar mata daban lokacin yi. Wayar maza da ban kusa tsari da ƙa’idar musulunci ku dena gwamutsuwa haka”.

    Jinjina kai Yaya Abba yayi yace.

    “Gaskiya ne kabamu shawarar data dace Insha Allah za’ayi haka zan faɗawa Baffa Jauro ayi haka”.

     

    Moddibo kuwa cewa yayi.

    “Ai ya kamata ayi haka yanzu Meye amfanin ga mata asama sannan ga maza aƙasa ko kuma duk suna gwamutse maza da mata ko da duk kan ku ‘yan uwane ai yakamata ayi abu duka bisa tsarin Addini ko ba haka ba bai dace ba duk da cewa yawancin ku ’yan uwane amma akwai auratayya atsakanin wasu”.

     

    Cikin jin daɗin Nasiyyar da ya masa da gamsuwa Yaya Abba yace.

    “Hakane Insha Allah za’a gyara malam”.

    Ita kuwa khausar sam batasan Moddibo sun zo wajen ba.

    Bayan sun gama gaisawa da Mommy.

    Mommy tace.

    “Khausar kwana biyu baki kira ba kuma kinsan ba zai yiwu na kira kiba”.

    Araunane Khausar da mutuwar Baffa Umaru ya dawo mata sabo tace.

    “Mommy ankashe Baffa Umaru har gida aka kashesa Mommy agaban idanuna aka kashesa!”.

    Shi kuwa Moddibo hankalinsa na kan yiwa Yaya Abba magana bai san mai take faɗa ba juyawar da zai yi yaji tana cewa.

    “Mommy har anyi sadakan bakwai hankalina ne bai kwanta ba”.

    ta faɗa hawaye na zuba daga idanunta.

    Shi kuwa Moddibo ido ya zuba mata ganin yanda hawaye ke kwaranya daga idanunta.

    Khausar tace.

    “Mommy ai zakizo kiyi mana ta’aziyya ko?”.

     

    Mommy da mutuwar ya kashe mata jiki tace.

    “Insha Allahu zamu zo, nasan idan na faɗawa Abbanki ba zai hana ba, ki shirya idan nazo zamu taho tare, dan Asma’u tazo tayi min magana batun zaku koma makaranta, kishirya kayanki idan muka zo zamu tafi tare idan Hajja Nana ta yarda”.

     

    lumshe Idanunta tayi tace.

    “Baza ma ta hana ba Insha Allah idan kunzo zamu tafi tare dan dama tace zanje Ɓadamaye wajen Baffa na nacan kuma sunzo ta’aziyya mun haɗu dasu, sannan ma Addata Ikki tazo mun haɗu da ita sai wani lokaci zanje Ɓadamaye nama karɓi number su, suma sunce dan suna sauri ne kuma mun haɗu amma da zasu je su duba ni anma munyi canjin number”.

     

    Cikin sanyi Mommy tace.

    “Toh shikenan babu damuwa ki shirya idan nazo zamu taho Insha Allah gobe zamu zo ta’aziyya”.

    Sallama Mommy ta mata.

    Juyawar da zatayi Idanunta suka sauƙa akan Moddibo daya tsareta da ido saida ta kusa faɗuwa saboda tsoron ganinsa.

    Da ido ya mata alamar  ta saƙƙo kafin ƙiftawa da Bismillah kuwa ta diro ƙasa.

    Kallon Dije dake jiranta tayi tace.

    “Mu tafi”

    Yaya Abba ya miƙa mata kwandon kayan Marmarin ta data zubar yace.

    “Gashi kin zubar dasu na ɗebo miki”.

     

    Kamar wacce aka fisgo maganar daga bakinta tace.

    “Banaso ka bashi na bashi”.

    Sai da ta rufe bakinta asannan ta tuna mai ta faɗa hannu Dije ta fusga tace.

    “Mutafi”.

    Shi kuwa Yaya Abba gyara riƙon kondon yayi.

     

    Shi kuwa Moddibo ɗaya daga cikin duwatsun wajen ya samu ya zauna tare da kiran wayar M Jameel.

    M Jameel na ɗagawa Yayi Sallama.

    Amsawa Moddibo yayi tare da faɗin.

    “Kada kaje kata nemana nasan zaka ne meni bana nan sannan ka kira wayata kaji akashe ina wani ƙauye ne da mukaje da Malam Arɗo amma Insha Allah zamu dawo kafin Azahar”.

    M Jameel yace.

    “Toh meyasa baka gaya min ba tun ɗazu”.

    Cikin yanayin shaƙuwa yace.

    “Nima zuwan ba zata ne, kuma lokacin nasan kana bacci”.

    Cikin sauƙe numfashi M Jameel yace.

    “Toh badamuwa Allah ya dawo daku lafiya”.

     

    “Ameen”. Yace tare da katse kiran.

     

    Bayan ankira sallan Azahar sun idar kai tsaye wajen motarsu suka nufa Yaya Abba ne ya zo ya miƙa masa kwandon kayan Marmarin da Khausar tace abashi.

     

    Cikin yanayin nutsuwarsa da kuma sanyin murya sa yace.

    “A’a Nagode amma ka ajiye awajenka”

    Murmushi yaya Abba yayi yace.

    “To ai bani ce na baka ba Khausar ce tace abaka”.

    Yana gama faɗa ya buɗe bayan motar ya saka masa.

    Malam Liman ma ya basu Zabbi Baffa Jauro kuma ya aiko musu da ƙwan Zabbi Hajja Nana kuma ta aiko musu da zuma sannan suka yi musu sallama suka tafi Moddibo kuwa yaba karamci ci halaccin mutanen sukayi.

     

    Suna shiga cikin gari ya wuce da Malam Arɗo gidansa ya ajiye sa sannan ya sauke masa ƙwan Zabbin da kuma Zabbin da goran zuma.

     

    Malam Arɗo yace.

    “Ka ɗauki Zabbin da kuma ƙwoyin mana”.

    Kai Moddibo ya girgiza yace.

    “A’a wannan zumar ma ya isheni”.

    Ya ida maganar tare da jan motar ya fice zuwa gidansa.

     

    Acan ɓangaren Mommy kuwa da daren ta samu Lamiɗo ta faɗa masa maganar rasuwar da kuma son zuwanta suyi ta’aziyya, Cikin jimami yace toh Allah ya kaimu gobe zasu zo.

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

    Washe gari Da safe suka ɗauki hanya zuwa Rugar Jauro Yaya sukayi ta’aziyya.

    Bayan sun gama gaisawa ne Mommy tace.

    “Hajja Nana zamu koma da Khausar dan gobe Insha Allah zasu koma makaranta”.

     

    Kai Hajja Nana ta gyaɗa dan mutuwar ƙaninnata yasa tayi sanyi baki ɗaya.

    Tace.

    “Badamuwa ku koma da ita amma idan an kwana biyu ta riƙa zuwa saboda su saba da ‘Yan uwanta”.

    Kai Mommy ta gyaɗa kana tace.

    “Badamuwa Insha Allah zata zo”.

     

    Kasancewar dama Khausar ta haɗa kayanta tun daren jiya yasa ta dauko jakarta sai kuma ta Rungume Hajja Nana tace.

    “Hajja Nana zanyi kewarki ki riƙa zuwa bishiyar ƙare zancenka kina kirana dan Allah”.

     

    Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.

    “Sai kace kin damu dani bayan rashin kunya kike min”.

    ƙaramin bakinta ta tura tare da ficewa tana cewa nidai zanyi kewarki.

    Baki ɗaya Kakannints suka rakata jikin mota bayan sun haɗa mata tsaraba iri-iri Kama daga, Zabbi, Kaji, Ƙwan Zabbi, Nono jarka-jarka da kuma zuma man shanu.

    Kawai sai Khausar ta fashe da kuka cikin raunin murya.

    Tace.

    “Aranan da nazo kamar haka da Baffa Umaru aka tareni yau kuma gashi babu shi!”.

    Hannunta Baffa Garga ya riƙe cikin rauni da zuba hawaye yace.

    “Kiyi haƙuri Khausar haka rayuwar take idan kaini yau gobe ba kai bane, kuma in sha Allah zasuga SAKAYYAH”.

     

    Hawayenta ta share tare da shiga mota tana ɗaga musu hannu Dije ma kan sosai tasha kukan rabuwa da Khausar.

    Fatan sauƙa lafiya suka musu sannan suka ja motar suka tafi.

     

    Khausar kuwa motarsu na isa harabar gidan Haiydar, Raudat da Ramadan suka taho da gudu suka rungumeta Ramadan ne yace.

    “Addah Khausi nayi missing ɗinki”.

    Kansa ta shafa tare da cewa.

    “Nima nayi missing naku”.

     

     

    “Addah Khausar Barka da dawowa daga zuwanki har gidan yayi haske, amma da bakinan duk saiyayi duhu”.

    Cewar Haiydar

    Ta wani wara manyan Idanunta tace.

    “Kada kayi masu gidan suji”

    ta faɗa tare da ɗaukar Ramadan suka shiga ciki afalon suka zube suna ta hiran bayan rabuwa.

    Cikin sakin fuska Khausar ta kalli Raudat dake zuzzuɓura baki tace.

    “A’a My happiness sis ya akayi ne?”.

    Baki Raudat ta kuma turawa tare da cewa.

    “Ba wani ai naga kinfi son Ramadan”.

    Dariya mai sauti tayi tare da jawota ta ruggumeta.

    Kana suka ci gaba da hirar yaushe gama. sallah kaɗai ke ɗagasu.

     

    Bayan kwana biyu ya kama yau Asabar zasu koma makaranta kasancewar Asabar ne farkon satinsu Alhamis da juma’a kuma Weekend.

    Tun wuri Khausar ta tashi bayan ta idar da sallar asbah tayi Azkharul sabah toilet ta shiga tayi wanka kana ta fito ta zauna gaban dressing mirrow ta shafe jikinta da lotion ɗinta kana ta shafa kajol a manyan Idanunta masu haske sai kuma ta shafa lips dinta Kaɗan tulin sumar kanta dake tsefe ta sanya farin Ribont ta kama ahankali ta buɗe duro ta ɗauki uniform ɗin ta dake goge maroon din wandon ta fara sanya wa sannan tasa ka farin riga sai kuma ta ɗauki farin ɗankwali ta ɗaura kana ta ɗauki maroon din hijab ta Sanya Wanda ya tsaya gwiwarta wani irin kyau tayi na ban mamaki sosai Uniform din ya amshets tamkar dan ita akayi.

    A gaban Dressing mirrow ta tsaya ta ɗauki kwalban turare sun kai kala biyar ta feshe ilahirin jikinta dashi sannan ta ɗauki combos Fari ta Sanya tare da ɗaukar school bag ɗinta ta rataya kana ta fito falo.

     

    Murmushi Mommy tayi tace.

    “Manana kinyi kyau”.

    Ta juya manyan Idanunta tace.

    “Nogode Mommy na”.

    Haiydar kam murmushi yayi yace.

    “Yau za’ayi ruwa da ƙanƙara shugaban ’yan letti ta riga kowa shiryawa”.

     

    Harara ta maka masa batare da tace komai ba ta shirya Raudat sannan sukayi Breakfast suka shiga mota Amina sai Harara take watsa mata ita kuwa khausar bata ma san tana yiba domin aƙasan ranta tunanin haɗuwarta da Moddibo take da kuma irin hukuncin da zai yanke mata.

     

    Suna isa Makarantar lokacin har anfara shiga class cikin sauri sauri Khausar ta riƙe hannun Raudat suka nufi side dinsu Raudat ta ajiyeta a class kana da sauri ta juya, zata fita class ɗin kenan.

    Taji Raudat ta saki ƙara tare da kiranta.

    Da sauri ta juya tare da kamo Raudat ɗin da taga tana jujjuyawa, tsugunawa tayi tare da cewa.

    “Raudat menene ya faru”.

    Cikin kuka da yarfa hannu Raudat tace.

    “Wayyo idona Adda Khausy ido, borkono”.

    Da sauri ta jawota tare da fara hura mata idon.

    Sai kuma ta amshi goron ruwar da Antin su ke miƙa mata.

    Wonke mata fuskar ta ta farayi tare da murza mata idon.

    Cikin Sa’a kuwa ɗan abin da ta shiga idon ya fita.

    A hankali ta buɗe idann nata, da tuni yayi jazir.

    Cikin sanyi  tace.

    “Ayyah Raudy na sannu ko, yanzu dai ya fita ko?”.

    Kai ta gyaɗa mata tare da kama hannun Antin nasu.

    Ganin hakane yasa Khausar juyawa da sauri ta fito ta nufi harabar makarantar.

     

    Shiru ba kowa a tsakiyar harabar alamun  an gama shiga class kenan.

     

    Cikin sassarfa ta fito daga side din ’yan nursery.

    Kana ta nufi sude ɗinsu.

     

    Da sassarfa ta nufi  kan step ɗin.

    Dai-dai lokacin kuma  Moddibo ya fito daga class dinsu  ya nufi ƙasa, a hankali yake take steps din yayinda hankalinsa baki ɗaya yana kan….!

     

     

     

     

    Ki biya ki karanta, kiji ainin manufar labarin kiyi dariya kiyi shauƙi kibi haushi kiki tausayi kiyi kuka. Kiyi murmushi

     

     

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Sakayyah 5

    Sakayyah 5

     

    📝🍇✨💫⏰🤴🏻👹❤️❤️❤️🍇

     

    *SAKAYYAH*

    _Page 5_

     

    *NA*

    *AYSHA ALIYU GARKUWA*

     

    🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

     

    *FREE PAGE*

     

    *LITTAFIN SAKAYYAH NA KUDINE, 1K NE KACAL ki biya ki karanta cikin Aminci ba haƙƙin wani a kanki. 0661110170 GTBank AISHA ALIYU GARKUWA, sai ki turo min shaidar biyanki ta WHATSAPP 09097853276.*

     

     

    Zare Ido Hajja Nana tayi cikin faɗa da fushi tace.

    “Ke! Ke!! Ke!!!.Faɗimatu ki kiyayi kanki dani fa zan tsige Miki fuka-fukinki!”.

     

    Ita kuwa khausar fuska ta haɗe Idanunta tsaye akan Hajja Nana tace.

    “Nifa ba tsuntsuwa bace da zaki tsige min fuka-fuki, ai gaskiyane tsakani da Allah da Annabi mahaifiyata zata tafi kinsa ankawo ni aise ki kirani muyi sallama na musu Allah ya tsare”.

    Ta ƙare mgnar tare da juyawa ta kalli Dija tace.

    “Fisabillilhi ba haka ya kamata ba Dija?”.

     

    Dija kuwa tuni ta sunkuyar da kanta yayin da jikinta ya shiga ɓari tsananin tsoro ya bayyana afuskarta sanin halin Hajja Nana babu wanda ya isa tana magana yana mayar mata da martani!.

     

    Cikin rawan jiki da tsoro daya bayyana amuryanta  tace.

    “Khausar kidena kar ki sake bata amsa ki bata haƙuri”.

    Tana ida maganar ta tsugunna gaban Hajja Nana tace.

    “Goggo Hajja Waɗɗu munyal”.

     

    Hajja Nana kuwa kwaffa tayi kana tace.

    “Aaaa Dija matsa kusa da ita inzo na same ta ai ke ba ruwanki”.

    Ita kuwa khausar batare da tsoro ba tace.

    “Toh kizo mana kawai dan mutum ya faɗi gaskiya don dai ba’a son gaskiya da zaman lafiya ai yakata dai akirani muyi sallama da Momyna tunda dai ansa an kawoni wataƙila ma sai nayi sati biyu ko uku bangan taba aida se akirani muyi sallama ince agaida mutanen gida sannan nayi musu fatan isa gida lafiya”.

     

    Ita kuwa Hajja Nana afusace tace.

    “To idan kece zaki kaisu gida lafiya kada Allah yasa ki kaisu shegiyar yarinya mara ji Ɓee Usmanu La’ilaha illallahu ohoho gabtarel”.

     

    Tuni Baffa Jauro da Baffa Sadu suka shigo idanun su akan yayar tasu suka ce.

    “Lafiya Addah Hajja?”.

    Kai ta girgiza tare da nuna Khausar dake cika tana ba tsarewa tace.

    “Ɓeee Usmanu,Nikam ban taɓa ganin fitsararriyar yarinya kamar ‘yar Usmanu ba”.

    Itade Khausar na jingine jikin bango tana tura ƙaramin bakinta dake ƙarawa fuskarta kyau.

     

    Kallon ta Hajja Nana tayi cikin harara  tace.

    “Nikam Usamanu na Kam ba haka yake ba, haka zalika Mahaifiyarki ko surukata ce bazan mata ƙazafi ba macece mao mutunci amma ke kam waya fitsare miki Ido? Kodan zama tsakiyan Mayun gidan kune yasa kika zama haka!?”.

     

    Khausar dake jingine da bango ta ɗago kanta kana ta wara manyan Idanunta masu kyau da tsari tace.

    “Nikam de kar kice min Mayya idan su Mayu ne toni ba Mayya bace idan kince ni Mayyace sede idan awajenki na gada!”.

     

    Baffa Jauro da Baffa Sadu suka dubi juna alokaci ɗaya cikin ƙasa da murya yanda Hajja Nana ba zata jiba Baffa Jauro yace.

    “Lalle akwai rigima anan? Addah Hajja ba abata amsa idan tayi magana amma ga ‘yar Usmanu daga zuwa tana bata amsa gatse-gatse jika kenan mafi akasari duk zafin mutum jikoki bazasuji tsoronka sosai ba”.

    Murmushi Sadu yayi yana jinjina kai.

     

    Baffa Jauro kuwa kan Khausar ya ɗan buga yace.

    “Kay Hausajo kidena mu ba’a rashin kunya agarin nan!”.

    Ita kuwa khausar inda ya ɗan bugeta tasa hannu ta riƙe tana sosawa duk da cewa bawai zafi ya mata ba ta tura ƙaramin bakinta tace.

    “To ai muma ba rashin kunya bane wannan kam”.

    Dan ƙolo ya mata yace.

    “Dije jata ku tafi”.

    Kai Dije ta gyaɗa wacce se alokacin ta samu kuzarin miƙewa tace.

    “Khausar kizo mu tafi“, Sannan taja hannunta suka fita.

    Suna fita Khausar kuwa hannunta dake cikin na Dije ta janye tace.

    “Yanzu ina zamuje?”.

     

    Murmushi Dije ta sakar mata tace.

    Rafi zamuje”.

    Murmushi mai sanyi Khausar ta sakar mata wanda ke ƙarawa fuskarta kyau tace.

    “Toh mu tafi”.

    Dan sosai weather garin yake abin burgewa da sha’awa.

     

    Cikin nutsuwa suka nufi Rafin suna hira.

    Da sauri Dije ta riƙon hannun Khausar tare da   nunawa mata gefen damansu, masu wasa da birine ke tafiya kana yaran rugagen dake gefe dasu na biye dashi, bisa alamun yanzu kuma rugarsu zasu shiga.

    wani ƙaton Biri yake ta kolongoiso yara nata ja da baya.

    Cike da nishaɗi Khausar tace.

    “Muje muma mu gani”.

    Kai Dije ta gyaɗa mata , kana suka nufi wajen me wasa da Biri suna ganin yanda Birin ke duk abinda aka sashi.

     

    Cike da farin ciki Khausar ta kalli mai wasa da Birin tana ƙara kusawa cikin yara matan tace.

    “Mai Biri yanzu duk abinda na sashi zai min?”.

    Kai mai wasa da Birin ya jinjina yace.

    “Idan kuma baki yarda ba ki gwada ki gani”.

    Kusa da Birin Khausar ta matsa tana murmushi tace.

    “Yauwa yaya salon mugun Malami yake idan zai daki ɗalibansa?”.

    Da sauri ta ware idanunta ganin.

    Birin ya wani ja baya tare da harɗe hannunsa aƙirji kana ya ɓata fuska tare da harɗe sawunsa sai kuma ya ɗauki wani sanda ya riƙe yana nuna Khausar da Dije.

     

    Hannu Khausar tasa ta dafa kafaɗar Dije tare da tintsirewa da dariya mai cike da sautin shauƙi yayin da ɗaya hannun kuma ta ɗaura saman shafefen cikinta tana mai cigaba da dariyar.

    Domin kuwa babu wanda ya faɗo mata arai lokacin da Birin ke gwadawa face Moddibo duk da kasancewarsa ba mutum ne mai Fara’a ba amma duk sanda zaisa a zaneta a makarantar Islamiyya seya sake tamke  fuskarsa..

    Dariya sosai takeyi wanda da yawa cikin yaran tayata sukeyi.

     

    Ganin bata da niyyar daina dariyar ne yasa Dije jan hannunta cikin dariya tace.

    “Khausar Mu tafi,Dariyar me kuma kike haka!?”.

     

    Tsagaita Dariyar Khausar tayi sai kuma lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi tuna wa da tayi Moddibo zai iya jira duk lokacin da tawo ya yanke mata hukunci ahankali tace.

    “Kawai na tuna da wani  Malamin mune”.

    Murmushi Dije tayi tace.

    “Allah sarki shike zaneki kena”.

    Kai ta jujjuya tare da cewa.

    “Wancan da shegen madarar ƙasaita sawa yake a zaneni dai yana nan jiki kamar auduga ai shi dukan ma aikine a wurinsa”.

    Murmushi Dija tayi tare da cewa.

    “Da Goggo Hajja zataji haka sai ta sa mishi al’barka”.

    Baki ta tura ba tare da tace komai ba sukaci gaba da tafiya.

     

    Suna shiga Rafin idanun Khausar ya sauƙa akan Bishiyoyin Piya,  Caɓɓulle, Mangoro, Ayaba, Gwanda, Gwaba, Lemo,  da sauran kayan itatuwa duk sun yiwa wajen ƙawanya.

    Sake wara Ido Khausar tayi ganin bishiyoyin Inabi guda uku a jere,

    Cikin farin ciki ta dubi Dije tace.

    “Harda Inabi Laha’Ila Ha’illalhu Masha Allah zan kuwa ci”.

    Ta ida maganar tare da nufar jikin Bishiyar zata hau.

     

    Saurin riƙe hannunta Dije tayi tace.

    “Kada ki hau Khausar Baffa Liman ya hanamu yace ba shida amfani ‘ya’ya mata su riƙa hawa bishiya ba tarbiyya bace mai kyau”.

    Ita kuwa khausar janye hannunta dake cikin na Dije tayi tace.

    “Ke rabu dashi da ƙa’idojinsa hawa za muyi mu cire abinmu, ai kuma ba har can sama zamu hauba”.

    Langwaɓar da kai Dije tayi kafin tayi magana suka hango wani farin saurayi kyakkyawa daga ɗaya gefen.

    Hannu Dije ta ɗaga masa da faɗim.

    “Yawwa Sadik dan Allah zoka cire mana Inabi wai zata ci”.

     

    Ƙara sowa Sadik yayi idanunsa akan Khausar yace.

    “Dije wannan yarinyar wa kika samo?”.

    Murmushi Dije tayi tace.

    “Yarinyar Marigayi Baffa Usmanu cefa yaron Goggo Hajja”.

     

    Murmushin fuskarsa ya faɗaɗa yace.

    “Allah sarki itace wacce take Birni ko?”.

    Kai Dije ta gyaɗa tace.

    “Eh itace”.

    Ita dai Khausar ba tace komai ba.

    Raɓar bishiyar yayi ya ciro musu Inabi kana ya koma bishiyar Ayaba shima ya ciro yasa musu aƙaramin kwandon dake hannunsa irin na saƙar kaba na gargajiya miƙawa Dije yayi.

    Sai asannan Khausar tace.

    “Mungode”.

    Murmushi kawai yayi ba tare da yace komai ba,

    suka fara tafiya cikin rafin akai-akai Khausar ke lumshe idanunta tana wasa da yatsun hannunta sosai weather garin ya mata daɗi.

    Juyowa tayi ta kalli Dije tare da cewa.

    “Garinku yayi min daɗi”.

    Cikin sauri Sadik yace.

    “Garinmu de kin cire kanki ne a ciki? Ko kin manta nanne tushenki kuma asalinki nanfa cibiyarki take abinne”.

    Dariya tayi kafin tace.

    “Hmmm Shiyasa ma naji daɗin garin inba haka bama masifar wannan tsohuwar yasa bana sha’awar zuwa garin nan”.

    Zare ido Sadik yayi yace.

    “Wacece masifaffiyar!?”.

     

    Asanyaye Dije za tace.

    “Wai Goggo Hajja take cewa masifaffiya”.

    Sake zare ido Sadik yayi se kuma yace.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n”,Ya dubi Dije yace.

    “Meye sunanta ma kika ce?”.

    “Khausar”

    Dija tace.

    Ya maida kallonsa kan Khausar da hankalinta yabi shuke-shuken da kallo yace.

    “Khausar kiyi Istigfari”.

     

    Khausar kuwa kallon mamaki tayi masa kafin tace.

    “Saɓon Allah nayi da zanyi Istigfari?”.

     

    Habarsa ya riƙe  still Fuskarsa ɗauke da Mamaki yace.

    “Goggo Hajjan kike cewa Masifaffiya”.

    Baki ta taɓe tace.

    “Yo ba masifaffiyar bace daga zuwa na fa kawai takama yimin bala’i”.

     

    Kai ya jinjina kafin yace.

    “Toh kar ki sake wallahi in Goggo Hajja taji abinfa baze miki daɗi ba”.

    Cikin sanyin murya Dije tace.

    “Allah de ya kyauta anma wannan baƙunta ai akwai kallo aciki”.

    Ba wanda ya sake magana har suka fito daga cikin Rafin.

    Gani tayi Sadik ya ɗauki wani babban kwando da sunyi ta fiya kaɗan sai ratsa cikin ciyawa ya buɗe ya ɗibi ƙwan Zabbi ya saka acikin kwando.

     

    “Me kakeyi haka?”.

    Khausar ta tambayesa tana kallon wajen da ciyayi masu kyau da tsari suka lulluɓe wajen.

    Murmushi yayi yace.

    “Ƙwan Zabbi nake tattarawa”.

    Cikin lumshe ido tace.

    “Ohhhh lalle kam Masha Allah abamu naci”.

    Murmushi yayi tare da faɗin.

    “Toh babu damuwa”.

    Haka suka riƙa tafiya suna hira jefi-jefi sun kusa fita daga cikin Rafin ne Khausar ta jiyo hayaniya na tashi kamar kasuwa anata surutu da dariya jujjuya wa tashiga yi amma bata ga inda sautin surutun ke tashi ba.Ta dubi Sadik da Dije tace.

    “mene nake tajin hayaniya da surutun nan kam a cikin daji?”.

    Sadik ne yace.

    “Mutanen Bishiyar ƙare zancen kane”.

    Da sauri ta sake duban sa tare da  cewa.

    “Bishiyar ƙare zancen ka?,Wai mene ma’anar Bishiyar ƙare zan cenka?”.

     

    Dije ce tace.

    “Ai mu garin nan bamu da service, Service ɗinmu waje ɗaya ne inde mutum yana so yaje yayi waya seya je ya hau bishiyar ƙare zencen ka anan ne ake samun network idan kina wajen zaki iya kira sannan za’a iya kiranki kina sauƙa daga bishiyar ko kuma kina Matsawa daga wajen bishiyar toh shikenan Service ya yanke ba zaki samu kiyi magana ba kuma shima sai in layin MTN ne ko Zain”.

     

    Cike da Mamaki Khausar tace.

    “Ikon Allah wannan wani irin ruga ne?. Dama ashe har yanzu akwai irin wuraren nan daya rage aduniya?”.

    Murmushi Dije tayi tace.

    “Sosai ma”.

    Ahankali Khausar ta ɗaga kanta nan ta hango manyan tsaunika da bishiyoyi Kallonta ta mayar kan Dije tace.

    “Haba ko wannan manyan tsaunuka da bishiyoyin ai sa tare muku service da network”.

     

    Kai Dije ta gyaɗa tace.

    “Lalle kam da alama shi ya tare”.

    Ta dubi Sadik dake tsintar ƙwai tace.

    “Muje inga wajen”.

    Kai ya gyaɗa sannan yashiga gaba ita da Dije na biye dashi ta cikin wata siririyar hanya Sadik na cigaba da tsintar ƙwo’yin suna fita asirin hanyar Khausar ta hango wani ƙaton bishiyar ɗaurawa dake ɗauke da rassan bishiya masu taren yawa  saura daga sama saura kuma sun zuba yayin da ƙasansa bishiyar duwatsu ne baƙaƙe masu sheƙi ke zube wanda suke kamar kujeru.

    Juyawa tayi ta maida Idanunta kan dandazon mutanen dake wajen mafi yawa Matasane sai kuma Dattijai tana ɗaga kanta sama ta hango Baffa Jauro yana waya.

     

    Dariya ta ƙyalƙyale dashi tace.

    “Baka tsoron ka faɗo ko tsohon nan?”.

    Dije ce ta ɗan bigi ƙeyarta tare da yi mata hararan wasa tace.

    “Baban nawa ne tsoho?”.

    Murmushi Khausar tayi tace.

    “Toh baya tsoro ne kiga ya hau kan bishiya ya ɗane kamar birin can”.

     

    Tsayuwa Dije ta gyara tare da mata hararar wasa tace.

    “Ai shikam dole seya zo nan yayi waya tunda shine Jauron garin nan akwai ɓuƙatar magana da Jauro da sauran Jaurorin garirruwa”.

     

    Khausar kuwa kai ta gyaɗa tace.

    “Ikon Allah lalle de kam irin wannan gari haka”.

    Tayi maganar tana kallon matasan dake sanye da kayan Fulani kowa na amsa wayar, Idanunta ne suka sauƙa akan wata tsohuwa dake waya.

    Ta maida kallonta kan Dije tace.

    “Wannan kuma fa?”.

     

    Dije tace.

    “Tafff!, Wannan ƙawar Hajja Nana ce”.

    Kallonta Khausar ta sake yi tace.

    “Ƙawar Masifa de zaki ce”.

    Sadik dake gyara kwandon ƙwai yace.

    “Ki bari fa”.

    Ta kallesa da manyan Idanunta dake lumshe tace.

    “Ai da gskene Hajja Nana in ba masifa ba meta iya!?”.

     

    Duk mutanen wajen juyawa sukayi tare da zuba mata idanu jin tana kiran Hajja Nana Masifa,Wasu daga cikin mutanen ne suka ce Dije ina kika samu wannan yarinyar.

    Dije kuwa  tayi murmushi tace.

    “ ‘Yar Baffa Usmanu ne”.

     

    Jin Abinda Dije tace yasa sauran mutane dake saman bishiyar kashe wayansu suka sauƙo.

    Wani kyakkyawan Matashi fari ne ya nufosu kallo ɗaya zaka masa kasan akwai wayewa atare dashi yace.

    “Wannan itace ‘yar Baffa Usmanu itace ƙanwar Nenne ko Masha Allah?”.

     

    Kai Dije ta gyaɗa tare da nunawa Khausar matashin tace.

    “Kinga wannan?”.

    Kai Khausar ta gyaɗa.

    Dije tace.

    “Yaron Baffa Liman ne acikin Birni yake karatun sa”.

    Murmushi Khausar tayi tace.

    “Ayyah Allah Sarki yayi kyau”.

    Ya dubi Khausar da murmushi afuskarsa yace.

    “Hi Sister how are you?”.

    Ta mayar masa da martanin Murmushin tace.

    “Am fine how’s everyone?”.

    “Fine Long time?”.

    “Thank God”.

    Dije ta wani ɓata fuska Idanunta akan Khausar tace.

    “Kuyi magana da yaren da zanji”.

     

    Murmushi Khausar tayi tace.

    “Ba wani magana muka yiba kawai gaisawa ne fa”.

    “Toh”.

    Dije tace sai kuma ta maida kallonta kan Matashin saurayin tace.

    “Ayyah Yaya Abba nima ka koya min turancin”.

    Murmushi yayi yace.

    “Ba matsala zan koya miki Kinga ga wata ma zata koya miki”.

    Hira suka cigaba dayi yayin da Sadik ya cigaba da tsintar ƙwoyaye wasu ma da yawa nata tsintar ƙwoyin ko wannensu da alama akwai inda  ƙwan Zabbinsa ke tsayawa akwai waya da ake sakawa atsakanin  waje-jen…

    Baffa Jauro daya gama waya ya sauƙo tare da zuwa inda Khausar take ya riƙe hannunta suka fara tafiya sai kuma ya fara matsa hannun, Janye hannun tayi tace.

    “Wallahi tsohon nan ka iya mugunta inka riƙe hannun mutum kaita matsewa da faratu ni banaso”.

    Murmushi Baffa Jauro yayi tare da sake matse hannun!.

    Ashagwaɓe tace.

    “Wayyo na tuba ka sake”.

    Sake mata hannun yayi yana dariya yace.

    “Ohhh in dai baki daina yiwa Adda Nana rashin jiba, toh fa hakan zanyi ta matse mata ke, ga jiki ba ƙwari ba’ason wahala”.

     

    Sai kuma ya juya ya dubi Dije yace.

    “Dije”.

    “Na’am Baba”.

    Yace.

    “Kishirya Gobe idan Allah ya kaimu da sassafe zaki ɗauke ta kuje kuyi  tsar Nono tare”.

     

    Kai Dije ta gyaɗa kana tace.

    “Insha Allah zan ɗauke ta muje tare”.

    Kallonsa Khausar tayi still hannunta na cikin nasa tace.

    “Nide inda wuya bazan yiba”.

    Dije tace.

    “Ba wuya ai zamu baki man shanu ki shafawa yatsunki yanda zai yi santsi.

    Kai ta gyaɗa tace.

    “Toh shikenan ba damuwa zanje”.

     

    Kallon Dije Sadik yayi tare da bata kwandon Ƙwan Zabbin yace.

    “Ki tafi dashi”.

    Sannan ya juya ya cigaba da tafiya.

    “Khausar kuwa murya ta ɗan ɗaga tace.

    “Kaifa baza ka bimu bane”.

    Girgiza Kai yayi yace.

    “A’a ban ƙarasa ɗiba ba”.

     

    Kai ta gyaɗa tace.

    “Toh inde kazo ka kawo min nawa”.

    “Toh”,Yace sannan suka juya suka tafi.

     

    Suna shiga rugar suka nufi hanyar gidan Hajja Nana kasancewar duk gidan da zaka je seka wuce ta ƙofanta,sannan duk lokacin da taji motsi seta tambaya waye.

    Sallama Dija tayi cikin ladani kana suka shiga, Hajja Nana dake cikin uwar ɗaka tace.

    “Waye”.

    Cike da ladabi Dije tace.

    “Dije ce”.

    Haɓa Khausar ta riƙe tare da cewa.

    “Ikon Allah duk mai wucewa saita tambayesa waye sai kace wata Traffick light?”.

    Ƙasa da murya Dije tayi tace.

    “Aaa ki bari Khausar kiyi ahankali kar taji”.

     

    Khausar kuwa baki ta taɓe tace.

    “Ai wannan abu yayi yawa wannan mulkin mallaka haka ake yi muku agarin nan”.

     

    Daga ciki Hajja Nana tace.

    “Dije keda waye naji kamar ana magana ƙasa-ƙasa?”.

     

    Dije tace.

    “Nida Khausar ce zamuje gida kai saƙo ne ƙwoyi muka kawo”.

    Ita kuwa Hajja Nana cewa tayi.

    “Toh shikenan”.

    Ajiyar zuciya Dije ta sauƙe sannan suka fice.

    Lokacin da suka fita makiyaya sun fara dawowa daga kiwo sannan sanyin magriba na sake sauƙa sanyin ya fara yawa ahaka suka isa gidansu Dije Khausar sai lumahe ido take.

    Suna isa suka ajiye Ƙwoyin.

    Dije na ƙoƙarin shiga ɗaki Khausar da Idanunta suka sake lumshewa tace.

    “Dije muje ki rakani ɗaukan Sweater na sanyi nake ji sosai”.

     

    Kai Dije ta gyaɗa sannan suka fice kallon garin Khausar tayi ko ina baƙi ba  alamar hasken wutar lantarki ta dubi Khausar tace.

    “Wai kam garin nan baku da wuta ne?,tun da nazo banga ƙyallin wuta ko sau ɗaya ba?”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tace.

    “Eh babu amma ana tada Generator”.

    Khausar kuwa hankalin tane ya tashi jin babu wuta garin!.

    Ganin yanda tayi yasa Dije sakin murmushi tace.

    “Kada ki damu kinga Yaya Abba shike tada Generator sannan yake sa kawa mutane Caji kuma aƙofar gidan Hajja Generator yake akwai ɗan haske kaɗan koda ba farin wata, bare kuma in akwai farin wata rana zakiga garin”.

    Sai asannan Khausar ta ɗan saki ajiyar zuciya dan Allah ya sani tana tsoron duhu.

     

    Bakinsu ɗauke da sallama suka shiga gidan shigarsu yayi dai-dai da kiran Sallar Magriba da akayi.

    A tsakar gida suka samu Hajja Nana na alwala, kallonsu tayi tace.

    “Kuzo kuyi alwala kuyi Sallah”.

     

    Kallon ta Khausar tayi tace.

    “Ni gaskiya sanyi nake ji yanzu ma rigar sanyi na nazo ɗauko kuma asamar min ruwan zafi dashi zanyi alwala”.

     

    Harara Hajja Nana ta watsa mata kafin tace.

    “Wa zai samar miki ruwan zafi?,Kina yarinya ƙarama yau har wani sanyi kirki akeyi! da har zaki nemi ruwan zafi”.

     

    Bakinta ta tura amma ba tace komaiba.

    Dije ce tace.

    “Muje gidanmu akwai ruwan zafi sai kiyi acan”.

     

    Kai Khausar ta gyaɗa da faɗin.

    “Toh shikenan”

    Sannan tashiga ɗakin Hajja Nana kasancewar akwai hasken lanta da aka kunna inda trolley ta yake ta nufa ta buɗe tare da ɗaukar Sweater ta sannan ta rufe trolley juyawar da za tayi Idanunta suka sauƙa akan kuliya (Mage) dake kwance akan ɗaya daga cikin gadon Hajja Nana kasancewar gado biyu ne aɗakin sai kuma ɗan shirge-shigen ta na Tsoffin ruga.

     

    Cikin matsananci tashin hankali da ruɗu mara misaltuwa daya bayyana afuskarta take faɗin.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n!!,Hasbunallahu!!!, wani’imal wakin Astagfirullah wa’atubu ilaik!!!”.

    Aruɗe Dije ta shiga ɗakin tana cewa.

    “Lafiya Khausar meye faru?”.

     

    Aruɗe Khausar ke yarfe hannunta takamar wacce ta ƙone duk jikinta na rawa  takasa furta komai numfashinta na wani irin fusga na tsananin tsoro da tashin hankali, da ƙyar ta iya furta.

    “Kuliya”.

    Sai asannan Dije ta lura da kuliyar da har zuwa lokacin ke kwance akan gadon Hajja Nana.

     

    Ita kuwa Hajja Nana wani dogon numfashi taja.

    Dan da kusan mutuwar zaune tayi dan jin irin karajin da Khausar ɗin tayi.

     

    Ita kuwa Dija hannu tasa tashiga koran kuliyar.

     

    Daga can waje Hajja Nana ke cewa.

    “Kuliyar take wa wannan Ihun? zata kasheni tun kwanana bai ƙareba”.

     

    Ina ita kam Khausar bata san sunayi ba, har zuwa yanzu tsalle takeyi a tsakiyar ɗakin tana yarfa hannunta tare da furta duk addu’ar da tazo bakin, istagfari takeyi ba ƙaƙƙautawa.

     

    A gigice Dije ta fitar da kuliyar tana mai cewa.

    “Khausar ki nitsu ya fita, na koreshi, kuliyar Goggo Hajja cefa.

    Cikin tsananin tsoro da rawar jiki cike da gigita,

    Ta fito cikin ɗakin Hajja Nana ta nufi gidan Baffa Jauro tana cigaba da faɗin.

    “Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n

    Ya Allah na tuba ka yafe min”.

    Yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke rawa na tsananin tsoratan da tayi.

     

    Jin shiganta Aruɗe yasa Goggo Nanne fitowa daga ɗaki wato Mahaifiyar Dije.

    Matsawa kusa da Khausar tayi ta riƙe Hannunta tace.

    “Lafiya”.

    Asanyaye Dije tace.

    “Kuliya take tsoro taga kuliyar Goggo

    Hajjs ce take haka”.

     

    Cike da tausayinta Goggo Nanne tace.

    “Ayyah Subhanallah ki kwantar da hankalinki nan babu kuliya kar ki damu Khausar ki kwantar da hankalinki ki nutsu kinji?”.

     

    Kasa furta komai Khausar tayi sai Innalillahi wa’inna ilahi rajiu’n da take yi aƙasan ranta.

    Addu’a Goggo Nanne tashiga tofa mata kafin ta samu hankalinta ya dawo jikinta.

    Jauro daya fito daga banɗaki yana alwala yace.

    “Yau kuliya ce haka kamar wanda taga kura haka?”.

    Ya faɗa yana kallon yanda tsananin razana ya bayyana afuskarta.

    Juyawa yayi yana kallon Goggo Nanne yace.

    “Lalle wannan baƙunta akwai saɓani a cikinsa. Ita Addah Hajja ba zata iya rayuwa babu kuliya ba ita kuma wannan ga tsoron kuliya”.

     

    Tana sakin ajiyar zuciya tace.

    “Nide bazan sake shiga ɗakinta ba shegen ɗaki ga tarukuce ga duhu sannan ga kuliya wannan ɗakin har macizai za asamu acikinsa bazan sake shiga ɗakinta ba”.

     

    Murmushi Goggo Nanne tayi tace.

    “Ki kwantar da hankalinki kada ki damu tashi kiyi alwala ga ruwan zafi abuta”.

    Batace komai ba ta miƙe ta ɗauki butar ta zaga bayi sannan ta fito tayi alwala ɗakin Goggo Nanne suka shiga da Dije cikin ɗakin duhu.

    Araunane Khausar tace.

    “Daƙin duhu ni gani nake ma ko ina akwai kuliya”.

     

    Dafa kafaɗar ta Dije tayi tace.

    “ki kwantar da hankalinki nan babu kuliya”.

    Ta ƙare mgnar tana kunna lantansu mai ɗan karen haske,

    Kai kawai ta jinjina tare da sauƙe ajiyar zuciya ganin hasken, sannan ta tada sallah suka idar da Sallah maghariba Khausar kuwa jingina bayanta da jikin bango tayi ta fara addu’a.

    Dije kuwa miƙewa tayi zata fita, Kallon ta Khausar tayi tace.

    “Ina kuma zaki je?”.

     

    Juyawa Dije tayi ta fuskance ta tace.

    “Zanje in dafa mana ƙwoyin da kika ce kina so ne”.

    “A’a kibari ba da fawa zamuyi ba soyawa zamuyi ina akwai attaruhu da albasa da kuma maggi?”.

    Kai Dije ta gyaɗa tace.

    “Eh akwai”.

    “Ok to kibari sai munyi Azkhar”.

    “Toh”,Dije tace.Sannan ta dawo ta zauna suka cigaba da yin Azkhar ɗin Khausar nayi da ƙarfi Dije na binta wani ta iya wani kuma bata iya ba sai Khausar ta tsaya ta gyara mata suna zaune har akira Isha’i suka Idar…

     

    GEMBILA

    Anutse Momy ta gama shirin baccinta bayan tayi addu’a sai kuma ta lumshe Idanunta ahankali ta sake buɗesu ta juya kwanciyar ta daga hagu zuwa dama sai kuma ta tashi ta zauna baki ɗaya kewan Khausar ɗin ta ke damunta acikin yini ɗaya da bata kusa da ita se taji kamar wata tayi ba tare da ita ba gashi basu da network bare ta kira taji muryanta.

    Jin ƙaran Knowking ɗin ƙofa yasa Momy gyara zamanta kana ta bada izinin shiga,Anutse Haiydar ya shigo bakinsa ɗauke da Sallama kana ya zauna kusa da Momy.

    Murmushi Mommy tayi tace.

    “Haiydar lafiya ko kana bukatar wani abu?”.

    Kai ya girgiza yace.

    “Momy wallahi yau gidan nan ba daɗi da Addah Khausi bata nan”.

    Murmushi Momy tayi cike da ƙaunar ‘ya’yan nata da kuma yanda suke nunawa juna kulawa tace.

    “Yau kuma?,Ko da yake dama haka kuke bakwa shiri sannan bakwa san rabuwa da juna”.

     

    Fuska ya Marerece kafin yace.

    “Allah yau gidan babu daɗi yau tunda gari Ya waye babu wanda yace min Haiydar kar kayi kaza, Haiydar zo in aikeka, Haiydar bakaji, Haiydar karenani,  Haiydar kada fa kaci komai wurinsu Umma, Haiydar ban girme ka bane kam wai da in na saka abu bazakayi ba, Yau duk babu wanda ya faɗa min haka nayi missing ɗinta! Sosai wlh Momy Ina son Adda Khausi”.

    Murmushi mai cike da shauƙi Momy tayi  tare da zuba musu ido.

     

    Raudat da shigowarta kenan ta Shagwaɓe fuska tace.

    “Wallahi nima nayi kewarta Mommy yaukam tare zamu kwana ko?”.

    Janyo hannunta Momy tayi tace.

    “Autanah ba dole ba yau In kwana dake tunda Addah Khausar bata nan”.

     

    Haiydar ne ya sake kallon Momy cikin yanayin kewar ‘yar uwarsa yace.

    “Momy dan Allah ki kira kice ta dawo munyi missing ɗin ta”.

    Ramadan da Raudat suma sukayi saurin cewa.

    “Please Momy ki kira”.

    Kai Momy ta girgiza tace.

    “Basu da network sai dai idan sunje wajen bishiyar ƙare magarka sun kira”.

    Ramadan yace.

    “Toh yanzu Mommy Gobe wa zai Miki shara?,da wanke-wanke da kuma gyaran falo?”.

     

    Murmushi Momy tayi tana shafa kansa tace.

    “Zanyi ƙoƙari nayi da kaina”.

    Zare Ido Ramadan yayi yace.

    “To wallahi Momy aɗauko Miki Addah Khausi yafi Miki gidan babu daɗi idan bata nan”.

    Murmushi tayi tace.

    “Toh”,Da haka hiran yazo ƙarshe Haiydar ya miƙe kana ya ɗauki Ramadan suka tafi ɗakinsu wanda zai ka fita falon Momy ƙofar nasu na jere da ƙofar falonta,

    ita kuma Raudat gadon ta hau ta kwanta gefen Momyn.

     

    Acan ɓangaren su Moddibo kuwa.

    Zaune yake Atsarerren falonsa da yagaji da tsaruwa kana yana fitar da sihirtaccen ƙamshi mai masifar daɗin shaƙa.

    Yayin da M Jameel ke kwance akan 3sitter da waya maƙale akunnensa, Anutse Moddibo ya juya ya zuba masa Idanunsa tare tsarasa da su, still wayan yake Amsawa ɗauke kansa yayi ya cigaba da operating system ɗin sa kana ahankali ya sake maida Kallonsa kan M Jameel still wayar ne maƙale akunnensa.

     

    Cikin ga jiyawa da wayar da yake yi Moddibo ya zuba masa idanunsa tare da motsa laɓɓansa da suka sake yin pinch kana suka tattare saboda tsananin sanyi da akeyi yace.

    “Wai kai da wa kake yin wayar?”.

     

    Gyaɗa masa kai M Jameel yayi tare da juya hannunsa alamar ya kusa gamawa.

    Ganin haka yasa Moddibo maida hankalinsa kan system ɗin sa yana cigaba da duba muhimman saƙonnin da suke shigo masa.

    Wayarsa dake gefen Centre table ne yayi ƙara hannu yasa ya ɗaga nan yaga sunan Abba na yawo a screen ɗin wato Abban M Jameel.

    Cikin han zari yayi picking call ɗin kana yace.

    “Assalamu alaikum Abba Barka da dare”.

    Daga ɓangaren Abba yace.

    “Barka dai Moddibo ya gida ya kuma ɗalibai?”.

    “Lafiya lau Alhamdulillah Abba”.

     

    “Masha Allah kana tare da Hassan ɗinna ka ne?”.

     

    Murmushi Moddibo yayi wanda ke sake fitar da ainihin kyawun fuskarsa yace.

    “Eh Abba muna tare waya yake tun ɗazu nayi zaton ma da kai yake yin wayar”.

    Abba yace.

    “Aina kira wayarsa naji Line busy shiyasa nace bari na kira ka naga dare yayi bai dawo ba za’a rufe ƙofar gida”.

     

    Murmushi Moddibo yayi yace.

    “Ayyah Abba yau kam abarshi mu kwana tare gashi naga alamun Agajiye yake bacci ma yake ji”.

     

    Kai Abba ya gyaɗa yace.

    “Toh shikenan Moddibo ayi bacci lafiya Allah ya tashe mu lafiya amma gobe da safe kuzo ina son ganin ku”.

     

    Kai Moddibo ya gyaɗa cike da mutuntaka yace.

    “Toh insha Allah Abbah”.

    Kana ya katse kiran.

     

    kallon M Jameel yayi sai kuma ya ajiye System dake kan ƙafarsa ya miƙe ya isa inda M Jameel yake yasa hannu ya cire wayar daga kunnensa ya duba screen ɗin sai yaga number ba suna saidai aƙasan Number ansa Bahrain wato ƙasan Bahrain.

     

    Kallon M Jameel yayi yace.

    “Ooo kaida Jalaludeen ne dama?”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa yace.

    “Eh shi ya hana ince da kai dashi nake waya”.

     

    Murmushi M Jameel yayi yace.

    “Yayi kyau”.

    Jalaludeen abokinsa ne tare sukayi karatu a Jami’atul Madina asalin Balarabe Bahrain ne…

     

    Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe yace.

    “Abba ya kira yace baka koma ba har dare yayi sai nace zamu kwana tare yace gobe yana son ganinmu”.

    Kai M Jameel ya gyaɗa da faɗin.

    “Allah ya kaimu”.

    “Ameen”.

    Moddibo ya amsa tare da kallon M Jameel yace.

    Bacci na keji zanje nayi wanka”.

    Zare Ido M Jameel yayi yana kallon Moddibo yace.

    “Wallahi inba cikin kashi na faɗa yanzu ba ba zanyi wanka ba yanda ake tsuga wannan sanyi agarin nan.

     

    Kai Moddibo ya girgiza ba tare da yace komai ba ya wuce Bedroom.

    wanka yayi da ruwa mai ɗumi, kana yayi shirin bacci.

     

    Washe gari, da safe bayan sun dawo daga masallaci sashen Innayi suka nufa lokacin da suka shiga tana zaune kan darduma tana lazimi   M Jameel ya zauna kusa da ita tare da riƙo tafin hannunta yace.

    “Barka da safiya tsohuwa mai ran ƙarfe!”.

     

    Murmushin fuskarta ta faɗaɗa tare da damƙe hannunsa dake cikin nata tace.

    “Jameel Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwarku”.

    Ya amsa da.

    ”Ameen Innayi”.

    Shi kuwa Moddibo kusa da ita ya matsa ya ɗaura kansa akafaɗarta yana mai lumshe idanunsa ahankali yace.

    “Barka da safiya Innayi”.

    Hannunta tasa ta shafa fuskarsa tare da cewa.

    “Fatan ka tashi lafiya ya ƙoƙari?”.

    Ya amsa da. “Alhamdulillah” sai kuma ya miƙe tare da kallon M Jameel da still hannunsa ke cikin na Innayi yace.

    “Mu je ko”.

    Bai jira cewarsa ba ya fice daga sashen nata kana ya nufi nasa yana shiga kai tsaye Bedroom ya wuce ya cire naɗin Hiramin dake wuyan sa da kuma jallabiyar.

    Kai  ya shiga bathroom Masha Allah Komai na cikin toilet wanka ya fesa kana ya fito bakinsa ɗauke da addu’a

    “Gufra naka”.Alokacin daya ziro ƙafarsa ta dama zuwa cikin Bedroom ɗin ya fito M Jameel kuwa jin ƙamshin sabulun wankan da kuma tularensa yasa ya ɗago kai sai kuma ya miƙe ya shiga toilet ɗin.

    Shi kuwa Moddibo zama yayi agaban dressing mirrow ya shafa mayukan sa tare da taje yalwataccen sumarsa kana ya miƙe ya buɗe durowarsa

    Masha Allah kayane aciki masu uban yawa fannin jallabiya da ban fannin yaduka da ban haka zalika fannin ƙananun kaya daban duk da cewa bai fiye amfani dasu ba yana tsaye awajen har M Jameel ya fito daga wanka bai ɗauki komai ba.

     

    Murmushi m Jameel yayi tare da nufar jikin durowar yana cewa.

    “Nasan koda zaka kwana nan ba zaka taɓa cire kayan da zamu sanya ba kai de inba jallabiya ba baka ganewa ko wani irin kaya”.

    Moddibo kuwa murmushi yayi Aransa yana jinjinawa M Jameel yanda yake iya fahimtar komai nasa koda kuwa ƙwaƙa-ƙwaran motsi yayi yasan me yake nufi…

     

    M Jameel kuwa Wani boyel Sky blue mai gidan dara-dara ya ciro musu tare da boxer da kuma singlet Fari ƙal.

    Kallon Moddibo yayi tare da miƙa masa.

    Murmushi Moddibo yayi tare da karɓa yana kallon kayan amma bai ce komai ba sai ya juya ya kimtsa.

    Masha Allah wani irin kyau na musamman Moddibo yayi acikin kayan kalar shigar sai ta kasance tamkar kalar sararin samaniya  ƙirjinsa na ƙiran jarumtaka ya bayyana acikin rigar kana yalwataccen sumar kansa ya kwanta luf yana sheƙi,Anutse ya juya wajen M Jameel dake miƙo masa takalmi da hula kalar sky blue Masha Allah m Jameel ma sosai Yayi kyau acikin kayan sai suka kasance tamkar tagwaye masu tsananin ƙaunar junansu.

     

    Atare suka fice sashen Innayi suka nufa tun daga farfajiyar tsakar gidan Moddibo ya lumshe idanunsa yana jinjinawa tsaftar Kakar tasa har sanda suka isa ƙofanta inda sanyayyan ƙamshi turaren wuta ke tashi.

    Ganinsu atare yasa ta sakar musu da murmushi atare suka shiga ɗakin suka zauna.

    Ta dubesu cikin ƙaunarsu tace.

    “Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwar ku Allah yasanya farin ciki acikin rayuwarku Ubangiji ya tsareku da dukkan sharrin mai sharri”.

     

    Cikin jin daɗin addu’ar da take musu ako yaushe suka amsa da.

    “Ameen Innayi”.

    Innayi kuwa miƙewa tayi ta haɗo musu tea mai zafin gaske saboda sanyin da akeyi sosai amsa sukayi.

    A hankali Modibbo ya ɗan zuƙan tea ɗin ahankali har ya Ida shanyewa zuwa lokacin tuni M Jameel ya shanye nasa.

    Yana ƙoƙarin ajiye Mug ɗin yaga M Jameel ya tsaresa da ido Harara Moddibo ya watsa masa shikuma saiya sakar masa da murmushi.

     

    Kallon Innayi Moddibo yayi yace.

    “Zamu je gaida Abba”.

    Jinjina kai Innayi tayi tace.

    “Idan kunje ku gaishe min dashi”.

    Moddibo na miƙewa yace.

    “Zaiji insha Allah”.

    Sannan suka fice.

     

    Suna fita suka nufi inda mota ke ajiye M Jameel ne ya buɗe gefen Driver ya shiga yayin da Moddibo ya shiga mazaunin mai zaman banza ahankali M Jameel yayiwa motar key  suna isa gate ɗin Moddibo ya fita ya buɗe musu gate sannan M Jameel ya cinna hancin motar yafita saida Moddibo ya sake rufe gate ɗin kafin ya koma cikin motar M Jameel ya tayar suka bar unguwar.

     

    Anutse M Jameel ya dubi Moddibo da idanunsa ke lumshe yace.

    “Anma aikin makarantar nan zai yi kyau domin masu aikin sun san makamar aikinsu”.

    Shi kuwa Moddibo kai ya gyaɗa da faɗin.

    “Sosai Insha Allah”.

    Tafiyar Mintuna Kaɗan sukayi suka isa gidansu M Jameel Hon yayi mai gadin ya taho da sauri ya buɗe musu tamfatsetsen gate din.

     

    Wow  Masha Allah babban gida ne wanda yake ɗauke da Sashe huɗu sai kuma BQ da kuma wajen ajiye motoci kamar takwas zuwa goma sai ɗakin mai gadi cikin gidan akwai shuke-shuke saida basu da yawa sosai bayan sunyi parking sun fito ajere suke cikin tafiyar nutsuwarsu da tazame musu jiki kai tsaye sashen mahaifin  M Jameel ya nufa dasu.

     

    Adai-dai ƙofar da zai sa dasu da falon Mahaifin M Jameel suka haɗu da Hajiya Karima kallon Jameel tayi  kana ta kawar da kanta wani irin tsuke fuska tayi ganin Moddibo abayan M Jameel.

    Cike da ladabi M Jameel yace.

    “Ina kwana Aunty Karima”.

    Fuska ta sake tace.

    “Lafiya lau ɗana ya gida ya kuma ƙoƙari??”.

    “Alhsmsulillah ya amsa”.

    Yana mai shafa sajensa

    Shi kuwa Moddibo cikin tsuke fuska alamun ba wargi ataƙaice yace.

    “Ina kwana”.

     

    Wani irin kallo ta watsa masa kafin tace.

    “Kaska raɓi mai jini anzo kenan?”.

    Shiru Moddibo yayi tare da kauda kansa kamar bai jitaba.

    Sai ma Murmushi da yayi tare da kallon gefen dama inda Aunty Larai Amaryar Aunty Karima ke tare da ce mata.

    “Yau barka dai”.yayi mgnar yana mai tsare fuskarsa da ido alamun yana nazartar ta,

    Ita kuwa Aunty Larai cikin sakin fuska tace.

    “A’a to Moddibo ya kuka tsaya nan ku shigo daga ciki man Jameel”.

    Ta ƙare mgnar tana kallon Jameel tare da juyawa ta nufi cikin falon Daddyn Jameel din.

    Cikin jin yanayin ɓacin ran da kalaman Aunty Karima suka sa mishi yace.

    “Gamu nan shigowa Aunty Larai”.

    Ya kare mgnar tare da

    ɓata fuska cikin rashin jin daɗin abinda ta yiwa amininsa yace.

    “Aunty!Aunty!!, Meyesa!!?, Meyesa!!!?”.

     

    Cikin taune lips inta dubesa tace.

    “Jameel gaskiya ne ai, amma ba zaka gane ba, ba zaka yarda ba  sabida ya fika wayo.

    Kawai dai ya zama dole in faɗa maka”.

    Shiru M Jameel yayi tare da juyawa wajen Moddibo wanda har zuwa lokacin yake tsaye hannunsa M Jameel ya riƙe yace.

    “Dan Allah kayi haƙuri inda sabo yaci kasaba da halin Aunty na roƙeƙa Kayi haƙuri mushiga daga ciki”.

    Murmushi Moddibo ya sakar masa ahankali ya furta.

    “Bakomai me zatayi ya dameni sam babushi tunda tana son aminina”. Yayi mgnar da iya gskyarsakan

    suka shiga cikin falon.

     

    Ita kuwa Aunty Karima  tsaki taja tare da barin wajen tana maijin tsanar Moddibo.

     

    Zaune suka samu Alh  Bashir Mafindi Shahararren mai kuɗi daya sharahara aƙasa da kuma faɗin Afirca baki ɗaya mutum mai tsananin tausayin al’umma da jin ƙai.

     

    Hannu ya buɗe musu cikin nutsuwarsu suka ƙarasa Moddibo ya nufi gefen damansa yayin da M Jameel ya nufi gefen hagunsa ya rungumesu tare da buga kafaɗar su.

    Cike da so yace.

    ‘Yan ta gwayena Ubangiji Allah ya Albarkanci rayuwar ku ina jin dadin ganinku atare kunyi kyau tamkar matasan Larabawa Allah Ubangiji ya nuna min aurenku”.

    Moddibo kuwa murmushi yayi shikam sai ya zo wajen Abban Jameel ake masa maganar aure sai yaji abin banbara ƙwai duk da yasa ba duk lokacin da yazo wajen Abba saiya masa Maganar amman kullum a baƙuwa yake jin kalmar a cikin kunnuwansa.

     

    Cike da ladabi da kuma girmamawa suka gaishesa cike da ƙaunarsu ya amsa da.

    “Lafiya”.

    Kana ya tambaye su ya ɗalibai?.

    Suka haɗa baki wajen faɗin.

    “Lafiya lau Alhamdulillih”.

     

    Zama Abba yayi bisa kujera.

    Kana su kuma suka zauna a ƙasa bisa tattausan carpet ɗin, cikin kula Abba ya  ɗan sunkuyo ya kalli  M Jameel  kana yace.

    “Yanzu kaga damuna ta kusa sauƙo za’a fara shuke-shuke to inason bana zan shuka Auduga mai yawa saboda ina son zan habaƙa  Company dake Marrocco muna buƙatar Auduga mai yawa domin mun samu haɗin guwar da wani ɗan Saudia wurin sufurin Sallayoyi da zannuwan gadaje da kuma Abayoyin na mata”.

     

    Kai M Jameel ya gyaɗa tare da cewa.

    “Eh Abba hakan yayi Allah ya sanya alkhairi”.

    Shima Moddibo yayi Murmushi da faɗin.

    “Allah yabada sa’a”.

    Cikin jin dadi Abban yace.

    “Ameen. Yauwa sai kuma noma shinkafa da zamuyi mai yawa da alkama, dan Company kayan masarufin dake Ɓadamaya yana  buƙatar ninkin abinda yake sarrafa a shekara, domin samun haɗin guiwa da shi’ar ƙasar Niger”.

    Kai suka jinjina alamun gamsuwa kana cikin kula Abban yace.

    “Na sani kuma na fahimta, cewa akan su Asma’u ne ka nacewa karantarwa da kai da amininka. To Alhamdulillah na baku dama, amman ku sani suna gama secondary School, dole ku bar karantar wannan Moddibo ina buƙar taimakonku a Company’s ɗin tunda Allah yayi kun karanci Business ɗin nan kafin ma ku tafi Jami’atul Madina.

    Babana yanzu girma ya cinmini abubuwa sunayi min yawa dole ina bukatar tai makonku”.

    Ya kare mgnar yana dafa kaɗan Jameel.

    Cikin sanyi Jameel ya ɗago kansa ya kalli mahaifin nasa kana cikin sashi farin ciki yace.

    “Allah ya kaimu lokacin Daddy in Sha Allah zanyi maka dukkan abinda kake so, muddin ina raye”.

    Cikin jin dadi yace.

    “Kaifa Moddibo baƙace komai ba?”.

    Murmushi gefen baki yayi tare da cewa.

    “Daddy duk inda J yake to in sha Allah ina nan”.

    Cike da jin daɗin Alh Bashir

    Mafindi ya shafa kansu tare da cewa.

    “Allah yayi muku al’barka”.

    Cike da jin daɗin sukace. “Amin Ya Allah Allah ya ƙara nisan kwana da lfy”.

     

    “Amin Ya Allah”.

    Abba ya amsa tare da nuna musu dinning area da hannunsa, inda Aunty Larai ke shirya dinning ɗin tama mai murmushin jin tattaunawarsu.

    Sai kuma ya kalli Moddibo kana yace.

    “Bismillah kuje kuyi Breakfast”.

    Moddibo kuwa kai ya girgiza a hankali yace.

    “Daddy na ƙoshi”.

     

    Kallonsa Daddy yayi cikin kulawa yace.

    “Meyesa haka ne Moddibo gsky ni bana son yadda kake  in kazo gidan nan kaci abinci sai kaƙi ci”.

    M Jameel ne ya amshi zancen da cewa.

    “Rabu dashi Daddy in baici ba sai muyi masa ɗure”.

    Murmushi Daddg yayi tare da faɗin.

    “Aikam”.

    Moddibo kuwa harara ya wurgawa M Jameel.

     

    Adam ƙanin  M Jameel yaron Aunty Karima  ne   yashigo ganin M Jameel yasa ya faɗaɗa Murmushin sa yace.

    “Yaya Jameel Ina kwana?”.

    Cikin murmushi M Jameel ya mayar masa da.

    “Lafiya lai alhamdulillah Adam ya school”.

    Adam kuwa kallon tsana ya watsawa Moddibo ba tare daya gaishe saba dan gani suke yana amfani da M Jameel ne wajen cin dukiyar mahaifinsu ko kaɗan M Jameel baiji daɗin abinda Adam yayi wa Moddibo ba, haka yasa ya haɗawa yaron fuska.

     

    Acan Rugar Jauro yaya kuwa Washe gari.

    Bayan Khausar sunyi Sallar asbah tare da Azkharul sabah ɗakin Goggo Nanne suka shiga ita da Dije suka gaisheta,

    Ta amsa fuska asake Idanunta akan Khausar tace.

    “Ya kwanar baƙunta da kuma tsoron kuliya?”.

    Murmushi Khausar tayi tana wasa da yatsun hannunta har yanzu Atsorace take idan akwai abinda tafi tsoro acikin dabbobin duniya to kuliya ce da ƙadaggare.

    Dije ce ta miƙe tace.

    “Mun tafi gidan Hajja Nana”.

    “Toh adawo lafiya”.

    Miƙewa sukayi suka fita ahanya Khausar ta dubi Dije cikin sanyin murya tace.

    “Idan munje Kar mu daɗe tsoron gidan nake”.

     

    Kai Dije ta gyaɗa suka cigaba da tafiya bakinsu ɗauke da Sallama suka shiga Hajja Nana dake hakimce akan kujeranta ta amsa Khausar kuwa kusa da ƙafafun Hajja Nana ta zauna tace.

    “Ina kwana Hajja Nana”.

    Ta dubeta fuska asake ta amsa tana jin ƙaunar ta aranta.

    Dije ma gaisheta tayi ta amsa fuska asake.

    Miƙewa Khausar tayi tace.

    “Mu tafi”.

    Kallonta Hajja Nana tayi tace.

    “Ki zauna mutanen garin zasu zo gaisheni zan gabatar dasu awajenki”.

     

    Khausar kuwa narai-narai da idanu tayi har cikin ranta take tsoron gidan Hajja Nana Allah ya sani tana masifar tsorob kuliya, jiki asaɓule ta zauna tare da riƙe Dije suka zauna tare.

     

    Suna zaune Baffa Jauro yazo cike da girmamawa da kuma ladabi yace.

    “Addah Hajja ina kwana”.

    “Lafiya ta amsa”,tare da kallon Khausar dake takure tace.

    “wannan shine ƙanina dake bina”

    Murmushi Khausar tayi tare da gyaɗa kai tace.

    “Baffa ina kwana”.

    Dariya yayi yace.

    “Lafiya Audiii ya fargaban kuliya!?”.

    Baki ta ɗan tura  amma batace Komai.

    Can sai ga Goggo Nanne

    Kusa da Khausar ta zauna tace.

    “Addah Nana ina kwana”.

    Ta amsa da lafiya tare da kallon Khausar tace.

    “Wannan itace matar Jauro wacce kuka kwana agidanta sunanta Nanne ita ce kuma takwaran marigayi yayarki”.

    Kai Khausar ta gyaɗa tana sake damƙe hannun Dije dake cikin nata.

     

    Can sai ga Garga yazo idanun sa akan Khausar ya mata murmushi hannunta ya riƙe yace.

    “Addah Nana ina kwana ya kwanan baƙuwa?”.

    Hajja Nana kuwa taɓe baki tayi tace.

    “Ga tanan matsoraciya saboda kuliya taƙi kwana anan”.

     

    Murmushi Garga yayi yace.

    “Audii ki zama jaruma Mahaifinki fa ba rago bane babban jarumi ne”.

    Murmushi tayi amma  batace Komai ba.

    Hajja Nanan ce tace.

    “Wannan shine Garga shike bin Jauro.

    Can sai ga wata mata tazo itama ta gaida Hajja Nana.

     

    Hajja Nana ta dubeta tace.

    Wannan itace Dijarro matar Garga”.

    Cikin sanyin murya Khausar ta gaisheta,

    Cikin sakin fuska Dijjaro ta amsa.

    Ba daɗewa saiga Liman yazo sanye cikin Alkyabba kansa naɗe da hirami kusa da ƙafafun Hajja Nana ya zaune cike da ladabi da kuma dattako yace.

    “Addah Hajja ina kwana”.

     

    Ta amsa da.

    “Lafiya”.Sannan ta dubi Khausar tace.

    Wannan shine Aliyu Limamin garin nan Uwarmu ɗaya Ubanmu ɗaya mutum ne mai tarin Ilimin addini”.

    Cike da ladabi Khausar tace.

    “Ina kwana”.

    “Lafiya lau ya kwanan baƙunta?”.

    Ta amsa da

    “Alhamdulillah”.

     

    Bayan tafiyarsa sai ga matansa biyu Rabi da Loddo,Kai kawai Khausar ke gyaɗawa.

    Ita de Khausar ta kasa sakewa,Ahaka suka riƙa  zuwa duk wanda yazo Hajja Nana zata gabatar wa da Khausar shi.

    Can saiga Yaya Abba yazo Hajja Nana tace.

    “Wannan shine Abba ɗan ƙanina ne liman shi aka tura karatu birni yana karatun arnanci irin wanda kike yi”.

     

    Abba kuwa ƙasa da kai yayi yana murmushi.

    Ita kuwa khausar kallon Hajja Nana tayi tace.

    “Wai waya ce Miki karatun Arnanci mukeyi?”.

    Hannu Yaya Abba ya ɗaya mata alamar tayi shiru!.

     

    Khausar kuwa ta wani juya masa manyan Idanunta tace.

    “Taya ba karatun Arnanci mukeyi ba tace karatun Arnanci mukeyi ko ance mata acoci muke zuwa karatun?”.

     

    Kallonta Abba yayi cikin harshen turanci yace.

    “Please Khausar Enough, Don’t sey anything again”.

    Zare Ido Hajja Nana tayi tace.

    “Abbah zagina kayi ka juya yare zaka zageni da yaren Arna!??”.

    Kai Yaya Abba ya girgiza yace.

    “Wallahi ba zaginki nayi ba Goggo Hajja na isa in zageki?,Ai Babana ma bai isa ya zageki ba bareni”.

    Kai ta gyaɗa kana tace.

    “Oooo”.

     

    khausar kuwa murmushi tayi tace.

    “Hajja Nana zamu tafi!”.

    Kai ta gyaɗa alamar toh kasancewar duk sun gama zuwa, Sai kuma ta kalli Dije tace.

    “Ki ɗauke ta ki zagaya da ita gidajen kowa ki gabatar da ita”.

    Kai Dije ta gyaɗa sannan suka miƙe suka tafi kamar yanda Hajja Nana ta faɗa haka Dije ta riƙe zagayawa da Khausar duk gida jen ƙannen Hajja Nana da kuma ‘yan uwa aƙarshe suka shiga gida Umar Autansu Hajja Nana…

     

    Abakin ƙofa suka samu Baffa Umaru kallo ɗaya zaka masa kasan jarumin namiji ne mai cike da haiba da kuma ƙwarjini.

    Ya dubi Khausar da murmushi afuskarsa yace.

    “Girman biredi wayon shayi”.

    Murmushi tayi tace.

    “Ni dai ba girman biredi bace”.

     

    Yana dariya yace.

    “Shekaranki nawa?”.

    Tayi murmushi da faɗin.

    “Sha takwas”.

    Ya wara ido yace.

    “A’a, ai babanki ma da kaɗan yafi haka”.

    Ɓata fuska tayi tace.

    Meyesa kuma zaka sa Babana?banaso shi kam baya rasu ba abarshi ya huta mana”.

     

    Murmushi  mai cike da ciwo yayi tare da janyo hannunta ya ajiye ta gefensa kana a yace.

    “Ai nima Babanki mutumi nane Shiyasa duk maganata nake kawo sunansa saboda banaso amanta dashi.

    Ni sa’an sane tare muka taso mukayi wasan ƙasa banaso amance shi ina so ko yaushe arika kiran sunan sa ana masa addu’a”.

     

    Khausar kuwa murmushi tayi tace.

    “Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi”.

    “Ameen”,Ya amsa sannan ya kamata hannunta suka shiga cikin gida.

    Da fara’a matarsa mai suna Adama ta yi musu sannu da zuwa sannan ta shimfiɗa musu abin zama bayan sun zauna ta kawo musu ɗumamen tuwon shinkafa da miyar taushe sai kuma madaran shanu mai zafi.

     

    Kallon Umaru Khausar tayi tace.

    “Har matarka ta gama abinci?”.

    Kai ya gyaɗa ita kuma matarsa murmushi tayi kana tace.

    “Eh saboda shi jarumi ne  baya son zama da yunwa kinsan shine garkuwan rugan nan”.

    Wara Ido Khausar tayi tana dariya tace.

    “Ba wani Garkuwa kawai de kina kurara sane”.

     

    Murmushi  Adama tayi tace.

    “Shikenan duk lokacin da Arnan maƙota suka kawo farmaki zakisan shine garkuwan rugan nan”.

    Murmushi sukayi Dukansu sannan ya fice Khausar da Dije suka wanke hannu suka fara cin abincin bayan sun gama ne suka tafi.

     

    Kai tsaye Ruga suka nufa  suna isa Rugar aka ɗaurewa Khausar shanu sannan Dije ta shafa mata man shanu ayatsu saboda yayi santsi tsugunnawa tayi aka ɗaura mata ƙwayar ya akan cinyarta kana cikin azama ta kai tatsuniya kan bakin n……!

     

     

     

     

     

     

    *WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

     

    _Ina kuke Ma’aurata masu sha’awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau’ikan sirrin sahihan magungunan ma’aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki…Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba’a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al’khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni’ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni’imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu…Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu’umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba…._  _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan  Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu’uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_

    _Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)…Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji  Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu’uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa ‘yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma’aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba’a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma’aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 09097853276 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah ‘yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci…._

     

     

     

    🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,

     

     

    By

    *GARKUWAR MARUBUTA*

  • Gidan Aunty book 2 Page 16

    Gidan Aunty book 2 Page 16

    BOOK 2

    Page 16

    Runtse idanuwanta tahee tayi tana jiran jin fad’uwarta , batayi auneba sai ji tayi ta fad’o jikin mutum, kamshin turaran da bazata ta’ba mantawa ba yana dukan hancinta,’kara runtse idanuwanta tahee tayi , idan mafarki take ma bata so ta farka, a hankali ta soma kiciniyar bud’e idanuwanta da sukai mata nauyi, Daidai lokacin da ruwa me ‘karfi ya fara sakkowa , ita kanta tahee bata san lokacin da ta rungumesa a jikinta ba , tana faman sauke ajiyar zuciya. King kuwa kasa motsi yayi gabaki d’aya sabida yadda zuciyar sa take bugawa da sauri Sauri, shikansa besan dalilin ba , har ynxu kuma be kalli wadda take jikin nasa ba , amma tabbas sai yau zuciyarsa ta motsa, irin motsawar da bata ta’bayi ba sai a kan mutum d’aya sauyin bugun zuciyar ke canzawa . Da Sauri ya hankad’ata baya batare da ya kalli ko fuskarta ba . Adaidai lokacin da ya hankada tahee kuwa bata san lokacin da ta ri’ko rigar jikinsa ba gabaki d’aya Sukai baya zasu fad’i yayi azamar ri’ko ‘kugu ta tare da zuba mata narkankun eyes dinsa za Suka canza kala zuwa ja, gabaki d’aya king ya canza sosai , Hutu da kud’i duk sunbayyana a jikinsa Amma gabaki d’aya fuskarsa babu d’igon murmushi ko alamun ya ta’ba fara’a a rayuwarsa , bin fuskarta ya soma yi da kallo kamar yadda itama ta zuba masa na ta eyes d’in, yarda fuskarta ta nuna alamun tsorone yasa shi lumshe idanuwa tuno fuskar tahee duk lokacin da take cikin tsoro, da Sauri kuma ya ware idanuwansa akan kande da gabaki d’aya hankalinta na kan kallan kyakkyawar fuskarsa, wani gajeran tsaki king yaja da sauri ya d’auke hannun sa a cikinta take a Wajan ta fad’i kasa Sabida yadda kwankwasanta ya bugu sosai har da ‘yar ‘kararta, yadda tayi karan ne yasashi juyawa a Suka ne yana kallanta, amaimakon ya shiga part d’in dada kamar ydda yace musu zai shigo sai kawai ya juya zuwa part d’insa . Yana shiga part d’in gabaki d’aya jijiyoyin kansa suka mimmike kamar yadda ya saba tun lokacin da ta ‘bata , fresh ruwa ya d’auko tare da fito da wani robar magani a jikinsa , tablet uku ya had’a lokaci d’aya ya shanye su tare da jefar da ragowar magungunan, gashin kansa kawai yake cikurkud’awa ,bai san dalili ba , he just need his wife back, lokaci d’aya kuma ransa yayi mugun ‘baci ganin be tsinka wa kowace mari ba ydda ta fad’o jikinsa haka, “ why ! Why ! Why !” Shine abunda king ke furtawa ,sai kuma ya dafe kansa tare da lumshe idanuwansa.

    TAHEE
    Ganin yadda yabar wajan yasa hankalin tahee tashi sosai fatanta Allah ya sa yana lapiya , kamar ta bishi taga halin da yake ciki Haka take jin ranta amma babu dama ganin duhu na ‘karayi , da’kyar ta samu ta lalla’ba ta mike Sabida zafin da ‘kugunta yake mata dan ba ‘karamun buguwa tayi awajan ba, da ‘kyar ta Samu ta Daidai tafiyar, ganin yadda lokaci ya ja haka sosai jikinta da ya bara ‘baci, tana shiga gabaki d’aya suka zuba mata idanuwa, sosai ta tsargu da hakan dan batasan me zatace musu ba , amma amaimakon taga ‘bacin rai wajan ummey sai kyautar murmushi da ta samu , tun kafin tayi magana ummey ta Rigata “ Hala ruwan sama da aka soma yine ya tsayar daku?” Wata ajiyar zuciya Tahee ta sauke da inka kalleta sosai zaka fahimci Hakan , da Sauri kuma ta d’aga musu kai tana sassaita muryarta ” wallahi hajiya na fita ne sai zuwa ya somayi sosai shine na d’an tsaya, da ya ragu kuma sai na manta ‘bangaran sai da nayi ta dubawa sannan na gane “, jinjina mata kai ummey tayi “ Ina saratun?” Zatayi magana saratu ta shigo cikin falon itama cikin girmamawa ta gaishe da gabaki d’aya familyn,tare da bawa ummey hakurin rashin zuwanta da wuri, ummey bata ‘kara cewa komai ba ta mayar da hankalinta kan abincin da take ci, “ ina leman da nace ki taho mun dashi ?” Cewar Ammeey tana kallan tahee , sai alokacin tahee ta tuna da leman da ta watsawa Wanda ya bita , cikin d’an rawar jiki tace “ hajiya dan Allah da manzan sa kiyi hakuri , nazo sakkowa daga matattakala shine ‘kafata ta zame ya zube…” ta ‘karasa a hankali ganin wani irin expression d’in kallon da ta samu wajan Ammeey , Ammey bata san lokacin da ta d’aga murya kamar zata sha ‘kota ta furta “ ya zube ? Menene ya zube ? Leman da nace ki rike ne kika zubar ? Kisan kuwa yadda akai na samo wannan maga….” Bata ‘karasaba tayi saurin toshe bakinta ganin ‘baran ‘baramar da take ‘ko’karin tafkawar ganin gabaki d’aya ilahirin falon sun zuba mata ido , sai ta wayance da “ hope baki ji ciwo ba !? Kinsan irin wannan abun sai kina bi a hankali karya ji miki ciwo “, murmushi abeey ya saki ganin yadda Ammeey ke kula da lapiyar kowa na gidan , Sabida juyawr da tayi yasa yan falon basu kula da gibin taba , ummey kuwa idanuwanta ta zuba Ammeey na d’an sakanni kafun ta d’auke eyes d’inta, itama Ammeey kan kujerar ta koma ta zauna ranta na mugun ta farfasa , wannan ce damar ta ta’karshe da ta samu maganin da zata kashe king, sabida ba ‘karamar guba bace da ko tava ka yayi sai yayi maka illah musamman idan Akace wanine yasha a hankali take tsitstsinka jijiyon cikin mutum,ranta yayi mugun ‘baci sai ‘ko’karin wantar da hankalin ta take , so take ciwan bakinta ya ‘kara kwanaki kafun taje wajan bokanya. Wayarsa Abeey ya d’auka tare da danna wani kira kafun ya kara a kunnansa , bansan me nacikin wayar yace masa ba sai amsar da abeey ya basa “ No son, you have to, zan sa akawo maka can side d’inka “, kafun ya kashe kiran , yana kallan ummey “ ku shirya masa abincinsa akai masa part d’insa yanxu. Hakance kuwa ta faru da kanta ummey ta shirya masa tray d’in hakan ya ‘kara ‘kuntata ran ammey sai bun idanuwansu Kawai take da kallo rai a’bace, ‘yan Matan kuwa kowa sai kakkaucewa yake gudun kar ace shi zai kai abincin dan sunsan tabbas da kun burarran fuska zasu dawo yau ma , gabaki d’aya king ya canza kuskure kadan Kayi masa sai ka gane kuranka a wajansa.kallan sumayya ummey tayi “ sumayya taso ki mi’kawa yayan ku abinci”. Summy kamar zatayi ihu amma badamar yi haka ta kar’bi tray din kamar zatayi kuka, wata dabara ce ta fad’owa summy tayi saurin kallan tahee “ kande d’an zo ki rakani”. Kallan Ammey tahee tayi , taga ta sakar mata ya’ke alamar suje, ajiyar zuciya ta sauke bayan ta kar’bi tray d’in hannun summyn , tunda suka soma tafiya babu Wanda yayi magana a cikin su musamman yadda tahee taji zuciyarta na bugawa da Sauri sauri, Daidai part d’in king sumy ta tsaya tare da nunawa tahee part d’in “ ki shiga ki kai masa abincin sai ki dawo kinji? “, Toh Kawai tahee ta ce mata, sanyi na ratsa zuciyarta , “ zata gansa? Zata ‘kara san yasa cikin idanuwanta?” Gabaki d’aya tanbayoyine suka taru suka tsaya mata a zuciya ganin tana ‘bata lokacine yasa ta nufi dole d’insa a hankali ta tura ‘kofar tashi sannan ta rufuto, a kan kujera ta hangosa dafe dakansa ga idanuwansa da yake a lumshe , ci gaba da kallansa har ta ‘karaso kan center table d’in bayan ta yi sallama a hankali amma ko motsawa baiyi ba , balan tana tasaka ran amsawar tasa, inda yake ta nufa cikin sand’a ganin idanuwansa a kulle, atunaninta ko yayi bacci ne shi yasa batare da tsoro ko fargaba ba ta nufeshi, fuskarta ta Daidai ta da tasa da take a kulle tun daga kan kyakkyawar sumar kansa ta soma bi da kallo har kyakkyawar fuskarsa tasa,ita kanta batasan ya akai ba sai jin hannunta tayi cikin sumar kansa tana sosa masa kan,da Sauri ya bud’e eyes d’insa , lokaci d’aya sukai eye contact da mamaki yake kallanta “ how dare she?” Ita kuma tahee tsorone ya hana ta motsawa ganin tsananin bacin ran dake kwance kan fuskarsa , da Sauri kamar wacce aka tsikala kuma tayi baya zata fad’a kan center d’in cikin azama yajanyota da hannu d’aya , bata fad’a ko ina ba sai kan cinyarsa , ajiyar zuciyar da besan ko ta menene ba yasauke, itama taheen ajiyar zuciya ta sauke daddad’an kamshin turaransa da bazata ta’ba mantawa ba yana ‘kara shigar hanci, a ydda take tana jin yadda zuciyarsa take bugawa da Sauri da Sauri, gabaki d’aya ta shagala hannunta d’aya ta d’ora a Daidai saitin zuciyarsa, cikin raunin murya hawaye na fara sakko mata ta furta “ we missed you so much “, king be san lokacin da ya fincikota yayi wurgi da ida ba , dukda kalamanta sun shiga kunnan sa , cikin azama ya nufeta da shirin tsinka mata mari tayi saurin kulle fuskar tata cike da tsoro, yadda ta tsoratar ne yasa shi tsayawa kallanta , “ why is she behaving like her ? Why ? Me hakan yake nufi ?” Tana ganin ya janye hannunsa ta mi’ke a guje zata gudu ya ri’ko hannunta, tasan tabbas ta tsaya komai zai iya faruwa da azaba ta fincike hannunta saka gudu, jikinsa ba kwari sosai shiysa ta iya fincike hannun ta , gabaki d’aya ‘ko’karin rasa control d’in kansa yayi lokaci guda, mamakin wacce yarinyar ya soma yi , a tunaninshi aljana ce ma dan yadda ya gani kamar aljanace take masa gizo , da ya kulle idanuwansa yadda ta saka hannunta a saitin zuciyarsa ne yake fad’o masa da lokacin daya d’ora hannunsa a kan kugunta, yanasan ya hukunta koma wacece koda kuwa aljanar ce , amma duk lokacin da yayi yukurin yin hakan , wifey d’inshi ce take masa gizo, why?” Yake tanbayar kansa kafun yasaka both hannayensa cikin gashin kansa yana ya mutsasu.

    Tahee kuwa tana fita sai da ta sassaita nutsuwar ta kafun ta nufi part d’in dada lokacin gabaki d’aya sun kammala cin abinci suna tattaunawa , dining din data ga su mimi suna gyarawa ta ‘karasa wajan, cike da iskanci Mimi ta ‘kurawa tahee kallo kamar tasan fuskantar wani abu, hararar da tahee ta buga wata lokacin da d’aya daga cikin masu aikin ne Yaso saka Mimi dariya amma ta danne tare da d’aga wa tahee gira d’aya , d’auke idanuwanta tahee tayi akan Mimi tasan ta biyewa Mimi zasuyi abunda zai jawo hankalin mutanan gidan ne Wanda ko kad’an bata san hakan ya faru. Sun dad’e sosai a part d’in dada gabaki d’aya yadda bikin ilham da wasu abubuwan suke tattaunawa akai. Sai wajan 11 suka koma part d’insu , har lokacin Ammey bata ‘kara ce mata komai ba , itama taheen bata damu da hakan ba ta nufi makwancinta , sai da ta tabbatar da ta kulle ko ina na dakin kafin ta cire abun fuskarta, tunaninsa abunda ya faru a tsakaninsu ne yai ta kaikawo cikin zuciyar ta, ita kad’ai sai faman sakin murmushi take , jan zoban nanne ya fad’o mata a rai da Sauri ta d’auko shi a inda ta ‘boye tana ‘kara binsa da kallo haka kawai taji zuciyarta bata kwanta da zoban ba, da Sauri ta sallaba ta shiga kitchen bayan ta mayar da face d’inta , ashana ta d’auka ta koma dakin nata ganin babu Wanda ya ganta sai faman sakin ajiyar zuciya take , gabaki d’aya windows d’in d’akin ta kulle hatta fanka sai da ta kashe ta yadda iska bazata motsa ba , zoban ta d’auko cike da Bismillah tana kunna masa asha guda d’aya kawai ya soma ci da wuta , ci sosai kamar Wanda ake fesawa kalanzir, abunda yfi bata mamaki ganin yadda tana kunna ashana tun kafin ta kai wajan zoben ya soma ci da wuta sosai , ‘karane ya soma karad’e ko ina na cikin kunnuwanta, me kama da ihu ihu na abun tsoro, lokaci d’aya ‘kofar d’akin ta soma jijjiga kamar zata cire kanta da kanta , windows d’in d’akin ma sosai suka soma jijjiga da ‘karfi, saurin toshe kunnuwanta tahee tayi tana ambatan sunan Allah sosai , ganin duk lokacin da tayi adduar sai zoban nan ya ‘karaci da wuta, tsawan a wanni biyu , har tsawan lokacin kuma kofar d’akin da windows din basu dena jijjigaba ka guru ruwar da take tashi. Lokaci d’aya kuma sai komai ya dakata , ihun ya dena tashi, ‘kofa da windows din ma kamar ba’a ta’basuba, inda zoban yake ta kalla ganin yadda ya koma ‘baki ‘kirin ga wani hayaki da ya soma Tashi daga cikinsa yana ‘bacewa , lokaci d’aya kuma gabaki d’aya zuban ya ‘bace kamar be ta’ba wanzuwa ba awajan. Addua Tahee ta somayi tun tanayi a zuci har ta soma yi a fili tana ‘kara bin ko ina na d’akin da kallo, Ta dad’e tana addua a bakinta kafun bacci ‘barawo ya d’auketa.

    ****** Lokacin da tahee take ‘kona zoban nan da yawa akwai mutanan da basu runtsa ba , musamman mutanan da suke da ala’ka da wannan zoban babu Wanda ya runtsa a cikinsu sabida tashin hankali,ko wannansu cike yake da fargabar abunda zai biyo baya , gabaki d’ayansu kasa ha’kura gari ya waye sukai , karfe 3:00am lokcin da kowa na mahalu’ki yana hutawa gabaki d’aya banda masu ala’ka da zoban da suka bayyana cikin falon su kamar kullum a yola , cike da tashin hankali sai faman kururuwar kiran boyankarsu suke tsawan lokaci, amma babu ita babu alamarta , duk da haka basu ha’kura ba suka dunga kiranta cike da tashin hankali, sun dad’e sunayi kafin suji saukar tsawa akansu , gabaki d’aya suka sunkuyar da kansu alamar girmamawa , bata bayyana ba kamar yadda ta sababa sai amon muryarta mara dad’in ji da ya cika ko ina na falon “ tabbas kun aikata babban kuskure da kuka bari zoben nan ya ‘kone , tabbas lokacin tonuwar asirin ko wannan zai fara daga lokacin da zoben ya ‘bata , yanxu komai ya dawo hannunku Amma kusani gabaki d’aya muguntar da kuka dad’e kunayi tun daga yanxu ya fara warwarewa , ta dawo , ta dawo , bazata ta’ba barin kuba , wannan karan a shirye suke , shirin da bazaku ta’ba warwaresaba,na fad’a muku a farko dawowarta kamar tonuwar asirin kune , toh lokaci yazo , lokacin tonan asirin ko wannan ku yayi “, sai kuma ta ‘barke da dariya mara dad’in ji da saurare. ‘D’aya daga cikinsu ne cike da fargaba ya soma magana “ tuba muke , tuba muke “, sai gabaki d’ayansu suma suka d’au ka , wata tsawar ta daka musu , tun farkon shigowarku na sanar da ku abinda zai biyo baya Aduk lokacin da kuka ‘Kona abun aljanu, kutabbata yanxu lokaci yayi sannan cikin zuri’arku zasu dunga shan jini “ ta sake sakin wata dariyar da ya rud’asu gabaki d’aya. Cike da fargaba d’aya daga cikin su ya soma magana “ ya shigabar mu wannan laifin na abar ‘kauna ce da masoyinta “, yimun shiru , ta fad’a kafun ta cigaba “ babu ruwana da matsalar ku , kanku a had’e yake , duk hukuncin da kuka ga dama kuyi mata babu ruwana , sabida itama yanxu lokacin tonan asirinta ne yazo , lokacin sadaukar da jininkune ya fito , hahahhahahahh, hahahahhahaha jinii, jini,jini , aljanun mu suna bu’katar Jininku, ku tabbata kun gyara abunku a tsakanin ku hahahhahaha “, share gumi kawai suke gabaki d’aya sun rasa bakin magana “ amma wacece wannan shegiyar da take ‘ko’karin ‘bata mana shirin mu ?”, yanxu ma dariya bokanyar tasa kafin ta bud’e musu tafukan hannunta, amaimakon suga wacce ta ‘Kona zoban sai haske ya kashe musu idanuwansu gabaki d’aya , har ‘yar rigan kulle ido suke “bansan taba , bansan wacece ba , sabida duk kogin tsafin mu sun kasa ganin fuskarta, kuma bazaku ta’ba sanin ko wacece ba sai ranar da asirin wasunku zai tonu “, tana kai ‘karshen maganarta ta ‘bace ‘bat.
    Gabaki d’ayan su babu Wanda hankalinsa be Tashi ba , ko wannansu duk da fuskokinsu da yake a kulle hakan bazai hana tsantsan tashin hankalin da suke ciki bayyana ba .

    WASHE GARI

    Kamar kullum kiran sallar asuba ne ya tasheta, hakanan take jin zuciyar ta a sake kamar ancire mata wani dutse me nauyi a ‘kirjinta, ga farincikin ganin masoyinta kuma mijinta da tayi , wani irin dad’i take ji cikin kasan zuciyar ta musamman idan ta tuna abunda ya faru jiya , komai take yi yau zaka ga fuskarta tana sakin murmushi lokaci zuwa lokaci, ko da bata ga fitowar Ammeey ba hakan kwata kwata be dameta ba , damuwarta d’aya ganin har yanxu be shigo part d’in Ammeey ba kamar yadda ya saba , tun d’azu take kallan hanyar shigowa ko zata gansa amma babu shi babu alamarsa , duk da hakan bata karaya sai da ta ‘kara kusan 30 Minutes, nan ma still shiru be shigoba, a sanyaye ta juya har ta kar kwanar d’akinta taji kamshin turaransa ya ratsa mata hanci , da Sauri ta juyo , shi d’inne kuwa , kamar kullum yana sanye cikin ‘kananan kayan yake ‘kara masa kyau da kwarjini, gabaki d’aya ta maida hankalinta kansa shi kad’ai kawai take kallo, shi kansa yaji alamun ana kallansa , a hankali ya d’ago da dara daran eyes d’insa , zuwa inda taji alamar mutum, yana d’agowa idanuwansu ya shiga cikin na juna , gabaki d’aya babu Wanda ya janye idanunsa daga shi har ita, kallon kallon kawai suke yiwa junansu, shi mamakin da yake me yasa tun da ya ganta nauyin da ya tokare masa ‘kirji ya sauka kamar wata aljana ? “, da hannu d’aya yayi mata alamar tazo, a sanyaye tahee ta nufi inda yake, tana zuwa ta saukar da inanuwanta , kallan yadda ta sunkuyar da kai tayi kafun a hankali ya furta “ Ammey ?” , bakinta har rawa yake wajan furta “ tun safe bata fito ba ,”kanshi kawai yayi nodding a hankali kafun ya sauke ‘kafarsa d’aya dayi crossing , lokaci d’aya ta bugu da wani glass na ado a wajan , tun kafun ya motsa tahee tayi saurin ta’ba kafartasa Tanaso taga inda yaji ciwan kamar zatayi kuka ta ke furta sorry , da mamaki ya ke kallanta kafun ya furta “ are you mad ? How dare you ? “,ya ‘karasa da d’aga hannunsa zai mareta , yadda ta kulle idanuwan hawaye na sauka akan fuskarsa ne ya tuno masa lokacin da tahee ta zuba masa coffee, the same reaction d’in da ya gani yanxu , cikin d’aga murya yake furta “ why ? Why ? Me yasa komai irin nata ? Why ?” Ynxu kam tsorone ya kama tahee , batasan me yasa ba , duk lokacin da tagansa sai ta kasa controlling kanta . Muryar Ammeey ce ta katse mata tunaninta tare da ajiyar zuciya , shi kuwa har yanxu idanuwansa na kan tahee da ta kasa kallansa , kallan tahee , Ammey tayi tare da yi mata alamar ta bar wajan, cikin gudu gudu sauri sauri kuwa tabar wajan .
    Samun waje Ammey tayi ta zauna a gefensa , duk Wanda ya kalleta zai san ko bata da lapiya ko wacce take cikin damuwa Sabida yadda tayi zuru zuru, kallanta king yayi na tsawan 1 minutes kafin ya furta “ Ammey baki da lapiya ?”, da sauri ta girgixa masa kai “ nashiga cikin damuwa ne ganin yadda gabaki d’aya ka canza , kwata kwata baka damu da rayuwar ka ba kamar da hakan yana sani cikin damuwa “, amaimakon ya amsa mata sai kallanta da ya ‘karayi “ the mouth ?”, da Sauri ta toshe bakinta, ranta a mugun ‘bace amma tana ‘ko’karin tannewa , murmushi ta d’an sakar masa “ karka damu son, burgewa nayi na daki hakwarana”, lumshe mata ido yayi a hankali kafun ya furta “karki damu za’ayi fixing d’insu da wasu, anytime you’re ready go and meet doctor maryam zan sa tayi miki cikin sauki “, cike da murya Ammeey ta amsa masa kafin ta ‘kara kallansa “ son kaci abinci kuwa ? Kalli yadda ka ‘kara Ramewa fa ?”
    Shiru yayi mata ba tare da ya amsa mata ba , cike da damuwa ta furta“ zansa yanxu kande ta kawo maka , ka tabbata kaci idan ba haka ba bazan samu kwanciyar hankali ba ,” yanxun ma bece mata komai ba sai lumshe mata eyes da yayi “ am going Ammey , ki kula “ , yana kai ‘karshen zancansa ya bar part d’in , da wani irin shu’umin kallo Ammey ta bi bayansa dashi , kafun ta saki wani murmushin da ita kadai ta san ma’anarsa, d’akinta ta shiga bata jima ba ta fito da wani abu a hannunta , batare da ta nemi temakon kowa ba soma girka masa lafiyayyan abinci , kamshi sai tashi yake , tana kammalawa ta ajje a dinning tare da komawa ta d’auko wani abu, warmers din ta bud’e tare da bar bad’a wani abu d’an kad’an a ciki,duk abunda take akan idan tahee dake kallanta daga nesa yadda Ammey bazata ganta ba , da Sauri kuma ta koma d’aki zuciyarta tana bugawa da Sauri Sauri , kwalla kiranta da taje Ammey nayi ne yasa ta saki ajiyar zuciya, da Sauri ta fito tare da karasowa Indai Ammey take , kamar kullum sai da ta gaisheta cike da bar kwanci, kallanta Ammey tayi sosia kafun ta nuna mata trays din, “ part d’in da kukaje jiya kuka kai abincin nan xaki kai and ki tabbata yaci abincin , kinjini ko ?” Kamar da gaske tahee ta zaro ido tana dafe kirjinta “ Ni hajiya ? Kwarankwatsi ballani zaiyi , ki temaka kiyi hakuri “, ajiyar zuciya Ammey ta saki daman abunda take san ji kenan daga bakinta , d’an had’e rai Ammeey tayi kafun ta nuna mata abincin “ maza ki Tashi kikai “ , cike da tsora tahee ta kalli Ammey , cikin zuciyar ta kuwa dariyar Ammeey Kawai take , zata sake ro’kan Ammey ta daka mata tsawa da Sauri tahee ta mi’ke ta nufi dinning , jikin ta sai karkarwa yake ta nufi hanyar part d’in nasa , sai da tayi nisa sosai sannan ta tsaya tana daidaita kanta , a hankali ta bude babbar ‘kofar falon , bakinta d’auke da sallama, sanyin ac da kanshin turaran wutane ya daki hancin sa , gefe guda kuma ga ‘kamshin turaransa da baya fita daga palourn. Babu kowa a cikin falon kai tsaye dinning ta nufa ta ajje tana tuna lokacin da take bashi abinci a baki , gabaki d’aya sai ta zubawa falon idanu tana tuna rayuwar su da sukayi a baya , sai data gama ‘karewa falour kallo, cikin sand’a ta nufi bedroom d’inta na sama , ko tsoron ya zo ya sameta a wajan batayi , tana shiga nan ma d’akin fess yake sai faman tashin ‘kamshi yake , d’akinta yananan kamar yadda yake , babu a bunda ya canza , nan ma bata tsaya ba , ta nufi d’akin dressing room dinta , tana bin ko ina na wajan da kallo , sai data gama ‘kare masa kallo ko tsoran ya shigo ya same ta a haka batayi , tasan yana part d’in abeey shiyasa gabaki d’aya bata damuba ta kutsa kai cikin toilet d’in , bataji alamun motsin mutum ba , sai ji tayi an fusgo hannunta da ‘karfin gaske , ta bud’e baki zata sa ido taji an toshe mata bakin nata da ‘karfi anjin ginata da jikin toilet d’in , zaro idanuwanta tayi a kansa ganinsa sanye da towel kawai , da Sauri kuma ta kulle idanuwanta, azuciye ya furta “ bud’e idanuwanki” da sauri kuwa ta bud’e idanuwan, amma bata kallesa ba sai ‘kasa da ta kalla , akau sashe ya furta d’ago ki kalleni, har yanxu ta ‘ki yadda ta kallesa sai jikinta da ya soma rawa , da ‘karfi ya furta “ ba dake nake magana ba ?” , kuka tahee ta saka masa tana d’ago da idanuwanta, hawayen da ya gani akan fuskarta ne yasashi kulle idanuwansa “ why ? Me ke shirin faruwa dani ? Me yasa nk ganin aljana me irin behavior d’inki? Why? “ ya furta cikin zuciyar sa , kafun ya matsa baya kad’an yana nuna mata hanyar waje , “ idan na ‘kara ganin me kama da fuskarki, uhmm” be ‘karasa ba ya nuna mata kofar da finger d’insa , da Sauri zata kwasa a guje , santsi ya nemi kayar da iya , cikin azama ya ri’kota yadda ta fad’o jikinsane yasa towel d’in kugunsa kwance wa , jikinta da nasa suka hadu waje d’aya ,a tsorace tahee ta saki ‘kara jikinta gabaki d’aya ya dena motsi alamar ta suma .

    Be san me yasa ba , sai kawai ya tsinci kansa da sakin murmushi, murmushin da ya dad’e beyi irin saba , da hannu d’aya ya d’auketa ya fito daga toilet d’in , akan sofa ya ajjeta ya shirya mintuna kad’an ya dawo d’auke da bottle water d’in gabaki d’aya ruwan ya juye mata a jiki a firgice ta farka zata kurma ihu ya daka mata tsawa “ shut up “,yana kai ‘karshen zancen sa ya juya bayar dakin, tunanin abunda ya faru d’azu tayi kafun ta d’auki hannunta d’aya ta mari fuskarta “ why ? Me yasa bana jin magana “, tunanin yadda zata fita ta soma ganin bata da wata hanyar fita , abincin data kawo masa ne ya fad’o mata arai , yanxu idan yaci abinci fa ? “, dukda yadda jikinta yake a ji’ke Hakan be hana ta saka gudu ba , da Sauri Sauri take taka steps, lokacin da ta sakko har ya gama zuba food d’in da zaiji, ganin yana shirin d’aukar spooon ne yasa tayi Sauri kwalla kara da karfi “ No karkaci “, be gama fahimta me take ba kawai sai ganin tahee yayi ta ture tray d’in gabaki d’aya hatta abincin da ya zuwa sai data ‘barar dashi , rai a ‘bace ya d’ago da eyes d’inta, batai aune ba sai saukar marin shi taji a bothside kumatunta, da Sauri ta dafe wajan tana binsa da kallo ganin yadda ransa ya ‘baci, ‘kara d’aga hannu yayi zai mareta sai kuma ya fasa a kausashe ya soma magana “idan na sake ganin ki cikin part d’in nan zakiga abunda zai faru,leave now “, ya daka mata tsawa , ita kanta ta tsorata zata gudu ya tsayar da ita “ washe kwashe miki Wannan trash d’in “, jijjiga masa kai tayi ta nufi haryan kitchen , duk da yayi mamakin yadda akai tasan hanyar kitchen d’in bece komai ba sbida yadda ransa yake a ‘bace , be san dalili ba amma yaji zuciyarsa tana masa ba dad’i, kayan kashe shara tahee ta kwaso tashare Wajan ta goge kamar babu abunda ya zube , komai a nutse take yinsa gabaki d’aya akan idanuwansa yana kula da movement d’inta hawayen ta da suke fitowa ne ya fi komai tsaya masa arai , ko data gama bata kalli indayake ba tayi hanyar fita , “ hey !” , yace mata , jiyowa tayi har yanxu hawayen be dena sauka ma , yadda ta saukar dakai sosai zata baka tausayi , zai yi magana sai kuma ya fasa “ get lose “, da Sauri ta juya tana goge hawayen fuskar tata , ta ‘kasan ido yake kallanta har ta fice , hannunsa ya d’ora akan saitin zuciyarsa , yadda take hawayene ya soma ya dawo masa akai , at the same time yana tuno hawayen tahee d’insa , he don’t know why he feel bad , kamar ya kira ta , but he will never do so, mamakin kansa yake yadda idan tayi abu take d’aga mata ‘kafa , abunda ya faru a toilet ne ya fad’o masa arai da lokacin da ta taho da gudu ta ‘barar da abincin . Abunda ya faru shekarun baya ne ya soma dawo masa kai “ dady no”, shine abunda ya fad’o masa lokacin da tahee ta ‘barar masa da coffee d’insa . Dafe kansa yayi da hannaye biyu sabida yadda yaji kansa ya fara sara masa , gabaki d’aya memories d’inshi shi da tahee na dawo masa cikin brain d’insa.

    **** Tahee tana futa ta gyara fuskarta , zuciyar ta bata mata dad’in musamman abincin da taga beci ba , tana tafiya tana tunanin mafita har ta ‘karasa part d’in Ammeey , tana shiga ta tarar da ita a tsaye tana ganin tahee ta ‘karaso inda yake , “ yaci abincin ?” Shine abunda Ammey ta fara tanbayarta , ‘yake tahee ta sakar mata sabida bata cikin mood d’in “ eh hajiya sai da na tabbatar yaji sosai sannan na fito “, murmushi Ammeey ta saki , kafun ta furta “ zaki iya tafiya “, a sanyaye tahee ta koma d’akinta . Gabaki d’aya rinin ranar tunanin yadda ta bar king take , hannu ta tasaka ta shafi face d’inta da ya mara , kamar wata ‘karamar yarinyar ta turo bakinta waje .

    ********
    *************
    Yau ya kama Wednesday , ayau ne kuma aka kawo lefin ilham , gabaki d’aya mutanan gidan sun shiga busy , kowa yana harkar tar’bar baki musamman abeey da take part din su dada da za’a kawo lefen , tun lokacin da king ya mareta kuma basu ‘kara haduwa ba amma kullum da tunaninsa take tashi , a cikin lokacin da ba’ki suke zuwane kuma mimi ta samu ta bawa tahee sa’kon yah moh , duk da batayi wani mamaki ba ta ydda kayan suka shigo Amma gabaki d’aya sai da ta saka ‘kananan camera a falon Ammey, hatta d’akinta lokacin da asabe ta bata ta kai mata abinci , Allah ya temaketa ta shiga d’akin Ammey ta saka mata sound recorder d’in da yah moh ya basu , d’akin da har yanxu bata ga Ammey ta shiga ba ne kawai bata sawa , hatta wajan sha’katawar Ammey sai da ta saka . Yau ne kuma take plan d’in yadda zata shiga cikin d’akin da ba mahalu’kin da yake shiga sai Ammey ita kadai. Ganin yadda kowa yayi busy hatta mutanan gidan kowa yana part d’in dada da ummey masu aiki ma sai faman kai kawo suke , da Sauri Mimi ta shigo palour Ammey tana kallan tahee da ke faman jiran ta “ tahee kiyi sauri bamu da time , zan miki gado gadi, bamu da time kiyi sauri ,” jinjina mata kai tahee tayi bayanta d’auki cameras din da sound record ta nufi d’akin tana tava door d’in taji wani irin zafi ya ratsa mata hannu , ‘kara saka hannunta tayi a karo na biyu wani s azaban da ya fi na farko ratsa mata hannu, da Sauri ta ja baya jin yadda hannun yake kamar an ‘Konashi. Lokacin da tahee ta ta’ba kofar nan sai da zuciyar Ammey ta buga , wani matsananciyar tashin hankali ya ziyarceta , mi’kewa tayi dan ta dawo part d’in ta ummey ta tsayar da ita , jitayi kamar ta sha’ke ummey , tarar ba’kin sukai lokaci d’aya , Adaidai lokacin da tahee ta ‘kara ta’ba ‘kofar . Wannnan karan kasa hakuri Ammey tayi ko sauraran ummey batayi , a hau kace ta fito daga part d’in dada .

    “ kiyi sauri tahee bamu da lokaci , kiyi sauri “, jinjina mata kai tahee tayi tare da ‘kara ta’ba kofar, alokacin da ta ta’ba sabida tashin hankali Ammey har fad’uwa kasa tayi a firgice . Runtse idanuwanta tahee tayi tare da furta Bismillah ta bud’e d’akin , tana bud’ewa wata iriyar guguwa ta karad’e d’akin , addua tahee ta soma jin yadda jikinta yasoma d’aukar karkarwa kamar zata rasa kanta , hatta ‘kafarta da ta taka , wani irin zafi ne yake ratsa mata kafafu, adduar datake cikin saurine yasa lokaci d’aya guguwar ta tsaya , da Sauri tahee ta soma bin d’akin da kallo komai na cikin d’akin jane kamar yadda yah moh ya fad’a musu , jin muryar Mimi na fad’in Kiyi Sauri tahee . Da Sauri ta fara duban inda zata saka cameras din, tayi sa’ar saka recorder din , zata saka camera d’in bata sani ba ta buge wasu abu kamar tangaran , take a Wajan suka fad’i kasa suka fashe , suna fashewa wani irin ba’kin hayaki yafito daga ciki lokaci d’aya kuma suka ‘bace batt , a rude tahee ta ke duba d’akin inda zata saka cameras d’in kamar zata haukace haka take jin kanta sabida azabar zafin da ya fara ratsata ji take kamar ta kurma ihu dan hauka . A lokacin kuwa da ta kurma ihu da babu abunda zai hana tahee ta haukace , wani d’an waje ta samu daga ba kowa ne zai san da wajan ba ta li’ka cameras din , duk dubawarka bazaka san dasu ba .dai dai lokacin da zatafito daga d’akin ‘kafarta ta buge wani abu take a wajan shima ya fashe , still wani ba’kin haya’kine ya karad’e kafin ya ‘bace , sabida yadda ta rud’e bata san lokacin da ‘kafarta ta zame ba Zata fad’i, Adaidai lokacin kuma Ammey ta saka hannu kan handle d’in kofar shigowa falon, tahee batai aune ba sai ji tayi an funcukota da ‘karfi an toshe mata baki ……..

    ????GIDAN AUNTY????

    07041879581
    MSS LEE

  • Gidan Aunty book 2 Page 9

    Gidan Aunty book 2 Page 9

    BOOK 2
    Page 9 ??

    4 YEARS LATER

    Abubuwa da dama sun fara cikin tsawan wannan lokaci , har zuwa lokacin kuma babu Wanda ya ‘kara samun labarin Tahee sai addua da kullum ake mata, gidan sai ya ‘karayin shiru babu Tahee babu king,Amrah da king ya Koreta sai da tayi good 2 years a gidan mahaukata kafun Allah ya bata lapiya amma duk da hakan ta d’an tabu , lokuta zuwa lokuta tana abu kamar na marasa hankali, yan kiran sunan king akai shiga taitayin take har lokacin kuma bata ‘kara kuskuran koda tako ‘kafarta gidan ba ,ga wani irin abu da take ji lokaci zuwa lokaci a ‘kasan ta na mata zutt zutt Amma babu Wanda ta ta’ba fad’awa sai ma harkar less da ta koma ita da wata friend d’inta ,kullum suna manne da juna ko basa waje d’aya toh kullum suna cikin yin vidoe call. Cikin Shawan shekarun nan wani irin soyayya khaleed yake yi shida ilham da basa kwana d’aya basuji muryar zunansuba , tun ana d’auka abun da wasa har saida khaleed ya nufi dady da cewar a Aura masa ilham . Dady ba ‘karamin farinciki da mamaki yashiga ba , sosai kuma yayi farincikin hakan . Zarah ma yanxu an zama big girl duk wannan surutun da rashin jin ta dena su da wuya kaji surutun ta inva a wajan oummey da ta zame musu tamkar uwa ba , me share Masu hawaye , sau da dama idan aka gansu tare sai a yi tunanin oumma ce ta haifeta musamman gogewa da oumma ta ‘karayi sosai ta zama babbar hajiya , ayanxu bayan mall din da take Dashi ta ‘kara gida guda biyu da gida guda uku dayake duk mallakinta,sai kuma filayen da take siyarwa, babu Wanda zai ga oumma yanxu yace Itace a baya sabida yadda kudi da kwanciyar hankali ya zauna mata dukda har yanxu tana yiwa ‘ya’yanta addua kuma batacire rai a sake ganinsuba, lokaci zuwa lokaci tana zuwa bunkure kuma , yanxu wani irin zumunta suke yi abunsu kamar babu abunda ya ta’ba faruwa a tsakaninsu , lokaci zuwa kuma suma suna kawo mata ziyara har Abuja sannan tasa a mayar dasu gida, ynxu gabaki d’aya sun sauya suma kamar basu ba , iya rufin asiri yanxu Allah ya basu sai faman cikawa da Imani , gabaki day sun mata da Dije ko wata bintalo da dad’ewa sun kira sabuwar rayuwar da oumma ta zama sanadin farin cikinsu.Ganin yadda khaleed yake bawa oumma labarin ilham kullum Yasa oumma tanbayar dadi akan auransu , shima yayi na’am da barin alokacin har ya samu Abeey da zancan, ba ‘karamin farinciki Abeey yayi da hakan ba , amma duk da hakan be yanke hukunci ba saida yakira uncle musaddiq da har da kukan sa Sabida farinciki, babu dad’ewa aka saka auren 7 month , a yanxu gabaki d’aya biyan saura 3month, duk lokacin da sukai waya da ilham sai yace mata lokacin yayi tsawa zaije ya zamu Abeey yace a rage , da ‘Kyar ta lallashe sa akan saura ‘kan’kanin lokaci Amma dukda hakan baya hana gobe ya ‘kara ce mata lokaci baya sauri.

    A ‘bangaran king tun bayar ‘batan Tahee gabaki d’aya ya ‘kara sauyawa kwata kwata baya zama a gida , saida yayi 3 years be je ko da Nigeria ba ,babu Wanda be kira ya lallashe saba Amma gabaki d’aya ya sharesu hatta small mom dake Dubai itama sai da takira sa amma babu abunda ya canza ganin ummey da dada na ‘kara shiga cikin damuwa yasa Abeey da kansa yaje U.S.A ya lallashesa akan ya dawo gida , still dukda ya dena fushin amma yace bazai iya zama babu matarsaba idan ba haka ba zai iya samun ciwan zuciya , sosai abeeey ya tausayawa son d’in nasa shiyasa be takura masa akan sai ya dawo ba , shima koda ya koma gida kwantar musu da hankali Abeey yayi , amma kusan kullum sai sun kira sa , dukda rashin magana da ya koya hakan baya hana in yana free ya kira ummey ko abeey, wani lokacin kuma ya kira dada da kullum sai tayi masa adduar Allah ya bayyana tahura .

    AMMEEY
    Cikin kwana bakwai d’in da abun bautar su ya bata ba ‘karamin shiga damuwa da rud’ani Ammey tayi ba , ganin har lokacin king be dawo ba , sosai ta shiga matsanan ciyar damuwa , da ‘kyar ta iya dannewa take kiran sa ko dan tace masa ya dawo amma itama amsarsa kamar ta sauran ce , “ he can’t, bazai iya rayuwa babu matar saba “, wannan kalla tasa ba ‘karamin sosa ran Ammeey yayi ba Amma cikin bariki itama ta nuna damuwarsa tare da baza goyan baya . Sosai ta saka ayi mata binciken a nemo mata tahee cikin SIRRI yadda zata kammala aikinta na ‘karshe amma duk magana d’aya ce ba a gantaba. Tun Ammeey na sa ran dawowar tahee har ta cire gabaki d’aya tare da shinfid’a sabuwar rayuwa acewarta abunbauta ya Mata ‘karya may be taheen ta dad’e da zama Matacciya shiyasa sosai ta saki ranta, kwarton ta da yake kulle fuska kuwa kusan kullum sai yayi sex da ita, ita kuma ko a jikinta ganin ta salwartar da mutanan da sukeso su zama cikas a rayuwarta, yanxu buri d’aya ne yayi saura ta cika, su kwashe gabaki d’aya dukiyar Abbey hatta ta king da ummey da suke hari sai kuma bayan Abeey da yafi komai tsaya mata arai da takeso ta kawar.

    ****************
    UNITED KINGDOM ????

    A wata mata shiyar budurwace so classy sanye cikin doguwar rigar material, farace kyakkyawa , hannunta na d’auke da siririyar fashion pose red colour , kantamemiyar tsadar wayarta ma pod d’in ta ma red colour ,cikin taku irin na wayayyiyar budurwa meji da kanta ta soma sakko wa cikin heels dinta shima red , agogon hannunta take dubawa tun d’azu, tana sakkowa daga steps ta soma kwalla kiran sunan “ momy kuna ina lokacin na tafi , nasan sister tana can tana jiran mu”, wani kyakkyawar baturan yaro ne ya fita daga wata ‘kofa cikin gudu gudu, yake furta “ My love , junior is hear “, kallan inda yaran yake tayi, tubarkalla Masha Allah , wani kyakkyawan yaro ne , sosai yake da kyau fari tass kamar a ‘bula Jini ya fita , sanye take cikin Red suit na yara da ya ‘kara yi wa kyakkyawar fuskarsa kyau, gashin kansa kuwa wani irin gyara akayi masa ne shegen kyau da ya kwanto masa har wajan goshinsa, d’an mitsitsin bakinsa pink colour sai faman shining yake , da Sauri itama matashiyar budurwar ta ‘karasa Wajansa, lokaci d’aya sukai hugging d’in juna , duk da hills d’in dake kafarta Hakan be hanata juyasa ba sai faman dariya yake , dimples dinsa na both side na lotsawa, fararan jerarrun hakoransa tass dasu. “Mimi?” Da Sauri matar shiyar budurwa ta juya , sai yanxu na ganeta sabida wani irin kyau da tayi gabaki d’aya ta canza ta zama so classy, yaron naganin guy din daya kira mimi yayi saurin sauka daga Wajan Mimi ya ruga a guje zuwa wajan guy d’in , shima hugging d’insa yayi cikin turanci ya furta “ Big Dady”, sai yanxu fuskar mutumin ta fito, bakowa bane face Yah moh , shima sosai ya canza ya zama wani kyakkyawan guy , sanye yake cikin wasu ‘kananan kaya shima , sosai kayan sukayi masa kyau . Murmushi ya sakar wa boy d’in “ you look so wow sweetheart “, kashe masa ido d’aya yaran yayi kafun ya ja masa kumatunsa “ and also you my Big dady”,suna tsaye momy da dady da Hutu ya kara rutsa jikinsu fitowa , gabaki d’aya ko wannansu tashi kalar d’aukan wankan , a wannan karan ma kyakkyawan boy d’innan wajan su momy da dady ya nufa cikin hausarsa da bata fitowa sosai ya furta “grandparents kun dad’e tun dazu muna jiran ku”, jan hancinsa momy tayi “ toh ai gamu mun fito sai mutafi ko ?” Kanshi ya jinjina mata kafun ya kama both hannunta dana Dady suka fito baban harabar gidan , motoci biyu kawai suka d’auka d’aya yah moh da Mimi , d’ayar kuma dady ne da kanshi zaiyi driving din sai momy da junior a gefenta. A hankali cikin tafiyar nutsuwa a mota suka hau kan babban titin da zai kaisu **The inner temple ** lokacin da Suka je mutane sai fuffuto wa suke daka ciki zuwa harabar filin Inda kowa zai had’u da family d’insa , da yawa daga cikin mutanan sanye suke da suit a jikinsu sai wig and gown na lawyers da ko wanne ya saka, fara dudduba sukai suna jiran Suga ta Inda zata fito tun suna sa ranganinta har Mimi tayi *kokarin kiranta a waya “daga bayansu sukaji wata daddad’ar siririyar murya ta furta “‘momy”, gabaki d’aya su lokaci guda suka juya zuwa inda muryar ta fito , kyakkyawar matashiyar budurwace ta a jikin karshe fara sol da ita , tsabar farin ta har yellow yellow jikinta yake , sanye take cikin suit ita ba’ka sai wig and gown dinta da ta ri’ke a left hand dinsa , fashion swag bag dinta ma nakegen hannunta na hagu black colour , sosai hill din data saka yafito da kyawun ‘kafarta , idanuwanta sanye yake cikin farin glass da kemar medical, siririyar cute lips dinta ya ‘kara fito tas dashi, duk da suit ne a jikinta hakan be nuna sura ko wani Shati na baiwar da Allah ya bata ba, da Sauri junior ya saki hannunta su momy yaruga wajan matashiyar budurwannan da kudi da jin dadi suka gama zama a jikinta, yana zuwa wajanta yayi saurin hugging d’inta, “ My love ! I missed you “, kyakkyawan murmushi ta sakar masa da ya ‘kara mata kyau lokaci guda both dimples dinta suka lo’ba, “ missed you too” cewar matashiyar budurwar tana sakar masa peck a goshi, inda su momy suke ta nufa cikin ta kunya na d’aukan hankali , tana zuwa ta rungume momy kafun ta koma kan mimi itama ta rungumeta , cikin jin dadi mimi ta furta “ Congratulations sis tahee , you’re now a barrister “, wacce aka kira da tahee da kalla da mugun shock , tabbas Itace Amma gabaki d’aya ta canza ta zama wata babbar mace meji da aji ga baiwar karatun da Allah ya bata na zama babbar Barrister, itama momy congratulations dinta tayi kafun yah moh da dady kowa yayi congratulations dinta, cikin farin ciki suka fara d’aukar hoto gabaki d’ayan su , junior ya ta’ba tahee kadan , kallan sa tayi da dara daran idanuwanta da suka ‘kara haske da kyau , alama yayi mata data matso, d’an rankwafo tayi batayi auneba taji saukar kiss a goshinta , cikin harshen turanci ya furta “ I love you mom”.

     

    ????GIDAN AUNTY ????

    07041879581
    Mss Lee ??

  • Gidan Aunty book 2 Page 14-15

    Gidan Aunty book 2 Page 14-15

    BOOK 2

    Page biyu na had’e muku na jiya da na yau …. ??
    Page 14&15

    Ita kanta tahee bata san lokacin da dariya ya kwace mata ba musamman yadda ta hango wawulon Ammey ,daka musu tsawa Ammey tayi rai a ‘bace , sai a lokacin suka kula da abunda Suka ai kata , gabaki d’ayansu shiga taitayinsu sukayi ganin yadda ranta ya ‘baci, wata dariyarce ta so kama taheee amma take ‘ko’karin danne ta gudun kar Ammeey ta ‘kara zuciya, cikin muryar fad’a ta ‘kara daka musu tsawa “ ku ‘bace mun dagani”, bashiri kuwa suka bar Wajan , tahee na shiga d’aki ta ‘kara fashewa da dariya ita kadai idan ta tunano bakin Ammeey sai ta ‘kara fashewa da dariya , knocking d’in dakin asabe tayi kafun ta shigo ciki kai tsaye, Allah ya te mako tahee bata cire face d’in ta ba , abincin ta asabe ta mi’ka mata itama idan ka kalleta zaka san da fara’a a kan fuskarta, lokaci d’aya kuma tahee da asabe suka ‘kara fashewa da dariya sai da sukayi me Isarsu tukunna asabe ta bar d’akin,breakfast d’inta tahee taci hankali kwance tana tunanin shirin da zata yi nagaba kar Ammey ta gano ta . 12 : 10 asabe ta ‘kara zuwa kiran tahee , yanxu ma abincin rana suka fara shirye shiryen yi fuskar kowa da annashuwa musamman tahee da take yi da biyu, har lokacin kuma tun da Ammey ta shige d’akinta bata kuma fitowaba hatta breakfast kai mata a Kai. Yanxu ma lafiyayyen lunch suka yi kusan rabin aikin asabe ce ke yi,sabida kallan tahee da take a bata waye ba bata san yadda ake abincin ‘yan gayuba , suna Kammala girkin asabe ta zubawa Ammeey cikin babban tray bayn ta zuba komai da komai cikin warmer, mi’kawa tahee jug d’in juice tayi ita kuma ta d’auki tray d’in “ Abincin Ammey ne tace na kai mata d’akinta ni kuma sun mun yawa shiyasa zaki rakani kinji”, toh Kawai tahee tace mata dan ko ita da Ammeey ta kawo ta bata ta’ba shiga d’akin ba sai ynxu da zata shiga , bakinta d’auke da addua ‘kasa ‘kasa ta biyo bayan asabe lokacin data bud’e mata kofar d’akin, Ammeey dake kishingid’e kan gado ce ta d’ago azabure , cikin firgita da tsoro gabaki d’aya ta Amma ta da hakwaranta da Suka jire , jikinta har mazari yake da ya bawa tahee mamaki, wani tsawa ta daka musu da Suka ji har saman kansu “ Me ya kawo ku d’akina na rawa asabe ta nuna tray d’in hannunta , a rarrabe ta furta “ da daman abincin ki ne muka kawo miki ganin baki fito ba…” bata ‘karasa ba Ammeey ta kwashe fuskarta da mari sakin jug d’in hannunta tahee taji jiki na rawa zata soma bawa ammey hakuri ta nuna musu kofa “ kafun ranku ya ‘baci banasan ganin d’aya daga cikin ku anan , ku ‘bace mun dagani” cike da Tsoro tahee ta nuna jug d’in da ya fashe “ hajiya bari na fara kwashe abun tangaran nan “, bata kai karshe ba Ammey ta ‘kara daka musu tsawa “ nace ku fita ko?” Bashiri gabaki d’ayansu suka bar d’akin, tahee harda janyo mata ‘kofa, tana ganin ‘bacewarsu ta zu’be ‘kasa tana dafa kanta “ nashiga uku meyake shirin faruwa dani? “ ‘ko’karin danna zobanta take amma ciwan bakinta ya hanata dan tasan abunda zai biyo baya , tana tsugunne a wajan kamar wani aljani ya bayyana a d’akin, inda Ammey take ya nufa shima gabaki d’ayansu a firgice “ me kike shirin aikatawa? Tonuwar asirin mu kike so ko kuma me?kinfi kowa sanin ‘ka ‘idojin bokanya, kara na biyu da kika ‘kara ‘bata mana shiri, bazan lamunta ba “ , na fad’a miki bazan lamunta ba, idan kika ‘karayin kuskuran akaro na uku to tabbas jininki ya zama salwantaccen,” yana kai ‘karshen maganar sa yayi wurgi da ita saida kanta ya bugu, shima gabaki d’aya hankalinsa a tashe ya ‘kara ‘bace wa daga cikin d’akin. Cikin d’aga murya da fita hayyaci Ammey ta soma magana “ bazeyu ba tabbas Kema kande lokacin aikin ki yayi , shirina bazai ‘baci ba, daga rana irin ta yau , aikin da ke kanki zai fara “ ita kad’ai sai surutai take yi .

    Tahee kuwa ranta fess suka ci gaba da ayyukansu bayn sunyi sallah, har yanxu idanunta na kan kofar da yah moh ya sanar da ita akai amma har ynxu shiru Ammey bata shiga ciki ba . Sai wajan yamma Ammey ta fito daga cikin dakin , daka kalli fuskarta kamar hadarin kaji, har lokcin le’banta daya kumbura be saceba, “ kande , kande “ , Ammey ta dunga kwalawa tahee kira , jiki na rawa tahee ta zo ta zube mata , kare mata kallo Ammey tayi ganin yadda jikinta yake rawa , kafun ta mi’kawa tahee wata ‘yar ‘karamar jaka , da Sauri kuwa tahee ta karba “ zaki ga bangarori da yawa , ki irga na ukun ciki daga hagu , idan kinga ‘yan mata a falon kice kina neman dada sai kibata, karkiyi kuskure fa “, ba’kin hakwaranta tahee ta bud’e mata “ insha Allahu hajiya bazanyi ba “, kamar sa kai Ammeey tayi daga ganin hakwaran tahee. Da Sauri tahee ta nufi kofar fita , da’kyar ta iya bud’e kofar acewarta wahala ne da kofar ‘yan gayu tana fita har zata nufi part din dada ki tsaye sai ta fara irgawa kamar tanasan cinkar part d’in, sai da tayi almost 5 minutes tana ‘karewa ko wane part kallo kafun ta nufi part d’in dada wani irin sanyi da iska me kamar hadari yana busata. Tana shiga kuwa ta tarar da su ilham sai baman za’ban kaya suke , da sallama tahee tashigo palour gabaki d’aya kallanta sukai lokaci d’aya kuma suka amsa mata sallamarta.jakar ta mi’ka musu cike da barkwanci ta furta “ wai hajiya ce tace a bawa dadu(dada)”,gabaki d’ayansu kwashewa sukai da dariya kafun ilham ta furta “ dada ko?”, washe baki tahee tayi “ kwaran kwatse haka tace , sunan yan gayun ne nakasa fad’a shiyasa “, yanxun ma wani saban dariya suka saki , Daidai lokacin da dada take Fito wa daga cikin d’akin, binta da kallo tahee tayi “ itama ta ‘kara tsufa, farin gashin kanta ya Fito sosai “, cike da girmamawa tahee ta tsugunna ta gaishe ta lokacin da taji hawaye ya sakko mata a ido , da Sauri ta goge gudun kar wani ya gani a gidan , itama dada ba yabo ba fallasa ta amsa mata kafun ilham ta mikawa dada jakar da tahee ta shigo dashi “ Allah sarki , kilishi bata gajiya da d’awainiya , toh Allah yayi albarka “, gabaki d’ayansu amsawa sukai da Ameen banda tahee . Zata tafi ilham ta tsayar da ita , “ kande bari na d’an aikeki part d’in ummey ki kai mata wannan”, tsayawa kallan bakinta da ta furta ummey tayi , zumudi nasan fito mata Amma tana ‘kara dannewa, ta mi’ka hannu daniyar kar’ba taji sallama a bayanta,da Sauri ta juya batasan lokacin da bakinta ya furta “ you!?”, tsayawa kallansu su ilham sukai , tahee sam ta manta suna wajan sai tayi saurin wayancewa da “ You You!! Nayi daidai ?”, yar dariya sukai tare da kawar da shashancin tahee, ajiyar zuciya Tahee tayi tana ‘kara bin Mimi da tashigo cikin shigar ‘yar aiki itama a fakaice ,” Yawwa shikenan tunda kinzo , ita kande ta koma wajan aikinta inyaso ke sai ki kai wa ummey kayannan “, kar’ban kayan Mimi tayi tana cewa toh , dariya duk ya cika mata ciki wato haka tace musu sunanta kande , ita kanta tahee saratu da aka kira Mimi sai da yaso bata dariya Amma tana dannewa , a fakaice ta yadda babu Wanda zai gansu Mimi ta d’aga mata gira d’aya da Sauri tahee ta d’auke idanuwanta tana musu sallama, ita kad’ai a ranta take magana “ yarinyar nan so take asirin mu ya Toni take mun signal ko ? Zan kamata , amma Yaushe ta zo gidan nan itama ?”da wannan tunanin tahee ta koma part d’in Ammey. Yanxu ma Ammey bata falon shiyasa kai tsaye ta nufi makwancinta, kan ‘karamin karfe d’in Wajan sai kayanta datayi fulo dasu har yanxu ta’ki yadda ta hau kan katifar sabida hakanan kawai bata yadda da katifarba. Da daddare ma asabe ce ta kawo mata abinci tunda babu wani aiki da zasuyi, ita kad’ai tana tsaya yadda zatayi magana Ammey. Part d’in king ne ya fad’o mata arai, “ kana ina nayi kewarka sosai !!!!!! Plx kana ina “, duk da acikin zuciya tayi magana dole ka gane kad’ai cin da take ji aranta , sosai yau take missing d’insa so badly, so take kawai tajita a jikinta, bata san lokacin da ta rungume jikinta ba tana lumshe ido gabaki d’aya tsananin kewarsa shida junior d’inta ne ya cika mata cikin zuciya . Bata san lokaci ya ja ba saida ta kalli agogo taga ‘karfe 9, da Sauri ta Tashi tayi sallahr isha’i tare da kulli ‘kofar da lock , sai da ta zauna tayi addu’o’in neman tsari sosai kafun ta soma akaratun alkurani a hankali a hankali, a haka bacci ya d’auketa tana karatun.

    Karfe 2:30am na safe tahee ta soma jin wani irin bugun ‘kofa a d’akin ta, tun anayi a hankali har aka somayi da ‘karfi kamar za’a ‘balla ‘kofar d’akin, a rud’e tahee ta soma karanto duk adduar data zo bakinta , ‘karar abubuwa da jijjigar’kofar da ake ne ya ‘kara tsoratar da ita amma duk da hakan sunan Allah ne a bakinta . Kamar ‘kiftawar ido aka koma side d’in window shima a haukace aka dunga bubbuga windows din kamar za’a ‘balla ga wasu irin kuka da suke tashi ta ko ina, side d’in kofar aka koma shima nan d’in bubbbuga wa akeyi had’e da kuru ruwa , mintuna kad’an kuma ya koma window , haka y dunga yi tsawan lokaci, sai wajan 3:10 kafun abun ya lafa , har yanxu tahee addua ce a bakinta daman tasan za ‘a rina , Ammey bazata ta’ba barin ta Haka ba . Gabaki d’aya tsoran komawa baccin take , saida bacci ‘barawo ya kwasheta.

    WASHE GARI

    Yau kam Ammey ta rigasu fitowa tunda suka fito take bun fuskokinsu da kallo kamar tana san fuskartar wani abu.har izuwa lokacin kuwa ciwan bakinta be gama sacewa ba, abun dariya facemask d’in da tasaka a rabin face d’inta,amma duk da haka idan tayi magana sai alamun rashin ha’kori ya fito mata. Gabaki d’aya yinin ranar kuwa Ammey a falo ta zauna duk yadda tahee taso had’uwa da Mimi abun yaci tura kamar dama Ammey ta san plan d’insu, duk yadda taso Zillewa Ammey bata , bata wannan damar ba , gabaki d’aya yinin tahee bata had’u da Mimi ba sai hakura tayi .

    *****Haka tahee ta cigaba da zama a part d’in Ammey matsayin yar aiki , ga biki da yake ‘kara kusantowa ,duk yadda taso ta Samu evidence akan Ammey abu ya ci tura gabaki d’aya babu wan sheda da zai nuna maka Ammey tana yin wani abu , har lokacin kuma bata ‘kara had’uwa da Mimi ba tun bayan had’uwar da sukayi a part d’in dada . Yau sati d’aya kenan da zuwan tahee , gabaki d’aya lamarin Ammey ya fara d’aure mata kai , duk dare idan ta kwanta wannan buga ‘kofar da ake a haukace me yake tashin ta daga bacci amma Sabida kariyar ubangiji babu abunda ya sameta, tsawan sati kenan har yanxu taheee bata kwana akan katifar d’akin, kome zatayi cikin taka tsan tsan take yinsa gudun kar asirinta ya tonu.

    ??????

    Yau ya kama Monday,batasan me ke faruwa ba, sai ayyukan da Ammey ta sasu na dafe dafe da soye soye kamar za’ayi wani babban taro gabaki d’aya Ammey yinin ranar a tsaye take sai faman rawar kai take ga wani farinciki da ya kasa ‘boyuwa akan fuskarta, abinci kuwa kala kala tasa su asabe aikinyi, 6:30 ta saka su asabe zaryar kai abincin part d’in Ammey , ban da wani kunun ayan da ta had’a da kanta sai faman tashin ‘kamshi yake , tahee na tsaye tana kallan ikon Allah ganin ita ba’a sata aikin komai ba , sai umarnin jiranta da Ammeey ta bata . Kiran sallar da akene yasa ta komawa d’aki saida ta kulle ko’ina tukunnan sannan ta cire fuskar, take kyakkyawar fuskarta tafiya kwanin burgewa gudun kar wani ya shigo ya sameta yasa ta yin alwala , tana idar da sallah ma ta mayar da face d’in , sosai take kewar su junior da momy gabaki d’ayansu. Kamar yadda tayi zato taba kammala sallar asabe ta kawo mata abincin Daren, ba musu kuwa ta ‘kar’ba duk da agaban ta akai komai ,snacks din da tayi da hannunta kawai ta ydda taji shima sabida yunwar da take ji hatta leman da aka bata, bata shaba sai ma juyeshi da tayi a cikin toilet. Har lokacin Ammey bata ‘kara nemanta ba , sai bayan kiran sallahr isha’i da ta da asabe kiranta. Tana fitowa taga Ammey ta sha uban kwalliya sai faman walwali take amma ba’kin zuciyarta ya hana a ga kyaun ta sai mununta cewar tahee . “ kande “ cewar Ammey tana katse wa tahee tunanin da ta fad’a , da Sauri tahee ta ‘karasa Inda tace cike da biyayya ta tsugunna , jug d’in kunun ayar Ammey ta nunawa tahee , “shi zaki d’aukomun ki biyo ni dashi”, da Sauri tahee ta amsa sa da to hajiya tana mamakin ne ya hana akai kunun ayar lokacin da ake kai abuncin, babu me bata amsa shiysa ta cire zancen cikin zuciyarta . Tunda suka fara nufar hanyar part d’in dada haka kawai zuciyarta ta soma tsinkewa , ka ‘kafafuwanta da sukai sanyi kamar me shirin zubewa ‘kasa , duk da Haka bata karaya ba addua take karantowa a ‘kasan zuciyarta . Suna shiga falon saura kad’an ta saki jug d’in hannunta, ganin gabaki d’aya ilahirin familyn suna Zaune kamar yadda suka saba , shi kad’ai ne babu sai zoya da samreen da basa nan sai kuma mahma , a d’ad’d’ai da d’ad’d’ai ta soma bin ko wannan su da kallo kafun ta sauke idanuwanta akan ummey, hakanan ummey ta tsinci kanta da sakin wa tahee murmushi , itama tahee murmushi ta d’an sakar mata , kafun ta tsugunna har ‘kasa tana gaishe da ko wannan su d’aya bayan d’ayan kukan da yake shirin kwace mata take ‘ko’karin dannewa sabida kar su fahimci halin da take ciki, gabaki d’ayansu cike da kulawa kowa yake amsa mata gaisuwarta.d’ago idanuwanta tayi ko zataga Mimi Amma gabaki d’aya ba Mimi babu alamarta. A wayance Ammi take Kare bakinta ta yadda basu fahimci cirewar hakwaranta ba, amma abunda bata sani ba Abbey da ummey sun gani shiru kawai sukai da bakinsu ganin kowa na cikin falon. Basu dad’e da zuwa ba gabaki d’ayansu suka nufi dinning area , kallan tahee ummey tayi kafun ta ‘kara sakar Mata murmushi “ idan kika fita ‘nan gare na biyu ki kiramun saratu kinji ?” Da Sauri tahee ta amsa mata gudun kar Ammey tayi magana yasa ta juya cikin sauri sauri ko tunanin ajje jug d’in batayi gabaki d’aya ta manta da wani jug a hannunta. Hadari hadari ne ya soma kad’awa ga wata sanyayyiyar iska da take kad’awa itama , part d’in king da yake d’an nesa da ita ta ‘kurawa ido , ynxu hawayen da suke zubo mata batayi ‘ko’karin dakatar dasu ba , tafi tsawan mintuna 5 tsaye a wajan ga inda take da d’an duhu duhu,batayi auneba taji an janyota baya an toshe mata baki ta yadda bazata iya ‘ko’karin guduwa ko yin ihu ba . Batasan ko wanene Sabida yadda aka rufe mata baki sosai har lokacin kuma jug d’in kunun ayar na hannunta.kai tsaye bayan part d’in uncle musaddiq aka jata ta ydda bazata iya Saurin guduwa ba , saida ya nisantata sosai daga wajan masu tsaro , kafun ya gwara kanta da jikin bango, yana ‘ko’karin ‘kara ta’bata kawai ta watsa masa kunun ayar hannunta gabaki d’aya . Duk da fuskarsa a kulle take hakan be hana jajayen idanuwansa fitowa ba , rai a ‘bace ya ciro knife d’in jikin wandansa yana nuna ta da ita, cikin muryarsa mara dad’in saurare ya soma magana “ dole aikina ya cika yau kamar yadda nake cika ko wace makafa haka Kema zanyi anfani da jikin ki wajan biyan bu’katata, idan kika gigin guduma sai na kasheki , na kashe banzan sannan na binneki ta yadda babu Wanda zai ga ko da sassan jikinki ne .”a tsorace tahee take bin fuskarsa da kallo tana san ganin fuskar wanda yake yake magana , ganin ya fara matsota ne yasa ta soma ja da baya, wata shegiyar dariya ya saki ko ‘ko’karin akamasa bayayi, gadan gadan ya nufo tahee da niyar yaje hijab d’in jikinta , take a Wajan kokawa ya ‘Barke tsakanin mutumin da tahee , adduar da take sanyima sai taji bakinta yayi nauyi ta kasa , suna cikin wannan kokawar taji ya saki ‘kara ya koma gefe , da Sauri ta kalli gefensa ,Mimi ce d’auke da dutsen da ta buga masa , da Sauri ta furta tazo mugudu, da Sauri tahee ta mi’ke ko takan jug din Ammey bata biba sai ma wani abu danaga ta du’ka ta dauka kafun su saka gudu ita da Mimi Suka bar mutumin kwance a wajan dafe da kansa. Direct basu tsaya a ko ina ba sai a part d’in ummey suna sakin ajiyar zuciya, dukda da wahalar gudun da suka sha hakan be hana Mimi kwashewa da dariya ba , “ amma anyi d’an iska da banga lokacin da yaje janki ba da uban me zai miki? Wallahi Allah ya temaketa babu makami a wajena da babu abunda zai hana nayi masa sabuwar kaciya, wani saban dariya Mimi ta ‘kara kwashewa da shi , harararta tahee tayi “ dad’ina dake wani lokaci kamar auta Sabida wauta,shima d’an iskancan koma wanene zan nemo shi, sai kuma ta bud’e ta fun hannun ta tana ‘karewa zoben data d’auka na mutumin kallo, wani irin jan zobe ne mara kyan gani , sai hotan idanu ako ina najikin zoben , kallan mimi tayi tana ‘kokarin yin magana tahee tayi mata alama da tayi shiru, shirin kuwa tayi tana bin tahee da kallo, cikin dabara yadda ba’a ji sauti ba ta nunawa mimi lokaci da kiran da ake mata , da Sauri itama Mimi ta d’aga mata kai alamar ta soma ta fiya, hakan kuwane ya faru tahee ta soma tafiya bayan ta ‘boye zoben da ta samu lokacin da take kokawa da wannan mutumin, gabaki d’aya hankalinta a tashe yake “ kenan akwai me bibiyata? Wanene wannan mutumin da ya kesan ta’bamun martabata? Me yake nufi da cikar burin sa?”, batayi aune ba kafarta ta daki wani d’an step d’in da zata hau , Adaidai lokacin da aka fara ruwa kamar da bakin ‘kwarya, azabar zafin da tajine yasa ta saki ihu tare dayin baya zata fad’i, gabaki d’aya ta sada’kar faduwa zatayi , batayi auneba sai jinta tayi ta fad’o jikin mutum .