Author: Novels

  • Amatulmaleek 3

    Amatulmaleek 3

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    3
    Maamah Bata taba yin qasa ko sanyaba akan tsaro da tarbiyarsu kaman yanda babansu ya dage ya tsaya kafin rasuwarsa duk da ta Wani bangaren dukansu har ita suna cikin hadari a gidan Dan ita kanta ansha shigowa bangarensu da dare da niyar a afka musu ko ita ko AmatulMaleek din Amma dai Allah na tsaresu shiyasa duk tsanani basa fitowa fitsarin dare gudun a keta musu haddi basuda abin yi Dan duk Wanda aka Bata gidan bayan hakuri Babu abinda zaiyi bawai Kuma Dan baa San masuyi din ba kawai dai bakada iKon magana ne ayita rigima da iyayensu ana Allah ya Isa da tashin hankali karshe dai cuta ce anriga an cuceka.

    Maamah Bata taba Dana sani da damuwar aure a gidan taro me tsanani ba irin wannan sai yanzu sbd illarsa tafi dadinsa da albarkarsa yawa,
    Amma dai tinda Allah yasa rabonta na ‘yaya anan yake Babu yanda zatayi da kaddara bayan dagewa.

    Ko islamiyya Bata barin AmatulMaleek tafiya ita kadai kullum tare suke zuwa lokacin tashi nayi taje su dawo tare duk da ta Dan girma Amma dai hankalinta baitaba Kwanciyar tabarta taje ita Daya ta dawo ita Daya sbd yawun da samarin gidan suka hadewa ‘yartata Dan haka tasan ko a hanya zasu iya binta.

    Ita kanta AmatulMaleek tasan rayuwarta a gidan tana cikin hadari Dan haka take kiyayewa tareda kame kanta Babu inda take taba zuwa Dan haka wasu da yawa a kauyen Basu Santa ba sbd Bata fita koyaushe tana dakin maamah ana tsaronta kamar wata gwal me tsadar gaske.

    Abdulhameed Daya kasance qaninta shi Kuma sai ya zama kowa shi ya sani sbd shi Kam yawonsa yake zuwa yi tinda bara yakeyi duk da Shima Maamah din na kokari akansa Amma dai tafi Maida hankali akan Amah,
    Yaron ya kasance Yana so da shaawan karatun Boko Dan haka kullum saiyaje makarantar bokon kauyen ya shige cikin Yara
    Wannan dalilin ne yasa ake yawan kawo kararsa ga kawu bello sbd sunyita korosa Amma Baya Dena zuwa Dan haka kawun keji Asmaun da ‘yayanta sun ishesa Daman kuka aure yakeson qarawa duk da manyancinsa sosai Dan haka so yake Asmau ta tattara tabar gidan ya samu bangaren sbd ya aje yar bazawarar da zai auro.

    *****
    Asmau tayi shekaru sosai rabonta da Abeeda a idanuwanta sedai aike Wanda Wani lokacin har mantawa akeyi dasu kafin su samu Wanda daga Yan Aiken ne da aka aje duk wata sukai musu abinci Amma Sam basa kaiwa sai bayan watanni watanni suke kaiwa ganin madame din Bata qasar sai Suma suke tasu zalamar.

    A yanzu da AmatulMaleek tafara zama yar budurwar yarinya tini hankalin maamah yabar jikinta Bata bacci Batada nutsuwa kowane dare Bata iya baccin kirki sbd tsoron rayuwar da ‘yarta zata shiga a yanzu da samarin gidan da babu nagari zasu iya cewa suna son aurenta kuma tasan batada abinda zai Bata damar hanawa tanaji tana Gani zaa lalata mata rayuwar ‘yarta gashi kowannensu yaga budurwa tafara tasawa a cikin gidan sai suce sunaso gashinan da qananun shekaru sunata Tara mata daga me mace biyu Se uku sbd suna cewa sunaso akeyin wuf ayi auren sbd karfafa zumuntar da Babu so ko jin qai a cikinta.

    ******
    Iyalan ASH TALBA sun sauka a kasar Nigeria a bazata sbd rasuwar mahaifin mom Aysha wanda yake tamkar mahaifin ASH din Shima Dan haka dolensu suka dawo Nigeria.

    Saukarsu da labarin rasuwar tasa yasaka Maamah shiryawa dole itada ‘yayanta sukai Shirin tafiya duk da batada kudin mota Amma hakanan ta siyar da akuyoyinta guda biyu datake ta Reno sbd auren AmatulMaleek idan zaizo kafin lokacin sun qara hayayyafan da zasu isheta yiwa AmatulMaleek din Wani abu.

    A wulaqance aka siyesu sbd anga tanason kudin amma Bata damu ba sbd zuciyarta Sam bamai Saka damuwa bace hakama Allah yayi mata sanyin hali da tsananin hakuri me yawa Dan haka baka gane ko ka quntatar da ita sbd tana hadiye komai da sanyin halinta.

    AmatulMaleek da batajin dadin tafiyar tasu Sam Amma Bata nuna ba itama sbd kusan halin mahaifiyarta itace ta dauko sak na boye damuwa da hadiye kowanne bacin Rai da sanyin hali Dan haka itace da maamah din sukai wankin kayansu da zasuce tsumma ne ma Amma Kuma su suke dasu Dan haka dasu zasu.

    Abdulhameed kuwa farin ciki yakeyi sosai sbd baitaba barin ko wajen kauyen ba bare zuwa babban birni ba dukda baimasan me birnin ke nufi ba Dan shi Kam asalin bafulatanin kauye ne.

    AmatulMaleek din ma dai kana ganinsu kaga fulanin kauye sun fito Amma Kuma nutsuwarta ke Hana duhun kansu fitowa.

    Ranar da zasu tafi gidan kaf murna sukeyi su tafi sbd bangarensu da kowa keso saikace ce musu maamah tayi bazata dawo ba,
    To sukam Koda zata dawo din to idan ta dawo sedai ta koma zauren gidan da zama Dan kuwa duk Wanda ya shiga baida niyar fita idan ta dawo tinda Daman Neman ta tafin sukeyi,
    Qalilan ne masu son zamanta gidan sbd AmatulMaleek dasuka qwallafawa Rai akan tana Isa aure zasu aureta su jefa cikin matansu.

    Duk Wani Shirin tafiyarsu sun kammala Dan haka washe gari tinda asuba suka hau mashin Abdulhameed na gaba maamah da AmatulMaleek a Baya suka fita kauyen zuwa kauyen gabansu da acan ake Hawa motar zuwa babbar hanyar titi da acan Kuma zasu hau motar zuwa cikin state din kafin daga can su hau motar zuwa Abuja.

    Tinda suka hau mashin din Abdulhameed ke washe Baki cikin tsananin farin ciki sbd Bai taba Hawa ko Keke ba bare mashin sai yau din.

    Tafiya me Dan tsayi sukai kafin suka Isa kauyen kurmawa,
    Saukowa sukai daga kan mashin din maamah na ajiye jakar kayansu gefe
    Ita Kuma AmatulMaleek Abdulhameed Dake zare idanuwa Yana kallan koina ta kamo hannunsa suka dawo gefen maamah din.

    Kudinsa Maamah ta Ciro ta basa na mashin ya juya Yana musu Allah ya kiyaye Abdulhameed ne kawai ya amsa da Amin cikin murna da farin cikinsa da Baya boyuwa.

    Wata motar a Kori kura suka nufa wadda ita kadai ce Daman a kauyen take fita da mutane Dan haka kusan Tama cika Dan haka ba Bata lokaci aka kama su Abdulhameed din da AmatulMaleek aka Dora a sama kafin Maamah ta miqawa Amatu jakarsu tukuna itama ta tattara zaninta ta kama motar ta Haye ta zauna gefen ‘yayanta suna Dan gaisawa da sauran mutanen Dake bayan motar a Bude kowannensu kura ta gama rife koina jikinsu kaman anyi juyen yashi a jikinsu sbd iska da akeyi.

    Tafiya suka fara Babu me magana acikinsu sai Abdulhameed Dake kalle kalle har bacci ya daukesa a jikin AmatulMaleek wadda itama tafara komawa kamar bokanya sbd iska da qura Dayake Kara sauya kamannin kowa Dake motar.

    Tafiya me tsayi Nan ma sukai sosai kafin suka iso babban titin hanyar shiga kauyukansu masu shegen Nisa.

    Saukowa sukai kowa qafafunsa sunyi sanyi gashi zuwa lokacin Rana tayi Dan kuwa sha Daya saura Dan haka komai Basu tsayaba ruwa kawai da biredi kawai maamah ta Siya musu suka fada wata motar da zata kaisu state acan su samu shiga motar Abuja.

    Babu Bata lokaci motar ta cika Dan haka suka sake daukan hanya.

    Biredin data Siya musu ta rarraba musu suka fara cin abinsu hankali kwance.

    Abdulhameed duk rawar murnarsa fara komawa ciki tayi sbd zuwa lokacinda suka Isa babbar tashar yola tsoro kamasa yayi sosai sbd Bai taba ganin mutane hakaba sosai da hayaniya anata ihun Neman passengers ta bangare daya ga masu talla takoina suna ihun azo a Siya abinda suke tallan,
    Hakama a Wani gefen fada akeyi sosai a cikin tashar..

    Ba Abdulhameed ba AmatulMaleek ma kanta tsoro ne da firgici me tsananin gaske ya shigeta Dan Basu Saba haka da mutane da wannan hada hadarba Dan haka dukkaninsu qanqame hijabin maamansu sukai ita Kuma ta riqe hannuwansu gam tana Basu kariya har suka samu motar da zata daukesu zuwa Abujan suka shiga ta rungume ‘yayanta tanajin hakanan zuciyarta na karyewa da tafiyar Kuma a yanzu sbd so da dama duk halinda take ciki a kauyen sai tanajin yafi mata nutsuwa akan zuwa birnin duk da wannan tafiyar taji hankalinta ya kasu kashi biyu zatayi ne sbd magana da Madame Abeeda ta rage nauyin zuciyarta da quncin Daya dabaibayeta akan rayuwar AmatulMaleek da batasan Yaya zatai da ita acikin zuriar Sanda Fulde ba.

    Shiru tayi tareda Nisa a tinanin rayuwarta tin kuruciya da irin gatan data samu a Baya da rayuwar data taso aciki har kaddararta ta sauya mata hanya zuwa kauye da auren kauye Wanda ayau ta samu kanta a tsaka me wuya sbd rashi na Miji Kuma uban ‘yayanta Wanda da ace Yana Raye da bazata samu Kanta a wannan halin na kakanikayi da ‘yayanta.

    AmatulMaleek Dake jin tsoro me tsananin gaske a duk Nisan da suke qarawa na tafiyar shiru tayi jikin mahaifiyarta tana Jin zuciyarta na shiga yanayi na rashin murna da tafiyar dakuma yanayi na sanyi Dan haka ta rufe idanuwanta tana barin baccin datake ji daukanta.

    Kallansu maamah ta sake bayan dukkaninsu sunyi bacci jikinta ta shafa kansu su dukan tana Bude zuciyarta cikin amincin Allah tace

    “Allah ya kawo madaukakin haske da girma a rayuwarki AmatulMaleek keda ‘dan uwanki,
    Allah yasa ki zama tauraruwar macen alfahari a duk inda rayuwa zata kaiki,
    Yakuma Baki mijinda zai Miki Mafi girmamman so me tsaftan gaske..Amin”

    Numfashi ta ajiye ahankali itama tana lumshe idanuwanta sbd zuciyarta Dake jin kaman tana gazawa da gwagwarmayar.

    ****
    Tafiya yankin azaba kaman yanda aka fada,
    Sai yamma lis suka sauka birnin Tarayya,
    Daga maamah har su duka kafafunsu sunyi Wani irin nauyi da riqewa Dan haka daqyar dukkaninsu suka iya tsayuwa bayan sun fito motar zuwa lokacin Abdulhameed da AmatulMaleek sosai suke Jin tsoron mutane Dan haka a maqale suke da maamah wadda itama tasan bazata iya Kai kanta gidan ASH TALBA ba Dan haka numbern Madame Abeeda datake cikin kanta kamar hadda ta karanto aka kira musu ita cikin rashin saa akaita kira baa dagawa sbd basa daga bakuwar lamba Dan haka dole guri suka samu a tashar suka zauna ana sake kira lokaci bayan lokaci.

    Yunwa da wahala ta Saka AmatulMaleek ringa Amai a gurin har Saida dole aka nemi guri aka kwantar da ita sbd take zazzabi ya rufeta.

    Sanyi jikin Maamah yayi ga Abdulhameed Shima duk yayi laushi sbd azabar tafiya da yunwa Dan haka duk taji hankalinta ya tashi damuwa na rufeta ta zuwan nasu.

    Sallar magrib ake kokarin shiga Wanda yaketa kira musu numbern ya ringa mata fada Yana cewa wayace suzo batareda sun sanar da inda sukazo din ba?
    Basusan baa zuwa Kai tsaye gidajen manya ba batareda an sanar musu ba sbd basason damuwa da takurar talakawa da dangin kauye.

    Shiru Maamah tayi sbd zuciyarta gabaki daya Bata mata dadi jikinta yariga yayi sanyi gaba Daya Dan haka batama San me zatace ba bayan sauke Kai kasa.

    AMATULMALEEK
    Regular 700
    Vip 2k
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

    #MAMUH#
    #AMATULMALEEK
    #ASH
    #MADAME
    #FRIENDSHIP
    #LA HOT
    #ROMANCE
    #LOVE
    #ABOKIYAR NISHADI TV CHANNEL
    #MEERAH HERBS

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 29

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 29

    Episode 2️⃣9️⃣*

    Zaune yamma tan Ammi suke a palon sama na ɓangaren Ammi, suna ta hira hiyana na duba takar dun ta na boko diyana na kallon awayar Zahra amrat na karatun qur’ani, Zahra da lamrat suna kallo a makeken Tv dake manne a bango,
    da sallama yaya Khalid ya shigo palon, har suna haɗe baki wajen amsa masa sallamar kariso wa chiki yayi ya zauna saman sofa mai zaman mutun 1 murya kasa kasa hiyana tace “ina wuni yaya Khalid ya mai jiki, kakalo murmushi dole yayi kafin ya amsa mata da “lfy sister ya shirye shiryen koma wa makaranta ina fatan kungama shiri, hiyana zatayi magana Zahra ta rigata “ina wuni yaya Khalid, dawo da kallan sa kan Zahra yayi kafin ya amsa da “lfy sis love ykk, sunkuyar da kai kasa Zahra tayi dan jin sunan da ya kirata yau ta tashi daga Auta ta koma sis love.

    Yaya Khalid ya mai jiki chewar diyana “jiki da sauki sister ya aikin kai coffee, sai lokachin diyana ta ɗauke blue eyes nata daga kan wayar Zahra ta mai da kallonta izu kan yaya Khalid “hmmm ai inayi ku jiyama na kai masa kuma.. bata karisa maganar ba tayi shiru kasan chewar ta tuna abun da yaya Aryan yace mata akan idan ta kuskura ta faɗa wa wani abun da baa tambaye taba to sai ya ɓallata,

    ganin tayi shiru ta kasa karisa maganar yasa yaya Khalid ɗan sakin murnushin kaɗan dan yasan Aryan ne ya mata gargaɗi kuma hakan ba karamin daɗi ya masa ba dan diyana tana sakin layi dayawa

    “To ku shirya fa gobe zaku koma school kunji daman abun da nazo faɗa muku kenan yana kai karshen maganar ya miƙa ya nufi hanyar fita, har suna haɗe baki wajen chewa to,

    Abangaren Ahmad kuwa

    Zaune Aryan yake a gefen gadon da Ahmad ke kwanche yana kallon face nashi “bro zaka chi wani abune, ɗaga ido sama Ahmad yayi alamar a’a “why bro, why ba zaka chi abinchi ba tunfa jiya da rana baka chi komai ba haba, ɗaga ido sama Ahmad ya kuma yi alamar aa ba zai Chi komai ba, Aryan zai sake magana sai ga Bgs ya shigo tare da wani likita
    zama Bgs yayi kusa da Aryan Dr kuma ya fara kokarin sakawa Ahmad ruwa dan ta taimaka masa tun da baya chin komai,

    “Yallaboi ko dai zaku gwada maganin gida ne tun da na asibiti yaki chewar Dr yayi Maganar dai dai lokachin da yake ɗaure hannun Ahmad dan neman jijiya,
    wani dogon tsaki Bgs yaja kafin yace “Allah ya kyauta abawa ɗan uwana wan nan dattin, zan nemo kwararrun likitochi daga kasa da ban da ban suzo su du bamin shi, “Allah ya baka hakuri sir, Chewar Dr ya karisa maganar dai dai lokachin da ya gama sawa Ahmad ruwan, ya tattara kayan aikin sa ya nufi waje

    Kallon Bgs Aryan kafin yace “bro wai yanzu menene abun yi, shiri Bgs ya ɗan yi kafin yace “ban yi tunani a kai ba amma muje zuwa anjima dole musan abun yi ya karisa maganar yana mikewa, mikewa Aryan ma yayi suka fita tare

    Misalin karfe 2 na rana gaba ɗaya family sun haɗu a palo dan chin abinchin rana ban da Bgs Aiman Fahad da kuma Ahmad, shiru palon ba abun da zakaji sai karan spoons

    “My daughter ya kama ki koma gidan ki yau kinji, chewar Abba yayi maganar yana kallon Aunty farida, Mardiya salma Maryam dukka ku shirya kuma kuwuche gidan mazajen ku, “Abba daman gobe in Allah ya kai mu zan koma nariga na faɗawa dady’n junior ma chewar Aunty farida, chikin dashe war murya wadda da kaji kasan tasha kuka har ta koshi Aunty salma tace “Abba pls ka barni na kara koda 2dys ne sai mugani y jikin Ahmad ɗin zai kasanche “a’a Salma ban yar da ba gobe idan Allah y kaimu kafin karfe 1 kowache ta koma gidan mijin ta, wai ma idan kuka zauna kara masa lfy zakuyi ne? Akoi waya duk abun da ake chiki zan sanar daku ai addu’a kawai yanzu ya ke bukata awajen ku bawai kubar gidan mazajen ku, kuzo ku zauna kusa da shiba,
    Har suna haɗa baki wajen chewa to Abba Allah ya bashi lfy, gaba ɗaya palon suka amsa da amin
    shiru palon ya sakeyi ba mai magana kowa kawai tsakuran abin chin yake dan kamar magani suke jin abinchin ba dan daɗi suke chiba sai dan kar yinwa ta musu illatasu,

    “My daughter kayan nan sun miki kyau Chewar Abba yayi maganar yana kallon diyana, daman kamar jira take tafara surutu “Abba ai yaya Aryan ne ya bani ji, daman tare ya kawo mana da su Zahra shine ya kulle nawa chikin jaka, sai jiya ya buɗe min kuma Abba kaga wata dan kareriyar sar…bata karisar da maganar ba tayi shiru kasan chewar ta tuna yaya Aryan yace idan ta faɗawa wani sai daketa, jin bata karisar da maganar ba yasa Aryan sauke wata nauyayyar Ajiyar zuchiya wadda yasa Abba ɗagowa ya kallesa, kuma sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa diyana ta dakata da maganar bata karisa ba.

    saboda jin baki irin na Abba sai yace

    “My daughter ya kika dakata da maganar, a sukwane Aryan ya ɗago yana kallon Abba, harara wasa Abba ya wurga masa, da sauri ya mai da kai kasa yana ɗan murnushi dan ya gano abun da Abba ke shirin yi, “babu komai Abba kawai dai na manta me zan faɗane diyana ta faɗa tana satar kallon yaya Aryan,

    mamakine ya kama Abba daman ya tambaye tane dan yaji shin diyana tayi hankali ne ko kuma dai da saura, abun da ya bashi mamaki kuma shine yau diyana che da karya abun da bata taɓayi ba tab lallai na yar da yanzu kam diyana na Son Aryan daman zargi kawai nake Amma bari dai na sake gwada su.

    “My daughter ina malamin makaranta kun nan daya taɓa chewa yana Son kin nan?
    Ɗaure fuska diyana tayi ta ɓata rai ta turo baki ta fara magana “to ai ni Abba bana son shi soja nake so kuma ai ni tun ranan ma ban sake ganin sa ba wata kila ma ya bar makarantar, kila kuma mutuwa yayi waya sanin masa, gaba ɗaya mutanen palon sai da sukayi mamakin ɗaure fuskantar da diyana tayi har shi kanshi Aryan dan tun da suke da ita basu taɓa ganin ta ɗaure fuska ko ta ɓata rai ba ita ko dukan ta akayi tana gama kuka zata koma dariya

    “My diyana menene abun ɗaure fuska kuma? Ai ba wan da zai miki dole mijin da ki ke so shi zamu baki chewar Aunty farida “to ai Aunty farida ni bama wan da nake So sai yaya Khalid a sukwane gaba ɗaya jama’ar palon suka ɗago ido suna kallon ta musamman ma Aryan da atake idon nasa suka sauya zuwa jaa saboda kishi, itakam diyana bata ma san sunayi ba ta chigaba da magana “yaya Khalid yaya Yusuf yaya Aryan yaya Bello Aunty Zahra Aunty mardiya Aunty salma Abba Ammi Ummi Aunty amarya hiyana lamrat da amrat da ke Aunty farida sai Bappa na da Inna ta, ku kaɗai kawai nake so aduniya, wani ajiyar zuchiya Aryan ya saki, ya duƙar da kai ya ɗauki wayar sa dake gefen hannunsa kan table ɗin, yashiga latsawa

    “Hiyana karfe 3 dai dai ki dama fura ki ka womin fada Chewar Abba yana magana faɗin hakan ya miƙe ya nufi waje,
    Nmiƙewa Aryan Khalid Yusuf sukayi a tare suka fice daga palon, “haidar muje mu duba jikin yaya Ahmad ko Chewar Umar “eh ya kamata kam ya kai karshen maganar tare ta mikewa, mikewa haidar ɗin ma yayi suka nufi waje, a tare Aunty Salma da Aunty mardiya ma suka miƙe suka fice daga palon, Aunty maryam Aunty amarya suma tare suna mike suka fita, Ummi da Ammi kuwa betroom ɗin Abba suka miƙe suka shiga, palon ya rage daga aunty Farida sai su diyana.

    “My diyana daga yau idan kinje ɗakin yaya Aryan karki sake daɗewa kina jina koh? Chewar Aunty farida, “to Aunty farida ai shi yake chewa in zauna muyi magana ta karisa maganar tana turo ɗan karamin bakin nan nata

    “eh ko yache ki zauna kiche kina jin barchi sosai, jiya fa har karfe 10 ina ɗakin ku ina jiran dawo warki, amma baki da wo ba, kamar zanzo na kiraki sai kuma nache bari na bari da safe sai na miki faɗa, “to Aunty farida ba ke ki kache idan naje ɗakin na rinƙa koya masa surutu ba tun da baya magana kuma kinche ni bazai bugeni ba ko na masa surutun “eh daaa ni nache hakan amma yanzu na fasa saboda idan namiji da mace suka keɓe to na ukun su sheɗan ne,duk da zan iya shedar kanne na a ko ina, amma dai daga yau kina kai masa coffee ɗin ki dawo kinji, “to Aunty farida kawai na daiii na kai masa coffee ɗin mana tun da hakane “aa karki dai na kai masa ki chigaba da kai wa kinji amma dai da kin kai sai ki dawo, “to kawai diyana tace tare da miƙewa ta nufi hanyar fita “kutashi muje Zahra, chewar Aunty farida, gaba ɗayan su, suka mikewa a tare suka nufi waje,

    Karfe 3:5

    Da sallama hiyana ta shigo fada hannun ta riƙe da kyakkyawar kwarya ta rufe shi da pai pai, ta sanya zumbulele hijabi har kasa ajikin ta fari tas, fiskar ta sai kyalli take bawani make up da tayi asalin kayan tane kawai,ga ɗan bakin nan nata pink sosai kamar tasa jambaki, geranta kuwa kamar tayi caving, idan mutun yaga hiyana zai rantse da Allah tayi make up, amma haka fuskar ta yake,halittar Allah ne duk da kwayar idon ta Blue ne amma idon nata farine tas manya manya kamar ball, kuma idan ta kalleka kache tasa kwalli amma ba ta saba haka idon yake gata da bakin kwanche cin gashi mai tsantsi a gaban goshinta ga wani baki haɗadɗen saje a kwanche a gefen kumatun ta dogon siririn hanchin nan nata kuwa baa magana har baka yake, duk lokachin da tayi murmushi sai wani haɗaɗɗen dimple irin na Bgs ya lotsa, ga hakoranta farare tas sai wani ɗan siririn wushirya a tsakiyan hakoranta na sama

    a hankali take takawa kamar mahauniya, gaban kujerar Abba taje ta duƙa kasa ta, dukar da kai chikin ladabi da girmama wa tace “barka da hutawa Abba, wani murmushi Abba ya saki dan shi har chikin ran shi yana kaunar hiyana sosai akoi ta da ladabi da girmama na gaba da ita ga sanyin hali bata son hayaniya son addini ga sun katun boko da arabic dukka,

    Da fara’a Abba ya amsa mata, san nan ta juyo kasa kasa ta kallin in da Bgs ke zaune tace “ina wuni yaya prince, bai amsa ba kuma bai ko kalli in da take ba saima latsa wayar sa da yake,chikin kwanchiyar hankali
    Hiyana bata damu da rashin amsa gaisuwar nata da Bgs yayi ba, dan in da sabo sun saba da halin sa, “Abba ga furan ta faɗa tare da ɗago kai ta miƙawa Abba kwaryan dake hannun ta,
    Ansa Abba yayi zai yi magana Bgs ya mike yana faɗin “Abba zanje ɗaki sai da daddare, “aa Safras dawo ka zauna ai ban sallame kaba, ba don yaso ba hakan ba ya koma ya zauna dan ba yadda zai yi da Abba ne kuma ba zai iya yiwa Abban musu ba
    dawo da kallon sa Abba yayi kan hiyana dake duƙe kanta na kallon kasa

    “My daughter jeki kawo wa yayan ki nashi furan kinji, to kawai hiyana tace san nan ta miƙe da sauri ta nufi waje

    “Abba nifa bazan sha wan nan abin ba Chewar Bgs ɗin ya faɗa yana yamutsa fuska kamar wadda yaga kashi, “Allah sai ka sha, na dai faɗama ni ba santin furar bane ya jani har nabi Ammin ku Yola na kasa samun kwanchiyar hankali sai da na Aure ta, kuma ita ta koyamin sha dan nima da bana sha ɗin, “to Abba ai kai kache ba ni ba ni kam bana so kyama yake bani “koma me yake baka Allah sai ka sha na dai faɗama ka, kasani ma ko daga sha…. Sai kuma Abba yayi shiru bai karisa maganar ba, dan yasan in ya karisa to wlh ko ya zai yi Bgs ba zai sha furar ba, shi daman Bgs ba wani sauraron maganar Abba yake ba kasan chewar yasa blooth a kunne ɗaya,

    Da sallama hiyana ta dawo fada hannun ta riƙe da kwayar nono da ta damawa Bgs, har gaban sa tazo ta duƙa chikin ladabi da girmamawa tace “yaya prince gashi nan, wani dogon tsaki yaja chikin tsawa yace “dole sai na ansa ne bazaki ajiye a kasa ba,

    “mikomin nan my daughter Abba ya faɗa yana miƙa mata ɗayan hannunsa joyowa tayi wajen Abba a hankali ta miƙa masa kwaryan muryan ta har rawa yeke saboda tsoro tace “Abba zan iya tafiya, “aa my daughter zoki zauna a kujeran nan kema muyi hiran dake yayi maganar yana nuna mata kujerar kusa da shi da ido.
    Ba musu ta miƙe ta koma saman kujerar ta zauna ta sunkuyar da kanta kasa,

    miƙawa Bgs kwayar nono Abba yayi yana faɗin “ansa kasha idan nima bazaka ansa a hannuna ba sai naji, rai a bace Bgs yasa hannu ya ansa kwaryar,batare daya kalli Abban ba,
    ajiye wayar sa a gefe yayi, yasa hannu yachire pai pai da aka rufe kwaryar, kara ɓata fuska yayi lokachin da green eyes nashi yayi arba da damammiyar nono,
    yaji fura ga kwakwa da dabino,amma duk da haka Bgs sai ɓata fuska yake, a hankali ya ɗauki ludayin ya ɗebi nono ya kai baki sa sai wani tsuke hanchi yake wai dan kar yaji warin nonon.

    ….Duk abun da ya keyi Abba na kallonsa, a chikin zuchiya sa yana faɗin ai yau sai kasha nonon nan.

    a sukwane Bgs yayi wurgi da kwaryar nono ya miƙe da sauri kafin ya kai bakin kofar fada ma ya fara kwarara amai,dukawa yayi kasa,kawai ya chigaba da Aman,

    da sauri hiyana ta mike jiki na bari a zuchiyar ta tana faɗin, nashiga uku wayyo Allah yanzu shike nan na sashi yin amai nasan sai ya hukun tani.

    Ajiye kwaryar nono dake hannun sa Abba yayi ya miƙe ya nufi Bgs dake duƙe yana ta kwarara amai kamar zai amayar da kayan chikinsa, dafa kafaɗarsa Abba yayi ta baya yana faɗin “sorry, my Son,
    sosai bgs yayi amai dan sai da idon sa suka sauya sukayi jaa saboda wahala “my daughter bani ruwa a freij Chewar Abba, chikin tsawa Bgs yace “bana so Abba banson duk wani abu da yaran nan zasu taɓa da hannun su, kyamar su nake ji Abba shiyasa nache maka ni bazan sha ba, shiru Abba ya ɗan yi kafin yace “to me tama ka da kake kyamar ta, “Abba ta taɓa zubamin jin… Sai kuma ya dakata yana yamutsa fuska “ok kawai Abba yace san nan ya wuche ya ɗauko masa ruwan da kansa ya kawo masa

    Chikin tsawa Bgs ya kuma chewa Abba kace ta bar ɗakin nan ban son ganin ta, tun Abba bai yi magana ba hiyana ta fita da gudu tana kuka, shiru Abba yayi yana tunanin me yasa Bgs ya tsani hiyana haka har zai che baya son ganin ta

    Kuskure baki Bgs yayi san nan ya miƙe ya nufi hanyar fita, ido kawai Abba ya zuba masa har ya fice daga fadan, Ajiyar zuchiya mai nauyi Abba ya sauke kafin yace “Allah ya shiryamin Safar ai ko me ta maka bai kamata ka tsane ta haka ba, yarinya bai war Allah, marainiya, bani da wani burin da ya wuche a che yau ka auri mace irinta shiyasa nake kokarin haɗa ku, Amma tun da hakan bazata yiwuba dole na samo maka wata matar dan tun da kafara furta ka tsaneta nasan da iya gaskiyar ka ka tsane ta, kuma idan nache zan haɗaku tofa ni da kaina zan kashe maraini yar Allah, Ya Allah ka sassautawa Safras wan nan zuchiyar tasa, yana kai karshen maganar ya juya ya koma kan kujeran sa, ya zauna, ya ɗauko waya ya kira masu aiki akan suzo su goge amai da Bgs yayi da kuma nonon da ya zubar,

    Ƙarfe 9:10 pm agogon Nigeria ta buga

    Taku take ɗai, ɗai, kamar wata mahauniya, sanye take da wata haɗaɗɗiyar doguwar riga abaya pink colour, ta yafa mayafin rigar a kanta, yau dai batayi kwalliya ba, mai kawai ta shafa sai ɗan man baki da tasa a bakinta,fuskan ta sai kyalli take, tasa high heel pink tana rike da ɗan karamin plate mai ɗauke da cup, san nan ta rufe cup ɗin ma da wani ɗan ƙaramin plate mai shegen kyau, ta nufi part ɗin Aryan

    ko sallama babu ta faɗa chikin palon kasa kai tsaye ta haye sama stair ɗin ta shige palon sama nan ma ba ko sallama ta shige, kai tsaye betroom ɗin sa ta shege, babu kowa a chiki, table ɗin tsakiyar ɗakin ta nufa ta ajiye cup ɗin, ta juya da sauri dan gargaɗin da Aunty farida ta mata akan karta daɗe.

    Dai dai zata fita taji an buɗe kofar toile ɗin, da sauri ta wai go karaf idon ta suka sauka kanshi ɗaure yake da towel a kugun sa.

    ga jikin sa a jike da alama wanka yayi, wani kara ta saki ganin yadda kiran jikin sa yake afili, kafin yaya Aryan ya juyo tayi waje, da gudu, a sukwane ya bi bayan ta,

    saboda high heel dake kafarta bazai bari tayi wani gudu sosai ba, a dai dai zata fita palon sama ya damko kugunta ta baya, sama ya ɗaga ta da hannu ɗaya ya juya da ita cikin ɗakin, ihu diyana keyi, tana faɗin “yau kam na shiga uku yaya Aryan dan Allah kayi hakuri wlh na rantse maka bansa zaka fito ba kaya bane da bazan gan ka ba kuma ai ni, ban ganka sosai ba, shidai ko sannu bai che mata ba saman katafaren gadon sa yayi kurgi da ita san nan ya koma ya rufe kofar ɗakin ya zare makullin ya nufi dressing room nashi,

    shiru diyana ta kwanta tana kallon sama kasa kasa ta fara magana “yau kuma aljanun mugun tan yaya Aryan ne ya dawo ko?, to ni me ma na masa shiru ta ɗanyi kamar mai tunani sai kuma ta chigaba da magana “kai lallai yaya Aryan ashe haka hannun shin nan yake kato kamar chinyar lamrat, kut lallai yana da nama sosai amma kuma shine yake saka riga ya ɓoye wlh in ni ne shi bazan ɓoye ba ai hannu mai nama sosai ɗin yafi kyan gani, bari ya fito idan bai dake ni ba zan che masa ya faɗamin me yake chine hannunsa tayi nama dayawa haka nima inrinƙa chi ko nawa zaiyi, jin motsin shine yasa ta miƙe zaune tana zare ido

    Fito wa yayi sanye chikin kayan barchi mai kyau da tsada gaban morrow ya tsaya yana gyara gashin kansa, Almost 10mnt ya ɗauka a gaban mirrow san nan ya juya ya nufi saman sofa ya zauna, duk abun da yake diyana na kallonsa ta wutsiyar ido amma bata bari ya kamata tana kallon sa ba duk da chewa shi ɗin ma duk abun da yake idon sa na kanta.

    A hankali ta zuro kafafunta kasa san nan ta sauko daga gadon ta nufi inda yake, gaban sofar da yake zaune,tazoe ta sugun na, Murya na rawa tace “yaya Aryan dan Allah kayi hakuri kaji,
    “laifin me ki ka min da kike bani hakuri, da sauri ta ɗago kai, “laaaaa yaya Aryan da gaske ban maka laifi ba, kallonta kawai yake dan yanzu tama dai na bashi mamaki, “yaya Aryan in tafi ɗaki ta Tambaya tana kallon face nashi yayin da shima ita yake kallo “a’a tashi ki kawomin coffee din kizo ki zauna muyi hira “aa yaya Aryan Aunty farida tace na daina daɗe wa a dakin ka “me yasa zaki dai na dadewa a dakin nawa, dariya diyana tayi kafin tace “Aunty farida tace idan namijin da mace suka keɓe to wai na ukun su sheɗan ne, a sukwane ne Aryan ya kara waro idon sa waje yana kallonta, ganin ita ko ajikin tane ma yasa yace “ok to dauko coffee din ki kawomin sai kizo ki buga game kaɗan da wayata kafin ki koma ɗakin na ku, da sauri ta nufi table din tana murna ta ɗauko masa coffee ta kawo masa, ya ansa ya mika mata wayar sa shi kuma, gefensa ta koma ta zauna tana latsa wayar.

    “Yaya Aryan kasan me, batare da tajira amsar sa ba ta chigaba da magana, Allah ko kwanan nan ina tunanin yaya bello sosai ina kewar sa

    , wani tarine ya sarke sa coffee din ta haura masa kai sosai yake tarin, asukwane ya ajiye cup ɗin coffee ɗin ya dafe kansa da hannu ɗaya yana tari,
    da sauri diyana ta ajiye wayar ta nufi freij ta ɗauko masa ruwa, ta dawo ta mika masa, bai ansa ruwan ba sai yasa hannu ya damko wuyar ta ya fisko ta da karfi ta faɗa kan faffadar kirjinsa, sosai yake tari ya kasa magana, ita kuwa da sauri ta ɗago kai daga kirjin nashi, jin yadda yake tari, chikin tsoro tace “yaya Aryan ka sakeni in ɗauko maka ruwa dan Allah, da kyar ya iya faɗin “babu ruwan ki da ni ki bari tarin ya kashe ni “dan Allah yaya Aryan kayi hakuri Allah bana son ganin ka kana tarin kaji pls, ta karisa maganar kamar zatayi kuka, “aa ba ruwan ki dani nache maki koh “hannu diyana tasa ta toshe masa baki tana girgiza tana faɗin “dan Allah yaya Aryan ka daina faɗin haka mana wlh akoi ruwana da kai kuma har da tsaki na, hannunta ya chire daga bakin sa, chikin dashewar murya saboda tarin da yayi, yace “tashi min ajiki kuma ki fitamin a ɗaki karki sake zuwa, yayi maganar in a serious matter, “yaya Aryan me na maka to? “Ban sani ba ki tashi ki fita nace, yayi maganar da ɗan karfi

    Nan take diyana tafara hawaye tana faɗin “yaya Aryan to dan allah ka faɗamin me nayi maka da kache kar na kara kawo maka coffee, kuma ai nasan kana son coffee din, wani irn raɗaɗi yaji a zuchiyar sa saboda kukan da take, slowly yasa hannu ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna runtse ido tayi ganin yadda yake kallonta, calmly ya fara magana “me yasa kike kuka kuma?, Chikin shesshekar kuka tace “to ba kai ne ba kaki ka faɗamin me na maka, “ya isa to kiyi shiru baki min ko mai ba kinji, da sauri ta buɗe idonta tana kokarin tashi daga jikin nashi kara firgota yayi ta dawo kirjinsa har sai da kanta ya bugi gemunsa.

    …ɗago kai tayi suna fiskantar juna pink lips nata har kerma suke, zata yi magana, yayi sauri ɗora yatsan sa a kan lips nata yana girgiza Mata kai, sauko da kansa yayi ya haɗe fuskokin su yana kallonta,Wani irin farin chiki da nitsuwa ya keji tana ratsa zuchiyar sa,
    lunshe ido tayi dan ba zata iya haɗa ido da shiba, goga hanchin sa ya fara yi a jikin nata hanchin, kasa kasa yace ” menene tsakanin ki da Bello?, da sauri ta buɗe ido tana faɗin “yaya na ne kuma shine idan Inna ta hana mu abin chi yake zuwa ya karɓo mana wajen Adda hasana,

    “shike nan alakar dake tsakanin ku, “eh shike nan “to amma me yasa ki ka che kina kewar shi? “To ai yaya Aryan kaga yana da kirkine kuma idan na samu kuɗi zan saya masa mota da gida dan shima ya dawo birni, “to idan Abba yace zai Aura miki shifa? dariya diyana tayi kafin tace “nifa idan ba soja ba to bazan yi aure ba soja kawai bake so.

    Wani dogon nunfashi Aryan ya ja tare da sauke ajiyar zuchiya kafin ya sake ta “tashi ki tafi ɗaki to tun da Aunty farida tace karki daɗe, da sauri ta miƙe har tana kokarin faɗuwa,key din ɗakin ya miƙa mata,
    Ansa tayi, ta nufi bakin kofar tasa key ɗin ta buɗe kofar ta fice da sauri, miƙewa shima yayi ya nufi kan katafaren gadon sa ya kwanta ya lumshe ido yana mai da numfashi,

    Washe gari misalin 9 na safe zaune suke a palon Abba kamar yadda suka saba dan yin breakfast.

    Ammi ta dubi diyana tace “ke diyana jeki ɗauki abinchin babban yayan ku a kichin ki kai masa, a sukwane Aryan ya ɗago dan yasan halin diyana yana son ya hanata zuwa sai dai kuma bai san surutan Aunty amarya dan yasan yana hana diyana zuwa sai Aunty amarya ta sa shi a gaba da tambaya, meke tsakanin su.

    Da sauri diyana ta mike Abba na kokarin ya dakatar da ita amma ina har ta fice, kichin ta nufa ta ɗauki abinchin nashi already an gama shirya masa fitowa tayi ta nufi part nashi.

    Bb ko Sallama ta faɗa palon babu kowa kai tsaye ta haye stair ɗin ta shiga palon saman nan ma babu kowa kofar da ta gani chikin palon ta nufa ba ko sallama ta shiga,

    tsaye yake gaban mirrow yana gyara gashin kansa sanye yake chikin Black jeans da t-shirt blue, bakarin kyau kayan suka masa ba,kamar dan shi akayi su, jin an buɗe kofar ɗakin yasa ya zubawa kofar green eyes nashi ta chikin mirrow, ganin diyana che yasa ya ɗaure fuskar nan kamar wani zaki ya kau da kallonsa daga kanta

    “Kai mai kama da hiyana ga abinchin ka nan anche na kawo maka, a sukwane Bgs ya juya dan jin sunar da ta kirashi kuma har da che masa kai, chikin tsawa yace “get out, diyana ko tsoro tsawar ma bata jiba ta ɗan ja tsaki kafin tace “dan ka samu ma na kawo maka abinchi wlh ba dan Ammi ba bazan…. Bata karisa maganar ba kamar wata walkiya ta gefar da kwandon abinchin tayi waje a guje, da gudun gaske Bgs yabi bayan ta sai huchi yake

    To masu karatu sai mun haɗu ranar Monday idan Allah ya kai mu, ina masoyan diyana? tofa yau masoyiyar ku ta taɓo gidan rina ato ku tanaji ruwan zafi gasa mata jiki idan ma ta saura da ranta kenan

    💖NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

     

     

    More comments an like pls

    *💫STAR LADY💫*30

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 25

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 25

    Episode 2️⃣5️⃣*

    ……..Ɗago ido Khalid yayi yana kallon su Ahmad san nan yafara Magana “yanzu menen mafita, Khalid bai gama rufe baki ba, Ahmad ma yamiƙe yabi bayan su Aiman, dawo da kallan sa kan yusuf dake zaune Khalid yayi san nan yace “Yusuf mene mafita ni fa gaskiya ina son Zahra sosai wlh ina san muyi Aure kuma gaskiya time yayi daya kamata a che munyi auren idan fa muka biyewa su DON baza mu taɓa yin aure ba awan nan rayuwar, dan su babu Aure a tunanin su kwata kwata,
    dogon numfashi Yusuf yaja kafin ya fara Magana “yaya Khalid ni kai na ina matikar son my baby wlh, duk da yarin yache sosai amma ina san muyi aure taje ta karisa girma a gidana amma bansa ya abun zai kasan cheba kanafa jin abun da yaya prince ke faɗe, wai har abada shida Aure kuma ni nasan mawuya chin abune a shawo kan sa ya yarda yayi Aure, “dole fa Yusuf musan abunyi Khalid ya faɗa yana kokarin miƙewa “jirani muje mana chewar Yusuf ya karisa maganar tare da miƙewa shiam, suka jera atare suka fice daga palon kowa yayi ɓangaren sa

    Abangaren DON kuwa yana fita palon Abba ɓangaren sa yanufa chikin sauri, yana shiga ɗaki ya zauna a bakin katafaren gado sa, ya dafe kai dan ji yake kansa na sara masa,kamar zai faɗi kasa, tunani ya shigayi, ni gaskiya Abba bai min adalchi ba tayaya zai wani haɗani dawani abu wai shi Aure, dole ma nazo nabar kasar nan, tun kafin Abba ya sake kawo wata maganar.

    Awan nan yanayi Aryan ya shigo ya same’sa, gefen sa ya zauna saman gadon yasa hannu ya dafa kafaɗarsa cikin cool voice yafara Magana “calm down my blood kafasan idan ka shiga damuwa nima dole nashiga damuwa, kuma ni nasan ba kasan ka ganni chikin damuwa ko, ɗago green eyes nashi yayi yana sauke su kan face ɗin Aryan, har sai da Aryan ya tsorata ganin yadda idon nashi suka sauya sunyi jaaa sosai ga jijiyoyin kan nan nashi duk sun tashi duk da sanyi A.c dake ɗakin hakan bai hana DON zufa ba, chikin wata iriyar voice mai sauti yace “why, why Aryan why Abba zai nemi ya chazamin kai why yake neman kassarani, “calm down my blood ya isa haka kayi shiru pls Aryan ya faɗa tare da dora hannun sa saman ɗan karamin bakin DON ya rufe masa, yana kokarin sake magana Aunty farida tashigo da sallama, zame hannunsa Aryan yayi daga kan dan bakin DON yana kallonta

    Karisowa chikin ɗakin tayi ta zauna a bakin gadon ta ɗayan gefen su kasa DON a tsakiya ita da Aryan a nitse tafara magana “nasan abun da Abba ya faɗa bazai muku daɗi ba amma hakan kar ya dame ku kuyi hakuri, ni nasan Abba ba zai so ya ɓata muku rai ba koma me zanyi magana dashi idan ya huche, yanzu dai banaso wani abu ya dame ku dan kunsan idan kuka shiga damuwa dole nima hankali na ya tashi kuma zan shiga damuwa, ɗan dakata wa tayi da magana tana mai da numfashi, buɗe ɗan karamin bakin’sa Aryan yayi zai yi magana kenan sukaji sallamar Abba, da mamaki suke bin kofar ɗakin da kallon,

    ƙarisowa chikin ɗakin Abba yayi, mikewa sukayi gaba ɗayan su, suna kallon Abba kai tsaye DON ya nufa yaje ya rungume sa, shiru Aryan da Aunty farida sukayi suna bin Abba da DON da kallo, tunani Aunty farida ta shiga yi anya bawani abun Abba ya shirya musu ba, bata gama tunanin nata ba taji Abba yana faɗin “bana son ɓachin ran ku ƴa’ƴana kune farin chiki na, yanzu dai ke farida jeki haɗa masa complex ki kawo mana muna sha muna hira

    ……ita dai Aunty farida gaskiya bata yar da da neman sulhun da Abba yazo yi ba, dan tafi kowa sanin halinsa yanzu wata kila wani idea ne tazo masa shiyasa zai musu wayo ta haka, jiki ba kwari tana ta tunani har ta fiche daga ɗakin,

    Sakin DON Abba yayi ya haye kan katafaren gadon DON ya zauna yana ta murmushi, haye gadon Aryan da DON ma su kayi suka saka Abba a tsakiya, “Abba ya kamata mu koma bakin aikin mufa Aryan ya faɗa yana kallan Abba, murmushi Abba yayi kafin yache “ku rubuta musu later akan za kuyi wani aiki a nan na tsawon wata uku dan gaskiya ina san kasan chewa da ku a’wayan nan watannin,

    …..DON yace “Abba a matsayi na BGS (Brigadier General Safras) ba sai na rubuta wani later ba, Aryan da Yusuf kuma dama a’wajena zasu tambayi permission na hutun, tun da kana bukatar mu kasan che da kai na wata uku su rubuto min later zan sa musu hannu, murmushi Abba yayi sosai kafin ya rungumi DON yana faɗin ilove U my Son, “ilove too my love my pleasure my only Boss, farinchiki kamar Aryan ya nitse kasa dan daɗi, ganin yadda Abba da DON suke zuba wa juna kalan kauna, “eyeee lallai Abba wato haka abun yake ko? chewar Aunty farida dake tsaye a bakin kofar shigowa ɗakin tana ta murnushi hannunta ɗauke da babban trey mai ɗauke da cup 4 na complex, sakin Abba DON yayi ya juyo yana faɗin “Aunty babba kin fa iya sa ido, kariso tayi chikin ɗakin ta ajiye trey ɗin saman table ɗin tsakiyar ɗakin ta zauna saman sofa tana murnushi

    A tare suka sauko daga gadon suka nufo ta, kowa ya zauna a saman nashi sofan suna fiskantar juna, Aunty farida zata mike ta ɗauko musu complex ɗin Aryan ya rigata yana faɗin “bari na hutar dake Aunty babba, ɗaukan trey ɗin yayi ya fara miƙawa Abba, ya ɗauki cup ɗaya san nan ya miƙawa Aunty farida itama ta ɗauka, ko da yazo mikawa BGS wani harara BGS ya wurga masa kafin yace “au nine karshe ko “hannu ɗaya Aryan yasa yaja dogon hanchin BGS har sai da yace wash mugu kawai, dariya Abba yayi yana faɗin “daman Aryan kai kake jan hanchin BGS koh shiyasa naga hanchin nashi kullun tana ƙara tsawo Sosai, taɓe baki Aunty farida tayi tana kallon Abba, da mamaki wato ma idan ana jan hanchi kara tsawo yake koh? Tab ai da kuwa hakane lilin baba shine mutun na farko da zai fara bawa ummi rahab tana ja masa dan hanchin nasa yayi tsawo

    …..Wani naushi BGS ya kai wa Aryan a kumatu sai dai ina kauchewa Aryan yayi yana ɗan murnushi, bai bari hannun BGS ya sauƙa a jikin sa ba, “wai zaka ɗauki complex ɗin nan ne ko kuma na ajiye, ɗaure fuska BGS yayi kafin yace “bazan sha ba, “oh my lovely bro pls ka sha idan baka sha ba nima bazan sha ba kuma wlh inasan sha amma dole zan haku in dai baka sha ba, ɗan sake fuska kaɗan BGS yayi kafin yasa hannu ya ɗauko cup ɗin yana faɗin “zan sha ne kawai saboda kana son sha kuma bani da wani burin daya wuche inga kasamu abun da kake so, matsowa Aryan yayi ya man nawa BGS kiss, a goshi kafin yace “ina kaunar ka kamar raina my blood, “Hmmmm faɗa ɓatawa my bro ai kaunar da nake maka ba zai faɗu ba

    … Abba dai ido kawai ya zuba musu a chikin zuchiyar shi yana gode wa Allah da ya haɗa masa kan ƴa’ƴansa suke matukar kaunar ju nan su haka,

    “Abba na, gobe idan Allah ya kaimu in mun gama raka Ahmad fada, zan bi jirgin yamma na koma, chewar Aunty farida “Allah ya kaimu bai lovely daughter, shiru su kayi suna shan complex nasu chikin ni shaɗi ,

    zubur Aryan ya mike kamar wadda akawa allura yana faɗin “Abba sai da safe da mamaki BGS da Aunty farida ke kallansa, Abba kuwa sai murnushi yake chikin ransa yana faɗin, Allah kasa na chinma abun da nake hari afili kuwa sai yace “to my Son yaka mata daman ka ajiye complex nan haka kaje kasha coffee mai zafi, a’sukwane Aryan ya dawo da kallansa kan Abba yana mamakin ya akayi Abba yasan abun da zaije yayi, kashe masa ido ɗaya Abba yayi yana murmushi yace “to ka tafi mana me kuma ka tsaya kana kallan mu, jiki ba kwari Aryan ya juya ya ajiye cup ɗin complex ɗin dake hannunsa a saman table yanufi hanyar fita, yana jiyo muryan Aunty farida na faɗin “wai meke damun Aryan ne muna zaune muna hira kawai kache sai da safe, bayan ga wayan nan manya manyan idon nan naka ba alamar barchi a chikin su, fichewa yayi da sauri dan karma Aunty farida ta jefo masa wani tambayar,

    a hankali BGS ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi ya furta “kila ya gaji da hiran ne, da sauri Abba ya chan za musu topic ɗin hirar dan karsu tsawai’ta magana a kan Aryan, yasan BGS ba karamin kwakwalwa bane da shi yanzun nan zai iya gane komai “My daughter ya kamata kema kije ki kwanta kinga yanxu almost 10, “to my lovely Abba tana faɗin hakan ta mike ta ajiye Cup ɗin hannun ta saman trey, san nan ta ɗauki trey ɗin ta juyo ta ansa cup ɗin hannun BGS dana hannun Abba ta ɗora kan trey ta ɗauka tayi waje,

    Dawo da kallansa Abba yayi kan BGS san nan yafara Magana “kasan me nake so da kai my Son “aa Abba “abun dana ke so da kai dan Allah ka dai na korar yarinyar nan idan na ai’kota wajen ka, kuma ka dai na yi mata tsawa kaji my lovely Son ya karisa maganar chikin sigar rarrashi, ɗaure fuska sosai BGS yayi kafin yace “Abba ni pls ka daina aiko min su ɗaki, wlh dan ma a’baya kache kar na kara bugun tane Allah da ɗazun da tashigo sai na ɓallata, ka rinka aiko Fahad ko ka kirani awaya mana Abba haba, ya karisa maganar kamar zai yi kuka, “to shike nan zan daina aiko ta tun da baka son,

    … hakan yayi maka? mikewa BGS yayi yaje ya rungumi Abba yana faɗin “shiyasa nake son ka my Abba murmushi Abba yayi yasa hannu yana ɗan bubbuga bayan BGS kamar karamin yaro yana faɗin “nima ai ina matikar kaunar ku sosai duk wani abun da zai saku farinchiki shina ke so, “Abba muma mu ma matikar son farinchikin ka ai yayi maganar yana raba jikin sa dana Abba, miƙewa Abba yayi yana faɗin lokachin barchi yayi good night my lovely son, “good night Abba na BGS ya bashi amsa yana nufar, kaban mirrow, Abba kuma ya fice daga ɗakin yanufi part nashi, jallabiyar jikin sa, BGS ya chire ya nufi toilet dan yin wanka.

    Abangaren Aryan kuwa yana fitowa daga part na BGS kai tsaye, part nashi ya nufa da sauri yana shiga betroom ɗin diyana na fitowa ta kawo masa coffee ta ajiye zata fita, karo sukayi kanta ya bugi faffaɗar kirjinsa ta fame chiwon nata wani ihu azaba ta saki tayi baya zata faɗi, da sauri ya rikota, nan take jini ya fara zuba daga goshin nata, rungumeta yayi sosai ajikin sa da kyar ya iya furta “sorry kiyi shiru, “yaya Aryan zafi ya kemin sosai “na sani nasan zai miki zafi amma ki daure ki daina kuka kinji muje na duba miki, ya karisa maganar tare da raba jikin su, ya kama hannun ta suka koma chikin ɗakin saman sofa ya zaunar da ita, ya zauna gefen ta ya zuba mata ash eyes nashi yana kallan yadda hawaye wani ke bin wani a kunchinta calmly ya fara magana “ba na che ki dai na kukan nan ba, turo ɗan karamin bakin nan nata tayi “to zafifa yake min, hannu yasa yana goge mata hawayen yana faɗin “to ki daure kinji bana son kukan naki ne ko kaɗan yana damun na idan ki nayi, ba kiga yadda ki kayi tsara kwalliyar ki ba ko so kike ya ɓachi “a’a bana son ya ɓachi “to kiyi shiru kinji, gyaɗa masa kai kawai tayi, shi kuma ya mike ya ɗauko A box,ya dawo kusa da ita ya zauna

    A hankali ya fara gyara mata chiwon nata, sai was Allah na take faɗi shi kuma yana che mata sorry, har ya kammala san nan ya miƙe ya mayar da Box ɗin ya koma gefen katafaren gadon sa ya zauna,

    …ɗaure fuska yayi sosai yana kallonta “ke wai bana che kada ki sake kwalliya da daddare ba, baki da lfy ma amma sai kin zana waɗan nan abubuwa a ɗan karamin face nakin nan ko? turo ɗan karamin bakin nan nata tayi kamar biro kafin tace “kayi hakuri bazan sake ba “kullun haka ki ke chewa ba zaki sake ba amma sake… Bai karisa maganar ba ash eyes nashi ya sauƙa a kan kayan jikinta,

    wasu shaggun riga da wando ne, Black jeans ne ya matseta sossi santala santalan chin yoyin nan nata kamar zasu fasa wando, sai yar figaggiyar T-shirt pink colour itama ta matseta kana ganin shap na breast nata sosai daman gasu nan masha Allah tula tula dasu, ga kanta ba ɗan kwali ta saki wan nan bakin lallausan gashin nan nata har baya,sai shekin gashin ke yi, ta zubo wani ɗan kaɗan ɗin gashi ta gaban goshin ta, tayi make up nata iya make up,ga wani shegun high heel pink da ta sa a kafar ta, mamaki ne ma yaka mashi wai wa ya koyawa yarinyar nan duk irin waɗan nan abubuwa, nan take yaji ransa ya bachi sosai chikin tsawa yace “ke kina da hankali kuwa haka daman ki ka fito,kika keto gaba ɗaya part part na gidan nan har ki ka zo nan ko? chikin tsoro ta ɗago dan jin yadda yayi maganar, ba karamin raza tayi ba data kalli yadda fiskarsa ta sauya lokachi guda, asukwane ta miƙe zata gudu,

    Taku ɗaya yayi ya tamki kugunta ta baya, tsabar raza da tayine bata san, lokachin da ta fasa ihu ba, asukwane yasa hannu ya toshe mata baki, chikin tsawa ya furta “kimin shiru,shiru tayi jikinta har bari yake . zame hannunsa yayi daga bakinta ya juyo da ita suna fuskantar juna, nan take kuma sai yaji ɓachin ran nasa duk ya kau sosai yake kallon face, nata a ranshe yana faɗin “yarinya sai kyau kamar ita tayi kanta komai tayi kyau yake mata,

    Ganin yayi shirune yasa diyana ɗago blue eyes nata karaf suka sauƙa chikin nashi, murya na rawa lips nata sai kerma suke saboda tsoro kamar mai jin sanyi tafara magana “yaya Aryan kayi hakuri wlh ba laifi na bane Aunty farida da che tache… Bata karisa maganar ba sakama kon fisgota da yayi ta faɗa faffaɗar kirjin sa, dan ba zai iya jure kallan yadda lips nata ke motsawa ba,mutuwar tsaye diyana tayi dan gaba ɗaya ji tayi kamar baa duniya take ba, ran kwafar da kansa yayi sai tin kunnen’ta chikin wata iriyar kasalalliyar murya ya fara magana kasa kasa “karki sake saka irin waɗan nan kayan kinji ko? idan ma kina so sakawa kisa a iya ɗaki kawai idan zaki fita waje kisa hijabi kinji ban son na kara ganin ki haka.

    ….da kyar ta iya ɗago kanta daga kirjin nashi dan ta samu iskan da zata yi numfashi kasan chewar ya matseta sosai,bata iya wani numfashi da kyau, a hankali ta buɗe ɗan ƙaramin bakin ta muryar har rawa yake tafara magana “to yaya Aryan ai Aunty farida che tache na rinka sawa idan zan… Bai bari ta karisa ba ta ɗora ya tsan sa a saman lallausan lips nata yana girgiza kai kafin yace “a’a koda Aunty farida ta sake chewa ki saka kiche mata na hana ki kinji? kuma ai ita Aunty farida gobe ma zata koma ni dai kar na sake ganin ki da irin wan nan kayan bana so, to kawai tace masa tana numfashi da kyar saboda matse ta da yayi,

    Shiru sukayi dukkan su shi yana kallanta ita kuma tana kallon kirjinsa, Almost 5mnt a haka, san nan diyana ta ɗago blue eyes nata slowly ta sauke su kan face nashi, karaf suka sauka chikin ash eyes nashi, dan kuwa ita yake kallo, da sauri tayi kasa da kanta dan bazata iya kallan chikin idon sa ba, “yaya Aryan na gaji da tsayuwa wlh jinake kamar zan faɗi “to ni kuma ban gajiba, da sauri ta ɗago blue eyes nata tana kallonsa ganin yadda ta ɗago ne yasa yashiga tunanin me ya faɗa ne, dan shi kwata kwata bai ma san me ya faɗa ba, sauko da ash eyes nashi yayi kan ɗan karamin bakin ta, yana kallan lallausan lips nata, da sauri ya sake ta yana furta a’uzubillahi minasshe ɗanin rajim, a chikin zuchiyar sa “ke wuche ki tafi ɗaki dare yayi kuma karki sake fitowa da irin kayan nan, yana kai karshen maganar ya juya yanufi toilet da sauri wai danma kar ya sake kallonta,

    Kwas kwas kwas diyana ta juya jiki ba kwari ta nufi waje,

    Aryan kuwa wanka yayi ya fito a gurguje ya shirya cikin kayan barchi riga da dogon wando masu kyau da tsada farare tas masu laushi, ganin dare yayi sosai yasa shi hayewa katafaren gadon sa batare da yashi coffee ɗin ba ja blanket yayi zuwa chikin sa ya sage gudun A.c ya lumshe ido ba jimawa barchi yayi awon gaba dashi

     

     

    *💫STAR LADY💫*

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star Lady*

     

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 26

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 26

     

     

     

    Episode 2️⃣6️⃣*

    Misalin karfe 7 na safe Ammi na zaune a bakin katafaren gadon ta sanye take da wata ɗankareriyar lace baki mai zanen flower manya manya ajiki jaa, ɗinkin bubu gawn, ta sanya wani dan kareren sarkan gold a wuya ka wasu manya manyan abun hannu masu kyau da tsada a hannunta, sai kamshi take zubawa,kamar anyi ɓarin turare ajikinta

    da sallama ɗauke a bakin sa BGS ya shigo, kauda kai gefe Ammi tayi tana amsa sallamar, ganin hakan yasa BGS ya kariso chikin ɗakin da sauri a gaban ta ya zauna saman lallausan karpet na alfarma dake shinfiɗe a ɗakin, chikin sanyi murya ya fara magana “ina kwana Ammi, kara ɗaure fuska sosai Ammi tayi kasa kasa ta amsa masa da lfy, kwantar da kansa yayi kan chinyar ta ya riko hannunta cikin ladabi da girmamawa yafara Magana “kiyi hakuri Ammi na, kinji nasan nayi laifi dayawa amma pls ki daina fushi dani kinji, kin fa san idan ki na fushi da ni, ina cikin fushin Ubangiji kuma kome nasa a gaba bazan yi nasara ba pls my Ammi for give me, ɗan daka tawa yayi yana sauraron yaji me zata che

    ….. Hannu Ammi tasa ta fara shafa lallausan gashin kansa kafin tace “ni ba fushi nake da kai ba kuma ba zan iya fushi da kai ba saboda na san idan iyaye suna fushi da ƴa’ƴansu, wache bala’i mai girma suke jawa ƴaƴan nasu, kawai dai abun da ka keyi ne baya da chewa, “zan daina Ammi na duk wani abun da baki so ki faɗa min zan dai na “kayi alkawari “na miki alkawari Ammi na keche fa farin chikina lokachin da bana kasar nan kin ta ɓa ganin nayi 2 hours ban kira ki ba, kome aikin da nake sai na daka tar na kira ki koda na 5mnt ne, saboda kawai inji ya kike, “eh hakane na sani kuma kana da gaskiya

    …. yanzu dai abu biyu ne kake yi a gidan nan yake ɓatamin rai, kuma nake son ka daina yi, da sauri BGS ya ɗago kai yana kallan ta, murnushi kaɗan Ammi ta sakar masa, shima wani cool murmushi wan da bai ta ɓayi ba ya sake har sai da dimple nashi ta lotsa, chigaba da magana Ammi tayi “ina son ka rage tsawar da ka kewa su hiyana abun yana damuna kaga marayune ba uwa ba uba pls ku jasu ajiki dan ku mantar da su marai chin nasu, kannen kane kai yaka mata kafi kowa sakar musu fuska da jansu ajiki,

    ..ɗaure fuska BGS yayi,bai che komai ba yayi shiru yana tunani, yanzu dai sulhu nazo nema wajen Ammi bai kamata nayi wani abun da zai sake ɓata mata rai ba gaskiya bari dai na bita a yadda take so for now, in yaso daga baya na koma normal, ɗan murmushi gefen fuska ya saki a hankali ya motsa ɗan karamin bakin nan nashi ya furta “daga shi sai mai kuma Ammi, ajiyar zuchiya Ammi ta sauƙe kafin tace “sai batun kannen ka su Umar, inajin ɓachin rai idan suka gaishe ka baka amsa ba, sai kache wasu abokan gaba, ai ko bazaka amsa gaisuwar mutane a waje ba to fa ya zama dole ka rinƙa amsa na kannen ka “to shike Ammi na i will try my best kinji daɗi ” kwarai kuwa naji daɗi “Thank God, my Ammi haka nake so in ga kina chikin farin chiki, zame hannunta Ammi tayi daga gashin kan nashi tana faɗin “nima ina son naka farinchikin ai, yanzu dai katashi kaje ka shirya kuje ku raka Ahmad fada “a’a Ammi ni bazan je ba “what Ammi ta faɗa tana kara waro fararen idon ta “baka isa ba ka tashi kuma Allah idan ban ganka a fada ba.. bai bari ta karisa maganar ba yace “a’a my Ammi yanzu ma zanje na shirya yayi maganar yana miƙewa, san nan yanufi waje

    Nauyayyar ajiyar zuchiya Ammi ta sauƙe, a fili ta fara magana, Alhadulillah Allah na godema da ka bani ɗa mai kauna ta mai jin tausayi na mai gudun ɓachin rai na, ya Allah ka tai makeni nima na rinƙa faran ta masa kamar yadda yake min ya Allah ka nunamin ranar da zaiyi Aure, bana son na chigaba da ta kura masa a kan batun Aure, yana min biyayya iya gorgidon iyawar sa yana son farinchiki na, bai kamata ni kuma ya dage wajen sashi abun da baya so ba zan rinƙa taya shi da addu’a har Allah ya karkato da hankalin sa kan Auren, karisa hayewa saman gadon tayi ta kwanta da kyau ya lumshe ido tana ta tunani

    Misalin karfe 9:30 gaba ɗaya family sun haɗu a faɗa sun sha kwalliya sosai Abba na zaune kan kujerar mulkin su Ammi suna gefe gefensa, ga wata ha ɗaddɗiyar gujera a gefen na Abba ba kowa a kan gujerar, su Aryan suna kujerun dake jere gefe guda kujerun su Aunty farida na fuskantar nasu Aryan, ga manya manya baki kamar su sarkin zaria sarkin gombe sarkin yola da dai sauran su,

    Miƙe Wa Abba yayi daga kan kujerar da yake zaune, yayi tattaki izu tsakiyar fada san nan ya fara magana “kai Ahmad tashi ka hau kujerar mulkin ka, jiki ba kwari Ahmad ya mike ya nufi kujerar, yana zama su wajiri suka miƙe suka nufoshi, nan take suka ɗauko farin kyalle suka fara naɗa masa rawani a kai, shidai kamar zai yi kuka haka aka naɗa masa rawanin sarautar,bayan su waziri sun gama na ɗawa Ahmad rawanin ne, Abba yace “salati goma ga annabi yayi maganar yana nufar gujerar kusa da Ahmad,

    …zama Abba yayi san nan su kafara yiwa annabi salata bayan sun gama salati, Abba ya ɗago ido yana kallan BGS “Safras ka rufe mana da addu’a, BGS bayasan yin magana ko kaɗan amma yana gudun ya sake ɓatawa Ammi rai Allah badan Ammi na wajen nan ba da ba zanyi addu’ar nan ba, slowly ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi, da wani zazzakar Muryar sa ya fara zuba addu’oe, gaba ɗaya palon sunyi shiru suna sauraron’sa slowly hiyana ta ɗago blue eyes nata ta sauke su a kan shi chikin ranta tana faɗin “wow dama haka yake da voice mai daɗi? shi yasa baya magana dan kar murinƙa ji hmmm sosai take kalansa, har ya kai karshen Addu’ar yana kai karshe ya mike da sauri ya fice daga fada

    sai sauri yake yana taku irin na jaruman maza, yazo dai dai zai shiga ɓangaren kamar daga sama yaji murya daga bayan sa tana faɗin “baka jiba, batare daya juyaba yayi shigewar sa, kai tsaye betroom nashi ya nufa yana shiga ya nufi katafaren gadon sa, ya haye ya kwanta ya lumshe ido yana jan tsaki

    A hankalin ta turo kofar ɗakin ta shigo kwas, kwas, kwas, take takawa har gaban gadon nashi ta zo, kashe murya tayi tafara magana “haba mana shine ina maka magana a waje ka shareni, kasan wacece ni? nifa yar Autan sarkin zaria che pls kyakkyawa katashi mana muyi magana wlh ni bana barin abu a rai na da abu ya burgeni nake faɗe, wlh ka tafi da ni tun da kafara addu’a a fada nake kallon ka, kuma SON ka nake da dukkan zuchiyata, ko motsi BGS bai yiba bare tasa ran zai yi magana “haba mana kyakkyawa nasan ba kayi barchi… Bata kai karshen maganar ba taga BGS ya mike batayi auneba taji saukar wani gigitatchiyar ma haukachiyar mari,a kan kunchinta wani ihun azaba ta saki

    .. a fusache ya zaro belt daga ma zaunin sa ya fara zuba mata ta ko ina a jikin ta, ihu take kamar ranta zai fita,shiko ko ajikinsa rai ambachi yake zabga mata belt ɗin, data ga dai BGS zai iya kashe ta ba wan da yaji ihun data ke bare yazo ya taimaka mata yasa ta miƙe da kyar tanufi hanyar fita, damko atachimen ɗin datayi chikon gashi da shi yayi ya daga ta da kai, yayi wurgi da ita gefe hakan yayi dai dai da shigowar Aryan ɗakin, a fusache BGS ya sake nufar ta, ko motsi batayi da alama ta suma chigaba da bugunta yayi

    Da gudu Aryan ya karisa chikin ɗakin ya sa hannu biyu ya damko damsen BGS yana faɗin “haba blood kisa zakayi ne, chikin tsawa BGS yace “sakeni Aryan nache kasake ni “bazan sake ka ba BGS bazan sake ka ba nache, ida kuma nima zaka haɗa har dani ka bugane to Bismillah, a fusache BGS ya ya kwache hannunsa daga rikon da Aryan ya masa ya fice daga ɗakin sai huchi yake, bin yarinyar da kallon Aryan yayi a ranshi yana faɗin ko wacece wan nan kuma ko me ya haɗa su, wayar sa ya chiro daga aljihun wandon jeans dake jikin sa ya fara kiran layin Aunty farida,

    ….Bugu ɗaya Aunty farida ta ɗaga tare da faɗin “hello bro “Aunty farida kizo ɗakin BGS ki ɗauki wata yarinya “wata yarinya kuma? Aryan “eh nima yanzu shigowa na ka nan, na samu yana bugun wata yarinya gashi da alama ta suma “Allah dai yasa ba diyana ko hiyana bace “aa Aunty babba basu bane wan nan ma ba yar gidan nan bache “to ke nan a chikin baƙin nan ne, me tamasa zai bugi yar mutane, “to nima dai ban sani ba idan kinzo kya tambaye shi yana gama faɗin hakan ya katse kiran, ya juya ya fice daga ɗakin

    Misalin karfe 2 na rana gaba ɗaya family Abba sun haɗu a babban palon Abba dan chin abinchin rana ban da ƴanma tan Ammi sune kaɗai basa nan sai BGS wadda daman ba tare suke chin abinchi da shi ba, “kin san me Safras ya aikata yau kuwa? Chewar Abba yayi maganar yana kallan Ammi “aa me kuma yayi chewar Ammi “hmmm yar sarkin zaria ya kama ya rinƙa bugu yanzu haka tana asibiti wlh bakiga yadda mahaifinta ya bata rai ba da kyar na bashi hakuri “kai wan nan yaro to me ya haɗa su Ammi ta tambaya tana kokarin ajiye spoon ɗin hannunta, da sauri Aunty Farida tace “aa baruwan DON ita taje ɗakin sa ta same sa ai, shiru sukayi dan Abba ya gane dalilin daya sa BGS ya bugi yarinyar

    wai ina yan mata nane chewar Abba “suna ɗaki kasan diyana sarkin kwalliya che tana chan wai sai ta gama kwalliya, zata zo chin abinchin, su hiyana kuma suna jiranta chewar Ammi, murmushi Abba yayi kafin yace “ai tana da gaskiya gara ta rinƙa kwalliya sosai dan ta samu miji da wuri na aurar dasu, a sukwane Aryan ya ɗago ash eyes nashi karaf, idon nasa, ya sauka chikin na Abba dan kuwa shi Abba ke kallo mayar da kansa yayi ya sun kuyar ya ajiye spoon ɗin dake hannun sa ya ɗauki wayar sa ya fara latsawa,

    …… Aure kuma Abba Aunty farida ta tambaya da mamaki, “eh mana my daughter yanzu su diyana basu kai Aure bane, ai da diyana hiyana Zahra sun kai Aure kuma nan ba da jimawa ba zan musu, wani dogon tsaki Aryan yaja wadda yasa gaba ɗaya mutanen palo suka ɗago suna kallon sa “Aryan lfy Ummi ta tambaya tana kallan sa daga sama har kasa, rai a ɓace yace “lfy Ummi, kau da fuska Abba yayi daga kallon Aryan ya chigaba da chewa “ita kam diyana ma ai tana da masoya ga yaya bellon ta, na Yola ga kuma malamin makarantar su duk da naji anche an karya masa kafa, baya tafi to in dai diyana na son shi zan fiddashi kasar india amasa aiki, “oh my god Aryan yafaɗa chikin tsawa yana dafe kai, wadda sai da gaba ɗaya jama’ar palon suka tsorata, “Aryan kana lfy kuwa Aunty farida ta tambaya da mamaki a fiskar ta, ban za yayi dasu ko sannu bai cheba, Abba kuwa chewa yayi “kai ku kyalesa mana tun da ba ya son magana, mikewa Aunty farida tayi daga nata kujerar tana faɗin “aa Abba wan nan irin tsawa haka ba lfy ba ta karisa maganar tana karisawa wajen da Aryan ke zaune, hannu tasa tana shafa kansa kafin tace “me nenen bro, ɗago ash eyes nashi yayi wadda suka sauya sukayi jaa ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi zai yi magana ke nan, sai sukaji yar siririyar muryan diyana tana doko sallama tun daga bakin kofar palon

    Mai da kallon su gaba ɗaya mutanen palon su kayi izuwa bakin kofar palon, anko su kayi gaba ɗayan su chiki jalla biya pink colour Zahra hiyana lamrat amrat duk sun yafa mayafin rigar amma ban da diyana, ita kam ta tasaki wan nan bakin lallausan dogon gashin nan nata har gadon baya, a nitse suka kariso chikin palon kowan nan su na zauna a kujera table ɗin,

    Wow my daughter kinyi kyau sosai chewar Abba yayi maganar yana kallan diyana, dan ita kaɗai che a chikin su tayi kwalliya, “laaaa Abba kasan me ranan ma yaya yusuf yace nayi kyau haka yaya Aryan ma da na kai masa coffee yace nayi kyau dana ɗan kwali, asukwane matasan gidan suka juyo da kallan su kan Aryan,

    ɗaure fuska sosai Aryan yayi kamar bai taɓa dariya ba ya chigaba da latsa wayar sa, ita kuwa diyaba ko ajikin ta sai murmushi take tana bawa Abba lbr, ganin Aryan ya ɓata rai sosai ne yasa Yusuf yace “eh mana my sister ai dole kowa yace kina da kyau, to ke ba sis ɗin mu bace idan bamu yabe ki ba, waza mu yaba, wani murmushi diyana ta saki tana faɗin “Allah yaya Yusuf idan nayi kwalli ina kyau? “kai sosai ma kuwa may sis ai duk gidan nan kin fi kowa kyau kuma kin fi kowa… Bai karisa maganar ba saka makon wani mugun kallon da Aryan ya wurga masa, irin kallon nan na ina ruwan ka da ita idan ma tafi kowa kyau, shiru Yusuf yayi a chikin zuchiya yana tunani kai yaya Aryan akoi bala’e kishi to kai kaki bayyana soyayyarka san nan kuma idan wani na ya bonta ko ya raɓe ta ka hukun tashi, yanzu da kake harara’ta ni ina ruwana ai ban che ina son taba kawai yabon ta nake ni da nake da mai baby . Juyawa Aunty farida tayi ta koma wajen zaman ta ta zauna, shiru palon yayi sai karar spoon kawai zaka ji

    “Yauwa yaya Aryan wan nan jakar da ka bani nan taki buɗuwa, kullun nache zan kawo ka buɗe min sai na rinƙa mantawa, chewar diyana tayi maganar tana kallon Aryan, tab aiko gaba ɗaya palon sun zuba musu ido suna jiran amsar da zai bata, ɗago ash eyes nashi yayi ya sauke su kan face nata sai murnushi take nan take kuma sai yaji wani sanyi na ratsa zu chiyar sa, calmly ya fara magana “eh nina kulle jakar zan buɗe miki amma ba yanzu ba, tirkashi Aunty amarya ji take kamar ta tashi ta shake diyana dan bakin chiki Amma tana tsoron Abba

    Ayya yaya Aryan ka buɗemin kaji, kaga su Aunty Zahra duk sun sa nasu tsara bar kuma wlh kayan nasu yamin kyau nima ina son saka nawa ta karisa maganar kamar zata yi kuka, zuba mata ash eyes nashi yayi sosai, ya kasa kawar da kallon sa daga gare ta, Abba dai ajiye spoon nashi yayi ya zubawa Romeo and Juliet ido kawai yana kallan su, Khalid Yusuf Aunty farida sai murnushi suke suna murna, Aunty amarya Aunty Maryam kuwa kamar zasu mutu dan bakin chiki, Ammi da Ummi kam ko ajikin su abin chin su kawai suke chi basu ma lura da Abun da ke faruwa ba, Fahad ma abinchin sa yake chi ko ajikin sa bai ma san suna yi ba haidar Umar sai satar kallan yaya Aryan suke suna mamaki, tsoro suke kar ya kama su suna kallon sa, Aunty salma Aunty mardiya wayoyin su suke latsawa han kalin su baya kan jamar palon

    Da kyar ya iya saita voice nashi kasa kasa kamar mai raɗa yace “an jima ki kawo min jakar na buɗe miki yana gama faɗin hakan ya miƙe da sauri ya bar palon, dawo da kallon ta Aunty farida tayi kan Abba, ta kashe masa ido ɗaya wani cool murmushi Abba ya sake mata a hankali ya motsa lips nashi, yayi ta alama da mun fara nasara, gyaɗa masa kai kawai Aunty farida tayi san nan ta chigaba da chin abin chinta.

    Misalin karfe 3 :30 na rana gaba ɗaya ƴanmatan Ammi suna zaune a karamin palon sama na ɓangaren Ammi hiyana na riƙe da Alkur’ani mai girma tana karatu, diyana na buga game a wayar Zahra lamrat da amrat suna kallo Film a makeken Tv dake makale a bango, Zahra riƙe da littafin husnul Muslim tana karatu addu’oe, hankalin su yayi nisa a kan abubuwar da suke,

    …. da sallama Yusuf ya shigo palon da sauri suka ɗago suna kallon sa, da gudu lamrat ta miƙe ta nufe’sa hannu ya buɗe mata ta faɗa kan faffaɗar kirjinsa ya mai da hannun sa ya rufe yana faɗin “my baby nayi kewar ki, cikin shogoɓa tace “nima nayi kewar ka yaya Yusuf, hannu yasa yana shafa kanta a hankali yana faɗin “my baby ina san gashin nan naki kyau yake min, lamrat zata yi magana yayi sauri raba jikinta da nashi kasan chewar yaji alamun tafiya ta bayanzu kamar mutun zai shigo palon, riko hannun ta yayi suka karisa chikin palon suka zauna saman sofa mai zaman mutun 3,

    da sallama Khalid ya shigo palon shima da gudu Zahra ta miƙe tanufe sa, har zata rungume sa sai kuma ta dakata, kallanta yake itama tana kallon sa “sannu da zuwa yaya Khalid ta faɗa tana sun kuyar da kai “Auta yau kam babu oyoyo ne ya tambaya yana ɗago haɓatar da hannun’sa, chikin shagwaɓa tace “Ammi che tace wai kai zan Aura kuma na daina yi maka oyoyo sai bayan Aure, wani nauyayyar ajiyar zuchiya Khalid ya sauke tare da faɗin “da gaske Auta Ammi ta faɗa miki ni zaki Aura, gyaɗa masa kai Zahra tayi alamar eh, gyara tsayuwar sa yayi kafin yace “to kina sona, juyawa Zahra tayi zata gudu yayi sauri riko hannunta sai lokachin idon’sa ya sauka kan Yusuf dake zaune ya zuba musu ido, diyana kam bata ma san sunayi ba game nata kawai take bugawa hiyana ma kanta na kan qur’ani karatun ta kawai take

    Harara Khalid ya wugawa Yusuf zai yi magana ke nan haidar ya shigo da gudu yana faɗin Ammi, Ammi ina kike yaya Ahmad ya mut….✍️

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    1 Duk Karfin Izzata
    2 Gidan Aunty
    3 Jini Ɗaya
    4 Sarki Sameer
    5 Kafita Zakka

    Kar kubari abaku lbr love Story’s

    *💫STAR LADY💫*27

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*
    Star lady

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 32

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 32

    Episode 3️⃣2️⃣*

    Da sauri ta juyo ganin jabir ne yasa ta ƙara ɗaure fuska sosai, ta sunkuyar da kanta kasa, “my hiyana me ya same ki kikayi kuka? Chewar jabir Ya yi maganar yana matsowa kusa da ita, ɗan ja da baya kaɗan tayi kasa kasa tace “ina kwana, batare da ya amsa gaisuwar nata ba ya sake mai mai ta mata tambayar daya mata da farko “me yasa meki ki kayi kuka? waya taɓamin ke?

    Chikin sanyin murya tace “ni ba wanda ya taɓani kawai nayi kuka ne saboda an mai da kanwata garinmu,
    “Eyya to sorry kinji kije class idan an tashi break kizo muyi hira dan ina missing naki sosai, ko dai ke baki missing na ne? Ya karisa maganar yana ɗan dukar da kai yana leka fuskan ta dayake ta sunkuyar da kan kasa, shiru tayi bata sake che masa komai ba, ganin bata da niyar magana ne yasa yace “to kije class ɗin idan antashi sai kizo na kawo miki tsaraba
    Bata jira ya karisa maganar shiba ta shige class nasu da sauri, binta yayi da kallo har ta shige sannan ya juya ya nufi nasu class ɗin

    Sosai Bgs yake sauri kamar zai tashi sama taku yake irin na sadaukin yaki, yazo dai dai zai shiga ɓangaren Aryan, yajiyo muryan Abba daga bayan sa yana faɗin “jirani mushiga tare, batare da ya juyoba ya tsaya har Abba ya kariso, wajen a tare suka jera zuwa chikin part ɗin,

    “Menene ya hana Aryan zuwa sallar asuba Abba ya tambaya yayi maganar dai dai lokachin da zasu haura stair case ɗin chikin palon Aryan,

    “Abba wlh nima ban saniba abun da nazo tambayar sa kenan, shiru Abba yayi bai sake chewa komai ba, har suka karisa betroom ɗin, da sallama suka shiga a tare

    Kwanche yake saman katafaren gadon sa,yana sharara barchin, da mamaki Abba ya juyo ya kalli Bgs wadda shima Abba yake kallo..

    ….Karisawa bakin gadon sukayi a tare zama Abba yayi a gefen gadon shi kuma Bgs ya haye saman gadon ya ɗan jayye bargon da Aryan ya lulluɓu, zuba masa ido Bgs yayi sosai kamar mai karantar wani abu a kan face nashi

    “Abba da alama ɗan uwana bai yi barchi jiya da daddare ba koda kuma yayi to kaɗan ne, ka duba time fa yanzu Almost 8:5am amma yana barchi ko sallar asuba bai yiba, anya Aryan yana da lfy kuwa? Dogon numfashi Abba yaja kafin yace “kila akoi abun da ya tsare sa ya hana shi barchi da wurine.

    Guntun tsaki Bgs yaja sannan yasa hannu yana ɗan bubbuga hannun Aryan,
    “Aa Safras ka barshi mana yayi barchin sa chewar Abba “aa Abba ya tashi dai kofa sallar asuba bai yiba ya tashi idan yayi Sallah sai ya koma barchin, shiru Abba yayi bai sake Magana ba, bubbuga Aryan Bgs yake yana kiran sunan sa “my blood, my blood

    Da kyar Aryan ya iya waro ash eyes nashi nan, sun chanza sunyi jaa saboda barchi chikin muryan barchi yace “Bgs lfy? Ɗaure fuska Bgs yayi kafin yace “zaka tashi kaje kayi sallar asuba ne ko dai sai na maka 1bloo 7 die,

    Wani sallar asuban kuma? I Already nayi sallar ton asuba ɗin, yayi maganar yana kokarin miƙewa zaune, da kyar ya iya miƙewa zaune, da sauri yasa hannu ya dafe kansa dan ji yake kamar kan nashi zata faɗi kasa ga wani azaban chiwo da take masa, sai sara masa kan keyi kamar zai fashe,

    Ganin Aryan ya dafe kai ne yasa Bgs saurin kai hannunsa saman goshin Aryan ɗin yana faɗin “my blood lfy? Menne? Kai ɗinne ke maka chiwo? Karisa hayewa gadon Abba ma yayi ya sa hannun’sa ya riko kan Aryan yana faɗin

    “Aryan meke damun kane? ɗago jajayen idon sa yayi yana binsu da kallo ganin yadda suka ruɗene yasa ya ɗan kakalo murmushi gefen fuska, da kyar ya iya motsa lallausan red lips nashi ya furta “bb komai, a tare Bgs da Abba suka chire hannun su daga saman goshin nasa,

    Aryan me yasa baka je masallaci da asuba ba? Chewar Abba yayi maganar yana sauƙa daga gadon, “Abba makara nayi wlh, lokachin da natashi already an gama Sallah “me yasamu wayar ka? na kiraka da asuba ai a kashe, Bgs ya tambaya yana kallon face nashi,
    “Eh Ni na kashe wayar jiya da daddare, to akan idan nazo barchi zan kunna sai na manta

    Shiru Bgs ya ɗan yi kafin ya chiro wayar sa daga aljihu wandon sa, ya kunna hasken screen ɗin ya chire password ya shiga contact nashi, layin Fahad ya fara kira ringing ɗaya Fahad ya ɗaga

    “Hello big bro, ina kwana, “lfy Fahad, baki buɗe Abba da yaya Aryan ke kallon Bgs tunani Abba yake wai daman Bgs ya iya amsa gaisuwa tab lallai Fahad yarone mai Sa’a ya chire tuta a gidan nan, kaiii

    Yaya Aryan ma tunani yake anya na taɓajin Bgs yana amsa gaisuwar wani ko wata kuwa? Yayi iya tunanin sa duk bai tunano in da Bgs ya taɓa ansa gaisuwa ba kwata kwata, ko awajen Aiki yaran mu zasu gaishe sa sai dai ya ɗaga musu hannu ko kuma ya musu alamar yaji da ido, ashe daman yasan yadda ake amsa gaisuwar kenan? Lallai yaya prince sai dai nace Allah ya shirya min kai.

    “Fahad ka kawomin coffee mai zafi ka haɗo da hot milk, ina ɗakin Aryan yana gama faɗin hakan ya katse kiran.

    ..dawo da green eyes nashi yayi kan Aryan dake zaune ya zuba masa nashi Ash eyes ɗin shima yana kallon sa
    “Aryan lfy kake kallo na haka? Kawar da kallon sa gefe Aryan yayi zai yi magana sai Abba ya rigashi da chewa “ba dole ya kalleka ba daman ka iya amsa gaisuwa? Dawo da kallon sa Bgs yayi kan face ɗin Abba yace “na iya Abba “au ka iya shine idan aka gaida ka baka amsawa “wlh Abba bawai da gangan nake kin amsawa ba, kawai ni ban son magana ne Allah harchena nauyi ya kemin idan zanyi magana

    “Ba shakka Safras nima shaida ne ba tun yanzu ba haka aka haifeka baka son yawan magana amma dai karinƙa daurewa kana Amsa gaisuwar yan uwan ka, shiru yayi bai sake chiwa komai ba

    A hankali Aryan ya zuro kafar sa kasa kafin ya sauko daga gadon, jiki ba kwari ya miƙe ya nufi toilet, wani irin jirine ta kwashesa batare da ya shirya ba kawai sai dai yajisa a faffadar kirjin Bgs, kara waro ash eyes nashi waje yayi, yana kallon face ɗin Bgs yayin da shima Bgs ɗin shi yake kallo

    “Aryan baka da lfy ne? Abba ya tambaya yana karasowa wajen su, da kyar ya iya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi yace “aa Abba lfy na kalau kawai kai nane ke ɗan min chiwo sai jiri da nake gani, ɗan duƙawa Bgs yayi batare da yayi Magana ba ya saɓi Aryan a kafadar sa ya nufi toilet ɗin dashi,

    komawa gefen gadon Abba yayi ya zauna yana tunani ” lallai Aryan ai ka makara ita soyayya baa nuna mata jaruntar, ai san da zaka kawo kanka ma ba wan da ya sani, Ni kuma inshaa Allah sai na koyamaka sanin darajar mace sai kasan chewa mace halittace mai daraja Abba yayi nisa chikin tunanin sa, bai maga shigowar Fahad ba sai dai yaga mutun yana ƙoƙarin hawa gado yana faɗin
    “Abba ina kwana, murnushi Abba ya sakarwa Fahad kafin yace “lfy ka tashi lfy, fuskar nan a ɗaure kamar bai taɓa dariya ba, da kaga Fahad ba sai an faɗa maka chewa kanin Bgs bane, zaka gane domin komai nasu iri ɗaya, kaman nin su ɗaya irin yadda Bgs ke haɗe fuska haka shima Fahad ke yi, rashin son maganar su ma irin ɗaya komai dai na Fahad sak na Bgs, dan yanzu ma da Abba yace katashi lfy Fahad, bai amsa ba sai ma kara ɗaure fuska da yayi ya zaro wayarsa yana latsawa, Abba kam ko ajikinsa dan gaba ɗaya ƴa’ƴan sa ba wanda bai san halin su ba,
    Hannun su riƙe chikin na juna Bgs da Aryan suka fito daga toilet ɗin, da alama brush Aryan yayi, saman gadon suka haye, Bgs yace “Fahad ina coffee ɗin, Fahad ba tare da yayi magana ba ya sauko daga gadon ya nufi table ɗin tsakiyar ɗakin ya ɗauko kwakkyawar plate mai ɗauke da haɗaɗɗun cups guda 5 kowani cup an rufeshi da ɗan karamin plate mai kyau, bakin gadon ya dawo ya tsaya yana faɗin “gashi nan, ɗago green eyes nashi Bgs yayi yana kallon Fahad, da mamaki yace
    “Fahad coffee da hot milk kawai nace ka kawomin ya naga cups har guda biyar?

    “Eh to ai naji kache kana ɗakin yaya Aryan ne shiyasa na haɗo muku kai da shi ni kuma na haɗawa kai na black tea dan nima na taya ku sha, kaga cups 2 naka 2 na yaya Aryan, ɗaya’n nan kuma nawa, girgiza kai Bgs yayi yana faɗin “to ai daman Aryan nace ka haɗawa coffee ba Ni ba Ni kataɓa ganina inashan coffee ne? Kaje ka ajiye a saman table ɗin, bari mu sauko, juyawa Fahad yayi ya maida plate ɗin saman table sannan ya zauna saman sofa mai zaman mutun 1, yanan jiransu
    Miƙewa Abba yayi yana faɗin sai kun fito fada sannan ya nufi hanyar fita, Aryan ne kawai ya amsa wa Abba da to

    A tare suka sauko daga gadon suka nufi Fahad dake zaune saman sofa yana latsa waya.

    A saman sofa mai zaman mutun 3 suka zauna da sauri Fahad ya miƙe ya ɗauko cup mai ɗauke da coffee ya miƙawa Aryan, sannan ya ɗauko cup mai ɗauke da hot milk ya miƙawa Bgs shi kuma ya ɗauki black tea ɗin sa ya koma ya zauna, shiru sukayi

    A hankali Bgs ke ɗan korɓan hot milk ɗin haka zalika Fahad yana latsa waya yana ɗan kurban Black tea, Aryan kuwa ya riƙe cup ɗin ya kasa kai wa bakin sa yayi shiru kamar mai tunani

    “Aryan me kake tunani? Meke damunka? Bgs ya jefo masa tambaya, ajiyar zuchiya ya sauƙe kafin yace “babu komai my blood bana jin sha coffee ɗin ne bakina ba ɗan ɗano

    ajiye cup ɗin hannun sa Bgs yayi sannan ya juyo da kyau yana kallon Aryan “Aryan wai nikam yaushe kadawo ragon namiji ne? Waro manya manyan ashe eyes nashi waje Aryan yayi a sukwane ya juyo da kyau shima yana kallon Bgs, da mamaki “rago ya mai mai ta kalmar chike da jin haushin dan gantashi da kalmar da Bgs yayi, nan take kuma yaji wani karsashi yazo masa, ji yayi duk wata damuwa ta gudu domin ba abun da ya tsana arayuwa iri amasa kallon ya gaza ko kuma yana da rauni ko dai ache masa rago.
    Ganin yayi shirune yasa Bgs yace “me ya sauya kane Aryan? da alama fa yanzu kafara zama… da sauri Aryan ya sa hannu ya rufe masa baki bai bari ya karisa maganar ba domi ba zai iya jin taba, zuba masa green eyes nashi kawai Bgs yayi yana kallon face ɗin sa

    A hankali Aryan ya zame hannun’sa daga bakin Bgs san nan ya ɗauki cup ɗin coffee sa ya fara sha, juyawa Bgs ma yayi ya ɗauki hot milk nashi ya chigaba da kurɓa a hankali, shiru sukayi ba wanda ya sake magana

    YOLA

    da sallama Inna habiba ta shiga gidan su buba, da kyar take iya jan kafarta, har ta karisa tsakar gida, inna yaya Bello da innar buba suna zaune saman tabarma guda, inna yaya Bello tana shafawa innar buba magani a kafarta daya kumbura sosai yayi wani green kamar ya ruɓe,

    Saman ta barman Inna habiba taje ta zauna “sannun ki da zuwa habiba Chewar Innan yaya Bello, wani harara inna ta wurgawa inna yaya Bello, tana faɗin “to ai ba wajenki na zoba munafuka sai ki tashi ki bamu waje, ajiye robar maganin hannun ta innar yaya Bello tayi tana kokarin miƙewa,

    Da sauri innar buba ta riƙe hannun ta tana faɗin “aa innar bello dalla kiyi zaman ki, ki rabu da habiba, bata da hankali ne, waro ido waje inna tayi chikin tsawa tace “ke larai ni zaki chewa bani da hankali eh, au yanzu da wannan munafukar kika haɗa kai,kenan? “habiba ki daina zagin min yar uwa wlh idan ba haka ba zamusa yaranmu su miki duka tsiya,

    Wani dariya Inna tayi har da shewa kafin tace yanzu ne kika san dachewa ita yar uwarki che ko? to wlh idan baki dawo chikin hankalin ki ba Allah sai na tona asirin duk abu da kika aikata wa yaron ta Bello, dariya Innar buba tayi kafin tace
    “Ki tona mana, dan Allah habiba ki tona ni bani da wata damuwa idan kin tona saboda nasan bello da innar sa, zuchiyar su ba irin na dabbobi bane wlh duk kauyen nan babu mutanen kirki kamarsu ki duba duk kuntatawa rayuwansu da nayi hakan bai hanasu taimako na lokachin dana shiga halin mutuwa ko rayuwaba, alhamdulillah kuma ni nasamu na roki gafarar su kuma sun ya femin, ke ma wlh idan dai baki tuba ba to karshen ki ba zaiyi kyau ba, ko da yake ko kin tubama dole sai kin karɓi azaba da hukunchi, domin Allah baya yafe hakkin wani bawan, sai dai idan bawan shiya yafe maki da kansa, to kuma aina zaki ga bappa ki roƙi gafarar sa ina zakiga su hiyana da mahaifiyar su, duk babu wlh habiba kekam kinshiga uku

    A fusache inna ta miƙe ta ɗaga hannu zata zabgawa innar buba mari, chikin tsawa Bello dake tsaye a bayan su tun ɗazun yace “wlh kina marin ta sai na shemeki da sandar nan, a tsorache inna ta juyo da sauri dan tasan Bello akoi shi da zuchiya sosai kuma idan yace zaiyi abu tofa zai yi ne “zo ki fita mana a gida Bello ya faɗa yana nuna mata hanyar fita da hannun sa, ba musu ta kama hanya fita tana jan kafa a hankali hankali har ta fice daga gidan

    Karisawa yaya Bello yayi wajen su inna ya zauna gefen innarsa yana faɗin “innar buba kinsha maganin ki kuwa? “eh bello nasha ni dai ba abun da zanche muku sai dai in muku fatan alkhairin kuna da kyakkyawar zuchiya
    “Ki daina faɗin haka Inna ai duk abun da muka miki yiwa kaine kuma ai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya faɗa chewa idan kana tare da mutun yana aikata abun da ba dai dai ba to karka kyamachesa karka gujesa ko da ka masa wa’azi bai jiba karka damu ka jashi a jiki kana masa alkhairin a hankali kana nuna masa abun da ya keyi ba mai kyau bane sannan kana binsa da addu’a, sai kiga Allah ya shirya shi ya chanza hali ya dai na, ba wai idan kaga mutun yana abun da bai dache ba sai kaje ka zauna kana zaginsa kana tsine masa a chikin mutane ba, yanzu ba gashi da muka jaki ajiki bamu je wajen kowa mun zage kiba bamuyi gulmar ki da kowa ba bagashi Allah da ikonsa ya shirya mana ke ba, kin gane gaskiya

    Ajiyar zuchiya Innar buba ta sauke kafin tace “hakane Bello zancheka gaskiyane to Allah dai yasa itama habiba ta gane Allah ɗaya ne, a tare innar yaya Bello da yaya Bello suka haɗa baki wajen chewa Amin,
    Miƙewa innar yaya Bello tayi tana faɗin bari naje na ɗora mana girkin safe dan yau naga kamar hasana batajin daɗi,
    miƙewa yaya Bello ma yayi ya nufi ɗakin sa dan ya duba jikin matar tashi, suka bar innar buba ita kaɗai,

    Maiduguri

    Da gudu junior ya fito daga ɗakin su diyana na biye dashi a baya tana faɗin “wlh idan na kama ka zakayi bayani da harchen larabchi, kai tsaye ɗakin Aunty farida suka nufa,

    Aunty farida na kwamche saman katafaren gadon tana shararan barchinta chikin kwanchiyar hankali, kamar daga sama taji diran mutane a kanta, a sukwane ta farka ta miƙe zaune, ganin Aunty farida ta miƙe zaune ne yasa junior ya faɗa jikin ta yana faɗin “na ɓuya ai, dafe kai Aunty farida tayi tace “my diyana zonan ki zauna, ba musu diyana ta zauna kusa da ita ta zuba mata ido

    “My diyana kina jina, gyaɗa mata kai diyana tayi alamar eh chigaba da magana Aunty farida tayi, “my diyana yanzu fa kin girma bai kamata kina wasan guje guje ba kinji ko? Gyaɗa mata kai diyana tayi alamar taji, “good yanzu dai kutashi kuje palo ku fara breakfast ina zuwa, bari nayi wanka “Aunty farida yaushe zaki mai dani gida? Diyana ta tambaya
    “My diyana ki saurareni da kyau kiji me zan faɗa miki, gida ba yanzu zaki koma ba, anjima dady’n junior zai dauke ki kuje yamiki registration a school nasu junior, ki fara zuwa school kinaji na ko? Turo baki diyana tayi kamar zatayi kuka tace “Aunty farida nikam ina son komawa gida Allah, ina son ganin yaya Aryan dasu Ammi,

    “My Diyana yaya Aryan fa ya koma London, dan haka ki daina tunanin sa gida kuma zamuje nan da wata 3 kinji yanzu dai kuje Aunty jummai ta zuba muku abinchi kuyi breakfast ina zuwa,

    Jiki ba kwari diyana ta miƙe ta riko hannu junior suka fito daga ɗakin, ajiyar zuchiya Aunty farida ta sauke kafin tace “gaskiya ina da aiki babba kafin na sauya ki my diyana, dan ba abun da kika sani sai shirme da wasa
    A hankali ta zuro kafar ta kasa sannan ta miƙe ta nufi toilet

    KANO

    Misalin karfe 3:10 dankareriyar family ka dake ɗauko su hiyana daga school che ta kutso kai ta chika katafaren gate ɗin gidan, kai tsaye parking space driver ya nufa, tun bai gama gashe motar ba hiyana ta buɗe kofar ta fito da sauri ta nufi part ɗin Ammi,
    Da sallama ta shigo palon betroom ɗin Ammi ta wuche kai tsaye, da sallama ɗauke a bakinta ta shiga

    Ammi na zaune a bakin gadon ta, tana riƙe da littafin addu’oe, gaban ta hiyaba tazo ta tsugunna ta sunkuyar da kai kasa
    da wanna zazzakar kuma sanyayyar muryan nata tace “barka da rana Ammi,

    “Hiyana lfy bakije kin chire uniform ba eh? Ammi ta tambaya tana ɗago haɓar hiyana da hannun ta, “Ammi daman nazo in roke ki ne dan Allah ni ki mai dani kauye sai ki dawo da diyana nan, kinji ni zan iya jure duk wata wahala, kuma zan iya hakuri da halin inna da buba, na san diyana bazata iya hakuri ba kome buba ya mata zata che zata rama kuma wlh Ammi dukan mutu buba yake mata tsoro nakeji kar su kasheta shiya gara ni ki kai ni chan sai ki dawo da diyana nan.

    tsabar tausayi Ammi batasan lokachin da kwalla ya chika mata ido ba har yana kokarin zubowa, gaskiya hiyana mutunche, wadda samun irinta a duniyar yanzu akoi wahala ya Allah kasa ta zama matar ɗaya daga chikin ƴaƴana

    “Ki kwantar da hankalin hiyana kinji, diyana bata kauye, tana chan wajen wata kawata hajj fatima dake zaune a saudia, ammafa karki faɗawa kowa kinji ko an tambaye ki, kiche tana kauye

    ɗago blue eyes nata tayi ta ɗan saki murmushi har sai da dimple nata ya bayya, tace “to Ammi bazan faɗaba “yauwa my hiyana koke fa kinga yadda kika kara kyau da kikayi murmushi nan kuwa? To yanzu dai ki tashi kije ki chire uniform kiyi wanka kuzo kuchi abinchi, karki kara saka wata damuwa a ranki, “to kawai hiyana tace sanna ta mike da murnar ta har sauri take tanufi kofar fita

    Tana tura kofar zata fita shi kuma yana shigowa karo sukayi kanta ya bugi faffaɗar kirjinsa nan kasan chewar ya fita tsawo sosai, waro blue eyes nata tayi nan take tafara ganin jiri, baya baya tayi tana kokarin faɗuwa..

     

    💖NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

     

     

    More comments an like pls

     

  • Amatulmaleek 9

    Amatulmaleek 9

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    9
    Su maamah na isowa gida babban tashin hankalin farko data fara cin karo dashi shine rashin gurin zama Dan kuwa tini kawu bello yayi Amarya ya Sakata a cikin sashen Dan haka suka rakube dakin inna lami data rasu cikin ‘yayanta da jikokinta data bari a dakin gashi dakik a cunkushe yake Babu ko filin da zasu aje kayansu sbd kaya da hargitsin dakin.

    Batada zabi bayan ajiye tulin kayansu waje a rumfar dakin inna lami din idan sunyo wanka anan suke shiryawa gashi yayanta sunyo Wani irin fresh da kyan Gani tini aka fara Saka musu Baki gashi ko bandaki Amatu zataje saita bita ta rakata Tayo abinda zatai sun fito tare sbd tsoro da fargaban abinda zai iya faruwa.

    Amatun ma kanta samun kanta tayi da tsoron gidan da mutanen gidan sbd yanda kowa yake binta da Bakin jiki data Dan yi sbd batada jikin kiba ko kadan Amma ta Dan ciko tayi haske sosai duk duhun da fatarsu tayi ta rinewa ta wanke daga ita har Abdul maamah ce kawai ta Dan yi rama ta wahalar aikin datake sha Amma Kuma duk da Hakan itama fatarta tayi kyau sbd cima me kyau muhalli me kyau.

    Kwanansu biyu da dawowa Akai addukar sati ta rasuwar Dan haka sai kowa ya koma sabgoginsa,

    Mafarin Bude babin dawowan damuwar maamah shine sace kayansu da aka fara yi Daya bayan Daya Kuma batada iKon magana zaayita fada ana tashin hankali a gidan akan ta maqalawa yayan mutane satar kayan kunce da aka Bata tazo dasu Dan haka sai ta Dena magana ko sun duba sunga an sace musu abu shiru takeyi Bata magana hakama yayan nata Babu me magana.

    Kudinta ma baa bari ba haka aka ringa sace mata su kadan kadan Dan haka ta tattara sauran canjin ta Siya abinci dashi ta aje Wanda zasu ringa dafawa da yayanta suna ci duk da tasan basuda ikom cin komai su kadai tinda tana dakin inna lami dole duk abinda zata nemowa yayanta suci Suma saita Basu.
    Kawu bello Daya ga Hakan Saiya barta da lalurarsu ya zame Dan kuwa sauki ne ya zo masa.

    Lalurar fara yiwa maamah din yawa tayi sbd ciyarda Yara da yawa bazata iyaba tinda ba Sanaa takeyiba gashi duk abinda tazo dashi din ya qare Dan Tama manta da anbude mata acct ansaka mata Koda Bata manta ba tayayama zata iya cire kudi tana cikin wannan kauyen dajin.

    Tin tana boye gazawarta tana Fadi tashin ciyar da yaran duka har gazawanta ya bayyana Amma Kiri Kiri kawu bello yayi mata biris yabarta da ‘yayansa tana wahala dasu Dan bazata iya samowa ta bawa nata yayanba su ta Hana musu Dan haka tinda tana zaune dakin mahaifiyarsu a rakube dole ta taimaka musu itama.

     

    *******Tafiya tafara Nisa sun wayi gari ko suturar sakawa Neman gagararta da yayanta takeyi sun koma inda suka fito ga yunwa da azabar aikin wahala Dan haka ciwo yafara kokarin kwantar da ita.

    Amatu data fara iya aikin wahalar sai tana kamawa mahaifiyar tata dasu suna samu suna Dan rufawa Kai asiri.

    Duk halinda take ciki Babu Wanda ya taba ko kallanta da daraja a gidan bare a tausayawa rayuwarta a dubi marayun yayanta Dan haka take Dan sake dauriya tana dagewa Dan inganta rayuwar ‘yayanta Amma jiki da jini dole Jikin ya fara kasawa sosai harta fara kwanciya ciwo kadan kadan saiga abu na Neman tsanani.

    Amatu ce dole tafara fita da kanta Tana debo itace da zogalan da suke dafawa ana siyarwa.

    Fara fitan Amatu shine yafi daga hankali da zuciyar maamah ba ciwontaba Dan kuwa tana tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo Bata kaunar abinda zai tana daraja da rayuwar ‘yarta,
    Tinanin idan ta kwanta jinya me karfi Yaya rayuwar Amatu zata kasance acikin wannan gidan?
    Yaya zata iya tsayawa ta taimaka gurin Bata kariya daga sharrin mazan gidan?
    Komai zai iya faruwa da Amatu tana daga kwance Babu abinda zata iya yi…

    Innalillahi wainna ilaihirrajiun,wannan tinanin kawai ke gigitata hankalinta yayi mummunan tashi harta Saka abin a ranta damuwa tayi mata yawa ciwonta sai qara gaba yakeyi.

    Babu abinda yafara zuwa ranta da tinaninta sai komawa Abuja gidan Abeeda sbd Koda Allah yasa ciwonta bana tashi bane tasan tabar yayanta inda zasu tsira da mutunci su kuma su samu kariya da kulawa.

    Wanna tinanin nata na sake komawa can din yake sake qarfafa a zuciyarta sbd Daman baaso dawowan nata ba ta dawo Amma Kuma babban abinda yake hanata zama acan din shine tayaya zataje tayi zaman dindindin gidan ‘aminiyarta duk da ta Dade da zama ‘yar uwarta tamkar jininta.

    Wanna tinanin shine yake sake addabarta,takasa tafiya takasa Jin nutsuwar zama Dan haka abin ya taru ya sake mata yawa.

    Su Amatu ma gaba Daya a tsorace suke da ciwon maamah din Dan kuwa a yanda suke ganin wainda iyayensu suka rasu a cikin wannan gidan almajirai suke komawa na karfi da yaji hakama lalacewansu yawa takeyi Dan haka tsoro ya kamasu Dan su tsoron ma irin wasu abubuwan Dake faruwa a gidan sukeyi sbd maamah datake Saka musu tsananin tsoron Hakan Tintini.

    Rashin takamaimai shawara da madafa yasa suke cikin garari kullum Kuma suna waya sosai da Abeeda a yanzu sbd wayar data dawo da ita wadda aka Siya mata tin acan Amma bata iya fada mata halinda take ciki ba.

    ****Acikin wannan mummunan halin dasuke ciki kwatsam suka wayi gari da Kiran Husnah a wayar maamah din cewan Abeeda ba lafiya sosai.

    Labarin shine Mafi tashin hankalin labarin Daya samu maamah sbd Abeeda Bata taba ciwon da harya kaita kwance ba Dan haka zuciyarta tayi nauyi da tsoron meya samu Abeedan,
    duk da ita ma a kwancen take Amma ciwon Abeeda ya sata danne nata azaban ciwon ta fara kokarin Shirin tafiya Dan kuwa ita kanta Abeedan zataso ta farfado Taga Asmau acikin wainda suke zagaye da ita.

    Halinda ta shiga na tsananin damuwa da kokarin boye nata ciwon akan son zuwa inda Abeeda da kwana biyu batasan inda kanta yake ba yasa Amatu shiga mummunan damuwa itama da tausayin mahaifiyarta datasan tana cikin nata mawuyacin halin Amma kaunar datakewa Abeeda yasakata dannewa idan ba ganin kanta tayi sun Isa inda Abeedan takeba bazata taba nutsuwa ba.

    Acikin kwanaki biyu sukai Shirin tafiya Abuja,
    Dayake batada lafiya yanda ya kamata da Kuma kudi da Babu a hannunsu dole tareda kawu bello suka taho har cikin garin Yola suka banki ta basa komai aka ciro kudi daga bankinta ya cire kudin da aka basu aro daga can na tahowa tareda nasa kudin komawar harma Dana Shan ruwa a hanyar komawa tukuna ya rakasu suka hau motar Abuja shikuma ya hau ta komawa kauye.

    Koda suka dauki hanyar Abuja a mota shiru Amatu tayi tareda zubawa hanya idanuwanta dasuka fada kwana biyu sosai sbd jinya da kulawa da maamah,

    Wannan tafiyar tasu kaman yanda maamah ta fada ba lallai me dawowa bace sbd tanason Koda zata kwanta tabarsu a hannun ‘yar uwarta,
    Meye makomarsu daga ita har Abdul idan maamah ta tafi kaman yanda take fada?
    Daga dangin uwa harna Uba basuda takamaimai inane kaddararsu zata kaisu Dan haka take fata da adduar Allah yabarsu da mahaifiyarsu har girma da tsufa su rayu tare su mutu tare.

    Kaman yanda sukasha wahalar hanya wancan Karan wannan ma sunsha sedai wannan da sauki sbd sunsan Daman tafiya ce me Nisa zasuyi ba kaman na farkon ba da basusan Nisan tafiyar ba.

    Sai bayan ishai suka sauka Abuja Dan haka Kai tsaye driver ne yazo daukansu harda Husnah wadda itace tazo da driver din sbd ta matsu su maamah din su iso.

    Tana ganinsu jikin Maamah ta fada tareda fashewa da kuka sbd tanata Neman Wanda zatai kuka a jikinsa Amma Babu Dan kuwa duk kauna da gatan da mum Aisha ke nuna mata ita Bata Jan Yara a jikinta ga mommynta akwance kwanaki batasan inda kanta yake ba.

    Ita kanta maamah Jin tayi idanuwanta na cikowan da hawaye na tsinkewan zuciya Amma hakanan ta daure tana boye nata ciwon suka nufo gida.

    Dayake dakinsu na Baya Yana Nan Babu kowa a cikinsa anan suka sauka bayan duk masu aikin gidan sun tarbeta tareda mata sannu da zuwa harma da gyara mata dakinta da wanke toilet da komai.

    Basu zaunaba sai da sukaje har palon mum Aisha suka gaisheta tareda mata jajen jikin Abeeda din.

    Sama sama ta amsasu tana kallan yanda duk suka sauya ba kamar yanda suka bar Nan din ba musamman Amatu data rame sosai.

    Abdul ne ma dai take Dan sakewa Dan haka shi ta ringa tambayar Yaya kauye da karatu Yana amsawa har suka fito suka koma inda suke.

    Wanka sukai dukkaninsu suka gasa jikinsu musamman maamah da jikinta yayi nauyi sosai na ciwo da gajiya.

    Abinci aka kawo musu Saida sukai salloli suka ci take kowannensu bacci ya kwashesa a qasan tiles din sai maamah suka barwa gadon sbd rashin lafiyanta.

    Washe gari Babu tinda Babu abinda sukeyi bayan cin abincinsu da mum Aisha zata asibiti ta tafi da Maamah gurin Abeeda din sbd yanda duk maamah tayi zuru zuru Babu baccin arziki sbd rashin sanin menene yake damu abeedan.

    Koda suka Isa babban private asibitin me tsadan gaske suka Isa sama har dakin da Abeedan ke kwance baa Wani shiga sbd baa son motsi me yawa ko karfi.

    Ahankali maamah ta iso har bakin gadon Abeedan tana kallanta da idanuwanta dasuka fara cikowa da wasu irin hawaye masu dumin kayewan zuciya na ganin mace kamar Abeeda a kwance gabaki daya kamar ba itaba a cikin qanqani lokaci Allah ya Maida ita Hakan,

    Tayi Wani irin haske tayi fayau kamar wadda Babu jini ko kadan a jikinta hakama fatarta kamar wadda aka shafe da yar farar Hoda.

    Kasa riqe hawayenta tayi suka fara gangarowa tana Sauke idanuwanta daga kan Abeedan tanajin kaman zuciyarta bazata dauka ba sai kawai ta fashe da Dan kuka mara sauti tana Jin halinda Abeedan ke ciki har cikin zuciyarta.

    Ita kanta mum Aisha duk tazo Jin takeyi zuciyarta na karyewa sbd abu ne dayazo lokaci Daya hakama ASH TALBA yakasa fada musu abinda likitoci sukace akanta tin ranarda aka kawota asibiti zuciyarsa ke cikin Wani mummunan hali Amma qarfin halinda yaqi nunawa,

    Abeeda wata tsoka ce a zuciyarsa dayakejinta musamman duk da baisan Menene so ba,
    Idan Hakan shine so to tabbas Abeeda tagama zama sonsa qwal Daya da bayajin zai samu sassauci akan Hakan.

    Kuka sosoi maamah Tasha a asibitin Wanda yasaka nata ciwon datake dannewa tashi sosai sbd Daman ita Kuma matsala ce ta zuciya datake kumbura tsaban kunci da damuwar datake ciki.
    #MAMUH#
    For more pages follow me @Mamuhgee at arewabooks or join vip

    *_AMATULMALEEK_*
    By Mamuhgee
    And
    *_YANCI DA RAYUWA_*
    By Hafsat Rano
    Na kudi ne
    For more page ku biya
    500 for littafi Daya
    1k for duka books din biyu
    at👇
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

  • Amatulmaleek 6

    Amatulmaleek 6

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest #

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    6
    A qasa kan tiles Maamah tayi kwanciyarta kan daddumar sallah tareda Abdulhameed Daya shige jikinta tin tana jiran farkowan AmatulMaleek har bacci ya Dan fixgeta itada Abdulhameed din.

    So biyu ana Aiko khaltume dubasu ko sun tashi Amma Basu tashi ba Kuma Madame tace kada a tashesu Dan haka aka barsu sukai bacci sosai batareda Maamah din ta san ta dauki lokaci sosai haka tan baccin ba.

    Sanyin tiles ya dayayi musu yawa ya farkar da ita dole lokacin karfe biyun Rana harda minti talatin da takwas Dan haka cikin sauri ta tashi tana janye Abdulhameed Daya cukuikuyeta sbd sanyi ta miqe tsaye tana kallan gadon Taga AmatulMaleek din itama tana motsawa alamar tashi zatayi Dan haka toilet kawai ta wuce Tayo alwala ta fito tayi sallah tana idarwa Amatu na farkawa Dan haka itace ta kamata da kanta takaita toilet tabarota.

    Ita kanta Amatu ta Dan iya aiki da wasu abubuwan bandakin sbd zuwan da suka taba yi tafara Dan wayo lokacin.
    Fitsari tayi Tayo alwala itama ta fito ta tsaya gefen Maamah tayi sallah tana idarwa Abdulhameed na na tashi daga baccin Shima.

    Da sauri Maamah ta miqe ta rakasa toilet sbd fitsarin dayake cewa ya matsesa.

    Bayan fitsari harda zawo yayi sbd abincin Daya Dan fara tabashi kasancewar ciki Bai Saba da wannan dadin ba,
    Fitowa yayi bayan Maamah ta wanko masa hannuwansa da kyau da sabulu
    Gefen AmatulMaleek ya zauna Yana kallan kayan abincin Dake gefen ajiye yafada mata nata ne sunci sun rage Mata tin dazu.

    Kallansa Amatun tayi bayan ta Kalli kayan abincin Amma Bata motsaba sbd ba Maamah ce ta Bata ba.

    Maamah kuwa toilet din tahau wankewa sosai sbd kada su lalata musu guri Dan tasan tsananin karfin tsaftan masu gidan sbd duk Wanda ko kalilan sani yayiwa ASH TALBA yasan inda qazanta take da inda yake akwai Nisa me yawa da zurfi.

    Sosai ta Saka karfinta ta wanke toilet din tayi masa fes ta fito tana kallan Amatu Dake zuru tana kallan Abdulhameed Dake ta fada mata dadin abinda suka ci din tana bacci.

    Wani sanyayyan murmushi maamah tasaki tana qarasowa fuskarta a sake ta kallesa tana cewa

    “Gashi Kuma bazaka sake ci ba yanzu sbd yafara lalata Maka ciki.”

    Dariya yayi Yana maqale kafadarsa Yana cewa

    “Zan sake ci mana ai idan munkoma bazan sake ci ba shikenan.”

    Daga Maamah har Amatu da batada karfin jikinta qaramar dariya suka saki sbd yanda yake matse da a dauko abincin.

    Maamah ce ta janyo abincin bayan ta zauna itama a tareda su qasan.

    Bude abincin tayi da kanta ta zubawa AmatulMaleek komai kaman yanda suka hade tana cewa

    “Ki cinye tas sbd Kinga ba karfi jikinki ta yanda zaku samu kuzari sai muje akaimu ku gaida mommynku Abeeda harma da sauran mutanen gidan.”

    Gyada Kai kawai AmatulMaleek tayi tana Saka hannu a abincin sbd itama ya shiga ranta sosai duk da batada kwadayi Amma shi abinci irin wannan basama ganinsa bare.

    Abdulhameed ma dole tareda Amatun ya sake cin abincin itama Maamah hannu ta Saka sukaci abincin tare su uku Abdul naci Yana tambayar AmatulMaleek idan tanajin dadin dayake ji a abinda sukeci din.

    Dariya Amatun ta Dan ringa yi masa tana cewa

    “Maamah wlh ‘dan Nan naki duk ya haukace sbd cin abinda be taba ci ba.”

    Itama Maamah din yar dariya tayi tana cewa

    “Kyalesa yaci ai na kwana biyu ne muna komawa kaman yanda ya fada shikenan.”

    Cikin kulawa da tsananin so da kaunar juna sukaci abincin su uku suna Dan magana Sam sama,Maamah kusan duk Rabin cin abincin nata su take gyarawa kidin tana ja ye musu qashinsa abubuwan data San bazasu iya ci ba tana musu fira cikin kulawa da kaunarsu.

    Suna gamawa wannan Karan su ukun suka shiga toilet suka wanko hannuwansu Maamah na fitowa ta tattara gurin tareda kayan ta fito dasu ta nufi hanyar kitchen tana isowa khaltume da Masu aikin abincin Dake girkin dare kallanta sukai tareda karban kayan hannunta.

    Kallan khaltume tayi tana cewa Ina zata wanke kayan saita wankesu da kanta.

    Karban kayan khaltume tayi tana cewa ta barshi kawai.

    Kasa tafiya maamah din tayi sai data taimakawa khaltume gurin wanke kayan kafin ta koma.

    Zama sukai a dakin shiru daga ita Se su Amatu suna Dan firarsu sama sama sbd daga Amatun har Abdulhameed sun warware kamar ba’a nade aka shigo dasu ba ba lafiya sosai Daman yunwa ce da wahalar hanya Se iska da sanyin kwanan Tasha.

    Har yamma Babu Wanda ya shigo inda suke aka nemesu Suma haka sukai zamansu.

    Koda Akai sallan magrib Wani abincin aka sake kawo musu Basu ci ba sai da sukai sallah tukuna suka zauna sukaci a plate Daya su dukansu dayake wannan Karan farar Basmati rice ce da brown chicken stew wadda Babu Mai sosai acikinta sbd lafiyansu da suke kulawa da ita sosai a gidan.

    Kazar Dake cikin miyan zata Kai guda harma da Rabi Kila Dan kuwa duk yanda sukaci ta Basu cinyeba hakanan suka tattara kayan Maamah dince ta sake fita dasu takai kitchen ta dawo.

    Har Akai ishai baazo antafi dasu can gurin masu gidan ba sbd umarnin da Abeeda ta bayar na a barsu suyi kwana biyu suci su huta yanda ya kamata kafin su fara Dan zagayawa sbd sam Bata kaunar ganinsu a yanda suke din.

    Da daddare maamah barwa Abdulhameed da Amatu gadon tayi sbd baida Wani girman da zai daukesu su uku Dan haka tayi kwanciyarta qasa tabarsu a saman sukai bacci.

    Bacci sukai sosai Wanda suka jima Basu irinsa ba sbd samun gurin baccin me nutsuwa ba sauro ba komai Dan haka har Akai asuba Basu saniba Saida gari yayi haske Maamah ta Farka tana tashi zaune kafin ta miqe ta nufi toilet Tayo tsarki da alwala tana fitowa kafin ta tada sallah ta tana Amatu tana Kiran sunanta a nutse.

    Cikin baccin dabe saki Amatun ba ta Bude idanuwanta masu Dan girma tana cewa

    “Maamah baccin be sakeniba”

    “Tashi kiyi sallah Se ki koma tinda Babu aikin da zamuyi anan din.”

    Sake Dan juyawa tayi tana Bude idanuwanta tareda Kai hannuwanta duka biyu tana ture kafafun Abdul Dake kanta cikin Wani shegen mugun bacci Wanda ko a gida haka suke kafin safe ba qaramin shuri takesha a gurinsa ba sbd Mayen baccinsa.

    Saukowa tayi gadon tana murza idanuwanta ta nufi bayin ta shige tana Bude idanuwanta dakyau sbd kada ta zame.

    Koda ta fito Maamah tagama sallah tana zaune tana Dan kokarin tada Abdul Shima cikin kulawa da rarrashin ya tashi yayi sallan.

    Sallah tayi tana idarwa itama ta zauna gefen maamah din wadda da kanta takai Abdul toilet yayo fitsari da alwala,
    Inda ma Allah yayi mata babban rufin asirin dukkaninsu yayan nata Babu me fitsarin kwance da batasan ya zatai ba.

    Bayan sun gama sallah Amatu ce ta kwanta qasa Maamah din Kuma da Abdul suka koma kan gadon suka kwanta dukkaninsu baccin ne ya sake daukansu hankali kwance.

    Se qarfe Tara aka kawo musu abincin breakfast Wanda Tintini Daman sun tashi har sunyi wanka sbd kada Azo a taddasu da kowacce irin rashin tsafta.

    Ayau ma lafiyayyan breakfast suka sake karyawa dashi Wanda kusan iri Daya Dana jiyan ne sedai yau tareda Wani Irin tea me shegen kauri Daya Saka Abdul ringa fadar akwai Madara sosai a cikin shayin.

    Haka suka sake wuni guda Babu Wanda yazo ya tafi dasu sedai abincin da aketa kawo musu da lokacin cinsa yayi.

    Bata damu da cewa Se sunje gurin Abeeda ba sbd tasan tana sane dasu Kila wata hidimance ta riqeta Batada lokacin ganinsu yanzu.

    Abdul kuwa Jin yayi shikam yafara son gidan sbd dadin dasuke ci Kuma basa komai bayan kwanciya da Shan AC Wanda sanyinsa yafara taba Amatu ita Dan Sam Bata son sanyi duk da tana yarinya yanzu ne ze tabata.

    ****Kwanaki kusan hudu masu kyau aka Basu suka huta yanda ya kamata bayan ci me kyau da sha me kyau Babu abinda suke Samu,
    Hatta yar suturar sakawa anbasu dukda ba masu yawa bane Amma sukam a gurinsa me yawan ce,

    Abdul sosai a yanzu yaji bayason su koma gida Dan kuwa shi ko wannan ci a koshin da abinci mekyau aka barsa ganin yakeyi duniyarsu ta gyaru Dan haka tini shi Kam ya fara kumatun Kwana biyu,
    Amatun ma ta Dan yi kumatun duk da batada jikin kiba ko kadan Amma dai ita cima me kyau da wuri take nunawa,
    Maamah kuwa sosai ta dage da kulawa da inda aka ajiyesu din sbd karsu lalata inda aka ajiyesun kafin su tafi hakama duk takai kayan abincinsu kitchen seta Dan taimaka musu da Wani aikin sbd Bata Saba da zama Babu aikin komai ba Jin takeyi duk ba dadi sbd su Basu Saba da Hutu ba da wahala suka Saba.

    Ranarda suka cika kwana biyar da zuwa aka Aiko khaltume ta tafi dasu cikin asalin gidan inda masu gidan suke,
    Kai tsaye sashen Abeeda aka nufa dasu khaltume na gaba suna biye da ita.

    Abdul na hannunsa na riqe cikin na maamah sbd kada yanda yake kalle kalle,
    Amatu kuwa tana gefen maamah din itama tana Dan kallan koina.

    Babban palon Abeeda ko yau aka nufo dasu suka zauna ‘yayanta na gefenta matse da ita suna Dan kallan makekiyar flat screen tv din Dake aiki a palon ba murya sosai.

    Abdul sai taba Amatu yakeyi Yana nuna mata abubuwan da duk idanuwansa suka Gani na mamaki ita Kuma tana gyada masa Kai sbd batasan me zata ce masa ba.

    Basu Wani jimaba Abeedan ta fito fuskarta dauke da murmushi me yalwa da kulawa tareda kauna a Fili tana kallansu ta qaraso sanye cikin Wani milk dry lace Daya gama bayyanar da kudinsa sbd yanda take a kwance kamar cotton.

    Zaunawa tayi idanuwanta dasuka fada suna kan AmatulMaleek wadda gabaki daya Babu abinda ta baro na mahaifiyarta Asmaun sai haske data Fi Asmau Amma komai na maamah dinne.

    Manyan idanuwanta farare ta kalla tana mamakin Irin kamannin Asamun da Amatu ta koma sak,
    Numfashi ta sauke ahankali tareda sake fadada murmushinta da kulawanta tana miqa hannunta ta Kila Abdul Wanda yake kallanta Amma ya kasa zuwa sai maamah Daya kalla wadda cikin murmurshi ta gyada masa Kai tana cewa

    “Jeka ka gaida mommyn UK da kaji Amatu na fada”

    Amatu kuwa cikin nutsuwa da girmamawa itama ta Bude Baki ta gaidata cikin Dan sakewan fuska da ganin mommyn.

    Amsawa tayi itama tana Jin kaunar yaran tace

    “Asmau AmatulMaleek ta fara zama budurwa Ashe,
    Allah yasa dai kada iyayen Nan nasu Maza suyi tinanin yimawa auren kauye da wuri sbd bazamu yarda ba Sam da wannan dabiar ta kauye”

    Dariya mara sauti maamah tayi tana cewa

    “Toh ai sedai ace Allah ya tsare Amma Kam Kila Hakan zaa samu”

    Dan kame fuska Abeeda tayi tana sake qarewa Amatun kallo Tana cewa

    “Sam wannan bazai yiyuba sbd zasu kashe rayuwarta ne,Ina Sam Sam,wannan ai rashin hankali ne da cutatar da rayuwar Yara qanana sbd wasu shekarun nasu da gaske Basu kaiba.”
    #MAMUH#
    #AMATULMALEEK
    #ASH
    #ROMANCE
    #NAUFAL
    #FAMILY
    #WEALTH
    #LA HOT

    *_AMATULMALEEK_*
    By Mamuhgee
    And
    *_YANCI DA RAYUWA_*
    By Hafsat Rano
    Na kudi ne
    For more page ku biya
    500 for littafi Daya
    1k for duka books din biyu
    at👇
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

  • Amatulmaleek 5

    Amatulmaleek 5

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    5
    Abeedan bazata iya daukanta ba Dan haka dole masu aikin ne suka dauki AmatulMaleek din maamah Kuma tana dauke da jakarsu suka dunguma zuwa ciki.

    Kai tsaye sashen masu aiki aka nufa dasu dayake akwai daki na musamman acan aka Bade musu Daya aka kwantar da AmatulMaleek din gefen Abdulhameed Daya farfado shi Amma baida karfin iya motsawa sai tsoro Mai karfin gaske Daya shigesa ganin inda suke kaman baa duniya ba duk da baisan yanda aljanna take ba da lahirar.

    Abeeda da kanta ta fice tana bawa masu aikin umarnin su fara yaran kafin a kirawo likita yazo ya dubasu cikin gaggawa.

    Abdulhameed suka fara yiwa wanka fes suka dirji uwar dauda da kurar jikinsa kafin suka fito dashi.

    AmatulMaleek kuwa kasa barinsu maamah tayi da kanta ta daure ta wanketa tsaf ta fito da ita.
    Kaya aka Basu suka Saka Wanda AmatulMaleek din take aka karbo kayan Husnah Talba daga bangaren iyayen gidan aka Bata maamah ta Saka mata hakama Abdulhameed kayan haidar aka Saka masa take suka Dan yi kyan Gani Babu Bata lokaci likita tazo ta fara dubasu Duk da shi Abdulhameed ana basa tea me tsananin kaurin gaske ya shanye katan Kofi yafara Dan samun kuzari.

    AmatulMaleek kuwa ana Bata tea din haka ta amayosa Dan haka dole aka sake gyarata kafin likitar tazo.

    Ita kanta maamah ta tsaftace kanta cikin ‘yar suturar da aka Bata Dan baayi qasa a gwiwar Kai kayansu store ba aka ajiye sbd Babu Wani sutirar arziki acikinsa.

    Da farko sosai hankalin Abeeda ya tashi da ciwon na yaran Dan Bata dauka yunwa da wahala ne tareda iska Dasuka wuni suna sha a hanya ba tin asuba ya jijjigasu gaba Daya.

    Likita Abdulhameed ta yara dubawa dakyau ya tabbatarda gajiya ce da azabar yunwa a tareda shi Dan haka ruwa kawai ya daura masa Dan karfinsa Daya tafi ya Dawo.

    AmatulMaleek kuwa bayan yunwa iskane ya shigeta sosai Wanda Bata Saba sha ba sbd basa zuwa koina koyaushe suna kauye cikin gida a zaune,Se yunwa da wahalar hanya ta doguwar tafiyar da tinda tayi wayo Bata taba ba.

    Itama ruwan ya daura mata tareda allura kafin ya tafi yace basa buqatan magani da sun samu hutawa sosai sukaci abinci wadatacce zasu warware Inshallah.

    Sai bayan tafiyar likita Maamah ta iya dagowa ta Kalli Abeeda datafi nuna damuwarta akan ciwon nasu sbd Bata taba ganinsu a wannan halinba bayan ciwo ga wahalalliyar yunwa Nan a tareda su bayyane a jikinsu.

    Kan maamah ta dawo da kallanta tareda qurawa Maamah din idanuwanta tana sake kallan qashin wuyanta Da kamar turosa Akai waje duk koina jikinta qasusuwanta a bayyane,
    Jin tayi hankalinta ya ninka tashi tareda shiga tsoro Amma tayi kokarin dannewa tareda boyewa sbd kada ta muzanta Maamah din da kallanta dakuma mamakin.

    Fitowa tayi maamah na biyeda ita kaman yanda ta umarta suka nufi sashenta sai alokacin maamah ta Dan saki numfashi sbd sanyin AC Daya gama kame koina na sashen da Wani irin kamshi na gidan kudi da basai anfada Maka ma.

    A palonta na farko ta zauna ahankali kan kujera tana nunawa Maamah gurin zama tareda sakawa aka kira me aikinta ta kusanta.

    Khaltume na zuwa ta Dan tsaya daga gefen Abeedan cikin girmamawa tace gata tazo.

    Abeeda Dake kokarin dauke kallanta daga Maamah sbd kallan yafara damunta da alama ta Dan juyo ta kalli khaltumen Kai tsaye tace a hadawa Maamah abinci a dining.

    Dawo da kallanta tai kan Maamah din cikin yar kulawa tace

    “Asmau meye kikeson ci??
    Me zaa dafa Miki kici a cikin gaggawa?

    Dan dagowa Maamah tayi tana kokarin Hana damuwa da sanyinta bayyana ta saki Dan numfashi tareda yaqe ta Bude Baki tace

    “Kowanne irin abincin ma yayi basai sun wahala ba”

    Juyawa khaltume tayi da kallanta kan Madame dinsu tana jiran umarnin abinda zaayi din.

    Abeeda Bata juyoba ta kalleta tace

    “Kije koma me Akai a ajiye mata ta taso taci batareda Bata lokaci ba.”

    Murmushin yaqe Maamah ta sauke tana dagowa ta zubawa Abeedan Idanuwanta cikin kulawa da ganin yanda itama Abeedan ta fada sosai tayi Wani irin haske kamar na Wanda beda jini ko kadan.

    Numfashi ta sauke kafin ta Bude Baki cikin kulawa tace

    “Abeeda Yaya muka sameku?
    Yaya Husnah da Haydar?
    Duk suna lafiya?
    Yaya labarin su hajiyar porthcrt?kowa lafiya dai ko?

    Numfashi Abeeda ta sauke kawai fuskar Asmau take kalla wadda magana takeyi Amma bakin dayake bushe da wuyanta ne suke kashe mata jiki Dan haka Bata iya Bude Baki sosaiba ta gyada Kai ahankali cikin sanyi tace

    “Kowa lafiyansa kalau,
    Asmau meya sameku haka keda yaran kuka koma kamar wainda ke rufe a kejin wahala?
    Meyake faruwa ne?
    Kuma cikin qunci da wahala ne?
    Bakwa samun abinci ne?
    Andena Kai Miki abincin da ASH yasa aringa kaiwa duk wata ne?

    Shiru Maamah tayi tareda Dan sake sakin murmushin yaqe tana cewa

    “Ana kaiwa kinsan gidan taro dakuma rayuwar kauye baka samun abu ka ringa cinyewa Kai Daya Se iyalinka,Idan ankai ana bawa kowa ya Dan Saka albarka,Allah dai yaci gaba da biyanki keda Mijinki har karshen rayuwarku,ai Kunata kokari….

    Katseta Abeeda tayi da cewa

    “Asmau bayan yunwa wane masifar kuke ciki haka da kika koma kaman wadda take kwance tana jinya??
    Asmau Kin ganki kuwa?
    Kinga ‘yayanki kuwa?

    Sake sauke numfashi maamah tayi tana Dan son Hana kanta da zuciyarta bayyanarda abinda zai damar da Abeedan Dan haka ta sauya tambayar ta Abeeda da jefa mata tata tambayar idanuwanta akan Abeedan tana cewa

    “Yaya maigida ASH TALBA? Yana lafiya?
    Yakuma akaji da hakurin rashin Alhajin??

    Numfashi itama Abeedan ta saki sbd sanin zurfin ciki da iya shanye damuwa da duk abinda ya wuce na Asmau Dan haka tasan ba komai zata fada mata ba ayanzu din sai kawai tayi Baya ahankali ta gyara zamanta a lallausan Luxury kujeran Dake palon nata tana cewa

    “ASH lafiyansa kalau yau da safen Nan yayi tafiya Dan Daman rasuwar Nan ta tsayar dashi,
    Alhaji kuwa lokacin yayi Se fatan Allah yayi masa Rahama da samun Jin qansa.

    Shiru sukai dukkaninsu kowanne zuciyarsa a sanyaye Banda Abeeda Dake jin bazata iya fadawa Asmaun damuwarta datai niyaba a duk randa suka Hadu sbd Bata taba tinanin ganinta a wannan mummunan halin itada yayantaba kamar wasu gawar dataqi Rami.

    Ita Kuma maamah Jin tayi itama jikinta na sanyi tareda Jin nauyin fadawa Abeedan damuwarta sbd kada ta damu sosai gashi da alama Sam rayuwarta da alama batasan meye ma damuwaba Dan haka bazata lalata mata komaiba da tata damuwar zasuyi kwana biyinsu su koma salin alin zata bar damuwarta a cikinta ta duqufa da yiwa yayanta addua.

    Abincin da akace a jera mata khaltume ta gama jerawa ta matso ta sanar musu angama jerawa.

    Kallan maamah Abeeda tayi tace mata taje taci abinci tukuna.

    Miqewa maamah tayi ta nufi inda abincin yake a Jere cike da table din da tasan zamansa yafi karfinta Dan haka sai kawai ta Kalli khaltume Dake ajiye kulan farfesun qaton catfish akan dining cikin nutsuwa da mutintawa tace bazata iya cin abincin anan ba akaita kitchen ko can dakin da aka saukesu taci.

    Abeeda Dake waya cikin nutsuwa da Wani irin sanyi na Wanda Hutu kawai ya sani batasan me suke fada ba har khaltume din ta fita da Maamah din suka dauki kayan suka fito dasu har zuwa sashen masu aikin.

    A lokacin AmatulMaleek tayi bacci hakama Abdulhameed Amma shi suna shigowa dakin ya Farka Yana ganin maamah din ya tashi zaune Yana kallanta tareda matar Dake bayanta Yana Jin son komawa gida gaba Daya na shigarsa.

    Ajiye kayan sukai a qasa gefen Dan madaidacin gadon Dake dakin tayiwa khaltume data juya zata fice Godia sosai cikin Nutsuwa.

    Bayan ajiye kayan da ficewar khaltume kallan Abdulhameed maamah tayi tana qarasowa gadon dayake kwance shida AmatulMaleek ta miqa hannu ta fara taba AmatulMaleek taji jikinta zafin Kai a sauka sosai ba laifi take ta sauke ajiyan zuciya me sanyi kafin ta Maida kallanta na Abdulhameed Shima ta tabasa taji ba zafi Sam Kwata kwata a nasa jikin Dan haka ta kamosa ya sauko gadon Yana kallan kayan abincin Dake ajiye kasa Yana cewa

    “Maamah yaushe zamu koma gida?”

    Zaunar dashi tafara yi a qasa kafin itama ta zauna tana cewa

    “Kwana biyu zamu insha Allah mu koma,
    Kaci abincin dai tukuna kafin Amatu ta tashi itama taci.”

    Doya da dankalin turawa ne da aka cakudasa da kwai dasu pepper sai kamshin spices yakeyi.

    Wani mugun yawu me kaurin gaske Abdulhameed din ya hadiye harda ita Maamah din Amma dayake sunada dangana sai jikinsu Bai Wani dauki rawa ba.
    A natse ta zuba musu kafin ta sake Bude dayar kulan sukai arba da farfesun kifin Shima ta zuba musu duk a cikin guri Daya sbd kada su Bata plates din dasuke qal tasan Se sunyi tsada,
    abinda ma ita Bata saniba shine ko spoon da matar gidan take amfani dashi baa bari Koda wasa yazo bangaren masu bare kayan abincinta Wanda wainnan din daga yau sun tashi daga kayan cin abincin madame Abeeda sedai Kuma a ajiyesu Dan baqin da basuda wani mahimmanci,
    Shi oga kwata kwata kuwa Sam bama kowa ke taba kayan da ake masa amfani dasu ba sbd Wani irin qyanqyaminsa da tsaftarsa data Baci tayi yawanda idan Yana gari aikinsa na musamman ne da ake taka tsantsan da kiyayewa dashi.

    Abdulhameed duk da Yana cikin kulaficin son komawa gida a take harma da tsoron inda yaga sunzo din Amma sosai ya saki cikinsa ya ringa cin cimar da Bai taba cinta arayuwarsa ba Dan kuwa baitaba ganin ko dankalin turawa da idanuwansa ba bare ci hakama doya har gwara kifi suna Gani a masu siyarwa na kauyensu da masu zuwa ruwa su kamo.

    Dadin dahuwar wadda take ta musamman Dan kuwa duka masu aikin gidan wainda suke da karatu akan aikinsu ake dauka Dan haka masu girkinsu komai nasu kamar a 5star restaurants kake,
    Hakama masu aikin tsafatace gidan Suma kusan sai wainda suka samu training me kyau ake dauka sbd kusan gaba Daya rayuwar taurawan datake cikin ASH TALBA tagama kama iyalinsa da kusan gidan komai a daki daki akeyinsa kan tsari da rashin tarkacen da zai damesa.

    Ita kanta maamah taci abincin sosai ba laifi suka sha Wani homemade drink da ko zaa kulla musu bomb ya watse dasu basusan dame dame acikinsa duk da fruits ne zalla Amma dai Sam basusan meye shi din ba sudai sunci Kuma sun koshi.

    Suna gamawa ta rabe kayan gefe sbd na Amatu da suka rage Mata.

    Toilet dayake dakin suka shiga
    Dayake ta iya amfani duk da irin wainnan abubuwan sbd tasowa gidan masu arziki Dan haka Bata manta yanda ake amfani da wasu abubuwan ba da yawa.
    Wanke musu hannuwansu tayi nata Dana Abdulhameed daketa lashe hannun.

    Sabulun tasaka ta wanke masa hannu da kyau itama ta wanke nata kafin ta goge musu bakinsu suka fito tana ce masa ya koma yayi bacci kafin azahar ta qarasa yi ya sake warwarewa.

    Hayewa yayi gadon Yana cewa

    “To Amma bazaki fita koina ki barmu anan ba ko?

    “Babu inda zani Ina Nan zaune harku tashi Nima Dan rintsawa zanyi kafin lokacin yayi.”

    Yana Jin Hakan ya sauko daga gadon Yana cewa
    “To zan kwanta a gurinki”
    #MAMUH#
    #ASH TALBA
    #LA HOT
    #FRIENDSHIP
    #LIFE
    #AMATULMALEEK
    #NAUFAL TALBA

    *_AMATULMALEEK_*
    By Mamuhgee
    And
    YANCI DA RAYUWA
    By Hafsat Rano
    Na kudi ne
    For more page ku biya
    500 for littafi Daya
    1k for duka books din biyu
    at👇
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

  • Amatulmaleek 7

    Amatulmaleek 7

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story #

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    7
    Maamah kasa cewa komai tayi sbd batasan mema zata ce din ba idan Akan wannan maganar ne Dan kuwa ko ita bazata taba son ayiwa AmatulMaleek auren wuri na kauye ba Amma Babu yanda zatayi idan su kawu suka Yanke mata Hakan.

    AmatulMaleek kuwa da Abdul dasuke gurin Basu Wani Maida hankali ga abinda su maaman ke magana akaiba Dan kallo sukeyi,

    Ganin Hakan Abeeda takira khaltume ta tafi dasu palon Husnah da Haydar suyi kallon acan.

    Bayan antafi dasu AmatulMaleek din zuwa can Abeeda kallan Asmau tayi a natse tana son jin da gaske idan auren kauye din zaawa AmatulMaleek.

    Shiru Maamah tayi sbd batasan me zata fada ba Dan kuwa kota Bude Baki ta fada ko kada ta fada Abeeda tasan batada ta cewa akan Hakan,

    San numfashi kawai ta sake tana cewa

    “Tinda Bata karatu Kam ai auren dole ne da wuri Koda bamuso Hakan ba”

    Cikin mamaki da Dan takaici Abeeda tace

    “Ke Zaki yarda kenan ayi mata Hakan?
    Kuma Asmau me zaisa ki bari ‘yarki taqi karatun Boko?
    Yanada mahimmanci fa kema kinsan Hakan.

    Fada Abeeda ta hau yi sosai Wanda ya Saka maamah yin shiru kanta a qasa batareda tasan me zata ce ba Dan kuwa fada ne Abeedan keyi kamar tanayi da ‘qanwarta ko ‘yar aikinta.

    Abeeda ji tayi duk haushin Asmau ya rufeta Dan haka ma ko firar kirki basuyiba saita damuwa da takaici.

    Su Amatu kuwa suna can zaune palon su Husnah duk da Husnah din Bata Nan tana can tareda mum Aisha tin da Akai rasuwar Basu dawoba tkuna Haydar ne kawai anan.

    Kallo sukasha sosai hankali kwance sai kusan magrib maamah ta jasu suka koma inda suke wato bangaren masu aiki.

    Kwana sukai Abdul na firar abinda suka ringa kalla a TV ita Kuma Maamah cikin damuwa ta kwana sbd Abeeda datai mata fada da maganganu dasuka Saka zuciyarta rauni akan rayuwar datake ciki da ‘yayanta.

    Amatu kuwa data fahimci damuwa a tareda mahaifiyarta itama sanyi jikinta yayi Dan haka dukansu a sanyaye suka kwana.

    Koda gari ya waye maamah data Dan fara sabawa da fitowa Taya masu aiki ayyukansu,fitowa tayi ta nufi dakin khaltume ta kwankwasa mata ta tambayeta idan akwai aikin da zaa Taya dashi.

    Ba musu khaltume ta nufi kitchen da ita ta tayasu da aikin fere dankali da doya harma da wasu ayyukan Dan kuwa maamah din tanada nutsuwan aiki da tsaftan Daya sakasu Dan bari tana Saka hannu a aikin.

    Dayake kowa ya samu Rana shanya garinsa yakeyi sai gashi cikin kwanaki kalilan masu aikin gidan Kokuma ace khaltume datake babba a cikin ma’aikatan gidan sun mayarda Maamah din kamar me aikinsu Suma kusan duk wasu ayyukan kitchen din Banda girki itace take yi musu,

    Ita Kuma Bata taba Jin gazawa ba ko jin an Renata ko wulaqanci ne sbd dadi ma takeji ganin tana yiwa Abeeda da Ash hidima a gidansu da karfinta tinda batada abin biyansu da tarin alkhairansu gurinta Dan haka da zuciya Daya take aikinta.

    Abeeda batasan tana aikinba sbd sam Bata zama sosai yanzu da asmaun iyakacinsu suzo su gaidata ta danyi fira sama sama da asmaun su koma.

    AmatulMaleek ma data ga dai aikin na gaske ne itama sai tana biyo maamah din kitchen tana kama wasu ayyukan Dan kuwa zuciyarta Bata nutsuwa ganin mahaifiyarta na wahala duk da aikin gidan Sam bama zasu kirasa da aikin wahala ba tinda komai a tsare akeyinsa yanda yake a tsare.

    Sunanan Babu cikakken sanin matsayin zamansu Wanda ake nufin jiran dawowar Me gidan sukeyi da mum Aisha maamah tayi musu gaisuwar rasuwar data sakota zuwa Amma ba alamar zasu dawo kusa hakama ita kanta Abeeda tafiya kamata tayi zuwa porthcrt ta kwana biyu Dan haka tana tafiya suka sake zama Wani iri a gidan.

    Abdul dai tini ya koma Dan masu aikin gidan sbd maamah aka barwa Haydar Dan haka akace su koma can cikin gida suna kwana sbd Haydar din kafin maamah ta dawo duk da akwai masu aikin Dake kulawa da cikin gidan dama Haydar din Wanda kusan shekarunsa Daya da Abdul.

    ****Acikin kwana biyu da tafiyar Abeeda Haydar yaji dadin zama acikinsu maamah da Abdul da AmatulMaleek sbd su Kam tsananin son junansu da kulawa da juna sukeyi tareda wasa,
    Duk da Amatu ta girmi Abdul sosai Hakan Bai hanata zaka qawarsa ba abokiyar wasansa Kuma abokiyar fadansa ba hakama itama Maamah sosai take sakewa da yayanta tana San biye musu wasu lokutan musamman idan ba kowa sbd idan akwai mutane tana bayyanarda kunyarta ta haihuwar fari ga AmatulMaleek sosai sosai shiyasa a duk lokacinda Abeeda tace mata “yarki AmatulMaleek” Jin Kalmar takeyi ta mata Wani irin nauyi.

    Tsakanin Abdul da Haydar harma da Amatu cikin kwana biyu sunyi wasa da ‘yar sabuwa Dan haka Koda Abeeda ta dawo tayi mamakin yanda Haydar yake wasa sbd sam Baya wasa Baya Wani fara’a kamar ‘dan dayake cikin qunci,
    Husnah ko tana Nan Sam Bata Wani sake masa sbd son girma da ganin batada lokacin wasan banza dashi ita datake zama ‘yan mata,
    hakama masu aikin gidan Babu me Dan wasa dashi kulawa kawai suke basa Dan haka Sam shi rayuwarsa ta yarinta Bai ganewa komai na Jin dadi da sakewan qananun Yara ba,
    Idan ya Dan samu wannan sakewan to Brother Naufal dinsa Yadawo hutun daga school Yana Nan Dan haka shi wata sabuwar rayuwar ya Gani a tattareda su Amatu da maamah.

    Abeeda bataji komaiba saima dadi dataji Haydar din ya sake Yana wasa sosai Dan haka saisu Amatu da Abdul suka samu sake da Daman zuwa sashen aduk lokacinda sukaso ganin Abdul din haka Shima da Bai taba sanin tayaya ma ake zuwa sashen masu aikin gidanba sai gashi yana zuwa a duk lokacinda yaso.

    Dawowar Abeeda ma ta fahimci maamah na aiki cikin masu aikin gidan ko datai mata magana maamah ta nuna mata ta gaji da zaman banzan ne shiyasa take taimaka musu.

    Abeeda Bata hanata ba duk da dai tasan Hakan Bai kamataba sosai Amma tinda asmaun naso saita barta kawai.

    Kullum da daddare suke zaunawa a palon na Asmau su tattauna maganganunsu da yar firarsu ta Aminai kafin Asmau ta dawo ta kwanta.

    Ita kanta Abeeda a yanzu datake samun Wanda kullum take fira dashi sai take Jin dadin rayuwar tata da kullum Hutu ne da Bada umarnin sai wayoyi Dan aiki ma ta Dena zuwa kwata kwata.

    *****Satinsu biyar harda kwanaki da zuwa Amma har lokacin ASH TALBA Bai dawo ba gashi Yara sunyi sabo sosai da Haydar Wanda a yanzu ko abinci yafison yaci gurinsu Abdul ko Amatu wadda yakejin yafisonta antinsa akan Husnah dasuke uwa Daya,
    Hakama maamah Jin yakeyi yafison zama a gurinta sbd yanda ko abinci sukaci itace take wanke musu hannuwa da Baki hakama yanda Abdul tasaba duk da ya Dan girma itace take masa komai Dan haka Shima a yanzu din itace take masa komai tini ya Dena son wankan masu aiki Sena maamah hakama Amatu itace ke masa Shirin zuwa school yafison nata.

    Duk wannan hidimar maamah bata Dena zuwa kama ayyukan gidanba Dan kada suyi zaman banza Dan haka a sane khaltume ta sallami masu aiki biyu daga cikinsu tabar biyi masu shara da tsafatace gidan kawai aikin kitchen kuwa daga me aikin girka abinci sai maamah Dake sauran duka ayyukan batareda Jin gajiyawaba ko damuwar komai.

    Shakuwar Amatu da Haydar yasa Abeeda Jin batason su tafi sbd ‘danta ya samu sakewan da suketa son yayi ya more yarintarsa Dan haka ta ringa Jin batason tafiyar tasu ko dan Haydar.

    Abdul kuwa yasamu abubuwa na karuwa sosai daga Haydar,
    Kamarsu sutura masu kyau da takarma dasu kayan wasa haka masu girma da tsada Dan haka shima tini yaji bayason su koma musamman idan suna garden na gidan suna wasa dasu keke da lilonsu Haydar din su basuma San akwai irin wannan duniyarba a gidan Saida suka hade da Haydar.

    Abeeda ba mace ce me yawan son fira ba shiyasa sai dare suke Dan zaunawa su zanta da Asmau wadda zuwa lokacin Asmau tafara Jin kanta a tsarge idan tana tareda Abeeda sbd matsayin ba Daya ba hakama ita datake cikin Yan aikinta Jin take kamar yanzu Abeeda tafi karfinta duk da so da kaunar junansu a jininsu yake Kuma Abeedan Bata taba nuna mata tafi karfin nata ba Dan kuwa bayan Maamah din Babu me zuwa ya zauna kujera Daya da ita suyi magana irin wadda Bata taba iyayi da kowa a duniya harma ASH TALBA Wanda yake mijinta da Bata hada komai da kowa dashi ba a zuciyarta da rayuwarta.

    Lokacinda suka cika sati Shida cif a gidan su mum Aisha suka dawo tareda Husnah wadda take matiqar ji da ita sbd yanda Ash Shima yake matiqar ji da Husnah din kasancewarta suna mata kallan ‘dan uwansu da suka Rasa.

    Daga isowarsu tun a harabar gidan mum Aisha ta hango garden din gidan da Haydar ke wasa tareda Abdul suna Jan gashin AmatulMaleek Da Maamah tagama kunce mata da wankewa tareda daure mata kafin da daddare ta mata kitsonsa Dan ta Saba itace ke Mata kitso tin tana yarinya Tin Bata iyaba kuma haryanxu bawai ta iya kitson bane sosai Amma de itace take mata ahakan.

    Jan gashin sukeyi suna guduwa tana binsu fuskarta a Dan sake sbd ko taso tayi fushin dasu kasawa takeyi Dan batada zafin Rai ko zuciya ko kadan.

    Abdul Daya Saba tsokanarta shike fadawa Haydar inda zasu ja gashin su gudu ai bazata iya kamasu ba.
    Haydar ma da wasan ke masa dadi sake kamawa yakeyi Yana Dan ja ahankali.

    Haydar din tafara kamawa tana cewa

    “Wa na kama??
    Zaku sake??

    Hannunsa take kokarin dagawa sama ta kama kunnensa yafara dariya sosai me hade da ihun Kiran sunan Abdul Wanda yazo da sauri yaja janyesa suna dariya itama Amatun dariya takeyi duk da taso maganinsu.

    Dakatawa mum Aisha tayi cikin Isa da Wani irin iKon Daya gama zama jikinta ta kallesu da kyau Taga Haydar ne ke wannan ihun da dariyar,abinda Bai tabayi ba,Babu Wanda a gidan ze ce ya taba ganinsa a cikin wannan Nishadin.

    Husnah data fito motar a hankali itama riqe da qatuwar Apple iPad dinta sanyeda doguwar English straight gown black kallan gurin tayi fuskarta da Dan mamaki Kai tsaye tacewa khaltume

    “Su waye wannan din??

    Cikin girmamawa khaltume ta Dan dubi mum Aisha da ba ita tayi tambayarba tace

    “Yar uwar Madame abeeda ce wadda take magana tazo tareda ‘yayanta biyu yau sati Shida da zuwan nasu.”

    Mum Aisha da take ta fahimci Asmau ce tazo Bata tsaya sake Bata lokacinta a tsayuwarba ta wuce a natse qamshinta na cike iskar gurin, Husnah ma bayanta ta bi tana wucewa sashen mahaifiyarta Kai tsaye khaltume na bayanta da set din akwatinta biyu na lv suka shige
    Ita Kuma mum Aisha saratu me aikinta ce ta ja nata kayan ta bita duk suka shige.
    #MAMUH#
    #MEERAH HERBS
    FOR MORE PAGES FOLLOW ME @mamuhgee arewabooks

    AMATULMALEEK_*
    By Mamuhgee
    And
    *_YANCI DA RAYUWA_*
    By Hafsat Rano
    Na kudi ne
    For more page ku biya
    500 for littafi Daya
    1k for duka books din biyu
    at👇
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 27

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 27

    Episode 2️⃣7️⃣*

     

    ……Ammi, Ammi ina kike yaya Ahmad ya mutu, a sukwane Yusuf ya miƙe yana faɗin “kai haidar ka dawo cikin hankalin ka, wani Ahmad ɗin? “wlh yaya Yusuf ina chikin hankalina yanzun nan muna zaune dashi a fada kawai ya fara tari, jini na fito kafin kache me ya faɗi, ai tun haidar bai kai karshen maganar ba Khalid ya saki hannu Zahra ya juya har suna karo da Yusuf wajen fita da gudu, Haidar kuwa ya nufi betroom ɗin Ammi, mikewa diyana hiyana zahra lamrat amrat sukayi suka bi bayan su Yusuf, tare Ammi da haidar suka fito suma suka nufi fada

    Koda su Ammi suka isa fada gaba ɗaya family sun haɗu awajen suna tsaye chirko chirko da kaga fiskokin su kaga alamun tashin hankali musamman Khalid da Aiman na su tashin hankali banne,

    BGS daune a tsakiyar fada ya ɗora kan yaya Ahmad kan chinyar sa yana zura hannun sa chikin rigan Ahmad, Abba Aryan Fahad Umar suna tsaye a kansu, Aiman da Khalid kam sun ma kasa kariso wa wajen saboda tashin hankali daga baya suka tsaya

    , shiru gaba ɗaya su kayi suna sun zubawa BGS ido suna sauraron suji me zai che

    .. Almost 5mnt san nan BGS ya ɗago green eyes nashi da suka sauya launi izuwa jaa sosai chikin wata iriyar voice mai kama da mara lfy ya furta “bai mutu ba suma yayi,ku bani ruwa mai sanyi sosai gaba ɗaya fada ta ɗauƙa da alhamdulliah san nan Khalid ya juya da sauri ya nufi katuwar freij dake cikin fadan ya ɗauko ruwa mai sanyi ya dawo ya miƙawa BGS, tsabar tashin hankali har ya manta ma ana buɗe robar ruwa..

    …Ansan ruwan Aryan yayi da sauri ya buɗe bakin roban san nan ya mikawa BGS, hannu BGS ya mika wa Aryan alamun ya zuba masa ruwan, zaba masa kaɗan Aryan yayi a hannun nashi, a hankali BGS ya shafawa Ahmad ruwa a fuska

    wani atishawa mai karfi gaske Ahmad yayi, ya fara tari da karfi karfi kamar makogoran sa zai fashe yana kokarin miƙewa, da sauri BGS ya rikosa yana faɗin “kubani ruwan, a hanzar che Aryan ya miƙa masa roban gaba ɗaya, ansa yayi ya ka fawa Ahmad a baki amma ina Ahmad yaki sha sai kokarin mikewa yake, gaba ɗaya ya sauya lokachi guda ya rame ya fita hayyachi sa,

    Da karfi Ahmad ya fisge jikin sa daga na BGS zai mikewa, a’sukwane BGS ya tamke sa ya mai dashi ya zaunar gaba ɗaya fada hankalin su ya tashi ganin halin da Ahmad ke chiki

    faɗa ne ya kaure tsakani BGS da Ahmad dan Ahmad ya dage sai ya tashi, shi kuma BGS ya hana shi,da BGS ya ga dai Ahmad ba zai sarrafu ta lalama ba sai ya mike, yasa karfi ya danne Ahmad a kasa ya haɗa hannayen sa dukka biyi ya taka da kafa ɗaya ya damki gashin kan sa ya ɗago da fiskar’sa ya kafa masa robar ruwan mai sanyi a baki, dan ruwan zata tai maka masa sabo da tarin da yake,

    ba shiri Ahmad ya fara haɗiye ruwan, dan dole, kawar da kai Ammi da Ummi su kayi daga kallon Ahmad suna kwalla, da gudu Aunty mardiya ta juya ta bar fada tana kuka, bazata iya kallon halin da Ahmad ke chiki ba, kuka Aunty salma keyi sosai rungumeta Aunty farida tayi tana ɗan bubbuga bayan ta alamar rarrashi,ita ma dai Aunty farida hawaye take, shi kansa Khalid daure wa yake amma ji yake kamar zai yi kuka, sosai hiyana ke kuka kamar ranta zai fita daman ita sarkin tausayine, haidar Umar duk kwalla suke, Fahad ma idon sa ya chika tab da kwalla amma basu zubo ba, Abba kuwa idon sa ta sauya tayi jaa sosai, ga tashin hankali nan karara a bayyane a kan fuskar sa, Aiman kam ba’a magana dan yafi kowa shiga damuwa saboda tare suke komai da Ahmad ko Aryan da suke yan biyu bai shaku dashi kamar yadda ya shaku da Ahmad ba

    Ganin yadda BGS ya taka hannun Ahmad yayi yawane dan har hannun nashi sun chanza izuwa jaa sun fara kunbura abunku da farar fata, yasa Aryan ɗukawa kasa yasa hannun’sa ya dan bubbuga kafar BGS alamar ya sassauta takun da yawa hannun, chire kafar sa yayi gaba ɗaya tare da chire roban ruwan daga bakin Ahmad din, ya zuba masa ido,

    shiru Ahmad ya kwanta a kasan kamar mai tunani,wani abu hannu Aryan yasa ya ɗan tattaɓa kuma tunsa yana kiran su nan sa, shiru Ahmad bai amsaba kuma idon sa a buɗe ya na kallon su, ganin hakan yasa BGS mikewa tsaye sosai ya ɗauki Ahmad ɗin ya saɓashi a kafadar sa ya fiche dashi, daga fadan gaba ɗaya family suka bi bayan su

    Kai tsaye ɗakin da suke jin yar duk wan da bai da lfy a gidan ne, dan in dai ba sun koma London ba, to ba wan da ake kai wa asibiti su suke duba kowa na gidan, dan babu abun da babu na jinyar ma jinyata a ɗakin

    akan katafaren gadon da aka tanada dan marasa lfy BGS ya kwantar da Ahmad, har lokachin idon sa biyu yana bin su da kallo amma ya kasa magana, kayan aiki BGS ya ɗauko ya fara duba shi,

    almost 30mnt BGS na kan Ahmad yana ɗuba shi,

    Slowly ya juyo ya kalli su Abba da su kayi chirko chirko suna jiran suji meke damun Ahmad “Abba ni fa banga wani abun da yake damun Ahmad ba, nayi iya bin chike na banga komai ba . Amma Aiman Aryan kuma kuzo ku gwada mugani, ya karisa maganar yana kallon Aiman da Aryan dake tsaye waje guda, da kyar Aiman ya iya buɗe baki yace “bazan iya ba bazan iya ganin Ahmad chikin chiwo ba shiyasa na kasa karisawa inda yake, gaba ɗaya mutanen ɗakin sun tausaya wa Aiman dan kowa yasan duk inda kaga Aiman to fa Ahmad na wajen tare suke komai .

    a hankali Aryan ya tako izuwa wajen gadon Ahmad, ya karbi na urorin dake hannun BGS ya fara nashi gwaje gwajen, shima almost 30mnt ya ɗauka san nan ya juyo a hankali yana kallon su Abba har bai san haɗa ido dasu “Aryan ka gano wani abu ne Abba ya tambaya a ruɗe, girgiza kai kawai Aryan yayi alamar a’a, dan ya kasa magana, jin hakan yasa Aiman juyawa da sauri ya bar ɗakin

    shiru gaba ɗayansu su kayi kowa da abun da yake tunani almost 1h, san nan BGS ya juya ya ɗauki alluran barchi ya yiwa Ahmad, yana zare alluran ya ajiye ya fita dakin da sauri dan ji yake kamar zuchiyar sa zata fashe, dan yana matikar kaunar yan uwansa mu samman Aryan Aunty farida Khalid Aiman Ahmad Yusuf Son da yake musu na da ban ne “Abba muje mu kyalesa alluran barchi aka masa mu barshi ya huta chewar Aryan yana gama faɗin hakan ya nufi waje shima, gaba dayan su suka bi bayan Aryan su ma

    YOLA

    Dawani matsanan chin ihu buba ya farka daga doguwar sumar daya faɗa, har sai da ya tsorata su inna dake zaune awajen kowa ya miƙe zai gudu, ban da yaya bello dake zaune ko motsi bai yiba, zubur buba ya miƙe yana ko karin fita waje, da sauri malam yace “ku riƙe sa

    a guje inna habiba da innar bubu su kayi waje saboda tsoro, yaya bello ne yayi ta maza ya riko buba sai kokarin fiskage buba keyi, malam daya ga abun tayi yawa sai ya che da yaya Bello “a ɗaure sa da igiya domin kuwa tun lokachin da kuka kawo sa na fahimchi ya bugu a kai sosai kuma hakan ya taɓa masa ƙwaƙwalwa gaskiya, yanzu dai sai dai a barshi a ɗaure ana masa magani idan da rabon samun sauki to Allah ya sauwaka, idan ku kache zaku sa kesa to ina tabbatar muku bola bola zai fara bi, wasu hawayen masu zafi na tausayin ɗan uwan sa yaya Bello ke yi, haka nan ya nufi wajen da malam ke ɗaure mahaukata ya sa karfi ya danne buba ya ɗaure sa, a zuchiyarsa yana tunanin “duk abun da ya faru da kai buba kai kaja ma kan ka, da kan ka, ka kun tatawa marayu, bayin Allah basu jiba basu gani ba basu maka komai ba ka takurawa rayuwar su ka addabe su ai daman alhakin su bazai taba barin ku ba,

    Sosai ya ɗaure buba, sai ihu buban ke yi yana surutai, miƙewa malam yayi ya nufo su hannun sa riƙe da kwarya mai ɗauke da magani, “kai bello riƙemin kanshi mu bashi maganin nan zata tai maka masa chewar malam, da kyar suka iya ɗurawa buba maganin san nan yaya bello ya sake sa ya fito daga bukkar, a bakin kofa ya samu inna habiba da innar bubu sai sare ido suke “kai bello ya ake chiki? innar buba ta tambaya tana ɗan leƙa ɗakin, haushi kamar yaya Bello ya shaƙeta ta mutu ya keji wai ɗan da kika haifa a chikin ki, ki ke gudu dan ya kamu da wata laluran ba duk ku kuka ɗorasa a kan gurɓatattiyar hanya ba

    banza yaya Bello yayi dasu bai tanka suba dan haushi, chikin tsiwa inna habiba tace “kai mara kunya, mara albarka ba da kai muke magana ba ne da zaka mana shiru, zaka faɗa mana ya jikin bubane ko sai na kwakkwaɗa maka mar

    rabawa ta gefen su yaya bello yayi ya wuche ba tare da yace da su komai ba, wani dogon salati inna habiba tayi tana faɗin “a lallai bello ka girma to ko zaka yiwa innar bubu rashin kunya ai ni ba zaka min ba ko? tun da ni kanwar uban ne, shi dai yaya bello tafiyar sa yayi yana jin inna na surutai amma ko ajikin sa yanufi hanyar gonarsa chikin zuchiyar sa yana tunanin diyana “ya take shin chiwon nata ya warke ne Allah sarki bayin Allah, ɗayan ban garen zuchiyar sa kuwa tunano masa irin kyan da diyana tayi yake, tayi wani fresh da ita daman diyana ba baya ba wajen son kwalliya wow ga kyanta ya kara fitowa, sosai yake tunanin ta oh ni Bello Allah ka bani diyana a’matsayin mata aure, da sauri kuma ya kawar da tunanin damun diyana a matsayin mata dan yasan yanzu kam tafi karfin sa

    Zama yayi chikin gonar tashi sai tunani yake yama rasa meke masa daɗi

    Kano

    gaba ɗaya family Abba suna zaune a babban palon sa sunyi jugum jugum daka gansu kaga alamar tashin hankali a kan fiskokin su

    “my daughter jirgin ku fa karfe 4:30 zai tashi yanzu kuma 4 tayi ya kamata ki tafi chewar Abba yayi maganar yana kallon Aunty farida “aa Abba ba zan iya tafiya ba sai naga yadda zata kasan che zan jira farka warsa, mugani “aa my daughter ya kamata ki koma tun da akoi waya zamu kira ki idan ya farka koma me ake chiki zaki ji “Abba Allah bazan iya tafiya na bar ɗan uwana a haka ba wlh Abba idan na tafi nasan zuchiya ta zata iya bugawa pls my Abba ka bari dai zuwa gobe, ta karisa maganar kamar zata fashe da kuka “to shike nan my daughter Allah ya kaimu Allah yasa idan ya farka ya dawo dai dai, gaba ɗaya palon suka amsa da amin, shiru palon yayi bakajin komai sai shesshekar kukan hiyana dan ita ta kasa yin shiru, tana da tausayi sosai, bare ma idan ta tuno lokachin da BGS ya haɗe hannun yaya Ahmad ya take a kasa sai ta sake rushe wa da kuka

    ……alama Ammi ta mata da hannu akan tazo da sauri ta miƙe ta nufi Ammi riko hannunta Ammi tayi ta zaunar da ita saman sofar da suke zaune ita da BGS, hiyana da BGS su ka sa Ammi a tsakiya kwantar da hiyana Ammi tayi kan chinyar ta tana ɗan bubbuga bayan ta kasa kasa tafara magana “kiyi shiru hiyana kukan ya isa haka kinji zai samu lfy ki masa addu’a,

    jin Ammi na magana kasa kasa ne yasa BGS ɗan wai gowa ganin yadda Ammi ta kwantar da hiyana a kan kafar tane, yasa shi sauri kawai da kai yana jan tsaki a zuchiyarsa yana faɗin “nikam ban san ya Ammi take san mai da yaran nan ba, yanzu wan nan abun zata wani kwantar da ita a kan kafar ta, gaskiya ni dole ma yaran nan su bar gidan nan ko kuma ni na koma gida na Abj dan bazan iya kallan abun haushi ba “BGS time ɗin farka wan Ahmad yayi fa chewar Aryan

    Gaba ɗayan su, suka mike da sauri suka fito suka nufi ɗakin da Ahmad ke kwanche,

    Koda suka shiga already Ahmad ya farka, idon sa a buɗe dan ya kai 5mnt da farkawa, da sauri BGS da Aryan suka kariso bakin gadon, hannun Ahmad BGS ya rike kasa kasa ya kira su nan shi “Ahmad, shiru bai amsa ba kuma dai idon sa a buɗe, kariso wa wajen gadon Aiman yayi cikin dashewar murya ya fara magana “Ahmad pls wake up ba zan iya juran ganin ka a haka ba, wlh idan baka tashi ba zuchiya ta zata iya bugawa pls my blood, kuka Aiman yake kamar karamin yaro yana Magana, ko motsi Ahmad bai yi ba kuma dai still many manya fararen idon nan nashi a buɗe, jijjiga shi Aiman ya farayi da karfi karfi yana faɗin “Ahmad pls wake up, ko motsi Ahmad bayyi ba ganin Aiman zai iya illata Ahmad yadda yake jijjiga shin nan yasa BGS riƙe hannun sa yana girgiza masa alamar ya dai na jijjiga shin, rungume BGS Aiman yayi chikin kuka yace “why, why, chiwon bata kama Ni ba takama Ahmad pls kuche chiwon ya dawo jiki na ya kyale min dan uwa na,ganin Aiman fa ya fita hayyachin surutai kawai yake hakan yasa.

    ….BGS juyowa ya kalli Aryan,ba tare da yayi magana ba, chikin sauri Aryan ya juya ya ɗauko allura ya haɗa ba tare da Aiman ya Ankara ba Aryan ya tsira masa alluran nan take yayi shiru difff kamar an ɗauke wuta sai kuma ya sake wa BGS dukkan jikin sa alamun yayi barchi, ɗaukan sa BGS yayi chak ya saɓa sa a kafaɗa ya nufi waje da shi

    Hannu Aryan yasa ya ɗago Ahmad daga kwanchiyar da yake ya zaunar dashi ya sa masa fillo a bayan da ya jingina shi da jikin bango yana kallon face nashi, ban da ido ba abun da ke iya motsi a jikin Ahmad, juyawa Khalid yayi ya bar ɗakin dan zuchiyar sa ta gama karaya dab yake da fashewa da kuka

    Aunty salma Aunty farida Aunty Mardiya hiyana sun fi kowa kuka a ɗakin shi kan shi Abba daure wa kawai yake, jiyake kamar yayi kukan shima ko zai samu sassauchi a zuchiyarsa, Ammi da Ummi sai sharan kwalla suke Aunty amarya kam bata wani damu sosai ba, dan ko kwallin hawaye bata yiba, sosai Aunty Maryam ma ta shiga damuwa dan itama har chikin zuchiyar ta tana son yan uwan ta, su hiyana ne dai bata so, Fahad ma daurewa kawai yake amma shima idon sa ta chika tab da kwalla, Haidar Umar sai kwalla suma suƙe dan gaba ɗaya ƴaƴan Abba suna matikar kau nar junan su, shiru Yusuf ya zauna dan shi tsabar tashin hankali ko hawayen ya gagara fita

    “Hauwa’u ki tattara su gaba ɗaya ku tafi kowa ta tafi ban garen ta kuyi shiru kukan ya isa haka, addu’a zaku masa chewar Abba yayi maganar yana kallon Ummi, jiki ba kwari dukka matan suka fita ya rage mazan

    da sallam BGS ya dawo ɗakin kusa da Abba yaje ya zauna suka zubawa Ahmad ido shima dai Ahmad ɗin su yake kallon kamar zai yi magana amma ya kasa, cikin tsawa BGS yace “kai ku mana shiru yayi maganar yana kallon haidar da Umar, nan take suka goge kwallan idon su suka nitsu,

    …..Dawo da kallan sa kan Abba BGS yayi kafin yace “Abba yanzu menen abun yi dogon numfashi Abba yaja kafin yafara magana “ina ganin mu fitar da shi waje kawai mu kai shi Us ko UK ko india tun da suna da kwararrun likitochi “aa Abba dan uwana ya fi karfin yaje wata gasa jinya sai dai ita kasar tazo ta same sa a nan, likitan wani kasa kake son yazo ya du bashi, zanyi waya koma wani irin likitane kake so gobe zai zo, “to ka kira likita daga India dan sunfi kwararrun likitochi chan “ok kawai BGS ya faɗa san nan ya mike ya nufi waje, mikewa Abba ma yayi yana faɗin “Aryan ka kwantar da Ahmad muje ko mu kwalesa ya huta, yana gama faɗin hakan ya nufi waje, juyawa Yusuf da Fahad su kayi suka bi bayan Abba haidar da Umar suka rufa musu baya

    a hankali Aryan ya mai da Ahmad ya kwantar, san nan ya shafa kansa yace “Allah ya baka lfy my bro, abun mamaki gani Aryan yayi Ahmad ya lumshe ido a hankali ya buɗe alamar ya ji daɗin addu’ar da Aryan ya masa

    …. A sukwane Aryan yace “Ahmad daman kana jin mu, lumsha ido Ahmad ya sake yi san nan ya buɗe alamar eh ina jin ku, a ruɗe Aryan ya zauna gefen sa ya riko hannun sa yana faɗin zaka iya buɗe bakin ka juya ido Ahmad yayi alamar a’a, “ok to shike nan bama sai ka buɗe baki ba tun da kana jin duk abun da nake faɗe, idan eh haka ne sai ka lumshe min ido idan kuma ba haka bane ka ɗaga min ido sama kaji,? Lumsha ido Ahmad yayi ya buɗe alamar yaji “akoi in da yake maka chiwo ne a jikin ka? ɗaga ido sama Ahmad yayi alamr aa “zaka chi abin chi? nan ma ɗaga ido sama yayi alamar a’a bazai chiba, wasu zafafan hawaye ne suka fara bin kunchin Aryan, wai yau Ahmad ne ke magana da ido kai duniya abun tsoro, ɗaga ido sama Ahmad yayi alamar Aryan yayi shiru ya dai na kwalla, fika kai Aryan yayi kan goshin Ahmad ya chigaba da kwallar sa, hawayen sa na zuba kan fiskar Ahmad,
    Sai da Aryan yayi kukan sa mai isar sa sannan ya ɗago yana bin Ahmad da kallo,

    …hawaye kwanche a chikin idon Ahmad ɗin ga wasu na bin gefe gefen idon sa alamar dai shima kukan yake, girgiza kai Aryan ya shiga yi yana faɗin “No bro No bai kamata kayi kuka ba kaga baka da lfy lunshe ido Ahmad yayi alamar yaji, hannu Aryan yasa ya goge masa hawayen, san nan ya miƙe ya koma saman sofa daƙe chikin ɗakin ya zauna yana kallan Ahmad, shiru sukayi dukkan su har bar chi ya ɗauki Ahmad, ganin yayi barchi ne yasa Aryan mikewa ya fiche daga ɗakin daman ya zauna ne dan bai san ya bar Ahmad shi kaɗai.

    Misalin karfe 9 na dare zaune Aryan yake a bakin katafaren gadon sa yana latsa waya, sanye yake chikin kayan barchi riga da dogon wando Sky Blue masu kyau da tsada, yayi nisa chikin abun da yake a wayar tasa, yaji wani fitinannen kamshin perfume ta kai mai karo a hanchi kan ya ɗago kai, sai yaji tafiya kwas,kwas,kwas, ai bai ma san san da ya saki wani cool murmushi ba tun bata karisa shigowa ɗaƙin ba,

    ba ko sallama diyana ta shigo hannun ta ɗaya rike da cup mai ɗauke da coffee, ɗayan hannun nata kuma rike da jakar da ya bata amatsayin tsaraba, from head to toe yake kallan ta,

    Sanye take chikin wata dan ƙareriyar lace Blue colour da ratsin fari, ɗinkin riga da sket kayan sun zauna a jikin ta sosai, yau ba ta yi make up sosai ba iya powder ta shafa sai man baki, tayi kyau kamar ita tayi kanta, ga ɗaurin dan ɗaurin ɗan kwali ture kaga tsiya da ta yi, yau kam ta rufe kan nata, gawani high heel fari da tasa a kafar ta sai wani fitinannen kamshin turaren humra dake tashi a jikin ta zubawa, a hankali take takawa tana wani rausaya ta kariso chikin ɗakin

    …..gaban shi tazo ta duka har lokachin bai dai na kallan ta ba, yama kasa ɗauke idon sa daga kanta “ina wuni yaya Aryan, wani dogon numfashi ya ja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya, kasa amsa gaisuwar nata ma yayi, jin bai amsa ba yasa ta ɗago kai a hankali, karaf blue eyes nata ya sauka chikin ash eyes nashi da sauri tayi kasa da kanta,

    “yaya Aryan dan Allah ka ansa mana wlh chinyata na min zafi kayan sun matseni sosai ta karisa maganar kamar zatayi kuka, slowly yasa hannun ya ansa cup ɗin ita kuma ta miƙe, tana faɗin yaya Aryan ga jakar ka buɗe min ta karisa maganar tare da miƙa masa jakar, batare da ya ansa ba yasa ɗayan hannun sa ya mata nuni da kan drawar gefen gadon alamar ta zauna, ba musu ta zauna ta ajiye jakar a kasa a gefenta

    “Bana hanaki kwalliya da daddare ba, yayi maganar yana ɗaure fuska turo dan karamin bakin nan nata tayi a shagwaɓe tace “to ai Aunty farida che tache nayi kwalliya nazo na kawo maka coffee, shiru yayi bai sake magana ba ya ɗago da cup ɗin sai tin ɗan bakin nasa ya fara sha coffee ɗin yana kallan ta, juyo da kallanta itama tayi kan sa, kallo ɗaya ta masa ta ɗauke idon ta kasan chewar yana kallon ta

    “yaya Aryan me yasa kayi kuka kuma meyasa naga ka rame, a’sukwane ya chire cup ɗin daga bakin sa ya kara waro manya manyan ashe eyes nashi yana kallan ta, batare da ta kallesa ba ta chigaba da magana “ko ɗazun fa da yaya Ahmad ya fara rashin lfy kowa a palon yayi kuka har da ni, nima nayi amma kai da wan nan mai kama da hiyana da kuma Abba ba kuyi kuka ba to yanzu kuma…..ba shiri ta ja birki bata karisa maganar ba saka makon hannun da Aryan yasa ya rufe mata baki, ɗago ido tayi tana kallansa zaro mata manya manyan ashe eyes nashi yayi ya ɗaure fuska sosai da kakkausar murya yafara magana

    Waya koya miki kallon maza? zaro blue eyes nata tayi sosai har sai da Aryan ya zame hannun sa daga bakin ta ba shiri, dan ganin idon nata yayi data zarosu waje kamar ta kara musu haske ne har wani kyalli suke, zuba wa kwayar idon ta ash eyes nashi yayi sosai yana kallan su abun ma mamaki ya bashi, ganin haka yasa diyana ta turo ɗan karamin bakin nan nata tafara magana “ni bana kallan maza ni ba maza bama har mata dukka bana kallon su.

    a fusache Aryan ya miƙe, ganin ya miƙe yasa itama ta miƙe da sauri “Ke ni zaki chewa baki kallon maza, baya baya ta fara jaa tana girgiza kai chikin tsoro, binta yafara yi har suka kure bango matse ta yayi sosai da jikin bangon, a tsorache tace “Allah yaya Aryan ni bana kallon kowa ma “baki kallon kowa ya akayi ki kasan gaba ɗaya mutanen dake palo lokachin da Ahmad ya faɗi sunyi kuka? ya akayi ki ka san nayi kuka? Ya akayi ki ka san na rame? “Allah yaya Aryan Saboda kana da mahimmanci ne awaje na shiyasa na sani kuma ai kaga kullun ina kawo maka coffee, kuma ai idan nazo kullun ina kallon ka sau ɗaya, shiru yayi har chikin ranshi ya ji daɗin amsar da ta bashi na chewa yana da mahimmanci awajen ta, “me yasa nake da ma himmanchi awajen ki? yayi maganar yana ƙara matsowa kusa da ita sosai “ai saboda yanzu ka dai na yimin tsawa kuma kana sona baka buguna ka kawo min tsara ba kuma ranar kache nayi kyau, tunani ya shiga yi sosai anya yarinyar nan mutun che kuwa yar karama da ita sai ƙwaƙwalwa yanzu duk waɗan nan abubuwan bata manta da suba ko wama ya faɗa mata ma’anar mahimmanci oho, ganin yayi shiru ne yasa tace “yaya Aryan Allah ni bana kallon kowa pls kayi hakuri kaji, “ok promise me that ba zaki rinƙa kallon kowa ba, da sauri ta ɗago a dai dai goshin ta bakin sa ya sauƙa saboda yayi kusa da ita sosai, wani irin shock yaji daga tsakiyar kansa har izuwa tafin kafar sa da sauri ya ɗan ja da baya, ita kam ko ajikinta bata ma san yayi kissed na goshin ta ba ..

    ….Yaya Aryan Allah nama alkawarin ba zan kalli kowa ba, batare da yayi magana ba ya wuche ya koma bakin katafaren gadon sa ya zauna, san nan yace “dawo ki zauna muyi magan, a hankali ta tako izuwa kan drawer da ta tashi ta zauna “kin san me nake so dake “aa tafaɗa tana girgiza kai “daga yai idan munje chin abinchi a palo kai bama palo ba ko ina ne, kar na sake jin kinyi magana da kowa,sai dai idan an tambaye ki abu, kuma idan an tambaye iya abun da aka tambaya iya shi zaki amsa karki kuskura ki ɗaura wani abu kinji, to kawai tace, ɗaukan coffee nashi da ya ajiye yayi ya chigaba da sha

    “yaya Aryan ayya bani wayar ka na buga game, batare da yayi magana ba ya ɗauki wayar ya chire pin ɗin ya miƙa mata, ansa tayi tafara latse latse “ayya yaya Aryan to ai ni banga game ɗin ba “shiga play store ki ɗauko dan ni kam bani da game, da murna a fiskar ta tace to
    Aryan a tunanin sa diyana batasan kan waya ba shiyasa ma bai damu ba ya miƙa mata wayar

    “Laaaa yaya Aryan daman hoton mun nan yana nan, a sukwane Aryan ya ɗago ya ansa wayar yana kallon screen ɗin “ke ya akayi ki ka ga hoton nan? yayi maganar yana mai do da idon sa kan face nata, shiru ta danyi kafin tace “kawai naga an rubuta KGA ne a jikin App ɗin shine na shiga “to ai akoi pin awajen ya akayi ki kasan pin ɗin?, “nima fa wlh ban sani ba kawai ni dai hannuna ya daddanna wayar ne shine naga ya buɗe, kara waro ido waje yayi a zuchiyar’sa yana tunani yanzu *kam zargin na ya fara tabbata koda diyana mutun che to tabbas tana da aljanu a kai* “yaya Aryan ka bani wayar mana na ɗauko game ɗin, pita chikin App ɗin yayi ya chanza pin ɗin san nan ya mika mata wayar

    Game har uku ta ɗauko daga play store, super killer mario subway, subway ta shiga ta fara bugawa, tani nisa chikin buga game ɗin da take, sai taji an fisge wayar da sauri ta bi hannun sa zata kwache wayar dan ita tama manta a dakin yaya Aryan take ita duk tunanin ta tana ɗaki kuma Zahra che ta fisge wayar, tafiya tayi gaba ɗaya ta faɗa kan faffaɗar kirjinsa, dukkan su suka zube kan gadon, kallon face nata sosai Aryan ke yi ita kuma ta runtse ido tana mai da numfashi

    wani irin bakon yanayi Aryan yaji gaba ɗaya jikin sa ya mutu, har wani sanyi yake ji kamar mai zazzaɓi, da kyar ya iya juyawa da ita a kan kirjinsa, ya mai da ta kan gadon ya mata runfa da faffadar kirjinsa yana kallon face ɗin ta, sosai taƙara runtse ido tana jiran taji saukar mari, chikin wata iriyar kasa lalliyar murya yace “ke me yasa kika faɗomin jiki? Lips nata sai kerma yake tace “wlh yaya Aryan na manta ne na ɗauka Zahra che ta anshe wayar shiyasa na bi hannun… Bai bari ta karisa maganar ba ya rufe mata baki da hannun
    sa sauko da kansa yayi ya haɗe goshin su waje guda han chin su na gogan na juna, yayi shiru yana mai da numfashi.

    …ko motsin kirki ya kasa saboda wata kasala da ta saukan masa lokachi guda almost 10mnt suna kwanche haka sai da yaji diyana na kokarin suma ne ya ɗago kai da sauri yana kallon ta, da kyar take numfashi saboda danneta da yayi wan nan ma iya rabin jikin sa ne kawai a kanta, da kyar ya iya miƙewa ya koma gefe ya jingina da jikin kayin gadon ya ɗaga kai sama ya lumshe ido, ita kam diyana ta kasa mikewa dan har lokachin numfashi ta bai dawo dai dai ba

    Sauko da kai yayi Slowly ya ware idon sa a kanta tana kwnache tana kallan sama chikin da shewar murya yace “tashi ki kawo jakar naki na buɗe miki ki tafi ɗaki dare yayi, da kyar ta iya mikewa itama ta ɗauko jakar ta miƙa masa ansa yayi yana faɗin “to jeki dressing room na kije wajen ajiye agogo zaki ga wani ɗan karamin a kwati awajen na gold ki ɗauko ki kawo min, a hankali ta nufi dressing room ɗin

    After some mnt

    Ta fito rike da wani ɗan karamin a kwati mai kyau sai ɗaukan ido yake tazo ta mika masa, ansa yana faɗin “to zauna yayi maganar yana nuna mata gefen sa a bakin gadon, zama tayi tana kallan yatsun kafar ta, buɗe ɗan karamin akwatin yayi ya chiro wasu key guda biyu, ya ajiye ɗaya a gefensa yasa ɗayan kuma ya buɗe jakar

    “ɗago to ki kalli abun da ke chikin jakar da kika damu abuɗe maki, ya karisa maganar yana kallan face ɗinta, da sauri ta juyo, idon ta na sauka kan jakar ta mike zubur tasa hannu a baki tana faɗin yaya Aryan…..✍️✍️

     

    💖