Amatulmaleek Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Amatulmaleek 6

Sponsored Links

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest #

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

6
A qasa kan tiles Maamah tayi kwanciyarta kan daddumar sallah tareda Abdulhameed Daya shige jikinta tin tana jiran farkowan AmatulMaleek har bacci ya Dan fixgeta itada Abdulhameed din.

So biyu ana Aiko khaltume dubasu ko sun tashi Amma Basu tashi ba Kuma Madame tace kada a tashesu Dan haka aka barsu sukai bacci sosai batareda Maamah din ta san ta dauki lokaci sosai haka tan baccin ba.

Sanyin tiles ya dayayi musu yawa ya farkar da ita dole lokacin karfe biyun Rana harda minti talatin da takwas Dan haka cikin sauri ta tashi tana janye Abdulhameed Daya cukuikuyeta sbd sanyi ta miqe tsaye tana kallan gadon Taga AmatulMaleek din itama tana motsawa alamar tashi zatayi Dan haka toilet kawai ta wuce Tayo alwala ta fito tayi sallah tana idarwa Amatu na farkawa Dan haka itace ta kamata da kanta takaita toilet tabarota.

Ita kanta Amatu ta Dan iya aiki da wasu abubuwan bandakin sbd zuwan da suka taba yi tafara Dan wayo lokacin.
Fitsari tayi Tayo alwala itama ta fito ta tsaya gefen Maamah tayi sallah tana idarwa Abdulhameed na na tashi daga baccin Shima.

Da sauri Maamah ta miqe ta rakasa toilet sbd fitsarin dayake cewa ya matsesa.

Bayan fitsari harda zawo yayi sbd abincin Daya Dan fara tabashi kasancewar ciki Bai Saba da wannan dadin ba,
Fitowa yayi bayan Maamah ta wanko masa hannuwansa da kyau da sabulu
Gefen AmatulMaleek ya zauna Yana kallan kayan abincin Dake gefen ajiye yafada mata nata ne sunci sun rage Mata tin dazu.

Kallansa Amatun tayi bayan ta Kalli kayan abincin Amma Bata motsaba sbd ba Maamah ce ta Bata ba.

Maamah kuwa toilet din tahau wankewa sosai sbd kada su lalata musu guri Dan tasan tsananin karfin tsaftan masu gidan sbd duk Wanda ko kalilan sani yayiwa ASH TALBA yasan inda qazanta take da inda yake akwai Nisa me yawa da zurfi.

Sosai ta Saka karfinta ta wanke toilet din tayi masa fes ta fito tana kallan Amatu Dake zuru tana kallan Abdulhameed Dake ta fada mata dadin abinda suka ci din tana bacci.

Wani sanyayyan murmushi maamah tasaki tana qarasowa fuskarta a sake ta kallesa tana cewa

“Gashi Kuma bazaka sake ci ba yanzu sbd yafara lalata Maka ciki.”

Dariya yayi Yana maqale kafadarsa Yana cewa

“Zan sake ci mana ai idan munkoma bazan sake ci ba shikenan.”

Daga Maamah har Amatu da batada karfin jikinta qaramar dariya suka saki sbd yanda yake matse da a dauko abincin.

Maamah ce ta janyo abincin bayan ta zauna itama a tareda su qasan.

Bude abincin tayi da kanta ta zubawa AmatulMaleek komai kaman yanda suka hade tana cewa

“Ki cinye tas sbd Kinga ba karfi jikinki ta yanda zaku samu kuzari sai muje akaimu ku gaida mommynku Abeeda harma da sauran mutanen gidan.”

Gyada Kai kawai AmatulMaleek tayi tana Saka hannu a abincin sbd itama ya shiga ranta sosai duk da batada kwadayi Amma shi abinci irin wannan basama ganinsa bare.

Abdulhameed ma dole tareda Amatun ya sake cin abincin itama Maamah hannu ta Saka sukaci abincin tare su uku Abdul naci Yana tambayar AmatulMaleek idan tanajin dadin dayake ji a abinda sukeci din.

Dariya Amatun ta Dan ringa yi masa tana cewa

“Maamah wlh ‘dan Nan naki duk ya haukace sbd cin abinda be taba ci ba.”

Itama Maamah din yar dariya tayi tana cewa

“Kyalesa yaci ai na kwana biyu ne muna komawa kaman yanda ya fada shikenan.”

Cikin kulawa da tsananin so da kaunar juna sukaci abincin su uku suna Dan magana Sam sama,Maamah kusan duk Rabin cin abincin nata su take gyarawa kidin tana ja ye musu qashinsa abubuwan data San bazasu iya ci ba tana musu fira cikin kulawa da kaunarsu.

Suna gamawa wannan Karan su ukun suka shiga toilet suka wanko hannuwansu Maamah na fitowa ta tattara gurin tareda kayan ta fito dasu ta nufi hanyar kitchen tana isowa khaltume da Masu aikin abincin Dake girkin dare kallanta sukai tareda karban kayan hannunta.

Kallan khaltume tayi tana cewa Ina zata wanke kayan saita wankesu da kanta.

Karban kayan khaltume tayi tana cewa ta barshi kawai.

Kasa tafiya maamah din tayi sai data taimakawa khaltume gurin wanke kayan kafin ta koma.

Zama sukai a dakin shiru daga ita Se su Amatu suna Dan firarsu sama sama sbd daga Amatun har Abdulhameed sun warware kamar ba’a nade aka shigo dasu ba ba lafiya sosai Daman yunwa ce da wahalar hanya Se iska da sanyin kwanan Tasha.

Har yamma Babu Wanda ya shigo inda suke aka nemesu Suma haka sukai zamansu.

Koda Akai sallan magrib Wani abincin aka sake kawo musu Basu ci ba sai da sukai sallah tukuna suka zauna sukaci a plate Daya su dukansu dayake wannan Karan farar Basmati rice ce da brown chicken stew wadda Babu Mai sosai acikinta sbd lafiyansu da suke kulawa da ita sosai a gidan.

Kazar Dake cikin miyan zata Kai guda harma da Rabi Kila Dan kuwa duk yanda sukaci ta Basu cinyeba hakanan suka tattara kayan Maamah dince ta sake fita dasu takai kitchen ta dawo.

Har Akai ishai baazo antafi dasu can gurin masu gidan ba sbd umarnin da Abeeda ta bayar na a barsu suyi kwana biyu suci su huta yanda ya kamata kafin su fara Dan zagayawa sbd sam Bata kaunar ganinsu a yanda suke din.

Da daddare maamah barwa Abdulhameed da Amatu gadon tayi sbd baida Wani girman da zai daukesu su uku Dan haka tayi kwanciyarta qasa tabarsu a saman sukai bacci.

Bacci sukai sosai Wanda suka jima Basu irinsa ba sbd samun gurin baccin me nutsuwa ba sauro ba komai Dan haka har Akai asuba Basu saniba Saida gari yayi haske Maamah ta Farka tana tashi zaune kafin ta miqe ta nufi toilet Tayo tsarki da alwala tana fitowa kafin ta tada sallah ta tana Amatu tana Kiran sunanta a nutse.

Cikin baccin dabe saki Amatun ba ta Bude idanuwanta masu Dan girma tana cewa

“Maamah baccin be sakeniba”

“Tashi kiyi sallah Se ki koma tinda Babu aikin da zamuyi anan din.”

Sake Dan juyawa tayi tana Bude idanuwanta tareda Kai hannuwanta duka biyu tana ture kafafun Abdul Dake kanta cikin Wani shegen mugun bacci Wanda ko a gida haka suke kafin safe ba qaramin shuri takesha a gurinsa ba sbd Mayen baccinsa.

Saukowa tayi gadon tana murza idanuwanta ta nufi bayin ta shige tana Bude idanuwanta dakyau sbd kada ta zame.

Koda ta fito Maamah tagama sallah tana zaune tana Dan kokarin tada Abdul Shima cikin kulawa da rarrashin ya tashi yayi sallan.

Sallah tayi tana idarwa itama ta zauna gefen maamah din wadda da kanta takai Abdul toilet yayo fitsari da alwala,
Inda ma Allah yayi mata babban rufin asirin dukkaninsu yayan nata Babu me fitsarin kwance da batasan ya zatai ba.

Bayan sun gama sallah Amatu ce ta kwanta qasa Maamah din Kuma da Abdul suka koma kan gadon suka kwanta dukkaninsu baccin ne ya sake daukansu hankali kwance.

Se qarfe Tara aka kawo musu abincin breakfast Wanda Tintini Daman sun tashi har sunyi wanka sbd kada Azo a taddasu da kowacce irin rashin tsafta.

Ayau ma lafiyayyan breakfast suka sake karyawa dashi Wanda kusan iri Daya Dana jiyan ne sedai yau tareda Wani Irin tea me shegen kauri Daya Saka Abdul ringa fadar akwai Madara sosai a cikin shayin.

Haka suka sake wuni guda Babu Wanda yazo ya tafi dasu sedai abincin da aketa kawo musu da lokacin cinsa yayi.

Bata damu da cewa Se sunje gurin Abeeda ba sbd tasan tana sane dasu Kila wata hidimance ta riqeta Batada lokacin ganinsu yanzu.

Abdul kuwa Jin yayi shikam yafara son gidan sbd dadin dasuke ci Kuma basa komai bayan kwanciya da Shan AC Wanda sanyinsa yafara taba Amatu ita Dan Sam Bata son sanyi duk da tana yarinya yanzu ne ze tabata.

****Kwanaki kusan hudu masu kyau aka Basu suka huta yanda ya kamata bayan ci me kyau da sha me kyau Babu abinda suke Samu,
Hatta yar suturar sakawa anbasu dukda ba masu yawa bane Amma sukam a gurinsa me yawan ce,

Abdul sosai a yanzu yaji bayason su koma gida Dan kuwa shi ko wannan ci a koshin da abinci mekyau aka barsa ganin yakeyi duniyarsu ta gyaru Dan haka tini shi Kam ya fara kumatun Kwana biyu,
Amatun ma ta Dan yi kumatun duk da batada jikin kiba ko kadan Amma dai ita cima me kyau da wuri take nunawa,
Maamah kuwa sosai ta dage da kulawa da inda aka ajiyesu din sbd karsu lalata inda aka ajiyesun kafin su tafi hakama duk takai kayan abincinsu kitchen seta Dan taimaka musu da Wani aikin sbd Bata Saba da zama Babu aikin komai ba Jin takeyi duk ba dadi sbd su Basu Saba da Hutu ba da wahala suka Saba.

Ranarda suka cika kwana biyar da zuwa aka Aiko khaltume ta tafi dasu cikin asalin gidan inda masu gidan suke,
Kai tsaye sashen Abeeda aka nufa dasu khaltume na gaba suna biye da ita.

Abdul na hannunsa na riqe cikin na maamah sbd kada yanda yake kalle kalle,
Amatu kuwa tana gefen maamah din itama tana Dan kallan koina.

Babban palon Abeeda ko yau aka nufo dasu suka zauna ‘yayanta na gefenta matse da ita suna Dan kallan makekiyar flat screen tv din Dake aiki a palon ba murya sosai.

Abdul sai taba Amatu yakeyi Yana nuna mata abubuwan da duk idanuwansa suka Gani na mamaki ita Kuma tana gyada masa Kai sbd batasan me zata ce masa ba.

Basu Wani jimaba Abeedan ta fito fuskarta dauke da murmushi me yalwa da kulawa tareda kauna a Fili tana kallansu ta qaraso sanye cikin Wani milk dry lace Daya gama bayyanar da kudinsa sbd yanda take a kwance kamar cotton.

Zaunawa tayi idanuwanta dasuka fada suna kan AmatulMaleek wadda gabaki daya Babu abinda ta baro na mahaifiyarta Asmaun sai haske data Fi Asmau Amma komai na maamah dinne.

Manyan idanuwanta farare ta kalla tana mamakin Irin kamannin Asamun da Amatu ta koma sak,
Numfashi ta sauke ahankali tareda sake fadada murmushinta da kulawanta tana miqa hannunta ta Kila Abdul Wanda yake kallanta Amma ya kasa zuwa sai maamah Daya kalla wadda cikin murmurshi ta gyada masa Kai tana cewa

“Jeka ka gaida mommyn UK da kaji Amatu na fada”

Amatu kuwa cikin nutsuwa da girmamawa itama ta Bude Baki ta gaidata cikin Dan sakewan fuska da ganin mommyn.

Amsawa tayi itama tana Jin kaunar yaran tace

“Asmau AmatulMaleek ta fara zama budurwa Ashe,
Allah yasa dai kada iyayen Nan nasu Maza suyi tinanin yimawa auren kauye da wuri sbd bazamu yarda ba Sam da wannan dabiar ta kauye”

Dariya mara sauti maamah tayi tana cewa

“Toh ai sedai ace Allah ya tsare Amma Kam Kila Hakan zaa samu”

Dan kame fuska Abeeda tayi tana sake qarewa Amatun kallo Tana cewa

“Sam wannan bazai yiyuba sbd zasu kashe rayuwarta ne,Ina Sam Sam,wannan ai rashin hankali ne da cutatar da rayuwar Yara qanana sbd wasu shekarun nasu da gaske Basu kaiba.”
#MAMUH#
#AMATULMALEEK
#ASH
#ROMANCE
#NAUFAL
#FAMILY
#WEALTH
#LA HOT

*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Leave a Reply

Back to top button