Amatulmaleek Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Amatulmaleek 7

Sponsored Links

Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story #

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

7
Maamah kasa cewa komai tayi sbd batasan mema zata ce din ba idan Akan wannan maganar ne Dan kuwa ko ita bazata taba son ayiwa AmatulMaleek auren wuri na kauye ba Amma Babu yanda zatayi idan su kawu suka Yanke mata Hakan.

AmatulMaleek kuwa da Abdul dasuke gurin Basu Wani Maida hankali ga abinda su maaman ke magana akaiba Dan kallo sukeyi,

Ganin Hakan Abeeda takira khaltume ta tafi dasu palon Husnah da Haydar suyi kallon acan.

Bayan antafi dasu AmatulMaleek din zuwa can Abeeda kallan Asmau tayi a natse tana son jin da gaske idan auren kauye din zaawa AmatulMaleek.

Shiru Maamah tayi sbd batasan me zata fada ba Dan kuwa kota Bude Baki ta fada ko kada ta fada Abeeda tasan batada ta cewa akan Hakan,

San numfashi kawai ta sake tana cewa

“Tinda Bata karatu Kam ai auren dole ne da wuri Koda bamuso Hakan ba”

Cikin mamaki da Dan takaici Abeeda tace

“Ke Zaki yarda kenan ayi mata Hakan?
Kuma Asmau me zaisa ki bari ‘yarki taqi karatun Boko?
Yanada mahimmanci fa kema kinsan Hakan.

Fada Abeeda ta hau yi sosai Wanda ya Saka maamah yin shiru kanta a qasa batareda tasan me zata ce ba Dan kuwa fada ne Abeedan keyi kamar tanayi da ‘qanwarta ko ‘yar aikinta.

Abeeda ji tayi duk haushin Asmau ya rufeta Dan haka ma ko firar kirki basuyiba saita damuwa da takaici.

Su Amatu kuwa suna can zaune palon su Husnah duk da Husnah din Bata Nan tana can tareda mum Aisha tin da Akai rasuwar Basu dawoba tkuna Haydar ne kawai anan.

Kallo sukasha sosai hankali kwance sai kusan magrib maamah ta jasu suka koma inda suke wato bangaren masu aiki.

Kwana sukai Abdul na firar abinda suka ringa kalla a TV ita Kuma Maamah cikin damuwa ta kwana sbd Abeeda datai mata fada da maganganu dasuka Saka zuciyarta rauni akan rayuwar datake ciki da ‘yayanta.

Amatu kuwa data fahimci damuwa a tareda mahaifiyarta itama sanyi jikinta yayi Dan haka dukansu a sanyaye suka kwana.

Koda gari ya waye maamah data Dan fara sabawa da fitowa Taya masu aiki ayyukansu,fitowa tayi ta nufi dakin khaltume ta kwankwasa mata ta tambayeta idan akwai aikin da zaa Taya dashi.

Ba musu khaltume ta nufi kitchen da ita ta tayasu da aikin fere dankali da doya harma da wasu ayyukan Dan kuwa maamah din tanada nutsuwan aiki da tsaftan Daya sakasu Dan bari tana Saka hannu a aikin.

Dayake kowa ya samu Rana shanya garinsa yakeyi sai gashi cikin kwanaki kalilan masu aikin gidan Kokuma ace khaltume datake babba a cikin ma’aikatan gidan sun mayarda Maamah din kamar me aikinsu Suma kusan duk wasu ayyukan kitchen din Banda girki itace take yi musu,

Ita Kuma Bata taba Jin gazawa ba ko jin an Renata ko wulaqanci ne sbd dadi ma takeji ganin tana yiwa Abeeda da Ash hidima a gidansu da karfinta tinda batada abin biyansu da tarin alkhairansu gurinta Dan haka da zuciya Daya take aikinta.

Abeeda batasan tana aikinba sbd sam Bata zama sosai yanzu da asmaun iyakacinsu suzo su gaidata ta danyi fira sama sama da asmaun su koma.

AmatulMaleek ma data ga dai aikin na gaske ne itama sai tana biyo maamah din kitchen tana kama wasu ayyukan Dan kuwa zuciyarta Bata nutsuwa ganin mahaifiyarta na wahala duk da aikin gidan Sam bama zasu kirasa da aikin wahala ba tinda komai a tsare akeyinsa yanda yake a tsare.

Sunanan Babu cikakken sanin matsayin zamansu Wanda ake nufin jiran dawowar Me gidan sukeyi da mum Aisha maamah tayi musu gaisuwar rasuwar data sakota zuwa Amma ba alamar zasu dawo kusa hakama ita kanta Abeeda tafiya kamata tayi zuwa porthcrt ta kwana biyu Dan haka tana tafiya suka sake zama Wani iri a gidan.

Abdul dai tini ya koma Dan masu aikin gidan sbd maamah aka barwa Haydar Dan haka akace su koma can cikin gida suna kwana sbd Haydar din kafin maamah ta dawo duk da akwai masu aikin Dake kulawa da cikin gidan dama Haydar din Wanda kusan shekarunsa Daya da Abdul.

****Acikin kwana biyu da tafiyar Abeeda Haydar yaji dadin zama acikinsu maamah da Abdul da AmatulMaleek sbd su Kam tsananin son junansu da kulawa da juna sukeyi tareda wasa,
Duk da Amatu ta girmi Abdul sosai Hakan Bai hanata zaka qawarsa ba abokiyar wasansa Kuma abokiyar fadansa ba hakama itama Maamah sosai take sakewa da yayanta tana San biye musu wasu lokutan musamman idan ba kowa sbd idan akwai mutane tana bayyanarda kunyarta ta haihuwar fari ga AmatulMaleek sosai sosai shiyasa a duk lokacinda Abeeda tace mata “yarki AmatulMaleek” Jin Kalmar takeyi ta mata Wani irin nauyi.

Tsakanin Abdul da Haydar harma da Amatu cikin kwana biyu sunyi wasa da ‘yar sabuwa Dan haka Koda Abeeda ta dawo tayi mamakin yanda Haydar yake wasa sbd sam Baya wasa Baya Wani fara’a kamar ‘dan dayake cikin qunci,
Husnah ko tana Nan Sam Bata Wani sake masa sbd son girma da ganin batada lokacin wasan banza dashi ita datake zama ‘yan mata,
hakama masu aikin gidan Babu me Dan wasa dashi kulawa kawai suke basa Dan haka Sam shi rayuwarsa ta yarinta Bai ganewa komai na Jin dadi da sakewan qananun Yara ba,
Idan ya Dan samu wannan sakewan to Brother Naufal dinsa Yadawo hutun daga school Yana Nan Dan haka shi wata sabuwar rayuwar ya Gani a tattareda su Amatu da maamah.

Abeeda bataji komaiba saima dadi dataji Haydar din ya sake Yana wasa sosai Dan haka saisu Amatu da Abdul suka samu sake da Daman zuwa sashen aduk lokacinda sukaso ganin Abdul din haka Shima da Bai taba sanin tayaya ma ake zuwa sashen masu aikin gidanba sai gashi yana zuwa a duk lokacinda yaso.

Dawowar Abeeda ma ta fahimci maamah na aiki cikin masu aikin gidan ko datai mata magana maamah ta nuna mata ta gaji da zaman banzan ne shiyasa take taimaka musu.

Abeeda Bata hanata ba duk da dai tasan Hakan Bai kamataba sosai Amma tinda asmaun naso saita barta kawai.

Kullum da daddare suke zaunawa a palon na Asmau su tattauna maganganunsu da yar firarsu ta Aminai kafin Asmau ta dawo ta kwanta.

Ita kanta Abeeda a yanzu datake samun Wanda kullum take fira dashi sai take Jin dadin rayuwar tata da kullum Hutu ne da Bada umarnin sai wayoyi Dan aiki ma ta Dena zuwa kwata kwata.

*****Satinsu biyar harda kwanaki da zuwa Amma har lokacin ASH TALBA Bai dawo ba gashi Yara sunyi sabo sosai da Haydar Wanda a yanzu ko abinci yafison yaci gurinsu Abdul ko Amatu wadda yakejin yafisonta antinsa akan Husnah dasuke uwa Daya,
Hakama maamah Jin yakeyi yafison zama a gurinta sbd yanda ko abinci sukaci itace take wanke musu hannuwa da Baki hakama yanda Abdul tasaba duk da ya Dan girma itace take masa komai Dan haka Shima a yanzu din itace take masa komai tini ya Dena son wankan masu aiki Sena maamah hakama Amatu itace ke masa Shirin zuwa school yafison nata.

Duk wannan hidimar maamah bata Dena zuwa kama ayyukan gidanba Dan kada suyi zaman banza Dan haka a sane khaltume ta sallami masu aiki biyu daga cikinsu tabar biyi masu shara da tsafatace gidan kawai aikin kitchen kuwa daga me aikin girka abinci sai maamah Dake sauran duka ayyukan batareda Jin gajiyawaba ko damuwar komai.

Shakuwar Amatu da Haydar yasa Abeeda Jin batason su tafi sbd ‘danta ya samu sakewan da suketa son yayi ya more yarintarsa Dan haka ta ringa Jin batason tafiyar tasu ko dan Haydar.

Abdul kuwa yasamu abubuwa na karuwa sosai daga Haydar,
Kamarsu sutura masu kyau da takarma dasu kayan wasa haka masu girma da tsada Dan haka shima tini yaji bayason su koma musamman idan suna garden na gidan suna wasa dasu keke da lilonsu Haydar din su basuma San akwai irin wannan duniyarba a gidan Saida suka hade da Haydar.

Abeeda ba mace ce me yawan son fira ba shiyasa sai dare suke Dan zaunawa su zanta da Asmau wadda zuwa lokacin Asmau tafara Jin kanta a tsarge idan tana tareda Abeeda sbd matsayin ba Daya ba hakama ita datake cikin Yan aikinta Jin take kamar yanzu Abeeda tafi karfinta duk da so da kaunar junansu a jininsu yake Kuma Abeedan Bata taba nuna mata tafi karfin nata ba Dan kuwa bayan Maamah din Babu me zuwa ya zauna kujera Daya da ita suyi magana irin wadda Bata taba iyayi da kowa a duniya harma ASH TALBA Wanda yake mijinta da Bata hada komai da kowa dashi ba a zuciyarta da rayuwarta.

Lokacinda suka cika sati Shida cif a gidan su mum Aisha suka dawo tareda Husnah wadda take matiqar ji da ita sbd yanda Ash Shima yake matiqar ji da Husnah din kasancewarta suna mata kallan ‘dan uwansu da suka Rasa.

Daga isowarsu tun a harabar gidan mum Aisha ta hango garden din gidan da Haydar ke wasa tareda Abdul suna Jan gashin AmatulMaleek Da Maamah tagama kunce mata da wankewa tareda daure mata kafin da daddare ta mata kitsonsa Dan ta Saba itace ke Mata kitso tin tana yarinya Tin Bata iyaba kuma haryanxu bawai ta iya kitson bane sosai Amma de itace take mata ahakan.

Jan gashin sukeyi suna guduwa tana binsu fuskarta a Dan sake sbd ko taso tayi fushin dasu kasawa takeyi Dan batada zafin Rai ko zuciya ko kadan.

Abdul Daya Saba tsokanarta shike fadawa Haydar inda zasu ja gashin su gudu ai bazata iya kamasu ba.
Haydar ma da wasan ke masa dadi sake kamawa yakeyi Yana Dan ja ahankali.

Haydar din tafara kamawa tana cewa

“Wa na kama??
Zaku sake??

Hannunsa take kokarin dagawa sama ta kama kunnensa yafara dariya sosai me hade da ihun Kiran sunan Abdul Wanda yazo da sauri yaja janyesa suna dariya itama Amatun dariya takeyi duk da taso maganinsu.

Dakatawa mum Aisha tayi cikin Isa da Wani irin iKon Daya gama zama jikinta ta kallesu da kyau Taga Haydar ne ke wannan ihun da dariyar,abinda Bai tabayi ba,Babu Wanda a gidan ze ce ya taba ganinsa a cikin wannan Nishadin.

Husnah data fito motar a hankali itama riqe da qatuwar Apple iPad dinta sanyeda doguwar English straight gown black kallan gurin tayi fuskarta da Dan mamaki Kai tsaye tacewa khaltume

“Su waye wannan din??

Cikin girmamawa khaltume ta Dan dubi mum Aisha da ba ita tayi tambayarba tace

“Yar uwar Madame abeeda ce wadda take magana tazo tareda ‘yayanta biyu yau sati Shida da zuwan nasu.”

Mum Aisha da take ta fahimci Asmau ce tazo Bata tsaya sake Bata lokacinta a tsayuwarba ta wuce a natse qamshinta na cike iskar gurin, Husnah ma bayanta ta bi tana wucewa sashen mahaifiyarta Kai tsaye khaltume na bayanta da set din akwatinta biyu na lv suka shige
Ita Kuma mum Aisha saratu me aikinta ce ta ja nata kayan ta bita duk suka shige.
#MAMUH#
#MEERAH HERBS
FOR MORE PAGES FOLLOW ME @mamuhgee arewabooks

AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070

Leave a Reply

Back to top button