Blog

  • Amatulmaleek 10

    Amatulmaleek 10

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    10
    Badan mum Aisha taso ba dole ta Bada dama likita ya duba maamah a asibitin sai gata itama anbata gadon sbd sosai jikinta ya rikice.

    Bayan likita ya gama komai akan mamah din ansamu tayi bacci yayiwa mum Aisha bayanin ciwonta da hutun datake buqata ya tafi.

    Babu abinda mum Aisha take tinanin tsayawa tayiwa maamah din Dan haka ta dawo gida saima data huta tayi sallah taci abincin ta Tina da maamah din tasaka khaltume ta hada Amatu dame aiki Daya aka kaisu asibitin gurin maamah.

    Amatu karan farko tana ganin halinda mahaifiyarta take ciki Jin tayi komai nata yayi sanyi sbd Koda sukazo tayi Amai Amma Babu kowa adakin bare ya taimaka mata harta koma bacci ahakan.

    Share hawayenta dasuka gangaro tayi ta qaraso tafara kokarin tsafatace maamah din batareda wadda aka hadota da ita ta taimaka mata ba duk da qarancin shekarunta ita kadai ta tsafatace mamanta ta gyarata zuwa lokacin jikin maaman ya sake rikicewa Dan kuwa kaman Wanda beso aka zo asibitin ba.

    Tsoro dukkaninsu suka shiga sbd Dena numfashin da maamah tayi hakama yanda take fizga tini suka kirawo likita Yana zuwa akace su fita.

    Suna fitowa dole Fatima ta tausayawa Amatu itama jikinta yayi sanyi sbd itama marainiya ce tasan suna rasa mamansu a yawon aikatau Kila Suma zasu qare.

    Zaman Jira suka dasa a wajen dakin har likita da sauran nurses suka gama duba maamah din suka fito suka wuce Babu Wanda yace musu komai sbd ganin basune sukeda iKon Jin komai ba sai mum Aisha tazo itada ta kawota.

    Ciki suka koma suka zauna shiru Babu me magana sai kallan maamah da Amatu keyi a Kai Akai.

    Anan Amatu ta kwana tareda Maamah ita kadai sbd ana kawo musu abincin dare aka koma da ita.

    Husnah ma taredasu Abdul da Haydar akazo dasu suka duba mommynsu da maamah din suka koma.

    Acikin kwana biyu da wuni biyu maamah ta zabge itama Takoma kaman ba itaba ciwo ya sauyata,
    Amatu ma sosai ta Dan sake figewa sbd Bata iya ko sabawa da dawainiyar asibitinba dukda Babu abinda sukasan ma Yaya ake biyansa komai Kai tsaye cikin bill na familyn ASH yake shiga.

    Madame abeeda kuwa jikinta itama dai sai ahankali har lokacin Dan haka aka fara shirye shiryen fita da ita waje Amma saita farfado Dan haka ana Saka ran farkowanta kowane lokaci.

    Maamah Saida tayi kwana bakwai tana jinya me wahala kafin sauki yafara zuwa lokacin Abeeda ta farfado itama jikin nata yafara sauki Kuma baa sanar mata maamah na asibitin tana jinya ba sbd kada a qara mata damuwa.

    Koda Maamah tafara samun kanta dauriya da qarfin hali ta Saka sosai ta warware aka sallameta sai alokacin taje ta dubo Abeeda wadda ramarta ta bayyana sosai,
    Ita kanta Abeedan dataga maamah sai data tambaya cikin sanyi da rashin qarfi cewan ko maamah din tayi rashin lafiya ne sbd yanda duk ya qanjame itama.

    Murmurshin karfin hali maamah ta saki tana girgiza kawai tana qarasa zama a kujeran gaban gadon tareda Dan dafa bakin gadon tana kasa kallan fuskan Abeeda ta tambaya Yaya jikin nata.

    Numfashi Abeeda ta sake ahankali tana Dan lumshe idanuwanta sbd gajiyan datake ji ta gyada Kai ahankali tana qure kallanta akan maamah din wadda take kasa kallanta.

    Amatu ma da Bata samu zuwa duba mommyn ba sbd dawainiyar kulawa da maamah sai alokacin tayi mata sannu tana fatan samun lafiya.

    Zuwansu Husnah tareda su Haydar ya Saka dakin Dan daukan hayaniya kadan sbd murnan ganin iyayensu sun samu sauki kowacce tana zaune da kanta sabanin yanda suke zuwa ganinsu a kwance Babu me sauki.

    A Nan dakin suka wuni sai dare suka tattara suka koma gida gabaki daya sbd an sallami maamah,
    Suna dawowa gida wanka maamah din tayi Amatu ta Sakata Shan maganinta kafin taci abinci ta kwanta hakama Haydar da Husnah na dakin nasu anan sukai dare kafin suka koma can cikin Mansion suka nufi dakunansu suka kwanta.

    Washe gari wankin kayansu Amatu tayi nata Dana maamah Dana Abdul,
    Bata gama ba sai Rana Dan haka tana gamawa sallah kawai tayi taci abinci itama ta kwanta ta samu baccin Hutu.

    Sai yamma sosai ta tashi tayi sallan laasar lokacin maamah Dan karfin hali tabi masu zuwa asibiti zuwa dubo madame,
    Amatu bataji dadin fitar maamah ba a halinda take ciki Amma Kuma batada abin cewa sai kawai tayi fatan samun lafiyansu su dukan.

    Sai dare maamah ta dawo cikin ikon Allah tareda madame din suka dawo anyi sallama.

    Madame din tareda daddynsu Husnah ta dawo Dan haka babu Wanda ya ganta sbd Kai tsaye bangarensa aka ajesu Kuma sun shige Dan haka Babu Wanda ya ganta sai washe gari Shima washe garin Se yamma ta fito sbd Babu abinda Babu acan da zata buqata,
    Masu Kai abinci ne kawai ke shiga sashen Se masu gyara Suma suna gama abinda yakaisu suke fitowa.

    Kowa yaje har palonta na kurya ya gaisheta ya mata sannu da jiki da fatan samun lafiya Mai dorewa kafin kowa ya fito aka barta dasu Husnah sai mum Aisha data shiga itama.

    Maamah da Bata gama warwarewa ba haka ta ringa yawon kulawa da ita sbd Abeedan tafison maamah a kusa da ita akoda yaushe,
    Tafi Jin sauki da qarfin jiki takeji idan maamah ce take kulawa da ita.

    Ita Kuma maamah Sam bazata iya fadawa Abeeda batada lafiyanba tinda harta Nuna ita takeson ta kula da ita to tabbas zata danne tayi mata komaima.

    Amatu a zuciyarta bataji dadin Hakan ba sbd maamah din kullum dare itama haka take kwana jikin Se ahankali.

    ******Da wannan kacokam lalurar kulawa da Abeeda ya dawo hannun maamah wadda har tsaftan bangaren Abeedan gaba Daya mum Aisha tasaka aka bar mata Dan haka sai maamah ta koma tamkar itace me aikin Madame abeeda a gidan.

    Tafiyan da akaso yi da Abeedan ganin ta warware yasaka ta buqaci ASH din ya barta taci gaba da ganin likita anan,
    Shawara yayi da likitoci qwararri suka ce zaa iya barinta Nan din duk ba matsala Suma sunada likitoci cancer masu kyau,,Hakan ya Saka ya barta din Badan hankalinsa ya kwanta sosai ba sbd bayyanar cancer a tareda Abeeda ya jijjiga duniyarsa da duk abinda yake cikinta sbd a ransa Abeeda wata haskensa ce da baya fatan rasawa a kusa Yana fatan su tsufa tare su mutu tare.

    ********
    Amatu da Abdul sun sake komawa bakin karatunsu da suka bari a Nan din sedai wannan Karan harda Boko aka sakasu makaranta me kyau da tsada Amma ba wadda su Husnah keyiba.

    Amatu Sam batajin kunyar girman data Dan Fi Yan ajinsu ba tace tafison tafara daga Js 1 din Daya kamata Dan haka anan aka Sakata akan idan anga kanta na budewa sosai sai idan zata shiga Js 2 a jefata Js 3 kawai.

    Abdul ma nursery aka sakashi duk da yayi girma kamata yayi ace an sakasahi primary 2 ko 3 Amma dai sbd baida komai na karatun dole aka sakosa daga can.

    Daga Amatu har Abdul Babu Wanda ya damu da girman da yayiwa Yan ajinsu su farin ciki ma sukai da Hakan Dan haka suka dage tareda Maida himma musamman Amatu datasan wahalar mahaifiyarsu ce suke mora da karatun Dan haka bazata bari uwarsu tayi wahalar banza ba Dan yanzu aiki bana madame Abeeda kawai takeyiba kusan aikin gidan Rabi yana rataye ne akan maamah din Dan haka tsufa na dole yafara rufarta ga ciwo shiyasa kowanne dare a wahalce take bacci gari ya waye Takoma aikin kamar engine.

    *****Fara karatunsu ya Saka sosai Amatu ke sake wayo da Jin damuwan mahaifiyarta da Babu ranarda bata kwana da abin,

    Ta bangare daya Kuma Husnah na taimaka mata sosai da karatunta hakama Haydar shima Yana taimakawa Abdul Dan haka abin yake zuwar musu da sauki suna ganewa.

    Madame abeeda kuwa jikinta yayi sauki sosai Kuma har lokacin Babu Wanda yasan Menene ciwonta daga ita sai ASH Wanda Shima a qurarran lokaci ya sani Dan haka a yanzu koyaushe cikin ganawa da manyan likitoci yake ana masa recommending qwararrin likitocin Cancer na qasashe da ze Kai Abeeda ayi treating dinta.

    Maamah dai a taqaice Takoma chief maid ta gidan Dan kuwa yanzu hatta abincin da masu gidan ke ci itace take girkawa Dan takanasa aka ringa koyar da ita bisa ga umarnin mum Aisha Dan haka tana qwarewa aka sallami chiefs din Dake girka abincin ASH TALBA maamah tayi replacing dinsu Dan haka ta sauya sosai ta sake manyanta ba kaman Abeedan Dasuke Aminai ba ita duk da tanada boyayyan ciwon da Basu saniba jikinta yananan me kyau da Hutu kamar yarinya take sake komawa.

    **AmatulMaleek karatunsu yayi Nisa ta sake zama Yan mata Dan ma karatu na cinyeta sosai sbd yanda ta qwallafa masa Rai,
    Kamar yanda aka fada idan anga tana ganewa zaa mata jumping to lokacin nayi Akai nata tsallake maimakon tayi Js 2 Kai tsaye Js 3 aka kaita wadda har sunyi jlc tayi SS 1 hakama yanzu tana Ss2 lokacin Husnah tagama harta shiga university.

    ***Ita rayuwa tana zuwarwa bawa ne a yanda ubagiji ya tsaro masa bawai Kaine kake tsarowa kanka ba,
    AmatulMaleek matashiyar budurwar Dake tasowa a lokacin,
    Wata irin rayuwa ce take gudanarwa ta kadaici da kamun Kai a cikin gidan dasuka Dade da zama ‘yan gida Kokuma tace gidan da suka Dade da zama ‘yayan me aikin gidan Dan kuwa ayanzu ba ‘yar uwa ko Aminiyar madame ake kallan maamah ba matsayin shugabar masu aikin gidan ake kallanta,matsayinta Daya da masu aikin,guri Daya da masu aikin gidan suke rayuwa,abinda ake bawa masu aikin gidan shi ake Bata,bambamcinta da masu aikin gidan shine Bata karban albashi hakama dauke ake da nauyin karatun yayanta Wanda zata iya qarasa rayuwarta a wannan wahalar sbd ‘yayan su samu gobensu me kyau duk da har Koda yaushe duk abinda takeyi na wahala da abinda ake mata a gidan bata taba Jin haushi ko damuwa ba sbd Dan Allah takeyi dakuma kaunar datakewa Abeeda wadda itama zata iya dawwama a wannan wahalar datake mata batareda taji komaiba.

    AmatulMaleek zuciyarta ta taso ta Ginu da damuwa da Jin radadin irin rayuwarda mahaifiyarta ke ciki wadda a yanzu ko tausayi Babu bare kauna a yanda yake treating maamah a gidan,
    Hatta dawainiyar Husnah data Haydar itace takeyi Wanda Hakan ke sake lullube zuciyarta da tausayin mahaifiyarta wadda har lokacin zuciyarta me tsafta ce Bata Jin qyashi ko gazawa.
    #MAMUH#
    #MERAH HERBS

    *_AMATULMALEEK_*
    By Mamuhgee
    And
    *_YANCI DA RAYUWA_*
    By Hafsat Rano
    Na kudi ne
    For more page ku biya
    500 for littafi Daya
    1k for duka books din biyu
    at👇
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

  • Amatulmaleek 14

    Amatulmaleek 14

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    14
    *INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
    *SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
    *Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*

    MAGANIN SANYI
    MAGANIN NONO
    MAGANIN HIPS
    MAGANIN SLIMMING
    MAGANIN NANKARWA
    GYARAN AMARE
    SET MAIJEGO
    MALLAKA
    SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
    TURAREN WUTA
    MATSI
    MAGANIN NI’IMA
    BACK TO VIRGIN SET
    INFECTION FLUSHER

    08142800199
    07068558096

     

    **********
    Husnah bayan dawowarsu komai tsayawa yayi a rayuwarta sbd duk yanda aka dauka zata iya riqe abin takasa sbd kanta da zuciyarta Sam basa iya daukan abinda Bata Saba gani ya faru a rayuwarsu ba Dan haka sai abin yafara yawa Yana bawa maamah tsoro da Haydar harma dasu Amatu Dan kuwa cikin kanta depression din yafara tabawa Dan kuwa a yanzu rayuwa ce sukeyi kamar mahaifiyarsu dai ta riga ta rasu Dan kuwa dukkaninsu sun saddaqar da ba tashin zatayi ba San haka take Jin ita mum din ma ta riga ta rasu.

    Dad dinsu sosai ya Maida hankali akan kulawa da lafiyarta sbd kada abin ya taba kwakwalwanta sosai duk da yariga yafara tabawa Dan haka ya tashi tsaye Shida maamah ne suka tsayu a gun kulawa da ita da yawon ganin likitocin da aka ringa yi da ita harta Dan fara samun sassauci tukuna Dad din yakoma harkokin gabansa maamah ta ci gaba da kulawa da ita.

    ***Maamah ta zama uwa ta zama kusan Uba ga ‘yayan Abeeda da nata yayan Dan kuwa Dad dinsu Bai fiya zama ba kusan youshe Yana hanyar zuwa dubo Abeeda duk da Babu Wani alamar nasara ko zata Tashi din Amma Bai cire tsammani ba kamar yanda yake Jin idan Abeedan ta tafi tabarshi zuciyarsa zata samu raunin da Babu healing har abada.

    Babu abinda Ba’a wadata maamah da ‘yayanta a yanzu da komai na ragamar gidan yake hannunta,
    Babu duniyar da basa samu,

    Lalurar Husnah itace Mafi wahalar da maamah Kesha a rayuwarta sbd tamkar me ciwon qwaqwalwan gaske Takoma mata Dan haka sai take Shan wahala da azabar kulawa da ita Dan kuwa itama abin sai yake Neman taba ta Dan ganin takeyi idan AmatulMaleek dinta ce Hakan ya sama duk abu Daya zata ji gashi kusan ayanzu marayu ake daukan su Husnah din.

    Ahankali ahankali lokaci yaja sosai Husnah tafara samun lafiya sosai bayan lokaci me Dan tsayi data dauka a halin na wuya da tausayi,
    Maamah nata yayan sun hakura sadaukarwa Husnah da ita Dan kuwa tin bayan shigar Husnah wannan halin maamah Takoma abin tausayi itama sbd kula da Husnah din,
    Ta wahala iya wahala akan Husnah,
    Wani tsufa da qanqancewa tayi sbd rayuwar data samu kanta aciki,
    Daidai da rana Daya Bata taba Jin gazawa ko jin ba ‘yarta ce ta jini take dawainiyar da ita ba,
    Husnah da ita maamah din sun samu Wani irin shaquwa da bond me karfi dayasa AmatulMaleek dole ta barwa kanta yarda da Babu abinda zai wanke ko rage kaunar da maamah kewa Abeeda da iyalinta,

    A yanxu Husnah data saddaqar ta rungumi rayuwa a yanda tazo musu ba magaifiya sai maamah da a yanzu itace take wa kallan uwa ta gasken gaske harka tana Jin kamar ta Fi Amatu so da buqatan maamah a rayuwarta Dan kuwa kauna da so me tsananin gaske maamah ta nuna make a babu sirk,

    Haydar kuwa Amatu ce ta cike masa gurbin uwa,Kuma ‘yar uwa harma da masoyiyar dayake fata a gaba Dan itama duk da karatun datake harta gama ta tsayu akan kulawa dashi da debe masa kewa da hanasa shiga kowacce irin damuwa itada Abdul Daya zama kamar twin brother dinsa Dan kuwa komai nasu a yanzu Daya ne Babu bambamci.

    A bangaren ASH TALBA kuwa a zuciyarsa Wani matsayi me girman gaske maamah ta samu da Babu abinda zai iya biyanta dashi har abada,
    Itace ta tsaya akan gidansa da ‘yayansa a lokacinda Babu Wanda zai tsaya masa,
    Alokacin da ‘yayansa suke buqatan uwa,
    Alokacin da Shima yake buqatan macen da zata tsaya masa gidansa,
    Ta sadaukar da rayuwarta da karfinta da lafiyarta harma da ‘yayanta Bata bari gidansa ya shiga maraicin matar gidan ba,hakama yayansa Basu shiga maraicin da zai illata kuruciyarsuba, haka ma dashi kansa da itace ta tsaya tsayin dakan kulawa da duk wata lalaurarsa da komai nasa harya same qwarin gwiwa da zuciyar komawa kan qafafunsa ya tsayu a harkokinsa ya koma yanda yake a Baya,

    Dan haka maamah itace jarumar rayuwarsu da bazasu taba iya biyan alkhairinta garesu ba daga shi har ‘yayansa Dan haka matsayinta yake me girma a garesa.

    Ta sadaukar da sauran karfinta da kuruciyarta ta tsufa karfi da yaji sbd wahalar data rataya akanta Dan bazaka kalleta kace tsaran Abeeda bace wadda itama aduk lokacinda yake dubata karyewa zuciyarsa keyi Takoma kamar ba itaba ciwo ya sauya kamanninta gaba Daya,Dan idan tanada Rabon tashi ba lallai ta sake komawa yanda takeba a Baya.

    Mum Aisha datai tafiyar zuwa dawo Saida ta share itama lokaci me Dan tsayi kafin suka fara Shirye shiryen dawowa Dan Bata yarda ta dawo batareda Naufal da baiso dawowan ko kadanba shiyasa ta jira ya qarasa kammala takardunsa suka hada komai tareda Shirin dawowa gidan da zasu bude sabuwar rayuwa.

     

    ******AmatulMaleek tinda ta gama secondary Babu inda ta qara a karatun sbd Babu Wanda ya Tina da Hakan tinda Daman Madame abeeda ce take kula da lamarinsu Se mum Aisha datake musu komai da manufa Dan haka a gida take zaune tareda daukewa maamah wasu ayyukan gidan duk da ankawo masu aiki sunayi Amma wasu abubuwan kaman kulawa da sashen madame dana Mai gidan kusan yanzu itace takeyi tinda ko islamiyya ma ta sauke Dan haka Babu komai datake a rayuwarta itama yanzu bayan bautawa gidan ASH TALBA da Madame abeeda wadda suka fara shafe tarihinta duk da bawai ta rasu bane Amma a gurinsu kaman hakanne Dan kuwa ko su Husnah yanzu karatu sukeyi sosai kowa ya dangana ya rungumi kaddara hakama so Daya Dad dinsu ya taba zuwa dasu suka dubota sai yaga abin na tabasu Sai Bai qara barinsu zuwa ba.

    ******Ayau gidan ya Dan rayu da hayaniyar dawowar mum Aisha da Babban matashin Gidan ASH TALBA wato Naufal Talba Wanda dawowarsa qasar ya gama zubar da duk Wani farin ciki da burin rayuwarsa Dan haka Koda aka daukosu airport fuskarsa Babu alamar wasa ko sakewa acikinta,
    Sanye yakeda black sweatshirt da sweatpants sai fcap da sunglasses.

    Husnah ce kawai tayi murnar ganinsa ita data sansa sosai Dan haka rungumeta yayi ahankali Yana sake mata kyakkyawar fuskarsa Yana cewa

    “Oh my gorgeous”

    Dariya ta Dan yi tana dagowa daga jikinsa tace

    “Sannu da dawo N Talba”

    Dariya yayi sbd tinowa da shine ya koya mata kiransa da N Talba Dan Uncle din Yana masa Wani iri kamar tsoho.

    Mum Aisha ta rungume itama tai mata sannu da zuwa cikin farin cikin ganinsu.

    Ciki suke kokarin qarasawa Haydar ya fito daga geam dayake ta hanyar cikin garden Yana ganinsu ya qaraso Shima cikin farin cikin ganinsu ya rungume Naufal din Yana cewa

    “Happy to see you Uncle, welcome”

    Dan rungumesa Shima Naufal din yayi Yana kallan yanda Haydar din duka duka shekarunsa Basu wuce 18 ba Yanaga amma sbd geamin da yaron keyi ya Bude sosai kamar Wanda yayi 25 koma fiye gashi
    Yana budewa kamanninsa da ASH TALBA na sake bayyana.

    Ciki sukayo dukkaninsu zuwa palon mum Aisha da tini Amatu ce ta gyaresa fes Dan tin can tafison aikin Amatu Dan yafi nutsuwa da tsari Dan haka ko yanzu Amatu ce ta gyare mata palonta da bedroom dinta da toilet.

    Shi Kuma Naufal sabuwar me aikinsu ce ta gyare bangarensa dayayi shekaru bayanan Amma ana gyarewa komai ya dawo fes kamar ranar aka sauya komai.

    Ko zama Naufal beyiba a palon mum Aisha ya jiya yanufi bangarensa da already ankai kayansa can.

    Yana Isa Bai tsaya Palo ba Kai tsaye bedroom dinsa ya wuce ya jefar da wayarsa kan lafiyayyan gadonsa Yana sake numfashi a bayyane tareda zare duk kayan Dake jikinsa a tsakiyar dakin ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwa.

    Mum Aisha ma wanka tayi ta fito tayi salloli Dake kanta dayake safiya ce ko abinci Bata ci ba ta kwanta bacci sbd ta huta.
    Shi kansa Naufal Yana Gamo wankan ya shafa abinda zai shafa na Mai da tirare ya Saka Wani tight short ya fada gadonsa hutawa yake buqatan yi.

    Su Amatu kuwa mum Aisha kawai suka samu damar yiwa sannu da zuwa bayan ta tashi bacci da kusan yamma.

    Kallan Amatu mum Aisha tayi ganin yanda a yanzu ta zama cikakkiyar budurwar da Babu abinda Bata rasa ba a jikinta na kyau da kyan jiki harma da jiri me kyau,
    Sannan nutsuwarta data Saka ake Gani kaman sanyine da ita duk komai na nan saima abinda ya qaru ga uwa Uba kamun Kai ko a cikin gida ba kowane zece AmatulMaleek ta sake dashiba sosai.

    Cikin gatse mum Aisha tana kallanta tace

    “Amatu yanzu da aka gama makaranta Se aure ko tinda ba Wani karatun gaba zakiyiba”

    Shiru Amatun tayi tareda Dan sauke boyayyan numfashi a boye kafin ta Dan saki kyakkyawan murmushi tana qarasa nade kayan mum din datake nadewa tana jerawa a wardrobe daga cikin akwatin Data dawo dashi batareda ta iya cewa komaiba.

    sake maimaita tambayar tayi itama fuskarta a sake Dan tabbas zata so Amatun tayi aure da wuri tabar gidan tinda Naufal ya dawo idan batai taka tsantsan da Yan matan gidan ba masu aiki komai zai iya faruwa da wuri halinsa da Bazata taba yarda ASH ya saniba to zai sani komai ya lalace musu Dan haka dole zata Bude wuta ayiwa Amatu aure tabar gidan Dan gwara Yan aiki idan ya lalatasu zata Basu kudi ta sallamesu asiri rufe Amma AmatulMaleek sbd matsayin maamah a gun ASH zaa iya samun matsala.

    Duk yanda mum Aisha din ta bugi cikin Amatu Dan Jin ko tanada saurayi Sam Bata samu Jin komaiba sbd zurfin cikinta dakuma saurayinka da batadashi.

    Harta gama gyara kayan mum din Janta mum takeyi da fira daban daban itama ta San amsawa da Wanda ta sani Wanda bazata iya fada Kuma sedai murmushi kawai.

    Kayan da zaa Saka cikin kayan wanki ta fito dasu basuda yawa kala biyu ne ma Dan haka ta fito dasu ta miqawa me aikin da zata wanke su.

    Tana kaiwa kofar ficewa mum ta kirata tareda cewa

    “Ki kawomin salad Amatu bazan iya cin white rice dinnan ba yanzu zata dameni”

    “Ok mum” ta fada a natse da muryarta me dadi tana juyawa zata wuce ba zato tai karo da mutum da sauran kadan kirjinta ya Hadu da nasa tayi saurin yin Baya tana dago idanuwanta da Dan mamaki.

    Naufal da sauran kadan numfashinsa yabar jikinsa sakamakon kamshin jikinta Daya shiga hancinsa sosai harma da Dan haduwar da jikinsu yaso yi sauke mata mayun idanuwansa yayi Yana kallan mamakin inda ta fito da inda zata,

    Wani numfashi ya hadiye tarewa yawu ta maqoshinsa da Saida Hakan ya nuna a wuyansa Yana kallanta da dukkanin idanuwansa Dake qarawa mata sonsa.

    Amatu dauke idanuwanta tayi daga kansa fahimtar waye shi Din
    Sai tasake yin gefe kadan tareda Bude Baki a hankali ta furta

    “Yi hakuri ban luraba,sannu da dawowa.”

    Har lokacin idanuwansa akanta suke sedai lokacinda ta Bude Baki tana magana idanuwansa a bakinta suka koma daqyar ya Bude Baki zai amsa mata mum Aisha ta katsesa da cewa

    “Amatu wuce kije”

    Batareda ta gama fadar ba Amatu ta rabasa ta wuce tana Dan sake gyara riqon kayan hannunta dasuka zame batareda ko waiwayosa ta sake yiba.
    #MAMUH#

    *_AMATULMALEEK_*
    By Mamuhgee
    And
    *_YANCI DA RAYUWA_*
    By Hafsat Rano
    Na kudi ne
    For more page ku biya
    500 for littafi Daya
    1k for duka books din biyu
    at👇
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

  • Amatulmaleek 21

    Amatulmaleek 21

    YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

     

    21
    *INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
    *SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
    *Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*

    MAGANIN SANYI
    MAGANIN NONO
    MAGANIN HIPS
    MAGANIN SLIMMING
    MAGANIN NANKARWA
    GYARAN AMARE
    SET MAIJEGO
    MALLAKA
    SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
    TURAREN WUTA
    MATSI
    MAGANIN NI’IMA
    BACK TO VIRGIN SET
    INFECTION FLUSHER

    08142800199
    07068558096

     

    ************
    Washe gari Koda aka duba dakin Naufal bayanan ya tafiyarsa ga mum Aisha a gida ta kwana Babu Wanda yake tinanin tanada Saka hannu a tafiyar tasa ko sani Dan kwata kwata baa asibitin ta kwana ba.

    Suna cikin wannan mamakin da baqin cikin maamah da Amatu suka farfado Suma Dan haka suka mayarda duk hankalinsu kansu Amatun.

    Amatu tinda ta farfado bayan kuka Babu abinda takeyi zuciyarta nauyi take mata sosai musamman mummunan labarin dasuka tadda ya gama zagaya koina.

    Maamah ma kukan zuciya takeyi me tsananin ciwo da radadin zuci,
    Wannan shine karo na farko dataji Babu inda take buqata da so bayan kebancewa daga wannan duniyar ta masu kudi,

    Rayuwar Amatu ta samu tabo me wuyan warkewa duk da baayi mata fyaden ba Amma duniyar daukakan Wanda suke qarqashinsa ta qarasa lalata sauran mutuncin Daya ragewa Amatun tinda gashinan koina an gama watsawa mummunan fyade Akai mata.

    Kuka da Hana kowa kusanto inda take yasaka yanayinta sake tsananta tanajin komai da kowa Bata son Gani ko kasancewa dashi.

    Maamah ce kawai ke iya rabarta ta rarrasheta duk da itama tata zuciyar quna takeyi tana yanka da azabar qunci da baqin ciki.

    Mum Aysha datazo tashin hankalin rashin ganin Danta kawai tayi ta gama masifarta ta juya Takoma gida tana jiran ta inda zasu fuskanci fushi da bacin ran ASH Wanda kusan koina yanzu abinda ya faru din aketa magana wasu na cewa bazasu zabesa ba tinda a gidansa ba Babu adalci ga masu aikinsa bare Al’umma.

    Abdul da su Haydar na cikin damuwa da sanyin jiki Mai tsanani na ganin halinda Amatu take ciki da yanda maamah ta kasa cewa komai har lokacin.

    Maamah aka fara sallama kafin aka sallami Amatu wadda ta batajin zata iya komawa gidan gaba Daya.

    Ita kanta maamah ta Yanke hukuncin bazata iya komawa gidan ba sai Kuma ga Kiran kawu bello da Babu labaran Daya shafi ASH TALBA da basa bi Dan sanin sunada alaqa da gidansa tinda Asmau na can da ‘yayanta dasukaci buri da jiran su zama Wani abin a duniya su fito suce sune dangin mahaifinsu.

    Samun wannan mummunan labarin ya girgiza su sosai Dan sun dauka iya irin gidajensu irin wannan yake faruwa sai gashi har gidan masu taka Naira ma Yana faruwa Dan haka kwadayin Asmau ya qare ta dawo gida kawai.

    Irin zagi da cin mutuncin da kawu sukai mata a waya tareda gori masu tsananin nauyi ya Saka zuciyarta ta kasa dauka ciwon zuciya na Neman kasheta cikin sanyi Dan haka hankalin Abdul ya sake tashi ya ringa rokon Amatu data sassautawa kanta ko maamah din zata sassautawa tata zuciyar.

    Daga asibitin maamah ta Yanke hukuncin tafiya su koma kauye gaba Daya,

    Wannan hukuncin na maamah shine ya girgiza duniyar Husnah Dake cikin tsananin tsaka me wuya sbd a Daren Haydar jirginsa ze tashi hakama idan maamah ta tafi tabarta zata iya haukacewa a rashin maamah da Haydar din lokaci Daya Dan haka ta haukace cikin tsananin tashin hankali da kukan rokon kada maamah tabarta rayuwarta zata lalace.

    Shi kansa Haydar yashiga damuwa sosai ta halinda Husnah ma zata shiga duk da zuciyarsa sai ta Wani bangaren take samun nutsuwar Amatu ta koma kauye Dan acan zatafi zama safe daga Maza ma gaba Daya har lokacin dawowansa to Amma Kuma Husnah tini ta rikice gwanin tausayi tana rokon kowa kada a tafi a barta ita Daya.

    Zuciyar maamah tariga ta Yanke hukuncin tafiya duk da zuciyarta na yanka sosai da ganin halinda Husnah tashiga na fita hayyaci kaman zata zauce Amma batajin zata zauna gasu kawu sunyi rantsuwar saita dawo da AmatulMaleek kauye idan ita bazata dawo ba saisu Amatu sun dawo.,

    To idan ta bar Amatu suka koma ita tana nan batasan mezai faruba acan Dan kusan duk abu Daya ne suke tsoro da can da Nan din.

    Haydar da zai wuce tin yamma yake asibitin tareda Amatun wadda itama adaidai wannan Gabar kukan rabuwar dashi takeyi Dan kuwa tabbas da Haydar ya Isa auren shi zata aura zuciyarta tafi nutsuwa dashi a aynzu fiyeda kowanne namiji a duniya.

    Kuka takeyi sosai Yana rarrashinta kamar zaiyi kukan Shima.

    Husnah kuwa har airport ta rakasa tareda Faisal Wanda dole Saiya kula da ita Dan tana cikin wani mummunan hali na kadaici da gariri yanzu.

    Qanqame Haydar tayi tana kuka sosai kaman shine yayanta itace kanwarsa,
    Shi kansa hawayen yakeyi sosai yake tausayinta Dana kansa duk da tareda Jameel zasuyi tafiyan sbd yariga Dad dinsu isowa.

    Husnah Jin takeyi kaman tabi ‘dan uwanta su tafi duk inda zasu tare Amma ba Daman Hakan tayi kuka sosai Wanda yasaka dole tausayinta cika zuciyan Faisal haka ya lallabota suka dawo gida kafin da safe tasake komawa asibiti ta Hana maamah tafiya Dan bazata iya rayuwa babu maamah dinba Babu Haydar Babu mahaifiyarta da tini ta barsu.

    Faisal ma daga mansion din gidansa ya wuce sbd dare yayi Saida safe ya koma asibitin.

    ********karfe Biyar na asuba su mamah suka Isa Tasha daga asibitin bayan Abdul yaje da kansa ya tattaro kayansu da duk abubuwansu da zasu iya tafiya dasu.

    Maamah Bata sanar da Husnah ba sbd kaucewa tashin hankalin da zata shiga ita Kuma mum Aisha Daman itace ma da kanta ta sake tsayawa akan tafiyar tasu duk da Basu ce mata komaiba kaman yanda Bata ce musu komaiba gameda abinda Naufal din yayi.

    Cikin saa Basu Wani jima ba karfe 6 na safe motarsu ta tashi Babu me walwala a cikinsu hakama Babu me magana suka dauka hanyar tafita me Nisa.

    Husnah kuwa lokacinda taje asibiti tinda safe karfe 7 ta Tararda sun wuce sakewa jikinta yayi ta zubewa Faisal da Shima isowansa kenan.

    Tashin hankali me tsananin gaske ta shiga da Bata gane komai bayan kawai dawowan maamah gareta kota halin Yaya.

    Babban tashin sa’ar da aka samu da sabani shine a ranar ASH ya sauka kasar,
    Securities masu yawa suka tarbosa sbd yanda Yan media suka cika suna jefa tambayoyinsu akan abinda ya faru Baya qasar dakuma mataki da adalcin da zaa yiwa me aikinsa wadda akace ‘yar uwar matarsa ce da ‘yarta.

    Ganinsa yanda ya kamata Yan media din basuyiba sbd tsananin tsaro da yawan securities dinsa harya shige mota Babu inda ya kalla bare Saka ran tankawarsa hakama kwarjinsa ya hanasu jefa wasu tambayoyin da sukaso.

    Koda ya iso Mansion din Daman tini aka qara securities Dan haka Babu Yan jaridu ko a anguwar.

    Bangarensa Kai tsaye ya nufa sai kusan bayan awa Daya ya fito cikin wasu kayan daban Dake nuni da yayi wanka.

    Kofar palonsa da zata sadasa da Babban palon iyalinsa ya nufa ya fito palon dayake tsit Babu motsin kowa sai AC da qamshin gyaran da Akai Dake tashi.
    Kai tsaye dakin Husnah ya nufa wadda ke kwance a dakin ita Daya Babu kowa shiru.

    So Daya yayi knocking tareda Murda kofar ya Kalli cikin dakin yaganta kwance a qasan tiles sbd ba zuciyarta kadai ke Mata radadi da zafi ba hatta gangar jikinta da jininta Jin takeyi suna mata zafi sosai.

    Lumshe idanuwansa masu haske sosai yayi ahankali tareda Jin zuciyarsa na yanka ya Tako a natse ya nufota cikeda tausayi da tsananin so da kauna irin na Uba da ‘yarsa.

    Idanuwanta Dake rife ta Bude ahankali batareda ta motsa ba Jin motsin mutum.

    A fafaren qafafuwan datasan Babu me irinsu a gidan idan ba Dad dinta ba Idanuwanta suka fara sauka ta motsa ahankali tareda yunkurawa ta tashi zaune idanuwanta suka sauka akan fuskar Dad din da shi kansa idanuwansa sun Dan fada sbd damuwar yayansa da akaita wannan tashin hankalin bayanan Dan haka yayi alqawarin daga wannan Karan bazai qara tafiya yabarsu a irin wannan rayuwarba zai zauna ya kula da yaransa da kyau tareda inganta rayuwarsu da kansa dakuma taimakon Asmau da kokarinta da bata gajiyawa.

    Husnah kasa cewa komai tayi ganinsa bayan hawaye masu tsananin gudu da suka balle mata Kai tsaye abinda tafara Bude Baki ta furta kuka na tsinke mata shine

    “Dad muna buqatan Mum kowace iri ce koba mum dinmu ba”

    “Dad I can’t live like this,
    Dad ka dawo min da maamah,
    Dad Ina tsoron kadaice,
    Dad maamah ta tafiyarta ta barni,
    Haydar ya tafi,
    Banda kowa,
    Mum Aysha Bata zama,
    Banda kowa,
    Ina son maamah ta dawo,
    Dad Dan Allah kayi aure ko zan samu wadda zata zauna damu batareda tace zata tafiyarta ba kaman Maamah……kuka ne me karfin gaske yazo mata ta soka kanta cikin qafafunta tana Jin tsanani kewan mahaifiyarta ayau fiyeda kullum.

    Shi kansa kasa cewa komai yayi ya qaraso a hankali kafin yayi magana ta fada jikinsa tana sake fashewa da Wani kukan sosai zuciyarta na Susa batareda kowa yasan irin radadin datake ji ba Dan kadaici tsananin tsoro da firgici yake Sakata.

    Kasa magana Dad din yayi sai Jin dayayi tinaninsa Shima ya tsaya cak da Jin Maamah ta tafiyarta,
    Tabarsa da yayansa itama kenan..

    Jin yayi kansa ya Sara Dan kuwa komai Yama wuce yanda yake tinani kenan tinda maamah ta tafi to tabbas abin ya girmama.

    Kukan da Husnah takeyi sosai Yana shafa bayanta cikin lallashi da kauna me karfi batareda yayi magana ba Dan idan ransa yayi mummunan Baci Baya iya furta ko Kalma Daya shiru yakeyi sedai aga hukuncinsa data Baya.

    Ciwo ne me qarfin gaske na zazzabi ya rufe Husnah dole ya kira asibiti aka Aiko likita da nurse wadda zata kula da ita sosai sbd mum Aisha itama a ranar ta silale tayi tafiyar kwana buyi kafin ASH ya Dan huce Dan tasan akwai babbar masifa a kwance.

    Kasa rintsewa ASH yayi a Daren Shima sbd kusan a qanqanin lokaci Naufal ya wargaza masa gidansa da rayuwar yarda harma da yar Asmau,
    Kewan Abeeda ce Shima ta dawo masa sabuwa Dan kuwa ya tabbatarda harda rashin matarsa ya Sakasa cikin wannan halin Shida yayansa.

    Husnah jikinta yaqi sauki gaba Daya ta daga hankalinta ta daga na Dad din akan dawowan maamah Dan tasan idan bata daga hankalinsa sosai ba bazaa dawo mata da maamah da wuri ba,
    Shi kansa baida niyar Bata lokaci batareda yaje da kansa ya dawo da Asmau ba sbd Bata adalcin datake buqata itada AmatulMaleek din bisa ga abinda akaiwa Amatu hakama a ayanzu da babu kowa mansion din sai Yan aiki Husnah na tsananin buqatan maamah da mutane a tareda ita.
    ##MAMUH#

     

    *_AMATULMALEEK_*
    By Mamuhgee
    And
    *_YANCI DA RAYUWA_*
    By Hafsat Rano
    Na kudi ne
    For more page ku biya
    500 for littafi Daya
    1k for duka books din biyu
    Vip for each 2k
    at👇
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

  • Amatulmaleek 11

    Amatulmaleek 11

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    11
    Rayuwa a Mansion din ASH TALBA tamkar rayuwa ne a wata aljannar duniya Amma Kuma ga AmatulMaleek ba Hakan bane sbd halinda mahaifiyarta yake ciki ya danne duk Wani farin cikin datake samu a gidan,
    A tsawon shekarun da suka share a gidan kowa yasamu ci gaba ya sauya daga sanin da Akai masa,sauyi kuma me girman gaske Amma Banda maamah wadda ta koma tsohuwar qarfi da yaji ga ciwon kirji Dana jiki Dana qafafu da Baya Wanda kowanne dare Bata iya bacci me dadi,
    Ita kadaice tasan halinda mahaifiyarta ke shiga kowanne dare,
    Maamah a Koda yaushe boye mata gajiyawarta da ciwonta takeyi sbd kada ta sani ta nuna damuwarta Dan haka maamah din ta zabi ta ringa hadiye damuwarta da ciwon dayake cinta sbd ganin AmatulMaleek na ajiye kowacce damuwarta a ranta kada Hakan ya taba rayuwarta da karatunta Amma Kuma abinda Bata saniba shine hakan ya Riga ya zaunu a zuciyar Amatun ta yanda take musu kallan Yan cin alfarma da jiran komai akashe abasu kaman yanda Husnah ke fada mata tin suna Yara.

    Su ‘yayan me aikin gidan ASH TALBA ne Kuma bazasu taba tashi daga Hakan ba shine kalmomin da mum Aisha akoda yaushe take fadawa maamah a gabansu tin suna Yara haryanxu dasuka girma Hakan Bai taba canzawaba.

    Ko mum Aisha da Husnah basa yawan tinatar dasu su din da matsayinsu Hakan a bayyane yake ba buqatan tini sbd haryanxu data zama budurwa Abdul yafara zama Dan saurayi a daki Daya suke su da mahaifiyarsu anan suke rayuwarsu.,
    Jimawa sukeyii baa dinka musu sabuwar sutirar rayuwa ba kayanda su Husnah suka cire su ake Basu,
    Basa shiga sashen madame Abeeda Sai Idan aikine ya kaisu Wanda tinda ta girma take kamawa mahaifiyar aikin gidan,
    Har gobe abincin dasuke ci da Wanda mutanen gidan sukeci akwai bambamci,
    Dan wannan matsayin dasuke Basai an tinanar dasu matsayinsu ba a cikin ASH TALBAs Mansion.

    Abdul ma duk da kasancewarsa namiji har cikin ransa Yana tausayin mahaifiyarsu da wahalar datake sha Amma Shima kusan Amatun ne su dauko halin maamah na danne abu a zuciya tareda nuna ba komai bane Amma kusan Shima Yana taimaka mata da wasu ayyukan duk Yana gida kamarsu aikin kitchen Dan dole daga shi har Amatu sun iya aikin girki sbd taimakawa maamah.

    Duk tsawon shekarun da sukai a gidan Babu abinda ya taba kaisu bangaren Mai gidan wato daddynsu Husnah sbd sam baa zuwa gurin hakama duk ganinda sukai masa daga nesa ne tinda ba mazauni bane sosai hakama Koda Hange Babu abinda ya hada bangaren masu aikin gidan da bangarensa bare su samu kusanci dashi.

    Husnah anan Abuja take karatunta Dan haka wayewarta ta yayan masu kudin qasa suke bayyane gata batada hakuri ko saukin kai ‘yar Kai tsaye ce Bata iya boye zance ko maganar Dake ranta ba shiyasa da dama ake mata daukan me wuyar shaani,
    Kusan Tako wanne bangare halayenta Dana AmatulMaleek sunyi hannun Riga Dan ita kanta Husnah duk yanda taso ganin bacin ran Amatu ko fushinta Bata taba iya Gani.

    Shaquwan AmatulMaleek da Haydar wata irin kaunace a tsakaninsu me girma Dan kuwa jinta yakeyi a ransa fiyema da Husnah hakama itama Amatu a cikin familyn TALBAs gaba Daya Haydar shine Wanda tafi so fiyeda kowa da komai na gidan bayan Maamah da Abdul Dan ma kusan yanda take Jin Abdul haka take jinsa a ranta.

     

    *******
    Ayau gidan ASH TALBA sun tashi da sabon tashin hankalin dawowan ciwon Madame abeeda wadda haka kawai aka wayi gari ta sake shiga mummunan halin data taba shiga kwanaki.

    Babbar rashin sa’ar da akaci shine ASH Baya Nan Dan haka su mum Aisha suka kira ambulance akazo aka dauketa hankalin gaba Daya jamaar gidan a tashe aka tafi da ita.

    Bayan antafi da ita asibiti lokacin dukansu suna makaranta Dan haka maamah da mum Aisha ne dole a asibitin.

    Wayar ASH da mum Aisha keta kokarin kira Bata samu ta sake Saka Kiran Amma dai still Bata samu Dan haka suka zauna jiran tsammani.

    Har yamma suna asibiti Kuma har lokacin baa samun wayar ASH Dan haka likitocin basuda zabi bayan sanarwa mum Aisha Cancer ce da Madame abeeda Kuma takusa kaiwa last stage.

    Shiru mum Aisha tayi idanuwanta akan likitan Daya gama bayanin cikin Hausa da turanci sbd bahaushe ne.

    Maamah kuwa dafawa tayi Takoma zaunen data miqe sbd nauyin da qafafunta sukai mata suna Gaza daukanta.

    Shiru sukai dukkaninsu Babu Wanda yake motsi sbd tinanin dasukai Nisa a cikinsa na ba zata da tashin hankali musamman maamah da hannuwanta duka dauki rawa ahankali
    Ta damqesu sbd rawar da sukeyi zai iya haifar da matsala babba gareta musamman ciwonta datakeji zuciyarta na Neman Dena bugawa.

    Cancer” mum Aisha ta furta ahankali tana Dan share guminta Dan duk abinta tana tsoron mutuwa haka Kuma duk lokacinda aka ambaci Cancer ga mutum Babu abinda suke fara hangowa akansa sai mutuwa a kusa kusa.

    “Innalillahi wainna ilaihirrajiun” maamah ta fada ahankali tana rintse idanuwanta dasukai nauyi suna son hawaye Amma sunma kasa haduwan.

    Mum Aisha a gurin ta ciro wayarta Babu Wanda ta fara kira sai ‘danta da kusan Babu abinda suke boyewa juna,kaf duniyarta shi kadaine Wanda takeso tsakaninda Allah da gaskia Dan haka ta tsaya akan karatunsa Dan yayi arzikin Daya kusa na ASH TALBA idanma har bazai fisa ba kenan.

    Ringing wayar tasa takeyi harta katsae Bai daga ba Saida ta sake kira karo na biyu jikinta na rawa ta isar masa da zancen sbd damarsu tazo ta dawowansa gida ya baro turai sbd tabbas hankalim ASH TALBA zai tashi daga dukiyarsa da harkokinsa ya dawo Kan Abeeda sbd mahimmancinta da matsayinta yafi na komai daya mallaka so yanzu ne NAUFAL dinta zai samu matsayi da Daman shiga cikin huldodi da dukiyar ASH EMPIRE.

    ****
    Madrid,SPAIN.

    kwance yake akan lafiyayyan gadon dakinsa acikin gidansa da babu abinda ya rasa na Jin dadin rayuwa da Hutu,
    Dagashi sai Men’s tight Wanda baida bambamci da Babu komai a jikin nasa sbd kusan daga saman ya zame kadan hakama ya kamasa sosai ta yanda kana ganin shape na komai nasa.,

    Fatar jikinsa Dake shining na qyallin Hutu da kyan fatar duk a Bude Dan bayan tight din baida komai a jikinsa,
    Gefensa wata lafiyayyar blown skin mace ce da itama Babu komai a jikinta sai pant da bra wadda itama kusan a zame take,
    Bacci sukeyi hankali kwance Wanda ke nuni da idanma da daddare idanma da safen to sungama mu’amalar mace da namiji ne kafin baccin.

    Ringing wayarsa keyi duk da tana silent Amma vibration din na tashi sosai harya fara jinsa cikin baccinsa Dan haka ya Dan motsa Yana Bude idanuwansa ahankali daidai lokacinda Wani Kiran ya sake shigowa.

    Akan fuskar sabuwar budurwarsa Dake kan jikinsa idanuwansa suka sauka ya Dan yamutsa fuska ahankali tareda janyeta daga jikin nasa Yana miqa hannu inda wayarsa take daidai kira na uku na sake shigowa.

    Qaramin numfashi da tsoki ya Dan sake lokaci Daya kafin ya duba Mai Kiran yaga sunan Mum dinsa baro baro.

    Ajiyar zuciya ya sauke me sanyi tareda tashi zaune Yana zamowa bakin gado ya sauko da qafafunsa qasa ya miqe daga gadon Yana daukan wayar Kai tsaye tareda dorawa kunnensa ya nufi hanyar fita dakin Yana cewa

    “Yes mum,good morning”

    Kallan time mum Aisha din tafara yi gana su anan din ba safiya bane Amma dai koma yayane bashine matsalarta ba cikin kulawa da ‘yar kamewa tace

    “Morning,ka tashi lfy?
    Ya karatun??

    Ruwan dumi Daya zuba a cup ya jefa lemon aciki ya Kai bakinsa Saida yasha sosai kafin ya amsa da cewa

    “All good mum,
    Yaya Su Husnah and Aunt Abeeda?

    “Husnah lfy kalau Aunt din taka ce dai take kwance asibiti batasan inda kanta yake ba.”

    Shiru yayi Yana ajiye cup din hannunsa ya nufi Daya daga tsadaddun kujerun palonsa ya zauna Yana cewa

    “Meya sameta mum?
    Wani abu ya faru ne?
    Meyake faruwa?

    Katsesa tayi da cewa

    “Cancer ne da ita duk tsawon lokacin Nan Amma ba Wanda yasani sai yanzu..

    Katsesa Naufal din yayi cikin mamaki da cewa

    “Uncle ASH fa? Ya sani?

    “Bansaniba ko ya sani Amma dai yanzu besan muna asibiti da ita ba bana samun wayoyinsa duka,
    And duka bayan wannan ka saurare ni da kyau kaji……

    “Heyy baby good morning” …shine abinda mum Aisha taji daga cikin wayar tayi shiru zuciyarta na yin nauyi sbd bata buqatan kowanne irin bayani ta sani mace ce a tareda Naufal din a cikin irin matan dayake kawowa gidansa suna kwana,

    Babban baqin cikin mum Aisha a duniya biyu ne zuwa uku,
    Na farko dukiyar ASH TALBA data tsone idanuwanta ta Hana zuciyarta sukunu tsawon shekarun datake zaune a gidansa cikin dukiyar tana yanda takeso da ita hakama ‘danta yake yanda yakeso da rayuwarsa tamkar shine magajin ASH TALBA din,

    Na biyu shine Neman matan da Naufal yekeyi kamar bunsuru Sam Baya iya kwana a rayuwarsa batareda ya kusanci mace ba
    Duk ranarda ya kwana biyu batareda mace a tareda shi ba to kamar zai zauce yake jinsa shiyasa gaba Daya Baya iya zama Nigeria sbd Jin Yana aikata irin wannan zinar haka kaman abinci zai iya Saka ASH TALBA nesantasa da ko inda zaibi ya wuce bare Kuma sakashi cikin dukiyarsa dasuke fata tin shekara da shekaru Shida mum dinsa.

    Abu na uku kuwa shine Haka kawai takejin tsana da rashin Jin nutsuwar zaman maamah da ‘yayanta a cikinsu sbd maamah din tamkar kariya ce ga Abeeda data Dade tana Jin qyashinta da kishinta ga Dan uwanta dayaqi qara ko kallan wata macen bare Wani tinanin qarin aure da babusa a tinaninsa ko rayuwarsa ma gaba Daya.,
    Zuwan maamah yasaka duk yanda Husnah take renanta Kuma tarbiyarta harma da yanda takeson ta zama sbd amfani da ita gurin ASH sosai ya ruguje sbd komai rashin saukin kan Husnah da zafin kanta tana kaunar maamah da gaskia Kuma kamar yanda maamah din ke tsananin sonta kaman AmatulMaleek da Abdul, Husnah Takoma kusancinta da maamah da shaquwarta da ita yafi na kowa Dan haka Sam yanzu sedai ayiwa maamah duk abinda zaa mata na cin zatafi ko aikin wahala Amma baa iya canza matsayinta gurin Husnah da zuciyarta.
    Wanna dalilin ne yasaka taji tayiwa shigowarsu Maamah rayuwarsu tsana me karfi.
    #MAMUH#

    *_AMATULMALEEK_*
    By Mamuhgee
    And
    *_YANCI DA RAYUWA_*
    By Hafsat Rano
    Na kudi ne
    For more page ku biya
    500 for littafi Daya
    1k for duka books din biyu
    at👇
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

  • Amatulmaleek 2

    Amatulmaleek 2

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    2
    Nisan dayake tsakanin Asmau da abeeda Bai taba rage kauna ko girman junansu ba a zuciyarsu,
    Babu dawowar da Abeeda zatai Nigeria Bata zo har kauye ta ziyarci Yar uwar tata ba Dan haka kusan kaf dangin mijin asmaun Babu Wanda baisan girman alaqarta da kaunar Dake tsakaninta da Abeeda ba,

    Duk wata sutura da abincin datake ci Daya bambamta Dana Yan kauyen duka abeeda ce ta tsaya Mata akansu Koda Bata qasa ko tana qasar duk lokaci bayan lokaci sai an aikowa da Asmau abinci da suturar datake sakawa.

    Acan dangin mahaifiyar abeeda Babu Wanda Bai gama sanin matsayin kaunar Dake tsakaninsu ba Dan haka Babu Wanda yayi yunkurin hanawa saima tsayuwa da sukai akan inganta rayuwar asmaun duk da tana kauye Dan haka itama asmaun Bata da tamkarsu.

    Nisansu Bai hanasu zama abokan sirrin juna ba Dan kuwa Babu matsalar Asmau da abeeda Bata saniba kamar yanda asmaun Babu damuwar abeeda da Bata saniba.,

    Rashin samun haihuwar Asmau da wuri yasaka Abeeda ta samu Samar dauko asmaun ta tafi da ita ganin Wani likita a porthcrt,

    Da farko hankalin Asmau Bai tashi ba da rashin haihuwarta ba Amma ganin yanda abeeda ta damu ta kwallafa Rai Akai sai hankalinta ya tashi Wanda yasaka dole aka tsaya aka ringa yawon asibiti da asmaun.

    Kamar yanda hausawa sukace ita dai kaddara yashi ce ko an dunkulata Bata dunquluwa, Abeeda ta tsaya da karfi da dukiyarta an nemawa Asmau lafiya Bata samu nutsuwa da Kwanciyar hankaliba Saida Asmau ta wayi gari ta samu ciki a jikinta.

    Cikin Asmau nada wata biyu Aka kulla Auren Abeeda da Wani ‘dan babban Aminin mahaifinta Aleeyu Muh’d Talba Wanda dagashi har ita bawai suna son juna bane Amma dayake Auren na connection ne Basu damu ba.

    Auren Abeeda da Aleeyu aure ne na fitowar Rabon haihuwa kawai Wanda Allah ya kaddaro a tsakaninsu sbd Auren da wata uku Allah ya karbi ransa sanadin jinyar ciwon cikin kwana Daya kacal.

    Bayan rasuwarsa ranar da Abeeda ta fita takaba ranar Asmau ta haifi AmatulMaleek wadda taci sunan Abeeda Amma suke kiranta da AmatulMaleek din sbd shine sunan da mahaifinta yafiso din Dan haka take amsa sunan AmatulMaleek din Amma a rubuce Abeeda AmatulMaleek ne sunanta.

    Abeeda Bata samu zuwa haihuwar AmatulMaleek ba sbd itama tana fama da tsohon ciki me tsananin wahala Wanda ya Sakata shiga ciwo sosai.

    Asmau duk da jegonta bata zaunaba haka taxo ta zauna jinyar abeeda harta samu sauki itama ta qarasa watanninta ta haifi ‘ya mace itama take aka Saka mata sunan ASMAU Amma ana kiranta da Husnah.

    A ranar da akai sunan Husnah a ranar aka daura Auren Abeeda da ASHRAF MUH’D TALBA ‘dan uwan Aleeyu Wanda suke Yan biyu batareda sun taba ganin juna ba Amma hakanan zuciyar abeeda tafi kamuwa da son Ash Talba akan Aleeyu sedai Kuma halin Aleeyu ya bambamta sosai da ASH Dan haka zamanta dashi yafara Bata wuya ta bangarora da dama.

    Wanna shine damuwar data fara Sako Auren Abeeda a gaba sedai Kuma Asmau ta tsaya sosai gurin Bata qwarin gwiwa Dan ta fuskanci aurenta ta tsaya ta riqe mijinta da kyau.

    ASH baida raayin Auren mace biyu Bai taba shaawan Hakan ba Dan haka a zuciya da gangar jikinsa ya amshi abeeda dari bisa dari sedai rashin fuskantar halin juna da sanin juna yanda ya kamata yake azabtar da Auren nasu Amma Kuma kasancewar sunada ilimi dukkaninsu ya Saka Basu taba nunawa junansu gajiya ko gazawa da zamanba bare juna ba,

    Matsalar datafi quntatar da Auren nasu shine rashin iya kulawa da soyayyar Auren Abeeda wadda Sam ta kasa yanda zata iya shiga zuciyarsa ta mallakesa ta hanyar kauna ko soyayyarta.

    A idanuwansa tana iya hango tsananin girmamawa ne kawai yake mata Babu wata soyayyarta bayan Hakan Dan haka ta dage sosai dan ganin ta mallakarwa kanta zuciyarsa da Babu kowa a cikinta.

    A duniya da yawa basusan ba Ash ne mahaifin Husnah ba kaman yanda Babu Wanda yasan matar Ash din bashine ya fara aurentaba.

    Zamansu me dadi da Kwanciyar hankali da wayewa suke rayuwar aurensu Dan haka ya dauketa daga kasar suka tafiyarsu inda yake rasuwarsa tareda mahaifiyarsa da kanwarsu qwalli Daya wadda ta kasance tana gida bayan auranta Daya mutu ta fito da saurayin ‘danta Wanda ya girma sosai Yana karatu Shima.

    Duk Nisan da Asmau tayi da Abeeda Hakan Bai Hana ASH yiwa Asmau farin sani ba sbd shaquwa da kusancinsu hakama da kansa ya fahimci irin girman junansu a zuciyarsu Dan haka yake respecting Asmau sosai tareda Mai gidanta Wanda yaso ya taimakawa sosai Amma Babah din yaqi yarda da Hakan Dan haka sai kawai mutunci da kusanci suka ya shiga tsakaninsu duk da Hakan ya taimakawa babah din sosai.

     

    Bayan shekaru sunja sosai a rayuwar kowannensu Abeeda tayi nasarar shiga zuciyar ASH sedai batada tabbacin ta mamaye zuciyar ne duka Amma ko a iya inda ta samu din a zuciyarsa tanada tabbacin babu Wani guri da wata zata samu shiga sbd ita kanta gurin data samu a zuciyar tasa sai data share shekaru a cikin auren kafin ta samu wannan gurin a zuciyarsa Dan haka ta tabbatarda zuciyar ASH ba guri me saukin samu ga kowace mace ba.

    Baida raayin mata kaman yanda baida Wani raayi ko time na abubuwan dasuka danganci soyayya bayan ta matarsa Abeeda wadda yake ganin iya sonta da ita din ta ishesa a rayuwarsa Bata buqatan Qari sbd baida Wani gurin bawa wata macen a rayuwarsa kwata kwata.

    Rayuwar Abeeda ta sauya ne ta tashi daga arzikin mahaifinta ta koma arzikin mijinta Wanda ya take ya rufe arzikin mahaifinta datake ganin yanada ta gado,
    A familyn ASH kusan shi kadaice me irin wannan arzikin duk da mahaifiyarsu ma nada arzikin Amma ba kamar na mahaifinsu da suka gada ba.

    ASH da Aleeyu mahaifinsu daban Wanda bayan rasuwarsa mahaifiyarsu tayi aure ta haifi Aysha wadda ita mahaifinta daban dasu Amma dai mahaifiyar tasu Daya ce.

    Sune masu arziki sosai sbd mahaifinsu shine me arziki sabanin Aysha da nata mahaifin baida Wani abun bayan rufin asiri.

    Da wannan qyashi da Jin zafin Aysha ta tashi a cikinsu har Allah yasa Akai mata aure ta haihu ta fito daganan aurenta uku tana fitowa karshe dai ta hakura da auren sbd takasa samun masu iri arzikin ‘dan uwanta ASH dashi kadaine yanzu ya rage mata hakama ummansu ta rasu Dan haka ta tattara itada ‘danta NAUFAL ta suka dawo karkashin ASH tamkar shine Uba mahaifin Naufal duk Wani gata da Jin dadi Babu abinda basa samu a gidan karshe dai kusan gidan ya dawo hannun mom Aysha kaman yanda ake kiranta da girma yazo mata sbd ta girma Abeeda sosai ba laifi Dan haka kusan gidan idan aka cire Mai girma me gidan the grt ASH TALBA mom Aysha itace me fada a ji Dan kusan kamar matsayinsu Daya agidan Ash itada abeeda.

    Rayuwar mom Aysha a cikinsu ya Saka duk yanda kusancin Asmau da abeeda yake yafara raguwa sbd mom Aysha Asmau ce macen datake Jin har cikin zuciyarta Bata kaunar kusantuwarta da Yan ahalin gidan Dan haka tsauri da kaidojin mom Aysha akan Asmau yasa taji Bata shaawan zuwa gidan Abeeda Koda suna gari Dan haka da wannan kusancinsu yafara raguwa dakuma manyanci Daya zo musu dukkaninsu.

    Bayan haihuwar husnah Abeeda Bata sake haihuwa ba Saida manyanci yaxo musu ta haifi ‘da namiji Wanda ya kasance a gurin ASH TALBA shi kadaine jininsa Amma Kuma a zuciyarsa haydar din da Husnah matsayinsu Daya Dan kuwa ita kanta Husnah duk da ta girma batasan ba ASH TALBA mahaifin Daya haifetaba.

    AmatulMaleek tanada shekaru goma sha uku a duniya maamah ta sake haihuwar ta haifi qaninta Abdulhameed Wanda harya girma baisan mahaifinsa ba tinda kafin sunansa Babah ya rasu yabarsu cikin halin qaqanikayi.

    Rayuwarsu ta zama me Wani irin babban gibine da basusan tayaya zamu cikesaba ko samun me cike musu shi,
    Qunci da wahala da yunwa da azaba tareda hantara suke rayuwa acikinsa har Abdulhameed ya girma yayi wayo,
    Tunda tagama primary karatunta ya tsaya,
    Abdulhameed kuwa karfi da yaji ya zama kamar almajiri sbd ko suturar da zai Saka basuda ita sai abinda Allah ya Basu kawai suke Samu.

    A gidan kaf Babu Wanda yake iya Basu abincim da zasuci sbd kowa ta kansa yakeyi kowa na fama da rashi.

    Madame abeeda wadda a yanxu matsayinsu da sunansu ya zarce na Baya sbd matsayin da ASH yake dashi a gurin Al’ummar Dake tsananin son ya tsaya musu a matsayin gwamnan jahar Amma baida raayin siyasa duk da Hakan jamaa sosai sukeyinsa Dan haka kusan Babu Wanda baisan the grt ASH TALBA ba.

    Rayuwarsa data iyalansa kwata kwata baa qasar yake yinta ba sai dai yakan Fi iyalan nasa zuwa Dan haka jamaa sukeyinsa sbd taimakon dayake bayarwa kaman baisan zafin dukiyar ba Dan haka manya da yawa mutanensa ne hakama talakawan ma mutanensa ne hakama masu kudin Dan haka kowa yinsa yakeyi duk da da yawa baisanma sunayi ba Amma Kam sosai aketa Daman gwagwarmaya da rigimar shi akeso amma Sam Baya raayi.

    Ta bangaren matarsa Abeeda kuwa wadda duniya ke kira da Madame abeeda Talba tini rayuwarta data ‘yayanta ta zama abin kallo daga nesa sbd tsaron da ake Basu bana wasa bane sbd ASH Bai hadasu da komai nasa ba Dan haka a yanzu tsakaninta da maamah aike ne kawai Shima sai can idan lokaci me tsayi yaja Dan haka itama maaman ta hakura ta rungumi marayun ‘yayanta.

     

    *****Bayan rasuwar Babah da shekara biyu kawu bello ya aure Maamah din wadda bayan wahala da ukubar data ringa sha a hannun kishiyoyi Babu abinda suka Qaru dashi itada ‘yayanta
    Ahakan suka ringa Shan kuncin rayuwa har kawun ya gaji ya saketa sbd yace bazai iyaba lalurar tai masa yawa Dan haka dai anan cikin gidan Akai auren anan Akai sakin taci gaba da gwagwarmaya itada ‘yayanta Wanda tanaji tana Gani Abdulhameed yakoma almajiri AmatulMaleek kuwa haka take zaman gidan Bata taba barinta fita ba Koda zuwa cikin gidan sbd yanda gidan yake sake zama hadari sosai ga duk Yan matan gidan da Yara qanana ma Dake tasowa duk da yawa sun lalace a tsakaninsu batareda sanin iyayensu ba.

    AmatulMaleek tinda tafara wayo rayuwarta ta zama tamkar kurma sbd rashin magana tinda basuda abin magantuwa akansa Dan bayan tarin kunci Babu komai a rayuwarsu Dan haka ta taso a miskilar gaske Wanda Hakan yafiwa maamah dadi da farin ciki sbd kullum kukan maamah a gaban Allah shine yanda zata bawa ‘yayanta kariya daga masifar gidan musamman AmatulMaleek datake mace.

    AMATULMALEEK
    Regular 700
    Vip 2k
    0022419171 Access bank Maryam sani
    09033181070

    #MAMUH#
    #LA HOT
    #LIFE
    #ASH TALBA
    #AMATULMALEEK
    #NAUFAL TALBA
    #MEERAH HERBS
    #ABOKIYAR NISHADI TV CHANNEL

  • Amatulmaleek 8

    Amatulmaleek 8

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story #

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    8
    Koda su Husnah suka dawo gidan take masu aikin gidan suka sake shiga taitayinsu sbd mum Aisha da Sam Babu sauki a lamarinta Dan kuwa ko barin kaya baa da iKon yi zaka iya rasa aikinka a gidan Dan kuwa itace me fada aji,itace me iKon zartarwa akansu.

    Husnah ma kusan halayenta tafi dauka Dan itace tamkar madubinta Kuma yar lelenta Dan haka kusan halayenta ne Husnan ke dauka duk da yanxu ne take zama Yan mata Amma dai halayenta a Fili suke Tin yanzu.

    Koda maamah taga dawowan Husnah sosai ta shiga farin ciki sosai da ganinta ta rungumeta tana ambatar sunanta cikin tsananin kaunarta tana tambayarta ya gajiyan hanya.

    Amsawa Husnah tayi tareda gaida maamah din Dan kuwa duk Wanda yake tareda mahaifiyarta Kona sati ne saiyasan maamah a bakinta da matsayinta a zuciyata Dan haka tasan wacece Maamah din a gurin mommynta.

    Maamah datake farin cikin ganin Husnah itace da kanta ta gyare mata dakinta fes yanda takesonsa tareda komawa kitchen aikinta,

    Ta sanar da AmatulMaleek da Abdul ‘yarta Daya ta dawo wato Husnah.

    Dayake Abdul shi dinma dayake qanqani yasan sunan Husnah a bakin maamah hakama shi a farko ya dauka da gaske ita din ‘yar maamansu ce sbd yanda take fadarta har cikin zuciyarta da gaskiar kaunar datake mata.

    Amatu da Abdul sunji farin cikin dawowar Husnah dan haka suka kwana da Shirin da safe zasuje su mata sannu da zuwa kamar yanda maamah tace.

    Washe gari maamah din da kanta sukaje tare takaisu suka gaisa da Husnah wadda Babu laifi ta Dan sake musu din Su Daman ba saurin sabo ne dasu ba Suma Dan haka suna barowa dakinta gurin mommy Abeeda sukaje suka gaidata itama cikin kulawa da kauna ta amsa musu kafin suka fito suka tsaya gurin Haydar Amatu ta shiryasa bayan Maamah tai masa wanka Yana ihun bayason Amatu ta shiryasa sbd kada ta gansa ba kaya Amma hakanan suka dannesa itada Abdul harta shiryasa suna masa dariya ya fito yaci abinci Suma anan suka ci abincin dole sbd mommy Abeeda din da Husnah suna kan dining hakama Haydar Dan haka dole akace Suma suzo su zauna.

    Dayake Amatu nada hankali sai Bata Wani sake taci sosai ba kamar yanda Abdul ya saki ciki yaci ya koshi Shida Haydar suna wasa da dariya Wanda Hakan ne ya Dan raya gurin daga tsit din Daya dauka.

    Suna Hakan mum Aisha ta fito take suka nutsu Amatu tayi saurin gaisheta tana sauke kanta qasa daga kallan dataga mum Aisha din na mata Wanda ya Sakata Jin jikinta na sanyi.

    Husnah ce ta gayar da ita tana sake fuska sosai.
    Itama mum din murmurshi tayi tana sake fuska tafara amsa gaisuwar Husnah kafin ta amsa ta Amatu data cire tsammanin zata amsata.

    Abdul kuwa Sam baima San da ita ba saida tayi musu magana cikin yar tsawar data Saka Abdul sauka daga kan dining din Yana dawowa gefen Amatu idanuwansa akan mum Aisha din wadda kyanta da fadan datakeyi suka sakashi yin shiru tsoronta na shigarsa.

    Daga wannan lokacin suka nutsu sama sama suka qarasa suka koma inda suka fito.

    Bayan tafiyarsu Babu Wanda yace komai sai Haydar Daya gama Shima ya sauko khaltume ce tazo ta tafi dashi zuwa inda driver ke jiran fitowansa ya shiga mota aka tafi dashi zuwa school.

    Koda suka koma daga Amatu har Abdul Babu Wanda ya fadawa maamah abinda ya faru saima zamansu da sukai daki suna abubuwansu.

    Koda Rana tayi zaa tafi Kai Haydar Islamic school taredasu mommy Abeeda tace atafi su fara karatun kafin su tashi komawa.

    Murna sukai sosai Dan kuwa Daman sunaso fita su Dan ga gari.

    Su hudu aka tafi dasu harda Husnah wadda ta kwana biyu Bata zuwa sbd tafiyarsu.

    A motar daga Abdul sai Haydar ne keta surutu suna farin cikin zuwan nasu makaranta tare,
    Itama Amatun tana farin cikin zuwan makaranta duk da Babu Wani sakewa tsakaninta da Husnah Amma dai tinda gasu Haydar tasan batada kadaici.

    Koda suka Isa makarantar tini akaiwa su Amatu komai Dan kafin zuwansu Akai wayar zaa kawosu.

    Hatta uniforms da littafai da jaka a makarantar aka Basu sai gasu sun saje da sauran dalibai ‘yayan masu fada aji.

    Dayake sunada karatun addininsu sai Basu Wani muzanta ba a cikin mutane aka Basu ajinda yakeda daidai da karatunsu
    Abdul cikin saa aka basa ajinsu Haydar Dan haka murnarsu ta Qaru,
    Amatu ma ajinsu Husnah aka kaita.

    Wuni Amatu tayi a makarantar a kame sbd rashin sabo da shiga mutane sabanin Abdul da kamar Daman anan yake Dan kuwa Haydar tini ya jonesa da abokansa suka ringa murnan samun sake.

    Koda yamma tayi sosai aka tadasu driver na gate Yana jiransu Dan haka suka shiga mota suka dawo gida.

    Koda suka dawo maamah taga yayanta cikin uniform din makaranta Jin tayi jikinta yayi sanyi da farin cikin ganinsu a Hakan tana tausayinsu yanda suke farin ciki gashi dole zasu koma inda suka fito.

    Da farin cikin da daddare suka ringa Bata labarin makarantar datake kamar a turai sbd kudinta da tsarinta.

    Ita dai murmurshi kawai takeyi tana sauraronsu har dai aka gama dokin Abdul yaci abinci yayi bacci.

    Amatu kuwa uniform din nasu ta nade musu ta tattara littafansa Daya barbaza ta mayar a jaka kafin itama taci abincin ta sukai sallar ishai da maamah ta kwanta
    Maamah kuwa ficewa tayi ta tafi gurin ‘yar uwarta Dan sake nuna godiyarta akan abinda take mata.

    ********Ahankali su Amatu suka Dena dokin makarantar har suka fara sabawa yanzu Kam ba Doki karatu kawai Wanda kusan duk su biyun sunfi Husnah da Haydar kokari da Maida himma sbd ganin sukeyi sukam sun samu babbar sa’ar rayuwa ta zuwa makaranta bayan Basu tana Saka Rai da shiga kowace irin makarantar ba.

    Husnah Sam babu Wani sabo sosai har lokacin a tsakaninta da Amatu Amma dai ta bangaren karatu hakanan take sakewa su koyawa juna ganin Amatu tafita saurin fahimtar karatun na islamiyya.

     

    ***ASH TALBA ya dawo kusan so biyu Yana sake tafiya Dan haka sudai su Amatu basuma San ya dawo gidanba harya komaiba sbd Basu taba ganinsaba Dan bayan ‘yayansa da matarsa sai mum Aisha Babu me shiga bangarensa Dan haka ko maamah dataje suka gaisa Saida yabada damar Akai mata iso tazo har palonsa suka gaisa Kuma sun Dan jima suna magana duk da rashin son Jan zancensa Yana tsayawa Dana gida su samu lokacinsa.

    Karatun su Amatu yafara daukan harama sbd karfin maamah da Abeeda taci akan komawarsu ba yanzu ba.

    Kowanne dare a palon su Husnah suke zuwa su Hadu su hudu suyi karatunsu na islamiyya harma da karatun Boko dasu Husnah din suke koyawa su Amatu Dan haka sukam su Amatun suka Bude Kai suna koya Dan daga Amatun har Abdul din suna shaawan na bokon.

    Ahankali ahankali sabo sosai ya shiga tsakaninsu duk da halin Husnah din akwai wuyar shaani Amma dai sanyin halin Amatu da zurfin cikinta yasaka take shanyewa zaman nasu na tafiya,

    A yanzu Husnah da batada qawaye Amatun ce kawarta har islamiyya har gida Dan haka sai duk abinda ta cire na kaya ko abun buqata da bataso sai tana bawa Amatun tareda nuna mata sai tagama da abu take Bata Dan nuna itace a qasanta Kuma take cin alfarmarta Wanda duk lokacinda takewa Amatun Hakan Bata taba Jin komai ba ita sbd maamah Dake nuna musu Husnah da Haydar Yan uwansu ne datakejinsu a ranta kaman yanda take jinsu.

    Kaf a cikin gidan mum Aisha ce wadda Basa zuwa ko inda tabi tabar kamshinta sbd tsananin fadanta da zafinta akansu musamman mahaifiyarsu Dan haka kusan Yan aikin gidan biyu ta sake sallama Dan haka maamah karfi da yaji ta koma ‘yar Aiki a gidan Kuma aikinma Wanda ma’aikata uku zasuyi ita aka barwa tanayi.

    Duk wannan wahalar da maamah din keyi haryanxu Bata taba Jin haushi ko bacin Rai ba,tsakaninta da Allah takeyi Kuma ko zatayi aikin dayafi wannan a gidan Abeeda batajin zataji Wani abu na dacin zuciya ko gajiyawa sbd Abeeda ta inganta rayuwarta tin kuruciyarsu har yanzu dasuka manyanta gashi Kuma yanzu tana inganta mata ta yaranta.

    Waya aka siyawa maamah tana waya da Yan can kauye tana Jin lafiyarsu da Kuma abubuwan Dake faruwa na zumunci da haihuwar da aketa sake yi a cikin Yan watannin da batanan
    Ahakan ne katsam aka sanar da ita rasuwar uwar gidan kawu bello wadda take tamkar Yaya agareta Dan haka dole suka fara Shirin komawa gida.

    Acikin gidan ASH TALBA Mansion Babu Wanda hankalinsa Bai tashiba da Jin maganar tafiyar maamah gida sbd baiwar data komawa kowa a gidan hatta masu aikin gidan aiki suke Sakata Kuma tayi,hakama tsaftar sashen Abeeda tini ya dawo hannunta hakama cimar Abeeda din,
    Ta bangaren mum Aisha ma Amatu ce sabuwar me mata shara duk da Bata Wani iyaba Amma so take ta koya sbd a Qaru dasu Suma,
    Su Husnah ma dasukai sabo da sakewa sosai ayanzu suyi wasa da guje guje harma da wasan ruwa a swimming pool dasu Amatun duk sai sukaji jikinsu yayi sanyi Dan haka suka roki mommynsu ta Hana maamah tafiya Amma dole saita tafi.

    ASH Baya Nan zasu tafi Amma Kuma Saida ya Saka aka Basu kudin Daya bawa maamah tsoro sosai Dan haka aka Bude mata acct kafin tafiyarta aka Saka mata sauran suka riqe hakama Abeeda ta Basu kudi sosai itama bayan tarin kayan sawa da aka basu Wanda duk kayansu Husnah ne Dana Haydar aka bawa su Amatu itama an bata kayan sawa sosai Dan haka kaya Niki Niki sukai bankwana suka tafi ana kewarsu.

    Bayan tafiyarsu har ciwo sosai Haydar ya kwanta kafin yaji sauki yakoma rayuwarsa ta Baya Babu abokin wasa Babu abokin fira bare karatu.
    Itama Husnah bataji dadin tafiyar tasu ba duk da Babu abinda takewa Amatun a tarensu bayan Gori da nuna mata kamar komai na rayuwarta saita kashesa tagama dashi take bata.
    #MAMUH#
    For more pages follow me @Mamuhgee arewabooks

    *_AMATULMALEEK_*
    By Mamuhgee
    And
    *_YANCI DA RAYUWA_*
    By Hafsat Rano
    Na kudi ne
    For more page ku biya
    500 for littafi Daya
    1k for duka books din biyu
    at👇
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

  • Amatulmaleek 3

    Amatulmaleek 3

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    3
    Maamah Bata taba yin qasa ko sanyaba akan tsaro da tarbiyarsu kaman yanda babansu ya dage ya tsaya kafin rasuwarsa duk da ta Wani bangaren dukansu har ita suna cikin hadari a gidan Dan ita kanta ansha shigowa bangarensu da dare da niyar a afka musu ko ita ko AmatulMaleek din Amma dai Allah na tsaresu shiyasa duk tsanani basa fitowa fitsarin dare gudun a keta musu haddi basuda abin yi Dan duk Wanda aka Bata gidan bayan hakuri Babu abinda zaiyi bawai Kuma Dan baa San masuyi din ba kawai dai bakada iKon magana ne ayita rigima da iyayensu ana Allah ya Isa da tashin hankali karshe dai cuta ce anriga an cuceka.

    Maamah Bata taba Dana sani da damuwar aure a gidan taro me tsanani ba irin wannan sai yanzu sbd illarsa tafi dadinsa da albarkarsa yawa,
    Amma dai tinda Allah yasa rabonta na ‘yaya anan yake Babu yanda zatayi da kaddara bayan dagewa.

    Ko islamiyya Bata barin AmatulMaleek tafiya ita kadai kullum tare suke zuwa lokacin tashi nayi taje su dawo tare duk da ta Dan girma Amma dai hankalinta baitaba Kwanciyar tabarta taje ita Daya ta dawo ita Daya sbd yawun da samarin gidan suka hadewa ‘yartata Dan haka tasan ko a hanya zasu iya binta.

    Ita kanta AmatulMaleek tasan rayuwarta a gidan tana cikin hadari Dan haka take kiyayewa tareda kame kanta Babu inda take taba zuwa Dan haka wasu da yawa a kauyen Basu Santa ba sbd Bata fita koyaushe tana dakin maamah ana tsaronta kamar wata gwal me tsadar gaske.

    Abdulhameed Daya kasance qaninta shi Kuma sai ya zama kowa shi ya sani sbd shi Kam yawonsa yake zuwa yi tinda bara yakeyi duk da Shima Maamah din na kokari akansa Amma dai tafi Maida hankali akan Amah,
    Yaron ya kasance Yana so da shaawan karatun Boko Dan haka kullum saiyaje makarantar bokon kauyen ya shige cikin Yara
    Wannan dalilin ne yasa ake yawan kawo kararsa ga kawu bello sbd sunyita korosa Amma Baya Dena zuwa Dan haka kawun keji Asmaun da ‘yayanta sun ishesa Daman kuka aure yakeson qarawa duk da manyancinsa sosai Dan haka so yake Asmau ta tattara tabar gidan ya samu bangaren sbd ya aje yar bazawarar da zai auro.

    *****
    Asmau tayi shekaru sosai rabonta da Abeeda a idanuwanta sedai aike Wanda Wani lokacin har mantawa akeyi dasu kafin su samu Wanda daga Yan Aiken ne da aka aje duk wata sukai musu abinci Amma Sam basa kaiwa sai bayan watanni watanni suke kaiwa ganin madame din Bata qasar sai Suma suke tasu zalamar.

    A yanzu da AmatulMaleek tafara zama yar budurwar yarinya tini hankalin maamah yabar jikinta Bata bacci Batada nutsuwa kowane dare Bata iya baccin kirki sbd tsoron rayuwar da ‘yarta zata shiga a yanzu da samarin gidan da babu nagari zasu iya cewa suna son aurenta kuma tasan batada abinda zai Bata damar hanawa tanaji tana Gani zaa lalata mata rayuwar ‘yarta gashi kowannensu yaga budurwa tafara tasawa a cikin gidan sai suce sunaso gashinan da qananun shekaru sunata Tara mata daga me mace biyu Se uku sbd suna cewa sunaso akeyin wuf ayi auren sbd karfafa zumuntar da Babu so ko jin qai a cikinta.

    ******
    Iyalan ASH TALBA sun sauka a kasar Nigeria a bazata sbd rasuwar mahaifin mom Aysha wanda yake tamkar mahaifin ASH din Shima Dan haka dolensu suka dawo Nigeria.

    Saukarsu da labarin rasuwar tasa yasaka Maamah shiryawa dole itada ‘yayanta sukai Shirin tafiya duk da batada kudin mota Amma hakanan ta siyar da akuyoyinta guda biyu datake ta Reno sbd auren AmatulMaleek idan zaizo kafin lokacin sun qara hayayyafan da zasu isheta yiwa AmatulMaleek din Wani abu.

    A wulaqance aka siyesu sbd anga tanason kudin amma Bata damu ba sbd zuciyarta Sam bamai Saka damuwa bace hakama Allah yayi mata sanyin hali da tsananin hakuri me yawa Dan haka baka gane ko ka quntatar da ita sbd tana hadiye komai da sanyin halinta.

    AmatulMaleek da batajin dadin tafiyar tasu Sam Amma Bata nuna ba itama sbd kusan halin mahaifiyarta itace ta dauko sak na boye damuwa da hadiye kowanne bacin Rai da sanyin hali Dan haka itace da maamah din sukai wankin kayansu da zasuce tsumma ne ma Amma Kuma su suke dasu Dan haka dasu zasu.

    Abdulhameed kuwa farin ciki yakeyi sosai sbd baitaba barin ko wajen kauyen ba bare zuwa babban birni ba dukda baimasan me birnin ke nufi ba Dan shi Kam asalin bafulatanin kauye ne.

    AmatulMaleek din ma dai kana ganinsu kaga fulanin kauye sun fito Amma Kuma nutsuwarta ke Hana duhun kansu fitowa.

    Ranar da zasu tafi gidan kaf murna sukeyi su tafi sbd bangarensu da kowa keso saikace ce musu maamah tayi bazata dawo ba,
    To sukam Koda zata dawo din to idan ta dawo sedai ta koma zauren gidan da zama Dan kuwa duk Wanda ya shiga baida niyar fita idan ta dawo tinda Daman Neman ta tafin sukeyi,
    Qalilan ne masu son zamanta gidan sbd AmatulMaleek dasuka qwallafawa Rai akan tana Isa aure zasu aureta su jefa cikin matansu.

    Duk Wani Shirin tafiyarsu sun kammala Dan haka washe gari tinda asuba suka hau mashin Abdulhameed na gaba maamah da AmatulMaleek a Baya suka fita kauyen zuwa kauyen gabansu da acan ake Hawa motar zuwa babbar hanyar titi da acan Kuma zasu hau motar zuwa cikin state din kafin daga can su hau motar zuwa Abuja.

    Tinda suka hau mashin din Abdulhameed ke washe Baki cikin tsananin farin ciki sbd Bai taba Hawa ko Keke ba bare mashin sai yau din.

    Tafiya me Dan tsayi sukai kafin suka Isa kauyen kurmawa,
    Saukowa sukai daga kan mashin din maamah na ajiye jakar kayansu gefe
    Ita Kuma AmatulMaleek Abdulhameed Dake zare idanuwa Yana kallan koina ta kamo hannunsa suka dawo gefen maamah din.

    Kudinsa Maamah ta Ciro ta basa na mashin ya juya Yana musu Allah ya kiyaye Abdulhameed ne kawai ya amsa da Amin cikin murna da farin cikinsa da Baya boyuwa.

    Wata motar a Kori kura suka nufa wadda ita kadai ce Daman a kauyen take fita da mutane Dan haka kusan Tama cika Dan haka ba Bata lokaci aka kama su Abdulhameed din da AmatulMaleek aka Dora a sama kafin Maamah ta miqawa Amatu jakarsu tukuna itama ta tattara zaninta ta kama motar ta Haye ta zauna gefen ‘yayanta suna Dan gaisawa da sauran mutanen Dake bayan motar a Bude kowannensu kura ta gama rife koina jikinsu kaman anyi juyen yashi a jikinsu sbd iska da akeyi.

    Tafiya suka fara Babu me magana acikinsu sai Abdulhameed Dake kalle kalle har bacci ya daukesa a jikin AmatulMaleek wadda itama tafara komawa kamar bokanya sbd iska da qura Dayake Kara sauya kamannin kowa Dake motar.

    Tafiya me tsayi Nan ma sukai sosai kafin suka iso babban titin hanyar shiga kauyukansu masu shegen Nisa.

    Saukowa sukai kowa qafafunsa sunyi sanyi gashi zuwa lokacin Rana tayi Dan kuwa sha Daya saura Dan haka komai Basu tsayaba ruwa kawai da biredi kawai maamah ta Siya musu suka fada wata motar da zata kaisu state acan su samu shiga motar Abuja.

    Babu Bata lokaci motar ta cika Dan haka suka sake daukan hanya.

    Biredin data Siya musu ta rarraba musu suka fara cin abinsu hankali kwance.

    Abdulhameed duk rawar murnarsa fara komawa ciki tayi sbd zuwa lokacinda suka Isa babbar tashar yola tsoro kamasa yayi sosai sbd Bai taba ganin mutane hakaba sosai da hayaniya anata ihun Neman passengers ta bangare daya ga masu talla takoina suna ihun azo a Siya abinda suke tallan,
    Hakama a Wani gefen fada akeyi sosai a cikin tashar..

    Ba Abdulhameed ba AmatulMaleek ma kanta tsoro ne da firgici me tsananin gaske ya shigeta Dan Basu Saba haka da mutane da wannan hada hadarba Dan haka dukkaninsu qanqame hijabin maamansu sukai ita Kuma ta riqe hannuwansu gam tana Basu kariya har suka samu motar da zata daukesu zuwa Abujan suka shiga ta rungume ‘yayanta tanajin hakanan zuciyarta na karyewa da tafiyar Kuma a yanzu sbd so da dama duk halinda take ciki a kauyen sai tanajin yafi mata nutsuwa akan zuwa birnin duk da wannan tafiyar taji hankalinta ya kasu kashi biyu zatayi ne sbd magana da Madame Abeeda ta rage nauyin zuciyarta da quncin Daya dabaibayeta akan rayuwar AmatulMaleek da batasan Yaya zatai da ita acikin zuriar Sanda Fulde ba.

    Shiru tayi tareda Nisa a tinanin rayuwarta tin kuruciya da irin gatan data samu a Baya da rayuwar data taso aciki har kaddararta ta sauya mata hanya zuwa kauye da auren kauye Wanda ayau ta samu kanta a tsaka me wuya sbd rashi na Miji Kuma uban ‘yayanta Wanda da ace Yana Raye da bazata samu Kanta a wannan halin na kakanikayi da ‘yayanta.

    AmatulMaleek Dake jin tsoro me tsananin gaske a duk Nisan da suke qarawa na tafiyar shiru tayi jikin mahaifiyarta tana Jin zuciyarta na shiga yanayi na rashin murna da tafiyar dakuma yanayi na sanyi Dan haka ta rufe idanuwanta tana barin baccin datake ji daukanta.

    Kallansu maamah ta sake bayan dukkaninsu sunyi bacci jikinta ta shafa kansu su dukan tana Bude zuciyarta cikin amincin Allah tace

    “Allah ya kawo madaukakin haske da girma a rayuwarki AmatulMaleek keda ‘dan uwanki,
    Allah yasa ki zama tauraruwar macen alfahari a duk inda rayuwa zata kaiki,
    Yakuma Baki mijinda zai Miki Mafi girmamman so me tsaftan gaske..Amin”

    Numfashi ta ajiye ahankali itama tana lumshe idanuwanta sbd zuciyarta Dake jin kaman tana gazawa da gwagwarmayar.

    ****
    Tafiya yankin azaba kaman yanda aka fada,
    Sai yamma lis suka sauka birnin Tarayya,
    Daga maamah har su duka kafafunsu sunyi Wani irin nauyi da riqewa Dan haka daqyar dukkaninsu suka iya tsayuwa bayan sun fito motar zuwa lokacin Abdulhameed da AmatulMaleek sosai suke Jin tsoron mutane Dan haka a maqale suke da maamah wadda itama tasan bazata iya Kai kanta gidan ASH TALBA ba Dan haka numbern Madame Abeeda datake cikin kanta kamar hadda ta karanto aka kira musu ita cikin rashin saa akaita kira baa dagawa sbd basa daga bakuwar lamba Dan haka dole guri suka samu a tashar suka zauna ana sake kira lokaci bayan lokaci.

    Yunwa da wahala ta Saka AmatulMaleek ringa Amai a gurin har Saida dole aka nemi guri aka kwantar da ita sbd take zazzabi ya rufeta.

    Sanyi jikin Maamah yayi ga Abdulhameed Shima duk yayi laushi sbd azabar tafiya da yunwa Dan haka duk taji hankalinta ya tashi damuwa na rufeta ta zuwan nasu.

    Sallar magrib ake kokarin shiga Wanda yaketa kira musu numbern ya ringa mata fada Yana cewa wayace suzo batareda sun sanar da inda sukazo din ba?
    Basusan baa zuwa Kai tsaye gidajen manya ba batareda an sanar musu ba sbd basason damuwa da takurar talakawa da dangin kauye.

    Shiru Maamah tayi sbd zuciyarta gabaki daya Bata mata dadi jikinta yariga yayi sanyi gaba Daya Dan haka batama San me zatace ba bayan sauke Kai kasa.

    AMATULMALEEK
    Regular 700
    Vip 2k
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070

    #MAMUH#
    #AMATULMALEEK
    #ASH
    #MADAME
    #FRIENDSHIP
    #LA HOT
    #ROMANCE
    #LOVE
    #ABOKIYAR NISHADI TV CHANNEL
    #MEERAH HERBS

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 29

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 29

    Episode 2️⃣9️⃣*

    Zaune yamma tan Ammi suke a palon sama na ɓangaren Ammi, suna ta hira hiyana na duba takar dun ta na boko diyana na kallon awayar Zahra amrat na karatun qur’ani, Zahra da lamrat suna kallo a makeken Tv dake manne a bango,
    da sallama yaya Khalid ya shigo palon, har suna haɗe baki wajen amsa masa sallamar kariso wa chiki yayi ya zauna saman sofa mai zaman mutun 1 murya kasa kasa hiyana tace “ina wuni yaya Khalid ya mai jiki, kakalo murmushi dole yayi kafin ya amsa mata da “lfy sister ya shirye shiryen koma wa makaranta ina fatan kungama shiri, hiyana zatayi magana Zahra ta rigata “ina wuni yaya Khalid, dawo da kallan sa kan Zahra yayi kafin ya amsa da “lfy sis love ykk, sunkuyar da kai kasa Zahra tayi dan jin sunan da ya kirata yau ta tashi daga Auta ta koma sis love.

    Yaya Khalid ya mai jiki chewar diyana “jiki da sauki sister ya aikin kai coffee, sai lokachin diyana ta ɗauke blue eyes nata daga kan wayar Zahra ta mai da kallonta izu kan yaya Khalid “hmmm ai inayi ku jiyama na kai masa kuma.. bata karisa maganar ba tayi shiru kasan chewar ta tuna abun da yaya Aryan yace mata akan idan ta kuskura ta faɗa wa wani abun da baa tambaye taba to sai ya ɓallata,

    ganin tayi shiru ta kasa karisa maganar yasa yaya Khalid ɗan sakin murnushin kaɗan dan yasan Aryan ne ya mata gargaɗi kuma hakan ba karamin daɗi ya masa ba dan diyana tana sakin layi dayawa

    “To ku shirya fa gobe zaku koma school kunji daman abun da nazo faɗa muku kenan yana kai karshen maganar ya miƙa ya nufi hanyar fita, har suna haɗe baki wajen chewa to,

    Abangaren Ahmad kuwa

    Zaune Aryan yake a gefen gadon da Ahmad ke kwanche yana kallon face nashi “bro zaka chi wani abune, ɗaga ido sama Ahmad yayi alamar a’a “why bro, why ba zaka chi abinchi ba tunfa jiya da rana baka chi komai ba haba, ɗaga ido sama Ahmad ya kuma yi alamar aa ba zai Chi komai ba, Aryan zai sake magana sai ga Bgs ya shigo tare da wani likita
    zama Bgs yayi kusa da Aryan Dr kuma ya fara kokarin sakawa Ahmad ruwa dan ta taimaka masa tun da baya chin komai,

    “Yallaboi ko dai zaku gwada maganin gida ne tun da na asibiti yaki chewar Dr yayi Maganar dai dai lokachin da yake ɗaure hannun Ahmad dan neman jijiya,
    wani dogon tsaki Bgs yaja kafin yace “Allah ya kyauta abawa ɗan uwana wan nan dattin, zan nemo kwararrun likitochi daga kasa da ban da ban suzo su du bamin shi, “Allah ya baka hakuri sir, Chewar Dr ya karisa maganar dai dai lokachin da ya gama sawa Ahmad ruwan, ya tattara kayan aikin sa ya nufi waje

    Kallon Bgs Aryan kafin yace “bro wai yanzu menene abun yi, shiri Bgs ya ɗan yi kafin yace “ban yi tunani a kai ba amma muje zuwa anjima dole musan abun yi ya karisa maganar yana mikewa, mikewa Aryan ma yayi suka fita tare

    Misalin karfe 2 na rana gaba ɗaya family sun haɗu a palo dan chin abinchin rana ban da Bgs Aiman Fahad da kuma Ahmad, shiru palon ba abun da zakaji sai karan spoons

    “My daughter ya kama ki koma gidan ki yau kinji, chewar Abba yayi maganar yana kallon Aunty farida, Mardiya salma Maryam dukka ku shirya kuma kuwuche gidan mazajen ku, “Abba daman gobe in Allah ya kai mu zan koma nariga na faɗawa dady’n junior ma chewar Aunty farida, chikin dashe war murya wadda da kaji kasan tasha kuka har ta koshi Aunty salma tace “Abba pls ka barni na kara koda 2dys ne sai mugani y jikin Ahmad ɗin zai kasanche “a’a Salma ban yar da ba gobe idan Allah y kaimu kafin karfe 1 kowache ta koma gidan mijin ta, wai ma idan kuka zauna kara masa lfy zakuyi ne? Akoi waya duk abun da ake chiki zan sanar daku ai addu’a kawai yanzu ya ke bukata awajen ku bawai kubar gidan mazajen ku, kuzo ku zauna kusa da shiba,
    Har suna haɗa baki wajen chewa to Abba Allah ya bashi lfy, gaba ɗaya palon suka amsa da amin
    shiru palon ya sakeyi ba mai magana kowa kawai tsakuran abin chin yake dan kamar magani suke jin abinchin ba dan daɗi suke chiba sai dan kar yinwa ta musu illatasu,

    “My daughter kayan nan sun miki kyau Chewar Abba yayi maganar yana kallon diyana, daman kamar jira take tafara surutu “Abba ai yaya Aryan ne ya bani ji, daman tare ya kawo mana da su Zahra shine ya kulle nawa chikin jaka, sai jiya ya buɗe min kuma Abba kaga wata dan kareriyar sar…bata karisar da maganar ba tayi shiru kasan chewar ta tuna yaya Aryan yace idan ta faɗawa wani sai daketa, jin bata karisar da maganar ba yasa Aryan sauke wata nauyayyar Ajiyar zuchiya wadda yasa Abba ɗagowa ya kallesa, kuma sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa diyana ta dakata da maganar bata karisa ba.

    saboda jin baki irin na Abba sai yace

    “My daughter ya kika dakata da maganar, a sukwane Aryan ya ɗago yana kallon Abba, harara wasa Abba ya wurga masa, da sauri ya mai da kai kasa yana ɗan murnushi dan ya gano abun da Abba ke shirin yi, “babu komai Abba kawai dai na manta me zan faɗane diyana ta faɗa tana satar kallon yaya Aryan,

    mamakine ya kama Abba daman ya tambaye tane dan yaji shin diyana tayi hankali ne ko kuma dai da saura, abun da ya bashi mamaki kuma shine yau diyana che da karya abun da bata taɓayi ba tab lallai na yar da yanzu kam diyana na Son Aryan daman zargi kawai nake Amma bari dai na sake gwada su.

    “My daughter ina malamin makaranta kun nan daya taɓa chewa yana Son kin nan?
    Ɗaure fuska diyana tayi ta ɓata rai ta turo baki ta fara magana “to ai ni Abba bana son shi soja nake so kuma ai ni tun ranan ma ban sake ganin sa ba wata kila ma ya bar makarantar, kila kuma mutuwa yayi waya sanin masa, gaba ɗaya mutanen palon sai da sukayi mamakin ɗaure fuskantar da diyana tayi har shi kanshi Aryan dan tun da suke da ita basu taɓa ganin ta ɗaure fuska ko ta ɓata rai ba ita ko dukan ta akayi tana gama kuka zata koma dariya

    “My diyana menene abun ɗaure fuska kuma? Ai ba wan da zai miki dole mijin da ki ke so shi zamu baki chewar Aunty farida “to ai Aunty farida ni bama wan da nake So sai yaya Khalid a sukwane gaba ɗaya jama’ar palon suka ɗago ido suna kallon ta musamman ma Aryan da atake idon nasa suka sauya zuwa jaa saboda kishi, itakam diyana bata ma san sunayi ba ta chigaba da magana “yaya Khalid yaya Yusuf yaya Aryan yaya Bello Aunty Zahra Aunty mardiya Aunty salma Abba Ammi Ummi Aunty amarya hiyana lamrat da amrat da ke Aunty farida sai Bappa na da Inna ta, ku kaɗai kawai nake so aduniya, wani ajiyar zuchiya Aryan ya saki, ya duƙar da kai ya ɗauki wayar sa dake gefen hannunsa kan table ɗin, yashiga latsawa

    “Hiyana karfe 3 dai dai ki dama fura ki ka womin fada Chewar Abba yana magana faɗin hakan ya miƙe ya nufi waje,
    Nmiƙewa Aryan Khalid Yusuf sukayi a tare suka fice daga palon, “haidar muje mu duba jikin yaya Ahmad ko Chewar Umar “eh ya kamata kam ya kai karshen maganar tare ta mikewa, mikewa haidar ɗin ma yayi suka nufi waje, a tare Aunty Salma da Aunty mardiya ma suka miƙe suka fice daga palon, Aunty maryam Aunty amarya suma tare suna mike suka fita, Ummi da Ammi kuwa betroom ɗin Abba suka miƙe suka shiga, palon ya rage daga aunty Farida sai su diyana.

    “My diyana daga yau idan kinje ɗakin yaya Aryan karki sake daɗewa kina jina koh? Chewar Aunty farida, “to Aunty farida ai shi yake chewa in zauna muyi magana ta karisa maganar tana turo ɗan karamin bakin nan nata

    “eh ko yache ki zauna kiche kina jin barchi sosai, jiya fa har karfe 10 ina ɗakin ku ina jiran dawo warki, amma baki da wo ba, kamar zanzo na kiraki sai kuma nache bari na bari da safe sai na miki faɗa, “to Aunty farida ba ke ki kache idan naje ɗakin na rinƙa koya masa surutu ba tun da baya magana kuma kinche ni bazai bugeni ba ko na masa surutun “eh daaa ni nache hakan amma yanzu na fasa saboda idan namiji da mace suka keɓe to na ukun su sheɗan ne,duk da zan iya shedar kanne na a ko ina, amma dai daga yau kina kai masa coffee ɗin ki dawo kinji, “to Aunty farida kawai na daiii na kai masa coffee ɗin mana tun da hakane “aa karki dai na kai masa ki chigaba da kai wa kinji amma dai da kin kai sai ki dawo, “to kawai diyana tace tare da miƙewa ta nufi hanyar fita “kutashi muje Zahra, chewar Aunty farida, gaba ɗayan su, suka mikewa a tare suka nufi waje,

    Karfe 3:5

    Da sallama hiyana ta shigo fada hannun ta riƙe da kyakkyawar kwarya ta rufe shi da pai pai, ta sanya zumbulele hijabi har kasa ajikin ta fari tas, fiskar ta sai kyalli take bawani make up da tayi asalin kayan tane kawai,ga ɗan bakin nan nata pink sosai kamar tasa jambaki, geranta kuwa kamar tayi caving, idan mutun yaga hiyana zai rantse da Allah tayi make up, amma haka fuskar ta yake,halittar Allah ne duk da kwayar idon ta Blue ne amma idon nata farine tas manya manya kamar ball, kuma idan ta kalleka kache tasa kwalli amma ba ta saba haka idon yake gata da bakin kwanche cin gashi mai tsantsi a gaban goshinta ga wani baki haɗadɗen saje a kwanche a gefen kumatun ta dogon siririn hanchin nan nata kuwa baa magana har baka yake, duk lokachin da tayi murmushi sai wani haɗaɗɗen dimple irin na Bgs ya lotsa, ga hakoranta farare tas sai wani ɗan siririn wushirya a tsakiyan hakoranta na sama

    a hankali take takawa kamar mahauniya, gaban kujerar Abba taje ta duƙa kasa ta, dukar da kai chikin ladabi da girmama wa tace “barka da hutawa Abba, wani murmushi Abba ya saki dan shi har chikin ran shi yana kaunar hiyana sosai akoi ta da ladabi da girmama na gaba da ita ga sanyin hali bata son hayaniya son addini ga sun katun boko da arabic dukka,

    Da fara’a Abba ya amsa mata, san nan ta juyo kasa kasa ta kallin in da Bgs ke zaune tace “ina wuni yaya prince, bai amsa ba kuma bai ko kalli in da take ba saima latsa wayar sa da yake,chikin kwanchiyar hankali
    Hiyana bata damu da rashin amsa gaisuwar nata da Bgs yayi ba, dan in da sabo sun saba da halin sa, “Abba ga furan ta faɗa tare da ɗago kai ta miƙawa Abba kwaryan dake hannun ta,
    Ansa Abba yayi zai yi magana Bgs ya mike yana faɗin “Abba zanje ɗaki sai da daddare, “aa Safras dawo ka zauna ai ban sallame kaba, ba don yaso ba hakan ba ya koma ya zauna dan ba yadda zai yi da Abba ne kuma ba zai iya yiwa Abban musu ba
    dawo da kallon sa Abba yayi kan hiyana dake duƙe kanta na kallon kasa

    “My daughter jeki kawo wa yayan ki nashi furan kinji, to kawai hiyana tace san nan ta miƙe da sauri ta nufi waje

    “Abba nifa bazan sha wan nan abin ba Chewar Bgs ɗin ya faɗa yana yamutsa fuska kamar wadda yaga kashi, “Allah sai ka sha, na dai faɗama ni ba santin furar bane ya jani har nabi Ammin ku Yola na kasa samun kwanchiyar hankali sai da na Aure ta, kuma ita ta koyamin sha dan nima da bana sha ɗin, “to Abba ai kai kache ba ni ba ni kam bana so kyama yake bani “koma me yake baka Allah sai ka sha na dai faɗama ka, kasani ma ko daga sha…. Sai kuma Abba yayi shiru bai karisa maganar ba, dan yasan in ya karisa to wlh ko ya zai yi Bgs ba zai sha furar ba, shi daman Bgs ba wani sauraron maganar Abba yake ba kasan chewar yasa blooth a kunne ɗaya,

    Da sallama hiyana ta dawo fada hannun ta riƙe da kwayar nono da ta damawa Bgs, har gaban sa tazo ta duƙa chikin ladabi da girmamawa tace “yaya prince gashi nan, wani dogon tsaki yaja chikin tsawa yace “dole sai na ansa ne bazaki ajiye a kasa ba,

    “mikomin nan my daughter Abba ya faɗa yana miƙa mata ɗayan hannunsa joyowa tayi wajen Abba a hankali ta miƙa masa kwaryan muryan ta har rawa yeke saboda tsoro tace “Abba zan iya tafiya, “aa my daughter zoki zauna a kujeran nan kema muyi hiran dake yayi maganar yana nuna mata kujerar kusa da shi da ido.
    Ba musu ta miƙe ta koma saman kujerar ta zauna ta sunkuyar da kanta kasa,

    miƙawa Bgs kwayar nono Abba yayi yana faɗin “ansa kasha idan nima bazaka ansa a hannuna ba sai naji, rai a bace Bgs yasa hannu ya ansa kwaryar,batare daya kalli Abban ba,
    ajiye wayar sa a gefe yayi, yasa hannu yachire pai pai da aka rufe kwaryar, kara ɓata fuska yayi lokachin da green eyes nashi yayi arba da damammiyar nono,
    yaji fura ga kwakwa da dabino,amma duk da haka Bgs sai ɓata fuska yake, a hankali ya ɗauki ludayin ya ɗebi nono ya kai baki sa sai wani tsuke hanchi yake wai dan kar yaji warin nonon.

    ….Duk abun da ya keyi Abba na kallonsa, a chikin zuchiya sa yana faɗin ai yau sai kasha nonon nan.

    a sukwane Bgs yayi wurgi da kwaryar nono ya miƙe da sauri kafin ya kai bakin kofar fada ma ya fara kwarara amai,dukawa yayi kasa,kawai ya chigaba da Aman,

    da sauri hiyana ta mike jiki na bari a zuchiyar ta tana faɗin, nashiga uku wayyo Allah yanzu shike nan na sashi yin amai nasan sai ya hukun tani.

    Ajiye kwaryar nono dake hannun sa Abba yayi ya miƙe ya nufi Bgs dake duƙe yana ta kwarara amai kamar zai amayar da kayan chikinsa, dafa kafaɗarsa Abba yayi ta baya yana faɗin “sorry, my Son,
    sosai bgs yayi amai dan sai da idon sa suka sauya sukayi jaa saboda wahala “my daughter bani ruwa a freij Chewar Abba, chikin tsawa Bgs yace “bana so Abba banson duk wani abu da yaran nan zasu taɓa da hannun su, kyamar su nake ji Abba shiyasa nache maka ni bazan sha ba, shiru Abba ya ɗan yi kafin yace “to me tama ka da kake kyamar ta, “Abba ta taɓa zubamin jin… Sai kuma ya dakata yana yamutsa fuska “ok kawai Abba yace san nan ya wuche ya ɗauko masa ruwan da kansa ya kawo masa

    Chikin tsawa Bgs ya kuma chewa Abba kace ta bar ɗakin nan ban son ganin ta, tun Abba bai yi magana ba hiyana ta fita da gudu tana kuka, shiru Abba yayi yana tunanin me yasa Bgs ya tsani hiyana haka har zai che baya son ganin ta

    Kuskure baki Bgs yayi san nan ya miƙe ya nufi hanyar fita, ido kawai Abba ya zuba masa har ya fice daga fadan, Ajiyar zuchiya mai nauyi Abba ya sauke kafin yace “Allah ya shiryamin Safar ai ko me ta maka bai kamata ka tsane ta haka ba, yarinya bai war Allah, marainiya, bani da wani burin da ya wuche a che yau ka auri mace irinta shiyasa nake kokarin haɗa ku, Amma tun da hakan bazata yiwuba dole na samo maka wata matar dan tun da kafara furta ka tsaneta nasan da iya gaskiyar ka ka tsane ta, kuma idan nache zan haɗaku tofa ni da kaina zan kashe maraini yar Allah, Ya Allah ka sassautawa Safras wan nan zuchiyar tasa, yana kai karshen maganar ya juya ya koma kan kujeran sa, ya zauna, ya ɗauko waya ya kira masu aiki akan suzo su goge amai da Bgs yayi da kuma nonon da ya zubar,

    Ƙarfe 9:10 pm agogon Nigeria ta buga

    Taku take ɗai, ɗai, kamar wata mahauniya, sanye take da wata haɗaɗɗiyar doguwar riga abaya pink colour, ta yafa mayafin rigar a kanta, yau dai batayi kwalliya ba, mai kawai ta shafa sai ɗan man baki da tasa a bakinta,fuskan ta sai kyalli take, tasa high heel pink tana rike da ɗan karamin plate mai ɗauke da cup, san nan ta rufe cup ɗin ma da wani ɗan ƙaramin plate mai shegen kyau, ta nufi part ɗin Aryan

    ko sallama babu ta faɗa chikin palon kasa kai tsaye ta haye sama stair ɗin ta shige palon sama nan ma ba ko sallama ta shige, kai tsaye betroom ɗin sa ta shege, babu kowa a chiki, table ɗin tsakiyar ɗakin ta nufa ta ajiye cup ɗin, ta juya da sauri dan gargaɗin da Aunty farida ta mata akan karta daɗe.

    Dai dai zata fita taji an buɗe kofar toile ɗin, da sauri ta wai go karaf idon ta suka sauka kanshi ɗaure yake da towel a kugun sa.

    ga jikin sa a jike da alama wanka yayi, wani kara ta saki ganin yadda kiran jikin sa yake afili, kafin yaya Aryan ya juyo tayi waje, da gudu, a sukwane ya bi bayan ta,

    saboda high heel dake kafarta bazai bari tayi wani gudu sosai ba, a dai dai zata fita palon sama ya damko kugunta ta baya, sama ya ɗaga ta da hannu ɗaya ya juya da ita cikin ɗakin, ihu diyana keyi, tana faɗin “yau kam na shiga uku yaya Aryan dan Allah kayi hakuri wlh na rantse maka bansa zaka fito ba kaya bane da bazan gan ka ba kuma ai ni, ban ganka sosai ba, shidai ko sannu bai che mata ba saman katafaren gadon sa yayi kurgi da ita san nan ya koma ya rufe kofar ɗakin ya zare makullin ya nufi dressing room nashi,

    shiru diyana ta kwanta tana kallon sama kasa kasa ta fara magana “yau kuma aljanun mugun tan yaya Aryan ne ya dawo ko?, to ni me ma na masa shiru ta ɗanyi kamar mai tunani sai kuma ta chigaba da magana “kai lallai yaya Aryan ashe haka hannun shin nan yake kato kamar chinyar lamrat, kut lallai yana da nama sosai amma kuma shine yake saka riga ya ɓoye wlh in ni ne shi bazan ɓoye ba ai hannu mai nama sosai ɗin yafi kyan gani, bari ya fito idan bai dake ni ba zan che masa ya faɗamin me yake chine hannunsa tayi nama dayawa haka nima inrinƙa chi ko nawa zaiyi, jin motsin shine yasa ta miƙe zaune tana zare ido

    Fito wa yayi sanye chikin kayan barchi mai kyau da tsada gaban morrow ya tsaya yana gyara gashin kansa, Almost 10mnt ya ɗauka a gaban mirrow san nan ya juya ya nufi saman sofa ya zauna, duk abun da yake diyana na kallonsa ta wutsiyar ido amma bata bari ya kamata tana kallon sa ba duk da chewa shi ɗin ma duk abun da yake idon sa na kanta.

    A hankali ta zuro kafafunta kasa san nan ta sauko daga gadon ta nufi inda yake, gaban sofar da yake zaune,tazoe ta sugun na, Murya na rawa tace “yaya Aryan dan Allah kayi hakuri kaji,
    “laifin me ki ka min da kike bani hakuri, da sauri ta ɗago kai, “laaaaa yaya Aryan da gaske ban maka laifi ba, kallonta kawai yake dan yanzu tama dai na bashi mamaki, “yaya Aryan in tafi ɗaki ta Tambaya tana kallon face nashi yayin da shima ita yake kallo “a’a tashi ki kawomin coffee din kizo ki zauna muyi hira “aa yaya Aryan Aunty farida tace na daina daɗe wa a dakin ka “me yasa zaki dai na dadewa a dakin nawa, dariya diyana tayi kafin tace “Aunty farida tace idan namijin da mace suka keɓe to wai na ukun su sheɗan ne, a sukwane ne Aryan ya kara waro idon sa waje yana kallonta, ganin ita ko ajikin tane ma yasa yace “ok to dauko coffee din ki kawomin sai kizo ki buga game kaɗan da wayata kafin ki koma ɗakin na ku, da sauri ta nufi table din tana murna ta ɗauko masa coffee ta kawo masa, ya ansa ya mika mata wayar sa shi kuma, gefensa ta koma ta zauna tana latsa wayar.

    “Yaya Aryan kasan me, batare da tajira amsar sa ba ta chigaba da magana, Allah ko kwanan nan ina tunanin yaya bello sosai ina kewar sa

    , wani tarine ya sarke sa coffee din ta haura masa kai sosai yake tarin, asukwane ya ajiye cup ɗin coffee ɗin ya dafe kansa da hannu ɗaya yana tari,
    da sauri diyana ta ajiye wayar ta nufi freij ta ɗauko masa ruwa, ta dawo ta mika masa, bai ansa ruwan ba sai yasa hannu ya damko wuyar ta ya fisko ta da karfi ta faɗa kan faffadar kirjinsa, sosai yake tari ya kasa magana, ita kuwa da sauri ta ɗago kai daga kirjin nashi, jin yadda yake tari, chikin tsoro tace “yaya Aryan ka sakeni in ɗauko maka ruwa dan Allah, da kyar ya iya faɗin “babu ruwan ki da ni ki bari tarin ya kashe ni “dan Allah yaya Aryan kayi hakuri Allah bana son ganin ka kana tarin kaji pls, ta karisa maganar kamar zatayi kuka, “aa ba ruwan ki dani nache maki koh “hannu diyana tasa ta toshe masa baki tana girgiza tana faɗin “dan Allah yaya Aryan ka daina faɗin haka mana wlh akoi ruwana da kai kuma har da tsaki na, hannunta ya chire daga bakin sa, chikin dashewar murya saboda tarin da yayi, yace “tashi min ajiki kuma ki fitamin a ɗaki karki sake zuwa, yayi maganar in a serious matter, “yaya Aryan me na maka to? “Ban sani ba ki tashi ki fita nace, yayi maganar da ɗan karfi

    Nan take diyana tafara hawaye tana faɗin “yaya Aryan to dan allah ka faɗamin me nayi maka da kache kar na kara kawo maka coffee, kuma ai nasan kana son coffee din, wani irn raɗaɗi yaji a zuchiyar sa saboda kukan da take, slowly yasa hannu ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna runtse ido tayi ganin yadda yake kallonta, calmly ya fara magana “me yasa kike kuka kuma?, Chikin shesshekar kuka tace “to ba kai ne ba kaki ka faɗamin me na maka, “ya isa to kiyi shiru baki min ko mai ba kinji, da sauri ta buɗe idonta tana kokarin tashi daga jikin nashi kara firgota yayi ta dawo kirjinsa har sai da kanta ya bugi gemunsa.

    …ɗago kai tayi suna fiskantar juna pink lips nata har kerma suke, zata yi magana, yayi sauri ɗora yatsan sa a kan lips nata yana girgiza Mata kai, sauko da kansa yayi ya haɗe fuskokin su yana kallonta,Wani irin farin chiki da nitsuwa ya keji tana ratsa zuchiyar sa,
    lunshe ido tayi dan ba zata iya haɗa ido da shiba, goga hanchin sa ya fara yi a jikin nata hanchin, kasa kasa yace ” menene tsakanin ki da Bello?, da sauri ta buɗe ido tana faɗin “yaya na ne kuma shine idan Inna ta hana mu abin chi yake zuwa ya karɓo mana wajen Adda hasana,

    “shike nan alakar dake tsakanin ku, “eh shike nan “to amma me yasa ki ka che kina kewar shi? “To ai yaya Aryan kaga yana da kirkine kuma idan na samu kuɗi zan saya masa mota da gida dan shima ya dawo birni, “to idan Abba yace zai Aura miki shifa? dariya diyana tayi kafin tace “nifa idan ba soja ba to bazan yi aure ba soja kawai bake so.

    Wani dogon nunfashi Aryan ya ja tare da sauke ajiyar zuchiya kafin ya sake ta “tashi ki tafi ɗaki to tun da Aunty farida tace karki daɗe, da sauri ta miƙe har tana kokarin faɗuwa,key din ɗakin ya miƙa mata,
    Ansa tayi, ta nufi bakin kofar tasa key ɗin ta buɗe kofar ta fice da sauri, miƙewa shima yayi ya nufi kan katafaren gadon sa ya kwanta ya lumshe ido yana mai da numfashi,

    Washe gari misalin 9 na safe zaune suke a palon Abba kamar yadda suka saba dan yin breakfast.

    Ammi ta dubi diyana tace “ke diyana jeki ɗauki abinchin babban yayan ku a kichin ki kai masa, a sukwane Aryan ya ɗago dan yasan halin diyana yana son ya hanata zuwa sai dai kuma bai san surutan Aunty amarya dan yasan yana hana diyana zuwa sai Aunty amarya ta sa shi a gaba da tambaya, meke tsakanin su.

    Da sauri diyana ta mike Abba na kokarin ya dakatar da ita amma ina har ta fice, kichin ta nufa ta ɗauki abinchin nashi already an gama shirya masa fitowa tayi ta nufi part nashi.

    Bb ko Sallama ta faɗa palon babu kowa kai tsaye ta haye stair ɗin ta shiga palon saman nan ma babu kowa kofar da ta gani chikin palon ta nufa ba ko sallama ta shiga,

    tsaye yake gaban mirrow yana gyara gashin kansa sanye yake chikin Black jeans da t-shirt blue, bakarin kyau kayan suka masa ba,kamar dan shi akayi su, jin an buɗe kofar ɗakin yasa ya zubawa kofar green eyes nashi ta chikin mirrow, ganin diyana che yasa ya ɗaure fuskar nan kamar wani zaki ya kau da kallonsa daga kanta

    “Kai mai kama da hiyana ga abinchin ka nan anche na kawo maka, a sukwane Bgs ya juya dan jin sunar da ta kirashi kuma har da che masa kai, chikin tsawa yace “get out, diyana ko tsoro tsawar ma bata jiba ta ɗan ja tsaki kafin tace “dan ka samu ma na kawo maka abinchi wlh ba dan Ammi ba bazan…. Bata karisa maganar ba kamar wata walkiya ta gefar da kwandon abinchin tayi waje a guje, da gudun gaske Bgs yabi bayan ta sai huchi yake

    To masu karatu sai mun haɗu ranar Monday idan Allah ya kai mu, ina masoyan diyana? tofa yau masoyiyar ku ta taɓo gidan rina ato ku tanaji ruwan zafi gasa mata jiki idan ma ta saura da ranta kenan

    💖NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

     

     

    More comments an like pls

    *💫STAR LADY💫*30

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 25

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 25

    Episode 2️⃣5️⃣*

    ……..Ɗago ido Khalid yayi yana kallon su Ahmad san nan yafara Magana “yanzu menen mafita, Khalid bai gama rufe baki ba, Ahmad ma yamiƙe yabi bayan su Aiman, dawo da kallan sa kan yusuf dake zaune Khalid yayi san nan yace “Yusuf mene mafita ni fa gaskiya ina son Zahra sosai wlh ina san muyi Aure kuma gaskiya time yayi daya kamata a che munyi auren idan fa muka biyewa su DON baza mu taɓa yin aure ba awan nan rayuwar, dan su babu Aure a tunanin su kwata kwata,
    dogon numfashi Yusuf yaja kafin ya fara Magana “yaya Khalid ni kai na ina matikar son my baby wlh, duk da yarin yache sosai amma ina san muyi aure taje ta karisa girma a gidana amma bansa ya abun zai kasan cheba kanafa jin abun da yaya prince ke faɗe, wai har abada shida Aure kuma ni nasan mawuya chin abune a shawo kan sa ya yarda yayi Aure, “dole fa Yusuf musan abunyi Khalid ya faɗa yana kokarin miƙewa “jirani muje mana chewar Yusuf ya karisa maganar tare da miƙewa shiam, suka jera atare suka fice daga palon kowa yayi ɓangaren sa

    Abangaren DON kuwa yana fita palon Abba ɓangaren sa yanufa chikin sauri, yana shiga ɗaki ya zauna a bakin katafaren gado sa, ya dafe kai dan ji yake kansa na sara masa,kamar zai faɗi kasa, tunani ya shigayi, ni gaskiya Abba bai min adalchi ba tayaya zai wani haɗani dawani abu wai shi Aure, dole ma nazo nabar kasar nan, tun kafin Abba ya sake kawo wata maganar.

    Awan nan yanayi Aryan ya shigo ya same’sa, gefen sa ya zauna saman gadon yasa hannu ya dafa kafaɗarsa cikin cool voice yafara Magana “calm down my blood kafasan idan ka shiga damuwa nima dole nashiga damuwa, kuma ni nasan ba kasan ka ganni chikin damuwa ko, ɗago green eyes nashi yayi yana sauke su kan face ɗin Aryan, har sai da Aryan ya tsorata ganin yadda idon nashi suka sauya sunyi jaaa sosai ga jijiyoyin kan nan nashi duk sun tashi duk da sanyi A.c dake ɗakin hakan bai hana DON zufa ba, chikin wata iriyar voice mai sauti yace “why, why Aryan why Abba zai nemi ya chazamin kai why yake neman kassarani, “calm down my blood ya isa haka kayi shiru pls Aryan ya faɗa tare da dora hannun sa saman ɗan karamin bakin DON ya rufe masa, yana kokarin sake magana Aunty farida tashigo da sallama, zame hannunsa Aryan yayi daga kan dan bakin DON yana kallonta

    Karisowa chikin ɗakin tayi ta zauna a bakin gadon ta ɗayan gefen su kasa DON a tsakiya ita da Aryan a nitse tafara magana “nasan abun da Abba ya faɗa bazai muku daɗi ba amma hakan kar ya dame ku kuyi hakuri, ni nasan Abba ba zai so ya ɓata muku rai ba koma me zanyi magana dashi idan ya huche, yanzu dai banaso wani abu ya dame ku dan kunsan idan kuka shiga damuwa dole nima hankali na ya tashi kuma zan shiga damuwa, ɗan dakata wa tayi da magana tana mai da numfashi, buɗe ɗan karamin bakin’sa Aryan yayi zai yi magana kenan sukaji sallamar Abba, da mamaki suke bin kofar ɗakin da kallon,

    ƙarisowa chikin ɗakin Abba yayi, mikewa sukayi gaba ɗayan su, suna kallon Abba kai tsaye DON ya nufa yaje ya rungume sa, shiru Aryan da Aunty farida sukayi suna bin Abba da DON da kallo, tunani Aunty farida ta shiga yi anya bawani abun Abba ya shirya musu ba, bata gama tunanin nata ba taji Abba yana faɗin “bana son ɓachin ran ku ƴa’ƴana kune farin chiki na, yanzu dai ke farida jeki haɗa masa complex ki kawo mana muna sha muna hira

    ……ita dai Aunty farida gaskiya bata yar da da neman sulhun da Abba yazo yi ba, dan tafi kowa sanin halinsa yanzu wata kila wani idea ne tazo masa shiyasa zai musu wayo ta haka, jiki ba kwari tana ta tunani har ta fiche daga ɗakin,

    Sakin DON Abba yayi ya haye kan katafaren gadon DON ya zauna yana ta murmushi, haye gadon Aryan da DON ma su kayi suka saka Abba a tsakiya, “Abba ya kamata mu koma bakin aikin mufa Aryan ya faɗa yana kallan Abba, murmushi Abba yayi kafin yache “ku rubuta musu later akan za kuyi wani aiki a nan na tsawon wata uku dan gaskiya ina san kasan chewa da ku a’wayan nan watannin,

    …..DON yace “Abba a matsayi na BGS (Brigadier General Safras) ba sai na rubuta wani later ba, Aryan da Yusuf kuma dama a’wajena zasu tambayi permission na hutun, tun da kana bukatar mu kasan che da kai na wata uku su rubuto min later zan sa musu hannu, murmushi Abba yayi sosai kafin ya rungumi DON yana faɗin ilove U my Son, “ilove too my love my pleasure my only Boss, farinchiki kamar Aryan ya nitse kasa dan daɗi, ganin yadda Abba da DON suke zuba wa juna kalan kauna, “eyeee lallai Abba wato haka abun yake ko? chewar Aunty farida dake tsaye a bakin kofar shigowa ɗakin tana ta murnushi hannunta ɗauke da babban trey mai ɗauke da cup 4 na complex, sakin Abba DON yayi ya juyo yana faɗin “Aunty babba kin fa iya sa ido, kariso tayi chikin ɗakin ta ajiye trey ɗin saman table ɗin tsakiyar ɗakin ta zauna saman sofa tana murnushi

    A tare suka sauko daga gadon suka nufo ta, kowa ya zauna a saman nashi sofan suna fiskantar juna, Aunty farida zata mike ta ɗauko musu complex ɗin Aryan ya rigata yana faɗin “bari na hutar dake Aunty babba, ɗaukan trey ɗin yayi ya fara miƙawa Abba, ya ɗauki cup ɗaya san nan ya miƙawa Aunty farida itama ta ɗauka, ko da yazo mikawa BGS wani harara BGS ya wurga masa kafin yace “au nine karshe ko “hannu ɗaya Aryan yasa yaja dogon hanchin BGS har sai da yace wash mugu kawai, dariya Abba yayi yana faɗin “daman Aryan kai kake jan hanchin BGS koh shiyasa naga hanchin nashi kullun tana ƙara tsawo Sosai, taɓe baki Aunty farida tayi tana kallon Abba, da mamaki wato ma idan ana jan hanchi kara tsawo yake koh? Tab ai da kuwa hakane lilin baba shine mutun na farko da zai fara bawa ummi rahab tana ja masa dan hanchin nasa yayi tsawo

    …..Wani naushi BGS ya kai wa Aryan a kumatu sai dai ina kauchewa Aryan yayi yana ɗan murnushi, bai bari hannun BGS ya sauƙa a jikin sa ba, “wai zaka ɗauki complex ɗin nan ne ko kuma na ajiye, ɗaure fuska BGS yayi kafin yace “bazan sha ba, “oh my lovely bro pls ka sha idan baka sha ba nima bazan sha ba kuma wlh inasan sha amma dole zan haku in dai baka sha ba, ɗan sake fuska kaɗan BGS yayi kafin yasa hannu ya ɗauko cup ɗin yana faɗin “zan sha ne kawai saboda kana son sha kuma bani da wani burin daya wuche inga kasamu abun da kake so, matsowa Aryan yayi ya man nawa BGS kiss, a goshi kafin yace “ina kaunar ka kamar raina my blood, “Hmmmm faɗa ɓatawa my bro ai kaunar da nake maka ba zai faɗu ba

    … Abba dai ido kawai ya zuba musu a chikin zuchiyar shi yana gode wa Allah da ya haɗa masa kan ƴa’ƴansa suke matukar kaunar ju nan su haka,

    “Abba na, gobe idan Allah ya kaimu in mun gama raka Ahmad fada, zan bi jirgin yamma na koma, chewar Aunty farida “Allah ya kaimu bai lovely daughter, shiru su kayi suna shan complex nasu chikin ni shaɗi ,

    zubur Aryan ya mike kamar wadda akawa allura yana faɗin “Abba sai da safe da mamaki BGS da Aunty farida ke kallansa, Abba kuwa sai murnushi yake chikin ransa yana faɗin, Allah kasa na chinma abun da nake hari afili kuwa sai yace “to my Son yaka mata daman ka ajiye complex nan haka kaje kasha coffee mai zafi, a’sukwane Aryan ya dawo da kallansa kan Abba yana mamakin ya akayi Abba yasan abun da zaije yayi, kashe masa ido ɗaya Abba yayi yana murmushi yace “to ka tafi mana me kuma ka tsaya kana kallan mu, jiki ba kwari Aryan ya juya ya ajiye cup ɗin complex ɗin dake hannunsa a saman table yanufi hanyar fita, yana jiyo muryan Aunty farida na faɗin “wai meke damun Aryan ne muna zaune muna hira kawai kache sai da safe, bayan ga wayan nan manya manyan idon nan naka ba alamar barchi a chikin su, fichewa yayi da sauri dan karma Aunty farida ta jefo masa wani tambayar,

    a hankali BGS ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi ya furta “kila ya gaji da hiran ne, da sauri Abba ya chan za musu topic ɗin hirar dan karsu tsawai’ta magana a kan Aryan, yasan BGS ba karamin kwakwalwa bane da shi yanzun nan zai iya gane komai “My daughter ya kamata kema kije ki kwanta kinga yanxu almost 10, “to my lovely Abba tana faɗin hakan ta mike ta ajiye Cup ɗin hannun ta saman trey, san nan ta ɗauki trey ɗin ta juyo ta ansa cup ɗin hannun BGS dana hannun Abba ta ɗora kan trey ta ɗauka tayi waje,

    Dawo da kallansa Abba yayi kan BGS san nan yafara Magana “kasan me nake so da kai my Son “aa Abba “abun dana ke so da kai dan Allah ka dai na korar yarinyar nan idan na ai’kota wajen ka, kuma ka dai na yi mata tsawa kaji my lovely Son ya karisa maganar chikin sigar rarrashi, ɗaure fuska sosai BGS yayi kafin yace “Abba ni pls ka daina aiko min su ɗaki, wlh dan ma a’baya kache kar na kara bugun tane Allah da ɗazun da tashigo sai na ɓallata, ka rinka aiko Fahad ko ka kirani awaya mana Abba haba, ya karisa maganar kamar zai yi kuka, “to shike nan zan daina aiko ta tun da baka son,

    … hakan yayi maka? mikewa BGS yayi yaje ya rungumi Abba yana faɗin “shiyasa nake son ka my Abba murmushi Abba yayi yasa hannu yana ɗan bubbuga bayan BGS kamar karamin yaro yana faɗin “nima ai ina matikar kaunar ku sosai duk wani abun da zai saku farinchiki shina ke so, “Abba muma mu ma matikar son farinchikin ka ai yayi maganar yana raba jikin sa dana Abba, miƙewa Abba yayi yana faɗin lokachin barchi yayi good night my lovely son, “good night Abba na BGS ya bashi amsa yana nufar, kaban mirrow, Abba kuma ya fice daga ɗakin yanufi part nashi, jallabiyar jikin sa, BGS ya chire ya nufi toilet dan yin wanka.

    Abangaren Aryan kuwa yana fitowa daga part na BGS kai tsaye, part nashi ya nufa da sauri yana shiga betroom ɗin diyana na fitowa ta kawo masa coffee ta ajiye zata fita, karo sukayi kanta ya bugi faffaɗar kirjinsa ta fame chiwon nata wani ihu azaba ta saki tayi baya zata faɗi, da sauri ya rikota, nan take jini ya fara zuba daga goshin nata, rungumeta yayi sosai ajikin sa da kyar ya iya furta “sorry kiyi shiru, “yaya Aryan zafi ya kemin sosai “na sani nasan zai miki zafi amma ki daure ki daina kuka kinji muje na duba miki, ya karisa maganar tare da raba jikin su, ya kama hannun ta suka koma chikin ɗakin saman sofa ya zaunar da ita, ya zauna gefen ta ya zuba mata ash eyes nashi yana kallan yadda hawaye wani ke bin wani a kunchinta calmly ya fara magana “ba na che ki dai na kukan nan ba, turo ɗan karamin bakin nan nata tayi “to zafifa yake min, hannu yasa yana goge mata hawayen yana faɗin “to ki daure kinji bana son kukan naki ne ko kaɗan yana damun na idan ki nayi, ba kiga yadda ki kayi tsara kwalliyar ki ba ko so kike ya ɓachi “a’a bana son ya ɓachi “to kiyi shiru kinji, gyaɗa masa kai kawai tayi, shi kuma ya mike ya ɗauko A box,ya dawo kusa da ita ya zauna

    A hankali ya fara gyara mata chiwon nata, sai was Allah na take faɗi shi kuma yana che mata sorry, har ya kammala san nan ya miƙe ya mayar da Box ɗin ya koma gefen katafaren gadon sa ya zauna,

    …ɗaure fuska yayi sosai yana kallonta “ke wai bana che kada ki sake kwalliya da daddare ba, baki da lfy ma amma sai kin zana waɗan nan abubuwa a ɗan karamin face nakin nan ko? turo ɗan karamin bakin nan nata tayi kamar biro kafin tace “kayi hakuri bazan sake ba “kullun haka ki ke chewa ba zaki sake ba amma sake… Bai karisa maganar ba ash eyes nashi ya sauƙa a kan kayan jikinta,

    wasu shaggun riga da wando ne, Black jeans ne ya matseta sossi santala santalan chin yoyin nan nata kamar zasu fasa wando, sai yar figaggiyar T-shirt pink colour itama ta matseta kana ganin shap na breast nata sosai daman gasu nan masha Allah tula tula dasu, ga kanta ba ɗan kwali ta saki wan nan bakin lallausan gashin nan nata har baya,sai shekin gashin ke yi, ta zubo wani ɗan kaɗan ɗin gashi ta gaban goshin ta, tayi make up nata iya make up,ga wani shegun high heel pink da ta sa a kafar ta, mamaki ne ma yaka mashi wai wa ya koyawa yarinyar nan duk irin waɗan nan abubuwa, nan take yaji ransa ya bachi sosai chikin tsawa yace “ke kina da hankali kuwa haka daman ki ka fito,kika keto gaba ɗaya part part na gidan nan har ki ka zo nan ko? chikin tsoro ta ɗago dan jin yadda yayi maganar, ba karamin raza tayi ba data kalli yadda fiskarsa ta sauya lokachi guda, asukwane ta miƙe zata gudu,

    Taku ɗaya yayi ya tamki kugunta ta baya, tsabar raza da tayine bata san, lokachin da ta fasa ihu ba, asukwane yasa hannu ya toshe mata baki, chikin tsawa ya furta “kimin shiru,shiru tayi jikinta har bari yake . zame hannunsa yayi daga bakinta ya juyo da ita suna fuskantar juna, nan take kuma sai yaji ɓachin ran nasa duk ya kau sosai yake kallon face, nata a ranshe yana faɗin “yarinya sai kyau kamar ita tayi kanta komai tayi kyau yake mata,

    Ganin yayi shirune yasa diyana ɗago blue eyes nata karaf suka sauƙa chikin nashi, murya na rawa lips nata sai kerma suke saboda tsoro kamar mai jin sanyi tafara magana “yaya Aryan kayi hakuri wlh ba laifi na bane Aunty farida da che tache… Bata karisa maganar ba sakama kon fisgota da yayi ta faɗa faffaɗar kirjin sa, dan ba zai iya jure kallan yadda lips nata ke motsawa ba,mutuwar tsaye diyana tayi dan gaba ɗaya ji tayi kamar baa duniya take ba, ran kwafar da kansa yayi sai tin kunnen’ta chikin wata iriyar kasalalliyar murya ya fara magana kasa kasa “karki sake saka irin waɗan nan kayan kinji ko? idan ma kina so sakawa kisa a iya ɗaki kawai idan zaki fita waje kisa hijabi kinji ban son na kara ganin ki haka.

    ….da kyar ta iya ɗago kanta daga kirjin nashi dan ta samu iskan da zata yi numfashi kasan chewar ya matseta sosai,bata iya wani numfashi da kyau, a hankali ta buɗe ɗan ƙaramin bakin ta muryar har rawa yake tafara magana “to yaya Aryan ai Aunty farida che tache na rinka sawa idan zan… Bai bari ta karisa ba ta ɗora ya tsan sa a saman lallausan lips nata yana girgiza kai kafin yace “a’a koda Aunty farida ta sake chewa ki saka kiche mata na hana ki kinji? kuma ai ita Aunty farida gobe ma zata koma ni dai kar na sake ganin ki da irin wan nan kayan bana so, to kawai tace masa tana numfashi da kyar saboda matse ta da yayi,

    Shiru sukayi dukkan su shi yana kallanta ita kuma tana kallon kirjinsa, Almost 5mnt a haka, san nan diyana ta ɗago blue eyes nata slowly ta sauke su kan face nashi, karaf suka sauka chikin ash eyes nashi, dan kuwa ita yake kallo, da sauri tayi kasa da kanta dan bazata iya kallan chikin idon sa ba, “yaya Aryan na gaji da tsayuwa wlh jinake kamar zan faɗi “to ni kuma ban gajiba, da sauri ta ɗago blue eyes nata tana kallonsa ganin yadda ta ɗago ne yasa yashiga tunanin me ya faɗa ne, dan shi kwata kwata bai ma san me ya faɗa ba, sauko da ash eyes nashi yayi kan ɗan karamin bakin ta, yana kallan lallausan lips nata, da sauri ya sake ta yana furta a’uzubillahi minasshe ɗanin rajim, a chikin zuchiyar sa “ke wuche ki tafi ɗaki dare yayi kuma karki sake fitowa da irin kayan nan, yana kai karshen maganar ya juya yanufi toilet da sauri wai danma kar ya sake kallonta,

    Kwas kwas kwas diyana ta juya jiki ba kwari ta nufi waje,

    Aryan kuwa wanka yayi ya fito a gurguje ya shirya cikin kayan barchi riga da dogon wando masu kyau da tsada farare tas masu laushi, ganin dare yayi sosai yasa shi hayewa katafaren gadon sa batare da yashi coffee ɗin ba ja blanket yayi zuwa chikin sa ya sage gudun A.c ya lumshe ido ba jimawa barchi yayi awon gaba dashi

     

     

    *💫STAR LADY💫*

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star Lady*

     

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 26

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 26

     

     

     

    Episode 2️⃣6️⃣*

    Misalin karfe 7 na safe Ammi na zaune a bakin katafaren gadon ta sanye take da wata ɗankareriyar lace baki mai zanen flower manya manya ajiki jaa, ɗinkin bubu gawn, ta sanya wani dan kareren sarkan gold a wuya ka wasu manya manyan abun hannu masu kyau da tsada a hannunta, sai kamshi take zubawa,kamar anyi ɓarin turare ajikinta

    da sallama ɗauke a bakin sa BGS ya shigo, kauda kai gefe Ammi tayi tana amsa sallamar, ganin hakan yasa BGS ya kariso chikin ɗakin da sauri a gaban ta ya zauna saman lallausan karpet na alfarma dake shinfiɗe a ɗakin, chikin sanyi murya ya fara magana “ina kwana Ammi, kara ɗaure fuska sosai Ammi tayi kasa kasa ta amsa masa da lfy, kwantar da kansa yayi kan chinyar ta ya riko hannunta cikin ladabi da girmamawa yafara Magana “kiyi hakuri Ammi na, kinji nasan nayi laifi dayawa amma pls ki daina fushi dani kinji, kin fa san idan ki na fushi da ni, ina cikin fushin Ubangiji kuma kome nasa a gaba bazan yi nasara ba pls my Ammi for give me, ɗan daka tawa yayi yana sauraron yaji me zata che

    ….. Hannu Ammi tasa ta fara shafa lallausan gashin kansa kafin tace “ni ba fushi nake da kai ba kuma ba zan iya fushi da kai ba saboda na san idan iyaye suna fushi da ƴa’ƴansu, wache bala’i mai girma suke jawa ƴaƴan nasu, kawai dai abun da ka keyi ne baya da chewa, “zan daina Ammi na duk wani abun da baki so ki faɗa min zan dai na “kayi alkawari “na miki alkawari Ammi na keche fa farin chikina lokachin da bana kasar nan kin ta ɓa ganin nayi 2 hours ban kira ki ba, kome aikin da nake sai na daka tar na kira ki koda na 5mnt ne, saboda kawai inji ya kike, “eh hakane na sani kuma kana da gaskiya

    …. yanzu dai abu biyu ne kake yi a gidan nan yake ɓatamin rai, kuma nake son ka daina yi, da sauri BGS ya ɗago kai yana kallan ta, murnushi kaɗan Ammi ta sakar masa, shima wani cool murmushi wan da bai ta ɓayi ba ya sake har sai da dimple nashi ta lotsa, chigaba da magana Ammi tayi “ina son ka rage tsawar da ka kewa su hiyana abun yana damuna kaga marayune ba uwa ba uba pls ku jasu ajiki dan ku mantar da su marai chin nasu, kannen kane kai yaka mata kafi kowa sakar musu fuska da jansu ajiki,

    ..ɗaure fuska BGS yayi,bai che komai ba yayi shiru yana tunani, yanzu dai sulhu nazo nema wajen Ammi bai kamata nayi wani abun da zai sake ɓata mata rai ba gaskiya bari dai na bita a yadda take so for now, in yaso daga baya na koma normal, ɗan murmushi gefen fuska ya saki a hankali ya motsa ɗan karamin bakin nan nashi ya furta “daga shi sai mai kuma Ammi, ajiyar zuchiya Ammi ta sauƙe kafin tace “sai batun kannen ka su Umar, inajin ɓachin rai idan suka gaishe ka baka amsa ba, sai kache wasu abokan gaba, ai ko bazaka amsa gaisuwar mutane a waje ba to fa ya zama dole ka rinƙa amsa na kannen ka “to shike Ammi na i will try my best kinji daɗi ” kwarai kuwa naji daɗi “Thank God, my Ammi haka nake so in ga kina chikin farin chiki, zame hannunta Ammi tayi daga gashin kan nashi tana faɗin “nima ina son naka farinchikin ai, yanzu dai katashi kaje ka shirya kuje ku raka Ahmad fada “a’a Ammi ni bazan je ba “what Ammi ta faɗa tana kara waro fararen idon ta “baka isa ba ka tashi kuma Allah idan ban ganka a fada ba.. bai bari ta karisa maganar ba yace “a’a my Ammi yanzu ma zanje na shirya yayi maganar yana miƙewa, san nan yanufi waje

    Nauyayyar ajiyar zuchiya Ammi ta sauƙe, a fili ta fara magana, Alhadulillah Allah na godema da ka bani ɗa mai kauna ta mai jin tausayi na mai gudun ɓachin rai na, ya Allah ka tai makeni nima na rinƙa faran ta masa kamar yadda yake min ya Allah ka nunamin ranar da zaiyi Aure, bana son na chigaba da ta kura masa a kan batun Aure, yana min biyayya iya gorgidon iyawar sa yana son farinchiki na, bai kamata ni kuma ya dage wajen sashi abun da baya so ba zan rinƙa taya shi da addu’a har Allah ya karkato da hankalin sa kan Auren, karisa hayewa saman gadon tayi ta kwanta da kyau ya lumshe ido tana ta tunani

    Misalin karfe 9:30 gaba ɗaya family sun haɗu a faɗa sun sha kwalliya sosai Abba na zaune kan kujerar mulkin su Ammi suna gefe gefensa, ga wata ha ɗaddɗiyar gujera a gefen na Abba ba kowa a kan gujerar, su Aryan suna kujerun dake jere gefe guda kujerun su Aunty farida na fuskantar nasu Aryan, ga manya manya baki kamar su sarkin zaria sarkin gombe sarkin yola da dai sauran su,

    Miƙe Wa Abba yayi daga kan kujerar da yake zaune, yayi tattaki izu tsakiyar fada san nan ya fara magana “kai Ahmad tashi ka hau kujerar mulkin ka, jiki ba kwari Ahmad ya mike ya nufi kujerar, yana zama su wajiri suka miƙe suka nufoshi, nan take suka ɗauko farin kyalle suka fara naɗa masa rawani a kai, shidai kamar zai yi kuka haka aka naɗa masa rawanin sarautar,bayan su waziri sun gama na ɗawa Ahmad rawanin ne, Abba yace “salati goma ga annabi yayi maganar yana nufar gujerar kusa da Ahmad,

    …zama Abba yayi san nan su kafara yiwa annabi salata bayan sun gama salati, Abba ya ɗago ido yana kallan BGS “Safras ka rufe mana da addu’a, BGS bayasan yin magana ko kaɗan amma yana gudun ya sake ɓatawa Ammi rai Allah badan Ammi na wajen nan ba da ba zanyi addu’ar nan ba, slowly ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi, da wani zazzakar Muryar sa ya fara zuba addu’oe, gaba ɗaya palon sunyi shiru suna sauraron’sa slowly hiyana ta ɗago blue eyes nata ta sauke su a kan shi chikin ranta tana faɗin “wow dama haka yake da voice mai daɗi? shi yasa baya magana dan kar murinƙa ji hmmm sosai take kalansa, har ya kai karshen Addu’ar yana kai karshe ya mike da sauri ya fice daga fada

    sai sauri yake yana taku irin na jaruman maza, yazo dai dai zai shiga ɓangaren kamar daga sama yaji murya daga bayan sa tana faɗin “baka jiba, batare daya juyaba yayi shigewar sa, kai tsaye betroom nashi ya nufa yana shiga ya nufi katafaren gadon sa, ya haye ya kwanta ya lumshe ido yana jan tsaki

    A hankalin ta turo kofar ɗakin ta shigo kwas, kwas, kwas, take takawa har gaban gadon nashi ta zo, kashe murya tayi tafara magana “haba mana shine ina maka magana a waje ka shareni, kasan wacece ni? nifa yar Autan sarkin zaria che pls kyakkyawa katashi mana muyi magana wlh ni bana barin abu a rai na da abu ya burgeni nake faɗe, wlh ka tafi da ni tun da kafara addu’a a fada nake kallon ka, kuma SON ka nake da dukkan zuchiyata, ko motsi BGS bai yiba bare tasa ran zai yi magana “haba mana kyakkyawa nasan ba kayi barchi… Bata kai karshen maganar ba taga BGS ya mike batayi auneba taji saukar wani gigitatchiyar ma haukachiyar mari,a kan kunchinta wani ihun azaba ta saki

    .. a fusache ya zaro belt daga ma zaunin sa ya fara zuba mata ta ko ina a jikin ta, ihu take kamar ranta zai fita,shiko ko ajikinsa rai ambachi yake zabga mata belt ɗin, data ga dai BGS zai iya kashe ta ba wan da yaji ihun data ke bare yazo ya taimaka mata yasa ta miƙe da kyar tanufi hanyar fita, damko atachimen ɗin datayi chikon gashi da shi yayi ya daga ta da kai, yayi wurgi da ita gefe hakan yayi dai dai da shigowar Aryan ɗakin, a fusache BGS ya sake nufar ta, ko motsi batayi da alama ta suma chigaba da bugunta yayi

    Da gudu Aryan ya karisa chikin ɗakin ya sa hannu biyu ya damko damsen BGS yana faɗin “haba blood kisa zakayi ne, chikin tsawa BGS yace “sakeni Aryan nache kasake ni “bazan sake ka ba BGS bazan sake ka ba nache, ida kuma nima zaka haɗa har dani ka bugane to Bismillah, a fusache BGS ya ya kwache hannunsa daga rikon da Aryan ya masa ya fice daga ɗakin sai huchi yake, bin yarinyar da kallon Aryan yayi a ranshi yana faɗin ko wacece wan nan kuma ko me ya haɗa su, wayar sa ya chiro daga aljihun wandon jeans dake jikin sa ya fara kiran layin Aunty farida,

    ….Bugu ɗaya Aunty farida ta ɗaga tare da faɗin “hello bro “Aunty farida kizo ɗakin BGS ki ɗauki wata yarinya “wata yarinya kuma? Aryan “eh nima yanzu shigowa na ka nan, na samu yana bugun wata yarinya gashi da alama ta suma “Allah dai yasa ba diyana ko hiyana bace “aa Aunty babba basu bane wan nan ma ba yar gidan nan bache “to ke nan a chikin baƙin nan ne, me tamasa zai bugi yar mutane, “to nima dai ban sani ba idan kinzo kya tambaye shi yana gama faɗin hakan ya katse kiran, ya juya ya fice daga ɗakin

    Misalin karfe 2 na rana gaba ɗaya family Abba sun haɗu a babban palon Abba dan chin abinchin rana ban da ƴanma tan Ammi sune kaɗai basa nan sai BGS wadda daman ba tare suke chin abinchi da shi ba, “kin san me Safras ya aikata yau kuwa? Chewar Abba yayi maganar yana kallan Ammi “aa me kuma yayi chewar Ammi “hmmm yar sarkin zaria ya kama ya rinƙa bugu yanzu haka tana asibiti wlh bakiga yadda mahaifinta ya bata rai ba da kyar na bashi hakuri “kai wan nan yaro to me ya haɗa su Ammi ta tambaya tana kokarin ajiye spoon ɗin hannunta, da sauri Aunty Farida tace “aa baruwan DON ita taje ɗakin sa ta same sa ai, shiru sukayi dan Abba ya gane dalilin daya sa BGS ya bugi yarinyar

    wai ina yan mata nane chewar Abba “suna ɗaki kasan diyana sarkin kwalliya che tana chan wai sai ta gama kwalliya, zata zo chin abinchin, su hiyana kuma suna jiranta chewar Ammi, murmushi Abba yayi kafin yace “ai tana da gaskiya gara ta rinƙa kwalliya sosai dan ta samu miji da wuri na aurar dasu, a sukwane Aryan ya ɗago ash eyes nashi karaf, idon nasa, ya sauka chikin na Abba dan kuwa shi Abba ke kallo mayar da kansa yayi ya sun kuyar ya ajiye spoon ɗin dake hannun sa ya ɗauki wayar sa ya fara latsawa,

    …… Aure kuma Abba Aunty farida ta tambaya da mamaki, “eh mana my daughter yanzu su diyana basu kai Aure bane, ai da diyana hiyana Zahra sun kai Aure kuma nan ba da jimawa ba zan musu, wani dogon tsaki Aryan yaja wadda yasa gaba ɗaya mutanen palo suka ɗago suna kallon sa “Aryan lfy Ummi ta tambaya tana kallan sa daga sama har kasa, rai a ɓace yace “lfy Ummi, kau da fuska Abba yayi daga kallon Aryan ya chigaba da chewa “ita kam diyana ma ai tana da masoya ga yaya bellon ta, na Yola ga kuma malamin makarantar su duk da naji anche an karya masa kafa, baya tafi to in dai diyana na son shi zan fiddashi kasar india amasa aiki, “oh my god Aryan yafaɗa chikin tsawa yana dafe kai, wadda sai da gaba ɗaya jama’ar palon suka tsorata, “Aryan kana lfy kuwa Aunty farida ta tambaya da mamaki a fiskar ta, ban za yayi dasu ko sannu bai cheba, Abba kuwa chewa yayi “kai ku kyalesa mana tun da ba ya son magana, mikewa Aunty farida tayi daga nata kujerar tana faɗin “aa Abba wan nan irin tsawa haka ba lfy ba ta karisa maganar tana karisawa wajen da Aryan ke zaune, hannu tasa tana shafa kansa kafin tace “me nenen bro, ɗago ash eyes nashi yayi wadda suka sauya sukayi jaa ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi zai yi magana ke nan, sai sukaji yar siririyar muryan diyana tana doko sallama tun daga bakin kofar palon

    Mai da kallon su gaba ɗaya mutanen palon su kayi izuwa bakin kofar palon, anko su kayi gaba ɗayan su chiki jalla biya pink colour Zahra hiyana lamrat amrat duk sun yafa mayafin rigar amma ban da diyana, ita kam ta tasaki wan nan bakin lallausan dogon gashin nan nata har gadon baya, a nitse suka kariso chikin palon kowan nan su na zauna a kujera table ɗin,

    Wow my daughter kinyi kyau sosai chewar Abba yayi maganar yana kallan diyana, dan ita kaɗai che a chikin su tayi kwalliya, “laaaa Abba kasan me ranan ma yaya yusuf yace nayi kyau haka yaya Aryan ma da na kai masa coffee yace nayi kyau dana ɗan kwali, asukwane matasan gidan suka juyo da kallan su kan Aryan,

    ɗaure fuska sosai Aryan yayi kamar bai taɓa dariya ba ya chigaba da latsa wayar sa, ita kuwa diyaba ko ajikin ta sai murmushi take tana bawa Abba lbr, ganin Aryan ya ɓata rai sosai ne yasa Yusuf yace “eh mana my sister ai dole kowa yace kina da kyau, to ke ba sis ɗin mu bace idan bamu yabe ki ba, waza mu yaba, wani murmushi diyana ta saki tana faɗin “Allah yaya Yusuf idan nayi kwalli ina kyau? “kai sosai ma kuwa may sis ai duk gidan nan kin fi kowa kyau kuma kin fi kowa… Bai karisa maganar ba saka makon wani mugun kallon da Aryan ya wurga masa, irin kallon nan na ina ruwan ka da ita idan ma tafi kowa kyau, shiru Yusuf yayi a chikin zuchiya yana tunani kai yaya Aryan akoi bala’e kishi to kai kaki bayyana soyayyarka san nan kuma idan wani na ya bonta ko ya raɓe ta ka hukun tashi, yanzu da kake harara’ta ni ina ruwana ai ban che ina son taba kawai yabon ta nake ni da nake da mai baby . Juyawa Aunty farida tayi ta koma wajen zaman ta ta zauna, shiru palon yayi sai karar spoon kawai zaka ji

    “Yauwa yaya Aryan wan nan jakar da ka bani nan taki buɗuwa, kullun nache zan kawo ka buɗe min sai na rinƙa mantawa, chewar diyana tayi maganar tana kallon Aryan, tab aiko gaba ɗaya palon sun zuba musu ido suna jiran amsar da zai bata, ɗago ash eyes nashi yayi ya sauke su kan face nata sai murnushi take nan take kuma sai yaji wani sanyi na ratsa zu chiyar sa, calmly ya fara magana “eh nina kulle jakar zan buɗe miki amma ba yanzu ba, tirkashi Aunty amarya ji take kamar ta tashi ta shake diyana dan bakin chiki Amma tana tsoron Abba

    Ayya yaya Aryan ka buɗemin kaji, kaga su Aunty Zahra duk sun sa nasu tsara bar kuma wlh kayan nasu yamin kyau nima ina son saka nawa ta karisa maganar kamar zata yi kuka, zuba mata ash eyes nashi yayi sosai, ya kasa kawar da kallon sa daga gare ta, Abba dai ajiye spoon nashi yayi ya zubawa Romeo and Juliet ido kawai yana kallan su, Khalid Yusuf Aunty farida sai murnushi suke suna murna, Aunty amarya Aunty Maryam kuwa kamar zasu mutu dan bakin chiki, Ammi da Ummi kam ko ajikin su abin chin su kawai suke chi basu ma lura da Abun da ke faruwa ba, Fahad ma abinchin sa yake chi ko ajikin sa bai ma san suna yi ba haidar Umar sai satar kallan yaya Aryan suke suna mamaki, tsoro suke kar ya kama su suna kallon sa, Aunty salma Aunty mardiya wayoyin su suke latsawa han kalin su baya kan jamar palon

    Da kyar ya iya saita voice nashi kasa kasa kamar mai raɗa yace “an jima ki kawo min jakar na buɗe miki yana gama faɗin hakan ya miƙe da sauri ya bar palon, dawo da kallon ta Aunty farida tayi kan Abba, ta kashe masa ido ɗaya wani cool murmushi Abba ya sake mata a hankali ya motsa lips nashi, yayi ta alama da mun fara nasara, gyaɗa masa kai kawai Aunty farida tayi san nan ta chigaba da chin abin chinta.

    Misalin karfe 3 :30 na rana gaba ɗaya ƴanmatan Ammi suna zaune a karamin palon sama na ɓangaren Ammi hiyana na riƙe da Alkur’ani mai girma tana karatu, diyana na buga game a wayar Zahra lamrat da amrat suna kallo Film a makeken Tv dake makale a bango, Zahra riƙe da littafin husnul Muslim tana karatu addu’oe, hankalin su yayi nisa a kan abubuwar da suke,

    …. da sallama Yusuf ya shigo palon da sauri suka ɗago suna kallon sa, da gudu lamrat ta miƙe ta nufe’sa hannu ya buɗe mata ta faɗa kan faffaɗar kirjinsa ya mai da hannun sa ya rufe yana faɗin “my baby nayi kewar ki, cikin shogoɓa tace “nima nayi kewar ka yaya Yusuf, hannu yasa yana shafa kanta a hankali yana faɗin “my baby ina san gashin nan naki kyau yake min, lamrat zata yi magana yayi sauri raba jikinta da nashi kasan chewar yaji alamun tafiya ta bayanzu kamar mutun zai shigo palon, riko hannun ta yayi suka karisa chikin palon suka zauna saman sofa mai zaman mutun 3,

    da sallama Khalid ya shigo palon shima da gudu Zahra ta miƙe tanufe sa, har zata rungume sa sai kuma ta dakata, kallanta yake itama tana kallon sa “sannu da zuwa yaya Khalid ta faɗa tana sun kuyar da kai “Auta yau kam babu oyoyo ne ya tambaya yana ɗago haɓatar da hannun’sa, chikin shagwaɓa tace “Ammi che tace wai kai zan Aura kuma na daina yi maka oyoyo sai bayan Aure, wani nauyayyar ajiyar zuchiya Khalid ya sauke tare da faɗin “da gaske Auta Ammi ta faɗa miki ni zaki Aura, gyaɗa masa kai Zahra tayi alamar eh, gyara tsayuwar sa yayi kafin yace “to kina sona, juyawa Zahra tayi zata gudu yayi sauri riko hannunta sai lokachin idon’sa ya sauka kan Yusuf dake zaune ya zuba musu ido, diyana kam bata ma san sunayi ba game nata kawai take bugawa hiyana ma kanta na kan qur’ani karatun ta kawai take

    Harara Khalid ya wugawa Yusuf zai yi magana ke nan haidar ya shigo da gudu yana faɗin Ammi, Ammi ina kike yaya Ahmad ya mut….✍️

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    1 Duk Karfin Izzata
    2 Gidan Aunty
    3 Jini Ɗaya
    4 Sarki Sameer
    5 Kafita Zakka

    Kar kubari abaku lbr love Story’s

    *💫STAR LADY💫*27

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*
    Star lady

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *