Blog

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 22

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 22

    Episode 22*

     

    Sosai Aryan ke kallan chikin idon ta, kasa tayi da kai dan bazata iya chigaba da haɗa ido da shi ba, sake matsowa kusa da ita sosai yayi, ya matse ta da jikin,bangon “murya na rawa tace dan Allah yaya Aryan kayi hakuri, maganar da tayin nan yasa yaji tamkar an chan ka masa mashi a zuchiya,da kyar ya iya buɗe baki kamar mai raɗa yake faɗin “wae banace karki sake magana ba, hannu tasa ta toshe bakin ta, a hankali ya haɗe fuskar su waje ɗaya,hanchin su na gogan na juna rutse ido tayi dan baza ta iya kallan chikin idon saba,calmly yafara magana “daga yau karki sake kwalliya da daddare,kuma idan wani yasake yima ki magana kika amsa shi sai na ɓab’ɓallaki, yau kuma ina ɗan kwalin ki, a tsorache ta buɗe baki har kerma lips nata keyi tana faɗin kayi hakuri…bai bari ta karisa ba da sauri ya ɗora ya’tsansa a saman lips nata, yana girgiza mata kai yana faɗin “ae banche kiyi magana bako, kiyi shiru ki saurare ni, kawai, shiru ya ɗanyi yana kallan yan da lips na ta ke kerma dan tsoro jiyayi tamkar yayi kissing nata, amma ba zai iya hakan ba itakuwa kara runtse ido tayi dan sai kerma gaba ɗaya jikin ta yake, almost 10mnt suna saye a haka, da kyar ya iya buɗe baki dan yadda yake ji, ya chigaba dace wa “me yasa bakya jin magana tane eh? ko dan kinga ina damuwa da kirinƙa sa ɗan kwalin shiyasa kike kin sawa, to shike nan zan fara hukun taki,a kan hakan,yanzu dai zo nan kifara tsallen kwaɗo yana kai karshen maganar a zafafe ya sake ta da sauri ya juya ya koma saman sofa ya zauna sai lumshe ido yake

    ahankali ta duka yafara frog jump tana kewaye palon tana hawaye,tun tana kuka a hankali har tafara da ɗan sauti, yana zaune yana jin ta sai faman runtse ido yake,yana chiza laɓɓan SA, dan har chikin ransa yake jin kukan nata, amma yazama dole yarin ƙa hukun tata, kodan tarin ƙa jin maganar sa, frog jump take sosai ga high heel a kafarta kamar an hanata chirewa, sai kuka take,kaɗan kaɗan tafara jin chiwon chiki,amma tana tsoran faɗawa faɗa masa, azaba yayi azaba,sae faman nishi take numfashin ta na fita da sauri sauri jinyadda take numfashine yasa Aryan ɗagowa, ya kalle’ta,Subhanallah, da sauri yamiƙe yanufeta yana faɗin lfy kike kuwa sis,bai kai ga karisawa wajen taba yaga ta sulale kasa kamar bata numfashi,da sauri ya karisa wajen ya duka, a ruɗe yasa hannu ya tallabo kanta yana faɗin Ke,ke,lfy kike kuwa,ɗayan hannun’sa yasa,a saitin kofar hanchin ta dan yaji shin tana numfashi, jin bata numfashi alamar ta sume,ne yasa ya miƙe da sauri ya ɗauke’ta chak yaɗora ta saman sofa, yanufi freij ya ɗauko robar ruwan Faro mai sanyi yadawo ya zauna a gefen ta, buɗe robar ruwan yayi ya tarbo a hannun’sa ya shafa mata a fuska,dogon numfashi taja, a hankali ya furta “ke kina lfy kuwa slowly ta buɗe idon ta a kan face nashi,da sauri ta sake runtse idon tana matsar kwalla, shiru yayi yana kallan’ta wasa wasa tafara juyi tana kara sautin kukan,”ke wae meke damun ki’ne,ya tambaya a ɗan ruɗe dan a’yanayin dayake kallanta kamar period nata ne ke san zuwa chikin kuka take faɗin “chiki yaya Aryan chiki’na wayyo Allah,hiyana ta kizo zan mutu, da sauri yasa hannu ya chire hannu’ta daga rikon datawa chikin nata,ya dora hannun sa awajen,a sukwane kuma yachire hannun nasa dan wani irin shock da yaji, kallan face nata yake dan ya tabbatar da abun dayake zargi shin period ko dai nomal chiwon chikine, ita kuwa sae kuka take, bazai iya jure kukan nata ba, a zafafe ya miƙe ya koma chikin betroom ɗin sa, jim kaɗan sae gashi ya fito riƙe da sirinjin allura,idon ta a lumshe sae kuka take tana juyi a saman sofan, a gefen ta ya zauna ya kama hannun ta a hankali,dan yasan in ta buɗe ido bazata tsaya ya mata allura ba,gashi tana bukatar alluran kodan period ɗin yazo mata da sauki,chikin dabara ya ɗaure hannun nata ya fara ne man jijiya,itakam sae kuka take dan ba tama san yana kusa da ita ba, gyara zaman’sa yayi da kyau, chikin dabara ya tsira mata alluran da sauri ya mata ya zare,sirinjin, a’sukwane ta buɗe ido tana ko’karin ihu,hannu yasa ya rufe bakin nata yana girgiza mata kae,”tashi kije ɗaki ki kwanta yayi maganar yana zame hannun sa daga bakin’ta, chikin dashe war murya take faɗin “yaya Aryan wlh bazan iya tafiya ba,ta karisa maganar tana sakin wani,kuka mara sauti,dafe kae yayi yana faɗin”wae banace kukan nan ya isaba kiyi shiru haka nan,yana gama faɗin hakan yamiƙe,ya ɗauke ta chak ya saɓa’ta a kafaɗar’sa yayi waje da ita,da sauri sauri yake tafi kai tsaye ɓangaren Ammi,yanufa da ita,da sallama ya’shigo palon babu kowa,a hankali yafara takawa izuwa ɗakin su kamar bai san taka kasan, kodaya shiga sae daya sauke wani nauyayyar ajiyar zuchiya,dan ganin su Zahra sunyi barchi, saman sofa ya kwantar da ita, ta buɗe baki zata masa godiya da sauri ya juya ya bar ɗakin,har yana tun tuɓe, chire takalman kafar ta tayi ta kwanta,ta dafe chikin ta ba jimawa barchi yayi awan gaba da ita

    Aban garen Aryan yana fita ɓangaren Ammi ɗakin sa ya koma,a gurguje ya shiga, toilet wanka yayi ya shirya chikin kayan barchi,riga zuwa goiwa mai igiya, gaban rigan a buɗe take faffaɗar kirjin nan nasa awaje rigar fari ne tas,mai laushi sae kamshi yake zubawa fitowa palo yayi ya ɗauki coffee ɗin da diyana ta kawo masa,ya koma betroom,kaɗan yasha saboda coffee ɗin yayi sanyi, ajiyewa yayi kan table ɗin tsakiyar ɗakin,ya haye saman katafaren gadan’sa ba jimawa barchi yayi awon gama dashi

    Washe gari tun asuba su Ammi suka shirya, Ammi Aunty farida hiyana diyana Zahra yusuf Khalid Aryan da kuma DON, lamrat da amrat kuma Anbar su wajen Aunty mardiya “wasu dan ƙara dan karan, motochi masu numfashi guda 5 suka ɗauƙesu zuwa Airport, ajere motochin suka jera har Airport, Ammi da Aunty farida mota ɗaya suka shiga,DON da Aryan motar’su ɗaya,hiyana diyana da kuma Zahra motar ɗaya Khalid da Yusuf ma motar’su ɗaya,ɗayan motan kuma sojoji ne a chiki,diyana sae murna take yau zataga yaya bello da innar yaya bello, Zahra ma sae murna take yau zataje kauye dan inba makaranta ba bata taba zuwa ko inaba,shiyasa ta dage sae tabisu, idan muka koma ɓangaren DON kuwa kamar zai mutu dan bakin chiki sae wani ɓata fuska yake kamar anche masa kwasan kashi zaije,Aryan Khalid Yusuf kam ko ajikin su basu damuba,

    “da private jet na yaya Aryan suka tafi,tun jirgin’su bai sauƙa ba motochi 6 daga gidan sarkin yola ke jiran’su a Airport karfe 10 na safe jirgin’su ya sauƙa, basu wani ɓata lokachi chikin jirgin ba suka fito,DON yafara fitowa fiskar nan tamkar wani mayin wachin zaki taku yake irin na jaruman maza,daka kansa kaga wadda akai wa zuwa dole,Aryan na biye dashi a baya,sai Khalid da Yusuf,Aunty farida rike da hannun diyana suma suka sau’ko Ammi na biye dasu Abaya,sai Zahra da hiyana,Shahram da Abdol ne karshen fitowa,kae tsaye wajen motochin suka nufa, da sauri Shahram da Abdol suka fara buɗe musu kofar motochin, Aunty farida da Ammi mota ɗaya suka shiga,DON da Aryan motar su ɗaya, Khalid da Yusuf suma motar su ɗaya,hiyana diyana Zahra matar su suma ɗaya,sai Abdul da Shahram suka shiga ɗayan motar suma,kamar dai yadda sukazo,a jere motochin suka bar Airport ɗin da ma tsakai chin gudu,

    kai tsaye kauyen jambutu suka nufa, wato kauyen su hiyana haka suka rinƙa keta dajin nan har kofar gidan su hiyana sukayi parking,na motochin, da yake yau kasuwar garine, shiru garin yayi ba jama’a duk sun tafi kasuwa,da sauri Shahram da Abdol suka fito daga nasu motar, Shahram yazo ya buɗewa Aryan, Abdol kuma ya buɗewa DON,kafa DON ya zuro waje batare daya fitoba yana zaune chikin motar,yana latsa waya yana wani kwaɓe fuska, Aryan kuwa,fitowa yayi yana kallan yanayin garin,Ammi da Aunty farida suka fito suka jera zuwa chikin gd “Ammi nikam bari naje dubo yaya bello tukun nan chewar diyana tafaɗi hakan tana murnushi,”bazakije ba wuche ki koma chikin moto Aryan yafaɗi hakan chikin tsawa,”Ammi dake tsaye a dai dai bakin kofar shiga gidan su hiyana, tace “a’a ina ruwan ka da ita, kasan halak chin da bello yamusu ne jeki abun ki diyana muma muna zuwa ai,bari mu gama da nan tukun nan, Tun Ammi bata kae karshen maganar ba diyana ta kwasa Aguje ta tanufi hanyar gidan su yaya bello, kwafa Aryan yayi a zuchiyar sa yana faɗin zamu haɗune, hiyana da Zahra ma fitowa sukayi su kabi bayan su Ammi, “to ni dai tun da Allah ya kawomu kauye yau barinaje naga gari chewar Khalid da sauri Yusuf yace “a’a jirani muje tare jerawa sukayi tare sukanufi chikin gonaki, wani dogon tsaki DON yaja yana faɗin “ni gaskiya an chucheni wlh da akasani dole nazo garin nan, Aryan dake tsaye kusa dashi bai san sanda dariya ta kub’che masa ba dan yadda DON yayi maganar, wani mugun kallo DON ya watsa masa yana faɗin me kakewa dariya to “kai nakewa dariya mana yanzu dan Allah prince menene laifin garin nan, ae kodan albarkachin a nan aka haifi Ammi ka girmama garin koh, tsaki kawai DON yaja batare daya sake chewa komai ba

    Diyana kuwa da gudu ta faɗa gidan su bello ko sallama babu tun a kofar gida take faɗin “yaya bello ina kake yaya bello ina kake, bello da buba suna zaune a kan tabar ma a tsakar gida innar bello na girki, inna buba bata nan, hasana matar bello tana Shara,a tsakar gd, da sauri bello ya miƙe jin muryan diyana,dan kuwa ko mutuwa zaiyi ya dawo bazai manta voice na diyana ba, da gudu diyana ta kariso chikin gida kai tsaye wajen yaya bello tanufa zata rungume’sa kome ta tuna sai kuma taja birki, tana kallan sa shima ita yake kallo chike da farinchi yace “diyana kece? diyana baki yaki rufuwa sai dariya take tace “yaya bello ina….bata kai karshen maganar ba ta sake wani ihu sakamakon san dar da bubu ya buga mata a goshin’ta, kan kache me jini ya wanke mata fuska ihu take sosai shi kuwa buba kamar mahaukachin ya sake ɗaga sandar ya buga mata a kafa, nan take ta faɗi kasa tana ihu, a zafafe bello ya ɗamki sandar yana kokarin kwache wa buba kuwa yaki saki nan take suka kaure da faɗa, da gudu innar buba tafito daga kichin tana salati, hasana kuwa jefar da tsintsinyar hannun ta tayi tanufi ɗaki da gudu dan tsoro, ganin buba da bello sun kaure da faɗane yasa diyana ta miƙe da kyar, tanufi hanyar fita daga gidan,asukwane buba ya sakarwa bello sandar yabi bayan diyana da gudu yana faɗin yau sai na kashe’ki shegiya, diyana kuwa ganin buba na zuwane yasa ta tattara iya sauran karfin ta ta watsa da gudu tayi waje tana ihu

    Jin ihun diyana yasa Aryan ɗagowa a’sukwane, ganin diyana na gudu ga jikinta duk jini yasa Aryan ya nufe ta da sauri, da gudu su Ammi ma sukayo waje jin ana ihu,

    Diyana na kokarin faɗuwa Aryan ya karisa a zafafe batare da ya damu da jinin dake jikin taba ya rungumeta a kirjin’sa yana faɗin “lfy me yasa me ki eh.. bai kai ga rufe baki ba sai ga buba ya fito da gudu yana faɗin “sai na kashe ki ni zanyi ajalin ki a zuchiye Aryan ya saki diyana tana tangal tangal zata faɗi bai ma luraba idon sa ya rufe gadan gadan ya nufi buba,da gudu Aunty farida ta kariso wajen ta riƙe diyana dake kokarin faɗuwa,ta rungumeta suka koma chikin gidan su hiyana na, bello daya biyo bayan buba dan ya dakatar dashi kar ya bugi diyana ganin dasu Ammi tazo yasa ya koma gefe ya harɗe hannu a kirji yana kallonsu, DON kuwa yana zaune ko kallan inda su diyana suke bai yiba bare ma ya tanka sai latsa wayarsa yake, dayaji hayaniyar jama’a na damun sa sai ya ɗauko bluetooth yasa a kunnen sa ya kunna kira’an Al qur’ani mai girma na minshawi ya kure volume ya jingina da kujerar motar ya lunshe ido

    Buba ganin Aryan ya tin’karosa gadan gadan ga fiskar nan tasa kamar wani,mayinwachin zaki, a’sukwane buba ya juya zai koma chikin gd, sai dai ina taku biyu Aryan yayi ya dam ki wuyar’sa ta baya ɗagashi sama Aryan yayi, yayi wurgi dashi gefe wani ihun azaba buba ya saki, gadan gadan Aryan ya nufeshi dam kar wuyar sa yayi ya kai masa wani naushi a fiska nan take wajen ta kunbura, ihu buba yake kamar makoshin sa zata fashe, baji ba gani Aryan ke kai masa bugu ta ko ina, jin yadda buba ke ihu da kyar muryar sa ke fita ne yasa Ammi ta nufesu da sauri dan kar Aryan yayi kisan kai, daga ɗan baya Ammi ta tsaya,a tsorache tace “Aryan ka kyalesa haka ya isa, Aryan bai ma san tana yi ba dan baya ji baya gani bugu kawai yake kai wa buba duk ya fashe masa jiki ga fuskar sa ta kun bura sun tum,

    Ammi ta ruɗe sosai dan Aryan baya chikin hayyachin’sa kotayi magana bazai jiba gashi Aunty farida tayi chikin gd da diyana, bare ma tayiwa Aryan magana, da sauri ta juya tanufi wajen DON zaune yake a chikin motar idon sa a lunshe hankalinsa kwanche, dan yada Bluetooth bai ma san meke faruwa ba”kai katashi kaje ka dakatar da Aryan daga bugun ɗan mutane Ammi tafaɗa tana kallo face nash, shiru DON bai amsa ba kuma bai buɗe ido ba, ganin hakan yasa Ammi tayi tunanin kodai barchi yake, da sauri tasa hannu tana ɗan bubbuga Shi, slowly ya ware green eyes nashi a kan face ɗin Ammi, da sauri ya chire bluetooth dake kunnensa yana faɗin Ammi lfy, “ina fa lfy ga Aryan chan yana kokarin kisan kai, katashi kaje ka dakatar da shi daga dukan ɗan mutane, ɗaure fuska DON yayi yana faɗin “to ni Ammi ina ruwana basu suka ja ya bugesu ba daman ai mutanen garin nan da dabbobi suke..wani birki ya jaaa da maganar asukwa’ne ya daɗa waro manya manyan green eyes nashi yana kallon Ammi, data ɗaga yatsu biyar zata zabga masa mari sai kuma itama ta dakata tana kallonsa, chikin fushi Ammi tafara magana “to a nan aka haifi uwar idan mutanen garin nan dabbobi’ne to fa kasa har dani ina daga chikin dabbobi nima ko naso ko baka so nan shine tushen ka ta ɓangarena kuma ina alfahari da hakan,idan kaga dama katashi ka dakatar da ɗan uwan ka idan kuma bakaga dama ka barshi yayi kisan kai tana kai karshen maganar ta juya a fusache ta koma chikin gida,

    dafe kai DON yayi yana faɗin “dan Allah Ammi kiyi hakuri na tuba, why why zan ɓatawa mahaifiya’ta rai sosai haka, har take kokarin yin abun da bata taba kotan tawaba mari Ammi, kuma ni NO yau gaskiya na kure ta, sosai dole naje na nemi yafiyarta ya karisa maganar yana miƙewa kai tsaye wajen su Aryan yanufa,yana taku irin na jaruman maza,
    yana zuwa yasa hannu ya damki damtsen hannun Aryan ya jashi baya, a fusache Aryan yasake nufar buba gadan gadan, rikesa DON yayi yana faɗin “wai wan nan dukan na menene haka ya isa baka ganin ya suma ne wai ma me ya haɗaku kune, shiru Aryan yayi yakasa magana sai huchi kawai yake ga wani iska mai zafi dayake furzarwa daga bakinsa, hannunsa DON yaja har wajen mota, ɗauko robar ruwa DON yayi a chikin motar ya buɗe bakin robar ya miƙawa Aryan, ansan ruwan Aryan yayi ya kafa robar a bakinsa ya farasha, ganin yakusa shanyewa’ne yasa DON ya ɗauko masa wani yabuɗe yana jiran ya karisa shan’yewa, tas Aryan ya shanye ruwan, yayi jifa da robar, yasa hannu ya anshi wanda DON ke riƙe dashi ya duƙa ya zuba ruwan gaba ɗaya a tsakiyar kansa,shiru yayi Almost 7mnt sai faman furzar da wani iska mai zafi daga bakin’sa yake, ganin Aryan bai da niyar miƙewa yasa DON kamo hannunsa ya mikar dashi ya zaunar dashi chikin mota yana kallon face nashi “are U okey bro DON ya tambaya yana nazarin face ɗin shi, jinjina masa kai kawai Aryan yayi batare dayayi magana ba “me ya haɗaka da mutanen kauyen nan,har ka masa irin wan nan duka, a zafafe Aryan ya ɗago kamar wadda akawa allura yasake miƙewa yana kokarin nufar buba, da sauri DON yasake kamo hannunsa, yana faɗin “it’s ok zo kayi zaman ka ya isa haka kodai so kake ka ɗau doka a hannun kane ya isa pls, da kyar DON ya shawo kan Aryan ya hakura ya kyale buba, shiru sukayi Aryan na zaune chikin mota DON na tsaye a kusa dashi yana kallansa, almost 15mnt san nan Aryan ya ɗago yana faɗin “ina su Ammi, wani dogon numfashi DON yaja tare da sauke ajiyar zuchiya kana yace, thank God daka dawo chikin hayyachin ka, tsaki Aryan yaja kafin yace “ni bansan wulakanchi da che maka akayi bana chikin hayyachi nane pls ka faɗamin ina su Ammi “suna chikin gidan chan mana yayi maganar yana nuna gidansu hiyana da hannu, shiru Aryan yayi kamar mai tunani jingina kansa yayi da jikin kujerar motar ya lumshe ido, zuba mi shi wan nan manya manya green eyes nashi nan DON yayi yana ta kallonsa kamar mai son gano wani abu a tattare dashi.

    A ɓangaren buba kuwa, a sume yake ga jiki duk jini, bello ya ɗauke sa Chak ya saɓasa a kafadar’sa yayi chikin gida dashi, saman ta burman dake shinfiɗe a tsakar gidan bello ya kwantar dashi san nan yakira hasana, yace ta kawo masa ruwa, da sauri hasana ta kawo ruwan a kwano bello ya ansa ya ɗiba a hannun’sa ya shafawa buba a fuska, shiru bai farfaɗo ba, sake ɗibar ruwan bello yayi yasha fa masa nan ma shiru, bai farfaɗo ba zuba masa ruwa mai ɗan yawa bello yayi shiru buba ko motsi baiyi ba, dukar da kai bello yayi sai tin kirjin buba yasa kunnensa dan yaji shin mutuwa yayi ne, tabbas zuchiyar buba na har bawa to amma an zuba ruwa an zuba bai farfaɗo ba, shiru bello yayi yana tunani a wan nan yanayi innar bello tafito daga bayi ta same’su chikin ruɗu da kiɗima ta nufe’su tana tana faɗin “bello me ka masa badai dukan’sa kayi ba “a’a inna bani na dake sa ba yan uwan’su diyana ne suka masa hukunchi “to yanzu bello ya zamuyi kasan, san dai bala’e mahaifiyarsa yanzu ko zamu tsallake inuwar mu bazata taɓa yarda ba kai ka bugesa ba, shiru bello yayi bai sake chewa komai ba ya zubawa buba ido .

    A bangaren su Ammi kuwa zaune suke a tsakar gd diyana na kwanche a kan chinyar Aunty Farida tayi barchin wahala duk da an wanke mata goshin nata jinin bai daina zuba ba, miƙewa hiyana tayi tana faɗin “Aunty Zahra kizo muje ɗakin bappa,”to Zahra tace san nan ta miƙe suka nufi ɗakin bappa, kamar yadda suka bar ɗakin haka yake ba’a taɓa komai ba sai uban kura da datti da ɗakin yayi, nan fa hiyana ta shiga kakkaɓe kurar ta fito ta ɗauki tsintaiya a waje ta koma chikin ɗakin ta hau gyaran ɗakin

    Gyara zama Ammi tayi tana fuskantar Inna tafara Magana “habiba kinsan kafin Ahmadu ya rasu babu Aure a tsakanin ku Koh, to yanzu mu ba wan nan che ta kawo muba, yanzu dai wan nan gida da kike chiki kirike mun barmi’ki, ki chigaba da zaman’ki a chiki da sauri Aunty Farida tace “Ammi ya zakiche kin bata gidan kuma ina che ae ba zai yiwu kiyi kyauta da dukiyan marayu, batare da izinin suba, murmushi Ammi tayi nasu irin na manya kafin tace “feeda wan nan dukiyar dakike gani bana su hiyana su kaɗai bane har da nawa a chiki nima ina da kaso, dabbobi 60 baban mu ya rasu ya bari ga filaye da gonaki, ba yadda za’ayi nayi kyau ta da abun da ba na waba Aunty farida zatayi magana hiyana tafito daga ɗakin bappa da gudu tana faɗin Ammi ki..

     

    *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*

    *

     

  • Amatulmaleek 1

    Amatulmaleek 1

    [11/8, 3:00 PM] +234 816 839 8310: Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    1
    BismillahirRahmannir Raheem

    Shiru tayi tana sauraron yanda muryar kawunta ke tashi sbd yanda yake daga sautinsa cikin fushi da bacin rai,
    Fushi da bacin rai ne sosai tareda gajiyawa bayyane a fuskarsa datake a hade Babu sauki ko rahama ko kadan,

    Duk wannan fushi da bacin ran tareda daga sautin mahaifiyarta Dake zaune tana sauraronsa yakewa,

    Daga ita maaman har ita ‘yar tata datai girman da ciwo takeji sosai aranta a duk lokacinda aka zaunar da mahaifiyarta ana mata irin wannan fadan takeji Babu Wanda ya dago acikinsu ya kallesa bare tankawa fadan dayaketa tada jijiyar wuyansa Yana yi,

    Shi kansa kawu bellon akoda yaushe ransa tsananta Kuna da Baci yakeyi a duk lokacinda zaizo ya ringa zazzaga kwandon masifarsa a gabansu Amma Babu Me tankawa acikinsu Seya gama maama din ta bisa da yayi hakuri kawai,ita JANNAT ko kanta Bata dagowa bare tai magana.

    Wannan Karan fadan nasa da maganganun nasa sunyi tsauri akansu Dan haka idanuwanta Dana maama din duk sun ciko da kwallan da Babu dayansu dakeson yaga hawayen Dan uwansa.

    Zufan goshinsa ya share da babbar rigar jikinsa cikin maimaitawa maaman kalman karshe yace

    “Tabbas idan Abdulhameed ya sake zuwa makarantar bokon Nan aka kawo min qararsa wlh tallahi almajiranci zan Kaisa bazan iya da baqin ciki ba ‘dan uwana ya mutu be barmun komaiba Se lalurarku,
    Idan bazaki tsaya inda Allah ya ajiyeki ba keda yayanki to ki tattara ko qara gaba bazamu iya ba”.

    Juyawa yayi yabar gurin batareda ya Dena masifa da fadan da yake yi din ba harya bar kofar qaramin sashen nasu da Tin bayar rasuwar mahaifinsu suke su kadai cikinsa.

    Numfashi maamah din ta sauke batareda Kalli gefen da AmatulMaleek din take zaune ba itama tana cigaba da dinkewa Abdulhameed wandonsa Daya barke da allura duk Bata Wani iyaba sbd shekarunta Basu Kai ta iya din sosaiba.

    Dukkaninsu Babu Wanda yace komai sbd AmatulMaleek din tsananin zurfin cikinta yayi yawa duk da yarintarta Amma sosai ta iya danne abu ta boyesa a ranta.

    Maamah datasan AmatulMaleek din ba magana zatai ba sai kawai ta hadiye hawayenta sbd kada ma AmatulMaleek din ta Gani ta miqe daga zaunen datake ta nufi kayan wankin data fitar masu shegen yawa tafara yi.

    Satar kallanta AmatulMaleek tayi tareda ajiye allura da zaren hannunta tana zubawa maamah din fararen idanuwanta batareda tace komaiba,

    Abu Daya ne koyaushe yake yawo aranta shine idan har Mommy ‘yar uwar maamah dince meyasa koyaushe Se dai a Turo musu kaya da abinci Amma takasa rabasu ta daukesu daga wannan azabar rayuwar wulaqanci da tozarcin da suke ciki a hannun dangin mahaifinsu,

    A duk lokacinda abincinsu ze qare qaninta dayake qanqani sosai bara yake zuwa yayo ya samo abinda zaici su kuwa Se dai su wuni su kwana ahakan Kokuma maamah tayiwa matan gidan aikin abincinsu na dare idan ta gama a San mata Wanda zataci da ‘yayanta.

    Babban mamakinta a duk ranar da aka kawo musu kayan abinci daga gurin mommyn a ranar ake taruwa a rarrabe komai abarsu da Wanda iyakacinsu kwana biyu ya qare sun koma cikin tsanani..

    A rayuwar dasuka taso gidan dayake dauke da iyayensu Maza yanne da qannen mahaifinta kowannen da iyalinsa daga me mace biyu sai me mace uku harma dame hudu Dan haka gidan yake na taro,

    Kowa acikin gidan kansa ya sani sai iyalansa,
    Babu me iya taimakawa Wani sbd kowa nauyin dayake kansa ma yafi karfinsa Dan haka kusan rayuwar kowa tasa ta fishesa akeyi.

    Su biyar ne manyan gidan Maza Kuma kowannensu Yana cikin gidan da nasa iyalan Babu Wanda ya bar gidan duk kuwa da zaman matsuwa da akeyi a gidan,

    Babanta shine qaraminsu gaba Daya Kuma shine yayi karatun Boko Kuma shi kadaine yake aikin gwamnati a primary school din Dake qauyen nasu wanda Babu yanda baayi dashi yabar kauyen yaje abasa Wani aikin Amma yakasa tafiya anan yake vice principal har manyanci yaxo ya rasu yabar matarsa da ‘yarsa Daya AmatulMaleek dakuma jaririn qanin Amatun Wanda aka mayar masa sunan mahaifinsa Abdulhameed.

    Kafin rasuwar Babah rayuwarsu acikin gidan ahalinsu me suna Sanda Fulde rayuwa ce data bambamta da duk ahalin gidan sbd gata da kulawa da Babah ke Basu itada mahaifiyarta,
    Babah baitaba raayin Kara aureba sbd matsi da rayuwar gidan take ciki dakuma ganin yanda tarbiya ma Neman gagara takeyi ga Yan uwansa sbd yawan iyalai duk da kusan da yawa yaran gidan shine yake dauke da lalurarsu sbd nasu iyayen bazasu iyaba ba hali Kuma ahakan bawai sun Dena haihuwar bane.

    AmatulMaleek itace hasken idon mahaifinta sbd burinsa da buqatansa na son kebantar da tarbiyarta daga sauran yaran gidan da tarbiyarsu takeda qaranci duk da Yana iya kokarinsa gurin Basu tarbiyar Amma Yana yi ne iyayensu na warwarewa Dan haka ya tsayu sosai Akan tasa ‘yar wadda yake burin tata rayuwar ta ingantu dama sauran kannanta da zasuzo Dan haka baiyi qasa a gwiwa ya Sakata karatu Wanda kaf gidan a mata ita kadaice ta shiga karatun bokon.

    Ya rufe idanuwansa tareda kunnuwansa ga duk abinda zaa fada akan ‘yarsa da rayuwar Daya zabar mata Dan haka ita kanta AmatulMaleek din ta taso tamkar miskiniya Bata Hulda ko iya shiga mutane sosai hakama Bata iya fita daga sashensu zuwa kowane sashe agidan sbd sunyi yawan sosai a gidan da kusan daga Wani bangaren idan zaka Wani bangaren sai Wani acikin mazan gidan ya tare yarinya ya lalatata a hanyoyin gidan dasukeda duhu wasu lokutan,
    Da yawa yaran gidan wasunsu sun lalace ne a tsakaninsu Wanda haka ake rufe idanuwa ana daura musu aure da junansu.

    Wannan shine Mafi girman abun Dake daga hankalin Babah da maamah akan rayuwar AmatulMaleek data fita daban a cikin yaran gidan Dan haka Sam Babu inda Amatun ke fita idan ba tareda mahaifinta ba Koda kuwa aike ne to tabbas hannunta na riqe dana mahaifinta.

    Akwai tsautsayin Daya taba kusan afkuwa ga AmatulMaleek din Wanda shine abu na farko Daya daki zuciyar Babah ya Sakar masa ciwon zuciyar Daya zamar masa ciwon jiki Wanda daga karshe kusan shine ajalinsa.

    Daga Aiken Amatun can kuryar gida Wani babban Dan kawunta ya dafeta cikin soron gaba ya rufe mata Baki batareda ya bari ta gansa ba yaso illata rayuwarta batareda laakari da shekaruntaba.

    Babah ne da kansa ya riski wanna mummunan kaddarar data Saka Yanke jiki ya Fadi Allah yasa Babu abinda ya faru din AmatulMaleek din ta tsira Dan haka ya tattara masu kayansu itada mahaifiyarta zuwa Abuja gurin ‘yar uwar Kuma Aminiyar maamah sukai zamansu acan sai bayan kusan watanni masu tsayi suka dawo.
    Bayan dawowansu zuciyarsa Bata taba samun nutsuwa ko kwanciya ba da rayuwa acikin gidan Kuma ba Dan haka ya kama haya a kusa da gidan ya koma da iyalansa,

    Acan rayuwarsu ta inganta hankalinsu ya kwanta a lokacin ne AmatulMaleek tafara wayon sanin alaqar mahaifiyarta da ‘yar uwarta Mommy abeeda wadda gabaki daya rayuwarta data maamah ta bambamta Kuma bambamci me girman gaske.

    Da farko Bata taba sanin ba uwa Daya Uba dayane ya haifesu sai daga baya idan sunje gidan mommyn Taga yanda mahaifiyarta ke aiki cikin masu aiki tafara fahimtar tabbas ba uwa Daya ce ta haifesu ba Amma har lokacin tana Saka ran Uba Daya ne ya haifesu.

    Kafin rasuwar Babah babu abinda yake daga zuciyarsa tareda cizonta da girmamman kunci irin yanda rayuwa zatayi da AmatulMaleek da mahaifiyarta a cikin Yan uwansa.

    Wannan dalilin ya Saka ya Yanke hukuncin karban aikin da ASH TALBA ke bibiyansa dashi tin tini.

    Bayan ya karbo offer ta aikin da muhallin zama acan Allah beyi zaiyi aikin ba ciwo ya kwantar dashi Wanda ya zama ajalinsa.

    Da farko bayan rasuwarsa Babu yanda Madame abeeda bataiba ta tafi ‘yar uwarta musamman sbd haihuwar datai ko suna baayiba Babah din ya rasu Amma Sam dangin Babah din suka qi yarda sbd Dan abinda yabari sukeso aci dasu Dan haka dole madame ta barta a cikinsu tareda AmatulMaleek wadda take tsarar tata ‘yar qwalli Daya itama.

    Rayuwa a gidan da Babah yabarsu tayi musu nauyi sbd qarin kulawa da suke buqata Dan haihuwar maamah din da basuda me kulawa dasu ga ciwo Daya shigeta sosai itama na rashin Miji da haihuwa Amma Babu me kulawa dasu.

    Hayarsu ta qare Dan haka tini suka tattara suka koma cikin gidan zuria da suka fito Allah yasa ma Babu Wanda ya shiga bangaren nasu Dan haka suka gyara sukai zamansu.

    Tin bayan rasuwar Babah madame tabar qasar tareda mijinta da Daman ba’a qasar yake zaune ba sai dai suzo su koma.

    Madame tabar qasar Bata San halinda yar uwarta da ‘yayanta suke ciki ba na qunci da tsananin buqata Kuma Daman kaf itace kadai ke kulawa da Aminiyar tata sbd sune danginta.

    Maamah ta taso ne a hannun kakarta Amma mahaifin madame Abeeda ne yake dauke da nauyin duk wata lalurarta sbd mahaifinta kafin ya rasu shine babban yaronsa.

    Itada abeeda baitaba bambamta tsakaninsu ba sbd daukansu matsayi Daya a ransa Kuma haka ya tsaya tsayin daka ya Saka musu tsananin so da kaunar juna suka taso tamkar Yan biyu sbd tsananin kaunar dasukewa juna tareda daukan junansu Wani bangaren na rayuwarsu.

    Abeeda ma marainiya ce mamanta ta rasu Dan haka a hannun matar mahaifinta ta taso,
    Duk Wani karatu tare sukai har matakin secondary Wanda suna shekarar karshe alhaji mahaifin Abeeda ya rasu Wanda Hakan ya kawo rabuwarsu Badan sun dena kaunar juna ba sai Dan lokacin rabuwar da yayi.

    Maamah wadda sunanta na Yanka yake Asmau ta koma kauye tareda kakarta inda acan riqonta ya koma hannun dangin mahaifinta itama.

    Bayan karatun secondary Wanda Bata qarasa ba Babu Wani cigaba daya sake kusanto rayuwarta har Allah ya kawo Babah Akai mata Auren kauye Wanda ya sake durqusar da rayuwarta gaba Daya zuwa qasa danma Allah yasa ta samu Miji me kaunarta da kulawa kamansa sai rayuwar ta Dan yi mata sauki.

    Abeeda kuwa bayan rasuwar alhaji dangin mahaifiyarta itama karbanta sukai da gadonta me tsananin yawa suka bar garin gabaki daya da ita zuwa porthcrt inda acan akaci gaba da inganta rayuwarta cikin gata da kulawa tareda tarin arziki me yawa.

    Abeeda ta wuce Malaysia acan tayi karatunta Wanda a daidai lokacin Kuma Asmau tana cikin zuriar Sanda Fulde tana ganin rayuwar Auren da Babu komai acikinta sai hakuri da jarabawa bayan jarabawa.
    ##MAMUH
    Regular 700
    Vip 2k
    0022419171 access bank Maryam sani
    09033181070
    [11/8, 3:00 PM] +234 816 839 8310: Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK
    Mamuhgee
    #ZafafaBiyar

    2
    Nisan dayake tsakanin Asmau da abeeda Bai taba rage kauna ko girman junansu ba a zuciyarsu,
    Babu dawowar da Abeeda zatai Nigeria Bata zo har kauye ta ziyarci Yar uwar tata ba Dan haka kusan kaf dangin mijin asmaun Babu Wanda baisan girman alaqarta da kaunar Dake tsakaninta da Abeeda ba,

    Duk wata sutura da abincin datake ci Daya bambamta Dana Yan kauyen duka abeeda ce ta tsaya Mata akansu Koda Bata qasa ko tana qasar duk lokaci bayan lokaci sai an aikowa da Asmau abinci da suturar datake sakawa.

    Acan dangin mahaifiyar abeeda Babu Wanda Bai gama sanin matsayin kaunar Dake tsakaninsu ba Dan haka Babu Wanda yayi yunkurin hanawa saima tsayuwa da sukai akan inganta rayuwar asmaun duk da tana kauye Dan haka itama asmaun Bata da tamkarsu.

    Nisansu Bai hanasu zama abokan sirrin juna ba Dan kuwa Babu matsalar Asmau da abeeda Bata saniba kamar yanda asmaun Babu damuwar abeeda da Bata saniba.,

    Rashin samun haihuwar Asmau da wuri yasaka Abeeda ta samu Samar dauko asmaun ta tafi da ita ganin Wani likita a porthcrt,

    Da farko hankalin Asmau Bai tashi ba da rashin haihuwarta ba Amma ganin yanda abeeda ta damu ta kwallafa Rai Akai sai hankalinta ya tashi Wanda yasaka dole aka tsaya aka ringa yawon asibiti da asmaun.

    Kamar yanda hausawa sukace ita dai kaddara yashi ce ko an dunkulata Bata dunquluwa, Abeeda ta tsaya da karfi da dukiyarta an nemawa Asmau lafiya Bata samu nutsuwa da Kwanciyar hankaliba Saida Asmau ta wayi gari ta samu ciki a jikinta.

    Cikin Asmau nada wata biyu Aka kulla Auren Abeeda da Wani ‘dan babban Aminin mahaifinta Aleeyu Muh’d Talba Wanda dagashi har ita bawai suna son juna bane Amma dayake Auren na connection ne Basu damu ba.

    Auren Abeeda da Aleeyu aure ne na fitowar Rabon haihuwa kawai Wanda Allah ya kaddaro a tsakaninsu sbd Auren da wata uku Allah ya karbi ransa sanadin jinyar ciwon cikin kwana Daya kacal.

    Bayan rasuwarsa ranar da Abeeda ta fita takaba ranar Asmau ta haifi AmatulMaleek wadda taci sunan Abeeda Amma suke kiranta da AmatulMaleek din sbd shine sunan da mahaifinta yafiso din Dan haka take amsa sunan AmatulMaleek din Amma a rubuce Abeeda AmatulMaleek ne sunanta.

    Abeeda Bata samu zuwa haihuwar AmatulMaleek ba sbd itama tana fama da tsohon ciki me tsananin wahala Wanda ya Sakata shiga ciwo sosai.

    Asmau duk da jegonta bata zaunaba haka taxo ta zauna jinyar abeeda harta samu sauki itama ta qarasa watanninta ta haifi ‘ya mace itama take aka Saka mata sunan ASMAU Amma ana kiranta da Husnah.

    A ranar da akai sunan Husnah a ranar aka daura Auren Abeeda da ASHRAF MUH’D TALBA ‘dan uwan Aleeyu Wanda suke Yan biyu batareda sun taba ganin juna ba Amma hakanan zuciyar abeeda tafi kamuwa da son Ash Talba akan Aleeyu sedai Kuma halin Aleeyu ya bambamta sosai da ASH Dan haka zamanta dashi yafara Bata wuya ta bangarora da dama.

    Wanna shine damuwar data fara Sako Auren Abeeda a gaba sedai Kuma Asmau ta tsaya sosai gurin Bata qwarin gwiwa Dan ta fuskanci aurenta ta tsaya ta riqe mijinta da kyau.

    ASH baida raayin Auren mace biyu Bai taba shaawan Hakan ba Dan haka a zuciya da gangar jikinsa ya amshi abeeda dari bisa dari sedai rashin fuskantar halin juna da sanin juna yanda ya kamata yake azabtar da Auren nasu Amma Kuma kasancewar sunada ilimi dukkaninsu ya Saka Basu taba nunawa junansu gajiya ko gazawa da zamanba bare juna ba,

    Matsalar datafi quntatar da Auren nasu shine rashin iya kulawa da soyayyar Auren Abeeda wadda Sam ta kasa yanda zata iya shiga zuciyarsa ta mallakesa ta hanyar kauna ko soyayyarta.

    A idanuwansa tana iya hango tsananin girmamawa ne kawai yake mata Babu wata soyayyarta bayan Hakan Dan haka ta dage sosai dan ganin ta mallakarwa kanta zuciyarsa da Babu kowa a cikinta.

    A duniya da yawa basusan ba Ash ne mahaifin Husnah ba kaman yanda Babu Wanda yasan matar Ash din bashine ya fara aurentaba.

    Zamansu me dadi da Kwanciyar hankali da wayewa suke rayuwar aurensu Dan haka ya dauketa daga kasar suka tafiyarsu inda yake rasuwarsa tareda mahaifiyarsa da kanwarsu qwalli Daya wadda ta kasance tana gida bayan auranta Daya mutu ta fito da saurayin ‘danta Wanda ya girma sosai Yana karatu Shima.

    Duk Nisan da Asmau tayi da Abeeda Hakan Bai Hana ASH yiwa Asmau farin sani ba sbd shaquwa da kusancinsu hakama da kansa ya fahimci irin girman junansu a zuciyarsu Dan haka yake respecting Asmau sosai tareda Mai gidanta Wanda yaso ya taimakawa sosai Amma Babah din yaqi yarda da Hakan Dan haka sai kawai mutunci da kusanci suka ya shiga tsakaninsu duk da Hakan ya taimakawa babah din sosai.

     

    Bayan shekaru sunja sosai a rayuwar kowannensu Abeeda tayi nasarar shiga zuciyar ASH sedai batada tabbacin ta mamaye zuciyar ne duka Amma ko a iya inda ta samu din a zuciyarsa tanada tabbacin babu Wani guri da wata zata samu shiga sbd ita kanta gurin data samu a zuciyar tasa sai data share shekaru a cikin auren kafin ta samu wannan gurin a zuciyarsa Dan haka ta tabbatarda zuciyar ASH ba guri me saukin samu ga kowace mace ba.

    Baida raayin mata kaman yanda baida Wani raayi ko time na abubuwan dasuka danganci soyayya bayan ta matarsa Abeeda wadda yake ganin iya sonta da ita din ta ishesa a rayuwarsa Bata buqatan Qari sbd baida Wani gurin bawa wata macen a rayuwarsa kwata kwata.

    Rayuwar Abeeda ta sauya ne ta tashi daga arzikin mahaifinta ta koma arzikin mijinta Wanda ya take ya rufe arzikin mahaifinta datake ganin yanada ta gado,
    A familyn ASH kusan shi kadaice me irin wannan arzikin duk da mahaifiyarsu ma nada arzikin Amma ba kamar na mahaifinsu da suka gada ba.

    ASH da Aleeyu mahaifinsu daban Wanda bayan rasuwarsa mahaifiyarsu tayi aure ta haifi Aysha wadda ita mahaifinta daban dasu Amma dai mahaifiyar tasu Daya ce.

    Sune masu arziki sosai sbd mahaifinsu shine me arziki sabanin Aysha da nata mahaifin baida Wani abun bayan rufin asiri.

    Da wannan qyashi da Jin zafin Aysha ta tashi a cikinsu har Allah yasa Akai mata aure ta haihu ta fito daganan aurenta uku tana fitowa karshe dai ta hakura da auren sbd takasa samun masu iri arzikin ‘dan uwanta ASH dashi kadaine yanzu ya rage mata hakama ummansu ta rasu Dan haka ta tattara itada ‘danta NAUFAL ta suka dawo karkashin ASH tamkar shine Uba mahaifin Naufal duk Wani gata da Jin dadi Babu abinda basa samu a gidan karshe dai kusan gidan ya dawo hannun mom Aysha kaman yanda ake kiranta da girma yazo mata sbd ta girma Abeeda sosai ba laifi Dan haka kusan gidan idan aka cire Mai girma me gidan the grt ASH TALBA mom Aysha itace me fada a ji Dan kusan kamar matsayinsu Daya agidan Ash itada abeeda.

    Rayuwar mom Aysha a cikinsu ya Saka duk yanda kusancin Asmau da abeeda yake yafara raguwa sbd mom Aysha Asmau ce macen datake Jin har cikin zuciyarta Bata kaunar kusantuwarta da Yan ahalin gidan Dan haka tsauri da kaidojin mom Aysha akan Asmau yasa taji Bata shaawan zuwa gidan Abeeda Koda suna gari Dan haka da wannan kusancinsu yafara raguwa dakuma manyanci Daya zo musu dukkaninsu.

    Bayan haihuwar husnah Abeeda Bata sake haihuwa ba Saida manyanci yaxo musu ta haifi ‘da namiji Wanda ya kasance a gurin ASH TALBA shi kadaine jininsa Amma Kuma a zuciyarsa haydar din da Husnah matsayinsu Daya Dan kuwa ita kanta Husnah duk da ta girma batasan ba ASH TALBA mahaifin Daya haifetaba.

    AmatulMaleek tanada shekaru goma sha uku a duniya maamah ta sake haihuwar ta haifi qaninta Abdulhameed Wanda harya girma baisan mahaifinsa ba tinda kafin sunansa Babah ya rasu yabarsu cikin halin qaqanikayi.

    Rayuwarsu ta zama me Wani irin babban gibine da basusan tayaya zamu cikesaba ko samun me cike musu shi,
    Qunci da wahala da yunwa da azaba tareda hantara suke rayuwa acikinsa har Abdulhameed ya girma yayi wayo,
    Tunda tagama primary karatunta ya tsaya,
    Abdulhameed kuwa karfi da yaji ya zama kamar almajiri sbd ko suturar da zai Saka basuda ita sai abinda Allah ya Basu kawai suke Samu.

    A gidan kaf Babu Wanda yake iya Basu abincim da zasuci sbd kowa ta kansa yakeyi kowa na fama da rashi.

    Madame abeeda wadda a yanxu matsayinsu da sunansu ya zarce na Baya sbd matsayin da ASH yake dashi a gurin Al’ummar Dake tsananin son ya tsaya musu a matsayin gwamnan jahar Amma baida raayin siyasa duk da Hakan jamaa sosai sukeyinsa Dan haka kusan Babu Wanda baisan the grt ASH TALBA ba.

    Rayuwarsa data iyalansa kwata kwata baa qasar yake yinta ba sai dai yakan Fi iyalan nasa zuwa Dan haka jamaa sukeyinsa sbd taimakon dayake bayarwa kaman baisan zafin dukiyar ba Dan haka manya da yawa mutanensa ne hakama talakawan ma mutanensa ne hakama masu kudin Dan haka kowa yinsa yakeyi duk da da yawa baisanma sunayi ba Amma Kam sosai aketa Daman gwagwarmaya da rigimar shi akeso amma Sam Baya raayi.

    Ta bangaren matarsa Abeeda kuwa wadda duniya ke kira da Madame abeeda Talba tini rayuwarta data ‘yayanta ta zama abin kallo daga nesa sbd tsaron da ake Basu bana wasa bane sbd ASH Bai hadasu da komai nasa ba Dan haka a yanzu tsakaninta da maamah aike ne kawai Shima sai can idan lokaci me tsayi yaja Dan haka itama maaman ta hakura ta rungumi marayun ‘yayanta.

     

    *****Bayan rasuwar Babah da shekara biyu kawu bello ya aure Maamah din wadda bayan wahala da ukubar data ringa sha a hannun kishiyoyi Babu abinda suka Qaru dashi itada ‘yayanta
    Ahakan suka ringa Shan kuncin rayuwa har kawun ya gaji ya saketa sbd yace bazai iyaba lalurar tai masa yawa Dan haka dai anan cikin gidan Akai auren anan Akai sakin taci gaba da gwagwarmaya itada ‘yayanta Wanda tanaji tana Gani Abdulhameed yakoma almajiri AmatulMaleek kuwa haka take zaman gidan Bata taba barinta fita ba Koda zuwa cikin gidan sbd yanda gidan yake sake zama hadari sosai ga duk Yan matan gidan da Yara qanana ma Dake tasowa duk da yawa sun lalace a tsakaninsu batareda sanin iyayensu ba.

    AmatulMaleek tinda tafara wayo rayuwarta ta zama tamkar kurma sbd rashin magana tinda basuda abin magantuwa akansa Dan bayan tarin kunci Babu komai a rayuwarsu Dan haka ta taso a miskilar gaske Wanda Hakan yafiwa maamah dadi da farin ciki sbd kullum kukan maamah a gaban Allah shine yanda zata bawa ‘yayanta kariya daga masifar gidan musamman AmatulMaleek datake mace.

    AMATULMALEEK
    Regular 700
    Vip 2k
    0022419171 Access bank Maryam sani
    09033181070

    #MAMUH#
    #LA HOT
    #LIFE
    #ASH TALBA
    #AMATULMALEEK
    #NAUFAL TALBA
    #MEERAH HERBS
    #ABOKIYAR NISHADI TV CHANNEL

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 20

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 20

    Episode 20*

     

    A fusache DON yamike ya ɗaga yatsu biyar zai zabga mata mari green eyes nashi ya sauƙa a kan face ɗin Aryan dake zaune ya zuba musu ash eyes nashi ” da sauri Ammi tace karka kuskura ka kai hannunka jikinta takarisa maganar a fusache”a hankali DON ya sauke hannun’sa sai huchi yake tamka wani zaki, bai karisa sauke hannun’sa ba, yaga Aryan ya miƙe ya ɗauke Aunty Maryam dawani gigitachen mari yasake kara mata ta ɗayan gefen kumatun a fusache yayi kanta daniyar bugunta ” da sauri DON ya rikesa yana faɗin NO Aryan NO idan kace zaka bugeta a yanayin dakake’n nan wlh zaka iya kasheta ” Prince kasake kasakeni nacema Aryan yayi maganar chikin tsawa da zafin rai ” bazan sake kaba Aryan kadawo chikin hayyachin’ka mana kasan me kakesan aika tawa kuwa ” Aryan idon’sa ya rufe chikin tsawa yake magana Safras nache kasakeni koh “DON yalura Aryan baya chikin hayya’chensa, dan kuwa baitaba kiransa da Safras ba sai dai yace DON kokuma prince dan haka sai yayi kokarin jansa sutafi ɗaki ” Aunty Maryam kuwa rungume Aunty amarya tayi tana kuka ” Ammi tamatso kusa da Aunty amarya tana faɗin kiyi hakuri Maryam ” chikin kuka Aunty Maryam ke faɗin munafuka ina ruwanki dani duk bake kika haddasa fitinarba ” wani kukan kura Aryan yayi ya kwache daga rikon da DON yamasa yanufeta gadan gadan fiskarnar tasa gaba ɗaya ta sauya idon’sa sun ƙaɗa sunyi jaa sai huchi yake jijiyoyin kan nan nasa duk sun miƙe gadan gadan ya tun kareta kamar wani mayinwachin zaki ” aguje kannen nasu sukabar palon, yarage iyayen nasu sai Aunty farida Khalid da kuma yusuf Aiman da Ahmad ma sun gudu dan sun san hali Aunty salma Aunty mardiya ma duk sungudu ” harɗe hannu a kirji DON yayi a zuchiyar’sa yana faɗin awan nan karon kam bazan hanaka ba Aryan dan kuwa ta tsallake iyakarta ka bugeta kai ɗin zaifi domin ni innace zan bugeta tofa sai dai a ɗau gawarta shiyasa tun ɗazun nake kokarin danne zuchiyata karta haura

    Aunty Maryam ganin Aryan ya nufota gadan gadan ne yasa ta zame jikinta daga na Aunty amarya zata gudu “wani damƙa Aryan yawa wuyar’ta, ta baya yajata ya bugata da jikin table,ya sake damkoh wuyar’ta yana kokarin kai mata wani bugun” ganin Aryan na kokarin kisan kai yasa Aunty farida ta nufesa da gudu ” a fusace yaɗaga hannu zai ‘kaiwa Aunty Maryam bugu a fuska da sauri Aunty farida ta kama hannun ta baya ” azuchiye yajuyo yana faɗin kasakeni DON tun bandawo kankaba ganin Aunty farida che ta rikesa yasa ya sassauta murya,pls pls Aunty farida sau ɗayan nan kawai ki kyaleni na hukunta Maryam, tun batayi aure ba takewa su Ammi wan nan rashin kunyar, dan Allah yau kubarni na dawo da ita kan hanya ”

    Aryan idan kasake ɗaura hannunka a jikin Maryam dasu nan duka ban yafemaka ba chewar Aunty amarya tayi maganar rai a bace, “runtse ido Aryan yayi ya kwache hannun’sa daga chikin na Aunty farida zuchiyar’sa na tafasa yajuya a fusace yanufi hanyar fita daga palon ” Abba dake tsaye a bakin kofa tun ɗazun yana kallan’su yakasa shigowa yasa hannu ya tare Aryan yana kallan fuskar’sa” juya mukoma chiki chiwar Abba, gaba ɗaya jama’a dake chikin falon suka juyo suna Abba ” a nitse Aryan yajuya ya koma ya zauna a kan kujeran table ɗin ” Abba bi bayan’sa da kansa ya buɗe robar ruwan faro mai sanyi ya zuba a glass cup yamiƙawa Aryan ” ba musu ya karɓa ya sha” ku zauna gaba ɗayan ku Abba yabasu umarni rai a bace ” zama sukayi a kan kujerun” tashi kema ki zauna chewar Abba yayi maganar yana nuna Aunty Maryam dake kwanche kasa tana kuka, da kyar tamike ta zauna a kan kujeran itama kusa da Aunty amarya, ga shatin yatsun Aryan biyar a kan kunchinta gefe dukka biyu “A nitse Abba yafara magana abu biyu zuwa uku nakesan faɗa a nan kubani hankalin’ku ta farko nan umarni’ne ba shawara ba duk wan da yayi laifi a gd yazama dole a hukuntashi dan haka hajara kijanye kalamanki nachewa kar Aryan yasake,taɓa Maryam yazama dole intayi laifi sumata hukunchi,duk datake babba a kansu intayi ba dai dai ba zasu mata hukunchi, na biyu wan nan maganar ta mutu daga nan ” na uku ke Maryam wlh kinji na rantse ko ko kallan banza kika sake yiwa yaran nan to ban yafe’miki ba, ba ruwanki dasu tunda bazuwa ɓan’garen’ku sukeba, ya karisa maganar chikin faɗa,sai dayaja, kutashi kuje kuyi sallah lokachin sallar issha yayi ” da sauri Aryan ya miƙe daman kamar a kan kaya yake dan baisan ganin Aunty Maryam, miƙe’wa DON ma yayi da sauri yabi bayan’sa, dan yaje ya taushesa, yadaɗe baiga Aryan a irin wan nan bacin ranba “Khalid da Yusuf ma suka mike sukabi bayan’su DON ” Aunty farida takama han’nun Aunty Maryam sukayi waje,”Ammi da Ummi ma suka mike a tare ” Abba yace Aisha keda hajara ku zauna zanyi magana daku,”Ummi najin haka tayi waje” Ummi nafita

    A nitse chikin sanyin murya Abba yafara magana,” ke Hajara banace kijanye maganar dakikayi tsaka’nin Aryan da Maryam ba,banji kinche komaiba ” na janye Aunty amarya tafaɗa tana ɗaure fuska ” to tashi kije kiyi alwala kiyi sallah,”mikewa tayi tana kunkuni tafice daga palon
    sai da Aunty amarya tafice san nan Abba yadawo da kallan’sa kan Ammi yafara magana, idan yaran nan sunyi sallah kisa diyana ta kaiwa Aryan coffee kinji ” to amma ranka shi daɗe kagafa ran’shi a ɓache kuma kusan diyana’ce ta hadda’sa masa ɓachin ran, idan taje bazai bugeta ba kuwa Ammi ta karisa maganar kamar zatayi kuka ” Abba yace aa Aisha bantaɓa magama kimin musu ba komai nace to kawai kike chewa yanzu’ma to kawai nakesan kice kuma ki isar wa diyana da sakoh na, ya karisa maganar yana kokarin mikewa a chikin zuchiyar’sa kuwa yana faɗin ae diyana ce kawai zata iyasa Aryan ya saukoh domin kuwa duk wani motsi na ƴa’ƴana ba wan da ban sani’ba duk wani abun da Aryan keyi ina sane dashi yanzu haka ba abun dayake bukata daya wuce yaga fuskar’ta da wan nan tunanin yashiga ɗaki, ” Ammi kuwa jiki ba kwari ta miƙe tafice daga palon tanufi ɓan’garen’ta

    Ammi na fita palon Abba kai tsaye,ɗakin’su diyana tanufa, da sallama tashiga ” kwanche suka su uku a kan gadon’su hiyana diyana Zahra, su amrat sun koma ɗakin’su ” suna ganin Ammi suka miƙe zaune,karisa shigo chiki Ammi tayi a bakin gadan ta zauna tasa hannu dafa hiyana tana faɗin sannu koh, Allah ya baki lfy ” hiyana tace amin, Ammi ina wuni ” murmushi Ammi tayi kafin tace lfy kunyi sallar issha’ne “aa bamuyi ba chiwar diyana ” to kutashi kuyi sallah zansa a kawo muku a’bunchi kuchi sai ku kwanta ku huta koh ” har suna haɗa baki wajen chewa to Ammi a tare suka miƙe,
    Ammi ma tamiƙewa tayi tanufi hanyar fita, har ta kai bakin kofa kuma sai tajuyo ta dubi diyana, ke diyana idan kinyi sallah kikai’wa yayan’ku Aryan coffee ” kaiii Ammi tsoran’sa fa nake ji kar naje ya bugeni ” aa diyana bazai bugeki ba kiyi sallah kije ki haɗa masa da sauri ” to Ammi amma zanyi wanka tukun nan ” to koma me zakiyi dai kiyi dawuri ki kai masa takai karshen maganar tana mai fichewa daga ɗakin

    Toilet diyana tashiga tayi wanka a gurguje ta ɗauro alwala tafito, tana fita Zahra tashiga itama danyin wanka,” shifiɗa dardu’ma diyana tayi ta ɗaura zani tasa hijab, kawai tatada sallah,”tana sallame, sallar tayi adduar, ta sosai tashafa ta mike zata naɗe, daddumar ” hiyana tace aa kibarmin zanyi Sallah” to kawai tace tanufi gaban mirrow ” diyana mezakiyi hiyana ta tambaya tana taɓe baki ” kwalliya,mana me zanyi,kuma ” kwalliya da daddare to Allah ya shirya’ki ” Ameen to tun da addua che diyana tafaɗa tana kokarin shafa foundation a fuska ” light make up tayi a face nata ta ammafa bakamin kyau tayiba, jan baki pink colour tasa a ɗan karamin bakin nan nata, sai kallan kanta take,a mirrow “Zahra dake zaune bakin gado tana jiran diyana ta matsa, awajen mirrow, itama tazo tashafa’mai,” tace kai diyana kinyi kyau har kingaji da kyau dan Allah kije, kisa kaya kikai’wa yaya Aryan coffee sa karyazo ɗakin nan ya same’mu ” dariya diyana tayi tana faɗin, Allah Aunty Zahra nayi kyau ” eh mana sosaima yanzu dai jekisa kaya,” da farinchiki a face ɗinta tajuya tanufi sip ɗin kayan’su doguwar rigar da Aunty farida ta kawo musu ta ɗau koh, zatasa ke nan ” Zahra tace diyana yakamata kisa bra kafin kisa rigar nan zaifi zama maki da kyauu dan kinga yana da igiya inba bra, aka ɗaure igiyar baya kyau ” yauwa Aunty Zahra idan dai zanyi kyau kawai kisamin diyana tafaɗa tana murna ” shiru Zahra tayi tana tunanin wai ita’kam diyana inazata kai kyau’ne, duk wan nan kyan da Allah yamata, bai isheta’ba take neman kari, duk wani abun da kacewa diyana zai ƙara mata kyau tofa koda abun bai mataba sai tayi amfani dashi itadai kawai taji anche taƙara kyau, Zahra tayi nisa chikin tunani bata an’karaba kawai sai taji ” diyana na taɓata Aunty Zahra kisamin abubuwan bra ɗin ” to juya nasa miki ” juyawa diyana tayi zahra tasa mata karfen bra ɗin ” hiyana dai baki ta taɓe tana ganin ikon god” komawa diyana tayi gaban sip ɗin ta ɗauki rigarta tasa, ta ɗaura igiyar rigar tayi kyau sosai ta ɗauki mayafin rigar ta rufa akanta tanufi wajen shoe rack nasu high heel blue kalar rigar ta ɗauƙa tasa tanufi waje kwas,kwas,kwas, abunta ”
    baki buɗe hiyana ke kallan diyana har tafita ajiyar zuchiya ta sauke ta dawo da kallanta kan Zahra”Aunty Zahra kinsan me ” Zahra tace aa bansaniba hiyana am sai kin faɗa ” wlh inaga nan gaba kasuwa kwalliya gaba ɗaya za a’ɗaukowa diyana ” dariya Zahra tayi tana faɗin eh gaskiya kam naga alama nima ” hiyana zatayi magana sukaji kwas,kwas,kwas, ” ba ko sallam diyana tashigo da sauri gaban mirrow takoma ta ɗauki kwal’bar turare hunrar da Aunty farida ta bata ta shafa a jikinta dan Aunty farida ta faɗa mata indai batasa turare bazatayi kyau ba da sauri ta ajiye kwal’bar tanufi waje ” su dai su hiyana sunga abun dayafi karfin’su ” miƙewa hiyana tayi daga kan daddumar takoma kan gado ta kwanta ” zahra Kuma ta ɗauki hijabin’ta tasa tatada sallah

    A gurguje ta haɗa masa coffee ta ɗauka tanufi ɓangaren’sa da sallama tashiga palon babu kowa kai tsaye tanufi betroom ɗin sallama tayi a bakin kofa, bata jira an amsa’ba kawai tashige chiki ” kwanche yake a katafaren gadonsa idonsa a lumshe farin singlet da short ne kawai a jikinsa asalin kirar’sa na jaruman maza ya bayyana ga wani gashi baki kwanche a chin yoyin’sa har zuwa kafofin’sa damtsen hannun’san nan kuwa kamar zasu fashe saboda karfi ” kan ɗan karamin table na chikin ɗakin ta ajuye coffee ɗin tanufi bakin gadon, zama tayi kusa dashi a nitse da cool voice kamar mai raɗa tafara kiran sunansa, tana ɗan bubbuga hannun’sa yaya Aryan, yaya Aryan katashi na kawoma coffee karyayi sanyi ” slowly yafara ware ash eyes nashi wanda suka chanza zuwa launin jaa, sauke idan nashi yayi a kan face ɗin ta, ƙara waresu sosai yayi yana kallan’ta ” diyana sai data tsorata ganin yadda idonsa suka chanza launi” mikewa tayi zata gudu ” hannu yasa da sauri ya riƙo hannun’ta, ya jata baya, ta koma ta zauna” kallanta yake sosai, nan take yaji wani sanyi na ratsa zuchiyar’sa wani farinchiki yaji, jiyake wani bakon yanayi na ziyartar zuchiyar’sa” turo ɗan bakin nan nata tayi kamar biro a shagwaɓe tafara magana yaya Aryan kayi hakuri kaji dan Allah karka bugeni, ta karisa maganar kamar zatayi kuka “shiru yayi yana kallan’ta, yakasa magana almost 10 mnt suna zaune haka yanata kallan’ta,kamar yamai data cikin’sa yakeji”turo baki diyana tasakeyi tana faɗin yaya Aryan dan Allah fa nace kayi hakuri ba dan niba” ɗan firgita yayi yadawo daga duniyar tunanin dayashiga” calmly yafara magana baki iya gaisuwa bane kuma wayace kiyi kwalli da daddaren nan” kayi hakuri to, ina wuni tafaɗa tana kun bura kumatu” sakin hannunta yayi tare da mikewa zaune ” itama ganin yasaketa tamiƙe tana kokarin tafiya ” ina zakije ya tambaya yana kallan’ta from head to toe ” ɗaki zanje ” nace kitafine ” aa kayi hakuri “to dawo nan ki zauna yayi naganar yana nuna mata drawer kefen gadon ” saman drawer taje ta zauna tana fiskantar kofar toilet
    “juyo nan ki kalleni magana zanyi dake, a nitse ta juyo tana fuskantar’sa,ganin itayake kallo yasa tayi ƙasa da kanta tana murza yan yatsun hannun’ta ” dawo da kallan’sa yayi kan hannun’ta sosai yake yakara waro idan’sa yana kallo lallenta, ba’ƙaremin kyau lallen yayi masaba ” wayamiki wan nan abin yayi maganar yana nuna lallen nata ” laaa Aunty farida ta kaimu a kamana mana kuma kasanme takawo min kayan kwalliya dayawa” zuba mata ido yayi yana kallan yadda take murmushi take magana a zuchiyar’sa yace thank God nima nasaya kayan kwalliyar
    afili kuwa yace baki bani amsa taba nace wayace kiyi kalliya da daddaren nan” nan take ta ɓata fuska ta daina murmushi ta turo baki tana faɗin yaya Aryan baa kwalliya da da’ddare’ne “anayi mana kuma kinyi kyau sosai kawai dai nine banasan kirinƙayi ” nan take kuma tafara murmushi tace laaaa yaya Aryan da gaske nayi kyau ta tambaya ” girgiza kai kawai yayi ya zuba mata ido yana kallan yadda take dariyar azuchiyar’sa yake faɗin kekam komai kikayi kyau yake maki inkina dariya ki ƙara idan kina murnushi makura che ke, kai ko kuka kike kyau yake miki ” katse mishi tunani tayi dachewa yaya Aryan intafine” girgiza mata kai yayi alamar aa “kallansa tayi sosai sai kuma tace laaaa Yaya Aryan kayi rashin lfy ne” me kikagani yayi maganar da ɗan mamaki a face nashi ” ae Naga karame’ne tafaɗa tana kara kallan’sa sosai ” yayi mamakin sosai da jin abun da tace,a zuchiyar’sa yake faɗin wow intelligent girl,tabbas ni kai na nasan na rame amma bawan daya gane hakan ko DON damuke tare bai gane hakan ba sai ke wow,

    Ajiyar chiya ya sauke ya ya juyo da idansa yayi kanta yaga itama shi take kallo,” sai yace aa banyi rashin lfy, jeki kawomin coffee ɗin karyayi sanyi ” da sauri ta mike tanufi inada ta ajiye coffee ɗin ta ɗaukoh,ta dawo tamiƙa masa ” ansa yayi yana faɗin to zauna muyi magana” zama tayi a inda tatashi ta zuba masa ido tana kallan,yadda yake shan coffee ɗin,”yaya Aryan kasan me” ɗago ido Aryan yayi yana kallanta batare dayayi magana’ba ” tachigaba dacewa Allah yaya Aryan kana kama da wan da yayi film ɗin Bahubali, nan Amma fa kafishi kyau, yama sunan shi, taƙarisa maganar tana ɗaga kai kamar mai tunani” da mamaki yake kallanta yana tunani wae daman yarinyar nan tana kallan mutane ne, murmushi kaɗan yayi yace nima bansan sunan shi ba ae ” to zan tanbayi Aunty Zahra sunan shi sai nazo nafaɗama ” batare da ya amsa mataba yace tashi kije ki ɗaukoh min trolley ɗin chan yayi maganar yana nuna mata inda trolley yake da hannun’sa ” da sauri ta miƙe tanufi wajen tayi tunanin trolley bai da nauyi, sai tasa hannu ɗaya zata ɗauka amma sai taji a’kasin hakan dan kuwa ko motsa trolley ta kasa, shi kuwa Aryan ya zuba mata ido yana kallan’ta
    Dad dagewa tayi da iya karfin ta ta jawo trolley baya baya tayi tafaɗi trolley ya faɗo mata a kan kafa kara ta fasa mai sauti ” a sukwane Aryan ya ajiye cup ɗin hannunsa ya ya miƙe ya nufuta hannu ɗaya yasa ya ɗaga trolley ya ajiye a kan gado, ya dawo kusa da ita ya duƙa yasa hannu ya kama kafar nata yana faɗin, menene abun kuka kuma, ” yaya Aryan wlh da zafi tafaɗa chikin muryan kuka” a haka kike chewa zaki auri soja matan sojoji fa jarumai ne ” turo baki tayi ga hawaye na zuba a kunchin’ta chikin shagwaɓa tace Allah yaya Aryan nima jaruma’ce ” zuba mata ido yayi yana kallan yadda take Magana gwanin burgewa, hannu ya kai kan fuskar’ta zai share mata hawayen sai dayaji wani shock saboda laushin da tsasin fatar ta, da sauri ya janye hannun’sa baya yamiƙe tsaye yana faɗin to tashi kizo ki karɓi tsaraba yayi maganr yana hawa kan gadon’sa ” a sha’gwaɓe tace wayyo Allah yaya Aryan Allah bazan iya tashiba “a sukwane Aryan ya juyo yana kallan’ta, dan yadda tayi maganar, ” a hankali kamar bayasan buɗe bakin nasa yace ki daina kukan nan ko gashi nan ae kina ɓata kwalliyar’ki ” da sauri tasa hannu ta goge hawayen tana faɗin yaya Aryan kwalliyar ya bacine ” dariyace ta kubche masa dan yadda tayi maganar,”bai bachiba yabata amsa yana murmushi ” da kyar tamike tanufi kan drawer tana ɗingisa kafa ta zauna “hayewa gadan yayi yajawo trolley ya ɓuɗe, wasu ma tsakaitan jakun kuna guda uku yachiro, daga chikin trolley ɗin, ya juyo ya dubeta yafara magana,”wan nan farin tsarabar kine a chiki, wayan nan bakake biyun kuma kibawa’su Zahra “da sauri tamiƙe ta haye kadon itama ta jawo jakunkunan tana faɗin Yaya Aryan har da kayan kwalliya”kallan’ta kawai yake yadda take zumuɗi, da farinchiki, bai ma san sanda yace, daman farinchikin da dariyar ki kawai nake burin, gani “sai jin diyana yayi tana faɗin to Yaya Aryan dariyana yana da kyau’ne ” firgigit yayi yana kallan’ta kwashesu kije ɗaki kiɓuɗe a chan” to kawai tace san nan ta saukoh daga dagon tasa hannu tajawo jakunan amma takasa ɗauka sunyi nauyi bazata iya ɗauka dukkaba” ido yazuba mata yana kallan’ta” turo baki tayi zatayi kuka ” da sauri yace aa karkimin kuka ki ɗauka mana ɗai ɗai ae bawanda yace dole ki haɗa’su koh ” nasu Zahra ta ɗauka ta bar nata zataje ta dawo suma da kyar ta iya ɗauka gakuma high heel a kafarta
    har tafita kallanta Aryan yake, wani ajiyar zuchiya ya sauke yamike yanufi toilet dan yin wanka

    lokachin da diyana ta dawo ta ɗauki ɗayan jaka’r Aryan na toilet yana wanka bai fitoba ɗaukar jakar tayi yajuya har takai bakin kofa saikuma tajuyo ta ɗaga murya yaya Aryan sai da safe tana gama faɗin hakan tayi waje, ko data’dawo ɗakin’su su Zahra har sun buɗe jaka’r nasu tsarabar dogayen riguna’ne masu kyau da perfumes masu kanshi da tsada sai murna suke, zama tayi a bakin gado itama tafara kokarin buɗe nata jakar amma sai’taga nata jaka’r an sawa zip ɗin kwa’ɗo, tayi tayi yaki,ɓuɗuwa sai ta ɗauki jakar tanufi sip dashi tana faɗin sai da safe na kaiwa yaya Aryan ya buɗemin,ajiye jakar tayi,tachire kayan jikinta ta ɗaura towel tashi toilet tayi wank atazo gurguje tasa kayan barchi tanufi kichin ta haɗa coffee tasha tadawo ɗaki ta haye gadon’ta nan take barchi awon gaba da ita

    Yau tun asuba ake shirye shiryen walima da naɗin sarauta ” Ammi tasha kwalliya da wata ɗankarekiyar,shadda tasha aikin har kasa Blue colour tasa wasu shaggun sarkan da abun hannu na gold mai shegen tsada ta ɗaukoh wani ɗankareriyar al’khaiba baki anmasa kwalliya da wasu suwasu mai kyalli fari tasaka a jikinta kai kace yar shekara 20 sosai kyanta yasake bayyana,”wayar’ta ta ɗauka tafa kiran layin Zahra, kira ɗaya Zahra ta ɗaga tare da faɗin hello Ammi” Ammi tace kuzo gaba ɗayan’ku kusameni a ɗaki tana gama faɗin hakan ta katse kiran, ta zauna a kan gado tare da ajiye wayar’ta a kusa da ita

    Da sallama su Zahra suka shigo sunsha kwalliya sosai riga da sket na atamfa Zahra hiyana diyana sukasa,”amrat da lamrat kuma duguwar riga, karisa shiga chiki ɗakin sukayi ” Ammi tace aa harkun shirya ne” har suna haɗe baki wajen chewa eh “ae ba wan nan kayan zaku saba Zahra’u tashi ki buɗe drawer kayana ki ɗaukoh muku kwalin kayan da zakusa, sai ku koma ɗaki ku chanza ” da sauri Zahra tamiƙe ta ɗaukoh musu sarine irin na indiyawa, kwali biyar kowa da kalan nasa ” Zahra baki,hiyana pink, diyana blue,lamrat jaa,amrat maroon” da zumuɗi diyana ta ansa nara tana faɗin Aunty zahra irin kayan danake ganin indiyawa suna sawa a TV nan ne ” Zahra tace eh shine” to ae Aunty Zahra ban iya sawaba tayi maganar kamar zatayi kuka ” dariya Zahra tayi tace to muje na koya miki” da fara’a diyana tamiƙe har suna haɗe baki wajen chewa Ammi mungoɗe

    Dakin su suka koma Zahra tafara nuna musu yadda ake sawa wow kayan yamusu kyau sosai da sosai hiyana da amrat nasu najaa a kasa sosai dan yafi tsawon’su
    yau make up sosai sukayi dukkan’su baƙaramin kyau sukayiba, hiyana kamar ita tayi kanta yau asalin kyanta ya bayyana datayi make up, Zahra sai santin kyan hiyana take har ita kanta diyana sai da tayaba kyan da hiyana,tayi” Zahra tace kai kuzo mutafi fada dan nasan yanzu gaba ɗaya an haɗu awajen kar ayi bamu kuyi sauri tayi maganar tana kokarin fita ɗakin ” da sauri suka bi bayan’ta

    Yau fada chike yake tab da jama’a baki dayawa sunzo dan naɗa sabon sarki da za’ayi Abba yasha kwalliya irin na sarakuna sosai yayi kyau yana zaune a kan kujerar sarauta Ummi Ammi Aunty amarya suna gefensa ga wasu kugeru a gefe dama da a ka jera wanda su Khalid, Aiman, Ahmad, Yusuf, Fahad, Haidar umar Aunty farida Aunty salma Aunty, mardiya, Aunty, Maryam, ne zaune awajen, “kujerun gefen hagu kuma manya manyan saraku daga sassa daban daban na Nigeria da ma makwabtar kasashe irinsu niger,Cameron, Ghana,chadi, da dai sauran’su , ga manya manyan yan siyasa a gefe guda ” DON da Aryan ne kawai basa wajen, fada yayi tsit kamar babu mutane a chiki kowa yayi shiru suna jiran juran jawabin Abba

    Da sallama ɗauke a bakinsu suka shigo fadan, gaba ɗaya jamar waje suka ɗago suna kallan’su kamar wasu taurari sai wal’wali da kyalli suke ” gaban Abba sukaje suka duka hiyana’ce tafara ɗagawa Abba gaisuwa “yusuf sai kallon lamrat yake yakasa ɗauke idonsa haka shima Khalid sai kallan Zahra’n sa yake ” da fara’a Abba ya amsa gaisuwar tasu ya ɗora dacewa kutashi kuje kuzauna kusa dasu farida, to sukache tare da miƙewa suka nufi wajen’su Aunty farida ” diyana kije ki kiramin Aryan ke kuma hiyana kije ki kiramin Safras Abba yafaɗa yana ɗaure fuska dan Aryan da DON sun ɓata masa rai tun dazun ake juran’su amma shiru” da sauri diyana ta juya ta fita, itakuma hiyana tafiya take kamar wadda kwai yafashewa,a chiki kamar zatayi kuka tafito daga fada ta nufi chikin gd

    A hankali ta tura kofar ɓangaren nasa tashiga, sallama tayi a palon, kasa babu kowa kamar zatayi kuka ta shigo chikin palon babu kowa, a nitse ta haura stair ɗin tsayuwa tayi a bakin kofar betroom ɗin tanata doka sallama amma shiru shiru almost 20 mnt bataji wani motsi’ba, a hankali ta hannu ta tura kofar tashiga, tana shiga taji kofar yayi kara alamar ya rufe kanshi juyawa tayi tana bin ɗakin da kallo wani katafaren gadone mai girma da kyau yana shinfiɗe da betshit na alfarma Sky Blue ga wani haɗaddɗen sofa guda ɗaya a gefe sai wasu tagwayen kofofi da alama ɗaya kofar toilet ne ɗayan kuma kofar shan iskane,

    shiru ta tsaya tana tunanin,kuɗin da aka kashe a ɗakin nan jin karar buɗe kofa yasa tayi saurin kai kallanta wajen zubawa kofar ido tayi dan taga wanene zai fito ” DON ne yafito ɗaure da towel a kugun’sa ga jikinsa da ruwa da alama wanka yayi ” wani kara hiyana tayi wadda yasashi juyowa a sukwane dan baiyi zatan da mutun a ɗakin’ba ” juyowar dayayi bakaramin rikitata yayi ba a guje ta juya taruɗe tama rasa ina zata nufa kawai sai tanufi kofar bangaren hagu tunda taga kofar a buɗe yake tana fita tayi rashin sa’a ta taka sarin’ta dake jaaa a kasa ta kai kai ta tafi kasan bene kallamar shahada kawai take dan tasan mutuwa zatayi..✍️✍️

    Tanbaya a nan shin hiyana zata faɗi kasan benen nan kuwa? Shin intafaɗa zata rayu kuwa? ko’ko kar ku manta bene hawa ɗaya tafaɗo daga sama kudai sai mun haɗu

     

    More comments pls 🙏🙏

    *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*

    *

     

  • Amatulmaleek 4

    Amatulmaleek 4

    Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

    AMATULMALEEK

    Mamuhgee

    #ZafafaBiyar

    4

    Duk fada da masifar daya daga cikin  ma’aikatan tashar yayi mata akan zuwan nata duk da baisan dalili ba bare Kuma alaqarta da Gidan ASH TALBA din datazo gurinsu Amma dai yasan Hakan datai na zuwan Kai tsaye nada hadari.

    Kallanta yayi Kai tsaye yace ta Fadi sunanta ya rubuta Sako ya tura mata ga numbern,

    Jiki a mace cikin sanyi ta fada masa tareda Dana ‘yayanta wainda yayiwa Wani kallan qyama da takaicin yanda ta kwasosu kaman wasu almajirai sunzo garinda basusan koinaba ko tsoro bataji.

    Kai tsaye sunanta Dana yayan nata ya rubuta a cikin sakon da cewan a taimaka a dauki wayar gasunan Tasha a zube harda mara lafiya.

    Tafiyar sakon ya sakashi kallanta yace ta zauna ta jira idan ankira to shikenan idan Kuma baa kiraba motar asubar safe su koma inda suka fito.

    Gyada masa Kai tayi cikin sanyi da nutsuwa tareda Bude Baki ahankali tayi masa godiya ta juya ta koma inda su Amatun ta zauna tana kallansu har zuciyarta bataji komai ba na haushi ko jin zafin rashin daukan wayar harma da fadan da ma’aikacin tashar yayi mata Dan kuwa Babu lefi a cikinsu saima uzuri datakewa kowa Wanda shine abin dayafi bawa mutane Daman cutatar da ita ko acan kauye sbd komai kayi mata a rayuwa tanai Maka uzuri Bata fushi Komai girman cutar da zakai mata.

    Zaune suke cikin duhu da rashin mafita hakanan ta miqe tayi alwala a gurin tayi sallah har lokacin AmatulMaleek a kwance take jikinta yafara tsanani sosai Abdulhameed ma tini Shima yafara kamuwa da zazzabin sbd wahalar yunwa.

    Har Akai ishai Babu Wani bayanin biyo sakon da suka tura da kira Dan haka ta Yanke komawarta da bin motar asuba Kila Wani uzurin ya Hana Abeeda ganin sakon Dan haka bazasu cigaba da damunta da Kiran ba akwai takurawa ga Hakan ta sani.

    Ruwa kawai ta ringa bawa Abdulhameed da AmatulMaleek har kusan asuba anan suka kwana cikin sanyi a sararin iska ga sauri da duhu harma da qwari kala kala Dan haka asuba nayi sallah kawai tayi suka miqe Dan shiga layin bin motar komawa.

    Koda gari ya fara haske AmatulMaleek kaman bazata tashi ba hakama Abdulhameed Dan haka sai hankalinta ya rabu biyu ga tafiyar sbd bazasu iya bin doguwar hanya a Hakan Amma Kuma Babu zabi na yanda zatayi Dan haka tayi shiru a cikin sanyin jiki Dana zuciya idanuwanta sunyi jajir da damuwar Dake riqe da zuciyarta.

    Isowar ma’aikacin tashar na jiya ne gurinta Yana qwala kiranta ya Sakata dagowa ahankali cikin sanyi ta Dan kallesa tareda sauke Kai tana gaidasa da girmamawa.

    Da farin cikin dayake tareda takaici ya kalleta Yana cewa tayi Maza tazo ana son magana da ita anbiyo sakon da kira yanzu.

    Numfashi ta sauke me dumi kafin ta fito layin a sanyaye ta biyosa zuwa inda ba hayaniya ya miqa mata wayar wadda daidai lokacin aka sake kira.

    Cikin nutsuwa ta Bude Baki tayi sallama nauyin zuciyarta na raguwa Jin amsa sallamar Abeeda cikin Wani irin nutsuwa ta wainda suke cikin duk wata ni’imar rayuwar duniya.

    Jin muryar Asmau ya Saka Madame abeeda sauke ajiyar zuciya a hankali tareda sake Bude Baki tace

    “Asmau kece??

    “Meyesa Baki kirani da wayarki ba?

    Yaushe kikazo?

    Sai yanzu nake duba sakon sbd Banda time na duba wayar rasuwar da Akai ya Saka Sam bana samun Hutu yanda ya kamata.

    Shiru sukai dukkaninsu sbd kowannensu da Wani girmamman quncin dayake mamaye cikin ransa Amma baisan tayaya zai tinkari Dan uwansa ba sbd Nisan daya shiga cikin kusancinsu da tsananin kaunarsu

    Numfashi mara sauti maamah ta sake saukewa ahankali kafin ta Dan saki murmushi me sanyi tace

    “Eh nice,jiya nazo sbd labarin rasuwar ta alhaji babba danaji daga bakin Dan gidan kawu bello dayake Dan shiga birni shine yazo ya sanar mun,

    Allah yaji qansa yayi masa Rahama,

    Munata damunki da kira ga fama da jamaa Anata zuwa gaisuwa.”

    Numfashi Madame abeeda ta sauke kafin tace

    “Ba komai yanzu ku Jira ga driver Nan zan Aiko yazo ya dauko ku keda yaran ai gwara da bakiyi saurin juyawaba Ina buqatan ki Asmau,

    Ina tsananin buqatan nawa a kusa Dani”

    Shiru suka sake yi jikin Maamah na sanyi ita Kuma acan nata bangaren wasu zafafan hawayen da babu Wanda ya taba ganinta dasu ne suka taru a cikin idanuwanta Amma Bata bari sun taba saukowa kan fuskartaba bare yau din Dan haka ta sake hadiyesu cikin dauriya da karfin zuciya kafin ta kashe wayar ta ajiye gefenta sbd Asmau kamar rauninta ce sbd Bata iya boye mata komai duk dauriya da jarumtarta.

    Ita kanta Asmau sanyi jarumtarta ke Neman yi Dan haka ta daure batareda ta dago ba tasake yi masa godiya tana koma gurin yaranta da suka koma kamar mahaukatan almajirai.

    Zaunawa tayi tareda zuba musu idanuwanta da suke boye duk Wani abinda yake cin Rai da zuciyarta tana musu fatan hayewa matakin nasara a duk inda suke rayuwarsu.

    Zaman jigum tayi tana sauke kanta qasa da jiran tsammanin Kuma Ina rayuwa da kaddara zatai dasu itada yayanta a gaba.

    Zaman jiran awa kusan Daya da Rabi tayi zuwa biyu kafin Daya daga cikin Mahaukatan motocin gidan ASH TALBA ta iso tashar daukanta.

    Da farko numbern da aka bawa drivern yazo daukanta ya kira shine ma’aikacin tashar ya kawosa har inda Maamah take zaune kaman almajira ita da yaranta yace “gatanan”

    Kallanta drivern yayi dakyau kafin ya dawo da kallansa kan mutumin Dake nuna masa ita Yana wasi wasin idan wannan din ce akace ya dauka yakai gidan ASH TALBA sbd ko masu aikin gidan bazasu dauki wannan aikin gidajensu ba bare gidan ASH din da kansa.

    Lura da fahimtar tinanin dayake gudana a zuciyar drivern yasaka Dan tashar sake basa tabbacin ita din dai ce,daga kauye ta fito shiyasa.

    Kasa cewa komai driver yayi sai kawai ya dauki jakar kayanta ya Bude bayan black range Rover Din dayaxo da ita yana sake kallansu maamah din cikin danne mamakinsa da Dan shakkar idan ba kuskuren daukansu zaiyiba.

    Maamah dasu AmatulMaleek ma da basusan inda kansu yake ba rakubewa sukai tareda dunqulewa guri Daya bayan motar Babu me iya motsawa sukai shiru Maamah din najin zuciyarta na Dan sake sanyi da taimakon gaggawar dasu AmatulMaleek din zasu samu Dan kuwa data koma dasu a wannan halin ba lallai ta samu Isa gida da duka yayanta biyu ba Kila ta rasa ran Daya a hanya kafin su Isa,sai gashi Allah ya dubi maraicinsu ya kawo sassauci a lamarinsu ta samun Kiran Abeeda.

    Tafiya me Dan tsayi sukai kafin suka Isa,

    Koda suka Isa tini sanyin ac yakusan sankarar dasu Abdulhameed Duk da sun Saba da sanyin Allah Amma wannan din yayi musu karfi da yawa sosai.

    Babban makeken luxury gate din gidan ASH TALBA aka wangalewa motar gidan dasuke cikinta suka shige harabar gidan datake da Wani irin girma da tsari irin na gidajen turai da Kuma masu abin duniyar qasa da qasa,

    Motacin Dake harabar sunkai takwas koma fiye,

    Motoci ne wainda babu me karamin kudin da zaka iya lissafawa bare manyan,

    Dukkaninsu baqaqe ne sai farare guda biyu aciki sai Ash Daya.

    Parking yayi daga gefen da ake ajiye duka motacin gidan Dana mutan gidan Banda na ASH dake gefensu daban sbd ta inda yake fitowa daga sashensa da Babu Wanda yake bin kofar idan ba shi ba Dan haka ta Nan yake fitowa ya shige motacinsa yabar gidan batareda ma kana gidanba bare kasan fitarsa.

    Tinda Sharif driver yayi parking ya fito yake Dan Jin zuciyarsa na sake shiga shakku idan baiyi kuskuren dauko Wanda Basu aka aikesa daukowaba.

    Bude musu motar yayi Yana kallansu yace maamah tafara fitowa tukuna idan ya tabbatarda sune aka sakasa daukowa saisu shiga.

    Wayarsa ya fitar cikin nutsuwa ya Nemo numbern Madame din ya Saka kira.

    Saida yayi mata kira biyu kafin ta daga Kai tsaye ya sake gaisheta Yana cewa

    “Hajiya ga baqin na dauko Amma bansaniba ko na samu kuskuren daukowa wainda Basu ba….

    Katsesa Abeeda tayi da cewa

    “Bata wayar naji”

    Da sauri ya miqawa Maamah wayar Yana cewa “yi magana taji”

    Karban wayar maamah tayi tana sallama Abeeda ta kashe wayar tareda miqewa daga zaunen datake ciki lafiyayyan bedroom dinta sanyeda jallabiya ash da mayafi me Dan girma na sallanta ta ajiye wayarta tana nufar kofar barin bedroom din sanyeda slippers masu tsananin laushi da tsadan kudinsu zasu ciyar da maamah din da yayanta na sati uku koma fiye.

    Tinda ta tinkaro babban palonta ta nufo kofa ma’aikatan Dake gyaran palon suka ringa gaisheta cikin tsananin girmamawa sun Dan sauke Kai sbd Koma me zai fitarda Madame din harabar gidan a daidai wannan time din me tsananin mahimmanci ne.

    Sharif dayaji madame ta kashe wayarta Babu amsar komai Shan jinin jikinsa yayi sbd ta tabbata kenan yayi kuskuren dauko wainnan kauyawan dajin.

    Kallan maamah yayi cikin sauri Yana cewa

    “Kinga maza shiga na mayar daku inda na daukoku kafin na Rasa aikina”

    Juyawa mota maamah tayi tana kokarin komawa batareda tace masa komaiba Dan itama batasan dalilin kashe wayar Abeedan ba.

    Cikin fada da daga murya yaci gaba da yi mata sauri sauri Yana cewa

    “Wai bazakiyi sauri ba muje?

    Kema kinyi gangancin biyoni bayan kinsan Babu ta inda kukeda arzikin Azo daukanku da mota irin wannan Amma haka kawai kika biyoni gashi Kuma Kinga irin gidan da akazo bazaki Bude Baki kice bakuda Hadi da irin wanna guraren”

    Shiga motar Maamah ke kokarin saiga fitowar Abeeda harabar gidan tini ta dagakata daga shiga motar tana tsayuwa a inda take gabobin jikinta na Neman saki idanuwanta dasukai Dan ja suna tsayuwa a kan Abeeda wadda itama nata idanuwan akan Maamah din suke tana kallan Wani irin mugun mummunan yanayin da Asmaunta ke ciki kamar wadda Tayo gudun hijira.

    Suturar jikinta ta kalla taji hankalinta na mummunan tashi kafin ta tsayar da idanuwanta akan fuskar Asmaun da sauran kadan takoma skeleton sbd rama da bushewa.

    Maamah kasa kurar da nata kallan tayi kan Asmau sbd alkunya da muzantar dataji tanayi agaban Abeedan sbd yanayin datazo gidan dashi kamar almajirar data debo tafiyar qafa.

    Qasa tayi da kanta lokacinda Abeeda ta tinkarota Kai tsaye jiki a tsananin mace da baqin cikin ganinta ahakan tana isowa hannunta take kokarin kamowa tana ambatar sunanta muryarta na rawa sosai.

    Kasa bari maamah tayi Abeeda din ta a kamata sbd jikinta Babu inda yake da tsafta ita kuwa tamkar wata tauraruwar datafi taurari take komai nata na musamman ne sbd Jin dadi,Hutu da daular da Allah yayisu acikinta.

    Sharif na ganin Hakan yasan ba kuskuren ne dai aka samu ba Dan haka a Jere ya Sako ajiyar zuciya Yana Bude mota da sauri yahau kokarin kamo Abdulhameed sbd AmatulMaleek bazata dauku garesa ba tinda ta fara zama yar budurwa.

    Yanda Sharif ya dauko Abdulhameed kamar matacce ya Saka gaban Abeeda mummunan faduwa tana kallan Motar cikin tashin hankali tace

    “Meya samesa?

    Ina AmatulMaleek?

    Meya samesu?”

    Jiki na rawa murya na sauri sharif yace

    “Ahaka aka daukosu daga Tasha inaga basuda lafiya sosai sunyi Nisa musamman ita macen ko numfashi ma batayi…””

    Bai qarasaba Abeeda ta katsesa da cewa

    “What??

    Kallan maamah tayi tana Isa motar jikinta na rawa takai hannunta kan AmatulMaleek Dake kwance ba Rai ta janyota kafin tayi Wani yunkuri tini sharif ya kira masu aikin gidan mata su biyu suka iso gurin Dan daukan AmatulMaleek Dan baiyi tinanin Madame din tasu zata iya taba mutanenba.

    AMATULMALEEK

    Regular 700

    Vip 2k

    0022419171 access bank Maryam sani

    09033181070

    ##MAMUH#

    #LOVE

    #ROMANCE

    #INSIDELIFE

    #ASH TALBA

    #NAUFAL

    #MADAME

    #ABOKIYAR NISHADI

    #MEERAH HERBS

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 19

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 19

    Episode 19*

     

    Lafayar da Aunty farida ta kawo musu ta ɗauko, Aunty farida da kanta ta ɗaura mata baƙaramin kyau tayiba ga kitso guda biyu a gaban goshita, kamar wata amarya ga lallenta ja da baki ” wow my diyana kin haɗu iya haɗuwa yanzu muje wajen flowers ɗin garɗing muyi hotan koh zaifi kyau ” to Aunty farida amma sai na ɗaukoh takalmi a ɗakin Ammi ” ina takallamar dana kawo muku ” aa shikam sai gobe zansa yanzu high heel nakeso ” murmushi Aunty farida tayi tare da jan hannunta tana faɗin to muje ” fitowa palon sukayi nan suka isko su Zahra suma sun sha kwalliya sosai sai dai su dukkansu hijabi suka’sa dan zuwa sallar idi ” Aunty farida ina zakuje Zahra ta tambaya ” hoto zamuje muyi a garding, ko zakuyine kuma ” aa nikam banso chewar Zahra ” to kufa tayi maganar tana nuna su lamrat “har suna haɗa baki wajen chewa aa bamusu ” da kyar hiyana tamike dan sarawar da kanta ke mata tana faɗin Aunty farida muje kimana tare ni kam ina so ” riko hannunta Aunty farida tayi dan yadda taga yanayinta kamar zata faɗi da kyarma take tafiya” a harabar gidan suka tsaya san nan Aunty farida tace my diyana kije ki ɗauko ta kalmar naki kinji, kiyi saurifa dan kinga hiyana bazata iya tsayuwa sosaiba ” da sauri diyana ta juya tanufi bangaren Ammi ” Shahram na ganin’su yazo wajen da sauri ya gaida Aunty farida san nan ya tambayeta ko fita zasuyi’ne ya kaisu ” aa tace masa ” juyawa yayi yakoma bakin gate ” suna tsaye har diyana ta dawo kwas, kwas, kwas, take tafiya, a nitse take zuba takunta da yanga ” daga nesa Aunty farida tafara ɗaukarta video sai faɗin wow take, sai da ta iso kusa dasu tukun nan Aunty farida ta tsai da video, suka nufi chikin garding ɗin ” hotona sosai, tamusu a tare san nan tawa diyana ita kaɗai kala kala, bayan sun gamane suka nufi chikin gd Aunty farida na faɗin to my diyana sai kije ki ɗaukoh hijabinki muje masallachi koh ” to diyana tace tare da wucewa ɓangaren Ammi ” Aunty farida da hiyana kuma suka nufi ɓangaren Ummi

    SAUDIA

    Tsaye yake a gaban mirrow ɗaure da towel a kugunsa da alama wanka yafito, yana shafa mayukan’sa masu kanshi da tsada’ bayan ya gamane ya gyara gashin kansa ya sake feshe jikinsa da turare mai kanshi da tsada, trolley’sa ya jawo ya buɗe ya ɗaukoh farar jallabiya, ya juya a jikinsa yayi kyau kamar balarabe,tsayuwa yayi a gaban mirrow yana kallan kansa, wayarsa dake kan gado tayi kara alamar kira yashigo, a hankali yake takawa kamar yana tsoran taka kasar ya isa gaban gadan,hannu yasa ya ɗauki wayar my blood ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar, da sauri yayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen’sa ” hello ” daga ɗayan ɓangaren DON yace jirginmu zai sauka 9:30 dai dai “ok by the i will be they ” thanks ya faɗa tare da katse kiran’ Aryan zai ajiye wayar ke nan yaji tasake kara alamar shigowar sako, ganin my lovely Aunty yasa ya buɗe sakon,
    da sauri ya zauna a bakin gado tare ta kara waro ash eyes nashi a kan’wayar,Sosai yake kallan wayar kamar zai chinye, wow dole Aunty farida ki ruɗe irin wan nan kyau haka,yarinya kamar wata aljana, yayi maganar yana manna wayar a kirjinsa, jinake kamar jibi yamin nisa jinake tamkar ranakun tsawo suke karawa, kusan 10 mnt yana zaune yana surutai, san nan a hankali ya miƙe yanufi hanyar fita,wayar na manne a kirjin’sa

    Kai tsaye ɗakin khalid ya nufa nan yasami Yusuf ma a chan dukkan’su sun shirya chikin fararen jallabiya bakaramin kyau sukayiba ” muje koh lokachin sallama yakusa ae chewar Aryan” Khalid yace wai Aryan ina DON ne tun shekaran jiya nake tambayar’ka kakemin wani kauce kauce koh ” nafaɗama’ka Khalid yana nan kawai yaje chikin madina ne ” lallai Aryan to karyan ma bai dace da kaiba, baka sabayi’ba shiyasa ma dakayi yanzu, karyan bata zauna ba ” dogon tsaki Aryan yaja tare da faɗin inkun gama kusameni a masallachi nayi gaba tun da naga baku da niyar tafi, yana gama faɗin hakan yayi waje ” kallan Yusuf dake zaune ya zuba musu ido Khalid yayi”muje koh ” hmmmm kasan’me Khalid wlh DON baya kasar nan wani lokachi sai Aryan yarinƙa magana kamar ba tare muka tasoba ina da tabbachin DON yana London zai wani chemana yana madina shi ko karyan ma bai iyaba ” kaga Yusuf kafita maganar Aryan da DON kazo mutafi masallachi kar murasa sallah, yakai karshen maganar yana nufar hanyar fita ” mikewa Yusuf yayi yabi bayan’sa ” suna fita waje suka samu gaba ɗaya family sun haɗu amma banda Aryan ” Khalid ina Aryan da Prince Ummi ta tambaya tana kallan fuskarsa ” sunyi gaba Ummi ” to muma ae sai muje koh dan kar lokachi yakure ” tare suka jera dayake masallachi kusane da masaukin’su ” suna isa suka rabu su Ammi sukayi ɓangaren mata su Abba kuma sukayi ɓangaren maza

    Nigeria

    Zaune suke a palon Ummi diyana yau baƙi ya buɗu ta tasa fruits a gaba sai chi take ” hiyana na rike da littafin addu’oe tana karatu ” lamrat na game a waya Zahra ” amrat na kallo a wayar Aunty farida ” Zahra kuwa ta kwanta ta tada kai da chinyar Aunty farida sai hira suke kamar saannin juna ” da sallama Aunty Maryam ta shigo palon ” Aunty farida ta amsa mata fuska ba yabo ba fallasa ” zama tayi a saman sofa mai zaman mutun 1 tare da faɗin, ina wuni Aunty farida anyi sallah lfy ” lfu lau ykk “lfy Alhadulillah ta faɗi hakan tana mikewa ” inakuma zakije kitsaya muci abinchin rana tare mana tun da lokachin yayi chewar Aunty farida ” aa bana buƙata a inda,na fitoma akoi abinchi dama dai kawai nabi dokar gd nanne nazo na gaisheki kuma namiki barka da sallah a matsayinki ta babba, SO no need na tsaya yin wani abun, tana gama faɗin hakan tayi waje ” Allah ya shiryaki Maryam Allah yasa ki gane.. bata garisa maganar’ba sukaji diran manya manya motochi a gd ” da fara’a Aunty farida ke faɗin oyoyo Aunty salma oyoyo Aunty mardiya” tun Aunty farida bata karisa magarba Zahra tamike a guje tayi waje, mikewa Aunty farida ma tayi tabi bayan Zahra suka bar su diyana a ɗakin ” hiyana ta dubisu diyana” kukam bazakuje kumusu oyoyo bane ” ni kam bazanjeba dan bansan’suba kilama halinsu irin na Aunty Maryam ne chewar diyana” lamrat da amrat ma sukache muma bazanjeba ” baki hiyana ta taɓe tana kallansu zata yi magana sai gasu Aunty farida sun shigo” Aunty farida rike da hannun Aunty Salma “Aunty mardiya rike da hannun Zahra da wani baby boy mai kyau dashi mai kama da yaya khalid,saman sofa suka zauna ” da sauri hiyana tafara ɗaga musu gaisuwa” wow Aunty farida wayan nan ƴa’ƴan larabawan fa kodai sune ƴaƴa Abba da ya faɗamin yasamu wasu ƴaƴa daga Allah Chewar Aunty salma ” eh wlh salma sune ” kai gaskiya bari Abba yadawo ya taimaka yabani wanchan da wan nan tayi maganar tana nuna hiyana da diyana ” tab ae kuwa wayan nan yaran nan gani nan bari, inji Abba dan tun farkon zuwar’su nida mardiya mun roka ya hanamu ” aa ae ni nace masa zanyi wlh har sai yabani ” to Allah yaba da sa’a chewar Aunty farida ” ameen Aunty salma ta amsa tare ta chewa ya su nanku ɗaya bayan ɗaya suka faɗa mata su nansu sai wow nice name kawai take faɗi ” kutashi kuje kuyi wanka kuzo muchi abinchi ” a tare Aunty mardiya da Aunty salma suka mike suka nufi dakinsu ” inakuma zakuje Aunty farida ta jefo musu tambaya ” ɗakinmu mana ” wani ɗakin ae sai dai kuje ɓangaren Ammi dan kuwa ɗakinku yazama ɗakin Yan mata’na har sai randa Ammi ta dawo zasu barmuku ɗakin sukoma nasu ” to ae danan da chan duk ɗayane badamuwa chewar Aunty mardiya tayi maganar tare da juyawa tanufi hanyar fita, bin bayanta Aunty salma ma tayi ” Auta ki kiramin masu aiki suzo ku shirya mana abinchi ina zuwa mikewa tayi tanufi ɗakinta ” Zahra kuma tasa hannu ta anshi wayar ta a hannun lamrat, tafara kiran layin binta, bugu binya ta ɗaya Zahra tabata umarni tazo ta shirya abinchi tana gama faɗin hakan ta katse kuran tamikawa lamrat wayar

    SAUDIA

    abinchi sukechi chikin nitsuwa shiru palon babu mai magana ” Abba me zai hana mutafi gobene dole sai jibine, Chewar Aryan “a sukwane DON ya ɗago yana kallan’sa, shi ko ajikinsa saima latsa wayar’sa yake ” meyasa kakesan mutafi gobe Aryan kodai ƙasa mai tsarkinne bakaso chewar Abba ” aa Abba bawai bansan kasan bane wlh nagajine inasan inkoma gida ” Khalid ya ɗago ya sachi kallan Yusuf sai murmushi suke ” Aiman kuma ya kalli Khalid san nan yajuya ya kalli Yusuf yana girgiza kai a zuchiyar’sa yana faɗin muna fukai asirinku yakusa tonuwa ae idanma wani abu kuke shiryawa ɗan uwana to kanku zai dawo ” Ahmad kam abinchin’sa kawai yake chi hankalin’sa kwan’che ” haidar ya matso kusa da Umar yafara masa magana katsa katsa anya yaya Aryan lafiyar’sa kuwa “umar ya ɗago kai zaiyi magana karaf idon’sa ya sauka chikin na Fahad dake gurga musu mugun kallo ” to shike nan Aryan tun da haka kakeso kukira’su farida ku faɗamusu gobe zamu dawo chewar Abba yayi maganar tare da mikewa yanufi hanyar ɗakin’sa ” mikewa Ammi da Ummi sukayi sukabi bayan’sa “Aunty amarya kuma tamike tanufi nata ɗakin ” kallan Umar da haidar DON yayi yana faɗin me kukejira ae tun bai kai karshen maganar’ba suka mike suka nufi waje, dawo da green eyes nashi yayi kan Fahad, tun baiyi magana’ba Fahad yamiƙe shima yayi waje ” green eyes nashi ya jubawa Aryan sosai yake kallansa” Aryan nasane da kallan da DON ke masa amma yaki ɗago kai dan bai da amsar tambayar da DON ɗin zai masa ” bazan sake tambayar meke damunka ba dan nalura kaima bakasan meke damun nakaba binchike mai kyau zanyi kawai a kan hakan ” sai loakchin Aryan ya ɗago yana faɗin da ka taimakamin bro dan koba komai zaka daina tunanin chewa ina ɓoyemaka wani abu ” ajiyar zuchiya ya sauke san nan yamiƙe yana faɗin to sai kuje kushirya ae tunda komawa gobe yakamamu gashi yanzu kusan karfe 4, da ɗai ɗai suka miƙe suka bar palan

    Yola Nigeria

    Inna tachi wankan ta tasa wata atampha da bappan, bubu ɗinka mata mayafi ta ɗauka tayi waje, kai tsaye gidan’su buba tanufa, da sallama tashiga gaba ɗayan’su suna tsakar gd ” inna sannu da zuwa chewar buba” yauwa buba ya kafar taka ” naji sauki ae yanzukam ina ɗab iya takawa batare da sandaba ” to alhamdulillah Bappa ina wuni” bappa dattijon arjiki halinsa iri ɗaya da bello mutumin kirki yace lfy habiba anyi sallah lfy ” lfy lau bappa inna larai mushiga daga chiki koh” inawuni inna chewar bello ” yamutse fuska inna tayi kafin ta amsa da lfy, san nan tawuce ɗaki da sauri dan karma wani ya gaisheta, bello ma albarkachin bappa yana nanne shiyasa ta amsa gaisuwar” miƙewa innar buba tayi tabi bayan inna, innar bello dai dake zaune kan tabarma ta taɓe baki tai tana kallansu har suka shige ɗaki a zuchiyar’ta tana faɗin Allah ya kare mutun daga sharrinku dan kuwa wayan nan idan suka haɗu ko sheɗan suransu yake ”

    Lfy inna chewar innar buba” lfy ba lau’ba kinga anyi sallah yau yakamata gobe mukoma wajen malam koh dan asamu ayi aikin nan dawuri ” aa to mezai hana muje yanzu chewar innar buba ” to me zakice wa bappan buba idan zamu fita ” aa ae yanzu zai fita dakin ɗan tsaya kaɗan’ma bazaki samesa’ba yanzu dai mujira fitar’sa ” to shike nan bari naje gd na ɗaukoh kuɗin nadawo,bata jira amsar innar buba ba tayi waje ” da sauri sauri ta shiga gd ɗakinta tanufa tana shiga ta ɗaga yar katifar chiyawar’ta ta ɗauki kuɗin ta kirga sauran 5k ,ta juya tanufi waje, a dab da bakin kofa tayi karo da bappan buba zai fita, matsa masa tai tana faɗin Allah ya kiyaye hanya adawo lfy ” amsawa yayi fiska bayabo ba fallasa yayi waje da sauri ” ita kuma tayi chikin gd

    Tare suka fito da innar buba sai sauri suke zubawa suka nufi hanyar kungurmin dajin nan tafiya mai tsawo sukayi, kafin su kai wajen duwatsun chikin kogon suka shiga, zaune yake kan wata ƙatuwar dutse ga tukunyar hayaki a gaba sa ” da baya baya su inna suka karisa wajen dan dokar wajenne shiga da baya baya

    (ma’anar shiga da baya baya kuwa shine kajuyawa Allah baya kajuyawa alkibla baya kabar halak ka kama haram kabar Allah ke nan ka fiskanchi boka, ya Allah ka tsare mana imanin’mu ya Allah duk halin da zamu shiga ka tausaya mana kabarmu da imanin’mu)

    Kan wani jar shinfiɗa suka zauna, wani mahaukachin dariya bokan nasu yayi ha, ha, ha, san nan yace kuɗin da kika rike ko warware tsarin jikin’su bazai yiba bare har aje gamaga nagaba ” to don Allah alagafarta malam..” ke dakata banace baa kiran su nan Allah a nan’ba ko ance maki aikin Allah muke a nan, sheɗan kawai zaki kira mana dan kuwa aikin’sa muke ” kayi hakuri to kataima’kamin ina chikin damuwane idan yaran nan na raye ” zan iya taimakawa na kunce tsarin dake jikinsu ke kuma sai kinemo kuɗin aikin daza’a amusu amma da sharaɗi ” menene sharaɗin komanene zanyi” to farko dai ajiye kuɗin dakikazo dashi, na biyu kuma zaki bani kanki ” to inna tace tare da ajiye kuɗin chikin wata kwarya, idon ta yarufe bataji bata gani” boka kuwa ganin inna ta aminche yasa ya umarchi innar buba da taje waje, ba musu ta tashi ta fice ” nanfa boka yafara biyar bukatar’sa da inna sai dai abun da bata saniba shine ta baya bokan zai nemeta, ba karamin wahala ta shaba tayi ihun azaba shiko ko ajikinsa bukatar’sa kawai yake biya bayan sun gamane, ya umarce’ta da taje gd bayan kwana uku ta dawo ” da kyar inna tamike tana hawaye, tanufi waje nan tasamu innar buba zaune a kan wani dutse ” innar buba na ganinta ta mike da sauri tanufeta, tana faɗin sannu, jerawa sukayi suka nufi gida dan yamma tayi sosai ” yanzu shike nan zai mana aikin chewar innar buba” aa wan nan abun damukayi iya warware tsarin jikinsu kawai zaiyi nikuma sai nasamo kuɗin aiki ” to yanzu ae na zaki samo kuɗin ” nima wlh ban saniba amma koma sata zanyi wlh sai na nemo kuɗin ” to shike nan amma nawa yace maki kuɗin aikin ” 15k yace ” tab lallai to Allah dai ya dafa’mana

    (nikoh nace aikin Allah kukene dazakuce Allah ya dafa muku)
    inna sai ɗingisa kafa take har suka isa, inna tayi gidanta innar buba ma tayi gida

    KANO

    Misalin karfe 8 na dare zaune suke a kan table ɗin chin abinchi, Aunty farida ta ɗago tana kallansu tafara magana ” Abba yakirani ɗazun yasanar dani gobe damisalin karfe 5 na yamma jinginsu zai sauka a airport” chike da murna Aunty mardiya ke faɗin alhadulillah alhadulillah ” ae chanake sai jibi zasu dawo Koh chewar Aunty salma” eh daman dawowar’su jibi ne bansan meyasa Abba yace sudawo gobeba Aunty farida tabata amsa tana kokarin goge bakinta ” to kunga yakamata muje mu kwanta dawuri dan mutashi dawuri saboda aiki shirye shiryen chewar Aunty Salma ” eh hakane yanzu mardiya keda salma kutafi bangaren Ammi nikuma zamuwuce nida sister’s ɗinna kamar yadda muka saba, kutashi muje my diyana ” ba musu suka mike gaba ɗayan’su sunai’wa juna sai dasafe

    Washe gari tun da sukayi sallar asuba basu mai da barchiba “Aunty farida ta shirya ta tsab chikin a tanfa mai tsadar gaske blue colour wuyarta da hannunta shaƙe yake da manya manya gwala gwala mai kyau da tsada tayi simple make up, plat shoe baki tasa da mayafi baki wayar’ta da ATM kawai ta ɗauka tayo waje, a palo tasamu su diyana” diyana sarkin kwalliya kullun tana chikin kwalliya tana saye da doguwar riga ash colour tayi rolling gyalen rigar a kanta, tayi kyau sosai ” Aunty farida ina zakije diyana ta tambaya” shopping zanje kozaki rakanine ” eh zanje” to duk wadda zataje tazo muje ” diyana da lamrat ne suka mike, suka nufi Aunty farida” Aunty farida na ganin hakan ta juya tayi waje, suka bi bayanta yau ma dai kamar kullun Shahram ne ya jasu da matsakai’chin gudu yafita gidan

    Sai karfe 4:30 su Aunty farida suka dawo, su Aunty mardiya gaba ɗayan’su sunyi kwalliya sunyi shirin tarban’su Abba ” a gurguje Aunty farida ta tanufi ɗaki dan yin waka itama tana faɗin my diyana kuyi sauri ku shirya kuma, tana gama faɗin haka tayi ɗakinta “ɗakin Aunty mardiya diyana da lamrat suka nufa a gurguje sukayi waka dan kar a tafi tarban’su Abba a barsu, diyana dai duk saurin datake sai da ta tsaya tayi make up” gida yachika da jama’a sosai karfe 5:10 dankara dankaran motochi masu numfashine suka jero guda 20 “guda 5 suka fito daga gidan Abba suka tadda 15 afarfajiyar babban get jerawa sukayi suna sharara gudu dan sunyi latti da 10 mnt, gudu suke shararawa sosai chikin ƙanƙanin lokachi suka isa airport, lokachin har jirginsu Abba ya sauƙa sai dai basu fara fitowaba,

    Fitowa daga motachin, su Aunty farida sukayi suka jingina da jikin motar suna jiran fitowar su Abba gaba ɗayan’su, sun kurawa jirgin ido
    Abba ne yafa saukoh wa a nitse yake takawa Aunty amarya na biye dashi sai Ummi da Ammi a baya ” da gudu Aunty mardiya tayi wajen Abba ta rungumesa ita kuma Aunty salma wajen Ummi tanufa, Aunty Maryam kuwa wajen Aunty amarya tanufa, su diyana kam wajen Ammi suka nufa suka rungumeta itama rungumesu tayi tana hawaye ” Aunty farida kam tana tsaye jikin mota ko motsawa batayi’ba
    Rike yake trolley a hannunsa yana taku irin na jaruman maza ya saukoh daga jirgin sanye yake da jeans da t-shirt bakake yasa p-cap baki, fiskar nan kafar an aiko masa da mutuwa,Aryan na biye dashi a baya shigarsu ma iri ɗayane basubi ta kan kowaba sukanufi wajen da motochin ke tsaye,” da sauri security dake tsaye a awajen ya buɗe masu kofar ɗaya daga chikin motochin san nan ya anshi trolley hannunsu, ” Aunty farida naganinsu tayi gunsu da sauri ” DON zai shiga motar ganin Aunty farida na zuwa sai ya ɗan dakata ya juyo tare da buɗe mata hannu, da sauri tafaɗa jikinsa, tana faɗin Wellcome my blood ” rungumeta yayi yana faɗin mun sameki lfy”sakin’sa tayi ta juya ta rungume Aryan dake tsaye tana faɗin, lfy ya hanya ” nayi kewarki lovely Aunty chewar Aryan ” nima nayi kewarku sosai wlh ta karisa maganar tana sakin Aryan,
    Chikin motar suka shiga gaba ɗayansu ukun, sukasa Aunty farida a tsakiya ” DON yabawa driver umarnin yawuche dasu gd ” ba musu driver yata da motar da ma tsakaichin gudu yabar airport ɗin ” mamakine yakama Abba har yake faɗin kai Allah ya shiryamin Safras da Aryan da farida, wato ita farida tunda taga yan uwanta shike nan batada wata damuwa to Allah ya kara haɗamin kanku, Amin dukkan jama’ar wajen suka amsa dashi san nan suka ranƙaya gaba ɗayan’su suka shiga motochin lokachin har anfara kiraye kirayen sallar mangariba,
    A jere kuma a nitse motochin suka bar airport ɗin suka miki titin gida
    A dai dai bakin katafaren babban gate motochin suka rage gudun nan take security suka wage musu gate ɗin, suka kutsa chikin gd, 15 daga chikin motochin sukayi parking a harabar wajen 4 daga chiki kuma suka kusa garamin gate suka shiga chikin gd gaba ɗaya,kai tsaye parking space sukanufa ” suna kashi motochin da sauri security suka fito suna bubbuɗe kofar motochin ” Su Abba suka fito, Abba ya dubesu yana faɗin kuyi sauri kuyi alwala gashi har za’a tada sallah, yana gama faɗin haka yajuya yayi ɓangaren’sa da sauri ” Ammi ma ɓangaren’ta tanufa rike da hannun amrat da lamrat dayana hiyana da Zahra na biye da ita a baya ” Ummi kuwa rungume da salma tana rike da Aunty mardiya da ɗayan hannun’ta suka shiga ɓangaren’ta “Aunty amarya rike da hannun, Aunty Maryam suma suka nufi nasu ɓan garen” su Khalid kuwa kowa yanufi nasa ɗakin

    Ammi nashiga palo ta saki hannun’su tana faɗin kuyi sauri kuyi alwala koyi Sallah sai muje palon Abba mu gaisa koh tana gama faɗin haka ta nufi hanyar ɗakin’ta suma kowa tayi ɗakinta hiyana diyana dakuma Zahra suka nufi ɗakinsu, Amrat da lamrat ma sukayi nasu ɗakin

    Bayan sunyi sallah sungamane gaba ɗayan’su suka nufi palon Abba already Ammi tariga da tatafi chan ” da sallama suka shiga gaba ɗaya family suna zazzaune kan table ɗin chin, abinchi ido kowa ya ɗaga yana kallan’su banda DON dayake duke yake latsa wayar’sa ” a hankali Aryan ya dago ash eyes nashi yana kallanta still dai da light make up face ɗin ta ɗan karamin bakin nan yasha lips’gloss, kasa ɗauke kansa yayi daga kallanta sosai ya zuba mata ido sai taunan chingom take ” yusuf ne ya dawo dashi hayyachin’sa dacewa oyoyo my baby ku karaso mana, wajen table ɗin suka karisa gaba ɗaya ba wanda ya lura da chiwon goshin hiyana dan dasafe anchire mata ban dejin
    Zama sukayi ” Aunty farida tabawa masu aiki umarnin su zuba musu ferfesu kayan chikin SA da chips ” sannu da dawowa Abba ya hanya chewar hiyana ” Ammi tace kibari mana sai angama chin abinchi sai ayi gaishe gaishen Koh ” aa Aisha karki takurawa ƴa’ƴana yayi maganar yana kallan Ammi, dawo da kallansa yayi kan hiyana lfy ya….. Bai karisaba maganar ba idonsa daya sauka kan goshinta, subhanallah hiyana meyasameki a goshi haka a razane yayi maganar ” gaba ɗaya idon mutanen palon yadawo kanta har shi kanshi DON sai daya ɗago kai dan jin yadda Abba yayi maganar ” sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da yan yatsun hannunta,” Abba faduw… Bata karisaba tajiyo,” diyana na faɗin Aunty Maryam che tamana bugun mutu har sai da aka kaimu asibiti ” nan take ido jama’ar palon yadawo kan diyana lbr tashiga basu dalla dalla kamar antam bayeta” what? Abba yafada yana mikewa ” shiru palon yayi ba mai magana, Abba zai sake magana ke nan sai sukaji sallama a bakin kofar palon, amsa sallamar Abba yayi tare da faɗin shigo mana ” ɗaya daga chikin security ne kasa ya duka yana faɗin yallaboi kana da baki a waje ” ok nasan da zuwan’su gani nan zuwa yana gama faɗin hakan yakama hanyar fita ” Abba nafita Ummi ta dubi Aunty Maryam dake zaune hankalinta kwanche tace haba maryam me yaran nan suka miki zaki musu irin wan nan bugun ” dogon tsaki Aunty Maryam taja san nan ta ɗora dacewa na tsanesu ne shiyasa na bugesu ko zaki rama musune” gaba ɗaya palon kallon Aunty Maryam suke ” me yasa kika tsanesu Maryam, laifinme suka miki Ammi ta tambaya a nitse ” ke Aisha badake nakeba banzo kankiba tu kun nan tsanar dana ke mikine ae tasha fesu ” a fusache DON ya mike ya ɗaga yasu biyar zai zabga mata mari green eyes nashi ya sauƙa chikin na Aryan dake zaune ya zuba musu…✍️✍️

    Yau nayi kokari namuku long page to ina buƙatar more comments

    Iya comments iya read more amma jiyama kunyi kokari kunmin comments dayawa ina godiya 🙏

    *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*

    *

     

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 21

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 21

    Episode 21*

    💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖

     

    Kalmar shahada kawai hiyana take tagama saddakarwa mutuwa zatayi “kamar daga sama taji an damki kafarta ɗaya,wani dogon numfashi taja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya” gaba ɗaya kayan jikinta ya zame ya dawo wuyar’ta daga ita sai ɗan karamin wandon da iya chinya ya tsaya mata ko bra bata saba tula tulan boobs nata awaje “da sauri, DON ya kawar da kan’sa kefe,yana faɗin mikomin hannunki yafaɗa yana ɗaure fuska, hiyana kuwa kayan jikinta ya rufe mata fuska bata ganin’sa hannu kawai ta ɗaga masa ” dogon tsaki yaja san nan ya kama hannu nata ya saki kafarta,ta juya suna fiskantar Juna amma idon ta a lumshe “a hankali ta buɗe ido karaf idonta ya sauka chikin nashi, da sauri ta kawar da idon’ta daga kallansa ” Ke taka karfe ki hauro yafaɗa yana kara ɗaure fuska ” dan Allah yaya prince kayi hakuri wlh bazan iya takawa’ba tayi maganar kamar zatayi kuka ” shiru yayi yana tunani wai meyasa ma naka matane, meyasa ban barta, tafaɗa ba wlh badan yanzu idan nasake’ta ta faɗa tamutu nina yi kisan kae ba da sai na saketa, yayi nisa chikin tunani yaji hannunta na zamewa daga chikin nasa,zata faɗa kasa, da sauri yajawota da karfi tafaɗa kan faffaɗar kirjin’sa” hiyana duk tunanin’ta sakin ta yayi tsabar tsorata datayi sai da numfashin’ta ya ɗauke “jin jikinta ya saƙi ne yasashi kallan fuskar’ta hannu yasa ya ɗago haɓar’ta da’alama ta sume “dogon tsaki yaja yana turnuƙe fuska ya saɓeta a kafaɗar sa yajuya chikin ɗakin da ita a saman sofa ya kwantar da ita ya juya yanufi wajen mirrow
    Mayukan sa masu kamshi da tsada ya shafa ya feshe jikin sa da perfumes masu kamshi da tsada a nitse ya gyara gashin kan sa sai sheki da kyalli gashin keyi, gashi dark black ga tsansi, a hankali yake takawa kamar baisan taka kasan yanufi dressing room almost 30mnt yayi a chiki san nan yafito chikin suite baki sosai kayan suka masa kyau asalin kirar kijin’sa na jarumin namiji ya bayya half cover baki yasa a kafarsa ga wata ɗankareriyar agogon daimon a hannun sa sai kyalli yake yana ɗaukr ido ya sake fesa,Dubai perfume a jikinsa yadawo gaban drawer ya ɗau wayar’sa yanufi waje, a hankali yake takawa kamar baisan tafiya dakaga fuskar nan tashi kasan yana chikin bachin rae

    A bangaren diyana kuwa da sallama ta shigo palon Aryan baya palo Kai tsaye tawuce betroom nashi, sallama tayi a bakin kofa bata jira ya amsaba,tashiga tsaye yake a gaban mirrow, yagama shiri yana fesa turare, dressing iri ɗaya da DON sukayi,jin anshigo ɗakin’ne yasashi ɗago kai ya kalle’ta tachikin mirrow, “asukwane ya juyo domin ya tabbatar wa da idon itace ko aljana che sosai yake kallan ta “itama shi take kallo dan yau baƙaramin kyau yayi ba ” ina kwana yaya Aryan tafaɗa tana kawar da kanta daga kallan sa “kasa amsa gaisuwar nata yayi ya zuba mata ido yakasa ɗaukewa “Abba yace wae kazo da sauri tana gama faɗin haka ta juya daniyar tafiya,”da kyar ya iya buɗe bakinsa yace inazakije kuma “juyowa tayi a hankali fada zan koma tafaɗa tana turo baki,”ok to jira muje yana gama faɗin hakan ya ɗauki wayar sa,ya nufota “a tare suka jera kamar wasu taurari, kyau iya kyau “kayan nan sun miki kyau sosa, yafaɗa yana kokarin jan kofar palon “Yaya Aryan to tunda sunmin kyau kamin hoto dan Allah ta karisa maganar a shagwaɓe “to tsaya namiki guda biyu da wuri kinga Abba na jiran mu,”to hutona wajen guda 15 ya ɗauke’ta batare daya sani ba,”har sai da tace Yaya Aryan baka gama bane,” nagama amma matso nan na mana mu biyu “da sauri ta matso kusa dashi,ya juyo da wayar yamusu selfie kala 5 san nan yace,to muje “to ae baka nunamin hoton ba a shagwaɓe tayi maganar tana turo baki “mika mata wayar yayi yana faɗin,to muje muna tafiya kina kalla har mu iso, “to tace tare da fara tafiya

    Da Sallama suka shiga fada,gaba ɗaya kallo yadawo kansu,” a sukwane Khalid ya ɗago yana kallan su kama yajuyo yana kallan Yusuf yayi da shima Yusuf ɗin kallo Khalid ɗin yake,” Abba naganin su atare ba faɗa ba ɓachin rae a fuskar Aryan sae ma annashuwa daya gani a tattare da Aryan ɗin gawani ɗan murnushi da Aryan ɗin keyi yakai kallansa,kan diyana dake gefensa sun gera kafaɗa rike take da wayan Aryan tanata sakin murnushi”wani daɗi Abba yaji ya lulluɓe sa baima san lokachin daya fara sakin murmushi ba,chikin ransa yana faɗin alhamdulillah alhamdulillah, Allah na goɗema saura Safras kuma ya Allah ka kar’katomin da hankalin sa shima yadawo mutun
    “kasa kasa Umar yace wa haidar wai haidar ba wayar,yaya Aryan bane a hannun yarin yar nan,”shine mana haidar yaba shi amsa yana taɓebaki,”Aunty amarya kuwa kamar zata mutu dan bakin chiki tayi kwafa a zuchiyar’ta tana faɗin wlh,nakusa kawo karshen ku,”Ammi da Ummi kuwa ko ajikin su

    “jerowa Aryan da diyana sukayi kamar wasu taurari,sae taku suke a nitse diyana na kallan waya Aryan kuwa ya ɗaure fuska yana kallan kasa sai da suka iso tsakiyar fada, Aryan ya juya yanufi wajen zaman su ” da sauri diyana tace yaya Aryan wayan,kafa ta tambaya tana kallan’sa “baga ɗaya jamar wajen ido kawai suka zuba musu “Aryan baiyi magana ba har sai daya kae wajen zaman’l su ya zauna kusa da Khalid san nan ya ɗago ya dubeta kije da wayar idan kingama kallan hoton sai ki kawomin,”mamakine yakama gaba ɗaya family Abba musan man Aiman Aunty mardiya Aunty salma Umar haidar Ammi dakuma Ummi,
    “Abba da Khalid da Yusuf kuma sae murmushi suke,”Aunty farida kam tafi kowa murna da hakan, “Aunty amarya na sanyin magana tana tsoran Abba gakuma taron jama’a kar aji kunya,Amma tachi al’washin yin maganin abun ” Aunty Maryam kuwa kamar,zata mutu take ji dan bakin chiki,”kusa da Aunty farida diyana taje ta zauna tana faɗin Aunty farida ki kalla tayi maganar tana nunawa Aunty farida wayar Aryan,dake hannun’ta “ansar wayar Aunty farida tayi tafara kallan hotu nan, mamakine ya bayyana a kam face ɗin ta a hankali ta ɗago kae tana kallan inda Aryan ke zaune,”shima ita yake kallo, suna haɗa ido yama alama da ta kashe masa wayar kar tabari kowa yaga hotan, Jinjina kai kawai Aunty farida alamar to san nan ta kashe wayar ta sa chikin jakarta,”ta chiro wayar ta tamikawa diyana “da sauri diyana ta amsa tana murmushi tafara buga game ” tunani Abba yashigayi ba hiyana ba DON anya lfy kuwa buɗe baki yayi zaiyi nagana sae ga DON yashigo shi kaɗai “taku yake irin na jaruman maza gaba ɗaya Jamaar wajen,sai kallansa suka dan yahaɗu sosai mazama burge’su yake bare mata, kusa da Aryan yaje ya zauna ” gyaran murya Abba yayi ya dubi DON yafara magana Safras ina hiyana take ” shiru DON yayi yana ɗan tunani wacece kuma hiyana,kodai wan nan yarinyar da aka aiko takirani ” Abba ne ya katse masa tunani dachewa wai ba kai nake tambaya ba “da sauri yace tana ɗaki Abba yafaɗa yana turnuƙe fuska “gaba ɗaya idon kowa yadawo kansa “to meyasa kabarta a ɗakin Abba ya tambaya yana karewa DON kallo ” akule yace suma tayi Abba zan zuba mata ruwa kuma na manta Fahad yaje ya’zuba mata ruwa yayi maganar yana nuna Fahad da hannu ” a ruɗe Ammi tace me kamata tsorata kayi koh ” ka daure fuska yayi yana faɗin tazo zata faɗine na riketa ta tsorata da yawane shiyasa ta suma, ya karisa maganar kamar zae fasa ihu dan haushi,a ransa yana chewa wlh badan iyayena,ke min wan nan tambayarba da bazanyi maganaba haba dan Allah ayita sa mutun magana, “Ammi zata sake magana,Abba ya ɗaga hannu alamar tayi shiru “mikewa Fahad yayi daniyar yaje ya zubawa hiyana ruwa “Abba yace kae Fahad dawo kayi zaman ka shi daya razana ta tasume shi zae farfaɗo da ita idan an gama taro sae kaje ka zuba mata ruwan yakarisa maganar yana nuna DON “wani kululun bakin chikine,ya tokarewa DON makoshi a ransa yake wae shin meyasa na tai’maki yarinyar nan ne, meyasa ban barta ta faɗi ta mutu kowa ya huta’ba wlh na tsani yarinyar jifa yadda Abba yake wani magana sae…bae karisa tunanin ba yajiyo muryan Abba na magana, gaba ɗaya fada tayi tsit kowa ya zubawa Abba ido yana jiran yaji wanene sarki

    Ina mai farin chikin sanar da al’umma a yau ni Abubakar Khalid saraki zan sauka daga kujerar mulki na miƙawa ɗaya daga chikin ƴa’ƴana “asukwane DON Aryan Aiman Yusuf Fahad suka ɗago suna kallan Abba ido chikin ido suna jiran suji su nan wa zai kira gaba ɗayan su kirjin su sae dukan uku uku yake dukkan su kowa na adduar Allah yasa bashi,bane “Aunty amaraya kuwa sae murmushi take dan tasan abun dasuka kulla” Abba kuwa sake gyara murya yayi hankalinsa kwan che yachigaba da magana,a chikin ƴa’ƴan nawa bakowa bane face Ahmad “dam dam gaban Aunty amarya ya buga ” DON da bai taɓa murmushi ba a rayuwar sa,yau sae daya saki wani cool murmushi “wani nauyayyar ajiyar zuchiya Aryan da Yusuf suka sauke a tare “Aiman kam har da faɗin alhlillah ” nan take zufa yafara ketowa Aunty amarya”Aunty farida kuwa sai alhamllh munyi nasara take faɗi ” zubur Ahmad yamiƙe zai yi magana, Abba ya watsa masa harara, bashi yakoma ya zauna “Abba yachi gaba dacewa ” kubani hankalin ku ban gama magana ba ae,shiru sukayi suka saƙe nitsuwa yanzu ba sae anjima ba waziri kutashi ku naɗa Ahmad a matsayin sabon sarki,Abba nagama faɗin hakan yamiƙe nanfa jama’a suka fara hira masu murna sunayi masu,blach stomach sunayi, “jama’a suka fara turu ruwa wajen gaisawa dasu DON, “a kafara shigo da abin chiye chiye da shaye shaye

    “sauri sauri gudu gudu Aunty amarya ta bar fada tanufi chikin gida ɓangaren ta tawuce tana shiga ɗaki tafashe da kuka mara sauti ta ɗaukoh wayar ta tana kuka tafara kiran layin sadiya,”bugu ɗaya sadiya ta ɗaga “chikin kuka Aunty amarya tafara magana sadiya mun shiga uku aikin gagarabadau baiyiba sadiya ba Aryan ko Aiman a kabawa sarautaba, Ahmad akabawa “dan Allah hajiya hajara kiyi shiru kidai na kukan nan,mubi komai a sannu,dan anbawa Ahmad sa rauta sae akache maki bazamu iyasawa a chan zashi bane,chewar hajj sadiya” Aunty amarya ta goge hawayen ta tana faɗin to dan Allah sadiya kikoma wajensa gobe inkinje ki tuna masa da batun aikin yaran nan kinji,dan suma yanzu sun fara wuche gona da iri a gidan nan,bakiga yadda samarin gidan nan suka fara shisshige musu bane har da Safras fa wai yanzuma ɗayar yarinyar tana ɗakin’sa ga shigiyar ɗayar kuma ta makalewa Aryan harda bata wayar sa gashi uban su shi ya ɗaure musu gindi yahana kowa magana a kan yaran takarisa maganar chikin ɓachin rai “kai, kai, abun har yakai haka to wlh dole mutsaya muyi maganin karki damu ae wan nan ni aka taba ba keba dan Safras na zulaihat che dole gobe zan tafi Enugu idan ma gagarabadau bazae iya aikin ba zan tsallaka niger dan ayi mana sha yanzu magani yanzu ” to shike nan sadiya badamuwa bari naturo miki kuɗi yanzu batare data kira amsar Hajj sadiya ta katse kiran ta zauna a bakin gado tachi gaba da kukanta

    Sai misalin karfe 1:30 a kagama taro jama’a suka fara watse’wa

    diyana kuwa sae chin chocolate suke itada Zahra da amrat “lamrat kuwa tana zaune kusa da yaya Yusuf suna hira kamar wasu kawaye,hiyana kam har yanzu bata farfaɗo ba tana ɗakin DON
    Diyana ta ɗaukoh wani carton na chocolate zata buɗe karaf idon ta ya sauka chikin na Aryan dake zaune kusa da Aunty farida suna hira, wani mugun kallo ya wurga mata da sauri ta ajiye chocolate ɗin tana turo baki ” diyana lfy kika ajiye chocolate ɗin ki buɗe mana musha mana chewar Zahra “ni Aunty Zahra bana sha sai dai ku kusha tafaɗa tana kunbura kumatu “Aryan daga inda yake zaune bai san san da yayi murnushi ba dan yadda tayi maganar ”
    Daga bayansu sukaji a na faɗin, meyasa bazakisha ba yammata da sauri suka juya dan suga wanene wani hadadɗeb saurayine kyakkyawa mai chikar sura “lfy malam Zahra ta tambaya tana kallan face nashi “zama yayi a ɗaya daga chikin kujerun wajen yana faɗin lfy wajen sister ki nazo” wace sister nawa daga chiki Zahra ta tambaya “gata nan yayi maganar yana nuna diyana da hannu “ɗago fiska diyana tayi zatayi magana caraf suka haɗa ido da Aryan, ” da mamaki diyana ke lallan yadda ya chanza lokachi guda ta shiga tunani wae Bayanzu naga yaya Aryan na ɗan murnushi ba to me aka masa kuma naga idon sa sun sauya sunyi jaa gashi yawani ɗaure fuska”Zahra che ta katse mata tunanin datake dachewa diyana ana miki magana “firgigit tayi tare da sake kallo inda Aryan yake sae taga bashi a wajen dawo da kallonta tayi kan saurayin,dake zaune gabanta “kallon shi tayi from head to toe a gatsale tace waye kai “ajiyar zuchiya ya sauƙe san nan yafara magana nidae sunana walid ni ɗane ga sarkin zaria,kuma maganar gaskiya son ki nake kuma so irin na aure ba wasaba ” wani dariya diyana tayi kafin tace ni kake so amma dai baka da hankali koh to ni matar soja che sojan ma mai manya manyan bindigu “da sauri walid yamike yana faɗin kiyi hakuri wlh ni bansan ke matar aure bace “baki diyana ta taɓe tana mamakin kowaye yafa ɗa masa ni matar aure che daga chewa ni matar soja che to ae ban auri sojan ba tukun nan tayi nisa chikin tunani taji, Zahra na faɗin tashi muje chikin gd muyi wanka muyi sallah “Aunty Zahra wae har yanzu hiyana bata dawoba diyana ta tambaya tana kwaɓe fuska “eh bata dawo ba amma kar ki damu bakiji yaya prince yace tana ɗakin saba “mikewa diyana tayi jiki ba kwari suka nufi chikin gd

    Misalin karfe 8 na dare gaba ɗaya family Abba sun haɗu a table ɗin chin abinch har da DON,”Abba yayi gyaran murya yafara magana,ina hiyana take ne yayi tambayar yana kallan Ammi”da mamaki Ammi tace kae badai tun safe yarinyar nan tana sume ba takarisa maganar tana watsawa DON harara “miƙewa DON yayi da sauri dan bai san Abba yafara faɗa yanufi hanyar fita dan shi wlh kwata kwata ya manta da yarinyar,yau kwata kwata bai koma ɗakiba tun daya fita, da sauri yanufi betroom nashi kamar yadda ya kwantar da ita da safe haka ya sameta “dogon tsaki yaja, yajuya yakoma palo ya ɗauko ruwan Faro mai sanyi a freij ya dawo betroom ɗin a gaban gadon ya tsaya,ta buɗe bakin robar ruwan gaba ɗaya ya duddule mata a fuska,”a razane tamike zaune tana ihu,”wani tsawa ya daka mata shoothup, “shiri tayi ta ɗago ido a hankali tana kallansa jikinta sai kerma yake “kawar da kansa gefe yayi yana faɗin tashi kifita min a ɗaki tun ban babballaki ba “da sauri ta miƙe danufin tatafi amma ina wani jirine ya kwashe ta tafaɗi kasa kanta ya bugu da jikin gadon, wani marayan kara tasake dan yinwar datake ji bazai bari tayi kara sosai ba “a fusace DON yace ke me haka kitashi kifita a ɗakin nan nace “chikin kuka da dashewar murya tace dan Allah yaya prince ka taimakeni wlh bazan iya tashiba jiri nake ji ga… Bata karisa maganar ba sakamakon wani mugun kallan daya wurga mata chikin tsawa yace wlh idan baki fita a ɗakin nan ba sai na ballaki “da kyar ta miƙe tana dafa bango tana tafiya, kamar zata mutu ga yinwa ga sarawar da kanta ke mata wasu siraran hawayen bakin chiki da azabar chiwon kae ke bin kunchinta ta kyar ta fito tanufi ɓangaren Ammi “shikuwa DON kwanchiyar’sa yayi a kan katafaren gadon’sa

    Abba yaga shiru shiru ba DON ba hiyana sae yace ke diyana tashi kije ki kiramin Safras “da sauri Aryan yace bari na kirasa Abba, batare daya jira amsar Abba ba yayi waje da sauri,”itakuma diyana takoma ta zauna jim kaɗan sai ga Aryan da DON sun shigo a jere tun basu zauna ba Abba yafara tambayar ina hiyana “tatafi ɗakin’su DON yabasa amsa yana ɗaure fuska “da sauri Ammi ta miƙe ta ɗauki plate ta zubawa hiyana abinchi da kanta ta fice daga palon ” Abba yayi gyaran murya yafara magana kubani hankalin ku, kai Safras da kae da Aryan da Khalid da Yusuf wan nan ba shawara bane umarnine gobe inasan kuraka Aisha dasu diyana kauye “a sukwane DON ya ɗago zaiyi magana ganin babu wasa a fuskar Abba ne yasa yayi shiru “nima zanje Abba chewar Aunty farida “aa my daughter bani zaki tambaya ba ae mijinki zaki tam baya,” to shike nan Abba zan tambaye’sa
    shiru palon yayi sae karan spoon kawae kakeji “Mikewa DON yayi rae a ɓache ya fita palon”miƙewa Aryan ma yayi yabi bayan sa har yakai bakin kofa sae kuma yajuyo yana kallan diyana ke kikawo min coffee da wuri yana gama faɗin hakan yayi waje da sauri “da ɗai ɗai suka watse kowa yanufi ɓangaren’sa

    Da sauri diyana tayi wanka ta shirya chikin wandon jeans blue da yar t-shirt fari, light make up tayi tasa lipsgloss a ɗan jaramin bakin nan nata ga kitso guda biyu a gaban goshi yakai har kan chikinta tasa turaren da Aunty farida ta bata tanufi shoe rack ta ɗauko high heel fari “hiyana na kwanche kan gado tana ta binta ta ido duk a galabaice take, Zahra kuwa tana palo suna hira dasu yaya Khalid da amrat da lamrat,” hiyana na tafi diyana tafaɗa tana kokarin fita da sauri “diyana bakisa ɗan kwali bafa chewar hiyana tayi maganar kamar zatayi kuka dan yadda kanta ke sara mata,”aa hiyana kyale ɗan kwalin nan zafi nakeji bata jira amsar hiyana ba tayi waje “a palo tasamu Zahra yaya Khalid yaya Yusuf lamrat da amrat sae hira suƙe ” har kasa ta duƙa ta gaida su Yusuf ” “khalid yace wow my sister irin wan nan kwalliya haka ina zakije “hannu diyana tasa tarufe fuskar’ta ta mike tana faɗin zanje na kae wa yaya Aryan coffee ne “kallon Yusuf khalid yayi suka haɗa ido suna ɗan murmushi Yusuf yajuyo ya kalleta yace to yi sauri kije kinji sister “bata jira ya karisa maganar ba tayi waje,dan daman yaya Aryan yace tayi sauri takawo mar gashi ta ɓata lokachi wajen wanka da kwalliya “kichin tanufa a gurguje ta haɗa masa coffee ɗin,ta ɗauka tanufi ɓangaren’sa

    Da sallama a bakin ta tashiga palon zaune yake saman sofa yana latsa waya karisa shigowa palon tayi gaban sa tazo da ɗuƙa a nitse tace yaya Aryan ga coffee ɗin,”shiru yayi tamkar baiji me take faɗe ba, yachi gaba da latsa wayar sa shiru shiru almost 10 mnt “a shagwaɓe takuma chewa yaya Aryan pls ka ansa mana wlh nagaji “tam kar bai’san da mutun awajen ba ko motsi bai yi ba wayar sa kawae yake latsawa shiru shiru almost 15 mnt again”a hankali tamiƙe tanufi ɗan karamin table ɗin dake tsakiyar palon ta ajiye coffee ɗin takama hanyar fita daga palon “ke zo nan yayi maganar chikin tsawa wadda yasa sai da ta tsorata “da sauri ta juyo tana kallan sa fuskar nan tasa kamar bai san menen dariya ba ga idon sa sun jaa, wani tsoran sane ya dira mata a rae da,gudu gaske ta juya zatayi waje amma sae dae ta’manta high heel tasa “a zafafe yamiƙe taku ɗaya ya ɗamko gashin kanta ta baya”kware baki tayi zatayi ihu yasa hannu ya rufe mata baƙi,a fusace yake faɗin kimin shiru ko na ɓabballaki a chikin ɗakin nan ” shiru tayi tana zare ido”sakin ta yayi yana kallan face nata chikin tsawa “yace me yahaɗaki da wan chan yaro “wani yaro kuma tafaɗa tana zare ido” nikiƙe tambaya wani yaro, dawaye kukayi hira ɗazun a fada “baya baya ta farayi yana binta har suka kure bango “bazaki bani Amsa ba sai na ɓallaki yayi maganar chikin tsawa “muryana na rawa tafara magana,wlh yaya Aryan,ban san shiba shine kawai yazo yace yana so na kuma ni nafaɗa masa ni matar sojane “ido kawai ya zuba mata yana kallan yadda lips nata ke motsi,wani irin sabon yanayi yake ji yana ratsa jini da kowanni jijiya na jikin sa har izuwa zuchiyar sa “yatsa ɗaya ya ɗora a kan lips nata yana faɗin shiiiiiii alamar tayi shiru dan inta chigaba da magana zata iya zautar dashi “ɗago ido tayi tana kallan sa shima ita yake kallo, da kyar ya iya buɗe baki muryan sa har sarke wa yake “wae bana hanaki yin kwalliyar dare ba yayi maganar tare da chire yatsar sa daga kan lips nata “murya na rawa tafara magana kayi, kayi,kayi,hakuri ba…. chikin sauri yasake ɗora yatsan sa a kan lips nata yana girgiza kai ” ido kawai ya zuba mata yana kallon ta a hankali ta ɗago idon ta itama tana kallan sa matso da fuskar sa yayi dab danata har suna iya jiyo nunfashin Juna “zaro ido waje diyana tayi tana..✍️✍️

    Sorry masu karatu sai mun haɗu gobe

    *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*

    *