Blog

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 14

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 14

    Episode 14

    A fusace jabair yanufi diyana, tana tsaye ko motsi batayiba kuma babu alamar tsoro ko kaɗa a face nata ” hannu Jabir ya ɗaga zai’kaiwa diyana bugu ” da sauri hiyana tarike hannun nasa ” a zafafe Yajuyo yaga waye yarike masa hannu, ganin hiyana che yasa ya watsa mata harara yana faɗin sakeni ” ita ma rai a bace tache wlh bazan sakekaba kafara buguna tukun nan kafin kabugi diyana ” fisge hannunsa yayi yasake ɗaga hannu zai mari diyana ” da sauri hiyana tashiga tsakanin’ su tana faɗin diyana kiwuche class naku ” diyana dake tsaye babu alamar tsoro a face ɗin ta tace babu inda zanje hiyana sai dai duk abun da zai’mana yamana tare ” ganin haka yasa jabir yajuya yabar wajen dan kuwa bazai iya bugun hiyana ba dan yana sonta itakuma bazata taɓa barin abugi diyana ba ” suna ganin jabir yatafi suka rungumi juna ” diyana nafaɗin wlh sauran kaɗan nayi fitsari a wandona dan tsoro, dayanzu jabir yabugeni da wan nan katakon hannun nasa ai nashi uku ” dariya hiyana tayi sosai san nan tace wlh ba kyaji diyana ae nima nakusa fitsarin saboda tsoro kawai dagewa nayi dan bazan iya ganin ya sauke wan nan jibgegen hannun nasa a jikinkiba ” dariya sukayi gaba ɗayansu san nan suka saki juna suka reke hannun’su chikin na juna suka nufi class,

    KASAR SAUDIA

    Tsaye yake gaban mirrow yana gyara gashin kansa sanye yake chikin wandon jeans Navy Blue da White t-shirt, bakaramin kyau kayan suka masaba sosai ya gyara gashin kan nan nasa ya tara ya ɗaure ta baya, yasake ɗaukan turare yafeshe jikinsa,ga sajen nan nasa kwanche a kan face nashi kamar wani balaɓe wayarsa ya ɗauka yafito wajen kai tsaye palon kasa yanufa, zaune yasamu yan uwan nasa gaba ɗayansu har dasu haidar, kallan DON yayi yafara magana ” zan fita inasan inje wani wajen ” da mamaki DON ya ɗago green eyes nashi yana kallan Aryan ya mai maita maganar zai fita inasan inje wani waje shiru yayi kamar mai tunani ” Aryan dai ido yazuba masa kawai yana kallan’sa ” zarginafa yafara tabbata a kanka Aryan chewar DON ” murmushi kaɗan Aryan yayi san nan yace au daman zargina kake ke nan ” yap zuchiyata na zargin wani abu ” matsowa Aryan yayi kusa da DON sosai san nan yafara magana karkabar zuchiyarka tana raya maka wani abu a kaina kasan dai wlh babu wani abun dazanyi batare da saninkaba yanzunma kasawu zanje kuma nasan bazuwa zakaiba konache muje, shiyasa banche mujeba nayi shirina na zuwa nikaɗai ” dogon numfashi DON yaja san nan ya jinjina kai yana faɗin ok to shike nan nayarda ba komai Allah ya tsare a dawo lfy yayi maganar yana kokarin mikewa kai tsaye stairs ɗin yanufa ” binshi da ido Aryan yayi har yakurewa ganinsa san nan ya dawo da kallansa kansu Khalid ” a nitse yache na wuche ” adawo lfy suka masa gaba ɗayansu ” san nan face yana amsawa da Amin
    Mikewa Khalid yayi yana faɗin Yusuf muje Koh ” mikewa Yusuf ɗinma yayi zasu wuche waje sukaji Ahmad na faɗin wlh akoi abun da kuke shiryawa, wani harara Khalid ya wurgawa Ahmad batare da sunyi magana ba suka nufi hayar fita palon ” kallan Aiman Ahmad yayi yana faɗin tabbas yaya Yusuf da yaya Khalid suna shirya wani abun ” mikewa Aiman yayi yanufi staircase ɗin yana faɗin zanyi binchike a kansu ae zan samusu ido sosai yanzu ” mikewa Ahmad ma yayi yabi bayan Aiman ” dogon tsaki fahad yaja san nan yace wlh yaya Ahmad da Yaya Aiman kunchika gulma ni barima naje na gaida su ammi yayi maganar yana kokarin mikewa ” haidar da umar suna ganin fitar fahad suka kwashe da dariya kamar abun haɗin baki sai dasukayi mai isarsu, tukun nan suka tsagaita ” kasan me haidar da alama fa akoi dirama a gd nan wlh chewar umar ” jijjina kai haidar yayi yana faɗi babbama kuwa, amma naga alamar yau yaya Aryan nachikin farinchiki sosai bakamar jiyaba ” kai dai tashi muje mu gaidasu Abba inmunje ɗaki makarisa magana chewar umar a tare suka mike sukayi waje,

    Mai martaba Ammi Ummi Aunty amarya zaune suke a nasu palon suna hira “Fahad yashigo da sallama” amsa masa sallamar sukayi yashigo chiki ya zauna saman sofa ya fara gaida iyayen nasu ” da fara’a suka masa ”

    Ummi ta dubi mai martaba tace ranka yadaɗe wai yabatun komawar yaran nan bakin aikinsune ” shiru Abba ya ɗanyi kafin yace bayan zuba sai bayan naɗin sarauta ” eh hakanma yayi chewar Ammi ” aa baiyibakam gaskiya sukoma wajen aikinsu chewar Aunty amarya ” jinjina kai mai martaba yayi yana faɗi aa aini ba zaɓinku nanemaba bare kufara musu hukunchina kawai nayanke sai anyi naɗin sarauta ” calmly Fahad yafara magana Abba inasan zuwa Us ” da sauri Ammi ta ɗago tana kallansa zatayi magana mai martaba yarigata dachewa sai kayi aure tukun nan dan inbakiyi aureba bazaka sake fita Nigeria ba ” baƙaramin daɗi Ammi tajiba jin amsar mai martaba ” Fahad kuwa a razane yace Abba Aure fa kace ” eh aure a kache auren wani mugun abune Ummi tabashi amsa rai a bace ” bahaka bane Ummi bawai auren ne mugun abuba taya zanyi aure su DON basuyiba ” dogon numfashi mai martaba yaja san nan yace ae suma a nayin naɗin sarauta, zansa su sufito da mata dan ya isheni ganinku haka ” dariya Fahad ya kwashe dashi yana faɗin wayyo duniya wayaga DON da mata chab to wai suda ko yanmata basu taɓayiba ai na zasu samo matar ” Ammi tace kai banfa san iskanchi kasani ne dasu kake fitane ” ae Ammi infaɗamiki duk wanda yasan yaya Aryan yaya Prince yaya Yusuf yaya Khalid yaya Aiman yaya Ahmad yasan basuda budurwa kuma basu taba chewa ko chikin wasa sunasan wataba suda ko kalloma mace bata ishesuba ” tashi kafita mana a ɗaki chewar Ammi ” fahad zai sake magana sai sukaji sallamar Haidar da umar ” Abba yace yauwa kuzo nan kuma daga yanzu kuje kufara neman matar aure dan wlh bayan naɗin sarauta duk aurar daku zanyi na huta ” ɗaure fuska haidar yayi san nan yajuya yanufi hanyar fita yana faɗin inazuwa ” salati Aunty amarya tayi kana tace yanzu maganar auren ne tasa kajuya kafasa shigowa koh haidar ” haidar dai baibi ta kansuba yayi waje da sauri ” da sauri umar ma yajuya yabi bayansa ” mikewa Ummi tayi tana faɗin kai jama’a zama bai gammuba wayan nan yaran sai na danganasu da ɗakin kaba barima naje nafara musu addua tun da sassafen nan yara saikache wadda aljana ta aura, ” Mikewa Ammi tayi tace muje tare wlh sai mun haɗa da sallar darema dan abun nasu yafara wuche hankali ” mai martaba ma yamike yana faɗin muje tare dan nima naga alamar sai na haɗa da tawa adduar ” a tare suka nufi waje Aunty amarya kuwa tamike tanufi ɗaki ta haye gado ta kwanta ” baki buɗe fahad ke kallansu Abba har suka fice afili yace wai muza’awa tsayuwar dare harma da danganamu da kaba yanzu mai mukayi hmmmm baridai naje nafaɗawa DON halin da ake chiki yamike ya fito ya haye lifter yakoma sama

    Da sallama yashiga ɗakin don kwachi yasameshi a kan makekiyar gadon sa yana latsa waya karisawa chikin ɗakin fahad yayi ya haye gadon ɗago kai DON yayi yana kallansa ” kwaɓe fuska fahad yayi kamar wadda ya taka kashi ” lfy kazo kana bata rai DON ya tambaya ” daman kamar jira Fahad yake a tambayesa nan take yafara faɗawa DON abun da yafaru a ɗakinsu Ummi yanzu ” dogon tsaki DON yaja yana faɗin to suyi tsayuwar asubama ba na dareba ni dallah tashi kabani waje na daukama wani abinne nine za’achewa na kawo mata aure niɗin never wlh babu aure a tsarin rayuwata ” da karfin guiwar fahad yamike yafito dan shi a tunaninsa DON zai watsa maganar auren

    KANO STATE NIGERIA

    Misalin karfe 4 na yamma suna zaune a palon Ammi hiyana na karatun qur’ani diyana na game a wayar Zahra ” Zahra kuma tana gyarawa amrat gashi ” lamrat kuma tana Assessment na English da a kabasu a school kawai sukaji diran motochi gidan jiniya kakeji ta ko ina ya karaɗe gidan ” diyana tamike tana faɗin kodai su Abba ne suka dawo ” aa basu bane chewar zahra ” hiyana zatayi magana ” Zahra tace kutsaya kutsaya naji kamar busan gidan sarautane hakan nanufin Aunty maryam ne tazo tab ” da sauri Hiyana ta ɗago tana kallan Zahra wacece Aunty Maryam hiyana ta tambaya tana kallon Zahra ” babban yarinyar Aunty amaryan che chewar Zahra ” tab wlh tun danaji yarinyar Aunty amarya che nasan muguwache irinsu yaya Aryan chewar diyana ” baki buɗe hiyana ke kallanta san nan tace ke diyana nikam taushe zakiyi hankaline haka a kachemiki ita muguwace ” da sauri zahra tace aa hiyana diyanafa batayi karyaba tabbas aunty maryam muguwace nabugawa ma a jarida ” lamrat tace to Aunty Zahra to daman ina Aunty maryam ɗin take ” tayi aure ne a gombe kinsan Aunty amarya yar sarkin gombe ne to yayan Aunty amarya shine yake rike da mulki yanzu yana da babban ɗa mai suna Mahmud to Mahmud ɗin ne mijin Aunty maryam shiyasa kukaji karan irin busar da akewa Abba idan zai fita ta ko ina ai mijin Aunty maryam ɗin shine yarima mai jiran gado ” to Aunty Zahra me tazoyi gidan nan yanzu chewar diyana ” itakam hiyana baki bude take kallan diyana tana tunani mutun da gidansu amma diyana ke tambayar me yakawota ” murmushi Zahra tayi san nan tace ai daman kowani sallah suna zuwa ammafa sai anyi sallah da kwana ɗaya suke zuwa ” to ai yanzu Sallah sauran kwana 10 meyasa tazo chewar diyana ” Zahra zatayi magana hiyana tarigata dacewa zaki iya zuwa ki tambayeta ai meyasa tazo ” mikewa Zahra tayi tana faɗin kuzo muje mumata sannu dazu kartace munajin zuwanta mun shareta ” mikewa sukayi gaba ɗayansu suka bi bayan zahra

    Kai tsaye bangaren Aunty amarya suka nufa da sallama suka shiga wasu yan mata guda 3 suka samu da alama kuyangun Aunty maryam ne ” yanmatan suna ganin su Zahra suka fara gaidasu ” lfy kawai Zahra ta amsa musu dashi san nan kai tsaye ta wuche tanufi wani ɗaki ” su hiyana suka rufa mata baya ” sallama zahra tayi a bakin kofar kusan 5 mnt tukun nan a ka amsa tare da izinin shigowa ” diyana kam sotake kawai taga wan nan Aunty Maryam ɗin ” shiga chiki sukayi gaba ɗayansu zaune a gefen gado suka samu Aunty Maryam dukawa kasa zahra tayi tace sannu dazuwa Aunty Maryam ya hanya ” ganin Zahra ta duƙa yasa hiyana da lamrat da amrat suma suka ɗuƙa ” diyana kuwa tana tsaye ” ɗago kai Aunty Maryam tayi tana kallansu itama kamanninta ɗaya da Aiman sosai ” bata amsa sannu da Zahra tamataba sai daima tsawar data dagawasu diyana ke kuma wacece, wasu kazamai’ne Zahra kika kawomin ɗaki ” murya na rawa Zahra tafara magana yan uwa na ne yayan kawuna..” a fusache Aunty Maryam tace get out of my room ” da sauri Zahra tamike tarike hannun amrat tana faɗin kuzo muje, mikewa hiyana da lamrat ma sukayi suka nufi kofar fita, har sunkai kofa sai kuka juyo sukaga diyana a saye bata ko motsaba ” diyana kizo mutafi mana ” firgigit diyana tayi alamar dai tunani tashiga maganarsu che tadawo da ita daga duniyar tunani datashiga juyawa tayi tanufesu tana faɗin dan kinsamu munzo kaisheki zakiwani che mufita to wlh badan Zahra bama bazuwa zanyiba ” what ? Ke dan uban ki zo nan chewar Aunty Maryam ” ba musu diyana ta juya takoma wajen Aunty Maryam ɗin ” dago ido Aunty Maryam tayi ta kalli su zahra ai tunkan tayi magana Zahra taja amrat sukayi waje hiyana da lamrat suka rufa musu baya ”

    dawo da kallanta kan diyana tayi from head to toe take kallan diyana, wayarta ta ɗauka ta danna kira jim kaɗan a ka daga kiran ” kushigo iya abun datache ke nan ta katse kiran ta ajiye wayar ” jim kaɗan saika wayan nan ƴanmatan dasuke palo zaune dazun sun shigo har ƙasa suka duƙa suna faɗin rankiya’daɗe kamu ” chikin izza danuna isa Aunty Maryam tafara magana kumike ku bugammin yarinyar nan ” diyana najin hakan ta watsa a guje tayi waje sukuma yan matan sukabi bayanta ” Ajiyar zuchiya Aunty Maryam ta sauke san nan tace ai ko ban tambayaba nasan kune Aunty amarya ke bani lbr kuma danku nazo gidan nan ubanku zakuchi wlh sai kungudu da kafarku kafinsu Abba su dawo

    Diyana kuwa tana fita kai tsaye wajen security tanufa da gudu kai tsaye bayan shahram tanufa ta ɓuya yan matan na isowa suma tsaya chirkoh chirkoh ” shahram da bajin hausa yakeba sai tambayar diyana yake what happened itakuwa diyana ba wani turanchin kirki takejiba ” ganin yammatan suna kokarin kama diyana yasa shahram ɗaga musu hannu kana yachiro wayarsa yafara neman layin ogansa ” tsayuwa yan matan sukayi shiru sunasan zuwa sukama diyana subuga dan inbasu bugetaba Aunty Maryam zata hukuntasu gashi sukuma suna tsoron sojojin nan ga Shahram fuskarsa babu annuri ” shahram kuwa kiran layin Aryan yashiga yi wayar tanata ringing har sai da takusa tsinkewa tukun nan Aryan yayi picking call ɗin ” a nitse shahram yafara masa bayanin abun dake faruwa chikin harshen turanchi ” give har the phone abun da Aryan yache kawai ” da sauri Shahram yamikawa diyana wayar, hannu tasa ta amshi wayar tamanna a kunne tana faɗin hello ” ajiyar zuchiya Aryan ya sauke yana faɗin ae daman nasan ke’che dan duk gidan nan ba mai neman faɗa sai ke meya haɗaki dasu , suwaye nema ” murya na rawa tace wlh yaya Aryan babu abun dana musu kawai dan munje gaishe da Aunty Maryam ne sai tace wai mu kazamaine mufita mata a ɗaki shine nukuma nace dan tayi sa’a ma…. Bata karisa maganarba Aryan ya dakatar da ita dachewa ya isa haka bawa shahram wayar mika masa wayar diyana tayi bata san me suka tattau naba sai dai taji Shahram yace let’s go madam ” gaba tayi yabi bayanta sukazo suka wuche yammatan ” da sauri yammatan suka juya zasubi bayansu shahram ya dakamusu tsawa bashiri suka tsaya, har bangaren Ammi shahram ya kai diyana san nan yajuya yakoma bakin aikinsa ”
    yan matan kuwa jiki na bari suka juya suka koma inda suka fito chike da zullumin hukunchin da Aunty Maryam zata musu dan basu bugi diyana ba da sallama suka Shiga ɗaki waya suka samu Aunty Maryam keyi duƙawa sukayi gaba ɗayansu a kan guiwowinsu suna jiran hukunchi ” bayan tagama wayarne ta ajiye wayar a gefenta afilli take faɗin bazanyi jayayya da kaiba Aryan amma kuma a chikin ruwan sanyi zan dafa yaran nan, dankuwa Aunty amarya bata sonsu suna sata baƙin chiki nikuma duk abun da zaisa Aunty amarya baƙin chiki bana sonshi, kuma dole na kawar mata dashi shiru ta ɗanyi san nan tadubi yanmatan tace kutashi kutafi , ” mamakine yaka masu mikewa sukayi suka bar ɗakin suka koma palo suka zauna

    A bangaren diyana kuwa shahram na shigar ta ita ɓangaren Ammi ta kwasa da gudu tayi chikin palo kai tsaye ɗakinsu tanufa ba ko sallama tashige ” Zahra na ganinta tamike tana faɗin bata bugeki bakoh diyana ” dariya diyana tayi san nan tashiga basu lbr abun dayafaru ” ajiyar zuchiya hiyana ta sauke san nan tace kai Allah yayiwa yaya Aryan albarka kekuma sai ki kiyaye bakinki ” shiru diyana taɗanyi kamar mai tunani ” Zahra ta dafata tana faɗin to tunanin me kuma kike diyana ” dariya diyana tai san nan tache ina tunanin yau wache rana yaya Aryan yayi abun arziki ” tsaki hiyana taja san nan tace ni kunga tafiyata lokachin shirya abun ɓuɗa baki yayi tana kaiwa nan tafice ” mikewa su lamrat sukayi gaba ɗayansu s Yanzu wasan zai fara k

    Pls more comments an share

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 24

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 24

    Episode 24*

    A gurguje Aryan ya karisa ɓangaren sa, kayan jikinsa yafara ragewa, ya rage da gashi sai shot ya nufi toilet dan yin wanka, after 45mnt yafito ɗaure da towel ya nufi gaban morrow, wayar sa dake saman drawer mirrow ya ɗauka yafara kiran layin Aunty farida, budu ɗaya Aunty farida ta ɗaga tare da faɗin “hello bro, “Aunty babba pls ki turomin yarin yar nan bari na dubata “ok bari na kawota da kai na dan bazata iya tafiya ba tana ganin jiri, batare daya sake magana ba ya katse kira da sauri sauri ya shafa mayu kan sa masu kamshi da tsada feshe jikinsa yayi ta haɗaɗɗiyar parfume nashi mai shegen kamshi da tsada, gyara haɗaɗɗen kuma lallausan bakin gashin kanna nasa yayi, ya ɗaure a bayan ya zuba jelar gashin a bayan wuyar sa sai kelli gashin keyi,

    zubawa mirrow sosai ido yayi yana kallan kansa, shiru yayi kamar mai tunani, jin motsi a pallo ne yasa ya juya da sauri yanufi dressing room nashi dan shiryawa,

    da sallama Aunty farida ta shigo ɗakin rike da hannun diyana sai faman lumshe ido take, ganin ɗakin ba kowa yasa Aunty farida tace “my diyana jeki zauna a saman sofa ki jirashi kinji, “to kawai diyana tace tanufi sofan da kyar take tafiya saboda sarawan da kan ta ke mata, Aunty farida kuwa juyawa tayi ta fice daga ɗakin,

    Zama diyana tayi ta jingina da jikin sofar ta kwantar da kanta ta lumshe ido kamar mai barchi, Almost 12mnt tana zaune shiru,har barchi yafara ɗaukar ta, wani fitinannen kamshi ne ya daki hanchin ta wadda yasata sauri waro ido karaf blue eyes nata suka sauka cikin ash eyes nashi, tsaye yake sanye da jallabiya Black colour zuba mata ido yayi sosai yake kallonta, da kyar ta iya buɗe baki tace “ina wuni yaya Aryan, juyawa yayi batare da ya amsa ba yanufi wajen drawer

    A box ya ɗauko ya dawo kusa da ita ya zauna,spirit and cotton ya fitar yafara mata dressing wajen, chikin shagwaɓa da murya kamar na mai kuka tace “yaya Aryan zafi ya’kemin sosai ta karisa maganar tana turo baki, subhanallah wani irin shock yaji saboda yadda tayi maganar, zuba mata ido kawai, yayi ya dakata da aikin da yake har takai karshen maganar, da kyar ya iya sai ta tunanin sa, ya buɗe baki murya kasa kasa kamar mai raɗa “sorry kinji dole zai miki zafi amma zan miki a hankali,

    Sake turo baki tayi tana faɗin “to ni kawai kabari tun da akoi zafi “kinfi san ki zauna da chiwon ke nan, gyaɗa masa kai tayi alamar eh “bakisan yin kwalliya ke nan, da sauri tace “a’a inasan kwalliya “to in baki tsaya an miki magani ba to fiskan ki zai ɓachi bazaki rinƙa kwalliya ba, chikin marairai chewar murya tace “to ayya yaya Aryan kamin a hankali kaji wlh akoi zafi, ta karisa maganar kamar zatayi kuka, shiru yayi batare daya sake magana ba ya mai da hannunsa kan goshin’ta ya chigaba da dressing na wajen,

    sai mutsu mutsu diyana keyi taki tsayawa zafi wajen ke mata sosai nan take tafara ruwan hawaye, dafe kansa yayi da hannun sa ɗaya yana faɗin “kinsan ban san kuka ko kiyi shiru ae nakusa gamawa kinji, gyaɗa masa kai kawai tayi amma bata dai na hawaye ba “wai ba ke che kika che zaki auri soja ba,ya tambaya yana kallan face nata, da sauri ta ɗaga masa kai alamar eh “to ai matan sojojin jarumai ne basa kuka, cikin shesshekar kuka tace “Allah yaya Aryan zafi yake yi mini ne shiyasa amma na daina kukan ta karisa maganar tana goge hawayen ta, girgizar kai kawai yayi ya chigaba da aikin sa sauri sauri yake mata dan karta chigaba da kuka bai san kukan nata ko kaɗan,in tana

    Bayan ya kammala ya mai da komai ya rufe Box ɗin ya ajiye a gefe ya miƙe ya koma bakin katafaren gadon sa ya zauna yana kallan ta, sai faman yamutsa fuska take tana turo ɗan bakin. “me ya haɗaki da wanchan wawan mutumin har ya bugeki haka, yayi maganar yana ɗaure fuska , dama kamar jira take tafara bashi lbr tun shigan ta gidan da yadda ya buga mata sandar duk sai data bashi lbr komai, tun da tafara magana ya kafeta da ash eyes nashin nan, ya kasa chire idon sa a kant, yadda take motsa lips nata nan jiyake kamar yamiƙe yaje yayi kiss na lips ɗin ko zai samu sauƙi abun da yake ji a zuchiyar sa, da sauri ya kori sheɗan ta hanyar furta a’uzubillahi minasshe ɗanir rajin kafin yace “to daman tun asali me tsaka nin ku kuna da dan gantaka da shine, “aa bamu da dan gan taka ɗan yayan Inna che, “what kara waro ash eyes nashi yayi sosai a kanta, nan take ya ƙara ɗaure fuska rai a ɓache yace “to daman kun taɓa samun matsala da shine a baya da har yake ikirarin zai kashe ki, “eh kullun idan inna ta aike mu ɗiban ruwa sai ya tare mu ya zubar mana da ruwa, nan dai diyana tashiga bashi lbr duk abun da yataɓa haɗa su da buba from A to Z har fyaɗen da yaso yayi mata,

    shiru yayi, nan take fuskar sa ta sauya kamanni idon sa suka sauya su kayi jaaa sosai, lokachi guda, a fusache ya furta “fyaɗe, a tsorace diyana ta gyaɗa masa kai alamar eh gaban sai faɗuwa yake dan ganin sauyawar yaya Aryan lokachin guda gawani huchi da yake duk jijiyoyin kansa sun tashi sosai, gawani zufa da yake kamar ba A.c a ɗakin jikinsa har wani tsuma yake gaba ɗaya ilahirin jikinsa ɓari yaƙe gashin hannun sa duk sun mimmiƙe,Sai faman chizan red lips nashi yaƙe da karfi kamar zai fasasu, kamar alluran sojan nashi ne ya tashi, nan take matsanan chin tsoran sa ya dira mata a rai, tunani ta shigayi anya bazan tashi in gudu ba kuwa karya bugeta,

    dafe hannun sofa tayi ɗakyar tamike wai dan ta gudu kar ya bugeta, cikin tsawa ya furta “ina zakije, jikinta sai kerma yake chikin wata iriyar voice kamar zatayi kuka tafara magana “dan Allah yaya Aryan kayi hakuri karka bugeni wlh ni bana san duka kaji ta karisa maganar tare da sakin wani marayan kuka mai ratsa zuchiyar mai sauraro, runtse ido yayi dan har chikin zuchiyar sa yake jin kukan nata, ya dafe kai,dan bai san kukan data keyi ko kaɗan sassauta sexy voice nashi yayi calmly ya fara magana “nache zan bugeki ne kimin shiru ki koma ki zauna, “yaya Aryan to kishi nake ji ina san in sha ruwa, Slowly ya waro ash eyes nashi a kan face ɗin ta, sai hawaye take wani na bin wani “ok jiki ɗauko ruwa a freij kizo, to kawai tace san nan tanufi palon tana jan kafa a hankali, ido ya zuba mata yana kallonta sosai har ta fice daga ɗakin, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ya sauke, kana yasa hannunsa yana yamutsa gashin kansa, wani iska mai zafi ya furzar daga bakin sa a hankali yafara magana “Aryan wai meke damun kane meyasa na kesan yarinyar nan ta rinƙa kasan chewa kusa dani, yanzu dache ta zauna me zan bata,anya ina lfy kuwa? meyasa nake ɓata rai na dan wani ya taɓa chewa zai mata fyaɗe? Meyasa zan bugi malamin makaranta su dan yache bazai dai na Son taba? why me ruwana da ita, shiru ya ɗanyi kamar mai tunani,

    sai jin voice nata yayi tana faɗin “yaya Aryan in tambaye’ka, ɗago ido yayi yana kallanta dan bai ma san ta dawo ɗakin ba, mamaki ne ya kama shi wai wan nan wace iriyar yarinya che yanzu nan fa take kuka a nan wai daga fitan ta palo ta dawo shike nan takoma fara’ar ta, jin yayi shiru yasa diyana sake chewa “yaya Aryan kasan me nake son tambayar ka bata jira amsar shi ba, ta chigaba da chewa, mata ma suna aikin soja ne? Tsaki Aryan yaja yana kawar da kansa gefe, dan ya lura in ya biyewa diyana zata chaza masa ƙwaƙwalwa “ke ban sani ba tashi ma ki tafi ɗaki yayi maganar da ɗan tsawa, miƙewa tayi da kyar ta kama hanyar fita, har ta kai bakin kofa sai kuma ta juyo karaf suka haɗa ido dan kuwa ita yake kallo, a shagwaɓe tace “yaya Aryan to pls ka faɗa min mana idan mata na aikin soja nima zan shiga ne dan Allah ina san riƙe bin diga kuma kayan sojoji na burgeni, ido kawai ya zuba mata ba tare daya bata amsa ba, ganin bai da niyar magana yasa ta fara bubbuga kafa ta turo baki tana yarfe hannu tafara magana “dan Allah yaya Aryan ka faɗa min kaji kodai zaka bani naka kayan sojojin da bindigar kane nasa nima, kallan ta kawai yake dan ya kasa magana tunani yake wai anya wan nan mutunche yarinya bata da tsoro ko kaɗan jiba yadda take min magana, “yaya Aryan na tafi tun,da bazaka faɗa min ba bari naje na tambayi wan chan mai kama da hiyana, yama sunan shi wan nan da baya dariyan nan, tayi maganar tana ɗaga kai sama kamar mai tunani, jin ta ambachi zataje ta tambayi DON ne yasa Aryan saurin chewa “mata basa aikin soja sai dai susa uniform ɗin mazajen su, wai bakin che kema soja zaki Aura ba, da sauri ta gyraɗa masa kai alamar eh “to kibari idan kin Auri sojan sai ki rinƙa saka uniform nashi, “to shike nan natafi ta karisa maganar tana ficewa daga ɗakin, girgiza kai Aryan yayi yana faɗin “da kinje kin tambayi DON kuwa da baki sake yiwa kowa magana a gidan nan ba, dan ina da tabbachi hakoran ki ko ɗaya ba zai rage a wan nan ɗan bakin surutun ba, wai yarinya’ne ba zaka ga baki ba sai magana, yayi maganar yana karisa hayewa saman gadon sa, ya kwanta tare da lunshe ido yana sauke ajiyar zuchiya.

    YOLA

    almost 30mnt inna na kwanche takasa miƙewa sai nishi take da kyar da kyar, a wan nan yanayin bokan nata ya shigo ya same ta hannunsa riƙe da wata bakar kwarya mai ɗauke da wani jan ruwa a chiki, kanta ya ɗago ya kafa mata kwaryan a baki yafara ɗura mata maganin, bashi tafara ha’ɗiyewa sai da ta shanye tas san nan yasaki kanta, ya miƙe ya fita ya koma wajen tsafe tsafen sa ya zauna jim kaɗan, sai ga Inna tafito da kwarin ta, tazo gaban sa ta zauna tana faɗin “zan iya tafiya, wani mahaukachin dariya yayi ha,ha,ha, kafin yace “eh ammafa gidawo bayan sati ɗaya dan kiji saka makon aikin ki “to tache tare da miƙewa tanufi hanyar fita har ta kai bakin kogon zata fita sai kuma dai ta juyo tace “zan iya zuwa anjima musake yin abun da mukayi ɗazun, wani dariyar mugun ta yayi a zuchiyar sa yana faɗin aiki ya fara kamaki ke nan abu yayi kyau kinshigo hannu, a fili kuwa che’mata yayi “eh idan kina soma yanzu ma ai sai muchi gaba, da sauri ta juyo ta nufoshi tana faɗin “eh ina so, sake kwashewa yayi da dariyar mugun ta kafin yace “to shiga chiki ina zuwa, tun bai karisa maganar ba ta shige chikin ɗan kewayayyen wajen nashi, ta chire mayafinta ta haye kan yar figaggi yar katifar nashi,

    ba jimawa shima ya shigo zindir babu kaya ajikin sa hayewa kanta yayi sai wani faman murmushi take, shima murmushi yake sai dai shi na mugunta yake, chire mata kaya yayi yafara aiki, awan nan karon ma sosai ya nemeta gaba da baya sai dai bata ji zafi kamar na ɗazun ba hakan kuma ya samo asali ne, saboda maganin daya bata, awan nan karon tare suka murji juna sai wani nishi suke dukkan su biyu,

    Bayan sun gama shike ayan sune ya kwanta a gefenta yana mai da numfashi, itama sai wani mai da numfashi take, sai misalin karfe 7 na dare Inna ta koma gida sai farinchiki da murna take tana faɗin “gobema komawa zanyi wlh irin wan nan abu haka, ko sallar mangariba babu bare issha batare da tayi wanka ba ta haye yar katifar chiyawar’ta ba jimawa barchi ya ɗauke ta ko abinchi bata nema ba.

    KANO

    Misalin karfe 8 na dare gaba ɗaya family Abba sun haɗu a palo ban da DON shi bai fito ba, gyaran murya Abba yayi, yana kallon diyana dake zaune kusa da Aunty farida tana chin ayaba, yafara Magana “naji duk abun daya faru zuwan ku Yola, sorry my daughter kinji ba zaku sake zuwa garin ba inshaa Allah. Shiru ya ɗanyi kafin ya dawo da kallan sa Abba yayi kan Ahmad dake zaune kusa da Aiman, ya chigaba da Magana, “kai Ahmad kashirya daga gobe zaka fara hawa kujerer mulki gobe misalin karfe 9 zaka fita fada,waro ido waje Ahmad yayi yana san magana, amma ba hali dan idan Abba yana magana ba wan da ya isa ya tanka har sai ya gama,

    ɗaure fuska Abba yayi ganin yadda Ahmad ya zaro ido, dawo da kallansa kan Khalid yayi ya chigaba da magana, “kai kuma baba jibi Monday su Zahra zasu koma school kaje kamusu abun daya dace,

    Shiru Abba ya ɗanyi yana mai da numfashi san nan ya ɗora dachewa sai magana ta gaba kuma, ke hiyana tashi kije ki kiramin Safras, ya karisa maganar yana kallan hiyana, mikewa hiyana tayi kamar zatayi kuka jikinta har ɓari yaƙe saboda tsoron DON, shi kanshi Abba ya lura da yanayin data shiga, amma dole ne taje ta kira masa DON dan haka sai ya shareta, tafiya take kamar wadda kyau ya fashiwa a ciki ta fito daga palon

    Part na DON ta nufa tun a bakin kofar palon kasa take sallama, amma shiru babu wadda ya amsa chikin palon ta shiga babu kowa, a’hakali kamar bata son taka kasa tanufi stair ɗin, ta haura a bakin kofar palon daman ta tsaya tasake, doka sallama, nan ma shiru, hannu tasa a hankali ta tura kofar palon, ta shiga shiru shima babu kowa, kofar betroom ɗinsa ta nufa a bakin kofar ta tsaya da murya kamar mai shirin fashewa da kuka tayi sallama shiru bai amsa ba, sake sallama tayi nan ma shiru bai amsa ba, shiru tayi tana tunanin, yanzu ya zanyi, in koma palo ne to idan ma na koma palo in che me, ban isa in che baya nan ba tun da sun san yana gida, to idan kuma na koma na chewa Abba na faɗa masa, kuma bayan ban faɗaba zasuji shiru bai zoba kar Abba ya masa faɗa shikuma ya hukun tani, idan kuma nashiga nan ma zai iya hukun tani, Almost 30 hiyana na tsaye tana tunanin mafita data ga dai tsayuwar ba abun da zai tsinana mata sai tayi shahada ta tura kofar betroom ɗin a hankali ta shiga da sallama.

    subhanallah kara waro blue eyes nata tayi sosai a kansa, kwanche yake saman katafaren gadon sa idon sa a lunshe kamar barchi yake, daga shi sai short a jikin sa faffaɗar kirjin nan nasa awaje,ga wani bakin gashi mai kyan gaske kwanche a kan kirjin, lallausan bakin gashin kan nan nasa kuwa duk ya bar bazu a kan face ɗin sa ya rufe masa ido, zubawa ɗamtsen hannun sa ido hiyana tayi tana kallo kara waro blue eyes nata tayi da kyau a chikin zuchiyar ta yana faɗin “kai ai wan iri hannun na sa ai ya kusa chin yata, tab idan ya bugeka da hannun nan sai ka mutu, dawo da kallonta tayi kan faffaɗar kirjin sa, gashin dake kwanche a wajen kawai take kallo tana faɗin, wow a chikin zuchiyarta, Allah ka bani miji mai kashi a kirji nima yana min kyau, sauko da blue eyes nata tayi izuwa kan chin yoyin’sa, wani bakin gashi ne mai kyau da sheki kwanche a kan chinyar nasa, sosai ta zuba masa ido tana kare masa kallo from head to toe, tana yaba irin kyansa da kyan jikin sa, tayi nisa chikin tunani sai taga alamar ya ɗan motsa hannun sa, a ruɗe ta ja da baya ta koma jikin kofa, a tsorache tace “yaya Prince Abba na kiran ka, shiru bai amsa ba cikin tsoro ta sake mai mai ta maganar, batare daya buɗe ido ba ya furta “get out chikin tsawa, ai tun bai gama faɗeba tayi waje daman ita burinta kawai yaji sakon Abba, tun da yaji shike nan

    da gudu tabar ɓan garen nasa ta koma falon Abba, sai numfashi sama sama take, gaba ɗaya idon mutanen falon ya dawo kanta ban da Aryan da Fahad abin chin su kawai suke chi “sister lfy kike numfashi kamar wadda tayi gudu chewar Yusuf ya yayi maganar yana kallon face nata, ita kam Zahra ko ajikin ta dan tasan dalili, Abba ma yasan hakan zata iya faruwa yasan sai DON ya kore’ta, da gangan yake aika ta daman dan yasan duka dai DON bazan duketa ba tun da yamasa gargaɗi a kan haka, dawo da kallansa Abba yayi kan su Yusuf yayi yace “kai ina ruwan ku da ita zoki zauna ki chigaba da chin abinchi ki kinji my daughter, ɗaure fuska Aunty Amarya tayi dan taso jin me DON yawa hiyana take numfashi haka ko marin’ta yayi,

    Zama hiyana tazo tayi awajen da ta tashi ta ɗauki spoon a hankali tafara chin abinchin ta, shiru shiru DON bai zoba da har suka gama chin abinchin, Abba ya dubi Khalid rai a ɗan bace yace “kai baba tashi kaje ka chewa Safras nifa na haife shi ba shi ya haifeni ba da zai ajiye’ni ina jiran sa, Khalid na kokarin mikewa, sai ga DON ya shi go sanye chikin jallabiya fari, yana taku irin na jaruman maza, fuskar san nan kamar bai san menen dariya ba sai wani kakkau da kai yake, gaba ɗaya su Aunty Maryam kowa ya shiga taitayin sa, har da Aunty amaryan, kujerar dake fuskantar Abba yaje ya zauna da sauri kannen nasu suka fara ɗaga masa gaisuwa, bai ko kalli inda suke ba bare ya amsa musu gaisuwar sai ma kara ɗaure fuska da yayi, sai da suka gama gai suwar nasu sukayi shiru kowa ya nitsu suna sauraren suji abun da Abba zai che.

    A hankali DON ya buɗe ɗan karamin bakin nan nashi kamar bai san motsa lallausan lips nashi, ya fara gaishe da iyayen nasu, fiska ba yabo ba fallasa Abba ya amsa haka Aunty amarya da Ummi, Ammi kuwa ɗaure fuska tayi sosai kafin ta amsa masa,Shiru yayi san nan ya sun kuyar da kai, shiru palon yayi gaba ɗaya Abban ne ya katse musu shirun da chewa “Zahra kutashi kuba mu waje, tun bai kai karshen maganar ba Zahra hiyana diyana lamrat amrat suka miƙe suka bar palon,

    dawo da kallansa kan su DON Abba yayi yafara Magana “abun da yasa na taraku a nan shine, duk kanku lokachi yayi da zakuyi Aure, a sukwane DON Aryan Fahad haidar Aiman da kuma Ahmad suka ɗago kai a tare suna kallon Abba kamar zasuyi ihu musam man DON Aryan Fahad Aiman,su nasu ɓachin ran na da ban ne kamar wayan da aka chewa uban su ya mutu, Khalid Yusuf Umar kam ko ajikinsu, Aunty farida ma ɓata rai tayi sosai dan tasan wan nan maganar da Abba yayi ba karamin ɗagawa su DON hankali zai yiba, dan babu hakan a tsarin su, tafiso a barsu sunemi mata chikin nitsuwa, dan idan akache za’a tilasta musu wlh duk wadda aka aura musu tashiga uku,

    “No Abba No gaskiya kabar wan nan maganar ni babu mace a tsarin rayuwa kamin wani hukunchin dai amma banda batun mace pls Abba, chewar DON, ya karisa maganar chikin wata iriyar voice wadda da kajita kasan tsantsar kiyayyar macece a ranshi,ga fiskar nan kamar an aiko masa da sakon mutuwa, shiru Abba yayi ya zubawa DON ido har yakai karshen maganar tashi, shi kanshi Abba yasan chewa mawuya chin abune DON Aryan su yarda da batun Aure, domin babu hakan a tsarin da sukayi wa rayuwar su,shiyasa ma bai takura musu ba tsawon lokachi ya bar su, to amma yanzu yazama dole suyi Aure dan chika sunnan ma aiki, kuma yafi son su kawo matan da zasu Aura da kansu dan idan yace zai Aura musu zaɓin sane, yasan matan sun shiga uku

    sosai Abba yashiga tunani, gaskiya bai kamata nayiwa DON dole ba idan yayi haka tofa akoi babban matsala tsabar tsanar mace dayayi ne jiba agaban kannen sa yau ya buɗe murya haka yana magana har da chewa sorry mutumin da magana wahala yi take masa, lallai bai kamata na takura masa ba idan kuwa nayi haka zanyi dana sani mai girma, addu’a kawai ya kamata na masa.

    Ganin Abba yayi shirune yasa Aryan chewa “Abba pls kabar maganar auren nan wlh ba muso babu mace a tsarin rayuwar mu pls my Abba kaji ya karisa maganar yana ɗan dafa hannun Abba, chikin fushi Ammi tace “babu mace a tsarin rayuwar ku ko, to ku chiremu muma a tsarin rayuwar ku tunda muma matane tana kaiwa nan ta miƙe ta fiche daga palon chikin fushi da ɓachin rai, dafe kai DON yayi a zuchiyar’sa yana faɗin jiya nayi ɗaya yau kuma na biyu am so so sorry Ammi ammafa aure kam ba zan yi ba gaskiya sai dai duk abun da zai faru ya faru, miƙewa Ummi tayi itama tana faɗin “ranka ya daɗe idan kun gama zaman ka kira malam mai rukiyya yazo ya musu dan ga dukkan alamu aljana che ta auri ƴa’ƴan nan, a sukwane suka juyo gaba ɗayan su suna kallon Ummi, ɗaure fuska tayi kafin ta juya ta fice daga palon, kallan Aunty amarya Abba yayi tun bai yi magana ba ta miƙe ta fita tana ɓata rai dan taso jin me Abba zai che musu wani amsa zai basu, “Maryam salma mardiya kutashi ku bamu waje,chewar Abba yayi maganar yana kallon su, jiki ba kwari suka miƙe suka fita.

    Palon ya rage daga Aunty farida, DON Khalid Yusuf Aryan Aiman Ahmad Umar haihar da kuma Fahad

    Dawo da kallansa Abba yayi kansu DON ko’wannen su sai faman ɗaure fuska yake sai wani chi chijewa suke, ɗan gyaran murya Abba yayi kafin yafara Magana “ke farida na barki ne saboda bakin ku ɗaya dasu ke che sirrin su basu taɓayin wani abu batare da kin sani ba dan haka ku saurareni, “ni bazan tilas ta muku kuyi Aure ba, wani dauyayyar ajiya zuchiya DON Aryan Fahad, suka sauke a tare, har da ɗan sakin fuska, ganin hakan yasa Abba murmushi yachi gaba da chewa “bazan takura muku kuyi abun da baku so ba, saboda farin cikin ku nake bukata, amma dai burina shine naga kunyi aure kun haifamin jikoki shine babba burina a duniya kuma farinchiki na, ni ina san farin chikin ku ban sani ba ko kuma kunason nawa, ban sani ba ko zaku iya chika min burina tun ina raye, ɗan dakatawa Abba yayi yana satar kallon fuskokin su,a ransa yana faɗin nina haifeku ai baku kuka haifeni ba a chikin ruwan sanyi zanyi maganin ku, nan take fuskar DON da Aryan ya sauya sosai dan sun gano tarko Abba ke neman yima’su da kalaman sa, Fahad kuwa sai murna yake Abba bazai yimasu dole suyi aure ba, shiru Aiman yayi ya ɗora hannu a gemun sa yana kallon kasa yana nazarin magan ganun Abba, Khalid da Yusuf kuwa ɓata rai sukayi sosai dan su gaskiya Aure suke so kuma suna da matan da zasu aura, amma DON da Aryan suna neman watsa musu farin chiki, Aunty farida kuwa jikinta ne yayi sanyi sosai jin kalaman Abba, tabbas Abba na da gaskiya yakama suyi aure amma banso Abba yabi musu ta wan nan sigar ba da an bi a hankali an bisu da addu’a inshaa Allah komai zai tafi dai dai

    Ganin sunyi shiru kowan nan su yatafi tunani yasa Abba chewa, “nifa ban takura’wa kowa daga chikin kuba, burina da kuma farinchiki na kawai na faɗa muku, kuma ban che dole sai kun chika min burina ba koma me ni zan zama mai chika muku burin,kuma mai saku farin chiki a ko da yaushe, kuje ku zauna kunitsu kuyi tunani yana kai karshen maganar yamike ya shige betroom ɗin sa,

    chikin fushi da ɓachin rai DON ya furta “never Abba aure fa, wlh I cannot do it I cannot do it gaskiya bazan iya chika maka wan nan burin nakaba, a fusache ya miƙe ya bar palon, da sauri Aryan ya miƙe zai bi bayan sa “ina zakaje Aryan Aunty farida ta tambaya, “Aunty farida baki ganin ɗan uwana yana chikin ɓachin rai ne ai bazan iya zama ba, yana kai karshen maganar batare daya jira amsar taba ya fiche da sauri, a fusache Aiman ma ya mike yaja tsaki yana faɗin “nima dai ba zan iya chika’wa Abba wan nan burin na shi ba sai dai in ku zaku iya bani da lokachin mace yanzu, yana kai karshen maganar ya juya da, sauri ya nufi hanyar fita dan bai dan Aunty farida ta. dakatar da shi

    Girgiza kai Khalid yayi kafin yache “gaskiya a wan nan gaɓar ya kamata mu chika wa Abba burinsa, domin duk wani abun da mukeso yana mana yanzu ki duba Aunty babba saboda bama son mulkin nan, Abba ya hakura da bamu mulkin duk dan muyi farin chiki, tun muna yara har muka girma har izuwa yanzu bamu taɓa chewa Abba muna bukatar abu kuma yaki yi mana ba, to meyasa mu kuma zamu rinƙa kin abun da yake so, yache zai bamu mulki munki ya hakura yanzu kuma kin fa ji auren mu shine kaɗai burin daya rage masa a duniya da yake san mu chika masa,to why bazamu chika masa burin sa ba. ɗan daka tawa Khalid yayi da magana yana mai da numfashi “Kana da gaskiya Khalid amma a hankali Ya kamata abi abun tun da kaga dukkan ku ba soyayya kuka taɓayiba babu wata alaka da ta taɓa haɗaku da wata mace idan ba mu yan uwan ku na gida ba, SO kaga abune mawuyache lokachi ɗaya a che zaayi muku maganar aure garama kai dasu Yusuf da sauki, amma kafini sanin halin DON da Aryan, basu san wani abu wai shi soyayya ba, bai da che amusu zuwa ɗaya haka ba a hankali za’a shawo kansu, yanzu dai zanje in same’su dan musan abunyi tana kai karshen maganar ta miƙe tanufi hanyar fita, shiru Khalid yayi yana tunani, miƙewa Fahad ma yayi yabi bayan Aunty farida, haidar da umar ma suƙa miƙe suka fita suka nufi ɓan garensu palon ya rage Khalid Ahmad Yusuf.

    *💫STAR LADY💫*

    👑UK Writers👑

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star Lady*

     

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 18

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 18

    Episode 18*

     

    Hannu Aunty Maryam ta ɗaga, har zata kai mata mari sai kuma ta dakata ” zuba mata ido Aunty farida tayi sosai,” me ya dakatar dake kimare’ni mana, ae kin girmane shiyasa har kike tunanin ramawa, kimare’ni nace koh tayi maganar a fusache” dan Allah Aunty farida kifita a ɗakin nan “hmmmm wlh Maryam bansan baki da hankaliba sai wan ‘nan karan,to kisani idan su Abba suka dawo kinemi abun da zaki kare kanki,dan kuwa babu wanda zaiga abun da kika’wa yaran nan ya kyale’ki, naso hukun taki da kai na, amma zan bari, ƴa’ƴayn Aisha dakike ikrari su hukuntaki, dan awan nan gaɓar su kikataɓa, “tana kaiwa nan tamike tafice daga ɗakin ” ganin Aunty farida tafita, yasa Aunty Maryam, tayi kwafa tana faɗin to inaruwan’ki inba shisshigiba duk chikin ƴa’ƴan Aisha akoi wanda ya isa yamin hukunci’ne, yara kuma na buga innasake samun dama’ma bugun zanyi, dan nayi alkawarin rabasu da gidan nan tunda Aunty amarya bata san’su, juyawa tai ta gyara kwanchiyar sai surutai take

    Da sallama ta dawo palon Ummi, duk datasan ba kowa, kai tsaye ɗakin’ta tawuce, tasamu diyana da amrat sunyi barchi ,”kayan jikin’ta ta chire san nan nufi toilet, after 45 mnt tafi ɗaure da towel da’alama wanka tayi, trolley ta tajawo, ta buɗe ta ɗauki kayan barchi, masu kyau da tsada farare tas masu laushin gaske, sai kamshi kayan keyi yasha turarukkan maiduguri,san nan ta ɗauko mayukan’ta masu kanshi da tsada sai dataɓi ko’ina na jikinta ta shafeshi da mai san nan,tasanya kayan barchi ta’sake feshe jikinta da turare sai kamshi take kamar anyi ɓarin turare a jikinta, “ta mai da mai da tureren chikin trolley ɗin ta rufe ta mai’dashi wajen zamansa, tadawo kan gadon ta gyarawa amrat kwan chiya, san nan ta kwanta a gefensu, tare dayin adduar barchi asuba ta gari

    Yau yakama Wednesday tun safe Aunty farida ta shirya chikin tsadaddiyar lace mai Bala’i kyau baki, da ratsin ja ta zuba sarkan gold a wuya da hannunta, ta jera wasu tsadaddun zobuna uku na gold a hannunta, tayi simple make up bakaramin kyau tayiba sai kamshi take zubawa kamar anyi ɓarin turare ajikinta, tasa plat shoe ja da mayafi ja san nan tayiwa yan matan Ammi kwalliya sosai, “diyana hiyana Zahra tasasu sukasa wani haɗaɗɗen duguwar riga mai kyan gaske, da pink colour an masa kwalliya da wasu duwatsu golden colour, bakaramin kyau sukayiba amrat da lamrat kuwa sun sa wandon jeans baki da yellow t-shirt,” gaba ɗayan’su ta ɗaure musu gashin nasu a tsakiyar kai ta zuba musu jelar a baya, sai dai ita hiyana har yanzu ba a chire bandejin dake goshinta’ba “Aunty farida ina zamuje kika mana kwalliya haka diyana ta tambaya tana kokarin gyara mayafin rigar” wajen lalle da gyaranjiki zan kai ku, da naso namuku lalle da kaina to amma nayi tu nanin gara na kai’ku ae muku har da gyaran jiki ” tsalle diyana tayi ta rungume Aunty farida tana faɗin mungode sosai” to sakeni mutafi kar lokachi ya kure mana ” to diyana tafaɗi tare da sakin Aunty farida” rike hannunta Aunty farida tayi sukayi gaba, su Zahra suka rufa musu baya,
    suna fita harabar gd da gudu Shahram yanufo’su ” ɗan dukar da kai yayi ya gaishe da Aunty farida chikin harchen turanci” bayan yagama gaishe da Aunty farida,su Zahra ma suka gaidashi ” bayan yagama amsa gaisuwar’su Zahra ne, ya tambayi Aunty farida ko zai iya kaisu inda zasuje da kanshi ” Aunty farida tace badamuwa ya fito da family car dan tafisan sutafi dukkan’su a mota ɗaya ” da gudu yajuya yanufi parking space na gidan,” har gabansu yazo yayi parking,”zai fito yabuɗe’musu ” Aunty farida ta ɗaga masa hannu, alamar yabari zasu ɓuɗe da kansu ” da Kanta tasa hannu ta buɗe kofar motar,” a nitse suka fara shiga sai da suka gama shiga san nan tabi bayansu ” da gudu gaske Shahram yaja motar yana zuwa bakin gate ya ɗan rage gudun motar nan’take securitys dake wajen suka wangale masa gate ɗin da’gudu ya danna hanchin motar waje, gudu sosai, Shahram ke shararawa a kan mikakkiyar titi ” ranki ya daɗe ina muka nufa yayi tambayar yana kokarin fita daga asalin babban gate ɗin gidan ” A&S muka nufa tabashi amsa ta kokarin picking call ɗin daya shigo wayarta ” miƙar hanya Shahram yayi sosai yake sharara gudu
    Yana hawa kan titi dazata sadashi da gate ɗin A&S ya rage gudun motar,horn ɗaya yayi wani dattijo ya taso ya wangale masu gate ɗin da’alama shine mai gaɗin ” A nitse Shahram ya danna hanchin motar chiki, parking space na wajen yanufa yana kashe motar yafito da sauri ya buɗewa Aunty farida” a hankali ta zuro kafafunta waje ta fito “su hiyana ma sukabi bayanta hannu diyana tariƙe suka nufi chiki ” wani haɗadɗen wajen gyaran jikine da lalle da kitso, wajen ya tsaru sosai iya matane kaɗai ke shiga koka’kawo wani naka sai dai katsaya awajen zaman baki, suna da ma aikata sosai inkaje basai kabi layiba, ” hannu bibbiyu a ka tarbi su Aunty farida ” chikin ƙankanin lokachi aka fara gyara musu jiki

    YOLA

    Da gudu inna tafito daga ɗaki, tayi kichin, da sauri ta sauke tukunyar ɗumamen, dake kan wutar abinchin har yayi bakin’kirin, zama tayi dirshan awajen kamar zatayi kuka tafara surutai,”oh ni habiba yanzu me zanchi wayyo Allah gashi ba azumi nake ba dole naje nasake ɗaukar 1k a chikin kuɗin nan na sawo masara nazo na surfa na niƙa nayi wani tuwon, mikewa tayi ta jawo itacen wutar ta kashe san nan ta wuche ɗaki ta ɗaga katifar chiyawar’ta ta irga kuɗin taga saura 6k ta zari 1k ta mai da sauran kasan katifar ta ɗau mayafinta tafuto tanufi waje dan zuwa yin chefene

    KANO

    A bangaren’su Aunty farida kuwa sai gyaranjiki ake musu an gama yiwa diyana da zahra da amrat bakaramin kyau sukayiba, kamar wasu larabawa haka suka zama daman, dukkansu fararene tas jikinsu sai kyalli yake gwanin ban sha’awa,
    yanzu aka fara yiwa lamrat da hiyana kuma,”Aunty farida kam already tariga da tayi nata a Maiduguri kafin tazo, ” yanzu lalle za’afara yiwa diyana da zahra ” sai zolayar’su Aunty farida keyi ” my diyana kingan’ki kuwa kamar wata sarauniyar kyau fa kinga fatar nan taki kuwa saikace na jariri gaskiya dole..bata karisaba, wayar’ta tafara ƙara alamar shigowar ƙira da sauri ta chiro wayar kiran iphone 14 daga jakarta ” laaa Aunty farida yaushe kika chanza waya chewar diyana ” last week tayi maganar tana kokarin picking call ɗin ” hello my bro ykk “lfy lau my lovely Aunty ykk y gd ” lfy lau alhamdulillah gamu nan ma awajen gyaran jiki ae ina Prince ” baya nan yayi tafiyar sirri ” murmushi tayi kafin tace kai Aryan dayayi tafiyar sirri nasan yace karka faɗawa kowa, shine kuma kafaɗamin ” murmushi kaɗan shima ma yayi san nan yace ae ke da kankima sirrinmu’ce ko bazamu faɗawa kowaba yazama dole ke kisani, ” inasu Khalid to ” suntafi kasuwa ” to yau kuma da kansu sukaje kasuwar ” eh wlh nima dai na ɗanyi mamaki ” kodai Zahra yaje yiwa tsaraba ” to waya sanin musu zaki gane kan Khalid da Yusuf ne ” to shike nan bari innakima gd mayi magana ” ok ya’jikin yaran nan ” da sauki sosai gasu nan ma ana musu lalle ” lalle kuma ya tambaya yana taɓe baki ” eh lalle mana kona baku ku gaisane ” eh to dai kibari sai kun koma gd zaifi tunda yanzu kince lalle ake musu ” ok to shike nan sai munyi waya,” ta karisa maganar tana chire wayar daga kunnen’ta ” katse kiran tayi tamaida wayar chikin jaka san nan ta ɗago tana kallan’su diyana da akewa lalle ” wow my sister’s kunganku kuwa kaman wasu amare gaskiaya idan Ammi suka dawo bazasu gane kuba wow ” diyana dai baki yaki rufuwa sai murmushi take ” Zahra kuma hannu tasa ta rufe fuska tana dariya ” bayan angama yiwa Zahra da diyana lalle ” aka fara yiwa amrat da lamrat

    SAUDIA

    Ammi che kwanche a kan chiyar Abba a ɗakinsu tana shafa fuskar’sa yayinda shikuma yake shafa gashin kanta ” ranka yadaɗe nayi kewar yanmata’na sosai, ” hannu Abba yasa yaɗan ja dogon hanchin nan nata yana faɗin to kwana nawa yarage mukoma, ɗazun ma munyi waya da farida take chimin zasuje wajen gyaran jiki ” Allah sarki feeda baiwar Allah, Allah yamata albarka na mata adduar samun aihuwa sosai jiya danaje masallaci ” kullun sainayiwa farida adduar bama ita kaɗaiba har da maryam da mardiya ba garama faridan tasamu ɗaya ba sauran kam aiko ɗayan basu samuba,chewar Abba ” wlh tausayi suke bani tayi maganar tana kokarin mikewa ” da sauri Abba ya rikota yana faɗin ina zakije kuma ” so nake naje nayi magana da yaron nan ” kallan chikin kwayar idonta sosai Abba yayi san nan yace wani yaro kuma, da gangan yamata tabayar, dan yanasan yau yaji takira sunan Safras da bakinta ” yaron Ummin nan mana tabashi amsa tana mai kawar da kai gefe ” to shi yaron bai da sunane ” juyo da kallan’ta tayi kansa san nan tasa hannu taja gemunsa chikin wasa take faɗin, bazadai kaji su nan a baki’naba ” murmushi yayi yana faɗin to idan inasan inji kumafa ” sai na kira maka mana ae duk abun da kakeso matikar bai saɓawa Allah da manzon’saba dole namaka ” rungumeta Abba yayi chikin farinchiki yafara magana ina kaunarki Aisha’ta nima bazan saki yin abun da baki so ba, tunda ba kyasan kiran su nan bazan saki kiraba aje a yaron kinji ” chusa kanta tayi kirjin’sa tana faɗin nima ae ina kaunarka sosaima ” nasani Aisha nasan kina kauna’na sosai nasani wlh ” to shike nan kamin izzini naje na dubo’shi dan jiya banganshi’ba kwata kwata kuma inasan magana dashi a kan yaran nan ” aa Aish ba yanzuba dan yanzu bansan ki raba jikinki danawa kibari sai anjima ” to kawai Ammi tace takara shigewa jikinsa ta lafe

    Da sallama Khalid da Yusuf suka shigo palon hannun’su ɗauke da manya manyan jakun’kunar sayayya Aiman da Ahmad dake zaune saman Sofa suka amsa sallamar suna binsu da kallo ” daga ina kuke haka Aiman ya tambaya yana ɗaure fuska ” to dakake ɗaure mana fuska, saiyasa muji tsoranka mufaɗa’maka inda mukaje ne chewar Khalid ” dariya Ahmad yayi yana faɗin nidai babu ruwana ” tsaki Khalid yaja yawuce yanufi hanyar ɗakin’sa ” da sauri Yusuf ma yabi bayansa ” miƙewa Aiman yayi yana faɗin lokachi yayi da zan gano mekuke kullawa kuma sai nayi maganin’ku ” Ahmad kam binsa kawai yake da ido har yafice daga palon ,yana ganin Aiman yafita ” ya kwashe da dariya, chikin dariya yake magana wlh nidai nawa ido kawai zanga wan nan game ɗin yasake kwashewa da dariya yana mai kwanchiya a kan kujerar

    NIGERIA

    Sai milalin karfe 4:50 aka gama yiwasu hiyana gyaran jiki da lalle sunyi kyau sosai kamar su’sukayi kansu yaran nan gawani kitso guda biyu da aka musu a gefe da gefen kunnen’su ansa manya manyan bit an zuboshi ta gaba har kan chikinsu tsawon gashin, sauran gashin an ɗaure musu a tsakiyar kai,anzuba jelar gashin ta baya har gadan bayan’su, musammanba hiyana da diyana gashinsu yafi tsawo da baki ga tsantsi, ba karamin kyau sukayiba kamar, ƴa’ƴan larabawa ” bill akayiwa Aunty farida ta biya san nan suka nufi waje ”
    Shahram dake zaune chikin mota,yana ganinsu ya fito da sauri yana faɗin wellcome ma ” da murmushi a fuskarta tace sorry Shahram for keeping U waiting ” buɗemusu kofar motar kawai yayi batare daya sake maganaba, suna shiga yarufe motar yashiga gaba yabawa motar wuta sai bakin gate mai gaɗin ya wangale masa gate ɗin ya danna hanchin motar waje da gudun gaske ya miƙi titi, gudu yake shararawa sosai, sai daya kusa isa bakin babban gate na gida tukun ya ɗan ragewa motar gudu horn ɗaya yayi nan take security suka wangale masa gate ɗin a nitse ya kutsa chikin gidan, kai tsaye parking space yanufa ,” yana kashe motar yafito da sauri ya buɗe musu ” fitowa sukayi gaba ɗayan’su suna faɗin thank U uncle ” Aunty farida ta rike hannun diyana sukayi chikin gd ” da sallama suka shigo palon ” da sauri nurse nasu dake zaune saman Sofa tamike tana faɗin ina kukaje natashi barchi ban gankuba, ” wajen gyaran jiki mukaje diyana tabata amsa ” dukawa tayi kasa ta gaida Aunty farida ” da fara’a ta amsa san nan tanufi ɗaki dan yin wanka tana faɗin sister’s kuje kuyi wanka kozo kubiya bashin sallar Azhar da la asar dake kanku ” har suna haɗa baki wajen chewa to san nan suka nufi ɗakin Aunty mardiya

    yau saura kwana ɗaya sallah sai shirye shiryen tarban su Abba ake, manya manya shanu 4 aka’yanka da raguna 5 ” hayar masu soya nama Aunty farida ta ɗaukoh mata’ne masu jini ajiki masu ji da karfi da lfy, san nan tasa aka fitar da manya manyan gas daga store, aiki ake babu kama hannun yaro ,gamasu yin chin chin a gefe, gamasu donut dubula alkaki da dai sauransu, Aunty farida yau bata zauna ba sai hidima take da jama’a ” Aunty Maryam kuwa tana ɗaki kwanche abunta

    Misalin karfe 1:50 diyana na zaune a ɗakin Aunty farida tadage sai make up take, wayar Aunty farida dake kan gado yafara ringing,” da sauri ta ajiye jan bakin dake hannuta tanufi wayar, ɗaukar wayar tayi zatayi waje dan takaiwa Aunty faridan, sai taga pic na Aryan ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar, sanye yake da kayan sojoji baƙaramin kyau yayiba fuskar nan tashi kamar bai taɓa sanin me dariya’ba,” da sauri tayi picking call ɗin ” daga ɗayan ɓangaren Aryan yace,”hello my lovely Aunty ” ba itabace yaya Aryan ni che ina wuni ” lfy lau y jikin naki ” nasamu sauki hiyana che kawai tarage bata samu sauki’ba ” subhanallah me ke damunta ina nurse naku ” nurse ta koma jiya wai zataje tayi shirye shirye sallah ” to meke damun hiyanar ” chiwon kai da jiri ” ok jibi zamu dawo ae sai na dubata amma duk da haka zansa a kawo mata magani ” to bari na kaiwa Aunty farida wayar ” daman kinsan zaki kai mata wayar’ne kikayi picking call ɗin ” eh ae nayine daman dan na gaisheka tun da mun daɗe bamuyi magana’ba ” to ae kece kika manta dani shiyasa ” dariya diyana ta ɗanyi kafin tace, ni ban manta da kaiba dan bani da waya’ne Allah dana kiraka ” wani ajiyar zuchiya ya sauke”to amma kina kewata kuwa ” eh mana ina kewar’ku dukkan’ku ” ok to shike nan ki ajiye wayar kawai anjima idan Aunty farida tazo ta kirani dan naji Abba na nemana ” to kawai tace tare da chire wayar a kunnen’ta ta mayar kan gadan ta ajiye,”takoma gaban mirro tachigaba da kwalliyar’ta

    YOLA

    Inna na ɗaki kwanche a kan yar gadon chiyawar’ta taji sallama daga kofar gd mikewa tayi daga kwanchiyar datake tana amsa sallamar,”ɗaukar mayafinta tayi tanufi waje ” ganin bello ne ke sallamar yasa inna ta ɗaure fuska sosai tafara magana to yau kuma dame kazo funafiki ” ina wuni inna ” daban wuniba zaka ganni’ne ” to Allah yabaki hakuri daman naga gobe sallane shine nache bari na sauke hakkin ma kwabtaka na kawo miki wan nan,”yayi maganar tare da ajiye wa inna gaji guda uku a gaban’ta, batare daya jira amsar’taba yayi wuce warsa gidan’su ” da mamaki inna ke kallansa har yashiga gida, duƙawa tayi ta ɗauki kajin tayi chikin gida,” a tsakar gida ta ajiyesu san nan ta ɗaukoh wuƙa tayanke igiyar da aka haɗesu aka ɗaure, ta samu wani igiya ta ɗauresu ɗai ɗai ta kaisu kichin tafito takoma ɗaki ta kwanta,” tana kwanchiya babu jimawa buba yashigo gidan da sallama yana ɗingisa kafa da sanda ” tana daga chikin ɗaki ta amsa masa san nan tace yashigo ” shiga ɗakin yayi hannunsa riƙe da buhu ” lfy buba ina zakaje da buhun nan ” bappa’ne yace na kawo miki, shin kaface wai kiyi girkin sallah ” da murna inna tamike zaune wayyo Allah kacewa bappa ngd sosai Allah yaƙara arziƙi ” amin yafaɗa tare da ajiye mata buhun ya juya yafita ” buɗe buhun tayi taga shin kaface mai kyau da murna ta tura buhun bayan kyaure ta ɓuye

    KANO

    Misalin karfe 7 na dare, sun haɗu a palon Abba suna buɗa baki ” kai my diyana sarkin san kwalliya chewar Aunty farida tayi magabar tana ɗan jan kumatun,diyanar ” ae kwalliyar dazanyi gobema sai yafi wan nan kyau ” Allah ko ae haka akesan mace takasan’ce mai tsabta da kwalliya ” Zahra tace Aunty farida ae muma munayi ” eh kunayi amma my diyana tafikuyi sosai, kuma kuƙara dagewa ” to shike nan zamu rinƙayi sosai ” ok to kuchi abinchin’ku dawuri muje mu kwanta dan kunga gobe sallah zamu tashi da wuri ” har suna haɗa baki wajen chewa toh ” shiru kakejin palon babu mai magana sai paran spoon kawai zakaji ” sallama sukaji anyi a bakin kofar palon ” amsa sallamar Aunty farida tayi san nan taba da izinin shigowa ” ɗaya daga chikin security bakin gate ne,har ƙatsa ya duƙa ya gaida Aunty farida ” ta amsa tare da tambayar’sa ko lfy ” eh lfy wani likitane yakawo saƙon nan wai inji oga yace abawa hiyana ” ok to ajiye a saman table ɗin gaban kan nan ” mikewa yayi ya ajiye sakon san nan yanufi waje
    Bayan sun gama chin abinchine suka mike zasu tafi ɗaki, Aunty farida tasa hannu ta ɗauki sakon tana faɗin muje ɗaki kisha maganin hiyana ” toh kawai hiyana tace, san nan suka nufi waje ” sai da Aunty farida ta tabbatar hiyana tasha magani san nan takama hannun diyana da amrat suka nufi,dakinta, a gurguje sukayi wanke sukayi sallar issha suka kwanta asuba tagari

    Tunda sukayi sallar asuba yau basu mai da barchiba ” diyana tun karfe 7 take gaban mirro ta goga wan nan ta fenta wan nan ba karya tayi kyau sosai tamkar zataje gasar sarauniyar kyau ” da sallama Aunty farida tashigo ɗakin tana waya da Aryan, wow my diyana kin ganki kuwa kamar wata sarauniya ” dariya diyana tayi tana faɗin ngd Aunty farida ” dawa kike magana kuma Aryan ya tambaya ” hmm nina mantama muna waya wlh, kyan my diyana ne ya rikitani ” shiru ya ɗanyi kamar mai tunani chan kuma sai yace to ɗauke’ta hoto ki turomin naga kyan daya rikitakin ” ae kuwa kai ma idan kagani sai ka rikiche ” to shike nan turomin ɗin dai kekam ” ok tace tare da chire wayar daga kunnen’ta ta katse kiran” tadubi diyana tace to tashi kisa kaya namiki hoto ” yauwa Aunty farida Allah yamiki albarka daman inasan inje in anshi wayar Aunty Zahra nazo nayi hotan, tayi maganar tana kokarin mikewa..✍️

     

     

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

     

     

     

     

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 15

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 15

    Episode 15*

    Bayan sungama shiryawa kamsu abubuwar dasuke buƙata na buɗa baki nan take masu aikima suka fara shigo da kulolin abinchi suna jerawa a kan table ɗin komawa ɗaki sukayi ɗaya bayan ɗaya sukayi wanka suka ɗauro alwalla hiyana diyana Zahra dogayen riguna na material sukasa maroon colour ” lamrat da amrat kuwa riga da sket na atamfa suka sa kai tsaye palon mai martaba suka nufa danyin buɗa baki da sallam suka shiga suka wuche kai tsaye kan table zama sukayi suna jiran time yachika a kira sallah ” shiru suka zauna kowa da tunanin dayake ” diyana che ta katse musu shirun dachewa Aunty Zahra sai narinƙa jin gidan ba ɗaɗi wlh saboda ba kowa ki kalla kan table ɗin nanfa da chika muke muna chin abinchi amma yanzu saura mukaɗai kai gaskiya na kosa su Abba sudawo ” Zahra zatayi magana saitaji an daƙa musu tsawa daga bakin kofar shigowa ” da sauri suka ɗago kai suna bin bakin kofar da kallo ” Auntyn Maryam suka gani tsaye fuskar nan babu annuri ko kaɗan nan take jikin Zahra yafara ɓari dan tasan halin Aunty Maryam sarai ” diyana kam kawar da idon ta tayi tachigaba da abun datake kamar bata san da wata Aunty maryam awajen ba “a nitse chikin sanyin murya hiyana tafara magana ina wuni Aunty Maryam ” wani mugun kallo Aunty Maryam ta wurgawa hiyana batare da ta amsa gaisuwarba chikin tsawa tafara magama uban waya baku izin kurinƙa zuwa nan kuchi abinchi inachewa Aisha itace yar uwar ku a gidan nan ” shiru sukayi basu che ko kalaba ” Aunty Maryam tachigaba dachewa to tunda wajen Aisha kukazo ku tsaya a iya ɓangarenta idan nasake ganinku a wani ɓangare na gidan nan, ba bangaren Aisha ba wlh sai na babballa yarinya kuzo kuficemin daga nan ko nashiga na muku mugun duka ” tunkan takai karshen maganarta suka mike gefenta sukabi zasu wuche ” hannu tasa ta damkoh wuyar rigar diyana tana faɗin ke ki buɗe kunnenki ki saurare ni da kyau daga yau bawanda zai sake share bangaren Aunty amarya keche zaki rinƙa yi har nabar gidan nan, ke bama shara kawaiba wankin kanana kayana wankin toilet mopping da yimini tausa kinajina bakinche ke bakida kunyaba to wlh zan gyara miki zama ” diyana binta kawai take da ido batace komaiba tayi shiru ” su Zahra kuwa wuchewa bangaren Ammi sukayi jiki ba kwari ” hannu Aunty Maryam tasa ta tsolewa diyana ido tana faɗin shegen ido kamar na mayu ai kedaga ganinkuma dangin mayune shiyasa aka faɗamin kun lashe zuchiyar kowa na gidan nan to nikam nafi karfinku ” hannu diyana tasa tana goge idonta tana hawaye zafi idon yake mata sosai ” sakin rigar nata Aunty Maryam tayi san nan tace yanzun nan kije ki wanke toilet’s dasuke bangaren Aunty amarya dukka san nan ki shiryamin abinchin buɗa baki ” ba musu diyana tanufi bangaren Aunty amarya tana hawaye Aunty Maryam kuwa ta wuche chikin ɗakin mai martaba

    Abangaren su Zahra kuwa palon Ammi suka koma suka zauna a kan sofa nan take Zahra tafara hawaye ” hiyana tamike ta dawo kusa da ita tana faɗin lfy Aunty Zahra kike hawayen ” chikin kuka Zahra tace diyana nakewa kuka wlh dan nasan tun da Aunty Maryam ta tsai da ita wani muguntar zata shirya mata ” kiyishiru Aunty Zahra ninasan duk abunda Aunty Maryam zatawa diyana bazai kai kaso ɗaya chikin goma na wadda inna tamana ba dan haka ki daina damuwa ba irin muguntar da’bamuganiba chewar hiyana ” mikewa Zahra tayi tana faɗin kuzo muje muyi buɗa baki gashi chan ana kiran sallah ba musu suka nufi kichin na Ammi ” ruwa ko wannensu yafara sha san nan sukachi dabino ” zahra tace ku zauna a palo kujirani bari naje palon mai martaba ba ɗaukoh mana abinchinmu ” inkinje Aunty Maryam bazata bugekiba chewar hiyana ” eh bazata bugeniba ai duk dokar datake kafawa ku take kafawa baniba nikam ai bata isa tahanani yawo a gidan babana ba tana gama faɗin haka yanufi hanyar fita .

    KASAR SAUDIA ✈️

    Gaba ɗayansu suna chikin masallahchin a nan sukayi buɗa baki bayan sungama sunyi sallane suka zauna hira ” Ammi ta dubi Ummi tace Maryam fa tazo ” yaushe tazo chewar Ummi ” yau tazo Mai martaba yabasu amsa ” ya akayi wan nan karon tazo dawuri chewar Ummi ” tsaki Aunty amarya taka san nan tace oh bakisan tazo daman koh to tazo kuma bayadda zakuyi da ita ” mikewa DON yayi zai bar wajen ” Aryan yace jirani muje tare, tare ya faɗin hakan yana mikewa tare suka jera suka nufi hotel ɗinsu ” mai martaba yama Ammi magana da fillanchi Mikewa tayi tana faɗin Ummi muje Koh, mikewa Ummi’n tayi dan tasan mai Martaba ne ya umarchi Ammi dasu tafi ɗaki dan baisan hayani kuma baisan subiyewa Aunty amarya ” Khalid Aiman Ahmad suma suka mike a tare sukabi bayan DON da Aryan ” dawo da kallansa mai martaba yayi kan haidar da umar dake zaune basu tashiba, to me kuke jira, ai tun bai karasa magana’ba suka mike suka bar wajen ”
    dawo da kallansa kan Aunty amarya daketa chika tana batsewa yayi a nitse yafara magana wai meyasa Hajara bakyasan zaman lfy’ne eh meyasa kullun ke kike tada husuma a chikinkune tunfa kina amarya kike irin wan nan hali wadda kikazo kusamuma baki kyaletaba haka wadda tazo tasamekima ” zatayi magana ya ɗaga mata hannu banasan inji komai daga gareki kawai abun danakeso karnasake jin wata fitina tatashi ,” ke ko kunyar ƴa’ƴanku ba kyaji kitashi muje mu kwanta yaƙarisa maganar yana kokarin mekewa hanyar ɗakinsu yanufa itama tamike tabi bayan’sa tanata chika tana batsewa

    NIGERIA ✈️

    Har wajen karfe 9 na dare diyana ta dawo ɓangarensu da kyar take tafiya saboda yinwa ko buɗa baki batayiba ko sallama babu ta shiga ɗakinsu ” tasamu su Zahra har sunyi wanka sunyi shirin barchi “Zahra na ganinta ta mike tana faɗin sannu diyana san nan tayi waje da sauri ” zama bakin gado tayi ta ɗago blue eyes nata dasuka sauya izuwa ja saboda yinwa da gajiya, tana kallan hiyana dake tsaye tana mata kallan karin bayani takeso ” diyana zatafara magana saiga Zahra ta dawo hannunta ɗauke da plate ɗin abinchi da cup mai ɗauke da tea mikawa diyana tai nantake ta karɓa tafara chi ” zama sukayi kusa da ita shiru itakuwa sai ɗura abinchi take hannu baka hannu kwarya

    Wayar Zahra tasoma ringing da sauri amrat dake rike da wayar tamiƙa mata my lovely bro ne yabayyana a kan screen ɗin wayar da sauri Zahra tayi picking call ɗin tare dasa wayar a H-free tana faɗin hello yaya khalid ” wani dogon numfashi Khalid yaja tare da sauke ajiyar zuchiya kana yace my lovely sister ykk ya makaranta ” muna lfy makaranta alhamdulillah Zahra zata sake magana taji ” diyana takwache wayar tana faɗin yaya Khalid ina yaya Aryan dan Allah inasan inyi magana dashine ” baki buɗe’su Zahra ke kallanta ” Khalid kuwa chewa yayi ai daman dan ke nakira shima magana yakesanyi dake ” yauwa to bashi,”miƙawa Aryan dake zaune kusa dashi wayar Khalid yayi ” ansa Aryan yayi yasa a kunnensa yana faɗin hello ” yauwa yaya Aryan ina wuni ” lfy lau y school ”
    khalid kuwa miƙewa yayi yana faɗin inazuwa hannunsa Aryan yakama yamai’dashi ya zauna yana harararsa ” yaya Aryan wlh yau wan nan Aunty Maryam ɗin takusan kasheni chewar diyana ” a zafafe Aryan yace what ? bana rabakuba mekuma yasake kai ki wajenta ” turo baki tayi kamar tana gabansa tafara bashi lbr abun daya faru daga farko harkarshe ” shiru yaɗanyi yana tunani daman yasan za’ayi hakan tunda yaji Aunty Maryam tazo ba lokachin zuwansuba yasan da dalili yayi nisa chikin tunani ” muryan ta ta katse masa tunanin dacewa ” yaya Aryan dan Allah kudawo kaga idan kun dawo Abba bazai bari tarinƙa buguna ba ” karki damu saura kwana 10 mu dawo kuma I next week Aunty farida zatazo domin tarbarmu idan Aunty farida tana nan bazata bari a muku komaiba, amma duk dahaka zanmata magana ” to shike nan sai dasafe ” murmushi kaɗan yaɗanyi kafin yace bakyasan hira danine kikechemin sai da safe ” khalid dake zaune kusa dashi ya ɗago a sukwane yana kallansa fisge hannunsa yayi daga rikon da Aryan yamasa yamike yana faɗin idan kagama hirar, kasameni a ɗaki kaga tafiyata ” harara Aryan ya wurga’masa ” khalid bai bita kansaba yayi waje
    Diyana kuwa dariya tai san nan tace to ai abinchi nake chi nifa yanzu nake buɗabaki ” shiru yayi zuchiyarsa tana masa zafi sosai yafara tunanin matakin daya kamata ya ɗauka wan nan wani irin zalunchi’ne yarinya tayi azumin san nan kijib’ga mata wan nan uban aiki kuma ki hanata buɗa baki yanzu kusan karfe 10 nadare wai batayi buɗa bakiba, dole na ɗau mataki ” jin yayi shirune yasa diyana cewa yaya Aryan kodai kayi barchine ” aa banyiba kawai ina ɗan tunanine ” to shike nan sai anjima bari nagama chin abin china ” ok kichi a hankali dai kuma banda chin fruits dayawa dan inchikin’ki yafara chiwo kinga bamunan bare namiki allura ” dariya tayi san nan tace to bazan chiba ” ok kawai yace san nan ya katse kiran ya ajiye wayar a gefe ya dafe kansa yana tunani ” dayaga dai tunanin ba wata mafita, sai yaike ya nufi kan katafaren gadansa ya konta yajawo wayarsa yafara latsawa

    Bayan diyana tagama chin abinchinta tamike tanufi toilet wanka tayi tafito daure da towel kayan barchi tasa doguwar riga mai siririn hannu yar shafal mara nauyi kwanche ta iske su Zahra sunata yar hirarsu, dayake yanzu su amrat ma sun dawo ɗakinsu, saboda suna tsoro tunda ba kowa a gidan sai suka haɗu suka chure waje guda
    Hayewa samar gadon nasu tayi itama tana faɗin Aunty Zahra kunna mana kallo ” to kawai Zahra tace tare da dauko wayarta dake gefenta ta shiga gallery tana kokarin neman film sai taga kira yashigo ” da sauri tayi picking call ɗin tana faɗin yaya Khalid bakayi barchiba ” eh banyi barchiba ya’za’ayi nayi barchi bamuyi wayaba ” Zahra zatayi magana sukaji an banko kofar ɗakin nasu da karfi gaske ” zubur suka mike gaba ɗayansu har sai da wayar Zahra tafaɗi kasa dan tsorata dasukayi ” a zafafe Aunty Maryam ta shigo chikin ɗaki kai tsaye wajen diyana tanufa damkoh wuyarta tayi tafara bugunta ta ko ina ” diyana tafara ihu ” nizaki haɗa faɗa da ɗan uwana koh to wlh yau sai na kasheki, tun danake dashi baitaba kirana a wayaba amma yau saboda’ke sau biyu yana kirana bugunta Aunty Maryam keyi tana surutai ” diyana kuwa sai ihu take ” hiyana naganin Aunty Maryam na kokarin kashe diyana da gaske ta kwasa a guje tayi wajensu tana kokarin kwache diyana a hannunta ” hankaɗe ta Aunty Maryam tayi da karfi ta tafi ta bugu da bango nantake kanta yafashe ” ihu mai karfi Zahra tabuga tayi kan hiyana tana kiran su nanta ” lamrat da amrat kuwa sai kuka suke ” duk da raunin da hiyana taji bai hanata sake mikewa a zafafe tayi kan Aunty Maryam tana faɗin karki kashemin ƴar uwa dan allah ” wani bugu Aunty Maryam tasake kaiwa hiyana a baki ” kukan kura hiyana tayi a fusace ta damki wuyar Aunty Maryam ta baya ” bashiri tasaki wuyar diyana ta juyo ta damki hiyana tashiga bugu ” da gudu Zahra tazo ta duƙa takama kafar Aunty Maryam tana rokonta ” dan allah Aunty Maryam kiyi hakuri ki kyalesu wlh marayune basu da uwa basu.. Zahra bata karisa ba taji saukar mari a faskar ta a zafafe Aunty Maryam tace. Kifita a ɗakin nan zahra’u kokuma na haɗa dake ” mikewa Zahra tayi tana kuka takama hannun amrat da lamrat tace muje ” kwache hannunta lamrat tayi tayi gun Aunty Maryam da gudu tana faɗin dan allah ki kyalemin yan uwana haka ” kafa Aunty Maryam tasa ta amɓare lamrat tafaɗi kasa tana kuka ” da kyar diyana tamike tana ɗingisa kafa ta karisa wajen ta duka gaban Aunty Maryam tace ninamiki laifi basuba kiyiwa Allah kisakemin yar uwata ni ki kasheni inkinaso ” juyowa tayi ta damki wuyar diyana ta damkoh hiyana ta haɗe kansu ta buga da karfin gaske wani kara suka sake a tare ” Zahra da amrat dake tsaye a bakin kofa da gudu suka dawo chikin ɗakin ” Aunty Maryam kuwa duk da hakan bata kyalesuba sake damkar gashin kan diyana tai tana janta a kasa har zuwa wajen mirrow tasa hannu kan mirrow ta dauki wani kwalbar turaren humra zata buga mata ke nan taji anche STOP chikin tsawa da sauri ta ɗago kai idanunta suka sauka akan…✍️✍️✍️

     

    More comments an share pls 🙏

     

    *

     

     

    💫STAR LADY💫*27*

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 11

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 11

    Episode 11*

     

    Mai martabane zaune a fada shida Aryan, Ahmad Khalid da’kuma Yusuf a nitse mai martaba yafara magana ” Aryan meyasa zaka mari diyana kanajin faɗan danayiwa safras fa ranan akan marin dayayiwa hiyana shine kaikuma kasake marin diyana koh wai bakuda tausayine nikam eh ” calmly Aryan yasoma magana kayi hakuri Abba wlh tabatamin raine sosai shiyasa ” nasani Aryan nasan halin diyana itakuma haka allah yayita hakuri zakurinkayi da ita ban hanaku kumusu faɗaba amma kurinka ragewa kuma bai’kamata kuɗora hannunku a jikinsuba bakuganin yanayin’sune, yanzu kaje kadubi fuskar diyana da kyau kagani shattin yatsunkane kwanche akai to na’menene hakan gaskiya bansan hakan karna karaji kuma karna kara gani ” inshaa allah Abba zan kiyaye chewar Aryan ” Khalid yace Abba yabatun zakkan nanfa ” eh kuna barwa ai kukula da komai ” Ahmad yamike yana faɗin aa Abba su yaya Khalid dai nikamma bari naje na dubo Aiman ” harara Yusuf ya watsawa Ahmad yana faɗin zakasani ne ai dakai da Aiman ɗin gaba daya wlh munkusayin maganinku a gidan nan ” Ahmad dai bai sake maganaba yafiche abunsa

    Aryan yace Abba yabatun komawarmu England ne ” aikuda komawa kam to banacheba kabari ayi naɗin sarauta tukun nan sai inyi tunani akai chewar Abba ” mikewa Aryan yayi yana faɗin to shike nan Abba allah ya kaimu san nan yafiche daga fadan ” Khalid da Yusuf ma mikewa sukayi suka fito sunayiwa Abba sai anjima

    Gabaɗaya family sun haɗu a palo dan chin abinchin dare amma banda don, dakuma yan matan Ammi subasu zoba , ” mai marbata yace waishin ina yan’matana’ne mesukeyi basu fitoba, ko dai daga buɗa baki shike nan bazasuchi abinchin dareba” Ammi zatayi magana sai sukajiyo sallamar’su nanfa kallo yadawo kansu banda Aryan da fahad kowa na palon kallansu yake, ”

    diyana na sanye chikin dogon wando baki da rigansa zuwa guiwa pink colour still dai ba ɗan kwali a kanta ta zuba gashin nan har baya sai kwalli gashin yake nakinkirin dashi har tsakiyar bayanta, dan karamin bakin nan nata yasha janbaki pink ga blue eyes yasha kwalli ta gyara sagenta ga zarazaran gashim idanta, tasa high heel pink kalar rigarta

    ” hiyana ma dogon wando baki tasa sai riga sky blue zuwa guiwa ta ɗaure gashin Kanta, tayishi kamar donut ta yafa gyalen kayan akanta paki kalan wando dan bakin nan nata yasha ret janbaki tayi kyau sosai kamar kasacheta ga blue eyes yasha kwalli sai’yaƙara kyau sosai yana kyalli sajenta kwanche a gefen kumatun’ta gashin geranta kamar tayi caving tasa flat shoe sky blue kalar rigar

    Zahra ma dogon wando baki tasa sai riga yellow tayafa gyalen kayan akanta shima bakine ɗan karamin bakin tan nan tasanya masa janbaki pink colour tayi kyau sosai itama daman zahra kama take da don sosai wan nan dalilinsaya suka zama kamar tagwaye da hiyana sai dai banbanchin kwayar ido dan zahra idanta bakine kamar nawa

    Lamrat kuwa dogon riga baki tasa mai shegen kyau,
    Tasa flat shoe fari, tayi rolling ɗin karamin farin gyale a kanta Zahra tamata make up sosai kamar wata balarabiya tazama

    Amrat kuwa dogon wanto fari dasa sai yar farar t-shirt navy blue itama batasa ɗan kwaliba amma zahra tamata pakin na gashin a tsakiyar kanta tazuba jelar gashin a’ baya har tsakiyar bayanta booth navy blue tasa a kafarta

    Yusuf ne yache wow my baby zo ” gaba ɗaya kallo yadawo kan Yusuf, a’ sukane Aryan yaɗago yana kallan Yusuf ɗin shi ko ajikinsa kallan su diyana ma yake baisanma jama’a na kallansaba ” bin inda Yusuf ɗin ke kallo Aryan yayi ” “Aryan kasa kawar da kannasa yayi daga kallanta ?

    Karisawa wajen table ɗin sukayi sukayi kowa tasamu waje ta zauna lamrat zata zauna kusa da Ammi ” yusuf yache zo nan kizauna kusa dani my baby ” bamusu lamrat takoma kusa dashi ta zauna ” haidar da umar sai gulma suke kasa kasa ” Ammi da Ummi kam ko ajikinsu abinchinsu kawai sukechi ” Aunty amarya kuwa sai chika take tanata harararsu ” ɗaukoh fura ki damamin hiyana chewar mai marbata ” da sauri hiyana tamike tanufi kichin, kwarya ta ɗaukoh san nan ta daukoh fura, tanufi freig ta ɗauki ruba ɗaya na nono tajuya takoma palan mai martaba, da sallama tashigo palan ta dawo wajen zamanta ta zauna tafara dama furar

    Sai’hira suke jefi jefi mai marbata yache banso a che muntafi umrah nan mun barkuba amma makaranta basu baku hutuba ” Ammi ne tache sai suje hajji kawai kokuma subari sai wata shekarar ” mai martaba zaiyi magana ” Ummi tace Fahad tashi ka kaiwa yayanku abinchi ” da sauri Fahad yamike yana faɗin ina abinchin ” yana kichin Ummi tabashi amsa , ” fichewa yayi daga palan

    Bayan hiyana tagama dama furan tamikawa mai marbata ” karɓa yayi yana murmushi kana yace duk gidan nan hiyanata tafi kowa iya dama fura ” turo baki diyana tayi tana faɗin wlh nafita abun dama nina ko…. bata karisa maganaba sakamakon wani mugun kallan da Aryan yake wurga mata ” shiru tayi

    Mai martabane kuwa sai kallansu yake yana murmushi yana farinchikin burinsa yafara chika aishi haka yakeso kodama hararanne Aryan kewa diyana daɗi zaiji dan daga harara sai kallan mutunchi ” Ammi che ta katse masa tunani dache ranka ya daɗe sai da safe ” hararar wasa mai marbata ya wuga mata kana yace inada magana dake ” to kawai Ammi tache ” jin mai marbata yace. yana da magana da Ammi yasa kowa yatashi suka fiche

    Mai martaba yadubi Ammi yafara magana jiya Yusuf yasame damaganar akan Khalid da zahra, Khalid yafaɗawa Yusuf yanasan Zahra tun tana karama ina faɗamiki hakanne bawai dan kifaɗa mataba sai hakkinki a matsayin uwa da’kuma kisamata ido karkibari tawa Khalid kishiya, danni tun da Yusuf yafaɗamin nariga nabawa Khalid auren ta, kokina da wani abun faɗe ” ajiyar zuchiya Ammi tayi san nan tace, nikaina inakaunar Khalid nina renesa a hannuna yagirma babu halinsa da bansaniba bawani abun da zanche saidai inmusu fatan alkhairi kawai ” to masha allah Amma fa kinsan yau a ɗakin’ki nake amma kikechemin sai da safe koh ” murmushi Ammi tayi tana tace tubanake wlh nagajine a’zumin yau ɗin nan ya wahalar dani ” haryanzu dai lallanchinki bai raguba Aisha, to muje chiki namiki tausar koh ” mikewa Ammi tayi tana faɗin mujedai ninamaka ” dariya mai martaba yayi san nan yamike yabi bayanta sukayi chikin betroom

    Karfe 10 na dare

    Rike take da cup ɗin coffee tanufi bangaren Aryan jikinta sanye da kayan barchi riga da dogon wando pink colour still dai kanta babu ɗan kwali tafiya take tana kunkuni” ni wlh barchi nakeji nagaji saikayitaba mutun wahala dan mugunta ” da sallam tashigo palan baya palo kai tsaye ta wuche betroom ɗin ” kwanche yake akan makekiyar gadansa yana latsawaya jin shigowarta yasa ya ɗago kai yana kallanta ” sai turo baki take tana magana kasa kasa ” from head to toe ya karemata kallo san nan ya ɗauke kansa da sauri ” karisa shigowa chikin ɗakin tayi tazo gaban gadan ta duka san nan tace. Ina wuni yaya Aryan ” shiru yayi bai amsaba kuma bai motsaba ” itama shiru ta zauna har kusan 15 mnt, san nan tache yaya Aryan dan allah ka karɓi coffee ɗin mana wlh nagaji ” banzah Aryan yayi da ita kamar baiji metake faɗe ba shiru shiru baiyi maganaba ganin bai daniyar magana yasata tamike, tanufi indayake wai dan taga yayi barchine
    Aji cup ɗin coffee ɗin tayi akan dan karamin table ɗin dake tsakiyar ɗakin san nan tanufi kan gado hawa gadan tayi taga idansa a lunshe , ta turo baki tana faɗin shine dan mugunta kabarni ina duke kan guiwowina har kafata namin zafi kaikuma kayi barchinka koh, to banyafe… Bata karisa maganarba taga ya waro manya manya ash eyes ɗin nan nashi akan fuskarta ” a’sukwane ta juya tana kokarin sauka gadan wani damka yayiwa gashin kanta wandayasa tadawo baya tafaɗa kan kirjinsa ” kware baki tayi zatayi ihu yasa hannu yarufe mata baki ” kasa kasa yace kina buɗemin baki ina harbinki da bindiga meya hauwar dake gadona yayi maganar tare da chire hannunsa daga bakinta ” murya na rawa tace dan allah yaya aryan kayi hakuri kasakemin gashina wlh zafi yakemin ” banche karna sake ganinki ba ɗankwali ba eh ” kayi hakuri zanrinka sawa chewar diyana tayi maganar chikin muryar kuka ” harchikin ransa yaji voice nata na karshe kayi hakuri zanrinka sawa a hankali yazame hannunsa daga kannata, yana faɗin to tashinmin ajiki ” da sauri tamike tana faɗin to ga coffee ɗin ” mikewa yayi shima kana yace bazanshaba ki mayar kije kisa ɗankwali saiki kawomin ” a shagwabe tace ayya dan allah kayi hakuri kasha allah gobe zan daura dan kwalin kafin nakawoma wlh yanzu nagaji kuma barchi nakeji ” kallanta yayi from head to toe san nan yache nikam, kekam kinada hankali kuwa kinsan chiwon kanki kuwa ” turo baki diyana tayi tana faɗin mekuma nasakeyi ” wlh azim idan kikasake fitowa a haka batare da hijabi ko kayan arziki ajikinkiba allah zakiyabawa aya zakinta ” binjikinta tayi da kallo achikin zuchiyarta tana tunanin to me laifin kayan nan tayi nisa chikin tunani taji ya daka mata tsawa ” wai badake nake magana bane nache kifitamin a ɗaki koh, da sauri tajuya tabar ɗakin binta yayi da kallo har tafita
    san nan yamike yanufi inda ta ajiye coffee ɗin ya ɗauko cup ɗin yadawo gefen gadansa ya zauna yafara sha,

    Bangaren diyana kuwa tana fita bangaren Aryan kai tsaye part nasu tanufa da sallama tashigo palan, da sauri taja burki tana faɗin ya yaya Yusuf kaima bakayi barchiba ” murmushi yusuf yayi yana faɗin eh ina hira da baby’s nawane suna koyamin fillanchi ” karisawa indasuke diyana tayi tana faɗin kema amrat hardake yau bakiyi barchiba sai kije school kiyita barchi a class koh ” lamrat tace ainikam ma yanzu zanje na kwanta ” zama diyana tayi kusa da Yusuf zatayi magana ” Yusuf yace kuje ku kwanta dare yayi kunsan akoi tashin asuba ga zuwa school yayi maganar yana mikewa yanufi hanyar fita ” suma mikewa sukayi suka wuche ɗaki

    Karfe 4 dai dai na asuba gaba ɗayansu sun haɗu a palon mai martaba danyin sahur amma banda don abinchi sukechi chikin kwanchiyar hankali ” Ammi tache hiyana da Zahra kuchi abinchin nan dawuri ku’ɗauki na yayanku ku kaimasa zahra najin Ammi tache sukaiwa don abinchi tafasa kara sai da kowa na palan yaɗago yana kallanta ” lfy auta ta chewar Abba ” Zahra dai taki magana sai kukanta kawai take ” hiyana kam datariga da tasan me Zahra takewa kuka ko kallanta batayiba, su Ammi sunyi tambayar duniyar nan amma Zahra taki magana sai kuka take ” Aryan ne ya daka mata tsawa zakimana shirune kosaina babballaki a nan ” tsit tayi kamar ruwa yachita ”
    Aunty amarya ne tamike tana faɗin kai umar kaje ka dauki abinchin yayan naku ka kaimasa kuma daga yau kai zaka rinƙa kai masa abinchi tana kaiwa nan tafiche tana tunanin aranta ai bazan taɓa barin yaran nan surinƙa kusantar samarin gidan nanba daga yau har ranar da gagarabadau zai musu aiki ido zan samusu sosai da sosai ɗakinta tawuche ta haye gado babu ko sallah takama barchi

    Bangaren”su hiyana kuwa sunajin Aunty amarya tace umar yakai abinchin yayansu nantake suka fara murna sukamike a tare suna faɗin barimuje muyi sallah ” Ammi ta kalli hiyana chikin harchen fillanchi tace wani sallah kuma badai kina period ɗin kike sallah ba ” shiru hiyana tayi dan ita batama san idan a na period baa sallah ba ” ganin tayi shiru yasa Ammi ta dubi zahra tace kije ki koyamata abun daya dace tayi ” to kawai zahra ta amsa dashi san nan suka fiche

    Mikewa Yusuf yayi yana faɗin gaskiya lokachi yayi dazan koyi fullanchi nima haba yanagama faɗin haka yayi waje ” Khalid ma yace tab aiko nima dole naje Zahra ta koyamin irin wan nan wariya daake nunamana kana yamike shima yayi waje ” dogon tsaki aiman yaja san nan yamike yafiche ” shidai Aryan zaune yake ahiru yana latsawaya har saida yafarajin kiraye kirayen sallah yamike yanufi bangarensa ” Ammi da Ummi ma suka fiche sukayi nasu bangaren danyin sallah ” palan yarage fahad haidar da Abba ” Abba yace wai kunyi arwala’ne kunfasan su safras sunafitowa zamuwuche masallahchi ” mikewa haidar yayi yana faɗin aa baridai naje nayi ” fahad ko chewa yayi nikam nayi Abba” ok kawai mai martaba ya amsa dashi
    Shiru suka zauna har sauran matasan suka fito sukajera zuwa masallachi

    Aɓan garen inna kuwa da sallama tashiga gidan su buba zaune tasameshi a tsakar gida ” buba na ganin inna yafara murmushi yana faɗin inna jamɓandu( inna ina wuni) ” lfy buba ya kafar taka ” da sauki inna” inna tache to allah yakara lfy ina innarka take ” tana garke tanabawa shanu ruwa da abinchi buba yabata amsa ” to barina dubota bata jira amsar buba tayi gaba abunta ” a garken shanun ta iskoh innar buba da sauri inna ta karisa wajenta tana faɗin albishir rinki yar uwa rabinjiki ” ɗago kai innar buba tayi tafara murmushi tana faɗin goro ” to kifito muje yau kuɗin sunchika dubu goma dai dai chewar inna ” da sauri innar buba ta ajiye sandar hannunta datake juyawa shanu ruwan gishiri tafito daga garken tana murmushi jerawa sukayi suka koma chikin gida innar buba ta ɗaukoh mayafi suka fiche

    Wani ƙungurmin daji suka shiga tafiya suke har suka isawajen wani dutse ga hayaki nafitowa daga chikin kogon dutsen chikin kogon sukashiga ” wani kasurgumin bakin bokane awajen ga idon san nan jajawur duk yabi ya huhhuda hanchi yasa wasu karafuna gawani katan karfe mai raun dayasa a kunnensa bashida kyan gani ko kaɗan
    Zama su inna sukayi kusa dashi ” zasu fara magana ke nan yayi wani mahaukachin dariya ha, ha, ha, da murya masa daɗin Ji yace aikin ku bazaiyuwu a chikin azumiba saboda duk an ɗaure mana mutanenmu amma kuje sai bayan sallah kudawo ha ha ha yana gama faɗan haka ya ɓache ɓat ” da sauri su inna suka mike suka fito inna tace to yanzu barinaje na ajiye kuɗin sai bayan sallah mudawo da haka suka kuche gida.

    Kamar kullum yauma zaune suke a wajen chin abinchinsu na makaranta karatu boko hiyana take yaukam tun da bata da tsarki ” zahra da diyana da faria kuwa hirar wani film suke waishi love story English movie
    Lamrat da amrat suna rubutu a takardunsu ”
    Kamar daga sama sukajiyo muryan jabir yana faɗin ke hiyana zo mutafi ” ɗogo kai hiyana tayi a nitse tafara magana kayi hakuri jabir wlh yau banida lfy ne chikina namin chiwo ” to yakikesan nayi ke nan ga abokaina chan kowa budurwarsa tazo ni bandani ke nan ba zaiyiwuba i don’t care koma meke damunki, nidai kitashi mutafi ” kamar hiyana zatayi kuka haka tamike tanufeshi tana faɗin muje ” kallan uku 10 diyana tawa jabir kasa kasa tache mugu wlh sainayi maganinka ” kallanta zahra tayi san nan taja guntun tsaki ” jabir tunda yakira hiyana suka tafi basu dawoba har saida a katashi nanma saida diyana da zahra sukaje wajen dayake zama da abokan nasa sukache hiyana tazo sutafi mai ɗaukansu yazo ” jabir dayaji haka sai yache to taje zasu haɗu gobe ” jerawa sukayi suka nufi wajen da suke tsayuwa sujira motochin dake ɗaukansu ”

    suna tsaye awajen sukaji magana daga bayansu ” gaba ɗayansu suka juya ” hiyana tace uncle Omar ina wuni ” da faraa a fuskanshi ya amsa san nan su Zahra suka gaidashi zaisake magana saiyaga motochin ɗaukansu yazo nanfa yamusu sallama yawuche ” sukuma suka shiga mota kamar yadda sukasaba hiyana Zahra diyana motarau ɗaya ” amrat da lamrat suma motarau ɗaya ” da gudun gaske motochin sukabar bakarantar” gudu suke sosai suna kan hanyane” zahra tace kinsanme hiyana ” girgiza’kai hiyana tai alamar aa ” uncle Omar fa wai san diyana yake chewar zahra ” kan uban chan niyakeso lallai kuwa yana ruwa wlh dannikam inba sojaba bazanyi aureba ” baki buɗe hiyana ke kallan diyana ” Zahra kuwa chewa tayi meyasa kikesan soja sojojifa mugayene ” eh ae a chikin sojanma mugun nakeso wanda zaiyimin maganin yaya Aryan kuma wanda yake da bindiga shima ” zahra tace to me yaya Aryan ɗin yayimaki haka dakike neman mugun soja yayi maki maganinsa ” to bashine kullun inna masa laifi saiyache zai ɗaukoh bindiga ya harbeni namutu kowa yahutaba ” aikuwa hiyana bata san sanda takwashe da dariyaba tana faɗin kai amma kuwa da yaya Aryan ya kyauta wlh ” Zahra kuwa chewa tayi dalla rabu da hiyana kinji faɗamin muguntar me yake miki ” bayan harbeni dayake chewa zaiyi saikuma jamin gashi da takuramin nasa ɗakwali dakuma kawo coffee kullun tayi maganar dai dai lokachin da motochinsu ke parking a parking space na chikin gida
    Fitowa sukayi suka nufi chikin gida rike da hannun juna

    Misalin karfe 4 na yamma gaba ɗaya yanmatan zaune suke a palon Ammi suna kallo hiyana kuma tana karawa lamrat karatun qur’ani gaba ɗayansu shiga iri ɗaya sukayi duguwar riga abaya dukkansu colour ɗaya baki ” Ammi ma nazaune a gefe tana gyarawa amrat jigidarta da Aunty farida ta saya musu to ya matseta sosai ” da sallama Khalid da yusuf suka shigo palan ” da gudu Zahra ta mike ta nufi Khalid,faɗawa kan kirjinsa tayi ta rungumesa sosai tana faɗin oyoyo yaya Khalid ” Yusuf ne yace my baby kema kizo kimin oyoyo mana ” da gudu lamrat ta mike tanufeshi hannu ya buɗe masa tafaɗa kirjinsa yana murmushi ” Ammi data tuno abun da mai martaba yafaɗa mata nachewar Khalid na san Zahra yasa da sauri tace ke zahra’u wai yaushe zaki girmane wlh idankika sake wan nan oyoyo zaki chi gidanku ” turo baki zahra tayi ” Khalid yasa hannu ya ɗan bugi bakin kana yace to wa’ake turowa bakin hannunta yarikoh suka koma kan kujera mai zaman mutun biyu

    Yusuf ma rikoh hannun lamrat yayi suka koma kan doguwar sofan suka zauna ” hannu Yusuf yasa yana shafa kan lamrat yana faɗin my baby gashinkin nan kyau yakemin sosaifa ” baki buɗe Khalid ke kallan Yusuf, azuchiyarsa kuwa chewa yake amma Yusuf iskanchinka yawuche tunani anya kaima baka kamu da san yarinyar nanba kuwa ” afili kuwa chewa yayi ai gashin Zahra yafi nakowa kyau ” harara Yusuf ya wurga masa san nan yace yauwa Ammi nikam inasan intambayeki kullum mantawa nake ” Ammi tace. Tanbayi inajinka ” wai aina mukasamu kalolin idon mun nan ne pls ” Ammi tace au kache tarihi kakeson ji to gyra zama ” murmushi kawai yusuf yayi yazubawa Ammi ido

    Kakanku wato mahaifiyar mai martaba itache asalin wanda takawowa family mu kalan idan nan kakanku namiji babban likitane aiki yakaishi Us, a chan yaje ya auro kakarku ta mace baturiyar Us, amma musulmache sunanta sarah to sarah itache mai ido light green irin naka kaida yayanku ” sarah kuwa mahaifiyar ta idonta ash ne mahaifintane mai light green ɗin ido shiyasa gaba ɗaya yayan sarah suka zama masu ido 2 colour wasu ash wasu green gashi abunkuma yabisu har kanku jikokinta, ” Khalid yace no wonder, shiyasa muke da kyau kamar yayan larabawa ashe ashe ” dariya Ammi tayi tana faɗin abun harda yabon kai ” Khalid zaiyi magana yusuf yache to ammi su hiyana fa ya akayi suka samu blue eyes

    Ammi tace sukuma sungadone daga wajen kakanmu namiji kuma duk family mu ma sukaɗai sukayi saar samun blue eyes ɗin kakanmu namiji shi ɗan asalin kasar sudanne yazo nageria, a garin jimeta yola, yahadu da kakamu mace yana santa sosai iyayenta sukache bazasu bashi itaba, sai dai idan zai zauna a rugarasu haka yayarda ya auri kakanmu kuma suka zauna a ruga harsuka haifi babana, da kanwarsa ɗaya allah yayiwa kakanmu rasuwa, kakanmu mace kuwa babana yayi auri umma’ta Kuma duk a’ruga ɗaya suke kuma a chan suka zauna an haifenima bajimawa kakanmu tarasu itama, kanwar babana kuwa bayan an haifi kanina Ahmadu babansu hiyana ke nan itama tarasu daga nan babanmu ya ƙaura daga rugar chikin yola yakoma rugar jimeta, a nan mukachigaba da rayuwa
    Rayuwar farinchiki muke sosai kanina da babana suje kiwo nikuma naje tallar nono a wajen tallar nono na haɗu da Mai martaba yabini har gida, da kyar babana yabasa aurena to na bayan aure ba jimawa innata tarasu, yarage saura baba da Ahmadu haka mukachi gaba da rayuwa bayardda mai martaba baiyi dasuba akan sudawo nan kano sunki har gida yasaya musu Amma sunki wai babu inda zasuje da waɗan nan uban shanaye babanmu yana da shanu dayawa kusan 700 ga awaki da raguna kaji da zabbi hakadai sukachigaba da zama a ruga
    Kolokachin dana haifi yayanku sunki zuwa mota mai martaba yatura a ɗauko su amma sunki zuwa, babana ko yaki zuwane saboda niche yar fari Ahmadu kuma yaki zuwane saboda shine mai zuwa kiwon dabbobinmu kai intakaichemuku har babanmu yarasu Ahmadu yayi aure basu taba zuwa wajena ba saidai ninaje
    Nidinma kunsan yanayin gidan nan sainafi shekara uku banjeba nanma saina matsa da kyar mai marbata yake barina, akoi lokachin dana ɗauki tsawon shekara 6 banje naduba Ahmadu ba a shakara ta 7 ɗinne nayita rokar mai martaba da kyar ya’yarda yabarni naje”
    Danajene masamu fati matar Ahmadu ta haifi ƴaƴa har uku hiyana diyana dakuma lamrat san nan ga chikin na hudu ajikinta nasha mamaki sosai shine nachewa Ahmadu tunda yanzu bamuda iyaye yadawo kano kusa dani yaki yarda, wai inyadawo yazaiyi da dabbobinsa, nachemasa musayar yaki yarda wai bazai bar garin iyaye da kakanniba haka na hakura na kyalesa nasaya’ waya nabashi amma yaki karɓa wai baiso bayadda na iya haka nadawo na kyalesa
    Sai danasake ɗaukan shekara 4 kafin nasake komawa kauye alokachin danaje nasamu mamansu hiyana tarasu wajen aihuwar amrat Ahmadu kuma ya auri habiba dan tachigaba da kulamasa da yara alokachinma saidana roki Ahmadu daya dawo kano amma yaki narokesa yabani hiyana da diyana nanma yaki ninasan halinsa da kafiya shine na kyalesa kuma tundaga wan nan lokachin dana dawo bansake zuwa kauyeba sai zuwan nan danayi na samu Ahmadu yarasu na daukoh su hiyana ” dogon numfashi yusuf yaja san nan yace. Tab lallai Ammi kina da hakuri sosai wlh allah dai yajikansu da rahma ” gaba ɗaya palon suka amsa da amin ” duba time yusuf yayi san nan yace. da Khalid muje koh mangariba ta kawo kai ” mikewa sukayi a tare yusuf narike da hannun lamrat sukayi wajen ” Ammi tace’wa su hiyana kutashi kuje kufara shirye shiryen kayan buɗa baki tare suma sukamike suka nufi palon kasa” Ammi ma tamike tayi ɗakinta

    Misalin karfe 7 na dare gaba ɗaya family suna palo dan yin buɗa baki amma banda don abinchi sukechi chikin kwanchiyar hankali shiru ba mai magana saidai karan spoon ” diyana tace. Abba kasan me ” sai dakowa yaɗago yana kallanta da mamaki ” mai martaba kuwa chewa yayi aa diyana ta bansaniba sai kinfaɗa ” dariya diyana tayi tace wai uncle Omar na makarantar mune yace yana sona ” what chewar mai marbata ” a’sukwane Aryan yaɗago manya manyan idan nan nanshi yana kallanta a jafafe yabuɗe baki…..✍️✍️

     

    Amin afuwa masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu more love

     

    Pls more comments an share

    *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star Lady*

     

     

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 7

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 7

    ⬇️
    *Star Lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *Episode7*

    Zaune suke a palan Ammi suna hira nan fa zahra take fada musu komai na gidan
    Zahra tache karku yarda kuyi wani laifi yanzu dankuwa shekaran jiya su yaya prince suka dawo baruwanku da kowa a gidan nan dan wlh duk yan gidan nan mugaye ne yaya Khalid ne kawai mutumin kirki dan haka karku kula kowa duk abunda kukeso ku tambayeni yauwa kuma inkun gaishesuma basu amsaba karkudamu kuma karkuyi wata maganar dan basa amsa gaisuwar kowa sukam haka suke
    Diyana tache to tunda basa amsa kaisu basai mu kyalesuba dole sai mun gaishe sune
    Zahra tache keeee. lallai da zafinki kikazo tab ai wlh idan sukazo suka wuche baki gaishesuba nan ma hukunchi zaki karɓa inkuma kingaishesu bazasu amsaba to zamanki lafi shine ki gaidasu koda basu amsaba karkidamu ” yauwa kunga wandayake zaune a kujeran gefen Ammin ɗazun din nan koh wan nan mai kama da Hiyana
    Da sauri Hiyana tache daman akoi mai kama dani a gidan nan ne ” Zahra tache eh mana ai shine ya zauna kusa da Ammi sunansa yaya prince to dashi da yaya Aryan da yaya yusuf da yaya Fahad wlh karku yarda hanya ta hadaku inba hakaba zaku jijiki basu da kirki Zahra zata sake magana taji takun tafiya a tari ta mike tawatsa dakinsu da gudu dankuwa tasan irin wan nan takun mutun ukune kawai a gidan nan keyinsa ” Don, Aryan , Yusuf shiyasa ta gudu dan batasan haduwa dasu
    Suna ganin Zahra ta gudu suma suka mike da gudu sukabi bayanta
    Yana shigowa ya tsaya shiru yana tunanin tabbas yaga wulkawar abu kuma kamar inuwar mutun wuchewa chikin palan yayi yasamu waje kan kujera mai zaman mutun daya ya zauna
    Yachiro wayarsa yafara daddan nawa kana yasa akunne jimkadan sai yache gani nanfa a palo banji me akacheba a dayan bangaren ba kawai naga ya katse kiran
    Fitowa Ammi tayi daga chikin betroom tazo ta zauna a kujera mai zaman mutun ɗaya a nitse Safra yache inawuni Ammi ta amsa masa da lfy yache yamukaji da hakuri tache hakuri yazama dole yache allah yajikansa da rahma amin Ammi amsa kana tache daman kuɗi nakeso kabani su farida zasuje suyiwa kannenka sayayya ” shiru yayi bai chekomaiba kusan 10 mnt tukun nan yache
    Ammi dan allah wai meyasa bazaki sabaki a magaAnar nanba nifa bazan iya mulkiba kinsanfa shugaba da adalchi da tausayi
    akasan shi to nikuma sojanefa
    Ammi baki sake take kallansa tache au kai bakada tausayi ke nan shiru yayi bai tankaba saima mikewa dayayi yanufi hanyar fita yana fadin Fahad zai kawo miki kuɗin
    Ammi dai ido tazuba masa har yafita tukun nan ta sauke wani nauyayyar ajiyar zuchiya afaili tache nida kaina nasan ba iya mulkar mutane zakayiba saboda wan nan irin hali naka bakayi kala da shugabanniba kadaifi dachewa da rike bindigar amma ni babu ruwa kaine zabin mahaifinka bazan chanza masa zabinsaba sai dai inshiyaga dama ya chanzaka da kansa amma zantayaka da adduar Allah yasa kar abaka mulkin nan dan in akabaka mutane zasusha wahala, zata sake magana sai taji alamar tafiya shiru tayi tana sauraran mai shigowa
    Aunty farida che tashigo bakinta dauke da sallama da fara’a Ammi ta Amsa mata sallamar
    Shigowa tayi ta zauna a gujerar da Prince yatashi kana tache Ammi barka da hutawa anche kina nemana gani
    Ammi tache yauwa sayayya nakesan kuje kiyiwa su Diyana dan kinsan basuda kaya to kisaya musu duk abun daya dache
    Aunty farida tache to inasuke suzo muje tare koh dan muzabi size dinsu dakuma colours din dasuke bukata
    Ammi tache aa kuɗan jira kadan kanin naki yache zaibawa Fahad kuɗin yakawomin
    Aunty farida tache aa basai ankarbi kudi wajen prince ba suzo mutafi kawai ni zan dauki nauyi sayayyar
    Ammi tache aa farida kada na daura miki nauyi da kinbari shidai yakawo kuɗin nafisan yamusu da kansane dan kuwa duk wani responsibility su yadawo kansa shi zai dauki komai shiyasama banbiya kuɗinba nache yabiya
    Aunty farida tache Ammi dani da prince duk ɗayane idan nabiya kamar shine yabiya kuma kamar yadda nakewa Zahra sayayya da kuɗina suma haka zanmusu saboda yanzu dasu da Zahra duk dayane awaje na
    Ammi tache to shike nan badamuwa kuje din
    Aunty farida tache Ammi dan allah inaneman alfarman kisa baki mai martaba yabani Diyana wlh tashiga raina ina kaunar yarinyar san nan kuma dan allah kutaimaka kubawa mardiya lamrat takuma da ita Abuja tunda kunga ita Allah bai bata aihuwaba
    Ammi tache kwarai ina matukar tausayin mardiya musanman idan kuka haɗu yadda take matikar son junior batasan yayi nisa da ita wani lokachin har kwalla nakemata amma bayadda zanyi inraba marayun allah nan Feeda tare suka taso komai tare suke dukda shekarunsu ba ɗayaba amma dai zan gwada kinji
    Aunty farida tache eh Ammi akoi chiwokam murabasu amma dan allah taimaka mana zakuyi muda bamuda yaya Ammi tache to zanyi magana da mai martaba da daddare
    Dukyadda mukayi zakiji
    Aunty farida tache to saikuma maganan prince Shima dan… Bata kai karsheba Ammi tache kingane tashi kutafi adawo lfy tana kaiwa nan tamike tanufi dakin su Zahra dan takirasu
    Girgiza kai Aunty farida tayi tache Ammi ” Ammi kinasan samana chiwon kai amma a hankali zanshawo kankine
    Fitowa Ammi tayi rike da hannun Amrat su Diyana na biye dasu abaya diyana da hiyana hijabai sukasa zahra kuma abaya tasa da gyalensa sunyi kyau sosai amrat da lamrat kuwa blaus ne ajikinsu mai kyau sai dan karamin gyale dasuka yafa akamsu
    Mikewa Aunty farida tayi san nan tache muje koh tayi maganar tana kokarin riko hannun Diyana
    Suna fita kai tsaye parking space suka nufa da sauri driver yazo ya bude musu motar hiyana da diyana da zahra suka shiga mota ɗaya
    Aunty farida kuma takama hannun amrat da lamrat suka nufi wata motar suka shiga
    suna shiga wayar aunty farida yafara kara da sauri ta dauki call din tache hello daga ɗayan bangaren yache inakikene insan muyi maganane
    Aunty farida tache gani nan yanzu nafito zamutafi shopping kazo karakamu mana sai muyi maganar a hanya ” yache aa bazanjeba amma barinasa sojoji surakaminke saboda tsaro” dariya Aunty farida tayi tache kai dai prince allah bansan irinkaba mutunne bayasan shiga jamaa to shike nan tunda bazakajeba saina dawo saimuyi maganar koh zata sake magana ke nan taga waso sojoji guda 4 a gabanta chiki har da abdol
    Tache laaaa yanzu muna waya yaushe kayiwa sojojin nan magana
    Prince yache lokachin danache bari na hadaki dasu mana alokachin na dannamusu kararrawa dasu nanki
    Dariya Aunty farida tayi tache to shike nan ngd saimun dawo
    Yache kikula mana da kanki tache to tunkafin takarasama ya katse kiran
    Juyowa tayi tabawa driver umarnin sutafi
    Abdol chikin harchen turanchi yache madan inbadamuwa barini naja motar dan oga yache nabaki kulawa sosai
    Aunty farida tache to badamuwa ” fita driver yayi yabawa Abdol wajen yashiga sauran sojoji ukun kuma suka shiga wata motar natake suka kunna motar suka miki hanya sai gate ” sojojin dake wajen suka bude musu pakekiyar gate din suna fita suka miki hanya
    Aunty farida tachewa Abdol to aibaka tambayi ina zamujeba
    Abdol yache oga yariga yashigarmin inda zan kaiku a chikin wayata
    Shiru Aunty farida tayi tana kallan ikon allah tana jiran taga inda za’a kaisu
    Kai tsaye wajen wani katafaren shopping Abdol yashiga yayi parking a parking space nawajen yafito yabudewa Aunty farida tafito kana takama hannu amrat ta tsaya saida su zahrama suka fito sukazo inda take san nan suka nufi chiki Abdol yabi bayansu sauran sojojin suka rufa musu baya Abdol yache su koma wajen mota sujirasu

    Kaya dayawa Aunty farida tafara ludan musu kuma tache suma suzaba duk abun dasuka ga yamusu su dauka ” Zahra kam duk abun datagani mai dan kyalkyali sai tache wan nan zayyiwa Hiyana kyau ta dauka mata sunyi sayayyar kayan sawa dayawa san nan sukaje wajen takalma da jaka suma dayawa suka dauka suka koma wajen kana nan kaya Hiyana naganin breziya tafa boye fuska Zahra nata mata dariya
    Aunty farida kuwa chewa take My Diyana kemafa kin kai sa bra ba Hiyana kawaiba dan kema naga ba bayaba wajen chikar halitta rufe fuska Diyana tayi da hannunta tana murmushi
    Amrat ne tayi magana da fullanchi tache zata sha ruwa Aunty farida tache ku fassaramin metache ” dariya Zahra tayi tache kai Aunty farida yakamata kema kikoyi fillanchi ruwafa tache zatasha
    Aunty farida tache to daga yau hausa zamu rinka yimata dan itama ta iya hausar to waima ya akayi ku kuka iya hausa ita bata iyaba
    Hiyana tache mu munazuwa tallan nono ne a chan akoi hausawa suna zuwa saye itakuma kullum tana gida tana aiki bata zuwa ko ina ” a gida kuma ba mai jin hausa sai fullanchi kawai shiyasa bataji
    Aunty farida tache to yanzu dai hausar za’ana mata har ta iya to kawai sukache san nan sukachigaba da sayayyar su
    Bayan sungama daukan bra da pant suka wuche wajen dankunne da sarka nanma dayawa aunty farida ta dauka musu har da gold saida sukachika keken zuba kaya uku da kaya tukun nan Aunty farida tache ya isheku ne kokuma akoi wani abun dakukeso ” da sauri Hiyana tache ya isa ” Aunty farida tache aa kuduba da kyau dai ” hiyana tache allah ya isa haka nan ” Aunty farida tache to shike nan kutura kayan muje wajen biyan kudi harsun kai wajen biyan kudin kuma sai Aunty farida tache inazuwa chikin shopping din tashiga bangaren always tanufa ta daukoh guda 6 ta dawo ta zuba musu a chikin kayan
    Diyana sarkin baki tache aunty menene wan nan kamar breadi Aunty farida tache nakine ke da hiyana da zahra kuma ba bread bane always ne ” Diyana ta mai mai ta su nan always to me akeyi dashi ko chi akeyi diyana ta tambaya.
    Aunty farida dai taga alamar kamar diyana bata fara period ba saitache mata inmunje gida ki tambayi zahra zata fada miki to kawai diyana tache
    Nanfa aka fadamusu bill na kuɗinsu Aunty farida ta chiro ATM nata tamikamusu suka chiri kudin san nan aka samusu kayan a leda Abdol yafara kwasan kaya shida yaran shagon suka kai mota
    Aunty farida kuwa takama hannun diyana sukayi waje su Zahra suka rufa musu baya
    Aunty farida tache Zahra da lamrat da hiyana suje su shiga motar da takawosu itakuma zata shiga motanta itada diyana da amrat . Tana kaiwa nan tashige chikin motar rike da hannun diyana amrat ma tashigo ta zauna kusa da diyana su
    zahra kuwa suka nufi motarsu suka shiga nantake sojojin suka tada motochin suka nufi gida
    Suna isa gida kai tsaye bangaren Ammi suka nufa a palo suka sameta nan suma suka baje kolinsu suka fara nunawa Ammi kaya. Ammi kam sai sannu da dawowa take musu tana sawa Aunty farida albarka takuma yaba kayan sosai tache su tattara suje su shiryasu a indaya dache, haka suka kwashi kayan sukayi dakinsu dashi

    Aunty farida tadawo da hankalinta ga Ammi tache Ammi gobefa zan koma Mai duguri
    Ammi tache ai naga wan nan karanma anbarki kindan dade ” Aunty farida tache eh wlh shiyasa nakesan komawa dan kar a hanani zuwa sallah kinga azumi yakusa ” Ammi tache ai garakam kikoma kije kikula damijinki yanzu dai kije ki kwanta ki huta a daki sai zuwa dare makarasa hirar
    Mikewa Aunty farida tayi tana chewa to Ammi dan allah dai kiyi kokari kishawo mana kan mai martaba daya taimaka yabamu diyana da lamrat
    Ammi tache to zanyi kokari . Betroom din Ammi aunty farida tashiga ta haye gadanta ta kwanta bajimawa barchi ya dauketa

    Zaune suke a tsakiyar gado gaba dayansu hiyana tache aunty zahra dan allah inasan kifara koyamin karatu kinji lokachin muna kanana bappa yana koyamana karatu har munyi nisa danni har nakai izu 10 a karatun qur’ani kuma inasan in iya karatun qur’ani sosai
    Zahra tache zan koyamiki hardana bokoma bana qur’ani kawaiba harda addoe dasu hadisai kuma akoi malamin dayake zuwa yana koyamin karatun islamiya kullum dayamma yanzu tare zamuna zuwa ya koyamana
    Diyana tache yauwa nima inaso aunty zahra ” zahra tache ai gabadayanku ma yazama dole kukoyi karatu yanzuma daga gobe zanfara koyamuku ” harsuna hada baki wajen chewa to

    Misalin karfe 8 na dare gaba daya family sun hadu a palan mai martaba
    mai martaba da don da aryanne kawai basa wajen shiru kowa yayi daga masu daddanna waya sai wayanda sukayi tagumi suna jiran fitowar Abba
    Aunty farida che ta kalli Fahad tache wai inasu prinse ne kullumfa sune suke bayan zuwa wajen nan ” Fahad yayi shiru kamar bazai tankaba kusan 2mnt tukun nan yache nimafa tun dazun damuka rabu bansake shiga wajensuba
    Ammi tache au ashe zaka tankamata ai nazachi bazakayi maganaba mutanene yadda kasan wasu kurmaye aimusu magana sunaji amma bazasu amsaba kukan wlh bakuji dadin halinkuba ” Fahad dai shiru yayi kamar baijin me Ammi ke chewaba
    Aunty farida tache kai Ammi hakafa akesan namiji yakasanche ba mai surutu barkataiba ” harara Ummi ta watsawa aunty farida kana tache aidaman ke’ki’ke kara injizasu dan kuwa ke awajenki komai sukayi dai dai ne basa laifi ” shiru aunty farida tayi bata tankasuba sai sukaji muryan mai martaba yanachewa aa karku dakurawa first born dina ku kyaleta haka nan irin wan nan faɗa haka
    Ummi tache ai daman bakinku daya zama mai martaba yayi yana faɗin eh dai munji babu ruwanki farida dawo nan kusa dani
    Mikewa Aunty farida tayi takoma kusa da mai martaba ta zauna
    Mai martaba yache Amrat ummu waru ( amrat tashi kizo) mikewa tayi taje zaunar da ita mai martaba yayi a kujerar kusa dashi aunty farida kuma tache diyana taso kidawo kusa dani mikewa diyana tai takoma kusa da ita
    Zahra’kam ko ajikinta dan ita koma kusa dawa zama zatayi amma yanzu da hiyana sukazo tare suke komai dan haka yanzuma suna zaune kusa da juna
    Takun tafiya sukaji wanda kobasu juyaba sunsan takun manyan boss ne nantake palan ya nitsu tsit wasuma da kyar suke numfashi chiki har da zahra da umar
    Su hiyana kam ko ajikinsu dan basumasan masu shigowarba
    Kai tsaye kan table din suka nufa suna sanye chikin fararen jallabiya dukkansu sai kamshi sukeyi kamar anyi barin turare ajikinsu zama sukayi ” don ya dauki bottle na ruwan dake kusa dashi ya bude ya tsiyaya ruwa a cup yasha san nan ya ajiye ragowar a kusa dashi nan take kannen nasu suka fara gaidasu amma babu wanda ya amsa a chikinsu saida kannen nasu suka gama gaidasune
    Zahra ta dan zunguri hiyana tamata alamun ta gaidasu chikin gurbatatchen hausarta tache inawuni hamma basu amsaba kuma ko kallanta basuyiba
    Diyana kam achikin zuchyarta tache wlh bazan gaishekuba mutane saikache wasu shadanu a muku magana bazaku amsaba kuma kuche inba amukuba zaku hukunta mutun to wlh nikam bazakumin hakan na daukaba yauwa dai dai nake da kowa

    Saida palan yayi shiru san nan chikin nitsuwa don yache inawuni Abba mai martaba ya amsa da lfy ” ya dawo da kallansa kan su Ammi suma yabisu ɗaya bayan ɗaya ya gaidasu
    San nan aryanma yabi iyayen nasu ɗaya bayan ɗaya ya gaidasu
    Shiru kowa yayi a palan sai aunty farida tachewa kuyangun dake tsaye a kansu dasu zubawa kowa rice an beans da sauri suka fara sarving nasu suna turawa kowa
    Aunty amarya tache nikam bashi zaku zubaminba kuzubomin semo da miyar agusi
    Bawanda ya tankata a palan sai aunty farida ne tache kuzuba mata mana tunda shi take raayi da sauri suka zuba mata suka mika mata
    Suna chikin chin abinchi hiyana tafara shakuwa shakuwa yaki tsayawa hannutasa ta dauki cup din ruwan da don ya ajiye kusa dashi daya tana kusa dashi tafara sha kamar daga sama taji saukar mari a fuskarta har saida tamike batasaniba,dafe kunmatunta tayi da hannu tana kallansa hawaye nazuba daga fuskanta wani tsawa ya daka mata wanda yasata zurawa aguje tabar palan tayi sashen Ammi kowa na palan sai daya tsorata banda mai martaba da aryan
    Aunty farida ne tayi karfin halinchewa haba prince meyasa zaka mareta bakaga yarinya bache kuma inkalura batasan ruwan shanka ta dauka bafa
    Ko kallan aunty farida baiyiba barema yabata amsa abinchinsa kawai yachigaba dachi shiru palan yayi ba abunda kakeji sai karan spoon
    Zahra kam jikinta sai rawa yake tanasan tashi tabi bayan hiyana amma tana tsoro
    mikewa diyana tayi tabi bayan hiyana lamra naganin diyana tamike itama tamike da gudu tabi bayansu amrat zata tashi mai martaba ya riketa yache zauna yata kichi abinchinki karki damu
    Kuka amrat ta pashe dashi tana fadin aa nakoshi nikam zanje wajen Aunty hiyana na ” mai martaba dayaga haka sai yache zahra dauki abinchin naku kikama hannun amrat kutafi kuje daki kuchi a chan ” da sauri zahra tamike ta dauki abinchin nasu takama hannun amrat sukayi waje

    Mai martaba yayi gyaran murya yafara magana ” meyasa zaka dora hannunka ajikinta kai bakada tausayine marayunefa ba uwa ba uba haka suka taso chikin kunchi da wahala yanzu kowani kukagani zai bugesu bazaku tsaya kutaremusu sai inda karfinku yakare amma kai da kankane ma zaka bugesu ” bakataba batamin rai irin na yauba gaskiya banji dadin hakanba kuma kasan lbr yaran nan babu abun da baka saniba agabanka aka bada lbr wahalar dasukasha, to bansan hakan tasake faruwa kanaji
    Kasa kasa don yache sorry Abba rainane yabachi ” mai martaba bai sake chewa ko uppanba
    Yusuf yache allah sarki wai daman Abba basu da iyayene wlh harsunban tausayi ” wani kallan banza aryan da don suka watsawa yusuf amma ko ajikinsa saima chewa yayi Abba gaskiya to indai hakane yakamata mubasu kulawa sosai dan sumanta da bakin chikin rashin iyaye
    Ammine tache haidar umar fahad duk kutashi kubamu waje zamuyi magana ” da sauri suka mike sukayi waje ” suna fita afusache Ammi ta dubi don tache idan kasake sa hannun ka bugi ɗaya daga chikin yaran nan to wlh ban… Bata karasaba mai martaba ya rufe mata baki kana yache aa bansanjin hakan
    Don kuwa dagowa yayi yana kallan Ammi yaga yadda ranta yabachi sosai tabbas baitaba ganin bachin rai a fuskar mahaifiyarsa irin na yau ba hakan yasa jikinsa yayi sanyi haryafara nadamar meyasama yayi sauri marin yarinyar meyasa baya iya controlling zuchiyarsane why gashi tunda yake da Ammi baitaba bata mata raiba sai yau gaskiya bai kyautaba
    Chikin nitsuwa da sanyayyiyar voice nashi yache kiyi hakuri Ammi inshaa allah zanrinka kiyayewa ” batare da Ammi ta kallesaba tache dazaifimaka
    Yusuf dai mamaki yake wai yau don’ne ransa yabachi haka kuma yayi saurin saukowa zuchiyar tayi sanyi tab lallai uwa tawuche wasa duk wani karfin izzan da mutun yake dashi bai isa yayiwa mahaifiyarsaba

    Mikewa mai martaba yayi yana fadin Ammi kisameni adaki inasan magana dake ita Ammi tamike tabi bayansa tana faɗin to ganinan ai muje tare tunda mungama chin abinchin
    Don da aryan ma mikewa sukayi suka nufi bangarensu
    Yusuf yache Aunty farida wlh yaran nan sunban tausayi wai yama su nansune
    Aunty farida tache wanda don yamara itache hiyana wanda tabi bayanta bayan ta gudu kuma itache diyana ta ukun kuma lamrat sai amrat itache karamar tayi maganar tana kokarin mikewa
    Yusuf yache ina zakije aunty farida ” zanje inyimagana da aryan da don ne dan kaga gobe zankoma
    Yusuf yache to shike nan nima zanbiyoki daganaya bari nasha coffee ina zuwa to kawai tache masa san nan tawuche tafita daga palan

    Tana fita palan bangaren aryan tafara zuwa da sallama tashiga palan babu kowa dan haka tanufi betroom dinsa zune tasamesa a kan kujerar mirrow yana hada wasu magunguna jin sallamarta yasa yadago kai yana kallanta
    aunty farida tache mezakayi da waɗan nan magungu nan kuma ” yache ina hadawa don ne ” bashi da lfy ne ta tambaya tana kokarin zama a gefen gadansa aryan yache aa banashi bane akoi wasu criminals da zaiwa amfani dasune ” aunty farida tache too allah yachechesu daga hannunku ” murmushi kadan yadanyi kana yache kai aunty babba muɗin kuma yau
    Aunty farida tache kuɗinfa aiku duk wanda yayi laifi kuma a kache kuzaku hukuntashi to wlh garama yachire rai da rayuwa dan kuwa inbai mutuba kadanne zai rage masa aryan zaiyi magana wayarsa tafara kara alamar shigowar kira bai dauki wayarba har kiran ta katse ” aunty farida tache wayake kiranka haka dakaki dagawa a takaiche yache faruq ne ” aunty farida tache faruq dai danasani best friend naku ” aryan yache eh shine ” aunty farida zata sake magana kira nabiyu yashigo bai dagaba har saida wayar takusa tsinkewa tukun nan yayi picking call din kuma yasata a H-free
    yache hello my tager daga dayan bangaren faruq yache my man ykk yanakira da farkoh baka dagaba . aryan yache hannuna nachikin wasu chemicals ne shiyasa ban dagaba daman innagama abundanake zankiraka saikuma kasake kira ykk y mom da dad ina zahra da zaina da maryam faruq yache Suna lfy yasu Ammi. Aryan yache suna lfy ina abdul soja ” faruq yache yana nan lfy ” amma katambayeni kowa baka tambayi inteesar ba
    Aryan yache wache kuma inteesar” faruq yache matar da zan aura mana ” dogon tsaki aryan yaja kana yache kaima auren zakayi ” faruq yache eh mana aryan yache tofa karkabari don yajika kaibama don bama nima yanzu..bai karisa maganarba aunty farida ta amshi wayar tana fadin yaushe zaka kawomin amaryan maiduguri inganta ” faruq yache aunty babba ashe kina kusa ” aunty farida tache eh wlh faruq amma gobe zanwuche ” faruq yache ina junior
    Aunty farida tache yana wajen Ummi kai bama wannanba yaushene auren, kuma kasa lokachi kakawomin amaryan inganta, ai garamaka kayi aurenka karka biyewasu Aryan dakuwa su basusan chewon kansuba
    Baki bude aryan ke kallan aunty farida sai zuba hira take da faruq dagajin yayi maganar aure waisu me matsalarsu dasuke san sai munyi auren nanne
    Bayan aunty farida tagama hirarta da faruq ta katse kiran ta mikawa Arayan wayansa san nan tache to daman nazo muyi sallamane gobe zanbi jirginsafe zuwa maiduguri
    Aryan yache ok karfe nawa
    Aunty farida tache 7 dai dai ” Aryan yache okay zanzo inkai ki airport. Aunty farida tache to ngd bari naje nayiwa donma sallama tayi maganar tana kokarin mikewa
    Aryan kuwa baisake tankamataba har tafiche daga dakin tama bar shashen nashi gaba ɗaya tanufi shashen don agurgije tamasa sallama dan tanasan taje ta shirya kayanta shima dai don chewa yayi zaizo yakaita airport

    Abangaren su hiyana kuwa tana parin palon dakinsu tanufa tafada kan gadonsu tana kuka diyana nashigowa ta haye kan gadan tana rarrashin hiyana saigasu zahra ” nan zahrama tashiga rarrashinta har tayi shiru takuma saukoh kasa suka karisa chin abinchinsu nan suka haye gado zahra ta daukoh takardun makarantar ta tafara koya musu karatun.

    Ammi na zaune a tsakiyar gadan mai martaba tana gyara masa gashin kansa suna yar hirarsu chikin nishadi Ammi tache ran’kayadade dan allah katausayawa mardiya kabata lamrat kaga batada ƴa allah baibata Aihuwaba gashi faridama tana san diyana
    Mai martaba yache oh bakyasan ganinsu a gabankine to idanma ke bakyasan ganinsu ni inabukatar ganinsu kuma babu abunda zai raba yaran nan sai mutuwa ko aure bazan yarda yarabasuba dan kuwa idan miji ba agarin nan yakeba babashi aurensu zanyiba wlh duk wanda yake sansu tofa saidai in mazauni kano inba hakaba yahakura kuma wan nan shine hukunchina bansan sake jin wata magana akan yaran nan
    Ammi tache to inshaa allah bazan sake magana a kai ba jawota mai martaba yayi tadako kan kirjinsa yana faɗin shiyasa nake sanki sosai kekadaiche a chikin matana innayi magana baki musamin kobakison abun danache haka kike hakura ki amsamin allah yamiki albarka ” shafa gefen fuskarsa Ammi tayi tache nima ai inasanka sosaima
    Mai martaba ya ɗan chije hannunta yache yanzu babu fullanchi ke nan
    Dariya Ammi tayi tasake ahigewa jikinsa tana faɗin eh kam akoi amma kaɗan kaɗan rungumarta sosai mai martaba yayi yafara raɗa mata magana a kunne

    Misalin karfe 10 dai dai aunty farida tashigo dakin Ammi da sallama abakinta Ammi na kwanche a kan gado tamike daga zaune ta amsa sallamar
    Abakin gadan aunty farida ta zauna tache Ammi gobe da asuba zantafi nazone naji yakukayi da mai martaba ” Ammi tache wlh feeda har kunyarki nakeji bansan yazanfara yimiki bayaniba ” Aunty farida taɗan kakalo murmushi kana tache karki damu Ammi aidaman nasan dawuya mai martaba yabanisu saboda tunfarko yanuna aa bazai bayarba amma bakomai wlh Ammi gobe zanwuche zanbi jirgin karfe 7
    Ammi tache to allah ya tsare hanya feeda Aunty farida tamike tana fadin ameen tanufi hanyar fita tana fita kai tsaye tayi bamgaren Ummi

    Washe gari misalin karfe 9 na safe gaba daya family suna palon mai martaba zaune akan table din chin abinchinsu gaba ɗayansu har dasu don amma banda su diyana da zahra da mai martaba
    Mai martabane yafito daga ɗakinsa yazo ya zauna a kujera nanfa kowa yafara gaidashi gaba ɗayansu yahadesu yabasu amsa ɗaya san nan yache inasu diyana
    Ammi tache suna daki ” mai martaba yache to mryafaru basu fitoba
    Ammi tache wlh nayi nayi suzo muchi abinchi hiyana tache itakam wlh tana tsoran yayansu bazata iya zuwaba gaskiya kuma daga yauma a daki zata rinka zama to saurankuma dasukaga yayartasu taki zuwa suma sukache bazasu iya zuwaba dana nuna zan matsamusu sai suka fara kuka shine na kyalesu zahra’ma na tare dasu,
    Mai martaba yache ai daman nasan zaayi hakan ɗayanku yaje yakiraminsu
    Mikewa yusuf yayi yache bari naje da kaina na shawo kansu kila idansuka ganni zasuzo
    Wani kallan banza don ke wurgawa yusuf amma yusuf ko ajikinsa aryan kuwa sai hararan yusuf din yake amma yusuf baibi takansuba yayiwaje

    Da sallama yashiga palan lamrat kawai yasamu zaune tana kallo tsayuwa yayi yana kallanta kusan 5 mnt yana tsaye itakuma Sai kallanta take batasan da mutunba
    gyaran murya yaɗanyi
    Ta ɗago aiko tana kallansa tamike tawatsa a guje sai chikin ɗaki “. Dan ita atunaninta don ne dan bata iya rabesu
    Binbayanta Yusuf yayi har chikin dakin da sallama yashiga suna zaune kan gado suna ganinsa dukkansu suka rungume hiyana suka kame jikinsu waje guda banda zahra ” zahra kam nitsuwa tayi murya na rawa tache ina kwana yaya yusuf ga mamakin ta sai taji yache lfy baki sake zahra ke kallansa tun datake dashi bata tabajin ya amsa gaisuwar waniba a gidan nan amma yau ya amsa nata tab to kodai mafarki takene tayi nisa chikin tunani saitaji muryan shi yana faɗin
    Hiyana tashi kizo ” murya na rawa hiyana tache dan Allah kayi hakuri tana magana tana hawaye wlh nibansan ruwanka bane shiyasa na dauka amma dan allah kayafemin karkasake dukana bazanma sake zuwa wajen chin abinchinbama kaji
    Tana chikin magana kawai taji ansa hannu ana share mata hawayen dake gangarowa daga fuskarta da sauri ta dagokai murya na rawa tache..

    Pls more comments an share
    *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Page 16

    Duk karfin Izzata Book 1 Page 16

    Episode 16*

     

    Idanta ya sauka, a kan shahram dake tsaye fuskar nan tamkar an aiko masa da mutuwa babu alamar wasa a tattare dashi ” sakin diyana, tayi tana mai da nunfashi ” karisa shigowa ɗakin yayi yana faɗin get out yayi maganar yana nuna Aunty Maryam ” kallan raini ta tsaya take masa daga sama har katsa dogon tsaki taja, tanunashi da ɗan ya tsa tace kai karamin marakunya ni kake chewa nafita to kashirya karɓan hukunchi ” shikam Shahram ko ajikinsa, dan daman bajin hausa yakeba bare yaji me tache, sai ma kallan Zahra dayayi yace all of U follow me yana gama faɗin hakan yajuya ya koma bakin kofa ya tsaya ” wuchewa Zahra tayi taje ta taimakawa diyana tamike ” Aunty Maryam na tsaye suka raɓa gefenta suka wuche, tanasan ta damkoh diyana tachi gaba da bugu kuma tana tsoron yadda taga fuskar Shahram ba wasa hakan yasa ta fiche a ɗakin a fusache ” Shahram ganin sun mike sun nufosa yasa yayi waje, suka bi bayansa bai tsaye wajen motochin gidan suka nufa da kansa ya buɗe musu marfin family car suka shiga gaba ɗayansu ” shima shiga yayi yaja motar da gudun gaske nan take security dake tsaron gate suka wangale masa gate ɗin ” dagudu ya danna hanchin motar yayi waje doguwar titi yamiƙa dasu gudu yake sosai chikin ƙanƙannin lokachi suka isa wani katafaren asibitin DON dake kan titin zoo road ” suna parking ya fito yabuɗe musu motar bayan sun fito yayi gaba suƙa bishi a baya ” diyana daker take ɗinkisa kafa ” hiyana kuwa goshi sai jini yake, gaba ɗaya jinin ya wanke mata face ” kai tsaye office ɗin baban dr yanufa ” security dake tsaye a bakin office ɗin suna ganin Shahram suka shiga sara masa kamar sunsan juna buɗe musu kofar office ɗin sukayi suka shiga ” babban dr naganin Shahram yamike yana miƙa masa hannu, miƙa masa hannu Shahram ma yayi suka gaisa san nan yakora mara bayani a kansu diyana ” da sauri dr peter ya ɗauki waya yakira nursing ” nursing na shigowa dr peter yabata umar a kan ta tafi dasu diyana tabasu gado gashi nan zuwa yadubasu ” har ɗakin da a ka kaisu sai da Shahram ya bisu sai da ya tabbatar sun fara samun kulawar Dr san nan yafito ya nufi motarsu yatayar yanufi gd

    A bangaren Aunty Maryam kuwa tana komawa ɗaki ta ɗau’wayarta tafara kiran layin Aryan dan taji ko shiya aiko Shahram amma ba’a ɗagaba sai data kira miss call 10 amma ba’a ɗagaba san nan ta hakura ta ajiyewayar tana ta surutai wlh Aryan kazo gaɓar da bazan kyalekaba, ina ruwanka dan nabuge yaran nan toma waya faɗamaka ina bugunsu dole na binchiko ta ina kasamu lbr, haka dai take ta surutun’ta

    Yadda akayi Aryan yasamu lbr Aunty Maryam na bugunsu diyana har ya’turo Shahram

    Lokachin da Khalid ke magana da Zahra yaji tayi shiru sai hello, hello kawai yake amma ba amsa har zai katse kirankuma sai yaji ihu, nantake hankalinsa yatashi yamike yanajin yadda Aunty Maryam ke bugunsu, da sauri yanufi ɗakin Aryan rike da wayarsa yana zuwa yamikawa Aryan wayar ” muryan Aunty Maryam sukaji tana faɗin nizaki haɗa faɗa da ɗan uwana,” bai taɓa kirana a wayaba amma yau yakirani har sau 2 saboda ke ” a fusace Aryan yayi wurgi da wayar Khalid yamike, nan take fuskarsa ta Sauya idon nan suka chanza sukayi jawur dasu kamar an watsa barkono, wayarsa ya ɗaukoh sai huchi yake kiran layin Aunty Maryam ɗin yafarayi Amma shiru shiru har 3 time rai a ɓache yayi wurgi da wayar, yanufi hanyar fita ” da sauri Khalid yarikesa dan ya lura baya chikin hayyachen’sa inazakaje Aryan chewar Khalid ” Nigeria zanje mana ” dariyane sabo kuɓchewa Khalid amma sai yadanne yace ai kokatafi yanzu ba yanzu zaka isaba kafin kaje kuma duk abun da zai faru yarigada yafaru, yanzu dai kakira wani daga chikin security nan suje su kashe wutar, ai tun Khalid bai kai karshen magana ba “Aryan yanufi wayarsa da sauri ya ɗaukoh yafara kiran layin Shahram, ” Shahram nayin picking call ɗin ” Aryan yabashi umarnin yaje ka dakatar da Aunty Maryam daga bugun su diyana datake san nan ya ɗaukesu ya kaisu asibiti, yana gama faɗin haka ya katse kiran ya zauna a bakin gado ya dafe kai
    Kusa dashi Khalid yazo ya zauna ya sa hannu ya dafa kafaɗarsa zaiyi magana ke nan sukaji sallamar DON

    Kallonsu DON yake sosai kamar mai nazarin wani abu a fiskokinsu wuchewa yayi ya zauna a bakin gadon ” calmly yafara magana me yake damunka Aryan wan nan shine tambaya ta karshe da zanmaka idan baƙa faɗaminba kasan sauran ” kakalo murmushi dole Aryan yayi yana faɗin wai meyasa kakesan saka wani tunanin banza a zuchiyar kane, nifa nafaɗama kwanan nan ina yawan fama da chiwon kaine amma bari namaka mai kankat wlh Allah nikam bawani abun dake damuna, kawai jinake tamkar a takure nake banajin daɗin ƙasar nan narasa meke min daɗin banda haka wlh babu wani abun ” jinjina kai kawai DON yayi batare dayache komaiba, dan yasan iya gaskiya ke nan Aryan yafaɗa masa dan bayadda za’ayi Aryan yayi rantsuwa a kan karya kuma tabbas zai iya shedan Aryan a ko ina baya faɗin maganar da ba hakaba, to amma tabbas yana da damuwar da shi da kansa baisan da itaba ” ganin DON yayi nshirune yasa gaba ɗayansu suka dawo kusa dashi, dafa kafaɗarsa Aryan yayi yana faɗin baka yarda da magana ta bane ” juyo green eyes ɗinsa yayi kan face ɗin Aryan tare da ɗanyin murmushi gefen fuska nayarda mana na yarda da duk abun da kafaɗa domin baƙa taba yimini karyaba matsalar ɗaya a nan shine tabbas akoi abun da kedamunka wanda kai da kanka bakasan meneneba ” zuba musu ido khalid yayi yana tunani a chikin ransa gaskiyane DON kachi su nanka Safras indai wajen basirane kai karshene ba abanza mai marbata ya dage sai kai za abawa sarauta’ba, yayi nisa chikin tunani sai yaji Aryan nataɓasa firgigit yayi ya ɗago yana kallonsu duk sun zuba masa ido ” lfy Khalid kodai kaima kana da damuwane DON yajefo masa tambaya ” aa bani da damuwar komai nikam kawai tunanin meke damuna ɗan uwana nake ” nifa babu abun dake damuna na faɗa muku ” DON zaiyi magana wayarsa tafara ringing hannu yasa chikin aljihunsa ya fitar da wayar, sunan Sadiq yagani ta bayyana a kan screen ɗin wayar dogon tsaki yaja tare da jefar da wayar a kan gado ” da sauri Khalid yasa hannu ya ɗauki wayar yana duba wanene yakira DON yake jan tsaki haka ganin sunan Sadiq yayi a kan screen ɗin bai yi mamakiba, dan DON yaki ɗaukar wayar Sadiq dan kuwa Sadiq yayi aure ” murmushi yayi yana kokarin picking na call ɗin kiran tayanke chire pin na wayar yayi dayake yasan pin na wayoyinsu dan ba abun dasuke ɓuyewa juna
    Kiran layin Sadiq ɗin yafarayi wayar nafara ringing Sadiq yayi picking call ɗin yana faɗin yau wace rana nayi sa’a an ɗauki wayata ” dariya Khalid yayi san nan yace ai kasan shikam bazai ɗauki wayarkaba ” my Khalid ykk ” lfu lau ya amarya suhaima ” first dai yanzu albishirinka ” da sauri Khalid yace goro ” my baby ta haifamin baby boy yanzun nan daman shi nakira nafaɗa muku ” wow my man inatayaka murna bari nabawa Aryan ma yatayaka murna ” Khalid bai jira amsar Sadiq ba yamiƙawa Aryan wayar ” satar kallan DON Aryan yayi yaga bama su yake kalloba yasa hannu ya’karɓi wayar yawa Sadiq congrat san nan yace ga DON nan, kuma da gangan yayiwa DON ɗin haka dan yasan idan shi yamiƙawa DON wayar tofa dole zaikarɓa kuma gaskiya yanasan DON yataya Sadiq murna kodan halakchin da Sadiq ɗin yamusu, yanzu matarsa na aihuwa tun bai sanar da kowaba yafara sanar musu, aiko basaso dole zasu danne sumasa congrat ” karbar wayar DON yayi badan yasoba kawai dan bazai iya kwasale Aryan a idon kowa bane

    Congratulations inatayaka murna chewar DON ” da murna Sadiq yace thanks ykk y gd ” lfy yasu mom ” alhamdulillah Sadiq yabashi amsa ” ok kawai DON yace san nan ya katse kiran ya ɗago green eyes nashi yana kallonsu ” zuba mishi ido Aryan da khalid sukayi sosai suna kallansa Khalid na mamakin hali irin na DON ” kallon me kukemin haka ” murmushi Khalid yayi san nan yace kyau kamana mana shiyasa muke kallanka ” mikewa yayi yana faɗin to aiki yasameku kuda kukasanma me kyau yake nufi, yana gama faɗin hakan yayi waje ” dariya Khalid yayi sosai san nan ya dubi Aryan yana faɗin wai gaji DON baisan me kyau ba kajimin iskachi ” tsaki Aryan yaja yana faɗin kai ma kake biye masa ae, to daman inban da kai da neman magama ina DON yasan maka wani abu Wai shi kyau, ko kuma mara kyau ai shi inba Bom, bindiga, bullet,ba to bawani abun dayasani mai kyau ” mikewa Khalid yayi yana faɗin good night anjima kakira Shahram kaji ya ake chiki ” da sauri Aryan yafara lalubar wayarsa yana faɗin yanzu dai wani anjima kuma, wan nan ke nan

    Nigeria DON hospital

    Washe gari misalin karfe 8 dinaya na kwanche a gado da drip a hannu ” hiyana ma kwanche a nata gadon ansamata bandeji a goshi ” sai lamrat da amrat dake zaune gefen gadon hiyana, zahra kuma tana kan kujera plastic dake chikin ɗaki ” shiru sukayi gaba ɗayansu na tsawon lokachi ” sallama sukaji a bakin kofar ɗago kai sukayi gaba ɗayansu Shahram suka gani tsaye shida Dr Peter karisa shigowa chiki ɗakin sukayi suna tattaunawa ” mikewa Zahra tayi daga kan kujerar ta koma gefen gadon diyana tana kana tacewa Shahram, uncle have a seat ” thanks dear san nan ya zauna a kujerar ” miƙamasa takardar magani Dr Peter yayi san nan ya juya yanufi waje ” Shahram kuwa wayarsa ya ɗaukoh daga aljihun wandansa yafara kiran layin Aryan, har saida wayar takusa tsinkewa tukun nan a ka ɗaga
    Chikin girmamawa Shahram yafara magana hello sir good morning ” morning how are U ” am fine sir ” where is she da sauri Shahram ya mikawa diyana wayar ” hannu tasa ta amsa ta ƙara a kunne hello yaya Aryan ina kwana ” lfy y jiki ” da sauki ina Ammi dan Allah yaya Aryan kafaɗawa Ammi ta dawo dan Allah wlh tsoran Aunty Maryam nakeji, nikam Ammi tazo taje tasayar da shanun Bappa gaba ɗaya tasaya mana gida mukoma ” shiru kawai Aryan yayi yana sauraron’ta har ta kai karshe ” chikin sanyin murya yafara magana karki damu ae munkusa dawowa saura 9 days ne kawai kuma kinga nafaɗa miki Aunty farida zatazo next week idan Aunty farida na nan babu abun da Maryam zata muku, yanzuma bazan barku hakaba kinji bazata sake taɓakuba ” to shike nan Amma pls yaya Aryan ka haɗani da Ammi da Abba mana ” mezakiche musu idan na haɗaku ” zanfaɗamusu abun da Aunty Maryam tamana ” aa to bazan haɗakuba gaskiya ” ayya yaya Aryan kayi hakuri ka haɗamu tunfa shakaranjiya da Ammi ta kiramu ta wayar Aunty Zahra bamu sake maganaba, jiyama ina wanka naji su hiyana na magana da ita, kafin nafito kuma sungama magana pls ka haɗani da ita takarisa maganar kamar zatayi kuka ” to zan haɗaku amma saikin min alƙawarin bazaki faɗamusu komaiba gaisawa kawai zakuyi ” da sauri tace eh namaka alƙawari wlh bazan faɗaba ” ok to yanzu bawasu Zahra wayar bari naji yanasu jikin idan mungama magana sai na haɗaki dasu ” to kawai tace san man tamiƙawa zahra wayar ” karɓa Zahra tayi suka gaisa san nan tamiƙawa hiyana ” ansa hiyana ma tayi suka gaisa ya tambayeta jikinsu tace da sauki san nan yace to tabawa diyana wayar, miƙamata wayar hiyana tayi ” da sauri diyana ta ansa tana faɗin hello ” idan ruwan da a’kasamiki yaƙare Shahram zai maidaku gd, dan na chanza shawara zan ƙira mijin Aunty farida na faɗamasa ya bar Aunty farida tazo goɓe kinji ” to shike nan yaya Aryan amma kuma, kuyi sauri ku dawo dawuri tayi maganar a shagwaɓe ” meyasa kikesan mu dawo dawuri kodai kina san ganina’ ne ” eh ba kai kaɗaiba dukkan kuma inasan ganinku, gd babu daɗi dabaku nan ” shiru yaɗanyi kafin yace ok inshaa Allah munkusa dawowa ae ” to Allah ya dawo daku lfy tana gama faɗin hakan bata jira amsar shiba tamiƙawa Shahram wayarsa ” koda Shahram ya ansa wayar yasa a kunnensa, sai yajiyo Aryan na faɗin nima inakewarki my sister ina kewar coffee ɗinki mai daɗin nan” a sukwane Shahram ya miƙa mata wayar kallansa diyana ta tsaya take damamaki batare da ta ansa wayar’ba ” mikewa Shahram yayi yazo har kusa da ita yasa mata wayar a kunne ” muryan Aryan taji yana faɗin sister ba kyajinane ” hannu tasa ta ansa wayar tana faɗin inajinka yaya Aryan “to ae naji inata magane kinyi shiru ” eh dazun banji me kafaɗa’bane ” ok to shike nan Shahram zai jira idan ruwan da a’ka ƙaramiki ya ƙare zai mai daku gida, nurse ɗaya zata biku tachigaba da kula daku ” to yaya Aryan makaranta’fa ” makaranta sai kunji sauri ba naji kun gama exam bama ” laaa waya faɗamaka to ” zuchiyata mana itace tafaɗamin ” to zuchiyar’ka tafaɗi gaskiya mungama ” to bazaku sake zuwaba sai ranar da za’ayi hutu yanzu kam ku huta kuyi jinyar jikinku ” to ka haɗani dasu Ammi mana ” sai da daddare idan kun koma zankira layin Zahra na haɗaku amma karki karya alƙawari’fa ” to bazan karyaba ” ok sai munyi waya anjima koh, yana gama faɗin hakan ya katse kiran ” jin ya katse kiran yasa ta mikawa Shahram wayarsa,

    Sai 12 :45 a ka sallamesu daga asibiti hiyana dai ba a chire mata bandejin’ba, saboda sosai taji chiwo a goshinta dan har ɗinki 6 a kamata awajen ” Shahram dakansa yabuɗe musu motan suka shiga tare da nurse ɗaya kai tsaye gd Shahram ya wuce dasu ” yana parking yafito ya buɗemusu motar suka fito, daka gansu kaga wayanda suka sha wahala, har ɓangaren Ammi Shahram ya rakasu sai dayaga shigansu palo tukun nan yajuya yakoma bakin gate
    Suna’shiga ɗakin’su suka nufa wanka suka farayi ɗaya bayan ɗayan suka sanya dogayen riguna abaya baki ” hiyana kam dakyar tayi wankan saboda zafin da kanta ke mata shiru suka zauna ” jim kaɗan Zahra tamike tana faɗin ina wayata bari nakira masu aikin sukawo mana abinchi nanfa tashiga nemar wayar’ta, chan gefen drawer ta gano wayar, da sauri ta ɗauka ta duba taga wayar ta mutu ba charji jonata a charji tayi san nan ta kunnata tafara neman layin binta
    Bugu ɗaya binta ta ɗaga Zahra tabata umarni kan ta kawo musu abinchi ”

    Chikin kankanin lokachi saiga binta tashigo da sallama, hannunta ɗauke da babban trey mai dauke da kulolin abinchi da plate a kai a tsakiyar ɗakin taajiye san nan ta gaidasu tafita ” saukowa kasa zahra da diyana sukayi ” Zahra ta dubi nurse ɗin tace kizo kichi abinchi sister, bamusu itama nurse ɗin ta saukoh ” kuma kunajiran saina kirakune? Zahra tayi maganar tana kallansu lamrat ” jiki ba kwari suka tsaukoh, ” Zahra da kanta tayi sarving na kowa kallan, hiyana dake zaune tayi ke bazaki zo muchi’bane ” Aunty Zahra nifa bazan iya chin komai”ba dan kaina chiwo yake min sosai ” aa hiyana karmuyi haka dake kawai ki saukoh ki daure kichi ko kaɗanne ” hiyana badan tasoba haka ta saukoh suka fara chin abinchin, jitake kamar magani takechi dan bakinta ba tes ko kaɗan
    ” Bayan sungama chin abinchi ne nurse ta basu magunguna san nan suka haye gado ” zahra a ita da hiyana a gadon’su, dayana da amrat da lamrat suma a gadon diyana ” nurse nasu kuwa suka kaita ɗakin’su amrat, suna kwanchiya ba jimawa barchin wahala ya ɗaukesu

    SAUDIA

    Wayarsa ya ɗauka yafara neman layin Aunty farida ringing ɗaya ta ɗauka ” hello my bro ” na’am lovely Aunty ykk ” lfy lau yasu Abba ya shirye shiryen dawowa ” alhadulillah ina junior ” yafita da baban’sa ” ok Aunty farida daman ina san magana da’kene “ok to inajinka ” sonake kije gd gobe ” ae sai ranar Monday zantafi amma meyasa kakesan naje dawuri ” Aryan zai sake magana idonsa suka sauka chikin green eyes wato DON tsaye yake a bakin kofar shigowa betroom ɗin, sanye yake da suite ash colour, bakaramin kyau yayi yatara gashin kansa ya ɗaure, fuskar nan tamkar an aiko masa da mutuwa ya harɗe hannu a kirji ya zubawa Aryan green eyes nan nashi ” hello bro baka jinane ” sorry lovely Aunty inajinki wlh hankalina yatafi wajen DON ne ” ok to injinka meye dalilinka nacewa naje’gidan gobe ” babu komai kawai dai inasan kijene ” jinjina kai Aunty farida tai kana tace ok badamuwa zanyi magana da dadyn junior idan yadawo ” ok kawai Aryan yace batare daya jira kozatace wani abuba ya katse kiran ”
    dawo da kallansa yayi kan DON yafara magana to meya tsayar da kai kuma a bakin kofa ” dogon numfashi DON yaja tare da sauke ajiyar zuchiya a hankali yafara takowa izuwa chikin ɗakin gefen gado ya zauna yana fuskantar Aryan ” ayayin da Aryan ɗinma shiyake fuskanta shiru sukayi na ɗan lokachin suna kallan juna ” DON ne ya katse musu shirun dacewa munyi magana da Aunty farida tace tafara magana da Abba a kan maganar sarauta amma kanaganin Abba zai chanza ra’ayi kuwa ” gaskiya dakamar wuya Aryan yabashi amsa a takaice ” mikewa yayi ya kwanta a gadon yana kallan Aryan ɗin batare dayace kalaba ” Aryan kuwa dayaga kallanda DON yake masa kamar kallan tuhumane, sai yamiƙe yana faɗin bari na dubo khalid yanufi hanyar fita ” meyasa kake guduna ne yanzu Aryan ” chak Aryan ya tsaya kirjinsa na bugawa da karfi a hankali ya juyo idansa suka sauka chikin na DON dan kuwa ya tsaresa da ido sosai yake kallansa ” meyasa zanrinƙa gudunka kuma ” wan nan dai kai kasan dalilin amma dai ninasan ba haka kawaiba ” nibawani gudunka danake yama za’ayi kace ina gudun kane bayan tare muke komai, har chin abinchi, wanka da barchine kawai ke rabamu, ” ok to yanzu dakamike ina zaka, eh bawai bani da aikin yi banefa nabari nazo wajenka muyi hira amma ko kara bakaminba kamike wai barika dubo khalid
    Shiru Aryan yayi yana tunani kuma yagane kuskuren dayayi nacewa bari yadubo Khalid dan haka sai yajuya ya dawo chikin ɗakin kusa da DON ɗin yadawo ya zauna yana faɗin am sorry bro ” jinjina kai kawai DON yayi batare dayayi maganaba ” shiru sukayi gaba ɗayan’su kowa da abun dayake tunani

    YOLA NIGERIA ✈️

    Zaune take a tsakar gida ta buga uban tagumi sai tunani take tayi nisa chikin tunaninta taji ana Sallama a kofar gd, amsa sallahar tayi san nan tamike ta ɗauko mayafi ta rufa a kanta tayi waje, tana fita tachi karo da bello ” aa Bello kaine mai doka sallama haka to ya akayi ” eh nine inna inawuni ” lfy meyakawoka ” daman goggon’su hiyanace wadda ta ɗaukesu ta aiko wani yazo yafaɗamin intattara dabbobin’su hiyana na haɗa da nawa narinka kula dasu bayan Sallah zasu zo ” wani tsalle inna tabuga tana faɗin banga uban daya isa ya taɓa dabbobin nan ba wlh ” to inna ae’ga yan sakon nan basu tafiba sai kifaɗamusu ” juyawa inna tayi tana kallan inda bello ke nunawa, wasu sojoji taga guda 3 sanye da kaki, fuskar nan tasu babu alamar wasa aguje inna takwasa tayi chikin gida ” juyawa bello yayi yanufi garken dabbobin yana faɗin muje ” bin bayansa sojojin suka har zuwa wajen dabbobin ” ƙirga dabbobin suka shigayi bayan sun gamane “bello yadubi sojan yace a nawa lissafin dukka dabbobin banda kaji, da zabbin, nan iya shanu, da raguna, da awaki, 1007 ne amma kufa nawa kuka samu a naku lissafin ” ɗayan daga chikinsu yace 1005 nasamu dayanma yace 1005 ” kai kumafa bello ya tambayi ɗayan da baiyi maganaba ” amsata iri ɗayane danake 1007 shiru sukayi chankuma Bello yace to kozamu sake ƙirgawane ” aa basai mun sakeba a barshi a lissafinka domin ina da tabbachin shine dai dai, dan kafimu iya ƙirga dabbobi, nasan kana kirga wayanda sukafi wan nan yawa to ni da kyarma na iya irgawa wlh sai rikiitani suke ” murmushi kawai bello yayi san nan yace to muje wajen kajin nan kuma ” no kaji da zabbi madam tace ka ɗauka bata buƙata ” nan take fara’a ta bayyana a fiskar bello sai godiya yake zubawa har suka fito ” sojojin sukaje suka shiga motar’su suka kama hanya ” bello kuwa da sauri yajuya yanufi gd dan yafaɗawa innnar’sa abun dake faruwa

    KANO STATE

    Misalin karfe 4 hiyana ta farka daga barchi tana duba time da sauri tafa tashin’su Zahra dan ko sallar azhar basuyi’ba, koda suka tashi sai faman yamutsa fuska suke ” hiyana naganin sun tashi tamike tanufi toilet danyin alwala zahra kuma wayarta tachiro daga charji ta kunna wutar screen ɗin nanfa tasamu miss call kusan 17 yaya Aryan 4 miss call, yaya Khalid 3 miss call, Ammi 3 miss call, mai Martaba 5 miss call, yaya Yusuf 2 miss call, ” tunani tashiga’yi wazata fara kira saiga wata kiran tashigo tana dubawa taga yaya Aryan , da sauri tayi picking call ɗin tana faɗin hello yaya Aryan ina wuni ” daga ɗayan ɓan garen Aryan yace lfy ykk yajikinku ” da sauki barchi, mukayine shiyasa kakira bamu ɗagaba ” ok ina sauran’suke ” miƙawa diyana wayar Zahra tai” ta ansa taba faɗin wanene ” idan kinsa a kunnenki ae zakiji koma wanene Zahra tabata amsa ” kara wayar tayi a kunnen’ta tana faɗin hello ” ya jikin naki ” laaa yaya Aryan daman kaine jiki ba sauki gaskiya dan har yanzu zafi kaina da kirjina yakemin sosai ” saura kaɗan ya kwashe da dariya amma sai ya danne yace to inshaa allah zai daina yimiki zafi kinji ” diyana zata sake magana sukaji an turo kofar ɗakin nasu da farfi anshigo a razane suka ɗago ganin Aunty Maryam yasa diyana fasa…✍️

     

    Pls more comments an share 🙏

     

     

     

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

     

    *

     

  • Duk karfin Izzata Book 1 Paga 5

    Duk karfin Izzata Book 1 Paga 5

    Episode 5*

    DON

    Misalin karfe 5 na yamma jirginsu yayi landing a malam Aminu information Airport kano, wasu dan kare dan karan motochi 5 sukazo ɗaukansu ga motochi 3 chike da sojoji, basu wani ɓata lokachi a chikin jirgin ba suka fito tare suka jera, sai wani kara ɗaure fuska suƙe da ka gansu kaga wayan da akawa zuwa dole, musamman DON nashi daban ne, Abdol da Shahram suna biye dasu a baya,rike musu da trolley sojojin nan na ganin fitowar su suka jinro daga nasu motochin suka nufe su, Fahad na ganin fitowar su ya nufesu da sauri, yana ɗan murnushi hugging na DON yaje yayi yana faɗin “Wellcome back bro, hannu DON yasa yayi taying ɗin yana faɗin “missed U my blood “missed U too yayi maganar yana zare jikin sa daga jikin DON, yajuya yayi rungume Aryan ma, yana faɗin yaya Aryan nayi kewar ku sosai, rungume sa sosai Aryan yayi yace “nima nayi kewar ka sosai my blood, ganin DON yayi gaba ya barsu ne yasa Fahad ya saki Aryan da sauri sukabi bayan DON wajen motochin nasu suka nufa,nan take su Haidar suka fara musu sannu da dawowa ko kallan in da suƙe DON bai yiba bare su saran zai amsa musu, ya shige motar ya zauna yana yamutsa fuska, Aryan ma shiga mota yayi riƙe da hannun Fahad sai da suka zauna san nan ya dubi kannen nasu yace “yauwa to ku shiga mota muje gd koh sai mu gaisa a chan zaifi, da sauri suka koma chikin mota, drivers su kama motochin key da gudun gaske suka bar Airport ɗin gudu suƙe shararawa sosai a kan mikakkiyar titi, sai da suka kusa da bakin gate ɗin gida suka rage gudun motochin, batare da ɓata lokachi ba security daƙe tsaron gate ɗin su wangale musu gate ɗin a nitse suka kutsa chikin gd, kai tsaye parking space suka nufa suna kashe motochin, Shahram da Abdol suka fito daga nasu motar da gudu su kazo suka buɗewa DON da Aryan kofar motar, a nitse DON ya zuro kafafun’sa waje kafin ya fito gaba ɗaya bai bi ta kan kowa ba yanufi ɓangaren sa, Aryan ma ɓangaren sa yanufa riƙe da hannun Fahad suna tafiya suna hira, Yusuf ya karɓi trolley DON daga hannun Abdol yabi bayansa da shi Ahmad ma ya karɓi na Aryan daga hannun Shahram ya nufi ɓangaren Aryan ɗin, su Haidar kuwa kowa yakama kansa yayi part nasa

    Ammi na zaune akan kujera a palan’ta tasha kwalliya chikin wata ɗankarekiyar lace baki da ratsin ja mai shegen kyau ga wasu gwala gwalan data zuba a wuya da hannu ta,ba karamin kyau tayiba inka ganta kace bata,wuce 25 years ba, Aunty farida tashigo da sallama ɗauke a’bakinta, da fara’a Ammi ta amsa mata sallamar, shigo chiki palon tayi ta zauna saman sofa mai zaman mutun 2,tana fuskantar Ammi “feeda dayake haka Ammi ke kiran Aunty farida feeda,ina junior yake “Junior yana wajen mardiya chewar Aunty farida ” ok kawai Ammi tace tana kallan face ɗin Aunty farida “Ammi magana nakesan muyi dan Allah “ae feeda tun shigowar’ki Na fahimchi hakan, badamuwa ina jinki “Ammi daman, magana che a kan price, tun!bata kai karshen maganar ba Ammi ta ɗaga mata hannu, tana faɗin a’a feeda, kinsan dai bazan saka bakina a maganar bako,babu ruwana, dan kuwa kinsan mai martaba idan yayi magana baya chan’zawa “Ammi mun san Abba idan yayi magana baya sau’yawa, amma ae ke ki nasashi ya sauya magana koh, dan Allah Ammi, ki samana baki pls takarisa maganar kamar zatayi kuka “aa feeda babu ruwa’na wai ni ina ruwa da wani prince, ae wan nan ɗan Ummi ne ba ɗa naba kije kisamu Ummi ita tashiga masa amma ban dani “dan Allah Ammi kinfasan Abba yafi sauraren maganarki fiye da kowa a gidan nan” Feeda kin dai san in nache bazanyi abuba tofa bazanyin bane koh dan haka kibar maganar kawai,”to shike nan Ammi na barta barinaje namusu sannu da zuwa “baki Ammi ta taɓe tana faɗin eh lallai feeda ɗaure wa karya gindi,su da suke kannenki basu zasuzo su gaida kiba ke zakije ki gaida su lallai yaran nan suna abun dasu ka gadama
    Aunty farida tamike tana faɗin kai Ammi kedai babu ruwan ki tsakanina da yan uwana ko inche yayyuna dan yanzu nabasu girma takai karshen maganar tana kokarin fita daga pallan bata tsaya ta jira amsar Ammi ba ta wuche abunta tana fita tayi part ɗin DON

    Da sallama tashiga palan nasa babu kowa, kai tsaye betroom ɗin sa tanufa, yana tsaye gaban mirrow yana gyara gashin kansa,sanye yake da bakar jallabiya, da alama wanka yayi, jin sallaman ta yasa yaɗago green eyes nashi ta chikin miron yana kallan’ta, batare da ya juyo ba “yace Aunty babba yanzu nake tunanin inje in ganki, kafin inyi barchi
    Harara wasa Aunty farida ta wurga masa tana fadin “daka ganniba dole kafaɗi haka nasan da banzoba ba zuwa zakayi ka nemeni’ba, slowly ya juyo ya zuba mata green eyes nashi nan kafin yace “a’a Aunty farida ae kema kinsan dole na nemeki

    Karisa shigowa chikin ɗakin tayi tai, a bakin katafaren gadansa dake shinfiɗe da White bet shit ta zauna tana faɗin,”to ya hanya “Tafiyar da bada san ranmu mukayotaba Tafiyar dole,ya kae karshen maganar yana ɗaure fuska , guntun murmushi Aunty farida tayi kafin tace, “hmmm yanzuma nagama magana da Ammi kafin nazo nan, kara ɗaure fuska yayi yana faɗin “ai dama baki mata magana ba, da baki ɓata bakin ki bama dan nasan baza ta saurare mu ba jinjina kai Aunty farida tayi kafin tache,mudaiyi addua karkadamu inshaa allah komai zaitafi yadda kakeso,tana kae karshen maganar tamike,bari na dubo Aryan, batare da ta jira amsar saba tayi waje dan tasan ba amsa war zai yiba,”juyawa yayi yachi gaba da abun daya’keyi

    Tana fita ɓangaren DON tanufi ɓangaren Aryan bakin ta ɗauke da sallama tashi palon babu kowa a palon sai sanyi A.c dake ratsa jikin betroom nashi tanufa, sallama tayi a bakin kofar kafin ta tura kofar tashiga kwanche ta same sa akan katafaren gadansa,idon sa a lumshe da alama barchi,yafara ɗaukan, jin an taba kofar ne yasa ya buɗe idon’sa da kyar, yana ganin ta ya dan saki fuska yana da kyar ya buɗe baki da murya irin na mai barchi yace “Allah ya barmana ke aunty mu wlh naso nazo,na dubaki amma barchi ya hanani, murmushi tayi tana faɗin “an dawo lfy my tagar “lfy lau lovely Aunty “to bari na kyale kayi barchin ka daman dai ina san inzo inji an iso lfy ne tun da lfy ba wata matsala ayi barchi lfy sai mun haɗu awajen chin abinchin dare ahuta gajiya,tana kae karshen maganar ta juya tanufi waje juyawa yayi shima yana fuskantar gefen dama yachigaba da barchin daya fara”

    Misalin karfe 8 nadare gaba ɗaya family Abba sun haɗu a palon, dan chin abinchin dare, banda Aryan DON da kuma Fahad, sun zauna shiru suna jiran fitowar Abba, Ammi che ta katse musu shirun da chewa “nikoh meyasa mairo da salma basu zo bane kodai basu da lbr meeting martaba ya shirya
    A tsiyache Aunty amarya tace ke Aisha kidaina ɓatamin su nan yarinya, kuma ina ruwanki da zuwar ta inba muna furchiba
    “haba Aunty amarya daga tambaya chewar Ummi “ke Ummi baa kasa dake ba idan kemaɗin muna furchinne sai naji akule Aunty mardiya tache “a’a wlh ya isheki haka gaskiya bazaki zauna kina zagin iyayen mu, a gaban mu’ba tayi maganar tana nuna Aunty amarya ta hannu, hannu Aunty farida tasa ta ɗan buge bakin Aunty mardiya, tana faɗin to ke ina ruwanki ae dukkan’su iyayen’mune wan nan fadar’sune tsakanin’su
    Umar ya ɗago rai a ɓache yana faɗin “to ae gashi muma Aunty mardiya rashin kunya kike neman kiyiwa mahaifiyar tamu, A’kule haidar yache “haba Umar kai bakaji abun da Aunty amaryan ke faɗe bane, dafe kai Khalid yayi yana faɗin, to ya isa haka ae kuyi shiru, amma ina ba wan da ya saurari Khalid sunki yin shiru wan nan ya faɗa wan nan ya faɗa abun hat’tafara zama kamar faɗa
    Dafe kai kawai Ammi da Ummi sukayi suna kallan ikon Allah kowa kokari yake yakare ma haifiyar’sa wan nan abu dame yayi kama” sai faman kache na che suke abu har ta fara zama kamar faɗa

    Kamar daga sama sukaji gyaran murya daga bayan su nan take, sukayi tsit dan kuwa ko basu juya ba sunsan mai wan nan voice ɗin tsaye yake a bakin kofar shigowa palon, yazura hannu a aljihun wandan,sa’ yana kallon su fuskar nan tamkar batasan menene dariya’ba a daure take tam, a nitse yafara takowa izu chikin palon,wajen table ɗin yanufa,da sauri Haidar yamike, yaɗan jamasa kujeran zaman, baya tayadda zaiji daɗin zama gaba ɗaya matasan suka mike,ban da Khalid da Aiman da Yusuf jiki na kerma sukafara “faɗin sannu da fitowa yaya Aryan zama yayi batare daya amsaba yana binsu da ido jiki ba kwari suma suka koma suka zauna, murya na rawa Zahra tache “sannu da dawowa yaya Aryan
    ko kallan in da take bai yi ba bai kuma amsa sannu nata ba ita ma,nan take kowa a chikin su yasha jinin jikin sa kallon fiskokin su yake sosai kamar mai karantar wani abu a tattare dasu

    “me za’a zubamaka ne Aryan Ammi ta tambaya tana kallan fiskar sa, sai lokachin yadawo da kallansa kan Ammi kana yaɗan saki fuska calmly yace “abun daya dache kawai “ok to bintu kuzuba masa ferfesu kayan chiki da fraid rice Ammi tabawa masu aikin umarni, da sauri suka fara zaran plate dan su zuba masa,hannun su har rawa yake dan tsoran sa da sukeji suna kokarin zuba masa abin chin’ne
    Aunty amarya ta daƙa musu tsawa “bashi zaku zuba masaba dan babu wanda ya isa ya zabawa ɗa na abun, da zai chi sai ni dana haife’sa kowa a gidan nan yana da nashi ɗan ae to kowa ya kula da nashi ba ruwan shi dana wani,dan haka tuwon shinkafa zaku zuba masa
    Shiru yan aikin sukayi sun rasa umarnin wa zasu bi “kamar daga sukaji Aryan yana faɗin ku bar’shima kawai am ok, Aunty amarya zatayi magana sukaji takun tafiya ta bayan su dukkan su suka juya ban da Aryan, tafiya suke chikin kwanchiyar, hankali sun jero kamar ,sanye suke chikin jallabiya dukkansu Fahad bakin DON kuma fari tas, fiskar sun nan dukkansu babu wasa a ɗaure taku suƙe irin na chikakkun maza, kamar wasu yan biyu haka suka jero dan dai kawai DON yafi Fahad tsawo dakuma chika sai kuma kalar kwayar ido daya ban ban tasu Fahad kwayar idon sa baki ne DON kuma green amma ban da haka kaman’nin su ɗaya

    A take palon yayi tsit suka kara nitsu wa dan duk gidan idan ka chire Abba Ammi da Ummi Aunty farida sai Aryan to kowa na gidan tsoran DON yake, har Aunty amarya tsoran sa take kamar me dan tasan DON ba wasa ba’a kawo masa wargi yanzu zai sumar da mutun, bakaramin tsoransa Aunty amarya ke jiba, da sauri Haidar yamike ya gyara musu kujerar da zasu zauna, a nitse suka zauna slowly DON ya ɗago yafara gai da iyayen nasu, da fara’a suka amsa masa, da sauri kannen nasu suka fara ɗaga masa gaisuwa, bai amsa gaisuwar kowa daga chikin su ba sai ma wayar sa daya chiro daga aljihun sa yafara latsawa
    “prince me Za’a zubama,Ummi ta tambaya tana kallan face nashi, shiru ya ɗanyi kamar mai tunani sai kuma ya dawo da kallan sa kan Aunty farida,batare dayayi magana ba, Aunty farida ta gane me yake nufi da sauri tace,da masu aikin “ku zubawa kowa ferfesun kaji da chips kawai
    Chikin sauri, suka fara zaran plate suna zubawa suna mika musu

    A hankali Aryan ya ɗau spoon yafara shan ferfesu, wani kululun bakin chikine ya tokare wa Aunty amarya makoshi tana san tayi magana tana tsoran DON a zuchiyar ta take faɗin wai komai farida tace a gidan nan ko, basaso sai sun yarda, gashi dai ni tana haifi yaran nan amma bani da wani iko da su, maganar farida tafi nawa muhim manchi dole nayi maganin abun wlh bazayyiwu’ba

    Da Sallama Abba yashigo palon yana sanye chikin jallabiya fara tas kai tsaye table ɗin yanufa,tun bai karisa zama ba suka fara gaishesa,Sai da duk suka gama gai’dashine ya haɗesu yabasu amsa ɗaya da sauri bintu mai aiki ta rari plate ta zuba masa abinchin zaɓin Aunty farida wato ferfesun kaji da chips
    Tunda Abba yaga irin abinchin’ne a plate ɗin kowa dake wajen yagane zaɓin Aunty farida ne dan haka shima karba kawai yayi yafara chi

    (sai yanzu nasan a inda yan gidan suka gado rashin magana dan kuwa shima Abba baya magana shiru shirune)

    Shiru kake jin palan ba mai magana sai karan spoon kawai zakaji,da sautin A.c dake tashi

    Bayan sungama chin abinchin ne DON ya mikewa ya nufi hanyar fita daga palon, harya kai bakin kofar sai kuma ya juyo yana faɗin “dukkan ku mazan nan kusameni a ɗaki,ke kuma Zahra karfe 10 dai dai ina bukatar ganin ki bai jira amsar su ba yayi waje, da sauri suma suka muke sukabi bayan’sa
    Suna fita Abba ya dubi su Ammi yana faɗin “sun aikata wani abun da ba dai dai bake nan,Ammi dai shiru tai bata bashi amsaba hakama Ummi
    aunty amarya che tache “zagina mana sukayi, Shiru Abba yayi dan yasan halinta sarai yanzu haka ita ta takalo faɗan “ranka shidade inasan magana dakai chewar Ammi, Abba zaiyi magana
    Aunty amarya tarigashi dache’wa “to ae yau ba ranar ki bane bake kike dashi ba sai ki bari sai yadawo dakin ki, shiru Ammi tai dukkansu ba wanda yasake magana

    DON na shiga dakin sa ya zaune a gefen katafaren gadon sa yana jiran kannen nasu
    Da sallama suka shigo gaba dayan su
    Aryan ya wuche ya zauna a kusa da DON a bakin gadan, shi kuma Fahad hayewa yayi kan gadon abunsa ya kwanta ya dauko wayarsa yafara latsawa,domin kuwa yariga da yasan dalilin kirannasu to shi baya chiki maganar

    Dukkan su zama sukayi a saman sofan dake ɗakin Khalid ma agefen gadon yazauna suka sa DON a tsakiya shida Aryan ryan
    Almost 10mnt DON bai che dasu komai ba kamar ma baisan da zaman su a ɗakin ba, shiru sukayi suna tunanin me yasa ya kira’su kodai yaji abun daya faru a palo ne calmly yafara magana “daga yau sai yau duk wanda ya sake,idan iyayen mu suna magana a tsakanin’su yasa baki kunsan me zai biyo baya ina ruwan ku da faɗan su
    Shiru sukayi bawanda yache kala
    DON yachi gaba dace wa “last warning nake muku idan kuka bari nasake kama’ku da irin wan nan dabiar bama sai nayi magana ba, kai Haidar da kai da Umar kuje wajen kwallo bayan nan kufara frog jump ina zuwa ya kai karshen maganar yana kallansu Haidar da Umar ɗin

    mikewa sukayi suka fita jiki ba kwari suna fitowa Umar ya dubi hadar yafara magana “mun shiga uku wlh, yau zamu gane kuren’mu wayyo sheidan baka mana adalchi ba daga dawowar big bro muzai fara yiwa hukunchi ke nan wayyo Allah,
    Chikin nar kewar murya Haidar yache “waima daman meyakai’mu shiga fadar matane yanzu gashi zamu karbi hukunchi,wlh ni nasan yau sai munkasa mikewa da kafafun’mu
    Haka’dai sukayi ta surutai suna tafiya har suka isa wajen kwallan dukawa sukayi suka fara frog jump ɗin.

    Miƙewa Yusuf Aiman Ahmad sukayi suka musu sai da safe suka fito nuka kowa yanufi part nashi ɗakin yarage daga DON Aryan Khalid Fahad, shiru suka zauna kowa na latse latse a wayar sa almost 10mnt Khalid ma yamiƙe ya musu sai da safe yayi waje, Khalid na fita Aryan ya ajiye wayarsa ya dawo da kallon sa da kuma hankalin sa kan DON yafara magana “zanje nayi magan da Aunty amarya batare da DON ya ɗago ba yace “a kan me fa “akan abun daya faru dazun a palo mana kasan komai kaji komai da kunnen ka,kasan wayafara taɗa rikichin to yakamata mu dakatar da abun tun bai yi nisa ba sai lokachin DON ya ɗago green eyes nashi yana kallan Aryan ɗin kafin yache “a’a ka kyaleta to idan ma kaje me zakache mata itafa ta haifemu bamu muka haifetaba dan haka kabar abun zamu’san abunyi a kai “a’a DON duk da ita ta haife mu amma ai idan tana kuskure addini ya halakta mana mu mata gyara,amma tun da kache in bari to shike nan zanjira matakin dazaka ɗauka
    DON bai sake magana ba shiru suka zauna na dan lokachi kafin Aryan yamike ya musu sai dasafe yanufi waje
    juyowa DON yayi yana kalli Fahad dake kwanche yana latsa waya “kai wai a nan zaka kwana ne, da sauri Fahad yace “a’a yanzu zan tafi ya kai karshe maganar yana miƙewa, “sai da safe yache da DON batare daya jira amsar DON ba ya sauko yanufi waje

    Karfe 11 nadare

    Sau kowa yake a nitse yana sanye da kayan barchi dogon wando da riga mai dogon hannu yan shara shara marasa nauyi white colour jikinsa sai kamshi yake, ya tara gashin kansa ya ɗaure a baya sosai kayan suka fito masa da surarsa na chikakke kuma jarumin namiji mai ji da lfy da karfi,taku yake irin na jaruman maza masu jini ajiki, kofar baya ya buɗe ya fito waje kai tsaye wajen kwallo yanufa

    Frog jump yasamu sukeyi da kyar da kyar suƙe iya ɗaga kafa duk sun galabai ta sama sama suke numfashi sun jiƙe sharkaf da zufa
    da kak’kausar murya yache “kutashi ku tafi ɗaki a gala bai che Umar yace “sorry bro wlh bazan iya miƙewa ba da kyar Haidar ya iya buɗe baki shima yace “wlh yaya prince nima bazan iya tashiba
    Chikin tsawa DON yafara magana “zaku kwana a nan ke nan, zaku tashi kutafi ɗakine ko sai nayi kwallo daku ai tun bai kai karshen maganar ba suka tattara sauran karfinsu gaba daya suka miƙe, har jiri suke gani rungume juna sukayi suna ɗungisa kafa da kyar da kyar suka nufi hanyar part nasu, shi kuma DON ya juya ya koma ta in da ya fito

    jimeta yola

    Jama’a ne zaune a kofar gidan su diyana suna karɓan kai suwar rasuwar bappa chikin gida kuma matane zaune suna yan koke koken su, hiyana diyana Amrat lamrat kuma suna zaune a kusa da rafe kasan wani bishiyar mangoro suna kuka, duk fuskar su ta kunbura kuka suke sosai kamar ransu zai fita chikin kuka da dashewar murya diyana ke faɗin “shike nan bappa ya mutu ya bar mu munshiga uku ina zamusa ranmu wayyo allah “da kyar hiyana ta iya buɗe baki muryan ta duk ya dashe saboda kukan data sha tafara magana “a’a diyana ki daina chewa munshiga uku gaskiya bamu shiga uku ba tun da mun rike Allah inshaa Allah, Allah bazai kyalemu muchigaba da wulakantaba chikin shessheka lamrat tace “eh hakane Aunty hiyana addua kawai bappa ke bukata, duk kansu suka haɗa baki su kache Allah yajikansa da rahma
    Diyana tache “hmmm jiya fa Bappa yarasu amma baza abar’mu mu dan huta ba muji da rasuwar bappa ba inna tace, dan Allah yanzu muji da wanne muji da rasuwar Bappa ne ko kuma muji da ɗebo ruwa
    Mikewa hiyana tayi tana faɗin “kutashi ma mukarasa ɗeban ruwan nan kar inna ta buge’mu da kyar suka mike suka nufi rafin suna rike da cups a hannunsu
    Sun ɗebo ruwan zasu wuche ke nan sai sukaji muryan yaya bello na kiran’su daga chikin gona, chikin gonar suka nufa, a zaune a inda yasaba zama suka same sa ga tulu sababbi guda 4 a gabansa
    A gaban sa suka duka suka gaidashi ya amsa chikin faraa san nan yamusu taziyar mutuwar bappa tare da adduar Allah ya jikansa suka amsa da ameen, kana yache ku ɗauki tulu nan nan dasu zaku rinka deban ruwa dan ku nasaya, duk da kukan rasuwar bappa dasuke hakan bai hana’su yin murna da ganin tulun ba ɗauka sukayi suna murna sai godiya suke masa suka fito gonar suka nufi rafi, ruwa suka ɗeba a sabon tulun su sai murna suke,suka nufi hanyar gida

    One day later

    yau Bappa yachika kwana uku da rasuwa, jama’a sun watse babu kowa a kofar gidan kowa kama kansa

    diyana hiyana da lamrat sunbar amra a gida tana tikar aiki duk kansu suna dauke da tulun da yaya bello yasa musu suka nufi rafi suna tafiya suna yar hirarsu
    Diyana tache “wai ya akayi inna batayi magana akan tulun nan bane Girgiza kak hiyana tayi tana faɗin “hmmm ai bata lura bane inda ta lura ai da saita tambayi waya bamu ko kuma ma ta fasasu
    Lamrat tache “to yanzu idan inna ta tambayi waya bamu tulun me zamu’che mata,dogon tsaki diyana taja kafin tace “sai muche muma ba mu san mutumin daya bamu’ba,yaga muna ɗeban ruwa da kofine sai yabamu “yauwa diyana gaskiya kin kawo shawara daman sai tunani nake idan inna ta tambaye mu me zamu’che chewar hiyana,tayi maganar dai dai lokachin da suka iso bakin rafin ruwa suka debo,a tulun suka juya suka nufi hanyar gd,

    “hiyana wai yan zu haka zaki Auri buba diyana ta tambaya, buɗe baki hiyana tayi zatayi magana sai taji an ture tukun dake kanta ta baya ya faɗi ya tar watse, asukwa’ne buba tagani tsaye yana mur mushin mugunta diyana naganin buba ta kwasa a guje tayi hanyar gida, gudu take iya karfinta har ta iso dai dai zata shiga ke nan tayi tun tube da dutsen kofar gidan ta faɗi kasa tulun ya faɗi kasa ya tar watse, wani kukan bakin chiki ta sake kuka take kamar ranta zai fita
    a wan nan yanayi Hiyana da lamrat suka zo suka sameta tai maka mata Hiyana tai tamike tsaye ga goshin ta sai jini yake, dukkanbsu sai hawaye suke haka suka shiga gida

    inna dake zaune a tsakar gd tache ina ruwan, kuma tun dazun na zauna a nan nake jiranku zan dora ruwan shayi
    Chikin shesshekar kuka lamrat tace “wlh inna buba’ne ya kifar da ruwan
    Da sauri inna tamike tana faɗin buba na zakuwa sharriko ai nama buba ya ganku bare ya kifar da ruwan to wlh yau zaku yabawa aya zakin’ta, suna tsaye awajen suna matsar kwalla, har inna tashiga ɗaki ta daukoh wasu manya manya bulalin bishiyar dalbejiya

    Ta nufosu gadan gadan baji ba gani tafara sauke musu zabga zabgan bulalun nan ajiki babu ko imani bare tausayi, ihu suƙe hiyana da diyana suka haɗu suka kare lamrat, duka inna ta musu sosai sai da ta kutun suna iya kuka har kukan nasu ya daina fita sosai, sai da ta bugesu iya san ranta san nan ta kyalesu tana faɗin kutashi tun kafin na rufe ido na buɗe ku ɗauki kofi ku tafi ku ɗebo min ruwa,yanzun nan kugama kuzo ku jemin tallah tana kai karshen maganar ta nufi ɗakin ta, da kyar suka mike suka nufi Kichin suka ɗauki cups suka fice daga gidan, Amrat dake duƙe a wajen wanke wanke tana wanke kayan inna sai kuka take kamar ranta zai fita ba abun da take tunawa sai mahaifiyar su a zuchiyar ta take faɗin yanzu da umman mu bata rasu’ba da tana nan inna bazata musu haka ba wayyo Allah ka jikan umma da bappa haka dai Amrat wunin ranan ta wuni tana kuka su diyana kuwa suna jidan ruwa da kofi ga yinwa ga nisan rafi ga zafin rasuwar Bappa.

    Misalin karfe 11 nadare zaune suke a dakin’su dukkan’su ba wan da yayi barchi saboda yinwar dasuke ji ta hanasu barchi diyana che ta dubi hiyana tafara Magana “hiyana yaufa tun safe jinin nan yasake dawowa na chanza zani har nagaji duk kayana sun kare jinin kuma bai daina fitowaba
    A ɗan tsorache Hiyana tache “bari na lallaɓa naje na tambayo innar yaya bello sai muji kodai akoi wani abun da zakisha sai ya daina zuwa a razane lamrat tace “Aunty diyana wani jini kuma, diyana zatayi magana hiyana ta rigata da chewa ina ruwan’ki dake ake magana ne, shiru lamrat tayi taba sake magana ba
    Amrat dai takasa magana jimamin mutuwar bappa har yanzu bai saketa ba, dan kuwa duk tafisu shakuwa da Bappa su basu yawan zama dashi sosai saboda aikin ɗeban ruwa da tallah, wani lokachima sai sufi kwana uku basu samu damar ganin saba saboda balai inna,shiya ita amrat tafisu shiga damu dan kuwa ita kullum tana gida idan tagama wa inna aikin gida sai tatafi ɗakin bappa, ta kwanta ajikinsa suyita hira.

    Mikewa hiyana tai tana faɗin, bari dai na lallaba naje wajen innar yaya bello dan nasan itama batayi barchiba,tana kai karshen maganar ta fiche daga ɗakin, lallaɓawa take kamar wata ɓarau’niya ta fiche daga gd tana fita ta kwasa da gudu dan tsoro dare yayi ga duhu, sai data shiga gidan su yaya bello san nan ta ta tsaya tafara tafiya a hankali hankali dan kar wani yaji ya ganta ya faɗawa inna

    Da sallah ta shiga ɗakin innar yaya bello sai wani sanɗa take innar bello na zaune a tsakiyar ɗaki ta tasa dakkere a gaba tana chi ganin Hiyana yasa tamike tana tambayar ta “lfy hiyana me yafito dake chikin daren nan “lfy inna daman nazo tambayar ki wani abune “to menen faɗi, hiyana tasanar da ita komai abun da yafaru da diyana har fyaden da buba yaso yayi mata san nan taɗora da chewa kuma inna jinin fa kwana binyu da suka wuche ya dai na zuba sai yau kuma ya dawo
    Shiru inna ta ɗanyi kafin tace “kai buba Allah dai yashirya mana shi batun jini kuma al’adane bari nabaki pant da tsunmma guda 2 kibata tasa summa daya yanzu dasafe sai tachire ta wanke ta shaya, sai ta dauki dayan tasa, ba’a ajiye summar jinin kinaji na da an chire za’a awanke, to wakai hiyana tace, inna tanufi kwallar kayan sawar’ta ta buɗe ta dauko pant da tsunmma guda biyu ta mikawa Hiyana, amsa tayi tana fadin “to inna tayaya zatasa, inna tasake amsar summar tasa a chikin pant ɗin ta nuna mata yadda zatasa, san nan ta miƙa mata, Hiyana ta ansa tana faɗin mungoɗe inna,tanufi hanyar fita har takai bakin kofa sai kuma ta juyo tache inna “menene al’ada kuma
    Inna tache “idan mace ta girmane yake zuwa mata kuma alokachin da mace tafara al’ada to karta yarda wani namiji ya sake tabata idan kuma tabari ya taɓata tofa zata samu chiki
    Zaro ido waje hiyana tai jin an ambachi su nan chiki murya har rawa yake tache inna to meyasa ni banyi al’adan ba kuma ai niche babba, dafe kai inna tayi tana faɗin “kai hiyana sarkin tambaya to ai kowa da irin halittarsa ne shiyasa wata zakiga shekara 13 take farawa wata kuma sai takai shekara 16 to kowa da irin tasa halittar “to inna kullun yake zuwane dan naga na diyana fa yanzu kusan sati 1 ke nan kuma diyana tache kwana biyu dasuka wuche ya daina zuwa yau ne kuma yasake dawowa, shiru inna ta ɗanyi kafin tace “ina gani diyana na da sanyi’ne shiyasa al adan ke mata rikichi, yanzu dai dare yayi kije gd inkin samu lokachi idan azzalumar innan kun nan bata nan sai kizo in baki maganin sanyi kibawa diyana, yanzu kinga dare yayi kuma ban haɗa maganin bama tukun nan Hiyana tache “to inna mungoɗe sai da safe ta nufi waje tana fitowa kofar gdsu yaya bello, da gudu tayi gidan su chikin duhu dan dare yayi tana tsoro
    In da ta barsu diyana a nan tadawo ta samesu zama tayi gefen Amrat tafara yiwa diyana bayanin da inna tamata
    Diyana kam tunda akafara bayani take sauraro anazuwa wajen da akache intabari namiji yataɓata to zata samu chiki a tsorache tache
    Hiyana yanzu ko yaya bello tab nashiga uku na wlh yanzu ke nan zan samu chiki tun da kunga ko jiyama na kama hannun yaya bello,wayyo Bappa na dan Allah meyasa katafi kabar mu yanzu ni ya zanyi da raina ni diyana da chiki
    Girgiza kai hiyana take tana faɗin “ki dai na kuka diyana kinji kibari dasafe sai muje mu tambayi inna muji kina da chikin ne ko babu, da kyar hiyana tasamu diyana tayi shiru, san nan to koyawa diyana yadda zata yi amfani da tsumma da pant ɗin kamar dai yadda innar yaya bello ta koya mata, mikewa diyana tayi hiyana ta taimaka mata tasa pant ɗin san nan tasa tsunmar, suka kwanta shiri babu wan da yasake magana da haka har barchi ya ɗauke su

    3 days later

    Zaune take a tsakar gida ita kadai diyana ta tafi tallah amrat tatafi wanki kayan inna a rafi lamrat kuma tana debo ruwa ita kuwa inna ta bartane tamata girki
    Shigowa gidan inna tayi babu koh sallama tache “ke hiyana ko ki shirya ko karki shirya gobe za’a ɗaura auren ki da buba
    Hiyana dai bata che da inna ko mai ba amma a chikin zuchiyarta tana tunanin yadda zata gudun wa Auren, wunin ranar kuka hiyana ta wuni yi dan yau rasuwar bappa ya dawo mata sabo fill tasha kuka har blue eyes nata suka kumbura suka kankan che.

    Da daddare bayan su diyana sun dawone suna zaune a dakinsu kamar yadda suka saba
    Hiyana ta dubi su diyana tafara magana “lokachi yayi da zamu bar gidan nan
    A tsorache diyana tace “to muje ina muda bamu san kowaba bamusan ko inaba “ko bamu san ko inaba yazama dole mu bar gidan nan, dan gaskiya bazan Auri buba ba wlh na tsanesa bansan ganinsa mugune, gaskiya bazan tsaya a ɗaura mana Aure ba hiyana ta karisa maganar kamar zatayi kuka “to yanzu idan mun bar gidan nan ina zamuje diyana ta tambaya fiskarta chike da damuwa “kidai na damuwa diyana, zanyi tunani a kai dole na nemo mama inda zamuje chewar hiyana da sauri lamrat tace “to ko zamu nemo addan (yaya) bappa ne ba yataɓa faɗa mana yana da adda ba (yaya)
    Hiyana tache “to ai na zamuganta kenifa baruwana da kowa, yauwa birni zamu tafi muje munemi aiki har musamu kudi
    Taɓe baki diyana tayi tana faɗin to yanzu muda bamu san hanyar birni ba ta ina zamu tafi, karfa mu bar gidan nan muje mu haɗu da masu yan kan kai suyan ke mana kai, da sauri Amrat tace “wlh bappa yataɓa faɗamin akoi masu yan kan kai a birni, kara zaro ido lamrat tayi, tana faɗin “tab nikam ba zanje ba wlh gara na zauna a nan ta karisa maganar kamar zatayi kuka, kallon hiyana diyana tayi tace “to yanzu ya zamuyi Shiru hiyana ta ɗan yi kafin tace ke dai karki damu zansan yazamuyi, yanzu kan mu kwanta muyi barchi, da safe in munje ɗeban sai mukarasa maganar a rafi, har suna haɗa baji wajen chewa to

    Suna kokarin kwanchiya kenan sukaga inna ta faɗo musu ɗakin kafin su ankara tafara sauƙe musu bulalun hannun ta ajiki, bugun su taƙe tana faɗin “buba ne bakiso ko to wlh koki mutu ko kiyi rai sai kin auri buba daga yau ba mai sake fita a gidan nan a chikin ku rufe ku zanyi a dakin nan ke hiyana gobe za’a kai ki gidan buba kukuma sauran yin’wache zata kashe’ku a chikin dakin nan dan kulle’ku zanyi ba inda zaku sake zuwa
    Kuka suke sosai sun manne da juna diyana da hiyana sun haɗu sun karewa lamrat da Amrat ajikin su kawai bulalan ke sauka, inna kuwa bugun su take baji ba gani da iya karfinta,sai da ta farfasa musu jiki tukun nan ta kyalesu ta fiche daga ɗakin, kankame juna sukayi suna kuka a haka barchi ya ɗauke su

    Kano ta dabo

    Ammi na zaune a gefen katafaren gadan Abba shi kuma Abba yana kwanche a nitse da sanyayyiyar murya tace “ranka yadaɗe inasan muyi magana, mikewa Abba yayi daga kwanchiyar da yake ya zauna yana fiskantar ta “ina jinki Aishstu na manene yayi maganar yana kallan chikin idon ta, kasa da kai Ammi tayi chikin ladabi da girmamawa ta fara magana ” daman inasan zuwa Yola ne wlh kwana biyun nan,bana jin daɗi ina ganin kamar akoi damuwa ina yawan mafarkin Ahmadu kasan shi ya ragemin kuma gashi na yaddashi, abun yana yawan damuna sosai, inajin a jikina kamar Ahmadu na chikin damuwa,tunaninsa har tafara yimin yawa, dogon numfashi Abba yaja kafin yace “ba’damuwa Aisha ae kin jima baki jeba kusan shekara 7 ke nanfa gaskiya yakamata kije, ki shirya sai kuje da su Safras su rakaki
    “da murna Ammi ta juyo ta rungumi Abba tana faɗin ilove U ilove U
    rungumeta sosai Abba ma yayi yana faɗin “eyeeee yau kam ba fullanchi ke nan,kara shigewa jikinsa Ammi tayi tana murmushi

    ( Nikoh nache oh ka jimin tsofaffin nan gaskiya Abba da Ammi kuna shaaninku tsufa bata hana soyayya)

    Misalin karfe 4 na yamma gaba ɗaya ilahirin family alhaji Abubakar saraki ne zaune a fada
    Abba na zaune a kugerar sarauta gasu, Ammi a gefensa gefe guda kuwa sarkin fada’ne dasu waziri ga uncle Aliyu ma a gefe DON da Aryan suna zaune saman sofa mai ma zaunin mutun 2 duk kansu fiskokin’su babu alamar wasa a ɗaure taƙe tam kamar basu san menene dariya ba kallo ɗaya zaka musu ka gane suna chikin baƙin chiki, Khalid da Yusuf suna zaune suma a saman sofa ɗaya mai ma’zaunin mutun 3 ko ajikin su sai ma murmushi mugunta da suƙe wa DON da Aryan

    gyaran murya Abba yayi yafara magana a nitse gaba ɗayansu suka tattara hankalin’su suka maida kan Abba suna sau raron’sa
    ” Dalilin dayasa na tara’ku inason sanar daku lokachi yayi da zan sauka a kan kujerar murki in mikawa ɗana Safras asukwa’ne DON ya ɗago kamar zai yi kuka nan take fuskar sa ta sauya sosai jiyake kamar yayi ihu shi gaskiya baya san mulki ai sojan shi kawai yake so, chigaba da magana Abba yayi “gaba ɗayan’ku ina mai baki umarni ku’nemi transfer a wajen aikin’ku kudawo kusa dani kuchiga da aiki a kasar ku Aryan Ahmad Aiman Khalid Yusuf a sukwane suka ɗago suna kallon Abba, Abba ko ajikinsa sai ma chigaba yayi da magana,”yau azumi saura wata 2 bayan Sallah da sati 1 zan sauka daga kan kujerar mulki na a naɗa sabon sarki Safras, buɗe baki DON yayi zai yi magana sai idon sa ya sauka a kan face ɗin Aunty farida, girgiza masa kai tayi alamar yayi shiru kar yayi magana shiru yayi, yafasa maganar ya mai da kansa yana kallon kasa, “akoi mai magana a chikin kune chewar Abba yayi maganar yana kallon fuskokinsu shiru sukayi gaba ɗayansu Almost 10mnt ba wanda yayi magana “ok tunda bakuda magana kutashi kuje sai bayan Sallah da one week

    Da sauri DON ya mike ya fice daman kamar a kan kaya yake da sauri Aryan ma ya miƙe yabi bayan DON da ɗai da ɗai suka watse kowa yayi nasa ɓangaren

    Aunty amarya na fita tayi part nata sai huchi take, tana shiga ɗaki ta ɗau wayarta tafara neman hajiya sadeeya, bugu ɗaya hajj sadeeya ta ɗaga tana faɗin hello aunty amarya tache “hajjiya sadiya kina ina “ina nan kano mana meyafa “akoi matsala hajj ya sadiya ae bama abun da bai faruba, kinaji wai Safras za’a bawa mulki ba Aryan’ba “what? gaskiya bazai yiwuba dolene musan abunyi wlh dole Aryan ne zai karbi mulkin nan karki damu gobe zanzo mu tattauna chewar hajj sadiya “to shike nan sai najiki amma dan Allah kiyi sauri dan jinake kamar zuchiyata zata buga “kar ki damu hajj Hajara ae damuwar ki damuwa tache inshaa Allah zan shigo da wurima,”to kawai Aunty amarya tace san nan ta katse kiran ta haye gado tanata kunkuni

    Zaune yake a Katafaren palon sa saman sofa mai mazaunin mutun 3 yana fuskan tar sofar da Aunty farida ke kai a zaune ga Aryan zaune a gefensa sun zubawa Aunty farida ido, Khalid da Aiman suna zaune saman sofa mai mazaunin mutun 2 sai Ahmad da Yusuf suma a kujera ɗaya suke zaune dukkansu sunyi shiru sun zubawa Aunty farida ido suna jiran suje me zatache ita maɗin dai shiru ta zuba musu ido DON ne ya katse musu shirun da chewa “Aunty farida yanzu me mafita wlh bazan iya rike mulkin nan ba, mulki baya chikin tsarin rayuwata aikin sojana kawai nakeso bayan shi bana bukatar wani abukuma,dogon numfashi Aunty farida taja kafin tache “kar’kadamu nan da bayan sallah fa Abba yache kaga da ɗan sauran lokachi zamu shawo kansa a hankali, shiya dazun na hanaka magana domin kuwa kokayi magana ba sauraran’ka zai yiba amma zansan yadda zamuyi kafin lokachin inshaa Allah ka kwantar da hankalin’ka duk yadda zanyi naga ba’a baka mulkiba sai nayi, da sauri Aryan yache “dan Allah Aunty farida kada’fa kibari idan Abba ya yarda akan bazaa bawa DON mulkiba Ni kuma a dawo kaina, dan Allah kar’kibar hakan tafaru,wlh nima banaso mulkin nan a bawa Aiman ko Yusuf ” da sauri Aiman yache “tab wlh banaso sai dai Yusuf, wani harara Yusuf ya wurgawa Aiman kafin yace kaima dakake likita kache bakaso to inaga ni soja kuma me soja zaiyi da wani mulki sai dai abawa yaya Khalid ko Ahmad, da sauri Khalid ya buɗe baki zai yi magana, Aunty farida ta dakatar dashi da chewa “a’a Me abun rigima bayan ga uncle Aliyu yana nan da ransa ae shi yadache ya karbi mulkin “good my lovely aunty ina sanki wlh akoi ki da basira chewar Aiman harara wasa Aunty farida tamasa zatayi magana sukaji sallama
    Dukkan su suka juya da gudu Aunty mardiya tazo ta rungumi Aunty farida tana faɗin “nayi missing naku sosai Aunty farida tache “sai yanzu kuka iso “eh yanzu shigowar mu Ammi ke sanar dani kuna nan Mikewa DON yayi shi da Aryan da Yusuf suka nufi hanyar betroom ɗin DON, jiki a sanyaye Aunty mardiya tache “bro kufa nazo gani ina kuma zakuje, tun bamu gai’saba tayi maganar kamar zatayi kuka,kuma dakaji muryan kasan a tsorache tayi maganar
    Dukkan su ba wanda ya juyo bare ya tanka mata sukayi shige warsu chikin betroom ɗin, har ita kanta Aunty farida bataji daɗin abun da suka yima mardiya ba, a hankali ta dawo da kallanta kan Aunty Mardiya daniyar tabata hakuri, sai taga hawaye wani na bin wani a kan kumatun Aunty mardiya “kiyi hakuri Mardiya bai kamata kiyi kukaba duk da nasan basu kyau ta miki’ba amma kimu’su uzuri watarana sai lbr Chikin kuka mardiya tache “wai Aunty farida me namu’su ne dan Allah meyasa ni basa sona eh why? “suna sanki mana sudai haka halinsu yakene kawai amma suna sanki,wani dogon tsaki Aiman yaja kafin ya miƙe yanufi hanyar fita daga palon, chikin jin haushi Aunty farida tace “kai ina zaka kuma, a ta kaiche Aiman yace “ɗaki zanje batare daya jiya amsar Aunty farida ba yafiche da sauri, Aunty farida zatayi magana Ahmad ma yamiƙe da sauri yayi waje baki Aunty farida ta taɓe, girgiza kai kawai Khalid yayi ya mike ya dawo kusa da Aunty mardiya ya zauna yana bata hakuri, da kyar Khalid da Aunty farida suka shawo kanta tayi shiru, Aunty farida ta miƙe ta riko hannunta tana faɗin “muje ɗakin Ammi, koh, to kawai Aunty Mardiya tace san nan ta miƙe suka fice daga palon shikuma Khalid ya miƙe yabi bayan su DON ya shige chikin betroom ɗin shima,

    Yola

    Jama’a sun chika gidansu hiyana sai faman shirye shirye ake ga maza a kofar gida suna zazzaune a kan tabarma,liman ya miƙe yana faɗin “kowa ya nitsu yanzu za’a ɗaura Auren ina wali amarya daya daga chikin dattijan dake zaune awajen yace gani nan liman yace to ina waliyin ango Baban buba yace gani na to kumatso kusa zama malam liman yayi kana yache “malam audu kayarda kabawa dan wajen malam sani auren yarka hiyana malam audu yache…✍️

    more comments an share *💫STAR LADY💫*

     

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    _💖Story And Written💖_
    ⬇️
    *Star Lady*

     

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawa

  • Duk karfin Izzata Book 1 Paga 4

    Duk karfin Izzata Book 1 Paga 4

    Episode 4*

    YOLA

    Almost 11 na dare hiyana na waje tana neman diyana amma shiru shiru ba diyana ba lbrn’ta hiyana tayi kuka har ta godewa Allah kamar zatayi hauka, ta juyo ta dawo gida jiki a sake ba kwari, yanzu tama daina jin yinwar da takeji burin ta kawai taga ƴar uwar’ta
    tana shiga gida ɗakin su tanufa kwanche tasamu lamrat da amrat manne da juna sunyi barchi, ga hawaye nan abushe a fuskar su da’alama sunyi kukan yinwa har sun gajine barchi ya dauke su
    zama tayi akasa kusa dasu su,ta zuba musu blue eyes nata, wasu siraran hawayen takai’ci nabin kunchinta duniyar tunanin inda diyana take tafaɗa, kamar daga sama taji an bude kofar zanan ɗakin nasu an shigo, zubur tamike tana kallan sa ɗauke yake da wani abu a’kafadarsa kamar mutun hasken fitilar baya haska su sosai shiyasa bata gane me yake ɗauke dashi ba, murya na rawa “tace yaya bello kaine, kasa kasa bello yafa magana “eh nine kana ya raɓa ta gefen su lamrat ya kwantar da diyana, a ruɗe hiyana tace “yaya bello me yasame’ta’? aina kagan’ta? Ta mutune’? Naga bata numfashi
    “hiyana kinitsu mana bata mutu ba suma tayi, kinga yanzu dare yayi zanje gida da safe in kunzo ɗeban ruwa saimuyi magana,in bahaka ba kinsan idan inna ta ganni to nashiga uku, dan haka kiyi shiru karma taji wani motsi, yana gama faɗin haka yajuya ya fiche daga ɗakin
    itakuwa hiyana ta gyara zaman ta, tana kallan fuskar diyana tana kuka, haka ta kwana kamar yadda taga rana haka taga dare

    washe gari tun asuba inna ta shigo ɗakin nasu hannu ta riƙe da tulu mai ɗauke da ruwa da karfi ta zubawa diyana nan take diyana ta farfaɗo tana ihu, inna bata bi ta kanta ba ta juya ta zubawa amrat da lamrat a razane suma suka farka, juyawa inna tayi ta zuba sauran ruwan a awajen Kwan chiyar hiyana a tunanin ta hiyana na ɗakin,Amma sai taga akasin haka ba hiyana a wajen a fusache ta juyo gun su diyana zatayi magana taji diyana na sambatu, tana faɗin “dan girman allah buba ka kyale ni kayi kahuri, wayyo allah hiyana ta ina kike kizo ki chech..bata karisa maganar ba taji saukar duka ta ko ina ajikin ta, ihu diyana ta fasa wayyo Allah na shiga uku hiyana kizo ki tai makeni buba zai kashe ni, wani bugu inna ta kai mata a baki sai da bakin nata ya fashe, ihu a zaba diyana ta saki, shake mata wuya inna tayi tana faɗin “me buba na yamiki da za kiche ya kyale ki, ko kinga buba a nan ne eh, kodai wani mugun abun kuke shirya masa, jin maganar inna yasa diyana ta dawo chikin hayyachin ta, da kyar ta iya faɗin “inna kiyi hakuri zan mutu dan Allah ki sake min wuya, naushi inna ta sake kai mata a baki tana faɗin “ki mutu mana ina ruwana daman uban me kuke tsinanamin a gd ba gara ku mutu kowa ya huta ba, kara shake diyana inna tayi sosai sai dataga blue eyes nata sun fir fito waje sosai tana kokarin mutuwa da gaske,da sauri ta sake ta tana mai da numfashi, juyawa tayi tana kallon amrat da lamrat in da suka takure waje guda suna hawaye chikin tsawa tace “ke lamrat kitashi kije ki ɗoramin girki idan kin gama kizo kitafi talla, ke kuma amrat ki wuche kije kimin wankin kayana kiyi shara da wanke wanke, itakuma wan nan shai ɗaniyar ni zata sa na zubar da ruwa a kasa koh to wlh gaba ɗaya ruwan gidan nan sai na zubar dashi ku ɗebo wani, ke diyana ki tashi ki ɗauki kofin ki nemo wan nan shai ɗaniyar kufara ɗebomin ruwa kuma wlh daga nan zuwa karfe 10 ku chika komai na gd nan, dan dole yau ku jemin tallah ba zanyi asara ba, tana gama faɗin hakan,
    ta juya tayi nufi hanyar fita har ta kai bakin kofa sai kuma tace wlh idan kuka bari na kai tsakar gd baku fito ba na lahira sai yafi ku jin daɗi, jiki ba kwari lamrat da amrat suka mike suka fice suka bar diyana kwanche baki na jini sai kuka mara sauti dake

    Inna na fitowa tayi karo da hiyana a tsakar gida hannun ta rike da cup guda biyu da alama ruwa take ɗebowa “ke ni zakiwa iskanchi to wlh barikiji duk ruwan dake gidan nan saina zubar dashi a kasa kun ɗebo wani, san nan kuma ke kafin kifara zubawa a randu nan nan, sai kinyi sahu 10 kina ɗebowa kina zubar wa a kasa har sau 10 tukun nan, kifara zubawa a tulu, ni zakisa nayi a sara ruwa ba nashiga ɗaki zan tashe ki ashe ba kinan ki kasani na zubar da ruwa a kasa koh, ke gaki mai wayau tun asuba kintafi ɗebo ruwa, kuma barikiji duk yadda zakuyi kuyi nan da karfe 10 dole kuchika ko ina na gidan, nan san nan ku jemin talla dan yau bazanyi asaraba, tana kaiwa nan ta wuche tanufi kichen, tafara zubar da ruwan dake chikin randu nan da kuma tulu nan,sai da ta tabbatar babu wani tulun daya yage da ruwa a chikin sa san nan tafito tawuche ɗakin ta ta haye gado, babusallar asuba
    Dur kushewa kasa hiyana tayi ta rushe da matsanan chin kuka, mai tsuma zuchiyar mai sauraro, kuka take kamar ranta zai fita sai datayi kukan, mai isar ta san nan ta ɗago kai tana kallan su amra dake tsaye a bakin kofar dakin su, alama ta musu da hannu aka sutafi sufara aikin su kar inna tafito ta gansu, ganin babu diyana a wajen ne na yasa ta mike da kyar tanufi ɗaki dan tadubo ta

    Kwanche ta samu diyana sai kuka take “ita chikin muryan kuma tace diyana kitashi mutafi mu fara aikin mu tafaɗi hakan chikin shasshakar kuka “wlh hiyana bazan iya tashiba jinake kamar zan mutu chikina murdamin yake saboda yinwa “to diyana ya zamuyi kinsan dai in kika zauna inna ta dazo ta sameki duka zata kara Miki, kitashi muje saiki zauna a gonar yaya bello ni kuma na ɗebo ruwan “to zoki rikeni natashi, matsowa hiyana tayi ta kama kafaɗarata, ta tai maka mata tamike har tangal tangal take kamar zata faɗi da kyar ta tsaya a kan kafafunta aruɗe hiyana tace “diyana yanaga jini a jikin zanin ki wai ma ina ki kaje jiya
    “a tsorache diyana tafara magana hiyana bansan ya akayi naga jininba nima, daga gabana ya fito
    shiru hiyana ta ɗanyi kafin tace to chanza kaya muje, zamuyi magana a hanya dan in muka tsaya magana a nan inna zatazo ta same mu, da sauri ta ɗauko wa diyana wani tsunmar zanin atampa yasha ruwa duk ya koɗe ta ɗaura mata, tariko hannun ta
    da kyar diyana ke ɗaga kafa da kyar take ɗin gisa kafar tana tafiya suka fito tsakar gida, suka samu su amrat kowache takama aikin ta, amma kallo ɗaya zaka musu kasan suna chikin tashin hankali ga yinwa duk sun galabaita, girgiza kai kawai hiyana tayi, ta duƙa ta ɗauki cups ɗin data ajiye suka nufi waje

    Suna futa hiyana tafara tambayar diyana “ina kikaje jiya diyana “jiya na kwantane awajen da kika barni sai barchi ya ɗauke ni ina chikin barchi kawai sainaji a’na kokarin chiremin zani, nabuɗe idona a razane sainaga bubane, da nayi kokarin guduwa shine yakamani ya wanka min mari, kuma yasa kafa ya takamin wuya ya chiremin zani, inata rokansa da ya kyaleni amma yaki da kyar na samu na laluɓi wani karfe nabuga masa a kafa, shine yachire kafarsa a wuyata yafaɗi kasa ni kuma natashi da kyar zan gudu kawai naji ya bugamin wani abu a kai daga nan kuma ban sake sanin komai ba saida inna ta zuba mana ruwa ɗazun ta kare maganar chikin shesshekar kuka “to ae na ki kasamu jinin jikin kin nan kuma “nifa hiyana nache miki ban’saniba kawai ganinsa nayi ” jinjina kai hiyana tayi tana faɗin yazama wajibi muneman wa kammu mafita wlh ” to yanzu ya zamuyi ke nan tayi maganar dai dai lokachin dasuka isa bakin rafin”hiyana tace ki bari inmun samu lokachi iri idan inna bata nan sai muje muyi magana da bappa, yanzu dai ki ɗebo ruwa ki wanke jinin jikin ki nan, san nan muyi al’wala kinsan jiyama bamuyi sallar azhar laasar mangariba da kuma issha ba, gashi yan zu kuma ana sallar asuba sai muhaɗa dukka,muje kasar itachen chan mubiya bashin sallolin kafin mufara ɗiban ruwa “to kawai diyana tace san nan tanufi bakin rafin ta ɗebo ruwa ta koma gefe ta wanke jikinta tas san nan sukayi al’wala suka nufi kar’kashi bishiyar mangoron suka shinfiɗa ɗan kwalin su suka ta da sallah,
    sai da suka biyan bashin sallar da akebin su, najiya san nan sukayi sallah asuba

    addua hiyana tai sosai” ya allah kayafewasu amra ba laifin su bane innache kehanasu yin sallah Allah mun’tuba haɗa sallah da muke Allah kayafe mana
    diyana kuwa adduar Allah yakawo musu mafita take hakadai suka gama adduar san nan su kamike ” hiyana tanufi bakin rafi tana faɗin diyana kishiga gonar yaya bello ki zauna ki huta, ruwa ta ɗeba a cups ɗin ta kama hanyar gd, ta kuma diyana tashiga chikin gonar yaya bello ta zauna da yake gonar a bakin rafin yake daga chikin gonar kana iya kallan chikin rafin

    har karfe 8 na safe diyana na zaune a chikin gonar bello, hiyana kuwa saifaman jidan ruwa take ammafa da cups yan zuma taɗebo ruwan takama hanyar gida tanajan kafarta da kyar da kyar har takai kusa da gida zata shiga ke nan, buba ya tare mata gaba ɗaure fuska hiyana tayi sosai” babu kabani hanya
    hannu buba yasa ya buge cups ɗin dake hannunta yafaɗi kasa ruwan yazube, hiyana kamar zatayi kuka ta duka kasa ta ɗauki cups din har kwallah yafara zuba a idan ta batachewa buba ko kalaba takama hanya tajuya tanufi hanyar komawa rafin, tana tafiya wasu siraran hawayene masu dumin gaske ke zuba mata a’kan kunchin ta.

    haka takoma rafin tasake debo ruwan tajuyo ta zata tafi ke nan taga diyana a tsaya a bayan ta “hiyana kawo in karɓa miki kekuma kije ki huta tunda tun asuba kike deban ruwan nan “aa diyana kingafa ke baki da lfy dan haka kije ki zauna kibari zanyi “diyana tace aa to kawo nayi ko sahu 10 ne sai ki karba ” sahu 10 yayi yawa diyana ki daiyi 3 “to bani cups din, mikama ta cups ɗin hiyana tayi, tawuche tanufi chikin gonar yaya bello
    diyana kuma tanufi hanyar gida kodataje itama zata shiga gida buba tagani tsaye a bakin kofar gidan su batache masa ko sannuba tazo taraba gefen’sa zata wuche, buba ba tsoran Allah yasa hannun sa yasake buge cups din ruwan da diyana take da shi suka faɗi kasa ruwan ya zuɓe “a fusache diyana ta ɗago zatayi magana kome ta tuna kuma sai tafasa ta duƙa ta ɗauki cups din tajuya takama hanyar komawa rafin, buba kuwa yana ganin ta tafi yayi murmushi mugun ta cheke da izza da iya shege yafara magana,”ai kunshiga uku dani wlh bazan taba bari ku zauna lfy ba, narinka kuntata muku san nan kuma in na Auri hiyana in maida ta baiwar kowa na kauyen nan,dariya yayi sosai san nan ya chigaba da chewa kai amma goggo habiba ma yar aljanna che wlh ta iya horaku ɗeban ruwa da kofi ai shine maganin ku, a hakanma nikuma ba barin ku zanyiba, narinƙa addaban rayuwar ku kenan ina kifar da ruwan, yau sai kafarku ta daina takawa yasake kwashe wa da dariya kamar mahaukachi

    diyana kuwa juyawa tai komawa rafin ta taɗebo wani ruwan tanufo gida, ko datazo kofar gida ba’tasami buba’ba ba’karamin daɗi tajiba alhllh ta furta san nan tanufi gidan zata shiga, kamar daga sama taji an buge cups ɗin hannunta sun faɗi kasa ruwan yazube
    a fusache ta ɗago ganin bubane a gabanta hakan yasa tarufe ido ta zabga masa mari a kumatu
    diyana daman bata da hakurin jure wulakanchi

    buba kuwa bai’yi wata wata ba ya kwashe kafafunta tafaɗi kasa kanta ya bugu da jikin wani dutse dake bakin kofar gidan, wani ihu azaba ta sake, buba kuwa bai tau saya mata ba ya hau bugunta kamar ai aikoshi
    diyana sai ihu take ganin zai mata illa babu wanda yakawo mata agaji yasa tamike da kyar tana kokarin guduwa
    damkoh hijabinta yayi tabaya ya shake mata wuya ya bugata da kasa wani azaba taji gashi yaki sakin hijabin nata ga wuyan’ta a shake da gyar take numfashi ,tagama sad’dakkarwa mutuwa zatayi sae kuma taji buba yayi ihu kuma ya saketa “da kyar ta iya buɗe ido ta sauke su a kan yaya bello dake tsaye rike da sandar kiwo,sai huchi yake kamar wani zaki, ga buba kuma sume a kasa
    hannu yaya bello yasa ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗarsa yanufi hanyar rafin da ita, nan sukabar buba kwanche, bello irin mazan nanne masu karfi gashi dogo sosai kakkarfa

    kai tsaye gonarsa yanufa da ita hiyana na zaune taga yaya bello ɗauke da diyana a kafadarsa
    da sauri tamike tanufi’sa tana faɗin hande miboni yaya bello me kuma yasame’ta bello bai yi magana ba sai da ya isa wajen dayake zama inyazo gonar, wajen shinfiɗe yake da katifar chiyawa, akai ya kwantar da diyana da sauri hiyana ta karisa wajen ta zauna a kusa da diyana, tana fadin “diyana me yasame’ki waya bugeki waya pasa maki baki “hiyana kiyi shiru mana ki kyale’ta ta ɗan huta tun da kika gammu tare ai koma me yafaru zakiji chewar bello” hiyana dai hankalin ta bai kwantaba mikewa bello yayi yana faɗin ina zuwa san nan yakama hanyar fita daga gonar

    hiyana na ganin yaya bello ya tafi, ta matso kusa da diyana ta rike hannun’ta murya na rawa tafara magana “diyana meyasame’ki, chikin sarƙewar murya diyana tache “buba ne ya bugeni, dafe kai hiyana tayi tana faɗin “diyana banache duk abun da buba zai miki kirinka hakuriba, ae’nafaɗa miki koma me kika masa a kan mu abun zai sake dawowa tun da mudai bamu da gata, bamu da mai tare mana fada ki dubafa kigani gaba ɗaya kauyen nan gudun’mu suke saboda kalar idon’mu, kinsa ni wasuma har mayu suke chemana, wai idon’mu ba irin na mutane bane irin na mayune bawanda yake kusantar mu kowa wai tsoro muke bashi, duk kauyen nan yaya bello ne kawai mai tausaya mana sai bappa, su biyu suka rage mana amma duk da kinsan da haka sai kije kirinka biyewa buba kina jawa kanki wata masifar koh
    hiyana zata sake magana kenan idanta ya sauka a kan jinin dake jikin zanin diyana,a ɗan razane tace “diyana wai wan nan jinin kam na menene haka, chikin dashe war murya diyana tache “nima wlh ban saniba tunfa dana tashi yau da safe naketa ganin jinin yana fitowa yaki dai nawa, girgiza kai hiyana tayi tana faɗin “kuma kin duba bakiji chiwo’ba “ni banji wani chiwo’ba, shiru hiyana tayi tana tunanin a dai iya karatun da bappa ya koyamu’su tabbas yataɓa faɗa musu idan mace tafara girma to zata fara jinin haila, to ke nan wan nan shine, to idan koh hakane ae no yakamata nafara jinin ba diyana ba, tun da ni che babba amma yau zanje na tambayi bappa gaskiya dan muji wan nan jinin na lfy tayi nisa chikin tu naninta
    sae’ taji muryan yaya bello yana faɗin tashi kuchi abinchi, dawo da kallanta kan’sa hiyana tai yana rike da samira rufe da pai pai, a dayan hannun’sa kuwa kwaryar nono ne, ajiye musu yayi yana faɗin “kutashi kuchi dawuri “yaya bello bazan’mu iya chin abinchin nan,mu barsu amrat ba, basu chi komai bafa tun jiya da safe hiyana tayi maganar kamar zatayi kuka,yaya bello yace “hiyana karki damu kuchi kinji zanje in sayo muku rogo a dan dali sae’ ku ɓoye ku kai musu yana gama faɗin hakan ya ɗau fatan yar’sa yanufi wajen da yake shuki, hiyana ta miƙe,ta kama hannun diyana ta tai maka mata ta miƙe zaune, san nan ta jawo musu samiran Abinchin gaban su ta buɗeq, ɗumamen duwon dawane mai kyau da miyar kuɓewa yaji man shanu gashi sai tiriri, yake kuma da yawa dan yakusa chika samiran nan fa sukafara chi, hannu baka hannu kwarya, saida suka chinye tas san nan suka jawo kwaryar nonon ma suka shanye, hiyana tamike ta ɗauki samiran da kwaryar nono ta nufi rafin ta wanke’su san nan ta debi ruwa a chikin kwaryar tash takuma kawowa diyana

    wai shin wanene bello?

    Bello dai dashi da buba babansu daya mamane daban daban baban su buba kuwa yaya inna habibache inna habiba kishiyar mamansu diyana bello yana da mata yayi aure kuma a chikin gidansu yake zaune da matar tasa shiyasa duk taimakon da zaiyiwa su diyana yakeyi a boye dan indai yabari inna habiba tasani to wlh sharri zata masa tache yana nemansune ta haddasa masa masifa tsakaninsa da matarsa shikuma yana matikar tau saya musune shiyasa yake tallafa musu wan nan takai checchen wanene bello ke nan

    hiyana ta kawowa diyana ruwan ansa diyana tayi tasha san nan hiyana ta dubi diyana tache to barinaje na chigaba da ɗeban ruwan “aa mutafi tare dai dan yanzukam nasamu karfi ae “to muje jerawa sukayi har inda bello ke noma sukaje, suka masa godiya tare da sallama, to bello yace san nan yaɗora da chewa “an jima zan kawo muku rogon bari na gama noma naje dan dali ya sawo muku koh sai kubawa su amrat ɗin “to yaya bello mun gode sosai hiyana tafaɗa tana kamo hannun diyana har sun juya zasu tafi hiyana takuma juyo tache yaya bello wai dan allah me buba yayiwa diyana jiyane naga jikin’ta sai jini yake

    Shiru bello ya ɗanyi kamar mai tunanin wani abu, a nitse yafara magana babu abun da yama’ta dayaso yama’ta fyaɗe’ne sai kuma Allah ya tsare najiyo ihun’ta shine naje na kwache’ta, amma lokachin dana shiga ɗakin buban, dai dai lokachin yabuga mata sandar’sa a kai shiyasa kikaga tasuma, batun jini kuma ina ganin girmane yazo mata amma kuje gida zansan abunyi a kai hiyana tace “yaya bello menene kuma fyaɗe “shikenan ku daije gida ba sai anmiki dalla dalla ba, chewar bello
    Jiki ba kwari suka’nufi rafin suka ɗebi ruwa a kofu nan suka wuche gida da sallama suka shiga gida inna na tsakar gida tana ƙirgawa lamrat robobin nonon dazata tafi talla dasu a tsiyache innar ta ɗago tana kallan’su ” kuzo ku ajiye kofin, ku ɗauki tallar nan kuje ku sayarmin idan kun dawo ko da dad darene kwa karasa ɗiban ruwan “da sauri sukaje suka ajiye cups ɗin a kichin, suka fito suka dawo gaban ta suka tsugun na

    Kirga musu nonon inna tayi tana gamawa ta fara musu kashe di, “wlh ko kwana zakuyi a chan ku kwana amma karku dawo baku sayar da nonon nanba
    to kawai suka che mata san nan suka ɗauki tallar kowa da nata kwaryar suka nufi hanyar fita daga gidan suna masu tau’sayawa amrat dan kuwa yanzu duk aikin gidan nan ita kaɗai zatayi innalillahi wa inna ilaihir rajiun suna fita “diyana ta dubi hiyana tafara Magana wai yanzu yazamuyi ne kinfasan mu ba’a sayan faran’mu, dan chemana suke mayu ajiyar zuchiya hiyana ta sauƙe kafin tace “Allah na tare damu ai, muje kekam muyi addua,
    kai tsaye dandali suka nufa dukkan’su uku diyana hiyana lamrat sukabar amrat a gida daman ita amrat ba’a ɗora mata talla sai dai aikin gida kawai inna ke kasheta dashi
    suna zuwa kowa ta ajiye kwaryar nonon ta nan take mutanen wajen suka fara matsawa nesa dasu, sudai ko ajikin su dan in da sabo sun saba zaman’su sukayi shiru bawanda yache dawani kala a chikin’su
    wani

    Wani katon mutunne mummuna baki yazo wajen dasu diyana ke zaune ko sallama bai yiba ya dubi diyana yace ke ki dama min fura da nono na naira 100 ki kawo min masauki na, ya karisa maganar yana nuna mata hanya da masaukin nashi yake “nifa bansan wajen masaukin naka ba diyana tabashi amsa “dakin fita daga dan dalin nan kika ɗan yi kwanar hagu zakiga wata bukka to nanne wajen nawa “to zan kawo ma chewar diyana, juyawa yayi yabar tafi,
    Hiyana ta dubi diyana dake kokarin dama nono a kwarya dan ta damawa mutumin tache “aa diyana wlh bazaki kai masaba’ nifa tunda nake zuwa dan dalin nan ban taɓaganin mutumin nan ba kai ni ko sau ɗaya ma ba a dan dalin kawaiba koma aina ban taba ganin’saba
    Girgiza kai diyana tayi tana faɗin aa hiyana kibari nakai masa in bahakaba Kinsan dai bamai sayan fura da nono mu ko “to shike nan diyana kije,ki kai masa amma kiyi addua dan wlh in tsoran, karya sacheki kinga ba sanin sa mukayiba a diyana ta amsa da “to tafara dama furan

    bajimawa tagama dama furan ta ɗauka tanufi inda mutumin ya nuna mata, a bakin kofar bukkan nasa ta tsaya ta masa sallama, yana daga chikin dakin ya amsa sallamar tare da faɗin “ki shigo mana, diyana ba musu ta shiga a zaune ta’sameshi a tsakiyar ɗakin, gabansa taje ta ɗuka ta ajiye masa damammi yar furan a gaban sa, tana faɗin a ban kuɗin murmushi yayi ya ɗago jajayen idon’sa yana kallan ta “yarinya mai kyau kinasan kuɗi koh, diyana zatayi magana sai taji ya riko hannun’ta yachi gaba da faɗin “ni zan baki kuɗi dayawa in kinaso ya kai karshen maganar, yana kokarin rungumar’ta
    Da karfi diyana ta ture’sa tamike da gudu ta nufi waje, tana waige waige ko mutumin yana binta, a dai dai bakin kofar ta waje tayi karo da bello, baya tayi zata faɗi da sauri bello ya riko kafaɗar ta yana kallon chikin idon tana yana faɗin lfy diyana ita kuwa sai waige waige take, murya na rawa tache “yaya bello wlh shine ya kamamin hannu wai zai bani kuɗi
    A’fusache bello yache “ae daman bayan’ki nabiyo, yanzu zuwa’na dan dali na tambayi hiyana ina kike shine fadamin kinzo kawo wa wani nono, yanzu dai ki koma dan dali ina zuwa yayi maganar tare da sakin kafaɗar ta
    Da gudu diyana tawuche tanufi dandali, shi kuma bello yanufi chikin ɗakin mutumin zaune ya samesa yana shan furan da diyana ta kawo wani kallan banza bello ya bishi dashi daga sama har kasa kafin yache malam wanene kai ” mutumin yaɗago kai daniyar yayiwa bello rashin mutunchi sai kuma yaga bello chikakken namiji’ne mai ji da karfi dan ko faɗa zasuyi bello zai masa dukan mutu, dan haka sae yanitsu chikin girmama’wa yace “ni bakoh ne rai a ɓache bello yafara magana “eh ae nasan kai bako ne tun da ban taɓa ganinka a nan ba chewa nai daga ina kake, kuma meyakawo ka garin nan shiru ya ɗanyi kafin yache “daga kauyen tongo nake kuma hanyache tabi dani tanan na tsayane dan na hutane, idan na huta sai nachigaba da tafiya “shine zaka lalata mana yara bello yayi tambayar chikin tsawa, shiru mutumin yayi
    Yaya Bello ya chigaba da chewa aradun Allah idan kasake yiwa ɗaya daga chikin kannena magana wlh sae dai a ɗau gawarka murya na rawa mutumin yace “kayi hakuri bazan sakeba, bello bai sake magana ba yasa kai yafeche daga dakin a fusache,

    wajen su diyana yanufa,suna zaune suna yar hirar’su bello yazo kusa dasu kamar mai sayan nono kasa kasa yafara magana “duk wanda ba zai sayi nono a nan ba sai dai abari, karku kuskura ku sake kai ma wani sai dai ya hakura san nan kuma ki damamin fura da nono na 100, da sauri hiyana ta bude kwaryar nono ta ɗauko roba biyu ta juyesu a chikin wani dan karamin kwarya tasa fura biyu ta dau ludayi tafa damawa, tagama ta juye masa a leda ta mika masa,hannu yasa ya ansa, yasa ɗayan hannun sa a aljihun ya chiro kuɗi naira 500 ya juya gabas da yamma dan yaga akoi mai kallan sane ko babu, dan bai san inna tasani, mikawa hiyana kuɗin yayi, Kin ansa tayi, tana girgiza masa kai alamar ya bar kuɗin kawai, kan pai pan dasuka rufe kwaryan nono ya ajiye musu kuɗin kasa kasa yache kichere 100 na nono kibawa inna, sauran 400 kisaya muku rogon 100 ki ajiye 300 kuma zai muku am fani gobe, bai jira amsar suba yajuya da sauri, dan ya lura hankalin mutane yafara dawowa kansu kar wata matsalar tazo tafaru

    wuni zumbur su hiyana sukayi awajen ban da bello daya saya nonon bawan da yasake saya, shima mutumin da diyana ta kai wa nono bai basu kuɗin ba, haka sukayita zama da nono har karfe 6 na yamma, san nan hiyana ta miƙe tana faɗin kutashi mutafi gida, mikewa diyana da lamrat sukayi suka ɗauki kwaryar nono suka ɗora akansu suka kama hanyar gida
    Suna tafiya ne diyana tache “wai lamrat waya saye furan ki na jiyane lamrat tace “ae dayake kinga jiya kasuwane akoi baki,ni kuma kinga ai idona ba irin naku bane ba wanda yake chemin mayya shiyasa bakin suka rinka sayan nonon
    Hiyana ta girgiza kai tana faɗin “ae kema da idon ki yayi irin namu babu wan da zai saya koda bakin nema, suma chewa zasuyi ke mayya che
    Diyana tache “yanzu ya zamuyi da inna, ɗaure fuska hiyana tayi tana faɗin “ya zamuyi kuwa dukane dai kamar yadda muka saba shi zamusha “Allah kakawo mana mafita chewar diyana, dukkan su suka amsa da ameen

    Da sallama suka shiga gidan sai faman rakuɓe rakuɓe suke, muryan inna che ta daki dodon kunnen su daga ɗaki, tana faɗin “ae shiyasa nakesan hiyana ta Auri buban kinga ita hanyar mutuwar ta mai sauki ne, sukuma sauran zamusan yadda zamuyi dasu
    amma bazamuyi kisa a chikin gidan nan ba dan kinsan al adar kauyen nan, amma na chi al’washin duk dabbobin nan nine zan gajesu wlh dukkan’su nizan zama sanadiyar mutuwar su , wata murya mara daɗin ji sukajiyo daga chikin ɗakin inna tana faɗin “ae wahalar da kike ba suma habiba am zata iya zama ajalin su, Wani dariya inna tayi san nan tace ae yanzu ma kara nin’ka musu wahalar zanyi, kuma sati nan mai zuwa za’a ɗaura Auren buba da shigiyar nan .

    Baya baya sukayi suka fita daga gidan suna fita suka rushe da kuka,suna kuka suna tafiya har suka isa kasan itachen mangoro dake ɗan bayan gidan su zama sukayi awajen,suka sauke kwaryan nono dake kansu suka chi gaba da kukan su, sai da sukayi kukan mai isarsu san nan sukayi shiru dan kan su, dan duk chikin su ba mai rarrashin dan uwansa

    Suna zaune awajen har aka kira sallar mangariba, tukun nan suka mike, suka ɗauki kwaryar nono jiki ba kwari suka nufi gida ko da suka shiga, a tsakar gidan suka samu inna jiki a sanyaye suka karasa chiki gaban ta sukaje suka tsugun na, suka sauke kwaryar,sukayi jugum jugum gwanin ban tausayi suna jiran hukunchi, inna naganin haka tagane basu sayar ba miƙewa tayi tanufi ɗaki ta dauko wani katan bulala tafito, tafara bugun su dashi
    Diyana da hiyana suka hadu suka rufe lamrat bulala na sauka ajikin su, bugun su inna take baji ba gani abun tun suna iya kuka ma har kukan nasu ya daina fita duk sai da tamusu ruɗu ruɗu da jiki, ta kyale su ta kuma fiche daga gidan tana ta mai da numfashi, Amrat na ganin inna ta fita, itama tafito daga ɗakin bappa tayo wajen su da gudu tana kuka haka suka haɗu a tsakar gida suka rungumi juna sunata kuka, sai da sukayi kuka mai isar su
    San nan su kamike jikin dukkan su jikin su sai karman yinwa da wahala yake, suka nufi dakin bappa da sallama suka shiga amma bai amsa musu ba, akusa dashi suka zauna yana kwanche idon sa Abuɗe yana kallan sama
    chikin shesshekar kuka hiyana tace “bappa ina wuni shiru bai amsa ba ” bappa bakada lfy ne diyana ta tambaya a ruɗe, nan ma shiru bai amsa ba Hiyana tasa hannu ta taɓa shi ko motsi bai yiba a firgiche tafara jijjigasa tana ihu tana kiran sunansa Amma shiru
    Chikin kiɗima hiyana tafito daga ɗakin tayi waje tana ihu

     

    London United Kingdom

    Tsaye yake a tsakiyar babban palon su hannun’sa ɗaya na rike da trolley ɗayan hannun kuma yana rike da wayarsa yana latsawa, sanye yake chikin black jeans da blue t-shirt ya rage tsawon gashin kansa, yanzu gashin bata wuche zuwa iya wuyar’sa ba, yana sanye da booth black colour a kafarsa dakuma p-cap shima baki hannun sa na ɗaure da wani haɗadɗen agogon daimon mai kyau da tsada fiskar nan kuwa babu alamar annuri akanta a taure take tam kamar an aiko masa da sakon mutuwa amma yayi kyau sosai laɓɓansan nan kuwa kamar yasa jan baki jaa sosai ga sajen sa a kwanche yasha gyara bakaramin kyau yayiba, faffaɗar kirjin san nan kuwa a tsaye dam dam kamar zai fashe ga damtsen hannun sa a chike kamar zasu yaga hannun rikar, almost 10mnt yana tsaye

    A hankali Aryan ke sauko daga saman stair ɗin shima shigarsa iri ɗaya dana DON abun mamaki shima ya yanke gashin kansa ya rage mata tsawo, rike da trolley shima yana ja sauko wa yayi yazo dai dai inda DON ke tsaye, da wan nan sexy voice nashin ya furta sorry bro,DON bai tanka saba yaja trolley sa yanufi kofar fita, da sauri Aryan yabi bayan sa sukayi waje tare, da gudu rundunar jibga jibgan sojojin masu ji da lfy da karfi sunsha trenin suka nufosu, da sauri abdol ya karɓi trolley hannun DON, Shahram kuma ya karɓi trolley hannun Aryan, suka samu su a chikin haɗaɗɗun motachin, da akajera musu dan tafiyar

    Aryan yadubi DON yace “muje a mota ɗaya koh,DON batare daya amsa ba yace “wai ina Aiman da Ahmad ne “ae tunjiya suka wuche naija Aryan yabashi amsa yana kallan fuskar sa kama hanya kawai DON yayi batare daya sake magana ba yanufi motar, da sauri abdol yabuɗe masa kofar motar, slowly ya shiga ya zauna, ɗaga hannu Abdol yayi ya sara masa san nan ya rufe kofar motar, zagayowa ta ɗayan kofar motan Aryan yayi, da sauri Shahram ya buɗe masa kofar a nitse ya shiga ya zauna Shahram ya sara masa san nan yarufe kofar motar
    Da gudu sojojin suka hau nasu motochin su suka tadasu, da matsakai chin gudu suka nufi gate ɗin tun basu kariso ba security suka wangale masu gate ɗin, da gudu suka danna hanchin motochin waje,motar sojoji 2 a gaba sai motar su DON a tsakiya sai motochi 2 na sojoji a baya gudu suke shararawa a kan mikakkiyar titin

    Aryan ya dubi DON yace sai dai fa mutafi da jet ɗinka dan kuwa nawa yana naija dashi su Ahmad suka tafi “Ok kawai DON yache, chikin kankanin lokachi suka isa Airport Already angama shirya komai su kawai a ke jira, batare da ɓata lokachi ba suka fito daga chikin moton su suka nufi kyakkyawa kuma haɗaɗɗen privet jet ɗin DON mai ɗauke da tambarin sunan’sa PRINCE SAFRAS suna shiga batare da ɓata lokachi ba jirgin yaɗaga sai malam Aminu Kano international Airport Kano Nigeria

     

    More comments and share pls