Author: Novels

  • Matar Makaho 62-63

    Matar Makaho 62-63

    Page6⃣2⃣&6⃣3⃣
    Kamo muhammad sukayi, suka d’aga sa sama suka tura a mota sai ihu yake yana ataimake sa, amma ina mutane kowa gudu yake kar a had’a dashi, muhammad naji aka turasa a mota suka ja….

    Khadija data tsallake titi, ganin yayan ta yasata tsayawa tana jiransa ya tsallako su karasa gidan tare,kamar a mafarki take ganin abinda ya faru da d’an uwanta, ihu tasa ta ruga a guje ta tsallaka titin kafun ma ta isa garesu tuni sunja motar sunyi gaba, kuka ta sake sosai tana a taimake yayan ta sai a lokacin jama’a suka fara dawowa.

    Sosai surutu ya tashi a unguwan anata bawa khadija hakuri wance ke kuka kamar ana tsikaran ranta da tsinke, wasu kam maida zancen yanda ya faru suke, khadija dake duke tana kuka taji an dafa ta, d’agowa tayi da sauri tana kallon sa.

    Lafiya khadija mai ya faru naga mutane na tare a bakin titi, gaki kina kuka kuma?

    Wayyo shagari yayana barayi suka sace, duk sun rufe fuskar su da mask, tana maganar tana kuka.

    Innalilahi wa’inna ilaihi raji’um yanzun fa yabar shago, ya d’auki lemo, yake sanar dani yau bazai fitoh ba na zauna a shagon, saida ya fita naga ashe ya manta bai d’au maganin daya shigo dashi a hannun sa ba, shine na biyo na kawo masa, yana maganar hawaye na zuba,

    Khadija mikewa tayi, har tana ganin jiri jiri shagari yana rike da ita da taimakon sa suka koma gidan goggo, don bazata iyya zuwa gun sumayya ba a halin yanzun da take cikin nan .

    Assalamu Alaikum,shagari yayi sallama a kofar gaggo.

    Wa’alaikumu salam, lafiya me zan gani meya samu khadijan?

    Zaunar da ita shagari yayi a hankali, shima ya zauna akasan koh kujera bai nema ba tsabar tashin hankali, khadija na kuka shi kuma yana hawaye duk da yana namiji Amma b’atan muhammad ya shiga jikin sa.

    Kun zauna kuna kuka bazaku fad’amin abinda ya faru ba, gabaki d’aya kunsa raina sai tsinkewa yake?goggo ta fad’a jikin ta na rawa har zani na kuncewa.

    Goggo wallahi oga Al’ameen ne, wasu sukazo suka d’auke sa?

    Kamar ya suka d’auke sa bangane ba?

    Eh ina ga kidnap ne fa.

    Kidnappers kuma wani irin yan garkuwa da mutane, kuma muhammad ina yaga kudin da yan garkuwa zasu sansa, sai kuma ta fashe da kuka, na shigesu ni Amina, ya Allah ka taimake wannan bawa naka ka tsaresa a duk inda yake, Albarkacin Annabi da Alkur’ani.

    Ameeen goggo, shagari yace yana dafe kansa koh mutuwar mahaifin sa baiji tashin hankali irin nayau ba koh don baban nasa ya rasu baiyi wayo sosai bane sai Allah.

    Goggo Aunty bata sani ba, ina tsoron kar wani yakai mata labari tazo ta d’aga hankalin ta, gwara dai ke, ki sanar da ita goggo.

    Hakane khadija ki daina kukan ya isa haka, addu’a yake bukata ba kuka.

    Dole nayi kuka goggo, shikad’ai nake dashi, nake gani hankali na ya kwanta, yau an waye gari bansan halinda zai shiga ba.

    Kiyi hakuri khadija, bara naje gidan yayan naki, na samu sumayya.

    Toh goggo, kawai tace tana cigaba da kukan ta, shagari ma mikewa yayi kamar ruwa ya cisa yayi waje.

    Ta bangaren sumayya kam bayan fitan muhammad, kwanciya tayi haka kawai takejin faduwar gaba, for no reason, har bacci ya d’auke ta.

    Goggo tunda ta fitoh gidan ta, sai zulumin ta ina zata fara sanar da mace an sace mata miji, amma dai gwara ita ta fad’a mata dataji a wani wajen, tana shiga gidan koh bi takan kofar yan uwan ta batayi ba,cikin kofar sumayya tayi tana kwala sallama.

    Sumayya dake tsaka da bacci ne, ta farka jin sallama ake, Amsa wa tayi, ta sauka a kujeran a hankali tana dingishi don yanzun dai Jikin da sauki tunda, ta shiga ruwan zafi.

    “Laaa goggo sannu da zuwa, bismillah goggo ki shigo”

    Ah ah sumayya kedai bari zan zauna a wajen, ban kujera kawai.

    Kitchen sumayya ta shiga zata d’aukowa goggo kujera, da ido gaggo ta bita koh ita yarinya ne ta fahimce meke faruwa.

    Hawaye ne ya shikawa goggo ido, duk yanda taso daurewa kasawa tayi.

    Sumayya kam sosai jikin ta ke rawa, wanda batasan dalili ba, tana ajewa goggo kujeran itama a bakin dakali ta zauna tayi shuru.

    Sumayya!!

    “Na’am goggo”

    Kin dai san a rayuwar d’an Adam tana tafiya ne, tare da jarabawa koh?

    “Kwarai kuwa Goggo” tace tana kara gyara zaman ta, don tasan tabbas akwai abinda ke faruwa

    Sumayya ina so ki kwantar da hankalin ki, kuma ki rungume kaddara a yanda tazo miki, ina son kiyi hakuri da abinda zan sanar dake sumayya, ki kwantar da hankalin ki addu’a kad’ai ya dace kiyi.

    “Meya farune goggo”?

    Sumayya ki kwantar da hankalin ki, tace ganin sumayya harta mike tsaye jiki na rawa tana kallon ta.

    ” goggo meya same shi?tabbas nasan abune ya faru dashi, tun d’azun wallahi zuciya ta tsinkewa take”ta karasa maganar da fashewa da kuka.

    Sumayya kiyi hakuri wasu da bamu san suwaye ba, suka zo suka tafi dashi,ki kwantar da hankalin ki in ma masu garkuwa ne zamu jira kiransu, insha Allah babu abinda zai f…….

    Goggo bata karasa magana ba, dalilin ganim sumayya ta zube tim akasa,da gudu tayi kanta tana girgizata tana kuka.

    Jin kuka akofar sumayya yasa inna asabe lekowa, wanake gani kamar Amina meya samu MATAR MAKAHO kuma?

    Wallahi inna muhammad aka sace, shine na sanar da ita kinga sai kawai ta yanke jiki ta fad’i.

    Toh ai saiki kamata muje asibiti, ashe abinda modi ya sanar dani gaskiya ne, wai an kama MAKAHO banda haukan kidnopas ina su ina kama nakashashe?koh d’an kudi da aka ga yad’an samune oho.

    Inna ki taimaka mini bara na zuba mata ruwa, da gudu goggo tayi d’aki,ruwa ta ibo a firij tazo ta watsa mata, amma sumayya bata tashi ba, cicibarta sukayi ita da inna asabe zasu fitar da ita waje sai ga khadija.

    Innalilahi inna meke faruwa?

    Khadija jeki rufe musu kofa kizo mu tafi asibitin kiyi sauri.

    Toh goggo tana kuka ta nufi kofar yayan ta, rufewa sumayya d’aki tayi da kofa tabi bayan su goggo.

    FMC suka kai sumayya, suna zuwa aka bata gado,khadija shagon yayan ta ta wuce saboda rashin kudi a hannun su, shagari dubu 10k ya baiwa khadija, yace na cinikin da yayi yaune.

    Ta bangaren kamila, bayan yan uwan babanta sunzo aka kaisu sukaga kamila, sosai suka tausaya mata ba kad’an ba, masu magani aka nema kowa yazo ya gwada, abu ba sauki kadangaru fa sunki barin kamila.

    Harira taso koma wa jalingo, Amma sam baban kamila yaki, mijin ta yayita kira tun tana masa karya harya gaji yazo da kansa, yaji ba’asin zaman ta a kauye.

    Sosai yasha mamaki lokacin da baban kamila ya masa bayanin abinda matar sa ta jawowa yarsu, baice kome ba ya juya ya koma jala.

    Bayan maman kamila ta farka, tace atafau sai an maida kamila gun nakan dutse, suje su basa hakuri in ma kudi za’a basa a basa, ya bar musu yarinya ta huta.

    Anyi yanda za’ayi aja kamila amma an kasa saboda kadangaru sunki daga an tinkaro ta zasu hayayyako ma mutum.

    da aka ga haka sai aka samo bulala ana kora kamila dashi kamar saniya ana mata barazana tana gudu, in zatabi hanyar da bashi suke soba sai wasu su tarota, a haka gwanin tausayi akayi gun nakan dutse da ita, Amma ina suna zuwa aka ga koh kokon sa yau babu filine shatt ba kome.

    Haka suna ji suna gani kamila tayi ta fama da kadangaru, ga watan azumi gashi sun rasa ya zasuyi su dawo da ita jalingo.

    Karshe dai motar akori kura, aka samu aka kora kamila tahau baya, da kadangarun ta mammanne a jikin ta, Aka ja motar sai jalingo.

    Sai ayau Harira ta samu dawowa gidan ta, jikin ta har rawa yake ta shigo gidan, da mamaki ganin mijin ta zaune da yaranta, suna bud’a bakin azumi.

    Assalamu Alaikum

    Ba tare da ya d’ago ba ya amsa mata, wa’alaikumu salam.

    Rikice wa tayi ta rasa ma me zatayi ta zauna a falon ne, koh ta shiga d’aki, tashi tayi ta shiga d’akin ganin kallon banza da mijin ke mata.

    Tana shiga d’akin ya taso ya bita, kee Harira sai yau kika dawo?

    Eh sai yau wallahi aka samu aka fitoh da ita.

    Yayi kyau karbi wannan,yace yana mika mata takardan dake kan mirrow ta.

    Jiki na rawa tace menene wannan baban Amir?

    Takandar sakin kine, kije bazan iyya zama dake ba, yanzun ma jira nake ayi sallah aure zanyi.

    Saki, aure?

    Kwarai ma kuwa na baki nan da awa biyu ki tattara kayan ki kibar mini gida now now…

    Don Allah kayi kahuri, baban Amir kayi hakuri na tuba, wallahi bazan sake bin koh mai tofi, kayi hakuri karka sake ni wallahi bazan iyya koma wa gida a yanzun ba .

    Au nan in gidan ubanki ne da bazaki iyya koma wa ba?

    Sosai harira tasha mamaki, yau mijin tane ke zagin ubanta, mutumin da koh d’aga ido bayayi ya kalli tsakar idon baban ta tsaban kunyan sa dayake ji.

    Koh bazaki fita bane? yace cikin tsawa.

    Mikewa tayi ta fara tattara kayan ta, tanayi tana kuka tana dana sanin sanin kamila, gashe a dalilin neman mata auren wani gata ta kashe auren ta ..

    Kamila kam har akayi sallah tana fama da kadangaru, yan unguwan su ba wanda baiji abinda ya faru ba, wasu suzo gulma wasu suzo musu jaje, mamar ta haukane kawai batayi ba, duk malamin da aka samo abu yaki sam har akayi sallah jiki yaki sauki kadangaru kam basu barta ba.

    Ta bangaren muhammad kam, tunda suka sasa a mota sai had’asu da Allah yake, su taimaka su barsa matar sa ba lafiya yanzun ma magani yaje sai mata, sumai hakuri, amma ba wanda ya kulasa, da suka ga surutun sa yayi yawa, gam suka likawa bakinsa.

    Shidai yana zaune yanaji sai tafiya ake dashi sosai, kafun yaji motar ta tsaya, d’aya daga cikin sune ya bude masa baki, suka jasa waje aka fitar dashi daga motar, ajesa sukayi a kasa, suka aje masa plate a gaba,

    kai muhammad d’auke abincin gaban kan nan kaci, tafiya ne a gaban mu.

    Don Allah kuyi hakuri ku maidani, wallahi matata bata da lafiya na barta koh karyawa batayi ba.

    Kai muahmmad banace kaci abincin gaban kaba, koh bakaji bane?

    Ai da sauri ya fara cin abincin, jikinsa na bari.

    Kasan me mukeso dakai muhammad?

    Ah ah sai kun fad’a ya basu amsa abinci cike a bakin sa, don ya tsorata ainun, tura abinci kawai yake.

    An bamu kwangilar kashe ka, Amma mu bazamu iyya kashe ka ba, don shekarun baya mune tsilar makantar ka, wanan karon bazamu iyya d’aukar ranka ba, bakaji ba, baka gani ba, ana buwayan rayuwar ka.

    Innalilahi kune daman wa’inda kuka zubamin abu a fuska, na makance?

    Ba zuba maka abin bane ya makantar dakai muhammad, tafiya mukai dakai a wancan karon ma.

    Toh me nai muku kuma, waya saku?yana maganar yana kuka.

    Kai mana shuru,abinda muke so dakai yanzun shine xamu fitar dakai daga NIGERIA, Bama son ka kara taka kafar ka a wannan kasar, kaje can kayi rayuwar ka, yafi maka Alkhari sama da zaman ka a kasar nan.

    Toh don Allah ku bari na d’auki matata da kanwa ta, saimu tafi tare wallahi na muku Alkawari bazamu sake taka nigeria ba.

    Kaiiii kana wasa da ranka koh? ana maka gata kana kokarin sa kanka a matsala, an gaya maka koma warka gida yanzun baka bata mana aiki bane, don haka barin kasar nan dakai ya zama dole mundin kana son rayuwa mai tsawo

    Don Allah ranka ya d….

    Bai bari ya karasa ba yace, rufemin baki wawan banza kawai, kome mata mata ai akwai mata da yawa a duniya, in sake jin ka am bace Hakuri anan saina sumar dakai nosense.

    Shuru muhammad yayi, agun suka kwana washe gari suka kama hanya, wanda shi ba gani yake ba bai san ma ina ake jansa ba.

    Lokacin da aka zo tsallaka border da muhammad ana tsallaka nigeria wani irin ihu ya sake yana birgima a cikin motar, ji yake kamar ruwan zafi aka watsa masa, sosai yake salati yana kuka jin jikinsa na tafarfasa.

    Abin mamaki mutanen basu wani damu ba, kuma abin bai basu mamaki ba, d’aya daga cikin sune ya masa Allauran bacci a take jikin sa ya sake.

    Ta bangaren sumayya sai da ta kwana biyu kafun ta dawo hayyacin ta, tunda ta farka sunan muhammad kawai take kira sai kuka, zaune take akan gadon asibiti An d’aura mata sabon ruwa a hannu, inka ga sumayya saika tausaya mata tsabar rama da tayi,

    Likita ce ta shigo d’akin, sumayya ta kalla ta sake kallon goggo dake zaune a gefe, ga khadija ma zaune tayi tagumi gabaki d’ayan su wujiga wujiga suka koma, abin tausayi.

    Sannun ku yamai jikin?

    Da sauki likita, goggo ta Amsa mata.

    Masha Allah, sumayya kam tana da mijine?

    Eh likita tana da miji.

    Ok koh zan iyya ganinsa?

    Kuka sumayya ta sake mai tsanani, tana dafa kirjinta jin zafin da yake mata.

    Subhanallah sumayya ki kula da lafiyar kifa, kina kokarin d’aurawa kanki wani ciwon kuma akan wanda kike dashi.

    Dole nayi kuka Dr mijina aka sace shikaran jiya da safe.

    Amma kun kai report wajen yan sanda kuwa?

    Ah ah waye muke dashi, da zai kai mana report, yan sandan ma in kaje sai sun nemi wani abu agun ka, mu ina muka ga abinda zamu basu.

    Duk da haka gwara kukai report yafi, sannan ina son kuban waje zanyi magana da sumayya?

    Ba kome likita, goggo tace tana fita, khadija ma tashi tayi tabi goggo har lokacin bata daina kuka ba inta tuna yayan ta.

    Sumayya hawan jini kika samu ya kamata, ki nutsu kisa tawakkali a ranki kiyi hakuri insha Allah mijin ki zai dawo.

    Dole nayi kuka Dr mijina shine kad’ai farin cikina daya saura mini, sannan a waye gari ban gansa ba dole na shiga damuwa.

    Kiyi hakuri, sannan ya kamata kima mahaifiyar ki magana ta ringa xuwa miki da ruwan zafi, kina zama a ciki saboda yanayin jikin ki kinji Allah ya sauwaka.

    Ameeen nagode likita, sumayya tace tana kallon likitar bazata wuce sa’arta ba koh ta bata yan tsiraran shekaru.

    Ta bangaren muhammad Sai da sukayi sati suna tafiya a motar, kafun suka iso kasar da suka shirya kaisa.

    Suna shiga kasar da suka yanke zasu aje sa, d’aya daga cikinsu ne ya kalli ogansa, oga anya wannan yaron, bazaice zai dawo kasa ba kuwa, ka sansa akwai fahimta ni inso samune mai zai hana a masa yanda zai manta da kome, na d’an wani lokaci.

    Bazai yuba hakkin yaron nan ya mana yawa, mu barsa haka wannan karon bazan sake cutar da yaron nan ba.

    Shikenan oga amma naga hakan ma, taimakon sa muke son yi, don mun masa hakan ba kome bane.

    Gaskiya ne oga, d’aya daga cikin su yace

    Kai ban Amince ba ku aje yaron nan mubar kasar nan, kar a kamamu jirgi ma zamu bi, bada mota zamu koma kamar zuwa ba.

    Haka suka aje muhammad suka kara gaba.

    Kamar Awa d’aya da tafiyar su muhammad ya farka, A hankali ya motsa hannunsa sai kuma ya fara kokarin bude idanusa a hankali, ya bude su yana kallon sararin samaniya, ai da sauri ya mike zaune, mafarki yake koh gaske jikin sa har rawa yake yasa hannu ya murza idon sa da kyau don kara tabbatar wa kansa abinda yake gani, gaskiya ne koh A mafarki yake……………🍀🍀🍀🍀🍀

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌
    Free book🤧

  • Matar Makaho 74-75

    Matar Makaho 74-75

    page7⃣4⃣&7⃣5⃣
    Abdul’aziz wanda aka fi sani da shugaba, haifafen mambila plateau(Gembu) ne, Ainahin su fulanin gembu ne, acan aka haifi Abdul’aziz,duk da yana kauye hakan bai hana shugaba karatu ba, yayi karatun sa na secondary kafun yayi aure, matar sa ta farko fatima wance ake kira da fa’i, ita ma yar gembu ce, auren dangi aka musu, kafun daga baya ya aure sumayya (Dada), a kauyen su yake rayuwar sa da matan sa biyu,da yaransa maza biyar, yaran fa’i uku, Abdul’aziz mai sunan babansa(babuji)sai Abubakar da gaddafi,sumayya(dada)nada maza biyu itama, Usmanu sai Abdulsalam(Abie)shine autar gidan su, akwai kyakkyawar fahimta da zaman lafiya agidan, shugaba(Abdul’aziz)hakan ya samu asaline daga zaman lafiyar da matan keyi, zamane na kwatance a kauyen su, kaf kauyen babu gidan da zaka shiga kayi mamakin zaman kishiyoyi iri na gidan shugaba, sosai abin ke bawa wasu mazan sha’awa, don shugaba adaline a gidan sa, duk da auren soyayya sukayi da sumayya hakan baisa ya nunawa fa’i banbanci ba.

    bayan wasu shekaru an samu fad’an kabilanci a gembu sosai,tsakanin mambilawa da fulani wanda yazamo sanadin mutuwar fatima uwargidan shugaba, da mahaifiyar shugaba, daman mahaifinsa ya jima da rasuwa, wasu da dama a yan uwansa sun rasa ransu, a rikicin da ya afku.

    Bayan kome ya daidaita, shugaba ya saida duk wani kadara nasa na kauye wanda mahaifinsa ya mutu ya bar masa, don shikad’ai babansa ya haifa namiji sauran matane kuma duk sunyi aure, ya dandanka musu nasu gadon.

    Jalingo babban birnin jahar Taraba, ya tattara iyalansa suka dawo jalingo, gida madaidaici shugaba ya saya, yasa yaransa a makaranta, dada tana kula dasu kamar y’ay’anta na cikin ta, sam bata nuna musu banbanci da nata duk d’aya ta d’auke su, wannan abin shiya kara dasa soyayyar ta, a zuciyar mijinta.

    Bayan wasu shekaru kudi sosai ya fara zama a Aljuhun shugaba, don business yake na manya manyan shaguna zanunuwa a kasuwa yana order daga kano, aje aje yakoma na mototi, Arziki kullum gaba gaba yake ga yaransa na makaranta, duk wanda ya gama secondary, kwasar waje yake turasa karatu.

    Lokacin da yaransa suka fara nisa a boko , hakan yasa ya sakar musu wasu kud’ad’e su gwada tasu kasuwar, babuji da Abubakar sune suka fara kammala karatu, suka fad’a business abinka da yan boko, kuma kwararu a bangaren business, kankace kome kudine ya zauna company suka kafa mai zaman kansa, tare da haden gwuwar junan su, sosai arzikin su ya fantsama.

    Babuji da Abubakar a rana d’aya sukayi aure , wasu yaran jalingo suka aura wa’inda suka hadu a makaranta, bayan auren su, saida suka haifi yara bibbiyu, kafun gaddafi da Usman sukayi aure.

    Abdulsalam ya kammala karatunsa Amma sam yaki aure kaman yan uwansa, duk yanda iyayen sa sukaso yayi sai abin yaki, dada har magani take saka masa a abinci koh Aljanane ta aura mata yaro, Amma ina shuru abu yaki kowa aka nuna masa yace baya so, bata masa ba hardai su gaddafi suma suka hayayyafa sosai , a lokacin yaran babuji biyar, na Abubakar uku, yaran gaddafi biyu, na usman hudu.

    Bayan wasu yan shekaru shugaba ya kwanta ciwo, baiyi wani dogon jinya ba Allah ya karbi rayuwansa, gadon da aka raba musu shi suka had’a suka gina katafaren gida a unguwan specialist, gabaki d’ayan su suka tattaro kan iyalansu suka dawo cikin gidan da zama, don a lokacin Babuji da Abubakar suna da company kansu har biyu, yayinda gaddafi yake aikin goverment, usmanu d’an siyasa ne, Auta Abdulsalam shi ma’aikacin Bank ne(Accounter)kasance warsu rikankun yan boko ga naira ga kyau, kowa yasan yanda fulanin gembu keda tsananin kyau.

    Rayuwa ake a cikin shugaba family house mai kyau, daban sha’awa, mazan basu bawa matansu daman da zasu kawo musu tashin hankali ba sam, koh kara kika kaiwa mijinki matar wansa ta miki kaxa, had’a meeting ake a kira kowa, ku maida maganar hakan yasa matan sam suka daina fad’awa mazajen su, saidai ayi iyya mata da mata kasa kasa.

    Auren Abdulsalam ne yaxo musu da sabon salo, saboda yarinyar da ya kawo akan ita zai aura, yar maiduguri ne Amma tana karatu a TSU, tazo bank inda yake aiki cire kudi, Allah ya had’asu kanuri ce, hakan yasa dada tace ita sam bata yarda da auren nan ba, bazasu aure babarbariya ba, abinda ya xamo cecekuce a gidan kenan, duk yanda Abdulsalam yaso fahimtar da ita son da yake ma yarinyar, abu yaci tura sam taki Amince wa katafau tace bata yarda ba, shikuma Abdilsalam yace muddin ya rabu da Hafsa toh shikam bazaiyi aure ba.

    Aijin haka yad’agawa dada hankali don tasan sarai halin Abdulsalam, akwai kafiya kamar me, tayaya ma aka samu ya samo hafsar kullum yace yakusa aure shuru baiyi ba, bare yanzu yace bazaiyi ba ai magana ta lalace.

    Babu yanda ta iyya da banbakin su babuji ta Amince da auren hafsa, har maiduguri akaje da zancen auren.

    su karan kansu iyayen ta sunso gardama amma ganin sannanen family ne, yasasu karbansu da hannu bibbiyu, tare da kafa sharadin yarsu zata cigaba da karatu insun amince, zasu basu ita?

    Amincewa kam sunyi saboda kaf gidan shugaba yan boko ne, hatta matan gidan na zuwa aiki, rainon yara ma dada keyi da masu aiki.

    BAYAN AURE
    Hafsa fa ta fara fuskan tan banbancin launi a gidan su Abdulsalam, kasancewar ta baka kuma kanuri, sabanin yan gidan shugaba farare ne, daga matansu har maza da yara gasu fulani kyawawa, don Abdulsalam baza’ace kyaune ya rud’asa akan hafsa ba, ah ah sonta ne kawai Allah ya diga masa a zuciyar sa yaji baya ganin kyaun kowace mace sai nata, sosai ake nuna mata banbanci kuma ba wanda ya fara asasa hakan sai dada, haka zasu zauna suna hira daga sun ganta zasu koma yi da yare basa janta a jiki, inta matso garesu basa sonta rabesu sam, kansu a hade Amma ita sun ware ta.

    Hakan dasuke, yama hafsa zafi, yasata watsar da kowa na gidan, ta kama karatunta daga ta dawo makaranta ta shiga kitchen tayi girkinta, zata haura upstair’s, ta shiga d’aki bata fita sai mijinta ya dawo.

    Abdulsalam yasha had’a meeting da korafi akan abinda akema matar sa, duk da bata fad’a masa ba, yaga alama yayunsa mazane kad’ai ke sonta.

    A haka fa abu yaki chanjawa abubuwa sai cigaba suke a haka, hafsa zaman hakuri take a gidan, babu zagi babu duka, Amma ana nuna mata mugun hali kam, a hakan cikin hukuncin Allah ta samu ciki, wanda kaf gidan babu mai farin ciki sai ita da mijin ta da yan uwan mijinta, amma babu ruwan matan dasu dada da ita, gashe cikin yazo mata da laulayi, bata iyya aikin kome, kuma babu mai taimakon ta, karshe dai Abdulsalam d’aukar hutu yayi a bank ya zauna a gida yana kula da matar sa, amma abu yaki karshe dai kiran iyayen ta yayi aka turo masa kanwar hafsa, tazo ta zauna da ita har cikin ya tsufa bata koma ba.

    Wata ranan Alhamis hafsa ta tashi da nakuda tsakar dare, Abdulsalam da kanwar hafsa ne, suka kaita asibiti don baiko sanar da yan gidan tana nakuda ba, hospital aka kaita kafun asuba Ta santalo yarta kyakkaywa fara tas, jinin gembu mai tsananin kama da zuriyar gidansu, koh kama da hafsa batayi kome na babanta ne.

    Sosai Abdul yayi farin cikin samun wannan baby, ga wani irin sonta daya ke sosai yaji son babyn sa, washe gari ne yan gidan suka tashi sukejin labarin haihuwar a bakin mazajen su, Dada da matan sunje asibiti bada son ransu ba, saidai ganin yanda Abdulsalam yahad’a wa kowa fuska, gaisuwa ma dada kawai ya gaishar, ya shiga yad’auko kayan baby ya fita, hakan yasan su zuwa duba baby.

    Ba karamin dadi sukaji ba ganin yarinya kamar su ta biyo, bama kamar dada a murna, zama tayi a asibitin taki tafiya ita kema yarinya wanka, duk da yar uwar hafsa tazo washe gari Amma dada ta karbi kome na baby, harsuka koma gida dada fa na leke da yarinya, ranan suna yarinya taci sunan dada sumayya ana kiranta da momcy, haihuwar sumayya shine musababin zaman lafiyar hafsa, sosai taga change agun dada haka ma matan gidan, sosai suka koma damawa da ita, itama bata rikesu a rai ba, a sannu sannu har itama ta fara jin fulatanci duk ta maida martani na bata wuya, amma babu abinda zaka fad’a da fulatanci bata sani ba, dayake gidan sosai suka rike yarensu, suna hausa Amma ba sosai ba.

    Sumayya(momcy) tana da shekara hudu Abie inta ya shigar da ita makaranta, lokacin hafsa(ummi)ta kammala karatunta na jami’a ta fannin koyarwa, taso kara gaba Amma abie ya hana, aiki yasama mata na koyarwa a makarantar secondary, wannan kenan.

    Sumayya na cika shekara biyar kanin Dada Allah ya masa rasuwa a gembu, dukansu sukaje taziya, bayan sadakan bakwai dada ta d’auko yarsa daya haifa guda d’aya, mai suna safina(momy), bayan dawowar safina family shugaba, sai abubuwa suka fara bullowa saboda tunda safina ta shigo gidan shikenan ta fara likewa Abdulsalam(abie)duk wani iyayinta abie baya kulata, asalima sai ya daina zaman falo kwata kwata koh abinci ne saidai suci da ummi a d’aki, abin har yakai ga dada ta lura da hakan, sosai ta nuna masa bacin ranta akan yana nunawa safina mugun hali don tana zaune a gidansu.

    Zama ya fara rashin dadi lokacin da safina ta fitoh karara tace ita abie take so, sam abi yaki zancen kuma ya nuna bazaiyu ba, ummi karan kanta a lokacin ba karamin bakin ciki taji ba, don gwara tayi kishi da kowa akan safina, irin yaran nan ne shegun kauye masu shiga idon mutane, gashi batada kunya sam.

    Dada fa ta tuntube abie akan zancen ya nuna bazaiyu ba, hakan yasa dada bata tilasta masa ba ta watsar da xancen, abinda ya konawa safina rai kenan, kaf gidan babu mai supporting nata, kowa ya nuna baya goyon baya akan zancen, harda matan babuji basa sonta.

    Safina makaranta aka saka ta na islamiyya, don sam taki zuwa boko duk yanda akayi bazata ba islamiyyar ma daker ta fara zuwa, zuwan ta islamiyya shiya had’ata da kawa nafisat, nafisa irin yaranan ne watsansu marasa jin magana, haduwar su da safina, yasa nafisa nunawa safina abubuwa da yawa, ta kara kangarar mata da kai, bata tsoron uban kowa.

    Abin yayi matukar d’agawa dada hankali duk yanda taso rabata da safina abin ya gagara, gashi a lokacin nafisa bazawarace harda y’a d’aya take dashi, hakan yasa dada mawa safina barazanan zata maidata kauye, amma safina koh a jikin ta, ta nunawa dada koh ta maidata kauye tasan hanya, duniya da fad’i.

    Bayan wata uku da haduwar safina da nafisa, lokacin sumayya nada shekara 6 a duniya, hafsa ta fara ganin change a zaman su, sam yanzun zaman ba dadi tsakanin ta da mijinta, kullum cikin rikici suke wanda itama karan kanta batasan dalili ba, sosai abin ke damunta, wasu lokacin har Abdulsalam na dukanta, Amma bata taba fad’awa iyayen ta ba, koh wani nata saboda tanason mijinta, sai kawarta wance suke karantar wa a makaranta d’aya, don lokacin kanwar ta da aka kawo mata lokacin cikin sumayya tayi aure, batada wani nata kusa.

    Yau an waye gari da wani masifa a gidan shugaba, amma dada satan sarkan gwal inta, sosai tayita masifa tana zagin yan aikin gidan wance ke mata gyaran d’aki kamma koranta akayi, koh sati ba’a kara ba aka sake ma hajjo(matar babuji) sata, ba’a kama barawon ba, haka aka ringa sace sace kusan wata har rashin yarda ya shiga tsakanin juna, kowa na zargin d’an uwansa, ba yan aiki kad’ai ba.

    Kamar yau aka sacewa Matar abubakar agogonta na demond, yau kam masifa aka sake akan sai anbi d’aki d’aki anyi bincike, sai an fitar da barawon don kaf gidan tunda safe babu bakon daya shigo koh ya fita, kuma kowa na gida ranan don weekend ne.

    Bincike aka ringayi har akazo d’akin hafsa, kamar a mafarki aka ga agogo da wasu sarkoki na dada a cikin wardrop na ummi abinda ya kawo cece kuce dacin mutuncin hafsa a gidan.

    Daman mai hakuri bai iyya fushi ba don ita da iyya gaskiyar ta, bata d’auki kome ba yama za’ace a iyya tsawon zamansu bata taba sata ba? sai yau sannan ita aitafi karfin sata tunda bayar matsiyata bace ita, sosai ta fara maida martani kowa ya gaya mata bakar magan fad’a masa take ita ma, ana cikin haka abie ya dawo daidai lokacin dada ke zagin hafsa, ita kuma ta gaya mata bakar magana, daman tun asali bata son zaman ta da d’anta, shiyasa ta had’a baki aka lika mata sata.

    Abie babu tambayar ba’asi yaja ummi d’aki ya rufe, duk da sumayya yarinya ce, amma a ranan tasan gidan shugaba sunyi ma mahaifiyar ta ba daidai ba, duka abie yama ummi kamar zai kasheta daker aka kwaceta.

    Cikin kuka ummi ta kira kawar ta a waya don ta tsorata lokacin, ganin jini nabin kafafunta, bayan zuwan kawarta, asibiti ta kaita ashe karamin cikine da ita wanda likitoti suka tabbatar daya zube, ga rauni kota ina a jikinta, wayar hafsa kawarta ta d’auka ta kira iyayenta, ta fad’a musu duk abinda ke faruwa tun zaman hafsa a gidan, kamar yanda hafsar ta taba fad’a mata.

    A ranan mutanen borno suka diro Taraba, cikin tsananin bacin rai, direct hospital suka dosa, duk da isan dare sukayi, ganin halinda hafsa take ciki abin yayi matikar musu ciwo sosai, kotu suka maka abie Amma ina abin ya gaggara saboda iko da kudi da abie suka fisu dashi a jalingo, hakan yasa shari’a taki bima hafsa hakkinta, karshe dai mahaifinta yayi rantsuwa hafsa bazata zauna da Abdul ba, saiya sakar masa da yarinyarsa, ba jinkiri agun abie ya saketa, ya basu takarda a hannu, wannan ciwon yasa mahaifin hafsa yace koh bayan ransa baiyarda hafsa ta kuskura ta sake taka gidan shugaba koh da wasa ne babu ita babu sumayya, ta manta ma ta taba haifar y’a, yajama abie kunne mundin ya taka kafa a gidansa koh sumayya , zai nuna masa ikonsu a maiduguri.

    Wannan shine dalili koh ince musababin rabuwar sumayya da hafsa, su karan kansu yan gidan basuso sakin hafsa ba duk da abubuwan da ta sace musu, Amma bakin Alkalami ya bushe.

    Bayan tafiyar hafsa sosai sumayya ke kewar mahaifiyarta, kullum haka zatayi ta kuka a kaita wajen ummin ta, duk yanda dada zatayi rarrashe ki take, karshe da abie yagaji bulala yake mata kafun tayi shuru, a haka haka ta fara cire abin a ranta, soyayya sosai ake gwada mata a gidan baga dada ba wanda ita ke kula da ita yanzun, d’akinsu d’aya haka matan gidan na mugun sonta da mazan, wannan karon harda safina amasu nuna mata so, ba kamar daba inta ganta kamar ta cinnnta a wuta, sosai yanzun sumayya ke wa yara lalle na wasa, daman tunda haka ta tashi da abin abien ta na kara mata karfin gwuwa, duk da kananun shekarunta don lokacin tana neman shekara 7.

    A wannan lokacin ne safina ta sake yad’a manufarta nason auren abie, kamar wanshan karon ma abie yaki amince wa, amma dada ta murza ido tace bata yarda ba aure dole koh yaso koh yaki, haka abie yana ji yana gani aka D’aura masa aure da safina, batare da son ransa ba, sam sam yarinyar batayi masa ba yaji baya kaunar ta.

    Tirkashi dada batasan wannan aure shine ummul’kaba’isin kome ba…………..🍀🍀🍀🍀🍀

    Anya gobe akwai update kuwa🤔🤔

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

  • Matar Makaho 56-57

    Matar Makaho 56-57

    Page5⃣6⃣&5⃣7⃣
    Tunda muka fitoh Banganta ba.

    Wani irin baki gantaba kuma hauka kike ne khadija koh me?

    Wallahi yaya da gaske nake banga Aunty ba.

    Nashiga uku ni muhammad, yace yana kamo hannun khadija suka tsallaka titi zuwa cikin masallaci sosai suka dudu ba Amma basu ga koh mai kamada sumayya ba sosai abin ya gigitashi, ke khadija a daidai ina kuka rabune wai?

    A kofar fitane fa yaya cunkoso yasa muka rabu.

    Jingina kawai yayi da jikin ginin masallacin shikam dai ya shiga ukun sa ina sumayyar ta shiga ne wai?

    Yaya koh dai aunty gida ta koma ne?

    Wani irin gida kuma khadija bayan saida nace ku jirani a global xaki wanice ta koma gida nadai san sumayya bazata koma gida ba

    Daga khadija har muhammad hankalin su ya tashi har hankalin yan agaji ya dawo kansu d’aya daga cikin su ya tambaye sa

    malam lafiya naga kana ta zaga masallaci kaje ka dawo, tun dazun yanzun fa ana neman 4:00 bazaka tafi gida ba ga kanwarka ma naga kuna ta yawo tun d’azun lfy kam?

    Ina fa lfy wallahi ranka ya dade da matata mukazo masallaci amma ban ganta ba gabaki d’aya na gama iyya dubata amma bangan taba

    Wace irin magana ce wannan ita matar taka yar yayece koh jaririya da za’a nema a rasa koh hanyar gidane bata sani ba?

    Ranka shi dad’e ni nasan bazata koma gida ba tunda nace ta jirani toh tabbas zata jiranin

    Kaga malam karkazo ka d’aga mana hankali a wani unguwa kuke ne?

    Sintali ne..

    Sintali😳A koh B?

    Sintali A ne ranka ya dade

    Amma dai kai d’an rainin wayo ne ina sintali A ina macilin da bazata iyya komawa da kanta ba kazo kana kokarin daga mana hankali?

    Kayi hakuri ranka ya dade

    Na hakura amma ka fita kakama kanwarka kubar masallaci nan ya zakazo da maganar da hankali bazai d’auka ba matar ka ta bata, ina macilin ina sintali?da bazata koma ba

    Kayi hakuri..

    Kama gabanka malam?

    Haka Al’ameen ya fita kaman k’wai ya fashe masa a ciki

    Da sauri khadija tazo ta kama masa hannu haka suka fito a masallacin gwanin tausayi
    Tsallake titi sukayi suna tafiya Gabaki d’ayansu inka gansu kaga wa’inda basu da nutsuwa gabaki d’aya zuciyar Al’ameen bugawa take kamar ance masa sumayya zata barsa

    Sunzo daidai titin doruwa kamar daga sama khadija ta hango mace da hijabi tana tsallako titi Allah yasa akwai wutan sola shiya bata daman ganin wance ta tsallakon da karfi ta kwala ma sumayya kira Aunty!!!

    Ai da wani irin mugun sauri Al’amesn ke magana, kee kin ganta ne ina sumayyar take tana ina?

    Kafun khadija ta basa amsa da gudu sumayya ta karaso karesu”lafiya har yanzun baku koma gida ba”?

    Kee sumayya kina da hankali kuwa banace miki kafun mu shiga masallaci, kujirani a gidan man sintali ba koh ba haka nace ba, shine zakisa kafa ki koma gida don tsabar kin raina min wayo gani d’an iska koh?

    “Don girman Allah kayi hakuri, wallahi sace mini takalmi akayi shine na tsaya nema na jira mutane suka fifita duk ban gane ba dana fitoh wajen global, nan ma ban ganku ba shine nayi tunanin kun koma gida saina koma nima danaje kuma naga baku dawo ba, shine nabiyo ku”

    Don Allah yaya kayi hakuri tsabani aka samu!

    Na hakura khadija Amma sumayya karki sake mini haka Am warning you?

    “Insha Allah” tace tana kama hannunsa dake cikin na khadija don baizo da sanda ba suka tsallaka titi

    Bayan sun isa gida ganin sun kusa makara yasa sumayya hana khadija zuwa gida abincin sahur ta iba mata tuwo ne miyan kifi d’anye suka zauna a waje suna ci

    Al’ameen kam tuwo kawai yakeci da miya baya cin kifin

    Da mamaki sumayya tace “yayan khadija ya bakacin kifin gashi mun kusa makara fa”?

    Sumayya bazan iyya cin kifi d’anye ba kar kashi ya makale min a wuya

    ” tarwad’a ne fa”

    Nikam ah ah

    Hannu sumayya tasa a kwanon miyan ta yago kifi tasa mai a baki”toh bude bakin nasa maka”

    Da sauri khadija ta kauda kai kamar bata gansu ba don wallahi sun bata kunya

    Al’ameen kam bude baki yayi sumayya sai da ta ciyar dashi kifi har yace ya isheshi kafun ta ci nata

    Bayan sunyi sallan asuba khadija ta koma gida Al’ameen kam bacci suka koma suna ramakon na jiya

    Yau koh tafsir basu samu zuwa ba saboda baccin dake idanun su har 12:00 suna bacci a d’aki

    Assalamu Alaikum!! wasu yan matane guda hudu ke sallama sunfi minutes 8 suna buga sallama shuru

    Al’ameen kamar a mafarki yake jin sallama akai akai mikewa yai hade da amsa musu

    Ina kwana?

    Lafiya, ya amsa

    Am wajen sumayya mukazo

    Ok lafiya kam?

    Eh munzo tambayar lallen sallah ne

    Ok bara na tada ta

    Ah ah ka barta in bata tashi ba inyaso gobe sai mu dawo

    Ok toh Allah ya kaimu

    Ameen, in ba damuwa inta tashi kace yaran gidan Malam yunusa ne sukazo tambayar Lalle kar wasu suzo su riga mu?

    Toh yace yana d’aukar boket bayan sun fita wanka yayi ya shiga dakin dayake yanzun yasan soket in kunna TV jin an kawo nepa ga fanka na hura d’akin danna soket in yayi daman jiya sunnah suke kallo aka d’auke, zama yayi yana sauraron wa’azi hannun sa d’auke da calbi yana ja

    Sumayya bata tashi ba sai azahar nan ma shiya tashe ta kafun ya tafi masallaci

    *******************
    Haka rayuwa yayi ta tafiya axumi nata karewa a hankali hankali customers na sumayya suke zuwa tambayar lalle tun sallah saura kwana goma ita karan kanta batasan adadin wa’inda suka tambaye lalle ba ita dai ta amsa zatayi amma suzo da wuri, sannan tana musu tallan wanda zaiyi kitson sallah kanwar mijinta nayi ai kuwa khadija ma tatara customers sosai,

    kayan sallah ma bana muhammad ne ya d’auke sumayya da khadija har kasuwa sukayi sayayyan sallah duk da sumayya taki yarda ganin tana da wasu zanunuwan a akwatin ta amma ina yace na akwati daban na sallah daban, ba laifi yasai musu kaya itama ta dad’a wasu da kudin ta haka ma khadija ta kara mata har kala biyu bayan wanda ya musu she karan kansa gezena biyu yasaya sumayya ta kara masa biyu duk sunka kai dinki.

    Akwana A tashi yau dai saura kwana d’aya sallah kofar sumayya makil da jama’a daga masu kitso harda masu lalle, harda su suwaiban adara yau ana bin layi a kofar, sumayya na hango sanye da riga da wando baki tana ta fama da lalle sai khadija dake ma wata yarinya kitson brazil kulu da bit

    Har yamma mutane ne makil ba ita ta rabu da mutane ba sai kusan goma na dare nan ba hakuri ta basu akan gobe su dawo da asuba

    Al’ameen dake d’aki kwance yana lazimi shiya raka khadija gida

    Yau sumayya koh girkin asuba bata samu tayi ba na bud’a bakin ma watace ta mata girki tana ma yarta lalle

    Yauma bayan sunje tahajjud suna dawowa ne suka samu tuwo a bakin titi na asuba suka saya, dashi sukayi sahur

    Sumayya suna komawa gida suna sallah ta kwanta ai koh gama d’aukarta bacci baiyi ba tafara jin sallaman mutane ga idonta duk bacci kin tashi tayi Al’ameen ne ya fita ya basu hakuri akan sumayya na bacci Amma haka bayin Allah nan sukaki tafiya taburma suka shimfid’a suka zazzauna🤣suna jiran sumy(masu lalle gaskiya kuna ganin abu a sallah har kwana ana muku a d’aki)

    Surutun su shiya hana sumayya komawa bacci haka tanaji tana gani ta kasa bacci dole yasa ta fitoh jin jama’a sai dad’uwa suke

    Ai tana fita saiga khadija da tawagar masu kitso sun tasata a gaba😎

    Haka suka dukufa suna neman halal nasu,

    Al’ameen fita yayi a d’akin sumayya! yakira sunan ta

    “Na’am”ta amsa tana mai mikewa ta bisa d’akin ganin ya koma

    Sumayya zan fita na karbo mana dinki, maganar zuwa kasuwan fa muna sa ran gobe sallah fa naga bamu shirya kome ba?

    “eh kam gaskiya nima naso naje kasuwan nan da kaina amma yanzun ba iyya fita zanyi ba sai dai ku tafi da khadija in yaso sai na rubuta mata list”?

    Ok nace na saya mana watanda ne?(naman shanu da ake yankawa a ranan jajeberi ana saidawa a unguwa)

    “Ah ah ka saya mana kaji gaskiya tunda sallah ne”

    Shinkafa koh tuwo zakiyi?

    “Habba tuwo ranan sallah, shinkafa zanyi da miya sai coslow da kaji sanan zanyi masa da miya”

    Ok daman so nake ranan sallan nan mu kaiwa gidan su Ammar abinci kuma muje mu gaida iyayen sa sai kuma nayi tunanin kar suce don kudin su yasa muke son rabansu fa?

    “Ah ah yayan khadija in zakayi abin Alkhari kayi kawai karma ka bari shaid’an ya saka maka wani tunani daban a ranka kaji”?

    Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben kinyi lalle kuwa?yana maganar yana kama hannun ta

    “Ina naga lalle daga ni har khadija ba lalle ba kitso”

    Kai gaskiya nifa an takurani tun sallah saura kwana hudu ban sake cin abincin kiba ki taimaka ki mana girkin sallah da kanki

    “Insha Allah la’asar nayi zan sallami kowa wanda ya samu da wanda bai samu ba duk sai suyi hakuri nima na samu nayi aikin sallah”

    Ok kiramin khadijan inkin gama rubuta list in mu tafi

    Haka koh akayi sumayya list ta rubuta ta baiwa khadija duk yanda jama’a masu kitso suka ringa roko sai da sumayya ta d’aga khadija suka tafi kasuwa

    dinki suka fara karbowa sai cefenen da sukayi sosai sukayi cefene sai da ya cika bairo.

    Bayan khadija ta dawo sumayya tashi tayi ta gyara kajin duk da wasu sunso karba mata Amma taki yarda soya kajin tayi daman guda biyar ya saya ta rabawa mutane d’aya sosai tayi ta ayyukanta wasu kamma ganin aiki take kuma ba karewa zaiyi ba, zuciya kawai sukayi suka tafi abinsu wasu kam kama mata aikin sukayi duk da ta nuna su bari amma kin bari sukayi wasu sun gyara mata tattasai wasu sunkai nika cikin kankanin lokaci ta kammala had’a abubuwan sallan ta miya ma ta soya amma bata sa ruwa ba saboda ba’a tabbatar anga wata ba vegetables ma bata yanka ba tadai sasu a firij ne

    Bayan Ansha ruwa sumayya sallamar mutane tayi wa’inda bata musu ba ta basu hakuri wasu kuma sukace gobe koh jibi zasuzo Amusu

    Yau kam saida muhammad ya saya mata matsala 8 tasha tsabar yanda bayanta ke ciwo amma fa gaskiya ta samu kudi bana wasa ba a sallan nan khadija karan kanta kudi ta samu sosai

    Har dare ba’a sanar anga wata ba haka su sumayya suka kwanta da niyar inba’a gani ba zasu tashi da azumi

    Aiko hakance ta faru don da asuba ji sukai ana atashi ayi sahur jama’a gobe ba sallah bane😌

    Ai yau kam sanin da sumayya tayi ba karamin mutane ne zasu zo ba yasa tana sallan asuba ta tattara boron lallen ta tayi gidan goggo Al’ameen ta bari a d’aki yana bacci tace masa zata saloon gyaran gashi sai tayi lalle tama khadija

    Gidan goggo taje tayiwa khadija lalle ja da baki itama tayiwa kanta sai dai bata ma hannun dama ba manna masa gam tayi khadija tasa mata lalle akai

    Lallen su na kamawa ita da khadija saloon suka wuce aka gyara ma khadija gashi don ita kam bata wanke kanta a sefe, kitso khadija ta watsa mata a saloon sai kusan la’asar sumayya suka dawo, kai taga ikon Allah jama’a ne tirem a kofar ta Al’ameen ya rufe kofar d’aki ya fita sukam suna zazzaune a baranda

    haka ba yanda ta iyya ta hau musu lalle

    Dayake ana da tabbacin gobe sallah ne yasa khadija had’a musu miyan sallah ta d’aura zobo tana gama had’awa ta juye a robobi tasa a firij

    muhammad ma ya turo kayan marmari da sumayya tace zata markad’a a blander tayi juice dashi

    Sai dare sosai mutane suka watse ita da khadija suka kai nikan shinkafa bayan sun dawo suka kwaba, yaukam khadija a gidan ta kwana da sumayya a waje yayanta na d’aki

    *RANAN SALLAH*
    yau take sallah ranar farin ciki ga dukan wani musulmi kowa ka gani fuskar sa d’auke da farin ciki hakan take a wajen su sumayya tun asuba khadija ta fara tuyan masa

    sumayya ma wuta ta hura ta d’aura shinkafa don yau dai ba’a gas koh hot plate za’ayi girki ba

    Vegetables inta ta kama yayan kawa su green beans green pepper yellow pepper piece cabbage carrot harda k’wai ta d’aura a wuta ga babban kwalban BAMA a zaune agefe

    karfe 7:30 sumayya sun gama girkin sallah,
    manyan kulolin ta masu shegen kyau, bata taba bude suba sai a ranan mai guda biyar ne ta zuba shinkafa masa coslow miyan ganye da miyan stew sai manyan manyan kofunan zamani ta juye zobo a ciki d’aya kuma mango juice duk sunyi sanyi har suna raba ta sake maidasu firij, wannan na gidansu Ammar kenan, sauran juyewa tayi a babban kula haka ma miyar duk d’aki ta shigar dasu sanin halin mutanen gidan

    Wanka tayi ita da khadija suka saka kayansu mai kyau da hijab Al’ameen ma gezena insa sabo ya saka koh sanda sumayya ta hanasa rikewa ita ta kama hannunsa khadija ta rike musu sallaya rufe kofa sukayi lokacin karfe 8:30 sauri suke karsu rasa sallah

    Suna fita a gidan sun tsaya a bakin titi amma ba keke koh wani keke suka tare a ciki haka suka fara takawa, kamar hadin baki saiga Ammar ya shawo kwana da motar sa packing yayi a gabasu hade da budewa ya fitoh sanye yake da wani d’anyen yadin shaddane mai kyau sai hula da takalmi agogonsa sai d’aukar ido yake.

    Ashe gwara danayi sauri tun d’azun ina ta tunanin bazan same kuba taima ?

    Laii Ammar kaine sannu ina kwana?

    Lafiya muahmmad barka da sallah.

    Ai ba’ayi sallar ba tukum, muhammad ya basa amsa

    “Ina kwana”?sumayya tace tana had’a fuska ganin yauma kamar kullum idonsa akanta

    Lafiya sumayya muntashi lafiya?

    “Lafiya mungode Allah”

    Khadija kam kuri tayi tana kallon sa toh a ina tasan bawan allah nan ne kam ta kasa tunawa, a hankali ta ma sumayya magana, aunty nikam a ina kukasan wannan ne?

    “Habba khadija kin manta mutumin da yazo asibiti lokacin da za’a mini tiyata ya baki kudi ki ban”

    Oh na tuna na tuna Aunty , ina kwana?tana gaida Ammar

    kin amsawa yayi hannun muhammad ya kama muje koh ku shiga mota muyi sauri karmu rasa sallah

    Ba musu dukansu motar suka shiga yaja suka kama hanyan masallaci

    Allahu Akbar anyi sallah lafiya jama’a kamar kasa suna ta fitoh wa a edi kowa ka gani fuskar sa a washe sai gaisawa ake da juna abin gwanin sha’awa kowa na sanye da sabin kaya sai dai na wani yafi na wani tsada

    Bayan su Ammar sun fitoh a cikin cunkoson jama’ar dake masallacin, yaso kaisu muhammad gidan su amma sukace ya maidasu gida zasu d’auko abincin da zasu kai gidan nasu

    Ba musu ya mai dasu gida abincin muhammad ya d’auko musu a kula ya fitoh waje dasu juice taburma ya shinfid’a musu ba kyama Ammar ya zauna sukaci abincin da muhammad sai santi hake don gaskiya abinci ne na kece raini

    Ta bangaren sumayya abinci ta sassaka a kwanuka ta baiwa khadija ta rabawa mutanen gidan ADARA kowa da plate nasa ta zubawa goggo ma ta kai mata tana dawowa sukaci abinci tukum kafun suka sake wanka lokacin azahar yayi sallah sukayi sumayya ta watsawa khadija make-up sosai khadija tayi kyau tana sanye da dogon riga na zani holland mai shegen kyau sai gyele da jaka tare da takalmi hada agogo da su sarka masu azaban tsada sosai sumayya ta kashewa khadija kudi a sallan nan

    Ita kam les tasaka sai mayafin ta babba powder kawai ta shafa sai kwalli da man baki don A matsayin ta na matar aure hakan baidace ba tayi kwalliya ta fita tana d’aukar hankalin maza

    Al’ameen ne ya shigo duba su sumayya sun gama shiryawa ne Ammar ya dawo yana jiransu

    “Don Allah yayan khadija ka sake wanka mana ka chanja kayan jikin kan nan”?

    Meya samu na jikin nawa?

    “Ba kome amma dai ya kamata ka chanja tunda gidan masu kudi zamu gwara mu kece raini”

    Kai sumayya kin cika shirme amma dai bara na watsa ruwan shap shap yayi wanka ya fitoh sabon gezena da sumayya ta d’inka masa shiya saka mai tsadane sosai sai takalmi da agogo yau harda glass sumayya ta d’auko tasa masa lias na hannu riga duk ta makala masa, hannunsa ta kama suka fitoh bayan khadija ta rufe kofar

    Kulolin suka d’auko guda biyar sai jup na juice da zobo duk suka jera a boot na motan Ammar

    Tunda sumayya ta fitoh idon Ammar ya sauka akanta gabaki d’aya ya tatara hankalin sa
    Gareta sai kallon ta yake kamar idanunsa zasu zazzago

    Sumayya kam tun fitowar ta ta lura da kallon da Ammar ke mata kamar maye duk d’aga ido da zatayi sai sun had’a ido ganin yanda duk yabi ya zuba mata na mujiya yasata juyawa da sauri cikin haushi tayi cikin gida

    Khadija dake kokarin shiga motar ganin sumayya tayi cikin gida yasa ta kwala mata kira, aunty sumayya kin manta wani abune?

    Sumayya koh juyowa batayi ba tayi shegewar ta ciki

    da sauri Al’ameen ya fita a motar jin khadija tace masa sumayya ta koma cikin gida yabi bayanta……….

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    08146017245 *hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na maman haidar*
    *Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah*

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

    *1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀
    2 *Gumbar ayu zallah* 🍀🍀
    3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀
    4 *Kaza mekwai* 🍀🍀
    5 *Zabo me zuma*🍀🍀
    6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀
    7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀
    8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀
    9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*
    10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar sanyice gwada wnnn*
    11 *Maganin nono. Sahihi*
    12 *Maganin hips and bobbs*
    13 *hodar. Ni I’ma koramar mata*
    14 *nakasan Mara babban sirri*
    15 *kafi jijjibi*
    16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*
    17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*
    18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    *Maman haidar Bata tsaya anan ba*
    *takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeta awannan number* 08146017245
    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

    *Wannan page nakune Queen fauzee da ogan ki naga comment naki jiya*😂

  • Matar Makaho 64-65

    Matar Makaho 64-65

    Page6⃣4⃣&6⃣5⃣
    Mafarki yake koh gaske, da idanun sa yake kallon duniya, wanda rabon sa daya gani yanzun ana neman shekara 13, Allahu Akbar Tsarki ya tabbata ga Allah, Alhamdulilah Alhamdulilah, shine abinda yake maimaitawa

    Mikewa yayi da sauri yana bin koh ida da kallo, kamar wani dolo, shi ganin abin yake kamar mafarki ne, an jima zaici gaba da ganin duhu,sai bin wajen yake kamar daji, haka ya ringa takawa a hankali yana tafiya cike da Al’ajabin abinda ke faruwa yau dashi, shine da kallo?

    Hango gonaki yayi a shimfide, gwanin sha’awa na kayan labbu, ga kogi babba yana gudana da gudu yayi saitin kogin da saurinsa ya shiga ruwan, don wallahi azababben kishi yake ji, ai yana shiga kogin ya tsoma hannun sa cikin ruwan ya iba yasha, ya sake tsoma wa ya iba yasha, kamar wasa yaji ruwa yana jansa daga bakin gaba, har tsakiya sai kokari yake ya fitoh amma ina abin yaci tura, salati ya fara yana innalilahi, wasa wasa ruwa ya fara nitsar dashi sai kokowa yake da ruwan, duk kokarin sa na fita, abu ya gagara, daman shi ba ruwa ya iyya ba, ina makaho ina rafi, koh lokacin tasowar sa baiyi yayin bin yara kogi ba.

    Sosai ruwa ya hadiye sa har wuya, sai kokari yake Amma ruwan yafi karfinsa, zuwa wani lokaci, shuuuuuuuu yaji ya burme cikin ruwa, da sauri yayi tsalle yafitar da kansa, sai kuma yaji ya sake komawa, kamar wasa Al’ameen ya fara shan ruwa, sannu sannu har yaji ruwan yaci karfinsa, tun yana gani dishi dishi har yaji bayanan ,

    Gid’ado ne tsaye da shanun sa, daya koro bakin gaba susha ruwa, kamar wasa yaga shanukan sa, na kuka a bakin gaba, Alamu dai wani abin suka gani.

    Da sauri ya karaso wajen don yayi tunanin kada ne, koh wani mugun abu, tsayawa yayi turus yana bin abinda yake gani shida dabbobin sa, mutum ne, kwance baya motse kamar gawa, da sauri ya kad’a shanunsa har ya juya zai tafi don gudu rigima, daman ba shiri suke da manoma ba kar ace shiya kashesa, ya shiga uku.

    Sai kuma ya sake dawowa, haka kawai yaji hankalin sa bai kwanta da tafiya yabar gawan ba, nade kafar fantalelen wandon sa, na kiwo yayi ya shiga ruwan, jawo Al’ameen yayi, kiiiiiiiiii ya fitar dashi a ruwan, ajesa yayi a kan tabon bakin kogi.

    Kurawa fuskar Al’ameen ido gid’ado yayi tabbas wannan ba kabila bane, duk da fuskar tayi irin na fulani,Amma ba fulani husul bane, kyaun sanan akwai mix,ganin Hakan yasaka sa ciccibar Al’ameen, ya d’aura a bayan wuyansa yayi Rugan su dashi.

    Tun daga mahadin rugan su ake binsa da kallo, ganinsa d’auke da gawa a wuya, kowa ya tare sa, cemai yake shima a ruwa ya gansa, sosai wasu ke zagin sa meye na kawo musu gawa salon ya jaza musu bala’i, Amma shi sam bai damu ba tafiyar sa kawai yake.

    Isarsa gida ya tarar da mahaifinsa zaune a gindin bishiyar tsada a tsakar gidan su, sai innar sa dake gindin murhu tana girki.

    Assalamu Alaikum

    Waalaikum…….sai kuma ta dakata, bata ma karasa amsa sallamar ba, hadde yan boni, gid’ado dun dume, miyiyata do ha bahoma?(me nake ganin nan a bayan ka)

    Shuru yayi yana kallon ta, ganin yanda gabaki d’aya tabi ta gigice, bappan sa dake zaune a gindin bishiya ne, yayi saurin tasowa jin abinda inna kece wa.

    Gid’ado d’obo?bappan sa ya tambaya, yana nuna Al’ameen dake kafadar gidado.

    Bappa, kuyi hakuri bara na sauke sa sai in muku bayani, duk cikin fulanci suke maganar.

    Wani irin mu kwantar da hankali?kawai ka ciccibo mutum baya motse a kafad’ar ka, ka shigo mana ruga akan me?

    Don Allah inna a wad’a muyal, nima ganin sa nayi a bakin gaba, alamu dai ruwane ya jasa, koh aka yardashi, gidado yace yana kallon matarsa data fitoh daga d’aki, d’auke da tsohon ciki tana nufosu.

    Kwantar dashi gid’ado, in yaso koh sallah Amasa tunda naga kamar musulmi ne, bappa yace.

    Sauke sa gidado yayi, sosai bappa ya kurawa fuskar muhammad ido, yana nazari sai kuma ya d’aga ido yakalli gidado, Ai ohmayai(ai bai mutu ba)suma yayi.

    Da sauri gidado ya kara maimaitawa suma bappa?

    eh, yi sauri ka d’auko mini kwaryar magani a bukka, yana maganar yana dukawa kusa da muhammad, danne masa ciki ya farayi, take ruwa ya fara fita, ta bakin sa duk da baiyi motse ba, amma dai ruwan na fita sosai, bappa ya mammatse masa ciki.

    Matar gidado kam kujera ta samu ta zauna a hankali daker, sai ga gid’ado ya fitoh bukan bappa, da sauri ya ajewa bappa magani a gefe, bappa da lenki mai.

    Maganin bappa ya d’auka a kwarya, yana shashafa ma Al’ameen a fuska, da wuya yana masa Tofi,yana gamawa ya d’aga ido ya kalli gidado, husumo ayara ha sudu(ka daukesa ka kaisa d’aki)

    Wai bappan gidado ban gane a d’auke sa akai sa d’aki ba, yadaga ganin mutum bamusan daga ina ba, mugune koh nagari?kawai mu d’auko mu aje a cikin gidan mu, ni gaskiya ban yarda ba.

    Talatu kena bani mamaki wallahi, yanzun ace mutun baya cikin hayyacin sa, ina kikeso mu kaisa?

    Koma ina a kaisa, amma dai gaskiya banda cikin gidan nan, taima ma mugune.

    Koh mugune, mu Allah zai dubi zuciyar mu, insha allah bazai basa ikon cutar damu ba, bare ma wannan yaro baiyi kama da mugu ba, daga ka gansa kasan akwai jinin fulani a jikin sa.

    Lantana matar gidado kam, mikewa tayi ta shiga d’aki ganin fad’an bappa da inna baya karewa in gari ya waye .

    Kai gidado d’auke sa ka kaisa d’akin kusa da gindin murhu.

    Toh bappa, yace yana ciccibar sa yakai d’aki, shanu kansa dake binsa a baya tunda ya d’auko Al’ameen har gida, suya kama ya d’ad’aure a turke…….

    **************************
    Ta bangaren sumayya yau satin ta d’aya a Hospital, har da kwana d’aya, Amma jikin dai za’ace Alhamdulilah, da sauki kad’an duk da baiyi kwari ba, sosai likitoti ke kula da ita, hatta Dr tana iyya bakin kokarin ta, ganin sumayya ta samu lafiya, Amma taki kwantar da hankalin ta sam.

    Khadija ma yau sati guda, rabon ta da makaranta,suna faman jinyan sumayya, Goggo ke zama a asibiti, ita kuma ke musu girki a gida ta kawo musu, duk da sumayya baci take ba, sai yan aikace aikacen gida duk ita keyi.

    Kamar yau ma, khadija ce ta kammala girki a kofar sumayya, zuzzubawa tayi a kula, tasa a kwando ga flask a hannun ta, ta fitoh gidan Adara, tsallaka titi tayi ta nufi shagon yayan ta, shagari ta samu zaune yayi tagumi gabaki d’aya yaron ya shiga damuwa ainu na b’atan Al’ameen, duk da shike kula da shagon yanzun, amma sai yanajin shagon kwata kwata baya masa dadi.

    Assalamu alaikum.

    Wa’alaikumu salam, khadija zaki wuce hospital in kenan harkin shirya?

    Eh na gama girki.

    Ok yace yana mikewa, laida ya d’auko ya zuzzuba ayaba da kankana mai yawa, ya rufe shagon, kwandon hanun khadija ya kamar ba, ya bar mata flask in yana rike da laidan kayan marmarin a d’aya hannun, suka kama hanyar FMC da kafa, don shagari duk da muhammad baya nan, amma baya masa Almubazza ranci da kudi, asalima tattalin sa na yanzun yafi nada, hatta kudin asibiti duk Abinda aka bukata shiyake biya, ya hana sumayya kashe koh sisi.

    Sunzo sharan kwanan doruwa, kawai suka ga anyi packing moter a gabansu, khadija kam koh duban motar batayi ba, kokarin kaucewa take ta gefe, ta wuce abinta, dayake shagari bai wani waye Ammar ba, yasa bai ma saurare saba yabi bayan khadija.

    Ke yar kauye, mai tafiya bata kallon gaban ta.

    Da sauri khadija ta d’ago jin muryar Ammar,ina kwana?tace.

    Kin Amsawa yayi ya dubeta, ina zaku kuma da abinci haka.

    Asibiti, ta basa Amsa.

    Waye ba lafiya?

    Aunty sumayya .

    Subhanallah, yayan naki nacan ne?nima yau na dawo da asuba, shine nace bara na biyo gunsa.

    Shuru khadija tayi bata basa Amsa ba, sai kaucewa da tayi taci gaba da tafiya.

    Da sauri ya fitoh a motar, yabi bayan ta, keee ba magana nake miki bane?kina tafiya?

    Kala batace ba, tana ta tafiyar ta.

    Hannun ta Ammar ya rike, da sauri ta juyo tana kallon sa, sakemin hannu?

    Naki na saken, ina miki magana kina manna mini hauka, ina wasa dake?

    Kuka khadija ta sake masa da karfi, ai da sauri Ammar ya sake mata hannu, ya juya yana kallon shagari, dake tsaye yana kallon su, fuskar sa A hade, haka kawai yaji ya tsani Ammar, ganin yanda ya wani rikewa khadija hannu.

    Kai meke faruwa ne?Ammar ya tambaye sa.

    Fuska a hade yace, An sace oga ne shiyasa daka mata maganar, ina yayan ta, take kuka.

    Sai a lokacin Ammar ya gane shagari, watoh shine wanda muhammad yace zai d’auko su zauna a shago, abu na biyu daya basa mamaki kuma wai an sace muhammad, sai kace kaza, ban gane an sace saba?

    Eh an sace sa, haka kawai wasu a mota sukazo suka d’auke sa, a bakin titi

    Tsabar razana har tuntube yayi, yau kwana nawa kenan?

    Sati d’aya.

    Amma har sati d’aya, police basu d’auki wani kakkauran mataki ba?mutum ya bata kamar wani kaza koh d’uriyan sa babu?

    Koh report bamu shigar ba, Shagari ya basa Amsa.

    What?? ba’a kai kara ba, akan me?

    Sumayya na asibiti, ni kuma tsoro nake ji, shiyasa ba wanda yakai.

    Amma ai koh baku kaiba, nasan labari zaije wa yan sanda, tunda kuna kusa da station, yaci su subibiye Lamarin.

    Shuru suka, masa.

    Ku shiga muje asibitin, yace yana karban flask in da khadija ta dongorar, yasa a mota.

    Shagari ma shiga yayi ya zauna a gaba, har lokaci tana tsungune a kasa, hannu kawai Ammar yasa ya fizgota, ya jefa a bayan motar, ya zagaya driver sit ya zauna, yaja motar suka nufi Hospital.

    Suna shiga hospital in, dashi da shagari ne suka d’auko kula da flask, harda laidan, khadija kam an kaikaya mata inda yake mata kaikayi, kuka har lokacin yinsa take, duk yanda shagari keta bata baki tayi shuru, amma ina.

    Keeee wallahi in na sake jin koh tarinki, a asibitin nan saina saba miki, banason shirme tun d’azun, sai cika min kunne kike nayi shuru, yanzun mun shigo asibitin ma bazaki rufe bakin bane? saikin tara mana jama’a.

    Shuru khadija tayi, harga Allah wannan Ammar in kamar mai Aljanu haka yake, zafi zafi sanyi sanyi.

    Shagari kam gaba ya kara, dayake yasan d’akin da sumayya take, bai saurare tahowar suba, yayi tafiyar sa, yana maijin haushi a ransa.

    Shiya fara shigowa d’akin, da sallama.

    Amsa masa sumayya tayi, wance ke zaune daga ita sai dogon rigan kanti, kanta koh d’ankwali babu, tana zaune a bakin gadon, rike da wayarta, hawaye nabin kumatun ta.

    Ina wuni Aunty, ya jiki?

    Kai kawai ta d’aga masa, ta mika hannu ta d’auki d’an kwalinta, dake gefen gadon ta yafa a kanta.

    Zama shagari yayi yana bin d’akin da kallo, ganin baiga goggo ba.

    Assalamu alaikum, Ammar ne yayi sallama a bakin kofar d’akin.

    Amsa masa shagari yayi, ba tare da ya d’ago yaga bakin kofar ba.

    itama sumayya bata d’ago ba, sanin wake sallamar, don ta shaida mai muryar.

    Shigowa Ammar yayi, idanun sa ya sauka akan sumaya, dake zaune gabaki d’aya ta chanja, ta rame sosai sai haske data kara a yan kwanakin nan, har yayi yawa,tayi fari kamar ka tabata jini ya fitoh.

    A hankali ya tako har inda take, hannu yasa ya amshe wayar, sai a lokacin sumayya ta d’ago ta dube sa, hade da mika masa hannu, Alamun ya bata wayar ta.

    Matsawa yayi gefe, ya kurawa screen in wayar ta ido, hoton tane da suka d’auka, ita da muhammad ranan sallah a gidan su.

    Sumayya ya kamata kima kanki fad’a, wannan abinda kike kara cutar dakan ki kike, kuka bashi ne magani ba, koh mafita, kin zauna kina kuka, gaki ba lafiya bane dake, ki dubi yanda kika koma fisabililahi.

    Gaya mata kam D’an nan, haka nake fama da ita, bansan me take gani a wayar nan ba, ta tura khadija ta d’auko mata, shikenan tamai dashi madubi, tana kallo tana kuka, goggo data fitoh a toilet na d’akin ne take maganar.

    Hoton mijin tane a ciki mama, Ammar yace yana latsa wayar sumayya, dake hannun sa.

    Au shiyasa take kuka?/lalle sumayya baki jiran kanki, kiga yanda kika zama gabaki d’aya kin koma, kashi da rai sai haske da kike tayi kamar mai ciwon far d’aya.

    Kyaleta mama, hotunan duka zan goge.

    Kuka sumayya ta sake, jin abinda Ammar yace wai zai goge hoton muhammad a wayar ta”ka bani wayata karka goge na rokeka don Allah”

    Ah ah bafa zan baki ba, in gaya miki, tunda zaki tasa wayar a gaba kina kallo kina kuka.

    “Allah nayi Alkawari zan daina” tana magana tana kuka

    Toh yanzun me kike in ba kukar ba?

    Don Allah ka bata wayar ta, sai kuka take tana maka magiya, kana wani ja mata rai, khadija ce tayi maganar cikin jin haushi ganin iyayin da yake ma Auntin ta.

    Wani kallo Ammar ya watsa mata, jin maganar da take masa kamar sa’arta.

    Bata sake magana ba, aje abincin tayi tana kallon sumayya, in zuba miki Aunty?

    “Ah ah banaci”

    Wani irin bakici?sumayya yau kwanan mu tara a asibiti, abinci kirki baki ciba ya za’ayi kiyi lafiya.

    Shuru sumayya tayi, ta koma ta kwanta bata kara magana ba, don ta fahimci bazasu gane abinda ke damun ta ba.

    Ammar kam kallon khadija yayi ya sake kallon, Goggo,meke damunta , sukace mama?

    Damuwa ce d’an nan, hawan jinine ya kamata, maimakon ta nutsu ta samu lafiya, Amma ina sai kara kwantar dakan ta take A gado.

    Allah ya bata lafiya, in ba damuwa mama, ina so zan fara bincike akan case in batar Al’ameen, in muna bukatar cikekken bayani zan tuntube ku.

    Ba kome yaro mun gode, Allah ya saka sai dai ban gane kaba?

    Abokin muhammad ne.

    Au koh dai kaine Ammar, da yake sanar dani ka bude masa shago?ai munga abin Arziki Allah ya biya ka.

    Ameeen mama.

    Sai a lokacin shagari da khadija, suka san Ammar ne ya bude ma Al’ameen shago.

    Fita Ammar yayi bai bawa sumayya wayar taba, ita ma bata sake magana ba.

    Ta bangaren Al’ameen kam har dare bai dawo hayyacin sa ba, gidado yayi ta zuwa dubasa yafi a kirga Amma shuru.

    sai da gari ya waye, ya farka jujjuyawa yayi sai kuma ya bude idanun sa, da sauri ya koma baya da mamaki, ganin yarinya budurwa zaune a gaban sa kyakky……………..🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

     

  • Matar Makaho 94-95

    Matar Makaho 94-95

    Page9⃣4⃣&9⃣5⃣
    Bayan ta ya rike sosai ga wani irin ciwo da taji a maranta lokaci d’aya ta gigice tana salata tunda take bata taba jin ciwo irin na yau ba, Ambaton Allah kawai take a ranta gabaki d’aya ta had’a gumi, jin wani abu na zuba babu control ya sata tsorata ruwa ne yake dundula, salati ta sake hade da kwalawa khadija kira.

    Khadija dake bacci kamar a mafarki taji muryar sumayya mikewa tayi ta nufi ban d’akin da sauri ta bude wazata gani? sumayya ce duke jikinta sai rawa yake gabaki d’aya ta had’a gumi a tsorace take tambayar ta haihuwa ne? sumayya bata samu Amsan bata ba, nuni kawai ta mata ta kira mata mota su tafi asibiti, ba musu khadija tad’au hijab tasa akan kayan baccin jikinta, ta ruga da gudu ta fita a falon, sakatan get in ta zare ta fita bakin kwalta, abinka da dare koh tsuntsu bata samu ba koh ina shuru, kuka ta sa da gudu ta dawo cikin gidan, kofar d’aya makwanciyar su ta wuce tana buga wa, amma basu bude ba gashi kaf gidan babu mai mota koh mijin laila ma ba motar bane dashi.

    Haka da dawo sashen su, tana shiga zuwa lokacin jikin sumayya ya kara tsanani sosai koh zama ta kasa har lokacin tana tsungune.

    Da sauri ta d’auki wayar ta layin kalamu ta kira, sai da ta masa kusan 4 miss call kafun ya d’aga cikin muryar bacci yake tambayar ta lafiya?

    Ai tana sanar dashi da sauri ya mike ya zura jallabiyar sa ya fitoh a d’akin sa, harya tura kofar falon su zai fita saiga nannen sa ta fitoh daga dakin ta, tambayar sa tayi ina zaije a daren nan?

    Sanar da ita yayi Auntin khadija ba lafiya tana labour, tambayar sa tayi mijin tafa,Amsa ya bata shidai bai taba ganin mijinta ba, yama ga alamu bata da miji, jin haka yasa nanne d’aukar hijab nata ta sanar da mijinta zasukai sumayya asibiti, suka fitoh tare dashi mota kalamu ya fitar suka shiga sai get insu sumayya, fita nanne dashi sukayi zuwa ciki.

    Zuwa lokacin sumayya tayi laushi sosai koh gane wake kanta bazata iyya ba, dayake dare ne nanne da khadija ne suka ririketa yayinda kalamu ya diauki akwatin ta, data jima da shiryashi a zaune, rufe musu kofar yayi suka tafi asibitin da sumayya ke awo.

    Suna zuwa aka karbesu nanne na zaune a waje ita da khadija, kalamu keta hidima na sayyan abubuwan da aka bukata koh zama bai samu, har 4 na asuba sumayya haihuwa ya gagara, gabaki d’aya karfin ta ya gama karewa sai da aka kira Assalatu kafun haihuwa yazo gadan gadan, cikin hukunci Allah sumayya ta haifi yaran ta guda biyu wanda koh sanin wani iri ta haifa bata sani ba, tsabar wahalar da tasha, tadai san ta haihu sau biyu, Alluran hutu aka mata bayan an kimtsata a take bacci ya d’auke ta.

    ******************
    Bugu d’aya Al’ameen ya d’auka a take Ammar ke sanar dashi anga wajen da khadija take, suna Abuja.

    Ai muhammad baisan lokacin da ya wantsalo daga kan kujeran falo, a take yayi sujjada akan tiles yana wa Allah kirari, goggo da mahmah dake zaune a kasan falo suna cin abinci da sauri suka mike suna tambayar sa lafiya?ai da sauri ya mike ya rungumi mahmah cikin farin ciki yake sanar da ita anga sumayya anga sumayya tana Abuja.

    Ai sosai suka nuna farin cikin su goggo harda kuka, a take Muhammad ya fitar da waya ya kira abie ya sanar dashi akan yanzun nan zai tafi gidan su Ammar zasu wuce abuja.

    Hanasa Abie yayi yace ya bari sai da safe sai subi fly zai sa a nema musu ticket sai su tafi tare da abie, ai a take goggo ma tace zata mahmah ma tace ita ma, dada dake kusa da abie tace itama baza’ayi ba ita ba, duk yanda abie da muhammad sukayi da tsofinnan su zauna a Taraba, su zasuje su dawo da sumayya amma kememen sukace kafar su kafar su abie, haka ba yanda abie ya iyya duka aka musu booking in fly tare da kiraye kirayen waya har nijar aka sanar dasu an samu wajen da suke, suma sun sanar dasu a cikin satin nan suna zuwa gabaki d’ayan su.

    Washe gari tun sassafe suka bar Taraba muhammad koh bacci jiya kasawa yayi, dada ma haka ta watsar da safina tace sai taje taga jikallen ta, Ammar ma tasa Abdul yayi a gaba tare zasu ya nuna musu gidan su kalamu.

    Karfe 9 su muhammad suka dira a Abuja, dayake yana da aboki, tun a taraba ya kirasa akan suna zuwa, tarba suka samu daga wajen abokin abie shiyazo ya d’aukesu a Airport, direct gidan su kalamu suka wuce, Amma abin haushi basu sami kowa ba wai Suna asibiti, haka mai ganin ya sanar dasu Alfarman ganin baban kalamu abie ya nema ba musu, mai gadi ya shiga ga sanar dashi, aiko sai gasa bayan sun gaisa ne sukace masa suna son sanin asibitin da kalamu sukaje in ba damuwa.

    Ganin girman su da kudin su, gashi kamar ba lafiya ba, hakan yasa baban kalamu yace musu bara ya bisu asibitin, shiga mototi sukayi ya kira nanne ya tambaye ta asibitin da number room nasu, da mamaki yake tambayar ta koh lafiya jin muryar ta ya dishe-dishe alamu dai ba lafiya ba, koh tayi kuka, ya tambaye ta lafiya tace masa ba kome, kashe wayar yayi ya sanar dasu abie ga asibitin da suke.

    Suna isa asibitin muhammad da gudu ya ruga bayan sanar dashi block inda suke koh kunyan su abie baiji ba da gudu yayi block in mutane sai kallonsa suke, da sauri sauri ya shiga d’akunan one by one yana dubasu, ana ukun ne ya shiga koh sallama babu ganin mace kwance akan gado ga yara sa’o’in juna zaune rike da jinjiraye a hannayen su, da sauri suma suka juyo jin mutun a d’akin babu sallama.

    Ai da sauri khadija ta mike ta kwala ihu yaya!!!!!!!! Da sauri kalamu dake kusa da ita rike da d’ayar babyn da sauri ya cafke wance ke hannun khadija, don saura kad’an ta buga jinjira, da gudu khadija tayi wajen muhammad batayi wata wata ba ta rungumi d’an uwanta tana fashewa da kuka yaya, kaine koh mafarki nake?

    Khadija nine nine khadija ina Aunty ki?

    Allahu akbar yaya kalli nan tace tana nuna masa kan gadon da sumayya ke kwance har yanzun tana bacci.

    Da sauri ya ware idanun sa yana kallon sumayya sai kuma ya juya ya kalli kalamu, ya sake kallon khadija?

    Gyada masa kai tayi tana murmushi, shima murmushin yayi sai kuma ga hawaye, tare da matsawa kusa da gadon da sumayya take kwance, dukawa yayi akan gwuwar sa hannu yasa a hankali yana shafa fuskar sumayya, dake kwance sanye da kayan asibiti, tayi kyau tayi fresh irin na masujego, wannan ce sumayyar tawa ashe haka take da kyau masha Allah?

    Itace yaya kaga wa’innan jarirai nakane.

    Da sauri ya juya yana kallon kalamu da sauri ya mike tsaye hannu yasa ya Amshi babies in yana kallon su, yarane mata masu tsananin kama da junan su tamkar An raba kunu a kofi, gasu masu tsananin kama dashi kome nashine a fuskar yaran, gasu farare tass, rungumarsu yayi ya fashe da kuka.

    Toh ragon maza baka da aiki sai kuka, mahmah da suka shigo cikin d’akin tun d’azun, amma basu ma san da su ba.

    Da sauri ya nufi mahmah yana ce mata, mahmah kalli yaran nan, wai yarana ne kallesu fa ga sumayya mahmah kyakkyawa fa sosai?
    .
    Sunkuyar da kai abie yayi yana mamakin surkin nan nasa yau koh dai ya mantasa a wajen ne, shima da sauri ya nufi wajen da yarsa ke kwance, zama yayi a bakin gadon yana shafa gashin kanta daya hargitse koh ribon babu.

    Mahmah ce ta karbi baby d’aya dada ma ta karbi d’aya goggo kam baki kawai ta sake tana bin kowa da ido, kalamu kallon babansa yayi dake gefe, ya gaidashi, amsawa yayi yana tambayar sa mai jiki.

    Matsawa kusa da abie muhammad yayi ganin sumayya ta fara motse, a hankali ta bude idanunta dalilin kukan da yaranta suka sake dukan su biyu.

    Tana bude idanunta bata sauke sa akan kowa ba sai muhamamd dake kanta a tsaye, kamar a mafarki haka ta kalli abin da sauri ta mike zaune har tana kokarin zamowa kasa, da sauri ya tarota, bi a hankali sumayya jikin ki ba kirfi.

    Ai jin abinda yace da sauri ta riko hannunsa gam tana kwalama khadija kira, Amsawa khadija tayi da sauri ta karaso wajen”khadija yayanki ke mini gizau na kamasa ”

    Aunty ba gizau bane yayane

    “Yaya kuma khadija mijina fa baya gani yau kuma naga wannan na gani”?

    Aunty ya warke ne.

    Ai sumayya najin haka ta sake dariya cikin farin ciki koh damuwa da jikinta batayi ba ta rungume mijinta, don ita sam hankalin ta vaikai wajen mutanen d’akin ba.

    Mikewa abie yayi dasu mahmah zasu fita a dakin su basu waje don sukam kunya ne zai kashe su.

    Nanne dake toilet tana wanke kayayyakin sumayya daya baci, tun d’azun take jin surutai a d’akin mikewa tayi tsaye da boket na kaya a hannunta ta bude kofar toilet ta fitoh, Wai khadija da kalamu anya kuna da hankali kuwa mara lafiya na bacci kuke surutai da wa……bata karasa ba tayi turus ganin jama’ar dake shirin fita a d’akin dasuka juyo suna kallonta.

    Dada ce ta kama salati tana tafa hanneye, wanake ganin nan?

    Abie ma da sauri yace Hafsa??

    Nanne kam bata wani nuna reaction ba, dayake tun daren jiya data gane sumayya tasan tabbas zata ga su abie, duk da saurin da take tabar asibitin kafun suzo don ita batasan sumayya gudu tayi ba, haka ma batasan itace Aunty khadija ba sai daren jiya.

    Nanne bata wani Amsa ba bare ma ta nuna tasan abie, sai tsayuwar da tayi tana kallon sumayya data sake muhamamd tana kallonta sosai irin kallon nan na kewa da soyayya, cikin kuka tace” ummi”?

    Sai a wannan karo nanne tayi magana, Na’am momcy?

    Da sauri sumayya ta sauka akan gadon tana takawa a hankali cikin dauriya tayi wajen mahaifiyarta fad’awa tayi jikinta tana kuka yau kam ta rasa ina zata sa kanta, murnan samun babies koh murnan ganin mahaifiyarta koh mijinta dole tayi kuka, ummi karan kanta hawaye ne ya cika a idanunta tana shafa kan sumayya ya isa haka momcy yi shuru kinga ba lafiya bane dake koma ki kwanta, tana maganar tana rike da hannun sumayya har ta kaita bakin gadon ta aje ta.

    Waini yau hafsa nake gani ne koh gizau idanuna kemin koh mafarki nake ne?

    Itace dada Abie yace yana dafe kansa cikin takaici da bakin cikin abubuwan da suka faru a baya.

    Mijin hafsa ne yace, Hafsa kin sansu ne daman nina d’auka koh iyayen yarinyar nan ce?

    Baban kalamu ne da kakarsa wannan kuma Addansa ce ta nuna sumayya.

    Daga sumayya har kalamu da Abie a tare suka jefowa Hafsa tambaya lokaci guda, baban kalamu wani kalamun?

    Da sauri abie yace hafsa ban gane ba wanene kalamu.

    Nuna masa kalamu tayi dake tsaye cikin shock na abinda nanne tace, yanzun wai sumayya Addansa, ta yaya kamar ya?baigane ba?

    “Ummi kina nufin kalamu d’an uwa nane”?

    Hafsa kina nufin wannan yaro, yaro nane?

    Kallon sumayya da abie hafsa tayi jin tambayar da suka jefo mata, eh kawai tace tana kama hanyar kofa zata fita tare da kallon mijin ta, yauwa Alan guburo mutafi naga dangin ta sunzo zasu zauna a gunta.

    Ah ah hafsa zuwan mu bazaisa ki daina hidima da yarki ba.

    Ah ah dada zan tafi , Allah ya sauwaka momcy.

    “Ameeen ummi in zaki dawo a kawo mini sabulun wanka”

    Toh momcy muje kalamu koh zaka zauna ne?

    Ah ah nanne muje yace yana kallon abie da mamaki wai wannan ne babansa, shi abin ma yajisa wani banbara kwai.

    Kokarin fita a dakin suke a hankali abie ya kama hannun kalamu daya wucesa zai fita a d’akin, kalamu bazaka ma abie magana bane?

    Murmushi kalamu yayi sai kuma yaji hawaye ya taro masa, abie ashe kanason na maka magana, shine zaka kyamace ni ka kyautata rayuwar yar uwata, amma ka wofantar da nawa rayuwar ka barwa uwata ni, na zauna a matsayin agola a gidan da, bana ubana ba ya maye gurbinka ina Amfani da sunan sa koh a makaranta, bai taba nunawa duniya bashi ya haifeni ba koni bansan bashine mahaifina ba, sai yau akan me zan maka magana ni bansan wani uba ba sai ……..

    “bai karasa ba sumayya ta mike ta wanke sa da mari cikin bacin rai ta soma magana, karka kuskura ka fara abinda zai dame ka wallahi kayi kad’an ka zagar min uba na barka,ni a haka nake son abina koma me zaimin bazan taba kinsa ba” sai kuma ta kama kuka.

    Da sauri nurses dake falo suka shigo d’akin, akan surutun dake tashi, hakuri aka basu akan za’a kiyaye magana ne mai muhimmanci ake, ganin kalarsu yasa su barinsu a dakin.

    Daker aka samu suka sassanta nanne ta koma gida dasu goggo yayinda mazan kuma suka koma hotel sumayya ma ita da dada kadai aka bari a hospital.

    Washe gari aka sallame ta saboda kyaun da jikinta yayi, don haihuwar duk da yazo da gardama amma tana haihuwa shikenan.

    Gidan nanne aka maidata bata koma gidan hayansu ba,sosai ake kula da ita muhamamd a rana sai yazo sama da sau hudu, sai da sumayya ta kwana hudu da haihuwa kafun suka koma shirye shiryen dawowa jalingo don anan ake son yin taron suna gashi yan nijar ma sunce suna shirin zuwa, duk yanda sukayi ta rokon nanne ta biyosu taki tace bazataki bin umurnin mahaifinta ba na raba kanta da zuriyar shugaba, saida mijinta ya nuna bacin ransa da nuna mata yaranta nada hakki akan ta, sannan kalamu bazaiji dadin hakan ba tunda shima so yake yaje yaga dangin babansa, daker dai ta Amince washe gari da sumayya ta cika kwanan biyar sukabi jirgi saijalingo.

    Muhammad murza idanunsa yayi yace a gidan sa da babansa ya sai masa a Amazon sumayya zata sauka, ba musu duk da abie yaso ta koma gida Amma ganin hafsa da Al’ameen basason hakan.

    Gidan sumayya ta sauka dayake babban gidane ga d’akuna shiyasa gidan ya d’auke su, duka harda su hafsa falmata su babayo muhamamd goggo dasu mahmah, kalamu kam shugaba family house ya sauka kuma ba karamin farin cikin ganinsa sukayi ba.

    Babu inda haihuwar sumayya bai bazu ba jama’a sai tururuwan zuwa dubata suke harda yan Abuja laila ma daga adamawa ta gangaro, a ranan yan nijar suka diro nageria gabaki d’aya yan uwan yusuf ne harda shi karan kansa ma, wannan zuwa harda lawiza da nabila, sosai gidan ya dad’a cika da yan uwa kota ina yan gidan shugaba ma tun a washe gari suna matan suka diro, yusuf a gidan sarki ya sauka dayake suma ana gobe suna suka zo, kai sumayya taga jama’a iyya jama’a ga wani irin lalle da aka watsa mata mai masifar kyau da ketson suna duka.

    Yau take suna yara sunci suna NA’IMA da NA’IFA , tun Asuba yan gidan Adara suka diro su inna asabe inna lami Ana gindin murhu a sauke wanshan a d’aura wanshan, shanu uku aka yanka da rago biyu, duk suna ta kan gyaran nama, ga abinci kala kala, gashi koh ina ka leka zakaga group group na mata kowa da angon su mai zafi, wanda abie ya d’auki nauyi duka, yan nijar nasu da ban haka dangin adara, yan shugaba family house ga yan gembu, ashan gefe naga MATAR MAKAHO FAN’S ansha anko na Atamfa mai ratsen flower green ana zazzaune ana dirkan shinkafa a manyan tireruka hhhhh.

    Sumayya dake sanye da wani hadedden material gown wanda yasha dinki ga sarka na d’anyen gwal da sarki ya bada aka kawo mata, sarkane da dankunne sai warwaro ga agogo mai zafi na mata duka, tasha heavy make-up sai d’aukan hotuna suke da kannen Ammar dake sanye da Ankon su, khadija da kalamu dake zaune a gefe suna cin shinkafa.

    Muhammad da Ammar harda su ramadan zulkiflu gidado badaru duk yanzun sun chanja kamar basu ba, suna zazzaune a kofar gida a rumfar da aka kakkafa abinci suke ci mairai da lafiya.

    Tun daga nesa suke jin ihun yara da mutane suna rugawa a guje, da sauri suka mike gabaki d’ayansu suna kallon abinda ke faruwa.

    Mutum suka gani kamar mace ne koh na miji bazasu gane ba, kadangaru manne a jikin sa tana gudu suna binsa wasu na jikin ginin unguwan suna rugowa suna binta sosai kota ina kadangaru ga wasu runduna na binta a baya, sai wata mata dake gefenta rike da sharbebeyar bulala tana kad’a mai kadangarun suna tafiya a haka.

    Da sauri su muhammad suka ruga cikin gida da gudu har ana rige rige, ganin wajen da suke suka nufo.

    Suna shiga suka rufe kofar gidan da karfi suna ji sai bugawa matar take akan don Allah abude mata, kiri kiri su muhammad sukaki budewa har abin yaja hankalin matan dake compound sosai, dada dake rike da jinjira zata kaiwa kawayen ta dake falo a zaune ssga dayar, itace taji hayaniya aje jinjiran tayi ta fitoh compound, ganin su muahmamd da jama’ar tsakar gidan a tsaye yasata karasawa bakin get in tana tambayar dalili, kafun ma su muhammad suyi mata bayani tuni tasa hannu ta zare sakatar get in, ihu Ramadan ya sake tsabar rikita yare ma ya fara.

    Dada na budewa idanunta ya sauka akan matar dake rike da bulala kwalalo ido tayi cikin mamaki tace wanake gani anan kamar Nafi………….

    kafun ma ta karasa maganar ta idanunta ya sauka akan wance ke tsaye mammanne da kadangaru ga bataliya a kasa, ai ihu dada tasa ta ruga ciki da gudu, da sauri inna lami tazo zata rufe get aida sauri wannan matar ta banke kofar ta kora mai kadangaru ta shigo, itama shigowa tayi, ai ana ganinta, ihu ne yake tashi abinka da mata atake masu Aljanu Aljanunsu ya soma tashi, gidan suna gabaki d’aya ya rikice ya zama gidan tsere kowa gudu yake yana burmuwa falo wasu kitchen masu Aljanu kam sun zuzzube…………..

    ✨Ruqeenjalal✨🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

  • Matar Makaho 60-61

    Matar Makaho 60-61

    Page6⃣0⃣&6⃣1⃣
    Da sauri ta d’ago kanta jin yanda yayi maganar a matukar sanyaye, kamar wanda zai nemi Alfarma itafa halaliyar sace,amma ga yanda yake had’ata da Allah, yayi matukar kokari, yanzun ana neman kusan wata uku da auren su, koh ma fiye da haka, ba tare da ya taba tilasta ta akan hakkinsa, kullum ya bukace hakan, zata saka masa kuka, koma hakan koh baya so yake kyaleta.

    Jin batace kome ba yasa sa lalubar fuskar ta,In baki Ra’ayi kiyi hakuri sumayya,na hakura.

    Da sauri ta kamo nasa fuskar hawaye na cika mata ido, “yayan khadija hakkin kane fa?kaima da kanka ka fad’a, kaga kenan ni bani da damar hana ka, tunda naka ne, duk abinda zaka bukata a gareni mallakin kane, na amince kayi duk abinda kake so dani, ta karasa maganar da fashewa da kuka.

    Jin ta fara kuka yasa muhammad, da sauri yace, sumayya kiyi hakuri nama hakura, shikenan tashi kisa kayanki mu kwanta.

    “Ba kuka nake ba”

    Hannu yasa ya shafo kumatun ta, toh me kike, kuma menene a fuskar taki?

    “Kayi hakuri”

    Fuskar sa ya had’a da tata fuskar, baki min kome ba sumayya.

    “Toh insa kaya koh haka xamu kwanta” ?

    Shikam ba karamin dariya sumayya ta basa ba harya kasa hakuri, saida ya dara, hhh menene haka kuma sumayya?

    “Toh ba tambaya nayi ba, koh tambaya laifine”?

    Ah ah ba laifi bane, yace yana d’aura fuskarsa a kafadar ta, yana goga mata gemunsa.

    A hankali sumayya ta manne masa gam a jiki, hannu tasa ta kama gashin kansa, jin kamar zai zautar da ita, jin bakinsa akan wuyan ta.

    Ahhhh, yace yana kamota, d’agota yayi gabaki d’ayan ta, yana lalube harya hau gadon, kwantar da ita yayi ya hau kanta, bakinsa ya jona cikin nata, sosai yake tsotsar bakin ta, jikinsa sai rawa yake.

    Sosai sumayya ke tare da farga ba, don yanayin muhammad kawai yau zai tabbatar maka, da gaske yake son Angon cewa.

    Washhh Ashhhhh sumayya tace, lokacin da taji muhammad ya yaye mata towel in jikinta, shima tuni ya watsar da nasa daga ita harshe babu sutura a jikinsu…….

    Zafafan Romance Al’ameen yake wa sumayya, da zafi zafi don A lokacin bazaka taba tunanin koh baya gani ba, aikin dake gabansa kawai yake.

    Sumayya dake kwance rumtsa ido tayi, jin Al’ameen na ware mata kafa, bakinsa d’auke da Addu’an saduwa da iyali

    Kara ta kwala da karfi, tare da ware ido, jin wani Al’amari mai girma daya ratso rayuwarta, a karon farko hannunta dake free, ta d’aga a zabure ta cakumo gashin kansa.

    Da karfi ya fizgo Hannunta, daga gashinsa ware hannun yayi ya danne da jikin katifa, sosai ya kara bada himma akan abinda yake, bai taba d’aukar zaiji wani d’adi ba tunda Abbajon sa ya barsu, wahalar rayuwa bai barsa ya tuna akwai wani dadin da zai iyya d’and’ana wa, maka mancin wannan dadin ba, sai gashi yau sumayya ke shayar dashi.

    Sumayya kam gumi ta had’a sosai, duk da an fara yayyafi, Amma daga ita har muhammad zufane ya jikasu, sosai sumayya ke kuka tana goga kanta da jikin pillow, ba zafin da Al’ameen ke d’and’ana mata bane yafi ratsata, wani irin sarawa taji kanta nayi kamar wance ake fisgar gashin kanta da karfi, haka takeji a kanta kuka tasa, don abin ya hade mata biyu, ga azaban da Al’ameen ke gana mata sosai, kanta ke bugawa ji take kamar kwakwalwarta zai fita, sai salati take tana murza kan da filo.

    Ta bangaren Al’ameen kam, yau ba’aji ba’a gani am amsa sunan MAKAHO yau, don koh kukan sumayya baji yake ba, hankali..sa na gefe, damuwar sa kawai yaji abinda yake gabansa.

    Sumayya jin wasu irin bugawa da kanta keyi akai akai jijiyoyin kanta takeji kamar zasu tsinke, koh gani bata iyyawa yanzun sosai, duk da a duhu suke Amma duhun da take kallo yanzun yafi karfin duhun d’akin.

    Sosai bakin ta ya bushe, sai shakuwa take, tana kiran ruwa da muryarta da baya fita sosai.

    Amma ina muhammad baisan tanayi ba abinda yasa agaba yake fama.

    Jan numfashi sumayya tayi da karfi jin wani irin wahalallen shakuwa, ya gudu da numfashin ta duka, sakewa tayi jagab ta koma jikin filo,

    Muhammad bai farga da halinda sumayya take ciki ba sai da ya gama samun nutsuwa, A hankali ya zare jikinsa a nata, aiji yayi kamar an watsa masa Allurai a idanun sa, soki yakeji a cikin kwayan idonsa, sunfi d’ari rumtsa idon yayi da karfi, yana kiran sunan Allah jin wani irin barkono da soki na cakansa, tunda yake bai tabajin azaba irin wannan ba, kansa ya had’a da jikin gado da karfi ya buga ji kake gauuuuu ………..ya sulale kan katifar baya motse.

    Har Asuba muhammad da sumayya suna sume, basu farfado ba, babu wanda yasan halinda suke ciki, sai mahallincin mu,

    A Hankali sumayya ta fara motse, a hankali take kokarin bude idanunta, sai kuma ta maida su ta rufe da sauri, jin wani irin nauyi daya mata, sai da tafi minutes 10 kafun ta sake bude idon, a hankali harta budesu duka, ware idon tayi tana kallo dishi dishi har idanunta suka sauka akan muhammad, dake yashe a gefe ga goshin sa a fashe.

    Cikin matukar razana ganin sa kamar wani matan ce, haftowa tayi da kuzari zata mike, kara ta sake tana Ambatan sunan Allah, ta koma ta kwanta jin wani irin rad’ad’i dake ratsata, ta kasa

    A hankali ta mike zaune, tana cije lebenta, ta fara rarrafawa zuwa garesa, matsowa tayi sosai ta tattabasa jin baya motse, yasata sake kara”innalillahi wa’inna’illahi raji’um nashiga uku, don Allah muhammad karka tafi ka barni wayyo nashiga uku, wayyo mijina na bonu,ganin kamar suma yayi, sai kuma ta rarrafa da sauri taja blanket in ta rufe masa jiki, da rarrafe ta sauka akan gadon, towel inta dake yashe a kasa ta d’auka ta d’aura.

    Firij ta wuce ta d’auki ruwa, haka ta rarrafa ta iso bakin gadon ta saitin da yake, hannu tasa ta bude bakin goran, ta tsiyaye ta wasa masa a fuska, Amma ina shuru muhammad bai tashi ba, kuka ta sake tana bulbula masa ruwan sanyin a fuska, Amma koh motse baiyi ba,”wayyo muhammad wayyo mijina, na shiga uku Allah ka taimake ni”

    A matukar gigice ta saka kunnen ta a kan kirjinsa, jin zuciyarsa na bugawa, yasa hankalin ta kwanciya don ta gane suma yayi.

    Tunawa tayi da number maimuna kanwar Ammar, a wayan ta koh ta kirata ne? ta had’ata da Ammar koh Zai taimaka mata mijinta ya tashi tunda itama, tana bukatn taimako, gashi bata san wazata kira ya tallafa musu ba.

    Da rarrafe ta isa kusa da wayan d’auka tayi jikinta sai bari yake, ta kira maimuna tanajin ta d’aga tace”Assalamu Alaikum”

    Wa’alaikumu salam Aunty sumayya ina kwana?

    “Lafiya maimuna don Allah Ammar na gida”?

    Lafiya kam aunty sumayya, naji muryan ki a dishe?

    ” nace miki Ammar na gida”?

    Ah ah wallahi yau yabar gari da asuba lfy?

    Kashe wayar in sumayya tayi, don bata da lokacin maimuna.

    Da sauri wani tunanin yazo kanta, ta rarrafa ta isa wajen kayan sa, budewa tayi tana ciro masa kaya, in yaso sai ta saka masa, ta fita ta kira keke su tafi asibiti, duk da ba lafiya bane da ita, koh da rarrafe zata fita ta taimake rayuwar mijinta.

    Kayan sa ta bude ta, dauko jallabiya tayi ta aje, tasa hannu zata d’auki gajeren wandon sa, taji hannunta ya taba wani abu mai karfi kamar gidan agogo, hannu tasa ta zaro abin, haka kawai taji hankalin ta bai kwanta da wannan karamin akwatin ba, hannu tasa ta bude.

    Da sauri ta rufe Idanun ta ganin wani irin haske daya kashe mata ido,A hankali ta sake bude ido ta kurawa sarkan ido, yayi haske yasa ke mutuwa farine sosai, mai kyau sai zanen zaki dake tsakiyar gaban sarka, sosai sarkan ke sheki yana komawa normal.

    Jiki na bari ta rike sarkan, indai bata manta ma Al’ameen yace baban shi ya basa sarka, koh dai wannan ne sarkan? menene dalilinsa na cirewa? a wuyansa, rarrafe tayi ta isa garesa, sarkan ta d’auka ta d’aura masa a wuya.

    Ai sarkan nan na shiga wuyan Al’ameen, ya wani irin haske sosai sai kuma ya koma normal bai sake hasken ba.

    Da rarrafe sumayya ta fita a kofar dikin”subhanallah”tace ganin har rana ya fitoh don lokacin ana neman, kusan karfe 8:00 na safe koh sallan asuba basuyi ba,da rarrafe ta shiga kitchen kittle ta jona a soket, tana zaune a wajen ya tafasa juyewa tayi a boket, ta sake saka wani saida ta juye kittle uku,sannan ta fara kokarin mikewa,don d’aukar boket in ta juye a band’aki, Amma ta kasa, kuka kawai ta sake, ta koma ta zauna.

    Muhammad kam tunda sumayya ta fita a d’akin ya farka, sosai idanunsa ke masa zoge kamar an kwakule masa su,tun d’azun yana kwance don duk jikinsa a sake yake.

    Da sauri ya mike zaune jin kukan sumayya ta window, sai yanzun tunanin abinda ya faru ya fado masa,take yaji tsikar jikinsa ya miki, hasbinallahu wani’imal wakin, yace yana mikewa zaune, dafa kansa yayi da karfi jin wani irin rad’adi a inda ya buge, a haka dai ya lallaba ya mike zaune, jin baida sutura a jiki yasa sa fara laluben gadon, ji kawai yayi hannun sa ya taba wani abu damshe damshe, ga karnin jini.

    Da sauri ya mike, sauka yayi ya d’auki wando a cikin kayansa ya saka, yana dafe da kansa har lokacin idanunsa a rufe suke.

    Sumayya!!!sumayya!! Menene?yace yana karaso wa kusa da ita.

    Ai barin kukan sumayya tayi, ta zare ido ganin Al’ameen akan kafafunsa, hannu tasa ta kamo nasa hannun”na kasa tashine, ga rana yayi bamuyi wanka ba, gashi ina son kai ruwa band’aki na kasa, gashi ka suma hankali na ya tashi”tana maganar tana kuka.

    Rungumar ta muhammad yai da karfin gaske, A hankali ya bude baki daker, kamar yanajin tsoron magana, sumayya ina sonki, sumayya ina tsananin kaunar ki, bazan taba mantawa da daren jiya a rayuwa ta ba, har abada kece cikon farin cikina, ina fatan har in koma ga Allah, karna miki butulci matata.

    Kara rungumar sa tayi sosai, taji wani sanyi a ranta da tausayin mijinta”nima babu abinda zance maka sai dai na mana fatan gamawa da duniya lafiya, mijina har abada bazan taba barin kaba harsai ranan da na daina numfashi in Allah ya yarda.

    Toh bakice kina sona ba?

    “143”

    Meyake nufi?

    “Kayi tunani mai zurfi, wanka nakeso nayi nayi sallah, rana yayi ka kaimin ruwa bayan gida”

    Toh yace yana saken ta, boket na ruwan zafin ya d’auka, yana tafiya har lokacin idanunsa zafi suke masa, kuma bai bude suba.

    Bayan ya aje ruwan, dawowa yayi ya ibi na sanyi a wani boket in daba.

    Sumayya dake zaune har lokacin a dakali”ga baf a kitchen ka kaimin ban d’akin”tace masa

    Haihuwa kikayi ne wai gimbiya?

    “Mutuwa nayi”

    Insha Allah ba yanzun ba, yace yana d’aukar boket in, kaiwa yayi band’aki yana fitowa, sumayya dake kan dakali ya ciciba yayi bayan gida da ita, ajeta yayi.

    “Toh ka fita mana, waima menene naga ka rufe ido yaukam kaki budewa”?

    Idanun ciwo suke mini, yau kamar borkono a ciki.

    Uhmm kawai sumayya tace tana had’a ruwan wanka, duk yanda taso muhammad ya rabu da ita ki yayi shiya taimaka mata tayi wanka, ya d’auko mata wani towel in, ta d’aura ruwa ya cika a buta ya bata tayi Alwala.

    Shima wankan yayi ya fita a d’akin har lokacin idanunsa a tamke, yayi Alwala yashiga d’aki, zuwa lokacin sumayya tayi sallah tana zaune tana lazimi.

    Bayan ya idar da sallan, a hankali yasa hannu ya shafo sarkan wuyansa da mamaki ya kalli sumayya, gimbiya yanaga sarka a wuyana kuma, ke kika d’auko koh?

    Da mamaki sumayya ke kallonsa, yau kuma gimbiya ta zama kenan”eh nina saka maka, kace babanka ne ya baka sannan baka sakawa, akan me”?

    Sumayya naki saka sarkan nan ne, dom sau biyu ana kokarin fizgesa a wuyana,shiyasa na daina sawa.

    “Kamar ya ban gane ba”?

    Wallahi barayi mana, kaje kasuwa xaka saida abu anki saya, Amma barayi na kokarin sata.

    “Allah ya kyauta , wai bazaka bude idon bane”

    Ba musu yad’an fara kokarin, bude idon a hankali a hankali harya budesu duka.

    “Ya illahih”sumayya tace lokacin da idanunta ya sauka akan kwayar idon muhammad, yayi jajazur kamar jini zai digo, inka ga idon zaka d’auka koh buga masa shi akai jini ya taru.

    Sumayya menene naji kina salalami?

    “Ba kome, yayan khadija kaga idanunka kuwa”?

    Taya zan gani, bayan ba gani nake ba, me idon yayi?

    Wallahi kamar jini zai digo jajazur”

    Kuma Nima rad’adin da nakeji sosai fa.

    Allah ya kyauta, bara naji sauki sai muje asibiti, Amma dai yanzun, kaje chemist ka siyo mini magani rage rad’adi, kaima saika sayawa kanka naga, har wajen ya kumbura”?

    Gaskiya ne, kannawa ciwo yake wallahi, gashi ma yunwa nake ji, kema nasan kinaji bara na had’a duka nasai mana.

    Nikam bazanci kome ba, ka biya shago kawai ka d’auko mini lemo, bakina d’aci, ka tura a kira khadja tazo tad’an gyara mini kofar, nikuma bara nayi sauri na fitar da zanin gadon ya baci sosai”

    Toh ki zauna kawai tunda tafiyar taki batayi kyau ba, bara na jika zanin gadon inna dawo zan wanke? yace yana fita a d’akin bayan ya d’auki zanin gadon, waje muhammad ya fita bayan yakai zanin gadon band’aki, tsallake titi yayi, yaro ya samu ya aika gidan goggo, a kira masa khadija, shikam ya wuce chemist in jambusko.

    Yana isa chemist yasamu layi dole ya zauna har akazo kansa, maganguna ya saya harda wanda zai diga a ido, yabi shagon sa lokacin har shagari ya bude, d’aukowa sumayya lemon yayi, yasai abinci duka yana rike da laidodin a hannunsa har lokacin idanunsa rad’adi suke masa.

    Yazo tsallaka titi kamar daga sama yaji mota yayo kansa gadan gadan da gudu ya fara kokarin kauce wa, Amma ina saida suka cin masa, kamar zasu kadesa, amma suna zuwa kusa dashi suka ja birkiii

    Sosai ya tsorata sai kiran sunan Allah yake, wasu kattai hannun su d’auke da bindigogi, suka fitoh a motar duk sun rufe fuskokin su da mask……..🍀

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 40-41

    Matar Makaho 40-41

    Page4️⃣0️⃣&4️⃣1️⃣
    Yusuf ne kwance akan zainab suna dambe

    Salati dumbin Alumman dake wajen suka sake,zainab Kam da sauri ta sake Yusuf ta matsa gefe tana kuka da rawan jiki

    Yusuf Kam ya kasa magana sunkuyar da Kai kawai yayi don bazai iyya hada ido da ubangari ba

    Yusuf Ashe Kai Maci Amana ne Yusuf Ashe Kai mugune Yusuf shiyasa tsawon shikarun nan kake zaune Dani da fuska biyu azzalumi maha’inci kawai wallahih nayi Dana sanin zama dakai, Allah ya isan mini tunda ka rasa Wanda zakabi sai Yar cikinka,yace hawaye na taruwan Masa a ido,matasan samarin nan basuye wata wata ba suka rufe Yusuf da duka duk yanda yaso musu bayani Basu basa dama ba

    Aisha Kam ba karamin shock ta Shiga ba Daman Yusuf ba D’an uwan ubangari bane? shiyasa inta tambaye sa Ahlinsa sai yahau fushi Ashe baida gaskiya ne kwata kwata, Aisha Kam kuka take tana dana sanin Yusuf, ya zubar Mata da mutunci ya ha’ince ta

    Matar ubangari waya ta d’auka ta Kira police lokacin Amma Yusuf jina jina Koh tsayuwa baya iyyayi,ga matan sa da yaransa duk suna kuka, A lokacin yaran basusan me uban yayi ba Amma tabbas sunsan ba lfy

    Police na zuwa daker suka k’wace Yusuf ganin ana kokarin kisan kai, lokacin da police suka Kama Yusuf za’a fita dashi cikin tsananin azaba yake rokonsu su barshi yaga MATARSA zai Mata magana.

    Ba musu domin tabbas su kansu police a lokacin sunji tausayin sa sosai da sosai,wani ne a cikinsu ya taimaka Masa suka nufi wajen da Aisha ke duke tana kuka

    Yusuf na Isa dukawa yayi yasa gwuwarshi a kasa cikin galabaita ya fara magana, Aisha Koh kowa zai yarda akan abinda yafaru don Allah Aisha ke kad’ai ki yarda Dani, yardan ki kawai nafiso akaf fad’in duniyan nan bayan yardan Allah,don kece abokiyar rayuwa ta in kowa zai juyamin baya ke Kika rungumeni bani da kaito Aisha Ina neman Wannan alfarman. ya karasa maganar hawaye nabin fuskar sa

    Aishan ADARA Kam yau Hali ya motsa jikinta har bare yake cikin kakkauran murya ta mike ,Yusuf Yusuf wallahih nayi Dana sanin haihuwa da Kai Yusuf, nayi Dana sanin auren ka Yusuf ka cuce kanka ka cuceni Yusuf bana bukatar ka a rayuwa ta ni daga yau mijina ya mutu.

    Sosai Yusuf ya fashe da kuka maicin Rai Wai waye zai fahimce sane kowa bazai yarda dashi ba kawai don an gansa a d’akin yarinya Babu bincike sai kawai ad’au mataki, me yasa tunani bazaizo musu ba duba da cewa ya rasa inda zai nemi zainab sai a cikin gidansu?

    Yunkurin magana yafara ais……,da saure Aisha ta d’aga Masa hannu Yusuf Koh Babu Kai zamu rayu da yarana Koh bakai Zan iyya rayuwa Koh ba Kai rayuwar zata Mana Dadi,Amma zaman ka acikin mu shine kuncinta ka tafi bana bukatarka a yanzun,tace tana Mai kokarin baren wajen.

    Da sauri yusuf ya Kama hannun Aisha,bataye wata wata ba ta tsinka Masa Mari.
    Da sauri Yusuf ya sake Mata hannu

    Da sauri Al’ameen Yayi wajen babansa cikin kuka ya rungume sa,abbajo menene Kaye musu suke dukanka abbajo ga fuskarka duk jini,abbajo muje asibiti a maka treatment kaji abbajon mu ka bawa police hakuri karsu tafi dakai,kuka Yusuf ya sake hade da rungumar d’ansa Dayake Jinsa Kamar bugun numfashin sa, cikin su biyun yafi kaunar Muhammad sosai.

    Karka damu muhammad Zan dawo kaji laifin da ba nawa bane aka d’aura mini Wanda duniya kaf ni ake gani da laifin ,Yusuf yace ma d’ansa Yana Mai d’aukar sarkan dake wuyansa fari Mai azabebben kyau da walkiya ya d’aurawa Al’ameen a wuya, Muhammad ka kula da mamanku da kaninka kaji in mamanku ta haifi mace kace asa Mata khadija Inna mijine asa masa Shitu,Yana fad’a Masa hakan police sukazo suka Tisa keyarsa zuwa cikin mota

    Bayan an tafi da Yusuf, Alhaji ubangari da danginsa Koran Kare sukama Aisha da yaranta,sosai Aisha tayita kuka tana tattara kayanta zubawa tayi a ak’watin karfe ta d’aurawa Al’ameen da salim,suka Kama hanyar sintali.

    Gari gabaki d’aya ya d’auka zancen Yusuf yayi kokarin mawa Yar ubangidansa fyade,bayan isar Aisha gidan ADARA zuwa lokacin labari yazo kunnensu Dayake unguwan da suke da sintali ba nisa

    Bayan isar Aisha gida ta sake haduwa da wani tashin hankali shine mahaifinta yace sai ta mayarda yaran Yusuf gun danginsa kafun ta zauna musu a gida Dayake mahaifiyar ta tarasu tun kafun auren ta,yasa ba Wanda yayi yunkurin baiwa baban ta hakuri

    Aishan ADARA ta shiga tashin hankali ba kad’an ba na rashin sanin asalin Yusuf abin yayi mugun daga Mata hankali,ta rasa Ina zatasa kanta taji Dadi,don da ta koma gidan ubangari tunda shine waliyin Yusuf ya fad’a Mata inda dangin Yusuf suke Amma rashin mutunci da aka Mata a gidan Koh kyaun gani Babu,karshe dai wani abokin Yusuf ne Wanda sukaye mutunci sosai ya taimaki Aisha bayan Jin labarin abinda ya faru tabbas shima ya shiga tashin hankali Amma Sam Bai yarda Yusuf ne zai aikata wannan abinba, d’auko Aisha yayi ya Basu d’aki a gidansa duk da MATARSA ta tsani zaman su Aisha Amma ba yanda zata iyya Aisha ta koma gidan abokin Yusuf da zama.

    Wannan zaman gidan abokin Yusuf shine mafarin haduwar
    Al’ameen da kamila

    An Kai Yusuf kotu,Amma bashi da hujjan Kare kansa haka yanaji Yana gani,laifinda ba nasaba aka yanke Masa hukunci.

    Bayan Shari’a abubuwa sun ma Aisha yawa na rashin mijinta don abinda zataci ma gagaransu yake Dole karatun su Al’ameen a private ya gagara ta ciresu ta maidasu Government school, sukaci gaba da zuwa,itakam wankau take Koh daka take sama musu abinda zasuci sosai Aisha take fama da rayuwa ga bakin cikin_ abinda Yusuf ya aikata,ba karamin bakin jini ya shafawa yaransa ba

    Hankalin Aisha Bai Kara tashi ba Saida lokacin komawar Salim asibiti Amma Bata da Koh sisi haka ta d’aukesa sukaje asibitin Amma abin mamaki duk yanda suka Saba da zuwa ganin likita Amma yau kawai da basu da kudin magani haka suka dawo gida kayan sakawarta Aisha ta tattara da kayan dakinta take sayarwa a hakan ta ringa ma Salim jinya da kayyakinta don abokin Yusuf d’aki kawai ya Basu Amma abinci Kam sai dai ta nema musu,

    Ta bangaren zainab Kam tayi Dana sani Dana saninda har abada bazata daina yinsu ba sai yanzun take ganin wautarta na biyewa khairat harta aikata wannan mumunan kazafi wa Yusuf gashi abin Bai tsaya iyya Yusuf ba ta raba ma’aurata ta raba uba da yaransa ganin Yusuf da take taji Dadi yanzun Babu shi gashi Koh samarinta ma yanzun duk sun gujeta a dalilin labarin da suka samu

    Zainab rayuwa ta Mata zafi Koh baccin kirki Bata iyya wa taso sanar da iyayenta gaskiya Amma kairat ta kwabeta don hakan zai iyya zubar Mata da mutunci fiye Dana yanzun da take ciki.

    Al’ameen da kamila yaran makwanta ne gidansu kamila.na kusa da gidan bala abokin Yusuf,

    Kamila dalibar makaranta i private school ne Wanda ke kusa da goverments day da Yusuf ke ciki

    Farkon haduwar kamila da Yusuf a hanyar makaranta zai tafi itama zata fita.

    Tunda kamila.taga Al’ameen take yawan shige Masa har gidansu take zuwa tun Al’ameen baya kulata hardai ya fara kulata Aisha Karan kanta da farko bataso mu’amalar Al’ameen da kamila ba ganin Al’ameen lokacin shikara biyar ya bawa kamila Amma haka ta barsu ganin karatu Yusuf ke koya Mata kullum insun hadu

    Bayan wata uku lokacin cikin Aisha ya Shiga wata bakwai,zuwa lokacin Aisha Bata da kome a dakinta sai taburma sai sarkan wuyan muhammad sai tsummo karansu saboda duk kudin sun Kare akan kudin maganin Salim ga rayuwa dai anata gargarawa

    Yau ranan juma’a Al’ameen da Salim sun dawo makaranta bayan sun kara kamila gida don yanzun shakuwane Mai tsanani a tsakanin su wanda in kamila bataga Al’ameen ba zatazo gidansu haka shima, suna zaune dumamen safe da ya rage shine Aisha ta Basu itakam haka ta hakura saboda yau sun tashi bako sisi,zainab ce ta shigo gidan da sallama a bakinta

    Aisha ta amsa Mata Dan Sam bata Jin haushin family ubangari don Koh itane abinda Yusuf ya aikata saita Masa fiye da haka

    Kallon zainab take Wanda duk tabi ta rame kallo d’aya zaka Mata kasan Bata cikin hayyacinta,bayan sun gaisa zainab ta d’aga ido tana kallon Aisha Bata San ta Ina zata fara ba yau tayi Alkawarin zata Fad’i gaskiya Koh zata samu sassauci a rayuwan ta

    Hawaye ne ya cika idanun zainab ta bude baki a Hankali tace,maman Muhammad akwai wani magana da zanfada Miki bansan ya Zaki d’auki maganar ba Amma na g’wammaci na karbi Koh wani hukunci akan Wanda nake ciki

    Cikin mamaki Aisha kam ke kallon zainab a iyya zamansu da zainab Bata taba ganin ta Mata magana a mutunce ba Kamar yau,toh zainab Allah yasa naji alkhari

    Gaskiyan abinda ya faru maman Al’ameen babu ruwan Yusuf aciki,tace tana kallon Aisha

    Kamar ya bangane ba zainab?

    Eh tabbas Kamar yanda nace , Yusuf Babu ruwansa a ciki nice da khairat Muka had’a kome a tunanin mu Koh in aka Kama Yusuf xai mini fyade babana zai tilastashi ya aure ni Amma ban taba tunanin abinda na aikata ba daidai bane Saida Naga yanda na wargaza muku farin cikin na dasa muku bakin ciki, wallahih maman Al’ameen nayi nadama,Dana biyewa khairat ban tashi nadama ba Saida naji jiya tana Hira da kawarta a waya suna mini dariya, na tsokancin danayi harna yarda da abinda ta gayamin Ashe itama son Yusuf take,ta karasa maganar hawaye ya zuba akan fuskarta

    Aishan ADARA Kam daskarewa tayi a zaune itakam wace irin mace ce Mai mantuwa me yasa ta kasa yarda da Yusuf, namijin daya yarda zai rayu da ita Bai damu da tarbiyan gidansu ba Koh halinta ba ya aureta Koda Yusuf Zina yayi hukuncin da ta yanke Masa yayi tsauri,wani irin murdawa mararta yayi na tashin hankali atake jini ya balle Mata durkusawa Aisha tayi tana Kiran sunan Allah.

    Da gudu matar Bala dake tsaye tun d’azun tanajin bayanin da zainab keye tazo da gudu,tana kwalawa mijinta Kira da gudu ya fitoh su uku suka ciccibi Aisha zuwa asibiti

    Al’ameen Kam Kama hannun Salim yayi suka Kama hanyar gidan ADARA,suna Isa kakansu suka samu a kofar gida suka fad’a Masa mamarsu ba lfy an kaita asibiti, hankali baban Aisha ya Tashi matuka don shi Karan kamshi korinda Yama Aisha na haushin yaran Yusuf ne, Amma Yana son yarsa tura su Salim yayi gidan Amina (Goggo) shi Kuma ya wuce gidan Bala agun ya samu wa’inda ke zaune aka fita da Aisha, aka Masa kwatancen asibitin da aka Kai Aisha

    Bayan zuwansa ne yaji labarin abinda ya haddasa ma Aisha nakudar Dole abakin Matar Bala,shima sosai ransa ya baci duk da Bai gamu da zainab a asibitin ba Amma ransa ya matukar baci gida ya koma ya sanar da yaransa da yaran Yan uwansa akan suje su fara d’aukar mataki akan zainab kafun hukuma ta shiga

    Ayarin gidan ADARA daga Yan Mata har zaurawa da samari sukaye Ayari guda suka fasa unguwa da kafa suka taka har gidan ubangari.

    Zainab Kam gabaki d’aya ta rasa nutsuwarta Koh zama takasa waje Daya, tunda ta gudo daga hospital karshe dai Saida mamarta ta tambaye ta Koh meke damunta haka? tunda abinnan ya faru ta fahimci walwalar zainab ya d’auke, zainab Kam kin fad’a Mata gaskiya tayi

    Suna zaune dukansu a gida dayake yau Friday ne ubangari ya dawo aiki da wure haka Yan makaranta,ji kawai sukaye an bankado get in gidan an shigo ciki kafun ma su gama tantance suwaye ne har kanwar Aisha ta nufi d’akin zainab jawota sukaye har kofar gidan da gudu su ubangari suka Mara musu baya.

    Rufeta da duka ADARA sukaye, saiga khairat tafitob gida makwantan su, Aiko kamota sukayi suka Had’asu suna jibga duk yanda Yan unguwa da ubangari suke kokarin k’wace zainab da khairat abin ya gagara ganin zasuye kisan kai don zainab ta Suma Amma haka Ayarin gidan Adara Basu daina jibgarta ba Saida ta farfado da duka

    Police aka Kira lokacin unguwan ya cika makil day’an kallo, abinka da Friday kowa na gida,

    bayan zuwan police kafun aka samu aka k’wace su zainab anso Kama Yan ADARA Amma Ina abin ya gagara don fad’ane ya kusa zama na police da Yan gidan Adara,ganin jaraba irin na Yan gidan yasa polisawan tambayar musabbabin fad’an don dai sunyi sunyi su bisu station aye kome agun Amma sunki, D’aya daga cikin samarin gidan ne ya nuna zainab,ke don uwarki fada musu meya faru tsakaninki da yusuf mijin Aisha?

    Hakika zainab tayi mugun tsorata hakan yasa Bata boye kome ba ta fad’a duk abinda ya faru,atake Alumman suka fara Allah wadai da zainab da khairat ubangari Kam yanke jiki yayi ya Fadi hawan jininsa ya tashi, police ma tafiyarsu sukaye Basu d’auki kowa ba.

    Ta bangaren Aisha Kam ganin tana kokarin rasa Ranta yasa likitoti Mata operation aka cire baby girl bakwaini aka saka a kwalba,Aisha na farfadowa sunan mijinta ta fara Ambata tana sambatu,tunda ta farfado batada magana sai a kaita wajen Yusuf ta nemi gafaransa Amma ba’a barta ta fita a asibitin ba saboda yanayin jikinta Dana baby.

    Ta bangaren ubangari ma hakan take jinya ya kwanta har kusan sati baisan inda kansa yake ba abubuwa sun taru sun Masa yawa,Yana Jin sauki kad’an ya Tashi da kafarsa ya koma wajen Alkalin da yayi musu Shari’a,

    An nemi ganin Yusuf don a wankesa a kotu Amma abin tashin hankali shine, Yusuf a Randa aka kaisa prison Bai kwanaba ya fita tare da sa hannun kotsosin kasa

    Wannan magana ita tafi ko wace magana tashin hankali agun Aisha don anye iyya bincike an had’a hannu da masu kudin da Yusuf yayi mu’amalan kasuwanci dasu don binciko inda Yusuf yake Koh suwa suka fiddasa

    Duk Wanda aka tuhuma Mai hannun a cire Yusuf magana D’aya yake fad’a baisan Yusuf ba kawai umurni aka basa daga sama

    Wannan magana tayi mugun dagawa Aisha hankali atake ta sake kwantawa ciwo Wanda an rasa kansa kullum gaba gaba yake duk abinda babanta ke dashi ya kare a jinyar Aisha da Salim don shima zuwa lokacin zuciyarsa ta fara tashi.

    Tsawon wata biyar ana binciken case in Yusuf Amma shuru ba wani cigaba,yau dai jikin Aisha da sauki,bayan Salim da Yusuf sunzo duba mamar tasu ,don yanzun suna zaune a gidan Adara ne

    A hankali ta Kama hannun Al’ameen ta rike cikin nata ta fara magana hawaye nabin Gefen idanunta,Al’ameen ga kaninka nan da Yar uwarka khadija Muhammad ka kula dasu ka zama uba a garesu Koda kowa zai gaji dasu Kai ka zaman musu gata, jagora,Garkuwa,inaji a jikina wata Rana zaka Hadu da mahaifinka,kace Masa ni Aisha Ina neman afuwarsa ya yafe mini Koh Zan samu salama,ka zamo Mai hakuri kamar mahaifinka duk abinda zakaye a rayuwa ka ringa bincike karka yanke hukunci a cikin fushi don karshin sa Dana sanine.

    Al’ameen duk da yarone Amma hankalinsa in yayi dubu toh ya tashe in Bai manta ba haka abbajonsa yayi Masa, shikenan ya gudu ya barsu don shi har yanzun baisan takammamen abinda yake faruwa ba,

    Mami kema gudu zakiye kamar abbajo ki barmu?yace Yana kuka shida Salim dake kusa dashi

    Ah ah Yusuf ba gudu zanye na barku ba inda zanje kowa ma zaije in lokacin sa yayi sanan abbajonka Bai gudu ba wata Rana zai dawo kaji,ga kaninka na kuka ka rarrashesa karka barsa ya zubda hawaye kasan ciwonsa bayason damuwa Koh?ta tambaye sa muryanta na shakewa

    Kai muhammad ya gyad’a Mata hade da Kama hannun Salim Yana rarrashensa,

    Ji kawai yayi mamin su na wani irin shakuwa hade da Kiran sunan Allah,da sauri ya fita a d’akin yaje Kiran Doctor

    Suna shigowa dakin da sauri Muhammad ya matso gareta cikin matukar razana ganin maminsu Bata m……………….

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense
    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 44-45

    Matar Makaho 44-45

    Page 4️⃣4️⃣&4️⃣5️⃣
    Al’ameen ne ya yanke jiki ya Fad’i,sosai mutumin ya rikice yahau salati cikin kidema

    Hayaniyar sa shiya matashe samarin dake kwana a d’akunan kofar gida,Suma dai sosai mutuwar Salim ta shigesu ruwa aka watsawa Al’ameen Amma Ina Koh farfadowa baiyi ba Dole tasa wasu daga cikin matasan d’aukar sa zuwa asibiti

    Usman makwancinsu shiya d’auki gawar Salim zuwa gidansa

    Washe gari agidan malam Usman aka shirya salim.

    Al’ameen dake asibiti kam Yana farfadowa da asuba ya tashi hankalin kowa sai ya dawo ankai Salim tare dashi

    Haka aka kamasa g’wanin tausayi zuwa gidan malam usman,Yana shiga gida aka Kaisa Kan gawar D’an uwansa a hankali ya zauna Kan cafet in hannu yasa Yana lalube ya bude gawan jikinsa na bare yasa hannu ya shafa fuskar Dan uwansa murya na rawa hawaye nabin kuncinsa yake ma D’an uwansa Addu’a

    Salim sosai ya samu jama’a kamar me don duk wanda yasansa, kuma yaji mutuwarsa yazo,tare da Al’ameen aka kai D’an uwansa kabari.

    Bayan mutuwar Salim sosai kewa da kad’aici ke damun Al’ameen Koh bacci baya iyya wa saboda kewan D’an uwansa shikenan yanzun baida abokin Hira baida Wanda zai fad’awa damuwar sa baida Wanda zai kwana tare dashi sai Yar kanwarsa khadija ita Kuma mace ce

    Mai gidan Salim shiya bawa Al’ameen kudi Ya sari mangoro Koh a bakin kofar gidane ya fara saidawa don Bai dace Yana tsallake titi kullum zuwa kasuwa zaman shago ba

    Ba musu Al’ameen ya karbi kudin yad’an fara business dashi,Kuma Allah yasama abin Albarka Yana samun na abinci da biyawa Khadija D’an hidindimun makaranta

    Zancen kamila Kam baiyi fushi ba duk da Bata Masa ta’aziyar D’an uwansa ba haka ya sake Kama Khadija don lokacin ta d’anye wayo sukaje gidansu kamila.

    Kamila ce tsaye da kawayen ta a waje tare da wasu samari uku A bakin mota

    Al’ameen suna Isa kofar gidansu kamila,yaji hayaniyar maganar mutane Kamar harda ta kamila hakan yasa cikin murna yau dai zasu gana, tunda ya jima Yana zuwa baya samun ganin ta

    Da saurinsa yace wa Khadija suye wajen da Yake jin muryan mutane

    Ba musu Khadija na rike da sandar sa suka nufi wajen, Assalamu alaikum

    Waalaikumu salam D’aya daga cikin samarin ya Amsa Masa

    Ina wunin ku, Al’ameen ya gaidasu

    Lafiya samarin suka amsa d’ayan ya zare kudi a Aljuhunsa Yana mikawa Khadija,ungo Yan mata

    Khadija Kam kin karba tayi don bata Saba bara ba koma yayanta ya hanata roko Koh karban abin hannun Wanda Bata sani ba

    Karba Mana yarinya D’aya daga cikin kawayen kamila ta fad’a don Bata San Al’ameen ba

    Yayana ya hanani karban kudin Wanda ban sani ba, Khadija ta fad’a musu tana noke kafad’a

    Da mamaki samarin ke kallon su Al’ameen mutum ya fitoh bara abasa yace bazai karba ba,toh lfy meya kawo ku gun mu inba bara ba

    Am don Allah Ina da tambaya ne? Al’ameen yace

    Allah yasa mun sani

    Yauwa Kamar muryan kamila nakeji d’azun a cikin ku?

    Eh ganinan lfy?kamila ta basa Amsa

    Lafiya kamila in ba damuwa inason magana dake ne

    Ina jinka,tace tana Masa kallon banza

    Don Allah mu koma gefe

    Kai MAKAHO akan me zaku kebe da matar da Zan aura Kai asuwa d’aya daga cikin samarin yace

    Wani abune ya cake zuciyar Al’ameen shikenan kamilar ma ya rasata shikam yaushe zai samu farin ciki ne duk mai kokarin faranta Masa wata Rana gudu yake ya barsa

    Kamila aure zakiyi?yace Yana kokarin faduwa tsaban shock

    Eh aure zanyi Koh kana da matsala da hakan ne

    Kamila Ina Alkawarin mu?

    Alkawari kana nufin na aure ka kana MAKAHO Kuma talaka da wanne zanji da ciyar dakai Koh da ciyar da yaranka Koh da maka jakora Koh d’awainiya?Zan dai iyya auren ka a Talaka Amma banda kana MAKAHO kam.

    Sosai zuciyar Al’ameen ta tsinke

    Dariya matasan da Y’an Matan suka sake na shekeyanci,Kai kamila bakida mutunci wallahi 😒 soyayya ce fa saikuje kusha love da lalube D’aya daga cin Yan matan ta fad’a tana dariya

    Budurwar da ke gefe sanye da hijab itace kad’ai Bata ma Al’ameen tozarci ba

    Kama hannun Khadija taye hade tacewa Al’ameen su tafe

    A hankali Al’ameen ke tafiya Kamar k’wai ya fashe Masa a ciki Bai d’auka Koh nakasa zaisa kamila gudunsa ba Koda kowa zai gujesa

    Suna sharan kwanan nayin, kawar kamila ta dube Al’ameen,kaga bawan Allah don Allah Ina Mai rokon alfarma a gareka shine ka rabu da kamila Koda itace autar Mata ka barta duniyace ai Koda zata rabu dakai bada tuzarci Koh kushen halitta ba Amma ita Bata dube hakan ba y
    Ta wulakanta ka kaima ka barta bari na har Abada,Kaye hakuri Allah Yana tare da musu hakure.

    Insha Allah baiwar Allah na rabu da kamila Nima na hakura da ita Allah ya had’a kowa da rabonsa,

    Ameen ta basa amsa tana Mai komawa layinsu tabarsa tsaye da Khadija

    Wannan shine Ranar da Al’ameen ya fita a Rayuwan kamila.

    Bayan wasu shekaru karatu ya fara zama sai da kudi, a hakan yake ta faman ganin Khadija tayi karatu Koh ba kome zata tallah fawa kanta, Amma Ina kudi ya gagara don yanzun mangoron ma sai a hankali Bai wuce a Rana yayi cinikin 200 Koh kasa da hakan. Gashi a ciki Kuma yake ciwa cikinsa hakan yasa karatun Khadija tsayawa iyya Junior.

    *An dawo labari* ………..
    Khadija Kam kuka take kaman me,haka ma Sumayya Allah sarki Ashe haka rayuwar wa’innan bayin Allah yake, tasu kaddarar kenan,a cikin Yan watanni nan da mahaifinta ya juya mata baya taji kamar tafi kowa matsala,ashe itakam ma in an had’a kaddarar ta dana Muhammad nata ba kome bane tunda har tayi karatu ta tashi cikin kudi da lfyr ta Amma shifa ga maraici ga kuncin rayuwa da Talauci.

    D’aga ido tayi tana kallon Al’ameen dake zaune a kujera fuska tayi ja”yayan khadija baka bani lbrn auren mu ba”?ta tambaye sa

    Khadija tashi ki tafi kinji kukan ya isa haka, Al’ameen yace batare da ya amsawa Sumayya tambayar taba

    Mikewa Khadija tayi zata fita a d’akin cikin kuka abin g’wanin tausaye”Khadija”Sumayya ta Kira sunan ta

    Na’am Aunty

    “Khadija kiyi hakuri kome na rayuwan duniya Mai karewane Sannan Yana da iyyaka kinji”?

    Toh Aunty tace tana share hawayenta

    “Ki d’auki doyan nan ki tafi dashi gobe da safe sauki kawo mini ducuments naki kinji Khadija”

    Toh Aunty kawai tace tana d’auki laidan doyan ta fita

    “Yayan khadija na tambaye ka shine kaci no face”

    Sumayya nagaji wallahih ki barni nad’an huta Mana waima me zakiye da ducuments in Khadija ne?

    “Oho ba’a sani ba Ina maka magana kana tambaya ta Nima naki fad’an”

    Shuru ya Mata tare da lumshe idanunsa

    Itakam ganin ya Mata shuru tasan dai akwai abinda bayason fad’a matane,tashi taye a hankali ta Isa garesa faduwa tayi a kansa da gangan

    Washhhh yace yana gyara Mata kwanciya

    “Don Allah ka fad’amin Mana”

    Kinga Sumayya nifa banason na fad’a Miki abinda zaizo Yana d’aga Miki hankali.

    “Allah bazan d’aga hankalina ba kawai ka fad’a mini”

    Ok toh shikenan Amma sai da dare Zan fad’a Miki

    “Gaskiya Nina gaji da abinda kake minin nan wani irin sai dare Kuma Wannan ai Jan Raine”

    Banace Zan fad’a ba ki barni Mana zuwa Daren in ban fad’a Miki ba saiki Tuhume ni

    “Uhmm toh yanzun me zakayi”?

    Bacci,ya Amsa mata

    “Bacci a hakan”?

    Eh…..

    Tashi Sumayya tayi taje ta d’aura abincin dare ta barsa a d’akin

    Bayan fitarta sosai yake tunani akan ya fad’a matane Koh karya fad’a Mata karshe dai ya yanke shawaran ya fad’a matan kawai

    Bayan isha’i Sumayya ce da Al’ameen kwance akan gado Sumayya taye matashe da cinyar Al’ameen sunfi minutes 20 a haka,tunda sukaci abincin dare sukayi sallah, suke a haka Amma Al’ameen baice mata kome akan labarin ba abin sosai ya dame ta Amma ta danne tunda yace zai fad’a zata barsa ya fad’an da kansa.

    Sumayya!!ya Kira sunanta Yana Mai shafa gashin kanta mai tsawo da kamshi

    “Na’am”ta amsa Masa

    Sumayya banso fad’a Miki dalilin auren mu ga ganin cewa kece kikafi kowa sanin hakikanin gaskiya don bana tunanin har yanzun ana cikin zamanin da za’a ma mace aure batare da tasan miji Koh miji ya santa ba.

    “Me kake nufi”? Sumayya ta tambaye sa fuskar ta a hade Jin abinda yake fad’a Mata

    Yanzun masifa Zaki mini Koh Jin lbr zakiyi?

    “Aiba labarin kake bani ba sukata kake”Sumayya tace,tana kokarin sauka a gadon

    Sorry toh, yace Yana kamota

    “Nikam ka sake ni ”

    Kin saketan yayi yana rungume da abarsa, naki sakin kin in kajimin mata fa

    “Allah ni ka sakeni nace maka”tace tana kokarin xame kanta a jikinsa

    Fushi kikayi ne Gimbiya?

    ” waye Gimbiyar”?

    Sumayya mana.

    “Gimbiyar wa”?

    Al’ameen…

    Uhmmm kawai tace bata kara magana ba

    Kinga na miki Alkawari, zan fad’a miki gaskiyan abinda na sani akan auren mu?

    “Nima nafasa ji yau sai gobe”ta fad’a tana mai sa hannu ta d’auko wayarta dake gefen filo, airp inda ke makale a jikin wayar ta manna a kanne

    Sai magana yake baiji ta amsa masa ba hannu yasa yana tattaba ta, Gimbiya ina magana kin mini shuru

    Duk da sumayya taji Al’ameen ya taba ta Amma taki koh sauraransa

    Shikam gane fushi take yasa sa dagota sama daga jikinsa ya jefata gefen gadon

    Ihu sumayya ta sake bawai zafi taji ba don laushin katifar dana blanket bazai bari taji zafi ba tsorata kawai tayi don bata tsammaci hakan ba” wayyo wuyana ya karye”

    Nashiga uku sumayya inga wuyan da gaske kinji zafi dan Allah kiyi hakuri ban dauka zakiji zafi ba, yace yana matsowa kusa da ita

    Sumayya kam langobewa tayi wai wuya ya bugu”wayyo wuyata shikenan ya kasheni jama’i

    Don Allah kiyi shuru muga wuyan wallahi bada niya nayi ba

    Sumayya kam kara lafewa tayi jin ya cicibeta ya daura a cinya kamar wata baby

    Sannu sumayya koh muje asibiti ne?

    “Nidai goyona nakeso kayi”ta karasa maganar da make murya

    Jikinsa na rawa yace, toh… toh… hau, yana dukawa a kan gadon

    “Nika d’agani bazan iyya tashi zaune ba”

    Cicibar sumayya yayi ya goya haka ya ringa lalube yana zaga d’aki zuwa baranda da ita sai kusan 10:00 sumayya taji gyangyadi kafun tace masa, ” ka kwantar da ni bacci nake ji”

    Ai da sauri bawan Allah yayi d’aki da ita da lalube ya shimfid’ata a gadon duk ya gama gajiya ba kad’an ba shiyasa daya samu taye bacci ba karamin dadi yaji ba gudun fitina ma koh tabata bayyi ba a gefe ya kwanta yanata tunanin wuyan sumayya don harga Allah ya d’auka da gaske ne

    Da asuba ma hakan take sashi tayi ya d’auketa har waje tayi alwala ya dawo da ita d’aki kafun ya tafi masallaci.

    Misalin karfe 9:12 na safe Al’ameen ne ke bacci a d’aki bayan dawowar sa sallan asuba

    Sumayya data gama aikinta a nitse tayi girki duka don bata tashesa ba saida ta gama harda wanka tayi kafun a Hankali tashigo d’akin wayanta ta d’auka ta danna play in waka ta kara volume, ta saka Eirps kunnen Al’ameen ta mannawa

    Ai kam yana cikin baccinsa yaji abu tibbbtibb ga waka kamar a kwakwalwarsa, da sauri ya mike zaune hade da furta, innalilahi sumayya wuyank……..sai kuma yayi shuru jin dariyan sumayy a kusa dashi

    Hannu yasa sosai ya damkota kwantar da ita yayi a gefensa yahau kanta sosai yayi lamo yana daidaita bugun zuciyarsa har lokacin abin na kunnensa

    “Wayyo menene haka”?

    Shikam koh jinta bayayi, sai dad’a lumshe idonsa yake jin wakar da ke tashi a kunnensa sosai yatafi dashi

    Da sauri sumayya ta zare eirps in jin sai magana take baya kulata

    Da sauri ya bude ido, tare da kamo hannunta data cire masa abin kunnensa, mena cirewa? wakarfa bai kareba

    “Inata magana kamin banxa badole na cire ba”

    Toh mekike son na miki kenan guda daya? tunda jiya ma ai magana nake miki kika saka abinnan a kunnenki kika manna mini nima, duk wai akan maganar jiyanne kiketa fushi koh?

    Shuru sumayya tayi

    Dalilin auren mu…….
    nidai bazance Miki nasan kome akan auren mu ba illah dai bazan manta ba wata Rana wani mutum yazo ya sameni agun sana’a ta yasai Mangoro ya tafi bayan kwana biyu Kuma sai gashi ya dawo Amma baifita a motarsa ba aika yaro yayi ya kirani nakai masa mangoro bayan naje ne yace na Shiga motarsa, Yana da magana Dani,ni kuma naji tsoro gudun kar Amaimaita na baya(Randa aka makantar dashi) shiyasa naki Shiga motar duk yanda yayi Dani ki nayi,karshe dai agun mukayi magana,Kamar haka

    Ni sunana mamman Ina da yarinya Naga hankalinka da nutsuwarka shine nayi maka kwad’ayin Koh zaka Amince in baka auren ta?

    Sosai naji mamaki nida bana gani ad’auki yar Mai mota sukutum a bani gani Talaka haka kawai sainaji Raina Bai Kama zancen ba, shiyasa nace Masa bana bukata batare da Kuma sauraransa ba nayi tafiya ta

    Bayan sati D’aya kawai bappa sulaiman yakirani Wai za’a mini aure,sosai abin yaban mamaki za’a mini aure kuma kamar mace,bappa aure Kuma Kamar Yaya?na tambaye sa

    Kamar yanda kaji bappa sulaiman ya bani Amsa

    Duk Azana Yar gidan nan za’a bani Amma bappa yace Wai Yar shugaba family ne tunda naji haka kawai nasan lallai wannan aure mai dalili ne ba auren Angani anaso ba,da farko naso nunawa bappa illan auren nan Amma ya murza ido yace sai anyi daga karshe ma cemin Yaya Wai yarinyar tanada Wanda zata aura matsala aka samu bayan anyi test shine aka samu tana d’auke da c…………….

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 46-47

    Matar Makaho 46-47

    Page 4⃣6⃣&4⃣7⃣
    Wai yarinyar tana d’auke da ciki shiyasa sukeso na rufa musu asiri na aure ta

    Sosai nayi mamaki kuma zuciya ta takasa Aminta akan zancen cikine kawai ba, tunda yaran masu kudi da yawa suna cikin shege Amma ba’a bawa talakawa saini MAKAHO sam nakasa yarda.

    Dana matsawa bappa da tambaya ma cemin yayi koh naki koh naso sati mai zuwa d’aurin aure

    Harga Allah banso auren ba sam, don inaji a jikina ba batun ciki bane, imma cikin ne taya za’ayi a d’aura aure da ciki a jikin budurwan kenan, koh an zubar?karshe fa akafi karfine kafun sati d’aya ba wanda baisan zancen auren mu ba saidai sam ba wanda yasan dalili kuma duk wanda yaji batun auren saiya digawa auren ayar tambaya

    Amma ke sumayya menene dalilinki na aure na?

    “Auren ka, ina ma na sanka kajimin mutumi fa” ?ta fad’a cikin kuka sosai abin ya mata zafi watoh bayan auren kaskanci da akaso mata har b’atata akayi a wajen mijin don aga abinda yafi wanda suka sata😭muni

    Sumayya nifa tambaya kawai nayi kuma abinda nayita gujema kenan, kika ga nake gudun fad’a miki gaskiyar abinda na sani, ya karasa maganar da kara rungumarta jikinsa

    “Shikenan yanzun koh inada cikin sai ka yarda ka zauna dani” ?

    Indai har cikin babu a jikinki koda kin tabayene zan zauna dake a hakan ma naji dadi ai, na samu mata

    Kuka sumayya ta sake sakewa watoh duk zaman da suke da Al’ameen na kokonto ne tayi ciki koh batayi ba kai wai meta tsarewa dangin mahaifintane, na mahaifiyarta kamma bata sansu ba bare

    Kiyi shuru sumayya mundin bakece kika gaji da zama dani ba ni bazan taba juya miki baya ba a duniya, bayan khadija da ke sai goggo bayan ku banida mutanen da suke sona tsakani da Allah, ke kuma kin nuna mini tsantsar hallaci a rayuwa, don wata koh da gaske tayi ciki aka aura matani bazatayi hakurin zama dani ba bare ta taso cikin kudi yanzun kuma tana fama da rashi harsai ta nemi na kanta

    Da sauri sumayya ta rufe masa baki cikin kuka tace”karka kara fad’ar haka banaso nima a yanzun kaine kad’ai Garkuwa ta kaine bangon da zan jingina ya rikeni, insha Allah kome zai wuce kamar ba’ayi ba.

    Allah yasa toh yanzun ya maganar kamilar?

    “Bazan koya mata ba gaskiya kartazo tana shigewa mijina don yanzun kai ba tsaranta bane”

    Yanzun shikenan saboda ni saiki rasa makudan kudi haka?

    “Wani makudan kudi kuma bayan jiya ma na samu mutum uku da zasu fara zuwa, shiyasa yau zamu fita dakai muje bank zan bude Account maganar kudin koyar, shiyasa zan bude Account transfer zasu mini ta bank kuma yaran manya ne sosai fa, inaga anya ma bazan bude shago ba”?

    toh Allah ya bada sa’a, Amma banda maganar shago kam banyarda ba matar aure da shago kamar wata inyamura.

    “Ayya koh a shagunan kofar gida saina kama d’aya tunda bakin titi ne”

    Sumayya ban Amince ba, yace yana tashi akanta hade da karban eirps in hannunta ya mayar kunnensa kawai ya kwanta

    Ganin ya kwanta yasata tashi ta d’auko musu karyawa jejjerawa tayi, ganin bai sauko ba yasa a hankali tahau kan gadon agadon bayansa ta kwanta luf ta lumshe idanunta “breakfast is ready”

    Shuru taji bai amsa ba Amma dai yasa hannu ya tabata,hannun ta buge hade da cire masa abinda yasa a kunnen san ta makala a kunnenta wakar umar m shareef ke tashi a ciki

    Jin ta cire masa yasa sa mikewa da sauri ya Amshi abin a kunnenta, wakar dadi tamin don Allah ki maida mini, ya fad’a mata yana mai mika mata wayar hannun nasa jin wakar ta chanja

    Hhh”waikai kam anya ka taba saka eirps a kunnenka kuwa”?ta karasa maganar da sauka akan gadon

    Da sauri shima ya sauko had’e da cewa wallahi kamar kin sani inadai jin ana zancen sa Amma ni bantaba sawa ba ashe da dadi

    “Hhh toh zauna kaci abinci sai na baka bluetooth harda wa’azi da karatun qur’ani zakaji a ciki ba waka kawai ba”

    Menene bluetooth kuma, banda na waya?

    “Baka san ana posted a waya ba? toh ai yakamata kasan bluetooth da mp”

    Nasan mp mana, bluetooth ne bansani ba saina tura abu a waya inaji anacewa kai bude bluetooth naka na tura maka waka koh vedio.

    “Kayi kokari wannan kuma na yayi ne a kunne zaka makala ba tare da igiya kamar eirps ba ka gane”

    Eh na gane..yace yana zama

    Abincin sumayya ta zuba musu mika masa tayi bayan ta damka masa shukali a hannu, wai nikam me kika maidani ne? an gaya miki bazan iyya d’aukar shukalin bane?

    “Waya sani koh abincin ma saina fara baka”

    Kwafa yayi kawai ya fara ci

    Suna tsaka da karyawa sukaji sallamar khadija amsa mata sumayya tayi hade da bata izinin shigowa

    Khadija bataso shigaba ganin yayanta na d’akin, Amma ba yanda ta iyya haka ta shigo, ina kwana Aunty?

    “Lafiya khadija ya goggo”?

    Tana lafiya ina kwana yaya, tana maganar tana kokarin zama

    Lafiya khadija…ya Amsa mata

    ” khadija matso muci” sumayya tace wa khadija

    Ah ah Aunty nagode, daman takarduna ne na kawo miki duka kamar yanda kika bukata.

    “Lallai ma khadija bansan yaushe zanna baki abu kisa hannu ki karba ba tare da kin mini filako ba”tace tana mikawa khadija plate na abincin data zuba mata sabo

    Ba musu khadija ta karba

    “Yayan khadija”

    Na’am sumayya..

    Inaso zamu fita da khadija, zanje na sama mata makaranta tunda yanzun muna first time bazamu sha wahalar samun aji ba, Amma yakace ka Amince koh yaya”

    Sumayya bazance miki kume ba sai dai nace Allah ya biyaki, tabbas yau zaki cikamin d’aya daga cikin buru kana dana so cikawa amma kana naka Allah na nasa.

    Aunty makaranta zaki sani😳??khadija ta tambaya cikin zare ido fuska a washe

    “Insha Allah kanwata zaki shiga makaranta yau yau ma amma wani school kikeson shiga”?

    Koh wanne ma aunty nagode kin gama min kome arayuwa tunda zaki sani a makaranta bani da wani zabi koh wanne ki sani.

    Matsalata dake kenan khadija in mutum yace kaza sai kice kaza, yanzun ni in baki fad’amin makarantar da kike soba ina zansan makarantan da ya dace ki shiga”

    Nidai aunty na baki zabi

    “Shikenan bari yayanki ya zaba miki”

    Da sauri Al’ameen yace, nikam ba ruwana tsakanin ku nida ba idone dani ba ina nasan makarantu inba na gw’annati tada ba

    “Shikenan yanzun Art kikeso koh science”?

    Aunty science nakeso.

    “Shikenan sai muje GSSSJ ina ga makarantar tafi inganci a harkan science”

    Kai Aunty tsadane fa da school in kuma ga kudin registration mai yawa gashi wai sai anye Attitude test kafun abawa mutum gurbin karatu.

    Khadija kenan indai kin yarda da kanki Attitude test bazai baki tsoro ba maganan tsadan registration, kuma ai kyaunsa yasa kudin yayi yawa, duk da makarantar goverment ne”?

    Gaskiya ne sumayya kinsan koh lokacin mu ba makarantar da ta kaita inganci kyau da doka kuma sai wane da wane ne a ciki a kaf Taraba daga goverment har private Amma yanzun xamani ya chanja saidai a sata a lissafin goverment school mafi inganci

    “Yauwa bara na tashi in shirya kaima sai muje dakai yayan khadija zan bude account a bank da voter’s card naka”

    Nikam gaskiya ba inda zani tunda khadija tazo da National ID card nata sai a bude miki babban Account kawai.

    “Kace kawai bazaka ba shikenan”sumayya tace tana mikewa,kaya ta fitar zata saka ganin haka yasa khadija fita a d’akin ta bata waje

    Nifa kawai zuwanne banji shiyasa nace kije da khadija

    “Toh zamuje daga nan saina wuce bank in, nama manta ban fad’a maka ba nayi posted na vedio n make-up da lalle harda photos yanzun haka next week za’ayi bikin yar kanwar Deputy Govnor an bani kwangilan musu lalle da make-up kawaye kawai da Amarya”

    Duk sunzo gidan nan?Al’ameen ya tambaya da mamaki

    “Ah ah a online fa muka gama kome har balance na fad’a musu yanzun ma jiran Amaryar take na tura mata account numbar na”

    Wow Allah abin godiya Amma dai sunan ki da suka ganine yasaka su baki aikin hala?

    “Wani irin suna kuma?toh ni ban ma saka sunana ba wani sunan na saka”

    Wani suna kenan?

    “Basai kaji ba” tace tana yafa gyalenda ta d’auko sai jaka da takalmi data rike a hannu zata fita a d’akin sai kuma ta sake juyowa ta kallesa jin tambayar da ya mata

    Sumayya baki bani bluetooth in ba?

    “Ikon Allah”tace hade da nufar cikin kayanta, Allah yasa ma tayi charge insa, makala masa tayi a kunne ta saita da wayanta,” waka zan saka maka koh wa’azi”?

    Waka….

    Wakar ta kunna masa”ga wajen da zaka taba ta gefe in zaka danna next koh back koh stop koh play”tana fad’a tana kama hannunsa tana nuna masa gun

    Eh na fahimta, saikin dawo

    “Allah yasa zanbi kasuwa duka me zan saya maka”?

    Kasuwa kuma sumayya?

    “Eh mana koh bakason naje? na saima khadija uniform ne da kuma d’an cefene nakeso na mana na sati uku kafun a fara azumi”

    Saikun dawo Allah ya kiyaye hanya

    “Ameen baka fad’a mini abinda zan sai maka ba”

    Am waken Gembu(Red beans)nakeso inkin iyya dafawa yanda suke innan asa tarugun Gembu(yellow pepper) da ice fish, irin dafin.

    “Hhhh eyeee kaima har kasan hadin dadi haka bansani ba”

    Allah inason abincin sosai…

    “Shikenan zan saya maka sai mun dawo”

    Allah yasa…

    Ameen, sumayya tace tana fita a d’aki, suka nufi kofar gidan da khadija

    Sunje makarantan kuma Alhamdulilah khadija ta samu gurbin karatu a makarantar science bayan interview da aka mata don an riga anyi Attitude test tun bayan sati uku, sun bawa khadija class, sumayya ta biya kudin kome atake aka mata registration aka bata su textbook, notebook , da tarkacen kayan makaranta su rigan sanyi rigan house socks vaji da sauran abubuwa

    Bayan sun bar makarantar yau kam duk wanda yaga khadija koh ba’a fad’a masa ba yasan tana cikin farin ciki sosai bank sukaje sumayya tasa aka budewa khadija Account .

    Kasuwa suka wuce tasai ma khadija uniform jaka da takalmi don sune kawai ba’a basu ba, a kasuwar ta baiwa tailor ya d’inka musu kala ukune jibi khadija zatazo ta karba Turare ta saima khadija da mayuka masu kyau sai Dutsen guga karami na wuta.

    Cefene tayi mai yawa sosai ta sai harda su drinks, doya, dankalin hausa, harda na turawa, vegetables, kai abubuwa sosai sumayya ta saiya saida kudin hannunta ya kare na machine kawai ya rage musu da d’an abinda baza’a rasa ba

    Bayan sun dawo gida da sallama, suka shiga gabaki d’aya dan dazon yan gidan suka bisu da ido ga kaya niki niki kamar masu kaura suka wuce suka shiga kofar ga yara na rirrike da laidodi

    Wa’alaikumus sallam, sannun ku da hanya Al’ameen yace yana cire hannunsa daga cikin kwanukan da yake wankewa

    “Yauwa yayan khadija” sumayya tace tana bin kofar da kallo ganin kayansu daya wanke ga randa a cike da ruwa Alamu dai jido yayi

    Yaran na sauke kayan sumayya 10 10 ta basu da murna suka karba kowa na jin dadi suka fita

    Sallah khadija da sumayya sukayi kafun suka baje cefenen suna dubawa, khadija kam ganin yanda sumayya ta loda mata kayan sayayyanta a gabanta kuka kawai ta sake tana rungumar sumayya,yanzun aunty duka wannan nawane? yaya kaga kayan kuwa wai duka nawa😅, tana fad’a tana kamo hannun yayanta ta d’aura akan damin kayayyakin abin ma abin dariya da tausayi

    Shima karan kansa Al’ameen yayi mamakin kayan, sumayya abubuwan nan basuyi yawa ba kinje kin kashe kudi da yawa haka sumayya kina ga ba aiki nake fita ba bazaki tattala kudinki ba sai kina fashaka haka.

    “Allah zai kawo kuma maganar baka aiki bazai hana nayi walwala ba kaima insha Allah kafun d’aya ga azumi zaka daina zaman gidan nan”

    Allah yasa Amma dai sumayya kayan yayi yawa

    Babu wani yawa yar fa makaranta ce sai da guga da wanki da gyara, kema khadija duk safiya kina zuwa kafun ki tafi makaranta kizo ki karya,ki karbi kudin tara dana keke kinsan sunce sai 2 ake tashi kuma ana dukan letti

    Toh Aunty amma zanna karyawa a gida saina zo na karbi na kudin.

    “Shikenan monday zaki fara zuwa jibi, kije ki karbi uniform in ki gobe ki goge, gata sai school”😃

    Hhh hakane Aunty in tafi da kayan naje na nunawa goggo kona barshi Anan?

    “Ai yanzun kayanki ne ki tafi dashi”

    Toh aunty tace tana rungumar kayanta ta fita

    Khadija na tsananin farin ciki yau wanda rabon dana gansa har na manta, Al’ameen ya fad’a yana lalubar hannun sumayya ya kama

    “Insha Allah zaka yita ganin sa yanzun harka gaji”

    Allah yasa, kema Allah ya biyaki

    “Ameen, na sai maka waken Amma na gaji gaskiya bazan iyya dafawa yanzun ba kasan sa da wahalar nuna”

    Shikenan sumayya Allah ya kaimu goben

    “Ameen”, tace tana d’aukar wayanta dake neman agaji”Assalamu Alaikum”

    Shuru tad’anyi sai kuma yaji tace “toh bara na tura miki ta WhatsApp”

    “Ok shikenan”, tace tana aje wayan

    “Kasan waya kira”?

    Ah ah …

    “Yar kanwar deputy ne waina tura account number”

    Toh Allah ya bada sa’a

    Ameen, bara na tura musu

    Tashi Al’ameen kam yayi yaje ya cigaba da wanke wanken sa

    sumayya kam Account numbar ta tura musu koh minutes 10 ba’ayi ba taji Alert kudine ya shigo account in khadija dayake da layinta aka bude account in…..

    Khadija kam na fita a gidan yayanta da kaya niki niki sai sauri take kamar zata fad’i damuwarta kawai taga ta isa gida ta nunawa goggo abin Alkhari data samu, bata hankalta ba tazo tsallaka titi koh ganin gabanta batayi, ji kawai tayi jama’a na illalilahi keeee kalli gabanki

    Ai jiii kawai kake kiiiiiiiiiiiii kauuuuuuuuu………….

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 34-35

    Matar Makaho 34-35

    Page3️⃣4️⃣&3️⃣5️⃣
    Al’ameen ne, Sumayya ta gani zaune ya zuba tagumi Koh abincin Bai d’and’ana ba.

    Cikin mamaki ta karaso cikin dakin”yayan Khadija lafiya kuwa”? tace tana matsowa kusa dashi

    Firgigit ya dawo hayyacinsa, Sumayya har kun Gama kwalliyar?

    “Eh mun gama,Naga bakaci abincin kaba Allah dai yasa lfy Koh” ta Kara tambayar sa.

    Lafiya Sumayya jiranki nake in kuka Gama saimuci”ya Bata Amsa

    Da mamaki sumayya ke kallonsa”banace kaci ba”?

    Sumayya na kasaci ne, kece Kika nema Kika dafa Taya zanyi na rigaki ci bayan ke kina ta faman aiki.

    “Karka Kara fad’amin irin wannan magana daga yau”

    Don me?ya tambaye ta

    “Saboda duk abinda na baka ni gani nake kamar kaika bani mukeci banason Kara Jin irin maganar nan,Ina zaune itdakai ne badon kome ba sai don Allah,rufin asirin ka nawa ne nawa nakane”ta fada tana kallonsa

    Shikenan Sumayya nagode,

    “Bana bukatar godiyan ka ka gode Allah”tace tana matsowa kusa da abincin budewa tayi tasa shukali”Bismillah muci”tace tana iba

    Toh yace Yana laluben nasa shukalin

    Abinci sukaci Amma cikinsu Babu Mai magana kowa Yana cin abinci ne,bare Hajiya sumy

    Suna Gama cin abincin Al’ameen ne ya tattara Kwanukan yafita dasu waje

    Sumayya Kam wanka ta shiga,tana fita tayi Alwala,kayan bacci tasa ta kwanta

    Al’ameen Jin ta kwanta yasa shima fita wajen ruwa ya Iba yayi wanka.kamar yanda yazamo musu Al’ada wankan dare kafun su kwanta,Yana fitowa ban d’akin kofar shashen su ya rufe,ya shigo d’akin,rufewa yayi a hankali yake takawa Yana laluben gadon harya iso, Hawa gadon yayi ya kwanta a hankali,

    Sumayya Kam mamakine ya kamata ganin sa a hakan Sannan yahau gadon ma Bai Saba Mata yanda yake Mata ba, watoh son mannuwa kusa da ita.

    A hankali ta mirgina kusa dashi hannu tasa ta Kama NASA hannun”yayan Khadija”

    Cikin sanyin halinsan nan ya amsa mata, na’am.

    “Menene yake damunka ne Wai” ?

    Ba kome Sumayya me Kika gani?ya tambaye ta Yana Mai dagota ya d’aurata a jikinsa gabaki d’aya

    “Ba kome, yauwa nace kanada National ID card ne”?

    Sai dai voters card bani da National ID card

    “Ok shima zaiyi Daman inason na bude account a bank ne kasan banzo da details nawa ba”

    Toh shikenan Allah ya kaimu goben saina baki

    “Zaka rakani bank in? Koh naje da kaina”ta fada tana gyara kwanciyar ta akansa

    Duk yanda Kika gani goben ne Zaki bank in Koh yaushe?

    “Sai na Gama lallen da akayi booking innan”

    Toh shikenan Allah ya kaimu saina rakaki,in khadija taji sauki Kuma sai kuje tare kinsan me?ya tambaye Sumayya

    “Ah ah”

    Khadija na son zuwa bank Kamar me haka lokacin kudin covid 19 ta dameni Wai sai naje mun bude account muma,mun cika Koh zamu samu kudi,Amma da mukaje bank hanani Shiga sukayi security Wai ba’a bara a banki,Kuma su tsaya su saurare mu sunki Haka suka kuramu waje.

    Sosai naji maganar ta tabamin rai”aiko Insha Allah da ita zani taga bank,Amma kaima fa Dole zamuje tare tunda account Kai za’a budewa ba niba.

    Toh Allah ya nuna Mana yace Yana zura hannunsa a cikin rigan bacci dake jikinta

    Jin hannunsa a riganta unexpected yasa ta zabura sai Kuma ta koma ta kwanta a hankali ta lumshe ido Jin abinda yake Mata da hannunsa a cikin riga”kasan me”?

    Ah ah ya Bata Amsa

    “Nikam Ina ga Zan Saida laptop Ina da waya”

    Akan me Zaki saidasu toh?

    “Saboda Banga amfanin suba inba kallo ba me nake dasu shiyasa Zan sayar”tace. Tana taimaka Masa ganin Yana kokarin zare rigar Tata

    Umm umm Sumayya waike bazaki ringa d’aukar kwalliya kina sawa a media ba Koh Allah zaisa asamu location naki Kinga ai sai afi saninki sosai a Jala

    “Kasan ba kowa keson asa hotonsa a social media ba shiyasa ban fara posted ba,Nima nayi wannan tunanin”

    Eh ai tambayan su zakinayi Zaki d’aura hotonsu kiyi Tallah Amma fa Yan Mata banda matan aure, insun Amince shikinan,tunda wasu da yawa in sunyi kwalliyar ma post suke.

    “Gaskiya ne Amma waya fad’a maka ana d’aura kwalliya a online?
    Kuma ya akayi kasan ana Post”?Sumayya ta tambaye sa tana kakkama Masa gashin kai Jin wani magic dake bin jikinta a sanadin abinda yake Mata

    Uhmmm ai inaji ana Hira koma ni lokacin da na makance ma waya tayi araha a hannun kowa ba,Kamar yanzun

    Washhhh toh,uhmm tace tana zillewa daga kansa ta sauka a gefe.

    Jin ta zame yasa ya bita shima, tana kwanciya ya kwanta akanta rumfa ya Mata da kirjinsa,ya had’a fuskarsa da Tata fuskar yayi Yana tsintsinar bakinta,dake kamshi

    “Wayyo ka sauka nauye”tace tana mutsu mutsu tana damke damtsen hannunsa

    Shagwaba Koh bafa nauyina na d’aura miki ba

    “Nidai ka sauka,kawai tsoro nakeji”

    Tsoron me?ko ni dodone?ya tambaye ta Yana Mai Kara matsota garesa

    “Ka sauka”

    Naki,yace Yana Kara Danna kansa akanta

    “Nifa bacci nakeji kaji muye bacci”

    Nikam banajin bacci

    “Nikam ai inaji Koh”?

    Sai kiye ai na hanaki ne?

    “Amma ai ka tokareni”

    Shuru ya Mata yaki kulata sai bidirinsa yake a kanta jifa jifa tana taimaka Masa

    Jin abin NASA ya fara yawa yasa ta fashe Masa da kuka

    A tsorace ya mike a kanta sauka yayi gefe cikin tsoro,yake tambayar ta,ke Sumayya menene,Yana tattabata yaji Koh lfy

    Saura kad’an dariya ya kubucewa Sumayya Jin yanda duk ya tsorata dagajin kukanta kawai,ta rasa ma wani irin namiji ne Mai shegen tsoro haka

    “Toh ba Kaine ba nace maka inajin bacci sai matseni kake”ta fada da muryar kuka tana kallonsa tana Masa gwalo ganin yanda sai zazzare ido yake kamar kace kittt ya ruga

    Shine abinda ya saki kuka?

    “Eh Mana”

    Toh Yi hakuri kwanta toh.

    Dariyace ta subuce mata Jin abinda yace Yana kwanciya a gefenta baima mannu kusa da itaba

    Cikin mamaki ya Tashi zaune Jin tana dariya, Sumayya Anya lfy kuwa daga kuka saiki koma dariya?

    Shuru tayi gudun karya harbo jirginta”babu kawai ji nayi kamar jakulkule ake mini a ciki”

    Shuru yayi baice kome ba illah rufe ido da yayi Yana nazarin Rayuwa yau Wai shine da Mata,Ashe haka zama da mace yakeda Dadi duk halinda kake ciki muddin ka samu mace na gari ka Gama samun Jin dadi,duk halinda namiji zai shiga mundin dare yayi zata ga tayi kokarin kauda damuwar tasa Koh Bata cireba,zatayi iyya bakin kokarin ta taga ta d’auke Masa hankali

    Jin yanda Sumayya keta motse yasa shi kiranta, Sumayya!!

    “Na’am”ta amsa tana gyara kwanciya

    Bakiyi bacci ba?

    “Umm banyi ba”

    Saboda me?

    “Haka kawai”

    Jin Amsar da ta basa yasa a hankali ya matso gareta,lumshe ido tayi Jin yanda tsikar jikinta ke tashi,Jin gashin kirjinsa na goguwa da bayan ta

    Hannu yasa a hankali ya Kama waist inta d’an zabura tayi kad’an,yasa hannu ya maidata,watoh kukan shugwaba Koh?

    “Bawani shugwaba,Kuma ni ba shagwabebbiya bace atoh”

    Shugwabebbiyace Mana ai duk lukutaye akwai shagwaba

    “Waye lukutar”?ta tambaye sa tana juyowa suka fuskanci juna

    Daga Sumayya har Al’ameen wani yanayi sukaji a tare da junan su sosai kusancin su yayi yawa akwance da suken nan

    Kece Mana, lukuta kiga nan naki fa Kato,yace Yana Kama Mata bombs,
    Hannu tasa ta buge Masa hannu”ai naka yafi nawa girma”

    Zare ido yayi Kamar tana ganinsa,ai Dana shiga uku ai,sai wando Mai shape za’ana dinka min.

    Hhhhh Sumayya ta Kama dariya “Wai wando Mai shape waya ganka kana tafiya kana murgud’asu a cikin jallabiya”ta karasa maganar da kamo hannunsa dake Kan kirjinta don wallahih kirjin zafi yake Mata

    Shi Karan kansa Al’ameen abin sai da ya basa dariya,Amma yakiye, murmushi kawai yayi,Jin ta Kama Masa hannu kafarsa ya daura Mata akan kafa.

    Kokarin mikewa ta fara har lokacin hannunsa na rike a nata Wai don karya taba Mata inda bataso

    Jin tana kokarin tashi yasa sa tambayar ta,Ina Zaki Kuma dare fa yayi.

    “Rigata nake nema”

    Kiye me dashi?

    “Me ake da riga”

    Sawa, ya Bata Amsa

    “Nima sawan zanyi”

    Nikam gaskiya banso kawai mu k’wanta haka.

    “Jikinka Koh nawa?wato mu k’wanta haka ka karasani ba”

    Sorry zafi yake mikine?

    “Eh Mana duk ka mammasa mini jiki”

    Amma ai kinji Dadi

    “Banjiba”ta basa amsa tana mikewa zaune

    Ai da sauri yasa hannu ya rike Tata hannun,yana kwance Bai tashi ba,kiyi hakuri mu k’wanta haka ba abinda Zan sake Miki.

    “Ai kasan bakyau kwana ba Kaya”

    Menene a jikinki Koh tsirara kike yanzun?

    “Rigan fa”

    Ai nace bazan miki kome ba yace Yana jawota jikinsa matseta yayi a hankali ya jawo blanket inda ke Kan kadon ya rufe jikinsu.

    ***********

    Washe gari Kamar kullum bayan Al’ameen ya dawo sallan asuba, sunnah TV Sumayya ta kunna musu daga ita harshi in suna kwance suna sauraron wa’azi.

    Sai wajen 7:3pm Sumayya ta mike shara tayi yayan Khadija ya Mata wanke wanke, ruwan zafi ta jona abuta,Yana tafasa ta juye a boker tasawa yayan Khadija nasa, ta shiga ban dakin

    tana fita yayan Khadija ma wanka ya Shiga.

    Vayan sun Gama shiryawa kudi ta mika masa 1k”ka sai Mana egg’s guda biyar sai bread na 500 Mai kyau ka hada Mana da butter ”

    Karban kudin yayi,ya fita.

    Bayan ya sayo k’wai da bread, soya k’wai in Sumayya tayi ta hada musu cornflakes ga tie,jira musu tayi a kasan cafet,kamo hannunsa tayi suka zauna a kasa, bubude abincin tayi”karbi shukalinka”

    Toh yace Ya karba shukalin ,tattaba plates in yayi Jin plate biyu ne ga bowl d’aya ga cups biyu,wannene abincin nawa Naga Kwanukan da yawa?

    Duka zakaci d’ayan soyayyen k’wai ne d’ayan bread ne da butter a jikinsa sai Kuma bowl na cornflakes,sai cups na tie”nace Ina tura Masa plate in k’wai a gabansa”kaci kwai sai kana Had’awa da tie ga bread”

    Shikam Al’ameen ya kasa magana Wai karyawane da abinci Kala uku shi Al’ameen,ganin Al’ameen bai fara ci ba ita har tayi Rabin cup na tie inta yasa ta aje kofin,hannu tasa a cikin k’wai in ta yagi babba ta tura Masa a baki

    Shikam Jin abinci a bakinsa da Kuma yatsarta sai faman tura Masa take yasa sa cizon yasan kad’an,

    Ai Kara ta sake hade da yarfa hannun nata”wayyo yatsana jini jini yake na bunu tace tana duba hannun”.

    Da mamaki Al’ameen yace jinii ma Sumayya?

    “Eh gashi shikinan ya gusuramin yatsa”

    Mu gani

    “Bazaka gani ba sai kace idone da kai”

    Toh muji.

    Bazakaji ba din,tace tana daukar kofin shayen ta

    Jin tayi Shuru yasa sa gutsurar bread Mai butter,Wai zai Bata itama d’ayar hannun nasa yasa ya lalubo fuskarta,Jin fuskar Tata yasa ya fara lalubar bakinta da hannunsa

    “Kasan Allah Inka samin hannun hagunka a bakina ba”tace ganin Yana ta tattaba Mata baki da hannun nasa

    Kayya abinci Zan baki,yafada Yana Mika Mata gutsuren bread inda ke hannun damansa a baki,

    Rufe bakin tayi Taki budewa.

    Shikam sai goga Mata bread in yake a lebe gashi duk butter ya Bata Mata fuska

    “Kanata Bata mini fuska da butter”tace bayan ta rike hannunsa

    Toh ba kinki bude bakin ba sai kokari nake,

    Kaga kaci abincin kan, ka barni naci nawa,tace Masa tana goge fuskar ta

    Toh ki bare na baki wanann kawai kinji

    Ganin yanda ya nace Mata yasa ta bude bakin Yana saka Mata bread in da sauri ta datse hakorin ta,Wai don ta cije yatsarsa shima abin mamaki da sauri taga ya cire hannunsa kafun ma hakorinta ya Sauka akan yatsar,Yana dariya

    Ai Daman nasan saikince Zaki Rama shiyasa Nima nayi taka tsamtsam da yatsana.

    Shuru ta Masa Bata tanka masa ba.

    Haushi ya shigane bakutuwa?

    Kara ta sake tayi kansa “nice bakutuwa”

    Jin ta hafto, yasashi Kare kansa, hannu yasa ya tare fuskarsa.

    Ganin haka sai abin yayi mugun Bata dariya waishi harga Allah tunani yake wani abin zata Masa haryana tare fuska.

    Jin shuru baiji tayi Masa kome ba yasashi fara laluben ta Aiko ya jita a kusa dashi,da sauri ya rikota, sorry kinji

    “Ni……shuru tayi Bata karasa ba Jin sallama a kofarsu amsawa tayi ta mike kaci abincin kafun na dawo”

    Toh yace Yana saka hannunsa ya d’auki cup inda ta aje masa…

    Sumayya tana fita taga wata budurwa irin classic innan zata Kai kusan sa’ar ta kyakkyawace Amma baka Tasha kwalliya tana rataye da school back “sannuki da zuwa”tace Mata tana shimfid’a musu darduma”Bismillah ki zauna”

    Yauwa Ina kwana?bakuwar tace tana zama akan sallayar

    “Lafiya ykk ya gida”?

    Lafiya Alhamdulillah,ya aiki?

    Lafiya klau,Ina zuwa Sumayya tace tana mikewa d’akin ta shiga ta hada cornflakes da ruwa Daya a fijrij ta hada a tire ta kawowa bakuwarBismillalahih ka abin Kari ba nauye Kam”tace tana ajemata a gaba

    La d’awainiyane haka Allah dakin barsa yanzun na fitoh gida zanje school ne ma nace bara na biyu dai ta gidanki

    “Allah sarki Amma dai ki saka Koh albarkane yafi dai kikici bazanji Dadi ba”

    Shikenan bara dai NASA albarkan tunda kin Masa tace tana iban cornflakes in da shukali uku tayi tace Alhamdulillah

    “Badai harkin koshi ba”?

    Alhamdulillah wallahih ya isheni,suna na kamila Ina zaune a unguwan gadi,Daman nazone wajen ki in Babu damuwa inason zan fara Training in make-up,Naga wanda kika ma kanwata a auren Asma’u shine nace tamin kwatancen gidanki inyaso sai nazo inji.

    “Toh gaskiya ni bana koyarda make-up saboda bani da shago sai gidana Kinga Kuma Ina da ayyuka yau da gobe”tace Mata tana tunanin ta yarda ne Koh karna yarda

    Ba damuwa sister Nima Ina zuwa school Kinga saiki bani time inda zanna zuwa Koh ki ban number ki duk lokacin da kike free sai ki kirani Koh Kika samu Yan make-up.

    “Shikenan yanzun dai ki bare Inna ma mijina magaa in ya Amince xakiji daga gareni”

    Ok ba damuwa saiki bani contact naki Koh in ba damuwa sannan nawane kudin da Zan biyaki Kinga Inna koma Koh yaushe Kika kirani saina tawo dasu

    Toh, make-up dai kashi kashine sanann yanayin kwakwalwar mutum wata a wata D’aya zata koye make-up wata biyu wata fiye da uku ma Bata iyya ba so ni bansan ya yanayin d’aukar kwalliyarki ba Amma dai inso samune wata uku kina koya”

    Ok yanzun wata ukun nawa ne kudina

    “50k Koh wani wata kudinki na wata uku 150k kenan”

    Wai habba sister kudin nan yayi yawa Mana dubu dari da hamsin,

    Gaskiya kenan Kinga a cikin kudin Zan Saya make-up kit sabo duka,saboda bazaiyu Ina baki na aikina kina koya dashi ba, sanan infa kika iyya a kwana uku Zaki iyya samun sama da kudinda Kika biya na koyo”

    Hakane Kam Amma dai ki duba ki rage mini kinsan baban mu yace in zaiyu nida kanwata zai biyawa.

    “Shikenan Zan rage dubu goma”

    ok shikenan an gode saina jiki

    Shikenan bara na baki number,daidai lokacin Al’ameen ya fito d’akin hannunsa rike da cup inda yasha shaye

    What?? wa nake ganin nan Kamar Muhammad Al’ameen Yusuf bakuwar tace tana zare ido

    A matukar razane har bakin sa na rawa yace kamilaaaaa………..

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯MATAR MAKAHO 🧑‍🦯
    ~ NA ~
    🍃Rukayya ibrahim🍃

    ✨Tsokaci wanna shine novlel na farko Koh da z a ga mistake ko typing error Amin afuwa👌

    Free book🤧

    *🍀wanann shafin sadaukarwa ne gareki haj Aisha Ahmad Allah yabar kaina🍀*

    Page 3️⃣6️⃣&3️⃣7️⃣

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌
    free book 🤧