Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 94-95

Sponsored Links

Page9⃣4⃣&9⃣5⃣
Bayan ta ya rike sosai ga wani irin ciwo da taji a maranta lokaci d’aya ta gigice tana salata tunda take bata taba jin ciwo irin na yau ba, Ambaton Allah kawai take a ranta gabaki d’aya ta had’a gumi, jin wani abu na zuba babu control ya sata tsorata ruwa ne yake dundula, salati ta sake hade da kwalawa khadija kira.

Khadija dake bacci kamar a mafarki taji muryar sumayya mikewa tayi ta nufi ban d’akin da sauri ta bude wazata gani? sumayya ce duke jikinta sai rawa yake gabaki d’aya ta had’a gumi a tsorace take tambayar ta haihuwa ne? sumayya bata samu Amsan bata ba, nuni kawai ta mata ta kira mata mota su tafi asibiti, ba musu khadija tad’au hijab tasa akan kayan baccin jikinta, ta ruga da gudu ta fita a falon, sakatan get in ta zare ta fita bakin kwalta, abinka da dare koh tsuntsu bata samu ba koh ina shuru, kuka ta sa da gudu ta dawo cikin gidan, kofar d’aya makwanciyar su ta wuce tana buga wa, amma basu bude ba gashi kaf gidan babu mai mota koh mijin laila ma ba motar bane dashi.

Haka da dawo sashen su, tana shiga zuwa lokacin jikin sumayya ya kara tsanani sosai koh zama ta kasa har lokacin tana tsungune.

Da sauri ta d’auki wayar ta layin kalamu ta kira, sai da ta masa kusan 4 miss call kafun ya d’aga cikin muryar bacci yake tambayar ta lafiya?

Ai tana sanar dashi da sauri ya mike ya zura jallabiyar sa ya fitoh a d’akin sa, harya tura kofar falon su zai fita saiga nannen sa ta fitoh daga dakin ta, tambayar sa tayi ina zaije a daren nan?

Sanar da ita yayi Auntin khadija ba lafiya tana labour, tambayar sa tayi mijin tafa,Amsa ya bata shidai bai taba ganin mijinta ba, yama ga alamu bata da miji, jin haka yasa nanne d’aukar hijab nata ta sanar da mijinta zasukai sumayya asibiti, suka fitoh tare dashi mota kalamu ya fitar suka shiga sai get insu sumayya, fita nanne dashi sukayi zuwa ciki.

Zuwa lokacin sumayya tayi laushi sosai koh gane wake kanta bazata iyya ba, dayake dare ne nanne da khadija ne suka ririketa yayinda kalamu ya diauki akwatin ta, data jima da shiryashi a zaune, rufe musu kofar yayi suka tafi asibitin da sumayya ke awo.

Suna zuwa aka karbesu nanne na zaune a waje ita da khadija, kalamu keta hidima na sayyan abubuwan da aka bukata koh zama bai samu, har 4 na asuba sumayya haihuwa ya gagara, gabaki d’aya karfin ta ya gama karewa sai da aka kira Assalatu kafun haihuwa yazo gadan gadan, cikin hukunci Allah sumayya ta haifi yaran ta guda biyu wanda koh sanin wani iri ta haifa bata sani ba, tsabar wahalar da tasha, tadai san ta haihu sau biyu, Alluran hutu aka mata bayan an kimtsata a take bacci ya d’auke ta.

******************
Bugu d’aya Al’ameen ya d’auka a take Ammar ke sanar dashi anga wajen da khadija take, suna Abuja.

Ai muhammad baisan lokacin da ya wantsalo daga kan kujeran falo, a take yayi sujjada akan tiles yana wa Allah kirari, goggo da mahmah dake zaune a kasan falo suna cin abinci da sauri suka mike suna tambayar sa lafiya?ai da sauri ya mike ya rungumi mahmah cikin farin ciki yake sanar da ita anga sumayya anga sumayya tana Abuja.

Ai sosai suka nuna farin cikin su goggo harda kuka, a take Muhammad ya fitar da waya ya kira abie ya sanar dashi akan yanzun nan zai tafi gidan su Ammar zasu wuce abuja.

Hanasa Abie yayi yace ya bari sai da safe sai subi fly zai sa a nema musu ticket sai su tafi tare da abie, ai a take goggo ma tace zata mahmah ma tace ita ma, dada dake kusa da abie tace itama baza’ayi ba ita ba, duk yanda abie da muhammad sukayi da tsofinnan su zauna a Taraba, su zasuje su dawo da sumayya amma kememen sukace kafar su kafar su abie, haka ba yanda abie ya iyya duka aka musu booking in fly tare da kiraye kirayen waya har nijar aka sanar dasu an samu wajen da suke, suma sun sanar dasu a cikin satin nan suna zuwa gabaki d’ayan su.

Washe gari tun sassafe suka bar Taraba muhammad koh bacci jiya kasawa yayi, dada ma haka ta watsar da safina tace sai taje taga jikallen ta, Ammar ma tasa Abdul yayi a gaba tare zasu ya nuna musu gidan su kalamu.

Karfe 9 su muhammad suka dira a Abuja, dayake yana da aboki, tun a taraba ya kirasa akan suna zuwa, tarba suka samu daga wajen abokin abie shiyazo ya d’aukesu a Airport, direct gidan su kalamu suka wuce, Amma abin haushi basu sami kowa ba wai Suna asibiti, haka mai ganin ya sanar dasu Alfarman ganin baban kalamu abie ya nema ba musu, mai gadi ya shiga ga sanar dashi, aiko sai gasa bayan sun gaisa ne sukace masa suna son sanin asibitin da kalamu sukaje in ba damuwa.

Ganin girman su da kudin su, gashi kamar ba lafiya ba, hakan yasa baban kalamu yace musu bara ya bisu asibitin, shiga mototi sukayi ya kira nanne ya tambaye ta asibitin da number room nasu, da mamaki yake tambayar ta koh lafiya jin muryar ta ya dishe-dishe alamu dai ba lafiya ba, koh tayi kuka, ya tambaye ta lafiya tace masa ba kome, kashe wayar yayi ya sanar dasu abie ga asibitin da suke.

Suna isa asibitin muhammad da gudu ya ruga bayan sanar dashi block inda suke koh kunyan su abie baiji ba da gudu yayi block in mutane sai kallonsa suke, da sauri sauri ya shiga d’akunan one by one yana dubasu, ana ukun ne ya shiga koh sallama babu ganin mace kwance akan gado ga yara sa’o’in juna zaune rike da jinjiraye a hannayen su, da sauri suma suka juyo jin mutun a d’akin babu sallama.

Ai da sauri khadija ta mike ta kwala ihu yaya!!!!!!!! Da sauri kalamu dake kusa da ita rike da d’ayar babyn da sauri ya cafke wance ke hannun khadija, don saura kad’an ta buga jinjira, da gudu khadija tayi wajen muhammad batayi wata wata ba ta rungumi d’an uwanta tana fashewa da kuka yaya, kaine koh mafarki nake?

Khadija nine nine khadija ina Aunty ki?

Allahu akbar yaya kalli nan tace tana nuna masa kan gadon da sumayya ke kwance har yanzun tana bacci.

Da sauri ya ware idanun sa yana kallon sumayya sai kuma ya juya ya kalli kalamu, ya sake kallon khadija?

Gyada masa kai tayi tana murmushi, shima murmushin yayi sai kuma ga hawaye, tare da matsawa kusa da gadon da sumayya take kwance, dukawa yayi akan gwuwar sa hannu yasa a hankali yana shafa fuskar sumayya, dake kwance sanye da kayan asibiti, tayi kyau tayi fresh irin na masujego, wannan ce sumayyar tawa ashe haka take da kyau masha Allah?

Itace yaya kaga wa’innan jarirai nakane.

Da sauri ya juya yana kallon kalamu da sauri ya mike tsaye hannu yasa ya Amshi babies in yana kallon su, yarane mata masu tsananin kama da junan su tamkar An raba kunu a kofi, gasu masu tsananin kama dashi kome nashine a fuskar yaran, gasu farare tass, rungumarsu yayi ya fashe da kuka.

Toh ragon maza baka da aiki sai kuka, mahmah da suka shigo cikin d’akin tun d’azun, amma basu ma san da su ba.

Da sauri ya nufi mahmah yana ce mata, mahmah kalli yaran nan, wai yarana ne kallesu fa ga sumayya mahmah kyakkyawa fa sosai?
.
Sunkuyar da kai abie yayi yana mamakin surkin nan nasa yau koh dai ya mantasa a wajen ne, shima da sauri ya nufi wajen da yarsa ke kwance, zama yayi a bakin gadon yana shafa gashin kanta daya hargitse koh ribon babu.

Mahmah ce ta karbi baby d’aya dada ma ta karbi d’aya goggo kam baki kawai ta sake tana bin kowa da ido, kalamu kallon babansa yayi dake gefe, ya gaidashi, amsawa yayi yana tambayar sa mai jiki.

Matsawa kusa da abie muhammad yayi ganin sumayya ta fara motse, a hankali ta bude idanunta dalilin kukan da yaranta suka sake dukan su biyu.

Tana bude idanunta bata sauke sa akan kowa ba sai muhamamd dake kanta a tsaye, kamar a mafarki haka ta kalli abin da sauri ta mike zaune har tana kokarin zamowa kasa, da sauri ya tarota, bi a hankali sumayya jikin ki ba kirfi.

Ai jin abinda yace da sauri ta riko hannunsa gam tana kwalama khadija kira, Amsawa khadija tayi da sauri ta karaso wajen”khadija yayanki ke mini gizau na kamasa ”

Aunty ba gizau bane yayane

“Yaya kuma khadija mijina fa baya gani yau kuma naga wannan na gani”?

Aunty ya warke ne.

Ai sumayya najin haka ta sake dariya cikin farin ciki koh damuwa da jikinta batayi ba ta rungume mijinta, don ita sam hankalin ta vaikai wajen mutanen d’akin ba.

Mikewa abie yayi dasu mahmah zasu fita a dakin su basu waje don sukam kunya ne zai kashe su.

Nanne dake toilet tana wanke kayayyakin sumayya daya baci, tun d’azun take jin surutai a d’akin mikewa tayi tsaye da boket na kaya a hannunta ta bude kofar toilet ta fitoh, Wai khadija da kalamu anya kuna da hankali kuwa mara lafiya na bacci kuke surutai da wa……bata karasa ba tayi turus ganin jama’ar dake shirin fita a d’akin dasuka juyo suna kallonta.

Dada ce ta kama salati tana tafa hanneye, wanake ganin nan?

Abie ma da sauri yace Hafsa??

Nanne kam bata wani nuna reaction ba, dayake tun daren jiya data gane sumayya tasan tabbas zata ga su abie, duk da saurin da take tabar asibitin kafun suzo don ita batasan sumayya gudu tayi ba, haka ma batasan itace Aunty khadija ba sai daren jiya.

Nanne bata wani Amsa ba bare ma ta nuna tasan abie, sai tsayuwar da tayi tana kallon sumayya data sake muhamamd tana kallonta sosai irin kallon nan na kewa da soyayya, cikin kuka tace” ummi”?

Sai a wannan karo nanne tayi magana, Na’am momcy?

Da sauri sumayya ta sauka akan gadon tana takawa a hankali cikin dauriya tayi wajen mahaifiyarta fad’awa tayi jikinta tana kuka yau kam ta rasa ina zata sa kanta, murnan samun babies koh murnan ganin mahaifiyarta koh mijinta dole tayi kuka, ummi karan kanta hawaye ne ya cika a idanunta tana shafa kan sumayya ya isa haka momcy yi shuru kinga ba lafiya bane dake koma ki kwanta, tana maganar tana rike da hannun sumayya har ta kaita bakin gadon ta aje ta.

Waini yau hafsa nake gani ne koh gizau idanuna kemin koh mafarki nake ne?

Itace dada Abie yace yana dafe kansa cikin takaici da bakin cikin abubuwan da suka faru a baya.

Mijin hafsa ne yace, Hafsa kin sansu ne daman nina d’auka koh iyayen yarinyar nan ce?

Baban kalamu ne da kakarsa wannan kuma Addansa ce ta nuna sumayya.

Daga sumayya har kalamu da Abie a tare suka jefowa Hafsa tambaya lokaci guda, baban kalamu wani kalamun?

Da sauri abie yace hafsa ban gane ba wanene kalamu.

Nuna masa kalamu tayi dake tsaye cikin shock na abinda nanne tace, yanzun wai sumayya Addansa, ta yaya kamar ya?baigane ba?

“Ummi kina nufin kalamu d’an uwa nane”?

Hafsa kina nufin wannan yaro, yaro nane?

Kallon sumayya da abie hafsa tayi jin tambayar da suka jefo mata, eh kawai tace tana kama hanyar kofa zata fita tare da kallon mijin ta, yauwa Alan guburo mutafi naga dangin ta sunzo zasu zauna a gunta.

Ah ah hafsa zuwan mu bazaisa ki daina hidima da yarki ba.

Ah ah dada zan tafi , Allah ya sauwaka momcy.

“Ameeen ummi in zaki dawo a kawo mini sabulun wanka”

Toh momcy muje kalamu koh zaka zauna ne?

Ah ah nanne muje yace yana kallon abie da mamaki wai wannan ne babansa, shi abin ma yajisa wani banbara kwai.

Kokarin fita a dakin suke a hankali abie ya kama hannun kalamu daya wucesa zai fita a d’akin, kalamu bazaka ma abie magana bane?

Murmushi kalamu yayi sai kuma yaji hawaye ya taro masa, abie ashe kanason na maka magana, shine zaka kyamace ni ka kyautata rayuwar yar uwata, amma ka wofantar da nawa rayuwar ka barwa uwata ni, na zauna a matsayin agola a gidan da, bana ubana ba ya maye gurbinka ina Amfani da sunan sa koh a makaranta, bai taba nunawa duniya bashi ya haifeni ba koni bansan bashine mahaifina ba, sai yau akan me zan maka magana ni bansan wani uba ba sai ……..

“bai karasa ba sumayya ta mike ta wanke sa da mari cikin bacin rai ta soma magana, karka kuskura ka fara abinda zai dame ka wallahi kayi kad’an ka zagar min uba na barka,ni a haka nake son abina koma me zaimin bazan taba kinsa ba” sai kuma ta kama kuka.

Da sauri nurses dake falo suka shigo d’akin, akan surutun dake tashi, hakuri aka basu akan za’a kiyaye magana ne mai muhimmanci ake, ganin kalarsu yasa su barinsu a dakin.

Daker aka samu suka sassanta nanne ta koma gida dasu goggo yayinda mazan kuma suka koma hotel sumayya ma ita da dada kadai aka bari a hospital.

Washe gari aka sallame ta saboda kyaun da jikinta yayi, don haihuwar duk da yazo da gardama amma tana haihuwa shikenan.

Gidan nanne aka maidata bata koma gidan hayansu ba,sosai ake kula da ita muhamamd a rana sai yazo sama da sau hudu, sai da sumayya ta kwana hudu da haihuwa kafun suka koma shirye shiryen dawowa jalingo don anan ake son yin taron suna gashi yan nijar ma sunce suna shirin zuwa, duk yanda sukayi ta rokon nanne ta biyosu taki tace bazataki bin umurnin mahaifinta ba na raba kanta da zuriyar shugaba, saida mijinta ya nuna bacin ransa da nuna mata yaranta nada hakki akan ta, sannan kalamu bazaiji dadin hakan ba tunda shima so yake yaje yaga dangin babansa, daker dai ta Amince washe gari da sumayya ta cika kwanan biyar sukabi jirgi saijalingo.

Muhammad murza idanunsa yayi yace a gidan sa da babansa ya sai masa a Amazon sumayya zata sauka, ba musu duk da abie yaso ta koma gida Amma ganin hafsa da Al’ameen basason hakan.

Gidan sumayya ta sauka dayake babban gidane ga d’akuna shiyasa gidan ya d’auke su, duka harda su hafsa falmata su babayo muhamamd goggo dasu mahmah, kalamu kam shugaba family house ya sauka kuma ba karamin farin cikin ganinsa sukayi ba.

Babu inda haihuwar sumayya bai bazu ba jama’a sai tururuwan zuwa dubata suke harda yan Abuja laila ma daga adamawa ta gangaro, a ranan yan nijar suka diro nageria gabaki d’aya yan uwan yusuf ne harda shi karan kansa ma, wannan zuwa harda lawiza da nabila, sosai gidan ya dad’a cika da yan uwa kota ina yan gidan shugaba ma tun a washe gari suna matan suka diro, yusuf a gidan sarki ya sauka dayake suma ana gobe suna suka zo, kai sumayya taga jama’a iyya jama’a ga wani irin lalle da aka watsa mata mai masifar kyau da ketson suna duka.

Yau take suna yara sunci suna NA’IMA da NA’IFA , tun Asuba yan gidan Adara suka diro su inna asabe inna lami Ana gindin murhu a sauke wanshan a d’aura wanshan, shanu uku aka yanka da rago biyu, duk suna ta kan gyaran nama, ga abinci kala kala, gashi koh ina ka leka zakaga group group na mata kowa da angon su mai zafi, wanda abie ya d’auki nauyi duka, yan nijar nasu da ban haka dangin adara, yan shugaba family house ga yan gembu, ashan gefe naga MATAR MAKAHO FAN’S ansha anko na Atamfa mai ratsen flower green ana zazzaune ana dirkan shinkafa a manyan tireruka hhhhh.

Sumayya dake sanye da wani hadedden material gown wanda yasha dinki ga sarka na d’anyen gwal da sarki ya bada aka kawo mata, sarkane da dankunne sai warwaro ga agogo mai zafi na mata duka, tasha heavy make-up sai d’aukan hotuna suke da kannen Ammar dake sanye da Ankon su, khadija da kalamu dake zaune a gefe suna cin shinkafa.

Muhammad da Ammar harda su ramadan zulkiflu gidado badaru duk yanzun sun chanja kamar basu ba, suna zazzaune a kofar gida a rumfar da aka kakkafa abinci suke ci mairai da lafiya.

Tun daga nesa suke jin ihun yara da mutane suna rugawa a guje, da sauri suka mike gabaki d’ayansu suna kallon abinda ke faruwa.

Mutum suka gani kamar mace ne koh na miji bazasu gane ba, kadangaru manne a jikin sa tana gudu suna binsa wasu na jikin ginin unguwan suna rugowa suna binta sosai kota ina kadangaru ga wasu runduna na binta a baya, sai wata mata dake gefenta rike da sharbebeyar bulala tana kad’a mai kadangarun suna tafiya a haka.

Da sauri su muhammad suka ruga cikin gida da gudu har ana rige rige, ganin wajen da suke suka nufo.

Suna shiga suka rufe kofar gidan da karfi suna ji sai bugawa matar take akan don Allah abude mata, kiri kiri su muhammad sukaki budewa har abin yaja hankalin matan dake compound sosai, dada dake rike da jinjira zata kaiwa kawayen ta dake falo a zaune ssga dayar, itace taji hayaniya aje jinjiran tayi ta fitoh compound, ganin su muahmamd da jama’ar tsakar gidan a tsaye yasata karasawa bakin get in tana tambayar dalili, kafun ma su muhammad suyi mata bayani tuni tasa hannu ta zare sakatar get in, ihu Ramadan ya sake tsabar rikita yare ma ya fara.

Dada na budewa idanunta ya sauka akan matar dake rike da bulala kwalalo ido tayi cikin mamaki tace wanake gani anan kamar Nafi………….

kafun ma ta karasa maganar ta idanunta ya sauka akan wance ke tsaye mammanne da kadangaru ga bataliya a kasa, ai ihu dada tasa ta ruga ciki da gudu, da sauri inna lami tazo zata rufe get aida sauri wannan matar ta banke kofar ta kora mai kadangaru ta shigo, itama shigowa tayi, ai ana ganinta, ihu ne yake tashi abinka da mata atake masu Aljanu Aljanunsu ya soma tashi, gidan suna gabaki d’aya ya rikice ya zama gidan tsere kowa gudu yake yana burmuwa falo wasu kitchen masu Aljanu kam sun zuzzube…………..

✨Ruqeenjalal✨🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

Back to top button