Author: Novels

  • Matar Makaho 32-33

    Matar Makaho 32-33

    Page3️⃣2️⃣&3️⃣3️⃣
    Keke napep na sayar ban kulasa ba

    Hajiya Ina Zaki?Mai napep in ya tambaye Sumayya.

    “MEGA restaurant” na basa Amsa

    Ok hau muje

    Sumayya restaurant Kuma?Koh dai banji daidai bane? Al’ameen ya tambaye ta

    “Daidai kaji,yau agun zamuci abincin dare,banyi girki ba”

    Sumayya ai akwai wajen Saida abinci Koh round about ana sai dawa basai munje restaurant ba.

    “Nidai gun zamu Kuma sai kaje”

    Wai hajiya bazaku hau bane? Koh nayi tafiya tane? ,kun tsaidani Kuna Bata mini lokaci ga dare nayi

    “Yi Hakuri.
    yayan Khadija muje” nace Ina Kama hannunsa muka shiga keken

    A MEGA restaurant, Mai keke ya saukesu

    Biyansa nayi kudinsa bayan mun sauka,Kama hannunsa nayi muka shiga ciki,

    Al’ameen Kam binta kawai yake baida baki ,sai dai yaji sun shiga wani waje Mai mugun sanyi sai Kuma D’an motsen jama’a d’aid’ai ku

    Har lokacin Ina rike da hannunsa,D’aya daga cikin kujerun dinning table dake wajen,na nufa ja Masa kujera nayi”ka zauna”nace Ina zama a nawa kujeran

    Ok , yanzun cikin inda muke nan shine restaurant in? ya tambaye ta Yana zama

    “Eh Mana Hala baka taba zuwa ba”?

    Nasan restaurant Amma bana shiga.

    “Toh yau ka shiga”

    Waiter ne yazo, sannunku da zuwa mega restaurant,ga list nan ka duba abinda za’a kawo muku,yafada Yana mikawa Al’ameen Takardan hannunsa

    “Yauwa bani Anan”nace Ina karban list in.
    “Me za’a kawo maka”?

    Duk abinda kike so, Al’ameen ya Bata Amsa

    “Tamabyar ka fa nayi”

    Amsa na b’aki

    “Ok toh a kawo maka tuwo Koh shinkafa Koh doya”?

    Aban doya

    Ok,mikawa waiter in nayi hade da basa amsa”ka kawo plate biyu D’aya na doya da miyar kaza,D’aya Kuma fried rice with chicken yaji vegetable sosai,in Kuna da exotic a had’a mana da ruwa”

    Ok ma, an gama,ya karbi takardan in ya wuce

    Sosai mutanen restaurant in suka bisu da ido tun shigarsu kowa yake gulman su da ido wasu Kam har kasa hakuri sukaye sunayi da baki,abin mamaki ya Basu ganin matsiyacin MAKAHO Koh suturar arziki Babu a jikinsa,mace Kamar Sumayya tana rike da hannunsa Koh tantama Babu daga ka gansu kasan ma’aurata ne,Amma kallo D’aya zakama Sumayya kasan ba karamar classic bane

    Bayan an kawo Mana abincin,tura Masa nayi nasa a gabansa shukali na Mika Masa”ungo shukalinka abinci na gaban ka”

    Abinci muka faraci a nitse idon mutane na Kan mu sosai har abin ya takurani

    Sumayya!!

    “Na’am”

    Nikam wajen nan akwai mutane sosai ne?

    “Eh akwai Amma ba sosai ba kasan yanzun dare ne”

    Amma dai kallon mu suke koh?

    Mamakine ya kamani Amma na maze, “ah ah ba Wanda ke kallon mu kowa harkar gabansa yake,Amma meyasa ka tambaya”

    Jikina ya bani ana kallo nane tunda muka shigon nan

    “Aiko ba Wanda ke kallon mu”,na basa amsa

    Taima ke kike kallona.

    “Akan me Zan kalleka Kuma”😒?

    Waya sani Koh kyau na Miki,Kinga dogon hanci

    “Ina abin yake bare a yabasa”

    Abinci muke ci muna Hira har muka Gama Amma dukan mu bamu cinye duka ba,
    list aka akawo mana,na duba kudin mu dubu 3,800 ne, bude Purse nayi nabiya kudin, ordern ice cream nayi aka Mana takeaway a laida

    Mamakine ya Kama Al’ameen yanzun abincin da sukacin nan shine 3800 ,ai cefenen dubu uku da dari takwas zai musu wata ma suna dafawa.

    Suna fitowa a restaurant in ganin titi ba napep yasa Sumayya duba wayar ta

    Karfe 10:3 na dare ne,”asaifa mun jima a wajen nan 8 fa Muka bar gida”

    Gaskiya Kam Kuma bana majin dirin machine sai mototi

    “Ba machine Kam sai dai mu taka da kafa”na basa amsa Ina Kama hannunsa muna tafiya inda Allah ya somu ma tsakanin sintali da mega ba nisa sosai

    “Nikam azumi saura wata nawane”?

    Saura sati nawa dai?ya Bata Amsa

    “Satitika kenan baikai wata ba?Ashe shiyasa aketa aure aure”

    Gaskiya Kam saura sati uku da kwana hudu

    Lalle kam,”kasan yanzun haka gobe, za’a yi bud’an kan Amarya da yamma,sai ayi fitan Angonci duka,da dare Kuma dinner,Kuma nice duka Zan musu kwalliya, shiyasa nake son in Allah ya kaimu gobe sai ka nemo mini yaro yaje Mana kasuwa Ina son Gama girki da wure”

    Yaro Kuma wani yaro.kike ga Zan iyya aika a unguwan mun nan har kasuwa ,sai dai naje kawai tunda khadija ba lfy.

    “Toh Allah ya kaimu,ni chemist ma nakeson mu shiga nasai maganin gajiya,Amma dare yayi”

    Ah ah Sumayya da kankantan shikarunki karki Bata shi dashan maganguna, don kina aikin gajiya,in Kika riga Kika saba,toh zai biki Koh yaushe kikaye aiki sai kinsha

    “Gaskiya ne Amma wallahih bayana ya tokare ni sosai,gashi yanzun ma sai tafiya muke da kafa”

    Da kafa suka taka har sintali suna tafiya suna Hira,Dayake gidan Adara ba’a rufesa Koh karfe d’ayan dare ne yasa suka samu kofa a bude,

    Shigan su, suka shige shashen su bakin su d’auke da sallama

    Al’ameen ne ya bude d’akin

    Muna isa ruwa na iba duk yanda nake tsoron toilet in dare yayi Amma zafin da nakeji Bai barni naji tsoron ba,
    band’akin na shiga na kwara ruwan na fito,
    d’akin na shiga.

    Al’ameen na zaune a Kan kujera Yana jiran Sumayya ta fito shima ya shiga Wanka don yaukam ba NEPA an d’auke

    “Assalamu alaikum”nace Ina shigowa d’akin

    Waalaikumu salam, gaskiya yau Kam Alhamdulillah akwai.zafi Kam

    “Gaskiya ni a waje ma zanyi shimfid’a yanzun”

    Ok.bara nayi wanka daidai kinyi shimfid’ar?yace Yana fita a d’akin ban d’aki ya shiga bayan ya ibi ruwan shima

    Yayan khadija na fita na saka.kayana saboda zafin da ake have vest na saka ,da wandon bacci fankalele shara shara har kasa,kayan shinfid’a na fitar na shinfid’a mana darduma a baranda na shinfid’a zanin gado da filoluka, kwanciya nayi a gefe tsabar gajiya Koh hula ban saka ba,bayana sai damuna yake koh bacci na kasa.

    Yana fitowa d’akin ya shiga 3quiter yasa Koh riga baisa ba ya rufe kofar, ya nufi inda yake kyautata zaton agun ta musu shimfid’a

    Ina kwance Ina kallonsa harya matso inda nake kwance hannu yasa ya tattaba shimfid’ar sai Kuma ya fara laluben Kan shinfid’ar bayan ya xauna.

    Jin ya tabata yasashe Hawa Kan shinfidar kwanciya yayi a Gefen pillow n da ta d’aura kanta akai

    “Bakaji pillow da na aje maka bane”

    Naji Mana Amma a naki nakeson kwanciya

    “Kaga ka rabu Dani jikina ciwo yake mini”

    Hannu kawai naji yasa a bayana Yana mammatsa mini baya,naso hanasa amma Jin yanda message in ke kauda tsamin da bayana yake mini yasa nayi Shuru

    Yana ta mamatse Mata baya da kafa duka har yaji tayi bacci, gyara Mata kwanciya yayi,daga kefuwarda tayi shima ya kwanta a Gefen ta bacci ya d’aukesa.

    Misalin karfe biyu na dare ya farka Jin iska na kad’awa ga kamshin kasa na tashi bude ido yayi sosai, ya mike zaune hannu yasa ya taba Sumayya Aiko tana kwance Koh juyawa Bata sake ba tun gyarata da yayi, Sumayya!! Sumayya!!

    “Ummmm menene”nace cikin magagin bacci don harga Allah yau dai baccin gajiya nake

    Ana iska ga hadari,ki tashi mu shiga d’aki

    “Da wani idon kaga hadarin ni wallahih ka barni nayi bacci”,na fada Ina gyara kwanciya

    Sumayya ruwane fa da gaske

    Shuru na Masa abina na koma bacci

    Jin Taki tashi yasa ya mike key ya d’auka ya bude d’akin, d’aukarta yayi a hannu a hankali yake tafiya Yana lalube harya shiga da ita d’akin,Kan gado ya haura ya kwantar da ita,Jin an Soma yayafi da sauri ya fitoh a d’akin shimfid’ar su ya tattara ya Kai d’aki randar robansu ya zubar da ruwan ya hada da bokataye ya jejjera a bakin baranda,daidai lokacin aka fara ruwa sosai Kamar me .

    Alwala yayi ya shiga d’akin sallaya ya d’auka ya shimfid’a wa yayi ya Tada kabbara,lafilfilu yake har kusan karfe uku na dare kafun ya kwanta shima a gefenta

    *Washe gari*
    Kamar kullum yaukam da safe kudi na basa yasai Mana manya manyan gongomin Madara da bornviter na sai suga Rabin kwano Lipton kwali d’aya na had’a da cornflakes,dashi muka karya ya fita

    Al’ameen kam yasan baida abinda zaiyi haka ya fita yaje ya zauna a bakin titi ya rasa mafita Allah ya gani Yana iyya bakin kokarinsa wajen niman abinda zai rufawa kansa asiri,Amma abin yaki yasan kome na Allah ne Kuma Bai manta dashi ba a hakan ma yana kara godewa Allah tunda Sumayya nada rufin asiri da ace Bata sana’a a war yanzun da kayan abincin ta ya fara karewa baisan yanda zaiyi ba.

    ***********
    Khadija ce ta shigo bayan sallan azahar lokacin Ina kanwa matan da suka zo make-up, Assalamu alaikum

    “Waalaikumu salam” dukan mu muka amsa Mata

    “Ah ah khadin Goggo idonki kenan”?nace Ina kallonta sanye take da atamfar dana Bata riga da zani sai gyle da takalmi harda jaka sai laida Mai tambarin asibiti a hannunta sosai tayi kyau fuskarta tayi fayau alamu dai batajin dadi,abinka da farin fata

    Wallahih Aunty na fitoh asibitine nace bara dai nashigo yau Goggo takece mini kun shigo da dare Ina bacci.

    “Eh wallahih mun shigo da yayanki nace abarki kawai kar a tasheki”

    Allah sarki,tace tana gaida matan dake zazaune suna jiran na Gama wa Wanda
    nakema make-up

    “Khadija ki shiga d’aki Mana akwai NEPA ki jona kittle akwai kayan shayi asaman freezer”

    Aunty bazan iyya shaba bakina ba dadi Sam shiyasa koh abincin dare ban iyya ciba Haka karyawa ma.

    Ah ah khadija dadai kin daure kinsha shayin Daya fi Amma ace bakinki ba Dadi saiki kicin abinci,ai ko magani in ba abinci baya aiki,D’aya daga cikin customers nawa ta fad’a

    “Gaskiya ne khadija,ki shiga in kinsha saiki kwanta ki huta”

    Toh Aunty tace tana shiga d’akin, kittle in ta d’auko ta zuba ruwa ta jona,shayi ta hada kad’an ta iyya Sha ta balle maganin Tasha kwanciya taye lokaci D’aya bacci ya d’auke ta

    Sai kusan 4:30 na Kamala wa sauran kwalliyansu Daman Amarya tun 3 na yamma na Gama Mata saboda bud’an Kai,

    Gaskiya yau na damki rabona mutane kusan goma nama makeup heavy make-up
    Simple make-up
    Light make-up
    Duk yau ba Wanda banyi ba sosai na samu kudi 50k yau na damka nan ma banyi na dinner ba kenan.

    Misalin karfe biyar khadija ta mike zata wuce gida Aunty nikam Zan wuce sai gobe

    “Toh khadija Allah ya Kara lafiya ga wannan ki D’an samu abinda kike bukata ki Saya dashi” nace Ina Mika Mata 10k

    Aunty ki barshi kawai d’awainiyar tayi yawa jiyama fa Goggo tace mini kun kawo Mana 5k naje asibiti danaje in ma,Ina saurayin da nace Miki yazo guna?

    “Eh na tuna har kikace bazaki fita ba”na Bata Amsa

    Ashe Dr ne Ina zuwa na gansa shine ya sayo mini magani kyauta,

    “Allah sarki, Allah ya saka Masa da alkhari”

    Ameen Aunty

    “Wancan yayan kine ya baki wannan Kuma nawane,ki karba khadija kid’an Saya Abubuwan da baki dasu”

    Gaskiya Aunty nagode Allah ya saka da alkhari,tasa hannu ta karbi kudin

    “Ameen khadija”

    Yauwa aunty nace Koh Zaki aje mini tunda Naga azumi ya kusa Inna tashi zuwa kasuwa saina karba naje na sai kaya,samun na samu dinki da wure?

    “Ah ah khadija insha Allah, Allah zai Bud’a Mana har yayanki ya sai Miki kayan Sallah, wannan dai ki sai Abubuwan bukata irinsu kananan Kaya da mayuka Turare pad omo sabulu ke dai irin Abubuwan bukatar Yan Mata haka”

    Toh shikinan Aunty Daman bani da kananan Kaya sai na saya pant biyu Brz sai vest shima biyu Amma na gwanjo Zan Saya aunty sauran chanjen, Ina materials da ake yayi yanzun ana yankawa a dinka dogayen riguna dasu?

    “Eh khadija”na gane su

    Yauwa yadi d’aya dari uku su Zan Saya kala biyar na dinka

    “Gaskiya khadija kinye tunani Mai kyau kema saiki samu na chanjawa kwana biyu”

    Toh Aunty Zan tafi nagode Allah ya Karo customers

    “Ameen khadija yanzun ma wasu na zuwa da dare maganar dinner aike alkhari ce tunda sanadin ki nake samun kudin”

    Ah ah Aunty Allah ne ya tsaga da rabonki , shiyasa kike ci

    “Hakane Kam khadija” nace Ina shiga kitchen da sauri nake na d’aura Mana abincin da zamuci

    Bayan fitar khadija girki na Gama na juye Mana a kula,sai goshin mangari ba yayan Khadija ya dawo

    Sumayya sannu da gida?

    “Yauwa sannu yayan Khadija sai yanzun”

    Eh wallahih ya aiki?

    “Lafiya klau” nace Ina kallon sa ganin Kamar a cikin damuwa yake

    D’azun Bashir wani makwancin mu ke tambaya ta Wai MATAR sace taji labarin Wai kina lalle ke kikama Asma’u na aure shine Wai yake tambaya ta zata samu lalle gobe,make-up jibi da Rana?
    nace ya bari saina tambaye ki inyaso in mun hadu a masallaci anjima na fad’a Masa amsar ki.

    “Lallen me za’a ma MATAR tasa”?

    Suna ne haihuwa tayi jibi suna

    “Gaskiya nifa bazanje home service ba,in mutum nason lalle Koh kwalliya yazo ya same ni a gidana”

    Amfa Sumayya haihuwa ne ya za’a yi mace maijego tazo lalle gidanki?

    “Wallahih yayan Khadija ni raini ne banaso a rayuwa na kar mutun yaga kaje Masa lalle ya Raina ka”

    Kai Sumayya ba wani raini ai sana’a ce ta kaiki ba maula ba,ki daure kije ki Mata kinji?

    “Shikenan Allah ya kaimu goben Amma bansan gidansu ba da yamma ta tura yaro yazo ya kaini”

    Sumayya har yamma?ya tambaye ta

    “Eh man saina Gama aikina,Koh so kake na tafi da safene,jibine fa sunan”

    Toh shikenan Allah ya kaimu yace Yana mikewa ,ruwa ya ibo a boket ya shiga bandaki

    Muna idar da sallan mangariba Koh abinci bamu ciba Yan make-up na dinner suka zo su biyar ne dukansu harda Amarya heavy make-up suke so,Dole tasa na hakura dacin nawa zuba Masa nayi na d’auko Masa ruwa a freezer na jira Masa,a d’aki na fitoh waje,don ni bana saka baki a dakina Sam kowa ya zauna a waje kawai

    Sai da yaye isha’i kafun ya shigo gidan, gaisawa sukaye da customers nawa,don na fahimci yanzun mutane na ganin kirmansa tunda kofarsa suka shigo

    “Abincin ka na d’aki yayan Khadija”nace Masa ganin ya nufi d’akin kar yaje ya zubar da abincin tunda a kasa na jira.

    Toh yace Mata Yana shiga d’akin

    Make-up na Amarya na fara, Gamawa ta biyani akazo aka d’auketa saura hudun ma duk na Gama musu kafun 9:00,kudin da suka bani 25k Inna hada Dana d’azun kusan dubu saba’in na samu kenan Alhamdulillah yau kawai na tashi da kudi dubu sittin da biyar in aka cire 10k Dana bawa khadija

    Wani tunanine ya fado mini akan kudin, murmushi kawai nayi na nufi d’akin
    Ina bude labulin idona ya sauka Akan plate inda nasama yayan Khadija abinci nakai dubana garesa da mamaki ganinsa a…………..

     

    *My Real and special Fan’S*

    *Princess* 🏵️
    *Maryam najibu* 🏵️
    *Mummy*🏵️
    *Shamsiyya Gombe* 🏵️
    *Ummu na’eem*🏵️
    *Faeexetion* 🏵️
    *Zainab*🏵️
    *Bebi* 🏵️
    *Maman khairat*🏵️
    *Oum Abdullahi*🏵️
    *UMSAD INCENSE* 🏵️
    *Ummul husnah*🏵️

    *Duk Naga comments naku Allah ya bar kauna Nima Ina yinku* 🏵️🏵️

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

    🍀 *Wannan shafin sadaukarwa ne gareki haj j Aisha Ahmad Allah yabar kauna* 🍀

  • Matar Makaho 30-31

    Matar Makaho 30-31

    Page3️⃣0️⃣&3️⃣1️⃣
    Ji kawai nayi ya rumgume ni ta baya,
    zare ido nayi jinsa shima ba riga,mannani yayi da jikin kofar shi koma ya rumgume ni sosai ya d’aura kansa a kafad’ata

    “Wai menene haka don Allah” ?

    Dadi ne,ya Bata Amsa

    “Dad’au matau”

    Jin Amsar da ta Bashi yasa ya juyo da ita da karbi ya rungume ta

    Ware ido nayi jina sukutum a kirjinsa dukan mu ba riga

    “Wayyo Allah meye haka”

    Mele,shima ya Rama

    “Nikam.ka sakeni”

    Bakinsu ya hada,a hankali yake kissing in lips nata na sama

    Bansan garin Yaya ba Koh yaushe ba na tsinci kaina da Kama lips nashi na kasa Nima na shiga tsotsa

    Jin ta Kama Masa lips yasa a hankali ya zame bakinsa cikin nata,ai da sauri yaji ta kamo kansa ta sake maisa bakinsa cikin nata

    Sosai suka shiga farantawa junan su Rai ,

    ba zatoh Koh tsammani muka zube a kasan cafet,nice a sama shi koma a kasa,

    da sauri ya birkitota kasa Yana lalube da D’an kokarinsa zai zame Mata wandon baccin da ke jikinta

    Da sauri na Kama hannunsa Jin aika aikan da yake so yayi

    Don Allah ki bari musamu nutsuwa

    “Nidai wallahih ah ah”

    Please kinji

    Kokarin mikewa na fara a jikinsa,

    Da sauri ya kamota,Ina Zaki

    “Anafa Kiran sallah”

    Sakinta yayi Jin da gaske Kiran Assalatu ake

    Mikewa nayi a hankali daga jikinsa Jin ya sake ni,”d’akin ba haske fa”

    Ki kunna glop Mana

    “Bana gani”

    Ok bara na lalubo glop in

    “Toh,Ina rigana”?

    Bara na kunna wutan sai ki duba,yace Yana mikewa daga kasan cafet

    Mikewa yayi Yana lalube ya Isa wajen makunnen NEPA ya kunna

    D’akin ya gauraye da haske,da sauri na rufe kirjina da hannu sai koma nayi tsaki tunawa da nayi bama gani yake ba

    Menene kike tsaki kuma?

    “Banga rigana ba”

    Riga Koh vest?

    “Oho”

    Wai kikam wace irin matane Mai tsewa

    “Green in Mata ka aura”

    Toh Green Sumayya,mu fita kar ashiga sallah?

    “Kai ka fita Mana Koh na d’aureka ne”

    Toh Green sumy

    Lalle mutumin nan ya Raina mini wayo,ji kawai nayi ya kamo mini hannu Yana kokarin fita Dani a d’akin cikin lalube

    “Ban saka rigaba ka sakeni Mana pls”

    Sakin ta yayi Jin Wai Bata da rigan da gaske

    Bayan fitar shi rigana na d’auka na fitoh Jin harya kammala Alwala ya wuce masallaci

    Bayan idar da sallah dukan mu bacci muka koma

    Misalin karfe 7:00 na safe aka doka Mana sallama a kofar d’aki,bude ido nayi a hankali ganin Yana kokarin sauka a gadon yasa na gyara kwanciya

    Amsa musu yayi ya zura jallabiyar sa ya fitoh,

    Ina kwana yayan Khadija?

    Lafiya Alhamdulillah

    Gun Aunty Sumayya mukazo,Yan matan sukace

    Ok,bara na kirata yace Yana komawa d’akin

    Hawa gadon yayi,ya yaye blanket inda ta rufu

    “Menene”?

    Baki kikaye,Kamar Yan lallen ne fa

    “Gaskiya bazan tashi ba suje su dawo anjima”

    Ah ah Sumayya wulakanci ba kyau ki lallaba dai ki tashi kinji Green sumy

    “Wallahih Inka sake fad’amin sunan nan Mai rabani da Kai sai Allah”

    Me Zaki mini ai Babu abinda Zaki mini sai abinda Allah yaso

    “Hmm” kawai nace na mike,fitowa nayi na shimfid’a musu darduma muka gaisa Yan matane guda biyu Amma ba kawaye bane,
    “ban fa Saya lalle jiya ba bansamu D’an aika ba gashi 8:00 ake bude kasuwa Koh zaku karba kuje ku sayo”?

    Eh Daman mu biyu mukace bara muzo kafun a Gama Mana kafun sauran su karaso,ba damuwa a bamu kudin bara muje mu sayo in

    “Ok bara na kawo muku kudin”dakin na shiga na d’auko musu kudin,suna fita wanka nayi na kimtsa kofata yayan Khadija ya ibo Mana ruwa,

    Shinkafa da wake dafa duka na dafa Mana direct harda na Rana

    Bayan mun karya fita yayi, ni Kuma muka fara lalle,
    Sai kusan 3 na karasawa matan lallen su dukansu su bakwai kowa hannu hannu na Masa ja da baki,sai kwalliyar walima

    Gaskiya yauma ba laifi na damka kudi Mai tsoka sosai..

    Naso.muyi cefene Amma yau khadija batazo ba ni koma ba fita nake ba bare na aiki yaro

    Yayan Khadija Kam Yana fita yaje ya bude mangoron sa duk sun rube haka ya zubar dasu don Koh ya bude ba Saya za’a yi ba haka yayita zama har yamma don yasan tabbas Sumayya zata sama musu na abinci Amma yanajin kunya ace kullum ita ke ciyar dashi

    Haka yayita zama sai mangari ba ya mike bayan yaje masallaci ya kamo hanyar gida jiki a sabule

    Bayan sallar mangari ba ruwa na Ina na shiga wanka

    Yana shiga gidan da sallama ya shigo kofar Jin shuru Bata Amsa ba ya zata Koh tana d’aki ne,ruwa ya Iba ya shiga ban d’akin

    Goga soso nake a zaune kawai naji mutum ya shigo bayan gidan

    A matukar tsorace na kwana Kara,”wayyooo”

    Shikam zuciya D’aya ya shiga bandakin Bai d’auka tana ciki ba shiyasa ihun yazo Masa unexpected,yasa ya gigice, Sam Bai d’auka dalilin shigarsa bane yasata ihun,d’auka yayi Koh wani mummunan abune ya same ta

    Subhanallah Sumayya lafiya? yade?
    yace Yana matsowa inda yaji ihun nata

    “Wallahih Inka zo inda nake saina kwara maka ruwan nan”,nace cikin tsawa Ina d’aukar bokatin ruwan wanka na in,damuwa na kawai na ja towel inda na makala a saman kofar band’akin,na d’aura

    Sai yanzun ya gane dalilin ihun nata,manna Mata hauka kawai yayi ya Kama cire riga

    “Wallahi ka fita a toilet innan na ratse Zan kwara maka ruwan nan”,duk tabi ta rikice

    Ikon Allah waini idone Dani bare na kalli abinda kike boye wan

    Kuturu,kawai nace,Ina daga boket in ruwan ganin Yana matsowa inda nake

    Jii kawai yayi shaaaaaaaa Sumayya ta kwarara Masa ruwa,Bai d’auka da gaske take zata kwara Masa ruwan ba,

    Nikam ganin Yana ta faman sharte ruwan fuskar sa yasa,na ruga zanyi waje da gudu Koh Kaya bansa ba ,

    Ai.jin gudunta yasa ya bita shima da gudun

    Ina kokarin fita a band’akin kawai naji ya jawoni ciki, Allah yasa Ina kusa ta towel jawosa nayi a hannusa

    Wallahih Sumayya baki Isa ba ki kwaramin ruwa Kuma ki.gudu

    Ganin fa na shiga hannu,inda Allah yasoni ma na d’aura towel in”don Allah kayi hakuri yayan Khadija kuskure ne”

    Kuskure ai baki isaba kinji na rantse

    Kuka na fara ganinsa in yaci serious,Babu Wasa a fuskarsa da gaske yake b barina zaiyi naci bulus ba
    “To Kayi hakuri”

    Naki,ke Inna Miki Abu ai baki hakura

    “Wallahih inayi kaji yayan khadija”

    Bazanfa hakura ba malama

    To me koma Zan maka Koh dukana zakayi ne?

    Ah ah wanka Zaki mini

    “Wanka”😳?

    Eh Kinga Daman ba gani nake ba kullum.bayana baya fita

    “Nima ai bana ganin bayana kuma ni ban iyya ma manya wanka ba”

    Ah ah kina kallo Mana,Kuma Zaki koya

    “Wallahih ni banason irin abinnan, nace maka ka sakeni kanaji fa ana Kiran isha’i Kuma sai magana kake sani a bayan gida kasan ba kyau fa”

    Tsakanin nida ke waya fara magana a ban d’akin nan tunda ba idone Dani ba, ba kallo Miki abin zanyi ba me na ihu harda kwara mini ruwa🤥

    “Toh kayi hakuri kaji yayan Khadija wallahih mantawa nayi baka kallo”

    Da gaske kina mantawa bana gani?

    “Eh sosai ma,ai ba kowa.ke.ganinka yasan baka kallo ba”nace don ya barni

    Ok wayo Zaki mini kenan harda wani yabona toh naki wayon in Kinga na barki kin fita toh kin zabi Daya a cikin ukun nan,
    Koh ki wanke mini baya
    Koh ki wanke mini Kai
    Koh ki haske mini gemu

    Lallai mutumin nan yaga wajen baccina nice ma Zan wanke Masa baya Kai Koh aski,

    Toh Zan maka aski Amma sai gobe kasan yanzun dare ne bazaiyi kyau ba gashi ba NEPA Kai Kuma bakada shaver”

    Kinyi Alkawari Zaki aske mini gobe?

    “Eh”

    Toh wanke mini

    “Toh,ka sake mini hannu Mana saika zauna na wanke maka”

    Na sakeki ki gudu

    “Allah bazan gudu ba”

    Ban yarda ba

    Yace Yana Jan hannuta,ya zauna akan kujiran hannunsa na rike da nata

    “Toh a hakan Zan wanke maka Kai kana rike da hannuna”

    Ai Inna sakeki nasan guduwa zakiye

    “Allah bazan guduba”

    Toh tunda kikace Allah na sakeki,yace Yana sake Mata hannu

    “Ina abin wanke Kai in”?

    Gashe yace Yasa hannu a k’wandon soson nasa ya d’auko guntun soda,gashi nan

    “Kana nufin da soda Zan wanke maka Kai”?

    Eh man ba Yana kunfa da cire datti ba

    “Uhmm Ina zuwa”,nace Ina kokarin nufar kofar band’akin

    Kinye alkawari fa Zaki wanke mini,shine kike son gudu

    “Abu Zan d’auko na dawo”

    Toh yace Yana kokarin cire jikekken rigansa

    Ina fita a band’akin na shiga d’aki bude akwatina nayi na d’auko Abubuwan wanke gashi, na Mata masu kyau da shaver,na dawo ban d’akin wayata na kunna na jinginasa da jikin gini matsowa nayi inda yake zaune daga shi Sai wando dogo na jeans

    Rangwafawa nayi na fara wanke Masa gashinsa sosai na zuzzuba Masa Abubuwan wanke Kai gashinsa mai yawa irin na Fulani,sosai ya fita nasa Masa Abubuwan laushin gashi cikin Yan minutes gashinsa yayi masifar kyau, shaver da na d’auko na saka Masa a fuska zan aske Masa gemu

    Ke sumayya ragewa fa zakiye ba askewa ba

    “Na sani ai”nace Ina gyara Masa gashin gemun

    Ina Gamawa nace NASA”ka duba Koh yayi”

    Ina Naga idon dubawa sai dai na taba,ya Bata Amsa Yana tana fuskar sa, gaskiya kin iyya gyaran fuska

    “Uhmm kasan me”?

    ah ah saikin fada

    “Ai…….ban karasa ba Jin ana kokarin shiga masallaci sallan isha’i yasa ban karasa maganar da nakeson Yi ba,
    “kaYi sauri ka kwara ruwa ana shiga sallah”Ina maganar na fita a band’akin

    Jin fitarta yayi wanka shap shap ya tafi masallaci

    Yana fita ruwan wanka na Kuma ibo wa na Shiga band’aki,Ina wanka inata tunanin shin yau meke damuna ne Abubuwan da suka faru sai bani mamaki suke

    Ina fita na shiga d’aki bayan nayi Alwala sallan nayi na kwanta akan kujira don yau ba karamin gajiya nayi ba don Koh girkin dare bansamu nayi ba gashi inason zuwa gidan Goggo Amina na duba Kan khadija yau kwata kwata ban ganta ba

    Sai kusan 8 ya shigo d’akin, Sumayya kin kwanta ne?

    “Eh Amma idanuna biyu”

    Jin muryar ta saitin kujira,yasa ya nufo inda take

    Ina kallonsa harya ido wajen kujiran Yana kokarin zama mini akan kafafu da sauri na mike zaune na nade kafafun nawa”yanzun zama mini zakaye akan kafafu daban d’aga ba ka karyamin kasusuwa Koh me”?

    Au kafarki nagun ne?ya tamaya

    “Kaji nace maka Ina kwance sannan kazo zaka zauna akujiran”
    Sanann yanzun kana tambaya ta Ina kwance ne”

    Sorry yace Yana zama a inda ta d’aga kafartata, Sumayya!!

    Na’am

    Sumayya Ina Mai baki hakuri nasan tabbas band’auke Miki nauyin da ya rataya akaina a matsayina na mijinki b Ina Mai neman afuwanki wallahih Sumayya bani dashine shiyasa yau kwana biyu ban baki kome ba

    “Ba kome ai nasan baka dashin ne sannan ni don na samu na sai Mana abinda zamuci ai ba kome wata Rana Allah zai baka kaima sauka sai mana”nace Ina kallonsa

    Nagode Sumayya Allah ya saka mini da alkhari

    “Ameeeeeen Daman jiranka nake kazo muje mu duba jikin khadija kasan yau ban samu zama ba tun safe”

    Amma bakin gaji ba ki bari gobe Mana sai muje

    “ah ah muje dai, gobe ma akwai masu zuwa kwalliyar bud’an Kai dana dinner har dare Ina busy”

    Ok toh yace Yana mikewa

    Hijjab nawa har kasa na d’auka nasa da karamin purse

    D’aukar sandar sa yayi ya tsaya Yana jiranta a kofar d’akin

    “Yau fa bazaka tafi da sandar nan ba atoh”

    Akan me?

    “Akan zaka fita Dani”

    Ke asuwa?

    “Asu masu ido” nace Ina kamo hannunsa ba musu ya aje sandar

    Tsaya na rufe kofar, yace

    Sake Masa hannun nayi ya rufe mana kofar,Yana rufewa sake kama Masa hannun nayi Muka fita a shashen mu

    Tsakar gidan kaman ba dare ba duk jama’ar gidan na zazaune wasu a taburma wasu a kujira,nidai ganinsu baisa na sake hannunsa ba

    Ke fasuma Wai me kika ganine a tare da miskini kike zaune dashi kamar auren tsafi,d’aya daga cikin Yan gidan Tama Sumayya gogar zana

    Ai toh auren tsafinne Mana inba haka ba mutun da arziki ya zabi Talauci,fasuma ta bata amsa..

    Nikam ban tanka musu ba Donna fahimci Yan gidan nan sai shiriyar Allah don mutum Kam sai wani ikon Allah,tunda mutuwar inno Bai saka sun tsakaita da dambe da cacar baki ba ai hukuma ma bazata iyya dasu ba, kamar yanda Al’ameen yace

    Waje muka fita,Ina rike da hannunsa muna tafiya,duk.inda muka wuce sai an bimu da kallo bare ga mazan unguwan da Basu sanni ba suna Daijin kwatance a bakin matansu,duk.madalisan da Muka wuce bin mu ake da kallo ga hasken sola ya haska Koh Ina, a hakan har muka shigo layin su Goggo Amina, na saima Khadija kankana da lemo,
    da sallama a bakina na shiga gidan,don shi yace bazai shiga ba sai ammasa iso

    “Assalamu alaikum”

    Waalaikumu salam barka dai Sumayya sannu da zuwa Goggo Amina ta fad’a tana shimfid’a mini taburma

    “Yauwa Goggo Ina wunin ku”

    “Lafiya Alhamdulillah Sumayya kece da Daren nan”

    Eh Goggo tare muka taho na fad’a Ina sunkuyar da Kai,(Wai kunya🤥)

    Shine ya tsaya a waje ai aikin muhammad kenan kamar gidan bakonsa ne,kice ya shigo

    “Toh Goggo” nace na koma kofar gida

    “Ka shigo”nace Ina juyawa

    Toh kin hanani rike sanda sanna kin tafi kin barni

    “Yanzun bazaka iyya shiga da kanka ba”?

    Eh bazan iyya ba

    Uhmm kawai nace na Kama hannunsa da yake dare ne koma ba NEPA sai da muka kusa isa kusa da Goggo na sake Masa hnnu,
    Zama nayi a taburman shi Kuma ya zauna a kujira,

    Goggon Ina wuni?

    Lafiya Muhammad hala kunzo duba khadija ne?

    “Eh wallahih Goggo shuru yau najita bata zoba shine muka taho mu duba Koh kan nata ne har yanzun”?

    Wallahih Sumayya ta fad’amin abinda ya faru,zaman gidan mu sai hakuri kuma.ku Kara hakuri kinji kome zai wuce

    “Ba kome gaggo”

    Aiko khadija kam.na kwance a d’aki yau Koh fita batayi ba Kai na ciwo ga zazzabi duka,Daman khadija akwai raki ku shiga ku duba ta,inji Goggo

    Mikewa mukayi, muka shiga d’akin
    Khadija ce a kwance tana bacci,

    Fita mukaye don bamu tashe taba

    “Toh Goggo zamu tafi ga wannan ba yawa Allah ya Bata lfy wannan Kuma 5k ne yayanta ya bani Wai na baki koh gobe saita je asibiti”nace Ina aje laidan da na shigo dashi,hade da mikawa Goggo kudin

    Wai Al’ameen d’awainiyane har haka daka bare Koh chemist taje goben sun Kara Mata wasu magani Koh na 200 ma

    Al’ameen Kam mamakine ya kamasa yaushi ya samu kudi har 5k da zai bawa khadija,Amma Sumayya tace in jisa,

    “Goggo taje asibitin dai zaifi tunda jiya chemist in ta fara zuwa ba’a dace ba”na fada Ina taka kafar yayan Khadija Jin yayi shuru baice kome ba

    Am am gaskiya ne Goggo ki karbi kudin inyaso taje asibitin

    Amma kudin yayi yawa ai muhammad

    Ba wani yawa Goggo In change ya rage ku rike zai D’an rage muku wasu Abubuwan

    Kai Amma mungode muhammad, Sumayya Allah ya saka

    “Ameeeeeen” har muna hada baki dashi

    Fita mukaye daga gidan Goggo Amina kafun na rike Masa hannu

    Jin tayi hanyar titi ba hanyar gida ba yasa yace Mata Sumayya Ina zamuje koma bafa nan bane hanyar?

    Sai da Kai zanyi nace Ina tare keke napep…………

    🏵️🏵️ *Gaisuwa na musamman da fatan Alkhari ga special FAN’S na MATAR MAKAHO Naga sakonku, Allah yabar kauna,Ina godiya* 🏵️🏵️

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    *Contact them vie*
    🪀08028827241 or 09033791049
    *IG @umsadincense*

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 24-25

    Matar Makaho 24-25

    Page2️⃣4️⃣&2️⃣5️⃣
    Karasawa tayi kusa dashi, Assalamu alaikum

    Waalaikumu salam khadija

    Na’am yaya, lfy Kam na ganka haka a zaune, a Rana gashi sai zufa kake

    Lafiya khadija wallahih Ina cikin damuwa ne, tun safe na fita nabar Aunty ki Koh karyawa batayi ba gashi har ana neman la’asar banyi cinikin Koh biyar ba

    Yaya gaskiya ya kamata ka shanja sana’a yanzun mangoro yayi a raha ba lallai bane kana cini ki sosai

    Gaskiya ne khadija Nima Yanzun so nake na sare lemo in gwada na gani Amma bani da jarin,

    Toh Yaya Allah dai ya Bud’a maka kaji kabar saka kanka a tunani kaje ka jawa kanka ciwo a banza

    Allah yasa khadija

    Yauwa gashe Aunty ta bani abinci na kawo maka

    Abinci kuma?ai na ta samu kudi har taye cefene?

    Ina Zan sani Yaya nidai data kirani saita aike ni kasuwa(ta Masa karya karyace Sumayya batajin maganar sa)

    Koh dai kayanta ta sayar ne khadija?

    Kai.yaya bana tunanin haka fa,ga abincin kaci pls kaji yayana sannan ka tashi a ranan nan ka koma Gefen shagon Haladu ka zauna

    Toh khadija,yace Yana karbar kulan da take hannunta,
    khadija Turaren wa Kika saka ne naji kina kamshi?

    Hh wayyo yayana lalle ne Aunty ta mini, yanzun ma kwalliya zata mini Inna koma

    Lalle Kuma khadija kuma yake kamshi?

    Eh Yaya Turare aka saka sai aka kwaba dashi

    Inta Miki kwalliyar Ina zakije?

    Kamun Asma’u Mana Yaya ka manta

    Ban manta ba sha’afa nayi khadija, Amma ya za’a yi bani da kudin machine in da Zan baki fa

    Yaya za’a d’auke mu a mota gidansu Amarya,kasan yaufa zansha kyau,ta fada cikin farin ciki, zanje sai mu tafi tare…

    Sai kin dawo Allah ya tsare mini ke kanwata,yace yanajin wani Annashuwa, kanwarsa na farin ciki Kuma Sumayya ce sanadi, gaskiya Sumayya Rahama ce Allah ya masa,daya basa ita

    Ameen Yaya,tace tana tafiya

    Bayan fitar khadija wanka nayi na chanja Kaya wando nasa da riga t-shirt na kwanta akan kujira Ina jiranta,

    Assalamu alaikum Aunty na dawo Aunty

    “Waalaikumu salam khadija kiyi Alwala sai kizo mu fara make-up in Kinga Koh an Kira Sallah sai kiye kawai”

    Toh Aunty, tace tana iban ruwa Alwala tayi ta shigo d’akin

    Make-up kit nawa dana aje a cikin drawer na d’auko budesa nayi babbane ba abinda babu na make-up a ciki,zama nayi na tsarawa khadija makeover,
    Kai Masha Allah duk Wanda yaga khadija mundin ba mugun sani ya Mata ba bazai taba zato Koh tsammanin ita bace heavy make-up na Mata irin na Amare, amaren ma sai agun dinner,”khadija muyi sallah sai kisa Kaya Koh”

    Toh Aunty, tace sai murmushi take

    Bayan mun iddar da sallah

    Less in na Bata ta saka black ne Mai ratsin pink, gel na samata a gashi na d’aura Mata dankwali Mai ubansu,
    sarka da d’ankunne warwaro, zube, na Bata dukansu golden colour,takalmi pink, gyale da purse black,Kai duk Wanda yaga khadija a yau Koh shakka bazaiyi ba zaice Amarya ce, Ina Gama shiryata

    Tsayawa tayi tana kallon kanta a mirror, kamar taga abin tsoro, Innalilahih Aunty nice na koma haka? Aunty Kinga yanda na koma kamar ba ni ba,ta fada hawaye na cika Mata ido

    “Kece khadija ki share hawayen nan karya Bata Miki kwalliya kinji maza share”

    Toh Aunty,tace tana goge hawayen ta

    Wayata Kiran iPhone na d’auko”tsaya Khadija na Miki hoto”nace Ina gyara Mata gyelenta

    Tsayawa tayi,Aunty ta ta Mata hotona harda video sosai tayi kyau

    “A Ina za’ayi kamun ne”?

    A Taraba hotel ne,Wai ta hanyar government house

    “Hhh ba Taraba hotel ba, Taraba motel ake cewa sannan Bata government house bane,hanyar ne Amma ta Amazon yake ”

    Au nikam Ina Zan sani Aunty ba zuwa nake ba, kawai nima naji jiya ana fad’ane

    “Ga 200 ki hau machine kije kinji ki dawo da wure fa khadija karki Kai mangariba”na fada Ina Mika Mata kudin

    Ki bare Aunty mota za’a kawo a gidansu amarya zai d’auke kawaye

    “Aikam yau a motar zaki,maza ki hanzarta Amma ki.karbi kudin Incase

    Toh aunty sai na dawo,tace tana fita a d’akin

    “Toh khadija Allah ya dawo dake lfy”

    Ameen, khadija na fita a kofar shashen yayanta, duk Yan gidan suna zaune a tsakar gida daga maza har Mata,ido suka bita dashe kureeeee suna mamakin bakuwar nan Sam tun safe suke zaune Amma basuga wucewar taba,baki a tsake suka bi khadija da ido harta fita,

    Khadija Kam duk tabi ta tsargu don Sam tunda take da wayonta Bata taba kwalliya irin na yau ba har kofar gida ta fita duk masu shaguna suka bita da ido suna mamakin Wannan kyakkyawar meya shigo da ita gidan Adara,
    Amma wasu basa mamaki in sun tuna MATAR MAKAHO fa Yar manya ce Kamar yanda aka saigunta musu, Kuma sun rasa dalilin auren nan Basu mamaki yake,mutum talaka miskini,a d’auki lafiyayye ya abasa Kuma Yar masu kudi,masu kudin ma zuriyan shugaba,abin nan na mugun Basu mamaki,Amma Basu da halin sani

    Khadija Kam ganin ido caaaa akanta yasa ta ruga gida da gudu ta koma kofar Sumayya

    “Kee khadija lfy meya faru Naga kin shigo kofa Koh sallama Babu Kamar an koroki”

    Aunty duk inda na wuce bina fa ake da ido,ni gaskiya tsoro nake ji

    “Kai khadija akwai wauta,don ana kallonki saiki kame jikinki ki nuna musu kauyanci,ai dakewa zakiye kici bom”

    “Koh gun kamu kikaje neman kujira zakiyi ki zauna abinki karki kuskura kicewa kowa kome Wanda ya gaidake ki amsa Wanda Bai Miki magana ba karki Masa kinji”

    Toh Aunty,tace tana fita

    Sai yanzun Yan gidan suka gane ta cikin mamaki Iro yace,buran uba muna d irin wannan kayan a gida Amma ace har yanzun banyi aure ba aradun Allah Naga Mata

    Kutumar ubanka iro D’an iska watoh kaga kasa ya rufe idon uwarka shine bare ka karya alkawarin da mukayi akan auren ka da salame,watoh munafurcine kullum akace ka fitoh a muku aure,sai kace baka da kudi,
    ah ah sai kayi gini ashe iskancine,baba lami tace

    Kinga baba lami wallahih kibini a hankali Daman ni har yanzun haushin ku nakeji,
    Aini ba shege bane dazan aure kanwar Wanda tayi sanadin mutuwar inno na ba,
    Koh inno ne ta dawo nasan bazata yafe mini ba Inna aure yarki, iro yace

    Kai karamin D’an Tasha wallahih karka kuskura, kace zaka zagarmin uwa inba haka ba naci ubanka a gidan nan, manu ya fada,babban yaron Inna asabe

    Inka fasa shege kake,iro yace Yana huci

    Ai Bai Gama rufe baki ba manu ya shakumosa suka hau dambe

    Duk yanda matasan ke ta kokarin rabasu abin ya faskara abinka da tamben maza,
    Mazan ma masu zuciya

    Hatta iyayensu maza an Kira Amma duk sunki rabuwa sai an rabasu an Kama D’aya sai D’aya ya fizge ya shakumo D’aya Inka shiga tsakani duka ya sauka akan ka

    Abin da yafi karfin Yan unguwan police aka Kira,suka zo suka kwashe su,inda sabo an Saba da ganin fiye da hakama agidan Adara

     

    *******************
    Bayan fitar khadija kwanciya nayi don yau dai naji na gaji da cin cimar mu tunda inada sauran 2k Kuma akwai kayan Miya da yawa,don haka yaudai zanci wani abin special

    Duk abinda ke faruwa Ina kwance Ina jinsu sai dai.bansan ainahin abinda ya had’asu ba”garin kallon fad’a a kasheni a banxa ” nace Ina gyara kwanciya na

    sai kusan 5:30 Al’ameen ya koma gida kwata kwata naira 30 yayi ciniki Sam yau Kam sai a hankali,ya shigo gidan jiki a sanyaye hannunsa d’auke da kwandon kwanuka,bakinsa dauke da sallama

    “Waalaikumu salam,sai yanzun”nace masa

    Eh Sumayya yau inne ba kasuwa shiyasa ban dawo Koh da Rana ba

    “Toh Allah ya bada kasuwa gobe”

    Ameen yace Yana aje Kwanukan a mawanki,Mika Mata talatin in yayi

    “Ka rike kawai agunka”

    Ok yace,boket ya d’auka ya ibi ruwa, band’aki ya shiga yayi wanka Yana fitowa yayi Alwala,daidai lokacin aka Kira mangari ba, masallaci ya wuce

    “Sallan mangariba,nayi wanka Nima zani na d’auka fille D’aya na had’a da t-shirt sai hulan bacci, Jin ana kukarin shiga sallan isha’i,
    Ina da Alwala hijab kawai nasa na Tada sallah,

    7:40 Al’ameen ya shigo d’akin bakinsa d’auke da sallama

    Amsa Masa nayi”yauwa jiranka nake ka dawo daman”nace Ina mikewa

    Toh Allah dai yasa lfy?yace

    “Kasan inda ake Saida tsire”?

    Tsire Kuma Sumayya?

    Eh “tsire de”

    Hmm eh na sani a tsallaken titi akwai Mai nama, kusa damai shayi

    Yauwa karbi kudin nan 2k ne ka sai Mana tsiren 1500 sai Kuma ka sama Mana drinks Mai Dadi guda biyu yau Dadi zamuci gaskiya”
    sai ka sai Madara bornviter da sugar in change ya rage kasai bread Nokia Ina da ruwan zafi a flasks,sai mu karya dashe gobe da safe”

    A Ina Kika samu kudin nan? haka Sumayya don khadija tace mini ba kayanki Kika sayarba

    Sosai naji Ina Kara kaunar Khadija yarinya Mai hankali hartasan ta rufa mini asiri agun D’an uwanta,
    Amma ni bazan Masa karya ba”uhmm uhmm nidai gaskiya bazan maka karya ba Turarena na sayar”

    Amma Sumayya banace ki daina Saida kayanki ba ,ni ban Kara Miki ba, Bai kamata in rage Miki ba

    “Habba ya Ina da abinda Zan sayar na saka abakin salati saina zauna da yunwa tsakani da Allah fa, yau baka samu kome ba da haka Zan zauna tun safiya har warhaka banci kome ba kenan”na fada Ina Bata Rai

    Ganin Kamar taji haushi sai ya sassauta murya,toh Yi hakuri kawo kudin naje na saya Miki

    Mika Masa nayi bance kome Ba

    Lalubar kudin yayi harya rike,ya fita

    Baifi hour 1 ba ya dawo lokacin Ina kallo a d’aki

    Shigowa yayi da sallama

    Amsa Masa nayi,Ina karban laidodi Daya ke mika mini, karba nayi, na mike waje na fita na d’auko plates da cups harda flasks na shigo d’akin,
    bude laidan tsiren na zuzzuba a plate,Goran pineapple juice in Mai sanyi na juye Mana a cup,d’aukan NASA nayi na Mika masa,”gashi naka”

    karba yayi hade da Mata godiya,a hankali yasa hannunsa a cikin plate in ya dauki Naman da Bismillah yasaka a bakinsa
    ,lumshe ido yayi,rabonsa da yaci tsire tun lokacin da mahaifinsa kenan,bazai manta ba shike sayo musu duk dare, lokacin ma ba’a haifi Khadija ba

    Nima cin namana nake Ina korawa da drinks ba karamin Dadi naji ba kai.talauci ba kyau talaka sai yafi wata baici nama ba,
    Ashe haka talakawa keji,tabbas badon jarabawar da Allah ya jarabceta ba bazata taba sanin rayuwan Talauci haka yake ba Alhamdulillah Alah kulli halim

    Daga ni harshi duk nacin mu bamu iyya cinye namarnan ba, sai da muka rage wani,nikam har zafi hakorina naji yake mini kafun na aje Naman don yau cin yunwa na masa,sabanin da, da nake ma nama cin kwad’ayi kawai

    Jin ta aje plate nata yasashe magana,sumy Wai harkin cinye ne ga nawa ki Kara wallahih na kasa cinye wa,

    “Kutt bazanci sauran abinda kaci ba,Kuma nima ga nawa ban ciny………

    Bai bare ta Gama magana ba taji ya fizgota sosai suka zube akan gado kanta yahau cikin gaggawa ya hada bakin su waje D’aya y’awonsa ya juye Mata a baki

    Ware ido nayi Jin y’awonsa cike a bakina so nake na zubar Amma ba Hali har lokacin bakin mu a hade,ji nayi kamar numfashina xai d’auke ai da sauri na had’iye Ina rumtsa idanuna

    Jin ta had’iye yasa a hankali ya kamo harshen ta sosai yake tsotsarta cikin zafi zafi..

    Fizge bakina nayi,”don Allah ka Bari banason abinda kake minin nan”na fada Ina ta kukarin turesa a kaina

    Ni Kuma inaso,ya Bata Amsa,Yana Kai hannunsa, akan t-shirt nata Yana kokarin cirewa

    Ai bansan lokacin da na Kama kokarin fizgo kaina ba ganin da gaske fa mutumin nan riga zai cire mini

    Jin ta isheshe da fizge fizge shima ya biye Mata inya d’aga riga sai yaji ta jawo rigan kasa,inya cire hannu D’aya sai tasa d’ayan

    Tambe muka fara sosai abin dariya abin haushi,daga ni harshi mun jikkata sosai Amma ba Wanda yayi niyar barwa Dan uwansa dama

    ni naki yarda ya cire mini riga shi Kuma yaki yarda ya hakura,

    Hannu yasa da karfi ya fizge zanin jikinta,

    Gwalalo ido nayi jina ba zani,wani yunkuruwa nayi da karfin gaske Zan mike zaune

    Cikin zafi nama ya maidata kwance Yana Kara Hawa kanta,

    daidai lokacin mukaji sallama na muryoyin Yan Mata a kofar mu….,…..

    🌾 *Juma’at Mubarak* 🌾

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth*
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 9

    Matar Makaho 9

    Page9️⃣
    Haka ya ringa lalube don Koh sanda Bai rike ba ya fita waje, da ita,yaje

    titin shuru haka ya ringa takawa a Gefen titi ba tare da yasan inda zai nufa ba,

    cikin ikon Allah sai ga wani Mai mota yazo wucewa ganinsu cikin wani Hali yasa shi tsayawa a saitin, Al’ameen Yana tambayar sa lfy kuwa ya gansa da mace a bakke a kafada Bata motse gashi Koh takalmi babu a kafarsa da asuban nan?

    Da sauri ya juyo wajen da yakejin muryar Mai motan don Allah ranka shi Dade ka taimaka mini matatace ba lfy wallahih tun jiya yanzun haka Suma tayi Ina son kaita asibiti Amma ban samu abin hawa ba,

    Allah sarki shiga muje Nima kwanace ta kamani a hanya sai yanzun na shigo gari,

    Allah ya saka nagode,ya fada Yana laluben murfin mota tsabar tashin hankali Yama kasa budewa ,abin ya bawa Mai mota mamaki, yadai malam lafiya Naga kana lalube baka shiga ba,?

    Bana ganine,ka taimaka ka bude mini,

    Ba karamin mamakine ya Kama Mai mota ba ace mutun Kamar Wannan baya gani lallai Koh wani bawa da kaddaransa,

    Fita yayi yazo ya bude Masa

    A hankali ya shimfida Sumayya asset in baya shima ya shiga Mai mota ya rufe ya zagaya shima ya shiga mazauninsa yaja motar ,

    Wani asibiti Zan kaiku?

    Duk asibitin da yafi kusa damu ka kaimu

    Ok ya kara gudun motar lokaci kankani suka iso FMC don yafi kusa da SINTALI ( sunan unguwansu Al’ameen)

    Suna Isa emergency Mai motar ya kaisu fita yayi ya shiga Hall in ya Kira nurses za’a d’auki Mara lafiya suka fitoh da sauri aka aza Sumayya bisa keken marasa lfy aka wuce da ita dakin taimakon gaggawa,

    Likituti suka,rufu a kanta don Bata taimakon. Gaggawa

    shi kuma nurse tace Masa yaje ya sai Mata card a bude mata file,

    Wajen sai da card in ma da taimakon Mai motar ya gane,

    kudin card naira 300 matar da ke windown tace,

    ba karamin tsinkewa yayi ba sai yanzun tunaninsa ya dawo jikinsa, don Koh sisi baida shi sai naira dari da hamsin na cinikin jiya, ya Allah ka taimake ni abinda ya ke fada kenan a ransa,

    Malam.koh bakaji bane nace 300 ne kudinka shuru yayi Yama ya kasa magana,

    Mai motar ne ya fahimci Koh sisi baida shi kenan

    fitar da dari uku ya Biya kudin card

    Menene sunan majinyacin?

    tambayar sa akaye me sunan Mara lafiya, Sumayya
    ,sunan surname?? Shuru yayi yana tunani a hankali yace Abdulsalam shugaba,ya fada Dan in Bai manta ba haka yaji agun daurin aure aka fada,sai da ta daga kai ta sake kallonsa Jin sunan da ya fada amasayin sunan mahaifin maralafiyar da suka kawo,

    lokaci kankani aka bude Mata file in ,

    Yama rasa bakin godiya sai gode ma mai motar yake, nagode nagode bawan Allah ba abinda zance maka sai Allah ya saka maka,

    Ba kome ai ka gode Allah,
    sunana Ammar Ina zaune da iyayena a unguwan millionaire’s sweet,ya fada Yana Kama hannun Al’ameen Yana Masa jahora zuwa masallacin asibitin sukayi sallah suka dawa Kan kujirun da ka jera a Hall in,suka zauna,

    Nurse ce ta fitoh tana tambayar suwaye suka kawo Sumayya Abdulsalam shugaba?

    Mekewa sukayi Ammar na rike da hannun Al’ameen suka Isa wajen da take

    Gamu nan

    Mika musu takardan magani,doctor yace ku saya maza-maza don ana bukatar sa emergency,

    Hannun Al’ameen na rawa ya amshi takardan hade da tambayar ta don Allah ta farfado ne ya jikin nata,??

    Eh ta farfado Amma ana bukatan kuje ku sai Abubuwan da aka rubuta muku,..

    Kama Masa hannu Ammar yayi suka wuce pharmacy suka je

    Mika takardan maganin sukayi

    karba sukayi suka duduba ruwane da allurai sai maganguna,

    Kudin ku naira dubu bakwai da dari biyar,

    Shikam Abu ya hade Masa goma da ishirin Ina zai samu kudi Mai dunbin yawa har dubu bakwai da dari biyar,

    Koh Kama sayar baidashi bare ya Kama ya sayar ya Saya mata magani Innalilahih wainnailaihir rajuun yake furtawa hade da karban takardan balance ya fita tsabar rudewa shikamma ya manta da wani Ammar suke tare,

    Ammar ne ya biyosa ganin yana faman lalube zai fita a pharmacy in da sauri ya rike Masa hannu,

    Habba Dan uwa karka dagawa kanka hankali Mana Yana fada ya karbi takardar ya rike hannun Al’ameen suka shiga waje biyan kudi

    Ammar ya biya kudin suka karbi magangunan da su ruwa da allurai suka Kai emergency, suka mikawa nurse in ta shiga dakin,

    sai a lokacin hankalin Al’ameen ya kwanta sosai yayita ma Ammar godiya shikam ma har kunya ya kamasa Kamar Wanda ya bawa million biyar,.

    Sai 8:30 aka barsu suka shiga suka ganta ta farfado Ansa Mata ruwa da alluran bacci don ta samu hutu sosai ciwon ya lafa

    Toh abokina Zan wuce Naga gari ya fara wayewa gashi sai kirana ake daga gida kasan Dana shigo *Jala* na Kira gida nace musu na shigo,

    Ba kome wallahih nagode sosai Ammar Allah ya saka da alkhari

    Habba wanna godiya ya Isa haka,baka fadamin sunan kaba fa har yanzun?

    Suna na Al’ameen,ya basa amsa

    A unguwan da na dauke ku kake ?

    ……Eh

    Ok toh insha Allah Zan dawo na duba Mai jiki

    Nagode nagode Ammar

    Sai anje ma, ya fada Yana kokarin fita a Hall in sai Kuma ya dawo,

    Koh xan kaika gida ka dauko Mata Kaya da Abubuwan bukata Kamar Kayan da zata chanja su maclen da brush da abubuwan bukata kaima ka samu ka kimtsa jikinka Naga Kamar a birkice ka fitoh Koh takalmi babu nasan har yanzun baka San kafarka ba takalmi ba hh ya fada cikin wasa Yana dariya,??

    Shima Al’ameen in dariya yayi kawai, Yana cewa toh muje don wallahih rudewa Kam na rude,

    Hannunsa Ammar ya rike masa suka fitoh ya bude Masa mota ya shiga ya ja suka wuce, suna tafiya suna Hira

    Amma dai ku sabbin aure ne Koh?

    Eh yau kwanan mu hudu,

    Kai kace ango ne da kansa Koh dai Mai kashane, amarya har asibiti

    Dariya kawai Al’ameen yayi baice kome ba don bazai iyya fadawa Al’ameen sirrin Saba duk da yaji bawan Allah ya kwanta Masa arai Yana da kirki sosai koma zasuyi sa’o’in juna Amma hakan bazaisa ya tsake jiki dashi ba don mutumin duniya ba abin yarda bane lokaci guda,

    Sun Isa har inda ya dauki Al’ameen tukunna ya tambaye sa sun iso wajen da ya dauke sa da asuba ata Ina gidan naku yake?

    Ah ah Ammar sauke ni ma anan na gode

    ah ah kaidai kamin kwatance

    Ah ah wallahih hakan ma nagode,ganin ya nace yasa Ammar sauke sa

    Sukaye sallama

    A hankali Al’ameen ke tafiya Yana Dan yaryarfa hannunsa don Ya tabbatar inda yake sa kafarsa ba mutum Koh wani abu inda Allah ya Sosa ma tsallaken titine aka sauke sa ta barin gidansu a hankali yake tafiya Bai Ankara ba yaji an bangajesa haryaso faduwa saura kadan da yakai kasa, wani zafi yaji a yasansa don ya buge dutse sosai yatsan ke Masa zafi a hankali ya mike, Jin Wanda ya turesan Yana bala’i, ku wasu irin mutane ne in ka San baka gani wani rawan Kaine zaisa ka fitoh babu D’an jagora babu sanda, irin hakane ai sai ku hau titi mota yabi ta kanku kujawa mutum jaraban jinya inkun mutu Kuma kusa mutun azumin kaffara mtwss,,

    Ya fada Yana tafiya

    A hankali Al’ameen ya d’uka ya taba yatsar Jin damshi yasashi gane jini ke zuba,

    Bai damu ba ya cikaba da tafiya har Allah yasa ya iso kofar gidansu ya shiga,

    Yana shiga cikin gidan ya samu Yan gidan a filin tsakar gida kowa na sha’aninsa daga masu wanke wanke sai masu wanki sai masu kitso masu Jan ruwa wasu Kuma group aka hada ana ta gulma ana xagin juna,,,

    Ganinsa ba takalmi sanan ga jini a kafa Yana zuba, yasa Rabi’u fara magana Kai MAKAHO daga Ina haka a bujaje yau tun safe ma bamuga fitarka ba?

    , kafun ma yayi magana iro dake goge takalminsa zai fita yace Wai fa D’an rainin wayon nan jiya Ina bacci yazo karfe kusan daya Wai nakai matar sa asibiti Bata da lfy kaji Dan rainin wayyo wama ya sani Koh turmushe Yar mutane yayi xaizo tsakan dare yana tashina,,gabaki dayan su suka saka dariya,

    Shidai kala baice musu ba hanyan shashen su yayi da lalube harya shiga sai a lokacin ya tuna Ashe fa kofa a. Bude ya barta cikin D’an fargaba ya shiga dakin don shi tsoronsa ma kar Yan gidan su shigo su Ma Sumayya sata don shikam baida abinda za’a sata, wayarta daya Mika Mata jiya da dare shiya fara lalubawa akan kadon aiku yajisa,

    Hakan ya tabbatar Masa ba Wanda ya shigo tunda ga waya a fili Amma da an shigo wayar nan dake zaune a fili haka da an sabe sa hamdala yayi ya gode Allah Basu San ya fita ba,

    iban ruwa yayi yashiga bandaki yayi wanka yasa wasu Kayan ya rufe kofar ya fita don bazai iyya gane inda kayanta suke ba,

    Sandar sa ya dauka ya fita a gidan hanyar gidan Goggo Amina ya nufa,

    Yana Isa kofar gidan ya tsaya a waje yayi sallama,

    Shan cikin gidan kuwa Khadija nawa Goggo Amina kitso taji sallama Kamar ta yayanta Aiko ita ince amsawa tayi tare da daukan hijab inta ta fitoh waje

    Yana tsaya yaji isowar Khadija bakin ta na amsa sallaman sa

    Ina kwana Yaya ya aunty?

    lafiya Alhamdulillah Khadija

    Ka shigo mana Yaya Goggo ne kawai a gidan yau ?

    Toh ya amsa Mata

    Ta Kama hannunsa suka shiga cikin gidan kujira ta aje Masa ya zauna Yana gaida Goggon tasu, Ina kwana Goggo?

    Ta amsa da kulawa

    Lafiya Alhamdulillah Muhammad y’ay’a iyalin taka?

    Lafiya Alhamdulillah sai dai bataji Dadi ba jiya da ciwon ciki ta kwana yanzun ma daga asibitin nake nazo na dauki Khadija tazo muje zata dauka Mata kayayyakinta Koh kadanne Zan Kai Mata asibitin,

    Subhanallah Allah ya Bata lfy wani asibiti ne?

    Ameen a FMC ne ya amsa Mata

    Khadija tashi maza kuje, toh Goggo ta amsa Mata tana mikewa

    Shima Al’ameen mikewa yayi,hannunsa Khadija ta Kama suna tafiya a haka,

    Yaya jikin nata da sauki Koh?

    Da sauki Khadija Yaya zan bika muje asibitin?

    Ah ah Khadija ki tsaya a gidan namu ke dafa mana abinci tunda Kinga asibitin FMC ne babu nisa saiki Kai Mana can,

    A wani block ne yaya?

    emergency ne

    har suka Isa gidan nasu suna Hira dakin ta shiga ta dau jakan Sumayya mabi da ket ta Ajjye tana iban Kaya a whtdrp tana zubawa hijab D’aya, sai dogayan rikuna biyu, zani fille fille guda biyu,sabbine kal ta hada da t-shirt biyu, da hula biyu, sai maclen da brush ta hada Mata da kananan Kaya su pants brz da vest ta rufe akwaitin,

    Yaya na Gama Amma dai tunda kace tun asuba kuke asibiti baka samu kaci karyawa ba koh?

    Kai Khadija kin cika surutu wallahih inkin gama kika kawo Mana ai zanci,

    Amma yaya yanzun fa ana neman 09:30 na safe baka karya ba in kaje asibitin Yaya ka samu abinda zaka saya muku kuci Kaida Aunty kafun na Gama,

    Toh Addata Khadija

    Hhh ye Hakuri yayana ..

    Baice Mata kome ba illah daukar jakar da yayi Yana lalube zai fita a dakin idon Khadija ya sauka a Kan kafarsa a matsanancin damuwa ganin yatsan sa a kumbure gashi ya karce sosai,

    Yaya meya same ka a kafa haka,?

    Tuntube nayi kawai yace Mata Yana fita,,

    fita yayi bakin titi Yana tare keke da hannunsa har Allah yasa wani ya tsaya,

    Malam Ina zuwa?

    …FMC yace Masa

    Shiga muje, da lalube ya shiga keken suka wuce cikin kankanin lokaci suka Isa hospital ya sauke sa abakin get don in ba majinyaci bane a Keke ba’a Bari ta shiga asibitin, ya bawa Mai keken kudin sa naira 50,

    Ya Kama hanya da lalube ya Isa cikin asibitin security n get yake tambaya don Allah wani shashine zaibi zuwa emergency don lokacin da suka zo da Ammar a motane bazai gane hanya ba gashi asibitin fadine dashi ga shashe daban daban,

    Kabi nan ka Mike har emergency zai kaika

    haka kuwa yayi har ya Isa emergency Yana shiga ya gane dakinda aka kwantar da ita

    yazo shigane ya hadu da nurse in d’azon tana ganinsa ta rufe sa da masifa

    Kai wani irin mutum ne zaka kawo Mara lfy kasa kafa ka fice ka barmu da ita, tun dazun nemanka ake likita nason ganinka,

    Kiye hakuri gida naje na dauko Mata kayane

    Me yasa she dayan bazai je ya dauka mata ba Kai ka zauna?,

    Taimakona yayi Kuma ya tafi,
    Jeka aje kayan kazo likita nason ganinka

    Da toh ya amsa Mata da lalube ya Isa inda gadon ta yake har lokacin Bata farka ba,
    Juyawa yayi ya fita a dakin sai da ya fita kafun, ya tuna baisan office in likitan bama tambayar wata nurse yayi da taimakon nurse innan ya gane office in doctor shiga yayi da sallama doctor ya amsa masa matashine kamarasa,

    Kaine ka kawo Sumayya Abdulsalam shugaba?

    Eh nine doctor ya basa amsa

    ..ok Sumayya na fama da apendes ya kunbura sosai don haka dole za’a Mata tiyata ga wannan sai kaje ka biya kudin,

    Atake zufa ta fara karyo Masa Innalilahih wainnailaihir rajuun,likita kudin zai Kai nawa,yafada Yana tambayan sa?,

    Bani bane Mai karban kudi in kaje wajen biya za’a fada maka……………..

     

    🪀My WhatsApp number
    08084453785

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌
    Free book🤧

  • Matar Makaho 14-15

    Matar Makaho 14-15

    Page1️⃣4️⃣&1️⃣5️⃣
    Aunty’ inno ta rasu tace tana Kara karfin kukanta,

    “Innalilahih wainnailaihir rajuun” Allah ya jikanta da rahama yasa ta huta” nace

    Ameen Aunty tace tana mikewa tadau hijab inta ta nufi cikin gida,

    **Banyi niyar zuwaba saboda jikina Amma ganin mutuwa ne Kuma Abu da gida babba hakan zai iyya zama abin magana, yasa na mike na fita zuwa cikin gidan,

    Ai ban tashi sanin Yan gidan ba sai da Naga manya da yara Suna kuka harda na tashin hankali kuka suke ba manya ba yara Mai makon a ma mamaci Addu’a sai ihu da kuka nidai Ina zaune a Gefen matan makwanta da suke shishigowa Ina kallon ikon Allah

    Al’ameen da wannan sanyin jikin ya iso kofar gida ya tarar da jama’a makil, inno ta rasu mutuwar ta dake sa sosai don alokacin sai da mutuwar mahaifiyar sa ta dawo Masa sabo,ganin yanda iro ke kuka Wanda yasan halin iro ba kome ke tsorata Sa bama Amma yau kuka yake,

    tabbas mutuwar iyaye akwai ciwo,(Allah kajikan iyayen mu)

    Ankai inno gidan ta na gaskiya yau har anyi sadakar bakwai gida ya koma kamar yanda yake kowa na sha’aninsa sai yaranta da sukayi sanyi kadan na rashin uwa,

    A tsawon satin nan na fahimci yayan Khadija baida aiki haka zaije yayi ta yawo Koh sisi bazai samuba ya dawo Yana kame kame taliya Koh Maggi Koh indomie nake iba na bawa Khadija takaima masu shago su Saya da araha kafun mu samu na shifenen Miya,..
    Duk da Al’ameen baisan Ina Saida garana ba,

    karshe dai ajesa nayi nace ya fadamin me ke faruwa, dashine yanzun,duk lokacin da ya zauna baida aiki sai tunani,

    Tukum yamin bayanin bashi da jari yaje tashan kayan marmari sun hanasa bashi duk inda yaje su taimaka Masa sunki,

    ,”Amma menace maka in Abu ya taso ta wajenka bance ka ringa fada mini ba”?

    Hakane Sumayya Amma ni sai Inga Kamar ni ya dace in bukatar ki ya Tashi ki tambayi ni ba Zan ringa daura Miki nauyi ba,

    “Au aini ma nufina bashi Zan baka Amma Ina ni Ina baka kyautar kudi sai dai bashi ”

    Duk da haka dai Sumayya….

    Ban Bari ya karasa maganar Saba na tare sa “na baka bashin ne ka rufawa kanka asiri Koh na rike kudina ka cigaba da yawo ba aiki ga azumi saura wata biyu”

    “Kuma bara na gaya maka in azumi yazo kayan Dadi zakana sai min Kuma kamin kayan sallah harda Khadija kaji dai na fada maka”

    Toh shikenan abani yace Yana gyara zama alamun dai baida mafita,

    “Ka Bari sai gobe Zan baka”

    Washe gari Khadija na tura yaro yace tazo, ba’a jima ba sai gata aikanta nayi *say* *box* ta Kira mini Daya daga cikin yaran masu shagunan sai da wayoyi da laptop’s suzo tare tace Masa amarya ce ni Kuma ban fara fita ba,

    Don nasan in na Bata laptop innan za’a Mata cinikin wulakanci ne kawai Koh ma wani ya Mata wayo ya gudu da laptop in don nasan say box ba irin mutanen da babu a ciki,

    Munyi ciniki da Mai sayan system in ganin yanda Yama laptop in cinikin wulakanci yasa nace na fasa sayar wa,

    Buhun flower na dauko a kitchen Daman ban taba bude Saba nace wa Khadija taje gun Haladu tace Masa xai Saya buhun flower Zan Masa sauki,

    Bata jima ba ta dawo tace min yace ta kawo flowern ya gani, Bata buhun nayi taje shagon Haladu ta sayar mini shima naira dubu bakwai ya Saya ba yanda na iyya haka na sayar Masa Amma ni Karan kaina nasan ba haka kudin yake ba,

    Yayan khadija na baiwa dubu uku yayi jari na rike dubu hudu na D’an Yi sayayyan abin bukata nayi irin su pad omo sabulu na baiwa Khadija dubu D’aya, tunda har yanzun Basu gyara Mana NEPAn kofar muba don sun biya ganin mu bamu biya ba sai suka yanke wayar kofar mu Khadija na baiwa dubu daya ta mikawa bappa sulaiman kudin wutan NEPAn mu aranan sukasa aka hada mana wayar aka gyara, na baiwa Khadija dari biyar itama 😉

    Haka rayuwa tayi ta tafiya Rana ya wuce sati ya shude yau Dadi gobe Akatsen sa har Muka cika wata Daya da sati biyu da aure, ba abinda ya taba shiga tsakanin mu Koh da kuwa hada gado ne, in munkwana waje D’aya toh ana zafi munyi kwanan waje ba nepa,

    A y’an kwanakin nan na fara fuskantan matsen rayuwa Wanda ban Saba ba,

    Dole sai abinda ya samu zamuci wani sa’in ma in Bai samo kome ba haka zamuci indomie d’anye wani a dafe da ruwa, in ya samu D’an ciniki Kuma muci shinkafa da Mai da yaji,Inda Allah ya sumuma garana Bai kare ba akwai taliya Mai Maggi kefe shinkafa, Amma duk da haka na D’an fada na chanjin yanayi, saboda yanzun ya hanani Saida Kayana don har Yan unguwa sun fara gulman ya kasa rikeni Kayana nake sai dawa,maganan har kunnen da yashiga shiyasa ya nuna mini baya so ,

    yau na shirya da niyar zuwa gidan Goggo Amina, da gidan mu tunda safe na kammala aikina yau mun Sami kudin kayan shaye mukasha da safe’ bayan ya fita na kammala aikina dake na sanar dashi Zan fita gidan Goggo Amina ( marikiyar Khadija ) Zan bi gidan mu d’uka Bai Musa ba saboda mun Riga munyi maganar dashi, dari da hamsin ya bani kudin Keke,

    Khadija zata rakani kasancewar yaune Zan fara fita, unguwa tunda nayi aure bayan asibiti ba inda naje,

    Sai goma Khadija tazo lokacin na fitoh wanka, Muka gaisa ta shiga Wanka Dayake tun jiya ta zo ta guge kayanda zatasa d’aya Daga cikin Wanda nake Bata,

    Shiryawa nayi cikin lufaya Mai tsada fari Mai Flowers brown NASA riga long sleeve brown NASA takalmi fari na dau jakama fari fuskata ba kome sai powder da man baki, Khadija dake gefe na tsaye baki bude tana kallona,

    “Rufe bakin ga guda zai wuce ciki”nace Mata cikin murmushi Mai karawa fuskata kyau,

    Hmm Aunty na gaskiya ke Mai kyauce Allah ne kadai yasan dalilin da yasa ya bawa yayana wannan k’yakk’yawar hallintar nan Ina ma Yana kallo yaga yaran da za’a Haifa Masa 😅

    Murmushi kawai nayi bance kome ba don na lura ita ta yara ma take,

    ” Khadija kiye sauri kisa kaya don Allah na masu na ganni a gidan mufa Naga abie na”

    Toh Aunty tace tana saka dogon riganda na taba Bata,tayi shafe shafen ta tana Gama shiryawa, Muka fita”

    Yaune rana na farko Dana taba karewa unguwan sintali kallo unguwa ne da ya hada ruwa biyu masu kudi da talaka wa Yan kasuwa da ma’aikata da masu zaman banxa unguwan nada kyau sosai da fasali,..

    Gidan Goggo Amina mukaje da kafa ,

    Mun samu tarba Mai kyau ba laifi matar nada kirki sai dai na Lura ita mace ce da Bata shiga abinda Bai shafe taba Sam babu ruwanta,mun D’an jima a gidan kafun Muka Mata sallama na aje Mata laidan Turare Wanda na d’auka a kayan aure na,

    ta rakomu har waje Muka tare keke napep ,

    Hajiya Ina kukayi? Ya tambaye ni

    “Specialist” zaka kaimu,
    Ku hau muje yace,

    Dukan mu Hawa mukai yaja machine insa muka nufe unguwan specialist,

    Muna shiga unguwan mu na Masa kwatancen inda zai sauke mu,

    “Yana sauke mu na tambayi sa “nawane kudin ka”

    Naira dari da hamsin kudin ku kubiyu,

    Sai a lokacin na tuna dari da hamsin inne a jikina kacal Wanda yayan Khadija ya bani Allah dai yasa abie na gida nasan zamu samu na dawowa don karyan mu taka da kafa daga specialist zuwa sintali,
    biyansa nayi muka nufi kofar gidan mu

    Khadija mutuwar tsaye tayi ganin wani irin gida Mai bala’in kyau Wanda Koh a mafarki Bata taba ganin irin Saba Daman ita ba yawo take ba iyya kacinta kasuwa sai unguwowin kusa da sintali irin mafindi unguwa gadi da sauran unguwowin kusa da unguwan su,

    Amma Bata taba zuwa unguwa Mai nisan nan ba sai dai tanaji a bakin Asma’u sunje unguwan specialist Koh millionaire’s sweet in suna Bata lbrn gidajin unguwan sai taga Kamar tatsuniya suke Bata bata taba zaton haka gine ginen unguwan yake ba Wai duka wannan a cikin Jala yake?

    ***Harna nufe get Amma sai naji Kamar ba Khadija a gefena juyawa nayi me Zan gani Khadija an sake hanci baki ido ana kalle kalle zuwa kawai nayi na jaho hannunta, sai a lokacin ta farga da kauyancin da ta nuna

    Cikin Jin kunya tace Aunty wallahih unguwan nan yayi kiga gidan da zamu shigan nan Kamar aljannan duniya,

    Kai Khadija kin cika shirme wallahih mu tafi nikam,

    **Get Muka nufa Mai girman gaskiya kamar get In gidan prison haka ma ginin gidan dogayene sosai anyi penti fari get in ma farine k’wank’wasa,makeken kofar get in,nayi

    Wani farin buzune ya leko ganina yasa ya washe bakinsa cikin hausar sa da baya fita yake cewa laaa Amarya Kaine hajiya Sumayya wallah nayi kewanka shannu da zuwa lale lalema barkama lale ya fada Yana bude mini get muka shiga,

    Shiga cikin gidan mu ya sake ruda Khadija ganin filin gidan mu filine babban bana Wasa ba Wanda yakai girman wani karamin unguwa,ga shuke shuke na Flowers ya kewaye gidan Wanda ya kara haska gidan sosai ga parking space babba Mai dauke da mototi na alfarma wanda akalla zasu Kai talatin duk ciki bamai araha,

    Nidai Ina rike da hannun Khadija Muka nufi wani babban part Wanda duk fadin gidan part inne kawai ba wasu Amma daga ganin part in kasan ba karamin duniya bace a ciki ganin shima ginine na gidan sama Mai Hawa uku,babban kofar falon NASA hannun na na bude da sallama a bakine duk da banida tabbacin za’a ji,saboda girman falon,

    Khadija Kam mutuwar tsaye ta sake tayi ganin cikin falon gidan mu,

    Kusa Kai mukayi cikin falon falone Mai girman gaskiya Wanda ke dauke da kujiru set biyar ga babban plasma na alfarma Kai fadar tsaruwar falon gidan mu Bata lokaci ne na barwa readers su keyasta,

    Babban falon gidan mu Yana dauke da d’akuna kusan Sha biyar haka upstairs shima dakuna goma Sha biyar ne Hawa na uku ma haka,Amma duk yawan d’akunan gidan munan falon mu dayane shine falon kasa, Wanda Koh a Hawa na uku kake kana hango falon,

    d’akunan kasa na samarine sai kakarmu dake zaune dasu a kasan Wai tana saka musu ido injita, dakunan Hawa na biyu na iyaye ne Hawa na uku shine na Yan Mata da d’akunan yaran gidan da sukayi aure maza,suna zaune da iyalansu ,..

    duk yanda Zan fasalta muku gidan mu saifa na rage wani abin,

    Kaf gidan mu da colour D’aya aka kawatashi da white colour sai surkin baki Kama daga kujiru labule Abubuwan da aka kawata gidan kome farine daga sama har kasa abin sai Wanda ya gani,

    Jama’ar gidan mu duk Muka samu a falo da yake yau weekend ne ba aiki ba makaranta kowa na zaune wasu na kallo wasu na Danna waya wasu na Danna laptop yara na wasa wasu abinci suke ci ganin mu yasa dukansu barin abinda suke suka zuba Mana ido Kamar yau suka fara ganina,tunda Khadija ce Basu sani ba,

    Idanuna ne ya sauka a Kan kakata dake zaune tanacin kefe sai uncle’s nawa dake zazaune wasu na cin abinci wasu na Hira wasu na duba takardu,

    wani abune ya tsayamin a makoshi Mai kamada Takaici sun aurar Dani Basu damu da rayuwar da nake ashan ba gasuna suna zaunen su Kamar Basu San wata Sumayya da aka bawa MAKAHO ba Basu neme sanin ya rayuwa ta kare ba waima me dalilin auran Dani ne tunda gasu Aunty miemie sun girme ni nesa ba kusa ba Amma saini kadai aka aurar auren ma da MAKAHO ba lafiyaye ba,Koh don anga mahaifiyata Bata gidan ne Kai Koh mahaifiyata Bata gidan ai ubana nanan

    Koh da kowa zai nuna Mini kiyayya dada zata sassauta tunda ita ta haifi babana amma Ina abin ba sauki,

    “Ina kwana dada,”nace Ina zama a cikin Daya daga cikin kujirun falon,

    Toh matan miskinai ne agidan namu yau Koh idonane,?

    Ah ah Kaka ba idon ki bane kinsan azumi ya karatoh anzo amsan zakkah ne,

    Hhhhhh Kai miemie baki da dama Amarya ce fa tazo ganin gida mutun da gidansu kece yazo karban zakkah,kubra ke fada tana dad’a tunsirewa da dariya

    Waiku yaran nan wasu irin Yan iska ne me yasa baku da mutunci shegu kawai ai gwara ita tayi aure Koh?

    Keee koh miskini kin samu yazo wajen kine da sunan aure, a cikin ku waye ta samu miskinin na zuwa wajenta,Yaya Abdu ya fada ransa a bace,

    Ai itama ba zuwa yayi ba lika Masa akayi,miemie ta basa amsa,..

    Rufe mini baki karna ci ubanki Yar iska Abdul yace Yana mikewa,

    Ai duk laifin dadane Sam bansan me yasaba, Dada (kakar mu) itace babba Amma ita ke sasafo Mana bala’i yaya kabiru yace Yana maijin takicin ahlin gidansu,

    Abubakar kanajin abinda shegen yaron Kan nan kabiru yake shimin mutunci kayi shuru kana kallonsa,,,

    Kiye hakuri Dada Kai kabiru zanci kaniyarka fa inka sake shiga abinda ba ruwanka uwarka aka zaga Koh me da zaka saka bakinka a ciki,

    Mikewa Kabir da Abdul sukayi sukabar falon,

    Ganin yanda aka Mai Dani Kamar kashi ba Wanda yabi ta kaina kowa na Harkan gabansa

    Ganin Banga Abie na a cikin falon ba yasa na mike nayi hanyar upstairs na nufi d’akin sa nabar Khadija a falo wance ke rakube Kamar ace kitttt ta ruga,

    Bude kofar d’akin nayi nasa kaina na shiga Abie nane zaune a kasan tiles Yana duke da Kai sai momy (yadikko na) zaune a bakin gado daga Gani dai magana suke………………

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense
    [9/19, 4:45 PM] +234 813 343 4840: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 5

    Matar Makaho 5

    Page 5️⃣
    Dan a irin lokacin da yake tashi sallolin dare,

    mikewa yayi ya riga ya gane ma’ajiyin Randa da buta fita yayi a dakin alwala ya daura ya dawo dakin,ya tada sallah sai uku ya koma ya kwanta, Kiran farko na asuba ya farkar dashi, Addu’a tashi daga bacci yaye.

    A hankali ya sauka a kujira cikin sanyi ya lalube gadon ya tsaya a bakin don bazai iyya Hawa ba kar a maimaita irin na jiya a hankali yake kiranta

    **sumayya!! sumayya!! *

    **A hankali na bude idanuna cikin bacci nace “naji habba” baice mini kome ba ya daga kafarsa a hankali da lalube ya bude dakin ya fita **Niko waya na laluba a gefen filo don dakin ba haske na kunna hasken ya haska dakin sauka nayi Nima nayi waje don d’auro Alwala, **fitana yayi daidai da kammala tasa alwalan mikewa yayi Yana laluben sandanrsa,Harna kammala alwala Bai gane sandar ba.

    *Ina kammala alwala na shiga daki daukar wayata nayi na fitoh na haska kofar aiko Naga sandar Ashe faduwa yayi a kasa, dauka nayi na zungure sa da sandar a hannu *

    da sauri ya mika hannunsa ya amsa cikin sanyi sanyin sa yace nagode,

    * batare da nayi magana ba don takaice waini sumy nice yau da miji MAKAHO shap wannan ai abin kunya ne ma Wanda ya sanni ya gansa a matsayin mijina, Tabbas nayi Wasa da Damata a rayuwa, shiyasa Allah ya jarabce ni a lokacin da ban taba tsammani Koh tunanin hakan ba,

    **Da sauri nayi istigifari na kauda tunanin a Raina

    * Koh amsa Masa banyi ba nayi shege daki na tada sallah, Ina idarwa Qur’an na dauka cikin jakansa Mai kyau na bude,

    *nayi azkar in safiya, dana sabayi kullun na mike nabi lfyn gado bacci ya dauke ni,

    sai shidda da rabi ya shigo dakin da sallama hannunsa rike da bakar laida na kayan shaye da kayan miya Jin ba’a amsa ba ya lalube kujira ya zauna, numfashi Daya ji kasa kasa hakan ya tabbatar Masa ta koma bacci a hankali ya mike,waje ya fita da lalube ya Isa kitchen aje laidan yayi ,

    shanyar kayansa ya dauko a igiya ya nade ya shigo dakin ya lalube Ghana must go in sa Daya aje a lungun kujira da firij yasaka kayan,ya dawo Kan kujiran ya kwanta a hankali wani irin bacci Mai Dadi ya sauke sa,

    **Ban tashi ba, sai Takwas na safe shima ihu da ashariya na dandazon mutanen gidan Wanda Koh tantama banayi tambe ake, shiya farkar Dani,mikewa nayi sanye da kayan baccina Wanda na saka jiya da dare riga da wando Mai taushi sosai sai hulan bacci d’uka farare ne tas.

    * da sauri na dirko daga Kan gado nafitoh dakin naje na rufe kofar shashen mu don nasha Alwashe yau bamai shigarmin kofa kallo Koh ganin daki bare naji yau da tambe aka tashi* 😂 (Anya ba tsoro ba kuwa?)

    *Kitchen na wuce, ganin laidan kayan Miya a kasa,

    * dauka nayi na bude kayan miyane su tarugu albasa da tattasai sai dayan kayan shaye ne yau harda Madara, na laida da bouviter, bread, sugar, da Lipton,

    ruwa na zuba a kettle nasa Lipton, don yau muntashi da NEPA na jona a socket bude caton indomie, na kayan garana laida biyu na dauka manya shap shap na daura na dau kwai na soya cikin 40 minutes na Gama hada breakfast na Kama shara,

    ✨ (tabbas aiki a wajen mace ribace babba duk kudin gidan ku duk mulki Koh gata ilimi da kyau in har mace Bata iyya girki ba gtoh Bata cika macen da za’a kira Tauraruwa ba Yan Mata a Kara bada himma karki xamantu baki da aiki sai adafa a baki kici ki kwanta kina Danna waya.koh makaranta kike zuwa at lest ki ware wasu lokutan a Rana kina Taya ma’aifiyarki,

    aikin da kika tsana kina ga ana matsamiki ana bautar dake wallahih ribarta na zuwa don bakisan inda Allah zai kaiki ba)✨ *shawarace*

     

    **Tun sa’ilin da aka fara Yar Hali watoh dambe, a tsakar gidansu ya farka Amma Bai Mike ba har **fitanta da rufe kofar duk akan kunnensa duk yanaji Yana kwance ,

    a hankali ya mike ya fitoh cikin sanyin halinsa da nutsuwa ya bude baki yake gai Dani,

    **shuru na Masa naki amsawa *

    baiyi fushi ba ya kara tambaya ta, Koh Zan Kama Miki wani aiki ? Abin nasa harda rainin wayyo kenan, Wai ya kamamin aiki? da wani idon Amma saina maze nace “wanke-wanke nakeso kamin” ba musu ya lalube sandarsa da takalminsa shinyayye ya saka
    Da lalube harya lalube boket, ya dauka ruwa ya Iba a Randa ya aje a gefe da laluba har yakai cikin kitchen nidai Ina binsa da ido kawai, ganin garajen sa,

    cikin tsawa nace “kaiiii aje kulanan abincine a ciki”

    ” tsaya na nuna maka kwanukan da zaka wanke”

    ” Wai baka ganewa ne?

    Hala banda rashin gani ma? harda rashin basira? zaka dauki kula kaje da nauye basiranka bazai baka abincine a ciki ba zaka zungumu??

    Kala baice mini ba ya ajiye kawai ya jingina a gefen kitchen ya tsaya,

    Zuwa nayi na dauki kwanukan nakai masa gefe na hada ruwan kunfa na aje kwando da kujira na tsaya agefe cikin masifa masifa nace gashinan Bismillah sai kazo ka wanke jiki a sanyaye yazo da lalube harya zauna Niko Ina saye a gefe ina ganin ikon Allah wanke kwanuka yake Kamar Mai ido tas suke fita Yana kifewa Kai Koh Mai ido albarka, mamakine y kamani Amma ban nuna Masa ba,

    **Shara na kammala na gera daki na na jona kask’wan lantarki na zuba Turarukan wuta a dakin fita nayi Naga har yanzun Yana Kan wanke wanke

    Kwanukan akwai Dan yawa na abincin jiya da yara sukaci ban samu na wanke ba Harda na dare,

    *Wanka na shiga Ina fitowa na tarar ya kammala Yana zaune a kujiran tsugunne,

    ” Koh Mai ban shafa ba na zura kaya atamfa super Mai kyau siket da riga Mai k’wala da hannun roba* dinkin zamani

    *abinci na zuba ina ci daidai lokacin shima wankan ya shiga yana fitowa wanka ya shigo dakin, Alhamdulillah Koh ba kome na Lura Yana da tsafta duk da bana rayawa a Raina Koh da Wasa zanyi rayuwar aure dashi Mai tsayi dole ya sake ni yaje ya nemi miskiniya irinsa Amma kafun lokacin bazan cutu da wari ba tunda Yana wanka ( lol😅uhmm muje zuwa zakiyi bayani )

    *Fita nayi na basa waje*

    Kaya ya saka wani jimemmen t-shirt da wando jeas duk da tsofene Amma sunyi Masa kyau sosai ya laluben kujira yayi ya zauna,

    Ina waje ban kulasa ba naci gaba da cin abinci na kammala zamana nayi A wajen naki basa abinci shi kuma Bai tambaye ni ba Danna waya nayitaye sai kusan goma na safe na iba Masa a plt da shaye a Kofi na shiga dakin na aje Masa na koma Kan gado na kwanta,

    ya jawo plt in yayi Bismillah ya fara ci

    Yana tsaka dacin abinci muka ji bugun kofar shashen mu mikewa yayi zaiji ya bude na dirko daka kan gado cikin fada fada nace “bazafa ka bude kofar nan ba don yau bamai shiga kofar nan ehen kaji na gaya maka don Naga alama Yan gidanku basuje islamiyya ba”

    Baice mini kome ba ya koma ya zauna

    Jin Mai bugun yaki barin kunne na ya huta,

    hijab na dauka na zura na fita ,don gani wani isheshshine,

    Bude kofar naye idona y sauka akan wata yarinya kyakkyawa sosai farace Mai Kama da MAKAHO sak banbancin ita mace Mai karancin shikaru 18 zuwa 19 she Kuma namiji ne sanye take cikin riga na kodadd’in shadda sai hijab wuyan duk ya sabule gashinta har ya leko ta gaban goshi,

    *Tunda aka kawoni wanna kaddararerren gida ban ganta cikin yaran gidan da suka zo kofana ba,

    Aunty Ina kwana tace

    hanya na Bata cikin dakewa nace “lafiya shigo”

    Shigowa tayi daidai lokacin shi kuma ya fitoh cikin dakin murmushe dauke a fuskarsa itama murmushin take da sauri tazo ta amshi kwanukan hannunsa hade da gaishe sa ya amsa,Yana tambayar ta ya su Goggo Aminar,

    Ta basa amsa

    Tace in nazo nace tana gaida Amarya,ta fada tana kallona

    Amsa Mata nayi ba yabo ba fallasa “Ina amsawa”

    Fita zaiyi hade da tambaya ta Koh akwai abinda za’a saya Kai tsaye nace “babu “sa Kai yaye ya fita hade da cewa Khadija in Zaki tafi ki biya ta guna, da toh ta amsa Masa

    Nidai daki na wuce naje na kwanta sai da Naji fitarsa tukum na kwala Mata Kira ” Khadija shigo daki Mana kina tsaye a waje” don haka kawai naji yarinyan ta kwantamin sosai a Rai duk da bansan Alakarsu ba amma nasan akwai alakar jini a tsakanin su,

    Da sallama ta shigo dakin na amsa Mata tana kukarin zama a kasa nayi saurin cewa tahau kujira Amma Taki da kerta zauna, firij na bude na dauko mangoron jiya da yayanta ya kawo na hada Mata da drinks harda ruwa na aje mata hira take mini Kamar na saba da ganin akwai ta da surutu sosai tun Ina amsa Mata har bacci ya dauke ni,

    Ban farka ba sai 1:30 na Rana shima kiraye kirayen sallane ya tashe ni sai a lokacin na tuna Ashe fa Ina da bakuwa,
    A hankali na sauke idona akan kujiran da na barta akai da mamaki sai Naga wayam ba kome,

    Sauka nayi a gadon na fita a dakin cike da mamaki nake bin kofar da kallo har idona ya sauka akanta cikin sabon mamaki ganin ta a cikin………………..

    Good morning fan’s 🌥️

    An gaishiku Yan free books💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

    🍀MATAR MAKAHO FAN’S GROUP 🍀
    Naga comments naku naji Dadi Kuma Ya karfafa mini gwwa

    🪀My WhatsApp number
    08084453785
    [9/27, 4:10 PM] +234 806 983 1049: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯 *
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌
    Free book🤧

    😒 *More comments*
    😏 *More post*

  • Matar Makaho 10

    Matar Makaho 10

    Page 🔟
    Cikin tashin hankali ya mike ya fita Dayake shi mutum ne Mai saurin fahimta yasa dakansa ya wuce wajen biyan kudi,

    Kudin 50k yaji ance Masa,

    Innalilahih wainnailaihir rajuun take yaji Kamar kansa xai rabe biyu haka ya karbi takardan ya wuce zuciyansa sai rawa take, shi Ina yasan zai samu kudi gabaki daya jarinsa ma baifi dubu daya da dari biyar ba Ina zai samu dubu hamsin, Koh bashi zai karba wazai tinkara in ma an basa Ina zai samu kudin biya?

    Har cikin ransa baya kaunan wani abin bukata ya Tashi ta bangarin Sumayya ya kasa Mata har sai Yan gidansu sun Mata duk da baisan dalilin da yasa duk cikin Jala Arasa mijinda zasu aura Mata sai shi suka zaba Mata Wanda har yau ya kasa samun Amsa dalilinsu,,

    Kuma bayason Koh da Wasa ta Saida abinda tazo dashi daga gidansu,saboda gazawarsa wajen Bata kulawa Bai santa ba Bai ta ba ganinta ba Bai taba Jin lbrn taba Bai San ya take ba muryarta kawai ya sani Amma a D’an zaman da sukayi Yana jinta har cikin ransa,,

    Ya Allah ka bani ikon kulawa da wannan Amanar da aka bani,

    A hankali yake tafiya harya fita a get in hospital in da taimakon wani Almajiri ya tsallake titi 100 da ke hannunsa ya Saya Mata Ayaban 100 guda biyar aka basa ya baiwa Almajirin ayaba daya ya sake tsallakar dashi, cikin hospital in ya shiga yanabi a hankali da sardarsa harya Isa kofar dakin da aka kwantar da ita da sallama ya shiga dakin,

    “Waalaikumu salam” na amsa Masa cikin dishashesshen muryata dagaji kasan na Mara lfyne maijin jiki

    Sannu Sumayya ya jikin ??.

    “Da sauki Alhamdulillah”

    Sannu ya sake cewa

    **Kai kawai na iyya daga masa

    Lalube ya fara Yana neman wajen zama,

    “Kujiran na Gefen ka na dama”nace Masa

    Laluben damansa yayi yaji kujiran plastic na roba ya matso dashi Kusa da gadon inda yaji muryarta ya laluba ya aje kujiran kusa da gadon saitin kanta a hankali ya zauna,

    Sannu Sumayya ga ayaba na sai miki yafada yana bude laidan hade da fitar da Ayaban masu k’yau guda biyar zai bare mini,

    “Ah ah ka ajiye,so nake sai nayi sallan asuba nayi brush da wanka Koh zanji dadin jikina kafun NASA Abu a bakina”

    Toh bara na taimaka Miki ki shiga bandakin sai kiye wanka da brush in duk na kawo Miki harda Kaya

    “Toh taimaka min na tashi ”

    A hankali a mike Yana lalube na harya lalubo hannuna ya Kama na mike a hankali na sauka a gadon Ina “takalmina”?

    Na manta ban hada Miki ba komawa nayi na zauna a bakin gado “gaskiya ni bazan iyya taka tiles na asibiti ba takalmi gaskiya” toh ga nawa kisa Yana fada Yana cire mini ciny’ayyen silifas insa “ah ah innasa naka kaikuma fa”? ba damuwa Zan tafi haka

    “Bazanfa saka ba sai dai ka saimin sabon silifas abakin get”

    Wallahih ban fita da kudi ba sai dai in Khadija tazo taji da dauko Miki”toh” na basa amsa Ina k’wanciya a Kan gadon,

    Khadija bayan fitar yayanta dakin ta fara kimtsawa ta share ta cire zanin godon ta shimfida wani ta share baranda da kasa ta hada wanke wanke tayi kafun ta shiga kitchen,da yake akwai NEPA ruwa ta daura a hot-plate ta zuba ruwa ta rufe, ta dauko wani bojuwan daban ta daura shima ruwan ta saka ta rufe Daya ke hot-plate in Mai uku ne,

    Tattasai ta dauka da dogo dogo sai albasa ta hada ta juye a blander Dayake taga yanda Sumayya tayi ranan da suka shiga kitchen kunnawa tayi ta markada she Kara Kara baiyi laushi ba dai dai irin na miyan taliya,

    Sannu ishesheya munafukar yarinya uwar me kike a kofar har yanzun Naga fitar *makaho* tun dazun ya fita? Taji muryan inna asabe take fada tana shigowa kofar

    Inna Aunty Sumayya ce ba lfy shine Yaya yace na musu girki,

    Oh lallai ai sai ke in zai Kira don duk gidan nan ba bawan sa

    Kala Khadija batace Mata ba

    Dan ubanki bara na kawo kwanona ki zubamin inkin gama saura kisamin kadan,

    Kala Khadija batace ba tana cigaba da gyaran waken da ta iba cikin Kofi Daya da rabi

    Keee ishassheya bakiji me nace bane

    Naji innah ,ta Bata amsa

    Fita Inna asabe tayi sai gata ta dawo da katon kula ta ajema Khadija a gaba ta fita abinta

    Ruwa na tafasa ta sauke taliya daya ta juye a tukunyan ta barbada gishiri ta rufe, dayan bujuwan wake ta wanke ta zuba ta rufe shima ta saka Masa gishiri,

    Wani sabon bujuwa ta daura ta zuba Mai da albasa Yana soyuwa ta juye kayan miyarta ta soya ya soyu tukum ta saka ruwa ta bare Maggi tasa da onga classic Wanda ta gani duk a cikin kitchen in caton in kefe ta bude ta dau uku masu kyau ta aje a roba,ruwan zafi ta zuba a kettle Yana tafasa ta juye akan kefen ta barsa yadan d’auki seconds kafun ta tsame tasa a ruwan sanyi ta gyara ta juye a miyar ta rufe

    Daidai lokacin taliya ya nuna saukewa tayi ta juye a k’wando ta tsame,

    Fita tayi a kitchen in ta dau omo da sabulu ta hada wankin yayanta Dana Sumayya harda zanin godo ta fitar waje ta aje ta fara iban ruwa a rijiya tana wanke kayan dashi lokaci kankani ta Gama wanke wa ta shanya a igiyar kofar shashen,

    Kitchen ta shiga ta duba miyar ta nuna saukewa tayi,ta dauki wani kula a caton insa Mai azabar kyau har Yana daukar ido Mai guda hudune uku ta dauka ta wanke dayan ta zuba taliya daya Kuma Miya sauke waken tayi shima ta juye a dayan Kular,

    K’wando babba na kaba Mai kyau ta jera kulan a ciki sai lokacin ta Tuna kulan Inna asabe zuba mata, tayi,

    Ta shiga daki firij ta bude ta dauki drinks guda biyu sai ruwan gora biyu ta hada a k’wandon da plate biyu shukali biyu,..

    Wanka ta shiga tana fita ta maida kayan da tazo dashi, Jin ana Kiran azahar tayi Alwala tayi sallah,

    Ta dauki sallaya ta ninke tana kokarin rufe kofar dakin sai ga Inna asabe tana zuwa kitchen ta nufa ta bude kulanta ganin abinci a ciki Kuma Mai yawa yasata dauka tayi gaba abinta,

    Rufe kofar tayi ta dauki k’wandon ta fita a shashen shima ta rufe kofar ta rike key in ta fita dashi lokacin karfe 1 na Rana hanyar FMC ta Kama da kafa,

    ***********Har lokacin muna zaune nida shi anzo an sake daura mini ruwa,Yana zaune cikin wani yanayi duk da na Saba ganinsa sanyi sanyi Amma nayau yafi na kullum Wanda bansan daliliba,

    Jin an fara kiraye kirayen sallah yasashi tashi Yana lulube yake cemin bara yaje sallah ya dawo,da “toh” na amsa masa,

    Fita yayi yaje masallaci yayi sallah ya zauna agun sai kusan 2 ya mike ya nufu Hall in emergency har yayi nisa yaji muryan Khadija daga nesa tana k’wala Masa Kira,

    Juyawa yayi saitin inda yake jiyo muryar Tata ya tsaya harta karaso Khadija kin isone?

    Eh Yaya na karaso tun dazun Amma ban gane dakin da kuke ba,

    Muje toh Khadija ya fada Yana tafiya,itama binsa tayi a baya,.

    Yaya ya cikin nata?

    ….Da sauki Khadija

    Yaya Yana ganka cikin damuwa haka meke faruwa ne Koh kudin magani ne baka dashi?

    Khadija Ina Zan samu kudin magani in badon Allah ya rufamin asiri ba ya hadani da wani bawan Allah ba ya biya mini kome na magani,

    A Ina ka Sansa Yaya?

    Bansan Saba yadaice sunansa Ammar

    Toh meke damunka?

    Wallahih khadija appendix ke damun Aunty ki Kuma kudin operation naira dubu hamsin shine yake dagamin hankali banda sisi Koh abinda Zan sayar na biya

    Amma yaya baka ganin gara a fadawa Aunty tunda bazata rasa kudi a hannunta ba, tabiya ??

    Ah ah Khadija karki fada Mata yanzun Ina son in munje ki zauna agunta ni Zan fita Koh Allah zaisa na samu bashi,

    Habba Yaya wazai baka bashi tsakani da Allah fa Kaida Koh sisi baka dashi in ba mangoron da ya rage jiya ba wazai baka bashi’

    Khadija kedai ki tayani da Addu’a na Allah basa karewa

    Hakane kam Yaya Allah yasa ka samu

    Yauwa ameen Khadija ta

    Daidai lokacin suka iso dakin, shiga sukayi Ina kwance,sauke k’wandon Khadija tayi tana gaidani Aunty Ina kwana?

    “Lafiya Khadija”

    Ya jikin ki Aunty?

    “Da sauki Alhamdulillah”

    “Khadija kiramin nurse tazo ta cire mini ruwan nan na samu nayi Sallah”

    Toh Aunty tace, tana fita,sai gata da nurse sun dawo cire mini sukayi, “Khadija hau godon ki zauna ki ban takalmin ki bara na shiga toilet” toh Aunty,

    *Ta kalmin nata NASA

    shi Kuma ya bawa Khadija tasa ta saka ya lalube bakin gadon ya zauna

    **Da taimakon Khadija na shiga bandaki ta koma ta dauko mini brush da maclen,da kayan da Zan saka,

     

    ***Wanka nayi da brush nayi Alwala na fitoh a hankali nake takawa Ina bin bango harna bude kofar na fitoh

    Da sauri Khadija ta tashi tazo ta taimaka mini ta shimfida mini Sallayan da tazo dashi ta shimfida mini ta Mika min hijab na saka na Tada sallah harda na asuba na biya,ina idar wa na cire hijab in,

    Khadija ta mikamin hula nasa, na tashi na koma Kan gadon dukansu sukaimin sannu har suna hada baki,

    Khadija takalminta ta saka Wanda na cire ta bawa Al’ameen nasa,

    Abinci ta iba min a plate ta Miko mini,

    “Khadija bawa yayanki abincin nan bazan iyya ci ba bakina ba Dadi Sam”

    Ah ah Sumayya ki karbi abinci kici ai ba’a jinya sai da abinci” Al’ameen yace

    Gaskiya ne Aunty rabonki da abinci tun jiya fa,ta fada tana aje mini,

    “Wallahih Khadija bazan iyya ci ba kidai Mika mini ayabar nan naci”

    Toh Aunty,

    Ayaban ta bani na samu naci uku ta Mika mini fresh milk in da tazo dashi daga gida nasha rabi

    Plate na abincin da ta bani ta Mika Masa karba yayi Bismillah ya fara ci,

    “Khadija ya Naga kin zauna ki ibi abinci kici Mana” na Bata umurni

    Iba tayi ta faraci,

    Yana Gama cin abinci ruwan gora daya Khadija ta bashi yasha, Khadija ki zauna da Aunty ki bara na fita sai na dawo,ya fada Yana tashi yayi hanyar waje,

    Toh yaya Allah ya bada sa’a

    …… Ameen Khadija

    Nidai da ido na bisa harya fita na juya Ina kallon Khadija” Khadija waya biya kudin magangunan nan Naga harda ruwa duka”?

    Nima ban sani ba Aunty yanzun nazo sai dai ki tambayi Yaya,

    **Shuru kawai nayi na koma na kwanta

    Al’ameen Bai Dade da fita ba, sai ga wani matashin saurayi baki k’yakk’yawa Mai matsakaicin tsayi da jiki ya shigo dakin mu da sallama a bakinsa

    Amsawa Khadija tayi nikam hannu nasa na dauki hijabina da na cire a jikin karfen gado nasa,

    Shigowa yayi ,barka kudai ya jiki Sumayya?

    Mamakine ya kamani Ina kuma wannan bawan Allah ya sanni,

    “Da sauki Alhamdulillah”

    Allah ya kara sauwa kewa

    “Ameen” nace

    Al’ameen ya fitane?

    Eh wallahih yanzun ya fita baku hadu ba? Khadija ta basa amsa

    Ah ah bamu hadu ba,

    Koh Kaine Ammar?

    Nine Hala lbrna ya baki haka kikayi saurin gane ni?

    Eh yadai fadamin abin alkhari da ka Mana Allah ya kara bude,

    …Ameen

    Nidai shuru nayi na barsa da Khadija suna Hira Kamar Wanda suka San juna,

    Khadija nikam Inaga Zan gudu fa har yanzun Al’ameen Bai dawo ba gashi Ina son muyi sallama tafiya ne ta kamani wallahih gobe Zan wuce shiyasa naso mu hadu kafun na wuce,

    Yace Yana zaro kudi a Aljuhunsa Yana mikawa Khadija ga wannan ba yawa a saiwa mara lfy lemo in yayan naki ya dawo kice Ina gaishe she ,

    Mungode Allah ya saka Kuma zaiji sakon ka,

    Allah yasa yace Yana kokarin nufar kofa

    “Nagode” nace masa ba tare da na dago ba ganin irin kallona da yake tayi kamar ya samu TV tun dazun da suke hira da Khadija idonsa na kaina,

    Ba kome yace yasa Kai ya fita………

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌
    Free book🤧

  • Matar Makaho 22-23

    Matar Makaho 22-23

    Page2️⃣2️⃣&2️⃣3️⃣
    Yau da Matata Zan kwana gaskiya

    Da mamaki nake kallonsa”waye matarka”?

    Ga tanan ya fada Yana kwanciya Da ita a jikinsa

    “Wai menene haka ka matseni fa” nace Ina kukarin tashi a jikinsa

    Fuska ta ya hada da tasa fuskar har hancin su na gogan na juna,

    Karan in TV nan Kam kyakkyawa ne shiyasa yake burgeki?

    Ikon Allah yanzun Kam na gane inda mutumin nan ya dosa, maganan Karan innan ya damesa”mummuna ne kamar Kai”na basa amsa,har lokacin Ina kwance a jikinsa don karfe ya saka mini sosai

    Murmushi yayi a hankali yake goga Mata gashin gemunsa a Gefen fuskarta

    Wani Abu nakeji sosai a tare dani”Kai me haka”?

    “Kana goga mini gonan ciyawa a fuskata Koh so kake ya garceni ni”

    Kinji Dadi kenan?

    Kuma ni ba mummuna bane sai dai kece mummuna

    Hhhh shap ai in fada maka “Kai mummuna ne sosai gaka bak’i,gajere, Mai guntun hanci, ga tumbi”

    Wannan Karo Kam dariya ya kamayi don sosai yake cikin nishadi, ganin ya samu abokiyar Hira

    Farine ni, Kuma hancina dogone Ina da ido bakina irin na khadijata fuskata dogone Mai dauke da gashin gemu Mai yawa haka na kaima, akwai tabon sallah a goshina,ya Bata Amsa yana Kai hannunsa kanta ya zame hularda ta saka a hankali ya Kama gashinta da khadija ta kitsa Mata har gadon baya,
    Da Ina Tara gashi sai yafi naki yawa

    “Kutt wallahih bazaifi ba duk ma Wanda ya farfada maka haka kamannin ka yake kawai zaginka yayi Amma ba wani yanda na fadan nan dai haka kake”

    Dariya kawai yayi sai Kuma yace,
    Da ace ban taba ganin kaina a madubi ba dayau kinyi Dani don d’auka zanyi da gaske hakan nake

    “Au Daman ka taba kallone kafun ka makance”?

    Shikarata 18 na zama MAKAHO Kinga ai zuwa yanzun kamannin Bai sauyaba

    “Ya sauya kam gashi harda tumbi kayi”na fada Ina murmushi haka kawai na tsinci kaina cikin farin ciki yau na samu abokin Hira Wanda rabon da nayi harna manta sai in khadija tazo

    Cikin hanzari ya birkitota zuwa kasa shi kuma ya koma Saman ta,

    Zaro ido nayi cikin Al’ajabi da tsoro bakina har rawa yake”yayan khadija me haka wayyo kirjina nauyi ka d’agani”

    Ina da tumbi Koh Babu kinsan ba gani nake ba shiyasa na saka Miki tumbin don kiji akwai Koh Babu

    “Wayyo Allah cikina kirjina nauyi ka sauka a kaina wallahih baka da tumbi washhhh numfashina xai d’auke”

    Jin yanda duk tabi ta gigice yasa a hankali ya d’aga nauyinsa akanta Amma Bai sauka ba,

    “Ashhhhh toh ka sauka a kaina Mana”

    Shuru yayi yaki magana yanajin ta sai masifa take, ya sauka a kanta ya Mata banza don yanzun Sam baicika Jin shakkarta ba Kamar da

    “Ina Jin fitsari”

    Yayi shuru don yasan ba fitsarin zatayi ba muddin ya saketa guduwa zatayi

    “Koh bakaji bane, ya matseni fa”

    Kiyi anan kawai, ya Bata Amsa

    Ganin ya manna mini hauka yasa nayi shuru ganin da gaske fa ba sauka zaiyi a kaina ba bare akan gadon,ganin baida niyar yimin kome yasa hankali na ya kwanta har kusan 1 na dare idanun mu biyu daga karshe dai bacci barawo yayi gaba Dani,

    Jin saukar numfashin ta ya tabbata tayi bacci a hankali shima ya ringajin bacci na d’aukarsa zamewa yayi ya kwanta a gefe ya dagota ya d’aurata a kansa ya lumshe idanunsa har yaji babushi,

    Kiran farko na Assalatu shiya sauka akan kunne na a hankali na bude idanuna na,masu cike da bacci jina ajikin mutum yasani tunawa Ashe fa jiya tare muka kwanta zame jikina nayi a hankali Zan mike

    Jin tana zame jikinta a nashe ya sakasa bude ido sai alokacin yaji Kiran sallah ake

    Daga ni harshe waje mukayi na ibi ruwa a buta na aje Masa”ga ruwan Alwala kar a shiga sallah baka Kama Alwala ba ka rasa jam’i”Na fad’a Wai karya tuna wani abu, don yau na iba Masa ruwan Alwala

    Butan ya d’auka Alwala yayi ya tafi massalaci sai tunanin abinda zasu karya yake baida Koh sisi Kuma inya bude Mangoro da safe ma ba ciniki yake ba kwana biyu nan, amfiya D’an Saya da rana Koh yamma

    Alwala nayi na shiga d’aki,
    Ina iddar da sallah na kwanta a Kan sallayan don harga Allah bacci nakeji jiya ban kwanta da wure ba

    Gida ya shigo don ya rasa mafita Sam baisan me zayi ba,a Ina zai samo musu na karyawa tsoro yake kar hakurin Ta ya Kare wata Rana ta guje sa, da sallama ya shigo d’akin Jin Bata amsa ba yasa ya fara laluben ta akan gado Amma Bai jita ba ya sauka Yanata tattaba kujira a tunaninsa Koh tana jinsa kin amsawa tayi,
    Sumayya!! Sumayya!! ya kirata baki biyu Amma shuru,hankalin sa a tashe ya shiga tattaba kome na d’akin Yana nemanta hardai yajita a kwance akasan cafet,sosai hankalinsa ya kwanta shi Karan kansa ya rasa meke damunsa akan Sumayya Sam baida jarumta akan lamarin ta, Koh don ta kasance mutum na farko dake da kusanci dashi a duniyarsa ta yanzun ne oho,hannu yasa a hankali ya cicibeta Yana lalube harya Isa bakin gado kwantar da ita yayi,ya fita waje,boket ya d’auko ruwa ya ringa ja a rijiya harya cika Randa ya wanke kwanuka harda shara yayi Amma dai sharan Koh na yara albarka saboda kwata kwata batayi kyau ba (sharan Mara ido)

    Yana Gamawa d’akin ya shigo da lalube ya isa Kan gadon Hawa yayi,hannu yasa ya fara tataba ta Yana neman fuskarta har hannunsa ya sauka akan kirjinta

    Waro ido nayi Ina kallonsa Jin yaki cire hannunsa a kirjina yasa na buge hannun”me haka don Allah”?

    Da nayi me?ya sake tambayar ta

    “Ai kafini sani waima menene kake ta faman laluba ta Ina bacci”

    Nidai bansan kome ba tunda ba gani nake ba nadai San na taba Abu mai laushi Amma bansan kome Nene ba,ya Bata Amsa

    Lallai mutumin nan ya Raina mini wayo ai Koh Bai taba kallo ba a rayuwar sa yasan meya taba bare harya Kai 18 Yana kallo,jin rainin wayone ma ban sake magana ba

    Kin tashi lfy?

    “Lafiya Alhamdulillah”

    Uhmm Sumayya Zan fita, Koh zan samu na karyawa anjima Zan dawa insha Allah ban kwana da kudi ba

    “Sai ka dawo” nace Masa Ina sauka a Kan gadon don wallahih yunwa nakeji ba kadan ba

    Allah ya yasa,Yace Yana fita a d’akin harya bude kofar shashen zai fita yaji Sumayya na kiransa tsayawa yayi

    “Am Daman nace in ka fita pls ka tura yaro ya kiramin khadija”Ina magana Ina bin kofar da kallo da mamaki

    Toh,yace mini zai juya

    “Wai waye yayi aikin nan duka haka”?na fada Ina murmushi ganin sharan Kamar wata yarinya Yar 3 ce tayi

    Nine na Miki aiki yau dai ki huta

    “Aiko naji Dadi na” nace Masa don na gane so yake ya burgeni 😌

    Da gaske?ya tambaye ta

    “Sosai ma,ka tafi Mana samun mu samu na karyawan ka tsaya surutu yanzun ana neman 8:10 na safe”

    Ok.toh sai na dawo

    “Yauwa”

    Yana fita a kofar gida ya aiki yaro gidan Goggo Amina ya Kira Khadija

    Nikam tsintsiya na d’auka na sake share kofar na gyara d’aki sosai kwana biyu nan. Nake jina a sake sosai

    Khadija ce ta shigo bakinta dauke da sallama,
    Assalamu alaikum

    “Waalaikumu salam”khadin Goggo

    Kai Aunty ni banso sunan fa nasan a bakin Yaya kikaji duk shike Bata mini suna

    “Toh khadin Yaya”

    Aunty ai khadin ne banaso

    “Toh khadija shikenan”?

    Eh Aunty Ina kwana ?

    “Lafiya khadija ya goggo”

    Lafiya Alhamdulillah,tace tana zama a bakin dakali

    “Wai ni khadija ya Fulani Dance in dai su kawayen Amarya jiya an rabashe kenan”?

    Shuru tayi sai Kuma Naga hawaye ya cika idanunta..

    Da mamaki nake kallonta “Khadija me ya faru kuma daga tambaya sai kuka wani abin na Miki”?

    Aunty don Allah nida yayana muna da wani abin kyemane a jikin mu, da mutane ke wulakanta mu Koh saboda mun kasance Marayu ne, Koh Kuma don Yaya baya kallo ne, ta fada tana fashewa da kuka

    “Subhanallah khadija meyasa Kika Fadin irin wannan kalaman haka”

    Dole na fada Aunty kaf unguwan nan yayana baida aboki Sam ba Wanda keson rabarsa gani ake Kamar Inka jashi a jiki zai zama maka kaya, Amma wallahih Aunty yayana baida zuciyan kwad’ayi kullun so yake yaga ya neme na kansa Amma duk da haka in Kinga yayana na Hira toh ta miskinai ne irinsa Amma bayansu ba Mai son Koh Hira da yaya, shiyasa har kullum nake mamakin auren ki,

    Ni Karan kaina mujiyace a cikin kawaye, me laifin mu aunty mu muka d’aurawa Kan mu Talauci ne Koh akwai Wanda yafi karfin maraici ne?

    “Gaskiya Babu khadija Amma meya faru ne haka”?
    Na tambaye ta idanuna na cika da hawaye tabbas khadija Allah ne ya tsare ta a irin zamanin da muke cikin nan yanda Yan Mata suka baci da son kyelekyele Amma ita ta kauda fuska ta cire buri a ranta ta zauna a matsayin da Allah ya d’aurata,samun irin khadija kalilan ne a yanzun yarinya Mai hakuri

    Aunty Kinga wulakancin da kawayen Amarya suka mini jiya a wajen bikin nan? ta fada tana kuka

    “Ah ah khadija me suka Miki”

    Aunty’ Wai daga zuwana naje na tsaya agun da kawaye ke tsaye kawai Ina zuwa suka mimmike suka koma wani wajen Wai kunya suke kar abokan ango suganni a cikin kawaye za’a Raina class nasu,kinsan ma Aunty me yafi Bata mini Rai?

    “Ah ah khadija”

    Wai Aunty danaga duk sun watse saina koma cikin mutane na tsaya kawai kowa na tsaya kusa dashe sai ya Kama matsawa Wai kar ace tare Dani yazo, don ban saka kayan Fulani ba koma banyi ado ba

    Sosai naji wani irin haushi kamar zai kashe ni

    Aunty bazan sake zuwa bikin kowa ba daga yau

    “Yau me za’a yi”?

    Kamu,ta bani Amsa

    “Zaki je bikin nan khadija har a Gama dake za’a Gama insha Allah”

    Aunty ni bazan sake zuwa ba a wulakanta ni,don Yaya yace Koh mutun baida kudi in dai ya rike mutuncin sa bazai wulakanta ba

    “Ki kwantar da hankalinki insha Allah bazasu sake wulakanta kiba” na fada Ina Mai Jin tausayin baiwar Allah nan

    D’aki na shiga na barta tana kuka akwatina na bude Kaya na d’auka Atamfa da les masu azaban kyau a dinke sai Turare na d’auka guda D’aya na fitoh a d’akin dasu a hannuna

    “Khadija rike kayan nan Naga kamar akwai tailoli a tsallaken titi ki Kai musu wa’innan kayan su rage Miki yayi daidan ki yanzun in Kika fita,
    wannan Turare Kuma kasuwa nakeso ki Kai shagunan masu Turare Koh zasu Saya kudin sa 20k ne Amma Koh 10k Kika samu Koh kasa dashe ki karba kawai”

    Aunty ba Yaya yace ki daina Saida kayanki ba?

    “Khadija Zan zauna da yunwa ne Ina da abinda Zan tsayar naci a cikina sai na zauna”

    Gaskiya ne Aunty Amma fa Yan kasuwa bazasu Saya ba don yanzun Suma tsoron sayan kayan hannu suke karsu Saya na sata,sai dai akwai wata Mata dillaliya ta bayan kasuwa sai na Kai Mata don ance itakam Koh kayan satane Saya take don Yar rikici ce sosai

    “Yauwa khadija Allah yasa ta Saya wannan kayan in kin fita ki fara kaisu shagunan dinki”

    Aunty wazaki bawa kayan Kuma ai Naga daidan kine naji kince a maidashe daidai na?

    “Ina ruwan Ki,nidai tashi kije mini aika na,
    sannan in ta Saya Turaren ki shiga kasuwa ki sai Gam bak’i Mai kyau ki hada da Turaren lalle,sajan,tsamiyan kanti, ki sai bakin lalle guda biyu shima”

    Aunty lalle zakije ne?

    “Kai Khadija banson tambaya ki sai mini kayan Miya duka,in kin dawo ki biya tailan kudinsa ki karbi kayan Saiki saimin doya soyayye a bakin titi na karya”

    Toh Aunty tace ta karbi kayan tasa a laida ta fita

    D’aki na shiga Ina ta tunanin halin rayuwa da khadija ke ciki

    Sai karfe 10 khadija ta dawo kayan na bubbude na Bata ta gwada Aiko yayi Mata daidai jikinta sosai kayan ya karbe ta,doyan na bude Mana mukaci tare

    Kam in na manna a tire na kwaba Jan lalle, “khadija zoki zauna na Miki lalle”nace Mata Ina zama akan dakali

    Aunty Daman ni Zaki ma lallen ne har Kika Saida Turaren ki Mai tsada a naira 5k?

    “Khadija bazan d’auki wulakanci ba Sam insha Allah yau saikin fi Amaryar kyau bama kawayen ba”

    Daman kin iyya lalle ne Aunty?ta fada tana zama

    “Sosai ma khadija ai lokacin da nake primary school innaje makaranta sai nayita zana flower lalle a takanda na Inna dawo gida sai ummie na tace zata buge ni sai abie ya k’waceni yace bazata bugeni ba ai batasan Koh baiwar da Allah ya mini ba kenan,
    sai ya sai mini takkadar lalle daban duk lokacin da zanyi Zane saina dawo makaranta sai ya bani takardar na zana, lokacin da na Gama primary sai ya sai k’wallon dayes ya baiwa Mai aikin mu ta dafa mini da lalle,sai nayi mole na zuba a ciki,abie ke saimin hydrogen Ina ma yaran gidan mu lalle harda yaran makwanta,
    harna girma Ina lalle duk yaran gidan mu da aka aurar Mata Ninake musu lallen aure da make-up haka kawaye na da Yan unguwan mu sosai nake Alfahari da lalle khadija”nace Ina manna Mata Gam a gafa

    Kenan Aunty kina sana’an lalle da kwalliya?

    “Ban taba yin lalle kudi ba Koh make-up khadija don ba abinda na nema na rasa a rayuwa a lokacin”

    Allah sarki, tace

    Lalle na tsarawa khadija sosai bak’i da ja sai bayan azahar Muka Gama, tunda nake da khadija ban taba ganin farin cikin Dana gani a lokacin da na Gama Mata lalle ba bini bini saita duba lallen tayi murmushi

    “Wai nikam khadija baki taba lalle bane”

    Aunty Kenan Koh a sallah bana lallle in Kinga nayi lalle toh gaggo ne ta mini yabe

    “Toh yaukam kinyi design na flower”nace Ina mikewa

    sallah Mukayi kafun Muka girka abincin Rana har lokacin yayan Khadija Bai dawo ba,

    Sai biyu da rabi na Gama abinci zuba Mana nayi mukaci har lokacin fuskar khadija na d’auke da murmushi

    ***Nima sai naji Ina cikin farin ciki ganinta tana walwala

    “Khadija ga abincin yayanki kikai Masa”

    Toh Aunty ta d’auki kulan tana kukarin fita,”yauwa khadija in kinje ki dawo da wure samun mu fara make-up in da wure”

    Toh Aunty nagode,tace tana fita,cikin farin ciki duk Wanda ya ganta yau yasan Bata da wata damuwa

    Tun daga nesa ta hango yayanta a zaune g’wanin tausayi sai zufa yake…………….

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *Albishirin ku Mata ku marmaso kuji sirrin,Koh kinsan mace sai da kamshi da gyara* 😉

    🍀🍀🍀🍀 *Turare suna d’ayace Amma sun banbanta kowanne da ingancinsa kamshinsa da aikin sa*

    🍀🍀🍀🍀 *Ina muku Albishir da UMSAD INCENSE Dan samun turaruka masu kamshi da* *gyara*

    🍀🍀🍀 *Tabbas Turare sirrine ga Koh wace mace*

    🍀🍀🍀 *Gamai bukatar turarukan UMSAD INCENSE*

    🍀 *Na tsunguno(habil)*
    🍀 *Na jiki (kwalaccam)* ( *khumra, black & white* )
    🍀 *Turaren turara jiki after birth* ,
    🍀 *Na d’aki(halud Al’oud)*

    *UMSAD INCENSE suna kofar waika wajen Ado bayaro layout Kano State* 💃🏼💃🏼

    🍀🍀🍀 *Suna bada d’aya Koh sare akan farashi Mai Rahusa*

    🍀🍀🍀 *Suna bada order kayansu Gamai bukata aduk jahar da yake a fadin Nigeria*

    Contact them vie
    🪀08028827241 or 09033791049
    IG @umsadincense

     

    🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa👌
    free book 🤧

  • Matar Makaho 4

    Matar Makaho 4

    Page 4️⃣
    Budurwa ce zata Kai kusan sa’ata cikin gadara da taunan cingum. tace amarsu ta ango karyawa ake ne? gashi nazo kallon dakin Amarya

    ***kala bance Mata ba

    shema duk da baiji Dadin hakan ba Amma shuru yayi ba abinda yace ,haushi sosai naji Amma naja bakina nayi shuru don banda lokacin wannan Mai zubin karuwai, abinci muka cigaba da ciii ba Wanda ya kulata cikin mu biyun,

    cikin bacin Rai tayi tsaki ta juya tafita. Koh ido ba mudu bane yasan kema ni ba sa’ar yinta bane kallo daya tamin ta gane ni ba kallan raini wayo bane Kamar yanda suka Saba Raina Masa,

    **mamaki ne ya kamani, lallai sai nayi da gaske Zan iyya zama da Yan gidan nan. don dagani Basu da mutunci wallahi😒

    Muna Gama karyawa ya mike ya dauki kwanukan da mukaci abinci harda nawa ha Hada ya fita dasu a kitchen ya Ajjye,

    Dawowa cikin dakin Yayi cikin sanyin halinsa ya bude baki a Hankali ya furta Zan fita wajin sana’a Koh akwai abinda Zaki bukata,?

    Kamar bazan tanka ba Amma na daure nace “babu”Koh zaka dawo kaci abincin Rana”? cikin natsuwa yace min ah..ah Zan saya naci sai yamma Zan dawo,

    “har Ina ne wajen sana’ar taka” ? Cikin D’anjin Dadi jin Ina kulasa yace bakin titin kofar gida ta gefen shagonan, su haladu

    ** Ni Kuma Ina nasan wani Haladu bare shagonsa😏a Raina nake fada

    Amma a zahiri cewa nayi “toh Inna Gama ka tura yaro yazo ya karba maka abincin”

    da zumudi yace toh ……toh Zan turo bayan azahar. Ya sa Kai ya fita

    ***Daki na koma na bubbude akwatunan Kayana na bubbude kayan Ina jirawa a whtdp wasu a dressed mirror kayane na alfarma atamfufe dinkaku da Wanda ba dinkaku ba takalma da jakunKuna gyeleluka abaya material duka na shirya Kayana a nitse make-up kit na aje sa a drowarn mirror mayuka da turaruka na jirasu saman mirror. sauran kayan da suka rage na mai dasu cikin akwaiti ba wajen jirawa duk ya cika ba fili na rufe na Mai dasu saman whdrp “,

    yarane suka fara shigowa ba sallama ba gaisuwa suka shigo mini daki harda Yan matan gidan suka cika dakin Wai sunzo kallon daki ga makwanta nata shigowa da sunan ganin daki Koh gulma ne oho, ana haka aka kawo NEPA Daya Daga cikin Yan matan ta Mike ta kunna TV

    haka aka sake cika Wai ana kallo har baranda nidai abin daya isheni kawai na dauki wayata na fita waje,

    ” kitchen na wuce kazar jiya nake son hada miya dashi Amma kayan miyar jiya tayi kadan dole na shiga daki jakana na hannu mai kyau na dauka na fito waje budewa nayi na dau gudan dubu daya na aiki yaro a cikin Yan kallo kayan Miya Mai Dan yawa na Kara Masa da dubu biyu ya sayo harda kaza, don so nake na Kara na jiya bazai isaba ga yara a kofar.

    Yaron na dawo mini da kayan Miya na fara aiki ba wance ta taimake ni Koh da jijjigen kayan Miya ne

    shinkafa da miya na dafa Ina Gamawa na zuba a sabon kula Mai kyau na saka a basket da shukali da plt, na Koma dakin na bude freezer na dauki ruwan gora, na hada Masa a basket in na Ajiye, d’aid’ai yaron da Zai aika ya shigo na basa.

    sauran abincin na zuba a babban faranti na hadawa yaran daban na sawa manyan daban daya ke nayi abincin da yawa sosai, Mika musu nayi ba kunya suka amsa gabaki daya Koh kwanukan Basu daga ba suka barsa a Inda suka ci sun batamin daki da datti sosai,

    na ibi nawa na zauna a baranda kan darduma nayi Bismillah na fara ci ban tashi agunba saiga wani yaro ya shigo da sallama amsa Masa nayi, “waalaikumu salam”ya gaidani, “amsa wa nayi don naji dadin gaidani da yayi kaf yaran gidan da suka shigo ba Wanda ya gaidani Koh sallama babu,

    Wai inji inji MAKAHO Mai mangoro aban abinci,

    Wani Takaici ne ya kamani Wai sunan sama da MAKAHO ake kira “shap wallahih bazaiyu ba watoh nima haka za’a na kwatantani da MATAR MAKAHO Ina bazaiyu ba” duk Araina nake zancen nan.

    Mikewa nayi na dauko masa basket in, basa nayi ya wuce

    azahar yayi Amma kaf yaran gidan ba Wanda yayi Haraman Sallah Nima bance musu kome ba, na mike na dauro Alwala na koma dakin Hijab na dauka na fitoh waje nayi sallah na kwanta a sallayan Ina Danna waya,

    Mutane Basu bar mini kofa ba har na Gama Tuwon dare na kwashe sukaci tukun suka fara watsewa daya bayan daya. Har suka watse suna fita na share dakina na goge, dakin Yayi kaca kaca sosai chanja zanin gado nayi yara sun kakama mini na jikin gadon da hannu yayi daud’a na fesa Turarukan daki na wanke dakalin kafun naji kofar yamin dama daman shekan iska Mai Dadi, wanka na shiga a gurguje nayi alwala na fada dakin na shirya nazo daukan turare Naga an min satan Mai Harda turare,

    Raina ya kara baci don na tsani mutun ya dauki abuna ban basa ba, na kudurta Araina bazan sake Basu wannan fuskan ba tunda basuda mutunci gobe ba shegen da zai shigarmin kofa😂( tab kofarki Koh na makaho) Kaya nasa na jona wayata a cherge da laptop duka,

    **na koma gefen gado na zauna

    tunani na shiga yi lallai rayuwa ba tabbas yau Koh mutun daya daga cikin dangina Koh kawaye, babu Wanda yazo. watoh tunda talaka na aura kenan,?

    alhalin duk wance tayi aure zuwa ake washe gari kallon gida da masu sallaman Amarya, a ranan. Amma ni ba Wanda yazo kallon daki ma bare sallama uhmm,

    Karfe biyar da rabi MAKAHO ya dawo gida da kwandon abinci a hannu sai sandar jagoransa da lalube yakai kulan kitchen ya aje, wanka yayi ya fada dakin Yana shiga na fita na basa waje ya shirya,

    Tana fita ya lalube Ghana must go insa ya dauki Kaya yasa ya fitoh waji lalube yayi ya dauki buta ya Kama alwala. ya wuce masallaci,don har an Tada sallah,

    **lokacin Nima sallah na Tayar ,Bai dawo ba sai da ya hada da isha’i Tukun ya dawo,

    *** abinci na zuba Masa
    ***na Koma Kan gado na zauna TV na kunna na kamo Tashar Arewa 24 Ana cikin Shirin kaddaran rayuwa. bayan ya Gama cin abincin, kwanukan ya dauka yakai kitchen hade da wanke hannu ya Sha ruwan Randa, ya shigo dakin,

    cikin lalube ya lalubo kujira ya zauna a hankali cikin magana Mai sanyi yace nagode da abinci yayi Dadi sosai Allah ya biya.” Amin” nace hankalina nakan TV,

    jawo laidar da ya shigo da ita baka yayi ya fitar da sabulu da omo. sai wata laidar mangoron yako, ya Miko mini ta inda yake tsammanin saitin nake,

    Cikin sanyin jiki da zullumin zata Amsa kuwa?

    Yace ga mangoro ba yawa

    ***ban gwatselesa ba na karba na mike naje na bude firij na aje.

    fita waje yayi, ya hada kayansa daya jika a ban daki da safe da Wanda ya cire dazun ya wanke ya shanya ya sake dawowa dakin yayi cikin magana d’ari..d’ari yace Koh Zaki kawo kayanki Mai datti na wanke miki,

    ***cikin mamaki nake kallonsa Wai ya wanke mini Kaya, lallai da wani idon Zan basa Kayana na fada a Raina, Amma a zahiri nace “ah ah na gode Zan bada wanki inya taru” baice kome ba ya lalube kujira ya zauna kawai yayi shuru ya kurawa TV da yake aiki ido kamar Mai kallo,

    ***abin har yaso bani dariya Amma na maze. muna zaune har goma, bacci na faraji,
    mikewa nayi na chanja kaya zuwa na bacci, kashe TV da glop nayi na Kara gudun fanka zuwa 3 Addu’a bacci nayi na shafa na kwanta,

    a hankali ya Tashi yaje ya rufe kofar duk Ina jinsa dawowa yayi kwanta, kwanta a kujira addu’an bacci yayi shima ya shafa.

    **Nima gyara kwanciya nayi,
    Tun daga jiya zuwa yau, a Takure nake Sam ban Saba kwana da namiji a daki ba, Amma ya zanye, dole na kwanta tunda daki D’aya ne bare na koresa falo.

    Misalin karfe biyu na dare ya farka………

    My WhatsApp number
    08084453785
    [9/27, 4:10 PM] +234 806 983 1049: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯 *
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌
    Free book🤧

  • Matar Makaho 6

    Matar Makaho 6

    Page6️⃣
    shanyan Kayana da sukaye datti harda zanin gado Ashanye a igiya an wanke harda kayan yayan Khadija (MAKAHO)

    Khadija na gani cikin kitchen, tana aiki,

    * a Hankali na daga kafata na Isa kitchen in,

    “Khadija kece akitchen?” da murmushi a fuskarta ta amsa mini da Aunty, Naga har Rana baki tashiba shine na daura Miki Abinci shinkafa da wake miyane ban Gama ba ya kusa,

    “Kayan nan fa waya wanke ?”

    Nice Aunty ta bani Amsa, *wallahih in banji Dadi ba nayi karya sosai naji yarinyar ta shiga Raina sosai da fara’a nace Mata” gaskiya Khadija nagode wallahih Amma aikin ya Miki yawa da baki wanke Kaya ba,

    La Aunty babu yawa fa kayan, ta bani Amsa

    “Khadija tashi muyi Sallah tukum tunda miyar kin daura a wuta”

    ..Toh Aunty

    Sallah mukayi, na sauke abinci na raba na zuba Masa na hada Kamar jiya, na Bata ta Kai Masa ” in kin Kaifa ki dawo Khadija” da toh ta amsa mini,

    Tana dawowa na iba Mana nida ita a plt daya, Muka zauna a waje munaci muna Hira cikin hiran nema nakejin ainahin sunan sa a bakin Khadija Ashe *Al’ameen* ne sunan sa saboda larurar da Allah ya daura Masa shine aka batar da sunan zuwa MAKAHO Kai duniya,

    “Tambayar ta nayi a gidan nan take”?

    Ah ah Aunty ni agidan Goggon mu nake ,

    “Har wani unguwa ne haka”?

    Ta bayan layin nan ne tsakanin mu ba nisa sosai Aunty,

    Sosai muke Hira Kamar mun Dade da sabawa,

    “Aikin dare na hanatayi nace ta Huta ni nashiga kitchen nakama girki*

    kin zama tayi dutsen guga ta dauka ta fara gogan kayan da ta shanya duk yanda na hanata sai da ta gogi,

    4:10 na yamma tace min zata tafi hanata, nayi sai da na Gama girkin abinci na sata tayi wanka Kayana na Bata cikin dogayen rigunana nakanti na Bata daya Dayake tana da tsawo sosai ya zauna Mata na hada Mata da gyele medium size kalar fulawar rigan,

    Sosai kayan ya karbe ta na hada Mata da Mai turare harda powder,man baki, da Jan baki biyu, maskaras da sauran kayayakina da basa cikin set na make-up kit Ina na babata daker ta karba sai godiya take min,

    *nayi nayi taci abinci dare Amma Taki,zuba Mata nayi a kula Taki karba sai da nace Goggo zata kaiwa kafun ta Amsa ta wace,

    Fitar Khadija sai da ta biya wajin yayanta sosai take basa lbrn abin arziki Dana Bata da irin sakar Mata fuska da nayi,

    Har cikin ransa yaji dadin daraja.masa kanwa danayi sosai,

    Hatta damuwar da ya fita da ita na safiya ganin yanda yau na tashi da zafi zafina abin ya tsaya Masa a Rai,

    Wannan abinda nama Yar uwarsa tilo da yafi so sai yaji zuciyansa wasai.

    Mangoro ya bata hade da naira dare ta rike a hannunta ya kara Mata nasiya sosai da hakuri A duk inda Allah ya ajita kafun ta wuce,

    *Khadija na fita wanka nayi nasa siket in kanti da t-shirt Mai kyau na daura gyele karami a kaina laptop na…..

    Sai kusan shidda ya dawo gida yauma da kwandon sa a hannu, da sallama a bakin sa *amsa Masa nayi, kaina nakan laptop, *

    Wanka yayi ya tafi masallaci yauma Bai dawo ba sai Isha waje na fita ganin yau ba NEPA, na fitar Mana da babban darduma na shimfida,

    *abinci na iba masa, nasa nawa na aje Mana tare da Masa Bismillah zama yayi shima Muka fara ci *

    Khadija ta tsanar Dani abin arzikin da kika Bata na gode, naji muryansa cikin sanyi sanyin sanan,

    Ba kome wallahih abinda ba yawa,

    Jin yanda na Masa magana a mutunce abin sai ya Masa Dadi sosai, mun Gama cin abincin har lokacin NEPA shuru na kasa shiga dakin saboda tsananin zafi da ake yau ga sauro,

    Tashi yayi ya fita yaje ya sai Mana maganin sauro, Yana dawowa na karba na kunna,

    kitchen na shiga na yaga caton in indomie, zanyi fifita dashe,

    * Wanka na sake shiga tsaban zafin da nake ji Kaya nasa vest sai wando Yale yale dogo har kasa,

    Kushin na dauko a daki na zuba akan cafet in na kwanta Ina fifita,Yana zaune a gefe shima ya jingina da jikin gini,

    Shuru mukaye dukan mu ba Mai magana,shikam tunani yake azaman da yaye da Sumayya ya fahimci Abubuwa cikin halayan ta,

    in Abu ya Bata Mata Rai, toh kowa ta shafa, in aka faranta Mata kowa zaiga fara’ar ta akwai ta da tsafta akwai iyya girki ga nutsuwa sam.bata da rawan Kai,

    *Har Sha biyu bamu shiga ba, ganin dare yayi ban tashiba ya mike a hankali yaji ya rufe kofar shashen mu, ya dawo ya shiga dakin ya cire kayan jikinsa yadau wando iyya gwuiwa sai riga Mara nauye , ya dauko filon kujira ya rufe kofar dakin harda k’wado key in yasa a cikin filon sa,

    Dawowa yayi ya tsaya a gefe cikin sanyin jiki yace “uhmm Daman Naga Kamar baki shiga daki ba kwanan waje zamuyi kenan?

    “Eh wallahih Amma tunda akwai maganin sauro”?

    Sake tambaya yaye in akwai wani abin kwanciyan a bani,Gefen dardumar na nuna Masa ya kwanta hade da furta” ita dayace” kwanciya yayi tare da Addu’an bacci, a hankali bacci ya dauke sa

    *Sai kusan karfe daya kafun bacci ya dauke ni da ker’

    Saboda rashin samun bacci da wure da bayi ba shiyasa yau Bai tashi yin sallar dare ba

    *Nikam ban sake sanin kaina ba sai asuba……..

    Ayi manage ba yawa😩
    Masu complain in page na kadan

     

    🪀My WhatsApp number
    08084453785
    [9/27, 4:10 PM] +234 806 983 1049: 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
    🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
    ~ Na ~

    🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

    ✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌

    🌿Jumma’at Mubarak to All my fan’s

    Free book🤧