Author: Novels

  • A Rubuce Take Book 2 Page 40

    A Rubuce Take Book 2 Page 40

    Part 02

    Page 40

    Jikinta yana rawa ta lalubi layin muneera don jin me widad ta haifa

    “innalillahi,na shiga uku” shine abinda hafsat ta samu kanta da fada bayan muneera ta tabbatar mata twins ta haifa kuma dukka maza,ta dinga safa da marwa cikin falonta kamar wata zautacciya,kamar kuma wadda ciwon naquda ya sameta,kuka takeyi wurjanjan,tana tsinewa widad a zuciyarta,yarinyar ta gama cutarta,cuta tahar abada,ta gama da rayuwarta gaba daya,haihuwa?,haihuwa tayi?,haihuwar kuma ta yara maza ma?,sai yaushe zata iya ruguza dukkan wannan ginin da widad tayi?,yaushe haqarta zai cimma ruwa?,rayuwa na qara tafiya,tana saqa widad din tana warware mata tana dawo da komai baya,ta gaji da wannan jiran gawon shanun,sai ta kira habiba ta fashe mata da kuka me cin rai ta fara gaya mata.

    Ajiyar zuciya ta sauke

    “Abinda nakeso dake kiyi haquri kawai,ko kowa ya kasa yi miki komai boka bagwaare ina mai imanin zai miki komai(wa’iyazubillah),saura wata daya kacal aikinka ya kammala,wallahi kinji na rantse miki,ko hajiya dake kabari inda zata dawo duniya tace masa yayi kaza wallahi wallahi naki zai dauka,kudade kika kashe bana wasa ba kin manta?, fiye da rabin jarinki kika bayar,ta yaya zan bari asara ta hauki?” Bayanan habiba sun sanyaya mata rai qwarai sun bata kuma qwarin gwiwa

    “Kedai abinda nakeso dake,kici gaba da lallabawa,ki sake ayi komai dake,yadda kome zaizo zaizo da sauqi”

    “Anya zan iya kuwa habiba?, zuciyata bata da wannan qwarin gwiwar”

    “Ke matsalata dake kenan, kwata kwata baki iya cinye jarabarki ba,wannan karon kuwa dole kiyi haka ko don amfanin kanki”

    “Zan jarraba in sha Allah”.

    Wunin ranar haka ya yishi babu wata walwala ko jin dadi,ranta a mugun quntace,a zuciyarta tanata fatan taji wani mummunan abu ya samu yaran kowa ya huta,duk bayan mintuna saita tsine musu su da uwarsu,amma cikin ikon Allah lafiya sumul widad ita da jariranta.

    Wannan karon ummu ce ta kashe kunya da kanta ta yiwo tattaki katsina,gidan widad din sai ya kasance kullum cikin jama’a yake abokan aikin abbas na nan katsinan,gashi kuma a gida take,garin ummanta,dangi tako ina barkowa suke barka ,haka daga kanon ma,wasu na zuwa barka,wasu kuma sai ranar suna sannan zasu iso,yara dai sunyo goshi sosai kamar affan,kowa yasan yadda twins suke da farinjini daman,widad din taga gata tako ina.

    Ko yaushe suna waya da abbas din da yakejin kamar yayi tsuntsuwa ya dawo,an katse masa hanzarinsa sosai,don bai gama kallon yaransa,iya kallo guda dayan da yayi musu qaunarsu sosai yakeji cikin rayuwarsa da ruhinsa.

    Komai ya sakar musu dai dai bakin samunsa,don yanzu babu abinda zaice da Allah sai godiya,hatta da hafsat da yara bai barta ba,sai daya gwangwajesu da dinkunan fitar suna na alfarma har kala uku,ta kalli kayan taja mugun tsaki ta nadesu a waje daya,wannan karon kam koda ba’a ce mata ba tabbas zataje suna,zataje kallon sunan widad na qarshe a gidan abbas din,zata je kuma ko don ta sake ganin yadda zata qara sawa bokanta ya qara tsanantawa da aikinsa.

    _batasan tuni qaddara tayi mata nata tanadin ba,tanadin da tabbas da tana da masaniya a kansa……da babu abinda zai kaita garin katsina_

    _hukuncin Allah,da kaf dube duben bokayen nata basu iso suka gano shi ba,hukuncin Allah TALALA mai kamar sake,lallai qaddarar kowanne nawa A RUBUCE TAKE_

    Ana ya gobe suna gidan widad din ya qara cika sosai da jama’a,ba laifi gidan yana da nashi girman,don haka kowa ya samu masauki da wajen zama,duk da dakuna biyu ne,nata dana baqi wanda aminatu ke ciki don na abbas a rufe yake,sai wasu dakunan guda biyu da toilet ta baya.

    A ranar widad ta gama komai,gyaran kai kawai ya rage mata,tayi wani mugun kyau na fitar hankali saboda yadda jegon ya fara karbarta tun a sannan,da safiyar ranar sukayi waya da abbas din yace ta bari sai azahar taje gyaran gashin,abun mamaki zuwa azahar din taji wayarsa,yace ta fito qofar gida ya miqata.

    Na’eema da marwa ta dauka, kowacce ta dauki baby daya suka fito,tayi kyau cikin maroon din abaya, fuskarta tamkar madubi.

    Tunda ta fito ya zuba mata ido yana kallonta ta madubi,ya lunshe ido sannan ya bude,yana tuna muryarta lokacin da take naquda,addu’o’i da salati kadai ke fita a bakinta cikin wani hali,ya sake gasgata lallai haihuwa ba wasa bace,duk dan a baibi uwarsa ba ba shakka ya tabe,hakanan duk namijin da bai girmama matarsa ba kodon darajar yaransu lallai ya cika abun zargi.

    Buda motar tayi ta shigo,suka hada ido ta saki murmushi

    “Amma fa ka shammaceni,shine baka gayamin zaka dawo yau ba?”

    “Bakiji dadi ba da kika ganni kenan?” Shagwabe masa tayi

    “Sosai ma uncle, Surprise fa kayimin”

    “Good me jego” a ladabce ta gaidashi,sannan suka gaisa dasu marwa da suka zama ‘yammata suma,ya tayar da motar yana tambayarta

    “To yaya?,meye labari?, Ya akaji da jama’a yan suna?,hope komai dai lafiya ko?”.

    Qasa qasa suke hirarsu cike da wani irin kulawa da juna,kosu marwa dake baya basajin me suke fada kamar masu rada,abinda yayi matuqat burgesu ya kuma tafi dasu,don basu taba ganin irin wannan soyayyar tsakanin miji da mata ba,sunfi ganinta ga saurayi da budurwa,amma yau anty widad da uncle abbas din sun karya musu record.

    A saloon din ya ajjiyeta sannan yace

    “Zanje na karbo dinkina gaba da nan,idan na tashi dawowa sai na daukeku mu wuce”

    “Tom,godiya nake sosai,Allah ya qara girma” ta fada tana dunqule hannu cikin salon jinjina da kuma rusunawa, murmushi ya balle masa,tana bala’in respect dinsa,ko meye zai hadasu bata kasa ganin wannan girman nasa.

    Yana ci gaba da tuqi yana murmushi,halaye da dabi’un widad din yaketa tariyowa,tun daga aurensu kawo yau,tana da sauqin kai da dadin mu’amala over,bata da fushi ko tsaurara abu indai ba bango taje ba.

    Ya isa ya samu tailor din ya masa halinsu,don a sannan yake qarashe hade dinkin,yana ganinsa ya rude

    “Sir…..ayimin afuwa yallabai,tuba nake” sai ya jawo stool ya bashi

    “Yanzun nan za’a kammala sir” bai zauna ba,yadai harde hannayensa a qirji yana dubansa

    “Kome zakayi ka dinga qoqarin cika alqawari,shine cikar kamalar mutum,sannan sana’arka,duk yadda ka riqeta haka take zamar maka”

    “In sha Allah sir” yaci gaba da qoqarin hada masa kayan

    “Ka zauna mana sir” ya sake masa tayin zama

    “Karka damu,qarasa aikinka” ya fada a nutse,don shi bayajin tsaiwa duba da yanayin aikinsa.

    Wayarsa ce dake aljihun trouser dinsa ta dauki ruri,ya saka hannu a hankali yana qoqarin cirota,yana duba me kiran kiran ya katse,saiya fara qoqarin kira sai gashi an sake kiransa.

    Hafsat ce,ya daga wayar a nutse ya kara a kunnensa

    “Kana ta wajen ina?,gamu a park kazo ka daukemu” ta fadi kanta tsaye cikin son nunawa wadanda take tare dasu lallai har yanzu itace da gwamnati,fiye da rabinsu jama’ar widad ne ta fahimci haka ta yadda suketa hirarta da fadan alkhairinta tun a mota,hakan ya sake hassala zuciyarta da wani mugun bacin rai.

    Cikin mamaki yace

    “Me ya biyo dake titi bayan na tura kudin ticket a siya muku keda yara,yanzun haka fahad inajin yana airport yana jiran saukarkuya dauko ku” baki ta tura gaba hadi da tura dankwalinta ma,haka kawai ga mota tana gani sai ta bari ayi asarar kudin a wani siya musu ticket,kudi ba dubu biyar ba ba goma ba

    “Kawai haka nafiso,na karba kudin ticket din nayi saving mayi wani abun dashi” yadda take masa magana a tsaitsaye yadan bashi mamaki,don tunda tayi kome ta danyi laushi

    “Okay,to yanzu haka ina cikin wani uzuri,ki kira fahad din ki kwatanta masa inda kuke sai ya daukoku” daga haka ya datse wayarsa shima.

    Sai yaushe zata bar son kudi?,yaushe zai saka doka ta daina karya masa kanta tsaye?.

    Sakato tayi da wayar a hannu,ranta yana mugun baci,batakai yabar duk abinda yakeyi ba kenan saboda ita yazo ya daukesu?,cikin wannan bacin ran ta kira fahad ta gaya masa inda suke din,wanda saboda dan nisan dake tsakanin airport din da station din sai daya dan dauki lokaci,sauran wadanda basuga amfanin abinda tayi din ba sukace tunda ba abun hawa na haya available na zasu tsaya wani jira ba sai kawai suka dauki taxi drop suka wuce suka barta ita da su baaba hassana ‘yan kanzaginta,sai da suka jima da wucewa sannan fahad ya iso,tayita masa bala’i amma yayi biris da ita bai kulata ba tunda ya riga yasan hali.

    Sai da aka gama hada masa dinkin sannan ya dawo ya dauki su widad,tuntuni an gama suna zaman jiransa ne ma

    “Ba komai,tunda dai ya gama alhmdlh” abinda tace dashi kenan sanda yake bata labarin abinda ya tsaidashi,shi kansa baiji dadi ba,don shima yana da baqi daga wasu garuruwan da sukazo masa saboda yana sanya ran zaiyi walima a goben kamar yadda ya saba kowacce haihuwa,haihuwar affan ce kawai bai samu yayi ba.

    Tunda suka isa gidan tana farfajiyar gidan a zaune ta kasa shiga ciki,kowa saidai yazo ya wuceta,tun a sannan hidimar da akeyi da yadda taga gidan ya fara tara jama’a ya tsaya mata a rai,kowa yana ciki yana huce gajiya harda su mimi,amma baqin kishi ya hanata sakat.

    Sanda motar abbas din ta shigo harabar gidan idanunta akai,baqin glass ne,bata lura da waye da waye a wajen a ciki ba sai da suka bude,su marwa suka fara fitowa sabe da yaran dake cikin wani lallausan blue din abun daukan yaran suka nufi cikin gidan,ta qurawa motar ido tanason ganin wadda zata fito,sai bayan kusan minti uku sannan widad din ta fito tana murmushi,da alama wata maganar sukayi da abbas din data bata dariya.

    “Kan abu ta kazar uba” hafsat ta fada cikin ranta,zuciya tayi mugun dibarta,batasan sanda ta isa gaban motar ba side din da abbas din ke zaune cikin wani mugun fushi

    “Ai dama odan bakayi haka ba ba kaine abbas ba,idan bakayi haka kai din ba namiji bane,dan kunama…..tabarmar qashi RIGAR K’AYA” ta da cikin madaukakin sautin da yaja hankalin mutanen cikin gida da sauran na farfajiyar wajen,ganin yadda hankula ke dawowa kansu bai saka ta fasa magana ba

    “Ni dana taho daga wata uwa duniya ka zubeni a station ka kasa zuwa daukata,amma ka dauki ‘yar gwal da danyen jego a gaban mota kana yawo da ita,kabi ka tattare a gindinta ita da danginta,kana musu wahala kana musu bauta……wallahi sai Allah yayi mana hisabi ni da…….”.

    Tsawar daya daka mata ta yanke sauran maganar,yayi wata irin fitowa daga cikin motar,Allah ya kissimawa widad ba za’a kwasheta da kyau ba,cikin gaggawa ta shiga tsakani ta dora hannayenta kan qirjinsa tanason yaja baya,ta tabbatar gamuwarsu da hafsat din ba zata taba kyau ba,batason kuma zuciyar nan data taso masa ta sanya ya biye mata ga mutane a wajen.

    ‘yan uwan abbas dake kusa ne suketa yima hafsat fada suna janyeta,ana tsaka da haka kiran dan auta a dakinsu baban abbas din ya shigo yana shaida masa sun bata kwatancen masaukinsu,sai ya kashe wayar yana huci ya juya ya koma cikin motar ya figeta ya fice daga gidan.

    Iska me zafi widad ta furzar,tabi hafsat da kallo wadda aka janyeta can bayan gidan

    “Barin hali sai mutuwa”ta fada tana mamakin halin halin tantagaryar hauka irin na hafsat din.

    Ranar gaba daya a birkice hafsat din ta yini,donma ‘yan kanzaginta suna dannarta,da qyar takai ga shigowa falon,saidai gaba daya a hargitse take.

    A yanzun widad din tafi qarfin raini,kuma tafi qarfin ta keta idanunta ta gaya mata maganar banza,uwa uba kuma tana tsakiyar danginta da hafsat din bataga alamun daukan raini ko wargi daga wajensu ba,haka ta yini har dare a falon tana qunsar takaici,saidai idan abun ya qume mata da yawa ta fita ta matse hawaye ta dawo.

    Har tayi shirin kwanciya abbas din ya shigo,har yanzu fuskarsa babu walwala,ta kalleshi cikin langabar da kai a shagwabe tace

    “Angon qarni babu fara’a, gaskiya ba kanta,abunma ko kyau baiyi maka ba” dole ta sakashi dariya,sannan ta gyara zamanta

    “Kaci gaba da haquri uncle don Allah”

    “Wanne haqurin?,haqurina ai ya gama qarewa……akwai abinda kuke buqata?,zan tafi masauki wajen baqi na” kai ta girgiza,don babu ce kawai basu da ita,ya tsugunna yayi kissing yaransa duka,harsu mimi da tasa aka debo mata suka kwanta gaba daya su bakwai kenan harda ita,da yake gadon babba ne ba wanda ya matsi wani.

    Har ya fita tana juya abun a ranta, zuciyarta duka ba dadi,batason bacin ran nan nasa,fatanta ko yaushe mummyn mimi ta gyara halinta ko zai samu nutsuwa.

    Dakin da su gwaggwo mero suka sauka ya leqa don ya musu sallama,baima san hafsat din tana cikinsu ba sai daya shiga,ya gama yi musu sallama ya miqe ya fice,sai hafsat din tayi zumbur ta dauki jakarta ta biyo bayansa.

    A tsakiyar falon ta cimmasa,tana riqe da qugunta,zuciya kuma na ingizata tace

    “Muje masaukin tare,acan nima zan kwana” wani banzan kallo ya watsa mata,yaja mata tsaki yayi gaba,saita sha gabansa cikin kuka

    “Wallahi na gaji da wanna wulaqancin da kakemin,kamar nima ba matarka bace,yau saidai duk abinda zaka yimin ka yimin,na gaji da wannan rashin adalcin” sosai zuciya ya ciyoshi,ya finciki jakar hannunta yayi wurgi da ita sai gata a bakin qofa

    “Na fiki gajiya,na gaji dake gaba dayanki,kije na sakeki saki daya,badai shikenan ba?” Wutace ta kawo mata ta kuma dauke mata a take,saita aza hannu aka ta kurma wata uwar kururuwa data zama tamkar shele ga dukkan wani me rai da yake gidan,shelar tata kuwa ta iske kowa,take falon ya fara karbar jama’a dake cikin gidan banda na harabar gidan da kunnuwansu baije wajen ba,a lokacin abbas ya jima da ficewa daga gidan yana jin kamar an zare masa qaya.

    Faduwa tayi tahau tirje tirje a wajen, gwaggwo hassana ce ta riqeta tana kiran sunan Allah kafin sauran su tayata riqe hafsat,tanata abu kamar wadda ke shirin hawa bori ko kuma tayar da iskoki

    “Ku cikani,ai kuna gani,a gabanku ya sakeni,saki uku kenan yayimin,saki uku kenan fa”.
    *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 42

    A Rubuce Take Book 2 Page 42

    Part 02

    Page 42

    Matashin ya sake gyara zamansa yana gyaran murya

    “Sunana AVM mu’awiya mani adam” da hanzari hafsat ta daga kai tana dubansa

    “AVM kuma?,air vice marshall kenan fa?,dama babban mutum ne shi din haka me muqami yaketa binta tana wulaqanta shi?,wato Allah yayi tana da rabo,da tayi wasa da damarta,saita gyara zama tana sakin masa fuska sosai harda murmushi

    “Ayyah,afwa yallabai,inata bata maka lokaci ko?,kasan komai sai Allah yayi” shima murmushin ya saki,da alama tarkon da ya dana yayi kamu

    “Ba komai,yau ai gashi zamu tattauna sosai” sakewa yayi yana bayyana mata waye shi da irin abinda yake dashi,cikin mintunan da basu gaza talatin ba taji ta gamsu ta kuma amince dashi,kuma lallai ta samu mijin auren da take fata wanda yafi abbas matsayi da dukiya,saidai ya nuna masa kyau,take ta bashi damar turo magabatansa,sukayi dan ciye ciye suka kuma sake tattaunawa,ganin shima din mawadaci ne sai bata boye masa komai ba ta gaya masa irin business din da takeyi,da kuma abinda ta mallaka yanzu haka,don ma tanata fama da ummanta dakeson ta hau kan kudin a dinga murqushewa,banda ta bade idanunta da toka zuwa yanzu Allah ne kadai yasan nawa za’a rugurguza,bayan kudaden abincinsu mimi da ake kawowa suke kashe mu raba,shi yasa taji ta matsu tayi aurenta ta samu inda zata sauke dawainiyarta ta daina facaka da kudinta.

    Sosai take kashewa kanta kudi,ita ala dole bataso aga ta canza bare ayi tunanin baqincikin barin gidan abbas ne yake damunta,idan tayi aure kuwa tunda ta samu mai farcen susa,zata tsula tsiyarta yadda taga dama,sai tasa widad taji ta muzanta.

    Ya jima wajen masu biyan kudi sannan ya qaraso wajen motarsa yana mita

    “Sai suce su basuson Dollar dole saida naira za’a biyasu,bayan ribarsu ne idan aka basu dollar din”.

    Kanta ya sake fashewa ta saki murmushi

    “Rashin wayewa ne kawai yake damunsu”

    “Wallahi kuwa,duk da haka saida suka riqe canji na wajen 5k” kamar ta juya taje ta karbo,amma sai taga kamar ajinta zai zuba,haka ta kanne sukaci gaba da tafiya.

    Tana tsaye tana jiran ya bude mata ta ciki motarsu abbas ta faka daga gefansu,tunda motar ta tsaya hankalinta ya dauku a kanta,don ba qaramin burgeta motar tayi baba jimawa ya bude ya fito cikin wani lallausan yadi da aka yiwa dinkin zamani.

    Mummunar faduwa gabanta yayi,abbas din ya canza yayi mugun fresh,ga qiba mai kyau daya hada,fatarsa ta qara haske,gaba daya qamshinsa ya cika wajen.

    Sanda madam widad kuma ta fito cikin wani fitinannen dinkin bubu sai yawun bakinta ya ida qafewa,abbas din ya sunkuya ya karbi sajjad daga hannunta,sajid yana wajen aminatu shida affan,sannan ya karba hand bag dinta ya riqe suka jera zuwa ciki.

    “Ina zuwa” tace da AVM mu’awiya tana komawa ciki da sauri saurinta kamar wadda tayi mantuwa,so take ta tabbatar da abinda idanunta ke gane mata,widad dince ta koma kamar wata basarakiya a fadar masarautun larabawa.

    Can ta gansu suna magana da receptionist din,tana dan jifan abbas din da harara,gurin zaben abinci ne,sun saba kuma irin haka,akwai saboda da fahimtar juna sosai tsakaninsu da ma’aikatan wajen,wani abu ya tsaye nata a wuya, tsabar hassada da baqinciki ya rufe mata ido,ta nufi gurin dason nuna musu itama cikin wadata take,kuma tare take da mijin zata aura

    “Hello” ta fada tana wani yatsina,tunda abbas ya waiwaya sau daya ya kalleta bai qara ba,a yadda yayi zaka tsammaci ranar farko ne daya taba ganin halitta me kama da ita,kuma basu da wata alaqa ko kusa ko alama,sai ya dauke kansa yanaci gaba da miqa musu atm dinsa kan su cira kudin

    “Takeaway zaku hada mana kawai,basai mun zauna ci a nan ba” abbas ya fada yana duban ma’aikacin,widad da ta yiwa hafsat din kallo biyu cike da mamakin yadda ta tsomale kamar dattijuwar kaza ta maida dubanta ga abbas tana mamaki,yace anan zasuci amma yanzu ya canza,batadai ce komai ba,dukkansu sukayi shuru sai.muryar hafsat daketa qoqarin mata kwaskwarima,ita ala dole ga ajebo.

    “Nice wadda muka zauna a wancan table din ni da AVM mu’awiya”

    “AVM mu’awiya kuma?” Ma’aikacin ya tambayeta cikin mamaki

    “Yes…..mijina da zan aura,akwai sauran 5k canjinsa dake wajenku…..idan ba damuwa zaku iya riqewa” junansu suka kalla cikin mamaki,saboda sudai sunsan indai wanda take magana akai ne da qyar ya cike musu balance dinsu ma,daya daga cikinsu ne ya girgiza kai

    “Aah,muba wanda muke riqewa canji,saidai idan bai fada miki dai dai ba,ko bakiji dai dai ba” fuska ta bata ganin suna niyyar yarfata

    “Me kake fada?,ya anyi muku alkhairi zaku saka ma mutane da sharri?”

    “hajiya wai me kike fada?,mufa ba wani canji a wajenmu,kije ki sake tambayarsa dai”

    “Okay,indai kuka sakani zuwa na dawo zaku gane kurenku,zaku gane da matar waye kuke musu” ta fada tana murza hannu,saita juya tayi hanyar fita tana taku dai dai,tanason murza power dinga a gabansu ko don yau ta hanasu barci.

    Jajantawa suke a tsakaninsu na abinda tayin,abbas dake tsaye yana jinsu yace

    “Inajin bata da hankali,ko damuwa ce tayi mata yawa” ya fada da salon shaqiyanci dariya tana cinsa yana dannewa,dubansa widad tayi da sauri ta galla masa harara

    “Hafsat dince bata da hankali?”

    “Oh…..wai dama kinsanta ne?” Yayi tambayar yana dubanta gami da dage dukka girarsa sama,sakato tayi tana kallon abbas din,sai kuma ta girgiza kai kawai,dai dai sanda suka juya suna barin wajen zuwa inda su aminatu ke zaman jiransu

    “Dama ai dole kace baka santa ba,kana kishi” wata dariya ce ta qwace masa sosai,ya dinga dariya yana duban widad din,bai tsagaita ba har suka shiga mota ya tayar da ita sannan yace

    “Bakisan tausayin wanda zai dauketa nakeyi ba?,niko a lahira horon da za’a yimin shine na sake zama da ita inuwa daya bare nan gidan duniya?,sam,haihata haihata,idan taso ta auri sarkin makka ma,ina mata murna,amma nikam abbas turaki har abada,ni kadai nasan me naji me na gani” shuru tayi tana girgiza kai cikin mamaki,wato mace na iya fidda kanta fit daga zuciyar namiji kenan,kamar yadda take iya kafa kanta kwatankwacin yadda ita tayi

    “Su mimi ne a raina,banajin zan iya ci gaba da bar musu yarana gaskiya,kullum haqurina sake qarewa yakeyi a kansu”

    “Yaushe zamuje ganinsu?”

    “Gobe……in sha Allah”

    “Yayi,Allah ya nuna mana” ta fada itama can qasan ranta da damuwa,Allah ya sani tana son yaran sosai,bataqi kuma a dawo dasu a mallaka mata su ba.

    Daren ranar kasa bacci gaba daya hafsat tayi,ta dinga zarya tana hango abbas da widad a idanunta,happy family,me zatayi wanda zai bata wannan jin dadin nasu?,bata samu hutu ba saida zuciyarta ta yanke mata abinda zata aikata musu,ta san yadda mata suka tsani riqo,musamman ma riqon dan kishiya,ba abinda zata cusgunawa widad din dashi saidai takai mata yaran,ta qara mata yawan aiki ta hanata hutu,wannan kuma tasan zaiyita hadata fada da abbas din,shikenan hankalinta ya kwanta.

    Da wannan shawarar ta kwanta, washegari kuwa tunda safe ta soma hada musu kayansu,har sun sanya uniform tace su cire,ummansu nata fada da mita

    “Dan hanyar samun alkhairin zaki toshe mana?”

    “Nifa aure zanyi umma,don haka yaci gaba da riqe yaransa,babu me masa wahala,yanacan yana holewa da matarsa mu ya barmu da raino” hakanan badon umman taso ba ta tasasu a gaba,ta sakasu a napep sai gidan abbas din kanta tsaye.

    Kusan kowacce safiya zaka samu gidan neat dashi,bama gidansu na katsina ba har na nan din,saboda basa kwanciya dama abar gidan da datti,har aminatu ta saba,ya zame mata jiki,duk inda takwas tayi ta gama komai,ta yi wanka ta yiwa affan din kansa wanka,saidai suyi wani abun daban kuma,kosu sake kwanciya bayan sunci abinci,ko suyi game na alphabet din arabic ko na english da dai sauran abubuwa masu amfani.

    Tsaye tayi a tsakiyar falon tana qare masa kallo,an tsara komai na falon daki daki bisa sha’awa da burgewa,hakanan ya samu cikakkiyar tsafta da kulawa,ba abinda yake fitarwa sai wani irin sassanyan qamshi da ya hade da sanyin ac din dake Parlor din.

    Muryarta ta ware cikin baqinciki ta kwarara sallama,aminatu dake daki ta jiyota,ta miqe ta fito tana riqe da hannu affan,hannunta daya kuma dauke da sajjad dake cikin wasu fafaren overall,ya cikata fam ma sha Allah,idan ka kalli yaran ba zakace twins bane ba.

    Tsaiwa tayi tana kallon hafsat din cike da mamakin ganinta a gidan,saita kalleta da harara harara

    “Ina mutan gidan?”

    “Antyn tana wajen daddynsu…..”

    “Na sani,dalla malama kiramin shi mai gidan” ido aminatu ta fiddo,tunda take dasu bata taba buga musu qofa ba ai,ba zata iya ba,barema dokar widad dince,indai ba wani babban abu bane ya faru basa kiranta idan tana tare da daddyn

    “Ba’a kiranta idan tana wajen daddy,kiyi haquri ki zauna ki jirasu,bari na kawo miki ruwa” ta fada cikin nutsuwa irin ta yarinyar tana sakin hannun affan,wanda mimi tayi caraf ta kamoshi

    “Qani…..ka manta ni ko?,ya naga kana kumatu,muji ko bread ka boye” ta fada tana dariya gami da fara lallatsa masa kumatun,yaron bashi da saurin mantuwa,ya tunata sarai,sai kuwa yahau bagala mata dariya,dukkansu sai suka matso kuwa,abinda ya qarawa hafsat takaici ganin yadda suka yanyame yaron dukansu cike da qauna suna masa wasa,ta daka musu tsawa,duk sai suka koma suka lafe.

    Sosai aminatu ta cika plate da kayan kaiwa baka ta ajjiye gaban hafsat dake tsaye,tabi kayan da kallo,rai naso amma kuma zuciyar ta hana,baqinciki qyashi da kishi mara amfani ya rufe mata ido,taso ta basar amma ta kasa,saita faki ido ta dauki lemo ta jefa a jaka,ta dan rarraba ido taga hankalinsu bai kanta,ta sake zarar wani abun ta jefa,tana kan jefa na uku ne qofar bedroom din abbas ya bude suka fito shi da ita,sai tayi sauri ta saki abunda ta dauka,saidai tuni sun gani,amma sai sukayi kamar basu gani ba.

    Riqe suke da hannun juna,perfect match couples da kowa ya kallesu sai sun bashi sha’awa,sanye take da wata rigar wani material da aka yiwa wani kyakkyawan dinki da ya zauna mata sosai a jiki,kanta ba dankwali sai sassalkan baqin gashinta me yauqi wanda kullum bata gajiya da gyaransa da yi masa style kala kala harda nasu bead,yau matseshi tayi cikin band ta kuma yiwa jelar kitso guda daya ta barshi yana yawo a bayanta,jikinta ba abinda yake sai fidda sassanyan qamshin turarukan jiki dana hayaqi data tsuma kanta dasu.

    Shima abbas din shirye yake tsaf cikin qananun kaya wadanda suka sake qara masa kyau da quruciya, hannuwansu cikin na juna,tana riqe da wayarsa da kuma takalmansa da baikai ga sakawa ba da alama wata magana suke me muhimmanci,don kowannensu fuskarsa dauke take da walwala,duk da kusan ko yaushe haka suke su din,zaiyi wuya kaga sabani a tsakaninsu.

    Kanta ta dauke kamar zatayi aman zuciyarta,saidai a fuska kuma bata nuna hakan ba,amma wannan yanayin ya bayyana har saman fuskar tata

    “Oyoyo mimin daddy,oyoyo nawwaraty…..a’ah ga baby yusra” widad din ta fada cikin farincikin ganin yaran,suka taho da saurinsu suka rungumesu duka har uban,sai ta sanyasu cikin jikinta sosai,tausayinsu yana ratsata,inama ace abban nasu zai bar mata su.

    Yana zaune yana gaisawa da yaran nasa daya bayan daya yana bincikar lafiyarsu ba tare daya dubi ko sashen da hafsatun take zaune ba,widad kuma na tsugunne gabansa tana sanya masa takalmi a qafafunsa,sun share hafsat din kamar ba ita a falon,tun bayan sannunku da zuwa da widad tace mata ta amsa da qyar sai itama ta watsar da ita,don a yanzun kuma bataga wani alaqa tsakaninsu ba bare ta dameta.

    “Yaranka na kawo maka,don nima aure zanyi” maganar data fada kenan cikin gadara,dai dai sanda widad ta gama saka masa takalman,sai ya miqe tsam ba tare da yabi takan maganarta ba yana fadin

    “Allah yayi miki albarka,zan fita amma idan na taho zan kiraki,karkiyi nesa da wayarki” ido ta lumshe tana gyada kai

    “In sha Allah daddy” har ya daga qafa saita tsaidashi

    “Kamar kai mummynsu mimi keson gani”

    “Ohhhh…..” Ya fada yana dan sosa girarsa

    “Yara ta kawo,kuma tayi abinda ya dace,shikenan ta ajjiyesu ta tafi,idan kuma akwai sauran wani damuwan ki wakilceni kawai dear,nasan zaki iya komai…..i trust you” ya fada yana jinjina kai fuskarsa kwance da murmushi.
    [26/05, 2:43 pm] +234 903 583 2936: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Gidan Aunty book 2 Page 10

    Gidan Aunty book 2 Page 10

    BOOK 2
    Page 10

    Da Sauri na ‘kara maida hankali na kan junior , daga nesa idan ka kallesa sak zaka ga tsantsan asalin balarabe, sai da ya matso da fuskarsa daidai inda tata yake kafun kamanninsa ya kara fitowa dukda kasan cewarsa yaro , amma sosai zaka hango tsantsan kamannin king, sosai suke kama , kamar tasu hartaso baci , banbancin shi junior har yanxu yaro ne , hatta yadda king yake kallan mutum haka shima junior yake , sosai suka d’auki pictures, sun d’anjima a Wajan kafun su kama hanyar komawa gidan bayan siyayyar da yah moh ya kaisu. Tahee na shigowa direct dakin ta tanufa sabida ba ‘karamin gajiya tayi ba , tana shiga wanka tayi kawai ta kwanta , amaimakon tayi bacci sai kawai ta fashe da kuka, Kukane take yinsa tundaga ‘kasan zuciyar ta , diamond ring d’inta da abun hannunta shima diamond da king ya bata take bi da kallo, lokaci d’aya kuma ta saki murmushin da dimples dinta suka lo’ba “ Ammi kin cucenii, kin rabani da farin cikina , why ? , me yasa “, ita kadai take tanbayar kanta,sosai take jin ‘kuna cikin ranta, yau ta kasance mata ranar farinciki da bakin ciki,sosai take sa’ke sa’ke cikin ranta , hannun da taji a kuma tunta ana share mata hawaye ta kalla , junior ne fuskarshi shi kamar zaiyi kuka “ Ammu me yasa kike kuka ?” Girgiza masa kai kawai taheee tayi wasu hawayen na ‘kara sakko mata , duk lokacin da ta kalli fuskar junior fuskar mijinta take gani, he’s eyes , mouth , cute face,he’s everything sak irin na king ne ,” Tohm ki dena kuka kinji “, ynxu ma kanta ta jinjina masa ta kasa magana , rungumeta yayi a jikinsa shima a hankali ya furta “ I love you!!!!!! Ammu”, a hankali ta furta “ Love you more and more my baby“. Kusan 3 minutes suna rungume da suna kafun da Sauri junior ya kalleta “ Ammu na manta, abinci fa zamuci grandpa yace na kira ki”, girgiza masa kai tayi “ Allah ya shiryeka son , bari na wanke fuskata sai mutafi”, tana kai karshen zancantawta wanke face d’inta tare da daukar junior kamar wani baby suka fito down stairs, gabaki d’aya kowa da kowa ya hallara tahee da junior kawai ake jira , kallan fuskarta Dady da momy sukai, duk da alamu ya nuna kuka tayi babu Wanda yayi magana , daman ta sabayin kukan , yau da kanta Mimi tayi serving d’insu abinci, tunda suka soma ci babu Wanda yayi magana sai junior da lokaci zuwa lokaci yake magana , suna kammalawa kowa ya bawa tahee gift ta zamowarta barrister , a nan d’in ma wani saban kuka ta fashe da shi, sun d’an jima a Wajan kafun dady ya mike , momy ta bi bayansa , yayi saura tahee da Mimi, daman yah moh shiya fara futa da junior.

    *********
    ***************
    **********
    ***************

    FLASH BACK

    Tun lokacin da tahee ta dawo Uk wajan Alhaji isma’il suka cigaba da kula da ita, tun tana kin sakewa dasu har ta fara sabida yadda ko wannan su yake janta a jiki, A bangaran momy ma sosai take bawa tahee kulawa kamar ‘yar da ta haifa da cikinta kome zatayi wa mimi shi zatayiwa tahee, sosai suke bata kulawa babu me nuna mata banbanci, kullum momy cikin dubata take kasan tuwarta kwararriyar Doctor . Shima yah moh kullum cikin siyo mata kayan kwad’ayi suke shi da dady. Gabaki d’aya family sai suke bata kulawa ta musamman. Lokacin da dady yakezo sa tahee a makaranta ta wayarta da baba Malam ya basa yayi anfani ya Fito da soft copy din makaranta dake cikin wayar, duk da yar hanzu be fad’a mata wayar na hannunsa ba . Koda sukaje school sabida kokarin ta yasa aka za tayi iya tafiya university, sosai tahee tayi farinciki da hakan, take a Wajan ta cike ‘bangaran law department, mimi ta cike nursing, haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin ahalin kullum tahee da tunanin a halinta take kwanciya take tashi , fatan ta Allah yasa suna cikin ‘koshin lapiya. A haka rayuwa tacigaba da tafiya da tahee tana samun kyakkyawar kulawa daga mutanan gidan , mimi ma sosai take janta a jikinta har soyayyar da suke wa juna tayi ‘karfi, lokacin da tahee ta fara labour gabaki d’aya family babu Wanda hankalinsa be tashi ba amma cikin iko na ubangiji ta sum’bulo d’anta kyakkyawan gaske fari tass dashi kamar ka ta’basa Jini ya zuba sabida kyansa, hatta Doctor d’in kowa ya gansa sai ya furta “ the baby is so beautiful” basu wani dad’e a asibitin ba aka basu sallama suka koma gida , gabaki d’aya familyn momy saida sukazo hatta wata sister d’in momy Itace tayiwa tahee wanka sabida yanda suke ‘kaunarta suma musamman da momy ta basu labarinta . Sosai dady da yah moh suka nuna bajintarsu ranar sunan kamar d’ansune ya haihu haka akayi tafi nagani na fad’a , baby da maman baby sosai suka tara gift sbd yaro yayi goshi sai san barka . Hatta friends d’inta na school wasu duk sunzo mata , ranar suna yaro yaci suna mohammad , Sabida shine sunan da kullum king yakece mata yanaso ya sa wa babynsu, sai suke masa la’kabi da junior .kullum momy da mimi ne suke kula da junior , har yaro yayi wayo sabida baiwar saurin fahimta da yake dashi, a haka tahee taci gaba da karatunta har zuwa ynxu da ta kammala karatunta amatsayin barrister.

    ??????

    BACK TO STORY

    Karfe 9:30 na dare dady yabu ‘kaci ganawa da kowa da kowa na cikin family d’in, gabaki d’aya taruwa sukai cikin babban falon dady, lokacin junior na jikin momy yana bacci , taro dady ya bud’e da addua bayan salatin annabi da sukayi, shiru dady yayi yana juya maganar da zaiyi , itama momy shiru kawai tayi batace komai ba , gyaran murya dady yayi kafun ya soma magana , “Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah , ina ‘kara gode wa Allah da ya bani ikon ganin ranar nan, ha’ki’ka nayi farincikin kammaluwar karatunku, ina ‘kara gode wa Allah, sannan ko wannan ku gift d’insa da na basa yana wajan momy a Wajan ta zaku karba , abi na biyu kuma maganata akankine tahee,” lokaci d’aya zuciyar tahee ta buga jin ya ambaci sunanta, amma bata ce komai ba sai ‘kasa da ta ‘karayi da kanta.Ba sai na maimaita abunda suka faru shekaru bayaba, amma yanxu lokaci yayi da za’a wuce wannan ga’bar, lokaci yayi da tabon mutanan da suke cikin‘kuncin ya goge, ko ba’a fad’a ba nasan kinsani junior ya fara wayo, yana bu’katar sanin mahaifinsa, yana bu’katar salin ahlinsa, ke matar aurece na tabbata Indai mijinki na raye to tabbas yana cikin kuncin rayuwa, mahaifiyarki tana cikin bakin cikin rayuwa haka ma d’an uwanki, lokaci yayi da zamu koma Nigeria gabaki d’ayan mu. Ba tahee data d’ago kanta ba hatta yah moh a mugun firgice ya kalli dady kansa na sara masa , cikin zuciyar sa ya maimaita “Nigeria ?”, kamar dady yasan me yake fad’a ya ‘kara maimaitawa “ eh Nigeria, Nan da 2 weeks duk Wanda yasan yana da abunyi yayi kafun nan da 2 weeks dan tafiya ba fashi “, idanuwan ya moh har sun fara yin ja, itama tahee da wani irin shock take maimaita Nigeria cikin zuciyarta. Wata waya ya ciro daga cikin aljihunsa tare da wani ‘karamin hoto da ya fad’i batare da sanin saba , wayar ya mi’kowa tahee “ Nasan bazaki manta da wannan wayar ba ko? Sabida tare da ita aka sameta cikin aljihunta”, ita tahee kuwa gabaki d’aya bata san me yake cewa ba , hankalinta yana kan hotan da ya fad’i a kasa , hakanan zuciyar ta take san ganin hotan, saida dady ya ‘kara kiran sunan ta kafun ta saka hannu zata kar’ba wayan ya su’buce mata a hannu sabida bud’ewar da hotan yayi ita kuma wayar ta gangara inda yah moh yake, da Sauri tahee ta d’auki hotan zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri , gabaki d’aya sai suka maida hankalinsu kanta, kallan Alhaji isma’il tahee tayi kafun ta mayar da hankalinta kan hotan, shima a Daidai lokacin da yah moh ya d’auki wayar tahee da ta fad’i, cikin wani irin zabura tahee ta furta “Oumma?”, da sauri Alhaji isma’il ya mi’ke tsaye yana ‘ko’karin yin magana wayar tahee tayi haske, cikin wani irin shock yah moh ya mi’ke take a wajan ya soma ganin jiri jiri na d’ibarsa , babu abunda yake maimaitawa sai “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”, nuna wayar tahee kawai yake yana ja da baya ga juwar da take ‘ko’karin kayar dashi , mimi har ta soma kuka babu abunda take fad’i sai yaya moh , meke damunka” . Ga baki d’aya sai abubuwan yaso d’aurewa dady kai musamman Wayar tahee da yah moh yake nunawa, kamar daka sama ya furta “ King” da ‘karfi, take a wajan kuma ya sulale ‘kasa . Da sauri dady da su momy suka nufa inda yake, tahee kuwa kasa ‘karasawa inda yake sai fuskarsa da ta tsurawa ido, kusan 2 minutes tana kallan fuskarsa kafin cikin shock ta mayar da kallanta kan junior dake bacci, sosai tashiga rud’ani kanta itama ya soma juyawa take a Wajan itama ta sulale. Tashin hankalin da ba’a sa masa date, sai suka rasa kan wa zasu tahee data suma ko yah Moh daya suma , babu abunda dady yake furtawa sai “ruwa ! Ruwa !” Da Sauri mimi ta nufi kitchen , cikin ‘kan’kanin lokaci ta dawo d’auke da bottle d’in ruwa guda biyu, momy ta karbi d’aya shima dady ya karbi, ruwan suka shafamusu gabaki d’aya suma sun rikice ganin abunda yake shirin faruwa . Tahee ce ta soma ajiyar zuciya har yanxu hotan data d’auka yana hannunta ta ru’keshi gagam. Yah moh kuwa har yanxu baya motsi abunda ya ‘kara tayar da hankalinsu, abunda ya bawa kowa mamaki, tahee tana farkawa inda yah moh yake a kwance ta zube tana fashewa da wani saban kuka , cikin murya kuka take furta “ Na ro’keka katashi, katashi dan Allah”, kasa magana dady yayi ganin irin kukan da tahee take ,sai abu yaso had’e masa ga momy data tayar da hankalinta ga mimi itama da take masa kuka, a ‘bangaran tahee ma gashi tana bashi tsoro ganin yadda take kuka akan Moh ya Tashi. Yana kara fesawa yah moh ruwa , ya fara motsi a hankali, bakinsa babu abunda ya ke am bata sai “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un “. Temaka masa dady yayi ya zauna sosai , da sauri tahee ta d’auki wayar tata tana nunawa yah moh, cikin rawar murya take nuna masa wayar , da ‘kyar ta samu bakinta ya furta “ yaya king” sannan ta nunasa a hankali kamar tana tsoran magana ta furta “ Akhieee?” Shima
    Fuskarsa gabaki d’aya tayi jawur bakinsa yayi nauyi ya kasa cewa komai sai d’an motsa mata kai da yayi alamar eh , murmushi da hawaye tahee ta fara lokaci d’aya sai momy da dady da kuma mimi suka zuba musu idanu gabaki d’aya sun kasa magana , maganar yah moh ne ya ‘kara rikitasu da ‘kyar ya kalli tahee kafun ya nuna junior dake kwance yana bacci, sai kuma ya nuna wayar hannunta “ junior !? Is my son”,murmushi tahee ta sakar masa tana d’aga masa kai , duk da haka sai da ya ‘kara furta “ junior is my brother’s son? ‘Dana ne ? ‘Dan king d’ina ? My dearest brother is now a father ?finally zan ‘kara ganin king d’ina ? Ummey? Abeey?Samreen? Dada?” Kai kawai tahee ta d’aga masa dan gabaki d’aya ta kasa magana , Sabida farincikin da ta shiga “ her lovely husband zai ‘kara samun farinciki? Wana irin farin ciki zai shiga idan ya ga brother d’insa , together with his wife and his baby?” Duka wad’an nan tanbayoyin kanta tahee take yiwa . Dakatar dasu momy tayi kafun ta furta “ kunsa mu cikin duhu, daman kun san junane?” Lokaci d’aya suka girgiza mata kai alamar a’ah . A sanyaye , dady ya furta “ kuyi mana bayani yadda zamu gane amma kafun nan inaso na tanbayeki tahee, naji kinkira matar cikin wannan photon da oumma ko kinsan me kama da ita ne?”. Sai yanxu hankalin tahee ya dawo kan hoton tana sakin murmushi, Oumma tace tare da brother d’inta da ya ‘bata “ da Sauri dady ya kalleta tare da nuna hotan “ oumman ki? “ yanxu ma kai tahee ta jinjina masa murmushi kwance a kan fuskarta. “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” cewar dady, hotan hannunta ya nuna sannan ya nunata , a hankali ya furta “ ke.. ke yar maryam ce ?”, dukda tahee tayi mamakin yadda yasan sunan oummanta hakan be hana ta amsawa da “eh” wani irin farin cikine ya kama dady har ya kasa ‘boyuwa akan fuskarsa “ Alhamdulillah!!! Alhamdulillah!!” Kawai yake furtawa , kallan momy dady yayi itama da take murmushi “ ina tare da Jinina tsawan lokaci Amma ban sani ba ?” Da Sauri Mimi ta furta Dady wacce ?”, farin cikin da ya dad’e beyi bane kwance a fuskar dady , amsawa Mimi ba sai ‘kara kallan tahee da yayi sosai , tabbas tana kama da maryam d’insa , alama yayi mata data matso, ba musu kuwa ta matso d’in hotan hannunta ya kar’ba kafun ya nuna mata oummanta , “ Maryam ‘kan wa tace , nine nan a kusa da ita “, yanxu ma su mimi zubawa sarautar Allah ido sukai har yah moh kallansu yake lokaci zuwa lokaci yana sakin murmushi idan ya kalli junior . Nunasa tahee tayi kafin ta nuna hotan , a hankali ta furta “ uncle isma’il?”, murmushi ya sakar mata sosai yana jinjina mata kai , cikin farin ciki ya furta “ Allah ya ‘kaddara zan ‘kara ganin ahalin Maryam Alhamdulillah, yanxu dare yayi zamu tattauna gobe da safe “, badan sun soba duk suka mi’ke dan gabaki d’aya baccin ya gudu sabida farinciki, kallan tahee ya moh yayi , kafun ya kalli junior “ please ki barshi yau a waje na “, dariya yaso bata kamar yau ne suka soma kwana tare kanta kawai ta d’aga masa , itama fuskarta cike da murmushi ta furta “ bari na d’auko kayan baccin sa “, kafun ta ‘karasa ma Mimi har ta hau sama taje d’auko masa , d’aukan junior yah moh yayi , Daidai lokacin da Mimi ta dawo d’auke da kayan sa, mi’kawa yah moh da yake binta da d’an kallo kawai tayi, har yanxu kanta a tushe yake , ganin komai take kamar a mafarki , jira take kawai gobe tayi . Gabaki d’ayansu kowa goodnight yayi wa junansa kafun su nufa d’akunansu, yau Mimi d’akin tahee ta nufa , lokacin da suka kwanta Mimi sai kallan tahee take har hakan yasa ta tsargu , d’akawa Mimi duka tayi “ wannan kallanfa?” Murmushi Mimi tayi kafin ta sha gefan fuskar tahee , a mai makon ta amsawa tahee tanbayarta “ ban ta’ba ganin farin ciki sosia haka a fuskar dady ba , ya dad’e yana neman ku, da ya samu free time zaice zai tafi Nigeria , wani lokacin har kishi nake , sai na dunga tunanin ko dady yafi sansu akan mune ? Amma yanxu sosai nake farinciki, finally Nima naga familyn dady na “d’an harararta tahee tayi wato da mu kike kishi?” Murmushi kawai Mimi tayi mata , shiru tahee tayi kamar me tunani kafun ta furta “ Yah moh fa”, juya mata baya Mimi tayi tare da kashe light d’in dakin kafun ta furta “ good night, ni bacci nake ji”, dariya ce ta so su’buce wa tahee Amma tayi ‘ko’karin dannewa so take washe gari Kawai tayi, “ one side d’an uwan mijinta da kowa yayi tunanin ya mutu, the other side yayan mamanta.”, a hankali yadda Mimi bazata ji ba ta furta “ ya Allah ! Allah ka bayyana mun su , ko zan ‘kara ganin farincikinsu. Gabaki d’aya ahalin gidan sai kowa ya kasa rintsawa kowa da abunda yake sa’kawa aransa , yah moh tunda suka kwanta yake bin fuskar junior da kallo lokaci zuwa lokaci yana kissing forehead d’insa.

     

    ????????
    ??????????

    BUNKURE

    ????GIDAN AUNTY ????

    07041879581
    MSS LEE ??

    LEESHARH DATA HUB

    BUY DATA AT AFFORDABLE PRICE:

    MTN AIRTEL
    500mb-120. 500mb-140
    1gb-240. 1gb-300
    2gb-440. 2gb-600
    3gb-620. 3gb-900
    5gb-1200. 4gb-1200
    10gb-2200. 5gb- 1500

    Validity : 30 days

    ACCOUNT DETAILS :
    2681892316
    AISHA UMAR , ZENITH BANK .

    For more information contact me through my phone number: 07041879581.

  • Gidan Aunty book 2 Page 2

    BOOK 2

    Page 2

    NIAMEY , NIGER

    Cikin wani madaidaicin gida motar da tahee take ciki aka bud’e gate, Daidai madaidaicin harabar wajan da mota zata iya tsayuwa akai packing. Matar ce ta fara fitowa ganin tahee bata motsa daga inda take bane Yasa matar ru’ko hannunta suka fito tare, babu kowa a wajan har matar ta bud’e kofar falonta suka shiga ciki ita da Tahee, cikin sakin murmushi ta kalli Tahee” kiji rani ba dad’ewa zanyi ba kinji”, ta fad’a tana kallan Tahee da kwata kwata batasan me take ba,”Kara maimaita mata matar tayi tare da nufar cikin bedroom d’inta har da saka key, da sauri tayi dialing wata number da bugu biyu aka d‘aga kiran cikin ‘kasa ‘kasa da murya ta soma magana “ kuna ina? “ banji amsar da aka bata ba saima ‘kara ‘kasa ‘kasa da murya da tayi “ Nasamo babban kaya yanxu, nasan ‘kungiya ba ‘karamun jinjina mun zasuyi ba sabida yadda suke bukatar akawo musu kayan na samu, yanxu haka tana falan gida na , zan yi ‘ko’karin duk yadda zanyi na ajjeta agidan nan zuwa gobe ,” banji me aka ce mata ba sai ma jinjina kai da tayi “ idan hakan zai samu babu matsala , amma kunsan mutane da sa ido kuma saura kwana 4 ayanka mutane goma da ake bu’kata , yanxu me muke jira tunda na samo cikin ta gomar?”shiru tayi tana sauraran abunda ake ce mata , cikin ‘kara ‘kasa da murya ta furta “ ba matsala ku hanzarta, na barta a falo karta ji ni shiru “, tana kai ‘karshen zancenta ta kashe wayan tana sakin murmushin farinciki, abayyane ta furta “ Tsuntsu daga sama gash she , fridge d’in d’akin ta bude tare da d’akko wani exotic me shegen sanyi, hand bag d’inta ta bude ta ciro wani allura , a cikin lemon tayi wa allura kafun ta ‘kara jijjiga lemon, fuskarta ta daidaita tare da fitowa daga d’akin.gaban tane ya fad’i bata san lokacin da ta yar da leman hannunta ba , duk da girman da jikinta yayi mata hakan be Haka ta yin gudu ba , ban d’akin falon ta duba wayan babu Tahee babu alamarta, da sauri ta fito harabar gidan nan ma babu kowa gashi bame fadi ne da itaba ballantana ta tanbayeshi, wayarta da ta soma ‘kara ce ta d’auka sai faman hard’a gumi take , bata jira me za a ceba tayi saurin bud’e kofar gidan ta , motar data gani ta nufa cikin Sauri, ba kowa bane face su wizi da ke cikin motar kowa kagani fuskarsa a cin kushe tun lokacin da suka nemi Tahee suka rasa , zu’kar sigari wizi yayi kafun ya furta “ Hajiya ina kayan suke , kinsan fa gobe za a fitar dasu “, a rud’e hajiyar ta soma duban hanya “ wizi ta gudu, ta gudu kuyi Sauri ku dubata nasan batayi ni saba “, cikin matsiyacin gudu driver ciki ya tada mota suka soma duba layin ko zasu ganta.

    Adaidai lokacin da suke nemanta ,ita kuma ta dad’e da yin nisa hawaye sai faman sakko mata yake akan fuskarta , ita kadai sai faman tafiya take ga duhu da ya somayi sosai , hannunta d’aya dafe da cikinta. Wasu manyan ba’ka’ken motoci ne guda uku Suka wuce , sai kuma ta dawo Daidai inda take sukai parking, wasu kamilallun mata da mijine suka fito cikin motar dattawa dasu, sai masu tsaran lapiyar su dattijuwar matarce ta matso inda take tahee take ,
    “ baiwar Allah ya naganki, akan titi ke d’aya sai faman kuka kike “ shiru tahee bata ce mata komai ba sai tafiyarta data somayi, dattijan mutuminne ya saki murmushi kad’an , “ ai bazata baki amsa ba “, da mamaki matarsa ta kallesa , shima kallan nata yayi yana jinjina mata kai alamar Hakane abunda yace kafin ya duba agogan hannunsa , “ dare yayi sosai mu tafi da ita gida , insha Allah ko zuwa gobene sai asan abunyi amma barinta anan zai zama illa agareta da abunda yake cikinta “, cikin gamsuwa matar ta jinjina masa kai kafin ta kama hannun tahee da ke kokarin tafiya suka tada motar sai unguwar Francophone dake cikin Niamey , sosai babbar unguwace da ta tara manyan mutane sabida gidajen da suke wajan ya isa ya tabbatar wa mutum haka , wani soja ne ya bud’e musu babban gate d’in gidan Daidai parking lot motocin sukai parking, cikin dattako matar nan tafito hannun ta d’aya rike da na Tahee da har yanxu bata dena hawayeva, matar ta juya daniyar nufar part d’inta da Tahee amma mutumin ya hanata, cikin kamilalliyar muryarsa ya nuna mata wani part “ ki kaita d’akin maganina “, toh kawai tace masa tare da nufar wani madaidaicin flat, dattijan nan na biye a bayanta , duk yadda akai da tahee akan tashiga kin shiga tayi saima ihun da ta fara yi a gigice da Sauri matar ta damki hannunta ta shigar da ita, kafun tayi wani motsi Tahee ta saka ihu tana neman hanyar fita , “jeki kira mun Isma’il, bai jira amsarta ba ya kunna wani hayaki da yasaka Tahee zubewa ‘kasa tana sakin nunfarfashi kamar ranta zai cire , cikin kankanin lokacin wani farin magidancin buzu yashigo d’akin bakinsa d’auke da sallah, yana ganin Tahee zuciyar sa ta buga , wani irin yanayi na taso masa , danne wa kawai yayi kafin ya ‘karasa wajan mutumin “ baba Malam Ance kana ne mana “gyada masa kai tayi tare da nuna masa wasu turaruka “ su zaka had’a” cike da girmamawa kuwa ya had’a turarukan da ya cika d’akin da hayaki har wani irin rawa jikin tahee ya soma bata soma zabure zabure sai lokacin da aka saka karatun Alkurani, ‘kara ta somayi kamar me aljanu cikin wani irin murya ta soma magana “ ku tsaya, ku tsaya karku ‘konani , ku tsaya “, basu tsaya d’Inba sai ma wani magani da isma’il Yasaka ,cikin shakewa ta cigaba da magana “ ku tsaya , ku tsaya “, cikin tsawa baba Malam ya furta “wanene ya aikoku, me yasa kuka shiga jikinta”, shiru Tahee tayi , suma su baba malam karatun suka cigaba tayi saurin da katar dasu “ Munshigq jikinta sabida muzubar mata da cikin jikinta ne , mu hanata zaman lapiya “, a kan me ? Baba Malam ya tanbaya “ cika aikine kawai namu bama tanbayar dalili”, murmushi baba Malam ya saki “ tafiyarta kuma fa “, nan ma kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta bud’e bakinta “ wannan ba mu mukayishiba wacce tayi mata asirin ce ta binne da kanta ,”Menene illarsa “bama fadar…..”, be karasa ba baba Malam ya daka matsa tsawa tare da cigaba da karatun sai da ya tabbatar ya jigata kafin ya soma amsa masa tanbayoyinsa “ bazata taba zama a kusa da kasar da take ba Sabida asirin da akai mata “, yanxu ina umartarka daka fita daga cikin ta yanxu, idan ba haka ba zan ‘kona’ka da ayoyin Allah”,gardama yasoyi Baba Malam ya soma karatun alkuraninsa hankali kwance shi kuma alhaji isma’il yana kara saka turaran wutar maganin ? Cikin azaba ya furta zan fita , zan fita “, sharesa baba Malam yayi sai da ya saka karar azaba Sabida yanda jikinsa ya soma konewa “ zan fita , zan fita “. Yana kai karshen zancansa sai Tahee ta soma atishawa, sai da tayi atishawa kusan sau uku kafin bacci ya d’auketa a Wajan , kallan tahee alhaji isma’il yayi abu na fad’o masa arai amma yayi kokarin kawar da hakan lokaci zuwa lokaci yana kallan fuskarta , take a wajan tahee ta shiga ransa .

    Gyaran murya baba Malam yayi, dare yayi sosai ya kamata muje mu kwanta , kallan wajan da tahee take Alhaji isma’il yayi, shima baba Malam ita d’in ya kalla kafun ya saki murmushin sa na dattako “ su Ameerah zasu kwana da ita , zuwa safe sai muga abunda Allah zaiyi”, cikin gamsuwa Alhaji isma’il yayi wa baba Malam sallama , shima baba Malam wasu yan mata ya kira a waya suka canzawa Tahee d’aki.

     

    NIGERIA

    WASHE GARI

    Haryanxu babu irin neman da ba a yiwa Tahee ba amma babu ita babu alamarta atta ma’kotan da suke kusa da Lagos sai da Abeey ysa aka bincika , sosai abeey ya saka kud’i akan neman Tahee babu inda ba a dubaba ba’a sametaba, hatta airports sai da aka bincika amma batanan . A ‘bangaran king ma har lokacin be farka ba yana cikin coma abunda ya ‘kara tayar da hankalin mutanan gidan , tsakanin mahma da ummey kuwa sai aka rasa wanene yafi kula da king , dan a wannan karan ummey kunya ta cire ta dunga kula da d’an ta , momy taji dad’in abinda ummey sukeyi sabida wani dalili nata , kusan suma a asibitin suke yini, su sumayya ma ko wa kagani zakaga irin damuwar dake kan fuskarsu, kabeer da haroon ma kusan suke kula da gidan yanxu . Sosai hakan ya ‘kara ba’kanta ran Ammey da har zazzabi saida tayi, atunanin mutanan gidan Sabida halin da king ya shiga ne da kuma ‘batan tahee , amma a zahiri sam ba hakan bane , tsantsan bacin rai ne da bakin cikin bata ‘karasa hallaka king ba gashi babu damar hakan sabida yadda mahma da ummey suka tsaya akansa ga dada da kullum cikin rubuto masa rubutu take ana shafa masa , Hakan kuma ba ‘karamin barazana bace a gareta.

    ????

    UNITED KINGDOM

    Momy zaune cikin akan kujera jikinta sanye da Abaya da yayi mugun yi mata kyau, Mimi ce ta zakka a guje daga kan steps tare da d’anewa jikin momy har saida ta tsorata , cikin fad’a momy ta tureta “Mimi meke damunki, baki da hankali ne Yaushe zaki dena jin magana ? Ban hanaki wannan guje gujen ba ? “, a shagwa’be Mimi ta turo bakinta “ Haba momy , rungumeki fa kawai nayi amma duk kin tsorata “,’karamin tsaki Momy taja “ banga lokacin da zakiyi hankali ba Mimi , bari ya yanki ya dawo, aure zan sa ayi miki da driver ko kinyi hankali “, a zabure Mimi ta mike tsaye tana bubbuga ‘kafa fuwanta “Haba , Haba momy wai me yasa ni kike mun haka kullum, gaskiya ni yanxu ba ‘kyaso na bari dady ya dawo , ni bansan me nayi miki Haka ba sai kace ….”, bata ‘karasa maganar taba sabida tsawar da aka daka mata , da Sauri ta juyo tana kallan Wanda yayi tsawar a tsorace , kyakkyawar guy ne fari tas dashi kamar ka tabasa Jini ya fita , kyakkyawane shi sosai , kyawawan idanuwansa yabi fuskar Mimi da kallo da take ‘kokarin ‘buya a bayan momy,” fito “ muryar kyakkyawan guy d’in ta ratsa mata kunnuwa , a ra’be ta fito daga bayan momy kamar mara gaskiya , murmushi momy ta saki tana nufo inda yake “ wannan bazata haka son , kace mun sai anjima zaka dawo”, murmushin da ya saka jerarrun ha’koransa fitowa yayi,” nayi kewar kune momy shiyasa ban bari Daren yayi ba “, murmushi ta sakar masa tana karban trolley d’in sa,” yanxu dai ka fara yin wanka son , kafun nan sea kaji abinci “, yanxu ma murmushi ya sakar mata “ okay ma”. Har ynxu Mimi na inda take ganin ya’ki kallanta kamar zatayi kuka , shima bece mata komai ba yayi wucewarsa,da Sauri ta ‘karaso Inda momy “ Bro ya’ki kulani please ki bashi hakuri”, hararar ta momy tayi tabar wajan , fashewa da kuka mimi tayi , da gudu ta nufi d’akinta Asama tare da saka masa key.

    Har guy d’in ya fito sanye da wasu kayan alamar wanka yayi mimi bata fito ba , tsakanin shida momy babu Wanda ya tanbaye inda take har ya kammala cin abincinsa, kallan momy yayi “ Ina Mimi momy”, wani saban murmushi momy ta saki, “Dakar barta ai Son , nasan tana can tana halinta na kullum, nakusa maganinta ai”, murmushi yayi tare da mikewa, kallansa momy tayi “ ina zaka “, kanshi ya d’an sosa kadan yana murmushi “ yanxu zan dawo momy”, gyada masa kai batare da tace masa komai ba , ita kad’ai tana murmushi abinta. ‘Dakin Mimi ya nufa ,sau d’aya ya murd’a yaji shi a kulle , nasa d’akin ya nufa tare da d’akko wani mukulli ya koma dakin mimin, sau d’aya ya saka key d’akin ya bud’e . A tsugunne ya same ta tahad’e kai da gwiwa tana shash she’kar kuka , har ya shigo cikin d’akin bata sani ba , kan kujerar gaban mudibin ta ya zauna tare da crossing Legs d’insa , “me akai miki kike kuka ?”, da sauri ta d’ago fuskarta ganinsa zaune a wajan tayi Sauri goge fuskarta “ ba kuka nake ba , abune ya shigar mun ido”, tafa har yanxu muryarta kamar zatayi kuka , gyad’a mata kai yayi tare da mikewa, itama da Sauri ta mi’ke tare da ri’ko hannunsa “ am sorry yaya moh “, kallanta yayi akaro na biyu ya ‘kaya maimaita maganarsa” me yasaki kuka ?”, sun kuyar da kanta tayi ‘kasa , shima d’auke hannunsa yayi daga cikin nata “ well “ da Sauri ta furta “Naga kana fushine and yaya moh , momy ce tace fa zata sa ka aure min driver”, ke kuma ba kyaso? Kanta ta d’aga masa alamar eh , murmushi ya karmata “ kar na ‘karaji momy na magana Kema kin d’aga muryar ki? Okay ? “ na dena , and yaya moh ina tsarabata? Goshinta ya d’an dallah “ in my room “, bata jira karashen maganar saba ta fita a guje , giirgiza kansa yayi “ Allah ya shirye ki mimi “, daga nan ‘kasa ya sakko inda momy take suka soma hira Yaushe gamo da ita.

     

    **********
    *************
    ??????

    NIGER

    Tunda Tahee ta farka take kuka ita kadai lokaci zuwa lokaci sai ta zabura zata mi’ke wasu ‘yan mata suna ri’keta , abun mamakin kuma da kanta tayi sallahr asuba daga nan kuma ta mike hawaye cike a cikin idanuwanta , duk yadda taso barin Wajan sun hanata jintake kamar zatayi hauka fad’i take su rabu da ita amma sun ‘ki sai ma baba Malam da suka kira , kallo d’aya yayi mata ya saki murmushi “ ku kyaleta “, suna sakin ta kuwa ta mike a zabure zata nufi ‘kofa ya daka mata tsawa, da Sauri ta nutsu, abincin da aka kawo mata ya nuna mata , cikinta har rawa yake lokacin da ta soma cin abinci har saida Alhaji isma’il d’in yace taci a hankali, gabaki d’aya sai data basu tausayi, rubutu baba Malam yasa aka bata , ita kad’ai sai sakin ajiyar zuciya take , karatun alkurani aka sa a d’akin , matasan ‘yan matan suka zauna da ita , baba Malam da alhaji isma’il kuma suka fita.

    Cikin wani d’aki suka shiga Alhaji isma’il ya kalli baba malam,”baba Malam idan ba damuwa ina san ro’kan wani Alfarma”, murmushi baba Malam yasaki kafin yace “ina jinka “,shiru yayi kamar bazai ce komai ba sai kuma ya soma magana “ baba Malam idan babu matsala inasan tafiya da wannan yarinyar can wajan iyalaina sai su cikaga da zama tare ,tun da alamu sun nuna zamanta anan kamar zai iya zamar mata had’ari ita da abunda yake cikin ta, tunda asirin da akai Mata ba iya nigeria bane har kusa da ita , kaga idan bata kusa da nan zata samu nutsuwar zuciya ko zata dawo hayyacinta sosai, ko ba dan itaba dan abin cikinta “. Yan Zuma baba Malam murmushi ya saki tare da gyara zaman sa “ Naji duk abunda kace isma’il, kuma na yaba da hankali da nutsuwar ka , amma kasani kamar Marainiyace kake kula da ita tunda bata da kowa , idan kaci amanar Allah , Allah bazai barka ba , ka kula da amanar Allah wannan kamar jarabawace Allah yakeso ya kwadaka”, sunkuyar da kai alhaji isma’il yayi “ insha Allah baba malam , nayi maka alkawari zan d’auketa kamar ‘yar cikina sannan na bata tar biya kamar ni na haifeta “, Allah yayi maka albarsa, yaushene tafiyar?” Cewar baba malam , “Jibi nake san komawa insha Allah “, jinjina masa kai baba Malam yayi “ sai a sanar wa iyali “cewar baba Malam,cike da girmamawa ya “amsa da insha Allahu”.

     

    ????GIDAN AUNTY ????

    07041879581
    MSS LEE ??

  • A Rubuce Take Book 2 Page 37

    A Rubuce Take Book 2 Page 37

    Part 02

    Page 37

    Tun bakwai na safe ya gama shirin barin bauchi ya wuce katsina,sai daya tabbatar yabar gidan hannun umar,yace ya kula da kowanne sashe na gidan,idan ya gama ya rufe gidan,ya kaiwa yaaya bara’atu key din,sannan ya dauki dukka wani abu me muhimmanci ya zuba a motarsa ya fice a gidan.

    Gidan yaaya bara’atun ya fara isa,tasa aka kawo masa breakfast ya taba sama sama,don shi yanzu kowanne abinci kallon hadarin kaji yake masa indai ba abincin widad ba,bayan ta sallami mai gidanta dake sammakon fita tazo suka zauna,a sannan su mimi na tare dashi,yaran duka babu wata damuwa a tattare dasu,ita mimi ma nata murnar

    “Daddy har anyi kana wanka munci abinci,daddy aiba yanzu zamu koma gida ba ko?” Sai ya gyada kai yana shafa kanta,tausayin yaran kawai yake damunsa,banda mutuwa babu abinda zai raba uwa da danta,amma da yake Allah ya jarabcesu da shashashar uwa bata wani shiga jikinsu da zasu damu can da ita ba,kawai yana baqincikin su girma su tuhumeshi da rashin samar musu da uwa ta gari,saidai yayi imanin Allah bazai taba tozartar dashi ba,tunda yayi dukkan iya bakin qoqarinsa bisa kyautatawa hafsat din zato ya zabeta a matsayin uwar ‘ya’yansa.

    Duk da yaaya bara’atu tana dojewa amma bai bar mata wahalar yaran ta sisin kwabo ba,komai sai daya ajjiye musu kama daga na islamiyya har zuwa na boko,sannan ya bada wasu kudaden yace a canza musu suturar sanyawa,saboda ya lura da yadda kaf kayansu suka qarasa macewa,harda tsadaddun laces din da ya dinka musu,wanda ko shekara basu rufa ba,don shi baya jiran sai wani lokaci na daban zaiyiwa iyalinsa dinki,kusan ko yaushe cikin yi musu suttura yake.

    A nan ne tace ba zata karba sisinsa ba, dole ya maida kudin dinkinsu,ya mata sallama ya wuce.

    Tunaninsa a hanya kaf ya qare kan yadda zai doshi widad da yadda zai hukuntata,don ya gaji da maganar da take yaba masa a fakaice,yanaji a jikinsa muddin taci gaba da haka wataran za’a wayi gari ya samu matsalar hawan jini ko zuciyarsa ta tabu,ta shiga rayuwarsa da yawa,a yanzun kuma ta sake kutsawa nisan inda baiyi zato ba,wannana abun da ya faru sai sake qara mata kima da daraja a idanunsa,ya sake qaunar iyayenta tare da ganin zallar dattakonsu.

    Tun tana bagarar da batunsa daga ranta har tadan soma jin damuwar rashin jin wayarsa da kuma dawowarsa,amma hakanan dai taci gaba da daurewar tana yakicewa.

    Ko a yau data tashi duk jikinta babu kuzari sosai,ta gama komanta da wuri wajejen azahar,saita zauna shuru,sai kallo da kuma duba littafi zuwa waya da ta dinga yi,affan baya nan,wata maqociyarta ta daukeshi tun azahar din,babbar macace,dukka yaranta sun girma,shi yasa suke da son qananun yara.

    Karfe uku da kusan minti talatin da tara ya sauka a cikin gidan,ya sanya motarsa cikin parking lot ya kasheta,ya fito yana yiwa yaron gidan magana ya bude booth na motar ya fidda tsarabar da yayo a hanya ya aje masa qofar falon sannan ya wuce.

    Knocking yayi,ta dauke fuskarta daga kan littafin dake hannunta,sai ta aje littafin ta miqe a zatonta affan aka dawo dashi,tana gyara wuyan rigar wata bubu ta net da aka yiwa shafin wani irin yadi me kyau daga qasanta,rigar tayi mata kyau sosai,saboda ko ina na jikinta ya a cike yake,babu wani rami loko ko lobawa sai inda yake dama a halittar diya mace haka yake,fatarta lumui lumui,wiyanta ta saka wani ziririn zaren sarqa me qyalli da ya ake qawata wuyan nata,ta riga data saba,ya kuma zame mata jiki,ko yaushe a haka zaka sameta fes tana fidda qamshinta me laushi.

    A nutse ta bude qofar,ta buda siraran labbanta zatayi magana sai maganar tata ta maqale,yana tsaye gaban qofar falon hannunsa harde a qirjinsa,idanunsu suka gauraya waje daya,sai wani abu ya tsarga ma kowannensu,wani abu ya tasowa widad mai matuqar qarfi da tasiri.

    Ashe dai qarya ne idan kace ka daina son mutum?,ashe dai qarya ne kace baka damu da masoyinka ba saboda wani sabani ko bacin rai,saita juya da hanzari zuwa ciki,batason ta bada kanta.

    Baice mata komai ba ya dauki kayan duka ya shiga dasu ciki,ya maida qofar ya rufe,ya tsaya tsakiyar falon yana sauke ajiyar zuciya hancinsa yana zuqar lallausan qamshin da yake bayarwa,qirjinsa yana masa wani irin wasai,duk uban nauyin nan da yakeji cikin qirjinsa a yanzu babu shi,yana jin kamar ya sauke wani uban dutse daya danne masa zuciya.

    Ya wuwwulga idanunsa bata cikin falon,yasan ba zata wuce bedroom dinta ba,don haka ya wuce kai tsaye.

    Gaban madubi ta wuce kai tsaye, tayi tsaye kawai tana kallon fuskarta da qirjinta dake motsawa saboda bugun da zuciyarta ke mata,ta lumshe ido tana tuhumar kanta akan yadda take samun sauyi akan abbas din,duk wani alwashinta yana sulalewa yana yin nasa waje.

    Sam bataji shigowarsa ba,sai sautin muryarsa daga bayanta

    “Me bakin tsiwa,ina tsiwar taki ta tafi?,kin iya gasama mutum magana ko?,ki barshi da ciwon zuciya kiqi nemansa” ya fada yana kafeta da ido,gami da hukuntata da kallon nan nasa,haka kawai batasan ya akayi ta juye masa kalar shagwabarta data saba ba,saita tura baki gaba taja baya tana qara kusancin dake tsakaninsu

    “Qarya nayi?,ai banyi qarya ba k…….” Kasa qarasawa tayi saboda yadda taku biyu kacal ya hade ratar dake tsakaninsu,yaci gaba da ritsata da kaifaffen kallon nan nasa

    “Uhmmm……qarasa mana” ya fada yana matsota.

    Ta hangi fitintinu bama fitina ba fal idanunsa,ta kuma tabbatar yau idan ya kamata zata ji jiki da kyau,don haka ta kulle bakinta taqi tanka masa,saidai duk da hakan bai fasa matsota ba,har ya danga da bangon dakin

    “Tunda kinji tsoro zan qarasa cire wannan rashin kunyar taki,kin dauka ni age mate dinki ne ko?” Kai ya shiga girgiza masa,saidai kafin tace wani abu yakai mata cafka,yayi mata wata wawuyar runguma har yana takure abinda ke kwance a cikinta,baiyi wata waya ba ya hade bakinsu waje daya,ya fara aika mata da wani zazzafan kiss,wanda ko sau daya ya gaza dauke bakinsa daga cikin nata.

    Cikin mintunan da ba masu yawa ba ya zare mata dukka wata laka ta jikinta,ya cire dukkan wani zafin rai taurin kai da kuma qwafar data yi masa,cikin qalilan din mintuna ya zautata,ya jefata wata duniya wadda ta mantar da ita wacece ita,ta sukurkuce gaba daya,ta kuma miqa masa kanta,irin miqawar da bata tashi gane cewa ta tafka abun kunya ba sai bayan da komai ya kammala,tana kwance a qirjinsa tana kukan da dai dai yake da nade tabarmar kunya.

    Tabbas taji jiki a hannunsa,ta kuma biya dukkan bashin soyayya da kewa da suka cima juna,yana maqale da ita tsam a jikinsa yana aikin lallashinta,hannunsa daya kan sumarta yana shafawa a hankali,zuciyarsa fes,nutsuwa tana saukar masa

    “Ka daina tabamin kai,bayan tunda na dawo baka nema komai a gurina ba,har dai kaje bauchi ka gama bincikenka” ta fada cikin kukan shagwaba tana turo baki gaba.

    Don dole dariya ta kubce masa,ya rungumeta da kyau jikinsa

    “Am sorry madam,bansan a matse kike ba ai…..”kuka ta fashe masa dashi,ta dunqule hannunta tana dan dukan qirjinsa

    “To na daina,na fasa fada,nine a matse” ya fada yana kare dukan da take kai masa da hannayensa shima.

    Sai da ya tsagaita dariyar sannan ya sake gyara mata kwanciya sosai a jikinsa,ya kira sunanta cikin sautin muryar data sanyata daga kai ta kalleshi

    “Banqi neman komai a wajenki da gangan kodon saboda wata mafita ba,a lokacin kina cikin zafi da radadin abinda na aikata miki,na tabbatar idan na nemi wani abu a wajenki a sannan,abinda zaizo kanki shine jikinki kawai nakeso,ban fara sonki saboda jikinki ba ke shaida ce akan hakan,kuma bazan fara saboda hakan ba in sha Allah,koda baki da komai tattare da ke banajin zan daina sonki har gaban abada” sosai kalamansa suka kashe mata jiki,tayi shuru tana saurarensa,tana kuma sake gasgata zancan nujood da tace mata,abinda uncle abbas yayi din tabbas ba halinsa bane,tafi gasgata asiri ne yake dawainiya dashi,a lokacin tace mata hafsat,saidai ita din har yau bata kawota cikin ranta ba.

    Sake kiran sunanta yayi bayan ya hade hannayensu guri guda cikin wani irin taushi da sanyi,sai data sake shigewa jikinsa da kyau saboda yadda sautin muryar yaratsa kowacce gaba ta jikinta

    “Don girman Allah ki yafemin,yafiya irin ta har abada,banason ki sake tuna wani abu makamancin wannan ya taba faruwa a rayuwar aurenmu” Abbas ya cancanci yafiyarta,koba komai uban danta ne wanda ta haifa da wanda zata haifa ma a gaba,ba zata taba mancewa kuma da yadda ya tsayawa rayuwarta ba,ya dauki wautarta da shirmenta,ya raineta har ta zama abun kallo ga kowa ba

    “Na yafe maka har abada” wani farinciki yaji yana ratsa zuciyarsa,har baisan adadin godiyar daya dinga jera mata ba.

    Cikin kwanakin komai ya wuce ya kuma zama tarihi a rayuwarsu,ba wanda ya sake tada zance makamancin wannan a tsakaninsu,ta koma masa widad din nan dake rikita duniyarsa,ta sake shigewa rayuwarsa da zafafan sirrikan mallakar zuciyar miji tsaftatacciyar hanya babu boka ba malam,sai addu’a data duqufa da ita haiqan a kowacce sujjadarta akan Allah yaci gaba da mallaka mata abbas din.

    Da yake zuciyarta akwai haske da tsarki,sai komai yake zuwa mata yadda takeso,abbas din ya samu a gareta har fiye da yadda ta zata,ta sake gasgata cewa addu’a ba qarya bace,hakanan duk macen data sadaukarwa kanta wa mijinta,tabbas zai zama bawa a gareta ba tare daya ankara da hakan ba.

    Samun nutsuwa da kwanciyar hankalin da yayi daga widad yasa yake aiki tuquru cikin garin katsina,aikin da ya sake tamfatsa sunansa,ya kuma sake sanya sunansa a bakunan manyansa,suka kuma ji tabbas hazaqarsa da qoqarinsa sun girmi wannan matsayin da yake kai a yanzu.

    Budi sosai ya dinga shigo masa,hatta da kasuwancinsa kamar an qara masa albarka,cikin lokacin ya rasa wanne tukuici ya kamata ya bawa widad din,ba tare da saninta ko shawara da ita ba ya dallo mata sabuwar mota,ya kuma siya wani babban gida daban acan qasan layinsu dake garin bauchi ya ajjiyeshi reserve.

    Randa ya danqa mata motar tsananin murna ya sanyata kasa runtsawa,kyau da tsadar motar sai takejin kamae tafi qarfinta kamar ba tata bace

    “Madam,azo a kwanta hakanan murnar ya isa,ko kin manta bake kadai bace?,anya bazan fasa wannan kyautar ba?” Da sauri ta qaraso ta haye gadon tana dariya

    “Afwan yallabai,suma babies din naka taya ummarsu murna sukeyi” ya saki murmushi ya yaye rigar baccin jikinta yayi kissing cikinta sannan yaja mata duvets ya rufeta.
    [24/05, 2:59 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 34

    A Rubuce Take Book 2 Page 34

    Part 02

    Page 34

    Tana kwancen saman gadon tana chart affan yana kwance a gefanta yayi bacci abinsa kira ya shigo wayartata,tadan saki murmushi ganin suna uncle muhsin ta zauna sosai ta daga wayar suka gaisa,cikin hikima ya sako mata zancan abbas din,yadda yaga tana kame kame ya fahimtar dashi gaskiyar zancan,sai ya fara yi mata fada cikin nasiha,nasihar data sanyata zubda qwalla,ya kuma umarceta ta buda qofarta,tabar uba da da suyi harkarsu,shi yaron ba ruwansa a fadansu,wannan tsakaninsu ne,bazai hanata hukunta abbas ba muddin zata huce,amma kada ta sako affan a ciki.

    Cikin share qwalla ta bawa uncle muhsin haquri tare da bashi tabbacin ba zata qara ba,ta ajjiye wayar tana sake jin zafin abbas a ranta,a daketa a hanata kuka?,har yana da qwarin gwiwar kaita qara?,saita gyada kai tana cije lebe,ya kirawa kansa ruwa kuwa,lallai ba shakka zata hukuntashi har sai ya gwammace kida da karatu,saita sake daukan wayarta taci gaba da abinda takeyi.

    Yayi aikin da yakeson yi sosai,ya kuma hada information masu yawa,wannan yaja masa lokaci,bai fita a office din ba sai da yayi sallar magariba,ko kafin yaje gida ana dab da kiran isha’i.

    Komai data saba yi a gidanta na kaduna ta miqe tayi,ta tsaftace gidan saboda ita kanta jurewa take,duk da bata rayuwa a falon amma tana jin ya dameta har ranta,sabo da qazanta masifa ne,kamar yadda sabo da tsafta yakebin jini shima,tayi girkinta amma iya cikinta dana affan,ta gama ta kwashe musu,ta gyara kanta da yaronta,saboda batason abbas din ya shigar mata daki saita dawo falon tana jiran shigowarsa ta bashi affan din ta wuce dakinta abinta,aqalla ai tayi qoqari,ta kuma bi umarnin kawun nata,bata watsa masa qasa a ido ba.

    Ya jima zaune cikin motar bayan ya shigo gidan,murfin motar a bude qafarsa daya a waje yana shaqar daddadan qamshin da tun daga harabar gdan kana jiyoshi, qamshin da gaba daya ya gama kashe masa jiki,bai fito ba sai da yaji ana kiran sallar isha’i sannan ya fita,ya daura alwala a famfon harabar gidan ya wuce masallaci.

    Rigima yaron yaketa mata,saita sakashi a kafada ta soma zarya dashi,sanye take da doguwar rigar wata atmafa mara nauyi,an mata budadden dinki daga qasa,saman kuma yasha tattara ya zauna dai dai qirjinta.

    Tana kawowa bakin qofar zata juya yana buda qofar,suka hada ido ita dashi,yayi wani irin kwarjini na musamman cikin uniform din, hular kayan na riqe a hannunsa,saita janye idanun nata ta juya zuwa ciki affan na qijrinta,yabi bayanta da kallo,ya tako a hankali zuwa cikin falon bakinsa dauke da sallama,ta duqa tana ajjiye yaron gami da amsa sallamar tasa muryarta can qasan maqoshinta,saita juya ta nufi dakinta ba tare da ta sake kallonsa ba,tana shiga ta tura qofar,ta koma saman gadon tayi kwanciyar ta gami da jan wayarta ta fara dubawa,saidai zuciyarta adan hargitse take kadan,don bugunta ma ya sauya ba kamar yadda yake a qa’ida ba,kuma ita kanta batasan dalili ba.

    Tsaye yayi kawai a wajen kusan minti biyu yana duban hanyar,sai ya dauke idonsa yana sauke ajiyar zuciya,gaba daya a wannan lokacin bazaice yana jin dadin duniyarsa ba,duk yadda yaso ga qaryata hakan da gayawa kansa komai dai dai yake,amma yasan ya fada dinne kawai bawai don dai dai din yake ba.

    Gurin affan ya qarasa,ya dauki yaron yayi masa wasa sosai sanann ya wuce dashi dakinsa,ya cikashi da kayan wasa ya shiga bandaki ya sake wanka, sanda ya fito harya bingire saman gadonsa yayi bacci,da alama dazun dama kukan rigimar baccin yakeyi,ya saki murmushi yayi kissing goshinsa a hankali ya gyara masa kwanciya yana jin qaunar yaron har cikin jininsa,sai ya tsaya gaban madubi ya shirya cikin qananun kaya,ya shafe jikinsa da turare sanna ya fito.

    A falo ya fara zama,amma kamar wanda magnet ke jan hankalinsa zuwa ga dakinta saiya kasa samun sukuni,bayason shurunta,kasheshi yakeyi,a qalla ko fada yana da buqatar su dinga yi,duk sanda tayi masa shariya irin wannan baya iya jurewa,bashi da juriya akan abinda yakeso,sai ya taka a hankali ya saka kai zuwa cikin dakin.

    Tana tsaye gaban wardrobe tana fidda wasu kaya,sau daya ta waiwayo ta kalleshi ta mayar da kanta kamar batasan da wanzuwarsa ba,ya tsaya daga bayanta yana dubanta

    “Ina abinci na?” Kamar ba zata amsa masa ba,saita zuqi numfashi ta fitar ta bakinta a hankali, zuciyarta tafasa kawai takeyi amma batason tayi wani abu da zai nuna bata ganin qimar uncle muhsin,ta saki kayan hannunta ta juya ta fice ba tare data tanka masa ba,yabi bayanta sai ya sameta saman dining tana serving dinsa.

    Kujera yaja ya zauna yana bin dukka motsinta da kallo,ko sau daya taqi duban inda yake,kamar ma ita daya ne cikin falon,wani irin fushi ne kwance saman fuskarta ba tare da ita kanta tasan da hakan ba,yaja ajiyar zuciya me nauyi ya sauke a hankali,dai dai sanda ta gama zuba abincin ta motsa da niyyar miqewa tabar wajen

    “Dawo ki zauna” ya fada a tausashe cikin muryar bada umarni,bata musa masa ba,kamar yadda bata kalleshi ba,ta kauda kanta zuwa wani sashen daban,yaja abincin gabansa ya fara ci,saidai gaba daya girkin kamar ba nata ba,ta cika masa yaji sosai,abinda tasan yafi tsana kenan,ya lumshe ido yana jin yadda yajin ke ratsa harshensa har kwanyarsa,ya sakeyin loma ya biyu ba tare da ya bari ta gane tsananin yaji da yakeji ba,saidai idanunsa suna kanta,ya tsatstsareta dasu ya hanata sakewa gaba daya,cikin jikinta takejin laifin data masa,amma zuciyarta taqi amsar haka.

    “Karomin” ya fada yana tura mata plate din,sai ta daga kanta da sauri cike da zallar mamaki ta kalli plate din ta kuma maida dubanta gareshi suka hada ido,idanun nasa da suka dan canza launi saboda tsananin zafin yaji,sai kuma ta janye idon nata ta basar,tasa hannu ta dauki plate din ta qara masa ta tura masa hadi da bashi qeya.

    Spoon ya sake sakawa ya kuma cinyewa,sanda ya sake cewa ta qara masa sai data zauna sosai ta dubeshi da kyau,bakinta yadan motsa kamar zatace wani abun sai kuma ta fasa,ta sake janyo plate din ta fara zuba masa

    “Wannan karon ki zuba yafi sauran yawa,muddin ta wannan hanyar zuciyarki zatayi sanyi……zan jurewa ci har sai kince na barshi haka”

    “Kayita ci,bazance ka barshi ba” ta gayawa zuciyarta hakan.

    Ta gefan ido ta dinga satar kallonsa ganin yana hanyar cinye uban abincin data sake loda masan,tun tana satar kallonsa harta koma kallonsa kai tsaye,ko sau daya bai kalleta ba yaci gaba da ci,ta kalli idanunsa zuwa sannan sun canza launi sosai,tasan yadda yajin abinci ke masa illa,musamman ulcer da yake da ita wadda idan ta tashi ba qaramar wahala take bashi ba,batasan lokacin data riqe hannunsa ba

    “Ka barshi haka” ta fada da sauri muryarta tana rawa.

    Jajayen idanunsa Ya daga ya kalleta dasu,sai ta gaza jurewa kuka ya qwace mata,ta saka dukka hannuwanta biyu ya rufe fuskarta dasu tana sakin siririn kuka.

    Tsam ya miqe daga inda yake zaune ya iso gabanta ya tsaya yana dubanta zuciyarsa na wani irin tafasa,kafin yace komai tayi hanzarin bude fuskar saboda wani irin amai mai zafi daya danno mata,yana qoqarin riqeta tana qoqarin zamewa,saboda tasan muddin yaci gaba da riqeta zata wankeshi da aman.

    Bata iya riqeshi ba kuwa ta fara kwararashi,bai damu da yadda ta batashi ba saboda gaba daya hankalinsa a tashe yake,dama bata da lafiya?,tun yaushe?,duka bashi da wannan amsar,ya riqe hannuwanta sosai daya hannun nasa ya dafe mata bayanta yana jera mata sannu kamar zai ari baki.

    Shi ya gyara wajen,ya hada mata ruwan dumi ta gyara jikinta da ta bata shima ya gyara nasa jikin,tana kwance tana maida numfashi idanunta a kulle ya qaraso dakin,ya canza kayan jikinsa, boxer ne kawai a jikinsa,qaqqarfar kuma lafiyayyar surarsa ta fita sosai,ya dawo gaban gadon ya durqusa dab da ita ya kama lallausan hannunta ya riqe cikin nasa

    “Tun yaushe ne baki da lafiya?”

    “Kada ka tambayeni” ta fada muryarta tana rawa

    “Why?” Ya tambayeta a mamakance,sai data zame hannunta daga nashi sannan tace

    “Saboda baka damu dani bama gaba daya bare lafiyata”

    Tashi yayi ya haye gadon gaba daya,ya jawota cikin jikinsa dukkaninta ya rungumeta tsam,bata da qarfin da zata qwace a jikinsa dole haka ta zauna,a hankali sai taji yadda zuciyarsa ke bugawa da Wani irin qarfi n da ya wuce qa’ida

    “Tun daga wancan lokacin da abun ya faru haka kullum zuciyata take bugawa,ban taba zaton zankai wannan lokacin ban kamu da ciwon zuciya ba,komai nina aikata miki shi,amma bisa wani umarni da bansan daga inda zuciyata take karboshi ba…….kiyi haquri da dukkan abinda ya faru,ki kuma yafemin,amma nayiwa zuciyata alqawarin bazan bar wannan abun ya wuce a haka ba, kowanne irin tunani nasan zaki iyayi a kaina,dai dai ne bazan hanaki ba,amma ki bani dama……i need a chance don Allah don kuma affan bawai don ni ba” daga wannan maganar ya zame jikinsa daga gareta,ya barta da tunani.

    Hijab ya dauko mata sannan ya dauko affan

    “Muje kiga likita,bai kamata ki kwana hakanan ba” shi ya taimaka mata har zuwa bakin mota,sai data shiga ya kwantar da affan a baya sannan ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan,dukkaninsu zuciyoyinsu babu dadi.

    Idanunsa qyar akan allon computer din sanda likita yake mata scanning,yara biyu ne gasunan kwance a mahaifarta har zuciyoyinsu sun fara bugawa.

    Da sauri ta dauke kanta gefe hawaye yana sauko mata,ta yaya zata iya rainon cikin ‘yan biyu?,bayan ko yaye affan batayi ba,a wannan yanayin da take ciki bata jin tana da qwarin gwiwar da zata iya rainon cikin ma gaba daya

    “Satin cikin sha biyu gashinan,congratulations” Dr anwar likitan mai matuqar kirki da barkwanci ya fada.

    Abbas dake jinsa kamar a duniyar mafarki ya miqa masa nasa hannun,Allah me yadda yaso a lokacin da yaso,cikin yanayin da yake na daukewar dukkan wani farinciki daga rayuwarsa sai ga hasken farinciki ya ratso daga ubangiji,ya maida dubansa ga widad hankalinsa ya tashi da ganin hawayen da take zubarwa,ya matsa saman kanta yana jera mata tambayoyin akwai abinda ke mata ciwo ne?,saita gyada kai

    “Bari ina zuwa” Dr anwar ya fada yana fita a office din,hakan ya bawa abbas damar dagata,ta zauna sosai yana riqe da hannunta,saidai ya kasa zama,yana tsaye ne tsakiyar qafafunta yana kallonta

    “Bani da qwarin gwiwar rainonsu da haifarsu” ta fada tana zubda sabbin qwalla,sai ya dora yatsantsa saman labbansa

    “Zan baki duk wani qwarin gwiwa da kika rasa,zan baki dukan hope,zamu rainesu tare na kuma tayaki naqudarsu,don Allah ki kwantar da hankalinki na roqeki,ina da buqatarsu,burin kuma hajiya kenan kullum taga tarin jikoki daga wajenki” furta sunan hajiya da yayi ya sake sanya damuwa da karyewar zuciya a zukatansu su duka biyun,sai ya matso ya sanyata cikin qirjinsa yanason saukar mata da nutsuwa.

    Tun daga wanna lokaci gaba daya ya maido hankalinsa akan widad din,ya bata dukkan lokacinsa ya rage ranakun fita aikinsa,ya hanata yin komai,komai shi yake mata,yayi nata yayi nasa yayi na affan,sai daya gama karantar komai da takeso naci sha da sauransu,wani lokacin har tausayi yake bata,duk da har yanzu ta kasa warewa yadda suke a baya,abinda yake qara masa damuwa cikin qirjinsa kenan,yake ganin kamar komai bai wuce a wajenta ba.

    Tun randa yaci wannan abincin qirjinsa yake yawan riqe masa da ciwo,amma sam bai nuna mata ba,don so yake ya dawo da dukkan farinciki da walwalarta.
    [22/05, 12:28 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 33

    A Rubuce Take Book 2 Page 33

    Part 02

    Page 33

     

    Ido suka kuma hadawa,ta sake janye nata idanun tana kuma hade fuskarta tsaf tamkar bata taba dariya ba,sai shima ya basar,yakai hannu kan kafadarta zai karba affan.

    Ji tayi sam ba zata iya bashi shi ba,don haka ta goce ta hanyar ja da baya,ya kalleta cikin tsantsar mamaki,ya sake takowa ya matso ta sake matsawa baya,sukayi haka har sau uku sai ya gaza daurewa,ya motsa labbansa da dan bacin rai a muryarsa

    “Yarona nakeson ki bani”

    “Sai yanzu ka tuna yaronka ne?,aina dauka shima a hotel nayo cikinsa” gam ya runtse idonsa yana jin saukar maganar kan qahon zuciyarsa kamar saukar mashi,karo na farko tsahon tarayyarsa da ita data taba gaya masa wata magana mai gautsi,ko kafin ya bude idanun nasa yaji giftawarta ta gefansa,ya waiwaya ya bita da kallo,ta doshi dakin data gani a bude ba tare data tsaya tambayarsa bedroom dinta ba.

    Tanata addu’a Allah yasa nata dakin kenan,ta kuwa dace don duka kayanta da aka shigo mata dasu suna ciki,wadataccen bedroom da aka saka komai na buqata daya dace da dakin kwana,ta qarasa a hankali ta kwantar da affan dake bacci saman gado,sannan ta jawo jakarta zuwa tsakiyar dakin,ta budeta ta fidda abubuwan da take buqatar cirewa,ta jefata dukanta cikin wardrobe na dakin,cikin ranta tana jin kamar ba wani zama zatayi ba,kamar na dan lokaci ne zata koma inda ta fito.

    Agogon hannunta ta cire ta ajiye saman madubi ta shiga bandaki tayi fitsari sannan ta daura alwala,tana fitowa ta hangeshi,tsugunne gaban gadon, hannunsa riqe da hannun affan dake bacci,ya sunkuya a hankali yayi kissing dinsa sannan ya miqe,suka sake hada ido ta kuma kau da kanta tana tabe baki,shima sai ya dauke kansa,amma duk da haka idanunsa na fusgo masa yadda ta wani murje,sai kishinta ya sake motsawa a zuciyarsa,yadan cije lips dinsa kadan,har yanzu zuciyarsa ta gaza samun nutsuwa akan abinda ya farun,kuma bayajin zata samu nutsuwar har sai ya sakeyin binciken qwaqwaf akai.

    Kamar yasan me take shirin aikatawa,har yasa qafarsa waje sai ya fasa ya dawo yana dubanta tana rolling mayafinta saman kanta tana jira ya gama ficewa ta saka sakata

    “Karki kuskura kice zaki kulle qofa,ki barmin yarona ya sake a gidan babanshi yadda yaso,inda ke daya ce sai nace bismillah,kiyita rufe qofar har Allah ya gajisheki” tabe masa baki tayi ta kauda kai ba tare da tako tanka masa ba,sai yaji haushi ya kamashi,yaso ko yaya ne tace wani abun,yaso ta magantu ko baqar magana ta gaya masa amma sai ta qiya,haka ya qarasa ficewa yana wani tsatstsare gida,yana jin Wani abu mai nauyi yana taba zuciyarsa.

    Bata kuwa fasa kulle qofarta ba,don batason ma ya wani shigo mata daki,don bata da buqatar ganinsa sam sam,zuciyarta wani irin zafi take mata idan ta ganshi,ta idar da sallar la’asar,zuwa sannan jikinta har yadan fara rawa,don bata jure yunwa kwata kwata,don dole ta fita ta laluba kitchen.

    Akwai komai a ciki,harda ruwan zafi a flask,ta shiga tunanin sassauqan abinda zata dafa kafin ya dawo gidan,sai kawai tayi amfani da ruwan zafin flask din ta tsaida ruwa,ta bare noodles ta zuba,ta kunna daya side na gas din ta soya qwai,cikin minti talatin kacal ta hada komai ta dauko ta wuce dakinta abinta.

    Tana murza key din yana shigowa,yaji qarar key din,yabi qofar da kallo,ransa ya baci,bata ji abinda ya fada kenan ba?,sai ya taka zuwa qofar dakin,ya daga hannu kamar zaiyi knocking me ya tuna kuma sai ya fasa Ya juya ya wuce kitchen.

    Wayam ya samu kitchen din,sai tukunyar data dafa noodles wadda ta cika da ruwa ta ajjeta a wajen,da spoon din da tayi amfani dashi wajen juyawa,bawon maggi dana vegetables din data zuba,sai yaji abun yayi masa banbarakwai,tsahon zamansu bai taba ganin tayi girki tabar gurin haka ba.

    Ci gaba yayi da duba kwanukan kitchen din,ko noodles din bata ajjiye masa ba,ransa ya sosu,haka ya jawo wata qaramar tukunya ya dora baqin shayi,don bashi da kuzari da kuma qarfin jikin dora komai a yanzu,girkinta yake marmari,ya kuma sanya ran ci,sai gashi ko ruwa bata dafa ta ajjiye masa ba.

    Jikin kitchen cabinet ya tsaya yana shan tea din,sau biyu ya kurba ya furzar,babu dadi sam bakinsa,sai a sannan ya ankara ashe ya cika komai yayi yawa,baisan kuma ya akayi hakan ta faru ba,haka ya kwarar da tea din ya fito yabar kitchen din.

    Parlor ya dawo ya zauna yana sauke numfashi saboda qirjinsa da yaji ya fara riqewa

    “Hasbunallahu wani’imal wakil” ya soma maimaitawa a hankali yana qoqarin cooling down kansa,likita ya gargadeshi game da dorawa kansa stress da damuwa mai yawa,jininsa ya hau an samu kuma ya sauka da qyar,idan kuma bai kiyaye ba zai iya dawowa.

    Yana tunanin akwai yunwa tattare dashi,ya manta rabonsa da cin abinci cikakke,ta riga ta batashi da taste din abincinta mai dadi,damuwa da rashin samun kalar taste dinta yasa ya watsar da lamarin abinci,dole ya cire waya ya kira daya daga cikin yaransa ya gaya musu irin abincin da yakeso.

    Ko da aka kawo din ba wani mai yawa yaci ba,cikinsa gaba daya a cushe yake,sai ya ture abincin ya koma ya kwanta kan doguwar kujerar falon,tunani ya masa yawa,a yanzun yake jinsa cikakken maraya gaba da baya.

    Sau kusan biyar yana ganin kiran hafsat,saidai yabi wayar da kallo,harta gama ringing dinta ta katse,bayason damuwa a yanzu,don haka bashi sa buqatar daga wayarta.

    Daga bangaren hafsat din sai ta dinga jin fargaba da dar dar,amma indai abinda malam ya gaya mata haka yake,me zai hana abbas din daga wayarta,tunda dai lokaci irin wannan da baya da lafiya ta tabbatar yana gida bare tace ya fita Wani aiki na musamman

    “Basa qarya a zancensu,tunda ta gayamin hakanne,kawai ki shareshi” zuciyarta ta bata shawara,saita aje wayar taci gaba da sabgarta.

    Washegari kafin ya fito ta gama duk abinda zatayi a kitchen din ta dawo daki ta rufe abinta,bata kuma sake fitowa ba sai bayan isha’i data tabbatar ya tafi masallaci sallah,ta zube kwanukan ta debi wasu ta koma.

    Cikin kwanaki uku abinda da dawowarta abinda ya dinga faruwa kenan,wani irin zama sukeyi na shariya da fita sabgar juna,saidai widad din ta fishi daukan zafi sosai,don bata fita a dakin sai idan ya fita sallah,da yake har yanzun bai gama warwarewa ba,yana gida yana sake hutawa,ko aiki bai fara fita ba,da zarar ya fita zata fita ta dafa musu abinda zasuci ita da affan ta zuba a cooler ta koma daki,ko wanke wanke taqiyi,haka ta dinga tarawa kitchen din kwanuka itama.

    Sau daya da wasa bata taba saka tsintsiyarta ta share falon ba tunda tazo cikin gidan,iya dakin da take ciki kawai take tsaftacewa,tun bai lura ba har ya lura da abinda takeyi shigen na hafsat,don kitchen din ya fara canza launi,haka qura ta fara yiwa gidan yawa,hakanan duk da baida lafiya ya zage ya gyara kitchen din da gidan,yayi tsammanin zata dauki haske ta gyara amma a banza,don ci gaba tayi da batawa tana jibge masa kayan a kitchen din,tun yana ganin zai jure har haqurinsa ya gaza,ya dinga fakonta ta fito amma ko sau daya bata bari hakan ta kasance ba,har ya gama murmurewa ya koma bakin aikinsa.

    Randa zai soma fita din haka ya hadawa kansa baqin ruwan shayi a tsaitsaye,yana tsaye a falon yana kurba,gaba daya sai yakejin bashi da sukuni,idanunsa qyar bisa qofar dakin,yana jiyo hayaniyar yaron,bama rashin isashen abinci da baya samu ne damuwarsa ba,wata kewarsu da yaji ta fara shigarsa da gasken gaske,tun bayan da ya duqufa da addu’o’in da aminin mahaifinsa ya bashi bayan zuwansa dubashi,ya kasa jurewa ya ajjiye cup din ya taka zuwa dakin.

    Sai da yayi knocking kusan sau biyar sannan aka tambayi waye a daqile

    “Kinsan ko waye ai ko ban fada ba” ya amsa mata adan kaurare,sai tayi banza dashi kamar bataji abinda ya fada ba,har sai da ya qosa da tsaiwar ya sake bugawa,amma sai tayi biris dashi

    “Open the door malama” ya fada da dan hargagi

    “Dakin ‘yar kwanan hotel din zaka shiga?,me zakayi da ita kai da kake da kamilar mace a bauchi?” Runtse idanunsa yayi yana jin zafin sunan data kira kanta dashi sannan ya bude a hankali yana aje numfashi

    “Stop it……ki budemin qofa kiban affan”

    “Affan kuma?,ai yarona ne ni kadai”

    “Widad!” Ya kirata da qarfi,sai taqi amsa masa

    “Ki budemin qofa nace” nan ma tayi masa shuru,har gwarancin da yaron yakeyi,da alama har yazo bakin qofar ne shima yaji.muryarsa,sai ya zame ya duqa a bakin qofar,yana jin kamar yayi zaana ya tsaga qofar ya shige,ba yaron kadai yayi missing ba,harda mamansa,yana son kallon wannan fuskar tata da ya jima bai gani ba,ya tabbatar ba zata sake ce masa komai ba,haka ya gama tsaiwarsa a wajen,ya juya a hankali ya dauki brief case dinsa ya fita a gidan.

    Rana ta farko a office dinsa amma bai iya wanzar da komai ba,shi kansa yasan baiyi tabuka komai ba,tunani fal kwanyarsa,gaba daya yana jin kamar an canzashi ne,kamar ba ainihin abbas ba,yaja tsaki yafi sau dubu,ya yarfa hannuwansa har baisan adadi ba,har cikin zuciyarsa yaji bazai iya jura ba,kawai sai ya dauki wayarsa yayi qundumbala ya kira muhsin.

    Kamar komai bai faru ba suka gaisa,sai abbas din ya samu kansa da bawa muhsin haquri

    “Ya wuce,amma tabbas saika dage da addu’a abbas,idan ba haka ba mata basu da kirki,zasuyita saka ka kana abu kamar Wani zautacce ko qaramin yaro” ajiyar zuciya ya sauke

    “Na gode” ya gaya masa

    “Alfarma nake nema don Allah idan zan samu”

    “Ba ‘yar wannan a tsakaninmu,fadi kawai”

    “Maman affan nakeson ka yiwa magana,ta hanani ganin yaron gaba daya,ta takureshi a daki, at least ta sakeshi ya dinga fitowa yana samun wadatacciyar iska” ya fada a mugun karye,karayar da shi kansa baisan ya nunata ba,sai dariya taso kubcewa muhsin,ya fahimci wani abu a cikin muryarsa wanda shi kansa baisan yana bada wannan amon ba,ba affan bane,maman affan din yake kewa gami da qishirwar gani

    “Kada ka damu,zan mata magana in sha Allah” yayi masa kuwa godiya sosai sannan sukayi sallama,ya ajjiye wayar yana sauke ajiyar zuciya,sai yake jin wani sassauci cikin ransa,ya jawo system dinsa zai fara rage wasu abubuwan saboda wani dan karsashi yanzun da ya samu,sai kira ya shigo wayarsa,daya duba sai yaga number hafsat ce.

    Da kallo yabi wayar yana jin wani abu yana yawo a ransa kafin daga bisani ya daga wayar,cikin salo da kisisinar jin cewa a yanzun ita daya ce a duniyarsa tace

    “Barka da yamma,ya gida ya jikin?”

    “Alhmdlh,ya yaran?”

    “Lafiya lau suke,yaushe zaka shigo?, inaga ya kamata ka taho gida don nafijin dadin kula da kai,ga rashin lafiya sannan kuma kai daya kake zaune ai baiyi ba abun” inda ace yau ya fara sanin halaye da dabi’unta sai yace ta bashi mamaki,wato ita ba zata iya takowa ta iskeshi a inda yake ba inda ace cikin buqatar hakan yake,saidai shi ya dawo ya sameta kenan,bai shirya gaya mata komai a kansa a sannan ba,saboda zuciyarsa ta fara tsara masa wasu abubuwa a kanta,shi yasa ya hana a sanar da ita komai game da abinda yake faruwa,har kuma dawowar widad din

    “Bazan iya tahowa yanzu ba,sai na warke sosai sannan”

    “K’nnnnn,ai shikenan,nace pampers din nawwara,kudin makarantar yara duka sun qare fa,naji Shuru”

    “Zan miki transfer ki siya” ya fada a gajarce,dama abinda takeson ji kenan

    “To yayi,sai anjima” ta fadi a gaggauce kamar wadda ake jira.

    Wayar yabi da kallo na wasu daqiqu,sai ya tafi contact nasa ya fara lalubar number wayar umar qaninsa.

    A ladabce ya gaida yayan nasa yakuma yi masa sannu da jiki

    “Kana ina?”

    “Ina kasuwa,muna lissafin qarshen shekara zamu danje hutu”

    “To yayi,idan kun gama ka ajjiye lissafin a wajenka,zan karba idan na nutsu na duba”

    “To yaya”

    “Aiki nakeson na baka,amma banason kowa ya sani,inason ya zama sirri tsakanina dakai”

    “To yaaya in sha Allah”

    “Ka hada kayanka ka koma gida na,karka taho har sai ranar da na umarceka,anjima idan na koma gida zan kiraka nayi maka bayanin abinda nakeso kayimin”

    “To shikenan,in sha Allah” yayi masa sallama,ya ajjiye wayar,saiya sake komawa kan system din,maimakon yayi aikin dake kai,sai kawai ya fita,ya saka sunan FAAZ HOTELS ya fara wani sirrintaccen bincike a kansa.

    [22/05, 12:28 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 38

    A Rubuce Take Book 2 Page 38

    Part 02

    Page 38

    Duk wajen wanda hafsat tasan zata ya yiwa abbas magana ya maidata taje amma abbas yayi biris,yaqi bawa kowa fuska yayi masa zancan hafsat din,suma din kuma suna kunya da nauyin yi masa maganar,saboda kowa yasan irin haquri da wahalar da yasha da ita,a yanzun sai yakejin ya samu wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali da ya jima baiji irinta a rayuwarsa ba.

    Duk yadda takai ga bugawa bataga alamun samun nasarar komawarta gidan abbas ba,cikin qasqanci mugun bacin rai da baqinciki mai tsanani ta dauki shawarar da ummanta ta bata

    “Tunda yanzun itace ke fada masa yaji,babu wata hanya data rage illa mu wanke qafarmu muje kanon,mu samu kakanta shi kadai nakejin yayi saura da zai gaya masa yaji,karkiyi baqinciki,idan kika samu nasarar dawowarki gidan,wannan karon ko komai nawa da naki zai qare saimun salwantar da ita,ko ta fita daga gidan d qafafunta,koshi ya koreta,ko kuma tabar duniyar gaba daya”.

    Washegari suka shirya suka nufi kano ita da ummanta,ummu ta ganesu,ta kuma tarbesu kadaran kadaham,basu gaya mata abinda ya kawosu ba amma sun nemi ganin alhaji tsoho,ta sanar masa tayi musu iso ta kuma basu guri.

    Yadda ta dinga kuka tana gaya masa qaramin ciki ne a jikinta tana roqon alhaji ya sanya baki ya karyar masa da zuciya,duk da yana sane da komai da yake faruwa,ba kuma wai bayajin ciwo ba,to amma hausawa sunce d’a na kowa ne,kuma har yanzu shi akwai wannan jinin na karamci cikin jikinsa,wannan ya sanya ya tabbatar mata da cewa zata koma dakinta in sha Allah ta riqe yaranta.

    Murna kamar ta taka rawa ita da umman nata,ta yamutsa fuska bayan sun fito ta goge sauran ruwan hawayen dake fuskarta

    “Yadda kika qasqantar dani kika sanya na nemi alfarma daga wajen iyayenki,na zubda ruwan hawaye na duk ta dalilinki wallahi bazan qyaleki ba” hafsat ta fada cikin cin alwashi da buri.

    Sanda alhaji yayi kiran abbas din yana office,yabar dukka aikin dake gabansa ya saurari alhajin.

    Yayi mamakin jin ta inda hafsat ta bullo,bazai iya musu da tsohon ba koda wuqa ya dora masa a maqoshi,saidai yasan maganin hafsat,idan tasan wata batasan wata ba,don haka bai musa din ba yace ya karbi komen ya maidata,amma alhajin yayi masa alfarmar sanar da ita cewa,daga rana irin ta yau,duk randa ta sake yunquri ko ta daga masa hankali to a bakin aurenta.

    Alhajin baiso yayi wanna furucin ba,to amma kuma mai daki shi yasan inda yake masa yoyo,duk mutumin da ya iya irin wannan hukuncin akan uwargidansa duk da zuri’ar dake tsakaninsu……shi kadai yasan irin abinda yake fuskanta.

    Saida alhaji ya nemi magabatan hafsa sukayi magana ta waya,ya kuma shaida musu sharadin abbas sannan yace musu ya maidata.

    “Alhmdlh,Allah ya qara girma,ya saka maka da alkhairi yasa a gama lafiya” kawunta da ya cire hannunsa daga lamarin saboda baqincikin hafsat da uwarta ya fada,yanason ‘ya’yan yan uwansa,amma hafsat ta fita zakka ko a cikin marasa mutuncin gidan,dukka qoqarin da yakewa rayuwarta yana yine kawai don girman zatin Allah da kuma hakkin zumunta.

    A washegari ta tattara kayanta ta koma gidan,gidan da har ta debe haso da tsammani daga zamanta a cikinsa.

    Ranar data koma ta tsammaci zai maido mata dasu mimi,saidai har washegari shuru,washegarin ma data saka rai shima dai shuru,haka ta wuni gidan ita daya kamar mayya,zuwa dare ta kasa haquri,ta daga waya ta kirashi.

    Dai dai sanda suke zaune a falonshi shida widad da tsohon cikinta da take gab da shiga watan haihuwarta,tana saman kujera yana zaune a qasa,ya dora qafafunta saman cinyarsa yana matsa mata saboda yadda suke yawan kumburar mata,iya girman cikin kawai ya isa ya gaya maka cewa lallai twince dinne da gaske,labari yake bata kan gagarumin promotion din da yake sanya rai za’a yi masa koda wanne lokaci,muqamin CP wato commissioner of police,saidai akwai masu so da yawa,amma yana fatan indai zai zame masa rayuwarsa data iyalinsa alkhairi Allah ya tabbatar masa.

    A yanzun widad din itace abokiyar shawararsa da baya iya boye mata kowanne sirri nasa,duk abinda ya taso masa zai zaunar da ita yayi shawara da ita,Allah ya hore mata wani irin kaifin qwaqwalwa da basirar da muddin ta bashi shawara yana ganin haskenta.

    “Waye yake kira?” Ya tambayeta saboda tafi kusa da wayar,ta kalli screen na wayar sannan ta amsa masa tana miqa masa wayar

    “Mummyn mimi ce” qaramin tsakin da baisan ya fito ba yaja

    “Ki daga kice mata hutawa nakeyi” kai ta girgiza

    “A’ah fa,ba ruwana,kayi mata dai bayani”

    “Bazanyi ba,ke nace ki daga,idan kuma ba zaki daga ba ki gayamin kanki tsaye”

    “Allah ya baka haquri” ta fada tana girgiza kai,sannan ta daga wayar takai kunnenta

    Cikin kwantar da murya da kuma laushi tayi sallama ta dora da

    “Daddyn Mimi yanzu ba yafiya tsakanina da kai kenan”

    “Sorry,yana hutawa ne yanzun haka,saidai ki sake kira anjima” wata ashar ce ta tasowa hafsat din amma ta haqura ta danneta, zuciyarta kamar zata fito ta bakinta,saboda tsabar wulaqanci ita zai bawa wata ta daga mata waya?,a duniya yanzu cikin wadanda ta tsana babu sama da widad,sai taja mugun tsaki ta dauke wayar daga kunnenta,saidai ashe widad din ta rigata gimtse kiran.

    Safa da marwa kawai ta dinga yi a falon,da qyar ta taushi zuciyarta da dare ta sake kiransa amma bata sameshi bama kwata kwata,haka ta kwana biyar cikin gidan,ga kayan amfaninta duka sunyi qasa,sai takejin gidan gaba daya ya sauya mata tunda ba haka ta saba rayuwa a cikinsa ba.

    Tasan yaran suna gidan yaaya bara’atu,koda ta kira tace don Allah tasa a kawo mata su sai tace

    “Babansu yace zai kirani ya gayan duk sanda za’a kaisu din” kan bala’in ubancan,ita da yaranta ma sai an shata mata layin sanda zata gansu?,me abbas ke nufi da ita ne?,anya zata iya jura kuwa?.

    “Dole ki jure muddin kinason zama cikin gidan” haka anty ummee tace da ita,haka taci gaba da hadiyar baqinciki,cikin lokaci kadan ta fara rama.

    Sai da tayi sati uku da dawowa sannan umar ya shigo mata da kayan abinci zallarsu,bata ga alamun nama kifi fruits ko drinks da ya saba hadawa dasu ba,babu kuma kudin da yake dora mata akai,wannan karon ta kasa daurewa ta kirashi

    “Iya abinda zan iya kenan,idan zaki zauna ki zauna,idan ba zaki zauna ba qofa a bude take” amsar da ya bata kenan ya kashe wayarsa.

    Tana kuka sosai ta kira anty ummee tana gaya mata,don ta kasa samun ummanta

    “Ke kin cika gajen haquri,tunda bada yunwa ya barki ba saikiyi haquri ai” ta fada a mugun gajiye,saboda itama yanzun ta kanta takeyi,nata ballin kissar ya fara tashi,miji da sauran danginsa sun fara ramfota.

    Cikin aljannar kare abbas din ya sakata,dukkan wani abu da bai zama dole a addini ba ya janye mata shi,kudi da yake bata na kashewa da qari da yake mata da sauran wasu kayan alatu da basu zama tabbas ba gaba daya ya janye,yanason ya gani shin da gaske ta rusuna?,saidai a yadda ta fara rawa da kiraye kiraye zuciyarsa ta gaya masa

    “Mai hali fa baya fasa halinsa”.

    Sai da tayi wata guda da komawa sannan ya shirya zuwa bauchi,wannan karon da widad din za’a je,abinda ta manta rabonta dashi,ta jima sosai rabonta da bauchin,gaba daya ma garin ya fita a ranta tun wancan lokacin,yanzun ma tsaowar bikin nujood ne zai kaita garin,don dole taje tayi kara duk da nauyin da tayi,abun kuma yazo dai dai da saukar ‘yar yaaya bara’atu.

    Ya zame mata dabi’a,a duk sanda zaiyi tafiya bata qasa a gwiwa ita ka shirya masa komai,koda weekend din kuwa zaije bauchi,duk dadai ya jima rabonsa da bauchin,tun bayan kammala bincikensa da sallamar hafsat da yayi.

    Koda ta gama da qyar ta iya miqewa da taimakonsa hannunta riqe da bayanta tana cije lebe

    “Anya madam,kodai triples ne computer bai gano dayan ba?” Ya fada cikin sigar tsokana yana boye dariyarsa,harara ta balla masa

    “Ta ina zasu fito?,yallabai ka barni ma naji da wadan nan guda biyun,bansan ina zaka kai son yara ba”

    “Yaya ai rahama ne,banqi kowacce shekara na dauki sabon baby cikin gidan nan ba” kukan shagwaba ta sake masa tana yarfa hannu,tayi tayi qafa ta taku takai gareshi ya rufeshi da duka kamar yadda ranta keso amma ta kasa,wannan ya sake hasalata ta sakar masa kuka sosai.

    Shi da affan suka dinga mata dariya,duk da yaran baisan me akewa dariyar ba amma ya taya babansa,sai daga bisani daya fuskanci da gaske take sannan ya aje affan din yana cewa

    “Baka kyauta ba affan,kawo hannun taho ki rabu dashi” data samu kanta tana isowa kuwa abbas din ranqwasa saman kansa,ya dafe wajen yana shafawa a hankali,sai tasa hannu ta tureshi gaba daya yayi baya ya fadi.

    Motarsa ya ajjiye ya dauki tata motar,a ciki suka tsara tafiya bauchin dama,tunda already yana da wata motar a gida,idan sunje sai ya bata abarta tayi ziyarce ziyarce itama.

    Tunda suka idar da sallar asuba basu koma ba,sun gama shiri tsaf sai suka dauki hanya,sammakon da sukayi ya basu damar isa da wuri,taso ta masa magana kan ya sauketa a gidan uncle muhsin amma sai tayi Shuru gudun ta zama mai yawan qorafi,tasan dai yana sane da sharadin raba musu muhalli.

    Sun shiga layin sai taga yana fakawa qofar wani gidan na daban,tabi gidan da kallo,yakai girman nasu gidan,a tsare yake kamar dai nasun,ya fita ya bude qofar sannan ya tura gate din,ya dawo cikin motar ya jata zuwa ciki.

    A parking lot ya tsaya ya kashe motar ya waiwaya yana kallon widad din,ya sakar mata murmushi sannan ya fita a motar,ya zagayo side din da take zaune ya bude mata sannan yace

    “Welcome to your new home” kallonsa tayi da alamun son qarin bayani,sai ya dage mata dukka girarsa

    “Eh ga naki gidan…..kin dauka mance?,ni na isa nayi saken mantawa da sharadin abba?,ban shirya rasaki bafa kwata kwata koda kuwa da wasa” yayi furucin yana miqa mata hannunsa,saita dora nata akai murmushi yana qwace mata,ya taimaka mata fita a motar,ya fidda affan ya aza a kafadarsa suka wuce cikin gidan.

    [25/05, 1:45 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Gidan Aunty book 2 Page 5-6

    Gidan Aunty book 2 Page 5-6

    BOOK 2

    Page 5&6

    Da Sauri Abeey ya nufi king da jini ke zuba a hannunsa, idanuwansa sun ‘kara rinewa, kallan dada kawai yake da tafi kowa firgita , a zuciye ya ‘kara furta “ ina matata ?”, yanxu ma babu Wanda ya iya amsa masa, Abeey na ri’ke hannun Ya fusge ko kallansa be yiba , dada ya nufa kamar zai tsakota, ya ‘kara furta “ ina matata?”, yanxu kam dada rud’ewa tayi ganin yadda ya canza mata kamar ba shiba , itama sai ta ‘kara rud’ewa har tana bugewa sabida yadda tayi baya baya kamar zata fad’i abeey yayi saurin tarota, duk da haka king be hakura ba ya ‘kara nufarta fadan fadan , gabaki d’aya idanuwansa sun rufe , zai ‘karayin wani maganar Abeey ya d’auke shi da mari, azuciye ya juya kan abeey,jijiyoyin kansa na ‘kara Tashi, shi kansa Abeey da yayi marin saida yayi danasanin marin nasa , lokaci d’aya yaji shakkar d’an nasa, kallo d’aya king yayi wa abeey ya nufi kofar fita ko takan wayarsa be biba , gabaki d’aya ukhti da ummey ‘ko’karin tsayar dashi suke musamman ydda Jinin hannunsa yake ‘kara zuba, doctor d’in da ya shigone yana ciwan king, ‘kokarin dakatar dashi doctor yayi, shima king ya d’auke fuskarsa da mari, yana fitowa zaki yabi bayansa cikin sauri ganin yadda ransa yake a had’e , da gudu ya bud’e wa king mota suka bar hospital d’in, tunda ya shiga cikin mota idanuwansa suke a rufe har suka ‘karaso cikin gida, Daidai part d’insa zaki yayi packing, kusan 5 minutes idanuwansa suke a lumshe , cikin kakkausar muryasa ya furta “ Me ya faru?”, sanin ba a ‘bata masa lokacine yasa zaki labarta masa abunda ya faru, tunda ga accident d’in da yayi har zuwa ‘batan Tahee, da yadda aka bincika ba a sameta ba, har kama sojojin da yayi saida ya sanar masa, lokacin da king ya bud’e idanuwansa shi kansa saida ya tsorata da ya nayinsa, gefen wuyansa wata Jijiyace ta fito masa , door d’in kofar ya bud’e tare da sakko da’kafarsa , cikin Sauri sauri ya shiga Cikin building d’in nasa kamar yana so ya gasgata abinda yaji da kun nansa “ Almost a month ?, itama ya rasata kamar yadda ya rasa shi”, tafiya ya soma yi cikin falon da yake da d’an duhu, da ‘karfi yake furta “ No hakan bazaiyuba, I don’t kiss them , bazan iya ba , my wife , my baby, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un “, yadda zuciyarsa take bugawa da sauri sauri ne yasashi yin baya , ga wani irin jiii da yaji yana neman kayar dashi, wani show glass da ya turene ya fashe gabaki d’aya akasa , muguwar yan kan da yayi sai faman zubar da Jini yake, gabaki d’aya Wajan ya baci, saitin zuciyar sa ya dafe, yana rintse idanuwa, bai da mu da yadda Jini ya ‘bata saba , tsugunnawa kasa yayi tare da runtse idanuwansa , da sauri abbey dake shigowa ya nufi inda yake , idanuwansa sun ‘kan’kance kamar yayi wa king kuka haka yake ji, araunane ya furta “ Am so sorry Tahnoon, Allah yayi bazamu ganta yanxu ba , but har yanxu ana kan bincikenta , nasan duk lefi nane da na sani lokacin da zamuje asibitin har da ita, kayi hakuri..” rufe wa abeey baki yayi tare da sakar masa kyakkyawan murmushi, kyakkyawan murmushin dake d’auke da abubuwa masu yawa a ciki, yadda idanuwansa sukayi mugun canzawa ne yasa be kalli abeey ba , ya kara sakar masa wani saban murmushi “ ba laifin ka bane Abeey, I lost Akhieeee for long time, yana sona sosai, and now I lost my wife again, and also her baby?, No Abbeey, tabbas a wannan karan abunda ya faru had’I, I don’t need anyone now , duk Wanda na tabbatar da sa hannunsa, I swear Abeey ko wanene bazan ‘kyalesa ba, the accident, and also ‘batan matata duk zan bun cika ..” rufe masa baki abeey yayi, “ ka dena fad’an irin haka , bana jin dad’i Allah ya ji ‘kan muhammad, na ro’keka da Allah da manzan sa karka yiwa kanka illa, tun lokacin da kayi accident dinnan Ummey bata bacci sosai, bata cin abinci sosai, kasan halin samreen idan ta sawa kanta abu, tana tunanin zata rasaka kaima , na ro’keka ka kwantar da hankalin ka ko suma nasu zai kwanta “, murmushi ynxu ma king ya saki be ce wa abeey kuma ba ya nufi stairs , a
    Jiyar zuciya Abeey ya sauke kafun ya kira sumayya ta gyara Inda glass d’in ya baci, gabaki d’aya falon ta had’a ta gyara , sai gashi ana shigo da kayan abincin daga part d’in Mamy da momy, su firdausi na shigowa dashi bayansu kuma samreen ce itama d’auke da wani ‘karamin tray a hannunta , kallan abeey tayi abun tausayi murya a hankali ta furta “ Abeey yana ina ?”, yana sama , ki bashi 20 minutes sai kije and please ki tabbata yaci abincin sannan ki masa dressing d’in hannunsa, Nima zan dawo nayi baki, jinjina masa kai samreen tayi sai da dau kusan mintuna 30 tukunna sannan ta nufi saman d’akinsa, gabaki d’aya ya faffasa glass da yawa na d’akin, sosai ya har gitsa d’akin yana zaune kan sofa idanuwansa a lumshe Jini na ta zuba daga hannunsa , da sauri samreen ta ajje tray d’in hannunta, da ‘kyar take wucewa Sabida in mutum be kulaba zai iya jin ciwo, first aid box ta d’auka zata rike hannunsa ya fincike, ‘kara ri’ko hannunsa tayi ya ‘kara fincikewa, a karo na uku da ta ri’ko hannunsa zai fuske itama a zuciye ta daka masa tsawa, kallanta yyi da mamaki gnin hawaye a fuskarta sai kuma cikin sanyin murya ta furta “ Dan Allah ka tsaya ba danni ba “, kallanta yayi be ce mata komai ba har ta gama dressing d’in ciwansa,tray d’in abincin ta d’auko shi kuma ya mi’ke tsaye zatayi masa magana ya ‘barar da tray d’in abincin, a zuciye cikin d’aga murya ya furta “ get out of my room” da mamaki samreen ta kallesa hawaye a kan fuskarta, “ Ni kake cewa na futar maka a d’aki? Yayi kyau , zan fita daga d’akin ka bani 10 minutes “, bata jira amsar saba ta fara gyara d’akin yana tsaye shima dafe da goshinsa, tana cikin gyarawa kwalla ta caketa da har saida tayi ‘kara da
    Sauri ya nufeta zai ta’basa ta dakatar dashi” kana ka kuskura ka tabani, kayi abunda ka keso “ Tana gama fad’ar hakan ta nufi kofa da niyar fita ya ri’ko hannunta “ Ukhtii why please? Zuciya ta ba dad’i, I’m feeling lonely, ina jin kad’ai ci, ina ji kamar….”, rufe masa baki ukhtii tayi itama hawaye cikin idanuwanta” komai yayi zafi maganinsa Allah, karka damu jikina yana bani zata dawo, zaku haifamana baby da yawa , ummey da abeey zasu zama grand parents, dada zata zama grand grand ma , ummey bata ci abinci ba tun jiya na ro’keka ka kwantar da hankalinka ko natama zai kwanta kaji?” Kanshi ya jinjina mata, itama saida yayi mata dressing d’in hannunta kafun ta bar d’akin cike da tausayinsa.

     

    ************
    *********************
    A ‘bangaran Abeey kuwa babban Amininsa tun na ‘kuruciya ne yazo duba king, sabida tafiyar da yayi kafun al’amarin ne yasa bezo ba , Abbey yana zuwa falourn sa ya tarar da Aminin nasa , kamar yara haka suka rungume juna , ba kowa bane face Alhaji kabeer, gefenshi kuma khaleed ne , shima hugging din Abbey yayi , cike da alhinin abunda ya faru, kallansa Alhaji kabeer yayi” ban ji dad’in abunda ya faru da son d’ina ba ,shiyasa nace dole na zo na duba shi da kaina dan nasan halinka kamar yadda ka’ki zuwa d’aurin aure na dukda nasan kana da babban dalili, to wannan karan dole a ‘kara d’aura zumunci, suma iyalina insha Allah wata rana zan kawo su,” murmushi abeey yyi “ baka canza ba har yanxu , ina zahra ta ? Nayi kewar ‘yata “, gaishe Abeey Khalid yayi, Daidai lokacin da ilham take shigowa falourn bakin ta d’auke da sallama , gaishe da Alhaji kabeer tayi , kafun ta gaishe da khaleed da ya tsareta da idanu, a fakaice ta dalla masa harara da yasakashi sakin murmushi, tana fita Alhaji kabeer ya furta “ kamar ilham ? “ Aushe baka manta sunayensu “ cewar abeey “ tana zan manta sunayen ‘yayana” tana fita da munti biyar khaleed ya mi’ke gabaki d’aya kallansa sukayi , “ zan d’an sha iska a waje ne , kafin king ya fito” jinjina masa kai sukayi a tare , ajiyar zuciya ya sauke shima kafin ya fito daga falourn, yana fita ya nemeta ya rasa gabaki d’aya bata filin Wajan, ‘karamin tsaki ya saki, tare da bugun ‘kafarsa har zai juya sai ya hangota tafito daga part d’in su zata nufi na dada da sauri ya ‘karasa inda take , d’aure fuska ilham tayi shikuma ya sakar mata murmushi “ kinyi kyau “, banza tayi dashi zata wuce ya dakatar da ita “ me yasa kike haka ? Nasan kin sanni , inaso muyi magana “ sai yanxu ta gane fuskarsa sosai , a hankali tace “ yaya khaleed ?”, oh da baki ganeni ba? , kai ta d’aga masa , ka canzane naga ynxu har d’an ‘kiba da kumatu kayi shiyasa ban gane ka ba sosai , sai anjima “, saurin me kike ? Ba komai , cewar ilham ,” amma kike guduna?” A hankali ta furta “ kayi hakuri “ kai ya jinjina mata kafin ya mi’ko mata kantamemiyar wayarsa “ samun phone number d’inki akwai maganar da zamuyi”, ba musu ta saka masa number d’in tai masa sallama ta bar Wajan, murmushi khaleed ya saki yana bin bayanta da kallo shi kadai yana sakin murmushi, king da ya hango ne yasashi sakin murmushi duk da yadda ya ga fuskar sa a had’e ba fara ‘a yasan daman za a rina , duk da yanayin da king yake ciki hakan be Hanasa hugging d’in khaleed ba kamar yadda shima khaleed d’in ya yi , fuskarsa d’auke da murmushi ya furta “ sorry dude “ be ce masa komai ba ya jinjina masa kai, tare suka nufi falon abeey, Alhaji kabeer na ganinsa shima yayi hugging d’insa “ my son? Ya kake? Ya jikinka? Take heart komai zai daidaita please bana san ganin ka cikin wannan yanayin”, shima king bece masa komai ba bayan gaisuwar da ta had’asu , minti 5 ya mi’ke zai fita khaleed yabi bayansa direct part din ummey suka nufa , gabaki d’aya jiyai yana bukatar mahaifiyarsa yau ko tunanin Ammey be yi ba , ummey na ganinsa shida khaleed ta saki murmushi , shima khaleed na ganinta yayi hugging din ta “ ummey nayi kewar ki sosai da sosai “, wani murmushin ummey ta saki tana kallan king “ Nima nayi kewarka sosai my son “
    Ni kuma fa?” Cewar samreen da ke fitowa, murmushi yasakar mata “ Ukhti waya isa ya manta dake kin manta kece ta gaban goshina “ hararar sa tayi , kana dai guduwana sabida nace Kayi aure ko? “ kai ya d’an sosa kadan “ karki damu ankusa insha Allah “ Allah yasa cewar ummey. King na zaune ba abunda yace mikewa ummey tayi batace komai ba ta kama hannunsa zuwa dinning, mamaki ne ya kamasu samreen , ukhti har da yi musu vidoe ganin abun mamaki, abunda ummey ta dad’e batayi ba , da kanta ta zubawa king abinci, shima mamaki ne ya kamasa Amma be nuna hakan ba, mamaki be gama kamasu ba sai da ummey ta d’auki spoon zata bawa king abinci a baki da kanta , ukhtii harda tsallan murna ita da khaleed kamar wasu yara suka fara musu vidoe , murmushi ummey ta sakar wa king kamar wani ‘karamin yaro ta furta “ haaw” bud’e bakinsa kuwa yayi ummey ta fara feeding dinsa, 5 spoon yayi ya d’auke face dinsa amma ummey ta hanasa Tashi saida ta tabbatar yaci sosai , shima king saban abinci ya zuba ya d’auki spoon zai fara bawa ummey abinci, samreen kamar ta taka rawa Sabida ganinsu da tayi cikin wannan yanayi, d’an harararsu king yayi , itama ummey bata bi ta kansu ba ta kama hannun king sukabar Wajan . Ai khaleed kam saida ya taka rawa ko ba komai hankalin abokinsa zai kwanta.

    ??????

    BUNKURE

    Tsawan wata d’aya abubuwa da dama sun faru cikin wannan yanayin, ciki har da islamiyya da Matan gidan Suka koma , da yamma kuma suna awarar siyarwa, idan babu makaranta kuma da safe suna yin Koko da ‘kosai, gabaki d’aya rayuwar gidan ta canza , babu Wanda zakaji yana fad’a da d’an uwansa, duk Wanda yyi sallah yanxu sai yayi wa oumma addua dan tayi musu Hallaci sosai , ta mayar musu da alkairi akan sharri, ta tallafesu a lokacin da suke bu’katar taimako, gabaki d’aya sun zanca , ga gyaran gida da Alhaji kabeer yake musu bayan kasuwa da ya saka mazan, duk wannan abun da ke faruwa oumma bata san yanayinsu. Har zuwa tsawan lokacin nan kuwa babu Dije ko bintalo babu alamarsu, Suma mutanan gidan gabaki d’aya babu Wanda ya damu da su, kullum Burunsu Allah ya ‘kara had’a kansu dan ba ‘karamin azabtuwa sukai wajan Dije ba ,yanxu ma marka d’an awara aka kawo musu matan gidun suke yi, kaka tabawa ma yanxu kullum cikin addua take wa oumma da muhammad, bata aikin komai sabida ciwan kafar ta , yan gidan ne Suke komai , babu nuna hantara a tsakaninsu, gabaki d’aya babu Wanda zaice akwai wani abu da ya ta’ba had’asu , sai ma insunga mutum yayi ba Daidai ba suyi kokarin dakatar da shi nayi masa nasiha .

    *********
    *************
    ******************
    AMMEY ????????????…….

    Lokacin da Ammey ta samu labarin farkawar king zaucewane kawai batayi ba , a har gitse ta shiga cikin d’akinta tana neman zoban tsafinta, bata Ankara ba taji ansha’ko wuyanta ta baya an bugata da ‘kasa, bata Ankara ba taji an ‘kara sha’ko wuyanta, mutumin da suke magana kwanaki ne yanxu kamar kullum fuskar sa a rufe , cikin ‘bacin rai ya furta “ kikace zaki kashesa kafin farfad’owarsa, me yasa kike ‘ko’karin ‘Bata mana aiki ? , ya mukayi dake ?karde kin fara tausaya musu?” A wahala Ammey ta fusge kanta daga sha’kar da akai mata,” karka ‘kara sha’keni haka ? me ya kawo ka d’akina ? Ka fice ka bani waje” wata ‘yar iskar dariya ya somayi kafun ya fincikota ya turata kan gado, girgiza masa kai tayi “ karka matso Inda da nake “. ‘Dauke fuskar Ammey yayi da mari” kinaso kisan me ya kawo ni ko? Yanxu zaki ga aiki da cikawa ai “ yana kai ‘karshen zancenta ya hau kan Ammey duk yadda taso turesa abun ya gagara, shima cike da mugunta ya fara faffarkewa Ammey kayan cikinta, be tsaya bi ta kanta ba ya shigeta da mugun ‘karfi cike da mugunta, wata gigitacciyar ‘kara Ammeey ta saka Sabida azabar da taji amma duk da haka be saurara mata ba , cike da mugunta Yake binta, saida ya tabbatar bazata moruba ya mayar da wandan sa ya ‘bace gabaki d’aya inda Ammey take Jini ya ‘bata wajan dan ba ‘karamin ‘barna ya mata ba dukda kasan cewar ba yau suka fara ba, amma yau ko sabuwar amarya ??( Allah shi ‘kara Ammeey ??????).

    ???????

    Kwanan khaleed biyu a lagos ya fara shirye shiryen komawa Abuja , already alhaji kabeer ya tafi shi tun aranar, sosai khaleed da king suka saka bincike tahee har yau babu ita babu alamar ta , gabaki d’aya ya canza ya koma asalin king d’insa mara fara’a , da surutu, tsakanin su ummey da abeey sai aka rasa wanene yafi kula da king, hatta su momy da mamy ba a barsu a baya , uncles dinsa ma sosai suka bada rawar ganin Wajan bincikar Inda tahee take, aunty ma tazo ta duba sa lokacin Amrah taje kidan su batasan da farkawarsa, Ammeey ce kuwa har yanxu bata shiga ba dan acewarta bata da lapiya, hatta abeey sai da yazo dubata amma bata ko ‘kafar king bata gani ba , dan har yanxu ko ‘kwakkwaran tafiya batayi sosai Sabida yadda ta ke tafiya kamar ‘yar kaciya,kowa na gidan yazo dubata banda king da hankalinsa yake kan iyalinsa.

    Karfe 2:30pm jirgin su khaleed zai Tashi, 12:20pm yana zaune falan dada , yana danna wayarsa su sumayya suka shigo falon, gaishe dashi Suka yi amma gabaki d’aya hankalinsa yana kan ilham , sanye take cikin doguwar rigar atampa, ta yi d’aurin zahra buhari, bakinta sai shinning yake , yadda yake kallan ilham yasa sumayya kallansa a fakaice tana danne dariyar ta da ido tanunawa firdausi, ka she mata ido ta tayi suka mi’ke a tare , kallan su ilham tayi” Ina zaku?” Danne dariyarta firdausi tayi kafun ta furta “ karki damu ynxu zamu dawo “ basu jira amsarta ba suka bar falon, da harara ta bisu zata mi’ke taji saukar muryarsa” please ko zan iya samun ruwa ?” Jinjina masa kai tayi kafun ta nufi fridge , ruwan ta d’auko masa had’e da lemo sai cup,tana ajje masa yace ta zuba masa kamar zatayi ihu haka ta zuba masa , “ kinyi kyau sosai kamar sarauniya”, da Sauri ilham ta kallesa zuciyarta na bugawa da sauri sauri, shima idanuwan nasa ya zuba mata, da Sauri ta d’auke nata , “nagode “, har yanxu be d’auke kallansa akanta ba , zata tafi ya furta “ please ki zauna” gabaki d’aya sai nutsuwarta ya d’auke ga bugun zuciyar da take samu , idanuwansa har yanxu akanta, waje ta samu ta zauna ba dan taso ba “ yanxu zan tafi, amma zanyi kewarki”yanxu kam gabaki d’aya ya gama kwancewa ilham notikan kanta, “ me yake nufi ?” Take tanbayar kanta , bata ‘kara sham mamaki ba sai lokacin da ya furta “ please ki kalleni ko zanji dad’i” kunya ce ta kama ilham kamar ta saka ihu, kujerar next to her ya dawo yana kallan yadda ta sunkuyar da kanta ‘kasa “ please baby kalleni “, yadda taji zuciyarta na tsanan ta bugu ne yasa ta mi’kewa zata gudu yayi saurin shan gabanta “ ba sai kin gudu ba ni bari na tafi tunda bakya bu’katar gani na, wani ‘karamin box ya d’auko ya ajje mata akan table , “ gift d’in kine wannan, please ki kulamun da kanki”, yana kai ‘karshen zan cansa ya soma tafiya, zuciyar ilham ce ta soma bugawa ga wani abu da take ji ‘kasan zuciyar ta ganin kamar be ji dad’i bane yasa ta zauna wa kan kujera tana bin ‘karamin box d’in da kallo, sumayya da firdausi ne suka fito daman ba tafiya sukai ba , cikin tsokana feedy ta furta “ please Baby”dariya summy ta saka itama kafin ta furta “ ki kulamin da kanki”, pillow ilham ta d’auka ta jefa musu, Wana ta suka ‘karaso tare da d’aukan box d’in zasu bud’e tayi saurin fusgewa , da ‘karfi ta furta “ banasan gulma”, tafawa summy da feedy sukai lokaci d’aya ganin yadda ilham ta gudu.

    ????GIDAN AUNTY????

    07041879581
    Mss Lee??

    Book 2

  • A Rubuce Take Book 2 Page 36

    A Rubuce Take Book 2 Page 36

    Part 02

    Page 36

    Har sun dauki hanyar gida ya cewa umar ya kaishi gidan hajiya,ya sakashi ya shiga da motar ciki ya karbi key din gidan ya bude ya shiga.

    Komai na gidan yana nan tsaf tamkar tana raye,ba qazanta ba komai,su umar suna kula da gidan yadda ya kamata,har ya bude parlor dinta zai shiga sai ya kasa daurewa,ya fito ya bude dakinsu umar din.

    Wanka yayi ya sanya boxer da farar riga armless,ya rage hasken dake shigowa dakin ya kwanta,a maimakon bacci sai tunani suka cika kwanyarsa fal,ya dinga bitar halaye da dabi’un hafsat din,yana kuma irgen shekarun da suka dauka a haka ba tare da wani sauyi daga gareta ba,har cikin zuciyarsa yana jin ya fara qosawa,haqurinsa kuma yana dab da qarewa,abu daya yake tunawa yake kuma tausayawa,mimi nawwara da yusra,bayason su girma su kalleshi a matsayin wanda ya gaza wajen samar musu da nagartacciyar uwa.

    Haka yayita saqe saqe,kansa kamar tsage saboda rashin bacci da tunani,dole ya jawo wayarsa yana dubawa,ya cika da mamaki fal na rashin ganin kiran widad ko sau daya daga jiya zuwa yau,wani abune da bai taba faruwa ba a tsakaninsu saida wannan ibtila’in ya fadowa rayuwarsu,ya gama lalubensa sai ya kirata kai tsaye.

    Tana zaune riqe da wani qaramin littafin addu’o’i da anty madeena ta hadota dashi tana dubawa tare da qoqarin haddace wadanda suke na ko yaushe suke fi kuma muhimmanci,tun jiyan yana ranta,amma kuma batason bada kanta ta kirashi,tanason ta auna yadda take da matsayinta a yanzu a zuciyarsa,akwai abinda ya sauya ne ko har yanzun tana nan dai a yadda take a wajensa bata motsa ba.

    Qarar wayar yaja hankalinta,koda ta duba taga sunan data saka masa akan wayar sai ajiyar zuciya ta qwace mata,ta kife littafin ta dauki wayar ta kara a kunnenta.

    Sassanyar muryarta ta sauka a kunnensa, abinda ya sakashi sakin ajiyar zuciya da sautinta ya shiga kunnuwan widad

    “Kina azabtar dani da yawa maman affan,na dahu haka na dahu,wallahi nayi laushi over,don Allah kiyi haquri ki sassautawa dan marayan da baida uwa baida uba……sai Allah saike……”

    “Sai kuma uwar gidansa,sarautar mata” ta tari numfashinsa tana qarasa maganar da ba ita ta daukota ba.

    Dif sukayi gaba dayansu shida ita,ita tana sauraren amsar da zai bata,shi kuma yana fama da wasu abubuwa data saukarwa zuciyarsa,sai yaji harshensa yayi nauyi,duk wani abu da yayi shirin fada ya kama gabansa,bashi da sauran zabi illa zame wayar daga kunnensa ya kuma kasheta gaba daya ya koma yayi rub da ciki yana sauke numfashi da qarfi.

    Taji lokacin da wayar ta tsinke,don haka ta cireta daga kunnenta tana kallon wayar,tausayinsa ya darsu a ranta,amma ya zatayi,ta kasa daina jin zafin wai hafsta ce zata hadasu?,har ta isa ta zama silar girgizar yadda tsaftatacciyar qauna shaquwa da soyayyar da suka ginata ita dashi?,wata zuciyar na raya mata ta kirashi,wata tana hanata tare da gaya mata ki barshi ya sake dandanar irin abinda kika dandana,duk da ranta ba dadi hakanan ta shareshi,ta dauki littafin addu’o’inta taci gaba da dubawa.

    Da qyar ya samu bacci ya daukeshi,saboda maganar data gaya masa tayi masa nauyi da yawa a qirji,ya samu baccin nasa yayi nisan zango,don har missing salloli biyu yayi,ya tashi da hanzari ya daura alwala ya bada su, kafin ya kammala wayarsa ta fara tsuwwa alamun shigowar kira.

    Miscall uku ne na ezekiel,kafin ya gama dubawa tex ya shigo masa akan idan ya samu miscall dinsa ya kirashi.

    Sai da ya gama ‘yan addu’o’insa sannan ya zauna sosai gefan katifa ya kira Ezekiel din,bugu daya ya daga,ya gaidashi cikin girmamawa,sannan ya fara bashi feedback akan aikin da ya basu.

    Tunda ezekiel ya fara bayanin idanunsa a kulle suke yana saurarensa,babu abinda zuciyarsa keyi illa bugawa

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” kawai yake maimaitawa a hankali bakinsa yana motsawa,sai da ya gama bayanin tas abbas yayi saluting nasa,ya kuma tattara komai kama daga recording na muryarsa da video ya turawa abbas din ta email dinsa sannan sukayi sallama bayan ya gaya masa kwana biyu yakeso lawan yayi a cell,zaizo da kansa ya fiddashi.

    Duk da jikinsa yayita bashi hakan,duba da sanya idanun da yasa umar yayi masa kan yanayin mu’amalar dake tsakanin hafsat da lawan din,amma kuma ya girgiza matuqa,yadda har lawan ya iya aminta suka hada baki suka shiryawa widad din wannan tuggun,wanda kai tsaye zai iya cewa shi suka cutar bawai widad ba,duk abinda zai cutar da iyalinsa kai tsaye za’a iya cewa shi ya cutar,bare mummunan al’amari irin wannan,ya jima yana juya dalilin da yasa hafsat din ta sadaukar da lokacinta da kudinta ta sanya akabi widad din har hotel din akayi mata hotunan,me hakan ke nufi?,me takeson ta cimma,tace gyara,amma ta haka ake bin hanyar gyara?.

    Bai dauki komai ba illa key din motarsa ya fita a gidan ya nufi gida,yana tuqi cikin qarfin hali ne kawai,babu wani karsashi a tuqin nasa,har ya isa gidan,ya wuce parking lot ya ajjiye motarsa.

    Sashensa kawai ya nufa,don sai yaji gaba daya ya tsani kallon fuskar hafsat,mutum ne tsayayye ma’abocin gaskiya da kuma son aiwatar da ita,wannan ya sanya ya tsani qarya da maqaryacin mutum qwarai da gaske,ya buda sashen nasa ya shige ya maida muqullin ya rufe,sannan ya wuce bedroom dinsa kawai ya fada saman gadonsa qwaqwalwarsa na zayyano masa kalolin hukuncin da zai dace za hafsat,don ta lawan ya tabbatar ko iya haka ya barshi ya zuwa yanzu ya gane Allah daya ne,bare shi dinma bazai qyaleshi haka ba,yabar masa gidansa bari na har abada.

    *H A F S A T*

    Tun da rana data aiki lawan take jiran dawowarsa amma shuru wai malam yaci shirwa,tun tana bashi uzuri harta tunzura ta fara fada,ta kuma fara neman layinsa amma anata gaya mata a kashe layin yake,ta zauna tayita masifa tana kumfar baki,ragowar lace din da aka siya na anko ne a wajenta guda daya bai cika ba,ta bashi kudin kan yaje kasuwa ya cikaso mata dayan,gashi sun gaya mata suna hanya amma shuru babu shi ba dalilinsa.

    Sai data gama fadan ta godewa Allah ta koma taraddadi kuma saiga kiransa,sanda ta daga da niyyar yin sababi sai maganarta ta tsinke sanda taji muryarsa a shaqe kuma cikin tashin hankali yana magana da ita

    “Ina hannun police,sun kamani ne akan batun maman affan, wallahi bakiga mugun dukan da nakesha a hannunsu ba,yanzu haka basusan da wannan wayar a hannuna ba,sun gama dukana sun fita su hutane na kiraki,don Allah kizo kiyi beli na,ki fitar dani daga wannan masifar da kika jefani a ciki”. Wata hajijiya ce ta kwasheta ta jefar,dama da gaske ne kenan?,ashe dai zancen bai mutu ba?,wannan wacce irin masifa ce,tana zaton komai ya lafa,tana zaton ta samu nasara ashe qura tana baya

    “Idan na sake nazo wannan wajen lawan na zama nama na tabbatar,ka jirani zan nemi abban mimi na gaya masa qarya da gaskiya,zaiyi magana kosu waye na tabbatar zaka fito” saita yanke kiran tabar lawan da waya a hannu cikin matuqar mamakin yadda takeso ta barshi shi kadai a masifar,bayan ita ya yiwa aikin.

    Sanda taketa yunqurin kiran wayar abbas din a kashe take,dai dai sanda ya kashe wayarsa bayan widad ta yaba masa maganar data masa zafi matuqa,tayita kira a jere amma amsar daya ce,haka ta fito wajen baqinta tana rarraba idanu,fuskarta a yamutse,gumi yana tsattsafo mata ta kowacce kafa ta jikinta

    “Don Allah ina zuwa” ta fada tana yin waje da hanzari zani a hannu kamar zata ci da baka ta fara kiran wayar habiba tana dosar sassan abbas da nufin fakewa a can tayi wayar,don can dinne bata da haufi dashi,tana da tabbacin babu kowa a ciki bare tayi shakka ko taji dar dar din wani zai iya jinta.

    Koda ta bude sashen abban din sai data tabbatar ta qule har cikin bedroom dinsa,tsabar hankalinta a tashe yake bata ma yi tunanin yadda akayi qofar bedroom din yake a bude ba,burinta kawai ta isa dakin habiba kuma ta daga wayarta.

    Sama sama ya dinga jin magana yana tsaye gaban madubin bandakin yana kallon fuskarsa,ya matsawa kansa da tambaya da kuma tunanin son sanin yadda akayi ya yankewa widad wannan hukuncin,ya akayi ya aminta da zancan hafsat,a irin baiwa da Allah yayi masa,a irin matsayi da yake dashi da rank a wajen aiki?, tabbas wannan babbar jarrabawa ce,kuma qaddara ce mai girma,wadda ya godewa Allah da ya taqaita masa komai,bai jarrabeshi da sakin widad ba.

    Sautin muryar hafsat da ya fara ji yasa ya tako a hankali zuwa gaban qofar,har ya sanya hannu zai bude qofar sai ya fasa,kalamanta cikin rudani da tashin hankali suka fara shiga kunnuwansa

    “Ina cikin tashin hankali habiba,komai yana iya faruwa dani,wannan maganar dai bata mutu ba yadda malam yace,yanzu haka lawan yana hannun ‘yan sanda ba,na tabbatar zuwa yanzu indai sun gama bincikarsa to asirina ya gama tonuwa,don ba lallai ya iya iurewa dukansu wallahi sunana zai fadi,ki taimakamin habiba a sake danne maganar nan,dama hankalina tun ranar da sukayi maganar zuwa kotu ba’a kwance yake ba,ko baccin kirki bana iyayi wallahi,idan har abbas yaji maganar nan bani da sauran dabara kuma sai abinda y……..” Gaba daya ya rasa karsashi da qwarin gwiwar tsaiwa yaji qarshen maganganunta,hankalinsa yayi mummunar tashi,bayan sharri makirci da qazafi harda bin malamai hafsat din ta hada dashi?,a yaushe?,kuma yana me?,sai kawai ya buda qofar da wani irin qarfi,qarar qofar taja hankalin hafsat har sauran maganar ta maqale mata a maqoshi.

    Batasan wanne yanayi ta shiga ba,suma tayi a tsaye ko mutuwa tayi ta dawo?,itadai ta bude idanunta taga abbas a gaban mudubi riqe da biro yana rubutu,ta dinga qoqarin zaqulo kalamai daga qasan maqoshinta amma kalma daya ta gaza fita daga bakinta,har ya kammala rubutun ya iso inda take ya ajjiye takardar a gefanta

    “Daraja daya zuwa biyu kawai zakici yau a hannuna,na farko iyayen widad tun sunan zallar tauhidinsu,sun miqa ki kotun ubangiji wadda babu wata kotu a gaba da ita,babu wani adalin alqali da yakai ubangiji iya hukunci,to kije ni dasu suka mun barki da wannan,na biyu kuma kinci darajar mimi nawwara da yusra,banason na fito na qara ganin fuskarki cikin dakin nan,idan kuma baki yarda ba……” Sai ya murza yatsunsa kawai ya gewayeta ya fice ya barta a wajen a tsugunne.

    Dukka hannuwanta ta saka ta kama kanta da kyau ta riqe,sai kuma ta saki kuka mai qarfi kamar wata zautacciya

    “Haba abbas……daddyn ya zakayimin haka?,ko meye nayi nayi ne saboda kai” sake rushewa tayi da kuka,tana jin abun tamkar a mafarki,yau ita abbas ya saka?,abinda bai taba giftawa ba tsahon zamansu sai a yanzu?,a dalilin wata?,wai shin saki nawa ma yayi mata?,sai ta zabura ta dauko takardar ta warware jikinta yana rawa kamar wadda zazzabi ya yiwa mugun kamu.

    Saki biyu ta gani a rubuce fes,ta saki takardar tana sake rushewa da kuka,duk da ta samu sassauci ganin akwai sauran igiya daya da tayi saura, saita miqe da sassarfa ta fita daga dakin nasa ta doshi sashenta.

    Wayam ta tarar babu kowa,ba yaran babu baqinta,ta shiga nemansu kamar zautacciya lungu da saqo na gidan amma babu su,a bakin gate shazali ya gaya mata yaga mai gida ya fita shi da yaran duka a mota,batasan sadda ta sulale a wajen ba ta sake fashewa da kuka,tsoro ya kama shazali ganin yadda take sheqa kuka yau a gabansa,gashi babu damar ya tambayeta ko kuma ya bata haquri saboda yasan cin mutunci irin nata,haka ya koma gefe yana satar kallonta,har ta gama me isarta taja qafafunta tayi cikin gida bayan tayi futu futu da jikinta a wajen.

    Baifi minti talatin ba sai gata da jakarta tana janta,ta buda motarta ta jefa jakar ta shige itama,ta dannewa shazali wani mugun hon,tuni ya durfafi gate din ya bude mata da hanzari gudun kada ta huce haushinta a kansa.

    Gidan yaaya bara’atu yakai yaran wadda ta cika da mamakin ganinsa,diyarta budurwa ta kira ta dauki yaran,tace ta hada musu abinci,tuni sukabi bayan mariya ta zuba musu abincin suka sake abinsu sunaci,don dama yunwa ce fal cikinsu,tunda tun rana rabonta da basu abinci,tana ta business dinta,sai kuma wannan tashin hankalin yazo ya ratso na kama lawan,hatta da yusra abinci taci sosai,suna gama ci ba dadewa dukkansu bacci ya kwashesu a wajen.

    A can falo kuwa Shuru yaaya bara’atu tayi kamar ruwa ya cita,jikinta gaba daya ya gama mutuwa murus,tausayi da kuma namijin qoqarin da abbas yayi na zama da ita har tsahon wadan nan shekarun duka sun gama kasheta,gidan abbas dama duka ba wajen zuwansu bane,don babu fuska daga wajen hafsat din,wannan yasa da yawan dangi suka janye jiki saidai idan an hadu a gaisa,wannan ya sanya da yawa basusan wanne hali yake ciki ba,sai idan taso kawo qorafinta a kansa ta hada qarya da gaskiya ta fada saboda ta bawa kanta kariya.

    “Inason yaran suci gaba da zama a wajenki kafin na gama settling komai”

    “Ko har abada zakace ka barminsu ina maraba da haka” ta fada tana girgiza kai zuciyarta tana karaya,tausayin yaran na sake kamata.

    Murmushi kawai ya saki,yana son yaransa sosai,bayajin zai iya kyautarsu.

    Daren ranar daga hafsat har ummanta babu wanda ya runtsa,sun raba dare suna jajanta abun,don basu taba zaton zai iya sakinta ba,sun masa mugun qullin da tun aurensa da hafsat din sukayi wannan shirin,tsohon shiri ne da ita kanta hafsat din ta manta anyishi,saboda a sannan zuciyarta najin zata iya zama da abbas ba tare da anji kansu ba,zata kuma iya sauke duk wani hakki nasa,tayi abinda yakeso tabar wanda bayaso,don sanda umman ke mata albishir din anyi abun ma ita bata wani daukeshi da muhimmanci ba.
    [24/05, 7:39 am] Mimah Yusuf: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)