Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 9

Sponsored Links

Page9️⃣
Haka ya ringa lalube don Koh sanda Bai rike ba ya fita waje, da ita,yaje

titin shuru haka ya ringa takawa a Gefen titi ba tare da yasan inda zai nufa ba,

cikin ikon Allah sai ga wani Mai mota yazo wucewa ganinsu cikin wani Hali yasa shi tsayawa a saitin, Al’ameen Yana tambayar sa lfy kuwa ya gansa da mace a bakke a kafada Bata motse gashi Koh takalmi babu a kafarsa da asuban nan?

Da sauri ya juyo wajen da yakejin muryar Mai motan don Allah ranka shi Dade ka taimaka mini matatace ba lfy wallahih tun jiya yanzun haka Suma tayi Ina son kaita asibiti Amma ban samu abin hawa ba,

Allah sarki shiga muje Nima kwanace ta kamani a hanya sai yanzun na shigo gari,

Allah ya saka nagode,ya fada Yana laluben murfin mota tsabar tashin hankali Yama kasa budewa ,abin ya bawa Mai mota mamaki, yadai malam lafiya Naga kana lalube baka shiga ba,?

Bana ganine,ka taimaka ka bude mini,

Ba karamin mamakine ya Kama Mai mota ba ace mutun Kamar Wannan baya gani lallai Koh wani bawa da kaddaransa,

Fita yayi yazo ya bude Masa

A hankali ya shimfida Sumayya asset in baya shima ya shiga Mai mota ya rufe ya zagaya shima ya shiga mazauninsa yaja motar ,

Wani asibiti Zan kaiku?

Duk asibitin da yafi kusa damu ka kaimu

Ok ya kara gudun motar lokaci kankani suka iso FMC don yafi kusa da SINTALI ( sunan unguwansu Al’ameen)

Suna Isa emergency Mai motar ya kaisu fita yayi ya shiga Hall in ya Kira nurses za’a d’auki Mara lafiya suka fitoh da sauri aka aza Sumayya bisa keken marasa lfy aka wuce da ita dakin taimakon gaggawa,

Likituti suka,rufu a kanta don Bata taimakon. Gaggawa

shi kuma nurse tace Masa yaje ya sai Mata card a bude mata file,

Wajen sai da card in ma da taimakon Mai motar ya gane,

kudin card naira 300 matar da ke windown tace,

ba karamin tsinkewa yayi ba sai yanzun tunaninsa ya dawo jikinsa, don Koh sisi baida shi sai naira dari da hamsin na cinikin jiya, ya Allah ka taimake ni abinda ya ke fada kenan a ransa,

Malam.koh bakaji bane nace 300 ne kudinka shuru yayi Yama ya kasa magana,

Mai motar ne ya fahimci Koh sisi baida shi kenan

fitar da dari uku ya Biya kudin card

Menene sunan majinyacin?

tambayar sa akaye me sunan Mara lafiya, Sumayya
,sunan surname?? Shuru yayi yana tunani a hankali yace Abdulsalam shugaba,ya fada Dan in Bai manta ba haka yaji agun daurin aure aka fada,sai da ta daga kai ta sake kallonsa Jin sunan da ya fada amasayin sunan mahaifin maralafiyar da suka kawo,

lokaci kankani aka bude Mata file in ,

Yama rasa bakin godiya sai gode ma mai motar yake, nagode nagode bawan Allah ba abinda zance maka sai Allah ya saka maka,

Ba kome ai ka gode Allah,
sunana Ammar Ina zaune da iyayena a unguwan millionaire’s sweet,ya fada Yana Kama hannun Al’ameen Yana Masa jahora zuwa masallacin asibitin sukayi sallah suka dawa Kan kujirun da ka jera a Hall in,suka zauna,

Nurse ce ta fitoh tana tambayar suwaye suka kawo Sumayya Abdulsalam shugaba?

Mekewa sukayi Ammar na rike da hannun Al’ameen suka Isa wajen da take

Gamu nan

Mika musu takardan magani,doctor yace ku saya maza-maza don ana bukatar sa emergency,

Hannun Al’ameen na rawa ya amshi takardan hade da tambayar ta don Allah ta farfado ne ya jikin nata,??

Eh ta farfado Amma ana bukatan kuje ku sai Abubuwan da aka rubuta muku,..

Kama Masa hannu Ammar yayi suka wuce pharmacy suka je

Mika takardan maganin sukayi

karba sukayi suka duduba ruwane da allurai sai maganguna,

Kudin ku naira dubu bakwai da dari biyar,

Shikam Abu ya hade Masa goma da ishirin Ina zai samu kudi Mai dunbin yawa har dubu bakwai da dari biyar,

Koh Kama sayar baidashi bare ya Kama ya sayar ya Saya mata magani Innalilahih wainnailaihir rajuun yake furtawa hade da karban takardan balance ya fita tsabar rudewa shikamma ya manta da wani Ammar suke tare,

Ammar ne ya biyosa ganin yana faman lalube zai fita a pharmacy in da sauri ya rike Masa hannu,

Habba Dan uwa karka dagawa kanka hankali Mana Yana fada ya karbi takardar ya rike hannun Al’ameen suka shiga waje biyan kudi

Ammar ya biya kudin suka karbi magangunan da su ruwa da allurai suka Kai emergency, suka mikawa nurse in ta shiga dakin,

sai a lokacin hankalin Al’ameen ya kwanta sosai yayita ma Ammar godiya shikam ma har kunya ya kamasa Kamar Wanda ya bawa million biyar,.

Sai 8:30 aka barsu suka shiga suka ganta ta farfado Ansa Mata ruwa da alluran bacci don ta samu hutu sosai ciwon ya lafa

Toh abokina Zan wuce Naga gari ya fara wayewa gashi sai kirana ake daga gida kasan Dana shigo *Jala* na Kira gida nace musu na shigo,

Ba kome wallahih nagode sosai Ammar Allah ya saka da alkhari

Habba wanna godiya ya Isa haka,baka fadamin sunan kaba fa har yanzun?

Suna na Al’ameen,ya basa amsa

A unguwan da na dauke ku kake ?

……Eh

Ok toh insha Allah Zan dawo na duba Mai jiki

Nagode nagode Ammar

Sai anje ma, ya fada Yana kokarin fita a Hall in sai Kuma ya dawo,

Koh xan kaika gida ka dauko Mata Kaya da Abubuwan bukata Kamar Kayan da zata chanja su maclen da brush da abubuwan bukata kaima ka samu ka kimtsa jikinka Naga Kamar a birkice ka fitoh Koh takalmi babu nasan har yanzun baka San kafarka ba takalmi ba hh ya fada cikin wasa Yana dariya,??

Shima Al’ameen in dariya yayi kawai, Yana cewa toh muje don wallahih rudewa Kam na rude,

Hannunsa Ammar ya rike masa suka fitoh ya bude Masa mota ya shiga ya ja suka wuce, suna tafiya suna Hira

Amma dai ku sabbin aure ne Koh?

Eh yau kwanan mu hudu,

Kai kace ango ne da kansa Koh dai Mai kashane, amarya har asibiti

Dariya kawai Al’ameen yayi baice kome ba don bazai iyya fadawa Al’ameen sirrin Saba duk da yaji bawan Allah ya kwanta Masa arai Yana da kirki sosai koma zasuyi sa’o’in juna Amma hakan bazaisa ya tsake jiki dashi ba don mutumin duniya ba abin yarda bane lokaci guda,

Sun Isa har inda ya dauki Al’ameen tukunna ya tambaye sa sun iso wajen da ya dauke sa da asuba ata Ina gidan naku yake?

Ah ah Ammar sauke ni ma anan na gode

ah ah kaidai kamin kwatance

Ah ah wallahih hakan ma nagode,ganin ya nace yasa Ammar sauke sa

Sukaye sallama

A hankali Al’ameen ke tafiya Yana Dan yaryarfa hannunsa don Ya tabbatar inda yake sa kafarsa ba mutum Koh wani abu inda Allah ya Sosa ma tsallaken titine aka sauke sa ta barin gidansu a hankali yake tafiya Bai Ankara ba yaji an bangajesa haryaso faduwa saura kadan da yakai kasa, wani zafi yaji a yasansa don ya buge dutse sosai yatsan ke Masa zafi a hankali ya mike, Jin Wanda ya turesan Yana bala’i, ku wasu irin mutane ne in ka San baka gani wani rawan Kaine zaisa ka fitoh babu D’an jagora babu sanda, irin hakane ai sai ku hau titi mota yabi ta kanku kujawa mutum jaraban jinya inkun mutu Kuma kusa mutun azumin kaffara mtwss,,

Ya fada Yana tafiya

A hankali Al’ameen ya d’uka ya taba yatsar Jin damshi yasashi gane jini ke zuba,

Bai damu ba ya cikaba da tafiya har Allah yasa ya iso kofar gidansu ya shiga,

Yana shiga cikin gidan ya samu Yan gidan a filin tsakar gida kowa na sha’aninsa daga masu wanke wanke sai masu wanki sai masu kitso masu Jan ruwa wasu Kuma group aka hada ana ta gulma ana xagin juna,,,

Ganinsa ba takalmi sanan ga jini a kafa Yana zuba, yasa Rabi’u fara magana Kai MAKAHO daga Ina haka a bujaje yau tun safe ma bamuga fitarka ba?

, kafun ma yayi magana iro dake goge takalminsa zai fita yace Wai fa D’an rainin wayon nan jiya Ina bacci yazo karfe kusan daya Wai nakai matar sa asibiti Bata da lfy kaji Dan rainin wayyo wama ya sani Koh turmushe Yar mutane yayi xaizo tsakan dare yana tashina,,gabaki dayan su suka saka dariya,

Shidai kala baice musu ba hanyan shashen su yayi da lalube harya shiga sai a lokacin ya tuna Ashe fa kofa a. Bude ya barta cikin D’an fargaba ya shiga dakin don shi tsoronsa ma kar Yan gidan su shigo su Ma Sumayya sata don shikam baida abinda za’a sata, wayarta daya Mika Mata jiya da dare shiya fara lalubawa akan kadon aiku yajisa,

Hakan ya tabbatar Masa ba Wanda ya shigo tunda ga waya a fili Amma da an shigo wayar nan dake zaune a fili haka da an sabe sa hamdala yayi ya gode Allah Basu San ya fita ba,

iban ruwa yayi yashiga bandaki yayi wanka yasa wasu Kayan ya rufe kofar ya fita don bazai iyya gane inda kayanta suke ba,

Sandar sa ya dauka ya fita a gidan hanyar gidan Goggo Amina ya nufa,

Yana Isa kofar gidan ya tsaya a waje yayi sallama,

Shan cikin gidan kuwa Khadija nawa Goggo Amina kitso taji sallama Kamar ta yayanta Aiko ita ince amsawa tayi tare da daukan hijab inta ta fitoh waje

Yana tsaya yaji isowar Khadija bakin ta na amsa sallaman sa

Ina kwana Yaya ya aunty?

lafiya Alhamdulillah Khadija

Ka shigo mana Yaya Goggo ne kawai a gidan yau ?

Toh ya amsa Mata

Ta Kama hannunsa suka shiga cikin gidan kujira ta aje Masa ya zauna Yana gaida Goggon tasu, Ina kwana Goggo?

Ta amsa da kulawa

Lafiya Alhamdulillah Muhammad y’ay’a iyalin taka?

Lafiya Alhamdulillah sai dai bataji Dadi ba jiya da ciwon ciki ta kwana yanzun ma daga asibitin nake nazo na dauki Khadija tazo muje zata dauka Mata kayayyakinta Koh kadanne Zan Kai Mata asibitin,

Subhanallah Allah ya Bata lfy wani asibiti ne?

Ameen a FMC ne ya amsa Mata

Khadija tashi maza kuje, toh Goggo ta amsa Mata tana mikewa

Shima Al’ameen mikewa yayi,hannunsa Khadija ta Kama suna tafiya a haka,

Yaya jikin nata da sauki Koh?

Da sauki Khadija Yaya zan bika muje asibitin?

Ah ah Khadija ki tsaya a gidan namu ke dafa mana abinci tunda Kinga asibitin FMC ne babu nisa saiki Kai Mana can,

A wani block ne yaya?

emergency ne

har suka Isa gidan nasu suna Hira dakin ta shiga ta dau jakan Sumayya mabi da ket ta Ajjye tana iban Kaya a whtdrp tana zubawa hijab D’aya, sai dogayan rikuna biyu, zani fille fille guda biyu,sabbine kal ta hada da t-shirt biyu, da hula biyu, sai maclen da brush ta hada Mata da kananan Kaya su pants brz da vest ta rufe akwaitin,

Yaya na Gama Amma dai tunda kace tun asuba kuke asibiti baka samu kaci karyawa ba koh?

Kai Khadija kin cika surutu wallahih inkin gama kika kawo Mana ai zanci,

Amma yaya yanzun fa ana neman 09:30 na safe baka karya ba in kaje asibitin Yaya ka samu abinda zaka saya muku kuci Kaida Aunty kafun na Gama,

Toh Addata Khadija

Hhh ye Hakuri yayana ..

Baice Mata kome ba illah daukar jakar da yayi Yana lalube zai fita a dakin idon Khadija ya sauka a Kan kafarsa a matsanancin damuwa ganin yatsan sa a kumbure gashi ya karce sosai,

Yaya meya same ka a kafa haka,?

Tuntube nayi kawai yace Mata Yana fita,,

fita yayi bakin titi Yana tare keke da hannunsa har Allah yasa wani ya tsaya,

Malam Ina zuwa?

…FMC yace Masa

Shiga muje, da lalube ya shiga keken suka wuce cikin kankanin lokaci suka Isa hospital ya sauke sa abakin get don in ba majinyaci bane a Keke ba’a Bari ta shiga asibitin, ya bawa Mai keken kudin sa naira 50,

Ya Kama hanya da lalube ya Isa cikin asibitin security n get yake tambaya don Allah wani shashine zaibi zuwa emergency don lokacin da suka zo da Ammar a motane bazai gane hanya ba gashi asibitin fadine dashi ga shashe daban daban,

Kabi nan ka Mike har emergency zai kaika

haka kuwa yayi har ya Isa emergency Yana shiga ya gane dakinda aka kwantar da ita

yazo shigane ya hadu da nurse in d’azon tana ganinsa ta rufe sa da masifa

Kai wani irin mutum ne zaka kawo Mara lfy kasa kafa ka fice ka barmu da ita, tun dazun nemanka ake likita nason ganinka,

Kiye hakuri gida naje na dauko Mata kayane

Me yasa she dayan bazai je ya dauka mata ba Kai ka zauna?,

Taimakona yayi Kuma ya tafi,
Jeka aje kayan kazo likita nason ganinka

Da toh ya amsa Mata da lalube ya Isa inda gadon ta yake har lokacin Bata farka ba,
Juyawa yayi ya fita a dakin sai da ya fita kafun, ya tuna baisan office in likitan bama tambayar wata nurse yayi da taimakon nurse innan ya gane office in doctor shiga yayi da sallama doctor ya amsa masa matashine kamarasa,

Kaine ka kawo Sumayya Abdulsalam shugaba?

Eh nine doctor ya basa amsa

..ok Sumayya na fama da apendes ya kunbura sosai don haka dole za’a Mata tiyata ga wannan sai kaje ka biya kudin,

Atake zufa ta fara karyo Masa Innalilahih wainnailaihir rajuun,likita kudin zai Kai nawa,yafada Yana tambayan sa?,

Bani bane Mai karban kudi in kaje wajen biya za’a fada maka……………..

 

🪀My WhatsApp number
08084453785

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya Ibrahim* 🍃

✨Tsokaci wannan shine novel na farko Koh da za’a ga mistake Koh typing error Amin afuwa 👌
Free book🤧

Back to top button