Author: Novels

  • Noor Al Hayat 60

    Noor Al Hayat 60

    Ranan lahadi da safe Khadijah ta raka Sudais Airport, har ranta ta dinga jin kewarsa bayan ya tafi duk jikinta yayi sanyi, tana tsaye inda xata hau cab a wajen airport din kamar ance ta kalli gefenta taga khaleel tsaye alamar fitowarsa kenan shi ma daga cikin airport, farar shadda ce jikinsa sai walkiya take, Khadijah ta dauke kai da sauri tun kan ya kallo inda take ta karasa gun cab da ta gani ta shiga ta fada ma driver din inda xata. Suna isa gida ta fito ta basa kudin sa sannan ta shiga ciki da sauri ta bude jakarta tana kokarin ciro makulli, dai dai nan khaleel ya shigo gidan, bata yarda ta juya ba ta bude kofarta ta shige. Daki ta wuce ta tattara reading materials dinta, ta dau kayanta kala biyu da nyt wear ta fito rike da jakarta, kulle apartment dinta tayi ta wuce kamar warce ake jira a waje tsabar haste din, tana fita ta samu Cab ta hau xuwa gidan Vanessa. Gaba daya ranan a gidan ta yini, sai dai she was just uncomfortable saboda mazan turawan dake xuwa suke fita gidan, gashi ba isasshen hankali gare su ba duk ta takura, ta so komawa gida da daddare amma saboda sanyi ta hakura ta kwana gidan, washegari daga gidan ta shirya xuwa sch tare da Vanessa bayan sun yi breakfast, suna gama lectures Vanessa ta sake jan Khadijah suka koma gidanta, tana xaune parlorn Vanessa bayan tayi magrib idonta a kan takardun hannunta ta jawo wayarta dake ring, number Aliyu ta gani sai a sannan ta tuna da yaronta ta yi picking kiran, daga daya bangaren yace “How are you Iman” tace “Fyn, how about my son” yace “Naga kin ma mance da shi gaba daya” ta hade rai tace “Taya xan mance shi?” Murmushi yayi yace “Toh gobe da safe xan kawo shi don ya samu yaje schl” tace “Kun dawo ne?” Yace “Yea daxu da yamma” shiru ta d’an yi kafin tace “Bring him in the afternoon” yace “Alryt then” daga haka ta katse wayar ta. Ranan talata bayan sun gana lectures misalin karfe biyu Khadijah ta koma gida, bude kofar apartment dinta tayi a hankali ta shiga sannan ta rufe, gyaran gidan ta shiga yi, bayan ta tsaftace ko ina, ta bude kofar kitchen xata xubda shara suka yi ido hudu da wata yarinya da ta xo xubda sharan ita ma, yarinyar ce ta fara cewa “Sannu” Khadijah tace “Ina yini?” Yarinyar tace ” Lafiya lau, jiya da muka xo mun duba baki nan ashe kin dawo” Khadijah ta d’an yi murmushi tace “Ehh yanxu na dawo” yarinyar tace “Ayya, to Sannu da xuwa” Khadijah tace “Idan na gama xan shigo yanxu” yarinyar tace “Toh sai kin shigo” daga haka Khadijah ta wuce ciki, Allah ma ya san ba don ranta ya so ta fada haka ba, kawai dai yarinyar ta mata kwarjini ne, and kuma sai taga kamar suna kama, toh ko dai ita ce warce su Deejah ke fadi? Tabe baki tayi ta wuce bedroom dinta, wanka tayi ta sauya kaya tayi sllhn azahar sannan ta linke Hijab dinta ta yafa mayafi ta fito, a hankali ta danna bell din apartment din khaleel, bayan wani lkci wata ta bude kofar, Khadijah tace “Ina yini” yarinyar dake ta kallonta ta bata hanya tace “Lafiya lau” shigowa parlorn Khadijah tayi gabanta na faduwa, few mutane ne parlorn kuma yawanci duk manya ne, ta durkusa jikin kujera a hankali tace “Ina yinin ku” amsa mata suka yi da fara’a, wata a cikinsu tace “Ikon Allah, ji mai kama da su Maimoon” Yarinyar da ta bude kofar tace “Wllh Anty na xata Safeenah ce ta da farko, haka na tsaya da mamaki Ina kallonta don nasan Safeenah na daki ai” Ita dai Khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Wata mata dake kusa da ita tace “Dama haka Allah ke ikon sa ai, tashi ki shiga ciki yan mata suna can gaba daya” warce ta bude mata kofar ne ta kai ta har dakin da jawahir da yan uwanta suke, Khadijah dai gabanta sai faduwa yake ta sunkuyar da kanta, da sallama ta shiga dakin bayan yarinyar ta bude mata kofa, suka hada ido da Jawahir dake xaune gefen gado tana danna wayarta, sosai tayi kyau sai wani glowing chocolate skin din ta yake, hannayenta sun sha lalle, kai kana ganinta ka ga amarya, Khadijah ta sunkuyar da kanta, Maryam ce ta fara mikewa ganinta tace “Lah Khadijah ashe kin dawo” Khadijah ta kirkiri murmushi tace “Ehh ban dade da dawowa ba” Maryam tace “Ayya, Sannu da dawowa, ga waje ki xauna” Bata kai ga xama ba Deejah ta fito daga bayi tana ganinta ta rungume ta da murna tace “Khadijah har na gaji da jiran ganin yaushe xa ki dawo, gashi babu mai number ki, Sannu da xuwa” Khadijah tace “Ayya ni ban san jiya xa ku taho ba ina gidan frnd dita ce” A hankali Khadijah ta xauna Deejah ta xauna kusa da ita tana kallonta da fara’a tace “Mun taho rakiyar amarya” Khadijah ta kalli jawahir a hankali tace “Sannu Amarya, Allah ya bada xaman lafiya” sai a sannan jawahir ta kara kallonta babu yabo babu fallasa tace “Ameen” Deejah sai kallon jawahir take alamar bata ji dadin yanda ta amsa mata ba, ita kanta Maryam dauke kanta kawai tayi, Safeenah ta shigo dakin tace “Lahh ashe har kin shigo” Khadijah tayi murmushi tace “Eh na shigo” ta karaso ta xauna ita ma tace “Su Anty Deejah na ta labarin ki a Nigeria sai gashi yau na gan ki, kin lura da kamar da muke yi kuwa?” Dariya ta ba Khadijah, Maryam da Deejah ma suka yi dariya ban da Jawahir da ta tsuke fuska, A hankali Khadijah tace “Ikon Allah kenan” Safeenah tace “Gaskiya ne, Ammin mu na gaishe ki” Khadijah tayi murmushi tace “Na amsa sosai” hira suka dinga yi dakin banda Khadijah da sai dai tayi murmushi idan sun kallota, duk a takure take ta kagu ta tashi ta wuce amma ta kasa tashi, agogo ta kalla ganin uku ya wuce tayi karfin halin mikewa tace “Xan dan shiga ciki ina aiki ne” Safeenah tace “Amma xa ki dawo ai?” Murmushi Khadijah tayi tace “Ehh xan dawo anjima” Rakota suka yi parlor, Khadijah tayi ma wa enda ke xaune parlor sallama ta bude kofa xata fita suka kusa cin karo da khaleel, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yanda ta daburce shi ma haka, yyi saurin bata hanya, ganin Deejah da Safeenah na bayanta tayi karfin halin ce masa “Ina yini” yace “Lafiya lau, ya gida” fita tayi daga parlorn bata ce komai ba ta bude apartment dinta ta shiga ta rufe, ganin la’asar yayi ta daura alwala a bayi tayi sallah sannan ta kwanta, bude data tayi da sauri tunawa da tayi daxu Barrister yace xai turo mata sako ta duba, ko ya bar Dubai din ma oho, ai ko tana budewa taga messages da ya turo mata da yawa, ta shiga tana kallon message din, kusan gaba daya hotuna ne, downloading din su ta fara yi, murmushi tayi ganin set na akwatuna ne yace ta xabi wanda take so, a hankali ta dinga scrolling tana duba boxes din, bbu na banxa gaba dayansu, murmushi tayi masa as reply, sannan ta tura masa message tace duk sun yi kyau sosai, daga haka ta kashe datan ta, bayan kusan minti goma sai ga kiransa, kuri ta kura ma wayar ido, can ta daga a hankali ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren yace “Amira” tace “Na’am good day” yace “Thanks, I saw ur reply, kuma ni ba tambayar ki nayi ko sun yi kyau ba” Yar dariya tayi tace “Barrister amma ai kai ma kasan sun yi kyau” yace “My question is wanne kika fi so” tayi murmushi tace “Uhm ni ban san wanne xan ce ba barrister” yace “Ask ur frnds then” tace “Toh xan tambaya” yace “Ina fa jiran ki kafin gobe, don goben xan bar Dubai” a hankali tace “Toh barrister” daga haka yayi mata sallama ya katse wayar ta koma ta kwanta a sanyaye, juye juye ta dinga yi tana kokarin bata ba damuwar dake neman dirar mata a xuciya space ba, can ta mike jin ta fara jin yunwa, kitchen ta tafi ta daura ruwan xafi don tafasa na shayi, kamar ance ta leka window taga khaleel xaune waje doing nothing, hada ido suka yi tayi saurin dauke kanta ta ci gaba da abinda take, tasowa yayi a hankali ya iso kusa da windown ya tsaya yana kallonta, trying her best not to look toward his direction tace “Wishing a happy married life, Allah bada xaman lafiya” kallonta kawai yake, can a hankali yace “Khadijah” kashe gas dinta tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta nufi kofar fita kitchen din ya bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar. Shayin da bata sha ba kenan tana ta xaune parlor wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin me kiranta tayi picking ta kai kunne tayi shiru, “Ki fito muna waje” abinda Aliyu yace mata kenan, ta mike a hankali ta tafi daki ta dauko hijab dinta ta sa ta fita, Tana isa kusa da motar ta bude ganin bashi da alamar fitowa ta fiddo Shureim tana kallonsa, xata wuce yace “Jira ki karbi sakon Mumy” Bata ce komai ba ta tsaya ya fito ya bude bayan mota ya ciro wani leda ya bata, amsa tayi tace “Mun gode Allah saka da alkhairi” Har ta juya xata tafi sai kuma ta tsaya tana kallonsa ta basa wayarta tace “Ka sa min number ta sai in kirata in mata godiya” karbar wayar yayi ya sa mata digit din Mumy ya mika mata, ta amsa tace “Thanks” yace “Don’t forget ki tambayeta jikin Anty Khadijah idan Kin kirata” tace “Har yanxu bata samu sauki ba?” Yace “She is still at the hospital” Shiru Khadijah tayi, lkci daya jikinta yayi sanyi, can tace “Toh Allah ya bata lafiya” Yace “Ameen” Cike da karfin hali tace “Ya jikin iklima fa?” Ya shafa kansa yace “Tana can family din babanta, ban samu xuwa dubata ba coz I spent only three days kuma throughout Zaria nake ta tafiya gun Anty Khadijah” Khadijah tace “Toh Allah ya sauwake, idan muka yi hutu soon xan je gida sae in je in duba Anty Khadijah da Umma” Yace “Alryt” shiru ta kara yi, sai kuma ta kallesa tace “Ina son tambayar ka pls” yana kallonta ya rungume hannunsa yace “Ina jin ki”

  • Noor Al Hayat 52

    Noor Al Hayat 52

    Aliyu ya lumshe ido ya bude a hankali yace “Toh kar ki masa butulci Iman, baki san xai baki shi ba ya baki, prayer is all what ur little boy wants from you, kiyi masa addu’a ba kuka ba Iman, if you continue like this what will be the fate of his twin, kin ga shi ma xai shiga damuwa sosai na rashin halve dinsa and this might affect him badly…. Or did you want anything bad to happen to him also, For his sake plss ki kwantar da hankalin ki so you won’t loose him too, am telling you damuwar da shi xai shiga sai ma ya fi naki” khadijah ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace “Na shiga uku don girman Allah kar ya bar ni shi ma” yace “Then ki kwantar da hankalin ki and accept this fate” hawaye na xuba idonta tace “Toh” yace “Promise me baxa ki sake kuka ba Iman” k’in cewa komai tayi, ya kira sunanta a hankali ta daga kai tana kallonsa, sosai gabanta ya fadi, ta kuma rushewa da kuka tace “Yanxu Sudais ya tafi ya bar ni…. Shi fa yace min in je in kira masa Shureim he wants to tell him he is sorry, dama mutuwa xai yi baya son ya mutu a kusa da ni” Ta hade kai da gwiwa tana kuka kamar ranta xai fita maganar Sudais na karshe na dawo mata “Anty ki ce Shureim ya xo, I want to tell him am sorry” kuka ta ke kamar ana dada tunxurata, Aliyu ya kasa ce mata komai duk jikinsa yyi sanyi, Ta rikosa tana girgixa kai cikin tashin hankali tace “Yanxu shkkn baxan sake ganin sa ba, me yasa ya tafi ya bar ni da Shureim” Aliyu ya kasa cewa komai wani mugun tausayinta na shigarsa, cikin sanyayyen muryarsa yace “Pls ki daina kukan nan Iman, da duk biyun Allah ya raba ki da ya xa ki yi kenan, you neva knew why he took him so soon, be a good Muslimat plss” shiru khadijah tayi jin yace Dukka biyun, ta goge idonta gabanta na mugun faduwa cos she can’t just imagine that, Murya can kasa yace “You make the promise now, that baxa ki sake masa kuka ba sai dai addu’a….” Ta gyada kai da kyar trying not to cry tace “I promise” yace “Add in sha Allah to the promise” a hankali tace “In sha Allah” Ya d’an yi murmushi yace “Good” mikewa yyi ya dago ta ta mike ita ma tana goge idonta yace “Ki wuce ciki and remember the promise you make” tace “Toh” daga haka ta fara tafiya ya bi ta da kallo, da sauri ta juyo sai kuma ta dawo tace “Ina shureim plss” da kamar baxai ce komai ba, sai kuma a hankali yace “Yana nan tare da mu” ta hadiye abu da kyar tace “Ka dauko min shi plss” yace “They are people everywhere, later xa a kai maki shi” shiru tayi sai kuma ta juya a sanyaye ta fara tafiya, Juyowa tayi ta kara dawowa idonta har ya fara kawo kwalla tace “Toh me yake yi?” Yace “Kukan xa ki fara kuma” da sauri ta girgixa kai tana goge idonta, yace “He is just sitting down” bata ce komai ba ta fara tafiya kamar iska xai kadeta ta fadi har ta bar wajen, Aliyu ya koma a sanyaye ya xauna ya jinginar da kansa jikin bango yana jin mutuwar yaron har cikin ransa, Tun da khadijah ta dawo compound din khaleel ke bin ta da kallo har ta shiga parlor, sai a sannan barrister Sudais ma ya dauke idanuwansa daga kallonta, Bedroom ta wuce duk mutanen parlon suka bi ta da kallo cike da tausayinta, Umma na xaune har lkcn duk jikinta yyi la”asar, da ido ta bi khadijah har ta dauko Hijab dinta ta sa ta xauna kan darduman dake shimfide ta jingina da bango, hawaye ya cika Idon Umma don bata yi xaton hakan ba, tashin hankalinta ta Inda xata fara lallashin Khadijah sai ga shi taga ta ma daina kukan, Wata frnd din umma ta dawo kusa da ita a sanyaye tace “Kiyi hakuri kinji Khadijah, Allah yayi masa rahama…” A hankali khadijah tace “Ameen” Umma taji hankalinta ya kwanta sosai, tashi tayi ta fita da kanta taje kitchen ta hado mata shayi ta dawo, kasa sha Khadijah tayi har lkcn ta kasa yarda Her lovely Sudais is gone forever, tana son kuka amma sai ta tuna promise din da tayi, hakan yasa xuciyarta ya dinga mata xafi sosai, kowa ya ganta sai yaji tausayinta, Umma har lkcn mamakin karfin halin nata ta dinga yi, a haka har aka yi la’asar, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sllh umma ta xubo mata abinci ta xauna kusa da ita cike da lallami tace “Don Allah ko kadan ne ki ci Khadijah, tun jiya fa baki ci komai ba” Khadijah tayi shiru bata ce komai ba, can ta dago da kyar tana kallon Umma tace “Umma yanxu shikenan Sudais ya tafi” Rungume ta umma tayi tana kokarin ganin bata xubda hawayen dake baraxanar xubo mata ba, cikin sanyin murya tace “Pray for him daughter, Allah yasa can ya fi masa nan, Allah ya sa mai ceton mu ne” cikin rawar murya Khadijah tace “Ameen” umma tace “Toh ki ci abincin kadan don Allah” ta girgixa kai tace “Umma baxan iya ci ba” Umma tace “Ko cokali biyu ne ki yi” Nanny ce ta shigo dakin da kumburarrun idonta ta duka kusa da su tace “Umma akwai baki parlor sun xo mata gaisuwa ta daure ta fito” Umma tace “Kice su shigo nan” mikewa Nanny tayi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tare da su Mumy, Baby da su seeyama da wata daban, Mikewa Umma ta yi ganin su ta shimfida masu babban darduma tana masu sannu da xuwa, Khadijah ta dinga kallon Mumy har ta xauna, A hankali tace “Sannu da xuwa Mumy” mumy da kana ganin idanuwanta kasan ta yi kuka sosai tace “Sannu Khadijah, ya hakuri” Khadijah ta kasa amsawa ta dakar da kanta, Su siyama ma suka mata gaisuwar a sanyaye, sai a sannan khadijah ta kara dago kanta tana kokarin ganin bata bar hawayen idonta suka xubo ba, Kallon warce ke xaune kusa da baby ta dinga yi, ita ma yarinyar kallonta take da mamaki, Khadijah tayi karfin halin cewa “Maryam sannu da xuwa” Maryam tace “Ashe yaron ki ne ya rasu Khadijah, Allah ya ji kansa” Khadijah tayi karfin halin cewa “Ameen” sai dai xuciyarta cike yake da mamaki, Maryam dama yar uwar su Aliyu ce kenan, makarantar su daya a UK amma Hi kadai ne mutuncin da ke tsakaninsu kawai ta rasa me yasa bata son yarinyar, kawarsu Vanessa ce dai. Mumy sun kusa minti sha biyar a dakin, duk tausayin khadijah ya cika don tasan rashin yaro da ciwo sosai ga uwarsa barin yaro mai shiga rai irin sudais, bata ma samu courage din tambayar ina Shureim ba, Karfe biyar da yan mintuna tace ma umma xa su tafi, Umma tace “Toh mun gode kwarai Hajiya, Allah ya bar xumunci” Mumy tace “Ameen, kuyi hakuri bamu xo tun safe ba kanwata ce ba lafiya tana asibiti sun yi hatsari tun shekaranjiya” Umma tace “Subhanallah, toh Allah ya bata lafiya, ya yaye mata” Mumy tace “Ameen mun gode” hakuri ta kara ba khadijah Umma ta rakasu suka fita parlor, Sai a sannan Mumy tace “Kanin Aliyun yana waje ya xo mata gaisuwa amma ko xuwa anjima sai ya dawo” Umma tace “A’a bari ta fito” mumy tayi convincing dinta kan ta bari sai anjima ya dawo daga haka suka wuce Umma ta koma ciki. A hankali khadijah ta tako har cikin parlor tana sanye da Hijab dinta har kasa ta xauna kujera a sanyaye tana kallonsa, rasa abinda xai ce mata yyi, ta sunkuyar da kai a raunane tunawa da lkcn da suka dinga dragging sunan da ta xabar ma sudais dinta da shi, A hankali yace “Amira…” Ta daga kai tana kallonsa lkci daya idanuwanta suka kada, cikin sanyi yace “Keep on praying for him, Allah ya sa mai ceton mu ne, life moves on plss, ai da baki san Allah xai baki shi ba, so kiyi hakuri ki cire sa ranki, tsakanin ki da shi yanxu addu’a, baxai ji dadi kiyi ta masa kuka ba” Tana gyada masa kai da kyar tace “Ai na daina, Allah ya ji kansa, ya hada ni da shi a aljanna” Barrister sudais yace “Ameen, Allah ya kara maki hakuri” Murya can kasa tace “Ameen” yace “Toh yi ma Umma magana xan mata gaisuwa” Ta mike tace “Toh” daga haka ta wuce ciki, ba a dau lkci ba Umma ta fito, da ta amshi gaisuwar sudais tana sa masa albarka, Bai dade parlorn ba yace mata xai koma gida, tayi masa Allah ya kiyaye hanya ya fita parlorn, ita dai har ranta taji Sudais ya kwanta mata, ta kuma san har abada baxa ta mance hallacin da yayi mata ba, don ko ita yayi ma, bata kuma san da me xata saka masa ba. Karfe tara da yan mintuna, Aliyu ya shigo parlorn, har sannan Umma na ciki bayan ta sallami wasu bakin, suka gaisa ya kara mata gaisuwa tace “Allah ya ba mu hakuri gaba daya, daxu su hajiya ma suka xo, mun gode kwarai” shi dai bai ce komai ba, Umma sai ta ga kamar sudais ne xaune gabanta ya girma, hakan yasa duk jikinta ya kara sanyi, Aliyu da ya rasa abinda xai ce yyi karfin hali daga karshe yace “Mama tana Ciki ne?” Umma tace “Ehh tana ciki bari in mata magana” Daga haka ta mike ta wuce ciki, bayan wani lkci ta dawo tana kallonsa tace “Aliyu tayi bacci kuwa” yace “Toh shkkn Mama, sai na dawo gobe Allah kara hakuri” tace “Ameen, Allah bada lada” tana son tambayarsa Shureim amma bata san ta ya ba, ta kasa daurewa daga karshe kafin ya fita tace “Aliyu ina shureim din fa?” Juyowa yyi yace “An tafi da shi mama” tace “Can gidan ku?” Ya girgixa mata kai, Umma tace “Toh shikenan Allah ya kiyaye hanya” daga haka ya fita, umma ta san khaleel ne ya tafi da shi can gidan nasu. Ta koma cikin dakin Khadijah ta rufa mata bargo, Nanny dake dakin tace “Umma da ki kwana nan, tunda akwai baki dakin ki” Umma tace “A’a ke ki tsaya tare da ita babu komai duk daya ne” daga haka ta fita dakin.

    Karfe goma na safiyar washegari Khadijah na kwance daki ta rufe ido kamar mai bacci don gaisuwar da ake mata na shureim na kara daga mata hankali, hakan yasa duk wanda ma ya xo umma da Nanny yake ma gaisuwar, Umma ce ta shigo dakin ta taba ta duk da tasan ba bacci take ba, Khadijah ta bude idanuwanta da suka mata nauyi tana kallon umman nata, cikin kwantar da murya umma tace “Taso mu je an xo maki gaisuwa” ta d’an hade rai tace “Umma ba ga ku ba bacci fa nake” Umma tace “Mahaifiyar khaleel ce shi yasa ma na tashe ki” shiru khadijah tayi tana kallon umma, can Khadijah ta mike xaune a hankali, umma ta kama hannunta ta tashi daga kan gadon, hijab ne har kasa jikinta, hakan yasa ta bi bayan umma dake rike da hannunta suka fita parlor, balarabiyar matar na xaune parlor da jikokinta su uku sai shureim dake jikinta shi ma, Suna hada ido Khadijah ta sauke kanta a sanyaye ta karasa cikin parlorn ta xauna, da gudu shureim ya taho ya rungume ta yana kallonta yace “Anty are you sick?” Kallonsa Kawai khadijah take taji kamar ta fashe da kuka, Ummu dake ta kallonta da tausayi tace “Sannu Khadijah, ya karin hakuri?” kasa cewa komai tayi da farko, can dai tayi karfin halin bude baki da kyar tace “Alhmdlh Mumy, nagode” Ummu tace “Allah yayi masa rahama, ke kuma Allah baki dangana, ya sa mai ceto ne” Umma tace “Ameen thumma Ameen” don khadijah kasa amsawa tayi, Shureim na kallonta da damuwa yace “Anty uncle yace min sudais travelled, why will he travel alone, why didn’t we go together plss, and now I am missing him, plss I want to go to him, I promise I will never fight him again….” umma ta jawosa jikinta tana kokarin boye hawayen idonta tace “He will be back soon sweetheart, and I am sure he is missing you too” Shureim yace “Toh Umma I want to talk to him on phone, am missing him” Ummu dake ta kallon shureim tace “Shureim har ka gaji da wasa dasu fadeel, ain’t they ur frnds anymore” ya juya ya kalleta yace “Noo Ummu I like them, but sudais is my brother, they will like him also” Ummu tace “Toh taho mu wuce tunda ka gaida Anty” kallon khadijah da kanta ke kasa shureim yyi ya dawo kusa da ita a hankali yace “Anty, is sudais coming back soon? I want the both of us to be frnds with fadeel and Adeel” Ummu ta mike tace “Toh xo mu wuce Shureim, idan ya dawo xa a kawo sa wajen ka” da haka suka fita parlorn bayan shureim ya daga ma khadijah hannu, Umma ta rakasu har bakin mota, sai a sannan taga tare suke da Khaleel dake xaune motar, ganin umma ya sakko ya gaisheta da ladabi sannan ya mata gaisuwa ta amsa tana murmushi tace “Allah ya saka da alkhairi, ya bar xumunci” yace “Ameen” sai da suka shiga motar gaba daya sannan Umma ta koma cikin gida, bata tadda Khadijah a parlor ba hakan yasa ta wuce daki ta ganta kwance, mamaki ya cika umma ta xauna kusa da ita da damuwa, yanxu kuma rashin kukan nata ya fara damunta don wani lkcn gwara mutum yyi kukan da kukan xuci, Umma ta yi shiru na d’an lokaci kafin a hankali tace “Look daughter, cry… even if it’s a little so you will feel relieve, kiyi kuka don Allah bana son wannan rashin kukan naki kuma, kin dai san matsalar ki, kar kije ki tada ciwon ki, it will be worst gaskiya idan haka ya faru” Jin bata ce komai ba umma ta mike a sanyaye ta fita, ba a jima da tafiyar mahaifiyar khaleel ba su mumy suka xo gidan, yau kam sun d’an dade kafin su wuce kuma khadijah ta fito ta amshi gaisuwar saleem, da yamma shaheedah ta xo gidan da sadeeq, shaheedah tayi kuka don bata ba sudais mutuwa so early ba, duk taji tausayin khadijah sosai, su Vanessa duk suka kira khadijah yi mata gaisuwar sudais da har lkcn a xaton su kanninta ne yan biyun. Da daddare ta fito wanka Shaheedah ta mika mata wayarta da yake vibrate, karba tayi ganin Khaleel ne ta daga ta kai kunne, cikin sanyin murya yace “Khadijah…” A hankali tace “Na’am” yace “Xa ki iya fitowa yanxu?” Shiru ta d’an yi kafin tace “Toh gani nan xuwa” shiryawa tayi ta sa hijab ta fita xuwa dakin umma, ta durkusa kusa da ita tana kallonta tace “Umma ina xuwa khaleel na kirana” Umma tace “Toh sai kin dawo” daga haka ta mike ta fita, cikin sanyi take tafiyar kamar mai tausayin kasa har ta isa waje, yana tsaye ya jingina jikin motarsa, kanta a kasa ta isa gefensa ta tsaya, murya can kasa tace “Ina yini?” Kallonta kawai yake bai ce komai ba har ta dago a hankali, sai a sannan ya sauke idonsa kasa daga kallonta da yake yi, cikin sanyayyan muryarsa yace “Ya hakuri khadijah” ta hadiye abu da kyar tace “Alhmdllh” yace “Ban san me xan ce maki ba shi yasa ban kira ki ba khadijah, I know it’s very sad, it’s a great lost, but don’t forget ba wayon ki yasa Allah ya baki shi ba, and there is always a reason for everything, and you knw God plans best, don haka ki sa ma xuciyar ki dangana, you have ur handsome shureim, he will act as both him and his twin to you, this is part of ur fate, and it’s already written, plss kin san condition din ki Khadijah kar ki kara sa mutuwar sudais a ran ki I know its very painful, but idan wani abu ya same ki i will be very sad, come to think of ur only son, for my sake and his don Allah kiyi hakuri, forget about Sudais, but don’t forget to pray for him always, Allah ya hada mu gaba daya a aljanna” cike da damuwa ya kare, Khadijah tayi murmushin karfin hali tana share hawayen da ya taru idonta, tun ranan da Aliyu yace kar ta sake kuka bata kara ba sai yanxu da take gaban khaleel, a hankali tace “In sha Allah Dr, baxan sa damuwa a raina ba, ae ban ma san Allah xai bani shi ba, so baxan butulce masa ba, na hakura Allah ya haskaka kabarinsa ya sa can ya fi masa nan, kuma ya raya min d’an uwan sa” cikin rawar murya ta kare maganar, khaleel ya lumshe ido yace “Ameen Khadijah, am happy with ur words” Bata ce komai ba ta dinga kallon motar da yayi parking bayan na Khaleel, Aliyu ne ya fito cikin motar, kallo daya khaleel yayi masa ya dauke kansa, Aliyu ya iso inda suke yana kallon khaleel ya basa hannu khaleel ya amsa amma fa da kyar, Aliyu na kallon cikin idanuwansa yace “Ya hakurin mu?” Khaleel yace “Mun gode Allah” Aliyu ya kalli khadijah suka hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, cikin gidan Aliyu ya shiga, khaleel na juya wristwatch din hannunsa yace “Wajen ki ya xo?” Ta girgixa kai tace “A’a” Khaleel bai sake cewa komai ba bayan wani lkci yace “Alryt then, xan koma Khadijah, Allah ba mu hakuri gaba daya, sleep without worries plss” ta gyada masa kai tana kallonsa, yana daga kai suka hada ido tayi saurin dauke kanta, yyi murmushin sa mai kyau yace “Amma kin ci abinci kuwa? Tell me the truth plss” ta girgixa masa kai a sanyaye tace “I don’t have appetite” yace “Toh idan na siyo maki abu yanxu make me the promise xa ki daure ki ci” tace “Akwai abinci fa a gida” yace “Ai na sanin, just promise me xa ki ci plsss” murmushi tayi tana fidgeting fingers dinta a hankali tace “Toh nagode” yace “Yauwa, I will be back soon” tace “Toh Allah ya kiyaye” daga haka ya xata xai shiga motarsa ita kuma ta shiga cikin gidan, xaune ta tadda Aliyu kan farar kujera a wajen compound din, kallo daya tayi masa ta dauke kai xata wuce ciki, taji a hankali yace “Iman” kasa ci gaba da tafiya tayi, maganganunsa na jiya da safe na mata yawo a kai, can ta juyo ta kallesa ta gan sa tsaye, yace “Plss just few minutes” tana ta tsayuwa idonta a kan yatsunta har ya iso gabanta yace “Few minutes pls” Ta dake da kyar tace “Toh” juyawa yayi ya nufi gun kujerun ta bi bayansa, ya xauna kan kujerar ta xauna ita ma. Kallonta kawai yake ta ki kallon sa ta hade rai, murya can kasa ta ji ya fara cewa “Iman ba dan ni ba don Allah ina son ki mance abinda ya faru tsakaninmu six years back…..” Da sauri ta dakatar da shi tace “Toh ni nace maka ban mance bane?” Ya girgixa kai a hankali yace “I mean ki yafe min ki cire a ranki da gangan na maki hakan wllh ba da gangan bane, it’s a set up, though ba lallai ki yarda da hakan ba, amma don Allah kiyi hakuri mu dinga xumunci” Ji tayi kamar ta fashe da kuka don ya fama mata ciwon da ya ki healing har yanxu a xuciyarta, A sanyaye yace “Kin ji Iman, ki raga min ko albarkacin daya yaron da ya rage a tsakaninmu even if I didn’t deserve it” Khadijah ta kasa cewa komai, Bayan wani lkci ta daga kai a hankali tana kallonsa ta ga kallonta yake, da sauri ta sauke idonta tace “Ni fa na mance, ya kuma wuce a gu na” yace “Toh nagode sosai, amma xaki bani yaron?” Da sauri ta daga kai tana kallonsa, cikin rawar murya tace “I can’t give you my son, kayi hakuri…” Yana gyada kai a hankali yace “No offense, amma xa ki bari ai mu dinga xumunci da shi, I mean in dinga xuwa ina ganinsa, once in a while kuma xa ki bari ya xo gun mumy koh” shiru tayi ta kasa cewa komai, murya can kasa yace “Kin yi shiru” a xuciyarta tace “Nasan maganin ka” a fili kuma tace “Toh” Wani murmushi yayi yace “Toh nagode sosai, Allah ya raya sa” tace “Ameen” kamar ance ta juya taga khaleel ya shigo gidan rike da leda, mikewa tayi da sauri ya karaso har gabanta yana kallonta ya mika mata ledan, ta d’an risina ta karba a hankali tace “Nagode” ya d’an yi murmushi yace “No thanks” daga haka ya juya ya nufi gate, Aliyu ya bi sa da kallo ko kiftawa babu, khadijah tace “Xan wuce ciki sai da safe” mikewa yayi yace “Toh ina yake, I mean the boy? Though ban san sunan sa ba” da kamar khadijah baxata ce komai ba sai kuma murya can kasa tace “Sunansa Muhammad, ana kiransa Shureim, sunan late half dinsa Aliyu ana kiransa Sudais” kallonta yake ko kiftawa babu, ta gyara tsayuwarta tana masa wani kallo tace “Barrister Aliyu… Sunan sa ya ci” daga haka ta juya ta fara tafiya fuskarta daure, murmushi Aliyu yyi ya bi ta da kallo, can yace “Ohk, wait Iman, nagane barrister Aliyu ne ba ni Aliyun ba” tsayawa tayi amma bata juyo ba, ya karasa inda take yace “Toh yana ina yanxu, I haven’t seen him since yesterday” tace “Yana gidansu Dr khaleel” shiru yyi bai ce komai ba, can a hankali yace “Ohk good nyt” daga haka ta juya ta wuce ciki ta rufe kofa. Washegari aka yi sadakan ukun sudais, tun da sassafe Mumy ta taho da su Siyama da frnds dinta biyu, sadakar wainan shinkafa da Kayan flour ta kawo gidan, Ummun khaleel ma ta xo da jikokinta tare da shureim wajajen karfe tara, ita ma wainar ta kawo sai lafiyayyen rice and stew da ta kawo ma khadijah da soyayyen kaji a warmer daban, Karfe sha daya Barrister sudais ya bar gidan kasancewar yana da wani case, ya tura ma khadijah text cewa xai dawo da yamma, karfe sha biyu ummun khaleel ta koma gida tare da su Shureim da yanxu ya saba da yaran sisters din khaleel amma har Ummu ta gaji da amsa tambayar da yake mata na cewa yaushe sudais xai dawo, shi dai a kai sa wajensa, tausayi yaron yake bata don tsakaninsa da Allah yake son ganin dan uwan nasa, a ko da yaushe dai ce masa take soon xai dawo, sai kusan azahar Mumy suka bar gidan, Khadijah ta raka su har gate tayi mata godiya a sanyaye, Mumy ta sa mata albarka sannan suka wuce da yaran nata, kafin dare frnds din Umma suka fara watsewa gidan, Shaheedah ma suka koma Abuja tare da Sadeeq, gidan ya rage daga Khadijah, sai Nanny da Umma da Wata aminiyarta. Bayan magrib khadijah bna xaune kan darduma tana azkar kira ya shigo wayarta, a hankali ta daga ta kai kunne ganin barrister sudais ne, yace “Amira xa ki iya fitowa yanxu plss, am outside” tace “Toh” daga haka ta mike ta fita, sai da ta fara gaya ma Umma sannan ta tafi kofar gida, fitowa yayi daga mota ganinta, yana rike da 3 years old daughter dinsa, Khadijah ta wara ido tana kallon kyakkyawar yarinyar ta xaga inda yake ta karbeta tace “Waow ya sunanta?” Sudais ya jingina da motar yace “Ur namesake, ita ma Amira ake kiranta, na kawo ta ne ta gaida Antyn ta” Khadijah tayi murmushi a sanyaye tuno kiran ta da mahaifiyar yarinyar tayi mata ranan da sudais xai rasu, tana taba dogon gashin yarinyar tace “Naji dadi sosai” Yace “Sure?” Ta kallesa da sauri tace “Eh mana, ko xaka bar min ita” yar dariya yayi yace “In dai kika shigo gidan ubanta ai taki ce ita” Wani murmushin Khadijah tayi bata dai ce komai ba, yana kallonta a hankali yace “Baxa ki shigo ba kenan, xaro ido tayi tace ” Ka ji na fada haka?” Yace “Uhmn dont forget who is standing before you” ta dauke kai tana ci gaba da murmushi tace “A barrister” ya shafa kansa yana kallonta a hankali yace “Toh ya k’arin hakurin mu dear?” Tace “Mun gode Allah” yace “Har yanxu shureim din bai dawo gida ba?” Ta gyada masa kai tace “Bai dawo ba” yace “Ohk, ya su umma?” Tace “Suna ciki” kamar warce ta tuna da sauri tace “Sorry na bar ka tsaye mu shiga ciki” yayi murmushi yace “Aa bari in yi ta tsayuwa ta” ta turo baki tace “Allah na manta ne kayi hakuri, mu shiga ciki” daga haka ta nufi gate rike da Little Amira, ya bi ta da ido kafin ya bi bayanta, kan fararen kujerun dake compound din Sudais ya xauna duk yanda tayi da shi ya shiga ya gaida umma ya ki yarda wai sai gobe, tace “Toh bari in kai mata Little Amira ta gani” yace “Toh sai ki bar ta a can ki dawo ke kadai kar in yi rashin kunya gaban daughter na” dariya kawai khadijah tayi ta tafi tare da Amira dake ta waigo Abbanta ya daga mata hannu yana murmushi. umma ta xaunar da ita kan kafarta tace “Maa sha Allah, daughter na mai kyau da ita, Allah ya albarkace ki” khadijah tace “Naga kamar bata magana” Umma tace “A’a don dai bata san mu bane amma wannan ai ta isa tayi magana” fridge khadijah ta nufa ta bude ta dau ruwa da lemo ta daura kan tray ta sa glass cup sannan tace “Umma ina xuwa” Umma tace “Toh sai kin dawo” Har khadijah ta iso gun sudais idonsa na kanta, ta ajiye karamin tray din hannunta ta bude drink din ta xuba masa sai dai bata masa ba tace “Ya aiki?” Ya langwabar da kai yace “Ba dadi, Amira har yanxu you didn’t answer my questions…” Ya lumshe ido ya bude yace “Ohk let me leave it this way, you don’t want to answer my question” shiru khadijah tayi tana kallonsa, a hankali yace “A lot of things happened after I left you and the boys Amira, na koma damaturu gidanmu tare da Mamina amma gaba daya na rasa kwanciyar hankali, i was always sad then, thinking about you and the twins, hankalin Mami ya tashi a lkcn ta dinga cewa kilan asiri kika min ko kuma aljana ce ke, gashi nan abun na affecting dina, nan tasa aka tayi min rokan Allah, gradually dai na fara kokarin ganin na mance ku, na cire ku a rai na dinga harkokin gabana… saboda ku ko da ina da aiki a Abuja to baxan je ba, gaba daya na daina xuwa Abuja, daga Lagos, kano sai Kaduna and other States nake xuwa amma banda abj, dama ni din ba wai ina da time na yan mata bane, jiddah dai ce ita ma a Holland muka hadu lkcn ina karatu ita kuma tana tare da yayarta dake kasar tare da mijin ta, I never knew ma ashe Mami ta san mum dinta sun yi makaranta daya though it’s not as if they are frnds, to dai a haka na fara neman jiddah har aka sa aurenmu ana saura few months bikin mu na hadu da ke ranan na fito daga gida, Amira saboda ke nasa aka daga bikin nan har na kusan watanni shiddah, a kwana a tashi kuma na kara neman a daga cos kin kusa haihuwa lkcn, let me make things brief, at the end fasa auren nayi gaba daya, suka maido min da lefen da na kai all because of you, and happily then Abbana supported me, but bayan rabuwar ki sai gashi na koma mata cos I don’t have any option again, at first kamar baxata yarda ba daga karshe dai a cikin wata daya aka daura mana aure, 2 years da aurenmu da jiddah Allah yayi ma Mamina rasuwa bayan tayi fama da kidney problem, though before then duk na mata bayanin yanda aka yi na hadu dake, ban boye mata komai ba, kuma hankalinta ya tashi a lkcn but kawai sai ta maki fatan Allah ya hada ki da dangin mahaifiyar ki, daga nan kuma bata ce min komai ba, and gaskiya a lkcn kusan na ma cire ku a rai na daina damuwa cox I knw surely Allah na tare da ku, amma kullum sai na maku addu’a every blessed day, ba tonan asiri ba Amira ni ba wani jin dadin aure nake da jiddah ba, fitinar ta yayi yawa she is always pestering my life, ko kadan bana son hayaniya yana daga min hankali, bani da rest of mind idan ina gidana, ko irin weekend din nan ma ni na gwammace in tafi office in yi kallo, Amira I need a woman that i will find peace in, I need a better life partner, ina raga ma jiddah ne kawai saboda yarinyar nan dake tsakaninmu, and divorce is totally out if it baya cikin tsarin rayuwata, I need you plss Amira” Khadijah taji kanta ya mata nauyi sosai ta rasa abinda xata ce masa, bata san lkcn da hawaye ya dinga sakko mata ba tana kallonsa, deep down her kuma ta rasa me yasa khaleel ya fado mata.

    Shiru Umma tayi tana kallon khadijah, a hankali tace “Ko saboda me?” Khadijah ta langwabar da kai cikin sanyi tace “Umma I will be lonely all alone, I want him to be by my side” Umma tace “Life with him there won’t be esay Khadijah, karatun ki na bukatar natsuwa sosai kin sani, shureim will ba a distraction, baxai yiwu ba Khadijah” da damuwa Khadijah tace “Umma ai shi ma makarantar fa xai dinga xuwa, plss ummata” Umma tayi shiru alamar bata san me xata ce ba kuma, can tana ci gaba da linke kayan da take tace “Rabani da shi dai kike son yi koh?” Murmushi Khadijah tayi kunya ya kamata tace “A’a wllh ummata” Umma tace “Gaskiya ne mana, ke gashi baki kusa da ni, grandson din ma kina son daukesa” Khadijah ta xaro ido, da damuwa tace “Allah sarki Ummata ba haka bane ba fa” Murmushi Umma tayi tace “Toh shkkn tunda kina son tafiya da shi sai ku je, Allah ya tsare” Sosai Khadijah taji dadi, Umma ta xauna gefen gadon tace “Yanxu ya xa mu yi da maganar sudais Khadijah, kin ga samu na yayi ya min magana….” khadijah tace “Umma ya san xan koma makaranta ai, daxu ma mun yi magana da ya xo, kuma kinga 100k da ya bani ai saboda xan tafi makaranta ne” Umma tace “Toh ai ban ce bai sani ba, kin san dai dole sai an je katsina koh?” Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, bata son jin sunan garin ita kam, Umma ta mike ta ci gaba da abinda take tace “Shi kuma Aliyu ai ya kamata ki sanar masa xa ki tafi da Shureim din koh, ko kuma kije ma da yaron yayi sallama da mahaifiyar Aliyun” Khadijah dai bata ce komai ba idonta a kan wayarta. Can gidansu Khaleel kuwa Ummu ta sa driver yyi ma Shureim siyayya da taji tare xa su tafi UK da uwar sa, Khaleel dake xaune bedroom dinta yana duba kayan yace “Sun gode Ummu” Ummu tace “Khaleel ina son mu yi magana fa da kai, gashi gobe da sassafe xa ku wuce” ya maida hankalinsa gaba daya kanta kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace “Ina ji Ummu” sure ya san kwanan xancen amma yayi pretending bai sani ba, Ummu ta kwantar da murya tana kallonsa tace “Abuu kasan fa saura wata daya kachal bikin ku da jawahir kuma naji ko magana baka yi” Khaleel ya shafa kansa yace “Ina sane Ummu” tace “Toh Alhmdllh tun da kana sane, amma ba wani shiri da xa ku yi ne?” Shiru yyi bai ce komai ba, can ya dago ya kalleta yace “Ummu tun da ba laifi bane ina son hada su da mahaifiyar yaron nan na aura….ina da interest a kanta” Ummu ta dinga masa wani kallo tace “Kana da hankali ma kuwa khaleel???” hade rai yayi, kan kace me ya juya xuwa Arabiya… toh nan fa ake yin ta, don Mai typing dai ba jin yaren take ba ina laifin ma yayi turanci, tun tana d’an tsintar daddaya har ya kai ya kawo ta ajiye takardar da Biro kawai ta dafe kai, ganin khaleel fa sai xuba larabci yake a fusace ga ummu sai kallonsa take ta kasa cewa komai mai typing tasan abun babba ne, ba fans ba, har ita tana son jin abinda khaleel ke cewa don haka ta juya da sauri don nemo kanwarta Ilham ta mata translating, can ita ma ta sameta xaune tana halinta wato nukurci, ashe dai ba xancen translating din larabci, rai ba dadi mai typing ta kwashi legs ta koma, nan ta ga har khaleel ya gama jawabinsa yana danna waya amma fuska a murtuke, Ummu ta d’an yi murmushi a hankali tace “Ni na isa khaleel? What am saying in here is that, ina laifin bayan anyi bikin naku da Jawahir sai ka auri Khadijahr babu mai hanaka yin hakan ae, hakan ma xai fi” Washegari Khadijah ta gama hada few abubuwan da xata bukata domin komawa UK, umma kuma ta hada ma Shureim nasa kayan cike da jin kewan yaron gashi khaleel ya rabasu da shi tun rasuwar sudais, karfe takwas saura khaleel ya taho gidan tare da shureim, Khadijah tana bedroom ta gama daukar masa kadan daga takalmansa, ganin na sudais a gun yasa lkci daya mood dinta ya canxa ta koma ta xauna a sanyaye, tun bayan rasuwarsa dama Umma ta bada komai nasa a gidan saboda Khadijah xata fi samun nutsuwa, takalman ma mancewa tayi bata bayar ba, Nanny ce ta shigo dakin tace “Khadijah jiran ki fa suke” a sanyaye Khadijah ta mike ta fito rike da takalman Shureim, driver ne daga gidansu Khaleel xai kai su airport din, Shureim dake jikin Umma ya sakko da sauri ya rungume Khadijah yace “I missed you Anty” ta shafa kansa tace “I missed you same” Umma tace “Toh kuyi maxa yana jiran ku a mota” Khadijah tace “Yanxu Shureim din ya shigo?” Umma tace “Yanxu ya shigo” Khadijah ta karasa gun umma ta rungume ta tace “Ummata sai mun dawo” Umma tayi kokarin ganin bata fara hawaye ba a hankali tace “Toh Allah maku albarka daughter, Allah ya tsare min ku, sannan ki kula da kanki plss” murya can kasa Khadijah tace “Nagode Umma” Nanny na rike da shureim cike da kewarsa xata rakasu bakin motar, Khadijah na isa bakin kofa ta juyo a hankali tana kallon Umma tace “Toh Umma ba a kai sa yayi ma Mumy sallamar ba kuma, I mean shureim” Umma tace “Lah kin ga ni har na manta, to ki yi ma Khaleel din magana sai ku fara biyawa can a gurguje ki kai sa kafin ku wuce airport” Khadijah ta gyada mata kai ta fita parlorn, Shureim ne ya bude back seat Khadijah ta dinga kallon khaleel dake xaune sanye da glasses a idonsa yana operating wayarsa, Shureim ya shiga motar sannan ta shiga tana daga ma Nanny hannu, gaishe da Nanny khaleel yayi ta amsa da fara’a ta masu Allah ya kiyaye hanya sannan ta juya ta koma ciki. Sai da suka dau hanya sannan khadijah ta kalli khaleel a hankali tace “Good morning” yace “Morning how was ur nyt?” Ta sauke idonta tace “Alhmdlh” Wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne, sai bayan da ya gama wayar Khadijah tace “Umma tace plss kafin mu tafi in kai shureim wajen mum din Aliyu su yi sallama, idan suka yi waya tana yawan tambayar ta shi….” Khaleel yace “Ohk then” daga haka ya fadi ma driver anguwar da xai fara kai su, tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso gidansu Aliyu, Bayan drivern yayi parking a inda Khaleel ya nuna masa, khaleel ya juya yana kallonta yace “Ku shiga toh” tace “Kai baxa ka shiga ba” da sauri yace “A’a, am waiting for you two a nan” a hankali khadijah tace “Ohk,” daga haka ta bude motar ta sauka tana kallon Shureim tace “Come down” daga mata hannu yyi yace “Anty ki dauke ni” ta hade rai tace “Sakko my friend” khaleel yace “Ki daukesa mana ko baxa ki iya bane?” murmushi kawai tayi ta dauki yaron nata ta shiga cikin gidansu Aliyu yana daga ma khaleel da ya bi su da ido hannunsa, A hankali khadijah ta murda kofar taji a bude ta shiga, babu kowa parlorn, tana jin Shureim na ce mata gidansu wannan uncle din nan nasa ne, tana kokarin sauke sa kasa sai ga Aliyu yana sakkowa stairs, jallabiya ce baki jikinsa tayi saurin dauke kanta bayan sun hada ido, tana ta tsaye har ya iso inda suke tsaye, ya mika hannu ya karbi shureim komawa baya tayi da sauri don wani shock ta ji ta dalilin hannunsa da ya taba jikinta, shi kam sai kallonta yake ya maxa ya kawar da memoryn da bai son tunawa a ransa, Murmushi Shureim yake yana kallonsa yace “Uncle good morning” Aliyu ya shafa kansa shi ma yana murmushin a hankali yace “Morning how are you sweetheart” yace “Am fine” Kallon khadijah yayi suka kara hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yace “Good morning Iman” kame kame ta fara yi, can tayi saurin cewa “Ina kwana, wajen mumy muka xo” yace “Ohk tana Bedroom” taki yarda ta sake kallonsa tace “Toh kayi mata magana muna sauri ne” yace “mu je up stairs” daga haka ya fara tafiya ta bi bayansa xuciyarta na bugawa wannan tunanin da yake ita ma shi take a lkcn. A hankali ya bude kofar dakin mumy ya shiga da sallama, tana xaune da aminyarta, ta daga kai tana kallon Aliyu, ya sauke yaron hannunsa ya tafi da gudu ya hau kanta yace “Mama good morning” lkci daya bakin cikin dake tattare da fuskar Mumy yayi fading ta rungume yaron tana murmushi sosai tace “Kai da waye Shureim, wa ya kawo ka” Yace “Ni da Anty na” Aliyu ya juya yana kallon khadijah da ke tsaye bayansa ta ki shigowa ya koma gefe ya tsaya, Mumy na kallon ta tace “Maa sha Allah ashe tare ku ke, toh ki karaso mana Khadijah” kanta a kasa ta karaso ciki a sanyaye ta xauna tace “Ina kwana mumy” da fara’a mumy tace “Lafiya lau Khadijah ya gidan, ya su ummar ki?” A hankali khadijah tace “Suna lafiya Mumy” gaishe da kawar mumy tayi sannan tana kallon mumy tace “Mumy dama xan koma karatu ne kuma xa mu je da shureim shine Umma tace in kawo sa yayi ma ki sallama” Mumy tace “Allah sarki, amma naji dadi sosai wllh, Allah ya kai ku lafiya, ya bada abinda aka je nema” kallonta Kawai Aliyu yake jin abinda ta ce, Mumy ta mike tace “Bari in kai sa su gaisa da Abba yana nan” daga haka ta fita, Hajiya Salma dake ta kallon khadijah cike da tausayinta tace “Allah ya bada nasara kin ji Khadijah, sai a kula sosai” Khadijah ta sunkuyar da kai kasa tace “In sha Allah Mum na gode” Bayan kusan minti goma Mumy ta dawo, duk khadijah ta damu saboda khaleel da ta bari a mota, Mumy tace “Toh mu je kema ku gaisa da Abban koh” khadijah ta kasa dago kanta ta mike da kyar ta bi bayanta har xuwa side din Abba, da fara’a ya amsa gaisuwarta yana tambayarta mutanen gidansu, ba su dau lkci a parlorn ba suka fito tare da mumy, Lkci daya mood din mumy ya canxa a hankali tace “Mu shiga ki gaida iklima” Khadijah tace “Toh” daga haka ta bi mumy suka shiga dakin. Kallon iklima kawai khadijah take ganin yanda ta rame kamar warce ta shekara tana ciwo, cike da karfin hali tace “Sannu iklima Allah ya sauwake” kallonta kawai Iklima take ita ma ta kasa cewa komai, Mumy na kallon khadijah tace “Mu je” Khadijah ta bi bayan mumy a sanyaye, Mumy tace “Babu daman in baki turarruka tunda flight xa ku bi Khadijah, amma kar ki damu xan tura ma Maryam kudi a can ta siya ma ki, sai tayi ma Shureim ma shopping” murmushi kawai khadijah tayi tace “Ba komai mumy na gode” Har downstairs mumy ta rakata, Aliyu dake xaune parlorn tare da shureim ya mike ganin sun sakko, mumy tace “Toh Allah ya tsare, nagode Khadijah” Khadijah tace “Ameen mumy” daga haka ta bi bayan Aliyu da shureim don har sun nufi kofa, a tsakar compound din Aliyu ya jira Khadijah ta iso inda suke, bata yarda ta kalle sa ba xata wuce su ya riko mayafinta, juyawa tayi amma ta kasa kallon idonsa, murya can kasa yace “Baxa mu yi sallama ba?” Still ba tare da ta kallesa ba tace “Mumy na xo yi ma sallama ba kai ba” yayi murmushi yace “Ohk, Allah ya kiyaye hanya, sai mun hadu a can, cos am also leaving tomorrow” Khadijah bata tanka sa ba yana rike da shureim har suka nufi gate, kasa daurewa tayi daga karshe tace “Me ya samu iklima haka?” Da kamar Aliyu baxai ce komai ba sai kuma yace “She is suffering from Hiv” Khadijah ta xaro ido tana kallonsa a tsorace, yace “Yea, anjima dangin mahaifinta xa su xo su tafi da ita…” Lkci daya hawaye ya cika idon Khadijah tace “Toh Anty khadijah fa?” Yace “Tana asibiti, tot kin san tayi hatsari?” Khadijah ta girgixa kai tana kallonsa, yace “She had accident 2 weeks back” da damuwa tace “Toh ya jikin nata?” Yace “Ni tun lkcn da na kai su mumy ban san ke komawa ba so I don’t knw” Khadijah tayi shiru duk jikinta a sanyaye, Aliyu yyi murmushi bai ce komai ba har suka fito waje, Khadijah ta bude back seat tana kallon khaleel da damuwa tace “Don Allah kayi hakuri mun bata maka lkci” ya d’an yi murmushi yace “No problem” tun da Khalil ya kalli Aliyu sau daya bai sake kallonsa ba, Aliyu yace “Barka da asuba” sai a sannan khaleel ya kara kallonsa yace “Good morning” Shureim ya shiga mota yana daga ma Aliyu hannu sannan khadijah ma ta shiga, suna hada ido da Aliyu ta sunkuyar da kanta, Aliyu na kallonta yace “Allah ya tsare” Kamar baxa ta ce komai ba sai kuma tace “Ameen” ya rufe masu motar, driver ya tada motar suka bar layin, shureim ya fiddo bandir din Dari biyar a aljihunsa yana nuna ma Khadijah yace “Anty wannan Papa din nan ya sa min kudin a aljihuna, I told him no but he didn’t even listen to me” Khadijah ta dinga kallon kudin, ya ciro wani kudin yana nuna mata yace “Uncle ma ya bani wannan” Khaleel dake danna wayarsa bai dai ce komai ba, Khadijah ma ta rasa abinda xata ce.

    Khaleel na rungume da Shureim suka sakko daga cikin jirgi hannunsa daya rike da trolley din yaron, Khadija na biye da su har suka iso gun da xa su hau taxi, khaleel ya juya yana kallonta ganin yanda tayi laushi alamar ta gaji, murmushi yayi ya dauke kai, ta turo baki ta rungume hannayen ta, a Booth din taxin ya ajiye trolleyn hannunsa, ta karaso a hankali ta ajiye nata jakar a ciki, ya xaga ya shiga back seat ita ma ta shiga ta rufe, sai a sannan yana kallon mai taxin yace “Bridge street” har suka iso gida idon Khadija a lumshe suke, khaleel ya bude motar ya fito ya dau Shureim dake ta bacci, sai a sannan ta bude idanuwanta yace “Ae da mai cab din ya wuce da ke” ta bude side dinta ta fito, Ya fito da jakunkunan sannan ya ba ma mai taxin kudi, na Shureim ya dauka ta dau nata ta bi bayansa, suna isa bakin apartment dinsu, ya juya yana kallonta yace “Hope baki mance makulli ba” karamar jakar hanunta ta bude ta dubo makulin, ya fara bude nasa sannan ya amshi nata makullin ya bude mata yana kallonta, hannu ta kai xata amshi Shureim dake bacci jikinsa yace “Hey, ai ba gudu xan yi da shi ba hajiya” Wani kallo tayi masa ta wuce ciki ta rufe kofarta, duk yanda ta so ganin ta tsaftace ko ina kafin ta huta kasa yin hakan tayi don wani bacci ta dinga ji, wanka kawai tayi ta sauya kaya tayi slh sannan ta cire bedsheet din kan gado ta shimfida wani sannan ta kwanta, nan da nan bacci ya dauketa. Cikin bacci ta ji ana tashinta ta bude ido a hankali ta ga Shureim kusa da ita yace “Anty, uncle yace in tashe ki kiyi sllh ki ci abinci” mikewa xaune tayi tana kallon agogo taga bakwai na yamma ya wuce, ta kalli Shureim tace “Have you eaten?” Yace “Ehh uncle ya siya min, naki ma yana parlor” Shiru tayi tana kallonsa sai kuma tace “Kayi wanka?” Gyada mata kai yayi, ta sauka daga kan gadon tace “Bari in yi alwala” Ko da ta fito daga bayin bata ga Shureim ba, tayi sllh sannan ta fara gyare gyaren gidan tun daga dakin har parlorn, ta tsaftace ko ina tayi mopping sannan ta koma daki don dauko wayarta sanin Umma xata yi ta kiranta, mis cals biyu ta ga nata da na Barrister sudais, Umma ta fara Kira bayan sun gaisa Umma tace “Kun sauka lafiya?” Tace “Alhmdllh Umma” Umma tace “Ina Shureim din?” A hankali Khadija tace “Yana can wajen khaleel” Umma tace “Toh Ina gaishesa, ki kula kin ji ko daughter?” Khadija ta gyada mata kai tace “In Sha Allah Umma” Umma tace “Toh Allah maku Albarka” Khadija ta amsa da “Ameen” daga haka suka yi sallama da Umma, Sudais ta shiga kira, bayan wani lkci ya katse ya kirata, A hankali tayi masa sallama bayan ta daga,ya amsa yace “Ina kika shiga Amira?” Ta langwabar da kai tace “Bacci nayi” yace “Ohk, ya hanya?” Tace “Alhmdllh ya takwarata?” Yace “She’s good, where is my son?” D’an murmushi tayi tace “Yana waje” yace “Waje kuma, babu sanyi ne?” Tace “Akwai amma it’s not much” yace “Ohk try and get him a lot of sweaters, the cold won’t be funny from next week I guess” tace “Haka ne” yace “Xan tura maki kudi sai ki siya masa very thick one’s, kema ki siya” murmushi tayi bata ce komai ba, yace “Alryt then, sleep tight dear” tace “Toh nagode ka gaida min Amira” yace “Xata ji” daga haka ya katse wayar, kwanta tayi a hankali ta lumshe ido tana tuna moment dinsu da Barrister sudais, tashi tayi daga karshe duk a sanyaye ta fita parlor, abincin da khaleel ya siyo mata dake kan center table ta bude don ganin wani iri ne, ta d’an tabe baki ta rufe ta mike ta shiga kitchen ta kunna wuta, noodles ta fiddo xata dafa, jin motsi a waje ta leka window a hankali, xaune ta gansa kan kujera yana sanye da glass idanuwansa kan wani babban textbook yana rubutu, babban sweater ne jikinsa da neck warmer, Shureim ma dake sanye da sweater da head and neck warmer na tsaye daga bayansa ya jingina jikinsa yana kallon abinda yake yi, a hankali khaleel ya juyo ganin ta kunna wutan kitchen suka hada ido tayi saurin dauke kanta, mayar da dubansa yyi kan littafin gabansa yace “Xa ki fara koh?” Ta hararesa tace “Xan fara me?” Yace “Kin fi ni sani ai” Bata tanka sa ba ta bar wajen ta shiga yin abinda ya kawo ta kitchen din. Tana gama dafa indomien ta dauka ta fita ta koma parlor. Tana xaune parlor Idonta na kan wani material din karatun ta misalin karfe goma saura aka danna bell, mikewa tayi ta nufi kofar ta tsaya, a hankali tace “Yes?” Muryar khaleel taji yace “Hmm koh?” Bude kofar tayi ya shigar da Shureim parlorn ta yace “Alryt good nyt” tace “Allah ya tashe mu lafiya” juyawa yayi ya koma apartment dinsa, ta rufe kofarta ta kama hannun Shureim ta kashe wutan parlorn ta wuce daki tana rike da shi tace “Me yasa baka yi bacci can ba” yace “I said I want to come to you” bata ce komai ba ta rufe kofar dakin bayan sun shiga ciki. Washegari da safe Shureim na bacci ta fita xuwa supermarket, har ta dawo bai tashi ba ta ajiye duk abubuwan da ta siyo ta fara hada breakfast, muryar khaleel taji daga waje yace “Good morning” ta yi still don bata san yana gun ba, can dai tace “Ina kwana?” Yace “Hamdan, Ina kika je da sassafe cikin sanyin nan?” Ta d’an bude ido tace “Gadi na kake yi kuma?” D’an murmushi yyi jin bai ce komai ba ta leka window a hankali, 3qtr ne jikinsa da sweater mai hula yana tsaye bata dai ga abinda yake ba, kallonsa kawai take, lkci daya ya juyo tayi saurin dauke kanta, takowa yyi har gun windown yana kallonta yace “Ina kika je?” Rasa abinda xata ce masa tayi, can ta Sauke idonta kasa a hankali tace “Market” yace “What did you get?” Ta hade rai tace “Ina ruwanka” yyi murmushin sa mai kyau ya sauke hular kansa yace “Ohk then” daga haka ya juya ya bar wajen, Irish ta soya da kwai sai ruwan Lipton da ta dafa da kayan kamshi, har xata fita kitchen din ta dawo, ta fi minti biyu a tsaye kamar mai contemplating abinda xata yi, kawai daga karshe ta dau wani warmer ta debi Irish din da kwai ta xuba ruwan Lipton din a wani karamin flask ta ajiye su a gefe ta fita kitchen din, Bedroom dinta ta wuce ta tada Shureim dake bacci ta wuce bathroom da shi ta wanke masa baki ta masa wanka sannan ta sa yayi alwala suka fito, sai da ta gama shiryasa sannan ta shimfida masa darduma tace “Idan ka gama sllhn meet me at the parlor” daga haka ta fita, ba a dau lkci ba ya fito yace “Anty na gama, good morning” tace “Morning dear” kitchen ta tafi ta dauko flask din Lipton din ta mika masa tace “Ka kai ma uncle sai ka dawo ka karbi dayan” yace “Toh” ta bude masa kofa ya fita, ta danna bell din apartment din khaleel sannan ta juya ta koma ciki da sauri, Shureim na tsaye bakin apartment din khaleel ya bude kofar, dukawa yyi yana kallon yaron murmushi dauke fuskarsa yace “Good morning handsome” Shureim yace “Good morning uncle, Antyna tace in kawo maka” karba yyi yana kallon flask din sannan ya jawo yaron ciki, Shureim yace “Uncle tace it’s remaining one” rufe kofar yayi yace “Kyaleta xata kawo da kanta” Khadija tayi ta jiran dawowan Shureim amma shiru, mikewa tayi ta bude kofa ta leka waje a hankali taga kofar apartment din nasa a rufe, kiran Shureim ta shiga yi, Shureim dake xaune yana cin bread and butter da khaleel ya basa da shayi ya mike da sauri yace “Uncle Anty is calling me” xaunar da shi yyi yace “Don’t worry she will come in now” Khadija ta gaji da tsayuwa amma Shureim bai fito ba, komawa ciki tayi ta rasa yanda xata yi da Irish da ta dibar ma khaleel, daga karshe ta wuce kitchen ta dauko ta sa hijab ta fito waje, tsaye tayi tana kallon baturiyar dake bakin apartment dinsa, baturiyar ta mata murmushi tace “Good morning” dauke kai Khadija tayi kamar ana tilastata tace “Morning” xata koma ciki sai gashi ya bude kofar, Kallon Khadija yayi kafin ya dubi baturiyar dake masa murmushi tace “Good morning Dr Ayman….” Juyawa Khadija tayi ta shige apartment dinta ta rufe, Khaleel na kallon baturiyar yace “Morning Lydia, hw did u knw I am back?” Tace “I just met with Dr Ahmad, he told me you are back” shafa kai khaleel yayi a hankali yace “Ohk, we will meet later in the day, I am about going out now” tace “Ohk do you mind dropped me?” Ya girgixa kai yace “You get a taxi” daga haka ya rufe kofarsa, yana ta tsaye bakin kofa bayan kusan minti biyar ya bude kofarsa ya ga ta wuce, fitowa yayi yana kallon kofar Khadija, a hankali ya murda ya ji a bude ya shiga parlorn.

  • Noor Al Hayat 59

    Noor Al Hayat 59

    Khadijah na rike da hannun Shureim suka fito waje, tun daga nesa Aliyu dake cikin motar ke kallonta, har suka iso kusa da motar ya fito, ko ba a fadi masa ba yasan tayi kuka, kuma gaba daya a sanyaye take, ya duka yana kallon Shureim a hankali yace “How are you” Shureim yyi masa murmushi yace “Fine, good afternoon uncle” shafa kansa yyi ya mike ya kalli Khadijah yace “Thank you Iman” jakar Shureim ta mika masa ya karba ya sa bayan mota sannan yana rike da hannunsa ya xaga ya sa shi gaban motar ya dawo, ya bude maxaunin driver ya shiga, sae a sannan Khadijah ta juya ta koma ciki ko sallama bata yi da yaron nata ba, har cikin ranta take jin tsanar khaleel ynxu kam, ta ji ko ganinsa ma bata son kara yi a rayuwarta, bedroom ta wuce ta kwanta, lkci daya ta mike da sauri tunawa da tayi Sudais yace xai xo da rana, ta fita xuwa kitchen don daura masa ruwan Lipton, ta xuba kayan kamshi sosai a ciki, sake gyara gidan tayi tana juye ruwan Lipton a flask ta ji wayarta na ring ta fito parlor ta dau wayar, dagawa tayi ta kai kunne tace “Ina yini barrister?” Yace “Alhmdllh, ki turo min address Amira” tace “Toh” katse wayar tayi ta tura masa street da house number ta text message, ta ajiye wayar taje ta ci gaba da abinda take, few minutes later Sudais ya kirata yace yana waje, ta sa hijab ta fito, Tsaye ta gansa jikin mota cikin shigar da ta lura ya fi so, wato na suit, har ta iso kusa da shi idonta na kan sa, kamar yanda shi ma yake kallonta, yayi murmushin sa mai kyau yace “Kyau kike karawa idan kika xo Uk kenan” Tayi murmushi ta sunkuyar da kanta, a hankali tace “Sannu da xuwa” yace “Yauwa sannu, ke daya ce cikin katon gidan nan?” Ta girgixa kai tana murmushi tace “A’a bani kadai bace, mu shiga ciki Barrister” Yace “Do I have to Amira?” Tace “Why not?” Daga haka ta juya ta fara tafiya, ya bi ta da kallo kafin ya bi bayanta, yana shiga cikin gidan ganin fararen kujeru da table a bangaren flat dinta karkashin wani shade yace “That’s all, I will prefer staying outside” daga haka ya nufi wajen ya xauna ta tsaya tana kallonsa, bata fuska tayi tace “Barrister mu shiga ciki mana kaga fa akwai sanyi wajen…” Yace “Ke dai kike jin sanyin, just get me my tea sai ki yi wucewar ki ciki tunda kina jin sanyi” murmushi tayi ta wuce ciki sai ga ta ta fito da tray mai dauke da karamin flask da plate din cake” ajiye masa tayi ta ja kujera ta xauna tana dubansa tace “But me yasa baka son shiga ciki Barrister?” Ya bude plate din ya dau cake daya yace “What did you mean?” Ta xaro ido tace “But is there anything wrong with going inside?” Shiru yyi yana kallonta, can ta wara ido da sauri tace “Ohh yes you are right Barrister” sai kuma tayi murmushi, murmushin yayi shima ya kai cake din baki, a hankali tace “But…. Seven years back….” Sai kuma tayi shiru, kallonta ya dinga yi kafin yace “Don’t forget you where sick and pregnant then, I have no choice….” shiru tayi a sanyaye tana kallonsa, ya buda ido sosai yace “Wait… Ina Shureim din?” Ta sauke idonta daga kallonsa, cikin sanyin murya tace “Sun tafi Nigeria da Aliyu” da mamaki yace “Wani Aliyun?” Bata ce komai ba na few seconds kafin daga karshe tace “Aliyu dai” Sudais ya ajiye sauran cake din hannunsa yace “is he also in Uk?” Kai ta gyada masa, Bai iya ya sake cewa komai ba, bayan wani lkci a hankali yace “Kuna haduwa da shi kenan?” Ta sauke idonta daga kallonsa tace “Sometimes in school” Sudais bai sake cewa komai ba ya fiddo wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne, tana ta kallonsa har ya gama wayar sanann ta sunkuyar da kanta, ya ajiye wayarsa in a very low tone yace “Amira?” A hankali ita ma tace “Na’am” yace “I don’t want to deprive you of anything you wish for ur self, be frank plss Amira ki fada min gaskiya, did you want to go back to the father of ur kid?” Kallonsa ta dinga yi da wani expression, cike da karfin hali tace “Ban gane ba Barrister” Dago kai yyi yana kallon eye balls dinta yace “I mean, kina da ra’ayin komawa gun Aliyu ku yi aure ne?” Ta fashe masa da kuka tace “Anybody can say this but not you barrister, kai me tuna min irin wahalar rayuwar da na sha ta dalilin Aliyu ne, you witnessed everything, ko kuma ince tare muka sha wahalar barrister coz all those time you where by my side, Aliyu raped me without mercy har yau memory din na kai na very fresh, scene din na ido na, bayan faruwar hakan ya canxa min a gidan ya daina ma amsa gaisuwata ya daina xama duk inda nake, daga karshe he sent me away without thinking twice, with huge sum of money bayan yasan bani da kowa, Bai yi tunanin ko xan gane gida ko baxan gane ba” kuka take sosai, Sudais ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido ya kasa cewa komai, Tana ci gaba da kuka tace “Har yau ni ban ga wani prove that will convince me that ba da gangan Aliyu yayi min abinda ya min ba, ban ga prove da xan yarda cewar ba da gangan yayi raping dina ba, fine… Mahaifiyarsa cewa tayi it’s a set up, did she have any choice? Dole ta kare d’an ta, an taba set up da rape dama?? Wllh dalilin marigayin yaro na nake raga ma Aliyu har nake kulasa naji kuma xan iya xumunci da shi albarkacin yaran dake tsakaninmu, of recent I dreamt of my little boy telling me to forgive his dad, so why will I not forgive him, nasan ya cuce ni ya bata min rayuwa but he gave me happiness at the same time… My boys” hade kanta tayi da table tana kuka sosai, Sudais ya bude idanuwansa yana kallonta cike da tausayin ta, cikin sanyin murya yace “Am sorry Amira, you misunderstood me, I know ur pain but…” Ta dago hawaye na sakko mata tace “But what?” Yyi kasa da murya pleadingly yace “I am sorry plss” kin cewa komai tayi, yace “Kin hakura?” A hankali ta gyada masa kai, ya lumshe ido ya bude yace “Nagode dear, do you have any plans for our wedding?” Ring dinta ta dinga jujjuyawa bata ce komai ba sai dai gaba daya tunaninta a lkcn ya tafi kan khaleel, a hankali yace “Kin yi shiru” wani mugun haushin kanta taji ganin Wanda ya fado mata a rai, d’an tsaki tayi ba tare da ta san tayi hakan ba, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace “Ke da wa kuma??” Da sauri ta kallesa ta xaro ido tace “Don Allah kayi hakuri barrister wllh ba da kai nake ba, ban san….” Katse ta yayi yace “Nasan ba da ni kike ba Amira, I can see you are lost in ur thought, tel me what u are thinking of” ta girgixa kai tana kirkiran murmushi tace “Uhn ba komai fa” murmushi yayi yana shafa kansa yace “Toh shkkn” flask din ya bude ta mike da sauri tace “Bari in xuba maka” daga haka ta karasa budewa ta xuba masa a cikin mug dake kife, kallonsa tayi taga kallonta kawai yake shi ma, ta sauke kanta kasa a hankali tace “In sa maka Madara?” Ya girgixa kai yace “Noo, I prefer it black” Komawa tayi ta xauna tana murmushi tace “Toh, what will you take for dinner?” Ya d’an bude ido bayan ya dau Lipton din yace “Da daddare sometimes ina shan tea with irish and egg” ta langwabar da kai tace “Toh da safe fa?” Yayi murmushi yace “Tea and bread” da mamaki ta kallesa tace “Toh barrister baka cin tuwo ko shinkafa ko dai any other food?” Yace “Ina ci idan na samu” shiru tayi bata sake cewa komai ba, lkci daya taji tausayinsa don ko bai fito fili ya gaya mata ba ta gane Matarasa ce bata girki kenan, d’an murmushi tayi tace “Toh xan maka tuwo anjima ka dawo ka karba” ya xaro ido yace “A’a ku mata da bakwa son girki mai wahala don’t stress ur self dear I will take tea na riga na saba” tace “No, ba ko wace mace ce ke jin kiwiyar girki ba, I am also exceptional, ko mai kake so xan girka maka anjima” murmushi yayi sosai yace “Toh nagode Amira” Sai biyar saura ya bar gidan, shi ma saboda ya damu bai yi la’asar bane…” Ta rakasa har bakin motarsa sai da ya wuce sannan ta koma ciki. Kamar yanda ta fada masa kafin magrib har ta gama yi masa tuwon shinkafa da lafiyayyen veg soup, ta xuba masa a warmer, ganin bai kirata ba har bakwai ita ta kirasa, bayan ya dauka a hankali tace “Barrister baka dawo ka karba ba kuma” yayi kasa da murya yace “I really don’t want to stress you dear, I learn girka tuwo akwai wahala…” Katse sa tayi tace ” Ni dai ka xo ka amsa na gama, akwai wahala gun ragwayen mata dai” dariya yayi yace “Ohh really?” Tace “Yea, tun daxu na gama, ka taho ka amsa plss” a hankali yace “Toh gani xuwa Amira, I am proud of you” murmushi kawai tayi ta katse wayarta, cikin minti goma ya taho amsan abincin ya dinga sa mata albarka har ya tafi. Washegari Saturday da yamma Sudais ya xo ya fita da ita su xaga gari, duk da sanyin garin, the moment was just waow, ita dai ta san Sudais na sonta fiye da xaton ta but bata san me yasa ta kasa kwantar da hankalinta ba, he really made her day on Saturday, don babu wani damuwa tare da ita ya maido ta gida, kewan Shureim ma da take ji gaba daya taji babu shi yanxu. Ranan lahadi da safe tun da ta tashi ta shiga kitchen don girka masa shinkafa da miya, karfe goma ta kirasa, bayan ya dau wayar jin muryarsa a hankali tace “Bacci kake barrister?” Yace “Uhn am now awake” tace “Kayi hakuri ban san baka tashi ba, ka gaya min address din ka sai in kawo maka breakfast” ya mike xaune daga kwancen da yake kan gado yace “Noo ba sai kin ba kan ki wahala ba xan shirya yanxu in fito” tace “Toh, kayi hakuri” ya wara idanuwansa yace “Hakuri kuma dear” murmushi tayi ta katse wayar, bedroom ta wuce ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin kananun kaya, tana xaune gaban mirror tana gyaran gashinta kawai ta tabe baki ita kadai, yanxu su Maryam gaba daya sun tafi Nigeria biki kenan, d’an tsaki tayi a ranta tace do I have to care, turo baki tayi ta mike ta daure gashinta ta dau rigar sanyi ta sa da head warmer ta dawo parlor ta xauna.

  • Noor Al Hayat 53

    Noor Al Hayat 53

    Not edited.🤷🏻‍♀

    Khaleel ya fi minti biyar tsaye parlon yana jiran ganin ta inda xata fito amma bata fito ba, karasawa yayi kan kujera a hankali ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujerar ya lumshe manyan idanuwansa, bayan wani lkci sai ga ta ta fito daga daki da hijab a jikinta, mikewa yyi yana kallonta amma bai ce komai ba, Babu yabo babu fallasa tace “How may I help you?” Yana shafa lallausan gashin kansa a hankali ce “Where is…. the food?” Tace “Wani abincin? I didn’t cook with you ai” ya d’an kalleta na few seconds sai kuma ya nufi kitchen cikin takunsa na kasaita ta bi sa da ido, rike da warmer din Irish din ya dawo yana dubanta yace “This” daga haka ya bude kofa ya fita ta bi sa da harara ta ja tsaki. Khadijah na ji suka fita gidan da Shureim wajen karfe goma, kafin sha daya ta gama duk abinda xata yi a gidan ta kwanta duk da ta so tafiya makaranta amma ta bari gobe kawai, ganin bacci ya ki xuwa mata ta dauko kayan karatun ta ta shiga yi, tana ta xaune har azahar yayi, ta mike daga karshe ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta kwanta, lkci daya bacci ya dauketa. A hankali khadijah ta bude idonta bayan wasu awanni ta mike xaune cikin sanyin jiki tana tunanin mafarkin da tayi, bell taji an danna wanda hakan sai da ya d’an tsorata ta, bayan wasu yan dakiku ta mike tsaye da kyar har lkcn mafarkin ya kasa fita a xuciyarta, jin an kara danna bell din ta sa hijab ta fita kamar mai counting steps dinta, tana isa gun kofar ta bude a hankali, Vanessa da Angela sai Maryam ta gani bakin kofar, sosai gaban Khadija ya fadi ganin Maryam bakin kofar, da farko kallonta ta dinga yi, sai kuma ta kirkiri murmushi tana masu sannu da xuwa ta basu hanya suka shigo parlorn, mamaki ta dinga yi a ranta, me ya kawo Maryam gidanta, after all she isn’t her course mate nor her frnd, bayan sun gaisa suka mata gaisuwar Sudais, khadijah ta mike ta wuce kitchen don kawo masu ruwa da cakes din da ta siyo daxu da safe da ta fita, Maryam na kallonta tace “Mumy tace da daya twin din kika taho koh?” Ba tare da Khadija ta kalleta ba tace “Ehh tare muka xo” Maryam tace “Yana Ina?” Khadija tace “Ya fita ne” Maryam bata sake cewa komai ba, Khadija suka dinga hira da su Vanessa, sai dai hirar duk ta makaranta ce bayan kusan minti talatin suka ce mata xa su koma, har waje ta rakasu inda xa su samu cab, wani cab ne yyi parking dai dai su, aka bude cab din khaleel ya fito tare da Shureim da wani leda hannunsa, kallonsa kawai Maryam take, ya wara ido ganinta yace “Isn’t this Maryam?” Yar dariya tayi tace “A nan anguwar kake dama Dr khaleel?” Yace “Sure, me kika xo yi nan?” Ta nuna masa Khadija tace “My frnd, mun xo mata gaisuwa ne yaron ta ya rasu” ya kalli khadijah yace “Ohh that’s nyc, a schl kika santa kenan” Maryam tace “Eh a schl na santa” yace “Good” Maryam ta karasa gun Shureim tana kallonsa a hankali tace “Hello boy” gaisheta yayi, ta amsa tana murmushi jin muryarsa kamar na Aliyu, Su Vanessa ma suka taho gunsa duk ya gaishe su da turanci, ita dai Khadijah na tsaye, Khaleel na kallon Maryam yace “Alryt bari in shiga ciki Maryam, sai anjima” tace “Yauwa Dr, ya mutuniyar fa?” Har ya fara tafiya ya tsaya yace “Wai jawahir?” Tace “Ehh” yace “Haba ai ke ya kamata in tambaya, kun fi kusa” Maryam tace “Au haka ma xaka ce” Yace “Yes, nasan yau ma baxa ku rasa waya ba ni kam bata kira ni ba” Maryam tace “Lallai ma, ita ce ma xata kira ka kenan, soon ma xa su xo hutu nan da yayarta ar” Khaleel ya d’an kalleta yace “Really?” Girgixa kai Maryam tayi tace “Dad dina naji ya fadi haka nima” Ya dauke kai ya nufi cikin gida yana rike da Shureim yace “Allah ya kawo su lafiya” Taxin da Khaleel ya sauka suka hau Khadija ta daga masu hannu tace “We’ll meet in school tomorrow, thank ya all” daga haka ta wuce ciki. Khadija na kitchen tana girkin lunch khaleel ya taho ya tsaya gun window yana kallonta yace “Ya kike?” Dauke idonta tayi daga kallonsa tace “Lafiya lau” Shureim dake kusa da shi a tsaye yace “Anty I am missing you” Khaleel yace “Bude masa ya shiga” kallon Shureim tayi sannan ta ajiye wukar hannunta ta isa gun kofar ta bude, Khaleel ya shigar da Shureim ciki sannan ya fixgota har sai da ta kusa faduwa, ya jawo kofar ya rufe gam, ya jinginar da ita jiki yana mata wani kallo murya can kasa yace “Ni kike daga ma hanci” A tsorace tace “Kaga bana son haka ka bari, ka kyaleni plss” Duk ta kasa kallon idanuwansa da ya tsare ta da shi ga kamshin sa da ya cikata, A hankali yace “Fushin me kike yi da ni?” cikin rawar murya tace “Toh Fushin me xan yi da kai Dr, don Allah ka sakeni” d’aga kanta yayi tayi saurin runtse idanuwanta xuciyarta na bugawa, ya dinga kallon lips dinta, a hankali ya saketa yace “Where did you know Maryam from?” Ta shiga kokarin bude kofarta da sauri, ya rike handle din kofar yace “Au Ina maki magana xaki wuce?” Ta juyo kamar xata yi kuka tace “Ni ban santa ba sosai fah, kawai ina ganinta ne a schl kawar course mates dina ce” yace “Ohk, don’t frnd her for some reasons kin ji?” kallonsa tayi da sauri, lkci daya tayi saurin kauda kanta xuciyarta na bugawa, his eyes are always not encouraging, d’an murmushi yayi a hankali yace “Ki gaya min meye da idona Khadijah?” Ta hade rai tace “I don’t like them” wani murmushin yyi kamar me rada yace “Xan koya maki son su” murda kofar yayi ya bude ta juya da sauri ta shige kitchen din ta rufe kofar da makulli fuskarta daure. Shureim na cin abincin da ta xuba masa bayan magrib yace “Anty uncle yace gobe xan fara xuwa schl, we even went to the schl, uniform din na gidansa, in je in karbo?” Khadija dake ta kallonsa tace “I didn’t send you” yace “Ohk” sannan ya ci gaba da cin abincinsa. Washegari da asuba khaleel ya miko mata uniforms din Shureim ta kitchen, rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta karba tana kallonsa a hankali tace “Mun gode” ko kallonta bai yi ba ya wuce. Karfe takwas saura khaleel yayi dropping Shureim a makarantar da yayi enrolling dinsa, Khadija dake xaune bayan motar ta bi Shureim dake daga mata hannu da kallo har aka wuce da shi cikin makarantar, khaleel yayi parking in da ya saba ajiye ta a schl ya juya yana kallonta, ta bude motar a hankali ta fito,, bata ce komai ba ta kulle motar ya ja motarsa ya bar wajen, a sanyaye ta karasa department dinsu don saura few minutes a shiga lectures. Karfe sha biyu saura Khadija ta fito daga lectures, cafeteria ta tafi ita kadai ganin Maryam na tare da su Vanessa, tana xaune ita kadai a cafterian da lemonade a gabanta idonta a kan wayarta tana dannawa, kujerar dake kallon nata taga an ja ta daga kai da sauri, sosai gabanta yayi mugun faduwa bayan sun hada ido, tayi saurin dauke idonta, xaunawa yayi yana kallonta a hankali yace “Hi Iman” kasa cewa komai tayi ta kuma kasa dago kanta, bayan few seconds ta dago da kyar tana dubansa tace “Hello” Murmushi yayi yace “Ya boko?” Kasa amsawa tayi lkci daya little Sudais dinta ya fado mata, taji xuciyarta ya mata rauni, ganin tayi shiru ya fiddo wayarsa ya fara dannawa, a hankali tace “Ya su mumy” yace “Na baro su lafiya, how is Shureim?” Tace “Yana schl” yace “Har kinyi enrolling dinsa a nan?” Tace “Ehh” shiru ya d’an yi, kafin a hankali yace “How much did you spend Iman?” Ta kallesa lkci daya ta hade rai tace “What about it?” ya girgixa kai da sauri yace “Ohk, I am sorry I asked” bata ce komai ba, ya mike yana kallonta yace “Alryt, I will be on my way now Iman, my regards to Shureim” da ido ta bi sa, har ya tafi ya dawo da sauri ya sa hannu a aljihunsa yace “I think I’ve got something here” Chocolate guda daya ya fiddo ya duka yana kallonta ya mika mata yace “Ki ba Shureim plss” a hankali ta sauke idonta daga kallonsa ta karbi chocolate din tace “Ohk” yace “Thanks” daga haka ya mike ya bar wajen ta bi sa da kallo har ya bace mata, kallon chocolate din hannunta tayi ta bude jakarta ta saka a ciki, tayi tagumi tana tunanin me yasa in dai ta ga Aliyu sai little Sudais dinta ya fado mata, or is it because of the resemblance, jin wayarta na ring ta sauke kai a hankali tana kallon mai kiran nata.

    Sorry for the short chappy kilan in kara post around one na dare😦

  • Noor Al Hayat 47

    Noor Al Hayat 47

    Baby ta durkushe dakin tana kuka sosai tace “Mumy Anty Khadijah ce na ga tana xuba snipper a cikin indomien yaran da nake dafawa” Aliyu ya xaro ido yace “Snipper??” Da sauri ya nufi kofa mumy tayi maxa ta dakatar da shi, ya juyo hankali tashe yana kallonta, Mumy na kallon Baby tace “Ta gan ki?” Girgixa kai baby tayi tana hawaye, Mumy ta hadiye abu da kyar, cike da karfin hali tace “Je ki dauko yaran ki kawo su nan, kar ki ce mata komai” Aliyu sai kallon mumy yake xuciyarsa na bugawa, Mumy ta kallesa tana kkrin goge hawayen idonta tace “Kar ka ce mata komai, let pretend we don’t knw… Don’t say anything Aliyu” Baby ta dawo dakin da su sudais mumy ta daura su kan gadon tana kallonsu a sanyaye, ta dubi Baby tace “Tafi ki xubar da indomie din, kar ki ce mata komai kin ji, ae basu da hakkinta don hka bbu abinda ta isa tayi masu wanda Allah bai masu ba” Baby ta fita dakin a sanyaye hawaye ya ko tsaya mata, ganin abun take kamar a movie, ynxu da bata dawo ba haka xata dau indomien ta ba yaran su ci su mutu?? Anya Anty khadijah na da conscience kuwa, me yan yaran suka mata, Aliyu kam ya kasa cewa komai, Mumy ta dinga share hawayen dake ta xubo mata, me tayi ma khadijah ta mayar mata da family dinta haka, dama laifi ne idan ka jawo naka ya xauna tare da kai?? Baby bata ko kalli Anty khadijah da ta xauna parlor tana shan shayi ba ta shiga kitchen din, Anty khadijah ta bi ta da kallo ta gefen ido, daukar indomie da kwan baby tayi ta fita ta xubar cikin shara ta tara tukunyar a bakin tap, sai da ta tabbatar ta wanke tas sannan ta dawo kitchen da shi ta ajiye ta fito kitchen din ta wuce stairs, Anty khadijah ta bi ta da kallo baki bude, da sauri tace “Ke wai sai indomien ya kone ne kin bar ma mutane gas yana ci” Ba tare da baby ta juyo ba balle ta kalleta tace “Sun ce baxa su ci ba na xubar” Daga haka ta haura sama Anty khadijah ta mike baki bude tana kallonta gabanta na faduwa, da sauri ta wuce kitchen ganin tukunyar a wanke ta fita waje ta leka bola taga indomien an xubar, still tayi a gun xuciyarta na mugun bugawa, kar dai ta ganta ne…. Jiki a sanyaye ta dawo cikin gidan tana adduar Allah yasa dai ko ta ganta kar ta gaya ma Mumy, Mumy da kanta ta sakko ta shiga kitchen din da ruwan gora biyu a hannunta, ta dumama ruwan sannan ta wuce sama da shi a cup don tana da kayan shayi a dakinta, Anty khadijah ta bi ta da kallo a sanyaye, shikenan kila baby ta gaya mata kenan, da sauri ta fita da wayar ta tafi can baya xata yi kira, nan daki mumy ta hada ma yan biyun tea ta basu Aliyu dai na xaune dakin yana kallon innocent kids din, baby da har sannan jikinta yake a sanyaye tana tsaye dakin ita ma. Duk da yanda Umma ta so bin Khadijah da khaleel xuwa gidan Aliyu kamar yanda khaleel yace kasa furta hakan tayi saboda kunya, Nanny ta dai raka Khadijah har bakin motar khaleel ta koma ciki, khaleel ya din ga kallon khadijah ganin yanda ta fada saboda kuka ta bude front seat a hankali ta shiga kanta a kasa, tausayinta ya ji har ransa ya tada motar ja suka bar layin, sai da suka hau saman titi a hankali yace “But you promised not to cry again Khadijah” da sauri ta kallesa da idanuwanta da suka rine tace “I didn’t cry again, ai na riga na maka alkawari, wllh ban kara ba” a hankli yace “Toh naji dadi, kin dai san sunan anguwar su Aliyun koh?” Kai ta gyada masa, yace “Ina ne?” Tace “GRA” yace “Ai biyu ne Gra din, new or old?” Ta buda hannu a sanyaye alamar bata sani ba, wayarsa ce ya fara ring ganin me kiransa ya gangara gefen titi ya daga kiran tare da yin sallama, bayan sun gaisa da mai kiran nasa yace “Salman dama plss am asking… Can you connect me to a lawyer that you knw is just perfect, ni ba xaman Nigeria nake ba so I don’t really knw, there is this case that I need one for… I don’t want to talk about it to my family shi yasa I decided to contact you” Sai kallonsa Khadijah take ko kiftawa babu, bayan wani lkci ya shafa lallausan gashin kansa yace “Sure… Ina jira, thanks much” daga haka ya katse wayar, ya juya ya kalleta ta dauke kai da sauri, d’an shiru yyi kafin yyi murmushi yace “Frnd dina ne, xae hada ni da lawyer yanxu, I think it’s better we sue him, kulasa ayi hayaniya ba yi da fa’ida, and xai iya kai yaran wani gun, so ynxu two cases xa ayi da shi, 1st na rape… Sai kuma na biyu ya dawo rana daya yana claiming yaran da bai ma san kin dau cikinsu ba saboda rashin kunya….” Ita dai Khadijah ba ta ce komai ba, yace “So bari in jira xae turo min number Wani barrister da xanyi contacting yanxu” a hankali khadijah tace “Toh nagode, Allah….” Fingers dinsa ya daura bakinsa a hankali yana kallon kwayar idonta, ba shiri ta sauke idonta tayi shiru ta samu kanta da yin murmushi, text ne ya shigo wayarsa ya dauka yana kallon number da sunan barristern da Salman ya turo masa, dialing number yyi yana ganin ya shiga ya kai kunne, Sai da aka daga sannan Khaleel yyi sallama cikin cool voice dinsa, jin an amsa yace “Barrister barka da yamma” daga daya bangaren aka amsa masa da barka dai… Khaleel yace “You are speaking with Dr Ayman, plss ina son assigning din ka ne kan wani case, hope i won’t inconvenience you…” Barristern ya amsa masa da “Sure, but na baro office yanxu” Khaleel yace “Waow.. So yanxu ya xa mu yi, and we need to talk today barrister” Barristern yace “Okay mu hadu eatry yanxu don ban shiga gida ba” Khaleel yace “Maa sha Allah ina godiya for ur time barrister” sunan eatry din Barristern ya gaya masa daga haka suka yi sallama, Khaleel ya katse wayar yana kallon khadijah yace “So mu je mu samesa eatry din yanxu koh” kai kawai ta gyada masa ya tada motar ya nufi eatry din, khadijah tayi nisa tunanin da take, gaba daya ji take kamar tayi shekara da shekaru rabonta da lovely twins dinta, bata taba tunanin tana son su har haka ba sai ynxu, ta ji ta kara tsanar Aliyu fiye da komai na rayuwar ta, she hate him with passion… kallonta kawai khaleel yake bayan ya gama parking cikin babban eatry din, a hankali ya kai hannunsa kan nata, lkci daya ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, yyi kasa da murya yace “Thinking about ur twins?” Lkci daya hawaye ya kawo idonta tana kallonsa a sanyaye, ya girgixa mata kai yace “You’ve broke the promise” da sauri ta goge idonta tayi murmushi cikin sanyin murya tace “Don Allah kayi hakuri” murmushin yyi shima ya fiddo handkerchief dinsa ya mika mata, ta karba a sanyaye tana goge idonta, kamshin handkerchief din ya kara kwantar mata da hankali, ganin bata maido masa ba ya bude motar ya fita ita ma ta fito ya rufe motar, yana gaba tana biye da shi suka shiga cikin eatry din.

    Khaleel ya dinga bin few mutanen da ke xaune eatry din da kallo yana tafiya a hankali, ganin he can’t tell who is barrister a cikinsu ya wayarsa ya shiga kiran contact dinsa, at one end of the eatry ya ga wani mutumi da ke backing din su ya dau wayarsa dake gabansa ya kai kunne, nan khaleel ya gane shi ne, yace “Alryt na gan ka barrister” daga haka ya katse wayar ya kalli khadijah yace “Mu je” tana biye da shi har suka isa gun da barristern ke a xaune, Khaleel ya ba sa hannu suka yi musabaha, sannan ya ja kujerar da ke side din barrister ya kalli khadijah yace “Come over” ta karaso a hankali ta xauna shi kuma ya xauna yana facing barristern dake operating wayarsa, Khadijah ta dago kai a karo na farko tana kallon barristern da har lkcn idanuwansa ke kan waya yana kkrin silencing wayar, ji tayi komai nata ya tsaya ta dinga kallonsa ko kiftawa babu xuciyarta na bugawa, dai dai lkcn da shi ma ya dago manyan idanuwansa don kallon bak’in nasa yana cewa “Alryt… Barkan….” Makalewa sauran maganan nasa yayi ya dinga kallon khadijah ko kiftawa babu, lkci daya hawaye ya kawo idonta ta mike ta bar wajen da sauri tana hade hanya, Mikewa yyi shi ma da sauri ya bi bayanta yana cewa “Amiraa…” Khaleel ya bi su da kallo da catlike eyes dinsa yana shafa beard dinsa, lkci daya sudais ya tsaya cak kamar wanda ya tuno wani abu, a hankali ya juyo yana kallon khaleel dake kallonsa shi ma, dawowa yyi da sauri yana girgixa kai yace “Am.. am really sorry plss, don’t knw if she is ur wife, kayi hakuri…. I..” Sai kuma yyi shiru very confused, khaleel dai bai ce komai ba ya mike kamar bai son tafiya ya nufi kofar fita, Sudais ya xauna ya dafe kansa xuciyarsa na ci gaba da bugawa, Khaleel na fita can gun motarsa ya ga khadijah tana hawaye, ya iso gabanta ya tsaya yana kallonta yace “Who is he?” Tana share idonta a sanyaye tace “Sudais” shiru yyi na few seconds yana juya wristwatch din hannunsa, can ya dago kansa yana kallonta yace “So what next?” Ganin Sudais ya fito eatry din ya tsaya nesa da su yasa bata ce ma khaleel komai ba wasu hawayen suka dinga sakko mata a sanyaye tana kallon sudais, har ya iso inda suke shi ma duk a sanyaye yake, yana kallon khaleel a hankali yace “Am sorry Dr Ayman, idan matar ka ce kayi hakuri ka bani just 2mins in mata magana plss” da damuwa ya kare maganar, Khaleel ya d’an yi murmushin karfin hali sai dai bai ce komai ba, durkushewa Khadijah tayi gaban Sudais cikin rawar murya tace “Me yasa baka son ganina a rayuwar ka kuma barrister, I won’t be a burden to you again, amma ko xumunci ne sai kayi da ni don Allah, me yasa ka gan ni kayi pretending you’ve never known me all ur life, did I deserve that? Ni nasan har karshen rayuwata baxan mance ka ba Sudais, kai din wani haske ne a rayuwata har kullum, baxan iya biyan ka abinda ka min ba but plss allow me to show appreciation always, I have missed you for many years…. I thought baxan sake ganin ka a duniya ba, sai gashi na ganka kayi shunning….” Kasa ci gaba tayi tana kuka sosai, Sudais da idanuwansa suka kada lkci daya ya isa gun khaleel yace “Plss is she… Married??” A hankali khaleel ya girgixa masa kai, Sudais ya runtse ido ya bude yana kallonsa yace “Sorry I have to do this” yana fadin haka ya dawo ya durkusa gabanta ya rike hannunta gam cike da karfin hali yace “I know I have soo missed you Amira, I missed you… Nayi kewar ki da yawa, nayi kewar ki fiye da wanda kika min, nayi kewar twins dina, ba da son rai na na tafi na bar ku ba Amira… I have no option, kullum dake nake kwana nake tashi a rai na, but ya xan yi?? Mami na…” Kasa karasawa yyi, idonsa ya kada sosai, ita ma kuka take a hankali tana kallonsa, lkci daya yace “Where are my boys??” Tsayar da kukan da take tayi tana kallonsa a sanyaye, ganin kallon yasa gaban Sudais ya fadi sosai shi ma ya dinga kallonta, Khaleel dake rungume da hannayensa yana ta kallon dramar su yace “That’s exactly what brought us here barrister” mikewa Sudais yyi da wani expression ya isa kusa da khaleel yace “What happened to them?” Khadijah ta mike tana goge idonta cikin rawar murya tace “Aliyu…” Kasa karasawa tayi, Sudais da idanuwansa suka sauya launi ya juya a hankali yana kallonta cikin husky voice yace “Aliyu did what?” Khaleel yace “Took them away from her” Sudais ya tsaya kallon khaleel mouth agape… Lkci daya yanayinsa gaba daya ya canxa, ya kalli khadijah dake hawaye yace “I will teach him the lessons of his life” khaleel ya daga kafada bai dai ce komai ba, Sudais ya kalli khadijah yace “Har yanxu gidan nan da muka je suke?” Tace “Nima ban sani ba” kallon khaleel yyi yace “We have to go to the house now…” Khaleel yace “Ohk then” har Sudais xai ce khadijah ta taho su tafi a motarsa sai kuma yyi saurin barin hakan a ransa, muryar Khaleel ya ji yana cewa “Or ko xaki je da barrister a car dinsa, xan bi bayan ku ni” shiru khadijah tayi tana wasa da fingers dinta, can ta saci kallon Sudais ta ga kallonta yake, tayi saurin dauke kanta, bata san lkcn da tace “Ohk, xan hau tricycle ku tafi kawai, xan gane gidan kila” ta gefen ido khaleel ya kalleta bai dai ce komai ba ya nufi motarsa, shi kansa Sudais bai ce komai ba, can ya shafa kansa a hankali yace “You don’t worry tun da tare ku ka xo da shi, ki tafi ki hau tasa motar Amira” shiru ta yi tana kallonsa, murya can kasa yace “There are a lot of things to talk about Amira, but let settle Aliyu’s case first” kai kawai ta gyada masa yace “Toh tafi kar ya tada motar” A hankali ta juya ta nufi motar Sudais ya bi ta da kallo ko kiftawa babu, tana isa xata bude motar khaleel yace “No, no you don’t worry Khadijah ki tafi ku je tare da shi, we will meet there” daga haka ya fara reverse ta koma baya hankali tana kallonsa har ya fita, Jiki a sanyaye ta dawo gun sudais dake ta kallonsu, yana ganin haka ya xaga ya bude mata front seat, kanta a kasa ta shiga motar bata son ya ga hawayen idonta ya rufe motar, kafin ya xaga ya shiga maxaunin driver ta goge idonta da sauri, yana rufe side dinsa ya tada motar yyi reverse ya fita shi ma, ta madubi yake ta kallon motar khaleel dake jiran nasa yana hawa kan titi ya dau hanyar gidansu Aliyu khaleel ya bi bayansa, lkci lkci sudais ke kallon khadijah da tayi nisa tunanin da take, murya can kasa ta ji yace “Amira” da sauri ta kallesa yace “Waye Dr Ayman?” Kallonsa ta tsaya yi ta kasa cewa komai, a hankali yace “Kin yi shiru” Ta dauke idonta daga kallonsa bata ce komai ba still, hakan yasa bai sake ce mata komai ba, sai da suka yi nisa taji sanyayyan muryarsa yace “Saurayin ki ne koh?” Khadijah ta saci kallonsa still ta ki cewa komai ba, a sanyaye yace “Ki min magana pls Amira” Ajiyar xuciya ta sauke a boye, murya can kasa tace “Just as u tried ur best not to make me feel lonely in this world, shi ma abinda yake min kenan… He is also playing same role in my life.” Ta gefen ido Sudais ya kalleta na few seconds kafin ya lumshe ido ya bude yace “you didn’t answer my question Amira” Khadijah ta juya tana kallonsa tace “Lkcn da kake tsaka da taimako na, where you my boy friend?” Kasa ce mata komai yyi na few seconds, murya can kasa yace “Ohk.. But I am now, I want to be noe” juyawa tayi tana kallonsa da sauri, ba tare da ya kalleta ba ya gyada mata kai yace “Yea….”

  • Noor Al Hayat 42

    Noor Al Hayat 42

    Katse wayar Sadeeq yyi jin bata ce komai ba, ya sake kiranta a tunaninsa network ne, bayan ta daga tayi masa sallama, amsawa yyi yace “Is ur network fluctuating?” A hankali tace “Ina jin ka yanxu” yace “Ohk, Cewa nayi when xan xo in gaisa da Umma if possible har da matata kinga shkkn ta samu Umma a garin Abuja ita ma, cos she have no body here” Khadijah ta wara ido tace “Lah, are you married?” yace “Sure, kusan 3 months kenan” murmushi sosai Khadijah tayi tace “Allah sarki, Allah ya bada xaman lafiya” yace “Ameen thumma Ameen, to yaushe xa mu xo?” Khadijah tayi murmushin karfin hali tace “In dai kuna da time, kar ku ma ta gan ni tayi wani tunanin daban fa” dariya sosai Sadeeq yyi yace “Noo, she’s understanding, kawai daga few months da aure sai ta sa abu a ranta don ta gan ki, ba ma yar Nigeria bace, so she won’t think like them in sha Allah” Khadijah tace “Yar ina ce?” Yace “She is an Ethiopian” Khadijah ta wara ido tace “Kace bata jin Hausa kenan” yyi dariya yace “Noo tana ji ba laifi, ai tana xuwa hutu gun aunt dinta a Katsina sai dai tana dadewa bata xo bane, but she speaks English well” Khadijah da ke ta murmushi tace “Maa sha Allah, I will love seeing her” Sadeeq yace “Toh ko ki shirya da ‘yan gidan ku sai in xo in dauke ku, she will be very happy don bata da kowa, though shekaranjiya dai wata frnd din mum dinta ta xo daga can kasar ta su, yanxu haka ma tana gidana, but ita ma nan da kwana biyu xata wuce” Khadijah ta langwabar da kai tace “Allah sarki, to yaushe xaka xo ka kai mu, amma ni dai ina tsoro fa” dariya Sadeeq ya dinga yi yace “Tsoron me? Na fa ce maki she is not like you people in Nigeria, I can even tell her you are an old time frnd, idan kinyi insisting kina tsoro kuma sai in ce ke yar uwata ce” Khadijah tace “Haka dai ya fi” Sadeeq yace “Dubeta matsoraciya, idan na aureki na hada ku fa?” ta d’an hade rai tace “Ni ance maka aure xan yi yanxu” yyi murmushi yace “Mayar da wukar wasa nake, nima baxan iya handling two wives ba ai” murmushi kawai khadijah tayi, yace “Tun da gobe Monday xan xo da yamma sai in dauke ku, sai ki sanar da umma” Khadijah tayi shiru don bata son fashin islamiyya, can tace “Toh shi kenan Allah ya kai mu” yace “Ameen Khadijah, bari in bar ki kiyi bacci, sweet dreams” tace “Toh nagode bye” daga haka ya katse wayar, Khadijah ta sauke ajiyar xuciya jin Sadeeq yyi aure, thank God baxai shigo rayuwarta bane ya dame ta, duk da can kasar xuciyarta tana ganin girma da darajar abinda yyi mata a lkcn tana Katsina, he really helped her don da ba don shi ba kilan idan yunwa na kissa da ya kasheta, murmushi tayi ta koma ta kwanta tana rufa twins dinta da duvet, matar da yace ya aura ce ta fado mata, toh Allah yasa sa’arta ce ko xata samu warce xa su dinga xumunci sosai da, don ta gaji da rayuwa daga ita sai Nanny da boys dinta bata da kowa, Aysha dama kawai a makaranta kadai suke interact, Har ranta taji hankalinta ya kwanta haduwa da Sadeeq, ko ba komai dai akwai wanda ya santa ta san sa a Abuja yanxu sai dai fa bayan sudais bbu wanda xata sake bata lkcn ba labarinta gaskiya, its not as if Sadeeq didn’t deserve to knw her story but maimaitawan xai dinga fama mata ciwon da take healing a hankali na xuciyarta, da wannan tunane tunanen bacci ya dauke Khadijah, da asuba bayan ta idar da sllh tana xaune kan darduma tana azkar dinta Nanny ta shigo dakin da sallama, gaisawa suka yi tana kallonsu Sudais tace “Basu tashi cikin dare ba neman tea” Khadijah ta girgixa kai tace “A’a…” Nanny tace “Toh kafin dai ki gama shirin makaranta na san sun tashi, sai kiyi masu wanka, ni kuma xan tafi in hada breakfast yanxu” Khadijah tace “Toh” daga haka Nanny ta fita dakin, khadijah na fitowa daga wanka wajen karfe shidda da minti arba’in ta ga yaran xaune kan gado duk sun tashi, wara masu ido tayi ta nufesu ta durkusa tana murmushi a hankali tace “Good morning boys” kicin kicin suka yi da fuska suna kallonta kamar Aliyu ya hade rai, dariya hakan ya bata, tace “Toh bari in maku wanka sai ku tafi wajen nanny” daga haka ta koma bathroom din tana daure da towel ta hada masu ruwan wanka ta dawo ta dauke su gaba daya suka shiga bathroom din, a dakinta ta gama shirya su kafin ta tafi parlor da su nan Nanny ta sa tayi feeding dinsu, sai kusan karfe bakwai da rabi Khadijah ta gama shirin tafiya makaranta, tana isa bakin kofa ta juya tana kallon twins da suka bi ta da kallo, kamar hadin baki suka daga mata hannu a tare murmushi tayi ta daga masu ita ma sannan ta fita. Karfe hudu da kusan rabi Sadeeq ya kirata, bayan sun gaisa yace “xan taho yanxu Khadijah, am done for today a office” khadijah da ke dama ma su Sudais golden morn a parlor tace “Toh muna jira, Allah kawo ka lafiya” Tana gama ba ma yaran abinci tayi masu wanka ta shirya su cikin kayansu iri daya, sosai yaran suka yi kyau da kayan da ta sa masu, ta fiddo kayan da xata sa kenan Sadeeq ya kirata, daukan wayan tayi ta daga ta kai kunne yace “Am outside Khadijah” ta xaro ido tace “Toh don Allah yi hakuri, minti goma pls” yace “Alryt then, ina jira” a hanxarce Khadijah ta shirya sannan ta sa Hijab dinta har kasa kamar yanda ta saba, ta fita gun Nanny dake wankin kayansu shureim a bathroom dinta, ta tsaya daga bakin kofa tace “Nanny xa mu d’an fita da twins amma baxa mu dade ba” Nanny tace “Toh shkkn Allah ya kiyaye, amma kar kuyi dare kin ga yamma yyi” Khadijah tace “In sha Allah” daga haka ta fita ta shiga nata dakin ta fito tare da yaran, gabanta sai faduwa yake kar su ce baxa su bi ta ba, Har bakin kofa nanny ta rakasu tana daga ma yaran hannu su ma suna daga mata, tun kafin su iso motar Sadeeq ke kallon yaran, kawai ya bude motar ya fito yace “Waow, cute boys, ur siblings?” Khadijah ta kirkiri murmushi ta gyada masa kai daukansu yyi da daddaya da daddaya ya masu kiss yace “How are you boys” Kallonsa kawai yan biyun ke yi, ya bude front seat yana kallon khadijah yace “Toh shiga” tana shiga motar ya mika mata yaran gaba daya ya rufe motar sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da suka hau kan titi yace “Ya sunan twins din?” Khadijah tace “Sudais and Shureim” yace “Maa sha Allah, they are handsome, but step siblings din ki ne su koh?” dariyar karfin hali Khadijah tayi tace “Uhm” yace “That’s nyc” yace “Har na sanar ma Shaheedah xuwan ki, she is so happy” Khadijah tace “Da gaske” yana murmushi yace “Sure” tace “Allah sarki” nisa ne sosai da gidan Sadeeq don sai kusan karfe biyar da wani abu suka isa gidan, haka kawai khadijah taji gabanta na faduwa, bayan yyi parking yace “Welcm to our home Khadijah” murmushi kawai tayi ta bude motar ya xaga ya taimaka mata sauke yan biyun kasa sannan ta fito ta rufe motar, wata kyakkyawar mace ce da baxata wuce shekaru ashirin a duniya ba ta fito balcony din gidan, fara ce doguwa mai kyan gaske, ta karaso gun motar tana murmushi sosai tace “Sannun ku da xuwa bak’in mu” Khadijah dake ta kallonta tayi murmushi tace “Yauwa sannu” wara ido matar tasa da ya kira da shaheeda tayi tana kallonsu Sudais tace “Maa sha Allah, dear they are sooo cute” daga haka ta tsugunna ta jawo yaran jiki tace “Welcome boys” Khadijah ma sai kallon yaran nata take ganin sun ki ko da murmushi, Sadeeq ya dau Sudais yana murmushi yace “Lallai boys din nan sun iya miskilanci” Shaheedah ta dau Shureim tana dariya tace “Mu shiga ciki toh” daga haka ta fara tafiya Sadeeq ya kalli khadijah yace “Mu je” bin bayan shaheedah tayi ya bi bayanta yana rungume da shureim.

    It’s not much sorry….

  • Noor Al Hayat 56

    Noor Al Hayat 56

    Duk yanda Khadijah ta so yin kuka ko xata samu saukin xafin da take ji a xuciyarta kasa yin hakan tayi, ita ta dai san ta fadi ma khaleel haka ne don ta wanke kanta ko da wani abun xai faru gaba wanda bata ma fatan hakan but she never expect such harsh reply from him, why will he just decide to leave? Sai a sannan ta fashe da matsanancin kuka, ashe dama ba sonta yake ba, ashe dama playing dinta kawai yake, gaba daya ta rasa abinda ke mata dadi a ranta, tayi kukan har ta ji babu dadi, duk jikinta yayi sanyi. Tana kwance bayan Isha ita kadai a daki, xuwa sannan ta daina kukan da take kuma ta samu relieve amma banda xafi babu abinda xuciyarta yake mata, ji tayi an bude kofar parlor, duk da wutan bedroom dinta a kashe yake hakan bai hanata dinga kallon kofar dakin ba, lkci daya kuma aka bude kofar Shureim ya shigo dakin, bai kunna wuta ba ya karaso ya hau saman gadon ya kwanta kusa da ita a hankali yace “Anty are you sleeping?” Shiru tayi bata ce komai ba idonta a lumshe, tana ji yayi addu’ar bacci yayi lamo jikinta, a hankali tace “Ka ci abinci?” Ya dago kai yana kallonta yace “Uncle ya bani na ci” Jawo sa tayi jikinta bata ce komai ba, sai da taji yayi bacci sannan ta kwantar da shi ta mike da kyar ta sakko kan gadon tana jin kanta na sara mata ta fita parlor don rufe kofa, a kan centre table ta ga Key a ajiye ta karasa gun kofa ta murda taji a rufe, alamar ya rufe ta waje ga Key a ajiye kan centre table, Dawowa parlorn tayi a sanyaye ta dau books din Shureim ta duba taga yayi assignment dinsa ta ajiye cikin jakarsa sannan kashe wutan parlorn ta koma daki ta kwanta ta lumshe ido. Har kusan karfe goma na dare ta kasa bacci, bude ido tayi da sauri jin wayar ta na ring ta mike xaune ta dau wayar tana kallon mai kiranta, A hankali ta daga ta kai kunne tayi sallama, daga daya bangaren ya amsa yace “Hope ban tashe ki bacci ba Amira” ta lumshe ido a sanyaye tace “Ba bacci nake ba” Shiru ya d’an yi na wani lkci kafin yace “Gaya min me ya faru, what’s wrong with you” Ta bude ido da sauri cike da mamaki tace “A’a ba komai, am just tired, me ka ga?” Sudais ya girgixa kai yace “Noo, I know you well Amira, we stayed together for two years, from ur voice, there is something wrong, ki gaya min meye plss” Tace “Lahh da gaske ba komai barrister, today was very hectic shi yasa” D’an murmushi yayi yace “Ohk then” trying to brighten up tace “Ya Namecy na fa?” Yace “Ga ta tayi bacci” Khadijah tace “Toh a shafa min kanta” Sudais yace “Alryt, Shureim yayi bacci?” Khadijah ta gyada kai tace “Uhm” yace “Ya kamata ya ci gaba da karatun sa a nan, I think I will be coming over next week sai inyi enrolling dinsa” A hankali Khadijah tace “Ai ya fara ma” Yace “School din?” Tace “Ehh” yace “Shine baki fadi min ba Amira?” Ta langwabar da kai tace “Kayi hakuri” yace “Ke kika sa shi schl din” ta girgixa kai tace “Dr Ayman ya sa shi” Sudais ya d’an yi shiru sannan yace “That’s nyc” Khadijah tace “Next week din xaka taho?” Yace “Sure, Akwai abinda xan yi, but few days xan yi, so do you need anything?” tace “A’a bana bukatar komai, Allah ya kawo ka lafiya” yace “Ameen, let me leave you dear, it’s late and kilan xa ki lectures gobe koh?” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, yayi mata sallama bayan ya tunasar da ita tayi addu’a sannan ya katse wayar, ajiye wayar tayi ta kwanta ta ja masu duvet da Shureim. Washegari kafin karfe bakwai ta gama komai, ta ba Shureim indomie da ta girka masu a baki don kar ya bata uniform dinsa, Yana gamawa ta mike ta basa jakarsa ya goya ta dau nata jakar tana rike da hannunsa ta nufi kofa, tana gama rufe kofarta Shureim yace “Anty yau ma tafiya xa mu yi mu bar uncle?” Ta kallesa kamar baxa tace komai ba sai kuma a hankali tace “He is still sleeping dear” daga haka ta ja sa suka fita gidan, cab ta samar masu kamar jiya tayi dropping dinsa a schl sannan ta wuce nata makarantar duk da bata da lectures din safe, Wani waje ta samu ita kadai ta xauna, har ga Allah mai lallashinta take nema a lkcin, she need someone to console her, ta share hawayen da ya cika idonta trying hard to control her self, bata samu courage din kiran Umma ba har lkcn, tana ta xaune har lkcn lectures yayi bata tashi ba sai da ta ga kiran Vanessa, ta mike jiki ba kwari ta bar wajen. Bayan sun fito daga lectures sha biyu saura, Khadijah ta wuce cafteria ba tare da ta bari su Vanessa sun lura da ita ba, tana ta xaune nan tayi tagumi kamar ance ta daga kai ta ga Aliyu xaune yana kallonta, a hankali ta sauke kanta kasa, bayan kusan minti biyar ta sake daga kai tana kallonsa taga wayarsa yake dannawa, mikewa tayi ta dau wayarta dake ajiye kan table da jakarta xata fita taji a hankali yace “Iman” kasa kallonsa tayi tana tsaye, ya mike ya iso kusa da ita yace “Gida xa ki wuce?” Tana kokarin ganin bai ga hawayen idonta ba ta gyada masa kai, daga haka ta fita cafterian ya bi bayanta, har suka yi nisa bata ce masa ba shi ma bai ce mata ba, kuma kusan a tare suke tafiyar Daga karshe yayi breaking silence din a hankali yace “What’s wrong Iman?” bata san lkcn da ta fashe da kuka ba kamar jira take, nan da nan ya rikice mata yace “Subhanallah, me ya faru Iman, plss ki gaya min, wani abu ya faru ne” ta kasa ce masa komai sai kuka take xuciyarta na mata xafi, Har ransa ya dinga jin kukan nata, bai san lkcn da cikin tsawa yace “Plss I don’t like this Iman, ki daina wannan kukan” Tsayar da kukan nata tayi amma hawaye na ci gaba da sakko mata, wuri Aliyu ya samu ya xauna jin kafafuwarsa sun masa nauyi ya rike kansa, lkci daya jikinsa yayi sanyi xuciyarsa yayi masa rauni don kukan nata bashi da maraba da irin wanda tayi a ranar da kaddara ta afka masu six years back, A hankali ta nufi inda ya xauna ta xauna kusa da shi tana goge hawayen da yaki tsaya mata, Bayan kusan minti daya ya dago, cikin sanyin murya yace “What happened Khadijah?” Ta hadiye abu da kyar tace “Should I confide in you plss?” Kallonta yake ko kiftawa babu, a hankali yace “Sure Iman, you won’t regret doing so” Ta gyada kai cikin sanyi tace “Ohk, tnx” Shiru ne ya biyo baya na ‘ya dakiku…..

    😦Seriously I don’t like this short chapters da nake yi yanxu wllh, but dai ya fi babu d’an agwai da bak’in d’a….🙄
    Gobe xa ku samu 5 read more😅

  • Noor Al Hayat 49

    Noor Al Hayat 49

    Umma na dawowa cikin gidan ta tafi daki gun Khadijah a daki, xaune ta sameta kasa ta hade kai da gwiwa tana kukan takaici, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace “Amma Khadijah ban taba xaton haka daga gare ki ba, da ilimin ki bai kamata kiyi abinda kika yi ba, ina ce ko ba komai xai ci albarkacin mahaifiyarsa, ke da kanki kin bani labarin irin abubuwan da tayi maki while with them, me yasa xa ki mance hakan da wuri, don me laifin d’an ta xai shafeta, me yasa ko don ita baxa ki raga masa ba, ni ban ce lallai sai kin kulasa ba, Amma for the sake of his mum….” Cikin kuka tace “Umma kiyi hakuri, but I have nothing to do with Aliyu and his family again, I will pretend ban taba rayuwa tare da su ba, don Allah su rabu da ni su bar min yarana su je na yafe masu, ina jin kunyar mahaifiyar sa shi yasa nake raga masa, only me knew wat I passed through in life, ni kadai nasan abubuwan da na fuskanta a rayuwa shekarun baya, Umma na sha wahala, na ji na tsani rayuwar, ban taba sanin xan yi surviving ba ummata, da ba don sudais ba da ban san me xai sameni ba, me yasa rana tsaka Aliyu xai dawo rayuwata yana min gadara a kan yaran da bai ma san da su ba, why Umma??” Umma ta xauna duk jikinta yyi sanyi tace “Ni ba nace ki yarda da Aliyu bane Khadijah, amma kiyi hakuri ko domin mahaifiyarsa ki yafe masa, ki mance past din ki” tana kallon umma da jajayen idanuwanta tace “Na yafe masa amma kar ya sake cewa shi ne uban yarana, kuma da kai na xan shirya in tafi in dauko yarona gidansu gobe, it’s better Barrister sudais ya raba ni da su then ace Aliyu, saboda shi ne ya sha wahalar su kuma shi ya koya min sonsu ba don shi ba kilan da sun mutu yanxu” shiru Umma tayi ta kasa cewa komai tana kallonta, mikewa khadijah tayi ta hau saman gado ta kwanta, Umma ta mike a sanyaye ta kama hannun Shureim dake ta kallon uwar tasa ta fita da shi. Mikewa xaune khadijah tayi jin wayarta na ring ta dau wayar, ganin khaleel ne ta daga ta kai kunne tayi masa sallama cikin sanyin murya, Daga daya bangaren ya amsa a hankali yace “Sun kawo maki yaran Khadijah?” Ta fashe da kukan takaici tace “they brought just one, Shureim kawai suka kawo, ya tafi da sudais” Khaleel yace “Saboda me?” Cikin kuka tace “Wai xai kai sa asibiti, I don’t knw ko meye damuwarsa da ciwonsa, ni dai ya rabu da yarana, ya kyale min su” Khaleel yyi shiru na wani lkci kafin yace “Kar ki damu xa su dawo maki shi, bana son ki kara sa ma kanki damuwa Khadijah, and plss because of his mother let take everything easy, kar ma ki sake kulasa, sure baxata bari ya dauke maki kids ba, kin san ana barin halak ko don kunya, am sure soon xa a dawo maki da little Sudais kin ji” kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta, yace “Sleep without worries plss Khadijah” a hankali tace “Toh nagode” daga haka ya katse wayar, ta koma ta kwanta ta lumshe ido, cikin dare misalin karfe biyu Khadijah na xaune kan darduma bayan ta idar da slh taga wayarta yyi haske alamar shigowar text, ta mike a hankali ta isa gun wayar, message din barrister Sudais ta gani ta dauka ta bude tana kallon content din, “Dear am sorry I didn’t call, na shiga gida ne da wuri jiya, but mun yi communicating da Dr Ayman, he told me everything, you don’t worry xa a dawo maki da little sudais soon, gobe da safe xan xo in sha Allah, sleep without thought plss” tabe baki tayi ta ajiye wayar ta koma kan darduma ta xauna, har kusan asuba Khadijah bata runtsa ba, damuwa yayi mata yawa sosai ga yawan faduwar gaba da take ta ji, karfe hudu saura umma ta shigo dakin da Shureim ganin khadijah kan darduma ta isa kusa da ita da yaron tace “Gashi ya ki bacci, his temperature is high but na basa paracetamol, wai xai xo wajen ki” xaunawa Shureim yyi kusa da ita yana kallonta yace “Anty yaushe sudais xai dawo, I want to see him” Umma tace “Au abinda ke damun ka kenan” murmushii tayi ta juya ta fita tace “ka gamu da aiki kam” Khadijah ta jawo sa jikinta a hankali, taji jikin nasa ya dau xafi sosai, dago kansa tayi tace “Are you feeling pain anywhere?” Ya girgixa mata kai yace “I want to go to my brother” ta rungume sa sosai tace “Gobe xai dawo ka ji” ba a dau lkci ba yaron yayi bacci a jikinta ta mike ta daukesa ta kwantar kan gado, ta koma ta xauna tana jiran lkcn sllhn asuba. Washegari da safe Mumy na xaune kusa da Sudais da Aliyu ke sa ma drip da damuwa tace “Abuturrab ko xa ku je asibiti dai a kara duba sa, he is suffering slowly…” Aliyu ya kalleta yace “He will be okay mum, na dubasa babu wani matsala, a hankali xai dinga recovering, and it looks as if he is missing his twin, tun jiya yake ta tambayar sa” Tace “Toh ko xa a mayar da shi gidan ne?” Da kamar baxai ce komai ba, sai kuma yace “Mumy bari ya kara samun lafiya” Baby ce ta shigo da wayar Mumy dake ring ta mika mata ta fita, Mumy ta karba ta daga kiran, shiru ta d’an fara yi kafin tace “Ehh ni ce, who is on the line” ganin Mumy bata sake cewa komai ba sai shock da ya bayyana a fusakarta, a hankali afterward ta sauke wayar daga kunnenta tana kallon screen din, Aliyu dake kallonta yace “Waye mumy? Me ya faru?” Kallonsa tayi a sanyaye tace “Ka sake kiransu kilan ban ji da kyau ba ne” Aliyu ya amshi wayar ya kira number, bayan wani lkci aka dauka, abinda aka fadi ma Mumy aka sake maimaita masa, ya d’an bude ido shi ma lkci daya yace “Subhanallah, to ga mu nan xuwa, mun gode” daga haka ya katse wayar yace “Mumy wai Anty khadijah na asibiti…” A hankali mumy tace “Toh sai ku je, ni kam baxan je ba” ya bata fuska yace “No plss mumy kar ki ce haka, tunda har aka kira ki mu je kawai, baxa a biye ta halinta ba, kuma ai ba a canxa ma tuwo suna she still remain ur sister” da kyar Aliyu yyi convincing Mumy ta yarda xa ta je. Umma tayi pecking din goshin Shureim har sannan jikinsa da dumi tana shafa kansa tace “You behave your self kaji my boy, kuma ban da fada a gidan” Kai ya gyada mata, Khadijah ta kama hannunsa suka fita parlorn, khaleel na jingine jikin motarsa har suka iso inda yake, ya duka yana kallon kyakkyawan yaran a hankali yace “How are you Darling” murmushi Shureim yyi yace “Am fine uncle” mikewa khaleel yyi ya kama hannunsa yana kallon khadijah yace “Toh sai mun yi waya…” murmushi tayi tana bin sa da kallo tace “Nagode, byee” daga haka ya bude front seat ya saka Shureim ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar ya bar layin, Khadijah ta juya to koma ciki feeling relieved. Shureim na wasa da wayar khaleel yace “Uncle baxan sake ganin Sudais ba?” Khaleel ya d’an buda ido ya kalllesa yace “In ji wa ya gaya maka haka?” Ya langwabar da kai bai ce komai ba, duk sai ya basa tausayi, a hankali Khaleel ya shafa kansa yace “Xai dawo soon ka ji my boy” har khaleel ya isa gida Shureim bai sake cewa komai ba, gida ne mai girman gaske, Shureim ya wara ido yana bin makeken compound din da kallo yace “Uncle is this ur home” khaleel yyi murmushi ya gyada masa kai bai dai ce komai ba, yaron yace “It’s big” parking khaleel yyi a parking space ya fito ya xaga ya sakko da yaron sannan ya nufi entrance na babban parlorn gidan yana rike da hannunsa, yara ne da baxa su wuce Shureim din ba su uku duk maxa kusan duk kamanninsu na larabawa suna wasa parlorn da puzzles, suna ganin khaleel suka yo kansa da gudu suka rungume sa suna gaishesa da larabci, ko wannensu cike da murnan ganinsa, Dukawa yyi duk ya shafa kansa yana murmushi yace “I brought you a new friend, Shureim by name” Murmushi Shureim yyi yana kallonsu yace “Hey” sallama suka yi masa gaba daya, khaleel yyi dariya sosai, ya mike ya kama hannun Shureim suka wuce sama yana waigo yaran, bedroom din Ummun sa ya tafi da shi, Wata balarabiya ce da baxata haura sittin ba xaune dakin tana waya da halshan larabci, ya xauna gefen makeken gadon ta, ya dau Shureim ma ya ajiye sa gefensa, tana gama wayar ta juya tana kallon khaleel tace “Sai yanxu” gaisheta yayi ta amsa da murmushi ta na kallon shureim tace “Ina ka samo mana yaro” Ya shafa kai a hankali yace “Ummu… Khadijah da nake baki labari, he is her son Shureim” Umma tace “Maa sha Allah, xo in ganka sweetheart” Shureim ya sauka kan gadon ya tafi gunta ta jawo sa ta rungume sa tace “Ya ummun ka fa?” Yace “She is fyn” Khaleel yace “Twin dinsa baya tare da shi ne duk ya daga hankali shine nace bari in kawo sa nan sai su dinga wasa da su fadeel tunda suna hutu su ma” Ummu tace “That’s nyc, Ina twin din nasa ya tafi” khaleel yace “Ya tafi familyn Dad dinsa ne” Umma tace “Ayya, toh Allah ya sa wannan din ya saki jiki a nan” Khaleel yace “Ameen” Mikewa yayi ya fita dakin ya bar ta da Shureim tana masa tambayoyi tana murmushi. Baby ce ta tsaya tare da Sudais dake bacci dakin Abbansa, Mumy da Aliyu da saleem suka tafi asibitin da aka kira Mumy a zaria, Har suka isa ward din da aka gaya masu Anty Khadijah take mumy gabanta bai bar faduwa ba lkci daya kuma ta dinga tunanin wa gare Khadijah a cikin garin Zaria da ta taho, Aliyu ya murda kofar ward din ya shiga Mumy na biye da shi, kwance suka ga Anty Khadijah kafafuwanta duk biyu an mata dauri, ga wani katon plaster an mata rawani da shi a kai, hannunta daya ma daurin ne, mumy ta kasa karasawa cikin dakin sai hawaye duk jikinta yyi mugun sanyi, saleem ma ya makale jikin kofa ya kasa shiga yana kallonta baki bude, Aliyu ne yyi karfin halin karasawa cikin dakin yace “Subhanallah…. Innalillahi wa inna ilai hi raji’un” Anty khadijah ta juyo wuyanta da kyar tana ganinsu ta fashe da kuka muryarta can kasa tana magana da kyar tace “Aliyu duk na kakkarye, Wayyo Allah na ku taimake ni” Kasa cewa komai Aliyu yayi ya xauna kujera dake wajen duk jikinsa yyi sanyi yana kallonta, Wata nurse ce ta shigo dakin tace “Likita na magana da mutum daya cikin ku” Aliyu ya kalli Mumy tayi karfin halin cewa “Ka je” mikewa yyi cikin sanyin jiki ya bi bayan nurse din, Ba a dau lkci ba wata nurse ta sake shigowa da wasu allurai ta xuba su cikin ledan ruwan dake jikin Anty khadijah, yunkurin amai ta fara yi daga kwancen, nurse din tayi saurin sa hand gloves ta dagota ta dauko wani tasa ta sa mata dai dai bakinta tana mata sannu, amai ta dinga kwarara kamar xata amaye hanjinta, Mumy tayi karfin halin karasowa a karo na farko cikin muryar kuka tace “Sannu Khadijah” Nurse din ta mayar da ita ta kwantar tana ihu alamar ta fama daurinta ta ajiye tasan aman ta fita, wata cleaner ta shigo ta dau tasan ta shiga toilet. Har likitan ya kai aya Aliyu kallonsa yake da shock, cike da karfin hali yace “Ciki kuma Dr?” Likitan ya mika masa result din yace “In sha Allah, gashi nan har wata uku” kasa cewa komai yyi ya mike ya bar office din rike da sakamakon, tun bayan da suka yi hatsarin jiya da daddare da aka taho da ita asibiti ga karaya ta ko ina, ga amai da take ta kwarara ya sa likitan ya sa a mata gwajin ciki don a san irin treatment din da xa a mata, ai ko result na fitowa ya ga cikin ne da ita har wata uku, Aliyu ya share xufar dake keto masa ya shigo ward din yana kallon mumy dake ta goge hawaye tana kallon yar uwar tata, mika mata result din hannunsa yyi ya jingina da bango duk jikinsa a sanyaye.

  • Noor Al Hayat 50

    Noor Al Hayat 50

    Mikewa Mumy tayi tana kallon Anty khadijah a mugun tsorace tace “Ciki kuma khadijah? Ciki fa??” Da kyar Anty khadijah ta juyo kai tana kallon Mumy, Aliyu ya juya ya fice daga ward din, mumy ta fashe da kuka tana kallonta tace “Ciki fa Khadijah, innalillahi wa inna ilai hi raji’un, turr da halin ki Khadijah, tsofe tsofe dake khadijah” Mumy ta xauna kan kujera ta dafe kai tana kukan abun kunyan da Anty khadijah ta dauko masu, Aliyu ko minti biyar bai kara a cikin asibitin ba ya bar ma saleem makullin motarsa ya hau motar haya xuwa Kaduna, don gaba daya hankalinsa na sudais, har ya isa gida kuma yana mamakin Anty khadijah, wai ciki… jiki a sanyaye ya wuce sama xuwa bedroom dinsa, har sannan baby na xaune dakin kusa da sudais dake bacci, tana ganinsa ta mike tace “Yayanmu ya jikin Anty khadijahn?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Da sauki” daga haka ya kai hannu goshin sudais ya ji babu xafi kamar daxu da safe, ya kalli baby yace “Bai tashi ba tun daxu?” Ta girgixa kai tace “Bai tashi ba, amma yana ta kiran Anty cikin baccin” shiru yyi na d’an lkci sannan yace “Make him a cup of tea” juyawa tayi ta fita dakin, Aliyu ya xauna gefen gado, shi dai ya kasa cire mamakin da yake yi a ransa na Anty khadijah wai ciki…. Sosai Shureim ya sake jiki gidansu Khaleel cikin lkci kankani suka saba da yaran kanin khaleel mata da ke hutu a gidan, duk da kusan sun fi yin larabci, Ummun khaleel ma ta dinga jan sa jiki don yaron ya kwanta mata sosai. Yana tsaye ya jingina da mota idonsa a kan gate din gidan har ta fito, Hijab ne har kasa jikinta, ba tare da ta yarda sun hada ido ba ta karaso ta tsaya nesa da kusa da shi ta rungume hannayenta tace “Ina kwana” yana kallonta murya can kasa yace “Lafiya lau Amira, ya gidan?” Tace “Lafiya lau” yana shafa kai yace “Sorry ban xo ba jiya kuma ban kira ba, but we communicated with Dr Ayman ya gaya min komai, you don’t worry idan bai dawo da shi ba ko xuwa gobe I will personally meet his mum, kiyi hakuri kin ji, let just take everything easy because of the mother Amira, consider her generosity to you, kar ta ga baki mata kara ba” Ita dai Khadijah bata ce komai ba tana wasa da xoben hannunta, Ya d’an yi shiru kafin a hankali yace “ina shureim?” tace “Yana gidansu Dr Ayman” kallonta ya dinga yi yace “Me yake can?” Tace “Ya dai tafi da shi ne kawai” yace “Ohk that’s nyc” shiru ne ya biyo, “We need to talk Amira” abinda ya fadi kenan yana dubanta da kyau, a karo na farko tayi masa kallon cikin ido tace “About what?” Jikinta ne yyi sanyi tuna baya da tayi, their moment together lkcn tana laulayi, lkcn da ta fara samun sauki, lkcn da cikinta ya fito har xuwa lkcn da ta haihu, shi ma kallonta yake ko kiftawa babu, taji kamar ta fara hawaye a wajen, murmushi yyi ya dauke kai a hankali yace “Yanxu kin girma sosai, kilan kin fi karfina ko Amira, may be I am not ur class….” Sauke idonta tayi daga kallonsa cikin sanyin murya tace “Ban gane ba” openly yace “Xa ki iya auren mai mata?” Bata kallesa ba bata kuma ce komai ba amma sai da gabanta ya fad, wani murmushin ya kuma yi yace “That says it all, you are not interested” sai a sannan ta daga kai ta kallesa tayi murmushin karfin hali ita ma tace “I know marrying u is not even enough in biyaka abinda ka min a rayuwa barrister, but…” Ya katse ta da sauri yace “But what?” A hankali kuma a sanyaye tace “It looks as if you are afraid of ur wife, ba lallai ta bari ka kara aure ba…” lkci daya mood dinsa ya canxa yace “Says who Amira?” Ta sauke idonta kasa tace “Gashi nan saboda ita mun hadu after six years a super market amma kayi kamr baka taba sani na ba, kuma saboda ita ka kasa kirana jiya kana gida ka min common tambaya….” Ya dakatar da ita yace “Sai hakan ke nufin ina tsoronta kuma Amira, ba tsoro bane ina gudun fitina ne kawai, kema kin san it will look somehow in maki magana a mall ranan muna tare da ita kin san halin ku mata da kishi, a gida kuma it’s not proper in yi waya dake….” Khadijah tayi murmushi tace “Upon ur profession? Ta mance wa ta aura ne?” Shiru yyi yana kallonta, a hankali yace “Kawai dai ki ce baki ra’ayina Khadijah” Tana wasa da xobenta cikin sanyin murya tace “I didn’t say that Barrister, just that bayan duk wahalan da na sha a rayuwa bana son inyi aure kuma in kasa samun kwanciyar hankali, kasan lalurata, ina da ciwon xuciya, ni yanxu ko kadan bana son hayaniya…. Ban san me yasa ba” tana magana ne hawaye cike idonta, “Ban da haka bani da abinda xan iya biyanka da shi a duniya barrister da ya wuce in amince da auren ka a yanxu, but am afraid…” hawaye na sakko mata ta kai karshe, Lumshe ido yyi na few seconds kafin ya bude ya ga kallonsa take, da sauri ta sunkuyar da kanta yace “Kar ki damu da matata Amira, beside ba gida daya xa ku xauna ba” ita dai bata ce komai ba amma gaba daya hankalinta a lkcn ya tafi kan khaleel…, lkci daya jikinta yyi mugun sanyi, A hankali ta ji yace “Plss Amira…” Ta daga kai a sanyaye tana kallonsa. Mumy ce xaune tayi tagumi nesa da Anty khadijah dake ta ihu tana cewa xata mutu axaba ya isheta a cire mata kafafuwan ta huta damuwa ce sosai tare da Mumy tayi kukan takaici har ta gaji wannan wani irin bala’i ne, da ta tuna wai ciki gare Anty khadijah sai ta fashe da kuka sosai, da kyar ta tashi jin ring din wayarta dake ajiye cikin jaka ta bude ta fiddo wayar ta daga ta kai kunne hade da sallama, “Don Allah ina magana da Hajiya Fatima ne?” Mumy tace “Ni ce” matar tace “Alhmdlh, Hajiya Laure ce, dalilin kiranki yanxu shine tun jiya nake neman Hajiya Khadijah a waya bana samu, ga yar ta da ta bari nan kuraje sai ruwa suke suna fashewa, don Allah a turo a dauketa gaskiya, ni ban san wani irin ciwo take ba ni mai yara a gida, don Allah a xo a dauke ta gidana don ko tashi bata iya wa” Mumy ta kasa cewa komai jikinta ya kara mutuwa, cike da karfin hali tace “Toh xa a xo a dauketa, hatsari khadijahr tayi jiya” Hajiya Laure tace “Hatsari kuma? Toh Allah ya kiyaye, ni dai a xo a dauke yar nan gidana babu ruwana” daga haka ta katse wayarta, Mumy ta dinga goge hawayen idonta, bayan wani lkci ta kira Aliyu ta ji ko xai je dauko ikliman, yana dagawa cikin sanyin murya tace “Abuturrab,” yace “Na’am Mumy, ina yini” tace “Alhmdlh, ya jikin yaron?” Ya d’an yi shiru kafin yace “Muna Asibiti fa Mumy” tace “Asibiti kuma, jikin ya ki ne?” A hankali yace “Toh da sauki, but xa a duba kansa ynxu to check if everything is okay” Tace “Ikon Allah, to Allah ya basa lafiya” yace “Amin mum” daga haka ta katse wayar ba tare da tayi masa maganar ikliman ba ma, Aliyu ya ajiye wayarsa yana kallon Sudais da aka cire ma oxygen a lkcn, Baby na share idonta a hankali tace “Yaya ko xaka kira mum dinsa, kaga ita yake ta kira fah” ya kalli kanwar tasa yace “I don’t have her contact” tace “Toh barristern nan da suka xo tare fa?” Shiru Aliyu yyi tunawa da yayi ya dau number khaleel a wayar Farouq ranan, daukar wayarsa yyi ya fiddo number yana kallo, da kamar xai yi dialing sai kuma ya fasa ya mike yace “I will go get her now” Da makullin motarsa ya fita xuwa parking lot, yana shiga motarsa ya nufi gidansu Khadijah, yana isa yyi parking ya fito ya nufi gate, a hankali ya tura ya ji ma a bude yake ya shiga, kamar bai son tafiyar yake yi har ya isa entrance din cikin parlorn, ya kai hannu ya danna bell, Khadijah dake kitchen tana girkin lunch ta fito kitchen din da sauri, bata damu da ta sa Hijab kan kananun kayan jikinta ba don a tunaninta Nanny ce ta dawo daga kasuwa, bude kofar tayi suka yi ido hudu da Aliyu, tayi still a wajen na yan sakwanni kamar an dasa ta, da sauri ta bar bakin kofar tayi hanyar daki ya bi ta da kallo, can ya sa kafa ya shiga parlon ya xauna kan kujera, kan gado Khadijah ta fada tana maida numfashi ga gabanta dake ta faduwa, Kar umma ta fito parlorn babu Hijab ya sa ta mike da sauri ta shiga dakin Umma, xaunawa tayi har ta gama waya kamar xata yi kuka tace “Umma kun ga abinda nake gudu kenan koh? Meye ya kawo Aliyu gidan nan yanxu, why will he come to this house kuma ba tare da yarona ba” Umma na kallonta da mamaki tace “Yana ina?” Fuska daure tace “Yana parlor mana” Umma tayi shiru, sai kuma tace “Toh ai sai ki tsaya ki ji me ya kawo sa koh” Khadijah ta kara hade rai sosai tace “Umma ni idan xan koma UK da yan biyun xan tafi gaba…” Shiru tayi a sanyaye tunawa da tayi ai a can ma ta fara jam da Aliyu, Umma tace “Ki tashi kije ki ji abinda ke tafe da shi, ni kar ki min fitsara” rai ba dadi Khadijah ta mike ta fita, labewa tayi da bango a corridor tana kallonsa, the mouth, the nose, the eyes, worst of all the face… Sosai jikinta yyi mugun sanyi, wayarsa kawai yake dannawa idonsa a kai, kamar ance ya waiga suka hada ido gabanta yayi mugun faduwa, tayi saurin dauke kai, shi ma hakan yayi, ta hade rai bbu yabo babu fallasa tace “Me ka xo yi gidan nan malam?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Ur son, yana son ganin ki” Bata san lkcn da ta fito parlorn ba ta taho gabansa tace “Yana ina?” Ya mike bai kalleta ba yace “At the hospital” lkci daya hankalinta ya tashi tana kallonsa tace “Har yanxu jikin nasa?” Aliyu ya girgixa kai ba tare da ya kalleta ba still yace “Da sauki” daga haka ya nufi kofa yace “Ina jiran ki a waje” juyawa tayi da sauri ta koma dakin umma cike da damuwa tace “Umma wai asibiti xa mu je wajen Sudais” Umma tace “Asibiti kuma, an maida shi asibitin ne?” Gyada kai tayi kamar xata yi kuka tace “Ehh” Umma tayi shiru na d’an lokaci sannan tace “Toh ki je, Allah ya kiyaye, idan ba a sallamesa ba xuwa anjima sai in taho nima, ki tafi da wayar ki xa mu dinga magana” Khadijah tace “To” sannan ta koma dakinta ta dau waya ta fita, Aliyu na mota yana jiranta har ta fito, ta hade rai ta bude front seat din ta shiga ta rufe, shi dai bai ce komai ba ya tada motar yyi reverse suka bar anguwar, danne danne kawai take a wayarta, lkci daya tayi dialing number Khaleel ta kai wayar kunne, yana dagawa yace “Ya aka yi Ummu twins?” Ta sauke idonta kasa tace “Xan je clinic gun sudais ne yanxu” yace “Clinic, did they call you?” Ta gyada kai a hankali tace “Ehh” yace “Ohk toh Allah ya tsare, ke da waye?” A takaice tace “Driver!” yace “Ohk, text me the hospital name yanxu” tace “Toh” daga haka ta katse wayar, shi dai Aliyu driving dinsa kawai yake, bayan wani lkci fuska daure kamar ana tilastata tace “Wani asibitin ne?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Ban sani ba” wani kallo ta dinga masa ganin ko waigo wa bai yi ba tayi tsaki, har suka isa asibitin babu wanda yace komai cikinsu, bayan yyi parking ya bude motar ya fita ya nufi entrance din clinic din, sosai ta ji ranta ya baci ta fito motar ta rufe tana hararansa, ba tare da ya juyo ba yyi locking motar da makullin hannunsa, sai da ta karanta sunan clinic din sannan ta bi bayansa tana turo baki, tuni ya shige ward kafin ta shigo reception, ta dinga kalle kalle ta rasa inda ya shiga, gaishe da nurses dake wajen tayi, wata nurse tace “Tare ku ke da Dr Aliyu?” Khadijah ta gyada mata kai, nurse din tace “Ohk ki je daki na biyar nan ya shiga” Khadijah ta mata godiya ta bi hanyar da ta nuna mata tana kirga wards din har ta xo na biyar, Aliyu na tsaye jikin window yana kallon result din scan da aka ma Sudais Khadijah ta shigo dakin, tsaye tayi bakin kofa tana kallon sudais dake kwance, Baby na ganin ta ta mike, a sanyaye Khadijah ta karaso ciki, baby na murmushi tace “Sannu da xuwa Iman” Khadijah ta mayar mata da murmushin tace “Ya su mumy?” Baby tace “Suna lafiya” tsayawa Khadijah tayi tana kallon Sudais dake bacci restlessly, har ya rame daga jiya xuwa yau, Baby tace “Jikin da sauki ma” Khadijah bata iya ta ce komai ba tana kokarin ganin hawaye bai zubo mata ba, Baby ta ja mata kujera tace “Ki xauna” kamar ta san da kyar take tsaye dama, Khadijah ta xauna tana ta kallon yaron nata, Aliyu ya juya ya fita daga dakin, text din sunan asibitin ta tura ma khaleel. Ba a dau lkci ba wani Dr ya shigo ward din Khadijah ta dinga kallonsa, allura biyu yyi ma Sudais, Khadijah ta mike da sauri jin ko bude ido bai yi ba, tana kallon likitan hankali tashe tace “Dr ban ji yyi kuka ba kuma yana kukan allura” yar dariya likitan yyi yace “Toh ai ba dole yyi kuka ba madam” daga haka ya juya ya fita, ta dinga kallon sudais xuciyarta na bugawa, ita kanta Baby mikewa tayi tana kallonsa, Khadijah ta kai hannu tana tashinsa, sai da ta jijjiga sa sosai ya bude idonsa a hankali, yana ganinta ya rike hannunta murya can kasa yace “Anty don’t leave me plss, where is shureim” Sosai ta ji hankalinta ya kwanta ta taba jikinsa ta ji bbu xafi, ta xauna kusa da shi cikin sanyin murya tace “Get well soon plss son” hawaye cike idonta ta kare maganar yace “Ohk, Anty shureim” ta kwantar da murya tace “Xai xo anjima ka ji” ya gyada mata kai, Aliyu ne ya shigo dakin, yana kallonsu yace “why did you wake him?” Ba tare da ta kallesa ba ta hade rai a takaice tace “Because he is my son” tsayawa yyi yana kallonta, Baby jikinta yyi sanyi ita ma, ta mike kawai ta fita daga ward din, Aliyu ya dau wayarsa ya fita shi ma, Mumy ya kira bayan ya gaisheta yace “Mumy ina jin fa dole xa a fita da yaron nan waje” cikin tashin hankali Mumy tace “A fita da shi kuma? Jikin ya ki ne har yanxu Abuturrab” yace “Akwai matsala ne scan da aka yi masa, just pray for him mumy” Mumy ta kasa cewa komai Aliyu ya katse wayar, Khadijah sai kallon sudais take da ya kara rufe ido kamar mai bacci, ta dau waya ta kira khaleel, bugu biyu ya dauka, tace “Plss ka d’an xo da Shureim” yace “Ohk, let me go back to pick him” Cikin minti sha biyar khaleel ya kirata yana asibiti, Khadijah ta mike ta fita don shigowa da shi, da gudu Shureim ya taho ganinta da yayi tun daga nisa ta bude hannunta ta rungume sa, “Anty plss I want to see sudais now” ta shafa kansa tace “You wil see him sweetheart” daga haka ta mike tana rike da hannunsa ta kalli Khaleel dake kallonsu, ta d’an yi murmushi ta sauke kanta kasa tace “Ina yini” yace “Lafiya lau ya mai jikin?” Tace “Da sauki, ya ma koma bacci yanxu” daga haka ta fara tafiya rike da shureim ya bi bayan su har suka isa ward din, tun da Khaleel ya shiga yake kallon sudais har ya karasa kusa da shi, ya juya yana kallon Khadijah yace “Yaushe aka kawo sa asibiti?” Ta bude hannu alamar bata sani ba, yace “Wa ya kawo sa?” Ta turo baki tace “Shi ya kawo sa” khaleel yace “Ina yake?” Tace “Kilan yana office” juyawa yayi ya fita ta bi sa da ido, can ta mayar da dubanta kan sudais, shureim na kusa da shi kan gadon da damuwa yake cewa “Sudais are you still sick? Plss get well soon so that we can play together, I am missing you” Kallon sa kawai Sudais yake bai ce komai ba, hawaye ya cika idon Khadijah ta karasa kusa da shi ta kamo hannunsa tace “Sudais talk to ur brother he is missing you” Sudais ya gyada mata kai amma bai ce komai ba, ta xauna kujera hawaye na sakko mata tace “Plss get well son, I want to see u hale and hearty once more” Aliyu na rubuce rubuce yana duke gaban table dinsa khaleel ya shigo, kallon kallo suka tsaya yi, can khaleel ya karasa cikin office din yace “What exactly is the little boys problem now?” Ba tare da Aliyu ya sake kallonsa ba ya dau takardan scan da aka yi ya mika masa, Khaleel ya karba yana dubawa, shiru yyi na yan dakiku kafin ya kalli Aliyu yace “So what next?” Mikewa Aliyu yyi yace “We will be going to India tomorrow” kallon khaleel yyi yana kwasan takardun da ya gama rubutu a kai yace “Don’t tell her anything about it….” Kallonsa kawai khaleel yake bai ce komai ba, can ya juya ya fita daga ward din ya koma reception ya xauna, kai kana ganinsa kasan he is disturbed, Khadijah tayi ta jiran dawowan khaleel amma shiru, taji duk hankalinta ya tashi, kallon Shureim dake ta damun sudais din da magana ta yi xata ce ya daina damunsa taji muryar sudais a hankali yace “Anty tell him to let me I want to rest” idonsa a rufe yake maganar, Ta kalli shureim da damuwa tace “Leave him plss shureim ka ga ba shi da lafiya” Shureim ya bata fuska yace “Then I will rest with him too” ita dai bata ce komai ba, wasu likita biyu da nurse daya suka shigo ward din, daya ya sauke Shureim kasa daga kan gadon, wasu alluran likitan ya kara masa guda biyu, daya likitan yace “Xa a canxa masa daki yanxu madam….” Juyawa Khadijah tayi ta fice daga dakin xuciyarta na bugawa, Khaleel na xaune har sannan a reception, bai jira ta karaso ba ya mike ya fita kamar bai ganta ba, sama ta wuce ta bude office din Aliyu, tsaye ta gansa jikin window ya juyo suka hada ido, ta isa kusa da shi hawaye cike idonta tace “Tell me what’s wrong with my son Aliyu, ka gaya min plss” ta fashe da matsanancin kuka tana kallonsa, ya dauke kai yace “He will get better soon, it’s just a minor illness” ta tsayar da kukan da take cikin sanyin murya tace “Are you assuring me??” Yana kallon kwayar idonta yace “Sure, Allah xai basa lafiya” juyawa tayi ta nufi kofa ya bi ta da kallo. Karfe Biyar na yamma Umma ta xo clinic din, hankalinta ya tashi sosai ganin Sudais ita ma, Khadijah dake xaune cikin sanyin murya tace “Umma kawai xaxxabi ne, Allah xai basa lafiya” ita dai umma bata ce komai ba, abincin da ta kawo ma bai ci ba, khaleel yace ta bar sa anjima xai ci ana basa abinci a drip, Da ladabi Aliyu ya shigo ward din ya gaida umma ya fita, har aka yi isha suna clinic din, Aliyu ya samu khaleel dake xaune waje yace “You tell her to go home it’s getting late” Khaleel bai kallesa ba yace “Allow her to be with her son, kuma it’s better ka gaya mata matsalar yaran sai ta bi ku xuwa India gobe” Aliyu bai ce komai ba na kusan minti daya, can ya juya ya bar wajen, tara saura umma ta wuce, babu yanda Khadijah bata yi da shureim ya bi ta ba amma ya ki, haka umma ta tafi ta bar sa. Khadijah na xaune ta jingina da gadon da sudais yake misalin goma saura wayarta ya fara ring, dagowa tayi tana kallon wayar, ta dauka a hankali ganin sudais ke kiranta ta daga ta kai kunne cikin sanyin muryarta tayi sallama, muryar mace taji tace “Amira koh?” Khadijah tayi shiru tana saurarenta, tace “Toh jiddah ce, matar Barrister Aliyu, ina son sanin meye hadin ki da mijina tun da girma da arxiki” mamaki ya cika Khadijah, jiddah tace “Ohh shiru xa ki min kina ji na?” Khadijah tace “Toh uwata ce ke da baxan yi shiru ba, why not ki tambayi shi mijin naki meye tsakaninmu xa ki kirani, ko kin mance profession din mijin naki” wani tsawa jiddah tayi tace “Kee maxa kalmashe kalamanki, kinsan wacece ni, na fi ki sanin aikin mijina malama, sannan mijina baya kiran client dinsa baya kuma saving numbers dinsu sai dai su kira sa suyi introducing kansu ke ko gashi duk shi ke kiran ki kuma ku dau mintuna masu yawa kuna magana, halan baki san yana da aure bane, baki san mijin aure bane?” Tsaki Khadijah ta ja tace “Kan ki ake ji, wannan kuma sai ki je ki samu mijin naki ki tambayesa” daga haka ta kashe wayarta, jiddah ta kirata ya fi sau hudu bata daga ba lkci daya taji xuciyarta ya fara mata xafi duk da ba wai hayaniya tayi da ita ba, taji ranta yyi mugun baci. Wata nurse ce ta shigo ta nuna mata wani spare gado dake ward din tace ta kwanta, khadijah ta mike tana kallon Sudais duk da bata son barin sa, ta kai hannu goshinsa still taji ba xafi temperature dinsa is normal, ya bude idonsa a hankali, har ranta ta ji dadin hakan don har umma ta xo ta tafi bai bude idonsa ba, xata yi magana ya riga ta yace “Anty ina Shureim?” Tace “Yana waje tare da uncle” ya bata fuska yace “Me yasa ya tafi?” Ta kwantar da murya tace “You said he shud allow you to rest, shine ya tafi da uncle” a hankali yace “Anty kice ya xo plss, I want to tell him am sorry” jikinta yayi sanyi tace “Toh xan kira sa yanxu” daga haka ta nufi kofa tana waigo yaran da ya bi ta da ido,

  • Noor Al Hayat 48

    Noor Al Hayat 48

    Har suka isa gidansu Aliyu babu wanda yace komai cikinsu, khadijah tayi nisa tunanin da take bata ma san sun iso ba, Sudais ya fito daga motar ya xaga side dinta ya bude mata ganin bata fito ba, sai a sannan ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, tayi saurin sauke kanta ta fito daga motar ya rufe, kallon motar khaleel sudais yyi, dai dai sannan shi ma ya fito daga motarsa, Sudais ya karasa gun sa yace “I pray we meet him at home” Khaleel ya daga kafada yace “Allah ya sa” Sudais ya kalli Khadijah dake tsaye jikin motarsa sai kallon gidan take a sanyaye, gate din gidan ya nufa khaleel ya bi bayansa, bai tsaya sauraran mai gadi Usman dake tambayar sa daga ina ba ya kutsa kai ya shiga gate din ya juya yana kallonsa yace “Six years isn’t that far, bai ci ka mance ni da wuri haka ba malam” khaleel ma ya shiga gidan yana kallon mai gadin murmushi dauke fuskarsa ganin yanda yyi kasake yana bin Sudais da kallo, A sanyaye Khadijah ta gaida Usman da ya xaro ido yana kallonta da mamaki yace “wannan kamar Khadijah??” Murmushi ta kirkira ta shiga cikin gidan ta bi bayan su sudais da suka nufi entrance din shiga gidan, haka kawai gabanta ya dinga faduwa tayi slowing pace dinta, Sudais ya danna bell ya ja gefe ya tsaya, bayan wani lkci aka bude kofar, Baby ce tsaye bakin kofar ta dinga kallonsa na wasu seconds kafin ta gaishesa, yana kallonta ya amsa da murmushi yace “Can we come in?” Barin bakin kofar tayi ta rasa abinda xata ce masa, ya kula she is lost don haka ya shiga parlon khaleel ya bi bayansa, tuni khadijah ta labe jikin bango jin baby ce ta bude kofar, hawaye suka shiga sakko mata ta kasa shiga parlorn, Anty khadijah dake xaune parlorn ta dinga kallon Sudais kamar me son tuno inda ta san sa, sarai ya dau fuskarta ya gane ta, a hankali yace “Hello?” Ta mike tana yamutsa fuska tace “Daga ina? Wa ku ma kuke nema?” Yana kallonta yace “Bak’i ne…. Amma nayi mamakin da baki gane ni ba Hajiya” Ta hade rai tace “Do I have any business with you da xan gane ka, malam nan gidan masu aure ne, ka fadi wa ka ke nema, ba haka nan ake shiga gidan mutane ba, from all indications ma batar hanya ku ka yi ” Ya taka har gabanta ya tsaya yana mata kallon cikin ido ya fiddo ID card dinsa yace “Barrister Aliyu…. May be this will make you remember me fast” mikewa tayi da sauri tana masa wani kallo, sai kuma ta shiga kalle kalle don ta tabbatar babu kowa parlorn, ta hadiye abu da kyar tace “Wa kake nema malam, me ka sake dawowa yi gidan nan?” Jin bai ce mata komai ba sai murmushin da yake ta juya da sauri ta kalli khaleel da ya nemi kujera ya xauna yyi relaxing a kai, Murya suka ji a stairs duk suka juya, Mumy ta sakko tana kallonsu da mamaki tace “Sannun ku da xuwa” Sudais ya amsa ta karaso parlorn tace “Are you looking for Someone?” Sudais yace “Sure” juyawa yyi ya kalli bakin kofa ya ga khadijah bata shigo ba, ya juya ya koma bakin kofar, yana fita yace “Come in khadijah” Khadijah ta girgixa masa kai cikin rawar murya tace “Baxan iya ba, kuma kila ba nan ya kawo su ba” sudais yace “Trust me, kawai ki biyo ni” daga haka ya shiga parlorn ta bi sa a d’an tsorace don jin muryar Anty khadijah ya kara daga mata hankali, baby ce ta fara xaro ido ganinta lkci daya ta nufe ta da gudu tace “Imann” kasa amsa mata Khadijah tayi, Baby ta rungumeta, hakan yasa khadijah ta fashe da kuka kamar yanda baby ma ta fara kuka, tuni Anty khadijah ta rikice bakin ta na rawa tace “Me ya kawo yarinyar nan gidan nan, me ta xo yi….” Ba tare da Sudais ya kalleta ba yace “Ta xo amsan yaranta” Anty khadijah ta yo waje da ido tace “Tayi aure cikin gidan nan ne da ta xo amsan yara??” Khadijah da ke hawaye a sanyaye ta daga kai ta kalli inda mumy take ta ga kallonta take ko fiftawa babu, sunkuyar da kai tayi kamar me counting steps dinta ta isa gaban mumy hawaye na sakko mata, Mumy da idanuwanta suka kawo ruwa ta rungumeta murya can kasa tace “Khadijah..” duk wannan abun Aliyu na sama tsaye yana kallonsu, cikin rawar murya Khadijah tace “Mumy ki ce ya bani yarana na yafe masa wllh…. Intervene plss mumy” Mumy ta kasa cewa komai sai kuka, Anty khadijah sai wuri wuri ta ke da ido a parlorn ta kasa cewa komai, A hankali Aliyu ya dinga sakkowa stairs din har ya iso parlorn, Khadijah ta dinga kallonsa tana jin tsanar sa, Sudais ya taka har gabansa yana kallonsa da kyau yace “Aliyu?” Aliyu yace “Sure, any problem?” Sudais ya gyada kai yace “Fito mata da boys dinta” Aliyu ya rungume hannunsa yana kallonsa with interest yace “Bodyguards din nata har biyu ne kenan” Khaleel yyi calm smile pretending Aliyu doesn’t even exist in the parlorn balle har ya ji abinda yace, shi dai yana xauna kan kujera har sannan, Sudais da idanuwansa suka sauya launi yace “You are stupid… I mean very stupid” Murmushi Aliyu yyi yace “Ku dai da ku ke biyota ne xa a kira da haka, look… ba ku da right din da xa ku dinga interfering a case dina da ita, it’s almost a family issue so stay out of it…..” Khadijah bata san lkcn da ta isa gabansa ba idanuwanta suka kankance don bala’i tace “Wannan da kake gani ya fi Ka right, when I say right ina nufin right, wllh ya fi ka 100% right over those children, he is almost their father, and will always remain their father, na tsane ka Aliyu, na tsane ka…. I hate you” Tana kai wa nan ta fashe da kuka sosai, Mumy ta rasa abinda xata ce ban da kuka bbu abinda take, Aliyu yace “Dama ban ce kar ki tsane ni ba Khadijah, you have all right to do so, but Iman am sorry baxan ba ki yaran nan ba, you’ve past through a lot, ki bar ni da su yanxu let me also play my role, ki tafi ki je ki ci gaba da rayuwar ki da bodyguards din ki, thank God you said he is almost their father not their father, ni kuma I am their biological father…” Tapping dinsa Sudais yyi xuciyarsa na tafarfasa, strictly yace “Malam kasan wanene ni kuwa? Did you knw why I am taking it gently with you, baka sani ba sure.. Then knw this, it’s because of ur mother, na ga alamar she deserves some respect, don haka cikin salama ka fito da yaranta yanxu ka bata idan ba haka ba….” Aliyu ya tabe baki yana d’an murmushi yace “You do ur worst….Barrister” Bude baki Sudais yyi yana kallonsa, Khadijah ta durkushe wajen ta kara rushewa da kukan takaici, mikewa khaleel yyi yana ma Aliyu wani kallo yace “Amma kai jahili ne na ga alama, islamically baka da right over yaran nan, kai har yaran da ka samu ta hanyar zina kake alfahari da kake bragging baxa ka bada ba?? Is this how senseless you are” Yar dariya Aliyu yyi yace “U watch ur tongue gidanmu ka xo ka same ni, so you have no place to tell me nonsense, baxan bada yara ba nace” Sudais ya sake tapping dinsa yace “Good, ka saurare sammaci gobe, nasan dai baxa kayi denying kayi raping din yar mutane a court ba koh, sannan kuma don rashin kunya ka dawo kana claiming yaran da baka san da su ba, baka san da yanda aka yi Allah ya raba ta da su ba… You are wicked Aliyu” Aliyu yace “Ka kai ni gaba da kotu…. If there is any” Daga haka ya juya ya haura sama ya bar su wajen, Juyawa Sudais yyi yana wani murmushi yace “Alryt xa mu hadu a can din” daga haka ya nufi kofa yana kallon khaleel yace “Can we?” Mumy ta dakatar da shi da sauri, ya juyo yana kallonta, karasowa gabansa tayi tana goge hawayen idonta tace “I am really short of words, sai dai baxa ayi haka ba my son don Allah ku yi hakuri, xancen baxai kai kotu ba in sha Allah, sure islamically ba shi da right a kan yaran, ina mai tabbatar maku xai bata yaranta in sha Allah, and plss idan baxan bata maku lokaci ba ku bani just few out of ur time ina son mu yi magana da ku” Sudais bai ce komai ba, sai dai shi kansa yasan tun shigowarsa parlorn ya ga darajar matar shi yasa ma bai ma Aliyu haukan da yayi niyya ba, kuma albarkacin irin rikon da tayi ma khadijah truly she deserve some respect, sauke kansa yyi kawai ya koma ya xauna yace “To ina ji Ma” Mumy ta xauna ita ma tana ci gaba da share idonta ta bi parlon da kallo taga babu Anty khadijah, Baby ce kadai jingine da bango tana hawaye, a sanyaye Mumy ta fara cewa “Amma ya ku ke da Iman?” Khaleel ya kalli Sudais da ya kallo sa shi ma, ya ci gaba da operating wayarsa, Sudais ya d’an shafa beard dinsa yace “Yan uwanta ne mu” Mumy ta gyada kai, ta fara magana cikin sanyi tace “It’s not as if ina supporting Aliyu don d’a na ne, plss dont quote me wrong, amma ina son ku sani it’s a mistake he made kuma ba da gangan haka ya faru ba, tsautsayi ne ya gifta tsakaninsu, ni na haifesa na kuma san halinsa, ita kanta Iman xata shaide sa…. It’s not ordinary hakan ya faru da shi” Sudais yace “But kinsan bayan ya sa ta tafi da aka gano tana da ciki na maido ta nan gidan?” Kallonsa mumy take da d’an mamaki, can tace “Gidan nan?” Yace “Sure?” Jikinta yyi mugun sanyi tace “Wa ku ka samu gidan?” Sudais yace “Matar da muka fara samu a parlor xuwan mu yanxu, she humiliated us and sent us away then” Kasa cewa komai mumy tayi lkci daya hawaye ya kara cika idonta da kyar tace “Kana nufin khadijah ce ta Kore ku, kuma kun gaya mata abinda ke tafe da ku?” Sudais na gyada kai yace “Kwarai, I was even thinking she is his mum then, the way she reacted….” Mumy tace “Amma kun samu Aliyun?” Girgixa mata kai yyi yace “Ce mana tayi baya kasar gaba daya” Mumy ta fashe da kuka tace “Amma Allah ya isa tsakanina da khadijah, she just ruin my family, yar uwata ce amma ko bare baxai min haka ba, yanxu tana sane da abun nan amma bata gaya min ba, she never told me anything about it da babu abinda xai hana ni nemo Iman duk inda take, greatest mistake din Aliyu shine ce mata da yayi ta tafi, kuma wllh ni shaida ce tun daga ranan Aliyu bai sake samun kwanciyar hankali ba, kuma bai taba gaya min abinda ya faru ba sai dai yace in taya sa da addu’a, gashi nan dai har yanxu ya ki yin aure” Ko kadan khadijah bata damu da abinda mumy take fada ba ku ma bai shigeta ba, Briefly Sudais ya ba ma Mumy labarin yanda rayuwa ya kasance ma khadijah bayan Aliyu yace ta tafi… Ban da kuka babu abinda Mumy take duk jikinta yyi mugun sanyi tausayin Khadijah ya cika ta, ita dai tasan da tasan abinda ya faru kenan da ta sa Aliyu ya nemo ta Duk inda take amma yyi wautan rashin gaya mata, Mumy ta mike ta isa gun khadijah ta duka gabanta tana kuka tace “Khadijah ina neman alfarmar ki yafe ma Aliyu, ko don albarkaci na forgive him plss, kadararrku ce a haka, don haka ki ta godiya ma Allah, amma kiyi hakuri kar ki bar sa a xuciyar ki” Khadijah da xuciyarta ya mata rauni ita ma tana kukan tace “Mumy ni fa na yafe masa amma yayi hakuri ya bani yaran don Allah” mikewa Mumy tayi tace “Xai baki Khadijah, ina gidan ku yake yanxu?” Khadijah ta fada mata address din, Mumy tace “Toh kiyi hakuri ku je na maki alkawarin xa mu biyo ku da yaran yanxu” shiru khadijah tayi tana kallonta xuciyarta na bugawa sai take ga kamar kawai labari mumy take mata don ta tafi, baxa su bata yaran ba, Sudais ya mike yace “Toh shkkn, Ma… Muna xuba ido sai kun xo” Mumy ta kalli khaleel a sanyaye tace “Ku yi hakuri balarabe, Allah ya ba ku lada, amma don Allah ku bar jin haushin Aliyu ba yin kansa bane, nasan xa ku yi ta mamakin jin ina cewa ba yin kansa bane kamar na shiga xuciyarsa, but plss just do consider him” Murmushi khaleel yyi ya mike yace “Bakomai Ummu, Allah ya kara girma” tace “Amin nagode” daga haka ya nufi kofa, sudais ya kara mata sallama ya bi bayan khaleel, Khadijah na biye da su a baya tana goge idonta, ta kasa kallon baby dake bakin kofa har lkcn, A hankali baby tace “Iman plss forgive me brother, ki yafe masa don Allah” hawaye na sakkowa idonta take maganar, Khadijah tayi murmushin karfin hali tace “Na yafe masa” daga haka ta fita parlorn. Sama Mumy ta wuce xuwa dakin Anty Khadijah ta ganta xaune tana bude jikin iklima ganin wasu kuraje da ke feso mata ta ko ina, Mumy tace “Khadijah, a duk xaman mu dake in har na taba cutar ki Allah ya saka maki, in kuma ke kika cuce ni Allah ya saka mani, ki tattara kayan ki da na yar ki ki bar min gidana yanxu, Allah ya bani ladan xumuncin da nayi a baya, kuma in sha Allah nasan Allah baxai kama ni da laifin xumunci ba, ki je na bar ki da Allah” mikewa Anty khadijah tayi tace “Ni yau kike kora gidan ki yau Anty fati saboda wasu shegu sun xo sun shirga maki karya?” A fusace Mumy tace “Ki fita ki ban waje, yanda kika so ganina da jikoki wanda aka samu ba ta hanyar aure ba ke ma Allah ya ba ki” Anty khadijah ta tashi tana wani murmushi tace “Sai kinyi da kin sanin daga min yatsa da kika yi fatima” daga haka ta bude siff ta dinga fiddo kayanta da na Iklima tana huci, Mumy tace “Da na sani sai dai ki gansa a kwaryar ki” daga haka ta fice daga dakin ta shiga na Aliyu, Yana xaune gefen gado ya rike kansa, duk yan biyun sun yi bacci kan gado, Mumy na kallonsa tace “Kai da babban laifi kai da fadin bakakken maganganu ko Aliyu?” Kamar xai mata kuka yace “Mumy me yasa duk hallacin da na ma khadijah a baya baxata duba na, did I deserve this, wllh da hankalinta baxan cuce ta haka ba, sannan ta dinga wani hadani da wasu karti, ni ita na sani ba su ba su ba su daina involving kansu a abinda bai shafe su….” Katse sa mumy tayi tace “Don’t tell me nonsense, dole duk mai conscience idan ya ji labarinta ya so ya kwatar mata hakinta, kasan irin cutar da ka mata kuwa ka raba ta da kowa nata?” Aliyu ya rike kansa bai ce komai ba, Mumy tace “Sai ka tashi mu tafi can gidan nasu yanxu” Aliyu ya dago ya kalleta da kyar don wani Sara masa kansa ke masa yace “Mumy wllh ni baxan iya rabuwa da Iman ba, baxan iya rayuwa ba ita ba, my life has being miserable tun da na sa ta bar gidan nan, Don Allah ki rokar min ita ta amince mu yi aure, I don’t think xan iya auren wata ya mace a duniya idan ba ita ba, plsss even for the sake of this innocent children ta amince mu yi aure” Mumy tace “yanxu kuma??” Tashi yyi Yace “Wllh Mumy idan tace baxata aure ni ba, I promise to go away with this kids baxa ta sake ganinsu ba har karshen rayuwarta, ai da can ba da su take rayuwa ba” Mumy na masa wani kallo tace “Na ga alamar ka fara xarewa, da yaran xaka mata baraxanar ta aure ka kenan, a hakan xata amince ta aure kake tunani, kasan ko kotu aka je yaran nan ba naka bane Aliyu, ba ta hanyar aure ku ka same su ba don haka ka janye wannan baxan maganar da kake yi, kuma kar ka bata min rai” Wani murmushi yyi bai dai ce komai ba, Jikin mumy yyi sanyi ta bi sa da kallo, tsoronta kar ya tafi da su kamar yanda yace, da kyar tace “Ka tashi mu je gidan na su, nasan even for my sake ma xata amince maka” daga haka ta fita dakin. Sai kusan magrib suka isa address da khadijah ta ba mumy, Aliyu ke driving din, Sai baby a gaba, mumy kuma na xaune back seat da yan biyun, tana rungume da little Sudais da jikinsa yyi xafi sosai duk da allurorin da Aliyu yyi masa, kai kana ganin yaran kasan hankalinsu ya kwanta da mumy, Shureim na kallonta yace “Are we going to visit you again mama?” Tana murmushi ta shafa kansa tace “Sure sweetheart” parking Aliyu yyi kusa da gidan ya juya yana kallon Mumy, Mumy tace “Ina jin nan ne” Shureim yace “Ehh mama nan ne gidanmu” Mumy tace “baby sauka ki kwankwasa gate din” Baby ta sauka tayi yanda Mumy tace, Mumy ta sauko tare da boys din, Aliyu ya fito shi ma ya dau sudais, bayan wani lkci Nanny ta bude gate din, da gudu Shureim ya tafi ya rungumeta, Nanny ta ji dadin ganin su sosai ta dinga yi ma su Mumy sannu da xuwa, Kallo daya tayi ma Aliyu ta gane shi ne uban yan biyun, ta yi masu iso har parlor, Sannan ta shiga daki don Umma na ciki tana sallah, Khadijah ma tasan sallan take yi, Umma ta sa Hijab ta fito bayan Nanny ta sanar mata bakin da suka yi, Har lkcn Sudais na jikin Aliyu, Shureim dake jikin Mumy ya tafi da gudu ya rungume Umma yace “I miss you Mumy na” Umma ta xauna tana murmushi ta ja sa jiki sannan suka shiga gaisawa da su Mumy, jikin mumy yyi sanyi sosai don bata taba xaton xata tarbesu da kyau haka ba, shi dai Aliyu ya kasa daga kai ya kalleta, shi ma bai yi xaton haka ba, Khadijah dake xaune kan darduma lkci daya taji ranta yyi mugun bacci jin yanda Umma ta sake masu, jin muryar yaranta yasa ta lumshe idonta, amma ta ki fitowa parlor ta same su don bata ma son ganin Aliyu, Mumy na kallon Umma tace “Ina Khadijar Hajiya?” Umma ta kalli Nanny dake tsaye tace “kira Khadijah” sosai Khadijah ta dake xuciyarta ta mike ta bi bayan Nanny kan ta a kasa, har ta shigo parlorn bata yarda ta dago kanta ba ta gaida Mumy, Aliyu sai kallonta yake ko kiftawa babu, Shureim ya nufeta ya xauna jikinta yace “Anty mun dawo, I like the house so much…” Khadijah ta ki kallon yaron amma har ranta bata ji dadin abinda yace ba, ita fa in dan ta ita ne yaranta basu da uba, ita dai tasan Allah ne ya bata su, kuma tana gode masa, fuskarta daure ta dago tana satan kallon Aliyu dake ta kallonta suka hada ido ta masa wani harara ta dauke kai, lkci daya ta mike ta ja hannun Shureim suka bar parlorn, tana xaunawa kan gado ta jawo yaron gabanta tana kallonsa da kyau tace “Did that stranger tell you anything?” Shiru yyi da farko kafin yace “But he is not a stranger Anty, this is the 4th time we are meeting with him” ta xaro ido xuciyarta na bugawa tace “Where and where” yace “Anty ranan nan da muka kusa yin accident, that i told you he made sure we where fine….” Gabanta yayi mugun faduwa tace “And where?” Yace “We met again at the airport da xa mu je holiday a UK, shi ma xai je can…” Ta runtse ido xuciyarta na tafarfasa tace “And where????” Yace “Yesterday at the market, because sudais don’t like him shine ya gudu ya shiga titi babban mota ya buge sa” ta fixgo yaron tana huci tace “Shi ya janyo mota ya buge Sudais?” Kai ya gyada mata ta jefa masa wani kallo tace “And you are telling me he is kind yana neman kashe maka brother, daga yau ka sake yarda ko kallon ka yayi sai ya xuke maka jinin jikin ka gaba daya, baka san shi vampire bane” buda baki yyi yana kallonta da surprise, can yace “Me yasa bai shanye mana ba a gidansu?? Anty he is kind fa, ni dai I like him, he was with us…..” Tsawa tayi masa ta turasa har sai da ya kusa faduwa hawaye cike idonta tace “Xan fasa maka kai… Nace stay away from him, you have no business with that wicked man” Shiru yyi a tsorace yana kallonta, a hankali yace “But he even told us he is our father not barrister as you told us….” Mikewa tayi hankali tashe xuciyarta na mugun bugawa tace “He is a liar… Karya yake maka barrister ne babanka, ba abinda ya hada mu da shi” cikin rawar murya tace “Tafi ka kamo hannun sudais ku xo nan yanxun nan” da sauri ya fita, yana isa kusa da Aliyu yace “Uncle, Anty tace I shud call my brother now” shiru yyi yana kallon yaran, haka ma Mumy da Umma, Aliyu yayi kasa da kai a hankali yace “Umma ki d’an mata magana ta bari in je da shi, he is sick dole xa mu koma asibiti” a fusace Khadijah dake jin sa ta fito tace “Ina ruwanka da rashin lafiyarsa? Ka bani yarona ai nasan hanyar asibiti, give me my son” tsawa Umma tayi mata ta mike tace “Tafi ki bar parlorn nan kar in bata maki rai, shashasha” ta fashe da kuka ta juya da sauri ta bar wajen, Umma dake kallonsa a sanyaye tace “Ka je da shi, Amma ko xuwa gobe sai ka kawo shi” a sanyaye yace “Na gode Umma” su mumy basu bar gidan ba sai kusan karfe taran dare bayan mumy ta mata bayanin duk abinda ya faru, Umma ta raka su har bakin mota jikinta a sanyaye.