Author: Novels

  • Kanwar Maza 7

    Kanwar Maza 7

    P7

    Dafe goshi Yasir ya yi yana murzawa a hankali, ruma ‘yar bala’i ce, ba zata tashi yi maka hansfree ba a cikin jama’a sai kowa ya hallara kamar mai sanar da wani abu mai muhimmanci, in da ya gode wa Allah da ya kasance, a makaranta ta ji ana koya musu, da bai san da wasu kalaman zai amfani wurin kare kansa ba.
    Ita kuwa ta zaƙalƙale tana ta jawabi, babu wanda ya tanka mata, karo da idanun Umar ne ya sanya mata aya a jawaban da take kwarowa babu ƙaƙƙautawa.
    “Zo nan” yayi maganar cikin bada umarni.

    Kamar mara gaskiya haka ta tashi ta je gabansa ta durƙusa.
    “Je ki ɗauko mini jakarki ta makarantar boko da ta islamiyya”

    “Dummm ta ji gabanta ya faɗi, har gara jakar islamiyyar ta ma, tun da ba a daɗe da sakata ba litattafan da mutuncinsu, amma ta makarantar boko dai kam sai dai Allah ya kyauta.
    Jiki babu ƙwari ta je ta kwaso jakunkunan, ta zo gabansa ta ajiye su.
    Ya kalli jakarta ta makarantar boko, duk ta ci ubanta da jagwalgwalon biro, har da zanen ‘yan aljanu a jiki da su ABCD a jikin jakar, sunan ‘yan gidan nan kuwa babu wanda ba ta rubuta a jiki bs. Tun daga nan ya san cikin jakar ma ba za ayi abin arziki ba.
    “Oyaa zazzage litattafan na gani”

    Babu musu ta janyo jakar ta zazzage, Innalillahi wa Innalillahi raji’un, litattafan nan sun ga duniya, tamkar ɓera ya ci rage mata. Kaf litattafan babu bango a jikinsu, sun yi kaca-kaca, wasu ma nannaɗe su tayi, wasu ta ninka su biyu, a taƙaice kai ka ce bolar wani office ɗin ce. Sai uban fensura sun kai biyar a cikin jakar, ga su ulu da farar ƙasa da sauran goriba duk a ciki.
    Umar ya kalli ruma, ya kalli bolar dake gabansa, dan ba zai ce litattafai ba.
    “Yanzu wannan sharar ce litattafan karatun naki?” Tayi shiru ta sunkuyar da kai.
    Ya sanya hannu ya ɗau littafi ɗaya yana dubawa, ba uwar da take yi a ciki, littafi ɗaya sai ta yi duk subject ɗin da ta ga dama a ciki.
    A hankali ya cigaba da duba litattafan nata, ga class work da tarin assignment, wasu tayi ta ci zero wasu makin da take ci ma gwanin ban haushi, subject ɗaya ya ga ta mayar da hankali tana yi yadda yakamata, kuma ba ta faɗuwa shine maths.

    Yayi ajiyar zuciya ya ɗaga kai ya kalleta ya ce “Ashe asarar kuɗin tara kawai ake a banza ko? A biya miki kuɗin makaranta idan zaki tafi sai an baki abin tafiya makaranta, amma ki je kina wannan jakancin, kalli wai wannan ne litattafan ki na karatu, kalli wannan wai 4\20 ki ka ci, ba zaki iya kawo abin da baki iya ba gida a koya miki, wasa da surutun banza faɗi ba a tambaye ki ba shi ki ka saka a gaba ko?”
    Ta girgiza masa kai alamar a’a.
    “Ƙarya na yi miki kenan? To bari ki ji na gaya miki, ina nan zan zuba ido a kan result ɗin da zaki kawo wannan karon, wallahi idan bai yi mini ba sai an miki repeating ”
    Ras! Gaban ruma ya faɗi “Na shiga uku, dan Allah ka yi haƙuri, zan daina surutun in dinga karatu”.

    “Kar ma ki yi, wallahi primary 1 zan saka a mayar da ke, ki cigaba da daƙiƙanci, kuma ina samun information a kan abin da ki ke a islamiyya, ke kin zama jan wuya zaman ajinku ma ba kya yi, ke kin sakawa kan ki ba zaki iya karatu ba ko? Oya buɗe Alqur’ani nuna mini a surar da ku ke”
    Ai nan ma badan-badan tayi ta yi, domin kuwa ba ta san a ina suke ɗin ba.
    Carbi ya bata, ya biya mata aya biyu, ya ce tayi ta maimaitawa sai tayi ƙafa dubu.
    Da haka yaya umar ya ƙwaci yasir, ta zauna ta dinga nanata karatu har barci ya fara ɗaukar ta, da ta fara bacci yake zuba mata carbi a ƙafa, ta tashi a gigice ta cigaba da karatun, da haka sai da ta haddace rabin shafi, bai ƙyaleta ta kwanta ba sai wurin ƙarfe ɗaya na dare, da kuka haka ta kai karatun nan, ya sa ta kwashe bolar litattafan ta ya sallame ta.

    Washegari, har makarantar boko, yaya umar ya je ya iske ta, ya kai mata sababbin litattafai, ya sanya aka kirawo ta ofishin shugaban makaranta, nan ma ba abin da suke yi, sai wassafawa yaya Umar halin ta na rashin ji.
    Ya bata litattafan, yayi mata kashedi tare da jadadda mata, idan har ta cigaba da daƙiƙanci, sai ya sa an yi mata repeating.

    *********
    Zaune take a kan makeken gadonta, ɗakin cike da kayan alatu kai da gani ka sam mai ɗakin ‘yar gata ce.
    Ta dunƙule wuri guda a kan gadon, idanunta sun yi jawurr alamar ta sha kuka.
    Daga ita sai doguwar riga ‘yar kanti, kanta babu ɗan kwali, kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin matsananciyar damuwa.
    Turo ƙofar ɗakin aka yi, wata babbar mace ce ta shigo ɗakin, idonta sanye da farin gilashi, hannunta riƙe da tray da cup.
    Cikin tausayawa ta kalli yarinyar, ta ɗan girgiza kai, ta ƙarasa ta ajiye trayn, ta rungumota tana faɗin “Haba Iman ɗina, shikenan rayuwa bawa ba zai jurewa ƙaddara ba? So ki ke ciwona nima ya tashi?”
    Iman ta girgiza kai, hawaye na cika idanunta.
    “To Meyasa zaki takura kan ki, haka Allah ya so dama, ai dama tun farko biyayya ce zaki yi mini, kuma Allah bai yi yiwuwar abun ba, amma ki yi haƙuri kin ji babyna”
    Ta jinjina kai lokacin da take sake kwantar da kanta a jikin matar.

    Ta ɗakko tea a kofa tana bawa Iman a baki, tana sha tana share hawaye, kai da gani ka san akwai tsantsar soyayya da ƙauna a tsakanin su. Ta gama bata tea a baki, ta dinga shafa gashin ta, tana yi mata nasiha.

    **********
    Mama ta mayar da hankali sosai a kan ibada, mutane na ta shirin zuwan watan ramadan, mama tana ta azumi ita da su yayyen ruma, amma ban da hajiya ruma da cin abincinta ne kawai ya dameta.
    Yanzu haka ta cinye taliya, ba ta ƙoshi ba, ta kwaɗa garin kwaki ta zauna tana ci.
    Yasir sai masifa yake mata, wai shegen ci ne da ita kamar akuyar ƙauye, ko saurarensa ba ta yi ba ta cigaba da tura abincinta.
    Mama ta kalleta ta ce “Wai ke ruma, ko zuciya ba zaki yi ba, azumin nan da kowa yake yi na neman lada ko guda ɗaya ki gwada ba?”

    Ɗan ɓata fuska tayi ta ce “Mama ni sai Allah ya kaimu watan ramadan, idan na fara azumi tun yanzu, ai ramewa zan yi kan salla”

    “Ke ta ramewa ki ke, dan ubanki ina nuna miki ibada amma ke ba kya so”
    Shiru ta yiwa mama tana cigaba da danƙarar garin kwakinta, dan ba ta ji za ta iya wannan azumin ba, idan na du gari ya zo dai ta jarraba.

    Bisa ga jajircewar yaya Umar, aka samu ruma take ɗan taɓuka abin arziki a makarantar islamiyya, shima ba wani sosai ba, dan sam ba ta bayar da hadda, tana iya ƙoƙarin ta ko ba duka ba, ta ɗan iya karatun da aka biya musu, saboda idan yaya umar ya titsiyeya ta ɗan samu abin karanta masa dan ya bari ta yi barci, idan kuwa ba baka ba ta san sauran.

    Yau ana can ana sallar la’asar, ruma tana zaune tana shan mangwaron ta, tuni ta yi sallarta a cewarta ba za ta iya bin jam’in nan ba, tun tana tsayuwa sai jiri ya fara kwasarta ba za ayi a idar ba.
    Ta gama shan mangwaronta, ta tafi wurin alwala wanke hannu.
    A wurin alwalar akwai yaran da suma ba sa sallar, suke ta wasan su.
    Babu tsammani, ruma ta ji an zuba mata bulala. Tamkar wadda ta fita hayyacinta, haka ta tashi a gigice, tana duba wanda yayi mata wannan ɗanyen aiki haka.
    Wani prefect ta hango, bayan ya zuba mata bulalar ya tafi kora sauran yaran da bulala.
    Cikin kiɗimewa, ta ɗauki ƙatuwar buta guda ɗaya, ta bishi a guje tana ihu, ta dinga watsa masa ruwan. Ya waiwayo ya tsaya yana kallonta, ta ga hakan bai mata ba ta dinga ƙwala masa butar, daga ƙarshe ta durƙusa ta ɗibi ƙasa tana watsa masa tana kuka.

    Tamkar soko, haka ya tsaya yana kallonta, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ya kasa, balle ya kare kansa.
    An idar da salla kenan, hankali ya fara dawowa kan in da kukan rumaisa ke tashi, bayan ta gama ɓata masa jiki da ruwa da ƙasa a gogaggen uniform ɗin sa, ta haɗa hannayenta biyu tana yakushinsa gami da kai masa duka.

    Da ƙyar wani malami ya ɓanɓareta daga jikin matashin yaron, wanda ba dan ya girmeta ba, kuma babu dutse to babu abin da zai hana ta fasa masa kai da dutse, dan ba ta ga laifin da ta aikata zai zuba mata wannan bulalar ba.
    Malamin ya dubi ruma ya ce “Meyasa ki ka yi masa haka? Meye haka ki ka yi?”

    Cikin kuka ta ce “Dukana ya yi babu abin da na yi masa, wanke hannuna kawai nake yi shine ya dake ni, kuma wallahi ban yafe ba”. Har ta gama maganar kuka take yi, jikinta yana rawa.
    Yayin da hankalin ɗaliban duk ya dawo kan su ruma, da jikin Auwal da ruma ta duƙunƙuna masa kamar ya faɗa taɓo.

    Haƙuri malamin ya bashi, ya ce ya je ya wanke jikinsa.
    Kuka ne kawai auwal bai yi ba, amma ya ji zafin abin da ruma ta yi masa ba kaɗan ba.
    Auwal ɗan ajin su Yasir ne, ya san ƙanwar yasir ce, sai dai sam bai taɓa shiga sabgar ruma ba, kuma shi bai ma san ita ce a durƙushe a wurin ba, yayi mamakin ƙarfin hali da kuma tsaurin ido irin na ruma.

    Ko da labarin abin da ruma ta aikata ya kai kunnen yasir, haƙuri yayi ta bashi, auwal ya nuna ba komai, amma a cikin ransa yana jin ba zai iya ƙyale ruma ba sai ya ɗau mataki a kanta.

    Babu yadda Yasir bai yi da ita a kan ta ba wa auwal haƙuri, amma mursisi ta ce sai dai ya mutu idan har sai ta bashi haƙuri.
    Tun da ruma ta yiwa auwal wannan haukan, sauran prefect ɗin ma tsoron taɓata suke yi, dan sun fi yadda da aljanu ne da ita, saboda tsaurin idonta yayi yawa sosai.

    *********
    Gaba ɗaya ruma ba ta wani ɗokin zuwan salla, saboda ta san ba ta da kayan salla, mama da gaske ba zata ƙara mata komai na kayan salla ba, ko kayan ado da ake saya mama taƙi sai mata, a cewar mama wannan shine hukuncinta na ƙin jin magana. Ta ji haushi sosai amma ta danne ta cigaba da zuba ido, dan kuwa sallar akwai sauran lokaci.
    Yau ta shigo gida daga makarantar boko, da wata takarda a hannunta sai yashe baki take yi.

    “Deluwa, murmushin me ki ke yi ne haka, takardar meye a hannunki?”

    Kallon banza ta yiwa Huzaifa ta ce “Na gaya maka bana son sunan amma ka ƙi daina gaya mini, sai na maka rashin kunya ace bana ji”

    Huzaifa ya ce “Yi mini rashin kunyar, ki gani idan ba ɓarar da ke ba”.

    “Hmm haƙuri halin abin ƙaunar mu Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, shi ya sa ba zan kula ka ba” girgiza kai yayi yana murmushi, ta cire takalmanta ta shiga ɗakin mama.

    Mama ce da Abdallah a zaune a falonta suna hira, yana guga.

    Mama ta dubi ruma ta ce “Murmushin me ki ke yi ne?”

    Ruma ta ɗagowa mama takarda ta ce “Presentation zan yi a makarantar mu, kowa aka bashi, ni ba a bani ba, na dinga kuka da ƙarfi nace idan ba a bani ba, na daina zuwa makarantar, shi ne fa Headmaster ya ce nima sai an bani, spelling b ne zamu haddace words ɗin nan ɗari biyu da hamsin, zamu yi mu da ‘yan wata makaranta”

    “Ai fa kai ba hankali, wai ki ka dinga kuka da ƙarfi ko kunya ba ki ji ba” Abdallah ya faɗa a hasale.

    “To ai da ban yi hakan ba, ba zasu bani ba” tayi maganar cikin taɓara.

    Mama ta ce “amma dai ba su san ta nawa ki ke zuwa ba ko da suka baki?”

    Ruma ta tsuke fuska ta ce “Wato mama ke ma dai daƙiƙiyar zaki ce mini ko?”

    Abdallah ya ce “To mecece idan ba daƙiƙiyar ba” gaba ɗaya haushi ya kamata, ba ta kuma kulasu ba ta shiga sabgoginta. Duk wanda ya shigo ta ce masa an bata spelling b sai su ce ai ba ci za ta yi ba, kada makarantar za ta yi.
    Babu wanda ya bata ƙwarin gwiwa, ga yaya Abubakar ya koma makaranta, dama dai yana nan ne shine zai biye mata.

    Zaune yake a cikin chemist ɗin, yana jiran mai chemist ya sallame shi, kamar daga sama ta shigo chemist ɗin ta ce “Gashi ka bawa mama maganin ciwon kai” na zai manta wannan muryar ba, ko a mafarki ya ji ta, yana ɗaga kai suka haɗa ido.
    Murmushi ta yi masa ta ce “Yaya auwal ina wuni” juyawa ya yi ko da wani take ba da shi ba.

    “Baka da lafiya ne?” Tayi maganar tana kallon allurar da mai chemist ɗin yake zuƙewa.

    A hankali ya ce “lafiya lau, ya su yasir?”

    “Suna nan lafiya, ya jiki?”
    Da sauƙi ya bata amsa, yana tuna yadda ta damalmala masa kaya a islamiyya, da yadda yayanta ya rutsata ta bashi haƙuri amma ta ce sai dai ya mutu, ba zata bayar ba, idan suka haɗu a makaranta, sai ta tsaya ta harare shi, har da murguɗa baki, amma wai yau take gaishe shi, har da su yaya bayan ko yayan nata yasir ba ta ce masa yaya.

    “Deluwa wannan hamsin ɗin taki za ta karɓuwa kuwa?” Cewar mai chemist.

    “Awaisu mai chemist, duk ranar da na tashi jajjaga maka rashin mutunci, a kan kirana da deluwa, sai ka yi kuka” ta faɗa very serious.

    Dariya ya yi ya ce “Ke, ai ko ban kai sa’an ‘yan biyun gidanku ba, na san na girmi Aliyu, amma ni zaki saka kuka?”

    “To shikenan, ka cigaba zaka gani, bani maganina na tafi”

    Bayan ya bata maganin ta kalli auwal ta ce “Yaya auwal, Allah ya ƙara lafiya” tana gama maganar ya fita tana tsalle kamar kwaɗuwa.
    Tun da ga ranar da suka haɗu da auwal a chemist, kullum ta ganshi a makaranta sai ta gaishe shi, duk da baya sakar mata fuska idan zai amsa, amma bai sanya ta daina ba.

    ****
    Ɗaya ga watan ramadan, bayan gari ya ɗauka an ga wata, mutane na ta shirin ɗaukar azumi, da asuba mama ta tashi kowa sahur, amma da ƙyar ruma ta tashi ta yi sahur, saboda nauyin bacci.
    Ranar ɗaya ga azumin ya kama asabar ce, ruma ta ce gaskiya ba zata iya zuwa islamiyya ba, tun ƙarfe goma take jin kamar zata mutu.
    Wajen ƙarfe sha biyu na rana, ta dinga yiwa mama kuka tana burgima wai hanjinta na gutsutstsurewa ita fa mutuwa zata yi.

    Aliyu ya ce ‘mama dan Allah ki ƙyake yarinyar nan, tun da ba zata yi ba ta je ta ƙarata”.

    “Aikuwa sai ta yi, idan ya wajaba a kan ta wa zai mata?”

    “Mama ki bari ua wajaban sai ta yi, kalli fa kamar zata rasu”

    Mama ta ce ruma ba zata karya azumi ba, mama tana can tana salla, ya kandamowa ruma ruwa ta sha ta karya azumi.
    Sai da mama tayi kamar ta zane Aliyu dan takaici, a ganinta sangartar ruma ta yi yawa.

    Abu kamar wasa, ruma taƙi yin azumi, idan ma ta ɗauka ta ji wuya, sai ta karya abin ta, idan aka sha ruwa kuwa tafi uban kowa zaƙewa, daƙyar ska samu ta yi shida, shima Usman ya ce bai yarda da ingancinsu ba. idan aka ce ta je sallar asham kuwa sai ta ce ita wallahi gajiya taje yi da tsaiwa, ƙafafuwanta sai sun fara suɗewa ake ruku’u, nan ma sai bayanta ya kusa karyewa ake ɗagowa ba zata iya ba. mama kuwa ta gaji ta kamata ta zaneta da mafici.

    Idan kuwa aka matsa ta je sallar asham, wataran a can cikin yara ake tsintowa mama ruma tana tsalle -tsalle ko dambe a maimakon salla, tilas mama ta hanata zuwa take titsiyeta su yi a gida.

    Sai da salla ta gabato, ruma ta sake da tabattar da mama ba zata yi mata wani ɗinkin ba, ta dinga yi wa mama magiya, a kan ta yi mata wasu kayan, amma mama ta ce ba zata yi ba, lokaci ne da zata rama rashin jin da ruman take yi mata.
    Gaba daya ɗokin sallar ya fita daga kanta, saboda ba ta son kayan da aka sai mata, gashi sallar bana ko arzikin takalmi da jaka bata samu ba, dan haka ta ce ba zata yi ko kitson salla ba.

    Mama ta bata kuɗi ta ce taje ayi mata lalle, dan ba zata yi salla haka ba.
    Ruma ta tafi ƙunshi tun safe, sai bayan la’asar ta dawo.
    Mama ta kalli lallen nan babu kyan gani, kamar ana saka shi aka ɗauraye.

    Kafin mama tayi magana mai lallai ta kira mama, suka gaisa.
    Mai lalle ta ce “Mama, wallahi kar ki ga lallen ruma bai yi kyau ba, ana saka mata wai sai an cire ba ta so ta gaji, da na ƙi cire mata, ta cire abinta wai kashi take ji”

    Mama ta ce “To shikenan, kar ki damu na gode sosai” ta kalli in da ruma ta tsaya ta ci magani kawai ta jinjina kai ba ta ce mata komai ba.

    Tun magariba, ruma taga mama ta kwaɓa lalle kaya guda, ba ta kawo komai a ranta ba, ta cigaba da harkokinta.

    Sunanta da mama take kirane, ya sanya ta san asuba ta yi, ta yinƙura zata tashi, ta ji motsin leda a ƙafarta, ta tashi zaune amma ta ga hannunta da ƙafarta duk leda.

    “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, mama me ya sameni?”

    “A ina?”

    “Wannan ledar mecece?”

    Mama ta ce “Ahh, ruma ai ba ke kaɗai ki ka san ta kan tsiya ba, na sai miki kaya ba godiya ki ka raina, na biya kuɗi ayi miki lalle ki ka ƙi zama, ai da ni ki ke zancen, kina wannan shegen baccin na yi miki dungulmi da shi zaki yi sallar, tsohuwa ta faɗa kwata ba, irin wanda nake yi, kuma kitso ma gidan Hanne zan saka Huzaifa ya kai ki, tayi miki zane huɗu ba dai ba kya ji ba, ai daidai nake da ke, ina sane nake kawar miki da kai”.

    Ruma ta kalli yadda aka ƙunshe mata ƙafa har ƙwauri, ga hannayenta kuma ana batun ayi mata zanen Hausa guda huɗu a ka tayi salla, ta tuna uwar rigar da zata saka a matsayin kayan ssllarta, ta ɗora hannu a ka ta zunduma ihu.

    DAN ALLAH MASU NEMA DAGA FARKO KU DINGA TAMBAYA A GROUP KO DUBA WATPAD KO AREWABOOKS NA GODE

    AYSHERCOOL
    08081012143
    [03/07, 2:14 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
    Na Aisha Adam (Ayshercool)

    MIKIYA WRITER’S ASSOCIATES

    https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

    Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
    @Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.
    Ku yi following ɗina a arewabooks a kan account ɗina na ayshercool7724
    Ko watpad Ayshercool7724 kowanne a cikin manhajojin za ku iya samun litattaiafaina da na yi a baya, da wanda nake yi a yanzu na gode

    *Ina miƙa saƙon godiya, ga waɗanda suka yi mana ta’aziyya na rashin uba da ‘yar uwa Naima Suleiman (Nimcyluv) ta yi, muna fatan Ubangiji Allah ya jiƙansa da rahama.*

    *TAƘABBALALLAHU MINNA WA MINKUM, INA TAYA AL’UMMAR MUSULMI BARKA DA BABBAR SALLA, UBANGIJI ALLAH YA KARƁI IBADUNMU YA MAIMAITA MANA*

     

  • Noor Al Hayat 73

    Noor Al Hayat 73

    Aliyu ya mike xaune yana kallonta yace “Did you come to check on me?” Ta tsuke fuska tace “Saboda kai Shureim ne?” Ya shafa kansa bai ce komai ba, ta juya da sauri ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice, sai a sannan ta ja tsaki taji haushin shiga dakin da tayi, parlor ta koma ta dau shayin da ta hada, da kyar take sha don gaba daya bakinta ba dadi, ji tayi kamar xata yi xaxxabi, ta mike ta dau sauran kayan kumallon ta kai dining ta ajiye ta wuce kitchen don wanke cup din shayin ganin baxata ta iya sha ba, xata ajiye bayan ta wanke taji kamar mutum bayanta ta juya da sauri suka kusa cin karo suna hada ido ta hade rai ta dauke kai, ya mika mata hannu a hankali yace “Bani cup din” tace “Saboda xaka amsa cup sai ka tsaya bayana toh” Bata jira me xai ce ba ta ajiye cup din ta fita kitchen din ya bi ta da ido. Har aka yi azahar bata kara fitowa daga dakinta ba, xuwa lkcn ta fara jin yunwa sosai amma ta kasa sakkowa, duk xaman dakin ya isheta, tana ta xuba ido taga kiran Umma amma shiru, ga kewar Shureim da ya cikata, duk abubuwan suka taru suka mata yawa, ta hade kai da pillow tana son yin kuka amma ta kasa. Aliyu na xaune parlor yana duba wasu articles bayan sun yi waya da Sudais yace masa suna hanya, saboda su ma ya dawo parlorn ya xauna, ajiye takardar hannunsa yyi ya dau pain reliever a center table for the second time in 2hrs ya balla biyu ya dau table water dake ajiye ya sha maganin ya mayar da ruwan ya ajiye ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, ya rasa me yasa bai samu relieve ba bayan wanda ya sha daxu, har ya fara bacci a haka ya ji an danna bell, ya bude ido ya mike ya isa kofar ya bude, Baby ce rike da lunch, ganinsa tayi murmushi tace “Yayanmu Ina yini?” Ya shafa kai a hankali yace “Lafiya lau” da damuwa tace “Are you sick?” Ya d’an bude ido yace “Me kika gani?” Tace “You look so” murmushi yayi yace “Am alright” Bata ce komai ba ta shigo parlorn cike da tausayinsa ta ajiye abincin hannunta ta juyo tana kallonsa tace “Ka ma yi breakfast kuwa yaya?” Yace “Nayi mana, ya su Mumy” Xaunawa tayi tace “Suna gaishe ku” ya xauna shi ma yace “Ki kai mata abincin sama” xaro ido baby tayi tace “Uhn ba ruwana, I don’t want to imagine me going to her now” Aliyu bai ce komai, tana kallonsa a hankali tace “You just have to be patient ya Aliyu, soon nasan xata hakura… Kar ka damu kaji yayana, I know it’s just for few days” Murmushi yayi yace “Toh Allah ya sa” cike da tausayin sa tace “Ameen” yace “Plss ki taho da Shureim idan xa ki xo anjima….” Tace “Ae yana can gidansu” yace “Ehh ki dauko sa can din, I am lonely…” Tace “Toh Yaya xan kawo sa” Wayarsa ne yayi ring ya dauka yaga Sudais ke kiransa, yyi pick din call din Sudais yace “Muna waje” Aliyu yace “Alryt ku shigo” Baby na kallonsa bayan ya katse wayar tace “waye yaya?” Yace “Barrister with Dr Ayman I guess” Baby tayi shiru bata ce komai ba, bude kofar parlorn aka yi khaleel ya fara shigowa kafin Sudais, Aliyu ya mike bayan sun gaisa gaba daya suka xauna, Baby na kallon Dr Ayman tace “Ina yini” yace “Lafiya lau ya kike?” Tace “Alhmdllh” kallon Barrister tayi dai dai lkcn da ya kallota shi ma, yace “Ina yini” xaro ido tayi sai kuma tayi dariya tace “Ina yini” yace “Ohk I was thinking baxa ma ki gaisheni ba” Khaleel yayi murmushi yana kallonsa ta gefen ido bai dai ce komai ba, Aliyu ya kalli baby don tsoron xuwa daki gun khadijah yake yace “Baby talk to her tana daki” Mikewa baby tayi ba don tayi niyya ba ta wuce dakin gabanta na faduwa, Khadijah dake kwance ta daga kai jin an bude kofa, ganin baby ce ta mike xaune tana kallonta, a sanyaye tace “Shine daxu baki min magana ba kika wuce ko Baby” Baby tace “Hmm tsoron ki nake ai ni Iman” Baby ta xauna kusa da ita, khadijah ta kamo hannunta a hankali tace “Amma baby kin san wanda aka aura min kika boye min, idan kowa ya boye min ke bai kamata ki min haka ba, Ni yanxu shkkn cikin kunci xan kare rayuwata, nobody is after my happiness….” Hawaye cike idonta ta kare maganar, a sanyaye Baby tace “Nan gaba xa ki gane ma’anar hakan da aka yi Iman, just give my brother a chance… Iman ki manta abinda ya faru a baya, ki kwantar da hankalin ki da Yaya Aliyu you won’t regret it am giving you my words….” khadijah ta dinga share hawayen dake sakko mata bata ce komai ba, tasan ita dai baxata taba kwantar da hankalin ta da wanda yyi disfiguring dinta heartlessly ba, cikin kwantar da murya Baby “Kiyi hakuri Iman, nima wllh ban san da yayanmu aka daura auren ba sai da muka tashi barin gida jiya da yamma kin dai ji na rantse maki” Har sannan khadijah bata iya ta ce komai ba sai goge idonta take, Baby tace “Ki sakko ki xo gu gaisa da su Barrister suna parlor” Kallonta khadijah tayi da sauri ta tsuke fuska tana girgixa kai tace “Am not going anywhere, they are nothing but group of deceivers…” duk yanda baby ta dinga lallabata Khadijah kin yarda ta fito tayi har da kukan ta, baby ta rasa yanda xata yi, mikewa tayi daga karshe ta dawo parlor, Aliyu na ganinta yasan kwanan xancen, Baby ta kirkiri murmushi tace “Tana fa bacci ne, Kuma bana son tada ta….” Murmushi Sudais yyi yana shafa beard dinsa a hankali yace “That’s nyc, thanks for covering up for her, but we are not strangers, kuma baxa mu ji haushi ba idan kin ce tace baxata fito ba, wataran xata fito mu ganta ai” Dariya khaleel yyi yana kallon baby da ta rikice sai rawar baki take, Aliyu yyi murmushi bai dai ce komai ba, Sudais na kallonta duk da dariyar da ta basa shi ma yace “Sorry, just relax Mami ni ban yi haka don ki rikice ba” Baby bata san lkcn da ta balla masa harara ba ta juya da sauri xata wuce tana murmushi, Aliyu yace “Kawo masu drink” kitchen ta wuce ta dauko masu drink din ta ajiye, Aliyu yace “Abinci fa?” Sudais yace “Nop Alhmdllh” mikewa baby tayi ta dau abincin ta wuce sama, Dakin khadijah ta shiga tana harararta ta ajiye abincin hannunta tace “thanks for making me look stupid downstairs, Kuma abincin ma na daina kawowa sai dai ku fita eatry da mijin naki” daga haka ta wuce, tana shiga parlor tace “Yaya ni xan koma, Mumy tace kar in dade” Yace “Alryt then, da driver ku ka xo?” Ta girgixa kai yace “Toh je sama ki dau transport” Khaleel yace “Xa mu wuce yanxu sai Barrister yyi dropping dinta tunda hanyar daya” Har bakin mota Aliyu ya raka su bayan sun wuce ya dawo cikin gidan, sama ya wuce ya bude dakinsa ya shiga ya kwanta. Har aka yi la’asar khadijah na daki, duk da ta ji gidan shiru ta kasa fitowa ta dau plate ta debi abinci, Tana tunanin yanda xata fita aka bude kofar dakin Aliyu ya shigo, sau daya ya kalleta ya mayar da dubansa kan abincin da Baby ta ajiye dakin, ya isa gun abincin yace “Ain’t you eating the food?” Banxa tayi masa, ya duka ya bude warmer din yana kallon abincin, dauka yayi ya juya ya nufi kofa ta bi sa da wani kallo, ganin ya fita ta tashi da sauri ta bi bayansa har ya shiga dakinsa ta shiga ya juyo yana kallonta, tace “Nace maka na ci abincin ne ni?” Kamar xata yi kuka tayi maganar, dariya ta basa, ya yi murmushi yace “You never told me” daga haka ya mika mata ta karbe abincin ta juya ta fita, yana jin ta sauka don dauko plate a kitchen ta dawo ta shiga dakinta, sai a sannan ya sauka xuwa kitchen ya hada shayi, duk da yunwan da khadijah take ji bata iya ta ci abincin me yawa ba, ta mike daga karshe ta fita, har xata kai abincin kasa sai kuma ta tsaya a hankali ta bude dakinsa ta gansa xaune yana rike da cup din shayin, ta sauke kanta kasa ta shiga dakin ta ajiye masa warmer din ta juya ta fita ya bi ta da ido. Karfe shidda saura baby ta dawo gidan tare da shureim, Sau uku tana danna bell, khadijah ta mike ta sauka bata san Aliyu ma ya fito bude mata ba, yana bude kofar Shureim ya wara ido ganinsa cike da murna yace “Unclee” nufo sa yayi da nufin rungumesa ya hango khadijah, Wara ido ya kara yi yace “Anty….” Murmushi ta sakar masa ta buda masa hannu, Har ya dau hanyar inda take sai kuma ya tsaya ya juyo yana kallon Aliyu dake kallonsu, dawowa yyi gun sa da gudu, Aliyu ya daga sa sama ya rungume sa yana murmushi yayi Pecking cheek dinsa, Lkci daya murmushin fuskar khadijah yayi fading, Baby bata san lkcn da ta fashe da dariya ba, Shureim ya xame daga jikin Aliyu ya nufi khadijah da gudu, wani kallo ta watsa masa tace “If I slap you” nan ya taka burki ya tsaya yana kallonta, Ta turo baki ta juya ta wuce sama, Murmushi kawai Aliyu yayi ya nufi yaron ya daga sa sama yace “How are you sweetheart” yace “Am fine” Baby ta ajiye abincin hannunta tace “Ina yini yayana” yace “Alhmdllh” tace “Driver na jira na waje, sai da safe” yace “Alright ki gaida mumy, tell her thank you” tayi murmushi tace “Toh yaya” daga haka ta juya ta wuce tana daga ma Shureim hannun, yana rike da Shureim suka haura sama ya shiga dakin khadijah ajiye mata shi yyi kusa da ita yace “Greet her now” a hankali Shureim yace “Anty good evening” dauke kai tayi ta hade rai tace “Evening” Daukansa Aliyu yayi suka fita dakin ta bi sa da wani kallo, har karfe kusan tara na dare khadijah bata ji motsin su ba, ta yi wanka ta shirya cikin night wear, jin shirun yyi yawa ta sa Hijab ta fita, ta fi minti biyu a tsaye, kafin ta tura kofar dakin a hankali, duhu ne dakin, ta laluba ta kunna switch, kwance taga Aliyu Shureim na kwance kusa da shi duk sun yi bacci, kashe Ac dake aiki tayi ta kashe switch din ta fita dakin ta koma nata ta kwanta. Kasa bacci tayi sai juye juye take har kusan sha biyu ta ji an bude kofa, sosai gabanta ya fadi ta kalli direction din kofar duk da wuta a kashe yake, rufe kofar yyi ba tare da ya kunna wutan ba ya iso har inda take ya duka, mirginawa tayi da sauri daga wajen tace “Meye haka?” Yace “Na xo duba ki ne kamar yanda ke ma kika xo duba mu” Xaro ido tayi tana kallonsa cikin duhun, yyi murmushi murya can kasa yace “Sweet dreams” daga haka ya fita ya kulle kofar dakin.

  • Noor Al Hayat 69

    Noor Al Hayat 69

    A hankali Khadijah ta bude idanuwanta ta sauke kan Khaleel dake xaune gefenta Aliyu na tsaye daga gefensa, Umma ta taho gunta da sauri ganin xata mike xaune ta riketa da damuwa tace “Sannu Khadijah, how are you feeling now?” Kirjinta kawai ta nuna ma Umma hawaye na xubo mata, Umma tayi kasa da murya a sanyaye tace “Xai daina in sha Allah, be strong daughter” Baby dake tsaye gefe daya ta karaso ta xauna kusa da ita tana kallonta ta kamo hannunta, rasa abinda xata ce mata tayi, lkci daya ita ma hawaye ya kawo idonta, Khaleel ya mike ya fita ward din sai gashi sun dawo tare da likita, Juyawa Aliyu yayi ya fita, likitan ya gama dubata suka fita tare da Khaleel xuwa office din sa. A sanyaye Umma tace “Kin dai ji abinda likitan ya ce maki, Kar ki sake kukan nan don Allah saboda lalurar ki” Khadijah bata ce komai ba ta kai hannu tana share hawayen idonta, bude kofar ward din aka yi Sudais ya shigo, tsaye yayi nan bakin kofar yana kallonta, A hankali Umma ta dauke kai kanta daga kallon da take masa, Baby ta hade rai kamar bata taba dariya ba, Tun da Khadijah ta kallesa sau daya bata sake yarda ta dago ba hawaye ya dinga xuba idonta, ya iso har kusa da ita, da kyar yayi gathering courage yace “Amira….” ta fashe da kuka sosai tace “Am begging you ka rabu da ni pls Aliyu ka tafi, My heart is aching at the sight of you, kayi hakuri ka wuce… let me rest plssss” cikin matsanancin kuka ta kare maganar, Yana mata wani kallo yace “Amma in har maganganun da Jiddah ta fadi maki sun yi tasiri xuciyar ki ba ki min adalci ba Amira, for good two years na boye ma mahaifiyata na ajiye ki gidana ko da kuskure ban taba sanar da ita ba ban taba tona maki asiri ba, hatta frnds dina ban da Yusuf babu wanda yasan labarin ki, sai a yanxu kike tunanin xan fallasa sirrinki, Kuma in rasa warce xan fada ma sai matata da ko kadan ba dadin xama da ita nake ba, am I that daftt??” Ya girgixa kai cikin bacin rai yace “I never expect such from you Amira, I thought ke me fadi ma wasu cewar makirci ta xo tayi displaying gidan ku….but I was mistaken” kasa ci gaba yyi ya juya ya fice daga ward din, Khadijah ta hade kanta da gwiwa tana kuka kamar an aikota, Baby dai ta kasa cewa komai duk jikinta yayi sanyi sosai, Umma ta sauke ajiyar xuciya tana kallon baby tace “Hope kin ji maganata ya fito ko, Ni nasan makirci ne kawai na mace, I know baxai taba yin haka ba, baxai xaunar da ita yayi mata tsarin da ta xo tayi ba, she set him up kawai saboda kishi….” Umma na magana tana goge hawayen dake xuba idonta, ta ji tausayin Sudais sosai, “Khadijah idan kika ce kin fasa aurensa kamar yanda kika yi ikirari before passing out kin yi butulci, baki kyauta masa ba, Kuma kin nuna ta ci nasara kenan matar tasa” Khadijah ta dago cikin kuka tace “Wayyo Umma kashe ni xata yi a gidan, baxan iya auren mata miji ba ni dai, ku rufa min asiri, Umma kin ji yanda xuciyata ke min ciwo, na hakura da auren gaba daya I prefer dying a spinster” Rungume ta Umma tayi tace “Ba abinda xa a fasa daughter, kuma tayi kadan ta kashe ki, we will prove her wrong, ta xo tayi masa sharri duk don kice kin fasa to xa a nuna mata iyakarta in sha Allah sai kin aure sa, sai in Allah yayi shi din ba mijin ki bane dama, Amma babu abinda xa a fasa” Tun da Sudais ya fita ward din ya tafi kan wani kujera a waje ya xauna ya jinginar da kai ya lumshe ido, he was totally lost and sad, Bai taba tunanin makircin jiddah ya kai haka ba, ya rasa gane inda ta samu lbrin Khadijah, yasan Yusuf baxai fada mata ba, infact ta ina ma xa su yi communicating bayan bata da number sa bashi da nata, Babu abinda ya kara sanyaya masa jiki sai yanda Khadijah of all people ta yarda da abinda jiddah taje ta fada, ai Ita mai ce ma mutane sharri jiddah ke masa, but she is among the believers, Khaleel dake jingine da motarsa yana ta kallonsa, tausayi ya basa sosai, and he knows what he is feeling, khaleel ya fi minti biyar yana jinjina kwarewar matar Sudais a fannin hypocritical action, she is just perfect, a hankali ya taka ya isa har inda yake ya xauna gefensa, Sudais ya bude ido a hankali jin mutum gefensa, Khaleel ya cire glasses din idanuwansa in a low voice yace “Sure it hurts…” Sudais na kallonsa da idanuwansa da suka sauya launi cikin sanyin murya yace “Can I confide in you Dr Ayman?” Khaleel na kallonsa ya gyada kai yace “Sure” Gyara xama Sudais yyi yana dubansa ya fara magana cikin sanyi…. Umma ce ta fito haraban hospital din bayan kusan minti sha biyar, duk iya kalle kallenta bata hango ko wannensu a nan ba hakan yasa ta koma ciki don dauko wayarta, Sudais ya dinga kallon Khaleel da yayi shiru idonsa a kasa, Sudais yace “Don’t forget I asked you before letting out my mind to you doctor, ka gaya min gaskiyar abinda ke ranka” Sai a sannan Khaleel ya dago yana kallonsa, d’an murmushin karfin hali yayi yace “Sure” bayan few seconds a hankali yace “Yea Barrister, May be it’s the right decision” Sudais na kallonsa yace “May be?” Khaleel ya shafa kansa yace “It’s just the right decision” a sanyaye ya kare maganr, Sudais ya kalli wayarsa dake ring ya ga Umma ce ke kiransa dauka yayi, ya kai kunne yayi sallama, Umma tace “Kana ji na Barrister, Babu abinda fa xa a fasa, don’t let anything spoil ur mind pls, idan har kana son Khadijah da gaske ka tafi, it’s almost time for prayer ana saukowa a daura auren ba abinda aka fasa in sha Allah” a hankali yace “Toh Umma nagode sosai Allah ya kara girma” tace “Ameen” katse wayar yayi yana kallon Khaleel dake kallonsa shima don duk ya ji me Umma ta ce, a tare suka mike Sudais na kallon agogon wrist din sa. Tun da aka sauko masallaci gaban Sudais ke faduwa, is he really making the right decision, Khaleel dake gefensa na lura da shi, a hankali ya matsa kusa da shi sosai yace “It’s not only the right decision but the best…. For many reasons” Sudais ya kallesa yayi murmushi bai dai ce komai ba, can ya kalli Khaleel yace “Kana da Number Dr Aliyu kuwa? I didn’t see him…” Katse sa Khaleel yyi yana yar dariya yace “Sheer jealousy, did you expect to see him here….” Murmushi kawai Barrister yayi, Khaleel ya fiddo wayarsa ya nemo masa number Aliyu ya mika masa, Dialing number Sudais yyi ya kai kunne ba a dau lkci ba aka dauka Sudais yace “It’s Barrister Aliyu, ban gan ka masallaci ba, or don’t you want to witness the nikka?” Aliyu yyi murmushi yace “It’s not a must I stay near you Barrister, though I can sight you from where I am, I am not what you might have thought of me, idan abun farin ciki ya samu d’an uwana musulmi ina taya sa murna, idan kuma otherwise….” Hangosa Sudais yyi tsaye not too far away from them tare da Salim da wasu frnds, Sudais ya katse wayarsa yana murmushi, Aliyu ya Karaso ya basa hannu Sudais ya mika masa nasa, sannan Aliyu ya mika ma Khaleel ma, Khaleel ya cire glass din idanuwansa ya basa nasa hannun. A can asibiti kuwa bayan an ma Khadijah allurai aka bata drugs aka sallamosu suka koma gida, har sannan hawaye ya ki tsaya mata, Babu abinda aka fasa na biki a gidan kamar yanda Umma tace don kamar ma ba ayi komai ba sai dai Amarya da bata da lafiya, Shayi Umma ta sa baby ta bata ta sha ta kwanta nan da nan bacci me nauyi ya dauketa….

    Breakfast, just light😎

  • Noor Al Hayat 72

    Noor Al Hayat 72

    Lumshe ido Aliyu yayi jin sunan da ta kira lkci daya jikinsa yayi sanyi sosai, ya bude idanuwansa ya taka a hankali har ya isa gabanta, ja baya ta dinga yi xuwa lkcn ta daina kukan da take tsoro ne fal xuciyarta, ya xauna dab da ita har suna jiyo numfashin juna xata mike da sauri, yyi hanxarin rikota ta fashe da kuka jikinta na rawa, a hankali ya jawota jikinsa ya rungumeta lkci daya ta hadiye kukan da take, ya dinga jin yanda xuciyarta ke bugawa a kirjinsa kamar xai fito, lumshe ido yyi hawayen idanuwan sa suka xubo, cikin rawar murya tace “Barrister ka kunna wutan bana son duhun plss, switch the light on” Murya can kasa yace “Imannn” Ta fi second talatin muryar da taji na kai kawo a kanta, a hankali ta xame jikinta daga nasa tana kallon fuskarsa cikin duhun dakin kamar yanda shi ma yake kallonta a sanyaye, hannu ta kai fuskarsa tana masa wani kallo da kyar tayi gathering courage din cewa “Aliyu?” Rungume ta yayi kamar xai mayar da ita jikinsa cikin rawar murya yace “Yes Iman, I beg you… don’t say no to me plsss, this our fate… na sha wahala kan ki a rayuwa Iman, na sha wahala fiye da tunanin ki, kashe ni ne kadai son ki bai yi ba, for good six years bani da kwanciyar hankali bani da walwala, forgive and forget the past plss, Barrister Aliyu…” Kasa ci gaba yyi bayan wani lkci ya ci gaba voice dinsa na breaking “I owe him… he gave up for me…. Ya bar min ke Iman, don girman Allah ki ji tausayina kar ki bani wahala….” Kamar warce aka yi moulding haka khadijah tayi stiff jikinsa maganganunsa na mata yawo a kai, she’s still trying her best to apprehend all what he is saying, Jin tayi shiru ya dago kanta jikinsa na rawa, hawayen dake makale idonta suka xubo tana kallonsa, ta fashe da wani matsanancin kuka kamar warce aka aiko ma wa da sakon mutuwa, sauka yyi saman gadon a rikice ya durkusa kan gwiwowinsa kusa da ita yace “Iman kiyi ma girman Allah kada ki wahal da ni, I have already had enough, don’t say no to this marriage, kar ki ce A’a Iman….” Kasa ci gaba yyi…. A hankali tayi baya ta fada saman gadon, ya mike da sauri ya riketa yana kiranta amma tuni idanuwanta suka rufe, ya dago ta ya rungume ta hawaye na sakko masa yace “Why Iman, kin yi saurin mance alkhairin da na maki a rayuwa, sharrin kawai kika bari a ranki, ba laifina bane, ba yin kai na bane, ni ba maxinaci bane, duk xaman ki gidanmu ban taba tunanin akwai ranan da xai xo in cuce ki ba….” Kasa ci gaba yyi ya runtse ido yana rungume da ita har sannan. Sai kusan karfe hudu saura na asuba khadijah ta bude idanuwanta a hankali, Aliyu da ke xaune kan darduma ya mike da sauri ya iso kusa da ita yana kallonta da damuwa, mikewa take kokarin yi tana kallon jikinta, riga ce mara nauyi jikinta maimakon atamfar da ta sa tun a gida, Aliyu ya xauna gefen gadon a sanyaye yana kallonta, kokarin sauka ta shiga yi daga kan gadon yana son riketa amma yana tsoron abinda xai biyo baya, cike da karfin hali yace “Iman you are not strong ina xa ki, Wait…” Bai san lkcn da ya riketa ba ganin tayi baya xata fadi, xai kwantar da ita ta kwace kanta tace “Let me” Dafe kansa yyi, ganin xata sake tashi ya kara rikota, tura hannunsa tayi muryarta na rawa tace “Dole sai ka rike ni ne, nace bana so” ko saurarenta bai yi ba ya ki saketa, ta fashe da kuka tace “I want to use the restroom ka kyalenii….” Tashi tsaye yyi ya dagota ya nufi bayi da ita, suna isa bayin ta kwace kanta ta shiga ta rufe kofar, a hankali ya koma gefen gado ya xauna duk jikinsa a sanyaye, tana fitowa ta nufi kofar fita ya mike da sauri yace “Iman” ganin ko juyowa bata yi ba ya karasa da sauri kafin ta isa kofar ya rufe ya marairaice yana kallonta, Xaunawa tayi nan bakin kofar ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka xuciyarta yayi rauni ga wani xafi da yake mata, yanxu dama duk yaudararta Sudais yake, me yasa xai ci amanarta ya sa a aura mata Wai Aliyu?? Of all people why Aliyu? The beginning and end of her problem, the person that shattered her life, me yasa xai sa a aura mata shi, ta dinga kuka a raunane taji duk duniyar ya isheta, gaba daya ji tayi haushin kowa take har Umma don tasan ita ma ta sani amma ta boye mata, a hankali Aliyu ya sa key kofar ya cire a jiki, Jin haka ta mike a mugun fusace hawaye na sakko mata xuciyarta na bugawa tace “Malam ka bude min kofa in fita…. Bana son ganin ka, bana so….” Bai bari ta kai karshe ba ya jawota jikinsa ya rungume ta ya lumshe ido, duk iya kokuwan da ta dinga yi xata kwace kanta kasa wa tayi daga karshe ta hakura ta dinga kuka, a hankali murya can kasa yace “Plss, tell me how many days will it take you to finish this drama?” Dago kai tayi tana masa wani kallo xuciyarta na heaving, a sanyaye yace “I just want to get prepared… Just tell me for how long it will take you to finish it? And in sha Allah I will endure” fuskarta daure tace “Sake ni” a hankali ya saketa ta koma baya ta mika masa hannu tace “Bani makullin” ya mika mata makullin hannunsa, ta juya ta bude kofar ta fice tayi banging din kofar, Ya d’an tabe baki ya juya a hankali ya koma kan gado ya kwanta don har wani ciwo kansa ke yi masa baccin da bai yi ba, har aka kira Asuba bai bari bacci ya daukesa ba ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito don wucewa masallaci, kwance ya ganta kan 3 seater a parlor tana bacci ta dunkune waje daya saboda sanyin parlorn, ya kashe A.c sannan ya nufi kofa ya bude ya fita. Ko da ya dawo masallaci bai ganta parlorn ba kuma, ya wuce sama ya bude kofar dakinta a hankali yana leka ciki ya ga bata nan, juyawa yyi da sauri ya bude wani dakin, xaune ya ganta kan darduma ta jinginar da kanta jikin bango, tana ganinsa ta daure fuska ta cinno baki gaba, a hankali ya rufo mata kofar ya shiga nasa dakin ya kwanta, sai a sannan bacci ya daukesa. Sai da gari ya fara wayewa khadijah ta mike jiki ba kwari daga kan darduman da take xaune ta bude kofar dakin ta fito, dakinta ta bude a hankali tana kallon ciki, ganin babu kowa ta shiga ta rufe kofar, bathroom ta shiga tayi wanka ta fito, bayan ta shirya ta kwanta saman gado jin kanta na ciwo sosai, bacci ne ya dauketa daga haka, Bata farka ba sai da aka danna bell a kasa, ta mike xaune da kyar tana kallon agogo, har sannan kanta ciwo yake ba kadan ba, karfe tara saura ta gani, ta sauka daga kan gadon ta dau hijab dinta ta sa ta fita, a hankali ta bude kofar ta ga Baby tsaye rike da basket din abinci tana murmushi tana kallonta, khadijah ta hade rai sosai ta juya ta koma parlor, Baby da ta bi ta da kallo a xuciyarta tace kya yi ki gama ne ma, A nan parlor ta ajiye basket din ta juya xata fita khadijah ta bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar sai a sannan baby ta fara dariya kasa kasa, khadijah da ta bi ta da kallo ta xauna kujera lkci daya hawaye ya cika idonta ta ji kamar ta bi ta ta mata magana amma ta kasa tashi, wato dai ita ma tasan wanda aka aura mata amma bata fada mata ba, tashi tayi ta wuce sama ta shiga daki ta fada kan gado tana kuka takaici, bayan wani lkci ta mike ta dauko wayarta ta shiga kiran Sudais, sau uku tana kira bai dauka ba, ta ajiye wayar tana share idonta ta kwanta xuciyarta ba dadi, ta jima kwance jin ciwon kai ya isheta tana son shan magani ta mike a hankali ta fito, downstairs ta sauka taga abincin da baby ta kawo na nan yanda ta ajiyesa, ta kalli agogo ta ga har sha daya ya kusa, sama ta kalla, ta fi minti biyar tsaye kafin ta nufi kofar da take xaton kitchen ne ta shiga ta dauko cup da spoon, shayi ta hada ta koma kujera ta xauna, kasa shan shayin tayi ta ajiye cup din hannunta a hankali ta wuce sama, dakin da take tunanin nasa ne ta bude a hankali, kwance ta gan sa kan gado idonsa a rufe, ta dinga kallonsa kafin ta karasa ciki kamar mai tsoron taka tiles din ta isa har kusa da shi ta duka, Bbu wanda ya fado mata a rai lkcn sai little Sudais, lkci daya taji jikinta yyi sanyi ta dinga kallonsa ko kiftawa babu, lkci daya ya bude idanuwansa ta mike da sauri tana kalle kalle kamar mai neman abu duk ta daburce…..

  • Noor Al Hayat 76

    Noor Al Hayat 76

    Mikewa Sudais yyi yana murmushi ganin su, Aliyu ya karasa gun sa shi ma murmushin dauke fuskarsa ya basa hannu suka gaisa, Sudais ya duka yana kallon Shureim yace “How are you son?” Shureim ya washe masa hakora yace “Fine Uncle” Khadijah dai har sannan bata dago kanta ba gabanta sai faduwa yake, Sudais ya dago yana kallonta yace “Good morning Amira” sai a sannan ta kallesa tayi murmushi a sanyaye tace “Ina kwana Barrister” yace “Lafiya lau, ya gida” a hankali tace “Alhmdllh” a karo na farko ta kalli direction din da Anty khadijah ke kwance, ita ma kallonsu kawai take, duk tayi baki ga ciki 6aro 6aro ya fito, khadijah bata ganeta da farko ba ta dinga kallonta babu kiftawa, gaba daya Anty khadijah ta canxa kamar ba Anty khadijahr da ta sani yar gayu fara ba, Aliyu ya karasa har kusa da ita yana kallonta a hankali yace “Sannu Anty, ya jikin?” Maimakon ta basa amsa sai ta fashe da matsanancin kuka ta dafe kanta, ya duka kusa da ita cikin sanyin murya yace “Haba Anty, kuka kuma? There is no need for that, in sha Allah xa ki samu lafiya soon, kiyi hakuri….” Shi dai Sudais kallonta kawai yake daga inda yake a tsaye, a xuciyarsa kuwa tunani yake anya ma da gaske kanwar mahaifiyar Aliyu ce ba kawai kara ake yi ba, shi bai ma wani ga resemblance ba, Khadijah ta sunkuyar da kanta hawayen da ya taru idonta ganin condition din Anty khadijah suka xubo mata, Anty khadijah na girgixa kai cikin kuka tace “Kaico na… kaico… don Allah ku rufa min asiri ku yafe min Aliyu, ku yafe min ko xan samu saukin abinda nake ji kullum, ku yafe min kar in…..” Katse ta yayi da sauri yace “Anty ni baki min komai ba na sha gaya maki, idan ma kinyi wllh na yafe maki duniya da lahira Allah ya yafe mana baki daya, don Allah ki daina cewa haka, Allah xai baki lafiya albarkacin annabi Muhammad S.A.W” kuka take yi sosai tace “Aliyu nasan idan ka san gafarar da nake nema gun ka baxa ka yafe min ba, ba lallai ka yafe min ba coz i don’t deserve it, ni din muguwa ce, na cuce ku, na ci amanar yayata, wllh sharrin shaidan ne ba yin kai na bane, ga sakayya tun a duniya Allah ya maku, ashe dama mugunta na komawa mai shi…..” mikewa Aliyu yyi bai sake ce mata komai ba don ji yayi har xuciyarsa ya karaya, Ashe tana sane mugunta take yi dama, cikin magiya da kuka tace “Aliyu don girman Allah, don xumuncin dake tsakanina da mahaifiyar ka ka yafe min abinda nayi maku da khadijah….” Aliyu na kallonta ya dake duk da yasan sauran xancen yace “Me kika yi mana ni da ita Anty?” Tana shessheka, fuskarta caba caba da hawaye tace “Wllh ni ce nayi asiri na xuba lipton din da baiwar Allahn nan ta kai maka ranan ka sha, Kuma na kwashi yaran duk muka bar gidan, na bar ku daga kai sai ita, ni ce silar abinda ya faru tsakanin ku, ni ce sillar lalata ta da kayi” shi dai Aliyu bai ce komai ba, sai dai har wani tafarfasa xuciyarsa yake duk da ya riga ya gama jin ranan da take waya, khadijah da Sudais dai ta bari cikin shock din xancenta, Baby ta mike ta kama hannun Shureim dake ta kallon Anty khadijah ta fice daga ward din, Anty khadijah ta kara rushewa da kuka tace “Wllh sharrin shaidan ne la’ananne, shi ya sa min tsanar ta khadijah, shi ya asasa min k’in ta a xuciya, don duk xamanta gidan bata taba min komai da ya wuce biyayya da girmamawa, abinda yasa na aikata abinda nayi ina tsoron kar wataran ka ce kana sonta da aure don naga yanda kake tausayinta kuma kake damuwa kan lamarinta, gashi naga yanda Mumy ma ke sonta, shi yasa nayi duk haka… ban mance ranan da suka dawo bayan ta bar gidan da wancan bawan Allahn ba wai tana dauke da cikin ka na ki saurarensu nace su tafi kuma suka tafi, toh yanxu wa gari ya waya, ka lalata mata rayuwa ta tafi ta fuskaci kalubale iri iri wanda da alama hakan alkhairi ya xame mata, sai gashi dai bayan shekaru da dama kai din dai ka aureta, Ni kuma ga yanda nawa rayuwar ta kasance, ga ‘ya ta can rai a hannun Allah, yanxu ina ji ina gani nima xan girbe abinda na shuka” ko kadan Sudais bai ji tausayinta ba sai ma kawai ji da yayi ya tsaneta, dama akwai mutane irin haka a rayuwa, the wickedness is just too harsh, khadijah dai na tsaye tamkar wanda aka dasa a gun, gaba daya jin xancen Anty khadijah ta dinga yi kamar a mafarki, lkci daya ranan da ta je kai ma Aliyu Lipton a daki ya fado mata, irin yanda ya dinga cewa ta tafi da yanayinsa a lokacin ya dawo mata fresh a memory dinta, bata manta ba har saloon yace ta tafi sanusi ya kai ta amma saboda tausayin halin da ta gansa ta ki tafiya, ashe duk asiri ne dama, sai a sannan ta fashe da kuka sosai ta juya ta fice daga ward din, Anty khadijah ta dinga kuka tace “Aliyu nasan ita ba lallai ta yafe min ba idan kai ka yafe min… Nasan da wuya don na xalunce ta da yawa” Aliyu bai iya yace komai ba, Sudais ya fita ward din, bin bayan khadijah yayi ya sameta can waje tana aikin rusa kuka, Baby ma na nesa da ita amma bata samu courage din xuwa inda take ba, Sudais na kallonta a hankali yace “Amira” juyowa tayi tana kallonsa hawaye wasu na bin wasu, yace “Kiyi hakuri, duk abubuwan da take fada anyi su an wuce ya kuma xama passed tense, this is ur new life… Don’t allow ur past to spoil ur happiness, kin dai ji da kunnen ki kuma kin tabbatar ba yin kan Aliyu bane, ba laifinsa bane, ba halinsa bane, babu wanda ya tambayeta kuma babu wanda ya matsi bakinta amma sanin cewar hakkin ku ke bibiyar ta shi yasa ta fallasa kanta, don haka just forgive her and life moves on, gashi ita ma ai tana reaping shukar da tayi, yanda kika haifi yara out of wedlock ita ma gashi haka xata haifa, gwara ke naki yaran masu gata ne, ita fa, kilan ba lallai tasan uban cikin ba, sannan ga karaya har kafa biyu, da wuya kuma kafufuwanta su dawo dai dai ba fatan hakan na mata ba, shi yasa idan mutum xai gina ramin mugunta yasan size din da xai gina, let bygone be bygone Amira, ki koma yanxu kice ke kin yafe mata, sai ki ga ta dalilin hakan kila ta samu wani saukin… ” Kai kawai khadijah ke gyada masa hawaye na sakko mata duk jikinta yyi sanyi, yace “Mu je” ba musu ta bi bayansa har suka koma ward din, amma ta kasa karasawa gadon tana daga inda take a tsaye cikin rawar murya tace “Anty ni na yafe maki,
    Allah ya baki lafiya ya kuma yafe mana gaba daya” kallonta kawai Anty khadijah take hawaye na sakko mata, sai a sannan wani tausayinta ya rufe khadijah, ita ma hawayen ya dinga sakko mata, ta isa har bakin gadon ta kamo hannunta cikin rawar murya tace “Na yafe maki, kema ki yafe min for making you go the wrong way, don nasan da ban je gidan ba baxa ki jefa kanki a halaka ba, Allah ya baki lafiya ya tashi kafadun ki Anty” cikin rawar murya Anty khadijah tace “Amin Nagode, Allah ya baku xaman lafiya da xuri’a dayyaba, ya kauda duk wata fitina tsakaninku, I wish Allah xai bar min rai na inyi witnessing din haka, amma ina jin kamar mutuwa xan yi, Alhmdllh naji dadi da na sauke wannan nauyin a kai na don kullum da shi nake kwana nake tashi, ban san ta ina xan fara ba, Allah ya yafe mana baki daya kuma ya shiryi masu xuciya irin tawa” Khadijah ta kasa amsa mata sai kuka kawai take, Aliyu yace “Ameen, baxa ki mutu ba sai lokacin ki yayi Anty” Ita dai bata ce komai ba sai kukan takaici da danasani da take yi, ganin kukan da khadijah take, Anty khadijah tace “Ku tafi Aliyu kar in bata maku mood, Allah maku albarka, ya kuma kaddara saduwar mu” Yace “Ameen mun gode, xan dawo nan da kwana biyu” tace “Allah ya kai mu nagode” Gun Barrister ya nufa yana kallonsa yace “xa mu koma Barrister, Allah ya bada lada” Barrister yyi murmushi yace “Ameen, Allah kai ku gida lafiya” Dawowa yyi ya kama hannun khadijah da kamar daman jiran hanyar kuka take suka fita dakin bayan ta daga ma Barrister dake murmushi hannu. Baby bata iya tace masu komai ba duk jikinta yyi sanyi, Aliyu ya kama hannun Shureim dake ta kallon uwarsa da damuwa ganin kuka take yi, ya bude back seat ya sa shi a ciki, ya bude mata front seat, shiga tayi tana goge hawayen dake xubo mata, ya rufe motar yana kallon baby, a sanyaye tace “Allah ya tsare hanya yayanmu” yace “Ameen, tare ku ka xo da Barrister?” D’an murmushi tayi bata ce komai ba, yayi dariya yace “Nasan rakiya kawai yayi koh?” Dariya tayi bata ce komai ba, yana murmushi ya xaga ya shiga driver seat ya ja motar suka fita asibitin, Shureim na kallonsa kamar xai yi kuka yace “Uncle why is Anty crying?” Aliyu ya kalleta yayi murmushi yace “Allura aka mata” Shureim ya fashe da kuka yace “Me yasa uncle” parking Aliyu yyi ganin kukan da yaron yake, yana kallon khadijah yace “Kinga dama idan ba neman hanyar kuka kike ba toh ya ishe ki haka Iman” ta balla masa wani Harara tace “Toh ina ruwanka, hanyan nake nema dama” murmushi yayi, ya kwantar da murya yace….

  • Noor Al Hayat 66

    Noor Al Hayat 66

    Umma na lura da khadijah dake jujjuya abincin gabanta, ko bata gaya mata ba taga alamar tana da damuwa sosai, Umma tace “Khadijah” da sauri ta dago ganin yanda Umma ke dubanta ta debi shinkafar gabanta ta kai baki, tana son tambayar Umma ko magana tayi mata amma tayi shiru tana cin abincin, Umma tace “Tell me ur problem, what are you thinking of?” Khadijah ta wara manyan idanuwanta tace “Ba komai Umma am just tired ne” Umma tace “Toh ki gama cin abincin sai kiyi isha ki kwanta” A hankali khadijah tace “Toh” da kyar ta dinga tura abincin don gaba daya bata da appetite, why is she finding it hard to erase jawahir’s hurtful words from her mind, mikewa tayi daga karshe ta wuce kitchen da plate din shinkafar, tana wankewa a sink Sudais ya fado mata, tasan baxai ji dadi ba ta taho bata gaya masa ba, tayi deciding ta tura masa test kawai ta gaya masa, tana dawowa parlor ta dau wayarta ta xauna gefen Umma ta shiga rubuta masa text din cewar ta dawo yanxu, ta kuma basa hakuri da bata gaya masa ba while coming back, Unfortunately Wayar na bedroom din Sudais, shi kuma ya shiga bathroom, dai dai shigowar jiddah dakin text din ya shigo, Atm dinsa dama tayi niyyar shigowa ta dauka without his consent, ganin wayarsa dake gaban mirror yyi haske ta nufi wayar da sauri, dauka tayi ganin message ta sa finger ta jawo yanda xata iya karanta content din, she was very cautious kar tayi erasing message din daga gaban screen din wayar, sake baki tayi tana kallon text din, ta nanata Ummu Shureim a xuciyarta ya fi a kirga, tayi wani murmushi, wato Amira ya mayar Ummu Shureim don kar ta gane, da sauri ta ajiye wayar jin alamar xai fito ta kashe wutan ta shiga dube dube a drawern mirror with a very serious face, sudais ya fito daure da towel yana kallonta, he was very surprise seeing her… da yake tun da ya kawo mata kayan fadar kishiya ta daina kulasa a gidan, ta kallesa fuska daure tace “Why are you staring at me that way?” Bai damu da abinda tace ba yace “Me kike nema?” A takaice tace “Razor blade, naga wani shekaranjiya a nan ina gyara, I want to sharpen my daughter’s pencil tayi assignment” tabe baki yayi yace “Duk Miscellaneous school materials dinta babu sharpener sai kin shigo nan neman razor?” wani kallo tayi masa tace “Ae dai you are not blind kana ganin komai ta kai makaranta xubarwa take ta dawo min haka kamar wata wawiya, or am I to become a razor to sharpen her pencil???” Bata sake saurarensa ba ta fice daga dakin, ya girgixa kai ya nufi gaban mirror, wayarsa ya kunna, ganin text din khadijah gaban wayar ya xaro ido sosai, can ya kalli kofa da sauri, shi dai bai ga alamar da ya nuna ta taba wayar ba, beside da ta dauka ai bude message din xata yi kuma baxai gansa gaban wayar ba, hakan yasa ya tabbatar bata dau wayar ba, Jiddah na komawa daki ta xauna gefen gado tana tunane tunane, to ita yanxu shawarar wa xata nema, anya jiran da tace xata yi har sai an daure auren bai yi nisa ba, kai gaskiya yayi nisa sosai, kawarta Amina ta shiga kira tana dauka tace “Amina don Allah gobe ki taho da sassafe, Ina cikin babban matsala” Aminar tace “Toh in sha Allah xan taho kuwa” Ajiye wayar tayi ta mike tana xaga dakinta, kai ina ma Allah xai bata sa’a taga Amiran nan ta fara nakada mata duka kafin ta bude mata sirrinta da ta sani, fita tayi dakin ta nufi dakinsa ta bude a hankali don taga mai yake, babu kowa dakin kuma ya dauke wayarsa, ta sauka downstairs da gudu, ganin an kunna wutan kitchen ta gane yana can, waya taji yana yi a kitchen din, ta labe jikin bango dai dai nan taji yana cewa “Alryt dear, my regards to him, gobe da safe xan taho…” Da sauri jiddah ta tafi stairs jin xai fito, yana fitowa ta maxa ta juyo kamar tahowanta kenan, Bai kalleta ba kamar yanda bata kallesa ba ya isa kan kujera ya xauna rike da cup din tea. Khadijah na kwance da Umma misalin sha daya na dare Umma tace “Ya Khaleel da matarsa?” Khadijah tace “Suna can lafiya” Umma tace “Ya sani xaki taho?” Khadijah ta gyada kai tace “Ehh ya sani, Umma Aliyu ne yyi accompany din mu” Umma ta daga kai tana kallonta kafin tace “Yana kasar ne?” Khadijah ta gyada kai tace “Ehh can yake xama” Umma bata ce komai ba ta koma ta kwanta, khadijah ta dinga nuna ma Umma kayayyakin da Sudais ya sa mata a lefe ta waya, don komai ya siya sai ya tura mata ko tana so, Umma tace “Maa Sha Allah, Allah sanya Alkhairi” khadijah tace “Ameen” a hankali tace “But Umma how will I cope with studies and marriage, ko ki ce masa kawai ya bar ni a can kasar in gama kawai idan anyi auren” Umma tace “Kwana nawa ne hutun naku?” Khadijah tace “Ba yawa fa, wata daya ne da few weeks” Umma tace “Bikin kuma nan da sati nawa yace maki?” A hankali tace “Biyu” Umma tace “Kema kin san baxai hana ki karatu ba, Kar ma ki ce masa komai, but surely xai bari ki gama” khadijah tace “Toh Umma” Umma tace “Allah ya kai mu lokacin lafiya” a hankali khadijah tace “Ameen, Amma Umma sai gabana yayi ta faduwa” Umma tace “Sai ki yawaita addu’a, babu abinda mutum ya isa ya maki wanda Allah bai maki ba” Washegari da safe tun da Jiddah ta tashi take tunanin yanda xa ayi ta san inda Sudais xai je ganin har ya gama shiryawa cikin suit yana xaune dining yana shan shayi ta sa hijab ta fita kamar xata xubda shara, ko amsa gaisuwar mai gadi bata yi ba sanin duk bakinsu daya da sudais komai ya faru gidan sai Sudais ya tambayesa, kamar kawayenta nawa suka xo a rana kuma duk da jan kunne da take masa sai ya fada masa, duk ta fita gidan to sai Sudais ya sani, har bakin titi ta taka suka gaisa da mai filling din gas dake bakin titi da d’an shagon container sa, yace “Maman Amira kaddai ki ce har gas ya kare in je in dauka, naga ko sati biyu ba ayi ba na cika” Tace “A Haba kamar muna shan gas a gidan, ba shi ya kawo ni ba malam rabilu, wani taimako nake so ka min don Allah, Kuma wlh ni me biyan ka ko nawa ne, amma kuma sirri ne tsakanina da kai” tana magana ne tana kallon cikin layi ko xata hango motar Sudais, Rabilu yace “Tohhh… Sirri kuma maman Amira” tace “Kaga ba wani abu bane, yanxun nan Abban Amira xai fito a motarsa, to don Allah so nake ka tada Machine dinka ka bi bayansa ka gano min inda xa shi, wllh ko nawa ka bukata xan biya ka Rabilu, kar ka ji komai ba wani sanin ka yayi ba” Dariya sosai mutumin yayi yace “Kai yanxu shi Barristern xan bi a machine maman Amira?” Ta hade rai tace “Kai dai biyan ka xan yi babu ruwan ka, Kuma ku din ne sai da haka, ban yarda da takun sa bane kwanan nan, yanxu dai don Allah ka rufe container din nan ka hau kan babur din ka ka jira sa anytime soon xai fito na sani, xuwa anjima xan dawo in ji yaya, da kudin ka kuma xan taho in sha Allah” daga haka ta koma cikin layin, ta kusa gida sai ga motar sudais kuwa, Dauke kayi tayi, ya tsayar da motar yana kallonta yace “Jiddah?” Ta juya fuska daure tana kallonsa, yace “Da ixinin wa kika fita, Kuma ina kika je?” Tana nuna masa gidan dake kusa da nasu tace “Matar gidan can ta kira ni yaronta ya kone da mai, Toh sai kar in je? Ko baka ga a gigice na fita ba?” Rufe glass dinsa yayi ya ja motarsa ya wuce, ta tabe baki ta shige cikin gida, office Sudais ya nufa direct don client na jiran sa. Khadijah dake kitchen tana duba miyar kubewar da Nanny ta daura ta juya tana kallon Shureim dake mika mata waya, ta hade rai tace “Waye yake kira yanxu kuma?” Yace “Doctor” tace “Nace kar ka sake kawowa baka ji Koh” yace “Am sorry Anty” daga ya juya ya koma da wayar, Khaleel ne ke kiranta tun daxu ta ki daukar wayar, da ya kira sai Shureim ya kawo wayar don yana hannunsa, Umma dake jin su a parlor tace “Wa ke kiran ki baxa ki dauka ba khadijah?” Turo baki tayi tana juya miyar tace “Umma number ne and I don’t want to pick” Umma bata ce komai ba duk da taji san da Shureim yace doctor ne, khadijah ta sauke miyar ganin yayi ta hade plates xata wanke sai ga Shureim ya dawo da waya yana mika mata, wani kallo tayi masa tace “Kana son duka koh?” Kamar xai yi kuka yace “Anty it’s a number, it’s not saved” karban wayar tayi taga Aliyu ke kiranta, tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, a hankali yace “Iman ya kike?” Tace “Lafiya lau ya su Mumy?” Yace “They are fine, Ina Shureim?” Tace “Gashi” yace “Ya jikin sa?” Tace “Ya ji sauki, only the cough” yace “Ohk basa wayar” Mika ma Shureim wayar tayi ta ci gaba da abinda take, bayan wani lkci ya dawo mata da wayar, share hannunta tayi ta amsa ta kai kunne, Aliyu yace “Baby wai xata xo wajen ki, is that okay by you?” Khadijah tace “Yaushe xata xo?” Yace “Anjima xan kawo ta” Khadijah taji dadi har ranta tace “Toh ina jiran ta sai ta xo” yace “Ohk” daga haka ya katse wayar. Bayan azahar Umma na xaune parlor da Nanny suna llissafin abubuwan da xa a siyo a Dubai na kayan daki, ita dai khadijah tana kwance tana danna wayarta Kiran Aliyu ya shigo wayar, Dagawa tayi ta kai kunne tana jin sa yace “Muna kofar gida Iman” khadijah ta mike xaune tace “Ohk ga ni fitowa” katse wayar tayi tana kallon Umma tace “Umma ta iso bari in je in shigo da ita” Umma tace “Toh sai kin dawo” mayafinta ta yafa ta fita xuwa kofar gida, fitowa baby tayi daga mota ganinta ta karaso da sauri ta rungumeta tace “Khadijah…” Khadijah tayi murmushi tace “Baby ya su Mumy” Baby tace “Suna gida, sun ce a gaishe ku” Khadijah tace “Ayya, Ina amsawa” Aliyu ya fito daga motar yana kallonta yace “Ina Shureim din?” Tace “Yana ciki” ta kama hannun Baby tace “Mu shiga ciki” Baby ta kalli Aliyu tace “Toh yayanmu nagode sai anjima” khadijah kawai yake kallo yace “Ki kawo min Shureim din mu je gun Mumy su gaisa” ba tare da ta juyo ba tace “Toh” Da fara’a Umma ke ma baby sannu da xuwa, Khadijah ta kama hannun Shureim bayan ta dauko masa takalminsa tana kallon Umma tace “Umma xai je su gaisa da Mumy wai” Umma tace “Toh Allah ya kiyaye” daga haka ta fita da shi, Aliyu ya kama hannunsa yana kallonta yace “Gobe xan koma Iman” ta kallesa tace “Toh Allah ya kai mu” yace “Ameen” har xata tafi ta juyo tace “Amma plss kwana baby xata yi koh?” Yace “Ban sani ba, ki tambayeta” tace “Tohm” daga haka ta wuce ciki bayan tayi ma Shureim dake daga mata hannu murmushi. Khadijah ita kanta bata san xata sake da Baby haka ba, closeness dinsu na da kawai take tunawa da irin halaccin da baby tayi mata a gidansu, hira kawai suke tana ba baby labarin abubuwan da suka faru bayan ta bar gidansu, tun baby na kallonta cike da tausayi har ta fara kuka ba tare da ta san tana yi ba, Khadijah ta xaro ido ta fashe da dariya tace “Kuka Kuma baby, toh an gama labarin” baby na share idonta a sanyaye tace “Don Allah ki ci gaba Iman, mara Imani ne kadai baxai xubda hawaye ba a labarin nan naki…” Khadijah tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Baby na ci gaba da share hawayenta a sanyaye tace “Ki ci gaba plss Iman” a hankali khadijah ta ci gaba da bata labarin har karshe, kuka kawai baby take khadijah na kallonta, Baby tace “Don Allah Iman ki yafe ma yayana plss” Khadijah tayi murmushi tace “Ba dole in yafe masa ba Baby, na yafe masa tuntuni, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana balle beings” A hankali baby tace “Allah saka ma barrister” shiru Khadijah tayi tana kallonta, can tayi murmushi a hankali tace “Ai shi xan aura baby” kallonta Baby take da mamaki tace “Yaushe?” Khadijah tace “In less then three weeks ne bikin” A sanyaye baby tace “Shine baki sanar mana ba Iman, haushin mu kike ji har yanxu koh?” Khadijah tace “Ayya ba haka bane, kin ga jiya muka dawo ai, dama nufina idan na dawo in kai ma Mumy kati” Baby tace “Ya Aliyu ya sani?” Girgixa mata kai Khadijah tayi, Baby tace “Toh Allah kai mu lokacin, ya sanya alkhairi, Amma barristern a nan garin yake?” Khadijah tace “Ehh nan yake, ae kin san sa” Baby tace “A’a ban san sa ba” Khadijah tace “Ranan da muka je gidan ku ai tare muka je da shi” Baby tace “Ai su biyu ne ranan” Khadijah tace “Ai anjima xai xo sai ku gaisa” Baby tace “Allah ya kawo sa” khadijah ta dinga lallaba baby ta kwana gidan ganin ta fara cewa yamma yayi, baby tace “Ae ban ce ma Mumy xan kwana ba” khadijah ta marairaice tace “Plss baby, kinga ko frnds bani da, am always lonely, xan ce Umma ta Kira Mumy tace xa ki kwana” Bata sake sauraren baby ba ta fita ta sanar ma Umma sannan ta sa mata number mum din su Aliyu a wayarta ta kira ta, tana sawa ta fita ta dawo dakinta gun baby tana murmushi tace “Toh yanxu Umma xata kirata” Babu yanda baby ta iya haka ta hakura xata kwana gidan. Bayan sun idar da magrib suna xaune daki baby na bata labarin halin da iklima ke ciki duk jikin khadijah yyi mugun sanyi, ringing din wayarta yasa baby tayi shiru, dagawa tayi ganin Barrister ke kiranta bayan sun gaisa yace “Am outside dear” murmushi tayi tace “Toh ae shigowa xaka yi”

  • Noor Al Hayat 79

    Noor Al Hayat 79

    Murmushi kawai Aliyu yayi bai ce komai ba, ya dau wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne tare da yin sallama yace “Muna hanya Dr, soon xa mu iso” ajiye wayar yayi, yana maida hankalinsa gaba daya kan driving da yake, bayan tafiya mai tsawo suka shigo wani anguwa, yayi parking dai dai wani gida, kalle kallen anguwar yake to make sure address din da aka turo masa daxu ne, ya dau wayarsa ya bude yana kallon number gidan, tada motar yayi yana driving a hankali har ya isa wani babban gida yayi parking, khadijah da ke ta kallonsa tace “Baka ma san inda xa mu ba kenan” ya kalleta ya wara manyan idonsa yana murmushi yace “Na sani mana, ba gashi mun xo ba” Dialing number Dr Ayman yayi yace “Ga mu a waje” Ba a dau lkci ba Khaleel ya fito daga babban gidan, duk a tunanin khadijah gidansa suka xo, Ya bude side din Aliyu ya basa hannu suka gaisa yana kallon khadijah yace “Good morning Madam” d’an murmushi tayi a hankali tace “Ina kwana Doctor” yace “Lafiya lau ya gida” tace “Alhmdllh” yana kallon Aliyu yace “Alryt, ku shiga ciki ni ana jirana xan wuce yanxu, sai na dawo anjima” Aliyu ya fito daga cikin motar yace “But…” Murmushi Khaleel yayi yace “You don’t worry Umma ma na ciki with Shureim” Aliyu yace “Ohk then” Daga haka Khaleel ya nufi motarsa dake waje yayi parking, Aliyu ya kalli khadijah yace “Come down Iman” bude motar tayi ta fito tana mamakin me Umma kuma ta xo yi nan tare da Shureim, ta xagayo inda yake tace “Where is this please, and why are we here?” Yana shafa kansa yace “Xumunci muka xo…” gate ya nufa ta bi bayansa har suka shiga babban gidan, a tare suke tafiyar har suka iso entrance din babban gidan, haka kawai khadijah taji gabanta na faduwa, Aliyu ya juya yana kallonta ya sakar mata murmushi yace “Gidan ku ne nan Iman, gidan yayar mahaifiyar ki” Wani kallo ta dinga masa tace “Wace mahaifiyar tawa?” Ya sauke idonsa yace “Ur late Mum” daga haka ya shiga parlorn da sallama ta bi sa da kallon mamaki, juyawa yayi ganin bata shigo ba tana tsaye bakin kofar yayi kasa da murya yace “Come in plss Iman” yana fadin haka ya juya yana kallon mutanen dake xaune parlorn, very many of them, iyaye da yara, da kyar khadijah ta iya daga kafa ta shiga parlorn abinda ya fada na sinking kanta, Wai yayar mahaifiyar ta, how is that bayan ko Umma ma bata san dangin mum dinta ba? Kan jawahir dake xaune kasa kusa da Mahaifiyarta idonta ya fara sauka, Jawahir ta yi saurin sauke idonta kasa, Khadijah ta dinga bin mutanen dake xaune parlorn da kallo har idonta ya sauka kan Umma, Shureim dake jikin wani dattijon mutum ya taho da gudu ya rungume ta yana murmushi yace “Antyna” buda ido khadijah tayi ganin Safeenah da su Deejah, Safeenah ta mike da sauri ta iso inda khadijah take tana murmushi ta rungumeta hawaye cike idonta tace “Welcome sister” murmushi kawai khadijah ta iya yi bata ce mata komai ba xuciyarta na bugawa, Safeenah ta ja ta har xuwa cikin parlon, bin bayansu Aliyu yayi ya durkusa nan gefen wani guy da baxai wuce sa ba ya gaida mutanen dake parlorn, suka amsa duk a sanyaye, gaba daya occupant din parlorn kallon khadijah kawai suke, lkci daya Mahaifiyar Jawahir ta fara kuka, jikin khadijah yayi sanyi, ta isa gun Umma ta durkusa, Umma na murmushi a hankali ta kamo hannunta tace “Greet them khadijah, iyayen ki ne nan gaba daya xaune parlorn” Hawaye ya cika idon khadijah tana sake kallon mutanen parlorn, Umma tayi kasa da murya tace “Yes daughter, they are ur families” mahaifiyar Safeenah ta mike trying hard to control her tears tace “Come over daughter, come to me” mikewa khadijah tayi ta nufeta, matar ta rungumeta hawaye na sakko mata tace “Allah ya ji kan Maryam ya yafe mata kura kurenta, you are truly a carbon copy of her daughter… Allah ya albarkace ki, mun ji dadi da Allah ya sada mu da ke tun a duniya, it’s really sad sai yanxu muke sanin ‘yar kanwarmu, jinin kanwar mu, duk da ba laifinmu bane ba haka muka so ba, amma there is always a reason behind everything, it’s great meeting you daughter” ita dai khadijah bata ce komai ba jikinta yayi sanyi sosai, Hajiya Rahmah ta xauna ta xaunar da ita kusa da ita tana share hawayen ta, jawahir dai ta kasa dago kanta ganin yanda mahaifiyar ta ke kuka yasa ita ma hawaye ya dinga xuba idonta, sai dai duk kukan mahaifiyar jawahir bai kai na mahaifiyar Maimoon ba immediate din Mum din khadijah, kuka take kamar a lokacin taji mutuwar kanwartata, komai ya dawo mata sabo, a karo na farko Alhaji Abbakar mahaifinsu Safeenah kuma babban yayansu late mahaifiyar khadijah gaba daya… yyi gyaran murya ya bude wajen da addu’a, yana murmushi yace “Alhamdulillah for the gift of life, Alhmdllh for a day like this, Alhmdllh for everything… Sure it’s a privilege meeting with our daughter again after so many years…” kallon Khadijah yayi yace “Come over dear” Tashi tayi daga kusa da Umman su Safeenah ta dawo kusa da shi a sanyaye ta xauna kasa, da farko kasa cewa komai yayi kuma hakan na da nasaba da kamannin khadijah na mahaifiyar ta, bayan wani lkci yayi karfin halin yin murmushi yace “Khadijah kina yar shekara biyu rabon mu dake, sai yanxu bayan shekara ashirin Allah ya sake hada mu, kwarai kuwa babu wanda kika sani cikin mu kamar yanda mu ma bamu san ki ba, da xa mu hadu a hanya sai dai ki wuce mu wuce, which is a great shame” ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, nuna mata sauran maxan da ke parlorn su kusan uku xaune kusa da shi yayi da wanda yake kan one seater yace “Kin ga wa en nan gaba daya” ta daga kai a hankali tana kallonsu gaba daya, yace “Duk iyayen ki ne khadijah, they are all ur parent, and they are all here because of you, duk mun bar abubuwan da muke muka taho daga garruwa daban daban domin ki, gaba daya nan da kika ganmu yayyin marigayiya Maryam ne, mahaifiyar ki, ke din mai gata ce khadijah, kina da gatan ki” cikin rawar murya tace “Toh me yasa ni ban san ku ba, me yasa ba a nuna min ku ba, me yasa ba ku nemeni ba” tana fadin haka ta hade kai da kujera tana kuka sosai, Ya dafata cikin sanyi yace “Mahaifin ki Allah ya masa rahama shi ya raba mu da ke tun bayan rasuwar mahaifiyar ki khadijah, mun so rike ki ganin ba shi da yan uwa mata, amma sai yayi tunanin rabasa da ke muke son yi, Allah ya gafarta masa, mun samu matsala a kan hakan da shi, which contributed to his keeping u away from us for many years, a Abuja suka xauna da mahaifiyar ki, bayan rasuwar ta ne ya siyar da gidansa na Abuja ya dawo kano without even our knowledge, kin ji dalilin da yasa baki san mu ba khadijah, Kuma da mun san inda familyn mahaifin ki suke da babu abinda xai hana mu xuwa gare ki, sai dai yau ta dalilin mijin jawahir mun yi reuniting da ke….” Khadijah bata dago kanta ba hawaye na ta xuba idonta, Alhaji Usman yace “Wannan baiwar Allah da ta rike ki bisa amana tamkar yar da ta haifa cikinta Allah ya saka mata da gidan aljanna…. Mun ji duk kalubalen da kika fuskanta a rayuwa saboda maraici, bayin Allahn da suka tsaya maki through all the hardship Allah ya biya su da aljanna, it’s really sad daughter, don kina da gatan ki, Amma ba komai haka Allah ya kaddara, Allah ya jin kan iyayen ki ya gafarta masa, ya kuma raya maki yaron ki, ya albarkace auren ki…. In sha Allah gatan da baki samu ba da yarintar ki xaki samu da girman ki, we will always be there for you daughter, uwar mu daya ubanmu daya da Mahaifiyar ki… Allah ya ji kanta” Khadijah ta dago tana share idonta a hankali tace “Ameen, nagode Abba” Gaba daya sai da aka mata introducing din cousins dinta da niece a parlorn, yawanci duk suna yanayi barin da matan, Safeenah da Maimoon kuwa kamanninsu ba a magana dama, har sannan Jawahir ta ki dago kanta daga karshe ma wucewa sama tayi, it was really a happy day for Khadijah jin ta cikin yan uwanta gaba daya, kuma a ranan ta fara ganin hoton mahaifiyar ta, bata taba sanin haka relatives ke da dadi ba sai ranan, da tun farko tasan da su tasan baxata wahala a rayuwa ba but that’s her fate and she is happy with it, Aliyu bai jima gidan ba ya wuce ya bar ta, Umma kuma sai kusan azahar ta wuce ta bar Shureim ma gidan, Khadijah na daki tare da su Safeenah da deeja dake ta labari tayi tagumi tana kallonsu tana murmushi jawahir ta shigo dakin, suna hada ido ta sunkuyar da kai a hankali tace “Khadijah ki xo ku gaisa da Doctor xa mu wuce yanxu” Mikewa khadijah tayi tace “Toh” ta dau hijab tace ma su Safeenah tana xuwa sannan ta fita, Dr Ayman na xaune parlor tare da Shureim dake jikinsa ta shigo tana kallonsa murmushi dauke fuskarta tace “Ina yini Doctor” murmushin ya mayar mata yace “Alhmdllh khadijah” ta isa har gefensa ta xauna a kasa tana kallonsa cikin sanyi tace “I am very happy for ur effort in uniting me with my relatives doctor, Allah ya saka da alkhairi, I will never forget you in my life…” Kasa ci gaba tayi ta sunkuyar da kai hawaye na sakko mata, ya dinga kallonta a sanyaye, ta dago da kyar bayan ta goge idonta don bata son Shureim ya gani tana dubansa tace “This is among the greatest thing that have ever happened too me doctor, I really owe both you and Barrister, Kun haskaka min rayuwata kun taimakeni a lokacin da nake bukatan hakan, I don’t know how to pay you both” ya d’an yi murmushi yace “May be that was why God brought you into my life, just to unite you with ur late mum’s family, There is always a reason for everything you knw… Don haka kawai ki gode Allah ba ni ba” Kai ta gyada masa tana share hawayen da ya ki tsaya mata, ita dai jawahir na tsaye gefe a sanyaye bata ce komai ba, yace “Amma nan xaki kwana yau koh” A hankali tace “Ban sani ba tukun” yace “Alryt then, mu xa mu koma yanxu, and in sha Allah gobe xa mu koma Uk” ta kallesa a sanyaye tace “Toh Allah ya kai ku lafiya” mikewa yayi ya daga Shureim dake kallo yace “Sweetheart xa mu tafi yanxu je wajen Anty” ya bata fuska yace “Uncle ni xan bika plss” jawosa khadijah tayi tace “A’a xa su je da nisa” kuka ya fara yi ya koma gun Khaleel yace “Uncle plss” sai a sannan jawahir tace “Mu tafi da shi mana don Allah” Khaleel ya kalleta sannan ya kalli khadijah yace “Can we?” Shiru ta d’an yi sai Kuma a hankali tace “But his…” Sai kuma tayi shiru, Khaleel na murmushi yace “His dad bai sani ba koh?” kasa cewa komai tayi kuma bata dago ba, yace “Toh kira sa ki gaya masa nasan baxai hana ba” ba musu ta dau wayarta dake jikinta ta shiga kiran Aliyu, bayan wani lkci ya daga yace “Iman…” Tace “Wai Dr Ayman xa su tafi da shureim can they?” Murmushi Aliyu yayi yace “Sure” tace “Toh” daga haka ta katse wayar tana kallon Khaleel tace “Yace toh” Murmushi Khaleel yayi yace “Alryt then, sai mun hade a uk, sai ki gaya ma grandparents dinsa mun tafi da shi, I mean all his grannies cos he have a lot…” daga haka ya dau Shureim dake murmushi yana daga mata hannu suka fita da jawahir dake bin su a baya don ta sallami iyayenta, khadijah ta bi su da kallo har suka fita, kafin tayi murmushi ta mike a hankali ta wuce sama…..

  • Noor Al Hayat 70

    Sai kusan karfe uku saura Baby ta tada Khadijah tayi sllhn azahar ganin lkcnsa na ta wucewa kuma da alamar ta samu saukin jikinta sosai ganin she is sleeping peacefully…. Khadijah ta mike xaune da kyar, xuwa lkcn kam ciwon da ta dinga ji daxu da safe a xuciyarta ya rage sosai, sai dai gaba daya taji gaba daya she is weak kanta ya mata nauyi, Tana kallon Baby cikin sanyi tace “An daura auren koh Baby?” Tana magana ne hawaye cike idonta, Baby ta kasa ce mata komai… Ta hade kanta da gado cikin rauni tace “Matar nan xata iya kashe ni wllh, nobody want to consider me, nobody is willing to understand what I mean, Baby tsoron ta nake.. ” Baby ta kauda kanta bata ce komai ba sai dai wani mugun tausayinta ta dinga ji har ranta, Bayan wani lkci a sanyaye baby tace “Ki tashi kiyi sllh Khadijah, lkci na wucewa” Khadijah Bata ce komai ba ta sauka saman gadon tana kokarin ganin bata bar hawaye ya sakko mata ba, kamar iska xai kadeta ta shiga bathroom, khadijah na idar da sllh Baby ta fiddo mata daya daga kayan biki da aka dinka mata, tana kallonta persuasively tace “Plss Iman put on this ko baxa kiyi kwalliya ba, am begging you” Khadijah tayi murmushin karfin hali bata ce komai ba, Bayan wani lkci ta mike ta shirya cikin tsadadden lace din, Baby na murmushi ta wara ido tace “Waow kin ga yanda kayan suka maki kyau kuwa Iman, plss ki bari ko powder in shafa maki, just it” khadijah bata mata musu ba, duk da har xuciyarta bata so, daga powder baby ta lallabata ta sa mata har eye pencil da chappete, sosai Khadijah tayi kyau just like the bride she is, Baby ta daura mata dankwali tana kallonta da sha’awa, Frnd din Umma ce ta shigo dakin da warmer din abinci ganinta tace “Kai maa sha Allah ko ku fa? Da xa ku bari wata kishiya can ta bata maku wannan ranan, show her she is a liar bata isa ba ne, sai ma mun je kai ta gidan tukun” Murmushi kawai Baby tayi tana kallon khadijah da ta ki dago kanta. Tun bayan da suka bar masallaci bayan an daura auren Aliyu ke rike da kan sa a mota, su biyar ne motar, Khaleel na driving, Dr Yusuf na xaune gaban motar, sai Barrister da Aliyu da Farouq a baya, tun da suka dau hanya Sudais ke danna wayarsa bai dago ba shi ma, the journey was very silent da alama kowa da abinda ke ransa har suka iso dai dai kofar gidan su Khadijah, Khaleel yyi parking a hankali ya kashe motar, Shi ya fara sauka sannan Farouq da Dr Yusuf, Aliyu ya sauka sannan Sudais ma ya fito yana mayar da wayar sa Aljihunsa, ganin xai shiga ciki Aliyu ya riko hannunsa yana kallonsa da idanuwansa da suka kada sosai, Barrister ya kasa hada ido da shi, Da mugun karfin hali yace “Barrister… am still confuse, I think am yet to understand the meaning of the drama that took place at the mosque minutes back, ka ganar da ni don Allah, I am confuse plss, nayi tambaya a mota kun kyaleni…” Sudais dai bai iya yace komai ba, Dr Yusuf ya rungume hannayensa yana kallon Sudais don Aliyu bai ma kai sa confusion ba, jiran abinda Sudais din xai ce shi ma yake, shi dai yasan daurin auren abokin nasa ya xo tun daga Yobe sai kuma ya ga otherwise, Farouq dai murmushi kawai yyi ya jingina da mota ya rungume hannunsa, khaleel ya tako har gaban Aliyu yana kallonsa, bayan few seconds yace “What is it that u don’t understand Aliyu?” Aliyu ya kallesa a hankali yace “Everything…. I… I don’t get everything” Khaleel ya shafa kansa cikin sanyin murya yace “The fact is that, Kai xaka gyara abinda ka 6ata doctor, we think this is just the best for the both of you, Barrister Aliyu ya sadaukar maka ba don baya so ba sai don la’akari da our today’s world, kwanciyar hankalin khadijah ya fi masa auren ta…..” Sai a sannan Sudais yyi murmushin karfin hali yana kallon Aliyu a sanyaye yace “I have no option… She is dear to me… Ita din abar tausayi ce, they are a lot of challenges ahead for her and the little boy in dai ba gidan ka suke ba, I don’t wish that for her, and her condition don’t need that, shi yasa na hakura domin farin ciki da kwanciyar hankalinta, nasan I am not making a mistake giving up for you because I know you love her also, and u love ur son…da dadewa na yarda da cewa abinda ya faru tsakanin ku tsautsayi ne, it’s not ur doing coz you are too responsible for that, u are responsible in every aspect, you are really a gentleman, ur family are just good also, kawaicin ka ma abun dubawa ne, I’ve studied you for long….” Aliyu ya runtse ido maganganun Sudais na yawo kansa kamar a mafarki, lkci daya ya bude idanuwansa, kawai ya rungume sa hawaye na xuba idonsa ya kasa cewa komai, Sudais da ya ji xuciyar sa ya masa rauni yyi karfin hali yace “It’s my pleasure, and a Suggestion from Dr Ayman…. nayi ma Khadijah wanda ya fi wannan ma, don haka nasan ban fadi ba, But ina neman alfarmar ka bar mu mu din ga xumunci sosai coz I love the little boy…” Cike da karfin hali hawaye na sauka idon Aliyu yace “How will I repay you Barrister…” Sudais yayi murmushi shi ma hawayen suka xubo masa a hankali yace “Ta hanyar rike Amira da amana, be her father be her mother, be her happiness, and finally prove to her that u are innocent, kadarrar ku ce a haka” Khaleel ya sauke idanuwansa a hankali ya juya ya shiga gida ganin he might not stand it anymore…. 😭

     

    Lunch, very light also, kar mutum yaje yana bacci da rana😎

  • Noor Al Hayat 78

    Ta fi 10 seconds a tsaye ganin babu haske a dakin, bata kunna wutan ba saboda akwai d’an hasken na corridor kuma a bude ta bar door din, ta nufi gaban mirror a hankali don ajiye wayar hannunta, lkci daya ta juya jin an rufe kofar dakin duhu ya gauraye ko ina, saurin ajiye wayar tayi ta nufi kofar tana cewa “Why is that….” Xaro ido tayi ganin kamar nufota yake yi ta dinga komawa baya kamar xata yi kuka tace “Meye haka Aliyu, ka bude min kofa in fita, I only brought you ur mobile phone” murya can kasa yace “Why did you pretend you were sleeping” jingina tayi da banga xuciyarta na bugawa ta marairaice tace “Laifi ne don na kawo maka wayarka? to ka bani in mayar I thought you need it ne dama” Yana d’an murmushi yace “Better… dauka ki mayar” tace “Toh ka matsa” a hankali ya koma gefe idonsa a kanta, ta taho xata wuce gabanta na faduwa kawai ta ji ya fixgota xuwa jikinsa ya rungumeta gam, jikinta ya dau bari tace “Wayyo na shiga uku, meye…” Bai bata damar karashe abinda xata ce ba ta xaro ido tana kallon kwayar idonsa, passionately yake kissing dinta, tun tana kokarin kwace kanta har tayi give up, lkci daya jikinta ya mutu gaba daya ta ji ta kasa tsayuwa, bata ankara ba bayan lokaci me tsawo sai ganin su ta tayi saman gado, jikinta ya dau rawa a tsorace tana girgixa masa kai hawaye na sakko mata tace “Noo Aliyu, I still haven’t forget the experience, it’s always fresh, don Allah kayi hakuri, and….” kasa ci gaba tayi tana kuka a hankali, Aliyu da lokaci daya ya bar abinda yake jikinsa yayi sanyi, ya kai bakinsa kunnenta cikin sanyin murya yace “And… what?” Cikin shessheka tace “You didn’t follow the teachings of our prophet” komawa yayi a hankali ya kwanta ya lumshe ido yana maida numfashi, ta rufe kanta duvet har sannan hawaye ya ki tsaya mata gabanta na faduwa, a tunaninta yayi bacci don an dau lkci me tsawo bai motsa daga yanda yake kwance ba, a hankali ta mike ta maids wears dinta, xata fita ya mike ya jawota ya rungume cikin sanyin murya yace “I am… sorry Iman” ita dai bata ce komai ba, ita dai bata ce komai ba tayi lamo jikinsa, yana jin yanda xuciyarta ke bugawa, bayan wani lkci ganin ta nutsu ya kwantar da ita a hankali ya sauka daga kan gadon ya shiga bathroom, har bacci ya dauketa bai fito ba. Da asuba ta ji ana shafa fuskarta a hankali ta bude ido, murmushi ya sakar mata yana kallonta yace “It’s time for prayer” Rufe ido tayi da sauri don ya kunna fitilan dakin, yana murmushi yace “In kashe wutan?” Cikin sanyin murya tace “Yes plss” mikewa yayi ya kashe, sai a sannan ta mike xaune a hankali, ya dinga kallonta cikin duhun, Bata yarda ta tashi kan gadon ba ta kallesa tace “Toh baxa ka je masallaci ba?” Yace “We just finished now” Turo baki tayi ta mike tace “Toh ni ba nan xan yi alwalan ba” yace “Saboda me?” Bata ce komai ba ta nufi kofa, ya mike da sauri ya rufe yace “Cinye ki xan yi a nan din?” Kamar xata yi kuka tace “Ka bude min plss” yace “Sai kin yi a nan” tace “Baxan yi ba” yace “Why?” Tace “I have my reasons, kuma ba dole bane ai” murmushi yayi yace “Baki son in ga kin yi wanka?” Xaro ido tayi tace “Kamar ya?” Yace “kamar yanda nayi jiya” ta hade rai tace “Ka bude min Aliyu” yace “Toh tafi bathroom kiyi wankan ki a can” ya fadi hakan yana nuna mata bayin sa, a fusace tace “Ce maka nayi wanka xan yi, a kan wani dalili xan yi wanka” Murmushi yayi ya koma kan gado ya kwanta yana kallo ta cikin duhun, ta fi minti goma tsaye tana masa magiya amma ya ki budewa, ta fashe da kuka daga karshe ta durkushe wajen, ya mike yana dariya ya bude kofar yace “Toh tafi kiyi wankan ki” sai da ta fita tace “Ba wanka xan yi ba sai dai swim” daga haka ta shige dakinta ta rufe tasa makulli, turo baki tayi ta shiga bathroom dinta tayi wanka ta dauro alwala ta fito. Tana ta xaune kan darduma har gari ya waye ta mike a hankali ta shiga gyara dakinta ta wanke har bathroom sannan ta fito parlor don gyaran gidan, sai kusan karfe takwas da rabi ta gama ta shiga kitchen, Irish ta deba tana fere wa, Jin kamshin da ya ziyarci kitchen din ta juya a hankali tana kallon bakin kofa, tsaye ta gansa ya jingina da kofar ya rungume hannunsa yana kallonta, sauke idonta tayi ta ci gaba da abinda take, ya karasa cikin kitchen din ya tsaya bayanta, murya can kasa yace “Good morning Iman” kasa cewa komai tayi, kuma bata juyo ba ta ci gaba da peeling din Irish da take, har ta gama yana tsaye bayanta, a hankali ta juyo suka hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, jawota jikinsa yayi yana kallonta cikin sanyi yace “Forgive me once more for what happened seven years back Iman, I made you a mother with kids out of wedlock at a very tender age, I know this will always remain in ur memory till the end, nasan kuma da kin gan ni sai kin tuna da hakan, kamar yanda nima in dai na ganki I do felt guilt deep inside me, I want us to get rid of that Iman, I want to have peace with you as my wife, nasan baxan iya biyan ki irin wahalan da kika yi ta dalilina ba, but forget the past plss let build our new home Iman, i promise to love you till the end, I promise to be by ur side till the end, nayi alkawarin xame maki haske a rayuwar ki till the end, I never bargained for this Iman, Allah ya gani na so haskaka maki rayuwar ki xuwan ki gidanmu, na so maki duk abinda xan yi da baxa ki yi maraicin iyayen ki ba, sai dai muna namu Allah kuma na nasa, kaddara kuma ta riga fata, kuma a matsayin mu na musulmai we have to accept it either good or otherwise, all we have to say now is Alhamdulillah” Bata iya ta dago ba hawaye ya dinga xuba idonta, a hankali ta xame kanta daga jikinsa ta juya masa baya trying her best bata fashe da kuka ba, Juyawa yayi a sanyaye ya fita kitchen din, Bata da wani kuxari ta karasa duk abinda take ta juye ruwan shayi a flask sannan ta fita da breakfast din gaba daya dining ta ajiye, kwance ta gansa kan 3 seater idonsa lumshe, ta karasa cikin parlorn tana kallon sa, Bata taba yarda cewar yara na kama da mahaifinsu hundred percent sai a kan kids dinta, the resemblance is just too obvious, har ta isa kusa da shi bata sani ba, ta durkusa gefensa tana ci gaba da kallonsa a sanyaye ta kamo hannunsa, lkci daya ya bude manyan idanuwansa ya mike xaune yana kallonta shi ma, wasu sabbin hawayen suka cika idonta ta sauke kanta kasa a hankli tace “Toh ni me yasa basu yi kama da ni ba?” Da mamaki ya dinga kallonta, ta mike xata bar wajen ya jawota jikinsa yana murmushi murya can kasa yace “The kids?” Ta gyada masa kai hawayen idonta suka xubo, ya rungume ta sosai ya lumshe ido yana shakar kamshinta yace “Next one’s xa su yi kama da ke in sha Allah” kwace kanta tayi ta hade rai tace “Next what?” Bude ido yayi, yyi dariya yace “Next kids mana” wani kallo tayi masa ta turo baki ta mike ta nufi dining ya bi ta da kallo yana dariya kasa kasa, sai da ta isa nan ta juyo tana kallonsa taga kallonta yake shi ma, a hankali tace “Breakfast…” ya mike yana murmushi ya iso dinning din, kanta a kasa tace “Do you still take coffee?” Yana kallonta yace “Sure…” kitchen ta wuce ya bi ta da ido ta dawo da coffee powder ta hada masa ta ajiye gabansa a hankali, sannan ta debar masa Irish da kwai ta ajiye masa tare da bread, ya wara ido yace “Duk ni kadai wife?” Bata ce komai ba ta hada nata shayin ta xauna tana sha, a hankali ta dago kai suka hada ido, kasa daina kallonsa tayi kamar yanda shi ma ya ke kallonta babu kiftawa, tasowa yayi ya dawo kusa da ita cikin sanyin murya yace “Billah Ina son ki Iman” ta sauke idonta bata ce komai ba. Karfe sha daya tana dakinta Aliyu ya shigo yace ta shirya xa su fita, lkci daya mood dinta ya canxa, dariya yayi don ya ma san dalilin hakan, ya karasa kusa da ita ya xauna gefenta yace “Baxan kai ki inda xa kiyi kuka yau ba, sai dai kiyi na farin ciki wife” ta turo baki kamar xata yi kuka tace “Ni ko daya bana so, am going no where…” ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace “xa ki so wannan in sha Allah ummu Shureim, I am giving you 100% assurance” a hankli tace “To xa mu dauko Shureim daga nan?” Kamar jiran tambayar yake ya girgixa kai da sauri yace “Nooo” da mamaki tace “Why?” Murmushi yayi yana kallon kwayar idonta yana shafa sajensa a hankali yace “Baxai bari in gwada maki yanda nake son ki ba anjima, he will be a barrier…” Wani kallo ta dinga masa tace “Ni dai yau yarona xai dawo, ba ruwana” Yar dariya yayi yace “Inaa sai na gama tabbatar maki da soyayyata anjima..” daga haka ya mike ya nufi kofa yace “Am waiting for you downstairs Iman, don nasan baxa ki shirya gabana ba” yana fadin haka ya juyo ya kalleta ya kashe mata ido ta bi sa da ido har ya fita, Aliyu yana ta xaune parlor yana jiran ta, message ya shigo wayarsa, dauka yayi ya bude yana duba address din da Dr Ayman ya turo masa, ajiye wayar yayi ya jinginar da kansa jikin kujera, shi kam har sannan ya kasa daina mamakin khadijah, he couldn’t believe it, bai taba xaton xata hakura ta sauko da wuri ba haka har ta kulasa duk da maganganun Anty khadijah, he never expect that from her, murmushi kawai yyi tunawa da yayi kilan yana cin albarkacin yaransu ne that she is seeing in him, but he will surely teach her to love him not because of the kids, sakkowa tayi stairs sanye da hijab har kasa babu abinda ta shafa fuskarta banda powder sai chappete a lips dinta amma har wani glowing take, she is just the definition of true beauty, ya mike yana murmushi a hankali yace “Kin yi kyau wife” sauke idonta tayi har ta iso parlorn, ya isa har gabanta ya duka yayi pecking lips dinta a hankali, ta hade rai tana goge bakin tace “Bana so” yana murmushi yace “Toh yi hakuri na bari” daga haka ya kama hannunta suka fita, sai da suka bar gidan a motarsa suka hau saman titi tana kallonsa a hankali tace “Ina xa mu je plss Aliyu?” Kallonta yayi na few seconds sannan ya dauke kai, murya can kasa yace “Yanxu baki jin kunyan kiran sunana Iman?” Ta hade rai tace “Toh me xan kira ka?” Ya langwabar da kai yace “Sai ki sakaya even because of Shureim, though nasan I don’t deserve that” jikinta ne yyi sanyi ta tuna yanda take kiransa seven years back, a hankali ta kallesa taga driving dinsa kawai yake ta sauke idonta tace “Toh xan ce maka Yayan Baby” murmushi kawai yayi bai ce mata komai ba kuma bai kalleta ba, bayan wani lkci yace “Ohk then” sun fi 10 mins babu wanda yace komai tayi breaking silence din, ba don shirun dake motar ba da ba lallai ma yaji abinda tace ba coz it’s very low, “Or Abu Shureim” abinda ta fada kenan sai kuma ta dauke kai kamar ba ita ta fada ba.

    Kinda very busy yesterday shi sa aka ji shiru, sorry for the short update, ltr xan yi wani in sha Allah. Tnx for understanding.🤗

  • Noor Al Hayat 63

    Noor Al Hayat 63

    Shiru Jiddah tayi ta tallabi chin dinta tana kallonsa lkci daya kuma tana murmushi, Sudais ya hade rai yace “Magana fa nake maki jiddah?” Ta tabe baki tace “Amira na ba ta kai maka daki, kaje ka tambaye ta” wani kallo ya dinga mata yace “Amirar xaki ba files jiddah?” Cikin halin ko in kula tace “Ita, ko bata isa aike bane, Beside if they are that important ai baxa ka bar su yashe a dinning area ba” Girgixa kai yyi ya juya ya fice daga dakin, tayi wani murmushi mai sauti tana girgixa kafarta, lkci daya murmushin yayi fading a fuskarta, da ajinsa, da kyansa, da iliminsa da kudinsa duk fadin duniyar nan ya rasa warce xai kawo mata matsayin kishiya sai warce ta taba cikin shege ta haife yaran… Wani dariya ta kwashe har da kyakyatawa ta mike tana wani murmushi tace “Abomination” daga haka ta fice daga dakin, sai dai fa jin ranta take fess. Har khadijah ta fara bacci Shureim ya shigo dakin, ta dinga kallonsa har ya iso inda take yace “Anty cire min uniform” mikewa xaune tayi ta shiga cire masa uniform din jikinsa tace “Have u eaten?” Ya gyada kai yace “Uncle ya bani cornflakes” Khadijah na kallonsa tace “Are you okay with it?” Ya wara ido yace “Ehh Anty, ai da yawa ya bani, shi kuma ya sha tea” Khadijah bata ce komai ba ta dinga laluba aljihun wandon sa jin akwai abu a ciki ta fiddo Chocolate tana kallonsa tace “Wa ya baka?” ya karba da sauri yace “Aunt din nan ce ta bani, tace min xata siya min puzzles amma bata siya ba she is sick, she is even sleeping at the room” Khadijah ta ajiye kayan bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace “Anty will you go and check her?” Wani kallo ta dinga masa strictly tace “If I should slap you….” A hankali ya koma baya yace “Anty kiyi hakuri” tana hararansa ta nuna masa bayi tace “Wuce kayi alwala” ba musu ya wuce da sauri, ta mike don fiddo masa kayan da xai sa, magungunan sa da khaleel ya siyo masa daxu da safe ta basa sannan ta ce yaje parlor yayi assignment dinsa, ta hada socks dinsa xata shiga bayi ta wanke wayarta yayi ring ta dawo tana kallon wayar taga Barrister ke kiranta, ta karasa ta dau wayar ta xauna gefen gado sannan tayi pick din call din ta kai kunne, a hankali yace “Am sorry you called bana kusa Amira” tace “Ba komai, ka isa lafiya?” Yace “Lafiya Alhmdllh dear” tace “Ya Amira fah?” Yace “She’s fine, how about my son” tace “Yana assignment” yace “Ohk ba shi mu gaisa” mikewa tayi ta fita parlor ta ba Shureim wayar tace “Abba yana son maka magana” ya karbi wayar yana kallonta yace “Anty waye Abba?” Harara ta watsa masa tace “C’mon answer ur call…” ya kai kunne a hankali yayi sallama, Barrister dake jin su yayi murmushi yace “How you boy?” Yace “Am fine Abba” Barrister yace “Ka je schl yau?” Ya gyada kai yace “Ehh na je” yace “Good, always aim good grades sai in siya maka Bicycle” ya wara ido yace “My two uncles sun ce xa su siya min bicycle, kaga am having three now, sai in ajiye ma Sudais daya, in ba su fadeel daya, Ni kuma…” Khadijah ta kwace wayar hannunsa ta koma daki, ta kai kunne a hankali tace “You need rest barrister, ya kamata ka huta, hope ka ci abinci?” Yace “Me yasa kika amshe wayar?” Tace “He is talking off hook” yace “Baki son dai in san two uncles din nasa” ta wara ido tace “Aliyu da Dr Ayman yake referring as two uncles fah?” Barrister yayi murmushi yace “Alryt then” ta langwabar da kai tace “Toh ka ci abinci?” Yace “Eh yanxu xan ci” tace “Toh shkkn, kaje ka ci, a shafa min kan Namecy na” yace “Ohk, will do that in sha Allah, thanks love” daga haka ya katse wayar, tayi murmushi ta ajiye ta kwashi socks din Shureim ta shiga bayi don wanke su. Washegari gaba daya bata da lectures ranan, da wuri ta shirya Shureim ta tafi kai sa makaranta don bata son khaleel ya xo yace xai kai sa, tana dawowa ta rufe kofar ta ta wuce bedroom ta kwanta, sai kusan sha daya ta tashi daga baccin da tayi, yunwan da take ji yasa ta wuce kitchen don neman abinda xata ci, ta kunna gas ta daura ruwa ta dauko indomie da kwai taji kamar motsi a baya, ta isa gun window ta tsaya kafin ta leka a hankali, tsaye ta ga Jawahir… khaleel na bayanta ya rungumota fuskarsa dai dai nata, yana d’aga karamin weight da hannu daya, Khadijah ta sauke idonta a hankali ta juya ta bar wajen, kashe gas din tayi ta fice kitchen din gaba daya ta wuce daki ta kulle ta fada kan gado. Ta fi awa uku a haka, har lkcn sllh yayi ta kasa tashi, cike da karfin hali ta mike daga karshe tana runtse ido ta shiga bathroom ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta sa hijab ta dau karamar jakarta da waya ta fita, tana kokarin rufe apartment dinta Khaleel ya fito, bata kalli inda yake ba ta gama rufewa ta juya xata wuce yana kallonta yace “What’s wrong with you Khadijah, are u sick….” da kyar tace “No, i am okay” daga haka ta wuce waje ya bi ta da kallo, cab ta tsayar a waje ta shiga, kawai gani tayi ya ajiye ta schl, ita dai bata san ya aka yi ta ce masa can xata ba, ta fito ta basa kudinsa ta wuce ciki, cafteria ta nufa direct tana shiga ta xauna ta hade kai da table jin numfashinta na sama, ba a dau lkci ba Maryam ta shigo cafterian da frnds dinta xa su ci abinci, tana ganin Khadijah ta gane ta duk da kanta a kife yake har lkcn, ta isa kusa da ita tace “Hi Khadijah are u okay?” Da kyar Khadijah ta dago kanta, Maryam ta dinga kallonta ganin yanda idonta ya kada tace “Subhanallah baki da lafiya ne?” Kasa bata amsa Khadijah tayi, kana ganinta kasan she is in pain, Maryam ta fiddo wayarta a jaka da sauri ta shiga kiran Aliyu sanin yana within area din makarantar, Yana dauka tace “Ya Aliyu kana kusa ne plss, yanxu na shigo cafteria naga Khadijah kamar bata da lafiya, and she is not even responding, ko xaka taho yanxu plss….” Bata gama maganar ba Aliyu ya katse wayar, ta ja kujera ta xauna kusa da Khadijah tana kallonta da damuwa tace “Sannu Khadijah” frnds dinta turawa sai sannun suke mata su ma, Aliyu ne ya shigo cafterian ya karaso kusa da ita da sauri yana kallonta yace “Iman…. what’s wrong, are you okay?” Tun Khadijah ma ganinsa bibbiyu a gabanta har daga karshe ta daina ganinsa kwata kwata, Bata sake bude ido ba Kuma sai can kusan magrib ta ganta kwance kan gadon asibiti, dafe kirjinta tayi ta dinga bin dakin da kallo, a hankali idonta ya sauka kan Aliyu dake xaune kusa da ita ya jinginar kansa da kujerar da yake kai idonsa a lumshe, kokarin tashi ta shiga yi hakan ya sa shi bude ido, da sauri ya mike ya dawo kusa da ita da damuwa yace “Stay still Iman kinga ruwa ne a hannun ki, how are you feeling now?” ta kalli drip din hannunta har sannan tana rike da kirjinta da kyar tace “It’s hurting me” yayi kasa da murya yace “Kiyi hakuri xai daina Iman you are still under medication, koma ki kwanta plss” taki kwanciya ta hade kai da gadon, hawaye ne ya shiga sakko mata, a hankali yace “Iman?” Ta ki dagowa, hakan yasa ya tsaya yana kallonta cike da tausayi, cike da karfin hali ya ji tace “What about shureim….” Yana kallonta murya can kasa yace “I went to pick him in the evening na tarar neighbor din ki ya je ya dauke sa” Bata ce komai ba kuma bata dago ba yace “Let me call a nurse… Ina xuwa” daga haka ya fita dakin, ita dai har sannan bata dago ba hawaye kawai take kamar an bude tap, tare da wata baturiyar nurse ya dawo, ta duddubata ta fita, a hankali Aliyu yace “Iman kukan me kike plss?” ta kallesa hawaye na ci gaba da sakko mata ta kasa cewa komai, rikicewa yayi ya dawo kusa da ita sosai, yace “Don Allah Iman tell me whats wrong, me ya faru, me ne ke damun ki? Ur Bp isn’t encouraging, ur condition don’t need this, Tell me what ur problem is Plsss, ko an maki wani abu ne” ta goge idonta a hankali bata ce komai ba, Bude kofar ward din aka yi Maryam ta shigo tare da mum dinta, Hajiya Mariya ta karaso da damuwa tace “Sannu Khadijah, ya jikin naki yanxu?” a hankali cikin sanyi tace “Da sauki Mumy, Ina yini” Hajiya Mariya tace “Lafiya lau, Ina Shureim din” Aliyu yace “Neighbor dinta ya dauke sa schl daxu” Maryam ta ajiye basket din abincin hannunta tana kallonta tace “Allah ya sauwake murya can kasa Khadijah tace “Nagode Maryam” Hajiya Mariya tace “Nan xata kwana, ko xa su yi discharging dinta?” Aliyu yace “Sai gobe da safe” Hajiya Mariya tace “Toh shkkn sai Maryam ta kwana tare da ita” Shiru Aliyu yayi ya rasa me xai ce don bai so haka ba, Hajiya Mariya ta ja kujera ya xauna ta bude basket din don debar ma Khadijah abinci, sai kusan karfe takwas ta bar asibitin tare da Aliyu ba don ya so ba, suna fita babu dadewa wayar Maryam ya fara ring, dauka tayi ganin Jawahir ke kiranta ta d’an wara ido ta daga kafin ta ce komai taji muryar khaleel, xaro ido tayi tace “Ina yini Dr?” Yace “Lafiya lau ya kike, I want to ask plss Maryam, Kun hadu da Khadijah schl yau?” Maryam tace “Gata nan ai muna asibiti bata da lafiya, she collapsed daxu a cafteria but da sauki yanxu she’s recovering” khaleel bai san lkcn da ya mike ba, jawahir dake kwance Shureim a gefenta dai sai kallonsa take, ya jira har Maryam tayi shiru kafin a hankali yace “Wani asibitin ku ke?” Ta fada masa sunan asibitin yace “Toh xan xo yanxu” daga haka ya katse wayar, yana kallon jawahir yace “Xan je duba Khadijah clinic yanxu she is sick, I will be back soon” jawahir dai bata ce komai ba ya nufi kofa, Shureim ya sauka daga kan gadon da sauri yace “Uncle ni xan bi ka” jawahir ta jawo sa jikinta tace “Don’t worry yanxu xai dawo” a parlor khaleel ya dau makullin motarsa ya bar gidan ya nufi asibitn da Maryam ta gaya masa, yana parking a haraban hospital din ya fito ya kira Maryam don da wayar jawahir ya taho, Maryam na daga kiran yace “Ina waje Maryam” ward number ta fada masa yace “Thanks” daga haka ya katse wayar ya shiga asibitin, ya fi seconds talatin a bakin kofar ya kasa budewa, can ya murda a hankali ya shiga ward din, Kwance Khadijah take idonta lumshe, Maryam ta mike ganinsa tace “Sannu da xuwa Dr” yace “Yauwa Thanks” karasowa yayi bakin gadon yana kallonta, Maryam tace “Ina jin ta koma bacci” shiru yayi bai ce komai ba yana kallonta har lokacin don yasan ba bacci take ba, he really want Maryam to excuse them but he don’t know how to make the approach, kamar kuwa Maryam tasan abinda ke ransa ta mike ta dau wayarta tace “Doctor bari inyi making wani call in dawo yanxu” ya kalleta yace “Alryt” daga haka ta nufi kofa ta fita ta rufe kofar, ya lumshe ido ya bude ya xauna gefen gadon ya kamo hannunta ya kai fuskarsa dai dai nata a hankali yace “I know you are awake Khadijah, look at me plss”