Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 60

Sponsored Links

Ranan lahadi da safe Khadijah ta raka Sudais Airport, har ranta ta dinga jin kewarsa bayan ya tafi duk jikinta yayi sanyi, tana tsaye inda xata hau cab a wajen airport din kamar ance ta kalli gefenta taga khaleel tsaye alamar fitowarsa kenan shi ma daga cikin airport, farar shadda ce jikinsa sai walkiya take, Khadijah ta dauke kai da sauri tun kan ya kallo inda take ta karasa gun cab da ta gani ta shiga ta fada ma driver din inda xata. Suna isa gida ta fito ta basa kudin sa sannan ta shiga ciki da sauri ta bude jakarta tana kokarin ciro makulli, dai dai nan khaleel ya shigo gidan, bata yarda ta juya ba ta bude kofarta ta shige. Daki ta wuce ta tattara reading materials dinta, ta dau kayanta kala biyu da nyt wear ta fito rike da jakarta, kulle apartment dinta tayi ta wuce kamar warce ake jira a waje tsabar haste din, tana fita ta samu Cab ta hau xuwa gidan Vanessa. Gaba daya ranan a gidan ta yini, sai dai she was just uncomfortable saboda mazan turawan dake xuwa suke fita gidan, gashi ba isasshen hankali gare su ba duk ta takura, ta so komawa gida da daddare amma saboda sanyi ta hakura ta kwana gidan, washegari daga gidan ta shirya xuwa sch tare da Vanessa bayan sun yi breakfast, suna gama lectures Vanessa ta sake jan Khadijah suka koma gidanta, tana xaune parlorn Vanessa bayan tayi magrib idonta a kan takardun hannunta ta jawo wayarta dake ring, number Aliyu ta gani sai a sannan ta tuna da yaronta ta yi picking kiran, daga daya bangaren yace “How are you Iman” tace “Fyn, how about my son” yace “Naga kin ma mance da shi gaba daya” ta hade rai tace “Taya xan mance shi?” Murmushi yayi yace “Toh gobe da safe xan kawo shi don ya samu yaje schl” tace “Kun dawo ne?” Yace “Yea daxu da yamma” shiru ta d’an yi kafin tace “Bring him in the afternoon” yace “Alryt then” daga haka ta katse wayar ta. Ranan talata bayan sun gana lectures misalin karfe biyu Khadijah ta koma gida, bude kofar apartment dinta tayi a hankali ta shiga sannan ta rufe, gyaran gidan ta shiga yi, bayan ta tsaftace ko ina, ta bude kofar kitchen xata xubda shara suka yi ido hudu da wata yarinya da ta xo xubda sharan ita ma, yarinyar ce ta fara cewa “Sannu” Khadijah tace “Ina yini?” Yarinyar tace ” Lafiya lau, jiya da muka xo mun duba baki nan ashe kin dawo” Khadijah ta d’an yi murmushi tace “Ehh yanxu na dawo” yarinyar tace “Ayya, to Sannu da xuwa” Khadijah tace “Idan na gama xan shigo yanxu” yarinyar tace “Toh sai kin shigo” daga haka Khadijah ta wuce ciki, Allah ma ya san ba don ranta ya so ta fada haka ba, kawai dai yarinyar ta mata kwarjini ne, and kuma sai taga kamar suna kama, toh ko dai ita ce warce su Deejah ke fadi? Tabe baki tayi ta wuce bedroom dinta, wanka tayi ta sauya kaya tayi sllhn azahar sannan ta linke Hijab dinta ta yafa mayafi ta fito, a hankali ta danna bell din apartment din khaleel, bayan wani lkci wata ta bude kofar, Khadijah tace “Ina yini” yarinyar dake ta kallonta ta bata hanya tace “Lafiya lau” shigowa parlorn Khadijah tayi gabanta na faduwa, few mutane ne parlorn kuma yawanci duk manya ne, ta durkusa jikin kujera a hankali tace “Ina yinin ku” amsa mata suka yi da fara’a, wata a cikinsu tace “Ikon Allah, ji mai kama da su Maimoon” Yarinyar da ta bude kofar tace “Wllh Anty na xata Safeenah ce ta da farko, haka na tsaya da mamaki Ina kallonta don nasan Safeenah na daki ai” Ita dai Khadijah bata ce komai ba sai murmushi da tayi, Wata mata dake kusa da ita tace “Dama haka Allah ke ikon sa ai, tashi ki shiga ciki yan mata suna can gaba daya” warce ta bude mata kofar ne ta kai ta har dakin da jawahir da yan uwanta suke, Khadijah dai gabanta sai faduwa yake ta sunkuyar da kanta, da sallama ta shiga dakin bayan yarinyar ta bude mata kofa, suka hada ido da Jawahir dake xaune gefen gado tana danna wayarta, sosai tayi kyau sai wani glowing chocolate skin din ta yake, hannayenta sun sha lalle, kai kana ganinta ka ga amarya, Khadijah ta sunkuyar da kanta, Maryam ce ta fara mikewa ganinta tace “Lah Khadijah ashe kin dawo” Khadijah ta kirkiri murmushi tace “Ehh ban dade da dawowa ba” Maryam tace “Ayya, Sannu da dawowa, ga waje ki xauna” Bata kai ga xama ba Deejah ta fito daga bayi tana ganinta ta rungume ta da murna tace “Khadijah har na gaji da jiran ganin yaushe xa ki dawo, gashi babu mai number ki, Sannu da xuwa” Khadijah tace “Ayya ni ban san jiya xa ku taho ba ina gidan frnd dita ce” A hankali Khadijah ta xauna Deejah ta xauna kusa da ita tana kallonta da fara’a tace “Mun taho rakiyar amarya” Khadijah ta kalli jawahir a hankali tace “Sannu Amarya, Allah ya bada xaman lafiya” sai a sannan jawahir ta kara kallonta babu yabo babu fallasa tace “Ameen” Deejah sai kallon jawahir take alamar bata ji dadin yanda ta amsa mata ba, ita kanta Maryam dauke kanta kawai tayi, Safeenah ta shigo dakin tace “Lahh ashe har kin shigo” Khadijah tayi murmushi tace “Eh na shigo” ta karaso ta xauna ita ma tace “Su Anty Deejah na ta labarin ki a Nigeria sai gashi yau na gan ki, kin lura da kamar da muke yi kuwa?” Dariya ta ba Khadijah, Maryam da Deejah ma suka yi dariya ban da Jawahir da ta tsuke fuska, A hankali Khadijah tace “Ikon Allah kenan” Safeenah tace “Gaskiya ne, Ammin mu na gaishe ki” Khadijah tayi murmushi tace “Na amsa sosai” hira suka dinga yi dakin banda Khadijah da sai dai tayi murmushi idan sun kallota, duk a takure take ta kagu ta tashi ta wuce amma ta kasa tashi, agogo ta kalla ganin uku ya wuce tayi karfin halin mikewa tace “Xan dan shiga ciki ina aiki ne” Safeenah tace “Amma xa ki dawo ai?” Murmushi Khadijah tayi tace “Ehh xan dawo anjima” Rakota suka yi parlor, Khadijah tayi ma wa enda ke xaune parlor sallama ta bude kofa xata fita suka kusa cin karo da khaleel, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, yanda ta daburce shi ma haka, yyi saurin bata hanya, ganin Deejah da Safeenah na bayanta tayi karfin halin ce masa “Ina yini” yace “Lafiya lau, ya gida” fita tayi daga parlorn bata ce komai ba ta bude apartment dinta ta shiga ta rufe, ganin la’asar yayi ta daura alwala a bayi tayi sallah sannan ta kwanta, bude data tayi da sauri tunawa da tayi daxu Barrister yace xai turo mata sako ta duba, ko ya bar Dubai din ma oho, ai ko tana budewa taga messages da ya turo mata da yawa, ta shiga tana kallon message din, kusan gaba daya hotuna ne, downloading din su ta fara yi, murmushi tayi ganin set na akwatuna ne yace ta xabi wanda take so, a hankali ta dinga scrolling tana duba boxes din, bbu na banxa gaba dayansu, murmushi tayi masa as reply, sannan ta tura masa message tace duk sun yi kyau sosai, daga haka ta kashe datan ta, bayan kusan minti goma sai ga kiransa, kuri ta kura ma wayar ido, can ta daga a hankali ta kai kunne hade da sallama, daga daya bangaren yace “Amira” tace “Na’am good day” yace “Thanks, I saw ur reply, kuma ni ba tambayar ki nayi ko sun yi kyau ba” Yar dariya tayi tace “Barrister amma ai kai ma kasan sun yi kyau” yace “My question is wanne kika fi so” tayi murmushi tace “Uhm ni ban san wanne xan ce ba barrister” yace “Ask ur frnds then” tace “Toh xan tambaya” yace “Ina fa jiran ki kafin gobe, don goben xan bar Dubai” a hankali tace “Toh barrister” daga haka yayi mata sallama ya katse wayar ta koma ta kwanta a sanyaye, juye juye ta dinga yi tana kokarin bata ba damuwar dake neman dirar mata a xuciya space ba, can ta mike jin ta fara jin yunwa, kitchen ta tafi ta daura ruwan xafi don tafasa na shayi, kamar ance ta leka window taga khaleel xaune waje doing nothing, hada ido suka yi tayi saurin dauke kanta ta ci gaba da abinda take, tasowa yayi a hankali ya iso kusa da windown ya tsaya yana kallonta, trying her best not to look toward his direction tace “Wishing a happy married life, Allah bada xaman lafiya” kallonta kawai yake, can a hankali yace “Khadijah” kashe gas dinta tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta nufi kofar fita kitchen din ya bi ta da kallo har ta fita ta rufe kofar. Shayin da bata sha ba kenan tana ta xaune parlor wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin me kiranta tayi picking ta kai kunne tayi shiru, “Ki fito muna waje” abinda Aliyu yace mata kenan, ta mike a hankali ta tafi daki ta dauko hijab dinta ta sa ta fita, Tana isa kusa da motar ta bude ganin bashi da alamar fitowa ta fiddo Shureim tana kallonsa, xata wuce yace “Jira ki karbi sakon Mumy” Bata ce komai ba ta tsaya ya fito ya bude bayan mota ya ciro wani leda ya bata, amsa tayi tace “Mun gode Allah saka da alkhairi” Har ta juya xata tafi sai kuma ta tsaya tana kallonsa ta basa wayarta tace “Ka sa min number ta sai in kirata in mata godiya” karbar wayar yayi ya sa mata digit din Mumy ya mika mata, ta amsa tace “Thanks” yace “Don’t forget ki tambayeta jikin Anty Khadijah idan Kin kirata” tace “Har yanxu bata samu sauki ba?” Yace “She is still at the hospital” Shiru Khadijah tayi, lkci daya jikinta yayi sanyi, can tace “Toh Allah ya bata lafiya” Yace “Ameen” Cike da karfin hali tace “Ya jikin iklima fa?” Ya shafa kansa yace “Tana can family din babanta, ban samu xuwa dubata ba coz I spent only three days kuma throughout Zaria nake ta tafiya gun Anty Khadijah” Khadijah tace “Toh Allah ya sauwake, idan muka yi hutu soon xan je gida sae in je in duba Anty Khadijah da Umma” Yace “Alryt” shiru ta kara yi, sai kuma ta kallesa tace “Ina son tambayar ka pls” yana kallonta ya rungume hannunsa yace “Ina jin ki”

Back to top button