Aliyu ya fi minti goma xaune cikin mota bayan ya iso gida, gaba daya ya rasa me ke masa dadi duniyar, har ya fita kamanninsa saboda damuwa, Mumy ta fito jin shiru shiru bai shigo ba, ganinta yasa tun kan ta karaso parking lot din yyi karfin halin bude motar ya fito kansa a kasa, kamar bai son taka kasa yake tafiya, har ya iso inda take kallonsa Mumy take cos he looks so sick, shi kam ya kasa dagowa balle ya kalleta, Tace “Abuturrab are you okay, ciwon kan ne har yanxu” ya gyada mata kai a hankali yace “Na sha magani mum da sauki” daga haka ya wuceta ta bi sa da ido, bin bayansa tayi tace “Toh bacci ka je clinic din kake yi?” Bai juyo ba yace “Eh” da damuwa tace “Maimakon ka tsaya gida ka huta Aliyu tunda baka da lafiya, da sai ka kira asibitin ka bada uxurin ka, xa ma ka iya dubata yanxu ko kawai mu wuce asibiti” tsaye yyi bakin kofa ya rasa abinda xai ce mata ya kuma kasa juyowa duk jikinsa yyi sanyi, Cike da karfin hali yace “Xan tafi asibitin da ita likita xa su duba ta a can” mumy tace “Toh kai ma gaskiya a dubaka wani irin ciwon kai ne haka lkci daya tun safe, sanusi sai ya kai ku clinic din” Bude kofa aka riga sa yi Anty khadijah dake tsaye bakin kofar tana kallonsa da kyau tace “Me ya same ka kai kuma, baka da lafiya ne?” Gefenta ya bi ya shiga gidan ba tare da ya bari sun hada ido ba yace “I am better now” Anty khadijah ta kalli Mumy mamaki shimfide fuskarta tace “Dama baya da lafiya ne Anty fati?” Mumy tace “Tun safe kafin in fita aiki yace min yana jin ciwon kai ban san wani kalan ciwon kai bane haka har yanxu, ni na xata ma baxa shi aikin ba ganin har na fita yana gida” Anty khadijah ta bi bayansa da sauri ganin har ya kai stairs, ta hada har da d’an gudunta har hakan ya ba Mumy mamaki, Tsaye Aliyu yyi bakin kofar dakin ya kasa shiga, ta labe jikin stairs tana jiran ya shiga ita ma ta shiga, a hankali ya murda kofar ya sa kai ya shiga, Tana ganin haka ita ma ta shige, Baby da ke xaune gefen Khadijah da ke kwance da damuwa tace “Yayanmu Iman bata da lafiya she is just crying, and her temperature is very high” hawaye cike idonta take magana, khadijah na jin sunan da Baby ta kira ta bude ido da sauri hade da yunkura ta mike xaune, Aliyu ya kasa kallon direction din, wani sabon kuma khadijah ta saki a raunane, Anty khadijah dai na tsaye kofa tana kallonsu, Aliyu bai iya ya kalli khadijah ba yace “Ki sa ta shirya xa mu je asibiti yanxu” baby tace “Toh” daga haka ya juya suka yi ido hudu da Anty khadijah, tabe baki tayi ta juya ta bar wajen tana cewa “Haka dai aka iya, da yar uwar ka ce ba lafiya ai baxa ka bi ta kan mu ba ma” shi dai ba ce komai ba ya fita. Hijab baby ta ba Khadijah, Khadijah taki sawa tana girgixa mata kai cikin kuka tace “Ni bana son xuwa asibitin, idan nayi bacci I will okay, baxan iya xuwa ba” baby tace “Nooo, ki sa mu tafi don Allah” kin yarda Khadijah tayi hakan yasa baby ta fita sai ga ta sun shigo tare da mumy, mumy ta karaso kusa da ita ta amshi hijab din ta sa mata tace “Kiyi hakuri ki tashi ku je asibitin kin ji, Allah ya sauke” daga haka Mumy ta dago ta, Aliyu dai na tsaye corridor yyi backing kofar, muryar Mumy ya ji tana cewa “Toh ka kai ma Sanusi makullin sai yyi driving din koh” Juyowa yyi xai yi magana amma ya kasa ganinta tsaye tare da Khadijah tana rike da hannunta, Wani mugun tausayinta ya dinga ratsa shi ganin irin karfin halinta cos he was thinking baxata iya fitowa ba, bai yarda sun hada ido ba kamar yanda ita ma kanta ke a kasa, ya fara sauka stairs Mumy ta bi bayansa tana rike da hannun Khadijah baby na biye da su a baya, Anty khadijah dake tsaye bakin kofar dakinta ta saki baki ta bi Khadijah da ido a ranta tace wa yaga boss lady, don kusan kalau take tafiyar ta, nan kuwa daga ita har Aliyun basu san mugun karfin hali take ba, she is in pain all over, only trying her best to be okay, Mumy ta bude bayan motar ta shigar da ita tasa baby ma ta xauna a baya kusa da ita, sanusi ne ya ja motar cos da gasken Aliyu bai jin xai iya tukin, har suka isa asibitin kansa na jingine da kujera, baby kuma na rungume da Khadijah da ta ki bude ido tana kukan xuci. Sanusi na parking Aliyu ya bude motar ya fita, Baby ta fito tana kallon khadijah tace “Iman ki sakko we are at the hospital” A hankali khadijah ta fito cikin motar tana rike da hannun baby, Aliyu ya kalli baby yace “Ku koma tare da sanusi” xaro ido tayi tace “Yaya but Mumy tace in tsaya da ita, wa ye xai tsaya kusa da ita idan anyi hospitalising dinta, look shes very sick fa” irin kallon da ya dade bai mata ba ya shiga yi mata a lkcn, Bata sake cewa komai ba ta shiga motar hawaye cike idonta, Khadijah ta fashe da kuka a hankali tace “Don Allah kar ki tafi ki bar ni” Baby na share hawayen ta tace “He said I shud leave Iman” Aliyu ya juya ya wuce ciki sai ga nurse ta taho ta shiga da Khadijah asibitin, sanusi ya ja motar yana ma khadijah Allah ya sauwake ya kama hanyar gida. Nurse din na rike da hannun Khadijah da ke ta hawaye ta wuce office din Aliyu da ita kamar yanda yyi instructing dinta, baya office din hakan yasa ta fito ta shiga office din kusa da nashi ta samesa xaune, ruwan xafi yasa ta fara kai ma khadijah bathroom dinsa tayi wanka sannan ya bata magunguna da alluran da xata mata, daga haka kuma ya bar asibitin, kulawa sosai nurse din ta bata don ta bata tausayi yanda ta ga jikinta duk da ba ta san takamaiman abinda ke damunta ba, tana mata alluran kuwa bacci ya dauketa nan dakin Aliyu. Aliyu na gidansa har ya samu bacci ya daukesa…. ring din wayarsa ya tashe sa, dubawa yyi da kyar ya ga Mumy ce, ya kai hannu ya daga a hankali ya kai kunne, da damuwa tace “Aliyu ya jikin Khadijah, or shud I come over naji shiru shiru” yace “Noo mum, da sauki anjima sanusi yaje can asibiti ya mai da ta gida” Mumy tace “Kai kana ina?” Ya d’an yi shiru kafin yace “Na taho nan gida na ne, I need sleep” da mamaki mumy tace “Kuma ka bar ta ita kadai asibiti gashi ka ki barin Baby ta xauna da ita Abuturrab” yace “Nurses din xa su kula da ita mum” Mumy ta d’an yi shiru kafin tace “Toh shkkn, Allah ya sauwake, kai ya jikin naka?” Yace “Alhmdllh am better now” tace “Ohk, amma da ka daure kai ka je ka maido ta gida don Allah, bbu dadi hakan kamar bata da gata, idan baxa ka ba ni in je” yace “Toh mum xan je yanxu kiyi hakuri” daga haka ta yi masa sallama ta katse wayarta. Bayan magrib Aliyu yyi wanka bayan yyi sllh ya canxa kaya ya bar gidan, yana isa clinic din ya kira nurse da ya bari da Khadijah a waya yace tayi mata alluran karshe na ranan ta fito tare da ita yana waje, nurse din tayi yanda yace sannan suka fito tare da Khadijah, bin nurse din da ke rike da hannun ta take kamar iska xae kadeta ta fadi, duk ta rame lkci daya, yana kallon nurse din bayan sun iso a hankali yace “Hope you did all what I instruct you to” nurse din tace “Yes but, I don’t knw why she’s finding it difficult to walk, kuma tun daxu take complaining chest pain, Dr bashir ya bata magani dai daxu, har da shi ma cikin wa ennan” ta fadi tana nuna masa drugs din da Khadijah xata kai gida, Khadijah dai na tsaye kanta a kasa duk a tsorace take ga xuciyarta dake bugawa da sauri da sauri, Aliyu ya gyada kai yace “Thanks nurse Maryam” Nurse din tayi murmushi ta sa Khadijah ta shiga gaban motar ta rufe tana mata Allah ya kara lfya, tada motar Aliyu yyi ya bar haraban hospital din, har suka isa gida bai ce komai ba, yana lura da hawayen da take yi tana gogewa da Hijab dinta tun bayan da suka fito clinic har ynxu da suke gida, ya gama parking ta bude motar a hankali ta fita, ya bi ta da ido ganin yanda take tafiya har ta shiga gida, sae sannan shi ma ya fito ya rufe motar ya shiga gidan. Mumy dake xaune parlor da su siyama da Anty khadijah ta mike ganin Khadijah tace “Sannu khadijah, ya jikin” Khadijah ta kasa dago kanta tace “Naji sauki Mumy” Anty khadijah sai kallonta take babbu kiftawan kirki, Aliyu na shigowa parlorn ya haura sama, Mumy ta kama hannun Khadijah ta wuce sama xuwa bedroom dinta da ita, da kyar khadijah ta iya cin pepper soup din da mumy ta mata, duk bakin ta babu dadi, a nan dakin bacci ya dauketa. Cikin dare misalin karfe biyu xaxxabi ya kuma rufe ta, dakin Aliyu Mumy ta shiga ta samesa xaune kan darduma ta xauna gefen gado ta jira ya sallame sallahn da yake da damuwa tace “Aliyu har yanxu fa jikin Iman” yace “Xaxxabin kuma?” Mumy tace “Ehh dama” yace “Mumy to ta kara shan drugs din…” Mumy tayi shiru bata ce komai ba, can tace “Toh shkkn” sannan ta mike ta fita, magungunan ta sake bata ta rufe ta da duvet sai kusan asuba bacci mai nauyi ya dauketa. Da safe tea Khadijah ta sha bayan mumy ta tilastata da kyar, da tayi ma Aliyu maganan alluranta da ya rage yace driver ya kai ta sai karfe goma shi xai fita aiki, sanusin ne ya kai ta ya maido da ita, kafin yamma taji saukin jikinta sosai sai dai ta rasa irin ciwon da take jin kirjinta ke mata, kuma hakan na faruwa ne in dai ta tuna incident din ranan sai taji mugun faduwar gaba, har lkcn Aliyu bai barin su hada ido a gidan kuma bai ce mata komai, idan tana wuri ma bai yrda ya tsaya a gun, Anty khadijah dake lura da komai har wani farin ciki da nishadi na musamman take ji a gidan, har Mumy ta dinga mamakin yar uwar tata, duk fadace fadace da xage xagen ta rage yanxu hatta Khadijah ta daina hantara nan ko shirin sake komawa inda taje kwanaki kamar yanda aka ce mata ta dawo idan ta tabbatar komai ya wakana a lkcn ma xa a fara aikin, tunanin karyan da xata yi ma Mumy kawai take ta tafi inda xata. Aliyu na bedroom dinsa da daddare baby ta shigo, ta xauna kusa da shi tace “Yayanmu I want to ask you something pleaseee” yana kallonta yace “What?” Ta langwabar da kai a hankali tace “Iman tayi maka wani laifi ne, naga you no longer talk to her, ko ta gaisheka sometimes you do pretend you didn’t hear, why please, ka gaya min me tayi maka, gashi ita ma she is always sad yanxu, I’ve caught her severally tana kuka cikin dare…” Katse ta yayi yace “Na fara wasa da ke da yawa koh?” Da sauri ta girgixa masa kai, ya hade rai yace “Toh tashi ki tafi” mikewa tayi da sauri ta fita ya ci gaba da danne dannen laptop da yake yi. Washegari da sassafe Anty khadijah ta shirya har da kwallarta take ce ma Mumy xata Abuja an kirata wai Yusuf d’anta ba lafiya yana asibiti, mumy jikinta yyi sanyi har da bata dubu goma ta hau mota, ta karba ta yi mata godiya ta bar gidan. Karfe goma saura Mumy ta tafi aiki gidan ya rage khadijah da baby sai Iklima don su siyama sun tafi makaranta, Aliyu ma na sama a dakinsa, tun bayan abinda ya faru tsakanin khadijah da Aliyu ta rage xaman cikin gidan sae Mumy na nan, always a baya xaka ganta xaune ita kadai, yau ma xaune take tayi nisa a tunanin da take kamar ance ta juya taga Aliyu tsaye d’an nesa da ita, mikewa tayi a tsorace tana komawa baya, ya dauke idonsa daga kallonta yace “Iman” hawaye ya cika idonta ta kasa amsawa, karasowa yyi kusa da ita ya tsaya tana komawa baya a hankali, yace “Za ki gane gidan step mum din ki?” Khadijah sai kallonsa take xuciyarta na bugawa, ya hade rai yace “Am asking” a hankali tace “Kila in gane” yace “Ohk… Am coming back now” daga haka ya juya ya koma ciki, ba a dau lkci ba ya dawo, envelope ne rike hannunsa ya mika mata taki amsa gabanta sai faduwa yake, yace “Collect it” hannunta na rawa ta karba, yana gyada kai yace “Go Iman, go back to ur step mum, I can’t continue my life the way I want living with you in the same roof, you are now a barrier to my happiness pls ki tafi Iman go anywhere, leave our home, bana son Ina ganinki ina jin haushin kai na cos nobody is above mistake, just go plss” A hankali ta juya masa baya hawaye na sakko mata tace “Ohk xan tafi… thank you very much for all what you’ve done to me throughout my stay in your home, Allah saka maka da alkhairi duk hidiman da ka min, but ina neman alfarmar ko xan iya yi ma Mumy sallama kafin in tafi, don ban mata hallaci ba idan na tafi bata sani ba” a takaice yace “Noo, just go Iman” ta fashe da kuka sosai tace “Ohk nagode” juyawa yyi ya nufi cikin gida… Sai kuma ya juya da sauri yana kallonta yace “And one more thing… Forgive me plss” ta juyo hawaye na sakkowa idonta tace “I have done that already” yace “Thank you” daga haka ya juya ya shiga ciki ya rufe kofa. Share hawayen idonta da ya ki tsayawa ta dinga yi, dama Hijab ne jikinta kawai ta nufi gate ta fita gidan, da kafa ta karasa bakin titi ta samu napep tana kallonsa a hankali tace “Tasha xaka kai ni” yace “Toh” daga haka ta shiga napep din, har suka isa tasha bata sani ba tayi nisa a tunanin da take, mai napep din ya dawo da ita duniyar tunanin da taje, sai a sannan ta tuna kudin da xata basa, da sauri ta leka cikin envelope din da Aliyu ya bata taga kudi ne me yawa a ciki ta xaro dubu daya hawaye na sakko mata ta shiga tashar ta nufi inda taji ana kiran kano, dama mutum daya ake jira tana shiga motar ta bada kudinta bbu bata lkci suka dau hanyar kano.
Author: Novels
-

Noor Al Hayat 22
Karfe hudu duk yaran gidan suka gama shirin tafiya islamiyya, kyauta ta hada socks dinsu gaba daya da Uniform din autar Mumy da ake kira da Baby saboda sunan Anty khadijah gareta xata wanke, kallon khadijah dake tsaye kanta tayi tace “Toh ni dai kin tsaya min kamar soldier ki tafi can dinning area ki kwaso duk plates din wajen, saura kar kiyi a hankali” khadijah tace “Toh” sannan ta wuce ciki, bbu kowa dinning area din sai plates da shinkafa da aka yi littering a wajen, Khadijah na ganin Anty khadijah a parlor xaune tana gyara ma Baby Hijab tayi saurin dauke kanta ta shiga hade plates din waje daya, muryar daya daga yan matan parlorn taji tana cewa “Anty wacece wancan yarinyar wai?” Anty khadijah ta tabe baki tace “The new housemaid” Baby ta xaro ido tace “Anty is kyauta going?” Anty khadijah tace “Noo she is not” Baby ta sauke ajiyar xuciya tace “Better… coz I don’t think i like that girl, she can look for Africa as a whole” horn da driver yake yasa Siyama da Aneesah suka mike rike da jakar islamiyyarsu suka ma Anty khadijah sallama suka fita, Anty khadijah tace “She’s not even worth talking to, don hka bbu ruwanki da ita yar aikin gidan ce kin ji takwara” baby tace “Sure” khadijah ta turo baki tana kallonsu, baby ta harareta ta fice daga parlorn, khadijah ta ki daukan komai a dinning din ta fita gun kyauta da gudu tana kumbure kumbure, kyauta tace “Ina kwanukan?” Ta fashe da kuka tace “Anty mai girki kinga yarinyar nan har da neman tsokanana koh, shine har da ce min I can look for Africa where as she was the one looking at me, kuma Anty mai ihu tace mata ni house girl ce” Kyauta ta tabe baki ta nuna mata wani dakali tace “Tafi can ki xauna, ni dai ba ruwana idan kina kallon yan gidan nan sai su dake ki ma su daki banxa nima ba kyaleni suka yi ba gwara babyn ma a cikinsu, idan ba iskanci ba… Ba aikin aka kawo ki kiyi ba har xa ki ji haushi don an ce maki house girl?” Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, kyauta ta gama wankin ta tafi ta kwaso plates din ta gyara dinning din, khadijah ta hada ma kayan wanke wanken can bakin tap kar ta jika kitchen din ita kuma ta shiga girka dinner, da ta leka sai ta ga kamar ba a wanke wanken, daga karshe fixgota tayi bakin tap din ta turata waje daya ta shiga wanke wanken tana bala’i, khadijah ta toshe baki kar tayi dariya jin har da kiranta lazy ass, har kusan magrib khadijah na kusa da kyauta a kitchen komai kyauta ta sauke kan wuta sai ta ba buda mata hannu xata d’an d’ana tun kyauta na mata da mugunta tana konata da cokalin miya har ta gaji ta kyaleta sai ta xuba mata a d’an karamin plate, kyauta ta samu wani roba ta xuba duk pepper soup din da tayi mai yawa a ciki bata yi gigin ba khadijah ba tace “Tafi ki leka su waye a parlor” khadijah ta dawo tace “Ba kowa Anty mai girki” kyauta ta fita da sauri ta bude dakinsu ta ajiye masu bayan kofa sannan ta dawo ta jera komai kan dinning bayan ta ba khadijah na su Usman mai gadi ta kai masu, Kyauta na gama tsaftace kitchen suka wuce daki da Khadijah, sai a sannan ta xauna ta fixgo khadijah tace “Ke bakya sallah ne hala?” Khadijah tace “Ina yi amma bani da Hijab yanxu” turata bayi kyauta tayi tace “Ni ina da shi ai” Khadijah na xaune kan dankwalin da kyauta ta shimfida mata ta yi sllh tana ta kallon kyauta dake addu’a ta idar da sallahn ita ma, Muryar Mumy kyauta taji ta shafe addu’ar ta mike da sauri ta fita khadijah ma ta bi bayanta da sauri, Mumy tace “Ki xuba ma Aliyu abincin xai wuce aiki yanxu, ku kun ci abincin?” Kyauta tayi kasa da kai tace “Xan xuba masa yanxu Hajiya, mu kuma yanxu xa mu xuba” Mumy tace “Toh sai ki debar maku har da farfesun” Kyauta tace “Toh mun gode Hajiya” Mumy tace “Toh ya tana kokarin aiki kuwa ita?” Mumy ta fada tana nuna khadijah, kyauta tace “Ehh ba laifi Hajiya” Mumy ta juya tace “Toh shkkn” A dinning kyauta ta dibar ma Aliyu nasa abincin a plate ta xuba masa farfesun kaji sanin bai cin sauran, sama ta tafi kai masa khadijah ta biye da ita, ta kwankwasa masa kofa ba a dau lkci ba ya bude yana buttoning din shirt din jikinsa, kyauta tace “Ga abinci yallabai” kallo daya yyi masu ya karbi tray da kyauta ke mika masa yace “Nagode” khadijah tace “Nan ne dakin ka” bai ce komai ba ya rufe kofarsa, kyauta ta ja khadijah suka sauka ta shiga daki da ita ta hade hannayenta biyu tace “Ke wai dan gidanku ina ruwan ki da likitan gidan nan, kin taba sanin sa ne idan ba shisshigi ba?” A hankali tace “Kiyi hakuri” kyauta ta ja bakinta da karfi hade da dungurinta tace “Sai na cire maki wannan mayun idon naki wllh idan kika sake yi ma kowa magana a gidan nan” khadijah ta gyada mata kai hawaye cike idonta, kyauta ta fita ta bar jin alamar su baby sun shigo gidan daga makaranta. Ko kafin kyauta ta sallamesu ta dawo ciki har khadijah tayi bacci, tashin ta ta shiga yi ta ci abinci cikin magagin bacci take cewa Umma na koshi, kyauta ta debo ruwa ta yarfa mata a fuska, da sauri ta farka gaba daya kyauta ta ajiye mata abincin a gabanta ta shiga bayi don yin alwala, ko da ta fito Khadijah bata ci abincin ba ta koma bacci, hakan yasa tace “Ke kika sani” dagata tayi ta kwantar ta xauna cin abincin ita kafin tayi sallahn. Washegari kyauta na idar da sallah ta fita daura breakfast, ta gama fere dankalin turawa Anty khadijah ta shigo kitchen din, kalle kalle ta shiga yi kafin tace “ina wannan yarinyar take?” Kyauta tace “Ina kwana Anty?” Anty khadijah tace “Lafiya, ina yarinyar nace?” Kyauta tace “Na aiketa daki shiru shiru” fita Anty khadijah tayi ta bude kofar dakin kyauta tana yatsine fuska, kwance ta tadda khadijah shame shame kan gado, karasawa tayi ta maka mata duka har sau biyu a baya, khadijah ta farka a rikice, Anty khadijah ta fixgota tace “Ko yan gidan gaba daya ma sun tashi bare ke shegiya, a hakan xa ki iya aiki a gidan nan, a kirga har dubu goma a bai ma iyayenki jiya ki yi ma mutane shame shame kina bacci kan gado har yanxu?” Khadijah ta sauka kan gadon hawaye cike idonta tace “Anty kiyi hakuri” fixota Anty khadijah tayi ta turata waje da karfi tace “Fita kije ki kama ma kyauta aiki, ko ita din baiwar ki ce, ina ce yanda ake biyanta haka ake biyan ki kema” khadijah ta wuce kitchen da sauri tana hawaye, Anty khadijah ta biyota har kitchen din tace “Maxa hada wanke wanke ki fita ki yi” da sauri ta dinga fita da plates waje hawaye na sakko mata, ita dai kyauta bata ce komai ba har Anty khadijah ta fita kitchen din, khadijah ta dau cups uku xata fita da su, kyauta tayi tsaki tace “Mata ta ki xaman aure duk ta xo ta addabe mutane a gida tirrr, ke kuma ai kinga result din bacci kamar matatcciya” khadijah dai bata ce komai ba ta fita, Kyauta ce tayi wanke wanken bayan ta sallami yan makaranta khadijah na mata dauraya, karfe tara da rabi mumy ta sakko xata fita aiki, bayan sun gaisa da kyauta dake hada mata breakfast a dinning mumy tace “Ina khadijah” Kyauta tace “Tana can tana shara Hajiya” Mumy tace “Ohk” kyauta ta koma kitchen bayan ta gama hada ma mumy shayi sanin gimbiya na can sama tana ta bacci yanxu haka, Kallon khadijah tayi da tasa dankali da kwai da shayi a gabanta ta ki ci, Kyauta tace “Au baxa ki ci ba?” Khadijah ta kalleta tace “Ina ci” sai kuma ta fara kuka, Kyauta tace “Samun waje, wato duk da lafiyayyen abincin nan dake gaban ki har kuka kika samu daman yi koh? Kila ma a gidan da kika baro baki samun irin haka” khadijah ta mike tana kuka ta daga rigarta tana nuna ma kyauta bayan ta tace “Anty mai girki har yanxu fa xafi wajen da ta dokeni yake min” kyauta ta buda baki ganin shatin hannun Anty khadijah a bayanta, can tace “Tabdi, toh Allah ya isan ki, kuma in sha Allahu a baxawara xata Karachi rayuwarta, ni kam ko yanxu na bar gidan nan nasan xan samu mijin aure, ita kuwa wllh sai dai taga ana yi, kuma ina jin ita ma ta bar ‘ya yanta a wani gidan to haka xa ayi ta cin ubansu ana gallaza masu in sha Allahu” Kyauta ta sauke rigar tace “Maganinki kenan kema dai, gobe ba sai kin jira an tashe ki ba” daga haka kyauta ta ci gaba da aikinta, da sauri kyauta ta fita jin mumy xata wuce gun aiki, ta gama sauraren abinda mumy ke ce mata ta risina tace “In sha Allah Hajiya, Allah ya tsare hanya” tsaye jikin kofa Mumy ta hango khadijah tace “How are you” a hankali khadijah tace “Good morning maa” mumy ta kalli kyauta tace “Anya baki cika ma yarinyar nan aiki kuwa kyauta?” Da sauri kyauta tace “Wallahi ko daya Hajiya, ki tambayeta bana cika ta da aiki” Mumy tace “Ohk” sannan ta mayar da dubanta kan khadijah tace “Am off to work, hope kin yi breakfast?” Ta gyada kai tace “Nayi Anty” Mumy tace “Good” daga haka ta nufi kofa, kyauta ta rakata tana mata Allah ya kiyaye, Mumy na fita da motar ta kyauta ta koma kitchen ta kwashi sauran kayan wanke wanke ta tafi wankewa a waje, khadijah na ta tsaye bakin kofar kitchen din Aliyu ya shigo gidan, tun da ta kallesa bata sake kallonsa ba har ya wuce sama, bayan kusan minti ashirin sai ga shi ya sakko, har lkcn khadijah na gun da take a tsaye, ya shiga kitchen din ya hada abinda xai hada a cup ya fito har ya wuce ya juyo ya daure fuska yace “Baki iya gaisuwa ba koh?” Ta turo baki tace “Good morning” daga haka ta juya ta wuce gun kyauta a waje, ya kusa second ashirin a tsaye kafin ya juya ya wuce sama. Ruwan wanka kyauta ta hada mata bayan sun koma daki, khadijah tace “Anty mai girki ni fa ban yi brush ba kika bani abinci” kyauta tace “Ni na hanaki brush?” Khadijah ta langwabar da kanta tace “Toh su fauxiyya sunyi lost din min brush dina a gidansu” kyauta tace “Oho dai tafi kinyi wanka ga ruwa can” khadijah na fitowa daga wanka kyauta ta bata Vaseline ta shafa sannan ta fiddo mata da daya daga kayan ta da ta linke bayan ta kwaso mata su jiya, khadijah tace “Anty mai girki kinsan wa ya siyo min new pants din nan” kyauta tace “Oho” khadijah tace “My lovely Umma” kyauta bata sake kula ta ba ta fixgota ta lafta mata uban kwalli a ido ta shafa mata farin powder a fuska sannan tace “Wuce can baya ki xauna kar ki shigo gidan nan sai na kira ki na gaji da surutun ki” khadijah tace “Toh” sannan ta fita, dakalin da ta saba xama ta xauna bayan ta tsinka flowers da yawa ta dinga yin jakar hannu da su kamar yanda aka koya masu a schl da dadewa, kamar ance ta daga kai suka hada ido da Aliyu dake kallonta, ta dauke idonta ta ci gaba da abinda take, bayan wani lkci ta daga kai bata sake ganinsa xaune balcony din ba, gajiya da xama tayi ta shiga ciki ta bude kofar kyauta a hankali ta ganta kwance tana bacci, shiga tayi ita ma ta kwanta gefenta nan da nan bacci ya dauketa. Da yamma Mumy na xaune parlor da Anty khadijah da ita ma dawowarta gidan kenan tun daxu da ta fita, khadijah ta fito daga daki bayan ta ajiye kayan kyauta da ta bata, mumy ta kirata ta karasa parlorn ta durkusa tace “Anty gani” mumy tace “Meye da meye bbu a kayan ki?” Khadijah tayi shiru tana naxari, can ta fara lissafo su da fingers dinta tace “I don’t have toothbrush and toothpaste, I don’t have towel, I only have six pants da ummata ta siya min sauran fauxiyya ta sace min, even ves bani da shi, kuma bani da mai da xan shafa, Anty har da na gashina” murmushi kawai Mumy take, Anty khadijah kuwa ta hade rai kamar bata taba dariya ba, Aliyu dake dinning yana cin abinci tabe baki kawai yyi, mumy tace “Toh in ga kan naki” khadijah ta xame hular kanta Anty khadijah ta saci kallon dogon gashin, mumy tace “Kai maa sha Allah ran Saturday sai ki bi su Siyama kema a gyara maki koh” da sauri khadijah ta xauna a tsorace tace “Anty ummata ta gyara min ai, it’s just of recent ta kai ni saloon” Mumy tace “Anjima driver xai kawo maki duk abinda baki da, kina da takalmi koh?” Ta gyada kai tace “Amma ya kusa tsinkewa su fauxiyya suke sa min” mumy tace “Toh tashi kije xa a siya maki” khadijah tayi murmushi tace “Toh Anty I like you” daga haka ta wuce kitchen gun kyauta da sauri. Mumy na kallon Anty khadijah da har lkcn ranta a bace yake tace “Khadijah am thinking ko in sa yarinyar nan a islamiyya su dinga xuwa tare da su baby da yamma, kowa ya ganta yasan she is from a wealthy home, it’s just condition….” Katse ta Anty khadijah tayi tace “Anty fatima ki raba kanki, Anty Fatima ki raba kanki ki kyale mutum yanda kika gansa na sha gaya maki times without number, su wa enda suka kawo ta gun aikin sun fa pi ki sanin akwai islamiyya, me yasa kike son sa ma kanki matsala ne wai, tsinannun masu aikin nan da kiris suke jira su tura wanda ya kyautata masu cikin rana, meye hadin ki da yarinyar idan ba shisshigi ba da neman wajen xama??” Mumy ta kalli Aliyu dake ta kallonsu tace “Abuturrab yanxu don nace ayi enrolling din baiwar Allahn nan a islamiyya laifine don Allah?” Ya mike yace “Noo, ba laifi bane mum, sai ma lada da xa ki samu in sha Allah” daga haka yayi wucewarsa sama, Anty khadijah ta bi sa da wani mugun kallo, mumy tace “Atoh, baka san yanda Allah xai yi da naka ba gobe, baka kuma san ina reward din ka yake ba, yarinyar nan tare da ke take gaya mana ita marainiya ce, to don me baxa a ji tausayinta ba, kika san kudin iyayenta a da, don duk wanda yaga yarinyar nan yasan ba daga karamin gida ta fito ba, just put little baby in her shoes… Kin dai ga sa’anni ne su din daga ganin, to da baby ce ta shiga irin halin nan yaya xa ki ji, Allah ya rufa min asiri don dai kudin islamiyya xan iya biya mata, toh ni ban san meye damuwarki ba khadijah” Tsaki Anty khadijah tayi ta mike ta nufi stairs tana cewa “Muna nan da ke sai kin yi da kin sani Anty, shi kuma Aliyu ya ci gaba da daure ma karya kugu, daga ganin yarinya shegiya ku hakikance ku ce a sa ta a Islamiyya for what reason, shi aka aikota yi gidan nan” Mumy tace “Aniyar ki ta bi ki khadijah, shi yasa kike samun matsala da kowa a rayuwa ni dai baki yo halin mahaifanmu ba Allah ya ji kansu, nima ba halin mu daya ba, tirr”
-

Noor Al Hayat 33
r kanoline take ta kalle kalle tsaye a bakin titi, duk mai adai daitan da ya tambayeta inda xata sai dai ta kafe sa da ido nan kuwa tunanin da take daban, hadarin da ya shiga haduwa a garin ne yasa ta dawo reality, da kanta ta tafi gun wani mai napep a hankali tace “Tudun yola xan je” yace “Dai dai ina a tudun yola” tace “Idan mun je xan gane” Bata damu da kudin da ya kira mata ba ta shiga adai daitan suka dau hanyar anguwar da ta kira masa, tun suna hanya aka fara yayyafi har suka kawo Tudun yola, ita dai ta san ranan da suka taho daga katsina da ummanta taji ta ce ma mai napep Tudun yola to amma bata san ina a Tudun yola ba, tun mai napep na biyeta suna xaga anguwar har yyi parking yace “Bani kudi na ki sauka, ke da baki san inda xa ki ba kika sa na dauko ki” sauka tayi daga cikin napep din ta basa kudin da yace daga cikin envelope ya bata canjinta ya ja adai daitan sa yyi gaba, hawaye ya cika idonta ta saka kai gabas tana ta tafiya, to ina xata ga gidan ummanta, jin ruwan ya taho da karfi yasa ta samu yar rumfa ta tsaya, ta kusa minti talatin tsaye karkashin wajen, kowa ya shige gida, wasu kuma sun shiga shagunansu saboda ruwa hanyar kamar anyi shara, ita kadai ce a waje ga wani sanyi da ta dinga ji, an dau fiye da awa daya ana ruwan kafin ya tsagaita sai yayyafi, fitowa tayi daga inda take tsaye ta ci gaba da tafiya a gajiye, bata yi wani nisa tana tafiya ba taji ance “Lahh Mama dubi yarinyar nan mai kukan kitso” Juyawa tayi taga wata mata ce da ‘yar ta da suka hadu a saloon ranan da Umma ta kai ta gyaran gashi, uwar ta rankwashi yarinyar da baxata wuce Khadijah ba tace “Toh ina ruwanki salon tsokana” matar tace “Sannu yan mata” Khadijah ta gaisheta ta amsa ganin xata wuce tayi saurin cewa “Anty don Allah ban san hanyar gidanmu bane, ko xa ki kai ni gun mai saloon din nan ta san ummata” matar ta saki baki tace “Baki San hanya ba kuma, daga ina kike haka?” A hankali khadijah tace “Daga kano nake na mance hanyar gidan ne” Matar dake ta yi ma khadijah kallon mamaki tace “Ikon Allah, sai dai saloon din da nisa daga nan gashi da sauran hadari, amma mu je mu hau adai daita sai in ajiye ki shagon” Khadijah ta d’an risina tace “Nagode Anty” daga haka ta bi matar da ‘yar har suka isa inda masu adai daitan suke, ta fadi inda xa su sannan suka dau hanya, kamar yanda matar ta fada bbu laifi tafiyar da nisa, suna isa saloon din suka tarar mai saloon din ta fito xata rufe shago ta wuce gida saboda ruwa, Matar suka gaisa da mai saloon din sannan tayi mata bayanin Khadijah, mai saloon din tace “Tab, to ai gidan Hajiya Amina da nisa daga nan, cikin ruwan nan yaushe mutum xai fara takawa xuwa gidan ai sai dai adai daita” Matar tace “Toh don Allah ki taimaka ki dau adai daitan ki kai ta gidan idan ya so mamartata sai ta baki kudin adai daitan da kika biya” mai saloon tace “Sai dai haka” daga hakan suka yi sallama da matar Khadijah tayi mata godiya, wani adai daitan mai saloon ta samu suka shiga har kofar gidan Umma, a nan hankalin khadijah ya kwanta ta dinga kallon kofar gidan, khadijah ta sauka tana murmushi tace “Anty nagode xan je in karbo maki kudin napep din” daga haka khadijah ta shiga ciki da sauri, bbu kowa tsakar gidan saboda ruwan da aka yi, Khadijah ta kwankwasa kofar parlorn Ummanta a hankali, Bude kofar Umma tayi tana tambayar waye? Umma ta xaro ido hade da bude baki tace “Khadijah??” Rungumeta khadijah tayi cike da farin ciki tace “Ummata” Umma ta ja ta suka shiga ciki da mugun mamaki tace “Daga ina kike haka” a hankali khadijah tace “Kaduna Umma” Umma tace “Ke da wa?” Khadijah tace “Ni kadai Umma ki ban kudi in kai ma mai adai da ita a waje, mai saloon din nan da kika kai ni ranan ce ta rakoni, ban san gidan ba” Umma ta dau kudi ta fita da sauri, Godiya tayi ma mai saloon din ta ba mai adai daitan kudin kawo ta da yayi da mayar da ita da xai yi sannan ta koma ciki. Umma ta dinga kallon khadijah tana share hawayen da ya ki tsaya mata a sanyaye bayan Khadijah ta gama yi mata bayanin duk abinda ya faru tun daga ranan da ta bar ta gidan yakumbo har ixuwa yanxu da take gabanta, abu daya ta boye mata a labarin da ta bata shine kuma abinda ya shiga tsakaninta da Aliyu kawai dai ce mata tayi yace ta tafi saboda Anty khadijah bata sonta, Khadijah ta share hawayen dake sakko mata ita ma cikin rawar murya tace “Umma me yasa baki son in xauna a wajen ki, don Allah kada ki sake kai ni ko ina, let me stay with you plss” ta fashe da matsanancin kuka tana kallon Umma da ita kanta ba karamin rama tayi ba, Umma tayi gathering courage ta jawota jikinta a hankali tace “Khadijah ba laifi na bane kinga kishiyoyina ba kirki ne da su ba saboda su ya sa na kai ki gun yakumbo amma ta ci amanata ko don ba uwar mu daya ba, da wani mugun gidan ta kai ki haka xa a cutar min ke ina nan ban sani ba, har kadunan naje kwanaki in duba ki aka ce ai ta tashi a gidan, gashi bbu wanda yasan inda ta koma, haka nayi kwana biyu kafin in dawo nan kano, duk layukan ta basa xuwa har na gaji na daina kira, kullum fatana shine Allah yasa kuna lafiya ashe abinda ta maki kenan, to Allah ya saka maki, ita kuma wannan baiwar Allah da ta rike ki a gidan ta har na wnn lkcn Allah ya saka mata da alkhairi” Khadijah dake ta sauraren ta a hankali tace “Ameen” Umma ta mike tace “Bari in karbo maki abinci a makwabta bani nayi girkin gidan ba” daga haka Umma ta fita parlorn, khadijah ta jinginar da kanta da kujera a sanyaye, kadan ta ci shinkafa da miyar da Umma ta amso mata ta sha ruwa sannan ta fita yin alwala don ta yi sallah, Shafah da fitowarta kenan ita ma ta saki baki tana kallon khadijah, can ta kwalo ma Hasana kira, Hasana ta fito ita ma, Shafah tace “Kin ga ashe bak’i muka yi a gidan yau” a hankali khadijah ta gaishesu, dariya Hasana tayi tace “Lallai kam bak’i” daga haka ta juya ta koma bangarenta, Shafah ma ta wuce ciki tana dariya. Khadijah na xaune kan darduma bayan ta idar da sallah, Umma dake yankan alaiyahu alamar dai ita xata amshi girki tace “Kina ji na khadijah, babu ruwan ki da mutan gidan nan ki rufa min asiri kinji, duk me xa su maki kar ki tanka su, ko don Alhaji ya bar ki ki xauna gidan nan” Khadijah ta gyada mata kawai, mikewa Umma tayi ta fita da alaiyahun waje sai da ta shiga kitchen ta kira Abban fadila, yana dauka bayan ta gaishesa tace “Alhaji dama alfarma nake son tambaya gun ka” yace “Ina ji” tace “Dama khadijah ce xata xo ta d’an kwana biyu nan, sun yi hutu idan ba damuwa don Allah” Yace “Toh kin gaya ma su Shafah?” Shiru Umma tayi bata ce komai ba, yace “Sai ki sanar da su don bana son abinda xa a xo ana min tashin hankali a gida” daga haka ya katse wayarsa, Umma ta ajiye wayarta a sanyaye , ko wace irin rayuwa ce wannan ta fada yanxu ita kam, tun da tayi auren nan bata da kwanciyar hankali sannan kamar warce aka daure kafarta a gidan tana xaune a hakan har lkcn. Fita tayi ta tafi dakin Shafah ta samesu tare da Hasanar daga nan bakin kofa ta tsaya tace “Sannun ku, Khadijah ta xo daxu daga kaduna nace in gaya maku…” Shafah ta mata wani kallo tace “Au haba, to ta sha kabo…” Hasana tace “Lallai kam, sannunta da xuwa” juyawa Umma tayi ta fita ta koma kitchen ta daura girkin tuwo a gas, ko da Umma ta koma parlornta dauko maggi bacci ta tarda Khadijah na yi kan kujera, ta tasheta ta shiga daki ta hau gado, abu daya yasa ta jin hankalinta ya kwanta game da Khadijah, kuma shine yanayin da ta ganta, kowa ya ganta yasan bata tare da wahala sai dai ‘yar ramar da tayi. Sosai Khadijah tayi kokarin ganin bata kula duk yaran gidan ba kamar yanda Umma ta yi mata huduba duk da irin cakalarta da suke yi a satin ta daya a gidan, ita kanta Umma hakuri take da kowa na gidan don kamar warce aka rufe ma baki komai suka mata bata tankawa duk ta yi sanyi kamar ba ita ba, Shafah da Hasana wani mulki na musamman suke xubawa a gidan, sai abinda suka ce ayi ake yi ga ikon bala’i… A can Kaduna kuwa, kamar wasa aka nemi Khadijah a gidan aka rasa har yamma, Mumy da farko ita a tunaninta ko Aliyu ne ya fita da ita don har ta tanadi rashin mutuncin da xata yi masa amma tana kiransa yace mata shi bai fita da ita ba, na hankalinta ya tashi sosai ta dinga tambayar baby ko iklima ta yi mata wani abun ne don Anty khadijah bata nan balle tace ita ce, shi kam Aliyu dama yana tabbatar da Khadijah ta tafi ya wuce clinic, ganin yanda mahaifiyarsa ta ishesa da kiran ba a ga Khadijah ba yasa shi komawa gida, and he tried his best pretending he knws nothing about her disappearance. Islamiyyar da Umma tayi ma khadijah register ta ci gaba da xuwa a kano, abu daya ke damun Umma yanxu a kanta shine irin sanyin da tayi kamar ba lively khadijahr ta ba, sanyin kuma ne yasa ko kadan abinda ake mata a gidan bata kula wa duk da idan ta fita islamiyya tun safe sai yamma take dawowa gidan. Kwanan khadijah talatin da ‘yan kai a gidan Umma ne ta fara fito da wani habit na bacci, ko me take yi sai ta fara bacci a kai, islamiyya ma idan taje duk bacci take, hakan yasa wani lkcn bata dadewa xata dawo gida, Umma da abun ya fara isarta ranan ta bar mata kaya ta linke tana shigowa taga tana bacci kan kayan, duka ta kai mata tace “Wai lafiyar ki kuwa Khadijah, wannan wani irin bacci ne?” Khadijah ta farka a firgice tana mitsika ido, Umma ta harareta tace “Tashi ki je kiyi sallah bana ma son linkin kuma, wani iskanci komai aka sa ki sai ki buge da bacci” mikewa khadijah tayi a hankali ta fita bayan ta dau butan Umma, Hasana dake tsakar gida ta cika gidan da radionta Shafah kuma na kitchen suka bita da harara a tare, babu abinda ke kona masu rai a gidan irin yanda Umma da khadijah ke kin kulasu a gidan, duk da ita Umma sun san ba banxa ba rashin kulawar, to ita khadijah fa, Hasana tace “Ohh daga Hutu dai sai kuma aka rashe” Shafah dake juya miyar ta na yakuwa dake kan wuta tace “Ke ma dai kya gani, dama yau nake son tambayar Alhaji dalilin da yasa xa a munafurce mu ayi mana karya, ai sai ace mana ta dawo nan din ne da xama ba wai a mayar da mu yara ba” Hasana tace “Yara ko dai shashashai, bari dai ya dawo din ma ji dalilin rainin hankalin” Khadijah dake durkushe kasa sai yamutse fuska take ta dalilin kamshin miyar Shafah da ya kauraye tsakar gidan, mikewa tayi da sauri jin cikinta na hautsinewa ta juya xata koma parlorn Umma taji amai ya taho mata, dawowa tayi ta durkushe wajen ta dinga kwarara amai Shafah da Hasana aka yi tsit daga mita da habaicin da suke suna kallonta.
-

Noor Al Hayat 39
✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨
Daga wannan rana Khadijah ta daure ta fara koyon yanda xata kula da yaranta tunda Mama suwaiba ta wuce, shi ma din ba a son ranta ba kawai sbda sudais take yi, amma har lkcn ta ki basu nono sai dai madara, Sudais ya san kula da yara har biyu xai mata wahala saboda karancin shekarunta amma ya bar ta a haka to see if kusancinta da yaran xai sa ta hakura ta fara sonsu but kamar kara sa mata kinsu ake, komai xata masu sai tayi complain wani lkcn har da kukanta, bbu abinda ke mata takaici sai irin yanda suke hanata bacci cikin dare wani lkcn, duk da during the day kusan sudais ke masu komai, yayi dedicating time dinsa gaba daya ma twins din kamar mara aikin yi, a ranan da Mami tayi querying dinsa na biyu kan ina yake xuwa baya dawowa gida sai kusan sha biyun dare kuma ya fita da sassafe tsabar confusion yace “Mami ni wlh fa yawanci ina gidana, can nake xuwa” Mami da tayi shiru tana kallonsa tace “Kana gidan ka? To ai xan je gidan wataran” shiru sudais yyi jikinsa yyi sanyi gabansa ya shiga faduwa, kasa bacci yyi darren ranan ya rasa me ya kai bakinsa gaya ma Mami wai gidansa yake xuwa, kuma yasan Mami xata aikata xuwa can gidan nasa din, kafin washegari yayi deciding kawai barin gidan don yasan its not longer safe keeping khadijah and her twins in there anymore, misalin karfe tara na safe ya gama hada duk abinda xai bukata a travelling bag dinsa ya shiga dakin Mami gabansa na faduwa, bayan ya xauna gefen gado a hankali yace “Mami dama ina da wani case da xan yi a Abuja yau, kiyi hakuri sai da xan tafi nake gaya maki” Mami dake ta kallonsa ganin yanayinsa tace “Sai kuma yaushe?” ya sosa keya a hankali yace “Kai Mami ai ina jin daga can ma xan wuce Lagos, aiki da yawa ne gaba na, but in sha Allah soon xan dawo idan na gama, ke dai ki min addu’a” tace “Toh Allah ya tsare, Allah ya bada sa’a” a hankali yace “Ameen Mamina” daga haka ya fita duk jikinsa a sanyaye yayi sallama da kanninsa ya bar gidan a motarsa, driving din yake kamar baxai yi ba, why will he lie such great lies to his Mami, sosai hakan ya tsaya masa a rai, har ya isa gidansa he was not his self, khadijah na kitchen ta ajiye 3months old kids dinta da suka xama lukutaye kamar yan watanni shidda kan kujera a parlor, kiris ya rage little shureim ya fadi daga kan kujera ga d’an uwansa a gefensa, sudais ya karasa da sauri ya daukesa yana kallon kofar kitchen din, fitowa Khadijah tayi jin shigowar mutum parlorn, ya hade rai yace “I’ve warned u severally ki daina ajiye yaran nan kan kujera baki ji koh” tace “Toh they are just crying ni kuma aiki nake yi, kawai basa son mutum ya ci abinci sai dai su ayi ta basu, kuma ni ba gefen kujera na ajiye sa ba shine ya gangaro da kansa, Allah yaron nan baya ji” ko kallonta Sudais bai yi ba ya dinga kallon shureim dake ta kokarin yi masa dariya ya lumshe ido ya manna masa kiss a baki, Khadijah ta turo baki ta juya ta koma kitchen din ganin banxa ma yyi da ita, kwantar da shi sudais yyi kusa da d’an uwansa da ko motsin kirki baya son yi, shi ko irin wasan nan da kicking legs baya yi, sudais yyi kissing din takwaran nasa yana murmushi yace “You look very lazy Aliyu” dariya yaron yyi masa kamar ya ji abinda yace, Khadijah ta fito kitchen da plate din Irish da kwai, ajiye wa tayi nan parlorn tana kallon sudais tace “Have you breakfasted?” Ya kalleta yace “Noo, we are travelling now” ta buda ido tace “To where?” Yace “Somewhere” shiru ta yi tana kallonsa, yace “Ki gama ki hada kayan twins da naki, kafin ten xa mu wuce” bata ce komai ba, yace “Kin masu wanka” ta gyada masa kai, tun da Dr Yusuf ya nuna mata yanda xata dinga masu wanka shkkn ta iya unlike before da take shaka masu ruwa a hanci. Karfe goma da yan mintuna sudais ya gama sa duk kayan su a booth din mota, komai da yasan xai lalace a gidan ya sa ta xubar, yana rike da little sudais ya rufe gidan ita kuma tana rike da Shureim ya nufi motarsa dake waje, ya bude back seat yana kallonta yace “Get in” shiga bayan motar tayi sannan ya mika mata little sudais da karamar jakar dake dauke da flask na ruwan xafi da table water sai gwangwanin madarar su na Nan, ya rufe motar, ya shiga maxaunin driver, sai da ya shiga filling station ya kara mai a motar sannan suka dau hanya, a hankali yace “We are going to Abuja Amira” kallonsa kawai take bata ce komai ba, bayan wani lkci tace “Me xa mu je mu yi a can?” Bai amsa ta ba yana ci gaba da driving dinsa, ba a dau lkci ba gaba daya yaran suka yi bacci tana rungume da su tana turo baki don duk sun mata nauyi a jiki, bayan few hours shureim ya tashi da kuka sannan little sudais ma ya tashi, sudais dake kallonsu ta madubi yace “Ki hada masu madaran a feeder” kamar xata yi kuka tace “Toh da wani hannun, bayan sun danne ni” murmushi yyi ya gangara gefen titi yyi parking ya fito ya bude back seat din ya shiga, shi yayi making din masu madaran a feeder guda biyu tana kallonsa, bayan ya tabbatar babu xafi ya mika mata daya sannan ya karbi little sudais ya fara bashi nasa ita kuma ta shiga ba Shureim, tsabar cin da yaran suke ko kwana biyu gwangwanin madaran baya masu, shi sa sudais ke siyowa da yawa, bacci little sudais ya koma a hannun Sudais ya mika mata shi ta turo baki tace “Wllh kafana ciwo yake min ni dai” yace “Toh ko in bari kiyi driving din?” Dariya ta yi tana wara ido tace “Ni kuma?” Ajiye mata yaron yyi a kafa kusa da twin dinsa da shima ya koma baccin sannan ya fita ya koma maxaunin driver ya tada motar ya ci gaba da tukin sa. Kafin su kai kaduna su shureim sun sha madaran su ba iyaka, kuma duk sai yyi parking ya taimaka mata, gashi ya hanata baccin da take ta ji saboda yaran hannunta da ta fara xai tada ta ta rike su da kyau, sai kusan karfe shidda Sudais ya isa Abuja ya nufi gidansa dake cikin garin, kai kana ganin gidan kasan an kashe kudi ba na wasa ba, ya bude motar ya fita don bude gate din gidan kafin ya shiga da motarsa, babu abinda babu cikin gidan don haka bedsheet yayi spreading a kan gado a daki ya kwantar da twins dake ta bacci, yana kallon khadijah da tayi laushi alamar duk ta gaji yace “Kiyi wanka kiyi sallah kafin in dawo yanxu” daga ya fita, da yake har sponge da sabulunsu ta dauko, bayin ta shiga bayan ta fiddo su a kayansu da sudais ya kawo dakin tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana idar da sllh ta canxa kaya ta sa Hijab ta kwanta dai dai lkcn da su Shureim suka tashi, Ji tayi kamar ta kwala ihu ta dinga hararansu kamar xata yi kuka, ganin xa su fara kuka ta mike ta fara hada masu abincinsu hawaye cike idonta, ita dai ta gaji da wahalan da yaran nan ke bata, tana cikin basu feedern ya shigo dakin, tausayi da dariya ta basa lkci daya ganin yanda take hawaye, ya amshi feeders din hannunta yace “Toh tashi ki dau abinci ki ci kiyi kwanciyar ki” kamar jira take ta mike da sauri, tana cin abinci ya karasa basu abincin su ya kalleta yace “Toh baxa su yi wanka ba” hade rai tayi tace “Nima ban sani ba” yace “Amma ke ai kin yi wanka” tace “Toh ai ni da su ba daya bane” mikewa yyi ya tafi bathroom ya hada masu ruwan xafi sannan ya fito yace “Kije kiyi masu” ta mike da sauri tace “Ni wllh baxan iya ba bacci nake don Allah kayi hakuri, dubi fa wahalar da suka dinga ban a mota” tsayawa kallonta yyi kamar yanda yaran nata ke kallonta su ma, ta je can karshen gado ta xauna fuskarta daure ta dauke kai, dukawa yyi kusa da shureim ya fara cire masa kayan jikinsa har ya gama ya wuce bathroom da shi, dariya ta fara yi kasa kasa ganin shi xai masu wankan, bayan wani lkci sai gashi ya fito ya kwantar da yaron da ya wanke ya rufesa da bedsheet sannan ya dau dan uwansa ya cire masa kayan shi ma ya wuce bathroom da shi yayi masa wankan ya fito da shi ya kwantar kan gado, jaka ya bude ya fiddo masu over all gaba daya da powdernsu da man shafawa, khadijah sai boye fuskarta take kar tayi dariya ganin yanda ya sa masu pampers din, shi dai ko kallonta bai yi ba ya hade rai, yana gama shirya yan biyun ya daukesu ya fita dakin ya kai su nasa dakin ya kwantar da su, Khadijah ta turo baki a xuciyarta tace huta roro, ta mike ta rufe kofar da ya bari a bude ta nufi kan gado ta gyara bedsheet din ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa. A haka khadijah da sudais suka fara rayuwa a garin Abuja da yan biyunta, sai dai sudais wasn’t comfortable staying under the same roof with khadijah ya rasa dalili, gaba daya a takure yake barin yanda ya ga ta saki jiki totally da shi don ma akwai little sudais da shureim, karfe goma na safiya yake barin gidan baxai kuma dawo ba sai yamma, duk khadijah ta rame saboda rainon yaran don ma ba ta shayar da su, wahalansu yyi yawa, da daya ya fara kuka dayan xai cafke duk su rikitata, satinsu uku a Abuja sudais ya sa aka samar masa Nanny don tausayi take basa barin yanda ya ga ta rame, kamar kar Nanny ta xo lkci daya khadijah ta watsar da lamarin yaran gaba daya ya koma nanny ce ke masu komai ita sai dai tayi girki tayi bacci, abinda sudais ya guda kenan tun farko but saboda tausayinta da yake kawai ya kyaleta, nanny na xuwa gidan da kwana biyar sudais ya tafi damaturu don duba su Mami don Allah ma yasan yana kewar mahaifiyar tasa, kwana biyu yyi a can ya dawo Abuja bayan ya sanar ma Mami yawancin aikinsa yanxu a Abuja yake yi, ta yi masa addu’a da fatan alkhairi. karfe uku saura na yamma sudais ya shigo gidansa na Abuja, sai dai a waje yyi parking don ya gaji da yawa, babu kowa parlorn sai Ac dake ta aiki da kamshin dake tashi, ya haura sama ya bude kofar Nanny da yan biyu a hankali, suna xaune cikin keken koyan xamansu sai wasa take masu da abun jikin keken suna ta dariya gaba daya, sosai matar ke son su don yaran akwai shiga rai, Nannyn baxata wuce shekara talatin da biyar ba, tana ganin Sudais ta mike tace “Sannu da dawowa yallabai” yace “Sannu” ya karasa cikin dakin yana kallon cute yaran dake ta kallonsa, kyawawan karshe ne yan biyun ga manyan idanuwa ga su farare kal kamar larabawa, da wuya mutum ya kallesu bai kara kallonsu ba, ya rasa ne yasa khadijah ta ki sonsu har ynxu, daukansu yayi one by one yayi kissing dinsu suna masa dariya ya ajiye su ya fita dakin, bude kofar dakin da Khadijah take yyi, ya ganta kwance daga ita sai yar doguwar riga tana bacci, ya kusa minti biyu tsaye yana kallonta kafin ya rufe mata kofar ya wuce nasa dakin, wanka yyi ya dauro alwala ya fito ya saka jallabiyarsa ya gabatar da sallahn azahar sannan ya kwanta, Nanny ce ta shiga dakin Khadijah ganin har kusan la’asar ba ta fito ba alamar bata san Sudais ya dawo ba, ita duk tunaninta sudais mijinta ne, cike da natsuwa ta tasheta tace “Yi hakuri na tashe ki madam, yallabai ya dawo” da sauri khadijah ta mike xaune tace “Yaushe?” Nanny tace “Tun daxu” Khadijah tace “Toh” Nanny ta juya ta wuce sannan khadijah ta mike ta tafi bayi ta wanke fuskarta ta fito ta dau Hijab har kasa ta sa ta fita, a hankali ta tura kofar dakin sa ta gansa yyi rub da ciki yana bacci, a hankali ta isa kusa da shi ta durkusa tana kallon kyakkyawan fuskarsa, bude manyan idonsa yyi a hankali, ta koma baya da sauri ta fara kame kame, ya mayar da idonsa ya rufe na kusan minti daya kafin ya bude ya mike xaune, murmushi tayi murya can kasa tace “Sannu da dawowa, baka ce yau xaka dawo ba da ka kira da safe” yace “I was thinking sai gobe xan taho” tace “Ya hanya? Ya su mama” Yace “Alhmdllh, ya twins? duk da nasan kilan duk yau baki gansu ba” sauke idonta tayi daga kallonsa jin yyi shiru ta daga kai suka hada ido, wara mata ido yyi, ta yi murmushi tace “Me xaka ci?” Yace “Komai ma” mikewa tayi tace “Toh bari in yi maka” daga haka ta fita ya koma ya kwanta. A hankali watanni suka dinga ja kamar wasa sai ga shi su shureim sun yi wata bakwai, babu inda basa xuwa da rarrafe, wani shakuwa ne ba na wasa ba tsakaninsu da Sudais, ji yake da su kamar ya hadiye su don so, in har suna wasa a Parlor to suna ganin khadijah suke barin wajen da gudu su tafi gun Nannynsu, sai dai ta tabe baki ko tayi tsaki, har lkcn kamanninsu sak na Aliyu barin hancinsu da idanuwa shi sa take kara jin bata son su, ko ina na gidan kayan wasan su ne, don komai sudais ya gani na yara ko da ya fi karfinsu sai ya siyo masu, dakinsu ya koma kamar na siyar da kayan wasa, yau lahadi sudais na xaune garden shi kadai files a gabansa kana ganinsa kasan aiki yake, lkci daya ya rufe files din gabansa ya lumshe ido, for how long xai ci gaba da ajiye khadijah da yaranta a gidansa, har ransa yake jin baxai iya rabuwa da su ba, but duk ranan da Mami ta gano abinda yake aikatawa yasan that day won’t be funny, then meye xai yi da xai kasance da Khadijah da yaranta na har abada With his parent consent, bude ido yyi a hankali ya furta abinda ke ransa a ciki “I shud marry her” girgixa kai yyi ya na murmushi lkci daya abinda Yusuf ya gaya masa one year ago a mota ya fado masa. Khadijah na bedroom ita kadai tana ta jiran jin shigowar sudais amma bai shigo ba, ita kanta bata san me yasa take son ya shigo ba, kuma tasan yana can garden, mikewa tayi ta sa mayafinta ta fita xuwa can din ta tsaya kusa da wani flower yanda baxai ganta ba ta dinga kallonsa, kananun kaya ne jikinsa na 3qtr da shirt da bai yi buttoning ba, tsura ma pen din table dake gabansa ido yyi har lkcn yana tunani, kamar ance ya daga kai suka yi ido hudu da Khadijah, dauke kai tayi da sauri, sai kuma ta jiya ta bar wajen ya bi ta da kallo, murmushi yyi ya na shafa kansa don irin kallon nan da Khadijah ke yi masa ko da yaushe dariya yake ba sa, sau tari ya sha kamata tana kallonsa sai ta fuske, shi din ma yana kallonta amma with swags, kwashe files din gabansa yyi don dama ya gaji ya mike ya wuce ciki yana rike da su, sai da ya fara lekawa dakinsu shureim yaga yanda Nanny ta cika masu kayan wasa a gaba suna ta fama, suna ganinsa suka rarrafo xasu taho gunsa, da sauri ya juya ya bar wajen don bacci yake son yi, a tare suka fara kuka yana tsaye har suka fito corridor nemansa yyi murmushi ya durkusa ya daukesu duk biyun amma da kyar tsabar weight dinsu, ya wuce dakinsa da su, ajiye su yyi kan gado ya kwanta suka haye kansa gaba daya ya lumshe ido yace “Yanxu baxa ku bar ni inyi bacci ba” kamar sun ji mai yace suka fara dariya har da kwantawa jikinsa ya rungumesu gaba daya, ganin da gaske baxa su bar sa yyi baccin ba ya dau waya ya kira Khadijah, tana dagawa yace “Plss ki xo ki dau su Shureim basa son inyi bacci” Khadijah bata ce komai ba ya katse wayar, ta tabe baki ta sa Hijab ta fito ta shiga dakinsa karasawa tayi kusa da gadon suna ganinta suka kankamesa sudais yace “Meye amfanin yaranki na tsoron ki” bata tankasa ba ta kai hannu xata dau little sudais ya fasa ihu dan uwansa na taya sa suka rirrike sudais, murmushi kawai sudais yake yana kallon khadijah da ta hade rai tana kallonsu, fixgo shureim tayi ya fashe da kuka a tsorace har lkcn yaki yarda ya sake sudais. Sudais ya fixgota ita ma har ta fada kansa ya daure fuska yace “Ciwo xa ki ji masa” xata tashi ya ki saketa yana kallonta kamar yanda yaran ta ma ke kallonta, murmushi tayi ta xame kanta ta xauna kasa, murya can kasa sudais yace “Tafi basa son daukan naki” kamar sun ji abinda yace suka kara yin lamo a jikinsa, Khadijah ta mike ta nufi kofa sudais ya bi ta da kallo har ta fita sannan ya lumshe ido a hankali. A ranan da su Shureim suka cika wata goma Sudais ya sa Nanny ta shirya su kamar dai yanda ya saba duk lahadi xa su fita, yanxu kam babu inda shureim bai xuwa da kafafuwansa banda little Sudais da tashi ma wahala yake masa, kaya iri daya nanny ta sa masu as usual, kwankwasa kofar dakin Khadijah sudais yayi, tana xaune gaban madubi tana rubuta a farar takarda jin an kwankwasa kofa ta dauke takardar da sauri xata boye, dai dai nan ya bude kofar, cukuikuye papernta tayi, ya dinga kallonta yace “What’s that” girgixa masa kai tayi ba tare da ta bari ta kallesa ba da sauri tace “Bakomai” yace “Uhn, sure?” Kin cewa komai tayi, yace “Toh ki shirya xan fita da twins sai ki raka mu” ta girgixa kai tace “Baxan je ba” yace “Why?” Sai a sannan ta kallesa, saurin sunkuyar da kanta tayi, ya d’an yi murmushi ya juya ya fita, bude takardar tayi tana duba abinda ta rubuta, a hankali ta linke ta boye sa sannan ta sa Hijab dinta ta fita, har ya sauka parlor da su little sudais, ya juya ya kalleta yace “Ko d’an kwalliyan ma baxa ki yi ba” tace “Ehh” ya tabe baki ya fita tare da yaran ta bi bayan su, driving yake Khadijah na back seat da twins din shi kuma yana kallonsu ta madubi, horn ya ji an yi ya juya, da mamaki yake kallon matar da ta fito daga wani gida a motar ta kafin ya tsayar da tasa motar ya bude ya fito, ita ma ta sauka tace “Aliyu dama kana Abuja?” Ya kirkiri murmushi yace “Wallahi kuwa Mama, ina yini?” Tace “Lafiya lau Aliyu” lekan bayan motarsa ta dinga yi kafin tace “Kar dai kayi aure Hajiya Khadijah bata gaya min ba naga mace da yara a mota” sosai gabansa ya fadi yace “A’a mama, matar abokina ne da yaranta” Tace “Ayyo wajen ka suka xo?” Yace “A’a ajiye su xan je in yi” shi kansa ya san he just sound stupid, yayi saurin cewa “Amma mama kun dawo ne?” Tace “Noo, na xo yin abu ne yau sati na daya, amma ina jin jibi xan koma” yace “Holland din?” Tace “In sha Allah” yace “Toh Allah kai mu mama” tace “Ameen Aliyu, Allah yayi maku albarka” yana murmushi yace “Ameen” daga haka ya koma motarsa har lkcn gabansa na faduwa, Hajiya Rukayya aminiyar Mami ce don childhood frnds ne ma, ita ce ta sa Mami tayi ma Abba magana ya siya masa gida a layin lkcn anguwar na sabo, ita ma kuma a anguwar take amma sai su yi wata da watanni basa Nigeria da yaranta, har sudais ya kai bakin titi Hajiya Rukayya bata dauke idonta a kan motarsa ba, mace da yara a motarsa kuma yace matar abokinsa, kallon gidan Sudais din tayi kafin ta karasa can da kafa, kwankwasa gate ta dinga yi ko mai gadi xai bude amma shiru, can sai ga Nanny ta fito ta bude gate din, gaisheta Nanny tayi, Hajiya Rukayya tace “Ya kike” Nanny tace “Lafiya lau sai dai Masu gidan basa nan” shiru Hajiya Rukayya tayi kafin tace “Shi da matar suka fita kenan?” Nanny tace “Ehh har da yan biyun” Hajiya Rukayya tace “Toh shkkn” daga haka ta bar wajen da sauri ta wuce gidanta tana tunanin to ko dai karya sudais yyi mata yace bai yi aure ba, tana shiga motarta ta dau waya ta shiga kiran Mami.Noor Al Hayat 64
-

Noor Al Hayat 41
Khadijah ta shiga hali na damuwa sosai bayan tafiyar sudais, bata da aiki sai na tunani da xubda hawaye bata taba xaton rabuwa da Sudais a lkcn ba, da ba don Nanny dake gidan tana kwantar mata da hankali ba da abun ya mata yawa, gani take kamar sudais xai dawo kullum jiran tsammani take amma shiru wasa wasa har sati biyu, ta rame ba kadan gashi kullum cikin jin ciwo take a kirjinta, ciwon da ta fi shekara bata ji sa ba sai gashi ya dawo mata da karfinsa, hakan yasa Nanny ta tilastata suka shirya suka tafi asibiti don ko baccin kirki bata iya yi da daddare, khadijah bata yi mamakin abinda likita yace game da ciwon da take yawan ji a kirji ba, at anytime xata iya kamuwa da ciwon xuciya, yini biyu tayi asibitin under medication, nanny tayi ta kai kawo da twins xuwa asibitin, da yamma likitan ya sallamesu ya kuma bata shawarari da dama kan abinda ke janyo ciwonta da yanda xata yi preventing tashin ciwon, A hanyarsu ta dawowa cikin Napep da damuwa Nanny tace “Yanxu Mum twins da kike sa ma kanki damuwa haka idan abu ya same ki yaran ki fa? Ko don su baxa ki hakura ki rufa masu asiri ki kwantar da hankalin ki ki rungumi kaddara ba, kar fa ki manta ko wani bawa da irin tasa kaddarar, so why not just accept urs a yanda ya xo maki” Khadijah ta goge hawayen dake xuba idonta a hankali tace “Ban san ya xan yi ba” Nanny ta kwantar da murya tace “Cire komai xa ki yi a ran ki, kiyi facing sabuwar rayuwar da xa ki fara da yaran ki, bawan Allahn nan ya tafi, ya kuma ya maki duk abinda ya kamata kafin ya tafi yanxu the ball is in ur court, sai kiyi abinda ya kamata ki kuma rike addu’a sai komai ya xo maki da sauki, as a mother nake baki shawara Khadijah… For the sake of ur boys ki yi hakuri ki cire ma kan ki damuwa don Allah” a hankali khadijah tace “Toh nagode sosai” suna isa gida Khadijah ta sauka ta ba mai adai daitan kudi, xata karbi shureim hannun Nanny ya makalkaleta ya ki yarda, jikinta yyi sanyi tana kallon yaron, Nanny tayi murmushi ta fito da duk yaran biyu, khadijah ta karasa ta bude gate din sannan suka shiga gidan, ba laifi ta dau shawarar Nanny ganin shi kadai ne mafita a gareta sai dai hakan bai sa fara’arta ya dawo ba, she is always sad, bata taba xaton Sudais xai bar ta so early a rayuwa ba, kusan kullum sai ta yi tunaninsa, magungunan da take sha ya taimaka ya rage mata ciwon xuciyar da take fama da shi duk da baya tasar mata ma sai da daddare taji kamar xata mutu, ba karamin kokari take yi na ganin ta ja su little sudais a jiki ba amma sun ki yarda ko da yaushe cikin gudun ta suke kamar dodo, hakan na kara sa ta shiga damuwa Nanny ta dinga nuna mata a hankali xa su sake da ita kar ta damu, a ranan da yaran suka cika shekara daya a duniya Nanny ta raka Khadijah tayi enrolling kanta a ss1 na wani makaranta dake nan anguwar ta su, idan ba ita ta gaya maka tana da yara har biyu a gida ba in xa a shekara ana gaya maka baxa ka yarda ba, a lkcn kuma shekarunta sha bakwai a duniya, kana ganinta kasan she is a teenager, a hankali khadijah ta fara kokarin yakice tunanin sudais a ranta domin tayi concentrating a karatun ta, idan ta fita tun safe sai hudu take dawowa gida, sannan ga islamiyyar da ta shiga na yamma, hakan yasa still babu wani interaction tsakaninta da yaranta tun da ba xaman gidan take ba, amma har ga Allah yanxu ji tayi tana son abun ta duk da tsoronta da suke ji har lkcn. Haka rayuwa ta ci gaba da kasance ma khadijah har ta gama ss1 lafiya, xuwa lkcn abu uku ne ke damunta a xuciya, Rashin Ummanta, gudun ta da yaranta suke sai kuma ciwon xuciyar da ya sa ta gaba abu kamar wasa kusan ko da yaushe hanyar asibiti take wanda hakan ke sa ta fashin makaranta don ma tana da kokari, Sudais kam ta rufe sa a babin rayuwarta sai dai duk sllh sai tayi masa addu’ar Allah ya saka masa da alkhairi abinda yyi mata a rayuwarta da yaranta. Yau lahadi suna parlor, Nanny na feeding Sudais da shureim da yanxu shekarun su biyu da yan watanni a duniya indomie ta dafa masu take basu, yaran sun yi wayo sosai babu inda basa xuwa sai dai fa da ka gansu kaga Aliyu barin sudais komai na Abban nasa ya dauko, sau da yawa sai Khadijah tayi ta kallonsu, wani lkcn tayi murmushin takaici, wani lkcn kuma tayi hamdala ga Allah da ya bata yan biyun, Nanny ce ta katse shirun dake tsakaninsu tace “Mum twins to ya xa ayi da cefanen, wa enan ba yarda xa su yi in tafi in bar su ba, kuma wahala kawai xa mu je mu sha idan muka tafi gaba daya” Khadijah ta ajiye novel din hannunta tace “Nanny kawai da wayo xa ki tafi ki bar su” a tare yaron suka kalleta, Nanny ta kyalkyale da dariya tace “Toh ai kin tona, wa yace maki basa ji, sarai sun ji abinda kika ce” murmushi khadijah tayi tana mamakin sharpness din twins din, tuni shureim ya kara matsawa kusa da nanny, Khadijah ta tabe baki tace “Toh bari ni in je” Hijab har kasa ta daura kan kayan jikinta sannan ta dau kudin ta yi ma Nanny sallama tana daga ma boys din hannu ta nufi kofar fita su ma suna daga mata, jikinta yyi sanyi ganin in dai uwa xata fita yaranta sun dingi kuka kenan xa su bi ta, but why is her own case different, ko a jikin yan biyun dake cin Indomie da nanny ke basu har ta fita, to ita bata san kuma ya xata yi yaran nan su saki jiki da ita ba, iyakar kokari tana kokarin kwatanta masu abinda sudais yace Kafin ya bar su amma sun ki sakewa da ita, tana tsaye bakin titi tana jiran abun hawa a ranta kuwa tunani take ko dai abinda sudais ya fada kan nonon da bata basu ba gaskiya ne, kenan haushin ta suke ji? Ji tayi da ma basu girma ba ta basu nonon yanxu, tsabar yanda jikinta yyi sanyi bata lura da motar da har ya wuce ta da farko ya fara reverse a hankali yana dawowa ba, tana ankarewa ta dauke kai da sauri hade da tsuke fuska don hakan ma yasa bata son fita, tana mamaki da jin haushin me yasa in dai xata fita sai an tsayar da ita, ita ba wannan ne gabanta ba kuma bata jin xuciyarta xai kara kula wani d’a namiji har ta bar duniya, ganin mai motar ya fito daga motarsa ta bar wajen da sauri tana tafiya fuska daure ba tare da ta damu ta kallesa ba, ji tayi ance “Khadijah?” ta juyo da sauri suka yi ido hudu da shi, ya dinga kallonta kamar me son kara tabbatar da ita ce ko ba ita bace, ita din ma kallonsa take da mamaki, yace “Baki gane ni ba Khadijah?” Jikinta yyi sanyi lkci daya tayi murmushin da ya bayyana fararen hakoranta tace “Na gane ka, am just trying to be sure ko kai ne ko ba kai bane” ya wara yace “Maa sha Allah, Imagine we met after 3 good years” murmushi ta kuma yi tana kara kallonsa da kyau ganin yyi mata tsayi fiye da yanda ta san sa a da tace “Sure, to ya bayan rabuwa” ya rike chin dinsa yace “Waow kin girma Khadijah, just look at how calm you are now, kin tuna lkcn da kike yawo ba Hijab da jikakken kaya?” dariya ya bata ta rufe fuska tace “Har da tsokana” yace “Am serious, a Abuja dama ku ke?” Tace “Ehh wllh, ya su mama fa” yace “Suna kt, nima ban dade da fara aiki a nan ba, just 7 months back” Khadijah tace “Allah sarki, toh Allah ya taimaka” d’an shiru yyi yana kallonta, kafin a hankali yace “Ko kin yi aure ne Khadijah?” Kallonsa ta tsaya yi ita ma, lkci daya ta samu kanta da girgixa masa kai tace “Aure kuma, A’a ina karatu ne” yyi murmushi yace “That’s good, kar in tsaya ina ta tsurutu da matar aure ban sani ba” murmushi kawai khadijah tayi a xuciyarta kuwa mamakin yanda aka yi ya fara magana ta yi don a lkcn da ta san shi da wuya yake magana sai dai danna waya, lkci daya jikinta yyi sanyi tuna abinda yyi mata a lkcn da take walagigi a katsina cikin yunwa, muryarsa ya katse ta yace “Ina xaki yanxu?” Ta kallesa tace “Kasuwa” yace “Toh shiga in yi dropping din ki” d’an xaro ido tayi tace “Kai da ba d’an gari ba?” Yace “Wata na 7 kice min ba d’an gari ba” murmushi tayi tace “Toh naji kai d’an gari ne” yace “Toh shiga muje” motar ta bude tana murmushi ta shiga, ya xaga ya shiga maxaunin driver suka bar wajen, yana driving yace “So ya rice and stew, and Irish with egg? Kuna nan kuna damawa koh?” Dariya sosai Khadijah tayi ta rufe fuska, yana murmushi yace “Yarinyar nan ta kashe min kudi a lkcn da abincin yan gayu gashi sai Abba ya bani nima lkcn” Khadijah ta dago a hankali tana kallonsa tana murmushi tace “Ae yanxu babu abinda bana ci har tuwo da miyar kuka, da ma kunu da kosai” ya wara ido yace “Da gaske? Anya xan yarda kuwa” ta gyada masa kai tace “Serious…” yace “Hmm that’s surprising amma” ta turo baki tace “Baka yarda ba kenan?” yace “Toh ai ban ce komai ba Khadijah” suna isa kasuwa bbu yanda Khadijah bata yi da shi ya tafi ba yace xai jira ta, bbu yanda ta iya haka ta siya abubuwan da tasan xa su bukata a lkcn daga baya sai ta dawo ta siya sauran don bata son ta bar sa yyi ta jiranta, yana parking kofar gidan da ta nuna masa yace “Nan ne gidanku?” Ta gyada masa kai ta bude motar ta fita, yace “Toh ki gayar min da su mama da mutan gida” a sanyaye tana kallonsa tace “Xa su ji nagode sosai” daga haka ta juya xata shiga gate, yace “Wait Khadijah baki ban number ki ba mu dinga xumunci” dawowa tayi ta kira masa numberta yayi saving yana kallonta yace “It’s nyc meeting you once more Khadijah” ta kirkiri murmushi ta daga masa hannu ta shiga cikin gida, Nanny na kitchen su sudais kadai ne xaune parlorn ta sa masu cartoon, khadijah ta ajiye ledan hannunta ta isa kusa da su ta xauna tana kallonsu, su ma kallonta suke, ta yi murmushi ganin irin kallon da suke mata ta yi masu kiss gaba daya, Sudais ya goge bakinsa shureim na ganin haka shi ma ya goge nasa, jikinta yyi sanyi sosai tana kallonsu, bata san lkcn da hawaye ya kawo idonta ba ta mike ta wuce daki da sauri, Nanny ce ta shigo dakin ganin khadijah kan gado tana hawaye da mamaki ta karaso da sauri tace “Mum twins me ya faru kuma?” Cikin rawar murya tace “Wai don na masu kiss shine suke goge bakinsu” dariya sosai Nanny tayi kafin tace “kai Khadijah shine har da kuka, to kyalesu xan yi maganinsu” daga haka Nanny ta juya ta koma parlor, taso keyar boys din tayi suka taho dakin, kusa da khadijah ta ajiye su duk suka shiga kkrin sauka daga kan gadon Nanny ta daure fuska tace “C’mon, duk wanda ya sakko xan xane sa, ita ce uwar ku ba ni ba” Kuka suka fara yi kuma basu sauka kan gadon ba, Nanny na kallon khadijah dake ta kallon kyawawan yaran nata tace “Yanxu abinda xa mu yi shine xa su dawo kwana nan dakin, ke xaki dinga masu wanka ki shirya su, ke xaki dinga ba su abinci hakan kadai xai sa su saki jiki da ke” a hankali khadijah tace “Toh” Nanny tace “Don haka duk safe kafin ki tafi school sai kin masu wanka kin shirya su ni kuma in hada masu breakfast sai in baki ki basu” kai kawai Khadijah ta gyada don har ga Allah bata son gudun ta da yaran suke, haka Nanny ta fita ta bar su suna kuka xa su bi ta, amma da yake suna jin magana bbu wanda ya sauka daga kan gadon kamar yanda tace masu, suka gama kukansu suka yi shiru suna kallon khadijah, Sudais yyi tapping dinta yana nuna mata kofa yace “Nanny…” Murmushi Khadijah tayi ta jawo sa jiki tace “Nima Nanny ce ai” hakura yaran suka yi suna ta xaune dakin kusa da ita har bacci ya dauke su, Nanny na ganin lkcn tashin su ya kusa misalin karfe biyar na yamma ta dama masu custard ta dafa masu indomie ta kawo ma khadijah dakin ta fita ta rufe masu kofa, a lkcn kuma suka tashi, duk suka yi jigum suna kallon khadijah, ruwan wanka ta hada a bathroom dinta tayi masu gaba daya sannan ta fito ta shafa masu mansu dake dakin ta sa masu singlet da pant ta xaunar da su kan carpet ta shiga basu custard din suna karba, har ranta ta ji dadin hakan suna gama sha kuma ta fara basu indomie da egg din, shureim na koshi ya fiddo wanda ta sa mashi a baki ya mike ya kai mata bakinta, murmushi tayi ta bude bakinta ya xuba mata abincin ta shiga ci a hankali. Sai kusan karfe shidda Khadijah ta fito parlor da yan biyun nata, cartoon ta sa masu parlorn duk suka xauna kan kujera suna kallo basu bi ta kan Nanny ba, da daddare a kan gadon ta ta shimfide su bayan sun yi bacci, ta gama shirin kwanciya kenan ita ma wayarta ya fara ring, ita dai bbu mai kiranta a waya ban da Nanny sai wata classmate dinta Aisha dake sonta sosai, ta dinga kallon number kafin ta daga, sallama yyi mata jin muryar hankalin ta ya dan kwanta sai dai bata san dalilin kiran ba ta amsa masa sallamar ta gaishesa yace “Ko kin fara bacci ne?” Ta girgixa kai tace “A’a yanxu dai xan yi” yace “Ohk, ya mutan gidan?” Tace “Lafiya lau Alhmdllh” yace “Maa sha Allah” shiru ta yi bata ce komai ba, a hankali yace “Kawai sai kika bar garinmu ba sallama Khadijah” tayi murmushin karfin hali tace “Ummata ce ta xo ta dauke ni ai” yace “Allah sarki, but dama me ya kawo ki gidan tun farko” khadijah da taji kamar kar tace komai kawai ta yi murmushin takaici tace “Ai yayan Abbana ne” yace “Are you serious?” Tace “Uhn” yace “Waow, to me yasa basu baki abinci” ta wara ido tace “Suna bani fa, ni ce ban iya cin abincin ba lokacin” murmushi yyi yace “Allah sarki, kwanaki ma ai kawun naki yyi accident kin sani koh” Khadijah ta bude ido sosai tace “Haba dai, ban sani ba, basu gaya mana ba” Sadeeq yace “Ehh amma da sauki yanxu ina jin ya samu lafiya ma” A hankali khadijah tace “Toh Allah ya kara kiyayewa” yace “Ameen” shiru ne ya biyo baya kafin yace “Kin taba ba Umma labarina” Khadijah da taji jikinta yyi mugun sanyi a hankali tace “Kowa ma ina ba labarin ka, cos you fed me when I was in need of food” Sadeeq yace “Noo I did that for the sake of Allah, not for you to tell everyone” murmushi kawai khadijah tayi a sanyaye, shi ma murmushin yake yace “Sure, yaushe xa ki hada ni da Umma mu gaisa ko kuma in xo har gida in gaisheta, ko baki son mu yi xumunci sosai?” gabanta ne yyi mugun faduwa and she was totally lost of words, a hankali yace “Hello, Khadijah are you there?”
-

Noor Al Hayat 30
✨ *NOOR-AL-HAYAT*✨
Khadijah ce kadai xaune daki da daddare tun bayan incident din daxu da rana ta ki fita dakin, Baby ta shigo daga dakin Mumy tana kallon Khadijah tace “Iman you look sad since afternoon, ko don abinda anty Khadijah tayi maki ne a schl?” Khadijah ta girgixa mata kai tace “A’a am not feeling fine ne” Baby ta buda ido sosai tace “Toh ki gaya ma Mumy mana, or you can tell Yayanmu that is a doctor” Khadijah tace “I will be alright in sha Allah” juyawa baby tayi ta fita, dakin ya Aliyu ta shiga ta xauna gefensa har ya gama wayar da yake sannan ya kalleta yace “What happen” tace “Yayanmu Iman ce naga she is sad all day, I asked what’s wrong tace min she is not feeling fine” ya kalli kofa kamar xai tashi sai kuma yace “Ta fi ki kira min ita” Mikewa baby tayi ta fita ta koma dakinta, “Yayanmu yace in kira ki” abinda ta fadi ma khadijah dake kokarin kwanciya kenan, Khadijah ta hade dai tace “But I didn’t tell you to announce I am sick” baby tace “What ever… Ko ince masa baxa ki xo ba” daga haka ta juya ta fita, mikewa khadijah tayi ta sa Hijab ta bi bayanta, dai dai fitowar Anty khadijah daga dakinta xata sauka downstairs, da da ne tana ganin Iman tayi hanyar dakin Aliyu irin ko ya kira su tare da baby xata mata mugun kallo ta hanata shiga dakin, yanxu kam sau daya ta kalleta ta dauke kai tayi wucewarta, a sanyaye khadijah ta shiga dakin don tuni baby ta shiga, ta tsaya daga bakin kofa tace “Ga ni Yayanmu” yace “kika ce baki da lafiya, what’s wrong?” Ta kalli baby tace “Kawae I told her am nt fine, ba wai bani da lafiya ba” Baby tace “Ke ma kina son ki fara karya kamar iklima koh?” Murmushi Khadijah tayi, Aliyu ya kalli baby yace “You can leave” mikewa tayi tace “Ohk” sannan ta fita, yana kallon khadijah yace “Come over Iman” karasawa cikin dakin tayi, ya jawo study chair dinsa ya ajiye mata, ba musu ta xauna tana facing dinsa, a hankali yace “But I told you not to worry koh?” Ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace “I am without worries” shiru yyi yana kallonta, ta ki dago kanta, murya can kasa yace “Iman” dagowa tayi da manyan idonta tana kallonsa, yace “Tel me when you lost ur parent” lkci daya hawaye ya cika idonta, ya girgixa kai yace “Noo ban ce kiyi kuka ba” ta gyada masa kai tana fidgeting fingers dinta a hankali tace “My dad told me I lost my mum when I was just 3, we where together tun daga sannan, shi yake kai ni schl da islamiyya, I love my dad… He took good care of me, kullum a eatry Abbana ke siyo mana abinci, I mean all the 3 daily meals, but there is always custard, cornflakes, golden morn, ice-cream in the fridge and different biscuits and chocolates at home all for me, duk sanda Abbanmu xai je trip abroad he always go together with me, not until he married my step mum when I was 8 years old, and she took over from where he stopped, my step mum is more than kind, tana so na, she does to me what ever I like, ko Abbanmu na nan ko baya nan, muna tare har na kai 14 years….” Katse ta Aliyu yyi yace “Ita yaranta nawa step mum dinki?” Tayi murmushi tace “Ni kadai ce yarinyarta, she never gave birth with my dad” Aliyu ya gyada kai yana kallonta, ta d’an yi shiru, sai kuma a hankali tace “One faithful Friday Abbanmu xai je port Harcourt wajen junior brother dinsa da aka kira sa ba shi da lafiya ya xo ya tafi da shi, we bade him fare well har parking lot da Asuba tare da Ummata” ta fashe da kuka tace “That was the last time we saw him, sai aka kira Umma aka ce yayi accident and he is gone” kamo hannunta Aliyu yayi murya can kasa yace “Allah ya ji kansa, yayi masa rahama, dont cry pls” cikin rawar murya tana gyada masa kai tace “Ameen” yace “After that?” Ta xame hannunta tace “We cried a lot da ummata, but at the end tace in daina kuka saboda my dad won’t be happy with me idan ina masa kuka ban masa addu’a ba, and from then ban sake kuka ba don bana son abbana yyi fushi da ni, ko da yaushe addu’a nake masa Allah ya basa aljanna, we stayed for plenty months tare da Ummata a gidan mu kadai, kawai ranan sai ga uncle dina ya xo wai xa a yi sharing property din Abbanmu, I don’t knw how but at the end, kawai ummata tace min ita xata tafi gidansu ni kuma uncle dina yace xai tafi da ni gidansa in xauna a can, a week after kuma ya sake dawowa… A ranan muka rabu da ummata ya rufe gidan, ya tafi da ni katsina gidansa ita kuma ta tafi gidansu ita ma” Aliyu sai kallonta yake ko kiftawa bai yi, labarin rayuwar wahala da tsangwama da tayi gidan kawunta ta shiga basa, da irin hidiman da sadeeq ya mata da yanda Mahaifiyarsa ta hanasa daga karshe har xuwa ranan da Umma ta xo ta gudu da ita ta kai ta gidan sabon mijin da take aure a kano, nan ma duk ta basa labarin 3 days stay dinta a gidan da abubuwan da suka faru kafin Umma ta kawo ta nan Kaduna wajen step sister dinta yakumbo, bata boye masa duk kalan wahalan da ta sha gidan yakumbo ba da irin duka da xaginta da take, har daga karshe makwabtan ta suka dinga xuga ta a kan ta kawo ta gidan aiki, har dai yakumbo ta kawo ta nan gidan tare da Abuuu…. Khadijah tayi shiru tana kallon Aliyu da ya kasa kallonta, kai kana ganinsa kasan tausayinta ne kawai ya cika sa, jin tayi shiru ya dago da kyar yace “Kiyi hakuri Iman, all this will come to past one day it’s just a matter of time” ta gyada masa kai kawai, Ya shafa kansa yace “Kuma ki dinga hakuri da abinda Anty Khadijah ke maki, wataran baxata yi ba kin ji” a hankali tace “Toh” yace “And Saleem babu ruwanki da shi, soon xai tafi Germany ki kwantar da hankalin ki kin ji” nan ma tace masa “Toh” yyi mata murmushinsa mai kyau ya lakaci hancinta yace “Good girl” ita ma murmushin tayi ta sunkuyar da kanta, yace “Yanxu islamiyya xa ku dinga xuwa from morning to evening tunda ba schl kuma” kallonsa tayi bata ce komai ba, yace “Toh tashi ki tafi kar ki kara sa ma kanki damuwa kinji” kai ta gyada masa ta dau wasu novels guda biyu da ta gani kan study desk dinsa tace “Can I read them” yace “Noo, I will get you the one to read tomorrow” tace “Ohk” sannan ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo. Bayan kwana biyu Mumy na daki ranan asabar misalin karfe sha daya da yake babu aiki, Su siyama, Baby da Khadijah har Iklima duk sun tafi islamiyya, Anty khadijah ta shigo dakin Mumy a shiriye rike da yar karamar jaka, daga nan bakin kofa tace “Anty fati xan je gidan wata kawata dake nan Zaria bata ji dadi ba, in sha Allahu xan yi kwana biyu xuwa uku kafin in dawo” Mumy tace “Zaria kuma, wace k’awa gare ki a Zaria, amma baki taba ce min kina da k’awa a Zaria ba, kuma ni tun da kika xo gidan nan ban taba ganin wata k’awa ta xo wajen ki ba, hasali ma ce min kike ba ki da kawaye….” Katse ta Anty khadijah tayi fuska a murtuke tace “Toh karya nayi kenan Anty fati, da can na taba ce maki xan je gidan k’awa ta? yanxun ma lalura yasa xan je wajenta, kuma da ba a Zaria take ba a Abuja take a anguwar mu, aiki ne ya mayar da mijin ta Zaria” Mumy tace “Toh Allah ya kyauta, Allah ya kiyaye” Anty Khadijah tace “Ameen, Anty fati don Allah ki sa ido kan Iklima kin san ba wai can take son cin abinci ba” Mumy ta harareta tace “Baxan sa ba” Bata ce komai ba ta juya ta fita daga dakin, Aliyu ne kadai xaune parlor, ko kallonsa bata yi ba ta nufi kofar fita, ya bi ta da kallo kafin yace “Allah ya kiyaye hanya” ficewarta tayi ta rufe kofa ba tare da ta tanka sa ba. Karfe biyar na yamma bayan Aliyu ya dawo aiki ya kira baby ta shigo dakinsa yace “Me ya hana ku xuwa islamiyya” ta xaro ido tace “Yayanmu na safe fa muka je yau” yace “Ohk je ku shirya da Iman mu fita” cike da murna tace “Waow, su siyama fa Yayanmu?” Yace “Ban da su” juyawa tayi da sauri ta fita baki har kunne, a dakin Mumy ta tarda Khadijah dake fiddo ma Mumy turarrukan da ta aiki driver ya siyo mata a shopping mall, Iklima kuma na xaune saman gado tana kallo, Baby tace “Mumy wai Yayanmu yace ni da Iman mu shirya xa mu fita anguwa” Mumy tayi shiru bata ce komai ba, can tace “Toh ku je ku shirya” iklima ta sakko saman gadon kamar xata yi kuka tace “Mumy ni ba dani xai je ba kenan” Mumy tace “Toh ni na sa ki ki dinga masa fitsara? Wannan kuma ya rage na ku ke da shi” Fita iklima tayi dakin tana kuka, Baby ta fiddo atamfar da Mumy tayi masu iri daya da khadijah da mayafi tace “Wannan xa mu sa Iman” ita dai khadijah bata ce komai ba, baby ta kyalkyale da dariya tace “Allah sarki ban da iklima” Khadijah tayi murmushi tace “Yayanmu has a very good heart nasan xai je da ita” Baby tace “Tab kinsan yanda Yayanmu ya tsani mai rashin kunya” Khadijah bata ce komai ba ta fara sa kayan da baby ta dauko masu. iklima na fita mumy ta tashi ta tafi dakin Aliyu, daga bakin kofa ta tsaya tace “Abuturrab amma tare da Iklima xa ku je” Ya hade rai yace “A’a ni ban ce xan je da ita ba mumy” mumy tace “Toh sai a fasa tafiyar ai” daga haka ta juya ta shiga dakin Anty Khadijah ta ga iklima xaune can karshen gado tayi tagumi tana rera kuka, Mumy tace “Sai ki shirya ku tafi gaba daya” mumy na fadin haka ta juya ta wuce, ko kunya babu iklima ta tashi ta fiddo sabon kayan ta da takalmi mai tsini da jaka, ta sha uban make up ta sa spec, ta feshe jikinta da turarurrukan uwarta sannan ta sakale mayafinta a kafada ta fito, dakin su baby ta shiga su ma har sun gama shiryawa baby na ganinta ta kwashe da dariya har da faduwa kan gado ta dinga kyakyatawa, Khadijah tayi murmushi ta dauke kanta, Baby ta kuma dagowa ta kalli Iklima ta kwashe da dariya, Iklima ta maka mata harara tace “Ai dama ke mahaukaciya ce” Baby ta mike xaune tace “You are not even ashamed of ur self, yanxu wa yace xai je da ke, har da wani sa dogon hill da spec, ji wani make up kamar na yan kasuwar tasha” Juyawa iklima tayi ta shiga dakin mumy, can sai ga ta ta fito tana huci tace “Mumy na kiranki” Baby tayi tsaki tace “Ae a haka xa ki kare da reporting din mutane” Dakin mumy ta wuce tana hararanta, har mumy ta gama ma baby fada bata ce komai ba, tana fita ta kira Khadijah suka sauka downstairs su jira ya Aliyu tana kumbure kumbure. Babu yanda Aliyu ya iya haka ya tafi har da iklima, baby ce gaban motar, iklima da Khadijah kuma a baya, babu abinda ya fi ba Aliyu takaici irin shegen make up din da tayi a fuska. Smart kids ice cream spot ya nufa da su, bayan ya siya masu ice cream da pizza da fries ya mayar da su gida duk da ba haka ya so ba amma saboda iklima ya fasa duk abinda yyi niyya. Ranan lahadi da daddare Anty khadijah ta dawo gidan, Mumy da Aliyu dake xaune parlor suka bi ta da kallo ganin yanda ta yi wujiga wujiga, bata yarda ta tsaya parlor ba sannu da gida kawai tayi ma yar uwar tata ta wuce sama da sauri, Aliyu ta kalli Mumy yace “Daga ina take mum?” Mumy tace “Allah kadai ya sani” Anty khadijah na shiga daki ta bude press dinta ta tura jakarta sannan ta rufe ta tube kaya ta shige bandaki, sai da tayi wanka ta sauya kaya sannan ta fito tana kwala ma siyama kira ta xo ta xuba mata abinci, xaunawa tayi parlor, Mumy dake ta kallonta tace “Lafiya na gan ki haka” da sauri ta kalli mumy tace “A ya kika gan ni?” Mumy tace “Atoh, kinga wani duhu da kika yi kamar warce taje kauye” Anty khadijah tace “Kauye kuma, Zaria fa nace maki xan je, kuma gashi har naje na dawo” Mumy tace “Toh Allah rufa asiri” Sai a sannan Aliyu ya gaisheta, fuska a murtuke ta amsa can ciki, ya mike yyi wucewarsa sama, tana kallon mumy tace “Ina d’a na saleem?” Mumy tace “Ya je Abuja jiya da kika tafi, ina jin daga can ma xai wuce Germany, toh wai ke da kika ce kwana biyu xa ki yi Khadijah ya aka yi kika dawo yau, jiya da safe fa kika tafi?” Anty khadijah ta hade rai tace “Kai Anty fati, to kwana biyun bai yiwuwu ba” daga haka ta mike ta wuce kitchen don xuba abinci ganin siyama bata sakko ba.
_Littafin Noorul Hayat na siyarwa ne, kindly patronize ur Novelist and read happily_🥰
-

Noor Al Hayat 34
Tun da suka iso kano Khadijah ta fito daga cikin tasha
Fitowa Umma tayi da sauri jin kakarin aman khadijah, ta karaso da ita ta duka tace “Subhanallahi…. Are you okay” khadijah ta kasa cewa komai duk ta galabaita lkci daya, Umma ta taimaka mata ta wanke baki sannan ta dagota ta wuce parlorn ta da ita, Khadijah ta kwanta kan kujera tana mayar da numfashi da kyar tace “Umma I don’t knw what’s wrong with me, I am always week” Umma tace “Sannu, ko malaria ne, bari Alhaji ya dawo sai mu tafi asibiti ni bani da kudi a gu na” Khadijah ta lumshe ido har lkcn tana sauke ajiyar xuciya, mikewa Umma tayi ta fita don wanke gun aman, tana isa bakin kofa ta ji muryar Hasana tana cewa “Wllh fah, sai kace mai ciki, ji fa salon aman ma daban ne, idan ma malaria ne ba yellow shataf kalan aman ya kamata ya xama ba” Shafah tace “Haka fa shekaranjiya ina lura da ta shiga kitchen duba mata girki daga xama kan kujera sai bacci, daxu kuma da safe nan bakin kofa ta xauna da abinci a gabanta tayi bacci, ace baccin nan ba lafiya ne?” Umma dake tsaye bakin kofa har lkcn gabanta yyi mugun faduwa, fita tayi parlornta a fusace duk da ta fi wata uku bata tanka su a gidan tace “Sai dai ku ga ciki can kan ‘ya yanku ko dangi, amma ba ‘ya ta ba, tunda baku da kirki baku da Imani har ku yi ma yar mutum fatan wannan mugun abun, Allah ya isa wllh” Hawaye cike idonta ta kare maganar, Shafah ta mike tana huci ta kunduma mata xagi tace “Bakin ki ya sari danyen kashi, ba ma ga mugun abu ba a ‘ya ya ko dangi, to wa yasan inda kika kai ta kwanki ko karuwanci kika sa tayi maki….” Umma ta juya ta koma daki hawaye na sakko mata sosai, kallon khadijah ta tsaya yi taga har tayi bacci, ta xauna duk jikinta a sanyaye a xuciyarta tana kara yi ma su Shafah Allah ya mayar masu mugun alkaba’in da suka yi ma ‘yar ta. Har karfe tara Khadijah na bacci bata tashi ba, tada ta umma tayi hankalinta ya tashi jin irin xafin da jikinta ya dauka, da kyar ta lallabata ta sha shayi kadan sannan ta bata paracetamol ta rakata bedroom dinta ta kwanta ita ta dawo parlor ta xauna har lkcn xuciyarta ya kasa dawowa dai dai, khadijah ce ta fito da sauri daga dakin umma na tambayarta me ya faru amma ta fita waje tun kan ta karasa can gun kwararon ruwa ta dinga amai a tsakar gidan, Umma da ta bi bayanta ta tsaya tana kallonta, jin sound din aman yasa Hasana ta leko sai ga Shafah ma ta leko, Umma ta koma ta dauko buta, ta durkusa kusa da ita har ta gama sannan ta wanke mata baki suka koma ciki, sai shivering take cikin rawar murya tace “Umma ki rufe ni sanyin” Umma ta dauko duvet da sauri ta rufe ta, nan da nan kuma bacci ya dauketa. Umma ta koma parlor ta xauna duk ta rasa me ke damunta, jin shigowar Abban fadila gidan ta jira har ya shiga part dinsa da minti sha biyar sannan ta fita, sallama tayi bakin parlornsa ya amsa ta shiga, Shafah ce a parlorn tana xuba masa abinci shi kuma yana kallon news, Umma ta xauna ta gaishesa ya amsa, a hankali tace “Alhaji dama idan da hali don Allah kudi nake so ka ba mu xan kai khadijah asibiti bata da lafiya tun safe” Shafah tace “Ae gwara aje asibitin nan kam wannan amai da bacci haka a gida” Umma tayi shiru tana kallonta, Abban fadila yace “Nawa ne kudin asibitin?” Shafah tace “Tun da ya sanka likitan kamar family Dr ne ko dubu 3 ka basu xai yi ai” ita dai Umma bata ce komai ba, Ya mike ya shiga ciki sai ga shi ya fito da dubu hudu ya mika mata yace “Gashi sai ku yi har kudin mota” ta karba da ladabi tace “Toh mun gode sai da safe” daga haka ta mike ta bar parlorn. Washegari da sassafe Umma ta sa Khadijah ta shirya bayan ta tilasta ta shan shayin da ta hada mata amma tas ta amaye sa gaba daya, duk ta xabge tayi laushi lkci daya sbda aman da take yi, A dai dai ta umma ta samo masu har kofar gida ganin kamar baxata iya tafiyar ba ma, Hasana dake sharar tsakar gida tace “Toh a dawo lafiya dai, Allah raba bawa da jin kunyan duniya da lahira dai” Umma bata tanka ta ba tana rike da Khadijah suka fita, wani asibitin daban ba wanda suka saba xuwa Umma taje ba, suna xuwa aka ce sai sun yanki kati dubu biyu, duk jikin umma yyi sanyi, shiru khadijah dake xaune tayi tana kallon nurse din dake tsaye Kansu, nan ko tuna kudin da Aliyu ya bata take yana bayan kujeran umma ta ajiye bata kuma nuna ma umman ba har lkcn, Umma ta mike tace ma nurse din tana xuwa yanxu, Cike da karfin hali Khadijah tace “Umma ina xa ki?” Tace “Yanxun nan xan dawo khadijah” daga haka ta fita. Gidan wata kawarta dake layin ta tafi ta ranto dubu biyu da yake suna mutunci da matar sosai ta bata sannan umma ta dawo asibiti, bayan an yankar masu kati suka samu ganin likita, Umma ce ke fadin abubuwan da ke damun khadijah ma likitan, don Khadijahr duk tayi weak, tambayar farko da likitan ya jefo ma Umma shine “Tana da aure ne?” Gaban umma yyi mugun faduwa ta girgixa ma likitan kai kawai, likitan yace “Toh xa ayi mata test…” Bai dai fadi wanne ba umma tace “Toh” ya kira nurse ya bata file din nasu yace su bita, Umma na rike da hannun khadijah suka dawo reception, Nurse din tace kudin test din dubu biyu da dari biyar haka Umma ta bata duk ta yi wani sanyi, suna ta xaune a reception har bayan mintuna da dama result ya fito matar ta ce su je office din Dr bayan ta kai ma sa, Likitan dake ta kallon umma yace “Yar ki ce yarinyar nan?” Umma ta gyada masa kai xuciyarta na bugawa, ya girgixa kai yace “Sorry madam, She is few weeks pregnant” mikewa Umma tayi a mugun gigice tace “Pregnant Dr?” Likitan ya gyada mata kai, Khadijah da ta xaro ido ta dinga kallon likitan xuciyarta na bugawa, kuka sosai Umma ta saki a gun ta juya ta fita, khadijah ta mike ta bi bayanta da sauri, likitan ya girgixa kai ya bi ta da kallo a ransa yace why Such a beautiful girl, Gaba daya asibitin Umma ta fita har lkcn tana kuka, khadijah da duk jikinta ya mutu ta dinga bin ta ita ma, har lkcn ita dai bata gane wani pregnant din likitan ke nufi ba, adai daita Umma ta hau tayi wucewarta gida, Khadijah da tayi still a inda take ta bi adai daitan da kallo ta kasa kwakkwaran motsi, lkci daya duk ta nemi xaxxabin da rashin kwarin jikin dake tattare da ita ta rasa, har sannan kuma ta kasa kukan, tafiya ta fara yi kamar warce kwai ya fashe ma, da yake ba wani nisa ne da asibitin ba har ta isa gida, Hasana da Shafah na xaune tsakar gida ta wuce parlorn Ummanta suka bi ta da kallo, bata ga Umma a parlor ba a shiga bedroom dinta, xaune ta ganta nan kasan dakin banda kuka babu abinda take, ta sulale kasa a hankali sai a sannan wasu hawaye masu xafi suka dinga sauka idonta, Muryar Umma taji cikin kuka tana cewa “Khadijah yanxu ni xa ki kunyata, ni xa ki yi ma tonon asiri a idon duniya, is this my reward for taking you as a daughter?” Khadijah na shessheka tace “Ummata kiyi hakuri” mikewa Umma tayi da wani force ta sauke mata mari, bata gama recover ba ta kuma kai mata wanda ya fi na da, kasa kwakkwaran motsi khadijah tayi a inda take durkushe lkci daya taji komai ya tsaya mata, Umma na mata wani kallon da xa a iya kiransa da na tsana tace “Kin cuce ni kin ci amanata, kin ci amanar late mahaifinki” hakan da ta fada ya sa khadijah rushewa da kuka mai ban tausayi cikin rawar murya tace “Na shiga uku, don Allah Ummata ki yi hakuri” ta kuma kai mata wani marin tana kuka sosai tace “Uban waye yayi maki Ciki khadijah” kamar numfashinta xai dauke take kuka tana girgixa kai tace “Ban sani ba Ummaa” rufeta tayi da duka har sai da ta gaji don kanta ta kyaleta kuma har lkcn kuka take, cikin raunin murya tace “Tashi ki bar min gidana kije duk Inda xa ki je tunda baki san wanda yyi maki ciki ba, Allah ya isa tsakanina dake khadijah, kin bata min suna, ki tafi khadijah xaman ki gidan nan xai iya kashe min aure ki tafi bana son ganin ki kije duk Inda xa ki” gyada mata kai kawai khadijah take tana sheshsheka, shigowan su Shafah da Hasana dakin yasa Umma tayi shiru har lkcn tana kuka, suka gama kare masu kallo sai suka saki shewa sannan suka fita dakin, khadijah ta mike da kyar don banda ciwo babu abinda ko ina na jikinta ke mata ta fita dakin tana goge jinin bakinta, bayan kujera ta tafi ta dauki envelope din da Aliyu ya bata wasu hawaye masu xafi na xubo mata, xaxxage bundle din kudin tayi gaba daya a kasa sai ga wani farar takarda a linke ya fadi, ta dau takardar ta warware tana kallon content din, *I don’t have much to say khadijah, na san har abada baxa ki mance abinda ya faru tsakaninmu ba kamar ynda nima baxan mance ba, tafiyar ki shine ma fi alkhairi sbda baxan taba samun kwanciyar hankali da nutsuwa ba matsawar muna gida daya, ina rokon gafarar ki Khadijah forgive me not because I deserve it but for the sake of Islam, Allah hada fiskokinmu a aljannatul fiddaus, ina maki fatan alkhairi a rayuwa da fatan miji na gari* cukuikuye takardar tayi ta fashe da wani kukan takaici taji dama ta kashe kanta ta huta amma bbu daman yin hakan, mayar da kudin tayi envelope din har ma da takardan ta mike ta fice parlorn tana share hawayen da ya ki tsaya mata, ko kadan bata ji me su Shafah ke cewa ba har ta fice gidan gaba daya, khadijah bata xarce ko ina ba sai tashar mota, tafiya kawai take a park din tana jin sunan garuruwan da ake fadi har ta isa gun motar garin Yobe ta hau bayan minti goma mota ta cika suka dau hanyar damaturu garin da bata san kowa ba bata taba xuwa ba.*What I want some people to get here is that, wnn labarin khadijah ne, kun riga da kun san rayuwarta a yanxu, she is living a normal life just dat abubuwa da yawa na memory dinta ne har ynxu, what I am writing now is her past ya riga ya wuce so I don’t knw why wasun ku ke damun Kansu being emotional, this is not what is happening presently, it’s just her past story*
Da tsakar rana Khadijah suka iso garin damaturu, ta fito a hankali daga motar tana bin ko ina na park din da kallo, wani jiri ke dibar ta a lkcn ga sanyin da take ji ba kadan ba, tana tafiya a hankali har ta fita park din, kallon masu adai daitan dake ta tambayata Inda xata ta dinga yi lkci daya hawaye ya cika idonta, bata ce komai ba ta dinga tafiya, bata san iyakar lkcn da ta dauka tana tafiya ba, jin baxa iya ci gaba da tafiyar ba ta samu karkashin wani bishiya da ta hango duk anyi littering dinsa da 6awon rake ta xauna tana sauke numfashi a hankali, cikin Hijab dinta ta ajiye envelope din hannunta, bacci ne ya dauketa lkci daya a hakan saboda iskan da leaves din bishiyar ke ta bayar wa, bata san lkcn da ta dauka tana bacci ba hayaniyar wasu almajirai ya tada ta, ta gyara xamanta da sauri tana kalle kallen wajen envelope dinta a hannunta, a hankali ta tashi da kyar ta ci gaba da tafiya kamar bata son yi kwata kwata ko yunwa bata ji sai kasala, wannan karan ma tafiya me nisa tayi da kafa ganin wani masallaci ta dau buta dake cike da ruwa ta samu gefe ta xauna ta daura alwala sannan ta tafi jikin wani shago tayi sallahn da bata yi ba, mayar da butan tayi ta ci gaba da tafiya, har aka kira magrib tafiya kawai khadijah take, ganinta a wani kasuwa ta dinga xaga kasuwar, a hankali a hankali kasuwar ta fara watsewa ta shimfida dankwalinta gaban wani shago da aka duk aka rufe tayi magrib da isha ta jingina da table din gaban shagon, wasu hawaye suka dinga bin kuncinta, sanyi sosai ke shigarta ga xaxxabi kan kace me kasuwar yyi tsit kowa ya wuce gida, duk da uban sauron da suka yi yawa a wajen hakan bai hana bacci me nauyi sake daukarta daga xaunen da take a gaban shagon ba, bata kuma farka ba sai da kiran sallar asuba ya farkar da ita, ta dinga bin wajen da kallo, can ta tashi da kyar tana tafiya a hankali kamar iska xai hura ta ta fadi ga wani ciwon xuciya da ta tashi da, banda xugi da axaba bbu abinda yake mata, duk wnn abun sai lkcn taji yunwa na damunta sosai, masallaci me hade da na mata take ta nema amma duk iya tafiyar da tayi bata ga alamar ko daya ba, wani wajen ta samu ta xauna nmta hade kai da gwiwa tana kuka cike da rauni, har gari ya waye mutane suka fara hada hadarsu tana xaune Inda take, cike da karfin hali ta tashi ta nufi titi ta tsaya jiran adai daita, bbu bata lkci wani ya ja ya tsaya, ta shiga a hankali nace “Central mosque xaka kai ni” yace “Na ina?” Tace “Wanda ya fi kusa dai” ba wani tafiya me nisa suka yi ba yyi parking bayan mmsun iso kusa da wani babban masallaci, kudin dake jikinta har lkcn ta fiddo ta ciri dubu daya ta basa yace ba shi da canji, a hankali tace “Toh ka tafi” sannan ta shiga masallacin, bangaren mata ta nufa ta daura alwala bayan ta xaga bayi sannan nmta shiga cikin masallacin ta tada sllh, tana ta xaune bayan ta idar tayi nisa tunanin da take jin agogo yyi stucking karfe tara ta mike a hankali ta fita ta dau tsintsiya tana taya bayin Allahn dake ta sharan masallacin shara, suna gamawa ta fito da kudin ta don duba abinda xata siya ta ci, waina da miya ta siya da ruwa ta dawo cikin masallacin, a haraban ta xauna ta bude ledan abincin tana daukan guda ta kai baki taji cikinta ya hautsine, tayi saurin tashi ta nufi gun da ake alwala da gudu nan ta dinga amai a wajen kamar xata shide, da kyar ta tashi daga karshe duk jikinta ba kwari nmta koma cikin masallacin nmta kwanta ba tare da ta sake bin ta kan masan ba, tana mayar da numfashi, dukunkunewa tayi waje daya jin sanyi na shigarta ta ko ina, wanda hakan na da nasaba da xaxxabin da ya rufeta lkci daya, sai azahar ta farka jin ana kiran sllh. Daren ranan a masallacin khadijah ta kwana, amma washegari da safe wata dattijuwa dake share sharen masallaci tace ta nemi gun da xata dinga kwana daga ranan don masallaci ba wajen kwana bane da ace kwana ake barin mutane ke yi a ciki da bai yi kyan gani ba yanxu, cike da fada take maganan, jikin khadijah yyi sanyi sosai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, karfe sha dayan safiyan ta bar masallacin, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata a lkcn sbda yunwa ce kawai ke dawainiya da ita ga xaxxabi, ramar da tayi ya fito sosai, karfin hali ta dinga yi tana tafiya, tafiya kuma ba na wasa ba tayi ba tare da tasan takamaiman inda xata je ba, ganin she can’t move any further don kafafuwarta sun ma Gmgaza daukar ta kuma ta fara tunanin xuwa wani masallacin ta kwanta, tana tsaye bakin titi tana jiran abun hawa da ta gaji sai ta tsugunna idan ta huta sai ta mike, kawai d’aga kai tayi ta ga wata mata da ta shiga titi da nufin tsallakawa wani mota da ya taho da uban gudu ya kwasheta sai da tayi sama da ita snn ta fado kan titin, duk da nesa da ita aka yi hatsarin amma irin ihun da ta fasa a tsorace xaka ce ita motar ta buge tsabar tsoratar da ta yi, daga nan kuma bata sake sanin abinda ya faru ba ta dai bude idonta da yyi mata nauyi ta ganta kwance wani daki da yyi kama da na asibiti da ruwa a hannunta, dafe xuciyarta dake mata xugi sosai tayi ta dinga bin dakin da ido a hankali lkci daya kuma tana son tuno abinda ya faru amma ta kasa, a hankali ta sauke idonta kan wani mutumi dake xaune d’an nesa da ita idanuwansa da hankalinsa gaba daya kan wayar dake hannunsa, duk da a xaune yake hakan bai boye tsayinsa ba, sajen dake kwance gefen fuskarsa kadai take gani da uban gashin da ya tara a kai, da dogon hancinsa duk ta side view take kallonsa, ta shiga kkrin mikewa xaune da kyar har lkcn tana dafe da xuciyarta dake mata axaba ba kadan ba wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, sai a nan ya kallo direction dinta, mikewa yyi da sauri ganin ta tashi ya karaso kusa da ita yace “Hello… how you feeling now?” kallon jajayen lebbensa kawai take don bata taba ganin haka ba, ya buda dara daran idanuwansa yace “Hey… Are you there?” Kin cewa komai tayi still, ya juya ya fita ba a dau lkci ba ya dawo likita na biye da shi, likitan ya tsaya kanta yace “Hi… How you feeling madam?” Ganin yanda duk suka tsura mata ido, ta sauke nata idon a hankali tace “Alhamdulillah” likitan yyi murmushi yace “Maa sha Allah, hope bbu Inda ke maki ciwo ynxu koh?” Ta gyada masa kai duk da axaban da xuciyarta ke ta yi matan, yace “Good” snn ya juya ya fita, kallon mutumin dake tsaye ya rungume hannayensa tayi cikin sanyin murya tace “Me nake yi a nan?” Sai a snn ya kalleta yace “Kar ki damu xa a sallame ki nan da anjima ki wuce gida, before then ki bani number ‘yan gidanku a kirasu, sure they are all disturb yanxu, you passed out since in the morning… And this is….” Ta kalli agogo da sauri kafin ya fada taga karfe bakwai, ta kallesa tace “Bakwai na safe?” Ya girgixa kai yace “No, Night” shiru tayi bata sake cewa komai ba kamar me naxari, sai a sannan kuma ta tuno abinda ya faru daxu, ta fashe da matsanancin kuka tace “Wayyo matar ta mutu koh?” Hade rai yyi yace “Nooo, an kai ta asibiti ita ma, am sure she’s recovering also” tsoro ne sosai tare da ita tana kallonsa, ya langwabar da kai yace “Ina xuwa” daga haka ya juya ya fita ta bi sa da ido, ko minti biyar bai yi da fita ba sai ga wata nurse da magunguna a leda, ta ajiye kan gado tana mata sannu tace “Idan kin samu abinda kika ci xan dawo in nuna maki dosage” daga haka ta fita. Da sallama ya shigo ward din rike da takeaway din abinci ya karaso ya ajiye kan table dake kusa da gadon yace “Ga shi ki ci abinci ki sha magani kafin a sallame ki….” Bata ce komai ba ya mika mata wayarsa yace “Before then, fara kiran mutanen gidan ku ki sanar da su kina asibiti” shiru tayi bayan ta karbi wayar, ya fada mata sunan asibitin sannan ya fita, hawaye ya cika idonta ta saki kuka a hankali tana tausayin kanta, bayan kusan minti goma ya dawo dakin… kallonta yyi sannan ya kalli abincin ya d’an daure fuska sai kuma ya karaso ya bude ya sa cokali ya mika mata ba musu ta karba tana kallon jollof rice da naman, yace “Kin kira su?” Gyada masa kai tayi yace “They are coming to take you now right?” Nan ma kai kawai ta gyada masa, yace “Alryt, ki ci abincin nurse xata shigo ta nuna maki dosage din maganin yanxu, I’ve paid the bill, Allah kiyaye gaba I will be on my way now…” Kai kawai ta gyada masa tana iya kokarin ganin bata bar hawayen dake taruwa idonta ya xubo ba a hankali tace “Nagode” ya buda ido sosai yace “No thanks” ta lura sauri yake don tuni har ya kai kofa, ta kalli wayarsa dake gefenta a hankali tace “Your phone” ya juyo da sauri yace “Ohh thanks har na mance” daga haka ya dau wayarsa ya fita ward din, ta rufe abincin ta ajiye ta hade kanta da gwiwa hawaye mai xafi na sakko mata, bayan kusan minti goma da tafiyarsa nurse din daxu ta dawo, da sauri ta goge hawayenta, nurse din tace “Kin ci abincin koh?” A hankali khadijah tace “Na ci” nan ta nuna mata dosage din drugs din sannan tace “Sai ki sha yanxu, an riga an sallame ki, yace yan uwanki na hanya koh?” Ta gyada mata kai tace “Toh Allah ya kawo su lfya” daga haka ta fita, ta fashe da matsanancin kuka xuciyarta na mata kuna, sai a snn envelope din kudin dake hannunta da ta fadi ya fado mata, bata wani damu ba don tasan me rabo ya dauke shikenan kuma, bayan wani minti ashirin din nurse din ta shigo tana mata wani kallo tace “Wai har ynxu ba su iso ba yan uwan naki?” Tana kallonta a sanyaye ta gyada mata kai kawai, nurse din ta tabe baki ta juya ta fita, taa ta xaune ta rasa me ke mata dadi har lkcn kanta na bisa gwiwanta nurse din ta shigo da likitan daxu, likitan yace “Ke daga wani garin yan uwanki xa su xo ne har yanxu basu iso ba, ko karya kawai kike ma mutane?” Hawaye cike idonta cikin rawar murya tace “Ehh” ya xare glass din idonsa yana xaro idon yace “Karyan kike?” Ta fashe da kuka a hankali tace “Ni bani da yan uwa, ban san kowa ba, ban san ina xan je ba” a mugun fusace yace “You must be joking, Look malama fita ki bar ma mutane asibitin su, get out yanxun nan, maxa dau sauran abincin ki ki fita kar in kira masu gadi su yi waje da ke” jikinta na rawa ta sakko ta dau abincin da yace tana jin kamar jiri xai kada ta hawaye na sakko mata sosai ta nufi kofa, nurse din ta bi ta da kallo, murya can kasa tace “Dr ko xaka kira shi wanda ya kawo ta tun da kasan shi?” ya jefa mata wani kallo yace “Toh me xai yi mata idan na kira sa, sanin wacece ita yayi aka gaya maki? He just helped her tayi collapsing a gefen titi daga anyi hatsari” khadijah ta bude kofa xata fita likitan yace “Tsaya malama” tsayawa tayi ta juyo tana kallonsa a tsorace, ya ciro wayar sa a lab coat din jikinsa yyi danne dannensa kafin ya sa hands free wayar ya fara ring, sae da ya kusa katsewa aka daga, likitan ya ce “Sudais, ga patient din da ka kawo mana taki tafiya fa….” daga daya bangaren aka ce “I don’t get you” a d’an fusace likitan yace “I also didn’t get what she meant by saying she don’t have relatives and she don’t knw where she’s heading, don Allah ka xo ka fidda min ita a asibiti plss” Wanda ya kira da Sudais cikin expression din mamaki yace “Ji min walakanci fa, toh ni da ka kira ni me xan yi? If I am not mistaken I told you I don’t knw her Yusuf, then why calling me? Me yasa kake kirana? Wait wllh sai ka gaya min me yasa ka kirani ma dai, are you not just suppose to tell her to leave kayi discharge dinta???” Likitan ya kalle Khadijah a fusace yace “Ke malama maxa nemi Inda dare yyi maki kada in sa a xo a fitar da ke yanxun nn, get out plss” kai ta gyada masa jikinta na rawa hawaye na sakko mata, Da sauri Sudais din yace “Wait Yusuf, you knw what? kaga dare yyi ynxu ka bari gobe da sassafe kace ta wuce plss since she’s lying she don’t have relative” likitan yace “Sai dai idan xata sake biyan kudin gado, don da ace haka ake yi a clinic din da ba mu samu ci gaba ba” Shiru Sudais ya d’an yi kafin yace “Toh naji xan biya ka, though I hate lies and liars let her just be safe there kafin ta wuce gobe, just dat 1st thing tomorrow morning send her away, good nyt” daga haka ya watse wayar, ko kallonta likitan bai yi ba yace “Bani hanya” ta bar bakin kofar da sauri yyi ficewarsa kamar xai tashi sama, Nurse din ta karaso kusa da ita tace “Me yasa kika yi karya yan mata, ke ba musulma bace?” Khadijah ta girgixa mata kai hawaye mai xafi na xubo mata, nurse din ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh tafi ki kwanta” daga haka ta fita ta bar ta tsaye, karasawa tayi kan gadon ta kwanta tana share hawayenta, wajajen karfe sha biyu ta tashi xaune jin yunwa na nemanmatat illa ta bude abincin daxu, amai ne ya taho mata bayan ta kai baki ta sauka kan gadon da sauri ta shiga bayi ta dinga amai kamar xata amaye hanjinta, jikinta a mace ta fito ta kwanta bisa gado tana sauke ajiyar xuciya ta kudundune waje daya daga haka bacci ya dauketa sanyi na shiga jikinta.
-

Noor Al Hayat 29
Throughout schl days ko assignment aka ba su Iklima ko average bata ci, daga 2 sai 3, baby ta samu abun dariya kullum cikin mata dariya take, ita dai Khadijah ba ruwanta nata ido, yau Friday tun da suka dawo schl khadijah ke kitchen gun kyauta tana bata labarin makaranta, kyauta tace “Toh ni abinda nake son sani a nan shine, ita ikliman bata gane karatu ne da bata amsa tambaya a aji?” Khadijah ta hade rai tace “Ni Anty mai girki am not gisting you about her ba ruwana kawai ina baki labarin masu kokari ne a aji” Kyauta tace “Ke dai kin fiye tsoro tsiya shi yasa baby ke burgeni, shegen duka take ma mummunar yarinyar” Khadijah tayi yar dariya tace “Ni dai ba ruwana Anty mai girki” Kyauta ta kyabe baki tace “Yo ai ba karya nayi ba, mummunar karshe ce yarinyar da nanikakken hanci kamar an taka amala a kan hanya, ido mitsi mitsi kamar na tana, baki kamar gidan tsutsa, ga gashinta kamar na hammata na” Khadijah ta fashe da dariya har da kyakyatawa, kyauta ta washe baki tace “Atoh, duk uwarta ce ta ja mata ai, da bata gallaza ma ‘ya yan wasu da Allah bai hada yar ta da kwakwalwar tantabara ba, da yanxu bata nuna maki tsana kiri kiri ba ai ke xa ki dinga assisting dinta kina koya mata kamar yanda ku ke yi da baby, amma uwar taki xaman lafiya da kowa, meye amfanin haka a rayuwa…. Da ta kwantar da hankalinta ma wataran duk baxa ta gan mu a nan ba sai dai idan Allah yyi xa a sake saduwa” ita dai Khadijah bata ce komai ba, kawai ji suka yi ana cillo da jakunkuna waje, duk suka kalli juna sannan suka fita da sauri, Anty Khadijah ce tsaye parlorn duk ta fiddo Ghana must go da jakar kyauta da komai nata dake cikin daki waje, Tana wani murmushi tace “Dama rana irin ta yau nake jira, har ni kyauta xaki tsaya kitchen kina yi da ni kina yi da ‘ya ta, to xaman ki ya xo karshe gidan nan yanxun nan kuma ba sai anjima ba, in dai ba gidan ubanki bane, ba kuma na uwarki bane nan din tattara ina ki ina ki ga su nan ki kama gabanki” kyauta tayi shiru tana kallonta, kofa Anty khadijah ta nufa kamar xata tashi sama ta fita compound cikin tsawa ta dinga kwala ma Usman kira ya biyota da gudu yana amsawa ta shigo parlor tana nuna masa kayan tana huci tace “Maxa kwashe tsummokaran nan ka fita da su can wajen gate” Khadijah ta fashe da kuka tace “Anty don Allah kiyi hakuri kar ki koreta…” Fixgota Anty khadijah tayi ta kai mata wani mugun dundu har sau uku a baya ta gware kanta tace “Tsinanniya ae nan ba da dadewa ba xa ki bi ta kema, mu dai je xuwa” Khadijah bata daddara ba ta durkusa tana kuka sosai tana kallon kyauta dake ta kallon Anty khadijah tace “Anty mai girki kice tayi hakuri don Allah” cikin tsawa Anty khadijah tace ma kyauta “Ki fita nace kar in fitar da ke da kai na munafuka annamimiya” Kyauta tayi murmushi tace “Xan tafi, ke kuma Allah ya hada ki da dai dai ke a rayuwa” Khadijah ta fashe da matsanancin kuka ta rike kyauta cikin rawar murya tace “Don Allah Anty mai girki kar ki tafi ki bata hakuri, kar ki tafi ki bar ni” haurinta Anty khadijah ta yi kamar ta samu ball tana huci tace “Tashi ki kwaso naki kayan ki bi ta kema…. Ba sai kin ce kar ta tafi ba” Tashi da sauri khadijah tayi tana kuka xata je dauko kayan nata Kyauta ta rikota tace “Kar ki damu Khadijah in sha Allah xa mu hadu wataran, ke dai ki kula da kanki ki rike maraicin ki Allah na tare da ke” daga haka kyauta ta saketa ta dau jakarta daya da ya rage parlorn ta nufi kofa ba tare da ta bi ta kan kudin aikinta ba, Baby dake tsaye parlorn ta fashe da kuka tace “Anty me yasa xa ki koreta, she is very kind, and she can cook” Anty khadijah ta ja kunnenta da karfi tace “Nan din gidan ubanta ne da baxan koreta ba, masu halin tsiya… Ga ku so dangi” daga haka ta bi bayan kyauta da sauri domin ta tabbatar ta tafi, bata dawo ciki ba sai da ta tabbatar kyauta ta bar layin gaba daya, mai gadi duk jikinsa yyi sanyi amma bai ce komai ba, ta dawo ciki tana yatsine fuska tace “Gayyar tsiya, ita kuma Anty fatima idan ta dawo nima sai ta koreni in ga” jan iklima dake ta murmushi a parlor tayi xuwa sama, don ita ce ma taje ta kira ta a daki wai kyauta na xaginta. Har mumy ta dawo khadijah na xaune can inda kyauta ta saba ce mata ta xauna farkon xuwanta gidan, tayi kuka har ta gode Allah, kasa cewa komai Mumy tayi bayan baby ta gaya mata abinda Anty Khadijah tayi ma kyauta, jikinta yyi mugun sanyi ta wuce daki da kyar ta kira Aliyu, ce masa tayi ya dawo gida yanxu, jin yanayin muryar mahaifiyar tasa yasa ko minti biyar bai kara ba a clinic ya taho gida, har ta gama bayyana masa abinda ya daga mata hankali bai iya yace komai ba yana tsaye dakin shi ma jikinsa yyi sanyi, can ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace “kiyi hakuri mumy, yanxu kinsan inda xa a samo kyautar?” Cike da damuwa Mumy tace “A ina xan sani Aliyu, matar da ba waya gare ta ba, gashi ko kudin aikinta ba a bata ba, yanxu Khadijah ciwon xuciya take son sa min ne a gidana shine abinda ban sani ba har yanxu, don me yasa bata son in xauna lafiya yanda nake so a gidana, me yasa khadijah take min haka, don nace ta xo mu xauna tare laifi nayi Aliyu da xata dinga cuta ta haka, don wannan wallahi cuta ce” Yyi kasa da murya yace “Don Allah kiyi hakuri mumy, Allah ya ganar da ita…. Xan ma mai gadi magana yanxu idan Allah yasa kyautar ta dawo ya bar ta ta shigo kawai” daga haka ya fita, labe ya ga Anty Khadijah jikin kofa tana eavesdropping duk abinda suke cewa, tana ganinsa tayi masa wani shegen kallo hade da tsaki ta shige dakinta, bai ce komai ba sai tabe baki da yayi ya sauka downstairs. Bayan ya sanar ma mai gadin ya bar kyauta ta shigo ko da xata dawo…. ya koma cikin gida, har lkcn baby na ta kumbure kumburen an kora kyauta a dinning, su siyama kam ko a jikin su, a ransa yace “xa su ci gidansu da aikin gidan nan kuma Yanxu” ya karasa dining yana kallon baby yace “Ina Iman?” Hannu ta buda masa alamar bata sani ba, kitchen ya shiga ya fita waje, xaune ya ganta har lkcn a gun idonta ya kumbura don kuka, ya tsaya yana kallonta can ya karasa wajen ta, tana ganinsa ta kuma rushewa da kuka ta kife kanta da gwiwa, ya durkusa gabanta yace “Kukan me kike?” Ta dago da sauri cikin rawar murya tace “Yayanmu Anty ta kori Anty mai girki” shiru ya d’an yi kafin yace “Ko xa ki bi ta ne?” Ta gyada masa kai da sauri, yyi murmushi yace “Toh kiyi hakuri, xata dawo in sha Allah” a hankali tace “Yaushe?” Yace “Mumy xata nemo ta” shiru khadijah tayi ya mike yace “Tashi ki je ki wanke fuskar ki” Tashi tayi ta tafi gun tap ta wanke fuskarta sannan ta dawo tana kallonsa yace “Kar ki sake kuka fa” tace “Toh” juyawa yyi ya shiga gidan ta bi bayansa, tsaye suka ga Anty Khadijah a kitchen ta hada kwanukan wanke wanke xata yi, Aliyu ya danne dariyarsa bai sake kallon direction dinta ba har ya fita kitchen din, Khadijah xata wuce tace “Zo nan…” Dawowa Khadijah tayi ta nuna mata tsintsiya tace “Maxa ki tafi ki share gaba daya gidan ai aikin ki ne kema, kuma babu uban da xai maki” daukan broom din Khadijah tayi ta fita, dai dai sakkowar mumy tana ganinta tace ta ajiye tsintsiyar su je daki su yi assignment da baby, ajiyewa tayi ta wuce sama dakin baby. Washegari da Asuba Anty khadijah ta shiga kitchen, Aliyu dake xaune parlor tun bayan da ya dawo masallaci sai murmushi yake jin yanda take ta dambe da utensils a kitchen, idan ta dauke wancan sai wannan ya fadi, tayi tsaki ya fi a kirga, karfe bakwai saura ya wuce sama don yin wanka ya tafi aiki, yana gama shiryawa ya fito ya shiga dakin baby kamar yanda ke yi duk safiya don ganin ko sun shirya, tsaye ya ga baby tana duba ma khadijah idonta da yyi ja, ya karasa dakin yace “What happen” baby tace “Yayanmu we where just on our own muna shiryawa fa, kawai sai ga ikliman nan ta shigo wai mun sace mata pen, can you imagine fa, alhalin karya ne she lost her pens gaba daya da mumy ta ba mu, shine ta dauke na Iman wai nata ne ta sace har da buga mata pen din a fuska shine ya taba idonta gashi yana mata ciwo yanxu, Yayanmu a daina siya mana komai iri daya ka gaya ma Mumy plsss, iklima don’t like peace, she is always looking for conflict, I really dont like that girl” Aliyu ya duba idon Khadijah yace “Ke kuma kina xaune ta tsone maki pen a ido koh” Baby tace “Noo, Yayanmu the thing in here is that Iman don’t like trouble, I just notice that, if not da ace ni ce… I will beat her blue black har sai Anty baxata ganeta ba” juyawa Aliyu yyi ya leka dakin Anty Khadijah ya ga ikliman bata ciki, fita parlor yyi ya ganta a dinning har uwar ta hada mata shayi ga uban soyayyen kwai a gabanta da bread, Saleem ma na xaune dinning din yana breakfast, fita yyi ya xaga ya k’arya branch din flower ya dawo, yana daga tsaye a bakin kofar parlor, yace “Iklima” tun da ta xo gidan sae ranan ya kirata, ta taso da sauri tace “Ni?” Yace “Eh xo” karasawa tayi kusa da shi ya jawo ta waje ya kulle kofar parlorn, ya rike duk hannunta biyu yace “Ni sa’an ki ne da sai dai ki kalle ni a gidan nan baxa ki gaishe ni ba” hade rai tayi xata kwace hannunta ya kai mata Rankwashi ya murda kunnenta da karfi, ta bare baki ta fara kuka, hakan ya basa daman tsula mata bulalan hannunsa, ya xaneta ta ko ina a jikinta to his satisfaction, sai ihu take tana kiran Anty khadijah, Saleem ne ya bude kofa da sauri uwarta kuma ta fito kitchen a rude tana tambayar me ya faru, ina iklimar, ko kallon Saleem Aliyu bai yi ba ya kara rankwashinta ya turata ya nufi gate da sauri ya fice daga gidan. Hauka ne kadai Anty khadijah bata yi ba barin da ta ga yanda bulala ya kwanta ta ko ina a jikin yar ta, Da ta tambayeta me tayi masa cikin kuka tace “Wai bana gaishesa” ran Anty khadijah yyi mugun baci, cikin fada tace “Shi gaisheni yake yi a gidan? Ae wllh sai dai idan baxai sake dawowa gidan nan ba, ina nan ina jiransa, sai ya gaya min dalilin haka, jaka ya samu ko tinkiya? Idan yana jin haushina sai aka ce ya sauke kan ‘ya ta, yayi facing dina mana, toh wllh xai dawo ya same ni sai ya gaya min ko a kansa kike xaune gidan yau, toh wai ma shi akwai wanda ya kai sa fitsara, yanxu idan nace Allah ya isa ace ban kyauta ba koh, yaushe rabon da yyi min gaisuwar kirki a gidan nan, toh wllh sai ya san ya doke ki” ita dai mumy na tsaye ta kasa cewa komai, Anty khadijah na huci ta ja iklima dake aikin rusa kuka tayi sama da ita, Baby har da rike cike saboda dariya a dakinsu, bayan ta yi mai isarta tace “Yayanmu and sense, that served her right” Aliyu kam yana fita aiki ya tafi abun sa ba tare da ya waiwaiyi motarsa ba. Haka rayuwa ta ci gaba da kasancewa a gidan har su Baby suka fara shirin yin junior waec, sosai Aliyu ya ji dadin tafiyar kyauta don yanxu kam kowa aiki yake a gidan, duk sanda Anty khadijah xata shiga kitchen in da safe ne to karfe takwas da rabi yaran xa su makaranta, idan da rana ne to sai kusan biyar xa a ci abinci gidan, idan kuma da daddare ne sai goma wasu har sun yi bacci, ga girkin ba kan gado yau ya yi half done gobe ruwa yyi yawa, hakan yasa Mumy ta gwammace ta shiga tayi da kanta tare da su siyama su yi ta turo baki, wanke wanken gidan kuma aka raba ma Baby, Khadijah da iklima, duk sanda iklima ce da wanke wanke idan Anty khadijah ta faki idon mumy sai ta sa khadijah tayi tana hantararta da xagi wai ai aikinta ne dama, idan kuma mumy na parlor toh ita da kanta take fita ta taya ‘yar tata wanke wanken tana cika tana batsewa kamar irin ba a son iklimar, shara kuma Aneesah da Siyama ke yi da goge goge, sai kowa ya gyara dakinsa ya wanke bayi, har lkcn khadijah ta kasa mance kyauta, kullum sai tayi tunaninta wani lokacin har da hawayenta baby tayi ta lallashinta, ga Anty Khadijah ta sa ta gaba fiye da da a gidan barin idan mumy ta tafi aiki, duk gidan gun Aliyu da Baby kadai take samun sauki sai Mumy, shi kansa saleem ko inda yake bai son ganinta, shi yasa idan yana gidan tayi ta xaman daki kenan tana karatu, sau tari ummanta kan fado mata, ko a ina xata sake ganinta kuma? duk da alamun girma ya fara bayyana sosai jikin Khadijah bbu mai gane hakan saboda yanda ta tsiri sa Hijab a gidan, kamar yanda Aliyu yace ta dinga yi, Mumy ta sha mata fadan sa Hijab da take a ko da yaushe amma ta kasa bari, hakan yasa mumy ta kyaleta kawai da ta lura baxa ta iya barin bane, a hakan suka fara junior waec, ko da yaushe tare xa ka ga Khadijah da baby suna karatu amma iklima daga kallo sai bacci uwarta bata ce mata komai, duk ta wani xama lukuta sai kumatu ko wa ya ganta yasan ba cin wasa take ba, idan mumy tayi maganar rashin karatunta sai Anty Khadijah tace ai tana yi cikin dare idan kowa yayi bacci, kullum suka dawo makaranta fuskar iklima a murtuke xaka gansa alamar dai bbu abun arxiki a exams din ranan, baby ce mai shiga harkarta dama tayi ta tsokanarta tana dariya, ita kam khadijah ba ruwanta. Ranan da suka yi last paper dinsu, Anty khadijah ce taje dauko su don Sanusi baya nan, su siyama kuma sai hudu dama xa su dawo gida, Khadijah na ganin Anty khadijah ce ta xo daukansu jikinta yyi sanyi sosai, bayan su baby sun shiga xata shiga Anty khadijah ta jefa mata naira Dari tana mata matsiyacin kallo tace “Wannan kuma baki isa ba, idan xa ki nemi abun hawa ki nema don kaza kazan ki” daga haka ta ja motarta, baby ta bata fuska tana kallon small mum din tata, Iklima kuma sai kallon khadijah take ta glass tana murmushi, a sanyaye Khadijah ta durkusa ta dau kudin hawaye cike idonta, a yanxu ne abinda Anty Khadijah ke mata ke damunta sosai ita kanta bata san me yasa ba unlike before, ni kam nace ko don ta fara sanin ciwon kanta ne? Napep ta samu ya kai ta har kofar gida ta basa darin sannan ta shiga cikin gida tana gaida Usman ya amsa da fara’a yana tambayarta ita kadai ta dawo yau ina sauran, murmushi kawai tayi masa tace suna xuwa, tayi mamakin da ta riga su dawowa gida, ta wuce cikin gidan wanda da alamar dai babu kowa ciki, sama ta wuce don cire uniform, tana cire riga aka bude kofar dakin ta juya da sauri, saleem ne tsaye bakin kofar ta sunkuyar da kai tace “Ina yini ya saleem?” Bai amsa ba instead sai ma shigowa da yayi ya rufe kofar, ta koma baya a hankali tana kallonsa, ya rungume hannayensa yana kallonta yace “Na maki wani abu a gidan nan ne da ba kya shiri da ni?” Kasa kallonsa tayi, da kyar ta tattaro abun cewa “A’a baka min komai ba” ya taho kusa da ita yace “Toh me yasa sai Aliyu kike kulawa” ta koma baya kamar xata yi kuka tace “Kai ma ina kula ka ai” kamo hannunta yyi ta fixge da sauri hawaye cike idonta a hankali tace “Bana son haka.. Am I not just like baby to you” Wani kallo ya mata yace “You are not, baby is my blood” ya sake riko hannunta ta kuma fixgewa, dago kanta yyi yana kallon kwayar idonta dake cike da hawaye yace “You are pretending you don’t want me to touch ur hands?” Hawayen idonta ya silalo tace “I am not, I just don’t want that” Yyi wani murmushi yace “then you have to, just for today” ta sauke idonta muryarta na rawa tace “Am sorry ni ba yar iska bace” daga haka xata wuce ya fixgota da karfi tayi wani kara yace “Ni ne d’an iska?” Ta fashe da kuka sosai tace ” Ya saleem don Allah kayi hakuri ka kyaleni, stop this…” Bai kai ga cewa komai ba aka bude kofar dakin, a tare suka juya da sauri, Aliyu ne tsaye bakin kofar, ya dinga kallon saleem ko kiftawa babu, saketa Saleem yyi ya nufi kofar, Aliyu dake kallonsa a hankali yace “Me kake yi a nan?” A takaice yace “Nothing” xai bi gefensa ya fita ya mayar da shi dakin sannan ya sauke masa mari, dafe kuncinsa yyi yana kallon yayan nasa da mamaki yace “Mari na kayi fa?” Aliyu yace “Toh rama” ya fi second ashirin yana kallon yayan nasa sannan ya fice daga dakin, Khadijah ta durkusa kasan dakin ta hade kanta da gwiwa tana kuka, karasawa yyi cikin dakin yana kallonta a hankali yace “Me yasa kika dawo gida ke kadai?” Cikin kuka tace “Anty Khadijah ce tace baxan shiga motar ba, shine ta bani kudin mota” bai sake cewa komai ba, bayan kusan minti daya ya durkusa gabanta, a hankali yace “Forgive him Iman, kiyi hakuri” hawaye na sakkowa idonta tace “I have done that” bai sake cewa komai ba, a hankali ta mike ta dau Hijab dinta ta sa ya bi ta da ido, mikewa yyi yana kallonta yace “Plss kar ki gaya ma Mumy komai Iman, she will be disturbed” ta kallesa a hankali tace “I won’t” daga haka ya nufi kofa, dakin saleem ya shiga ya samesa xaune gefen gado, strictly yace “Saleem this shud be ur 1st and last attempt idan ba haka ba, I will make u start imagining if I am ur blood or not” daga haka ya fice masa a dakin. Anty khadijah ce xaune dakinta tana ta kallon Saleem da wani expression tace “Ya mare ka fa kace?” Saleem dai ya hade rai bai ce mata komai ba, a fusace tace “Toh don me baka rama ba?” Ya kalleta yace “In rama Anty?” Tace “Ehh mana, tun da bai rike girmansa ba, fuska ya fi fuska ne? Sannan uban me ma ya dawo da shi, da na bar gidan fa baya nan….” Saleem ya tabe baki bai ce komai ba, kwafa ta yi ta cije yatsa, can tayi wani murmushi tace “Ohk, ai idan ya san wata bai san wata ba, kuma shine da jin kunya, kunya babba kuwa, sai ya gwammace ina ma ba shi bane”
-

Noor Al Hayat 25
Ranan Monday da asuba Mumy ta shiga kitchen gun kyauta dake ta kokarin hada ma yan makaranta breakfast, cike da ladabi ta gaida Mumy, mumy ta amsa tana mata sannu da aiki sannan tace “Khadijah bata tashi ba?” Kyauta tace “Ina jin tana can tana sallah ne” kyauta ta dai fada haka ne amma in dai khadijah tasan tana can tana bacci, Mumy tace “Wai boko nake son ta fara xuwa yau…” Kyauta ta xaro ido tace “Boko Hajiya, Allah ya saka maki da alkhairi, ya kara daukaka, Allah ya biya maki bukatun ki masu kyau Hajiya, yanda kike taimako kema Allah ya ji k’an ki a nan duniya da ma lahira” Mumy da ke ta kallon kyauta tayi murmushi tace “Toh Ameen” daga haka ta juya ta wuce, kyauta ta rike ha6a baki bude murya can kasa tace “Ko ya baxawara xata dau xancen nan idan ta dawo, Ashe ko akwai karamin yaki a gidan nan” a stairs mumy ta hadu da Aliyu ya shirya xai fita aiki, tace “Da asuban xaka fita aiki?” Yyi kasa da kai ya gaisheta ta amsa tare sa cewa “How was ur nyt?” Yace “Alhmdllh” tace “Breakfast din fa?” Yace “Xan yi a office” tace “Bawan Allah ai bbu xancen yin sammakon fita aiki xaka kai khadijah makaranta anjima” Juyowa yyi ya kalleta da sauri yace “A’a ni Mumy baxan iya xuwa ba, Ba ga sanusi ba da mai aikin can su kai ta mana” kallonsa mumy ta tsaya yi, can tace “Directly ma kake ce min baxa ka iya xuwa ba koh?” Yace “Toh Mumy ni da xan fita aiki kuma wani makaranta xan kai ta, komai fa sanusi xai iya yi kin sani” Mumy bata kuma saurarensa ba tayi wucewarta sama, fuskarsa daure ya juya ya koma sama shi ma. Tun da kyauta ta tada Khadijah tayi mata albishir din xancen da Mumy tayi mata khadijah ke ta murna har da rawanta, can kyauta dake taya ta murnar ita ma ta hade rai tace “Wato ni ce dai hajiya bata so a gidan nan ba arabi ba boko, sai dai in sauke in daura in yi shara inyi wanke wanke, akwai Allah” khadijah da har xata shiga bathroom ta dawo da sauri ta yo waje da ido tace “Anty mai girki? Katuwa da ke baki gama school ba dama, me kika tsaya yi toh?” Kyauta ta dunguri hancinta tace “Ai ban kai baxawara ba da take kamar buhu” Khadijah ta wara ido tace “Ni kinsan yaushe rabon da in je school, to in gaya maki tun ina gidanmu tare da Ummata, Allah ya sa ban girma ba da shikenan yanxu ni ma baxan je ba” bata sake sauraren kyauta ba ta shiga bathroom da sauri ta rufe. Kafin karfe bakwai duk yaran gidan sun shirya kyauta ta tabbatar khadijah ma ta shirya cikin daya daga kayan da ta siyo mata a kasuwa shekaranjiya ta lafta mata uban kwalli a ido, ta shafa mata jan powderta a fuska, Da kyar khadijah ta yarda xata yi breakfast saboda excitement, duk ta kagu su wuce makarantar, shi dai Aliyu na xaune parlor hannunsa rike da mug din coffee, su siyama kuma na dinning suna breakfast, Khadijah kuma na kitchen kyauta ta shimfida mata wani xaninta a kasan tiles din kitchen din don kar kayan jikinta yayi stain, jin Driver na horn a waje Kyauta ta daga khadijah da sauri ta kwace bread din hannunta ta turata waje tana cewa “Shegiya sai ta sa sun canxa ra’ayinsu maxa tafi xa su wuce” Aliyu ya fita ya samu Driver yace “Sanusi ni xan kai su, don’t worry” Har su Siyama sun fita Sanusi ya gaya masu abinda Aliyu yace, Siyama ta tabe baki hade da jingina da motar tace “Shine yana ganin mun fito baxai gaya mana ba, I don’t just like this Ya Aliyu sometimes” Aneesah tace “Ni kuma ina son sa haka, ya ma fi min ya Saleem” Siyama tace “Shi yasa nake ta addu’ar ya saleem su dawo tare da Abba anjima” Motar Aliyu suka nufa, baby da fitowarta kenan ta bi bayansu, Aliyu ya wuce upstairs dakin mumy ya sameta har ta shirya xata kai khadijah makarantar da kanta, ya d’an bude ido yace “Mumy kin fa san I didn’t mean it, ko baki fada ba ai xan kai ta…” Ta katse sa tace “Toh tunda Allah ya ban lafiyata ba gwara in fita in biya ma kai na bukatar dake gabana ba, Saleem will Neva look into my face yace min baxa shi ba ai, so this is just ur differences” Aliyu yayi kasa da murya yace “Toh kiyi hakuri Mumy, ban san ran ki xai baci ba, I am very sorry” tace “Noo ni rai na bai baci ba, kai dai da na bata ma rai xaka iya tafiya aikin ka kayi hakuri, ni da ya xame min dole xan kai ta da kai na” murmushi yayi yace “Don Allah mumy kiyi hakuri ni xan kai ta ba sai kin je ba” da kyar Aliyu ya samu ya lallaba Mumy ta hakura ta bar shi ya kai khadijah makaranta tare da Kanninsa, babu yanda bata yi ya amshi wayarta ya masu transfer din duk fees din a can makarantar ba ya ki yace xai yi da nasa kudin, da haka dai ta hakura ta kyalesa ya sakko parlor rike da makullin motarsa, makale ya tadda Khadijah jikin kofar parlor da alama su siyama dai sun korota ne, Kyauta ma na bakin kofar bayan sanusi yace mata Aliyu ne xai kai su, sai leken su siyama take tana Allah wadaran da halin baxawara da suka yi, tana ganin Aliyu tayi tsit, tayi kasa da kai tace “Sannu da fitowa yallabai” yace “Yauwa” sannan ya fita, tura khadijah tayi ta rufe kofar parlorn. Khadijah ta dinga bin Aliyu har suka isa gun motarsa, su siyama suka yi shiru daga xancen da suke ko wacce na kallonsa, Yace “Wacece ta korata a cikin ku?” Da sauri baby tace “Allah ya so bani bace ba wllh yayanmu” yana kallonta yace “Toh waye?” Nuna masa su Aneesah tayi, yace “Why did u both send her away?” Aneesah tace “Toh yaya kawai ta xo gun mota ta tsaya mu da makaranta xa mu” yace “Ita ma makarantar ae xata” Da sauri siyama tace “What??? Wani makarantar?” Baby tace “Na mu mana, ai Mumy ta gaya min da na yi wanka a dakinta daxu” Siyama da ta rikice tace “Yaya kamar ya makarantar mu, ni yaya ko xa a sa ta makaranta let it not be ours, they are a lot of schools out there don Allah a kai ta” Har da guntun hawayenta, Aneesah ma duk hankalinta ya tashi, ita dai khadijah na daga gefe tana kallonsu, yace “Alryt idan na kai ta makarantar taku kada ku bari ayi admitting dinta” daga haka yace baby ta shiga mota, baby ta shiga gaba ya bude back seat yana kallon khadijah yace “Get in” da sauri ta shiga motar ya rufe ya bude driver seat ya shiga yana kallonsu siyama yace “Ku je sanusi ya kai ku coz xan iya maku abinda ke raina idan ku ka shiga motar nan, mind u kada warce ko da wasa ta sake shiga cikin gidan can, it’s either ku je sanusi ya kai ku makaranta or you remain here till 4” daga haka yayi warming motarsa mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan, siyama ta fashe da kukan takaici Aneesah na taya ta. Essence int’l school, abinda khadijah ke ta nanatawa kenan a xuciyarta tun shigiwarsu cikin babban makarantar, baby ta bude kofa ta fita, ya juya yana kallon khadijah, xaro ido yyi yana kallon nata idon yace “Meye wnn din a idon ki?” Ta buda hannu tace “Anty mai girki ce ta sa min kwalli” tsaki yyi ya Ciro handkerchief a aljihunsa ya mika mata yace “Common goge wannan bakin abin da ta goga maki a ido kamar herbalist” khadijah ta kyalkyale da dariya ta karba tace “Herbalist kuma” bai tanka ta ba ta shiga share kwallin, jawota yyi ya fixge handkerchief din a hannunta ya fara goge mata idon, sai bata fuska take xata yi kuka, ya hade rai yace “What?” A hankali tace “It’s painful” yace “Good… Next time idan xata sa maki baxa ki yarda ba” ajiye handkerchief din yyi bayan ya tabbatar bbu sauran kwallin a idonta ya fita, ita ma ta fito ya wuce direct office din principal din kasancewar shi ma makarantar da yyi kenan, kuma har lkcn ba a canxa principal ba, da ladabi ya gaisa da principal din da shi ma yyi murnar ganinsa sosai, nan Aliyu ya sanar masa ya xo enrolling khadijah ne, principal din ya tambayi khadijah class din da take xata ce jss2 Aliyu yyi saurin cewa Jss3, xaro ido tayi ta kallesa ya mata wani kallo ya ci gaba da yi ma principal din bayani, farkon abinda principal din ya bukata shine transfer letter daga previous schl dinta, Aliyu ya d’an yi jim, can yace masa xai karbo ya kawo, da yake principal din ya san shi yasan family dinsu bai masa gardama ba, nan kuma yasa aka yi interviewing dinta, babu bata lkci kuma aka yarda a sa jss3 din coz she is capable, a take Aliyu yyi transfer din school fees da other fees da ake biya na makarantar har takardu da uniforms guda uku, Principal na kallonta xai cike mata receipt yace “What’s ur name” kafin Khadijah tace komai Aliyu yace “Khadijatul Iman” Khadijah ta xaro ido tana kallonsa, principal din yace “Surname” sai a sannan Aliyu ya kalleta, ta langwabar da kai a hankali tace “Muhammad” principal din ya so aliyu ya maida ta gida gobe tayi resuming yace A’a ta fara yau din shi aiki xai wuce ba gida ba, a tare suka fito da Khadijah office din principal din bayan yace Aliyu ya nuna mata ajinta, Tana biye da shi a baya ya juya yana kallonta yace “Wani makarantar kika yi primary da jss1?” Tace “Yan dutse” yace “Kano?” Ta gyada masa kai, bai sake cewa komai ba har ya isa class dinsu Baby ya nuna mata ta shiga tana daga masu hannu, ya juya ya tafi gun da ya bar motarsa. Karfe hudu saura driver ya ajiye su a gida, sai da su siyama dake ta kumburi cikin motar suka fita sannan khadijah ta fito rike da ledan uniforms dinta da takardu, Baby ma ta fito rike da sauran takardun khadijah, Duk sai da kyauta ta bi ta yi ma uniforms din tsirara daga ledansu tana washe baki tace “Yarinya ta xama yar boko, toh me suka koya maku yau a makarantar” Khadijah tayi dariya tana cire kayan jikinta tace “anty mai girki yanxu xan yi wanka ne, idan na fito xan koya maki” daga haka ta shiga bathroom da sauri, har daki kyauta ta kawo mata abinci bayan ta xuba ma su siyama nasu a dinning, khadijah dake ta kallon pepper soups kala kusan uku da ta xubo mata tace “anty mai girki, kinyi girki da yawa kenan yau?” Kyauta tace “Ke Alhaji da kanin Aliyu xa su dawo anjima, yanxu haka suna can cikin jirgi a sararin samaniya, ai girkin da nayi ya fi kala shidda yau tun safe nake kitchen, na kuma ji Hajiya nacewa kila baxawara ma ta dawo yau” Khadijah ta tallabi cin dinta tace “Waye Alhaji anty mai girki?” Kyauta ta hade rai tace “Babansu Aliyu mana” Khadijah ta xaro ido da mamaki tace “Dama yana da baba, ai na xata shine baban gidan” Kyauta tayi tsaki tace “Dadina dake shegen shirme, toh an ce maki shi ya haifi kansa, ubansa nace maki xai dawo anjima tare da kanin sa saleem” Khadijah ta turo baki tana d’and’ana naman ragon gabanta tace “Toh naji” Baby ce ta shigo dakin bayan Khadijah ta gama cin abinci kyauta ta fita da plates din, baby tace “Mumyna tace in kira ki” Mikewa Khadijah tayi ta bi bayanta suka wuce sama, tun bayan da Anty khadijah ta koreta sai ranan ta sake hawa saman gidan, baby ta bude kofar dakin mumy ta shiga, khadijah ta tsaya daga bakin kofa tana lekan dakin, Mumy da ta hangota tace “Shigo khadijah” khadijah ta shiga ta xauna kasa tace “Ina yini Anty” mumy tace “Lafiya lau, ya school din” Khadijah tayi murmushi tace “I like it Anty” Mumy tace “Sun baki uniform?” Khadijah ta gyada mata kai, Baby tace “Mumy same class fa muke da ita” Mumy tace “That’s good, ina books din da suka baki” mikewa Khadijah tayi da sauri ta ce “Xan dauko” daga haka ta koma kasa ta dauko books din ta ajiye ma Mumy, Mumy na kallon book din ganin Iman a jiki tace “Iman? Is that ur name?” Khadijah tayi murmushi ta gyada mata kai a hankali, mumy tace “Maa sha Allah” wani sabon jaka da bakin cover shoe da socks uku mumy ta dauko ta mika ma khadijah tace “Gashi sai ki xuba books din ciki” khadijah ta wara ido tace “Anty nagode, thank you” Mumy tace “Welcm, tashi ki tafi” mikewa khadijah tayi cike da murna ta fita, baby dake kallon mumynta tace “Mumy ni yaushe xa ki siya min sabon jaka?” Mumy tace “Soon” har kitchen Khadijah ta kai ma kyauta abinda mumy ta bata, kyauta ta amshe tana washe hakora tace “Allahu Akbar barin baxawara gidan nan ya maki rana dije, Allah ya makaleta a duk inda take har Hajiya ta gama dake ta dawo kai na nima” Shigowar Aneesah kitchen din yasa Kyauta tayi shiru sum sum ta fita don kai kayan daki Khadijah na biye da ita a baya. Suna shiga dakin ko minti biyar ba ayi ba aka kwankwasa kofa kyauta ta tashi da sauri ta bude, Aliyu ne tsaye rike da wani jakar mai kyau ya mika ma kyauta yace “Gashi ki bata” kyauta ta risina ta karba tace “Toh ta gode, Allah saka da alkhairi” bai ce komai ba ya juya ya bar wajen, kyauta ta bude jakar jin da nauyi ta ga takalma har biyu da safa uku a ciki sai water bottle irin nasu baby, kyauta ta rike haba tace “Ni dai ce ba a so a gidan nan wllh” Khadijah dake jera books dinta a jakar da mumy ta bata ta taso da sauri tace “Anty mai girki menene” Kyauta ta dungura mata tace “Duk kin fi ni goshi wllh” Khadijah ta kyalkyale da dariya ta karbi jakar da a gabansa aka rubuta *Iman* ta wara ido tace “Waowww”
-

Noor Al Hayat 35
✨
Kasa tashi sallan asuba Khadijah tayi washegari ta dalilin xaxxabin da ya rufe ta, jin an bude kofar ward din ta bude idanuwanta a hnkli taga gari ya waye sosai, likitan da mutumin jiya da ya kira da Sudais suka shigo ward din a tare, tun daga bakin kofa sudais dake sanye da milk jallabiya ke mata wani kallo har karaso gadon yace “jiya da na baki waya wa nace ki kira?” Khadijah ta mike xaune da kyar ganin ynda ya hade rai ta marairaice tace “Relatives dina” ya kara hade giran sama da ta kasa yace “Then why didn’t you call dem?” cikin rawar murya tace “I don’t have anybody to call, ni marainiya ce, my father is late so also is my mum, My step mum…..” Kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai, cikin tsawa yace “Karya kike yi, shut ur mouth plss” likitan dai rungume hannu kawai yyi yana kallona yana murmushi, ta hade kai da gado tana kuka cikin rawar murya tace “ku yarda dani don Allah, wallahi ni bana karya, laifi nayi ma step mum dita tace min in bar mata gidanta, I love my step mum and she loves me same, but tace in tafi sbda laifin da nayi, she raised me up as a mother even after my late dad passed away 5 years back, don Allah kada ku ce in tafi ban san kowa ba a garin nan ban taba xuwa ba, ku taimakeni ku kaini gidan marayu in dinga kula da yaran wajen don Allah” tsawa likitan yyi mata da ya firgitata ta dago da sauri, yace “You are mad, wa xa ki raina ma wayo, ni ko wannan da ke kusa dake?” Ya fadi hakan yana nuna sudais, Shiru tayi tana kallonsa, kafa mata ido shi ma yyi, can ya karaso kusa da ita yana kallon kwayar idonta da kyau, ya kai hannunsa ya bude eye lids dinta, can ya kalli fingers dinta sai kuma ya kalli Sudais dake tsaye, daga kafada yyi ya nufi kofa yace “I have better patients to attend to Sudais…” daga haka yyi ficewar sa daga cikin ward din, a sanyaye khadijah ta kalli Sudais dake mata wani kallo yana rungume da hannunsa, harara ya watsa mata bayan mun hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, muryarsa ya daki ear drum dinta, “Wani laifin kika yi ma mum din taki, kuma daga wani gari kike? Kina min karya xan gane kuma daga nan station xan kai ki” Shiru tayi tana kallonsa hawaye na ci gaba da sakko mata, cikin sanyin murya tace “Daga kano na xo” yace “Wato kin saba tafiya garruruwa kenan ko” ta girgixa kai da sauri tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba tace “Wallahi A’a” yace “Toh wani laifin kika yi mata?” Share hawayen idonta ta shiga yi a hankali ta hadiye wani abu da ya tsaya mata, can ta sakar masa kuka tace “Kilan baxa ka min taimakon da nace ka min ba idan ka ji dalilin bari na gida” strictly yace “Malama ki bude baki ki gaya min, stop wasting my time xan je aiki” jinginar da kai tayi da gadon ward din tace, “Duk abinda xan fada maka ka yarda dani sbda Allah, ni bana karya, I knw d consequence of it…. Domin ka min taimakon da nace ka kai ni orphanage yasa xan fada maka ni wacece” Bai tanka ta ba hakan yasa a hankali tace “I lost my mum at a very tender age, and my beloved last year” ta kallesa taga he is listening but not looking toward her direction, ta lumshe ido, a haka ta fara basa labarinta tun daga farko har xuwa yanxu da yake gabanta, bbu abinda ta boye ma Sudais, Kallonsa tayi a karo na farko tun da ta fara gaya masa ita wacece, hawaye masu xafi suka shiga xubo mata, Sudais ya dinga kallonta da wani expression da ta kasa fassarawa a fuskarsa, tana girgixa kai a raunane tace “I told you all but the blank truth about me, believe me plss” kasa ce min komai yyi sai bayan kusan minti biyu yana nuna ni da yatsa da wani irin mamaki yace “You mean… You are pregnant?” Ta gyada masa kai a hankali tace “That’s what the Dr told me and my step mum” Jinginar da kansa yyi jikin bango yana kallon saman ward din ko kiftawa bbu, bai kuma ce min komai ba har na kusan minti uku, Khadijah dai sai kallonsa take don bata san tunanin da yake a xuciyarsa ba domin kuwa duk wanda ya gan sa yasan yyi nisa tunanin da yake, bude kofar aka yi duk suka kalli kofa, Dr Yusuf ya shigo yana kallonsa da kyau yace “Ya? Ka gama sauraren karyar ta Malam?” Sudais bai ce komai ba ya shiga shafa uban gashin dake kansa, likitan yyi murmushi yace “Very good then, naga kamar har karyar tayi tasiri a xuciyar ka” Likitan ya karasa kusa da khadijah yana kallonta da kyau yace “Are you married?” Shiru tayi tana kallonsa ko kiftawa bbu, wani murmushin ya sake yi ya kalli Sudais, Sudais ya lumshe manyan idonsa ya bude su a hankali yace “Yea xaka cire mata cikin soon as possible…..” Wani kallo Dr Yusuf ke yi masa, Sudais ya dafa kafadarsa yace “Yeah… She told me about d pregnancy, an illegal one at it’s early stage, i think you just have to flush it Yusuuf, I will pay what ever amount it will take” tunda ya fara magana khadijah ke kallonsa baki bude, can ta fashe da kuka tace “Noo plss, it’s illegal but it doesn’t deserve that, Allah xai yi fushi da ni, baxan iya ba…” wani mugun kallo Sudais ke mata ya karaso kusa da ita cikin tsawa yace “You are very very stupid, shegen xaki haifa?” Ta kuma rushewa da kuka tace “Eh, saboda Allah ne ya bani, kuma it’s not my fault it came this way, beside soul din ba shi da laifi da har xan xubar da shi…” Yusuf ya rungume hannu yana kallonta, Sudais ma wani kallo yake mata lkci daya yana mamakin furucinta cos she look young to think that way, ya matsa dab da ita yace “Then ya xama dole ki koma gidansu Aliyu kika kirasa ko wa???” Khadijah tayi shiru tana kallonsa hawaye na xubo mata, ido ya kafeta da shi yana jiran jin abinda xata ce, ta sauke idonta a hankali tace “Toh me xan ce masu?” Strictly yace “Abinda likita ya gaya ma ke da Ummar ki” tana share hawayenta tace “Toh amma ni yanxu bani da kudin mota” yace “Xan baki” juyawa likitan yyi ya fita, shi ma ya nufi kofa kafin ya fita ya juyo ya kalleta yace “Ki sameni reception yanxu” daga haka ya fita, ta sakko a hankali ta dafe gado jin jiri, da kyar ta karasa reception din sbda jirin dake debanta tana isa ta xauna kan kujera ganin baya gun, office din Dr Yusuf sudais ya shiga, Dr Yusuf yace “What are you trying to do Sudais?” Sudais ya shafa kansa a hankali ya xauna kan table dinsa yace “I don’t really knw Yusuf, kawai nayi analyzing naga babu karya a labarinta, I tried hard to figure out….” Yusuf ya katse sa da sauri yace “Da alama lauyancin ka bai fada maka gaskiya ba yau, look at you… sau nawa muke ganin cases irin wannan, tayi ciki ta gudu ta bar gida ta xo nan ta shirga maka karya a matsayin ka na barrister har karyar yyi sinking kan ka? Don’t let me call u a disgrace to ur profession…” Sudais ya girgixa kai yace “Babu karya a xancen da ta min, and profession dina yasa nayi figuring din hakan, she told me nothing but the truth” Dr Yusuf yace “Toh naji gaskiya ta fada maka, what do you intend doing now?” Shiru Sudais yyi yana kallonsa, can ya dauke kai cikin damuwa yace “I don’t knw frnd, I have never being confuse like this all my life, Yusuf just look at her, she is too young, baxa ta wuce sa’ar Rabi’ah ba, had I known wllh da ban tsaya a motata ba jiya” Dr Yusuf yace “Toh ko gidanku xaka kai ta” sauka Sudais yyi da sauri daga kan table din yana xaro manyan idanuwansa yace “Gun wa Yusuf?” Yusuf yyi dariya yace “Mami wai da” Sudais yace “Mami ta kashe ni kenan, cewa ma xata yi ni nayi ma yarinyar cikin, kai ma kasan ko hauka na fara baxan fara kai ta hanyar gidanmu ba, what for?” Yusuf dai sai dariya yake sanin wacece mahaifiyar sudais, Sudais ya tabe baki yace “Wani lkcn ma d’an Adam na xaman xamansa yake dauko ma kansa matsala da kansa a rayuwa if nt meye haka na sa kai na ciki??” Yusuf yace “Kawai ka ka ita orphanage din da tace xai fi” Sudais yace “In dai kai ta can gidan su dan iskan da yyi mata cikin” Yusuf yace “Wa yaga bata lkci” Sudais ya nufi kofa yace “Muyi waya frnd” Mikewa Yusuf yyi ya bi sa suka fita. Ba tare da Sudais ya kalli khadijah dake ta xaune duk ta gaji a reception ba yace “Mu je” mikewa tayi a hankali ta bi bayansa, gun motarsa dake parking space ya nufa, ya bude ya shiga, ganin bata shiga ba Yusuf yace “sai ki shiga” a hankali ta kai hannu ta bude motar ta shiga, Sudais na kallon Yusuf yace “I will give you a call” Yusuf yace “Alright then” daga haka ya ja motar muka bar asibitin, bbu wanda yace komai cikinsu, yyi driving din kusan minti sha biyar suka iso wani anguwar masu kudi, nesa da gidansu Sudais yayi parking, ba tare da ya kalleta ba yace “I will be right back” daga haka ya fita ya fara tafiya, tafiyarsa kadai ma abun kallo ne, ya wuce gidaje kusan hudu kafin ya xo na su, Mahaifiyarsa Mami ce xaune parlor da wata bakuwa da tayi, ya karasa ya gaishesu da ladabi, bakuwar ta amsa da fara’a tace “Wannan uban gashin da aka bari fa Barrister, sai kace a turai” Ya kirkiri murmushi yace “Sunna ce….” Katsesa Maminsa tayi fuska daure tace “A hakan da ka bar shi irin na wa ends basu da mafadi, am very serious kada ka shigo min gida anjima baka asks gashin nan ba, ka jira idan ka koma UK din sai ka kara barin gashin, wnn iskancin kam ba a gidana ba” kansa a kasa yace “Toh Mami” daga haka ya mike ya wuce bedroom dinsa, press ya bude ya fiddo wani makulli ya sa aljihu sannan ya fito yayi masu sallama ya fita, bacci ya tadda khadijah ke yi, dauke idonsa kanta yyi ya tada motar ya bar layin, tafiyar wani minti sha biyar din yyi ya isa wani anguwar daban yyi parking a gaban wani gida, ana ganin gidan ansan sabon gini ne, ya fita ya bude gate din gidan da makulli sannan ya dawo ya ja motar ciki yyi parking ya fita ya koma ya rufe gate din, tuni khadijah ta bude ido tana bin gidan da kallo, dawowa yyi yace “Come down” ba musu ta fito, tafiya ya fara yi xuwa entrance din main house din ganin haka ta bi bayansa sai dai gabanta faduwa yake kawai, ya sa makulli ya bude kofar shiga parlorn ya shiga, kasa shiga tayi tana lekan parlorn, ya juyo yana kallonta, hawaye ne cike idonta, wani kallo yyi mata ya shiga parlorn ya bar wajen, a hankali ta taka ta bi bayansa, tuni ya wuce bedroom ita kuma ta xauna nan kan kujera a parlorn, bayan wani lkci ya fito yace “Ki shiga ciki kiyi wanka, xan fita in dawo yanxu” daga haka ya fita ya rufe kofar, tashi tayi da kyar ta shiga dakin da ya fito, towel ta gani kan gado sai sabulu ta karasa ta dauke su ta bude kofar da take tunanin na bayi ne ta shiga taga har ya hada mata ruwa me dumi, wanke bakin ta ta fara yi da mouth wash, bayan kusan minti ashirin ta fito daga bayin da kayan da ta cire a bucket ta wanke, sai taji ta samu karfi jikinta, hijab kadai ne da bata wanke ba ta daura kan towel din jikinta sannan ta fito parlor, wani kofar dake parlor ta shiga taga kitchen ne, ta dauko sweeper da mop ganin gidan is very dusty, tun daga dakin da tayi wanka ta fara gyaran ta fito har parlor duk da sanyin da take ji sosai, tana goge goge a durkushe ya shigo parlorn ya ajiye ledojin hannusa ba tare da ya kalleta ba yace “I didn’t tell you to do anything madam, ga kaya nan ki shiga ciki ki canxa ki fito yanxu” ta mike tsaye tace “Toh nagode” bai tanka ta ba ta dau ledan ta shiga dakin, dogayen riguna ne na kanti da undies sai Hijab biyu da perfumes, cikin lkci kankani ta gama shiryawa ta fito parlorn, xaune yake ya tallabi chin dinsa da hannu biyu yayi nisa tunanin da yake, why is he involving him self in such case ya fa san daga irin gidan da ya fito ya san waye iyayensa, jin ta fito tun da ya kalleta sau da ya bai sake kallonta ba har ta iso nesa da shi ta durkusa tace “Na sa kayan” ledan abinci ya nuna mata yace “Breakfast” ta mike ta isa gun ledan ta bude, a hankali ta ja baya tana rike numfashinta sbda aroma din abinci, Fried Irish ne da soyayyen kwai da plantain sai ketchup, yace “You can go to the kitchen and make a cup of tea for ur self” kai kawai ta gyada masa, ta mike ta shiga kitchen din tana fatan ta iya shan shayin, ta gama hadowa ta fito, ganin kallonta yake bayan ta ajiye shayin ta dau Irish daya a hankali ta kai ba ki, ji tayi cikinta ya fara hautsinewa tun kafin ta fara taunawa, ta dau shayin ta kai baki da sauri don ta kora, tana sha tayi saurin ajiye cup din da sauri ta shige dakin da tayi wanka tun kafin ta karasa cikin bathroom din aman ya xubo mata, tun da ta fara amai sai yau tayi Wanda ya galabaitar da ita don bbu komai cikina, ta kasa motsi wajen duk jikinta ya mutu, ganin shadow dinsa ta juyo hawaye kwance fuskarta, tausayi karara ta gani a kwayar idonsa, yyi saurin dauke kai murya can kasa yace “Sorry” daga haka ya shiga bayin ya debo mata ruwa ta wanke bakinta ya xuba ruwa wajen, kasa tashi tayi ta jingina da bango, ganin jira yake ta tashi, ta runtse ido tayi karfin halin tashi bata xarce ko ina ba sai kan gado ta fada kai tana mayar da numfashi, ya karaso yace “Toh me xa ki ci yanxu” kai kawai ta iya girgixa masa, yyi jim yana kallonta kafin ya juya ya fita a koma parlor, xaunawa yyi yana tunanin how many hours will take them to kaduna.