Author: Novels

  • A Rubuce Take Book 2 Page 26

    A Rubuce Take Book 2 Page 26

    Part 02

    Page 26

    Hafsat da lawal ta hango tsaye jikin motar hafsat din suna magana,da alama fita zasuyi ko kuma sun dawo,ba kasafai takeson shiga sabgarsu ba,amma yanzun dole tayi tambaya taji ta inane wurin yake tunda ba garinta bane,saita sauya akalar tafiyarta zuwa wajensu.

    Dif sukayi sanda suka ganta a wajen,hafsat ta dauke kai kamar bata ganta ba

    “Don Allah lawal ta ina faaz hotels yake?” Tambayar data fusgi hankalin hafsat,saita waiwayo ta zubawa widad din ido

    “Faaz hotel kuma?”

    “Eh nayi baqi ne zan taho dasu”

    “Okay” ya fada sannan ya fara mata kwantance inda yake ya qarashe da cewa

    “Kibi ta nan ahmadu bello way”

    “Aah,ta sa’adu zungur road kaman yafi” hafsat ta tsoma bakinta,bata kawo komai a ranta ba,cikin tsarkakakkiyar zuciya tace

    “Yauwa na gode” kamar tace lawal din ya kaita ganin suna rufe motar sun gama uzurinsu da ita amma saita fasa,ta shige part dinta da sauri ga sauya kayanta zuwa abaya wadatacciya tayi rolling,saita saba affan a kafadarta ta dauki key dinta da kudin napep da zai kaita ta fita,tasan ba zata jima ba,duka duka da zuwa da dawowar ba lallai ta wuce awa daya tunda basu da wani nisa sosai.

    Wani irin duumm yaji kansa yayi,ya sake daukan wayar jikinsa yana rawa ya kuma buda hotunan,itace dai….. widad dinsa ce dai babu canji, itace dauke da affan dinsa,yaron dake tsananin kama dashi

    “Hasbiyallahu la’ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem” ya fada wannan karon har bakinsa yana rawa,kansa ya sara masa yasa hannu bibbiyu ya dafe,wani sashen na zuciyarsa yanata qoqarin kawo uzuri da kariya a gareta,amma wani sashen kuma yana qaryata haka hadi da sukan duk wani hanzari da zuciyarsa ke badawa,sashe mafi qarfi kuma mafi rinjaye kenan.

    A hankali sai zuciya ta fara ayyano masa irin abubuwan da suka faru a jiyan,ita tafara tashinsa a bacci,ta kuma shirya masa komai na tafiyar tun lokacin tafiyar baiyi ba,ta dameshi kuma ya tashi ya shirya kada yayi latti,hakan yana nufin dama akwai abinda ta shirya zatayi a ranar shiyasa take Allah Allah ya tafi?.

    Bayan nan yayi kiranta da yammar kusan miscal uku,bata biyoshi kiran ba,har sai cikin dare bayan bacci ya daukeshi,sai da safe yaga miscal,bata kuma sake nemansa ba,me hakan yake nufi,duka wadan nan abubuwan da ido yake gani ya zama gaskiya kenan?, innalillahi wa inna ilaihi raji’un ya sake fada kansa yana qara sara masa sosai yayi qas da kansa yana jin yadda zuciyarsa ke masa wani masifaffen zafi.

    Yafi awa uku cikin matsanancin halin da baisan dame zai kwatantashi ba,kafin daga bisani wata qaqqarfar zuciya ta yunquro masa,ya miqe ya fara hada kayansa,abinda sam baiyi shirinsa a sannan ba har sai zuwa gobe da safe.

    Bashi da kuzari ko qarfin halin da zai iya tuqi daga sokoto zuwa bauchi,dole ya nemi daya daga cikin yaransa da sukayi tafiyar tare ya bashi driving din.

    Tunda suka dauki hanya bai iya katabus din komai ba,sunci rabin tafiyar saiga kiran widad din ya shigo,ya kalli wayar sosai kamar widad dince a gabansa,zuciyarsa na wani irin bugawa,wani sashe na zuciyarsa na bashi izinin dagawa,wani sashen kuma yana hanashi tare da tuna masa girman laifinta a gareshi,daga qarshe daya sashen yayi rinjaye,sai yayi rejecting kiran,yama kashe wayar gaba daya,ya maida kansa jikin kujera ya kwantar yana lumshe idanunsa,kanshi yana ci gaba da sara masa

    “Widad fa,widad” abinda zuciyarsa keta maimaitawa kenan cike da wani irin zulumi tashin hankali tsoro da kuma fargaba.

    Cikin mamaki ta sauke wayar tana kallon fuskar wayar sosai,zuciyarta na gaya mata rejecting kiran nata yayi amma ta kasa gasgatawa,saita katse shakka da mamakinta ta sake yunqurin kiransa a karo na biyu,saidai computer ta gaya mata wayar tasa a kashe take.

    Jim ta danyi,to kodai wayar tasa babu charge ne,ya qare sanda take kiran nasa?,bata sani ba,amma daga qarshe saita barwa kanta cewa hakanne,don baka ta miqe ta soma aikace aikacenta lokaci lokaci tana gwada sake kiransa,saidai babu wani abu daya canza,a kashe din dai take.
    [18/05, 6:54 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 22

    A Rubuce Take Book 2 Page 22

    Part 02

    Page 22

    Gifatatan da tayi shi ya fahimtar da hafsat dake zaune tana huci fitowar ta,ta bita da kallo daure da towel din daya bayyanar da kyakkyawar surarta da farar fatarta dake ta glowing mai daukan hankali saboda gyara da mai da sabulan wanka masu kyau data samu.

    Qamshinta ya cika mata hanci,ta gaza dauke idanunta daga kanta har zuwa sanda ta isa gaban tv din ta kasheta.

    Kashe tv din tayi sannan ta dawo ta sake wuceta kamar batasan Allah yayi wata halitta ba a wajen,ta sake nufar bedroom din abbas din cikin takun na isa,tana shiga ta maida qofar ta rufe hankalinta kwance.

    Gefan gadon ta koma ta zauna tana qissima abubuwa da yawa cikin ranta,bata taba ganin mace kidahuma irin hafsat din ba,sau tari idan ta zauna tana nazarin rayuwar abbas din tausayinsa kamata yakeyi,yana da matuqar kirki sanyin hali da qoqarin sauke haqqin da ya rataya a wuyansa,yana da mugun haquri,mutum ne mai nisan haquri sosai da kuma idan aka qureshi fushinsa yakanyi tsahon da ba kasafai yake sakkowa da wuri ba,tako ina babu digon match atare dasu,idan ka kalleta ka kalleshi ba zaka taba zaton miji da mata bane,to amma kuma kowanne bawa da kalar tasa qaddarar,TASHI QADDARAR KENAN.

    Yayi mamakin ganinta a zaune daya fito,yana goge jikinsa sa towel yana tsokanarta

    “Ko nazo na qarasa aikina ne kawai mu samu ladan me gaba daya?” Ya fada yana kashe mata ido,saita dan jefa masa hararar wasa yana karya wuya

    “Naqi wayon…..na yarda ka kashemin jiki,kazo dai ka rakani kitchen saimu debo kayan abincin gaba daya”

    “As you wish maaaa” yadda yayi maganar sai ya bata dariya,gefe guda kuma tausayinsa ya kamata,tasan yanzun nan jahilar matarsa zata jagula lissafi da kuma nutsuwar da ya samu.

    Tana gaba yana biye da ita daure da towel shima,yadda widad din ta tsara ma ranta kuwa haka ya kasance, idanun hafsat din a kansu ya fara sauka,saita miqe tsaye cak kamar wadda aka yiwa barin wuta,yayin da abbas ya dubeta cike da mamaki,take zuciyarsa ta fara tafasa

    “Da izinin waye kika fito?” Ya tambayeta da kakkausar muryar,maimakon ta amsa shi saita sauke dubanta ga widad

    “Shegiya la’ananniya,dama nasan yana wajenk…….”

    “Dakatamin……karki qara kuskuren kirana da wannan sunan,idan ba haka ba wallahi zakisha mamaki na……tunda kike haukarki kinga na taba bi ta kanki?,saboda ni ba take nake ba,ta mijina nake,shine a gabana,ya samu farinciki da nutsuwa daga gareni,ta yadda zan tsaya gaban kowa na amsa suna na na mace,bawai muna mata ba,sannan zanji gamsuwa ba mata na rako duniya ba” ta qarashe maganar tana watsa mata wani banzan kallo,kallon da ya kusa fin maganar da widad ta yaba mata zafi,sai ta fige mayafinta ta watsar da jakarta

    “Yau saina nuna miki wace mace wace muna mata”

    “Karki kuskura ki sake taku ko guda daya idan ba haka ba yau zakiga abinda baki taba gani ba daga gareni” abbas ya fada idanunsa na sauya launi

    “Wuce” ya juya yana gayawa widad,saita fara taku a nutse fuskarta fes da murmushin d hafsat taji kamar ta watsa mata garwashin wuta a fuska.

    “Kana gani fa……kana kallon gaskiya kake taketa?,sau nawa ina kamaka a gidan nan abbas?”

    “Tunda kwartanci nazo yi saiki tsayarmin da haddi,da izinin wa kika fito nace miki!!!” Ya daka mata tsawar da sai da cikinta ya kada,amma taurin zuciya da tsaurin rai ya sakata ci gaba da tsaiwa tana dubansa

    “Dole ne ka fake a bayan na fita baka sani ba,tunda idonka ya rufe ka manta sanda na gaya maka bani da lafiya ko” kallonta yakeyi yana jin kamar ya yanke mata hukuncin da zuciyarsa ke raya masa ko zai samu sassauci daga abinda yakeji a ransa na zallar bacin rai

    “Idan kika qara minti daya tsaye a nan wallahi saikin raina wayonki” abinda ya fada mata kenan ya juya ya koma dakinsa.

    Tana kuka wurjanjan ta fita a gidan ta wuce titi ta samu abun hawa,bata jin zata iya jurar ci gaba da zama a garin kaduna,bata da sauran amfani a wajen abbas,ba wata soyayya ko qauna data rage tsakaninsu.

    Tsaf ta shirya abincin ta fito dashi bayan ta sauya kayan jikinta,da taga baya falo saita wuce bedroom dinsa.

    Ko towel din jikinsa bai cire ba,yana zaune a gafen gadon dafe da kansa,ta ajjiye abincin a nutse tausayinsa yana kamata,ta tako a hankali ta zauna gefansa tana dafa kafadarsa hadi da kiran sunansa a tausashe.

    Hannunsa dake dafe da kansa ya sauke, sannan ya dagashi zuwa gareta yana duban fararen idanunta da nashi idanun da suka rine

    “Kayi haquri…..”

    “Na gaji widad…..na gaji,nayi duk iya bakin qoqarina,na kuma yi irin haqurin da nake ganin zan iya,shekara nawa?,shekara nawa amma har yau babu sauyi?,har yau jiya iyau,sai yaushe zata canza?”

    “Mai haquri baya taba tabewa daddyn mimi,kaci gana da haquri ko don yaranka” dan shuru yayi sannan ya fara magana a sanyaye

    “Ina da dubban hanyoyin da zan hukuntata,amma ta kowanne fanni idan na duba mafi yawan hukuncin da duk zan mata sai ya shafi yarana,inda ace bamu da zuri’a ko daya da ita,wallahi wallahi bazan zauna da ita ba” maganar ta daki widad sosai,don duk wanda yake wajen yadda maganar ta fita daga bakinsa zai fahimci tun daga qasan zuciyarsa ne.

    Sosai tayi qoqarin kwantar masa da hankali da dadadan kalamai da ban haquri,ta tayashi sukaci abincin tare duk da ba yunwa takeji ba,sannan ta taimaka masa ya sake shiryawa cikin wasu uniform din,don idan ya watsa ruwa da rana kamar haka baya maimaita kaya,takan tsokaneshi da cewa

    “Ban taba ganin police din da kayan aiki sukewa kyau irinka ba,hakanan ban taba ganin dan sanda mai tsafta kamar ka ba” murmushi yakeyi sannan yadan harareta

    “Kina nufin qazamai ne kenan?” Takan maida masa murmushin hadi da salute nashi

    “Afwa nake nema yallabai,ni na isa na fadi haka,kada kasa hukumar ‘yan sanda ta kamani”

    “Waya isa,wane mutum,kina da Abbas turaki” ire iren hirarrakin da suke sakawa basa gajiya da junansu.

    Relief din da ya samu daga wajenta yasa zuciyarsa ta sauka sosai,ya kuma yi aikinsa cikin sukuni,sanda ya tashi komawa gida sai yaji kamar ya koma gidan widad din,amma hakan bashi yiwuwa,kodon yaransa da kuma hakkin Allah dake kansa.

    Daya koma din kamar wancan lokacin,baibi takan komai nata ba,hidimarsa yayi dasu mimi,gefan abincinta ma bai kalla ba,saida sukayi baccin ua debesu ya wuce dakinsa dasu,yabar musu gadon ya kwanta saman sofa bed.

    Da safe da wurwuri ya shiryasu ya wuce aiki,ya ajjiye mata kudin cefane,bayan ya zabge fiye da rabin abinda ya saba batan,yana sane yayin hakan,don yanason ko yaya ne ya horata taji a jikinta.

    Koda aka tashi daga aikin gidan widad ya wuce,bai koma ganinsu ba yadda ya saba,bai kuma kirata ba,baisan ya akayi ba washegari suna waya da lawal kawai yaji muryar su mimi,tsananin amaki ya cikashi

    “Suwa nakeji kamarsu mimi?”

    “Eh….eh sune” yadan fada a daburce,saboda yasan yadda akayi tahowar,baiso kuma yaji wani bayani daga bakinsa ba

    “Ok,shikenan yayi” abinda ya fadi kenan,don ba hurumin yaron bane suyi kowacce magana dashi ba,suka gama maganar da zasuyi ya kashe wayar.

    Duk yadda yaso yayi controlling fushinsa amma ya gaza,tattarawa tayi ta koma bauchi ba tare da izininsa ba kenan kwatankwacin abinda tayi masa wancan karon da yayi sanadiyyar haramta mata kaduna kwata kwata kenan?,sai ya sake daukar wayar ya fara kiranta.

    Sai da yayi mata miscal biyar bata daga ba,abinda bai taba yiwa wani dan adam ba,ya sauke wayar ya shiga gurin rubuta saqo ya aika mata da saqo kamar haka

    _Ki wuce gidanku har sai na nemeki_

    Abinda ya aika mata kenan a taqaice,saqon da yayi mugun gigita mata hankali,ta fara kiransa babu qaqqautawa,amma sai shima yayi biris,daga qarshe ma da kiran yayi yawa sai ya kashe wayar gaba daya,widad dake zaune gefansa tana tayashi shigar da wasu bayanai system dinsa batasan abinda yake faruwa ba,sai da taji yana ta jan tsaki sannan ta kalleshi

    “What’s….”

    “Shshsh…..”ya fada yana dora yatsantsa saman labbansa yana dan lumshe idonsa,saita dage kafada da gira tana murmushi,bata sake cewa komai ba taci gaba da tayashin,yayi qoqarin shima tattara duk wata damuwar hafsat din ya watsar.

    Kwana uku rak kawu hassan yayi kiransa,yace a jirashi sai ya shigo weekend,weekend din da baije ba sai da bayan wata guda cif!.

    Widad sam batasan me ake ba,taga dai ya dawo gidan gaba daya,ta kuma sake samun wata sabuwar zazzafar soyayya da kulawar data dinga sakata jin kunya muddin cikin mutane suke,takan tambayi kanta wai wacce irin soyayya abbas din yake mata?,tasha tambayarsa amma shima baida amsa illa yace

    “Min indillah” daga qarshe itama haka ta barwa ranta daga Allah ne,saidai tabbas ZUCIYA TANA SON ME KYAUTATA MATA,TANA KUMA QIN ME MUNANA MATA KOMAI SOYAYYAR DA ITA ZUCIYAR KE MASA.

    Suna sauka a bauchi ya wuce gidan kawu hassan din,don akwai maganganun da zasu tattauna,yanason wannan karon su halarci bikin qara musu girman da akayi,itama bata zauna ba tace zata je gidan uncle muhsin,da fari ya hana don mugun kishinta yakeyi,yace ta jira ya dawo ya kaita.

    Amma ta kafe da roqo da nacin ya barta,don akwai abinda take shirya masa,batason kuma ya sani sai ranar,daga qarshe da qyar ya yarda idan ya isa gida zai turo umar ya dauki motarsa guda daya ya kaita,ta saki murmushi sanda yake fita

    “Uncle dina” ta fada qasa qasa cikin murmushi,wani kaffa kaffa yakeyi da ita,hatta da kayan sawarta yanzun ya hanata saka wasu muddin fita zatayi,yafi ganewa kowanne dinki ma ayi mata doguwar riga sakakkiya.

    Abbas sun tattauna sosai da kawu hassan harma da yaaya sa’id da Bashir akan batun hafsat din,sun tausheshi sosai sun bashi haquri,yace yaji,amma su qyaleshi,ko zai maidata ba yanzun ba,ya fara gajiya yana son shima ya huta,ba wanda ya tilastashi a lokacin,babban wansa yaaya sa’id ne yace

    “Shikenan,zan nema kawun nata zamuyi magana,amma dai ka daure kaci gaba da haquri ko don zuriar da Allah ya qaddara a tsakaninku”

    “In sha Allah” ya fada cikin girmamawa,sun qyaleshin,suka ajjiye batun suka shiga tattauna sauran maganganun da ya shafesu.

    Kafin yabar gidan ya bawa umar key din motarsa yace ya dauko masa su mimi,saboda yanason su koma kaduna tare,ko don makarantar yaran.

    Abinda yayi matuqar bata mamaki da daga mata hankali kenan,a dauko su mimi fa?,to me yake nufi?,kada fa ya zamana ta fita kenan a gidan gaba daya,kada yarinyar ta zama sanadiyyar fitarta haihata haihata a gidan,ta kadu don irin hakan bata taba faruwa a tsakaninta dashi ba,amma ummanta ta kwantar mata da hankali

    “Kada ki damu,ki bada yaran,kinsan muddin ina raye bazan bari irin haka ta faru dake ba” hakanan ta daure ta hada musu tsummokaransu.

    Kafin abbas din ya dawo ita ta rigasu dawowa,ta gyara bangarenta da nashi,ta dora abinci,sanda yaran suka iso ta gyarasu fes ta canza musu kaya,sai gashi sun sake sunata walwala abinsu,musamman mimi data dinga fadin

    “Nidai wajenki zan zauna anty”, murmushi kawai widad tayi

    “Dama ta wajena ce ke” abbas na zaune yana binsu da kallo,sai yakejin gidan nasa ya sake masa dadi, widad nata kai.kawo tana hidima dasu,affan yana hannun su mimi suna masa wasa,wanda inda mahaifiyarsu na nan basu isa su samu wannan damar ba.

    Waya ta shiga daki ta amsa,koda ta fito sai ya tsareta da ido,daga bisani kuma murmushi ya kubce masa

    “Madam…….tsakani da Allah ban yarda dake ba,me kike shiryawa silently” dariya takeson yi amma bataso ta bashi qofar da zai gane plan dinta

    “Siyar dakai zanyi” tayi maganar tana kashe masa ido daya,wani qawataccen murmushi ya subuce masa yana jin kansa fes cikin wata irin walwala

    “Girmanki ne,don kin siyar da DSP,har IG ma zaki iya siyarwa,duka girmanki ne” sai dariya ta qwace musu su duka biyun.

    Washegari bayan ya fita ta kuma tambayarsa zasu fita ita da yaran gaba daya,ya langabe kai a inda yake zaune

    “Babyn uncle…..ki jirani zuwa dare na kaiki please,wallahi banaso…… inajin kishin ki fita a kalleki,banason kihau motar haya”

    “Allah uncle ba zamu jima ba,kuma inda zanje din basa fitowa ai da daddare,don Allah ka turon umar ko ko muneer,saika bamu aron daya motar taka ya miqamu ya dawo damu”

    “Shikenan nan,amma awa biyu kacal na baku”

    “In sha Allah bazan wuce haka ba” ta amsa masa a ladabce.
    [16/05, 5:20 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*

  • A Rubuce Take Book 2 Page 11

    A Rubuce Take Book 2 Page 11

    Part 02

    Page 11

    Yana turo qofan dakin ta kalleshi,irin kallon mamakin nan wanda tuni ta shiryama hakan

    “A’ah,abban mimi ba kwanana bane” idanunsa ya zube fes akan fuskarta,yana iya hangen wani abu fake behind her face,sai ya lumshe ido kadan ya gyada kai

    “I know” sai ya qarasa ya dauki duvet dinsa da pillow ya juya ya fice yana ja mata qofa.

    Da kallon mamaki ta bishi,saita miqe ta nufi qofar yana leqensa,saman kujerun parlor din ya shimfidashi ya yada pillow din ya kwanta bayan ya rage hasken qwan falon,ranta yayi mummunar baci,wato ita bai isa ya kwana gurinta ba,saboda kwanan gimbiya ne?,har ta buda qofar zata iskeshi a falon wata zuciyar ta haneta,saita koma da baya ta maida qofar ta rufe.

    A wannan daren haka kowa cikinsu ya kwana,kowa da irin abinda ke kai kawo a zuciyarsa.

    *******Tun daga ranar suka koma ‘yar haka dashi,sai sa’ar gaske yake iya sanyata a qwayar idanunsa,tuni ta ajjiye girkinta dama komai da komai,iyaka ta gyara bedroom dinta da kanta,idan tana da ra’ayin hira ta kira wanda takeso cikin ‘yan uwanta,ummunta anty deena ko anty madeena koma mom dinta,ko kuma ta fice wajen maari susha hirarsu,ita kuma dake mata kallon me qaramin ciki tayita mata dafe dafe na abubuwan gargajiya,wanda da gudu widad din ke ci,don wasu abubuwan ma ta manta dasu sam,ummu ke musu lokaci lokaci a gida dama.

    Ba wanda ta taba gayawa abinda ke faruwa,don sai taji abun baya ma wani damunta gaba daya,yammaci tana yi dab da zai dawo zata koma dakinta ta kulle.

    Yadda hafsat take ganin damuwa qarara tattare da abbas din sai hankalinta yayi mugun dagawa,bata taba zaton baka ya damu da yarinyar ya kuma bata muhimmanci mai yawa cikin rayuwarsa ba irin wannan lokacin,ta auna ta auno……taga kaf zamansu bata taba irin wannan sakarcin ya damu da ita haka ko yabi ta kanta ba,hasalima wani lokacin saidai ta bude qofar ta tarar ya koma wajen aikinsa ya ajjiye mata dan note.

    Kishi sosai ya tasata a gaba,ta daina jin dadin gidan gaba daya,ba zata iya jure ganin soyayya da damuwar abbas akan wata diya mace ba a gaban idanunta tana raye ba,sai ya zamana bata da aiki sai mita da qorafi

    “Gaba daya qaramar yarinya na neman rikita maka lissafi,totally ka canza abban mimi,ba ita ta zabi haka ba,aiba wansa ya tilastata,saika qyaleta idan ta gaji ta watsar…..banda ma iyayin banza da samun waje,mema akayi mata?” Sai taja qaramin tsaki.

    A sannan yana shiryawa ne bayan ya fito a wanka,sanda take wannan maganar ma yanata bulayin neman wankakkiyyar singlet da zaisa duka babu,ya watsar dana hannunsa yana duban idanunta

    “Kin gaza ta abubuwa masu yawa,wannan ya sanya dole nayi kewar kebance kanta da tayi daga wajena,abubuwan da kika kasa ita din duka bata daukesu a komai ba…….ki jiqamin singlets dina da hypo zan wanke da kaina,na gaji da siyan sabbin undies,idan kin gama ki gyara parlor zuwa cikin dakin nan,idan Fresheners dinmu ne suka qare ki gayamin,idan na fita zan shigo da wasu,banason na dawo na samu gidan nan a yadda yake” daga haka ya juya yaci gaba da shiryawa.

    Turqashi!,ita yake kafawa misali da widad din?,daya kafa mata misali da ita gwara ya buga mata misali da mutuwarta,sai ta rikice masa gaba daya itama,tana ganin bata da wani amfani a wajensa,baya ganin kimarta sam a cewarta,gaba daya saboda yarinya guda daya jal ya rasa walwalarsa ya rasa sukuni,yanata qoqarin shawo kanta tana wahal dashi,ita kuma da take iya bakin qoqarinta a kansa baya gani,bai dauketa da daraja ba.

    A hankali sai damuwa ta fara yi masa yawa,tako ina ba dadi,widad itace sanyin idaniyarsa,ita ta zamewa rayuwarsa wani bango da zai jingina ya samu relief a duk sanda wani damuwa ta sakoshi gaba,ba damuwar hafsat kadai ba,hatta damuwoyi da matsalolin gurin aiki,don rigimar hafsat ya riga ya saba dasu,to amma a yanzun da suka hadu da juya bayan widad sai abun yayi masa tsauri da yawa,dole ya dauki hutun kwana biyu don ya samu ya gyara komai,bauchin da zasuje ma ya daga tafiyar sai satin gaba,bayason su tafi bauchi a haka,yasan bazai fahimci komai ba har suje su dawo.

    Ranar farko wuni yayi a parlor din gidan shi da yaran,salla ce kadai take fiddashi,gaba daya zaman yayishi ne a bisa dole,don yadda widad din ke bashi kulawa ta musamman a duk sanda zaiyi wunar musu a gida irin haka bai samu koda quater din wannan daga hafsat ba,saidai ya share ya maida hankali ga yaransa da kuma gyaran bedroom dinsa da hafsat din ta tasamma sauya masa kamanni da halayen baqar qazantarta,ya gama sukayi gyaran parlor tare da yaran,baiko nema sa hannunta ba,saita fake da girki a kitchen.

    Duk bidirin da akeyi widad din tana jinsu tana daki a kwance abinta,tunda ta fuskanci wunin gidan zaiyi sai taqi yarda ma ta bude qofan bare ya ganta,ta kunna data tayi chart sosai irin wanda ta jima batayi ba,daga baya ta koma youtube ta vidmate ta dauko K dramas da chinese masu yawa na soyayya ta shiga kalla abinta,abinda ya rage mata tsahon wunin sosai.

    Da mamaki ya kwana,washegari bayan ya tattara su dukka ya kaisu wankin kai,don ya gaji da kallon buyagin kan hafsat din da bata damu ta gyara ba,daga nan yace ayi mata harda manicure and pedicure

    “Amma dai…..da kudin yaran ka bari a hannuna,sai nayi musu su a gida” ko ta kanta baibi ba ya tashi motar yana cewa

    “Idan kun gama let me know,zanzo na daukeku” yaja motar abinsa,don tuni ya tura kudin komai ta Account din kamfanin, gurin da widad ke zuwa ne,kuma gyaransu yana da kyau,already yana da details nasu dama saboda yadda ta saba da zuwa wajen duk bayan wani lokaci.

    A masallaci ya fara tsaiwa yayi sallar azahar sannan ya qaraso da motar cikin gidan.

    Duk da yasan babu kowa cikin Parlor din amma hakan bai hanashi yin sallama ba,kai tsaye ya doshi dakinta,yana jin cewa yau zaiyi maganinta,murdawa daya ga mamakinsa qofar ta bude,ya tura ya shige,ajiyar zuciya mai tafe da numfashi mai nauyi ya sauke, sassanyan qamshin nan da yayi mugun kewa shi ya fara masa maraba,ko ina na dakin fes dashi yana bada qamshin nan daya cakude ta turarukan jikinta,he missed her badly….. He missed komai da ya shafeta.

    Ba kowa a dakin sai ya tura qofar toilet din,itama wayam ba kowa,saidai da alama ba’a jima da gama amfani dashi ba,farare qal qal din undies dinta shanye a ciki suna digarda ruwa fari tas da alama sun wanku da kyau,sai qamshi suke fiddawa dasu da toilet din gaba daya.

    Da baya ya koma yana tunanin ina zata,ya tabbatar ba zata fita daga gidan ba ba tare da ya sani ba,tunani ya fado masa,saiya koma da baya yayi boys quaters.

    Dai dai sanda tayi rashe rashe abunta a dan qaramin parlor din maari tana cin dumamen tuwo miyar kuka,har tsakiyar kanta takejin dadin tuwon,maari na daga bakin famfo tana dauraye kwanukan da baba mai gadi ya gama cin nasa abincin,suna dan hira kadan kadan taji sallama daga bakin qofa.

    Sam hankalin widad baikai kai ba,tuwonta kawai take azawa cikinta, maari ta aje kwanon taja mayafi ta leqa,sai taja da baya cikin matuqar girmamawa da jin nauyin abbas ta soma gaidashi,ya amsa mata a mutunce yana tambayarta widad din,tace masa tana ciki

    “Zaka iya shiga yallabai” ta fada tana rabeshi ta fice a sassan ta wuce sashen hajiya,don dama akwai gyaran da zata mata yau din,gobe ko jibi zasu dawo daga balaguron da sukayi,tayi hakane don ta karanci kamar akwai ‘yar matsala ko sabani a tsakaninsu,batason saka baki ne a abinda bai shafeta ba,kuma ba’a yi mata tayin shiga ba.

    A nutse yake ratsa tsakar gidan nasu har ya isa qofar rumfar tata,idanunsa ya zube a kanta yadda take cin tuwon nata kamar ta samu nama,harma batasan ya iso wajen ba,ya qare mata kallo a nutse,kallon da bai samu yi mata shi ba tsahon sati kusan biyu,ta sake wani mugun cika,hatta da idanuwanta sun qara haske da girma,farinta ya sake daduwa kamar jini zaiyi tsartuwa a jikinta,duk da akwai madaidaicin hijab a jikinta,amma hakan bazai hanaka ganin yadda qirjinta ya cika fam ba,daga inda take zaune kuma baka isa ka nuna ciki a jikinta ba,abun yana mugun daure masa kai,yadda cikin yabi jikinta sosai,kamar bayason a ganshi,ya lumshe idanunsa kishinta yana cikashi,haka ta sake cika amma kullum take baro dakinta tana wuni a nan?,ko waye da waye suka taba kallon masa ita?.

    Tayi matuqar fusgar hankalinsa,wata kewarta mai zafi ta dinga taso masa,sai ya gaza jurar ci gaba da kallonta,ya tsugunna ya zare takalminsa,sannan ya miqe ya saka kansa rumfar maari,duk da ba haka yaso ba,amma yana jin kamar wani magnet ke jansa zuwa gareta.

    Sai daya kusa isowa gareta sannan turarensa ya ankarar da ita,tana dagowa idanunsu suka sarqafe waje daya,ta tsame hannunta zata miqe,ya saka dukka wani zafin namansa ya riqeta gam,ya kuma jawota zuwa jikinsa suka zube a wajen,bai tsaya wata wata ba ya hade bakinsu guri guda ya fara sauke mata french kiss mai zafi,wanda ya sanya cikin lokaci kadan jikinsa ya dauki rawa gaba daya,kamar wanda aka watsawa ruwan qanqara a lokacin hunturun sanyi,yayin da bugun zuciyar widad din ya qaru qwarai,har tana jin yadda abinda ke cikinta ya takure ya cure waje daya kamar yasan abinda ke gudana tsakanin mamarsa da abban nasa.

    Sai da yiwa zuciyarta laga laga,ya luguiguitar da ita,ya kuma sauke duk wani fishi dake maqare a zuciyarta sannan ya saketa yana maida numfashi,abun ya zame musu kamar wani faamin ciwo ne da tayar da tsohuwar soyayya da kewar juna da sukayi na nisantar juna da sukayi tsahon satittikan.

    Saida bugun zuciyoyinsu suka daidaita sannan ya sauke mata kallonsa da wani irin zazzafan kallo dake saka mutum a shauqi,tayita kauce masa tana jin nauyin yadda ta sake masa jiki haka ba tare data iya kare kanta ba,tabbas ta karbi saqo yadda yakeso,don yaga alamun haka a tattare da ita

    “Widad….” Ya fada muryarsa a mugun sanyaye,bata iya amsa masa ba,shima kuma bai damu ta amsa din ba ya dora da cewa

    “Fushi kikeyi dani?……wanne irin fushi ne haka widad?,so kike zuciyata ta buga?” Statement dinsa na qarshe ya sakata dago kai da sauri ta kalleshi,ya samu yadda yakeso,ya kuwa riqe qwayar idanunta da kyau ya hanata motsawa.

    Fuska ta narke cikin salon shagwabar nan tata da yayi mugu mugun kewa

    “Ba kai bane ba…..” Kawai sai ta fashe masa da kuka,gaba daya ta ida rikitashi

    “Ya salam” ya fada yana matsowa gareta gaba daya yahau aikin lallashi baji.ba gani,har zuwa sanda zuciyarta tayi sanyi

    “Pardon me please,I assure you it may not happen again” ya fadi hannayensa hade da juna,shi kansa yana mamakin yadda ya dinga misbehaving nata a lokacin,baisan me ya shiga kansa ba,amma a wannan lokacin sai zuciyarsa ke bashi kawai hafsat keda gaskiya,yasan ya mata abubuwa marasa dadi da yawa wannan shine kusan na biyar ko goma,amma ko a fuska tana qoqarin cinyewa,iyaka ta tura masa baki ya kama bakin yadan ciza shikenan an wuce wajen,a wannan karon ne itama ta gwada masa tata matantakar.

    Kai ta gyada tana sharar qwalla,sai yakejin kamar tana yankar naman zuciyarsa ne

    “Don’t cry mana,haba babyn uncle,It really hurting me when I see you crying” ya qarashe maganar yana tayata sharar hawayen.

    Fadan masoya hutu inji hausawa,cikin qanqanin lokaci ya wanke kansa a zuciyarta,daga qarshe dai jawa maari qofar sassanta tayi tabi mijinta.

    Tun daga parlor ya fara sauke mata dakon lodin soyayyarta daya dauka bashi,ta kuwa sakar masa kanta yayi yadda yakeso da ita,harma fiye da yadda ya zata,saboda sabon karatu data sakeyi wajensu fanna,kuka ya dinga mata saboda gaba daya ya gaza controlling kansa,duniyar da widad ke kaishi a duk sanda yake tare da ita……wata irin duniya ce mai nisan gaske da babu a inda yake nasarar zuwa nan idan bata bangaren widad din ba,’yar gaske ce ta wannan bangaren,mai madaukakiyar baiwa da ni’imar da ita kanta bata gama fuskantarta ba.

    “Me kuma nayi maka uncle kake kuka?” Ta fada tana tura baki gaba,fuskarta a tsakiyar tafin hannunsa,idanunsa jiqe da lema ya girgiza kai yana murmushi

    “Komai ma widad,komai ma kinyimin” saita zare ido,ya dora hannunsa saman lips dinsa yana fidda mata fararen mayanyan idanunsa

    “Shshshs…..ba zaki gane ba ko meye zance miki yanzu, I don’t know how to stop my self from crying duk sanda na kasance tare dake,bazan iya misalta dad…..” Tasan me zaice,kalmar kuma na masifar bata kunya,hakan yasa tasa tafin hannunta da sauri ta rufe lausasan labbansa tana boye kanta,sai ya dora nasa hannun saman nata yadan ciji tafin hannun nata kadan

    “Wayyo hannuna” ta fada tana janye hannun cikin shagwaba tare da yarfar dashi gefe,ya lakuce mata hanci

    “Shagwababbiya kawai” suka saki dariya a tare.

    Tare sukayi wanka,ta shirya cikin doguwar riga umbrella shape data bude sosai,mayyar dogayen riguna ce ita din,wanda hakan ya taimaka sosai wajen sake sirranta cikin dake jikinta,shi ya taimaka mata ta gyara shimfidar gadon da ya yamutsa,hatta da pillows a qasan gadon ya tsinto mata su,tanata tsokanarsa yasha mur cikin wasa yana basarwa

    “Duk aike kika jawo”.
    [09/05, 4:06 pm] +234 816 283 5575: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 13

    A Rubuce Take Book 2 Page 13

    Part 02

    Page 13

    *W A S H E G A R I*

    K’arfe shida da mintuna na saafiya ya baro masallaci,bayan ya gama ‘yan addu’o’insa.

    Daga bayansa yaji tafiya,kafin ya waiwaya an ambaci sunansa,tuni ya gane muryar sai ya rage tafiyar da yakeyi yaja baya kadan hadi da waiwayawa.

    Karasowa mutumin yayi fuskarshi qunshe da murmushi ya miqawa abbas din hannu,maimakon ya bashi hannun shima sai ya rusuna yana gaidashi cike da matuqar girmamawa.

    Kin amsa masa yayi har sai da sukayi musabahan,duk da har yanzu abbas bai miqe tsahonsa ba saboda bashi girma

    “Ban sani ba ko yara sun gaya maka saqona” yayi murmushi

    “Eh abba…..sunce kazo zamu gaisa”

    “Eh…..to ma sha Allah,na sake dawowa amma ban samu ganinka ba dai,mu qarasa gidan,inason magana da kai” tare suka jera da mutumin,suna tafe suna dan taba hirarrakin da suka shafesu,har suka isa cikin gidan.

    Bayan gaisawa da ma’aikatan gidan,kai tsaye suka wuce setting room dinsa.

    Sunansa abban ya kira yana duban fuskarsa

    “Nazo jiya sau biyu kamar yadda na gaya maka,saidai duk zuwan da nayi din na iske rikici ne da hayaniya tana fitowa daga gidan har harabar gidan nan,ya akayi kabar gidanka yake neman zama haka?,me yake faruwa?” Gyara zamansa abbas yayi yana sunkuyar da kansa,abban kamar mahaifi yake a wajensa,babu abinda zai boye masa,don haka ya gaya masa komai.

    Shuru yayi na wasu mintuna sannan ya sauke ajiyar zuciya

    “Ba yadda za’a yi ka ajjiye mata biyu a guri irin wannan sannan kayi zaton samun kwanciyar hankali,muddin kanason zaman lafiya saidai ka raba musu muhalli,wannan shine kawai hanya daya da zaka samu dai daito akan irin wannan matsalolin,daya bataga ‘yaruwarta ba bare wani abu ya biyo baya” kai abbas yake jinjinawa yayi, masa godiya sosai,lallai shawarar abban tayi masa qwarai,ya kuma bashi mafitar da shi a kansa ma bai kawo hakan ba

    “Amma…..ita hafsatu meye ya dawo da ita kaduna idan ba zallar neman fitina bama?” Abban ya fada cikin mamaki, saboda fes yasan halinta ya kuma san abinda ya wakana wancan karon,abbas din yayi qasa da kansa,yama rasa wacce irin amsa zai bawa abban,Allah shine masanin gaibu,kuma shi daya yasan yadda yakeji a qirjinsa game da dabi’a da halayyar hafsat din,shi kadai yasan irin haqurin da yakeyi da ita

    “Kada ka damu,kaci gaba da addu’a,sannan kaci gaba da jajircewa,Allah ya kawo mafita ya shige gaba”

    Ranar bai fita aiki ba,gaba daya sai yaji bashi da kuzarin fita aikin, widad din ta gama kashe masa jiki da xuciya da soyayyarta,a irin abinda take masan,yaso ace gidan nasu kamar daa ne sanda suke daga shi sai ita.

    Rashin fitarsa aiki ya sake harzuqa hafsat din qwarai,ta sake birkicewa sanda ya fiddo kaf kayansa dake dakin widad da wanda yake dakinta,ya kuma raba komai yace kowacce ta dauka,ranar kamar zata ara hauka

    “Wallahi na yarda…….yarinyar nan mallaka da asiri takeyi mai matuqar qarfin da yafi nawa” hankalinta ya tashi sosai,tana ganin abubuwan kamar suna fin na baya lalacewa da jagwalewa,ta rasa inda zata tsoma ranta ranar taji dadi,tanason tayi waya kuma tana shakkar kada ya shigo ko wani ya jita,dole ta dinga hadiyar bacin ranta ita kadai zuciyarta kamar zata fashe.

    To tun daga ranar abbas din ya fara neman wani gidan ba tare da sanin kowa a cikinsu ba,satin gaba kuma da zasuje bauchi hutu,zuwansu na farko bayan tahowarsu dukka gaba daya kaduna.

    Daren da suka isa da qyar widad takai safiya cikin gidan,saboda wani birkicewa da tayi,an dasa ma zuciyarta wani mummunan tsoron gidan,kwanan zaune tayi tana rusa kuka,tana jin kamar ta fita da gudu tanar cikin gidan,wani irin qunci ne ya cika mata qirji,tana jinta kamar wadda aka jefa cikin dokar daji ita daya.

    Sosai hankalin abbas ya tashi lokacin da ya biyo da asuba dubata ya sameta firgai firgai,tana ganinsa ta fada jikinsa ta saki kuka,tambayar duniya me yake faruwa ta gaza yi masa bayani,abu daya dai take fada

    “Banason gidan nan uncle don Allah,ka kaini wajen hajiya ko gidansu nujood” ko fita a part din ta hanashi,bata wani damu da jarabar hafsat da zata iya biyo baya ba saboda zamansa a part din nata ranar kwananta,haka shima abbas din,ba wannan bane damuwarsa,abinda ya sauya widad din yasa ta firgice haka ke bashi mamaki,bayan yasan lafiya qalau suka baro kaduna.

    Ko part din bai bari ba ya sanyata ta shiga toilet tayi wanka,wankan ma da da tace tayi idan sunje gidansu nujood yace aah,kafin ta fito ya shirya mata jakarta da kansa,ta fito ta shirya agurguje kamar wadda ake jira suka fito ya kulle mata sashen da kansa,yanata binta da kallo cike da mamakin abinda yake damunta.

    Sai data shiga motar sannan yace mata yana zuwa,ya juya zuwa sashen hafsat.

    Da sauri ta bar bakin window din,ta koma saman dining tana ci gaba da gyara kwanukan data zuba akai,duk da ba wani abun kirki ta dafa ba,a cewarta ta gaji,ba zata iya wani dogon aikin abincin safe ba.

    Amsa sallamarsa tayi kamar bataga komai ba,ta daga kai tana dubansa,shima ita yake kallo, already ya saba ba kasafai yake gaidashi da safe ba,wani lokacin yayi mata gyara wani lokacin ya watsar da ita

    “Zan kai widad gidan muhsin kada ki jini shuru”

    “A dawo lafiya” ta amsa masa ba tare data dubeshi ba hankali kuma kwance,tana jin wani dadi yana ratsata,sai ya shafa kan yusra dake kwance cikin kujera sannan ya juya ya fice.

    Yana fita taja wani mugun tsaki sannan ta saki dariya

    “Habaaaaa yarinya,ki hanani sakewa a can a nan ma ki hanani?,Allah ya raka taki gona,da ikon Allah ma kin fita kenan ba zaki sake dawowa ba” ta sake rufe zancan nata da tsaki,tabar aikin da takeyi din ta koma saman kujerar tana karkada qafa,a duniya ita daya tasan yadda yarinyar tayi mata karen tsaye a rayuwa,duk yadda takai ga zuba iskancinta bata taba fuskantar matsala irin wannan daga wajen abbas ba sai yanzu,ta sake jan wani tsakin

    “In sha Allahu sai nayi maganinki,bazan gaji ba wallahi” ta fadi a fili kamar ita da wani suke magana.

    Kamar cirar qaya haka taji bayan fitarsu daga gidan,sai taji komai yana raguwa cikin kanta, nutsuwarta tana dawo mata a hankali a hankali.

    Sanda suka isa gidan ta shiga ciki mamaki ne ya kama hajjaa,koda ta tambayeta lafiya?,ce mata tayi ba komai,kawai ta gaji da zaman gidanne.

    Cikin mintuna qalilan ta sake sosai kamar ba ita ba,zuwanta ya yiwa yaran gidan duka dadi,ta ware sosai abinta,har zuwa sanda abbas dake setting room sunata hira da uncle muhsin,irin hirar da suka jima basuyi irinta ba ya tashi tafiya,ta miqe ta yafa mayafin abayarta ta fice don suyi sallama.

    Idanunsa qur bisa qofar,kamar daman jiran isowarta yakeyi,ta yaye labulen ta shigo a hankali,saiya miqa mata hannunsa,ta kama a hankali ya jawota a tausashe yayi mata masauki saman cinyarsa.

    Hannusa guda daya ya dora saman cikinta,kamar yasan me akayi yayi wani zillo,tadan motsa da sauri tana zare ido,don har yau ta kasa sabawa da irin wannan motsin,abbas da yaga irin yadda ta motsa sai ya saki murmushi

    “Kin gani ko?,shi kansa yana cewa zaiyi kewar babansa,amma mamansa kamar bata damu ba” ya qarashe maganar yana langabe mata kai kamar wani maraya me neman agaji.

    Yadda yayi din ya bata dariya,tadan saki siririyar dariyar data bayyanar da fararen haqoranta dake burge abbas sosai,ta saka hanuwanta duka biyu ta riqe kansa cikin tafukan nata tana dubansa

    “Mamansa zatayi kewarka fiye da yadda shi zaiyi……”

    “Amma me yasa kika zabi kibar gidan?,kinsan yadda nakeji duk lokacin da na juya cikin gidan naga babu ke a cikinsa?,widad…..duk gidan da babu ke a cikinsa shida kango daya suke a wajena.

    ,inji a zuciyata kina gidana wata babbar rahama ce a wajena,kallonki yana bani dukkan nutsuwa da zuciya da ruhi suke buqata…..ban taba kasancewa tare dake ba…..koda wata mu’amala bata shiga tsakanina dake baba tare dana samu nutsuwa ba” yadda yake tsara mata kalaman da yadda yake karanta mata su cikin kunnuwanta sai suka kashe mata jiki,ta matsa a hankali ta kwantar da kanta saman kafadarsa tana rufe idanunta gami da jin yadda bugun zuciyarta ya bugawa a nutse,irin bugun da bata samu irinsa ba daren jiya.

    Ita kadai tasan irin yadda take fighting da wani mugun tsoro….. tsoro irin wanda bata taba jin irinsa ba….. qunci da damuwa da wata irin qaguwa na tabar gidan,ta matsa a wajen,tana jin kamar tana taka qayoyi a qafafunta duk sanda take taka kowanne sashe na gidanta,amma batasan ya zata gaya masa ba,ya zatayi masa bayani,tunda ita daya takejin hakan,ta sani tana addu’a kuma tana samun sauqi lokaci lokaci.

    Sun jima a haka suna shan dumin jikin juna,kafin ya dagata yana duban fuskarta

    “Gobe ne kwananki,zanzo na daukeki,babu cin bashi” narke masa tayi,ya dora yatsantsa saman labbansa

    “I will bring you back,right?” Murmushi ta sakar masa sannan ta gyada kanta,tashin hankalinta dama yace zata ci gaba da zama har zuwa sanda zasu koma Kaduna.

    Kwana daya tak tayi yazo ya dauki abarsa,hajja nata tsokanarsa ko surukuta babu?,bai amsa ta ba illa binta da yayi da miskilin murmushinsa.

    Hafsat ta sake sosai ganin widad bata gidan,hankalinta kwancw tana ganin zata ci gaba da riqe abbas muddin suna bauchi saidai idan sun koma kaduna,a can dinma tunaninta ya fara karkata…..me zai hana tayi wani abu a kaine kwatankwacin abinda ke wakana yanzu?.

    Sosai shawarar ta zauna mata cikin kai,don a yanzun da take zaune ita daya cikin gidan sai takejin kamar bata da sauran matsala a duniya.

    Ba qaramin kaduwa tayi ba lokacin da ta fara jiyo qamshi na fita daga part din widad din,qamshin turaren wuta da na abinci duka lokaci guda,sam sam batasan sun shigo gidan ba,daga ita har abbas din,zuciyarta tayi wani irin nauyi,mamaki ya kusan kasheta

    “Wannan wacce irin musiba ce” ta furta a fili kamar zata zunduma ihu,duk ta inda take hangen nasara sai alamun nasarar sun fara bayyana kansu sai komai ya rushe.

    Kasa jurewa tayi ta aika yaran su gano mata abbansu yana nan,baya nan din don tunda ya ajjiyeta ya fita yace zaije ya dawo,saidai sun dawo mata da tsarabar lafiyayyen samosa da yaji nama carrot dankali da wadatacciyar albasa.

    Samosan yana daya daga cikin abinda take mugun so,qyuya son jiki da rashin maida hankali a koyi girki yasa bata iya ba,duk da suna da komai na amfani a gidan da zata iya yi da kanta,sa’annan son kudi da son abun duniya kuma baya barinta ta siya a wani waje,saidai idan anci sa’a ta fita wani gurin sha’ani ta samu a can taci.

    Duk sonta dashi yau din quncin zuciya da kuma tsanar widad din ya hanata ci,duk da yawan wanda ta bawa yaran,suka sanya abinsu a gaba suka cinyeshi tas suka sha ruwa,duk sai suka hau bacci.
    [10/05, 9:20 pm] +234 816 283 5575: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *UCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 14

    A Rubuce Take Book 2 Page 14

    Part 02

    Page 14

    Tun daga ranar sai ya zamana duk sanda sukazo kadunan gidan hajja take sauka abinta,don a yanzun ta yiwa gidan hajiya qaura,mugun kunyarta takeji saboda cikin da yake jikinta,ranar da hajiyan tayi mata addu’ar Allah ya raba lafiya kamar zata mace a wajen saboda kunya,taso qwarai ma ya dinga barinta kaduna,amma yaqi,saboda hajiyan nayin fada duk sanda yazo babu ita,bugu da qari shi kansa bazai iya wadan nan kwanakin tana wani gari yana wani ba,a haka rayuwar taci gaba da juyawa,har suka share watanni uku,mugun nufin hafsat din bai cimma gaci ba yadda takeso take kuma tsarama ranta,saidai a wasu abubuwan da dama ubangiji kan yiwa bawansa talala ya barshi da zabinsa.

    *_B A Y A N W A T A U K U_*

    Sanye take da wata farar gown ta wani cotton material dake da wani irin ado mai qyalli na golden din zare,ta bude sosai daga qasan rigar,hade take da mayafinta mai dan yalwa,tana tsaye gaba madubin dakin nujood tana shafawa fuskarta farar powder,nujood din na saman gadonta daga bayan widad din,hannunta dauke da littafin da widad din ke karantawa,tana tsaka da karatun abbas yayi kiranta kan cewa zai shigo.

    Yadda widad din keta qalqale jikinta yasa nujood ta kasa yin shuru

    “Ni banga amfanin wannan qaqale qaqalen da kiketa yi ba,just yaushe kikayi wanka ma?,wannan skin din naki da baya riqe dauda kwata kwata?,a wannan kyan da cikinki ya sakaki kikayi indai baso kike ki matso muninki ba don Allah kibar face dinki haka” murmushi ya qwacewa widad din ta juyo tana kallonta

    “Uncle abbas ne fa zaizo,ke waya gaya miki ana wasa da lokuttan da za’a kebe da miji,kin mance kishiya gareni?” Dariya sosai nujood ta kece da ita sai itama widad din ta saki dariyar,ta tashi ta zauna sosai saman gadon

    “Ni wanna kishiyar taki ita da zero duk daya,kinsan Allah tun bankai haka wayo ba nake tunanin uncle abbas me aji,dan gayu wanda bai rasa komai ba…..me ya gani a tattare da wannan wai?,wai kinsan tun asalinta qazama ce?,da sallah abba yayi yayi muje gidan uncle abbas muqi,ya rasa dalili in gaya miki,baisan idan munje wuni muke da yunwa ba,bata iya dafa mana abinci saidai ta hadamu da kayan tarkace,ci banza ci wofi,ga uban wanke wanke da wankin undies da zata hadaka dashi” sauke hannuwanta data goya widad tayi tana jinjina kai,qazantar hafsat din ita kanta tana matuqar daure mata kai,harta kama jikinta,don ko kumbarta ka kalla kasan akwai burbushin qazanta a tattare da ita

    “Allah ya kawo mata sauqi”

    “Ai wannan ba zata daina ba har ta mutu”

    “Banason wulaqanci,mamar yaran masoyina ne fa” widad ta fada tana jifan nujood da hararar wasa,saita fidda ido

    “Wai yaushe kika zama rasa kunya ne?,komai naki uncle abbas,baki da aiki sai maganarsa?” Fararen idanunta ta juya kafin ta saukesu akan nujood

    “Kin manta shine rayuwata?,a kansa na fara sanin soyayya qauna kulawa da tattali,a kansa na fara sanin rayuwa, ga kuma d’a ko ‘yarsa a jikina” baki sosai nujood ta kama tana gwalalo ido

    “Na shigesu,widad yanzu kinfi qarfina,Allah yasa dai nima gab nake da auren nan bare ki sani a uku” dariya suka sake qyalqyalewa da ita

    “Wai nikam……mamar mimi tasan da cikin nan?,banji har yanzu ta nuna kowanne reaction ba” baki widad ta tabe,har zuciyarta bata qaunar zancan matar,ita a yanzun ta mijinta kawai takeyi

    “Idan nace miki muna iya sati daya bamu hadu ba zaki yarda?”

    “Haba dai?” Juyawa widad tayi tana zizarawa idonta kwalli

    “Bata da aji gaba daya matar,da farko kallon mamata ma nakeyi mata,bana iya.musu ko qanqani da ita,ta cutar dani taso gurgunta rayuwata ta hanyar yin amfani da quruciyata,to a yanzun kuma meye yayi saura tsakanina da ita,ina kishin uncle sosai,shi yasa bana hada inuwa daya da ita,har muzo bauchi mu gama zamanmu bama sake haduwa sai a mota idan zamu koma,to me zai hada ni d……..” Maganarta ta katse sanda kira ya shigo wayarta,ta duba fuskar wayar tana murmushi

    “Uncle dina ya iso…..”kafin ta daga wayar kiran ya katse,dai dai nan hajjaaa ta turo qofa tana gaya mata tayi ta fito ga uncle abbas dincan a setting room

    “Saina dawo” ta fada rana zira wani plate white shoes na fata daya dace da qafarta

    “Allah ya kiyaye hanya Juliet matar romeo”

    “Babanki ne dai” ta amsawa nujood ta fice tana dariya,itama dariyar ta saki tana bin widad din da kallo,gaba daya rayuwarta da uncle abbas din burge nujood take,wata qauna da soyayya yake bata irin wadda bata iya boyuwa,duk inda kayi musu kallon farko zuwa.na biyu zaka fahimci hakan

    “Ashe dama uncle din nan dan duniya ne” ta fada qasa qasa a fili tana dariya, saboda ta tuna sanda yake zuwa gidansu,tsakaninsu dashi gaisuwa,sai qarancin fara’a da kuma tsare gida da yake dashi,amma fa duk da haka dama can din shi mai kirki ne da yawan kyauta.

    A nutse tayi masa sallama da sassanyar muryarta wadda ta tanadeta musamman sabodashi,kasa amsa sallamar yayi,saima ya miqe tsaye cak yana jiran isowarta.

    Hannuwansa ya bata duka biyun,ya kuma jawota zuwa jikinsa yayi mata kyakkyawan masauki,ya sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi yana tura kansa cikin mayafinta da kyau,tare da shaqar daddadan qamshin da take fiddawa.

    Ya jima a haka shi da ita suna jin dumin jikin junansu,kwana biyu tal amma yana jin kamar ya shekara ba tare da ita bane

    “Ka zauna uncle” tayi qarfin halin fada,saiya dago fuskarsa ya hade da tata

    “I missed you har bansan yadda zan kwatanta miki ba”

    “I missed you too uncle” ta fada tana qanqameshi sosai,sai ya saki murmushi tare da ajiyar Zuciya gaba daya,yana jin dadin yadda kullum widad din ke sake zama cikakkiyar mace data karanci abinda yafiso da wanda bayaso,tamkar yana mata sharinga wani part na qwaqwalwarsa ne.

    Ita ya fara zaunarwa sannan ya zauna a gabanta,ya dauko dukka qafafunta ya dora saman cinyoyinsa yana matsawa a hankali hadi da sauke mata wani narkakken kallo kamar zai cinyeta.

    Kusan ta saba da irin wannan yanayin,duk da yana azama zuciyarta wani sabon naiyi ne,amma ko tace ya koma saman kujera ya zauna bazai zauna ba,yakance yana matuqar jin dadin hakan,duk da tana zaune sai data rusuna da dukkan girmamawa tace

    “Barka da yamma yallabai”

    “Barka kadai yallabiya maman biyu” saita zaro ido

    “Uncle…..kanason na mutu ko?” Kai ya girgiza da sauri

    “No…..idan kika mutu babynuncle……na tabbatar a ranar nima zan biki,just kawai ina sha’awar twince dinne,amma tunda bakiso shikenan” ya fada yana dariya cikin ransa,ta wani bata fuska kamar shine mai bayarwa ko kuma yace lallai twince din zata haifa.

    “Ya bakaso dasu mimi ba?” Ta sake tambayarsa

    “Ban qarasa gida ba,daga sokoto direct nan nayo…..ba zama ma zanyi ba,ki koma ki dauko abinda zaki dauko mu wuce gida” fuska ta narke masa sosai tana kallonsa

    “But uncle…..a wajen mummyn mimi ya kamata ka sauka,kuma ma ka manta…..gobe fa na gaya maka zasu wuce kano anty madeena ta haihu,inason na bisu,i missed ummu alort,nayi missing kowa,abba na….su Aarifa da kowa”

    “I know…..i know,bance kuma ba zakije ba,amma ina buqatar ki cike ragowar kwananki,kwana daya nayi miki aka kirani sokoto,kin tuna?” Baki ta turo masa gaba,a kwanakin gaba daya ciwon mara ne yake damunta,abunka da rashin kan gado fa rashin sanin makama irin na masu haihuwar fari saitake ganin duka takurarsa ne ya jawo mata,don kamar wanda aka qarawa qaimi a kanta,baya iya daga mata qafa a dukka kwanaki biyun da zaiyi a wajenta,shi kansa yasan tabbas tana qoqari,wannan ya qara mata matuqar kima da martaba mai tarin yawa a idanunsa,abinda wadda ta linka shekarunta ta gaza qanqanuwa da ita tana iyayi,kai bama ita ba,hatta da muhsin yanzun ganin girmansa yake qwarai da gaske

    “Uncle a daina tuna baya fa”

    “Wannan tuna bayan ya zama dole ai” ya fada yana lumshe ido,yana zagaye lips dinta da suka dan qara tudu kadan da yatsun hannunsa

    “Nidai nidai”

    “Baki zuwa?,sai naje na kaima mummyn mimi kwanan naki” ya dauka zatace bata yarda ba,don ya gama sallamawa kan yadda take kishinsa,saidai kishi ne irin na hankali da sanin ya kamata,wanda zakayi zaton wasu shekaru gareta masu yawa,amma sai yaji yace ta yarda.

    Kicin kicin kuwa yayi,ya kasa ya tsare yace ta shiga ta fito yana jiranta,cikin sa’a Allah ya jefo da uncle muhsin,ya goya masa baya ya tayashi koro qaryarta,harda guzurin

    “Kada ka yarda gobenma ta wahalar dakai,zasu biyo ta nan gidan su dauketa basai tazo ba”.

    A mota ta dinga masa fishi,bai damu ba ya biye mata kawai,ya yita yawo da ita ya cikata da qwalaman kayan toshiyar baki,bakin kuw aya tosu,ta tasa kayanta a gaba ta dinga ci,saidai a yau din bata wani ci da yawa ba taji ta qoshi.

    Yau dinma bayan widad din kawai hafsat din ta gani sanda shiga sashenta,mugun kishin da takeji a ranta ba kasafai ma yake barinta take iya mata wani kallo mai tsaho ba,don duk sanda tace zata zurafafa kallonta zuciya na ingizata ta aiwatar da abubuwa masu yawa,wanda ta tabbatar muddin ta aikata hakan sakamakon bazai mata kyau ba,takanji kamar ta samu wani ruwan guba da zai bata mata fuska ta watsa mata,ko tayita dukanta har dai ta galabaitar da ita,ko kuma ta shaqeta har sai ta daina motsi

    “Baqar matsiyaciya” ta fada a ranta,tana sake jin qwarin gwiwar ci gaba da jarraba sa’arta akan widad din har sai sanda ta cimma nasara.

    K’arfe sha biyu na rana suka sauka garin kano,cikin gidansu,gidan dake da tsohon tarihin a wajen widad,gidan da tayi wata rayuwa ta gata shagwaba da sangarta,batasan me kalmar matsala ke nufi ba,batasan bacin rai ko damuwa ba,a lokacin ko baka sonta bata jin zafin abun saboda zallar quruciya da rashin damuwa da ire iren wadan nan abubuwan.

    Duk yadda zuciyarta ke matuqar dauki da son ganin ummunta amma qafafunta da suka dan tasa saboda zaman mota sunqi bata dama,tana hanya kafin ta qarasa su nujood suka dinga wuceta suna mata dariyar sai sun rigata ganin ummu,ta kuwa kebe baki shagwabar ta motsa,hannunta riqe da bayanta dake dan motsa mata lokaci lokaci ta isa falon ummun,dai dai sanda nujood ke dariyar

    “Saida kowa ya gama gane miki ita sannan kika iso” tureta gefe ummu tayi ta miqe tana cewa

    “Ba wanda ya rigata gani na,ni na fara ganinta,kuma itama ni ta fara gani” sai widad din tayi qaramar dariya tana jefawa nujood harara hadi da cewa

    “Munafuki dai baiji dadin halinsa ba wallahi” ta fada jikin ummunta,ummu ta riqeta da kyau,farinciki ya cika zuciyarta gaba daya,widad dinta kullum girma takeyi,kullum kuma alamu suna nuna soyayyar mijinta a jikinta,ta zama wata babbar mace kamar ba ita ba,idan ka ganta zaka musanta shekarunta,ga kuma albarkar aure a tattare da ita,duk da batasan watanninsa ba amma tasan dai ya fara mata nauyi,Allah zai cika mata burinta na ganin dan widad a duniya?,saita share hawayenta cikin dabara ta zaunar da widad din a nutse tana fadin

    “Me yasa kikayi tafiyar mota ga qafafunki nan sun tasa”

    “Bazan iya jurewa ba ummu,a taho kano a barni?” Saita girgiza kai tana dariya,kai itama ummun ta girgiza

    “Ki shiga ciki to ki fidda kayan nan,ki watsa ruwa sai a dumama miki qafar ki shafa man zafi,kici abinci saiki kwanta ki huta”

    “Duk ita kadai ummu?” Aafiya dake shigowa ta fada,cikin madaukakin farinciki suka rungume juna ita da widad

    “Wai ashe dai da gaske mun kusa zama iyaye” ta fadi tana kallon cikin widad da wahalar tafiya tasa a yau din ya fito sosai,kamar damar ranar yake jira,kamar jira yake su shigo kano din.

    Da sauri ta kwabi Aafiya, saboda ita har ga Allah kunya takeji idan akace ciki ne da ita,sai taji kamar ta nutse

    “Ba abinda ummu fa zata miki,tafi kowa ma murna,randa aka gaya mata ko abincin kirki kasa ci tayi” ta fada tana sheqa dariya,don dukkansu sunsan danbarwar boye cikin data dinga yi,sai suka sanya dariya gaba daya qasa qasa.

    To wanka da hutu dai baiyiwu wajen widad ba,don gidan nasu cike yake da baqi kasancewar jibi sunan yarinyar da anty madeena ta haifa,baqi anata shigowa,yan uwa da abokan arzuqi gidan a cike yake,wannan ya shigo wannan ya fita,anata hirar yaushe gamo,sai widad din take jin ranta fes,kamar bata da sauran matsala,hatta da wayarta ta mantata a jaka gaba daya.

    Jin hajjaa zata fita ziyarce ziyarce danginta da nasu uncle muhsin din sai widad din tace zatace,ummu ta kasa ta tsare tace ba inda zata fita,ta marairaice mata da kyau

    “Don Allah ummu ki barni naje,yaushe rabona da kano,koda zamuje aikin hajji kwana nawa duka nayi,da muka dawo kuma ko gidan nan uncle bai barni na shigo ba muka wuce bauchi”

    “Ki barta taje ummu,ta dan tattaka ma,tunda acan nasan ba wani waje kike zuwa ba” anty halima dake wajen ta roqar mata ummun.

    Yawo sukayi sosai harda tafiyar qafa,kafin su dawo kuwa jikinta ya soma gaya mata,a ciwon mara da bayanta ya sake qaruwa time to time,a haka take cinyewa ganin idan ya motsa yana daukan wasu mintuna masu tsaho sai basake motsa mata ba.

    Basu suka dawo ba sai ana gab da sallar magariba,kai tsaye ta wuce dakin da ummu tasa aka gyara mata ta fidda kayan jikinta tayi wanka da ruwa me mugun dumi wanda mutuniyarta latifa ta hada mata.

    Tana fitowa daure da towel taji marar tata ta sake riqewa da kyau,saita lallaba ta zauna gefan gado tana cije lebe har zuwa sanda ya lafa mata,ta yunqura zata miqe don ta shirya ta sake ficewa, hankalinta yayi gaba saboda sautin hirarraki da take jiyowa daga falon ummu sai taji ringing din wayarta,ta dafe baki tana mamakin yadda yau wuni sur ta manta da wayarta,suna gama waya da mommynta kiran abbas ya shigo,tunda sukayi sallama ta maidata jakar,tasa hannu ta dauko jakar da aka aje mata saman pillow wanda duka tasan aikin latifarta ne,ta buda ta ciro wayar.

    Ido ta zazzaro ganin tarin miscall din abbas kusan guda ashirin,ta bude pattern din tana yunqurin kiransa sai gashi ya sake kira.

    Ajiyar zuciya ya fara sauke mata kafin yayi mata sallama,ta amsa tana jin kewarsa a take tana saukar mata

    “Kin dagamin hankali sosai,banda yanzun muka gama waya da naadir ya tabbatarmin lafiya da tuni na kamo hanyar kano” ido ta zaro cike da mamaki

    “Uncle?,da gaske?,kano fa kace?,don kawai ban daga wayarka ba?” Murmushi ya fidda mai sauti,ko yaya zaiyi mata bayanin girman matsayinta a idonsa ba lallai ta gane ba,saidai kwanyarta ta dauki iya abinda zata dauka

    “Wudd…” Ya kirata da sunan da kaf duniya shi daya yake kiranta dashi,ta amsa masa a tausashe

    “Matata fa…..da yarona ne suke neman bacemin,yaya zan saka wasa?” Dariya ta subuce mata mara sauti,saita jinjina kai

    “Allah ya qara maka lafiya da nisan kwana”

    “Inason hakan musamman ya zamana tare dake zamu mori lafiyar da kuma nisan kwanan” kunya tadan kamata,yadda uncle din yake mata kamar baya tuna cewa ya ninkata a shekaru,ita din sa’ar ‘yar abokinsa ce,ba ruwansa da wanann,kwata kwata baya iya boye mata soyayyar da yake mata.

    Wata irin hira mai sanyi sukeyi shi da ita,sau uku latifa na leqota taga waya takeyi saita koma,basu rabu ba har sai da mararta ta tsikareta tace

    “Wayyo Allah” cikin matuqar kulawa yake tambayarta lafiya,data gaya amsa yace ta ajjiye wayar taje taci abinci ta kwanta ta huta sosai,gobe sur yakeso ta yini a gida kada ta sake fita,shima a goben tun asuba zai fita shida Samuel zasu sokoto,tayi masa kyakkyawar addu’ar nan tata dake qara masa qwarin gwiwa sannan suka rabu.

    Doguwar rigar da tasan ba zata takura ba ta sanya,ta zura hula ta sakawa qafarta socks sannan ta fito.

     

    [11/05, 2:59 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 6

    A Rubuce Take Book 2 Page 6

    Part 02
    Page 06

    Hannu ya miqa mata yana dubanta da idanunsa da sukayi laushi,saita noqe kafada alamun a’ah,ya sauke hannunsa muryarsa adan shaqe yana tambayar

    “Waye?”

    “Nice” kakkausar muryar hafsat ta bayyana,ya miqe cikin wata irin kasala hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya isa bakin qofar yasa hannu ya bude mata.

    Idanu suka zubawa juna shi da ita,ita din tanason karantar cikin wanne yanayi yake,yayin da shi kuma yakeson jin ba’asanin bugun qofar

    “Tazo ta kwashe kayan nata” sai daya lumshe idanunsa ya lumshe ya budesu lokaci guda sannan ya amsa mata a nutse

    “Meye damuwarki ne?,badai kinyi complain ba?” Mugun haushi ya cikata,yadda ya bata amsar sam shi bashi da damuwa ma kenan

    “Eh…..amma dai kasan yau din kwana na ne da zakazo har cikin dakinta ku rufe qofa” sai daya dubi bayansa wato cikin dakin ta gefan idanunsa sannan ya maida dubansa kanta

    “Stop it hafsat……kisan irin abinda zaki dinga fada,yara kin sani suna jinki”

    “Eh ai.hakkin……”

    “Dalla ya isa……bacemin agun” ya fada cikin bacin rai ganin bata da niyyar yin shuru,gasu mimi dake zaune daga falo ta fara calling attention dinsu.

    Ido ta zuba masa cikin bacin rai,saita jijjiga kanta da qarfi ta juya da sauri tana barin wajen saboda hawayen da suka ciko mata idanu,cikin bacin rai yaja siririn tsaki ya koma da baya cikin dakin,zuwa sannan har widad ta nema doguwar riga ta saka.

    Wani kyan yaga ta sake masa fiye dana dazu,yasa hannu ya dan shafi cikinta kadan wanda shima har yanzu yake mamaki idan ya tuna tuna akwai d’a a ciki

    “Ki shiga dakina ki dauke abubuwanki masu muhimmanci,mamansu mimi zata aje kayanta” ido tadan lumshe sannan ta kauda kanta tana jin wani abu ya soki zuciyarta,a taqaice dai an koreta daga dakinsa mummy Hafsat din ta tare kenan

    “To” ta amsa masa ciki ciki tana dan tura baki gaba,ya fahimceta sarai,qaramin murmushi ya kubce masa,yadda take kishin nan nasa yana nurgeshi sosai,sai ya.miqa hannu ya jawota jikinsa

    “Bamu rabu ba babyn uncle,ko yaushe ina cikin gidan nan,ranar girkinki kuma zamu kasance tare anan har sai kince kin gaji” da sauri tadan tureshi tana dariya

    “Nifa ba haka nake nufi ba,kuma ma bance komai ba uncle” dariya ya saki cikin jin dadi,Allah baya hadawa bawansa zafi biyu,idan ya rageka ta wani bangaren saiya sanyaya maka ta wani,sam bata daukar abubuwa da zafi,uzuri guda daya kacal ya isa ya wankeshi a wajenta.

    Shi ya taka mata har dakin gudun fitina,yana tsaye ta hada kayanta tsaf ta baro dakin,shima duk sai ya dinga jin ba dadi,har ya fara tunanin sauya muhalli wadatacce muddin hafsat din ta dage da zaman kadunan.

    Kamar jira take widad din ta fita a dakin ta fito daga bandakin data shige sanda taji motsin shigowarsu,gudun kada widad din taga hawayen da takeyi ta rainata, qorafi taso dasa masa kan wanda ta fara dazun amma bai bata fuska ba,hasalima sai ya fice daga gidan abinsa,dole ta tattara dukka wani quncinta ta adanashi waje guda,don ko widad dinma tana cikin dakinta tana sabgarta,bata ganta ba bare ta juye a kanta.

    Da dare shi ya kira widad din akan tazo suci abinci,hafsat din tanata wani cika tana batsewa kamar wadda tayi wani abun kirki,shinkafa ce da miya ‘yar kullum,sai nama da bai gama rusuna ba cikin miyar.

    Wata armless chiffon gown ce a jikinta ruwan zama, tsahonta duka duka iyakarsa qauri,ko sauko mata batayi ba sosai,hafsat din ta bita da kallo ranta kamar zai fashe,ta cika tayi fam a rigar saboda cikinta da yabi jikinta sosai zuwa qirjinta,ita batayi don wata hafsat ba,tayine saboda sabo,ire iren shigarta kenan dama a kadunan,da wuya ka ganta da atamfa.

    Da qyar take zuba abincin,ta gama ta turawa kowa tabar widad da zuba nata,kadan ta zuba,don ko a ido ma ta dinga jin abincin bai mata ba tun batakai cikinta ba,aikuwa da qyar tayi loma biyu ta miqe,ya bita da kallo yana tambayar ba’asi

    “Na qoshi ne uncle” ta fada adan shagwabe,yasan inda matsalar take,shi kansa da ya saba cin wannan collabo din nata yana ci ne kawai don babu yadda zaiyi,bare widad din da bata saba ba.

    “Amma…..me zakici?” Tadan juya fararen idanunta cikin dan tunani

    “Zan duba wani abun ko cikin fridge ne” kai ya gyada

    “Make sure kinci wani abun kafin ki kwanta,karki sake ki kwanta da yunwa” ya fadi yana dan jin damuwa a ransa,ya dauko abinda ya zame musu damuwa duk su duka,kai ta gyada

    “In sha Allah uncle” sai ta fara takawa zuwa cikin dakinta,yayin da hafsat ta kasa daurewa taja wani mugun tsaki mai masifar qara

    “Ayidai mu gani” kallonta yayi baice komai ba yaci gaba da cin abincinsa ganin widad din ko waiwaye batayi ba bare tasan abun ya shafeta,sai yarinyar ta sake burgeshi,yasan ta tsani taja masifa aqi tanka mata,yanzu zata sake haukacewa

    “Sai wani rawar qafa kake a kanta,idan banda daurewa qarya qarqashi,ayi abincin tace wani wai bataci,sannan kai ka biye mata da zancan ta nemi wani abun taci tsabar ciwa mutum fuska” tayi maganar muryarta tana rawa.

    Sosai ya kalleta kafin ya aje spoon din hannunsa

    “Ki shiga taitayinki hafsat,ni ba haka na saba rayuwata a Kaduna ba,nutsuwa da kwanciyar hankali sosai nake samu,ba zaki zo ki hanamin wannan ba,indai kikace irin wanan halin zaki dauka to ki tabbatar ba zaki taba jin dadi na ba” daga haka ya miqe shima yabar mata wajen.

    *******Kwanakin girkinta guda biyun nan ta rasa inda zata tsoma ranta taji dadi,itadai widad bata fasa sabgoginta ba kamar yadda hajiya fanna ta bata shawara,illa iyaka ganinta ma wuya yakema hafsat din bare ta takaleta,wuni a daki baya yi mata wahal,tayi kallo ko tayi chart ko ta buga game,idan ta fita falo daukar abu tazo yi zata dauka ta wuce abinta,yaran suna son zuwa wajenta amma uwar ta kasa ta tsare,idan ta bari sun rabeta to uban yana gidan ne babu yadda zatayi tana shakkar hanasu.

    Abbas din yana ta qoqarin ganin tana fitowa ta sake a cikinsu amma taqi bada wannan damar,don ta sake sanin ciwon kanta zuwa yanzu,uwa uba kuma kishin hafsat din itama takeji sosai,musamman ta ganta ta fito daga dakin uncle din nata sai taji kamar zuciyarta zata fashe,tafi ganewa tayi zamanta a dakinta tayi sabgoginta,ko abincin darenma na washegari tsakura tayi tabar falon,hafsat din nata binta da harara kamar idanunta zasu fado,amma ita bata ma kalleta ba bare tasan me takeyi.

    ********Kwanansu biyu da dawowa widad din ta karbi girki,ranar tunda safe datayi wanka ta shirya cikin wata farar wide leg jumpsuit,sai baqar gatsby cap data dora saman kanta.

    Duk sa cewa tayi shigarta ne kawai normal bada wani manufa ba amma wani mugun kyau tayi,shigar ta karbeta sosai,saika dauka wata baturiya ce,musamman yadda sassalkan gashinta ya fita ta qasan hular kan nata.

    Ta lura da lalacewar falon kwanaki biyu kacal,saboda haka can ta fara fita bayan ta zura lallausan bedroom slippers dinta.

    Yadda take tsammani haka ta samu falon,a wargaje tarkace kota ina,haka ta dinga kawar da duk abinda tasan bai kamata ya zauna a falon ba tana killaceshi,cikin mintuna qalilan ya fara daukan saiti.

    Tana tsaka da aikin hafsat ta fito dauke da qaramin mug da plate dinsa,suka hada ido widad ta janye kallonta daga kanta tana ci gaba da aikinta,wata irin harara da widad din batasan tana yi ba ta zabga mata,taja wani dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta,gaba daya yarinyar ta gama shige mata rayuwa,banda tsabar raini me ya hadata da taba mata falo?,ko tana tunanin itama tana da power ne irin yadda ita take da ita?

    “Iyayin banza da wofi kawai” ta fada tana wuce widad din,wadda tabi bayanta da kallo,saita samu kanta itama da cillama bayan nata harara kafin ta maida dubanta ga qofar dakin uncle din nata,wanda a yanzu ya zama nasu shida hafsat din,wani zafi takeji a zuciyarta,tunda mommyn tazo komai ya sauya a tsakaninsu,a baya kullum suna manne da juna,amma yanzun ta shiga tsakaninsu,siririn tsaki taja data tuna uncle din nata yana dakin,tare suka kwana,kuma duk wani abu da yake mata itama mummyn yana mata kenan?,tana shaqar wannan daddadan qamshin nasa?,tana jin wannan lallausar fatar tasa?,yana bata wannan soft kiss din irin wanda yake bata?,sai taji ranta ya baci amma tayi saurin koren shaidan yadda anty madeena ta koya mata.

    A kitchen kuwa tsaki hafsat din tayita ja a jajjere,yau abbas din zai raba musu kwana da yarinyar?,saita zube cups din kawai ta fito tabar kitchen din.

    Wuceta ta sakeyi ta gefanta kamar zata gogeta,ko daga kai widad din batayi ta kalleta ba taci gaba da aikinta,ba jimawa aka turo qofar dakin,bata juya wajen ba,amma duk da haka lallausan qamshinsa ya gaya mata waye.

    Tsaye yake daga bakin qofar yana qare mata kallo cikin police uniform dinsa dake matuqar qara masa kyau da wani irin kwarji na musamman,hannayensa cikin aljihunsa fuskarsa ta wadata da murmushi,duk kuwa da cewa bata ma san da tsaiwarsa ba,tun tana basarwa hadi da qin kaon qofar har zuciyarta ta gaza,tana jin saukar idanunsa a dukka jikinta,yana kuma haifar mata da kasala sosai.

    A gajiye ta daga fararen manyan idanunta ta sauke masa,idanuwansu suka gauraye waje guda,sai shima ya gaza…..ya zaga da tsaiwa a nan ba tare daya iskota ba,ya fara takowa a hankali har yanzu ya kasa dauke idonsa daga kanta

    “Good morning babyn uncle” fuska tadan narke kadan ta karyar da wuya,kishi nason taso mata amma tana danneshi,uwa uba kuma ya mata wani irin kyau me taba zuciya

    “Morning uncle din baby” maganar tata ta sanya murmushi ya subuce daga labbansa,kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai hafsat din ta fito daga dakin,dauke da briefcase dinsa, idanuwanta a kansu har ta iso ta miqa masa jakar,ya karba yana gyara rufinta

    “Ina kwana?” Ta fada tana russuna masa cikin girmamawa

    “Lafiya lau baby,kin tashi lpy?”

    “Lafiya uncle” ta amsa masa a narke tana karyar da wuya,ya gyara jakar yana mata duban tsakiyar ido,yana jin kamar ya jawota ya rungume cikin jikinsa,shi wani mutum ne da muddin yana so ba kasafai yake iya boyeshi ba,ba soyayyar mutum ba,soyayyar komai ma

    “Ba wani matsala ko?” Kai ta gyada tana dan murmushi, idanunsa kawai sun wanke mata komai a ranta

    “To shikenan sai na dawo”

    “A dawo lafiya uncle,Allah ya tsare”

    “Ameen babyn uncle” tsaiwar mashi cak sunan ya yiwa hafsat a tsakiyar ranta,wanann zallar iskanci ne da wulaqanci,a gabanta suke irin wadan nan abubuwan?,sai kawai tayi fuuuu tayi gaba,hakan ya bashi damar qarasa sallamarsa a nutse ya fice yana qorafin tayi masa qauro,ai ba irin wannan sallamar suka saba yi,tana ta masa dariya hadi dace masa aiba ranar girkinta bane,yayita juya zancan cikin ransa,wato har ta fara rarrabewa da wani girkinta da ba girkinta ba,yadan daki sitiyarin motar kadan,shikam wannan tafiyar da hafsat ta tauyeshi da yawa.

    Aikinta taci gaba da yi,saidai sanda ta shiga kitchen ta gane hafsat ta jiqa mata aiki,komai a qazance,sak dai yadda ta saba barin sassanta na bauchi,saita zage ta shiga gyara haiqan,wanda tun batayi nisa ba taji cikinta ya wani cure kamar an sakar mata dutse,ta miqe tana dora hannunta saman cikin,tana mamakin wani dan tudu da take iya ji cikin nata yayi,idan ta kalli kanta cikin madubi kuma bata iya ganin komai,saita koma da baya ta huta kadan sanann ta qarasa.

    Duka abinda akeyi hafsat tana falo ta kasa ta tsare,wata irin dakiya ce ta zoma widad din,bata fasa aikace aikacenta ba kamar yadda bata bi ta kanta ba,da taga bata ko lura da zamanta ba saita fara zirya tana qananun maganganu daga kitchen din zuwa falo,burinta yarinyar ta tanka,ta samu ta likideta ta fake sa rashin kunya tayi mata.

    Tana jiyo su mimi daga falo suna nemanta ta daka musu tsawa ta zaunar dasu waje daya,saida suka fara kukan yunwar da suka farka da ita sannan ta wuto kitchen din daukar musu abinci,sannan harta gama kintsa kitchen din,tana adana kayan cefanen da tun randa suka dawo hafsat din ta karbi girki abbas din yayosu masu yawan gaske,amma haka nan hafsat din ta barsu,komai saidai ta farka ta diba yadda ranta yakeso ta barshi a wajen,hatta da kayan miyansu haka ta wurgasj fridge babu gyara.

    Zuciya tazoma hafsat din iya wuya,me yarinyar ke nufi,duk abinda ta fita a girki ta barshi ta sauya masa fasali daga yadda yake wai ita zata karba girki,har tazo fita ta dawo baya a zafafe

    “Ke nifa banason iyayin banza da wofi,duk kin kama abubuwa kin sauya musu waje kamar kinfi kowa iyawa?” Tana ware tomatoes din da suka lalace ta daga kai ta dubeta,ido tadan zuba mata ba tare da tace komai ba

    “Dake nake magana kika zuban ido,ba zaki zo gidana kice zaki isheni da kinibibi bafa” sai a sannan ta janye idanunta,qasa qasa tace

    “Gidanmu dai”

    “Qunquni kikemin?,me kika ce?” Ta tambayeta a zafafe

    “Gidanmu dai” ta amsa mata kai tsaye tana kallon qwayar idanunta.

    Wani abu ne ya saukar mata a kanta mai nauyi,mamaki yayi bala’in cikata,yanzu haka har tana da qwarin gwiwar maida mata magana haka kai tsaye?,lallai tayi sake,tayi kuma barci kwana biyu

    “Zaizo me daure miki gindin ya gaya min idan shine ya gaya miki gidan nan kema gidanki ne” sai tayi gaba widad ta rakata da ido tana tabe baki,sai kuma ta gwada yadda tayi maganar sannan ta saki dariya,ita abinda ke bata mamaki,mummy hafsat din babba da ita,amma kullum aikinta tsaiwa taja magana tsakaninta da ita,taja tsaki tana sake tabe baki taci gaba da aikinta.
    [06/05, 9:00 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 7

    A Rubuce Take Book 2 Page 7

    Part 02

    Page 07

    Wuni hafsat din tayi tana zirga zirga cikin gidan,bata falo bata kitchen,ita kuwa widad hakan bai hanata zagewa ta shiryama uncle abbas dinta abinci lafiyayye ba, hafsat din na zaune daga falo sanda qamshin ya fara mata sallama,ta baza qofofin hancinta, Zuciyarta na gaya mata ko daga babban sashen hajiya na gidan qamshin ke fitowa?,to amma data nutsu da kyau saita gane daga kitchen din gidansu ne,mamaki ya daskarar da ita a wajen,ta gaza daurewa ta nufi kitchen din kamar zata dauko wani abu.

    Qamshin da tayi arba dashi yafi na falon,ta gefan ido take kallon yadda yarinyar keta aikin girkinta komai da komai tsaf,kai bakace girki takeyi ba,zarcewa tayi da dauko ruwa zuciyarta na wani irin tsalle daga qirjinta saboda zallar kishi,ta dauka ruwan ta juyo ta fito,saita ajeshi kawai gefanta ranta yana baci.

    Tako ina yarinyar ta bata mata tsari,komai na yarinyar canzawa yakeyi ko tace tama canza totally,komai nata a yanzun na cikakkun matan aure ne,yaushe ta iya girki mai bada matsiyacin qamshi haka?,cikin wadanne watannin ne da bata banbancesu ba?.

    Tana tsaka da wannan nunqufurcin da tunanin harta gama komai ta kuma fito daga kitchen din zuwa dakinta,a nan yaran suka ganta,suka ruga da saurinsu suka bita dakinta,a sannan bata da kuzarin hanawa,don tayi nisa cikin tunani da lalubowa kanta mafita.

    Sosai yaran suka sake suna wasansu a dakin nata,ta fidda chocolates ta basu ta shiga wanka,ta fito tana baza qamshin shower gel dinta mai taushin qamshi,ta tsaya gaban madubi ta soma gyara kanta.

    Tunda wuri yake qoqarin yaga ya kammala duka aikinsa ya dawo gida,duk wani motsi da zaiyi tana maqale cikin ransa,haka yayita kokawa da ayyuka don ya samu dawowa gida da wuri ya kasance da ita,amma hakan bai yiwu ba,sai yamma liqis sannan ya samu ya ture wasu ayyukan ya fito.

    Sai daya tsaya ya siya dukka nau’in fruits din da yasan tana so,ha hadama yaran da kayan kwadayi sannan ya dauki hanyar gida,cikin ransa yana jin wani zallar nishadi da farinciki,wata walwala da baisan tushenta ba ita ke wanzuwa saman fuskarsa,lokaci lokaci yakan saki murmushi idan ta fado masa a rai,a haka har ya cimma gida,yadan dannan hon mai gadi ya dage masa qofar.

    Sautin hon din motarsa daban yake a kunnuwan widad,ta lumshe ido dai dai sanda ta gama shirya kanta tana duban kanta da kanta cikin madubi

    “Ga daddy nan fa ya dawo” tace da yaran tana dan dubansu,wani shauqi da qaguwar riskarsa tana ratsata,sai takejin kamar tayi shekara ne bata rab’i uncle din nata ba

    “Yau sai na riga kowa zuwa taro daddy” mimi ta fada tana tattare kayanta,murmushi widad ta saki

    “Zamuga waye zai riga wani” sai ta dauki turare ta sake feshe jikinta,sannan ta nufi qofa da sauri tana yiwa mimi gwalo,wannan ya sanyata zubda kayan ta miqe tana qyalqyala dariya

    “Allah anty saina rigaki” ganin yarinyar ta biyota sai ta dan saka sassarfa tana mata dariya tayo gaba mimi din ta rufo mata baya.

    Dai dai sannan hafsat da taji muryarsa daga waje suna gaisawa da ma’aikatan gidan ta fito falon,daga kujerar dake daura da bakin qofa ta zauna,ta yadda idan ga shigo idanuwanta zasu iya gane mata komai,uwa uba ma tasan babu wanda ya isa ya keta idanunta ya tsallaketa ya isa gareshi,ta baza dukka idanunta tana qarewa gyaran da aka yiwa falon zuciyarta kamar ta fito,lallai ba shakka sai taci uban yarinyar,sai tayi maganin dukka wannan kinibibin nata,taja qwafa tana karkada qafafunta.

    Yana doso part din ransa yana sake yin fari,tun bai isa falon ba ya tabbatar ya koma saitinsa yadda yakeso,qamshi mai sanyi ke hudowa ta tsakanin labule da qofar yana fitowa har harabar gidan,ya buda qofar falon a nutse bakinsa dauke da sallama,hafsat din ta miqe tana dan sakin murmushi tare da amsa masa sallamar.

    Taku biyu tayi zuwa gaba da niyyar amsar jakar hannunsa muryar widad hade data mimi ta karade falon.

    Hankalinsa da nata gaba daya ya koma kansu,sanda suke rige rigen tarbarsa kowa yanason ya fara isa a tsakaninsu.

    Sosai ta fusgi hankalinsa ta kuma tafi da dukkan nutsuwarsa,yadda take tahowa da sassarfa yaji ya masa kadan,ya fara takawa shima ha ruskesu,cikin sa’a ta riga mimi isa,ya bude hannunsa ta fada jikinsa tana fadi cikin dariya

    “Oyoyo daddyn mimi” sosai yake kallon fuskarta da narkakkun idanunsa dake kanta,yasa hannu ya daga fuskar tata yana murmushi wanda yafi kama da dariyar farinciki

    “Kinwa ‘yarki wayo ko?”

    “Dama na gaya mata,sai na rigata” saita jefawa mimi gwalo,yarinyar ta tabe baki kamar zata saki kuka,sai widad din ta miqa mata hannu tana sakin dariya

    “Taho…..taho mimin dadd……” Sautin kuka shi ya maida hankalinsu duka ga hafsat,duk sai sukayi sak suna dubanta,har ga Allah abbas din ya manta da wanzuwarta a wajen gaba daya,widad tasan tana gurin amma batajin zata iya fasa abinda ta saba yiwa uncle din nata,uwa uba kuma dazu da taji yana cika baki da tinqaho akan uncle din,abun ya bata haushi amma saita qyale kawai,tana ji a ranta zuwa yanzu ko meye mommy hafsat din tayi mata ta daina qyaleta.

    Kuka sosai takeyi,kafin abbas ya samu damar cewa wani abu ta juya da sauri ta nufi dakinta,batason yarinyar taga hawaye har haka a fuskarta saboda gudun raini.

    Bayan wucewarta sai suka koma kallon kallon a tsakanin,a nutse ya zare widad daga jikinsa yana cewa

    “Ina zuwa” yabi bayan hafsat din,tabe baki widad tayi ta dauki.jakarsa daya aje a wajen suka wuce dakinta ita da mimi,yarinyar nata murnar tare daddy ya tarbesu,saidai sama sama widad din ke amsawa,don dukka hankalinta nakan abbas din.

    A nutse ya tura qofar dakin ya shiga,tana daga zaune bakin gadonta tana sharar qwalla,ya taka ya isa gabanta ya tsaya kawai kallonta hannayensa goye a qirjinsa

    “Me akayi miki?” Ya jefa mata tambayar data sakata dago kai idanu jiqe da qwalla ta dubeshi,wani baqinciki ya tokare mata wuya,wato baisan me yayi ba?

    “Bakasan me kayimin ba abban mimi?,ko yaushe baka da burin da ya wuce ka wulaqantani ka tozartani a gaban yarinyar nan,nice na fara welcoming dinka,amma tana fitowa ka kasa tarata ka koma kanta saboda tsabar cin fuska” iska ya furzar daga bakinsa yana gyara tsaiwarsa

    “Yanzu wannan shine abinda yakai ayi masa kuka?” Shuru tayi bata amsa ba tana ci gaba da goge qwalla,baisan yadda takeji ba a yanzun,da bai tsaya kanta yana magana fada fada ba

    “Dole sai kinyi haquri kin dauke kai,akwai banbancin shekaru a tsakaninku, infact ma ta riga ta saba ita kadai take rayuwa a gidan nan,wasu abubuwan sai a hankali zata dainasu” saiya fara takawa zai fita a dakin,ta bishi da kallon takaici,bataso ya shigo dakin ya fita haka da sauri,tana so ko yaya ne ta bata masa lokaci yadda zata dasa zargi a zuciyar yarinyar,tunda ta lura zuwa yanzu zaman kishi sosai takeso suyi,ta wuce wancan lokacin da zata dinga juya ta da raina mata wayo yadda taso.

    Sunansa ta sake kira,cike da qosawa ya tsaya ya waiwayo,saita taso ta iso gabansa ta fada jikinsa ta fashe da kuka sosai,ba yadda ya iya haka yasa hannu ya tallafeta,rigimar hafsat din tayi yawa,matsaloli kala kala marasa tushe balle makama,qanqanin abu saita hurashi ya zama babba,har yau ta kasa gane girmanta balle ta riqeshi.

    “Bansan me yasa kakemin haka ba,bakasan yadda nakeji a zuciyata ba” ta fada cikin kuka,tilas ya bata lokaci yana lallashinta tare da nusashe da ita cikin hikima,saidai abinda bai sani ba,duk abinda yake fada tana bi ta bayan kunnenta ne,burinta kawai ya jima a dakin.

    Ta samu yadda takeso kuwa,don ya jima yana jan hankalinta kafin ya baro dakin bayan ya umarceta data sake gyara dakin, saboda tuni ya fara fita daga kamanninsa a kwanki uku kacal,baya jin kuma zai jura,ba kamar bauchi bane,a yanzun bashi da wani dakin daban da zaice zai kebance a cikinsa.

    Bacci ya dauke mimi sai widad dake zaune gefan gadon,ta cika tayi fam,bata taba jin bacin rai irin wannan ba,shi yasa sam ko ganin mummy hafsat din batasonyi,tana jin wani zafi a zuciyarta duk sanda ta fahimci ko taga sun kebe,koda yayi sallama saita zumbura baki ta miqe ta nufi toilet kawai tana amsa masa ba tare daya tsaya a nan ba,qaramin murmushi ya saki bayan ya kalli agogo,sai a sannan ya fuskanci laifinsa,ya qarasa bakin gadon ya duqa ya dauki mimi ya maidata wajen hafsat sannan ya dawo dakin,ya jingina da mirror yana jiran fitowarta.

    Kamar bata ganshi ba sanda ta fito daga bandakin,ya bita da kallo yana sake tantance kyan da tayi,wani abu na motsa masa a ransa game da ita,a strong desire,idanunsa na zagawa bisa jikinta,bomshort din jikinta yayi masifar fidda shape na qugunta,kaman ana fusgarsa haka yaji,ya isa gareta cikin sassarfa ya jawota jikinsa.

    Abun yazo mata a bazata,wanann ya haifar da motsi a cikinta,abinda yayi matuqar firgitata tunda bata bata taba ji ba,a zabure ta saki ihu da ya sanya abbas riqeta da kyau yana lalubar abinda ya faru,hafsat kuma dake maqale a bakin qofa tana jiran jin taqaddamar da zata faru a tsakaninsu sanadin dadewarsa a dakinta ta sake gyara tsaiwarta da kyau,dadi yana cikata da jin ihun widad din,may be ta masa wani rashin kunyar ne yaji bazai iya jurewa ‘yar cikinsa tayi masa haka ba ya kaiwa bakinta bugu.

    “calm down…..menene?” Kasa amsa masa tayi sai hawaye da ya fara bin idanunta,ta kama hannunsa ta dora saman cikinta,dai dai sanda motsin ya ratsa tafin hannunsa ya aika saqo kwanyarsa,sai kuma ya tsaya cak.

    Sosai ya shiga mamaki da tunani,ya dubeta cikin mamaki

    “Yaushe ya fara irin wannan motsin?”

    “Bai taba yi ba sai yau” ta fada tana sharbe hawaye,qaramin murmushi ya saki,saita saki baki tana kallonsa

    “Karki damu,zan kira dr yanzu nayi mata bayani,zauna a nan ki nutsu,don’t bother”.

    A nutse ya zaunar da ita sannan ya lalubi wayarsa ya fara neman number din dr maryam,daya daga cikin personal doctor dinsa.
    [07/05, 1:36 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 10

    A Rubuce Take Book 2 Page 10

    Part 02

    Page 10

    Kamar ta bawa mimi kudin ta maida mata,sai taga kada tayi asara,ta bata kudin kuma tazo batayi musu girkin ba,don haka sai ta ajjiye kudin tanata qananun mitoci.

    Tun tana saka ran ganin widad din ta shigo sashen har ta fidda rai,don yamma ta riga tayi,ga yunwa suna ji ita da yaran,dole ta shiga kitchen ta dora dafa dukan shinkafa.

    Tana kitchen din tana fama ga magrib ya kawo jiki widad ta dawo,dakinta ta wuce kai tsaye,bata bi ta kan jagulallen parlor din nasu ba,tana mamakin yadda suke iya hargitsa guri har haka suci gaba da zama a cikinsu abinsu hankali kwance.

    Ta taho da sauran faten tsakin daxu,da zafinsa don a wani warmer mai kyau da hajiya ta bawa maari yake a ajjiye,saita hada ruwa me zafi ta cire kayanta ta shiga toilet tayi wanka ta gasa jikinta sosai,ta dawo ta zura wata armless riga da iya tsahonta gwiwa,ta wadata jikinta da turare,ta sake jona humidifier sannan ta dawo tana laluben hijabin da zatayi sallar dashi wanda zai saukar mata har qasa.

    Sosai yau ya hado yunwa da kuma gajiya a jikinsa,ya tabbatar zai samu dukkan wani hutu da kulawa hadi da kwanciyar hankali daga gurinta,wannan yasa ya hada dukkan yunwarsa ta yinin ranar,bai wani tsaya yaci cikakken abinci ba,don yasan zai tarar da irin taste din da yake muradi,har fiye ma da yadda yakeso.

    Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya kashe motar tasa,ya waiwaya baya ya dauko ledar fruit din da ya siyo da chocolate nasu mimi ya fito,ya kashe motar sannan ya nufi cikin gidan.

    Tun kafin ya qaraso ya fara buda hancinsa yana tsammatar samuwa sassanyan qamshin nan dake masa maraba a duk sanda girkinta ya shiga,saidai babu shi ba alamarsa,duk da haka yaci gaba da takawa cikin hope da kuma karsashi.

    Sosai mamaki ya cikashi sanda ya yaye labulen falon ya sameshi a tarwatse,komai yana zaune zaman kansa,sai su mimi dake ta hada hada da kayan ciye ciye na leda irin wanda yake siyowa ya jibge musu,ko ina tarkacen kayan ledojin da tsinken sweet ne,dukansu suka watsar da abinda yake hannunsu suka nufoshi suna rige rigen qarasowa,ya tsugunna ya tarbesu gaba daya.

    Miqewa yayi yana dauke da nawwara mimi na hannunsa,yaji motsi a kitchen,don haka zuciyarsa ta bashi widad ce,sai ya wuce kitchen din dasu kanshi tsaye yana amsa tarin tambayoyinsu da suketa damunshi dasu.

    Tun bai gama shiga kitchen din ba idanu da hancinsa suka gaya masa ba widad bace,hafsat ce sanye da doguwar rigar wani material ruwan qwaiduwar qwai,sulbinsa ya sanya dinkin da aka masa a wasu sassan ya zazzame yayi zare zare,tana goye da yusra daketa mutsu mutsun son a sauko da ita,ya qarasa yana amsar yarinyar,ta sauke masa ita tana masa sannu da zuwa muryar a cunkushe.

    “Ina antyn nasu?”

    “Tana dakinta mana” hafsat ta amsa adan fusace tana juya dafadukan data fara kamawa

    “Lafiyarta qalau?” Juyowa tayi kamar ta banka masa harara,amma kwarjinin nashi idanuwan sun shallake nata

    “Aiba wannan ya kamata ka fara tambaya ba,kamata yayi ace ka tambayi wanda ya bamu abinci wunin yau,ta shige daki saboda ta samu daurin gindi tayi kwanciyar ta wuni guda ta barmu da yunwa ni da yara” sam hankalinsa bashi akan maganarta, zuciyarsa da tunaninsa sun karkata kan sanin lafiyarta da abinda ya hanata fitowa wunin yau,sai ya juya yana sabe da yusra ya fice a kitchen din.

    Ana fara knocking ta gane shine,ta riga ta saba da komai nasa,hatta takun takalminsa ya banbanta dana kowa,tana kuma iya banbancewa,ranta yadan quntata,itakam ko son ganinsa batason yi,space take da buqata, batason takura,to amma batason tayi wani abu na rashin girmamawa a gareshi gaban yaransa,dole ta ajjiye qaramar hular da take qoqarin sanyawa sassalkar sumarta daketa sheqi saboda yadda tayi oiling dinta da mai,tana tura baki da shagwababbiyar fuskarta ta isa qofar ta bude masa,sai taja ta tsaya daga bakin qofar,kamar wadda aka zo gayawa saqo take jira a gama gaya mata a fita ta kulle qofarta.

    Tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa wani abu ya tsarga masa,yadda batasaka brassiere ba amma hakan bai hana na shanunta tsaiwa kyam suna nuna kansu ba,lafiyayyun cinyoyinta sun fita sosai ta cikin tsingilalliyar rigar,yadda ta turo bakinta gaba kuma ya qarasa kunnashi,soft pink lips dinta daketa sheqin lip gloss,sai yaji kamar ya jata cikin jikinsa ya kama bakin ya tsotse,amma yusra na kafadarsa,tilas ya daure,ya qarasa gefan gadon ya zauna ya dora yarinyar saman cinyarsa

    “Sannu da zuwa” shuru ya ratsa maimakon ya amsa mata,ya tsareta da ido yana jin yadda kallonta kawai yake saukar masa da kasala

    “Banda na shigo na nemeki bakisan ma na dawo ba kenan?”

    “To me zanzo nayi maka?,bayan maganar matarka kawai kake ji” ta fadi haka cikin ranta,amma a fili saita sake tura baki gaba tana yamutsa girarta hadi da sarqafe yatsunta waje daya tana ballaqasu

    “Zonan” ya fada a tausashe yana nuna mata kujerar madubin dake gabansa,ta kalli wajen sannan ta kalleshi,ko yaushe girma da kimarsa ke sakata ta kasa masa musu ko wasu dabi’u da basu kamata ba,ta sauke hannuwanta ta dawo inda ya nuna matan ta zauna,wannan karon idanunta cikin nasa tanason jin abinda zai gaya mata kuma.

    Rage kaifin nasa idanun yayi kadan daga kanta sannan ya magantu

    “Ya akayi gidan ya zamana yau duk a hargitse,infact ma yau girkinki ne amma baki fito kwata kwata ba,ko yanzun ma antynki ce cikin kitchen din” wani haushi ya kamata,aiki?…..a nan tafi kauri kenan, idanunta ta lumshe kadan tana daukesu daga kansa,abinda ya sake fusgarsa da wani madaukakin shauqi zuwa gareta,duk da ba tayi bane don ta burgeshi ko kuma da wata manufa

    “Gida a hargitse?,ina cewa mummyn mimi tana cikin gidan,amfanin zaman mutum biyu kenan,idan dayan ya gaza ko ya gajiya sai dayan ya tallafa masa…….girki kuma ni na daina girki,na bar mata komai da komai harda kwanana” mamakin widad din sosai ya kamshi,yadda tayi maganar ya tabbatar da gamewar hankali a jikinta,don tana maganar ne with seriousness in her sound,baibi takan maganarta ta farko ba,maganarta ta qarshe tafi fusgar hankalinsa tare da tabashi,don abune da bayajin ko sama da qasa zata hadu zai amince da hakan

    “Kin daina girki?,meye dalili?,da kuma izinin wa kika dauki wannan matakin?” Sake tura bakinta gaba tayi sosai tana hade fuska,ta kuma kaucewa dubansa

    “Saboda gidan da mijin duka nata ne,so komai da yake cikin gidan yafi cancanta ya zama nata” sai yanzu ya sake gano inda ta dosa,can qasan ransa murmushi ya kubce masa,kishi take da gaske…..ta kuma ji haushin abinda yayi mata kenan fiye da yadda ma shi ya zata,amma bayason ta dore da haka don haka ya miqe yana dora yusra a kafadarsa

    “Ki shirya komai kamar yadda kika saba,banason dawo da zance,abinda ya wuce ya wuce” sai ya taka yana ficewa a dakin.

    Sam maganarsa bata bawa zuciyarta sassauci ba,saima tunzurata da yayi,bazai iya daukan mataki ba kenan kwata kwata?,indai haka ne itama bataga dalilin da zai sanyata saukowa ba,don haka yana fita sallar magariba ta sakawa dakinta key tayi sallarta ta jirayi isha’i ta bada ita sannan ta haye gado ta nutse cikin duvet hankali kwance.

    Sai daya dawo daga masallaci sannan ya zarce dakinta don ya samu ruwan nan nata me wani irin dumi da qamshi don yayi wanka,ruwan da ita kadai tasan yadda take hada masa shi,don koshi ya hada da kansa baya jin dadinsa kamar haka.

    A nutse ya tsaya yana knocking a bakin qofar,tana jinsa ta share,saita saka earpiece ma a kunnenta,don haka batasan adadin awannin ko mintunan da ya dauka yana bugun ba.

    Sosai ransa ya quntata,don yadda yayi tsaye yana bugun har mimi taji ta fito ya tabbatar tana jinsa,ya kirayi sunanta kusan biyar shuru,dole ya juya dakinsa dakin kuma hafsat,tana zaune a qasa ta tara kayan qazantar yusra tana waresu,ya wuce gaban cupboard dinsa yana rage kayan jikinsa.

    Binsa tayi da kallo ta tabe baki,ita da zasu tabbata a haka sai tafi kowa farinciki,duk bugun akan kunnenta akayishi,tana sane tayi bakam

    “Ba kwananta bane?,ya na ganka a nan dakin?” Ta jefa masa tambayar da tasan amsarta.

    “Na sani,hadamin ruwa zanyi wanka” ya fada muryarsa da wani irin laushi daya bata mata rai,komai na yarinyar tabashi yakeyi,saka masa damuwa yakeyi,duk qoqarinta na kau da hankalinsa amma baya wani tasiri yadda take da buqata,ita sau nawa suna irin wannan sabanin,amma ko a fuska bata taba gani yayi laushi irin haka ba,komai dadewar da zasuyi,sai yanzu akan qaramar yarinya kwana uku kacal amma duka ya canza?.

    Da tunani iri daban daban ya shiga wankan,sam ruwan baiyi masa ba,hasalima ya cika zafi da yawa,yaja tsaki ya saki famfo akai,sai kuma yaso salance masa,ya sake jan wani tsakin yana komawa cikin bathtub din ransa duka a jagule.

    Koda sukazo cin abinci ma yasa mimi ta bubbuga mata,duk da yadda hafsat ke faman hada rai tana ganin ya girkinta ne batayi ba ita ta zauna tayi kuma saboda gata wai a kirata taci,itama mimin haka ta qaraci bugunta ta haqura ta dawo jiki a sanyaye

    “Bata bude ba” sai ya shafa kanta

    “Inajin tayi bacci” a yadda yake jinsa koda lafiyayyen girki hafsat din tayi abincin bazai masa dadi a baki ba,bare tafashi kadan hafsat din wadda ta cuccure waje daya,kamar gidan da aka yiwa gorin man girki,bayan komai a wadace yake a store dinsu,zuciyar tata ce dai haka.

    Da qyar yayi loma hudu ya ture abincin,ya maida hankalinsa ga news da ake haskowa a channel din al_hadath,duk da a badini fiye da rabin hankalinsa yana kan qofar dakinta,duk bayan mintuna biyu saiya kalli qofar dakin,amma ko motsinta daga ciki baiji ba bare ya sanya ran zata bude ta fito.

    Har yaran sukayi bacci hafsat ta debesu takai daki ta dawo tayi masa sallama yana zaune a wajen,sanda sha daya na dare ta buga sai ya tashi yana sake gwada bugun,a lokacin tuni tayi bacci,bugunsa ne ya tasheta,ta sauko a hankali ta wuce toilet abinta,tayi fitsari ta sake alwala ta dawo ta kuma kwanciyarta.

    Wannan karon yaji motsinta shigarta bandaki zuwa fitarta,hakan ya nuna masa tana jinsa,bata kuma da niyyar bude masa,ya koma da baya ransa yana baci,ya juya yana nufar dakinsa.

    Dadi ya kama hafsat dake labe,saita koma bakin gado ta zauna tana kada qafa a hankali,itakam gaba ta kaita,dole yau ya kwana dakinta,sannu a hankali dai gida yana shirin dawowa hannunta sai yadda ta juyashi, murmushin nasara da farinciki ya kubce mata.
    [09/05, 4:06 pm] +234 816 283 5575: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 16

    A Rubuce Take Book 2 Page 16

    Part 02

    Page 16

    “Subhanallahi, garin yaya?” Bayan ya iso yana duba kayan,komai ya tarwatse ya hade waje daya,saita duqa da hanzari jikinta yana dan rawa tanason boye hadiye tashin hankalinta,ya duqa shima yana tayata tattare wajen sannan yace

    “Qanwarki ta haihu……” Ya fada yana tattare wajen ba tare daya ko kula da yanayin da fuskarta take ciki ba

    “Ta samu d’a namiji ba……abinda ni hafsat na gagara baka har kaje ka qara aure don ka sameshi,burinka ya cika” ta fada da wata irin shaqaqqiyar murya sai kuma ta saki tarkacen data fara kwashewa ta wuce daki tana sakin boyayyen kuka mai bala’in cin rai,komai ya qarasa lalacewa kenan,yaushe akayi cikin?,yaushe harya girma?,sannan data tashi haihuwa ma ba mace ba?,namiji?,saita quma kanta da bangon dakin wanda har tsakiyar kanta taji zafin buguwar da tayin,amma radadi da zafin dake cikin zuciyarta ya zarta wanda taji.

    Da kallo ya bita sanda take wucewa dakin,mamakinta yana kasheshi,banda yasan bata da aljanu da tabbas wasu lokutta sai yaga ruqiyya ce tafi dacewa da ita,yanzun a batun haihuwar widad din meye abun daga hankali?,harda qirqirar batun d’a namiji da ‘ya mace?,bashi karan kansa ba,ko a cikin danginsa ba wanda ya taba zancan mata take haifa,hakanan tsahon zamansu bai taba kawo wannan tunanin a ransa ba banda yanzu data furta,don shi a wajensa d’a duka d’a ne,yadda ake haifar namiji haka ma mace,sai wanda Allah ya sanya yafi wani albarka kawai.

    Yadda yaran sukayi carko carko suna kallonsa yasa bayan ya gama sharar wajen ya wuce dakin nata bayan ya zaunar dasu a falon,kuka ya sameta tanayi sosai hadi da safa da marwa,ta kasa zama waje daya,ya isa tsakiyar dakin a nutse hannayensa zube a aljihun wandonsa yana kallonta

    “Hafsat,ki nutsu mana,duka wannan abun na meye?” Sosai tayi qoqarin saita kanta, batason ya karanci yaron da aka haifa takejin buri da muradin mutuwarsa yana ratsata

    “Na nutsu fa kace,wai meye ka maidani abbas?, yarinyar tayi ciki harta haihu ban sani ba sai ranar data haihu din?” Mamaki ya sake kamashi,lallai idan mutum bashi da abun fada to fada yakeyi da kowa ma

    “To naji,amma relax please,kin saka yara duka hankalinsu ya tashi,yanzun dai tunda ta haihu ai ya wuce ko?,sai kiyi haquri” ya rufe da bata haquri duk don bayason tashin hankali.

    Kuka ta sake fashewa dashi ganin wani lafiyayyar nutsuwa da walwala shinfide saman fuskarsa

    “Ko yaushe cutata kake abbas,ko yaushe zaluntata kakeyi” abinda ta fada kenan,kalmomi biyun da ya tsana kenan a rayuwarsa,ko zai yarda da komai amma bazai dauki kalmar cuta ko zalunci ba akan wani,babban dalilin da yasa yake da abokan adawa sosai akan aikinsa, don baya yarda a zalunci kowa,mai gaskiya ne kai ko mai laifi,kowa sai an tabbatar masa da hakkinsa.

    Ganin yadda ta birkice ba bisa gaskiyarta ba sai kawai ya juya ya fice daga dakin ba tare daya sake bi ta kanta ba,ta sake tunzura ainun sanda tashin motarsa,data leqa falon ba kowa duka ya tattara yaran ya fice dasu banda yusra da tayi bacci ya kwantar mata da ita saman couch ya tareta da pillow don kada ta fado,saita sake rushewa da kuka,a fili tana cewa

    “Widad ta haihu?,kuma d’a namiji?” Ta fadi hakan ya kusa sau biyar,tanason idan wai mummunan mafarki takeyi Allah ya taimaketa ta farka,saidai still sake samun tabbacin cewa idanu biyu take tayi,musamman da taji muryar sagir dan yayansa daya dauko yake zaune a gidan,saboda samun security na gidan idan suna kaduna.

    Yana tuqi a hanya amma tunani barkatai yana zuwan masa,lamarin hafsat ya fara sakashi a kokwanto,ko a labari bai taba ganin mace mai baqin kishi irinta ba,ya maida dubansa gasu mimi dake ci gaba da murnarsu ta samun dan uwa,wanda a gidan basu samu sukuni ba saboda gargadin da hafsat din tayi mata,yaran fici fici dasu,ko wanka babu amma haka ya daukosu saboda yasan idan ya barsu a gidanma akansu zata huce idan ba’a yi wasa ba.

    Yana tsaida motarsa gaban gidan hajiya ya bude yace su shige ciki,da gudunsu kuwa suka fella,ya dauke idanunsa daga kansu yana murmushi bayan sun shige din,wayarsa ya ciro ya sake trying number widad amma taqi shiga, shikam bayajin yau zai iya kwana bai sanyata cikin idanunsa ba,don haka ya shiga kiran number din suraj karo na biyu

    “Yaya dai angon qarni”

    “Don Allah idan ba wani muhimmin uzuri gareka ba,ka ajjiye komai kazo kayimin rakiya kano”

    “Da zafi zafi haka?”

    “Kaima kasan bazan iya jurewa ba” ya amsa masa yana murmushi

    “Bani nan da awa daya”

    “Godiya mai kima” ya fada yana jin dadi,suraj din aboki ne na gari dake tsaya masa cikin kowanne irin yanayi.

    Suna gama wayar mimi ta fito da gudu tana kiransa

    “Wai ka shigo inji hajiya”

    “Gani nan mimin daddy” ya fada yana dariya hadi da kashe motar,ya fito suka jera zuwa cikin gidan tana riqe da hannunsa tana gaya masa zasuyi party dasu nawwara da qawayenta

    “An gama mimi na” ya bata amsa yana murmushi hadi da shafa kanta.

    Da waya a hannu ya samu hajiya,ya tsugunna yana sake gaidata duk da sun gaisa dazu ta waya.

    A nutse ta amsa masa tana kallonsa,cikin muryar nan dak cike da dattijantaka tace

    “Wai meye yake faruwa a gidanka Abbas?” Tayi maganar cikin qosawa,sai ta kasa jira yace komai ma

    “Me dame kake boyewa matarka” sosai ya dubi hajiyan,yasan kwanan zancen

    “Hafsat ce ta kawo qara ta hajiya?” Ya tambayeta a sanyaye,saita gyada masa kai,tana jin tausayinsa yana kama ta,ya hadiye wani abu mai tauri sannan yace

    “Wai na boye mata cikin widad,ni kaina ban dauka lokacin haihuwar yayi ba,saboda duka scanning dinta da awon da ake mata bata cemin komai” yayi maganar da sound na damuwa da takaicin dabi’ar hafsa.

    Zama hajiyan tayi a gefansa sabanin dazu da take zaune,sannan ta fara masa magana da harshe irin na uwa,tana tausarsa da kalamai masu kwantar da hankali da suka sanya jikinsa mugun sanyi,saboda yadda hajiyan ke masa magana kamar wadda ke bashi wasiyya ne

    “Kaci gaba da haquri,ibada kakeyi,kuma nasan tabbas Allah bazai taba wofantar da kai ba,bazai kuma tauye maka ladanka ba,wataran sai labari,kuma wadan nan abubuwan da dukka nake gaya maka ko bayan raina zaka tuna,nidai abu daya da nake godewa Allah,widad da Allah ya baka,ko babu ni nasan zata kula dakai….in sha Allah”

    “Hajiya ki daina fadin bayan ran nan don Allah” ya fada yana son katse zancan,sai tayi murmushi kawai

    “Bara’atu harta kirani tayimin zancan zuwa kano”

    “Eh nan da awa daya zamu tafi ni da suraj in sha Allah,su kuma ina ganin saisu bari ko bayan kwana biyar ne ko shida ko ranar suna”

    “Ba laifi hakan yayi,Allah ya tsare”

    Kaye kaye ta masu uban yawa hajiya ta hadama widad din,a yau tana jin zuciya da ruhinta fes,tana sake godewa Allah da ya bata iko tayi wannan hadin,ko ba komai abbas din ya samu wani sassaucin rayuwar gidansa ta wani gefen.

    Sun dauki hanyar kano a lafiyayyar motar abbas din,daga shi sai suraj,wanda suraj ke tuqin,hira sukeyi sosai a junansu,wanda kusan fiye da rabin zancan na widad ne, zaiyiwu wuya kawo yanzu muddin akwai shaquwa da aminci irin wanda yake tsakaninsa da suraj kuyi dogon zama baiyi maka maganar widad ba

    “Ka godewa Allah daya baka wani bangere da zaka dinga samun sassauci,amma koni.ina ganin qoqarinka,tabbas inda nine keda hafsat,da tuni na jima da qara mata mai” murmushi abbas yayi sannan ya miqe ya zauna sosai,ba daga bakun suraj kadai.yake jin wannan maganar ba,sai ya dan dubeshi kadan sannan ya maida dubansa ga titi

    “Saki ba shine hanyar maslaha kadai ba,bai kamata saki ya zama wani abu mai sauqi ga kowanne magidanci ba,idan hakan kuwa ta kasance al’ummarmu zata zama bata da wata makoma,tunda kowacce al’umma gidan aure shine tushenta,tunda daga can ake samar da nau’i na dan adam,nagartacce ko gurbatacce,wanda daga baya shi zai fito ya zama madubi na al’umma,imma malami jagora ko shugaba,mun ruguxa gidajen aurenmu da aure aure da sake sake,me muke tunanin zamu tsinta a gobemmu?,idan kayi qoqarin gyara ko canza matarka hakan bata samu ba,ba saki bane kawai hanyar da zaka samu gyara,infact idan ma bakayi wasa ba,sai ya bude qofar wata barnar,wani lokaci ya kamata mu dinga duba da wasu abubuwa kafin afkuwar saki,kamar makomar yaranmu,da wanne ido zamuyi musu bayani sanda suka budi idanu sukaga babu iyayensu a tare dasu?,wanne alkhairi matar nan ta taba yi maka a rayuwarta komai qanqnatarsa?” Kai suraj yake jinjinawa,ya jima baiga mutum kamar abbas dinsa ba,ko yaushe yana gayawa kansa da kansa abbas din na dabanne,samun irinsa sai an tona,inda hafsat zata gane waye take aure,lallai ba shakka zata fahimci a duniya tana cikin mata masu sa’ar da ba kowa ke samunta ba.

    Misalai kala kala yaci gaba da bashi,wadanda suka fahimtar da suraj abbas ya fishi gaskiya da kuma hangen nesa,saidai a halittarsa bazai fa iya daukan abinda shi yake dauka ba.

    Wayarsa da tayi qara ita ta katse zancan,ya daukota daga inda ya zurata yana duban me kiran, al’ameen ne abokin aikinsa,sai ya daga wayar ya kara a kunnensa tare da sallama

    “Oga…….kasan an saki signal kuwa?” Abinda ya fara cewa dashi kenan bayan sun gama gaisawa

    “Ah…..haba,yaushe?”

    “Jiya cikin dare,ban kwanta ba sai dana duba list,saiga sunanka a farko farko,You have been promoted to DSP…..congratulations” sosai labarin ya tabashi,saboda baisan ma abinda ke faruwa ba banda al’ameen din ya gaya masa yanzun.

    Hajiya ya fara kira ya gaya mata,tayi masa addu’a sosai cikin zallar farinciki da fatan ci gaba da samun nasara,widad itace tazo ata biyu,don a yanzun a duniya bayan hajiya widad itace number two dinsa,ya gaza haquri har sai ya isa,tayi amsa addu’a sosai data burgeshi, shigen addu’ar da hajiya tayi masa,sai yaji zuciyarsa tana qara sanyi tare da samun nutsuwa a ransa.

    “Lallai muhammad yazo da alkhairi da albarka” suraj ya fada yana murmushi,kai abbas ya jijjiga sosai,yana tuna sanda ya samu promotion sanda maganar aurensa da widad din ta taso,haka Allah yake al’amarinsa,yana tsara komai bisa yadda yakeso ya kasance.

    Daga sanar masa haihuwar zuwa isarsu kano duka duka ba’a cika awanni uku ba, lokacin da sukayi ido biyu da widad din sai yaji gaba daya duniyarsa ta dawo sabuwa,tausayi girma da kimarta suna sake ratsashi,ya sanya hannu biyu ya karba yaron idanuwansa suna qishirwar ganinsa.

    Wata irin qauna da soyayyar yaron mai qarfi ta saukar masa sanda idanunsa suka sauka akan fuskar da marabarta da tashi shekaru ne kawai

    “Subhanaka rabbi…..maa a’azama sha’anik, Hasbunallahu wani’imal wakil” ya fadi zuciyarsa na bugawa da soyayyar yaron,ya daga kai yana duban widad da wani irin narkakken murmushi

    “Yau wannan babyn ta zama uwa…….wannan babyn ta zama maama,babyn uncle ta zama maman baby” kunya sosai ta kamata,ta kama hannunsa ta kifa fuskarta a ciki tana dariya qasa qasa.

    Tamkar abbas bazai bar gidan ba,yana jin kamar yayita zama yana kallon yaron nasa dama widad din gaba daya,saidai abisa tilas yayi musu sallama saboda tafiyarsa sokoto da dole ta koma washegari.

    Bai bar garin kano ba sai da ya tabbatar hatta da magi da widad zatayi amfani dashi ya tanadar mata,duk da cewa bata rasa komai ba a gidan,ga jibge mata komai na amfani,banda kayan sawa na barka nata dana baby wadanda musamman ya sake sabuwar siyayya banda wadda sukayi a saudiyya,wanda kowa ya gani sai ya shaida irin soyayya qauna da kuma yadda take da muhimmanci cikin rayuwarsa.

    A ranar ya yiwa yaron huduba da suna muhammad muhsin,wanda zabi ne ya baiwa widad kuma ta zabi sunan uncle muhsin din

    “Hakan yayi miki?” Saita gyada kai tana murmushi

    “Uncle muhsin ya bani komai a rayuwa da yayi silar wanzuwar rayuwata tare da taka,ya bani komai da ya bani kai” ta furta kalaman da wani irin sanyi,har cikin zuciyarta tana jinta cikin mata masu sa’a data samu abbas.

    Kalamanta sun sake gina mata matsayi mai girma cikin jiki da zuciyarsa cikin qanqanin lokaci,ya saki wani tattausan murmushi

    “Ni zan fadi haka widad,ya kawowa rayuwata alkhairi,ya kuma yarda ya kawowa rayuwata dauki a sanda take gab da dulmiyewa,samunki wani babbar tagomashi da baiwane daga Allah, ubangiji na ya gama yimin komai,babu abinda zance dashi sai godiya mara yankewa har ya zuwa qarshen numfashi na”.

    ********JEGO widad takeyi sosai,irin jegon da ake kira jego ja ainihi,don hajiya umma kakarta ta wajen mahaifiya wadda ta haifi mommynta ce ta taso takanas daga katsina ta taho yi kata zaman dabaro,tace damar da ba’a basu ba lokacin bikinta ba yanzu zasu nuna tasu bajintar.

    Nan sashen ummu ta sauka cikin dakin da aka warewa widad din,zamansu gwanin sha’awa,gurin sai ya zama majalisar gidan,abinda ya qarawa widad dadin zaman gidan kenan,sai ‘yan qananun abubuwa dake damunta,rashin sabo da raino,da kuma shayarwa da sai an tsaya a kanta take shayar da yaron saboda tsoro da rashin sabo.

    Gyara iya gyara widad tana shansa,jego take irin na da wanda a wajenta yake kamar takura ce,har sai da anty madeena tace da ita

    “Ki godewa Allah,ke yar gata ce gaba da baya,irin wannan gyaran da kulawar mata da yawa suka rasa,wanda daga ita ne kika samun sbauwar daraja da kima idan kin samu kula da gyara me kyau,daga itane kuma komai yake qwace miki ki kasa fahimtar inda mijinki ya dosa idan kinyi sakaci da ita”.

    Ta sake yarda da haka bayan hajiya fanna tazo mata barka,daga cikin abinda ta kawo matan itama kayan gyara ne ‘yan maiduguri masu shegen kyau,ta kuma jadda mata lallai lallai tayi duk abinda tsaffin suka ce mata,domin sun fita sanin me sukeyi,yadda taga kuma suna kula da ita itakam hakan ya burgeta.

    Fadin irin alkhairin data dinga samu ma bata baki ne,abun sai ya zamana kamar lokacinne aka yiwa abbas din haihuwar fari,abokan aikinsa kota ina,basajin tafiya daga bauchi zuwa kano ganin jariri,abun har mamaki ya dinga bawa kowa.

    To amma ba abun mamaki bane,duba da dabi’a da halayyar abbas din,mutum ne mai tsananin kirki kyakkyawar mu’amala da kuma budadden hannun alkhairi ga kowa,haka suka yita karbar jama’a,har akayi kwana biyar,aka fara shirin gagarumin suna.

    *********Ita kadaice a zaune a falon nata tana yankan farcenta da wannan karon da kanta tayi amannar yayi datti yadda ya kamata,don babu ko sirkin jan lalle a kansa ko baqi balle ya taimaka ya boye datti ko tsahon da yayi.

    Gaba daya tunda akayi haihuwar takejin wani gagarumin sauyi yana tunkarar rayuwarta,tana fuskantar motsin kowa,kowa cikin family kamar rawar jiki yake da haihuwar,abbas kuwa duk da dama can nutsatse ne,komai nasa kuma bisa tsari da dacewa da kuma mutuntaka yakeyinsa……amma walwalarsa ta qaru dari bisa dari,jifa jifa tana tsintar hirarsa da yaransa akan sabon qaninsu,abinda yake matuqar quntata mata,ya kuma jefata cikin baqincikin da yake sake sakata cin alwashin da takejin muddin ranta ba zata sauke ba,sai taga abinda ya turawa buzu nadi.

    Ko a yanzun ma da take zaune ita kadai a gidan sai yusra,ya kwashesu suna wajen tailor dinsu karbo dinkunan suna,sunan da batajin ko sama da qasa zata hadu zata bar yaranta suje,badai a gobe zai wuce kaduna ba saboda tasowar wasu ayyuka masu matuqar muhimmanci?,taga wanda zai tareta da maganar zuwansu kano.
    [13/05, 9:33 am] +234 907 874 7031: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 2

    A Rubuce Take Book 2 Page 2

    *A RUBUCE TAKE*
    (K’addarata) Book 02

    Ta hadu da mutane masu karamci,don haka bata wani jima ba ta sake sosai a cikinsu,zamu iya cewa tafiyar ta zame mata wani mabudi na alkhairi tare da sake sanin wacece ita,wanne aiki ne a gabanta?,wanne muhimmanci abbas ke dashi a rayuwarta wanda abaya duka hankalinta bai taba mata hasashen hakan ba,duk kuwa da yadda take jinsa sosai a jikinta zuciyarta da ruhinta.

    Abun ya fara ne daga yadda suka maidata kamar qanwarsu,koda a aikin hajjin kowa qoqarin tallafarta tare da nuna mata abubuwa yakeyi,musamman daya zamana ita daya ce farkon zuwa wajen,cikij taimakon Allah sukayi hajjinsu lafiya suka gama,sai ya zaman lokacin komawa gida nigeria kadai ya rage musu.

    A sannan taga kowacce hankalinta ya tattaru kan mijinta da sukazo tare,a lokacin suka lura da yadda ita din bata maida hankalinta sosai akan hakan kamar yadda su sukeyi,hajiya sha’awa ita ta fara fahimtar hakan,wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,tuntuni suka gane quruciyar dake dawainiya da ita,wadda wasu abubuwan take gaza yinsu,babu wadda taji kunyarta acikinsu,dukka suka hadu kamar yadda zasu yiwa qannensu uwa daya uba daya suka fara dorata akan sabon saiti…..sabon karatu da sabon darasi.

    Bata taba jin kunyar wasu mutane kaf rayuwarta ba irin yadda suka sanyata jin kunya,amma ta dole sukayi mata ta sake ta kuma soma bin karatun nasu.

    Abinda bata sani ba kusan kowannensu tasan halayyar hafsat ciki da bai,wannan yasa hatta gidan babu wadda tayi masa zuwa uku, lokacin da sukaga widad din a mazaunin kishiyar hafsat qaunarta da tausayin yadda zata iya zama da ita ya shigesu,wannan yasa suka samu qarfin gwiwar dora mata abubuwa masu nauyi da yawa,wadanda sukasan koda bayan rabuwarsu zai zauna a kanta ya kuma bi jikinta.

    Ranar farko kuma karo na farko da taji itama tanason kasancewa da mijinta kamar kowacce mace,ta dauki waya ta kirashi,a sannan suna tare da sauran abokansu da basu taho da matansu ba,saidai dukka kewarta ya isheshi,bayason ya fiya takura mata ko matsanta mata ne kawai,duba da situation din da take ciki,amma he really needs her,kullum kwanan duniya sake shigewa rayuwarsa takeyi.

    Cikin karsashi ya daga kiran,saidai muryarta kawai ya kashe masa jiki,ya jingina da kujerar yana saurarenta sanda take magana dashi cikin narke murya

    “Bakayi kewata ba ko uncle?” Maganar tata tadan tabashi,har sai daya murmusa

    “Har bansan yadda zan misalta miki ba babyn uncle,kawai dai baison takurawa maman baby dama babyn” har ranta taji dadin amsarshi

    “Indai hakanne to kazo mu tafi,yau a wajenka zan kwana” mutuwar zaune yayi yana mamaki,widad dinshi ce ke fadar haka da bakinta?,ya rasa amsar da zaya bata har sai data sake cewa

    “Hello”

    “Than you baby,gani nan zuwa” abinda ya iya fadi kenan jikinsa yana dan rawa kadan,wanda ba lallai ne kai ka fahimta ba

    “Ina zuwa” kawai yace musu yana barin wajen.

    Kiran wayarsa ya shigo wayarta sanda ta fito daga wanka,tana tsaye jikin madubin dakin nasu tana mulke jikinta da wasu oil perfumes da hajiya fanna ta bata sanda zasu fice subar mata dakin,hajiya khairi ke tsokanar hajiya fanna

    “Allah dai yasa ba kyautar turaren banza kikayi mata ba,wala’alla ki dawo ki sameta nade a gado ma tayi baccinta”

    “A’ah ai ba za’ayi haka ba,na tabbatar karatunmu yana shiga,nidai ina ganin canji” qas tayi da kanta tana murmushi,dukkaninsu kunyarsu takeji,tunda sun girmeta,tana jinsu suna tsokanarta har suka fice.

    Wayar ta daga tace masa gata nan fitowa,ta gama shirinta a nutse,ta dauki duk wani abu da takega ya dace da wanda taga suna dauka suma idan zasu fita din,ita kanta tana jin banbanci da canji a tattare da ita,ta kammala komai a nutse ta fito.

    Ko sau daya baiji ya qosa da jiranta ba har ta iso,kasa magana yayi sanda qamshinta ya gaurayeshi,sai ajiyat zuciya mai nauyi daya sauke kawai,suna shiga dakin ya maida qofar ya rufe da wani irin zafin nama,ko ina na jikinsa yana daukan rawa.

    Zaucewa ya kusa yi sanda widad din ta miqa masa kanta yadda yakeso,ta kuma hada da bashi gudunmawa,sai kansa gaba daya ya kunce,jikinsa ya dauki rawa tako ina ya fita mata a hayyancinsa.

    Bawai shi ba,ko ita din a yau ta gane da banbanci,ta fahimci kuma maganganun su hajiya fanna,bayan komai ya kammala wata kunya ta kamata,yayin da shi kuma ya hanata sakat,bakinsa kuma ya kasa yin shuru,ya dinga zuba sumbatu ya kasa tsuke bakinsa,domin kuwa ta shammace shi fiye da kima,ta kuma kaishi wata duniya da tunda hajiya ta kawoshi sararin duniyar nan bai tana zuwa can din ba,ko sanda yake kidansa yayi rawarsa shi kadai yaya ya qare?,bare yanzu data bashi tallafi ta kuma miqa masa kanta kacokam.

    Wannan canji na widad ya tabashi fiye da kima,ya sake kuma cusa wata irin zazzafar soyayyarta a zuciyarsa,ya sake susucewa,har abun yake bawa widad din mamaki,yadda ya dinga cire kudi yana mata siyayya abun sai ya dinga daure mata kai,wanne irin so uncle din nata yake mata haka?.

    Ranar da suka fita siyayyar data sake sanya widad sallamawa abbas rayuwarta da jikinta……ta sake yaqini da yadda yake yawan fadin yana sonta,cikin shagon gold ya mallaka mata wata sarqa da farashinta yakai naira dubu dari tara da hamsin.

    Kanta ya daure sosai,a wauta da quruciya irin tata tace ba zata karba ba,sai bayan taje dakinsu da ita su hajiya sha’awa suka dinga mata dariya

    “Karki qara cewa ba zaki karba ba,tunda ya siya baifi qarfinsa bane,kuma tukuici ne tabbas yake baki,lallai soyayyar da yake miki tana da girma da fadi,saiki sake kula ki kuma tabbatar duk abinda yakeso kina aikatashi sau da qafa,tabbas gaba saikin mallaki abinda yafi haka muddin zaki sallamawa mijinki tare da tsare duk wani abu da yakeso,ki kuma guji wanda bayaso” ta jima a kwance tana tariyo rayuwarta ta baya,da kuma abubuwa da suka faru a yanzu,ko addu’a ce da ummu da mommynta suka yita jaddada mata ta yiwa kanta mijinta da kuma rayuwar aurenta?,ba shakka akwai tasirin addu’ar data dinga yi tuquru,sai gashi tanata ganin abubuwan da ada bata iyasu ba batama san dasu ba.

    Ranar da suka qara fita siyayya gefe ta koma kawai tana kallonshi,yadda ya zage yana siyan kayan babies kamar yasan me za’a haifa,har sai data gaji da ganin yadda yake diban kaya kamar baisan ciwon kudinsa ba tayi magana

    “Uncle” ta fada a narke

    “Baby” ya amsa bayan yabar dukkan abinda yakeyi ya waiwayo yana duban idanunta farare masu haske sosai,wanda suka dan qara girma kadan

    “Wai don Allah bakajin kunya?,ciki fa ka yiwa mace” dariyar da bai shiryawa ba ita ta kubce masa,nutsatstsiyar dariya mai wani irin siririn sauti da tasa fararen haqoransa bayyana,sakalci da shirmen quruciya dai a cikin jinin widad qilan yake,sai tayi kaman ta daina sai wataran ta sakankance ta yanko maka wata wautar,kallonta yake kawai yana dariyarsa,yama rasa wacce amsa zai bata.

    Turo baki gaba tayi ganin yadda yaketa mata dariyar yana kuma kallonta

    “Kaiko a jikinka,ka yiwa mace ciki kuma kana siyan kayan jarirai,bakajin kunya ma mutane su gane”. Takowa yayi gaba kadan ya tsaya a gabanta yana kallonta,ko yaushe qara kyau takeyi tana zama wata balarabiya,ba wanda zai kalleta ya yadda ta iya hausa,hakanan babu wanda zai kalleta ya yarda akwai ciki a jikinta

    “To ko mutanen duniya zasu fara boye kawunansu ne?” Kai ta daga ta kalleshi don bata gane me yake nufi ba,saiya kashe mata ido daya

    “Ai kowa ma ta yadda wannan cikin ya samu ta haka yazo,ciki harda ni dake da…….” Da sauri ta rufe masa bakinsa bayan ta danyi dage kadan,saita janye hannunta da sauri

    “Kuma me ya kawo wannan maganar?”

    “Kece mana” ya amsata yana qunshe dariyarsa

    “To naji,amma bakasan fa me za’a haifa ba kake diban kaya”

    “Ko meye kika haifa wuud(qauna/soyayya matsananciya) inaso,idan ana haifar rabin mutum ma kika haifamin zan karba hannu bibbiyu” ido ta zaro tana kama haba

    “Rabin mutum?,wai?” Yadda tayin ta bashi dariya,sai.ya janyeta cikin hikima sukaci gaba da zaban kayan unisex a tare,ya kuma tura mata option na zabar favourite colors dinta a dabarance,ta zaba din sosai,duk da tanayi tana waiwaye kamar wadda ke aikata wani abu ba dai dai ba.

    **************Karfe sha biyu da mintuna na dare motarsu ta tsaya qofar gidansu na bauchi,a sanyaye widad din ta maida bayanta jikin kujera tana kallon gidan,wani mugun tsanar gidan na shigarta sosai,tana jin kamae ta balle murfin motar ta fice ta kama hanyarta,inda zai bata zabi….da salin alin zatace masa ya kaita gidan hajiya ko gidan uncle muhsin,to amma koda ta fada din tasan ba lallai yayi hakan,don zaice mata ne dare yayi,ko baya ga haka ma…..iya kusancin da suka samu a yanzu a tsakaninsu,bata tunanin zai bari tayi nesa dashi.

    Shi ya fara fita daga motar yana cewa

    “Ina zuwa” saita gyada kai kawai,tana jin yadda qirjinta yake bugawa,tana iya hangensa daga inda suke zaune a motar ita da umar qaninsa daya daukosu,yanata knocking.

    Tun yana qwanqwasa a hankali har ya koma bubbugawa da dan tsauri,wasa wasa sai gashi sun kwashe mintuna masu tsaho yana bugawa,amma qofar ko gezau,babu alamun za’a bude musu gidan,har umar dake zaune cikin motar ya miqe ya fita ya soma tayashi bugun.

    Tun ransa bai baci ba har ya soma baci,don ba cikin gida ba……muddin dai ba wani abu bane ya samesu ba a irin bugun da yakeyi yasan har maqota sun jishi,sannan ma ba ita daya bace a gidan,idan ita bata ji ba saboda tayi ciki……shi kuma lawal fa dake kusa kusa?(dan dan uwanshi daya dauko sanda zaiyi tafiya).

    “Kira number lawal ka hadani dashi” ya fada yana duba agogon hannunsa,umar ya fidda waya ya fara kiransa,amma wayarsa na a kashe,sabanin ta hafsat daketa ringing kuma ba’a daga ba,a handsfree take don haka yaji me computer ta fada, kafin wani a cikinsu ya sake cewa komai sunji motsi ana tambayar waje,abbas ya tsaya kam yana riqe da qugunsa yana kallon qofar,umar ne ya amsa mata da

    “Mune” sai aka fara buda qofar gidan a hankali kamar mai ciwon hannu