A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 10

Sponsored Links

Part 02

Page 10

Kamar ta bawa mimi kudin ta maida mata,sai taga kada tayi asara,ta bata kudin kuma tazo batayi musu girkin ba,don haka sai ta ajjiye kudin tanata qananun mitoci.

Tun tana saka ran ganin widad din ta shigo sashen har ta fidda rai,don yamma ta riga tayi,ga yunwa suna ji ita da yaran,dole ta shiga kitchen ta dora dafa dukan shinkafa.

Tana kitchen din tana fama ga magrib ya kawo jiki widad ta dawo,dakinta ta wuce kai tsaye,bata bi ta kan jagulallen parlor din nasu ba,tana mamakin yadda suke iya hargitsa guri har haka suci gaba da zama a cikinsu abinsu hankali kwance.

Ta taho da sauran faten tsakin daxu,da zafinsa don a wani warmer mai kyau da hajiya ta bawa maari yake a ajjiye,saita hada ruwa me zafi ta cire kayanta ta shiga toilet tayi wanka ta gasa jikinta sosai,ta dawo ta zura wata armless riga da iya tsahonta gwiwa,ta wadata jikinta da turare,ta sake jona humidifier sannan ta dawo tana laluben hijabin da zatayi sallar dashi wanda zai saukar mata har qasa.

Sosai yau ya hado yunwa da kuma gajiya a jikinsa,ya tabbatar zai samu dukkan wani hutu da kulawa hadi da kwanciyar hankali daga gurinta,wannan yasa ya hada dukkan yunwarsa ta yinin ranar,bai wani tsaya yaci cikakken abinci ba,don yasan zai tarar da irin taste din da yake muradi,har fiye ma da yadda yakeso.

Ajiyar zuciya ya sauke sanda ya kashe motar tasa,ya waiwaya baya ya dauko ledar fruit din da ya siyo da chocolate nasu mimi ya fito,ya kashe motar sannan ya nufi cikin gidan.

Tun kafin ya qaraso ya fara buda hancinsa yana tsammatar samuwa sassanyan qamshin nan dake masa maraba a duk sanda girkinta ya shiga,saidai babu shi ba alamarsa,duk da haka yaci gaba da takawa cikin hope da kuma karsashi.

Sosai mamaki ya cikashi sanda ya yaye labulen falon ya sameshi a tarwatse,komai yana zaune zaman kansa,sai su mimi dake ta hada hada da kayan ciye ciye na leda irin wanda yake siyowa ya jibge musu,ko ina tarkacen kayan ledojin da tsinken sweet ne,dukansu suka watsar da abinda yake hannunsu suka nufoshi suna rige rigen qarasowa,ya tsugunna ya tarbesu gaba daya.

Miqewa yayi yana dauke da nawwara mimi na hannunsa,yaji motsi a kitchen,don haka zuciyarsa ta bashi widad ce,sai ya wuce kitchen din dasu kanshi tsaye yana amsa tarin tambayoyinsu da suketa damunshi dasu.

Tun bai gama shiga kitchen din ba idanu da hancinsa suka gaya masa ba widad bace,hafsat ce sanye da doguwar rigar wani material ruwan qwaiduwar qwai,sulbinsa ya sanya dinkin da aka masa a wasu sassan ya zazzame yayi zare zare,tana goye da yusra daketa mutsu mutsun son a sauko da ita,ya qarasa yana amsar yarinyar,ta sauke masa ita tana masa sannu da zuwa muryar a cunkushe.

“Ina antyn nasu?”

“Tana dakinta mana” hafsat ta amsa adan fusace tana juya dafadukan data fara kamawa

“Lafiyarta qalau?” Juyowa tayi kamar ta banka masa harara,amma kwarjinin nashi idanuwan sun shallake nata

“Aiba wannan ya kamata ka fara tambaya ba,kamata yayi ace ka tambayi wanda ya bamu abinci wunin yau,ta shige daki saboda ta samu daurin gindi tayi kwanciyar ta wuni guda ta barmu da yunwa ni da yara” sam hankalinsa bashi akan maganarta, zuciyarsa da tunaninsa sun karkata kan sanin lafiyarta da abinda ya hanata fitowa wunin yau,sai ya juya yana sabe da yusra ya fice a kitchen din.

Ana fara knocking ta gane shine,ta riga ta saba da komai nasa,hatta takun takalminsa ya banbanta dana kowa,tana kuma iya banbancewa,ranta yadan quntata,itakam ko son ganinsa batason yi,space take da buqata, batason takura,to amma batason tayi wani abu na rashin girmamawa a gareshi gaban yaransa,dole ta ajjiye qaramar hular da take qoqarin sanyawa sassalkar sumarta daketa sheqi saboda yadda tayi oiling dinta da mai,tana tura baki da shagwababbiyar fuskarta ta isa qofar ta bude masa,sai taja ta tsaya daga bakin qofar,kamar wadda aka zo gayawa saqo take jira a gama gaya mata a fita ta kulle qofarta.

Tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa wani abu ya tsarga masa,yadda batasaka brassiere ba amma hakan bai hana na shanunta tsaiwa kyam suna nuna kansu ba,lafiyayyun cinyoyinta sun fita sosai ta cikin tsingilalliyar rigar,yadda ta turo bakinta gaba kuma ya qarasa kunnashi,soft pink lips dinta daketa sheqin lip gloss,sai yaji kamar ya jata cikin jikinsa ya kama bakin ya tsotse,amma yusra na kafadarsa,tilas ya daure,ya qarasa gefan gadon ya zauna ya dora yarinyar saman cinyarsa

“Sannu da zuwa” shuru ya ratsa maimakon ya amsa mata,ya tsareta da ido yana jin yadda kallonta kawai yake saukar masa da kasala

“Banda na shigo na nemeki bakisan ma na dawo ba kenan?”

“To me zanzo nayi maka?,bayan maganar matarka kawai kake ji” ta fadi haka cikin ranta,amma a fili saita sake tura baki gaba tana yamutsa girarta hadi da sarqafe yatsunta waje daya tana ballaqasu

“Zonan” ya fada a tausashe yana nuna mata kujerar madubin dake gabansa,ta kalli wajen sannan ta kalleshi,ko yaushe girma da kimarsa ke sakata ta kasa masa musu ko wasu dabi’u da basu kamata ba,ta sauke hannuwanta ta dawo inda ya nuna matan ta zauna,wannan karon idanunta cikin nasa tanason jin abinda zai gaya mata kuma.

Rage kaifin nasa idanun yayi kadan daga kanta sannan ya magantu

“Ya akayi gidan ya zamana yau duk a hargitse,infact ma yau girkinki ne amma baki fito kwata kwata ba,ko yanzun ma antynki ce cikin kitchen din” wani haushi ya kamata,aiki?…..a nan tafi kauri kenan, idanunta ta lumshe kadan tana daukesu daga kansa,abinda ya sake fusgarsa da wani madaukakin shauqi zuwa gareta,duk da ba tayi bane don ta burgeshi ko kuma da wata manufa

“Gida a hargitse?,ina cewa mummyn mimi tana cikin gidan,amfanin zaman mutum biyu kenan,idan dayan ya gaza ko ya gajiya sai dayan ya tallafa masa…….girki kuma ni na daina girki,na bar mata komai da komai harda kwanana” mamakin widad din sosai ya kamshi,yadda tayi maganar ya tabbatar da gamewar hankali a jikinta,don tana maganar ne with seriousness in her sound,baibi takan maganarta ta farko ba,maganarta ta qarshe tafi fusgar hankalinsa tare da tabashi,don abune da bayajin ko sama da qasa zata hadu zai amince da hakan

“Kin daina girki?,meye dalili?,da kuma izinin wa kika dauki wannan matakin?” Sake tura bakinta gaba tayi sosai tana hade fuska,ta kuma kaucewa dubansa

“Saboda gidan da mijin duka nata ne,so komai da yake cikin gidan yafi cancanta ya zama nata” sai yanzu ya sake gano inda ta dosa,can qasan ransa murmushi ya kubce masa,kishi take da gaske…..ta kuma ji haushin abinda yayi mata kenan fiye da yadda ma shi ya zata,amma bayason ta dore da haka don haka ya miqe yana dora yusra a kafadarsa

“Ki shirya komai kamar yadda kika saba,banason dawo da zance,abinda ya wuce ya wuce” sai ya taka yana ficewa a dakin.

Sam maganarsa bata bawa zuciyarta sassauci ba,saima tunzurata da yayi,bazai iya daukan mataki ba kenan kwata kwata?,indai haka ne itama bataga dalilin da zai sanyata saukowa ba,don haka yana fita sallar magariba ta sakawa dakinta key tayi sallarta ta jirayi isha’i ta bada ita sannan ta haye gado ta nutse cikin duvet hankali kwance.

Sai daya dawo daga masallaci sannan ya zarce dakinta don ya samu ruwan nan nata me wani irin dumi da qamshi don yayi wanka,ruwan da ita kadai tasan yadda take hada masa shi,don koshi ya hada da kansa baya jin dadinsa kamar haka.

A nutse ya tsaya yana knocking a bakin qofar,tana jinsa ta share,saita saka earpiece ma a kunnenta,don haka batasan adadin awannin ko mintunan da ya dauka yana bugun ba.

Sosai ransa ya quntata,don yadda yayi tsaye yana bugun har mimi taji ta fito ya tabbatar tana jinsa,ya kirayi sunanta kusan biyar shuru,dole ya juya dakinsa dakin kuma hafsat,tana zaune a qasa ta tara kayan qazantar yusra tana waresu,ya wuce gaban cupboard dinsa yana rage kayan jikinsa.

Binsa tayi da kallo ta tabe baki,ita da zasu tabbata a haka sai tafi kowa farinciki,duk bugun akan kunnenta akayishi,tana sane tayi bakam

“Ba kwananta bane?,ya na ganka a nan dakin?” Ta jefa masa tambayar da tasan amsarta.

“Na sani,hadamin ruwa zanyi wanka” ya fada muryarsa da wani irin laushi daya bata mata rai,komai na yarinyar tabashi yakeyi,saka masa damuwa yakeyi,duk qoqarinta na kau da hankalinsa amma baya wani tasiri yadda take da buqata,ita sau nawa suna irin wannan sabanin,amma ko a fuska bata taba gani yayi laushi irin haka ba,komai dadewar da zasuyi,sai yanzu akan qaramar yarinya kwana uku kacal amma duka ya canza?.

Da tunani iri daban daban ya shiga wankan,sam ruwan baiyi masa ba,hasalima ya cika zafi da yawa,yaja tsaki ya saki famfo akai,sai kuma yaso salance masa,ya sake jan wani tsakin yana komawa cikin bathtub din ransa duka a jagule.

Koda sukazo cin abinci ma yasa mimi ta bubbuga mata,duk da yadda hafsat ke faman hada rai tana ganin ya girkinta ne batayi ba ita ta zauna tayi kuma saboda gata wai a kirata taci,itama mimin haka ta qaraci bugunta ta haqura ta dawo jiki a sanyaye

“Bata bude ba” sai ya shafa kanta

“Inajin tayi bacci” a yadda yake jinsa koda lafiyayyen girki hafsat din tayi abincin bazai masa dadi a baki ba,bare tafashi kadan hafsat din wadda ta cuccure waje daya,kamar gidan da aka yiwa gorin man girki,bayan komai a wadace yake a store dinsu,zuciyar tata ce dai haka.

Da qyar yayi loma hudu ya ture abincin,ya maida hankalinsa ga news da ake haskowa a channel din al_hadath,duk da a badini fiye da rabin hankalinsa yana kan qofar dakinta,duk bayan mintuna biyu saiya kalli qofar dakin,amma ko motsinta daga ciki baiji ba bare ya sanya ran zata bude ta fito.

Har yaran sukayi bacci hafsat ta debesu takai daki ta dawo tayi masa sallama yana zaune a wajen,sanda sha daya na dare ta buga sai ya tashi yana sake gwada bugun,a lokacin tuni tayi bacci,bugunsa ne ya tasheta,ta sauko a hankali ta wuce toilet abinta,tayi fitsari ta sake alwala ta dawo ta kuma kwanciyarta.

Wannan karon yaji motsinta shigarta bandaki zuwa fitarta,hakan ya nuna masa tana jinsa,bata kuma da niyyar bude masa,ya koma da baya ransa yana baci,ya juya yana nufar dakinsa.

Dadi ya kama hafsat dake labe,saita koma bakin gado ta zauna tana kada qafa a hankali,itakam gaba ta kaita,dole yau ya kwana dakinta,sannu a hankali dai gida yana shirin dawowa hannunta sai yadda ta juyashi, murmushin nasara da farinciki ya kubce mata.
[09/05, 4:06 pm] +234 816 283 5575: *H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button