Author: Novels

  • A Rubuce Take Book 2 Page 30

    A Rubuce Take Book 2 Page 30

    Part 02

    Page 30

    Mummy ce dauke affan da yake faman tsala kuka,kukan nasa daya dinga shiga kunnuwan widad kamar a duniyar mafarki

    “Karbeshi ki bashi yasha,kamar bacci yakeyi” mummyn ta fada tana miqa mata shi,saidai ko motsawa batayi ba bare tayi azamar karbarsa,abinda yaja hankalin mummyn kenan

    “Ke widad…. widad lafiya?” A hankali ta ajjiye affan ta zauna tana jan widad din cikin jikinta gami da ambaton

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Hasbunallahu wani’imal wakil” ganin kamar tana neman fita a hayyacinta,addu’o’i ta soma karantawa tana shafa mata a fuska,a hankali sai nutsuwarta ta fara dai daita,ganinta ya fara dawowa dai dai,ta zubawa mummyn idanu wasu hawaye masu zafin gaske suka fara zarya akan fuskarta.

    “Meyake faruwa?,me ya sameki?”

    “Mummy cikina ne yakemin wani irin ciwo”

    “Ya subhanallah” ta fada wani sashen na zuciyarta yana mata wasi wasi,yanayin da taga ta shiga baiyi kama da yanayin ciwo ba,yafi kama da wanda yaga wani mummunan tashin hankalin

    “Bari na kira saleem sai mu muje kiga likita,ai bai kamata a zauna ba” kama hannun mummyn tayi

    “Aah mummy,addu’a zakici gaba da yimin,ko yanzun da kika yimin na samu sassauci” kai ta jinjina badon ta yarda da widad da abinda yake damunta ba,a haka ta sakata ta shayar da affan saita sake karbarsa ta fita,saidai fiye da rabin hankalinta yana kan widad din,duk bayan wani lokaci saita leqata tare da tambayarta ya jikin?,akwai abinda take buqata?,saidai tace babu.

    A ranar yadda taga baqar rana haka taga baqin dare,baqin daren daya zame mata baqiqqirin,yayi mata kuma tsaho tamkar daren mutuwa,tayi dukka Wani qoqari na fahimtar da abbas abinda yake zato ba haka bane amma yaqi saurararta,ta kira har sau ba adadi,ta tura masa tex na bayanai har batasan yawansu ba amma ba abinda ya canza,kafin gari ya waye ta fige ta fita hayyacinta da tashin hankali,kamar yadda shima a nasa bangaren wani irin firgici tashin hankali da razani yaso da’ai d’aitashi,duk sanda ya tuna har lawal ya shaida fitar tata ya kuma bashi tabbacin zuwa take hotel din tana kuma kawo maza sai yaji kamar zuciyarsa ta fashe ya mutu.

    Sanda mummy ta shigo da safen ja da baya tayi tana salati ganin yadda fuskar widad din tayi jajur da ita ta tasa

    “Ke tashi,tashi ki gayamin gaskiyar abinda yake damunki” mummyn ta fada tan ajjiye kayan tea data shigo mata dasu,ta nemi gefanta ta zauna ta a nutse tana rutsata da ido.

    Batasan ba zata iya daukan wannan tashin hankalin ba,batasan zuciyarta ba zata iya jure wannan al’amarin ba sai data dora kanta a kafadar mummyn,a sannan ta sake gasgata uwa rahamace da babu kamarta a doron duniya,tayi kuka tayi kuka,har sai data zagwanye dukkan wasu damuwoyi data jima tana dakonsu a ranta,sannan a hankali cikin wani irin ciwo da zuciyarta ke mata ta furta ma mummyn abinda ke faruwa

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta maimaita sau uku cikin mugun gigicewa tana daga widad daga kafadarta

    “Da wannan abun kike boyewa?,wacce iri ce ke widad?,to ni kaina wannan abun yafi qarfina,yafi kuma qarfin jina da kunnuwana,bazan iya jin wannan abun ni kadai ba,maza tashi”ta fada tana dauko ruwan tea din data shigo dashi

    “Tashi kisha wannan yanzun nan fita ta kamani,banga ta zama ba” haka ta dinga bata tea din,tana kurba tana jin kamar mutuwa takesha,mararta kamar zata fashe saboda tsananin ciwo,amma wannan ciwon bashi ke damunta ba,salama ne akan ciwon dake danqare cikin zuciyarta.

    Mummy na bata tea din tana sake maimaita innalillahin saboda yadda batun ya daki zuciyarta,ta sani ta kare kanta da mutuncinta tsahon rayuwarta,dai dai da rana daya kuma bata taba hutawa da yiwa yaranta da jikokinta addu’a kan samun kariya daga zina ba,tayi imanin addu’arta ba zata tashi a banza ba.

    Da cup din ta fice bayan ta sakata kwanciya sanda taga gumi yana yanko mata ko ina

    “Ki cire damuwa a ranki,Allah yana tare dame gaskiya muddin kinsan kedin me gaskiya ce,komai daren dadewa Allah bazai bar gaskiya ta tozarta ba” da wannan kalamin na mummy widad ta samu nutsuwa kadan,saidai duk da haka hawaye baibar fita daga idanunta ba,yadda abbas ya rufe idanu kamar yau ya fara saninta,yaqi ji yaqi gani,yaqi tsaiwa ya saurari gaskiyar ta.

    Shiryawa mummyn tayi tsaf suka fice zuwa gidan yayanta,tabarsu a gidan ita da affan da su saleem,tace su kula da ita su dinga yawan leqata,zasuje su dawo ita da usama.

    Shi kansa uncle bashir ya kadu da jin batun da mommyn tazo dashi,yayi Shuru yana jinjina maganar cikin ransa

    “Abinda nake gani,mu basu iska shida ita,shi din na tabbatar tunda jami’in tsaro ne bazai gaza bincike ba,zuwa sannan ya huce ba kamar yanzun da yake kan doron zargi ba,kuma wala’alla ya kammala bincikensa sai mu tuntubeshi muji daga gareshi,zan shigo naga widad din in sha Allah,kici gaba da tausarta komai zai dai daita in sha Allah” mummyn ta gamsu da shawararsa,da wannan kuma ta dawo gida ta shiga kula da widad din,dukkan qoqarinta ta sanaya akanta,bata barinta ta kebe kwata kwata saidai idan ya zama dole gudun kada ta shiga damuwa,saidai abar zuciya da abinda takeso,wata muguwar damuwa keta cin ranta ta can qasa,duk da tana ta qoqarin sakewa saboda yadda take ganin mummyn nata tana wahala da ita.

    Komai nata mutanen gidan sun bashi muhimmanci,kowa qoqarin ganin ya nuna mata damuwa da kulawarsa yake,amma har yau al’amarin abbas yaqi sakinta,mamakinsa ke cikata a duk sanda ta tunashi,a kowacce rana tana duba wayarta sau babu adadi waiko zataga kira ko saqonsa,kozai bayyana mata ya gano qarya ne sharri ne,ya gano kuskuren fahimtarta yayi,a kullum dakonsa takeyo ko zataga saqon ban haquri,amma shuruuuuu kakeji,babu shi babu dalilinsa.

    Idan tace zata kwatanta yanayin da rayuwarta ta fada a wannan tsukin ma bata baki ne,wata irin damuwa me cin gangar jiki da ruhi,duk yadda take wuni cikin jama’a idan dare yayi tazo bacci saita kasa,kuka kuwa ta yishi kamar hawayen idanunta zasu qare,wai yau ita uncle dinta ke tuhuma da laifin zina,zina fa?,saita rushe da kuka tana jin kamar ranta zai bar gangar jikinta ta huta.

    *H A F S A T*

    Duniya ta zame mata sabuwa,sai takejin kamar bata da sauran wata matsala kuma yanzun,duk sanda ta dubi sassan widad ta ganshi a garqame,ta tafi kuma ba’asan ranar dawowarta ba,tayi rawa tayi juyi duk ita kadai,ta kuma kira habiba tayi mata godiya mai yawa,tare da fadin zasu koma wajen malaminta nan kusa,amma abu daya dake damunta,irin yadda abbas din gaba daya ya canza,bashi da kuzari bare walwala, fara’a kam babu ita,tuni tayi nata waje,duk da qoqarin da takeyi taga ta gyaggara yadda widad keyi amma babu abinda ya canza,sai abubuwa suka fara mata wuya,ga qoqarin ganin ta dauki pattern din widad wanda dukka jiki da zuciyarta suka gaza saboda bata saba ba,ga sauyin yanayin abbas din.

    Shikam kome baisan yana yi ba,duk yadda yaso ya manta komai ya cisge widad daga rayuwarsa amma ya gaza,abun ya masa tsaye a rai,ya tsaya masa fiye da duk yadda ya zata,ko mutuwar mahiafiyarsa ya dangana amma ya kasa dangana da widad din,ya tsaya a gaban mudubi ya kalli kansa da kansa ya yiwa kansa fada amma ko gezau,yasha rasa bacci cikin dare idan abun ya taso masa amma abu guda zuciyarsa keta nacin bashi shawara

    “Ki saketa kawai ka huta,ka saketa zaka manta da ita” saidai sam hannuwansa sun gaza rubutu takardar sakin.

    Irin wannan maganar hafsat din tayi masa,bayan sallar isha’i yana zaune a falonsa yana kallon labaran duniya a tv,ga mai zuzzurfan hankali duba daya zaiyi masa ya gane tunani yakeyi bawai kallo ba,ta turo qofar ta shigo idanunta a kansa,ta dauke kai tana jan tsaki qasan ranta

    “Haka zakayita yi kazo kuma ka haqura,kun rabu kenan har abada billahillazi” kafin ta qaraso ta sauya fuskarta zuwa yanayi na tausayi

    “Daddyn mimi,nifa banajin dadin ganinka a haka gaskiya,wannan abun tunda ya riga daya faru,kawai ka sawwaqe mata,saika samu nutsuwar zuciya idan aka rabu gaba daya,badai affan ne zai hada ba?,ka dauko yaronka,na maka alqawarin zan riqeshi tare dasu mimi” kamar wanda wuyansa ya sage haka ya daga kai yana kallonta,wani irin duba ne da yafi kama da duban baki da hankali,duk yadda zuciyarsa ke bashi shigen wannan shawarar amma ai bata taba ma kawo masa ya rabo affan da mamarsa ba,sai kawai ya ajjiye remote din hannunsa ya miqe tsam ya wuce bedroom dinsa.

    Da kallo ta bishi cikin mamakin yadda abubuwan har yau suka kasa saitan mata yadda takeso

    “Wai me yake faruwa ne?” Ta tambayi kanta,sai ta miqe tabi bayansa,saidai ta sameshi ya wuce toilet,da alama kuma alwala yakeyi,dole ta fito,ta wuce sassanta ta kirayi habiba ta tsegunta mata damuwarta

    “Ai dama yace kibi a hankali,don har yanzu zuciyarsa na ga yarinyar,zuciyarsu guri guda take,rabasu sai anbi da nutsuwa da taka tsantsan,don haka kibi a sannu,a hankali komai zai shigeshi ya rabu da ita harma ya manta da ita ba tare da ya sani ba,a yanzun dai gidanne ta barshi har abada,malam yace bazai bari ta dawo miki ba” taji dadi tayi maya godiya,ta kuma koma sashen,saidai tana murda qofar ta jita a kulle,tayita knocking amma ba’a bude mata ba,abun ya mata ciwo yadda a yanzun yake banzatar da duk wasu al’amura nata fiye da yadda take gani a baya,to amma data tuna da zancan da suka gama yi da habiba sai taji zuciyarta ta wanke,ta juya tana cewa

    “A juri zuwa rafi da tulu da diban ruwa,baqar matsiyaciya yadda kika fiddani daga rayuwarsa,kin bar gidan nan har abada,kuma saikin fita daga zuciyarsa kema haihata haihata” ta fada a fili a hankali kamar me sambatu.

    Yana fitowa kira yana shigowa wayarsa,kamar bazai dauka ba amma sai ya koma saman sofa bed ya zauna yana daga wayar,daga can uncle bashir yayi sallama jin ya daga wayar,ya amsa masa da muryarsa data zama me sanyi sosai.

    Gabatar masa da kansa yayi,sai suka sake gaisawa cikin mutuntawa,sannan uncle bashir ya sanar masa da dalilin kiransa.

    Wani irin zafin tururi ya dinga ji yana taso masa a qirjinsa,ya dinga furzar da iska daga bakinsa,da qyar ya iya controlling kansa kafin ua fara magana

    “Na sameta da laifin cin amanata ne,tana zuwa hotel tana kuma kawomin maza har cikin gidan aurena,yanzu haka ina da shaida a hannu na,kuma ita kanta ta amsa da bakinta taje”

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” uncle bashir ya dinga fadi

    “Yanzu babu ta inda kake gani za’a gyara lamarin?”

    “Sai nayi bincike shine abinda zan iya cewa” ya fada a taqaice,don gaba daya bai qaunar maganar,sai yaji numfashinsa yana riqewa.

    A sanyaye uncle bashir ya kalli mommyn widad

    “Ya kukayi dashi?” Bai boye mata komai ba ya gaya mata,ta sake maimaita innalillahin da tun zuwan widad bata bar bakinta

    “Ina zaki?” Ya tambayeta sanda yaga ta miqe

    “Kiranta zanyi naji waye din yazo kuma da gaske taje hotel din ita?” Daga haka tayi gaba,ta isa qofar dakin ta tura ta budeta, widad ta daha jemammun idanunta wanda ta manta rabon da suga kwalli tana duban mahaifiyarta,tana zaune saman abun sallah,ta hade tafukan hannayenta waje daya,da alama addu’a takeson yi amma ta rasa me zatace

    “Taso” mommy ta fada tana yafitota,saita miqe tsam tabi bayanta.

    A nutse ta amsa musu duk tambayar da sukayi mata

    “Dama shi baisan abubakar ba?”

    “Zuwansa na farko kenan shida baaba hamisu” duk sai sukayi shuru suna jinjina abun da yadda za’a warwareshi

    “Bari nayi kiran mahmuda,dole yasan abinda ake ciki,don na fuskanci abun babba ne” uncle bashir ya fada,ya sake fidda wayarsa ya zayyanewa abban komai.

    Shima dai kiran sunan Allah ya dinga yi

    “Ku kawomin ita kano” shine abinda ya fada,a washegari mummyn da uncle bashir suka yi mata rakiya zuwa kano,a gidan ummu suka sauka,suna shiga kuma widad din ta fada jikin ummu tana sakin kuma me tsuma zuciya.

    Wani mawuyacin hali ummun ta shiga,ta dinga goge qwalla zuciyarta fal tausayin widad din tata,ganin yadda tayi wata rama ta sake yin fari faaattt,hatta fatar bakinta a bushe take

    “Tun yaushe kika shiga wannan yanayin amma ba’a sanar min ba?,kiyi haquri ki kwantar da hankalinki,Allah yana tare dame gaskiya,kuma zai fiddaki ko ba dade ko bajima” haka ummu ta dinga fada cikin tashin hankali da yanayi na tausayi,zuciyarta kamar zata tsaga qirjinta ta fito,tasa aka gyarewa widad din daki,sannan aka shirya mata abinci kamar yadda aka shiryawa mommy da uncle bashir,amma komai widad din ta kasa tabawa,saboda bata iya cin komai,daga ruwa sai lemo,na fata kona gora,ita kanta mummyn tayi tayi ta dinga cin abincin amma baya wuce mata,kota kwatanta ci baya ciyuwa sai tayi amansa.
    [20/05, 8:46 am] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 15

    A Rubuce Take Book 2 Page 15

    Part 02

    Page 15

    Parlor din kuwa cike yake da surukan ummu da jikokinta,saboda wasu a nan zasu kwana sai ranar suna ko washegari zasu tafi,duka kowa baida matsalar wajen da zai sauka,don gidan nasu badai girma da yalwar masaukin baqi ba.

    Cikinsu ta zauna latifa ta kawo mata abinci akaci gaba da hira da ita,bataci mai yawa ba ta ture tana yatsina fuska,don ciwon mara da bayan kamar ma yafi na baya.

    Ummu dake ankare da ita tace

    “Lafiya?,mene?”

    “Baya na ne yaketa ciwo ummu”

    “Ehaan,kaji ba,shi yasa nace kiyi zamanki kika qi,saiki tashi ki shirya bari a yiwa wani cikin yaran nan magana ya dauko mota kuje asibiti” kai ta girgiza

    “Aah,kawai a bani man zafi na shafa har qafafuwana ma”

    “Basai taje asibiti sun jagulata ba ummu,tunda naga cikin kamar bai isa haihuwa ba ai,a bata.man ta shafa,zai ware,idan bai ware bama sai suje” anty halima ta fada cikin kulawa.

    Ummu da kanta ta shafa mata ta kuma tasata a gaba kan ta wuce daki ta kwanta ta huta hakanan,a hadu gobe,tunda hirar tasu bata qarewa,dole badon taso ba ta wuce dakin tayi musu sallama,su kuma suka rakata da sannu.

    To abu kamar wasa maimakon ciwo yayi baya sai yake qara gaba,tun tana daurewa daga kwance harta miqe ta zauna sosai,kafin wani lokaci mararta ta dauka itama,ta hada gumi sharkaf duk da ac din dake aiki a dakin.

    Cikin ikon Allah ummu ta leqa dakin da kanta ganin nujood da zasu kwana dakin tare bata gama tata hirar ba bare ta shiga,da sauri ummu ta qaraso tana mata sannu

    “Bayan ne?”

    “Harda marata ummu” ta fadi muryarta na karyewa tana dafe da marar saboda wani irin ciwo da take mata.

    Daga nan inda take bata matsa ba ta fara qwalawa latifa kira,kiran da yaja hankalinsu anty halima suka shigo.

    “Amma fa kamar mai naquda,kuma cikin kamar baiyi girman da zata haihu ba”

    Mmn muhassana matar uncle dinta ta fada

    “Shine nima abinda na gani,inaga ki shirya keda halima ku bita,kome mene zasu fada,Allah ya sawwaqe” ummu ta fadi tana dafe da widad din,kamar ta cire ciwon daga jikinta,ba jimawa naadir yace ya fidda motar,anty madeena na riqe da ita suka fice kowa na mata sannu.

    Babban private hospital ne daya hada qwararrun ma’aikata a cikinsa,kai tsaye sukayi amfani da file din mommyn muhassana tunda a nan suke ganin likita,kuma family file ne dasu,aka turata labor room bayan sun gama nata gwaje gwaje da tambayoyi.

    Idanu ta dinga rarrabawa sanda sukayi maganar ta cire pant dinta,bata fahimci me za’a yi ba,ta cire ta tsaya suka buqaci ta kwanta ta kuma bude su gwadata.

    Qwalla ta dinga yi sosai,ga zafin ciwon mara dana baya ga kuma budetan da nurses sukayi

    “Labor kikeyi,kuma nan da asuba zuwa wayewar gari zaki iya haihuwa,don yanzun haka kinkai 4cm” abinda suka gaya mata kenan,abinda ta gayawa su anty halima.

    Mamaki sosai suka dinga yi,don duk kowa kallon cikin suke baifi watanni biyar ba,tunda bai fito ba sosai,ba jimawa suka bata gado da daki,anty madeena kuma tayi waya gida ta gayawa su ummu,nan da nan saiga ‘yan gidan sun fara zarya zuwa,itakam widad batasan ma me akeyi ba,don tana labor room private room da aka bata,basu sukabar asibitin ba sai sha biyu na dare,aka bar anty halima da anty deena.

    *_A R U B U C E T A K E_*

    K’arfe takwas na safiyar ranar Allah ya bawa widad ikon haifo santalelen d’a namiji mai kama da abbas SAK!,tamkar yayi kakin yaron ya ajjiye,ko kuma photocopy dinsa akayi yana yaro aka ajjiye,wannan kusan itace kalmar da kowa yaga yaron ke fada

    “Tabdi,wai don Allah a wanne waje wannan yaron yaje ya boye kansa?” Tambayar da anty haleema ta yiwa mommyn muhassana kenan

    “Kin rigani ne a fili,na rigaki a zuci halima,ciki a ido dan qarami amma yaro tubarkalla ma sha Allah?,wacce addu’a kikeyi ne widad?” Widad dake jingine da jikin gado idanunta a lumshe murmushi kawai ta saki cikin jin nauyi,babu abinda take tunawa sai iein gwagwarmayar da tasha,wai dama hakan kowacce mace keji a sanda tazo haihuwa?,amma duk da hakan duniya cike take da ‘ya’ya?.

    A safiyar ranar asibitin yayi wata irin cika da ‘yan uwa da abokan arziqi,duk wanda ke asibitin a ranar ya fahimci lallai haihuwa ce me kima da daraja aka yiwa wannan family,bata wani jima ba suka sallameta bayan sun tabbatar da komai nata lafiya.

    Ita a cikin jikinta take jin wani banbarakwai,idan ta dubi kyakkyawan jaririn mai fuskar uncle abbas dinta taga wai a yanzun danta ne itama,mallakinta.

    *A B B A S*

    Yana tsaye sakiyar parlor din yana saka links din hannun rigarsa,yanayi yana duba agogo gami da dubansu mimi da nawwara da suka sanya yusra a gaba suna mata wasa,su a lallai ga manyan yayye.

    Lokaci lokaci yana kallon qofar kitchen dinta,ya danja tsaki yana yarfe hannuwa,shikam gaba daya yayi dana sanin sanyata aikin ma,da yasan haka zata jawo masa yayi late da da kansa zai shiga ya hada breakfast dinsa yadda ya saba wasu lokutan,ta sani fa yau din zaiyi tafiyar,amma ta kwanta tana bacci abinta babu abinda ya dameta har sai da ya tasheta, just ruwan baqin shayi da soyayyen qwai amma ya gagara ta kammala masa,a lokacin widad ke ransa,yaji wata muguwar kewarta ta saukar masa,sai yake tunanin zaiyi wuya idan bai biya ya taho da ita ba idan ya tashi dawowa daga sokoto.

    Wayarsa dake aje saman briefcase dinsa ta dauki tsuwwa,ya sunkuya ya dauki wayar yana duba me kiran,ya dan saki fuska ganin muhsin ne,jiya jiya suka gama waya dashi,ya danyi mamakin kiran,to amma maybe wani abun ya taso ne,saiya daga wayar ya saka a kunnensa.

    Agurguje suka gaisa ya sanar masa da saqon kiran

    “Ni zan tayaka murna….ko kaine zaka tayani?,…ko duka mu taru mu taya juna?” Dan murmushi ya sake,fararen jerarrun haqoransa suka bayyana

    “Eheen……me ya faru?”

    “Kayi d’a,ni kuma nayi jika,widad ta haihu” unexpected maganar yazo masa,sai ya fidda idanu waje

    “Bama haka dakai muhsin”

    “Kuma yau ba zamu fara ba,ka samu d’a na miji alhmdlh”

    “Allahu akhbar,Allahu akhbar,Alhamdulillah, Alhamdulillah” shine abinda bakinsa kawai ya iya maimaitawa cikin wani irin yanayin madaukakin farincikin da shi kansa baisan adadinsa, uncle muhsin yayi masa barka don tabbas yasan ya fishi cancantar ayi masa barka,ya kuma ce yana jiran goron albishir dinsa sanann ya katse wayar don ya barshi yayi sharing farincikin wa danginsa.

    Wayar kamar zata fadi a hannunsa haka yaji,ya rasa da wa zai fara sharing wannan abun farincikin,sai kawai ya kamo.su mimi ya rungumesu cikin jikinsa yana ta maimaita hamdalar da tun dazu taqi barin bakinsa

    “Daddy menene?” Mimi ta tambayeshi tana kallon fuskarsa

    “Antynku ta haihu yanzu” wani irin tsalle ta buga cikin farinciki tana kallon nawwara

    “Nawwara mun sake samun baby,anty ta haihu,yanzu mun koma mu haka ko daddy?” Ta fada tana daga yatsunta guda hudu,kai ya jinjina mata murmushi yaqi barin fuskarsa,bakinsa kuma ya gaza rufuwa

    “Bari naje na gayawa mummy” tayi maganar tana zame jikinta daga na abbas din,ta kuma ruga kitchen da gudu.

    Ta gama zuba ruwan tea a flask kenan mimi ta fado kitchen din,ta juyo ta zabga mata harara

    “Ban hanaku wannan guje gujen ba?,saikun fadi ku ishi mutane da koke koken banza”

    “Anty ce ta haihu mummy” da sauri ta juyo tana dubanta

    “Wacce antyn?”

    “Antyn nan gidan,anty widad” wata mummunar faduwar gaba da tunda take zata iya cewa bata taba jinta ba banda randa abbas ya sanar mata qarin aurensa ba taji,ta zaro dukka idanunta tana kaiwa bakin mimi bugu

    “Kijimin yarinya da shegen jawowa kai masifa,shashasha wadda batasan ciwo da matsalar ‘yan uba ba,baku da ‘yan uba a cikin gidan nan,kada na sake jin kinyi wannan maganar” dafe bakinta yarinyar tayi duk da Allah ya taimaketa bata sameta da kyau ba

    “Wallahi mummy d……..” Tsawa ta daka mata ba tare data barta ta gama fadin abinda zatace din ba

    “Fitarmin a kitchen masu shegen surutun da zai halakaka idan bakayi wasa ba”(subhanallah,yana da kyau mu dinga iya bakinmu akan yaranmu,komai qanqantar kalma mu kiyayeta mu guji fadarta akan yara saboda tsanani girma da kuma saurin tasirinta a kansu).

    Bin yarinyar tayi da kallo harta fice sannan taja tsaki kamar zata tsinke harshenta,ta kuma juya tana ci gaba da rufe flask din,saidai har a sannan qirjinta bugawa yakeyi.

    Komai ta shirya kan tray,duk da ba wani abun azo a gani bane,amma.bataso takai masa wani abun yace babu kaza ya sake sakata tashi

    “Maimakon ya wuce ya samu eatery akan hanya yayi breakfast dinsa shima” ta fada cikin ranta tana gunguni,har yanzu zuciyarta ba dadi idan ta tuna abinda mimi ta fada,dole ta kwabi yarinyar don kada ma ta sake magana irin wannan,kada wataran ta fada da bakin mala’iku,’yan ameen suna kusa su amsa.

    Cikin tray din ta dauko flask da cups din ta fito daga kitchen din,dai dai sanda suke waya da yaaya bara’atu bayan sun gama waya da hajiya

    “Yanzun ina shirin tafiya sokoto muhsin ya kirani ya gayamin” shuru ya danyi fuskarsa daukr da wani irin murmushi da zai fayyace maka farincikin dake zuciyarsa bazai misaltu ba,ya sake murmusawa sanann yace

    “Eh wallahi…..an samu baby boy”.

    Cak komai nata ya tsaya da aiki na wucin gadi,kunneta yayi toshewar data kasa jiyo abinda yaci gaba da cewa,kalamansa zuwa ga yaaya bara’atu sai taji kamar ba hausa bane wani yare yake daban,sai ta dinga jinta kamar a duniyar mafarki ko kuma daga bacci ta tashi,daga bisani kuma kamar wadda babbar mota tazo ta daka haka taji kowanne sashe na jikinta ya saki,har kwanukan hannunta suka zame suka tarwatse a wajen,qarar faduwarsu da kuma fashewar flask din mai cike da ruwan zafi yaja hankalinsa daga wayar kan wayar da yakeyi,ya miqe da sauri yana katse wayar hadi da furta
    [11/05, 2:59 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 17

    A Rubuce Take Book 2 Page 17

    Part 02

    Page 17

    Sallamar anty ummee ce ta tsinkar mata da zuciya,a sanyaye ta amsa mata,anty ummee din ta shigo idanunta na dan shawagi cikin falon,cikin ranta tana Allah wadarai da halin qazantar ummeen da har yau ta gaza rabuwa dashi.

    “Ya naji gidan shuru,ina yaran?” Ta tambayeta bayan sun gama gaisawa,kamar jira takeyi sai kawai ta sakewa ummeen kuka

    “Ke meye haka?,ai sai a dauka wani abu nayi miki daga shigowata” kamar zuciyarta zata fito daga qirjinta sanda take gayawa anty ummeen damuwarta,sai data gama tsaf sannan ta tabe baki

    “Ai wallahi yanzu yadda kissa ke ci asirin bai isa yayi wannan aikin ba,ke ko masu asirin aida kissar suke hadawa bawai ki tsaya haka sungungum ba,ni ai tunda umma ta gwasaleni saina tsame hannuna,yanzu ki yiwa kanki hisabi,da lokacin da muke kan takunmu da yanzu wanne lokaci ne kikafi samun yadda kikeso?” Shuru tayi tana nazari,ko ba’a gaya mata ba tasan amsar,a wancan lokacin ta samu dukka wata dama da rashin haqurinta yasa ta gaza kaiwa ga gaci ta koma bin malamai,duk da suma nasu aikin tana samun biyan buqata duk kuwa da bamai yawa bace,amma babu jinkiri a hanyarsu,sha yanzu magani yanzu ne(wa’iya zubillah).

    “Nasan kin riga da kin baiwa kanki amsa,to koda zakibi malamai saikin hada da kissa,saboda haka idan kin shirya bismillah,duk da dai yanzun bani da lokaci isashe,muna shirye shiryen tashi zuwa sabon gidanmu,idan na hada hankalina waje daya saimu tsara yadda zamu gyara komai,muga kuma yadda Allah zaiyi”.

    A ranar saita samu walwala sosai,daga ganin anty ummeen sai taji kamar matsalarta tazo qarshe,ta dan jima a gidan,wanda bata fita a gidan ba sai data yagi wani abu daga jikin hafsat,bata hanata ba,don itama yanzu taimakonta take nema,daga qarshe ma sai data bawa dan riqon gidanta dan yayan abbas din key din motar ta ya maida anty ummeen gida.

    Sau biyu tana fitowa tana shige kitchen amma tana ganinsa a zaune inda ta barshi,kusan awa guda kenan yana zaune a wajen,yaran suna kwance daga gefansa sunyi barci.

    Tunda ya dawo ya watsa ruwa ya zauna zaman cin abinci,ta dire masa abincin ta qara gaba,don tun ranar da widad ta haihu haka take masa,zafinsa takeji,saidai ko.sau daya bai taba nuna mata ma ya gane wai fushi take ba,don shidai kaf a abinda ya faru baiga abin yiwa fushi a ciki ba,shi yasa ya tattara ya bawa banza ajiyarta.

    Cikin zafi yake amsa wayar tsahon awa gudan kenan da gurbataccen turanci (brooking),da alama yana magana da wasu cikin yaransa ne akan abinda ya shafi aikinsu.

    Fitowarta ta qarshe daga kitchen din ya sauke wayar a kunnensa bayan yaja tsaki,sau da yawa ire iren abubuwan dake janyo musu bacin suna kenan daga wajen al’umma suke musu kallon abu daya,yanzun ya zama dole ya tafi kaduna a gobe

    “Zoki dauke yaran nan ki kaisu daki” kakkausar muryarsa da amonta babu wasa kwata kwata a ciki ta ratsa kunnenta,saita ratso ta tsakiyar kujerun ta fara daukesu daya bayan daya,shi kuma ya buda warmer din abincin yana qare ma abincin kallo.

    Bacin ransa ya sake daduwa sosai,ya maida murfin ya rufe,ya koma.ya jingina da kujera yana sauke ajiyar zuciya,ya dade da sanin irin muhimmancin widad cikin rayuwarsa,amma nisan da tayi dashi a yanzu ya sake haska masa girman da muhimmancin da take dashi ga rayuwarsa.

    “Idan kinkaita ki dawo” saita tura baki gaba tana cure fuska kamar wadda aka yabawa kashi,tana tsammanin yana buqatar wani abune daga gareta,indai.kuwa hakane yau a jikinsa zata fanshe abubuwa da yawa da ta qudirta,don haka koda takai nawwara sai da taja lokaci sannan ta dawo cikin falon,zuwa sannan ma har ya shiga kitchen ya hada coffe da kansa,don ya gwammace ya shashi ya kwanta akan yaci wannan qaddararren abincin nata.

    Gefe ta zauna tana hada rai, baice komai da ita ba sai daya gama sha ya dire cup din,ya jawo system dinsa dake cike da rubutu yayi saving ya kasheta,sannan ya bude briefcase din gefansa ya ciro kudade ya ajjiye mata.

    “Nasan hajiya ta gaya miki gobe zaku wuce kano suna,gashi nan,kudin transport ne dana amfanin gida,nasan zasu isheki harda ragowa ma” ya qarashe maganar ba tare daya dubi fuskarta ba,sai jakarsa da yake rufewa

    “Ni ba inda zani fa,saboda haka sai sun dawo” wani kallo ya watsa mata bayan ya miqe yana kallon cikin idanunta

    “Ba shawararki nake nema ba,umarni ne na baki, bijirewa magana ta kuma bazatayi miki dadi ba,banason doguwar magana,gobe zaku kano period” ya juya a nutse yana tafiyar nan tasa majestically kamar bashi da sauran damuwa,duk kuwa da cewa qasan ransa bacin rai ne fal,ga na shirmen da aka masa a office ga matsalar hafsa din da har yau babu alamun gyaruwa ko nutsuwa a tattare da ita sam sam.

    Dakinsa ya wuce ya ajjiye jakar sannan ya fara hadawa kansa ruwan wanka a mugun gajiye,abinda baisan dashi ba muddin kwanan widad ne,koda ya gama gado kawai ya haye,sannan yaja wayarsa ya kira widad din don ya tabbatar zai samu relief.

    Ya samu har fiye da yadda yakeso ma,ta sauke masa dukkan wani bacin rai dake ransa,daga qarshe ma video call sukayi ita dashi,ta nuna masa duk wata kwalliyar suna

    “Wannan ai tsomo ni kawai zakiyi,nayi missing……nayi missing sosai,ina da aiki amma banda haka ya kamata nazo naga kwalliyar sosai”

    “Za’a yi maka wadda tafi wannan,kada ka damu,ka maida hankali ga aikinka,wanda na tabbatar muhimmncin da kake bashi shine mabudin dukkan wannan nasarorin da kake samu”

    “Sirrin kuma nasarorin kece ba……nutsuwar da kike bani widad…….I don’t know how to explain it to you,you become part of me”.

    Irin wadan nan hirarrakin dake qara dasa kowanne cikin zuciyar dan uwansa su sukaci gaba da gudana,daga qarshe yace a karbo masa muhammad zai ganshi,dole ta ajjiye wayar duk da yadda takejin kunya don yana hannun ‘yan suna,ta samu nujood ta lallabata ta karboshi.

    Ya jima yana kallon yaron ta cikin video call din sannan ya sauke ajiyar zuciya

    “Bazan iya hana wannan taron sunan ba,amma don Allah….. please na roqeki,ki kulamin da kanki,ki kuma kularmin da yaro na,kada ayita wannan shige da ficen da shi” dariya ma ya bata yadda ya marairaice,kuma yake maganar da gasken gaske

    “Oh…… dariya ma na baki?, seriously madam……am in pain na yadda za’a kallemin ke a gobe,don Allah ki kula”

    “Nifa taka ce,mallakinka ce ta har abada,infact ma saboda kai Allah ya halicci widad,no need ka damu,kayi aikinka hankalinka kwance don Allah” maganganu tayi masa masu kwantar da hankali,dole daga bisani sukayi sallama saboda yadda aketa kiranta daga falo.

    Suna gamawa ya ajjiye wayar yayi addu’ar kwanciya barci,yaja duvet abinsa ko takan hafsat baibi ba.

    Sanda ta gama baqin ran nata tana zaton zai biyota taga bai biyota ba saita shirya ta taho,koda ta iso tuni ya jima da yin baccinsa,abinda ya qara mata baqinciki da takaici,ta kasa kwanan dakin ta rufe masa qofa ta koma nata dakin.

    ********Tun asuba ya shirya ya fice abinsa,bai sake tada mata zancan zuwa kano ba alamun zabi kenan ya rage nata.

    Duk abinta tasan iya lokuttan da take iskancinta,ta sani sarai idan ya kafe bashi da dadi sam,dole ta fara shirin tafiya,bayan ta kira muneera taji qarfe nawa ne tafiyar.

    A ranar sai data fidda kayan sawarta daga cupboard dinta gaba daya amma ta rasa wanda ya dace ta saka,kowanne akwai nashi illar,sutura iya sutura masu tsada,don abbas baya siyan abun banza,saidai idan ita ya bawa kudin ta siya na banza ta soke sauran kudin,wannan kuwa ko ta kanta baya bi.

    Wata rigar tasha squeezing,wata bata ga dan kwalinta ba,wata na buga tsami,saboda an saka an maidata cikin kayan ba tare da an wanke ko an barta tasha iska kafin a maidata din ba.

    Bata taba jin haushin irin abun ba sai yau,so takeyi tayi shiga ta kece raini,amma maimakon taji haushin kanta sai haushin ya tattara akan widad da abbas,kamar dole sai taje sunan?,amma kuma data tuna maganar anty ummee da tace gwara taje ta ganewa idanunta barnar kudin da yayi musu sai taji babu case,taci gaba da bincikawa,da qyar ta dace ta tsamo wata ABC england dark blue,itama a yamutse take,saidai atamfa ce mai laushi cotton sosai,don haka ta fesa mata ruwa ta zauna akai ta samu tadan miqe.

    Duka mayafanta masu tsada da abbas ke siya sanyasu takeyi cikin kayan siyarwarta ta saida,a nan ma da qyar ta samu wani baqi ta dora,sanann ta laluba jaka da takalmi duka ta yamutsa abinta.

    Idan kika ganta zakiyi tsammanin amaryar ‘yar talla ce daga wani qauyen ranar fitowa daga gidan miji na farko,ga jambaki ja ya kama ya haska baqar fatarta data rasa gyara bare tayi kyan da masu duhun fata keyi idan ta samu kula ba tare da canza launin fata,to amma da yake ba saban bace ta fannin ado da kwalliya,sai take ganin ta gama qure adaka,qarfe goma na safe motar da abbas ya sanya ta kaisu kanon ta iso ta dauketa suka wuce.

    Daga ita sai gwaggwo mero qanwar hajiyarsu,sannan muneera yaaya bara’atu,sai gwaggwo fanteka da gwaggwo hassana matan uncles dinsa,da kuma qanwar abbas wadda take binsa nasma.

    Tunda suka dau hanya babu wanda ta kula a cikinsu,saboda kowa fuskarsa babu alamun damuwa ko bacin rai sai ita kadai,har gwara gwaggwo hassana da yake suna da alaqa da ita,takan tabe baki lokaci lokaci ko tayi magana qasa qasa akan tafiyar.

    A can kano kuwa ko cikin family ranar kowa yasan sha lelen ummu ta haihu,gata tako ina a ranar ya nuna kansa,ba daga wajen mommy mahaifiyarta ba,ba kuma daga wajen ummunta ba,ba daga wajen tsoho mai ran qarfe alh salim ba ko mahaifinta Alhj mahmud da Allah ya dorama son jikan nasa,kamar a kansa aka fara masa haihuwar jika ba,ga kuma mai dungurungum din wato DSP abbas turaki.

    Wani kalar suna ake gudanarwa,irin sunan da tsiya da babu suke gudu da qafafunsu, komai a wadace,hatta da almajirai da mawadata ranar sun shaida sunan,tun da sassafe widad ke sanya sutura tana canzawa harta fara gajiya,qarfe sha biyu saiga motarsu hafsat tayi landing cikin tsakiyar harabar gidansu widad??????

    _to mai karatu,ya zata kaya ne?,anya kuwa hafsat ayau zata iya cinye kishinta?,kuzo dai mu rakasu ciki mu gani_??????????????????????????????????????????????
    [13/05, 9:33 am] +234 907 874 7031: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 20

    A Rubuce Take Book 2 Page 20

    Part 02

    Page 20

    A tsaye yake yana fuskantar qofar shigowa falon,hannayensa duka zube a aljihun trouser din dake jikinsa,qananun kaya ne a jikinsa da sukayi matuqar dacewa da lafiyayyar fatarsa da kuma qirar jikinsa dake bayyana halittarsa ta qaqqarfan namiji.

    Tun kafin ta qaraso ya saka hannunsa ya zare baqin gilashin fuskarsa yana qureta da kallo,totally ta sake canza masa,kamar ba widad dinsa ba,a yanzun wata cikakkiyar mace yake gani,wadda komai nata ya cika goma cif cif,kama daga kyan halitta zuwa qirar jikinta,yanayin takunta mai daukan hankali wanda a baya yafi kama da na shagwaba,a yanzun ya zama wani irin taku me aji.

    Itama shi take kallo sanda ta shigo setting room din,uncle din nata ya canza,yadan rame kadan amma fatarsa tayi fresh sosai,manyan idanunsan nan masu matuqar kwarjini da fusgar hankalin suna tsaye kyam a kanta,sai kawai ya bude mata hannayensa,batayi qasa a gwiwa ba ta tafi a tausashe ta fada,ya maida dukka hannayensa ya kulleta gam yana sauke ajiyar zuciya yana rufe idanunsa

    “Welcome back abbas” ya furta da murya can qasa,saita daga kanta sa sauri tana duban fuskarta,dai dai sanda shima ya bude idanunsa ya zubasu cikin nata

    “Back from where?” Murmushi ya saki,ya kama tsinin hancinta yadan riqe sannan yace

    “from an unhappy life to a life full of joy and happiness” murmushi ya subuce mata,tayi juyi me kyau cikin qirjinsa,tana sake tuna kalaman sha’awa da tace indai mijinki yana jin kece rayuwarsa,indai mijinki yana jin bashi da sauran farinciki da walwala sai idan yana tare dake,lallai kincika mace,kin amsa sunan daya cancanci a hada miki da yabawa.

    Matseta yayi gam cikin jikinsa yana sansanarta da kyau,duk sai qamshinta ya ida rikitashi,ya fara kai hancinsa ko ina a jikinta yana sansanawa,kafin Wani lokaci sai ya nemi ya birkice mata gaba daya.

    Itama da qyar ta saita kanta,tadan tureshi tana cewa

    “Uncle,gidan surukanka kake fa” dauke fuskarshi yayi daga inda ya boyeta cikin jikinta,yana dan jan hancinsa kamar me mura,ya lalubo nutsuwa da qyar ya azama kansa

    “Oh…..haka…..ina fata kin shirya tafiya” noqe kafada tayi

    “Uncle,ban gama shiryawa ba,da saura fa” kai ya girgiza,ba zai iya tafiya ya barta ba a yau din,don shi kadai yasan yadda yakeji,shi kadai yasan irin azbtuwar da yayi watannin data dauka basa tare

    “Pack your stuff we will go home,ko mu wuce a kawo miki kayan daga baya” duk yadda taso ya bari ko zuwa dare ne amma yaqi,dole hajjaa ta kira uncle muhsin a waya ta gaya masa zasu wuce

    “Har sai an gayamin banda abinki?, shi da matarsa?,tunda ya tako da kansa yazo ya gaza haquri zuwa randa sukayi dashi ai kinga akwai dalili”

    “Amma uncle,akwai abubuwan da ba’a gama hada mata ba ko.kayanta ma bata shirya ba”

    “Kinga please stop it……ta bishi kawai,koma meye a aika mata dashi daga baya,tabar hada kayan sawar nata nujood takai mata su gobe ko jibi” hakanan aka bi umarnin uncle muhsin din,sukayi sallama sun cika da kewar affan tun kafin ma su qarasa barin gidan.

    Sanda suka isa gidan lawal ne ya buda masa gate yana masa sannu da zuwa,daga haka ya saka kai zai bar wajen,sai abbas din yayi kiransa,ya sanyashi debe dukka kayan da suka shigo dasu,yadan rusuna ya gaida widad,ta amsa tana mamakin yadda yau ya gaidata din ma,don dan dakin hafsat ne,ba wani magana bace take hadata dashi ba wanda ya wuce gaisuwa,gaisuwar ma da sai idan sunyi clashing sosai ba yadda zai wuceta.

    Ba kowa a gidan dama sai mai gadi,sai kuma lawal din da yana shirin fita suka dawo,don haka bayan ya fice gidan sai ya sake zama shuru.

    Tare sukayi aikin komai da komai,suka gyara part dinsa sannan suka koma suka gyara nata.

    Cikin lokaci kadan gidan ya koma fes,iska mai dadi hade da wani lallausan qamshi ya shiga kai kawo,ta gyarawa affan kwanciya saman dan qaramin gadonsa da abbas yasa aka hada masa,sannan ta fidda kayanta ta shiga wanka.

    Tana gama zare towel din jikinta ya tura qofar toilet din ya shigo,ta waiwayo a hankali suka hada idanu,kowa ya kafe dan uwansa da kallon nan mai cike da shauqi da wata irin qauna mai fusgar hankali tare da kewa,ya zame idanunsa a hankali ya saukesu kan qirjinta,wani abu ya jashi kamar lantarki,sai ya gaza ci gaba da tsaiwa a wajen,ya shigo ciki sosai,ya maida qofar toilet din ya rufe.

    Kayan jikinsa ya fara zarewa,har yanzu idanunsa yana kanta

    “Bari nayi joining dinki,ruwanki yafi nawa dumi da qamshi” ya fada yana fidda qaramin murmushi hadi da kashe mata ido daya.

    Kafada ta maqale a shagwabenta,kamar dai widad din nan da aka kawo masa lokuttan baya da suka shude wadda batasan komai ba

    “Allah uncle wayo dai,iri daya na hada mana fa,kaje toilet din naka ka dub……” Bata qarashe ba ta tsinceta manne da jikinsa,abinda ya kusa sanyata shidewar numfashi saboda yadda fatar jikinsu ta hadu guri guda,daga nan bakin dukkansu ya mutu ita dashi,wani irin feeling mai qarfi ya dinga kewaya cikin jini da zuciyarsu,sai gashi gaba dayansu kowa ya birkice tsananin ita dashi,wankan da ba’a ida gamashi ba,suka zarce zuwa gadonta daya samu kyakkyawan gyara.

    Kai tsaye zata iya kiran ranar da second first night dinta,don sai komai ya zame mata sabo kamar bata haihu ba,taci wuya a hannunsa,har shi kansa ya shaida hakan,tana rungume tsam a jikinsa,kwanyarsa cike fal da tunani,dama ana samun hakan bayan d’a ya tsaga jikin mace ya fito?,lallai da gaske mata suna suka tara,kamar yadda suka banbanta a abubuwa da dama haka suka banbamta ta wadan nan guraren.

    Sati guda sukayi a bauchi suna bare wani amarcinsu,irin amarcin da a baya ma bai sameshi ba,a yanxun ya samu fiye da abinda yakeso,ya samu fiye da yadda yake zato,ya kuma samu fiye da abinda yake tsammani,gaba daya widad din ta gama zama cikakkiyar mace ta kowanne fanni,yana samun fiye da abinda yake buqata daga wajenta,bata fannin kwanciya kadai ba….. a’ah,ta kowanne fanni ma ta cike masa dukka wani gurbi.

    Wannan yayi matuqar tasiri a rayuwarsa da zuciyarsa,ta sake shiga ransa da wani irin matsayi mafi girma da yakejin kaf kafin duniya a yanzu babu diya macen data takashi.

    Randa suka cika kwanaki bakwai ranar suka tattara suka wuce kaduna,kai tsaye kuma ya zarce da ita sabon gidan da ya kama mata,ya kama haya ne saboda bashi da tabbacin zasu yita zama a Kaduna,koda yaushe yanayin aiki yana iya canzashi daga kadunan zuwa wani gari na daban.

    Yayi mata ba zata matuqa,al’amarin kuma da ya faranta mata rai fiye da zatonsa,ko ba komai zata samu sakewa,ta rabu da wata matsalar,zata kuma tattara hankalinta ta kula da mijinta da kuma yaronta yadda ya kamata,gida ne two bedroom,kowanne da toilet a ciki,kitchen parlor da kuma dining area,sai madaidaiciyar harabar da zata iya dauke motar abbas din,yayi matuqar tsaruwa gidan,dole ya burgeka,an shirya komai bisa mizanin hankali da ilimi.

    *H AF S A T*

    Batasan cewa zata damu ba da gidan da widad ta koma din ba sai bayan ta koma din,tunda ita da kanta ta zaba cewar ba inda zata motsa daga nan gidan da suke,saidai ita widad din ta qara gaba ta barta,tunda itace babba,babu mai cire gwamnatinta.

    Murmushi kawai abbas ya saki sanda take wannan bayanin cike da izza fariya da kuma alfahari

    “Gwamnatinki saidai kuma wata,mai guri yazo mai tabarma dole ya nade abarsa” abbas ya fada cikin ransa,yana matuqar tausayin hafsat din amma ita sam bata tausayin kanta,yana hango mata rasa abubuwa da dama cikin rayuwarta amma ita bata gani,Allah ya sani,ko ra’ayin auren mata biyu baya dashi,ko meye ya faru tamkar itace ta bashi lasisin aikata hakan.

    Widad kam cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta tsara gidanta ta kuma ci gaba da tafiyar dashi,cike da qwarewa da kuma gogewar da take sake samu daga mutanen dake tare da ita,cikin ikon Allah ta hadu da maqota na qwarai,macace mai matuqar karamci dake kallon widad din kamar qanwarta,jininsu ya hadu qwarai tashi guda,wannan ya sanya widad din taja babbar ‘yar matar da ba zata wuce shekara sha daya ba a jiki,aminatu yarinyar nada matuqar hankali,ta iya komai ita kewa mamanta ayyuka da yawa,amma yawan alkhairan widad a garesu ya sanya maman tabar mata ita,rainon affan da sauran ‘yan aikace aikace ita take mata,wannan ya sake bata nutsuwa a zaman gidanta,tana dame debe mata kewa kuma ta rage mata ayyuka,saita samu cikakken lokacin tsara duk wani abu da zai faranta ran abbas ya kuma sake zaunar da ita a ransa.

    Gidanta yana dab da wajen aikin abbas,wanda ko a qafa zai iya takawa ya qaraso gidan nasa,abu na farko kenan daya soma hana hafsat sukuni,ta dinga tunani kala kala,a duk ranar kwananta bata da kwanciyar hankali harma ranar da ba tata ba,tana ganin a yanzu widad din ta fita samun kusanci dashi,kamar ko yaushe suna tare,kwata kwata a lokacin tunaninta bai bata hakan zai iya kasancewa ba,kawai a sannan tanaso ta nunawa widad ta koreta daga mazauninta ne don ta isa,ita kuma ta maye gurbinta,daga iya haka tunaninta ya tsaya.

    *F I T S A R I N F A K’ O*

    Tunda ta dawo kusa ya daina cin abincin rana a ko ina sai gida,idan ayyuka sun masa yawa sai ya aiko yaransa su daukar masa,idan kuma ya samu chance da kansa yake dawowa yaci abincinsa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ya koma,wani lokaci ma idan akayi sa’a aminatu ta fita da affan ko suna dakinsa sai ya more lokacinsa sosai sannan yake komawa din,a wannan lokacin ya samu wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali daya jima bai samu irinta ba,don har wata qiba da murjewa ya sakeyi,gaba daya hafsat da matsalolinta ya sanyasu a mala,dai dai da abincinta ba damuwarsa bane yanzu,ita kanta ta lura da wannan sauyin daya sake daga mata hankali matuqa,har take ganin widad din ta fara aiki a kanta ne da ‘yan tsubbu don ta janye hankalinsa daga kanta,ko sau daya a tsukakkiyar qwaqwalwarta bata taba shawartarta ta duba inda ta gaza ta gyara ba.

    **********Tunda ya sallameta a safiyar dazu data fita a girki ranta yake suya,komai nata yanzun ya koma yana shakulaton bangaro dashi,ta kalli inda ta ajjiye masa gantalallen breakfast din da ko ta kansa baibi ba ranta yana sake baci,zuwa azahar ta gaza daurewa,bayan mimi ta shirya kanta ita da nawwara ta zubasu a mota ta ajjiyesu a islamiyya duk da ba ita ke kaisu ba,sai kawai ta dauke kan motar tata tayi hanyar police college.

    [15/05, 6:22 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 23

    A Rubuce Take Book 2 Page 23

    Part 02

    Page 23

    Wankin kai da qunshi akayi mata,haka suma yaran duka,sunata murna don ba’a taba musu gyara da lalle irin wannan ba,bata wuce awa biyun ba ta dawo,koda ya dawo gidam ya samesu da gyaran bai kawo komai ransa ba,tunda yasan dama already ita kullum cikin gyara take ta saba (qalubale gareki, keda bakya komai sai sallah ko idan zakuyi biki ko wani sha’ani na taro ya kama,mai gida har ya gane hakan,yara suyita tambayar umma unguwa zamu?,umma biki za’a yi,ba lalle ba gyaran kai babu kitso).

    *******Karfe hudu na yammacin washegari tayi wata kyakkyawar shiga cikin wani tsadajjen crystal swarovski lace,duk inda ta motsa ko ta gifta daddadan qamshi ne yake fita daga jikinta da wani irin qyalqyali mai daukan hankali.

    Ta nutsu ita daya daga can bakin gate,ta yadda abbas data kirashi gida urgently bazai gane abinda ke faruwa cikin gidan ba har sai ya shigo.

    Daga waje ya kashe motar,ya bude ya fito ya kulle yana kallonta cikin mamaki,tace yazo gida yanzu yanzu,yazo kuna ya tarar da ita cikin ido me narkar da zuciya da idanunsa

    “Wow……amma kin kyauta da kika kirani naga wannan kwalliyar kada nayi missing nata” ya fada yana murmushi,batace masa komai ba sai kama hannunsa da tayi suka shiga cikin gidan.

    Mutuwar tsaye yayi sanda yaga yadda aka maida harabar gidan nasa kamar wani event center,har yaushe akayi hakan bayan fitarsa daga gidan duka duka bai wuce awa uku ba,ko ina ya daga kai manya banners ne masu dauke da hotonsa cikin full police uniform a tsaye,da wasu rubututtuka na nuna murnar tayashi qarin samun promotion da yayi,ga family saman kujeraru da shigowarsa ta saka kowa miqewa yana masa maraba,a lokacin wani irin sassanyan abu yaji yana tsarga masa akan widad din

    “Ya rabbb,wacce irin yarinya Allah ya azurtashi da ita?”

    “Surprise?” Ya fada yana sauke idanunsa a kanta yana lumshesu cike da wani irin shauqi,saita jinjina kai lallausan murmushi yana kubce mata,shima kan ya jinjina,ya kuma kama hannunta da kyau cikin nasa ya fara takawa zuwa ciki suna riqe da hannun juna ya nufi yan uwa dake dakon isowarsa don a gaggaisa kafin a fara ciye ciye na abinda aka tanada a wajen.

    Cikin wani yanayi me kyau da qayatarwa aka kammala taron lafiya,abu yayi masifar qayatarwa,ya burge masoya, abokan adawa kuma da masu taya hafsat kishi kamar su mutu

    “Yar qanqanuwar yarinya ta iya kidifiri da iyayi,ta kora sa’ar uwarta uwar gida cikin yaranta gida tazo tana shimfida abinda taga dama” ire iren abinda su gwaggwo hassana da gwaggwo fanteka suke fada kenan,saidai babu bakin cewa komai saidai gulma daga gefe,hakanan kuma sukaci suka sha suka watse.

    Sai data tabbatar an sallami kowa harabar gidan ta barwa su shazali zasu qarasa gyarawa sannan ta dawo cikin gidan duba yaran,tasan bata da matsala don suna tare da aminatu,tare suka taho wannan karon.

    Aminatun kam akwai hidima,ba qyuya sam,harta sake musu wanka,affan da nawwara sunyi bacci,ita da mimi ne kadai suna kallo a ipad din widad da abbas din yabar mata kwanan nan,don dama itace bata da ita,hafsat nada tata duk da ta bari yara sun tsoma tatan a ruwa.

    Bayan ta tabbatar sunci abinci sai ta dauki affan tayi musu sai da safe,don ta gaji tubus,ta kuma ji shigowar abbas din tun kusan dazun ma tana waje tana sallama da mutane.

    Tana tura qofar suna hada ido,waya yake amsawa,da alama kuma mai tsaho ce,don haka ta daga masa hannu kawai,ta ajjiye masa affan ta kitchen ta hado musu baqin shayi me kayan qamshi sosai,don ya koya mata itama,sanann ta wuce toilet ta hada ruwa mai zafi tayi wanka.

    Daure da towel ta fito,fatarta sai sheqi takeyi,ya ajjiye wayar gefe ya miqa mata hannunsa,batayi qasa a gwiwa ba ta miqo masa nata hannun,yayi mata mazauni saman cinyarsa yana sansanarta,yana bala’in son qamshinta,ba qaramin burgeshi yakeyi ba

    “Sannu da hidima madam” murmushi tayi tana saqalo wuyansa da hannunta

    “Kaine da sannu yallabai,don dukka aikinka ne wannan” da mamaki ya daga kai ya dubeta,don dai shi yasan sisinsa babu a ciki,hasalima baisan zata shirya ba sai daya shigo gidan.

    “Aikina kuma?” Gira ta daga tana murmushi

    “Sosai,mun samu kyakkyawar kulawa daga gareka,ka sauke dukkan wani haqqi naka dake wuyanmu,wanann yasa har a cikin zuciyata naji ka cancanci fiye da haka ma,donma ni din ba wata bace,da fin haka naso ya kasance” cikin jikinsa ya qanqameta yana cusa kansa tsakanin qirjinta,abinda ya sanya tsigar jikinta tashi,ya sauke mata zazzafan numfashin da dole ta riqe kansa da hannunta tana ‘yar dariya

    “Ji nakeyi kamar na maidaki cikina na boyeki,zuciyata har wani irin zafi takemin saboda sonki” yana kaiwa nan saiji tayi ya watsata saman gadon ya kuma maye gurbin towel din jikinta.

    Washegari ta tsinci alert a wayarta da sunan mijin nata har na naira million daya,ta sameshi a bayan gidan shi daya da wasu takardu data tabbatar ayyukansa yake,da alama za’a baza komar kama wani mai laifi ne

    “Yallabai kudinka sunyi batan kan shigowa account dina fa,da saninka?” Takardun ya aje gefe,ita daya duk duniya yakema haka idan yana aiki irin wannan

    “Zonan” yace tana bata hannunsa,saita qaraso din ta zauna

    “Ba batan kai sukayi ba,sun shiga inda ya dace ne,nawa kika kashe jiya.” Fararen idanunta tadan juya kadan

    “Bazance ba,amma dai bazai wuce three hundred thousand ba” kai ya jinjina

    “Kice duka tattalin arziqinki kika kwashe” saita saki dariya,kome zata bawa abbas din batajin zatajishi a matsayin asara

    “To yayi,kudin dana tura duka naki ne,inason ki zauna kiyi tunani ko kiyi shawarar sana’ar da kike sha’awa,inason ki fara kasuwanci cikin gida” sosai ya bata mamaki kamar yadda itama ta bashi mamaki jiya,ta sauko saman gwiwoyinta ta fara masa godiya,ya kamata ya tayar da ita

    “Ban miki komai ba,saboda ke din kin bani komai”

    *H A F S A T*

    Kai kawo taci gaba da yi,wayar hajiya habiba tana hannunta,duk hoto daya da zata bude tashin hankali ne yake sauko mata mara adadi,kamar ta hadiyi zuciya ta mutu,abbas dinta mijinta da kuma yaranta,duka under control na widad,wacce irin asara take shirin tafkawa?.

    “Nidai gaskiya kin bani mamaki,am totally disappointed wallahi,ni duk sai kunya ta kamani ma da naga irin abinda akeyi a wajen,sai lawal ne ya bani address na gidan nan,shima yana daga gefe takaici ya isheshi,don dai bashi da yadda zaiyi ne”.

    Kananun qwalla ce suka kubcewa hafsat,tana jin tata ta qare,duk wani abu da zatayi akan widad tayi amma jiya iyau

    “Aah,ai kuka bai ganki ba,mafita ya kamata ki nema” komawa tayi ta zauna,don gaba daya jikinta babu sauran qwari ko karsashi

    “Meye ma banyi ba,kissar nayi babu ci,malaman nabi amma sai abun yayi kamar zaiyi tasiri saiya wargaje” murmushi haj habiba ta saki

    “Malamai kika bi ko muna malamai?,hajiyata kiqi kudinki kizo na kaiki inda zaki mori kudinki,kissa kuma iri iri ce hakanan iyawa ce,ki fita batun yarinyar koda an miki aiki yayi,ko agabansa ki dinga nuna bata gabanki shine kawai”

    “Wallahi na shirya,ko nawa zan kashe a shirye nake,ai ranar biyan buqata rai ba’a bakin komai yake ba” murmushi ta saki

    “Gwara da Allah ya ganar dake ai” (hmmm,kodai shaidan ya batar da ita,Allah yasa mufi qarfin zukatanmu,muje dai zuwa masu karatu,aci gaba da haquri,so nake mu sauke dukkan darasin dake ciki,saboda labarina yafi rinjaye da true life story)
    [17/05, 7:35 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 21

    A Rubuce Take Book 2 Page 21

    Part 02

    Page 21

    Riqe yake da hannunta gam cikin nasa,yana sauraren shagwabarta da ‘yar qaramar muryarta mai taushi,murmushi ne yake fita kadan kadan daga saman fuskarsa,har bayason ta dakata daga magiyar da take masa, sosai muryarta take masa dadi,ta narke masa sosai,ita kano takeson zuwa,shi kuma baya jin zai iya barinta a yadda yakejinta cikin rayuwa da zuciyarsa a yanzun tayi nesa dashi.

    Wata farar long sleeve blouse ce a jikinta fara sol,sai mini side button skirt a jikinta mai tsaga daya baya shima fari sol,ta kame gashinta mai tsaho da sulbi a tsakiyar kanta,jikinta ba abinda yakeyi sai fidda tattausan qamshin turarenta daya hade da kabbasar da takewa kowanne kaya nata da mabanbantan qamshin turare.

    Tuntuni ta gama haddace yadda yake mutuwar son yaga tayi shigar qananun kaya,wannan ya sanya ta mayar dashi al’adarta,don zata iya cewa ba zata iya tuna sau nawa ta saka atamfa kace ko material a jikinta ba muddin tana cikin gidan,walau ran girkinta ko ba ranar girkinta ba,har ya riga da ya zame mata jiki,hakanan fararen kaya na mugun yi mata kyau,da yake kuma ya hadu da mace mai tsafta idan ta saka saika dauka kowanne sabo ne bata taba sakashi ba.

    Gidan ba kowa shi yasa ta baje masa tabararta sosai,har yaji kamar bazai iya komawa gurin aiki ba,dama cin abincin rana ya dawo dashi,affan yana wajen aminatu,tun daxun gab fa zata gama abincin rana ta goyashi suka shiga gidansu.

    Waiwayowa yayi,har yanxu murmushi na bisa fuskarsa yana dubanta,sai ya zare hannunsa daga nata

    “Baby……wallahi kinason yau nayi satar kwana kenan,da irin wannan shagwabar taki zan kasa kaiwa yayarki kwananta fa” kai ta girgiza tana dan bubbuga qafa

    “Nidai ba ruwa na,abinda nace kawai inason naje kano,sanya ranar Aafiya za’a yi fa”

    “Ba yanzu ba baby…..idan bikin ya taso dai zakije” jikinsa ta shige tana fadin

    “Don Allah…..don Allah” dai dai sanda aka angizo qaramar qofar dake jikin gate din gidan aka shigo.

    Idanuwanta a kansu,zuciyarta na wani irin bugawa,wannan shine karo na hudu da zuciyarta ke raya mata yana gidan yarinyar,kuma idan tazo din take cimmasa,bata taba kuskuren zuwa bata sameshi ba.

    Waiwayawa sukayi gaba dayansu suna kallonta,widad ta janye idanunta tana jan tsaki can qasan ranta,ko daya bata sani ba,bata kuma gane dalilin wannan safarar da take musu a gida ba,bayan ita tunda tabar gidanta bata sake koda marmarin taka qafarta ba,idan ta shiga unguwar ma,mutanen da sukayi zaman arziqi tajewa jaje ko taya murna,daga nan kuma bata qarawa ko ina take dawowa gida abinta,duk da tanason ganin mimi amma haka take haqura.

    Dage tayi sosai,ta mannawa abbas din kiss a goshi a tausashe sannan tace

    “Allah ya kiyaye hanya,im gonna miss you baby” ta danyi rolling idanunta hadi da daga masa hannu,taja baya a hankali tana takawa zuwa cikin gidan,da gayya take juya mazaunanta da kyau,duk kuwa da cewa koda batayi hakan ba salon tafiyarta ne dake tafiya da abbas din ainun.

    Tare sukabi bayan nata da kallo shida hafsat din,nashi kallon na zallar qauna tare da jin wani iri,kwana biyu kawai da zaiyi ba tare da ita ba sai yakejinsu kamar shekara dubu,duk da zai leqota a qalla sau biyu a wuni kafin ya tashi a office,yayin da kallon hafsat ke cike da wani mugun baqin kishi,wanda a wannan lokacin inda zata samu dama tabbas saita nakasta wannan surar da akemata barazana da ita.

    Kasa jure ci gaba da kallonta tayi,sai take ganin kamar taqi sauri ta shige falonta ne da biyu,ta maido dubanta ga abbas din,saidai gaba daya hankalinsa baya kanta,kamar ma ya manta a inda yake tsaye,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,har taji ba zata iya magana ba,sai kawai ta juya da mugun sauri ta koma cikin motarta,wadda ko kasheta batayi ba saboda tsabar sauri ta shiga ta rufe murfin da mugun qarfi,taci ribas ta fice daga layin.

    Qarar buga murfin motar ne ya dauki hankalinsa,ya juya yana kallon qurar data tayar,sai a sannan ma komai ya dawo masa,yaushe sukayi da ita zata fita?,ya gyada kai ransa na mugun sosuwa,ya taka yana fita a gidan ya nufi tasa motar don ya koma office.

    Gudu kawai take shararawa a hanya,sauran masu ababen hawa dake bin hanyar sunata binta da kallo,wasu na kaucewa wasu suna Allah wadai da ita,kuka takeson yi amma idanunta sun soye,a bisa qa’ida ai ya shiga lokacin girkinta,karo na hudu kenan tana ganin irin haka,dama wannan shine dalilin da ya sanya ya canza mata gida ya kaita kusa da office dinsa?,zaizo zasu hadu,yau din saidai kowacce wacce.

    Batasan abbas din ya fita bacin ran fitar da tayi ba tare da izninsa ba,ba kowanne sakarci yake dauka ba ko kuma ya qyale,tunda suke da widad koda wasa bai taba kamata da laifin yin leqe bama bare har takai ga fita,fitarma irin tata mara tushe bare ma’ana,tunda me tazo yi gidan widad din a wannan lokacin?,abinda ta saba?,bin qwaqwafi da bin diddigin yarinyar da ta haifeta?,bai taba jin widad tayi zancanta ko ta damu da lamarinta ba,amma ita ko yaushe damuwarta widad,ko yaushe qorafinta yana kan widad din,sai yaushe ne zatayi hankali?,yaushe zata gyara halinta?.

    Lokacin da ya koma gida baibi ta kanta ba,hidimarsa ya shiga yi da yaransa,hatta da abincinta ma bai nema ba,ya shiga kitchen ya dafa musu wani bayan ya tambayi yaransa me sukeson ci.

    Banza ya bawa ajiyarta suka baje a qasan carfet da yaran suka hau cin abincinsu,kamar ma baisan da wanzuwarta cikin falon ba.

    Ta sake cika tayi fam kamar zuciyarta zata fado saboda yadda take mata ciwo,cikin sa’a za’a ce ko rashin sa’a mimi tace

    “Mummy ke bakyacin abincin?”

    “Zan tsinka miki mari,aiba a yunwace kika ganni ba ko?” Sauke idanunsa yayi a kanta a nutse,sannan ya motsa labbansa

    “Tashi kibar nan gurin” a dan fusace ta kalleshi,amma a kallo dayan ta karanci bacin ran dake kwance cikin qwayar idanunsa,saita miqe da wani irin qarfi tana kade jikinta,amma kuma ya dakatar da ita ta hanyar cewa

    “Ki miqomin key din motarki yanzun nan” ya bata umarni nakai tsaye ba tare da ya ko dubeta ba

    ” a mamakance ta juyo tana kallonsa,amma ko kallon inda take baiyi ba,ta dauke kai ta jinjina sannan ta taka zuwa ciki,ta dauko key din ta dawo ta ajjiye masa ta wuce daki wasu hawaye masu zafi suna qwace mata.

    Koma wanne karin magana bahaushe yayi akan kishiya,koma meye aka fada akan kishiya tabbas ya dace da ita,wasu baqaqen dabi’u da halaye da batasan dame zata kwatantasu ba abbas din ya koyo,saidai koma meye ita ba zata taba bari widad din taga faduwarta ba.

    *_A N K U M A M A C E T A H A I F I M A C E inji bahaushe_*

    Watan affan bakwai dai dai wanda yayi dai dai da samun qarin matsayin abbas din ya sake samun wani promotion din daga DSP(deputy Superintendent of Police) zuwa SP(superintendent of police) din gaba daya,wani irin ci gaba da budi yaketa samu tako ina wanda bai zaci samunsa haka a kurkusa ba.

    Randa aka saki signal sunansa ya fito widad din na falo a kwance,sanye take da wata armless chiffon gown,yatsunta na hannu da na qafa sunsha jan lalle jajir gwanin sha’awa,basu jima da dawowa daga wankin kai ba ita da aminatu,ta dauki affan suka fice sai ita kadai a gidan,gashinta mai tsaho santsi da baqi yayi kyau sai sheqi yakeyi,wannan gyara ne daya zame mata jiki jiddin zaka sameta cikinsa.

    Yau din ba ranar girkinta bane,sai a gobe zata karba girki,amma ta gama shirya tarbar abbas din tun a yau din,ta gama komai,zuwa yanzun yadda abbas din keyi a kanta ya daina damunta,ta riga ta saba,ya zamar mata jiki,hasalima tausayi yake bata,don ta tabbatar inda yana samun kulawa yadda ya kamata daga wajen hafsat itama zata samu sauqin wani abun,to amma ita daya ce ke iya kashe masa qishirwar komai,ita kadai ke tsaye a kansa take samar masa nutsuwa da kwanciyar hankali.

    Tunda ya duba sunansa yaga ya fito yaji har cikin jiki da zuciyarsa ita yafi dacewa ta fara sani,a nutse yake tuqa motarsa bakinsa dauke da hamdala da godiya ga Allah fili da badini,don yayi masa dukkan wata baiwar da rufin asiri,kuma dama a rayuwa baka taba samun komai cif cif dari bisa dari.

    A kofar gidan ya kashe motarsa sannan ya fito,yasa key ya buda gidan yana sanya kai,yau gaba daya aiki ya sashi a gaba,ko zuwa ya dubasun da yakeyi baiyi ba sai yanzun da ya samu break,amma da yake gwanar alkunya ce tare da yi masa uzuri,da sukayi waya ita ta fara bashi uzuri ma kafin ya bata.

    Lumshe idanunsa yayi sanda ya tura qofar falon,sassanyan qamshin nan na kullum da kullum dai shine a falon cakude da sanyin ac da aka daidaitashi dai dai da buqatar dan adam.

    A duniya gidanta ne waje na farko da yake fara saukar masa da nutsuwa a rayuwarsa,bazaiqi ya dawwama a cikin gidanta ba kaf rayuwarsa,yasan bazai rasa komai ba,ba kuma zaiyi kuka da Komai ba.

    Tana daga kwancen ta daga fararen idanunta masu girma ta.kalleshi,ta sakar masa murmushi tana miqewa daga kwancen ta zauna tana dubansa

    “Welcome home sir” tsaiwa yayi ya moqe kafadarsa kamar qaramin yaro yana kallonta

    “Ban yarda da wannan qwangen da akeson yimin ba” saita miqe da sassarfa ta isa gareshi,ya buda mata hannuwansa kamar yadda suka saba ta fada jikinsa,ya maida hannun ya lullubeta gam cikin qirjinsa yana sauke ajiyar zuciya,kamar yaron da yayi kuka ya qoshi

    “Alhamdulillah ala kullin ni’am…….na samu promotion,now am SP abbas” wani irin qanqameshi ta qara yi cikin wata siririyar qara

    “Seriouse abbin affan?”

    “Da gaske nake sarauniyata” ya fada a tausashe yana shafa sumarta da taja hankalinsa sosai,qamshin jikinta kuma yana neman birkitashi,yana jin yadda bugun zuciyarta ya qaru saboda murna,zamewa tayi a jikinsa ta kama hannuwansa dukka biyun,ta dinga jera masa addu’ar samun nasara tare da fatan alkhairi mai yawa a rayuwarsa,har sai da qwalla ta cika idanunsa,zuciyarsa ta tabu sosai.

    Mutum daya…… mutum daya ke tsaiwa tayi masa irin wannan,hajiyarsa,zayaso ace yau tana raye taga abinda ubangiji yaketa yima rayuwarsa.

    “Zan samu abinci madam” ya fada yana langabe mata kai,a gabanta kawai yake komawa hakan,inda zaka ganshi a fagen aiki zaka dauka bashi bane.

    Kafada ta noqe tana tura baki gaba

    “Girkin mummyn mimi ne fa daddyn mimi” girarsa ya daga

    “Yes i know….amma kinsan banason cin abincin waje baya ina da mata har biyu,gida kuma yanzun yamin nisa,infact ma abincinki nakeson ci,in kuma ba za’a bani ba to shikenan” ya fada yana komawa kamar wani abun tausayi,dole ya sanyata ta saki wata shagwababbiyar dariya

    “Ni na isa na hanaka abinci?,zauna sosai na zubo maka” tayi maganar tana miqewa,saiya riqo hannunta ta baya,ya kashe mata ido daya

    “Zafi nakeji,hadamin ruwa nadan watsa tukunna,yau aiki zai riqeni inajin har wajen isha” kai ta jinjina masa,saita sauya akalarta zuwa bedroom dinsa ta hada masa ruwan kamar yanda ya buqata sannan ta fito ta gaya masa ta wuce kitchen.

    Tana tsaka da shirya masa abincin taji yana kiranta,ta ajjiye warmer din ta fito.

    Tana tura qofar toilet din unexpected kawai taji an fincikota,ko kula dashi ma batayi ba,bata zame ko ina ba sai cikin bathtub,ta jiqe jalaf har saman kanta,tabi jikinta da kallo sannan ta waiwaya tana kallonsa ta gefe,don tuni ya mata masauki cikin jikinsa

    “Daddyn mimi……”

    “Shshshs…..”ya fada yana dora yatsantsa saman labbansa

    “Karkice komai,minti biyar kawai zakiyi ki tafi,ba abinda zan miki,kawai ina buqatar ki a jikina kamar haka” bata iya masa musu a wannan bangaren,saboda tasan koda ransa bai masa dadi ba bazai nuna mata ba,uwa uba kuma tasan ba inda zai samu hakan sai wajenta,saita lumshe ido kawai ta jingina da jikinsa.

    Sun kusa mintuna goma a haka sannan ta samu ta zame,haka ta fita da kayanta suna diga,sai data shiga bedroom dinsa sannan ta ciresu,ta dauki bababn towel dinsa ta daura ta nufi qofar fita don ta koma nata bedroom din ta saka wasu kayan.

    Gabanta yayi mummunar faduwa sansa ta bude qofar dakin,don kwata kwata bata tsammaci ganin mutum cikin falonsu ba,ta kafeta da idanu wani bacin rai yana taso mata,ita din wacce irin dabba ce?,don ta wuce a kirata mahaukaciya,haka kawai saika buda gidan mutane ka shigo babu sallama babu komai?,ba neman izini kamar naka gidan,yau kuwa zata nuna mata ta fita hauka da danyan kai,idan akace ta sake zuwa mata gida ba zata qara ba,saita fasa shiga nata dakin,ta tako a hankali ta nufi gurin tv dake aiki.
    [15/05, 6:22 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 9

    A Rubuce Take Book 2 Page 9

    Part 02

    Page 09

    Yana zaune saman kujera sanye da uniform din nan nasa dake qara masa kyau da kuma kwarjini,ko boots din qafarsa baikai ga cirewa ba,hafsat na tsaye daga gefansa,hannayenta goye a qirjinta,fushi ne kwance saman fuskarta.

    Idanunshi a kanta,wani abu daya kasa tantance meye yana tsinkulin zuciyarsa,mabanbantan abubuwa guda biyu daketa faman gogayya da juna,har ta iso ta zauna gefan kujerar dake daura dashi tana masa sannu da zuwa.

    “Me ya hadaki da hafsat…..har kikayi mata rashin kunya?” Maganar tazo mata a bazata,mamaki ya kamata,ta dubi hafsat din suka hada ido,sai hafsat din ta aike mata da saqon harara,ta daure ta shanye sanann tace

    “Ni bansan yaushe nayi mata rashin kunya ba”

    “Kina nufin bakisan maganar kayan da kika kwashe ba?” Ta tambayeta kamar wata diyar cikinta,sai abbas din ya daga mata hannu

    “Ya isa…..me yasa kika kwashe kaya da aka dawo dasu daga laundry?” Cak ta tsaya ta zuba masa idanu,mamaki yana kasheta,duk yadda taso hana taruwar qwalla a idanunta amma ta gaza,saita gyada kai tana hadiye wani abu mai tauri daya tsaya mata,cikin rawar murya ta fara masa bayani

    “Baba mai gadi ne ya kawo su,tana.bacci yace a kwashe maka kada yara su tattaka,don ma debe shine nayi laifi?,ina cewa kusan kaso uku cikin hudu na kayanka suna dakinta a wajenta,na taba magana?” Sosai ta taba zuciyarsa yadda hawaye ke sauka saman fuskarta,tana kuma maganar muryarta tana rawa cikin sautin kuka,yanason yace ta tashi taje,tayi dai dai amma kuma kamar ana ingiza zuciyarsa,kamar kuma ana hura masa bacin rai haka yakeji.

    “Tashi kije ki debosu!” Yadan fada a kausashe,idanunta ta sanya cikin nasa mamaki yana sake daskarar da ita,totally uncle abbas din canzawa yakeyi cikin kwanakin,ba yau ya fara ba amma na yau yafi qona mata rai da tsaya mata a rai,ba yau ya fara ba,cikin kwanakin ko meye hafsat din tayi gaskiya yake bata,yana kuma qoqarin goyuwa da bayanta,sai ta miqe tsam cikin matsanancin bacin rai,ta dauke idanunta daga kansa ta maida ga hafsat,sai taga tuni yanayin fuskarta ya sauya zuwa madaukakin farinciki.

    Janye idanunta tayi daga kan fuskokinsu gaba daya,ta kuma juya da sauri ta nufi dakinta, abbas ya rakata da idanu yana jin kamar ya bita amma kuma wata zuciyar na gaya masa yayi dai dai,sai yaci gaba da kallon qofar da kuma tsammanin fitowarta.

    Cikin bacin rai ta fara tattara dukka wani abu da tasan nashi ne cikin daki,bata bar komai ba koda kuwa agogo ne,tana hade kayan hawaye na fita a idanunta,ta tsani rashin gaskiya,ta tsani a bata rashin gaskiya a rayuwar ta,ta tsani batayi abu ba ace tayi,tana jin kamar ta mutu idan akayi mata haka.

    Debo kayan ta fara yi hannu bibbiyu,ba ruwa ta da wadanda suke zubewa ta riqosu zuwa falon,tana zuwa batayi wata wata ba ta watsar dasu a wajen ta juya da sauri taci gaba da debo sauran tana zubarwa a wajen,ran hafsat ya sosu sosai,wanne irin raini ne wannan?,ta tsammaci zaice wani abu,sai taga bai ko motsa ba yana kallonta ne kawai,yana karantar zallar fushin dake fuskarta,wanda bai taba ganin irinsa ba a tattare da ita ba

    “Wai baka ganin abinda yarinyar nan takeyi?,kaga fa yadda take watso mana kaya?” Maganartata yayi da gama kwaso kayan,ta juya abinta da nufin komawa dakinta

    “Widad” ya kirata a tausashe,bata ko waiwayo ba bare ta saurareshi,don kuka takeyi sosai ta wuce daki abinta.

    Cikin qarfin ikon Allah ya miqe da wani irin zafin nama,zuciyarsa yaji kamar zata fashe da kukan da widad din keyi,ya tuna meye a jikinta,ta yaya zai barta tana irin wannan kukan?,sai ya nufi dakin da wani irin sauri wanda yasa hafsat ta zaci zuwa zaiyi yayi maganinta,ya dauki mataki akan abinda tayin yanzu,don haka ta saki wata qaramar dariya cikin nishadi da jin dadi,ta tako cikin rashin damuwa ta fara tsince kayan tana dibansu zuwa dakinta,sai a sanann ta lura da mimi dake sharar qwalla

    “Ubanki kike a wajen?,wato an saka uwarki kuka shine kikazo kika rabe a nan kina naki kukan,zaki tashi ki wuce ciki ko sai nayi ball dake?” Ba shiri yarinyar ta zame ta wuce daki tana tura baki gaba hadi da ci gaba da goge qwalla.

    Rub da ciki takeso tayi kukanta yadda takeso ko zata rage zugi da radadin da zuciyarta ke mata,amma tudun da takeji a cikinta ya hana,dole sai saman pillow ta dora fuskarta tana sakin kuka sosai.

    Jiki a matuqar sanyaye ya qarasa shigowa dakin,sai ya kasa qarasowa ya tsaya daga bakin qofa yana kallonta,shi kansa baisan me yake damunsa ba,baisan me yasa yake wasu abubuwan ba,duk da abinda yakeyi din bata taba nuna damuwarta ba,koda ta nuna mintuna kadan take sakin fuskarta kamar ba’a yi ba,sai ayau data nuna fushinta har haka.

    A nutse ya qaraso ya zauna gefanta,tunda ya buda mata qofar daki tana jinsa amma bata nuna tasan da shigowarsa bama,hannu yasa a tausashe ya zare pillow din ya maye gurbinsa da tattausan tafin hannunsa,sai tayi saurin kawar da fuskarta daga wajen kamar ya dora mata wuta,yasan halin kayarsa,ta iya rigima a duk sanda taso ko aka tabota,don haka yayi amfani da dukka qarfinsa ya azata saman jikinsa.

    Dukka qarfinta ta sanya ta zame a jikinsa,bai gaji ba ya sake maidota yana kiran sunanta tare da qoqarin son su hada idanu amma taqi bashi wannan damar.

    Kin zama tayi bare ta saurareshi ba,haka ya gaji da son yin magana da ita ya haqura ya fice yana sauke ajiyar zuciya,ransa gaba daya a jagule babu dadi.

    Da kanta ta lallashi kanta,saidai a ranar ta yiwa kanta hukunci qauracewa abbas din da dukka abinda ya shafi hafsat dama cikin gidan,ba zata iya gani ba bazata iya jura ba,duk jarumtar ta abun ya taba ranta,tana iya bakin qoqarin bashi farinciki da son ganin walwala da nutsuwarsa…..gefe guda yana bawa hafsat go ahead tayi duk abinda yake shine dai dai,yana kuma mara mata baya,ta yaya ita tata zuciyar zata samu nutsuwar bashi nutsuwa?.

    Washegari ranar girkinta ne,tun safe tana kwance a dakinta wanda tun dare ta saka muqulli ta rufe abinta,tana da abubuwan ciye ciye da yawa a dakinta da bata rabo dasu,don a lokacin abbas da ya shafe babin fita da iyalinsa zuwa wasu guraren shaqatawa a baya,a yanzu widad din ta dawo masa da wannan dabi’a tasa,ko rana daya hafsat din bata taba yunqurin binsu ba,sai mugun haushi da takaicin da take fama dashi,har zuwa sanda zasu dawo cikin gidan,takan ce ita tafi qarfin zuwa nan wajen.

    Zamu iya cewa borin kunya ne takeyi,don tun sand yake marmarin kaita take watsa masa qasa a ido,take nuna tafi qaunar ya bata abinda za’a kashe a wajen ta adana,har abun ya fita a kansa,ko ssnda ta haifi su mimi yana son kaisu amma bai samu wannan qwarin gwiwa daga wajenta ba,don haka sai a jima bai fita da yaran ba sai sanda ya samu hutu mai tsaho,gaba daya ita din opposition na rayuwarsa ne totally,bata kuma taba sawa a ranta ta sauya wani tsari yanayi hali ko dabi’a tata saboda shi ba,saboda a samu dai daito da zama me dorewa.

    Tana jin motsinsu daga parlor din amma bata ko motsa ba bare tayi yunqurin fitowa,ciye ciyen da tayi a daki ya dauketa fes,don dama bata iya cin abinci me yawa,yana zaune dining area amma hankalinsa yana kan qofar dakinta,jiya da abun ya kwana dashi ya tashi,duk kuwa da yadda hafsat din keta qoqarin mantar dashi da wasu salo da sam baibi jikinta ba bare ya dace da ita,don ba dabi’arta bane.

    Ya kammala shan tea din da babu qamshin komai a ciki saina Lipton da milo,ya ajjiye cup din ya miqe yana sauka daga wajen,hafsat din na zaune tana kallonsa batace komai ba,tanason ganin ya za’a qare,ya isa qofar dakin nata ya tsaya a nutse ya fara knocking yana amsa wayar data shigo masa a lokacin.

    Taso ta shareshi taqi bude qofar,saboda Wani mugun zafinsa da takeji har cikin ranta,amma sai taga hakan bai kamata ba,tunda tasan a lokacin kowa yana parlor,ta kuma tabbatar hafsat din tana ganin komai da zai faru,don haka ba’a son ranta ba ta miqe a hankali tana gyara zaman yaloluwar rigar jikinta ta zura bedroom slippers dinta ta nufi qofar.

    Tana bude masa ta saki qofar ta koma,yabi bayanta da kallo tsigar jikinsa tana zubawa,ko kadan baya gajiya da ita,baya qosawa da ita,kwanaki biyun da basu tare mugun yunwar ta yakeyi,yaci gaba da kallonta yana dan hangen cikinta daya turo kadan,wanda sai ka saka ido da tsananin kula zaka iya ganinsa.

    Guri ta samu ta zauna ta gaidashi ba tare data kalli fuskarsa ba,yanata qoqarin su hada ido amma taqi

    “Ya jikin naki?”

    “Lafiyata qalau” ta amsa masa a shashance,ya sake duban fuskarta sosai yadda taketa basarwa,sai ya ajjiye mata kudin cefane yayi mata sallama ya fice.

    Dashi da kudin gaba daya tabi da kallo, zuciyarta ta tsinke kuka yaso qwace mata amma ta danne,ta kalli agogo sannan ta miqe ta shiga bandaki ta watsa ruwa,ta fito taa shirya cikin dinkin doguwar ruga bubu gown ta yane kanta da madaidaicin mayafi ba tare data daura dankwali ba,fuskarta tayi kyau,ta sake wani fresh da haske mai daukan idanu,inda ya ajjiye kudin cefanen ta isa ta dauki kudin,sannan ta qarasa inda wayarta take ita dauketa tare da daukan wasu abubuwan masu amfani sannan ta fito falon.

    Babu kowa,sai ta zarce kitchen,ta dan samu abinda zataci wanda bazai mata wahalar narkewa ba,don yanzun matsalar da take fama da ita kenan.

    Ta gama ta dauraye cup din ta maidashi inda ta dauko tana kallon yadda kitchen din ya hargitse,kamar ba kwanaki biyu baya ya koma hannun hafsat din komai fes bisa tsari,saika dauka watanni aka dauka ba’a gyarashi ba.

    Baki ta tabe ta fice abinta,yau daga kitchen din har Parlor din babu inda zata sama hannu,itama tasan dadin jikinta,kawai dai tanayin komai ne don samun walwala da nutsuwarsa,tunda ta fuskanci babu abinda ke daga masa hankali a rayuwa irin qazanta,amma tunda bai gani itama ba zata dinga wahalar da rayuwarta ba,zata barsu shida hafsat din tasa.

    Tana isowa falon sukaci karo da mimi

    “Ina kwana anty?”

    “Oyoyo mimin daddy,kin tashi lafiya?”

    “Lafiya lau anty,yau duka baki fito ba”

    “Banajin dadi ne,ungo wannan ki kaima mommynki kice kudin cefane ne inji ni” ta hada dukka kudin da abbas din ya bata ta sanyashi a hannun mimi,sai da taga ta shiga dakin sannan ta fice abinta harabar gidan.

    Kai tsaye boys quaters ta nufa wajen maari matar baba mai gadi,sosai taji dadin ganinta kuwa,don bata taba zuwan mata ba,ko yaushe widad din tafi ganewa zamanta daki tayi kallo ko chart,ta marabceta sosai suka fara dan taba hira,tun widad din bata sake ba har ta saki jikinta suka shiga hira sosai,kasancewar hajiyan bata nan,babu wani aiki cikin gidan haka suka wuni tare.

    Maari din saita tuna mata da latifanta,cikin awanni kadan ta gane tana da kirki matuqa da jan mutum ajiki,har tafi tsohuwar me aikin hajiyan data dinga tayata kwana sanda abbas yake tafiya bauchi ba tare da ita ba.

    Tayi musu faten tsakin masara da yasha gyada da yakuwa,batayi zaton zata iya ci ba,sai gashi taci sosai sunata hira,kirkin widad da yadda take girmama kowa cikin rashin nuna qyama ya sanya maari ma taji ta shiga ranta,ba kamar hafsat din ba,dake dagawa izgilanci da wulaqanta na qasa da ita.

    Hafsat na tsaka da barci taji mimi na qwala mata kira saman kanta,da qyar ta bude idonta tana jan mugun tsaki,kafin daga bisani kuma ta buda hancinta sosai saboda warin bayan gida da take jiyowa,dole ta wartsake ta miqe sosai ta zauna tana duban mimi

    “Ban hanaki idan ina bacci ki dinga tashina ba don ubanki?” Kebe fuska yarinyar tayi kamar zata saki kuka

    “Ai ban tasheki ba harma su nawwara sukayi kashi,yanzunma anty ce tace na kawo miki kudin cefane”

    “Kudin cefane kuma?”ta tambayeta da mamaki,saita jinjina kai,ta miqa mata hannu ta saka mata kudin,ta waresu tana irgawa.

    To me yarinyar take nufi?,nufinta ta ajjiye girki kenan saboda abinda ya faru jiya?,aiko ba zata sabu ba,ita dinma ai ba jaka bace da zata zauna tayita girka musu suna ci.
    [08/05, 4:58 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 19

    A Rubuce Take Book 2 Page 19

    Part 02

    Page 19

    Hafsat ce a wani birkice sanye da hijabi ruwan qasa,fuskar nan cike taf da bala’i,tun sanda ta dawo taji sunyo gida da abbas din hankalinta yatashi,kullum fatarta da addu’arta yarinyar ta tafi kenan,sai gashi ta dawo rayuwarta tsundum

    “To mayya natacciyar dole,da kika tashi dawowa ai saiki jira girki yazo kanki,bawai ki biyomin miji kihau aikin da ba naki ba” sosai maganar tata tayi mata ciwo,kamar ba zata tanka mata ba,amma saita dago daga gyaran throw pillows din da takeyi ta kalleta

    “Maita da naci ga miji inajin isace wannan,wadda bata isa ba ko tayi babu riba,mukan da mukeyi alhmdlh akwai riba, miji kuwa babu wata rana da na kebe da zan tsame hannuna daga bashi kulawa saboda na girkina bane muddin yana da buqatar kulawata,ke meye ya hanaki tsaiwa ki bashi kulawar idan har kin damu dashi?” Ta fadi kanta tsaye tana kallon idanun hafsat da mamaki ya kasheta.

    Turqashi!,anzo wajen,yau ta samu dama,tanajin babu abinda zai hanata cin uban yarinyar yau abinda ta jima tana buri,kamar widad din ta karanci hakan,kuma bataso tayi abinda zai tada abbas di daga bacci,don haka tayi hanyar kitchen da dan saurinta

    “Dawo mana qaramar mara kunya kiga yadda ake yinta yau a fidda raini” hafsat ta fada tana bin bayan widad,dama abinda widad din keso kenan,don haka tadan daga qafa,tana shiga kitchen din ta tsaya tana ajjiye plate din hannunta,dai dai sanda hafsat ta qaraso ta dora hannunta a kafadar widad da nufin damqota.

    Tankwabe hannunta widad tayi cikin fushi tana kallonta

    “Sakeni,karki sake gigin riqeni,idan raini kikeso a fidda ki bari ya gama baccinsa ya fita a gidan ya zaman dagani sai ke,a sannan zan nuna miki cewa jaa da baya ga rago ba tsoro bane,shashasha wadda har yau batasan ta girma ba” ta dire maganar da tsaki mai mugun qarfi.

    Tsananin mamaki ya sanya hafsat din mutuwar tsaye tana kallon widad,cikin fushi ta yunquro a karo na biyu kafin tace komai widad ta rigata yin magana

    “Kika sake kika dora hannunki a jikina…. wallahi tallahi sai nayi miki wanka da wannan ruwan zafin,sauna kawai,shashasha”tayi maganar tana fidda manyan fararen idanunta waje a kan hafsat din.

    Abu makamancin wannan bai taba hadasu da wida din ba,don haka furucinta ya tabata sosai,sai taja da baya tana tafa hannuwa

    “Ashe da ‘yar kalare nake zaune?,dama kanawa ‘yan sara sukane mazanku da matanku?,to shi wanda ya baki daurin qarqashin yimin rashin mutuncin bari na tasoshi” saita juya tana haramar fita a kitchen din.

    Ai widad bata barta takai qofar ba ta sanya hannu ta fincikota saiga hafsat warwas a qasa,ta isa bakin qofar kitchen din ta tsaya riqe da qugunta

    “Azzaluma mara imani,wanann baccin dai yau sai ya yishi wallahi duk baqincikinki da baqin halinki” sai kawai taja qofar kitchen din ta kulleta aciki,bata da wata hanyar fita kuma saidai tabi ta qofar baya ta kitchen din ta fice,saita isa qofar part din nasa shima ta kulle,sannan ta saki ajiyar zuciya tana jan tsaki a ranta.

    Sam ta daina ragawa matar,zata nuna mata ita din bakanuwa ce,duk da ba jininsu bace amma kuma cibiyarta na bunne anan,tana jjn surutanta da zage zagenta sama sama har ta daina ji,da alama tabi ta qofar bayan ta fice.

    Yayi bacci kuwa sosai,don bashi ya tashi ba sai dab da magariba,a sannan widad din tayi wanka a nan sashensa ta sauya shigarta da wani sky Blue din material me kyau,ta daure kanta da band ta kuma dora dan yalolon mayafin material din,affan na kwance daga gefe cikin farar overall yana bacci abinsa shinfide cikin farin towel.

    Tunda ya fito yaga dukansu sunyi masa kyau uwa da dan nata,karon farko da ya fara ganin mai jego mai tsafta irin haka,abinda bai saba gani ba,idan hafsat na jego idan kaji ana jaga jaga ko itace,duk wani kalar qarni da bashi bashi zaka jishi,idan anyi magana takance jego take,dama wannan ai shine jegon inji hausawa,sallamawa sassanta dama yakeyi gaba daya,saidai tazo nashi da ziyara ta wuce.

    Ta daga kai daga wayar dake hannunta tana duba saqonnin watsapp suka hada ido,ya sauke mata murmushi yana jin zuciyarsa tana yin sanyi,ya samu nutsuwa kaso hamsin cikin dari daga qunci da rudanin da zuciyarsa ke ciki,ya durqusa a hankali yayi kissing affan dake baccinsa cikin qauna, qamshin da jikin yaron keyi ya ratsa hancinsa,ya daga kai yana sake kallonsa

    “Kullum kamanninmu da muhammad sake fitowa takeyi” ya fada da sassanyar muryarsa,ta saki dan murmushi

    “Sosai…….kun nunamin son kai ai” ta fada tana dan masa hararar wasa,sai ya saki murmushi yana cewa

    “Ba komai,next time by now ya samu yaruwa,ita na tabbatar zatayi miki karar” ido ta fidda sosai tana kallonsa sannan ta langabar da kai

    “Habba mana uncle…..” Kai ya jinjina yana tarar numfashinta

    “Yes…..inason yara da yawa babyn uncle,mutuwar hajiya tasa naji ina son in tara yara masu yawa sosai,just pray Allah ya bamu nagari da zasuji qanmu”sai ta jinjina kai tana cewa

    “Ameen”.

    Bai fita sallar magariba ba sai da yaci abinci ya sake wanka,kafin ya dawo ta sake gyare komai,ta budade falon da qamshi yadda zai masa dadin zama.

    Sai da akayi isha’i ya dawo,ya zauna a falo suna taba hira,yana kan kujera tana zaune a qasa,qafarsa saman cinyarta tana matsa masa qafafunsa a hankali cikin wani salo da ya sake saukar masa da nutsuwa,kamar an jehota saiga hafsat ta sake shigowa falon tana kumbura.

    Kallo daya widad tayi mata ta dauke kai kamar batasan Allah yayi ruwanta ba a wajen tana ci gaba da tausawa abbas qafarsa,yayin da abbas din ya tsirata da idanu yana kallonta ba tare da yace komai ba

    “Daddyn mimi,zuwa nayi na gaya maka ka jawa matarka kunne sanna kayi mana tsakan……..”

    “Dakata da Allah”ya fada da kakkausar muryarsa yana daga mata hannu

    “Bana buqatar wata hayaniya ko tashin hankali,idan ba zaman lafiya bane ya kawoki ba….. please stay away from here” yadda yayi maganar yana nuna kamar ta gundureshi yasa ranta ya quntata sosai

    “Adalcin da zakayi kenan?,ba zaka tsaya kaji abinda akayimin bama…..dama kaine kakar daure mata gindi shi yasa kullum take kallon mutane sa’aninta,to wallahi……”

    “Shut up” ya miqe tsaye a zafafe yana nuna mata hanya

    “Fita banason hauka” hawaye ne suka balle mata

    “Yanzu a gabanta kakemin haka abbas?,na rantse da Allah……” Wani mahaukacin mari yakai mata wanda widad ta tabbata inda ya sameta saita rasa haqoran gaba,Allah ya taimaketa ta goce,ba shiri ta juya tana fita daga falon,hannunta dafe da kuncin nata cikin kuka kamar wadda marin ya sameta.

    Hannunsa cikin kana ya zauna yana yamutsashi,ya samu ciwon kan ya ragu amma tana neman maido masa bara bana,miqewa widad din tayi tayi mazauni gefans kamar zata shige jikinsa,da kalamai da hikimomi data koya ta samu nasarar saukeshi,ya dinga sauke ajiyar zuciya yana matsa hannunta dake cikin nasa,ba shakka mace ta gari rahama ce,inda bai samu widad din ba ashe da haka zai qare rayuwarsa cikin wahala da baqinciki?.

    A daren tason ya barta ta kwana sashenta ta kira hafsat din ta kwana tare dashi,tunda ita din na abinda zata iya masa amma yace bata isa ba,muddin ta tafi ranta sai ya baci,shiba wani abu yake buqata ba a situation din da yake ciki ba,koda batayi masa komai ba kasancewarta a damansa yafi komai kwantar masa da hankali.

    Kwanan daga fuskanci widad din tayi ya sake ingizata sosai,wutar qiyayya ta sake ruruwa a zuciyarta,ranar tayi kukan fili tayi na boye,ta kuma tsinewa duk wata kishiya dake duniya.

    Washegarin da akayi addu’ar bakwai suka shirya komawa kaduna bakin aikinsa,yabar widad a nan don ta gama arba’in dinta,taso komawa kano amma muhsin yace tazo kenan,dan tsoho alhj salim ya goya masa baya,hakama abbanta,don dole ta zauna a nan,amma ta koma gidan hajjaa ne saboda yadda gidan har yau yake bata tsoro.

    ********To sannu a hankali kwanaki suka ci gaba da tafiya,al’amuran rayuwa kuma sukaci gaba da gudana yadda suke a baya,duk da ciwon rashin hajiya yana zukatansu,amma dole a yadda da hukuncin ubangiji a kuma rungumi rayuwa a duk yadda tazo.

    Zamanta gidan hajjaa taci gaba da samun kulawa,tana kuma sake gogewa da rayuwa da sanin makamarta.

    Sanda sukayi arba’in affan yayi wata qiba gwanin sha’awa,yaron kamar ka saceshi ka gudu saboda kyau da wani kwarjini da yake dashi,farat daya yake shiga ran kowa,hakanan itama widad din,kana kallonta zakasan lallai girma da hankali ya soma gameta,ta samu hutu da nutsuwar rai sosai a tattare da ita,ta zama wata big madam,ta kula da jikinta da kyau ciki da waje.

    Ranar da sukayi arba’in ranar abbas da yammaci ya diro,da safen sunyi waya da tace masa basuyi arba’in ba sai jibi,saboda batason yace mata zaizo,akwai abubuwan da takeson qarasawa,to ashe yana lissafe tsaf da kwanakin.

    Dariya nujood ta dinga yi mata sanda aka saukeshi a setting room,tana zaune dafa’an a qasan carfet sanye da wata riga me qaramin hannu mai kama jiki kamae robber,sai palazzo pants daya zauna mata sosai ya kuma bude yadda ya kamata daga qasa.

    Harara ta watsawa nujood din ta miqe tana cewa

    “Karki bari aji kanmu dake wallahi” tayi maganar tana zare ribbon dinta da yayi sakwa sakwa tana gayara gashinta,duk da cewa itama taji dadi qasan ranta,don ba qaramin kewarsa tayi ba,to amma kuma taso ta kammala komai ne

    “Bani nakar zomon ba” ta gama gyarawa tsaf ta duqa zata dauki affan nujood ta rigata tana cewa

    “Rufa masa asiri,kada a jawo masa a matse dan bawan Allah,ku gama gaisawar tukunna sai na kawo miki shi” ta fuskanci jan magana nujood din keji,sai bata sake ce mata komai ba ta juya ta fice.

    [14/05, 12:25 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 8

    A Rubuce Take Book 2 Page 8

    Part 02

    Page 08

    Bai jima yana kira ba aka daga,suka gaisa cikin yanayi na sanin juna,sannan yayi mata bayanin dalilin kiran nata idanunsa akan widad da dukka ta sauya lokaci daya tayi wani laushi,idanunta cike da tsoro.

    “Indai cikin yakai watannin da zaiyi motsi ai zaiyi dama,hakan kuma alamu ne na cikin lafiyayye ne,watansa nawa?” Kai ya girgiza

    “Bansan watanninsa ba”
    Dan murmushi ta saka mai sauti

    “An gaisheku gaskiya,ina ganin gobe ka kawota asibitin sai ayi mata scanning da komai da komai,har EDD dinta sai mu gani,amma kace mata kada ta damu,babynta ya fara rayuwa sosai cikin qoshin lafiya ne” godiya yayi mata ya ajjiye wayar,ya saka hannayensa a aljihun uniform dinsa daya kasa cirewa tun shigowarsa gidan, idanunsa a kanta yana sakar masa murmushi,duk da cikin tsoro take amma hakan bai hanata basar dashi ba,zata miqe ya kamo hannunta da sauri ya sakata cikin jikinsa yana sansanarta kamar wata ‘yar mage,yunqurin tureshi takeyi amma yaqi bata dama

    “Ka koma wajen hafsa kawai” ido ya fidda yana dariya

    “Yau kuma?,hafsa zalla?”

    “Eh sunanta ne ai” ta fada tana dan murguda bakinta,har qasan zuciyarta tana jin kishi yana tsunkulinta,juyo da ita yayi suna fuskantar juna

    “Yanzu dai na gane,kishi ne kikeyi,to ayimin afuwa” kafada ta maqale

    “Ni ban haqura ba,saidai idan zaka kaini na siyo ice cream” kai ya girgiza bayan ya fidda ido

    “So kike ki debarwa babyna sanyi?,bayan dr tace da alama lafiyayye ne?” Fuska ta kwabe ta langabar da wuya,yadda tayin tilas tasa yace

    “Shikenan ki shirya,amma yau kawai” cikin farinciki ta amsa masa,tuni har ta manta komai ta fara shiryawa,shi kuma ya fara rage kayan jikinsa don ya shiga ya watsa ruwa,wanda already ta hada masa,yana shiryawa shima yana tsokanarta akan cikin,ita kuwa kunya takeji,saida tayi masa kamar zatayi kuka sannan ya qyaleta.

    Sai da qafafunta suka gaji da tsaiwa bata sake jin komai ba,uwa uba da taga lokaci yana matsowa na fitarsa zuwa masallaci,dole taja jikinta tabar gurin tsakanin kokwanto da rashin tabbas na samuwar matsala a tsakaninsu,saita koma dakinta tabar dan space tana leqensa,har ya fito daga dakin tsaf dashi ya wuce masallaci yana baza qamshi,saita koma bakin gadon ta zube tana riqe da kanta,idan akwai abinda ta tsana a duniya shine taga walwala da zaman lafiya na gudana a tsakaninsu,dole ta sake kashewa tsinanniyar yarinyar kudi,dole ta sake aiki a kanta.

    Sai da yasa yara suka kirata sau uku akan ta fito suci abincin dare sannan ta fito,dai dai lokacin da widad ta fito daga kitchen dauke da babban try data zuba.

    Kofta(ire iren abincinsu ne na ‘yan yemen da ake sarrafashi da nama).

    Hafsat din na shirin zama sai taji qafafuwanta zuwa bayanta ya sage,da qyar ta danni zuciyarta ta zauna zuciyarta na wani irin tuquqi da suya,wannan zallar cin fuska ne kawai abbas din yaso yi mata,banda haka ta yaya zai kirata cin abinci jikin yarinyar da wadan nan kayan?,duk kuwa da cewa ta dora wata ‘yar kyakkyawar farar riga mai budadden gaba,amma hakan baikai ga boye dukkanin adonta ba.

    Da ido kawai take bin abincin,sunata walwalarsu tsakaninsu,abbas din yana tsokanar mimi widad na tare mata,ta gama serving kowa suka fara ci a nutse.

    Har qasan zuciyarsa yakejin nutsuwa tana saukar masa,ba shakka lafiyayyen abinci mai daddadan dandano ma rahama ne a rayuwa,bashi ba,hatta mimi ta soma santin abincin,abun ya taru.ya yiwa.hafsat yawa,duk yadda qamshin abincin ya karade falon yake tsinkar da yawu amma sai taji ya fice mata aka,ta ture plate din ba tare da tace komai ba ta saba yusra a kafadarta,tana gyara zaninta daya tattare.

    Sai da yakai lomar kufta din bakinsa sannan ya daga kai a nutse ya dubeta

    “Ya haka?,ina zuwa?”

    “Bazan zauna a nan ba tarbiyyar yara na ta lalace ba,don ba wajen zama bane,ta saka wasu kaya fingil fingil yarana suna zaune suna kallonta?,ke nawwara……mimi ku tashi muje” ta fada a tsawace,haushin yadda yaran ke wasoson abincin yana sake qureta

    Bata fuska dukkaninsu sukayi,saboda sudai suna jin dadin abincin sosai

    “Mommy ki zauna kici,da dadi wallahi” mimi ta fada fuska a narke,abunda ya sake hasala hafsat din ta kwaza mata tsawa,sai abbas din ya daga mata hannu

    “Kinga ya isa,jeki abinki ke daya” yadda yayi maganar tayi mugun baqanta mata,nan da nan hawaye suka cika mata idanu,sai ta girgixa kai kawai tayi gaba da sauri hawayen nason subuce mata.

    Ko tunata babu wanda ya sakeyi,abunda yayi masifar baqanta mata rai kenan,don tayi tsammanin zai biyo bayanta kamar dazun,saidai a maimakon haka ma sai tashin motarsa da taji,koda ta fito Parlor din wayam babu kowa,saita zauna anan hawaye na qwace mata,ya wankin hula yake shirin kaita dare?,saita miqe zumbur ta koma dakinta tana lalubar wayarta.

    Cikin kwanakin girkin widad din gaba daya hafsat ta tsangwami kanta,ta rasa nutsuwa bare sukuni,bata daki bata falo,komai widad din zata aiwatar idanuwanta suna kai,hakan ko kadan bai damu widad din ba,don zuwa yanzu ta fahimci meye ma’anar kishiya da abinda zamansu yake nufi ita da hafsat din,ko daya idanunta bai sanya widad din ta fasa duk abinda ta saba yi ba,hasalima yi tayi kamar bata gane ba,kamar dai har yau wautar quruciyan ne ke dibanta,abinda ke masifar hargitsa hafsat din,tana ganin kamar abbas din yana biyewa duk abinda takeso ne,yana kuma fifitata a kanta,wannan ya sanya ya ta sake cin alwashin wargatsa komai da lalata duk wani farinciki na widad din kota tsiya kota tsiya tsiya,sam ba zata gajiya ba.

    Ta gaza shuru ta gaza haquri da yadda yarinyar ke gudanar da komai kamar wata babbar mace,cikin kwanakin komai na gidan tsaf yake a kammale,bata bari komai ya lalace ko a barshi wasarere,tun daga cikin kitchen zuwa parlor dinsu,duk kuwa da yadda hafsat din keta qoqarin ganin ta watsa komai,widad din taja yaran a jiki,ta koya musu yadda zasu bar waje da kyansa bai lalace ba,ta koya musu koda sweet suka sha inda zasu saka ledan,abun ya yiwa hafsat din ciwo,tayita jaraba tana fadan su yar amma qememe sai suqi,kada ma mimi taji labari,maganar anty widad awajenta kamar fadar Allah,hafsat tayi dukan tayi banbamin ta hanata zuwa duk inda take amma kamar turi,abun ya soma taruwa yana mata yawa,ta rasa inda zata taro,yaran ko abbas din?,dole ta zauna ta fidda kudi sosai ta turawa ummanta,tana hasashen samun mafita.

    *******Yammaci ne lis,inda suke zaune cikin falon ita da yaran suna kallo,duk da cewa girkin hafsat dinne,amma ko alamun shirin dora girkin dare batayi ba,hasalima tana daki kwance abinta.

    Hakan gaba daya ba damuwar widad bane,don dama da qyar take kaiwa labari da abincin hafsat,wani irin girki mara tsari mara fasali kuma,sam ko a ido bashi da wani qayatarwa bare kakai ga bakinta,Allah ya bata wani irin kurman ciki da har yanxu ya gaza nunawa a jikinta,saidai can cikin jikinta tana jin wasu sauye sauye da ita kanta tasan wani muhimman al’amari ne yake tunkarota,takan zauna tayita lissafin scanning din da dr tayi mata,wai cikinta watanni shida harda kwanaki,ta sha ganin ciki amma itadai ba haka taga ana ciki ba,tasha tsayawa gaban madubi amma bata ganin komai idan ba turoshi gaba tayi sosai ba,duk da yana motsa mata sosai amma yabi jikinta da kyau,ya qarawa breast dinta cika ne sosai,abinda ke matuqar daukar hankalin abbas kenan kamar zai zauce mata.

    Waya ce a hannunta tana duba wasu sabbin recipe da Chief deeja Berver ta basu,tana yi tana murmushi,saboda yadda take fahimtar komai kamar a gabanta akeyi,har ya fada hasashen yaddaa gobe zata tashi kan gidan da nau’in kalolin sabbin girke girke.

    Taji qarar bude qofad sarai,amma bata ko kalli bakin qofar ba,don tasan wacece,sai taci gaba da duba wayarta kawai ba tare da tako motsa ba.

    Idanuwan hafsat din a zube fes akanta,ko wacce rana tana kwana ta tashi da mamakin yadda yarinyar ta gaza tabuwa,duk kuwa da kudin data kashe akanta,sai wata ‘yar qaramar nasara data samu,wadda har yau wannan nasarar bata gamsar da ita ba,don bata ga wata alama ta shiga damuwa ko qunci daga wajen yarinyar ba sam,duk kuwa da cewa a yanzun tana iya juya wasu abubuwa na gidan,wanda a kwanaki ko watannin baya bata isa ta juyasu ba.

    “Ke mimi….. nawwara,uban me kuke zaune kukeyi a nan?” Ta jefawa yaran tambaya tana zare idanu a kansu,cikin tsoron kada ta hanata zama mimi ke kallonta,yayin da nawwara tayi qirmisisi abinta

    “Baba me gadi ne ya kawo kayan abba,yanata buga qofa shine na bude masa”

    “Da kika bude masa kuma sai kika samu waje kika zauna?,ina kayan suke?”

    “Suna dakin anty widad”.

    Wani abune yazo ya tsaya mata a rai,ta kalli widad da har yanzu bata kalleta ba koda sau daya,miskilancin yarinyar yana qona mata rai,tanaso tayi mata cin mutunci wasu lokutan,amma bata kulata ma bare ta bata dama

    “Ke…..ki tashi ki debo kayan wankin abbansu ki kawomin nan” cak ta tsaya da danna wayar,saita daga kai a hankali karon farko ta kalleta,daga samanta cukurkudadden gashinta data daura dankwalin atamfa,zuwa jikinta dake sanye da rigar atamfar da wuyanta ya yima yawa,ta sauko ga fallen zaninta wani kalar atamfar daban.

    Kamar zata fashe da dariya amma kuma bacin ran da take ciki ya zarta tayi dariyar,don cikin kwanakin kawaici kawai takewa hafsat din,ta dauka har yanzu wai widad din dai data sani ce?,cikin kwanakin gaba daya ta fito da wata sabuwar gadara cikin gidan,komai ta taba komai zata gyara ko zatayi amfani dashi sai ta tsoma mata baki,tana tutiyar cewa gidanta ne,yadda takeso haka za’a yi,yadda taga dama haka takeson ta gani.

    Koda ranta ya baci bata taba tsaiwa tabi ta kanta ba,abu daya ta lura kamar abbas ya kasa dai daita hakan,abinda ita kuma takejin tazo maqura,ba zata lamunta ba itama.

    “Dakina nima akwai wajen ajiya” amsar data bata kenan a taqaice taci gaba da danna wayarta,abinda ya harzuqa hafsat din kenan

    “Ba shawara nake baki ba,umarni ne” sake sauke wayar tayi ya dubi idanunta da kyau,ta gaji da rainin hankalinta,kusan fiye da rabin komai da komai na abbas yana dakinta,tunda shine asalin dakinsa,amma ko sau daya bata taba nuna damuwa ko tayi qorafi ba,shine yanzu

    “Ajiyar ce akace miki ni ban iya ba?,wai meye damuwarki?,naga dai kayan mijina ne ko?”

    “Miji?,ni kike cewa mijinki ne?,turqashi!,wallahi saina nuna miki isata,saina nuna miki ni wacece,kuma wadan nan kayan saikin fiddosu” ta fada tana nunata da yatsa,kamar ma batasan me take ba, saita bawa banza ajiyarta taci gaba da abinda takeyi,ita abinda bata sani ba,tana jin zafinta fiye da yadda ita takejin nata,tana kishin uncle abbas fiye da yadda ita take kishin nasa,saidai ita an gaya mata,matsayinsu daya hasalima gaba take da ita,dole tayi respecting nata,amma ko daya bataga alamun daukar girma a wajenta ba.

    Banbami tahau yi tana sauka akan yaran,ta tattarasu ta wuce kitchen dasu,widad ta tabe baki taci gaba da abinda takeyi,saidai can qasan ranta zuciyarta tana mata zugi,ta gaji da rainin hankali irin na hafsat din,ta kuma daina daga mata qafa.

    Ko daga kitchen din tana jiyo masifarta da kuma mitarta,ta kasa zaune ta kasa tsaye,daga bisani ta kashe girkin data dora ta dauki yusra suka fito

    “Sai maganinki,bazan zauna qaramar yarinya dake kina maidamin magana ba kamar sa’arki” abinda ta fada kenan tana ficewa daga falon.

    Gyara kwanciyarta ma tayi tana maida hankalinta ga kallo,tsahon mintuna kusan goma sha biyar saiga maari matar me gadinsu tayi sallama,widad ta miqe ta zauna cikin fara’a da yake mutuniyarta ce sosai,suka gaisa sannan tace

    “Hajiya ce tace ayi kiranki” mamaki sosai ya kama widad din,hajiya kuma?,irin hakan bata taba hadasu ba illa iyaka gaisuwa

    “Bari na fito muje tare” ta fada tana miqewa tayi daki,maari tabi bayanta da kallo cikin tausayawa yarinyar,Allah ya hadata da BAK’AR KISHIYA.

    Tana sallama ta hangi hafsat daga zaune tana bawa yusra nono,a nutse widad din ta qarasa tana gidata,sama sama ta amsa mata fuska a hade,tun daga nan sai itama widad din ta kama kanta.

    “Kinsan alaqata da babanki?” Ta fada kai tsaye,saita dubeta sannan ta girgiza kai,tadai san suna da alaqa amma batasan wacce iri bace,kwanaki da ummu tazo mata suna yawan zama suna hira,hakanan itama tana aiko mata da abinci kullum

    “Kamar qanwa nake a wajen babanki,wannan dalilin ya sanya nayi kiranki,mummyn mimi ta kawo qararki,ki shiga taitayinki,banason rashin kunya da diban albarka,kizo ki sameta da mijinta da komai nata amma ki dinga qoqarin nuna kinfi kowa iyawa?,ki dinga yi mata isa da gida?” Wani abu ne ya taso mata,taji sam ba zata iya daukan zancan ba,don haka ta runtse idanu tayi nesa da tunaninta na tsahon wasu mintuna kafin daga bisani ta miqe

    “Ai bansan gidanta bane ba,amma yanzu na sani” abinda tace kenan ta soma takawa tana yin gaba,duk sai suka bita da ido,nauyi da kunyar yadda yarinyar tayi yana kama hajiya,yayin da hafsat ranta ya baci,ta kawo qarar wajenta ne saboda taji akwai alaqa a tsakaninsu,amma kuma haqarta bata cimma ruwa ba.

    Ranta yanatason ya baci amma tana qoqarin dannewa,tayi nasarar korar wannan,taci gaba da sabgoginta,bata ce ga sanda hafaat ta dawo ba,ta daiji motsinta cikin kitchen da kuma qananun mitocinta qasa qasa.

    Kwance tayi a dakinta har aka kira magrib,ta shiga toilet dinta ta sake wanka sannan tayi alwalar sallar magariba,wanna din sunnarta ne,ta riga ta saba koda bata da girki sai tayi wankan nan ta canza kaya,abinda hafsat din tayita son ganin ta hanashi faruwa,a cewarta ba ranar girkinta bane,don me zata dinga fitowa tana mata kwarkwasa da turare da kwalliya,saidai bata samu wannan nasarar ba.

    Ana idar da sallah taji alamun shigowar abbas din,duk sanda ya shigo gidan koda motarsa na anesa,ko motar office ce ta ajjiyeshi daga nesa sai taji hakan cikin jikinta,har zuwa sanda ya shigo sassan nasu, tanajin muryar su mimi suna masa oyoyo,taso tashi amma sai taji duka bata da interest akan hakan,kuma ma tasan bazai wuce minti uku bai qaraso dakinta ya dubata ba,don haka taci gaba da zama tana qarasa addu’o’inta da bata rabo dasu.

    Tun tana zuba ido harta soma qosawa,shuru bataji sake jin motsinsa ba,ta kalli agogo minti kusan ashirin kenan,tana sauke ido yayi dai dai da tashin muryarsa daga parlor yana kiran sunanta,duk sai taji banbarakwai,abinda bata saba dashi ba,amma kuma yau da gobe sai Allah,sai ta miqe a nutse tana gyara hijabinta sanan ta nufi qofa,gefe daya tana jin yadda cikinta yake qara tauri,wanda ita daya keji da ganin hakan.
    [08/05, 4:58 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 18

    A Rubuce Take Book 2 Page 18

    Part 02

    Page 18

     

    Tun daga harabar gidan ta fara fahimtar daga wanne irin gida widad din ta fito,daga yadda taga abubuwa suna gudana tun daga farfajiyar gidan da aka cika da rumfuna jikinta ya fara sanyi,wani irin kishi da bacin rai yayi mata tsaye a wuya,a haka dai ta daure,ta fita a motar,suna biye da hajjaa data zame musu jagora cikin gidan.

    Tarba ta girma akayi musu bisa jagoranci anty deena,ta shirya komai yadda zai qawatar da baqin cikin girma da karamci,komai kasa cewa tayi,sai idanunta dake biye da komai na gidan,tun daga falo zuwa wani falon da aka tanada don su kadai,ko da mutum guda bata gaisa ba,sai ido da takebin mutane dashi,sannan ta watsar kamar babu ita a wajen.

    Komai dake gudana gwaggwo mero na ankare dashi,har zuwa sanda suka kadaita a falon,aka kuma turo musu widad dake shirye cikin wani dandasheshen lace da mummyn ta ta dinka mata,wanda kudinsa yakai dubu sittin.

    Lace dim shine abu na farko daya fara tsone ma hafsat din idanu,tasan kudinsa sarai tunda sana’arta kenan,wani tashin hankali ya rufto mata,har ta gaza dauke idanunta daga kan lace din,tana jin kamar ta tashi ta yageshi daga jikin widad.

    Duk yadda taso ta tausa zuciyarta ta amsa gaisuwar da widad din ke mata,ranta fes fuskarta cike da walwala amma ta kasa,daga qarshe ma sai tayi bandaki kamar wadda wata buqata ta kama.

    Kasa riqe kukanta tayi,sai data matsi hawaye sosai sannan ta fito bayan ta waske da dauro alwala,ta riga kowa tayar da sallah tun farkon muhtarin sallar azahar.

    Tana kan abun sallah ba tare data waiwayo ba,tana jinsu suna yaba yaron da aka shiryashi cikin wasu irin kaya masu asalin kyau da tsada na qasar saudiyya,kowa ya daukeshi sai ya fadi kyau da kuma tsantsar kamannin dake tsakaninsa da babansa,abinda ya sake dagula mata lissafi kenan.

    ‘yan awannin da sukayi ta shiga quncin da sai data gwammace bijirewa zuwan tayi koma meye suyi da abbas din,idanunta sunga abubuwa kala kala,wadanda da wannan bacin rai tayi guzurinsu zuwa gida.

    Taro ya watse lafiya cike da tarin alkhairi da yaron ya zoma iyayensa biyu dashi,widad kuma ta shiga ci gaba da samun kulawa irin ta tsaffin da sukaga jiya sukaga yau,gefe guda ga gudunmawar yayyen zamani irinsu anty deena anty madeena,da matan abokai na qwarai irinsu fanna da sha’awa.

    *_DUKKAN ME RAI MAMACI NE_*

    Cikin sati biyu kacal muhammad da suke kira da affan ya fara wayo da wani irin girma dake alamta qiba zaiyi,daga shi har mamansa widad fatarsu ta qara gogewa,sunyi wani irin kyau na samun nutsuwa da kulawa,jegonta take hankali kwance,kulawa da soyayya tako ina,kusan ko yaushe suna manne a waya ita da abbas din,sukan shafe lokuta sosai suna hira,irin hirar dake debe kewa da sawa zuciya nutsuwa.

    Kwana biyu kacal yin wayarsu yadan ja baya,data tambayeshi yace hajiya ce bata jin dadi a kwanakin,a ranar sau biyu tana kiran hajiyan taji jikinta,cikin dauriya da murmushi take amsa mata

    “Da sauqi fa,kawai abbas ya tashi hankalinsa ne” kiran data mata a washegari da safe wanda shine kiran na kusan biyar hajiyan ta daga suka gaisa,ta tambayi dan jikallen nata wanda yake kamar shi daya ne jika a wajenta saboda yadda takejinsa a ranta

    “Allah yayi miki albarka widad,ya dafawa al’amuranki,kiyi haquri,kiyi juriya,Allah ya baki ikon kula da mijinki da dukka abinda ma zaki haifa a gaba” bata kawo komai a ranta ba,saima nauyin addu’ar hajiyan ta qarshe,duk da haka saita samu kanta da cewa

    “Ameeen” suka dan sake gaisawa sannan sukayi sallama da hajiyan.

    A ranar duka basuyi waya da abbas ba,tadan shiga damuwa amma daga baya ta bayar wataqila yanayin aiki ne,wanda wasu lokutan dama idan ya sakasu a gaba basu da wani sauran sukuni har sai sun gama sannan suke samun sauqi.

    Washegari affan yana saman cinyarta tana shayar dashi cikin dakinta,ita dashi dukkansu sunyi wankansu fes,sai qamshi suke fitarwa,so take ta gama bashi ya qoshi ta kaiwa latifa shi ta goyashi,kamar daga sama sai taji muryar uncle muhsin daga falo,cikin zumudi ta zare maman daga bakin affan ta sanyashi a kafada tana shafa bayansa,don yana shirin fara rigima ne,don da alama bai gama qoshi ba,tayo falon dashi.

    A tsaye ta sameshi shi da tsoho me ran qarfe da kuma ummu,yadda dukkansu suka bita da idanu haka kawai sai taji ta tsargu,saboda basu taba yi mata irin wannan kallon ba,duk sai taji qafafuwanta sunyi laushi,ta daure ta qarasa falon tana masa sannu da zuwa,ya miqa hannu yana cewa

    “Bani takwara na,shiga kitchen ki yiwa latifa magana ta tayaki hada kayanki zamu wuce bauchi” sosai maganar ta daketa,ta dubeshi da kyau

    “Bauchi kuma uncle?,ina cewa yanzu ka shigo?” Kai ya gyada mata

    “Eh,rakani zakiyi,flight zamu bi,kuma yanzun haka da nasa a siya mana ticket saura awa daya duka duka lokacin tashinmu yayi” kasa ci gaba da tambayarsa tayi,kawai saita juya tayi abinda yace din,saidai ko latifa dake hada mata kayan batace komai ba,bata tambayi ba’asin irin wannan tafiyar ta gaggawa ba,sai ta sake jin cewa lallai akwai wani abu dake faruwa.

    Samun kanta tayi da gwada wayar abbas don ta tambayeshi yasan wani abu akan tafiyarta?,ta kuma shaida masa tahowarsu amma amsa daya computer ke bashi wayar a kashe take,dukka.layukansa,da personal da na aikin gaba daya,saita jefa wayar jakarta kawai ta dauki mayafin abayarta ta roller ta fito.

    Sallama ta dinga yi da mutanen gidan,duk da tana gaya musu zata dawo sai tayi arba’in zata koma,ba wanda yace mata komai daga uncle muhsin har ummu,a haka suka fice a gidan ta cikin motar daya daga cikin samarin gidan da zai saukesu a airport.

    Tun saukarsu a garin bauchi taji gabanta yana wani irin faduwa mai tsanani,nutsuwarta tana neman barin gangar jikinta,ta dauka irin yanayin da take tsintar kanta ne duk sanda sukazo bauchin,amma saita karancin yanayin ya sha bambam da wannan da take tsintar kan nata a ciki,tayita kokawa da zuciyarta har zuwa sanda taga sun doshi hanyar gidan hajiya.

    Waiwayowa tayi tana duban uncle muhsin

    “Na dauka gidanka zamu sauka?”

    “Aah” ya fada a taqaice,daga haka shi da ita ba wanda ya sake magana,har zuwa sanda suka gangara gefan titi suka shiga faffadan layin dake malale da kwalta.

    Mummunar faduwa gabanta yayi lokacin da taga jama’ar dake zaune a qofar gidan,qarqashin rumfar tempol,qofar gidan cike yake jama’a,haka ta dinga ratsa mutanen qafafunta kamar ba’a jikinta ba, zuciyarta na wani irin bugu,ta kuma kasa tambayar uncle muhsin komai,burinta kawai ta isa cikin gidan ta gano abinda yake faruwa.

    Bata tsaya ba har sai data isa falon hajiya da shima yake tanqam da jama’a,sai surutai kadan kadan da kuma koke koke,kamar wata mutum mutumi ta tsaya tana qarewa kowa dake falon kallo,bakinta ya gaza cewa komai

    “Kamata ki zaunar da ita” taji muryar Gwaggo mero tana fada,sai a sannan ta samu qwarin gwiwar kallon hajja dake sama mata wajen zama bayan ta karba affan ta miqawa yaaya bara’atu

    “Waye ya rasu hajjaa”

    “Kiyi haquri ki zauna,hajiya ce Allah yayi mata rasuwa” kamar an qwala mata qarfe haka taji,kunnuwanta suka daina ji na wasu sakanni kafin su dai daita, bakinta da dukka ilahirin jikinta ya fara rawa,Allah ya taimaketa ta kama kalmar

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” kuka mai tsananin qarfi ya qwace mata,sai kuma numfashinta ya fara sarqewa,ta fara kokawar qwatarsa,daga haka kuma saita daina gane komai.

    Sanda ta farka cikin setting room ta samu kanta ita da hajjaa nujood da bilkisa matar suraj,suna mata sannu amma sake tanbayarsu take da gaske hajiya ta rasu ko kuma mafarki tayi?.

    “Allahn da ya fimu sonta ya dauki abarsa,addu’a ce kawai zata nuna zallar soyayyar da muke mata ba koke koke ba” nasihar da suka dinga mata kenan cikin kwantar da kai, saita fashe da kuka sosai tana jerawa hajiya addu’o’i har kamar ba zata tsaya ba,a haka suka miqo mata affan daketa rigima ta soma shayar dashi,amma hawayen fuskarta yaqi tsayawa,duk sanda ta kalli affan din sai taji zuciyarta ta sakeyin rauni,yayi rashin kaaka,kuma masoyiyarsa,wanda tun yana ciki take qaunarsa da begen ganinsa amma Allah bai qaddara hakan ba.

    Ba shakka hajiyan ta dace,domin dukkan wata siffa dake alamta kyakkyawan qarshe hajiyan ta sameshi,kama daga yanayin yadda ta mutu da cikakkiyar kalmar shahada a bakinta,zuwa yabo data dinga samu daga wajen mutane,gidan kamar xai tsage da jama’a,har maqwafta a cike yake babu masaka tsinke.

    Ta idar da sallar la’asar tana zaune saman abun sallah,har a sannan qwalla bata bar fita daga idanunta ba,tuni kanta yake sara mata da matsanancin ciwo,husna ‘yar nasmah qanwar abbas ta shigo mata da abinci,ta kalleta ta kalli abincin

    “Ina abbansu mimi ne?”

    “Ni tun safe ban qara ganinsa ba” hankalinta sai ya qara daukuwa a kansa,tasanshi sarai,tasan irin soyayyar dake tsakaninsa da hajiyan,ya kamata a duba halin da yake ciki,itama tunda tazo bataji an ambaceshi ba,don haka ta miqe ta goyawa husna affan sannan ta canza hijabin jikinta zuwa babban daya saukar mata har qasa ta fita a dakin.

    Da qyar aka gano mata shi a dakin su umar,sanda tayi sallama ta shiga dakin kasa ganinsa tayi saboda duhun da dakin yake dashi,ta laluba makunnin fitilar dakin ta kunna,haske ya wadaci ko ina,mamaki ya kamata ganinsa zaune saman abun sallar, idanunsu suka hadu waje guda,sai taji wani rauni ya ziyarceta,kuka take da muradin yi amma kuma zuciyarta na gaya mata ba haka ya kamata tayi ba.

    Takowa tayi a hankali zuwa inda yake zaunen har yanzu idanunsu na manne da junna,fuskarsa ta fada wuni guda,sai wani irin jigata da idanunsa sukayi,dab da zata iso ya shafa addu’a sannan ya miqa mata hannunsa,ta dora nata hannun akai,zai mata masauki saman cinyarsa ta zame ta zauna daga gefansa tana kallon qwayar idanunsa dake cike da wani irin tashin hankalin da ba kowa bane zai iya karanta,tsananin jarumtarsa ya boye komai

    “Yaushe kukazo?” Ya tambayeta da wata irin murya dake cike da sanyi da jigata,ta danyi gyaran murya kadan don kada ta fashe masa da kuka

    “D’a…..d’az……” Kasa qarasawa tayi,dukkan wata jarumta ta qare,saita fashe masa da kuka harda sheshsheqa,baice komai ba illa rungume kanta da yayi a qirjinsa yana shafa bayanta,yadda kanta ke qirjinsa haka take jiyo yadda Zuciyarsa ke wani irin bugawa a hagunce.

    Mintuna kusan biyar ta dauka a haka sanann ta fara qoqarin saita kanta,ta daga kai tana dubansa da idanunsa da suka sauya kala,hannu biyu yasa yana goge mata hawayen sanann yace

    “Nasan ba wannan ne kukan da kika fara ba,pls karki qara yin wani kukan,hajiya bataso,kiyi mata addu’a” kai ta jinjina cikin aro jarumta,ta gaidashi tare da yi masa gaisuwa,don ya fita cancantar ayi masa gaisuwa,duk kuwa da cewa itama kallon uwa takewa hajiyan,ba zata taba mantawa da gudunmawa da soyayya qauna da kariya data baiwa rayuwarta ba.

    “Amma uncle,me kakeyi a nan kai kadai a duhu?”

    “Sallah nayi,baki gani ba sanda kk shigo?” Kai ta jinjina

    “Na gani,amma idan ka shiga cikin jama’a kamar sai yafi,a nan din tunani zaiyi maka yawa ne” kai ya jinjina kawai

    “Kaci abinci?” Ya sake girgiza mata kai,saita ajjiye masa affan ta shiga cikin gida ta samo masa abinci me kyau,saidai gaba daya ya kasa ci,ya ture plate din yace

    “Samomin coffee kawai ya isa” haka ta koma ciki ta hado masa coffee din,a hanya ne suka hadu da hafsat tana shigowa goye da yusra,yadda ta dauke mata kai itama haka ta bawa banza ajiyarta ta shige.

    Coffee din ya shige cikinsa da qyar,ya kama hannuwanta ya riqe cikin nasa yana cewa

    “Allah yayi miki albarka” don badon tazo ba yanajin azumin yini biyu zaiyi,don shidai ko qyallin hafsat bai gani ba,duk da ya tabbatar tana gidan,don suna gaban gawar hajiya ta shigo gidan tana runtuma ihun da sai da akayi mata magana.

    Bata barshi shi kadai ba sai data sashi gaba ya fito daga dakin ya koma cikin mutane,duk bayan wasu lokutta kuma tana sawa ana duba mata shi da yadda yake.

    To rashin mahaifiya wani rashi ne mai mugun ciwon da fadin radadinsa bazai misaltu ba sai wanda Allah ya jarabta dashi, rasuwar hajiya rashine na dukka dangi dama mutanen unguwa,kowa yaga tsananin jarumtar abbas,don ba wanda baisan irin shaquwa da qaunar dake tsakaninsu ba.

    A gidan yake kwana shi da widad din,amma daki daban daban,hafsat kuwa yaran take diba su wuce gidan iyayenta su kwana,sai kusan azahar take zuwa har akayi kwana uku.

    Randa akayi sadakar ukun da safe ne tsananin ciwon kai na rashin bacci da kuma damuwa suka sanya abbas a gaba,dole ya buqaci tafiya gida don ya kwanta ya huta,duk da bashi da tabbacin yiwuwar baccin.

    Farko hafsat yasa widad ta nemo masa su wuce tare,don yasan gidan kansa yayi qura,sanann widad din tana jego ga kuma mutuwar itama yadda ta bugeta tilas tana buqatar hutu,to amma sama da qasa babu hafsat din ba alamarta,dole yasa widad ta shirya suka wuce gidan.

    Sosai ta gyara masa bedroom dinsa irin yadda tasan yana so,sannan ta shirya masa dan abinda zaici mai dadi da ruwa ruwa,ta kuma hada masa ruwan wanka mai dumi sosai da qamshi,yayi ya canza kayan,ta sashi a gaba yaci abincin ya kwanta sannan ta baro masa dakin bayan ta sanyashi yayi addu’a.

    Falon ta dawo taci gaba da gyaranshi,tanayi tana duba affan dake kwance yana watsal watsal da qafa,ya cusa yatsunsa biyu a baki.

    Doko qofar falon akayi lokaci guda ba zato ba tsammani,har affan dake kwance yadan firgita

    “Subhanallahi” widad ta fadi tana duban bakin qofar.
    [14/05, 12:25 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)