Author: Novels

  • A Rubuce Take Book 2 Page 31

    A Rubuce Take Book 2 Page 31

    Part 02

    Page 31

    Zuwa azahar abba mahmud ya iso,ba dadewa saiga uncle muhsin shima takanas,wanda sam baisan abinda yake faruwa ba sai sannan,suka zauna shida sauran qannensa biyu dake binsa dukka cikin falon ummu,ya dubi widad da fuskar nan tasa dake nuna tsantsar da gaske yake,ya kirayi sunan widad din,wadda duna daya ta yiwa fuskarsa yawun bakinta ya dauke tsaf!!,tasan waye abban,tasan halinsa sarai,baya daukan wasa ko raini,hakanan bayason rashin gaskiya kaf rayuwarsa

    “Ki gayamin tsakaninki da Allah me ya faru?” Bakinta ne ya fara rawa,cikin kakkausar murya yace

    “Ki nutsu kiyimin bayani,idan kuma baki da gaskiya ne kiyi gaggawar fadamin basai kin batawa kowa lokaci ba” ta rufe idanunta sosai tana son bawa zuciyarta haquri ta kuma dai dai tata,saita fara gaya masa komai daki daki harta kammala.

    “Wayeshi abubakar din?”

    “Abubakar dai fa daka sani” uncle bashir ya amsa masa,sake waiwayawa abba yayi ga widad

    “Wannan abun da kika fada ayanzun idan baki qur’ani zaki iya dafawa ki sake rantsewa da hakan shine iya abinda ya taba faruwa?” Da sauri ta jijjiga kai

    “Zan rantse abba wallahi zan rantse”

    “A bani number wayar abubakar din” ya miqawa uncle bashir wayarsa,ya saka masa number abubakar akayi kiransa.

    Yadda widad ta fada din haka shima ya fadi,abba yayi masa sallama ya kashe wahar yana duban widad idanunsa tsar a kanta

    “Ashe kece duk kika jawa kanki wannan,ki gayamin uban da yace miki koni na mutu zaki fita daga gidanki kafin ki shaidawa mijinki,kadin kuma ya baki izni ta hanyar amincewa?”

    “Nayi kuskure abba,kuma naga indai fita ta uzuri ya kama yana barina ko ban gaya masa ba,saidai idan ya dawo din saina gaya masa……. astagfirullah” ta fada a rude hawaye yana zirarowa saman kuncinta sannan ta fashe da kuka,har affan yana daga kai yana kallon fuskarta sosai,dukka saida kowa a wajen zuciyarsa ta karye, dukkaninsu sunsan halinta,bata qarya ko za’a yanka ne zata fadi gaskiya,tun tashinta haka take.

    Sosai ran abba ya sosu,ransa ya kuma baci har ya gaza jurewa

    “Wanne irin aure ne wannan kukeyinsa da zargi?,ina akace anayin aure da zargi irin haka,zina fa?”

    “Wai ba zargi yakeyi ba,har hujja yana da ita”

    “Idan ba zargi bane waye ya gaya masa?”

    “Abokiyar zamanta ce” wani balaeen bacin rai ya tasowa abban, musamman shi da ya taba fuskantar halin makirci irin na mata

    “Abokiyar zamanta?” Ya maimaita wani bacin ran yana ciyoshi,sai kawai ya kasa sake cewa komai saboda tsananin bacin rai,ya miqe tsam yana cewa ummu

    “Ta zauna a wajenki ummu” daga haka ya fice,kowa a wajen ya fahimci yadda ransa yayi mummunar bacin rai,na biyunsa kuwa uncle muhsin ne,wanda shima ya miqe ya fita,ya kuma lalubi number abbas din ya kira.

    Daidai lokacin da yake tsaka da aiki da dukkan qananun police dake qasansa da zasuyi aikin tare.

    Cikin uniform dinsa dake qara masa kwarjini sosai,fuskarsa a dinke tsaf,a yau din baya ga yanayin aiki da yake sawa ya koma hakan,harda wannan qulalliyar damuwar dake qasan zuciyarsa,wadda ta koma masa abokiyar rayuwar ruhinsa,ya saka hannu a aljihun wandon uniform dinsa ya fidda wayar,ganin sunan muhsin din sai yadan gyara tsaiwarsa,tunda abun ya faru ko sau daya basuyi magana ba,sai ya juya a hankali ya taka yana fita zuwa qofar dan qaramin hall din da suke ganawar sirri.

    Kan qaramar barandar dake wajen ya tsaya ya daga wayar,suka fara gaisawa kamar komai bai faru ba,sannan a nutse ya jefa masa tambayar abinda yake faruwa tsakaninsu da widad.

    Yadda ya gayawa uncle bashir haka ya gayawa muhsin din,ransa yabaci shima

    “Yanzun ka yarda da abinda ita ta fada?”

    “Bana ce ba,sai nayi bincike kawai,zan sake bincikawa yanzun haka ina katsina ne” kai muhsin ya jijjiga ransa a bace

    “Saika gaggauta,saboda ran yaaya mahmud ya baci,kuma nasan halinsa sarai” daga haka ya yanke wayar,abbas din ya sauke wayar daga kunnensa yana kallonta,daga can qasan zuciyarsa ana gaya masa bakayi dai dao ba baka kyautawa,wani sashen kuma yana gaya masa shine dai dai,ya rufe idonsa a hankali yana jin kansa yana masa nauyi,a hankali sai ya fara jinsa kamar iska na kadashi hagu da dama,jinsa ya fara yin qasa hayaniyar dake kusa dashi ta fara komawa nesa dashi,sai kuma yaji kamar qafafunsa sun lanqwashe an turashi,ya tafi luuuuu zai fadi,mutumin dake dauke da posting later dinsa ta sauyin gurin aiki daga kaduna zuwa katsinar ya isa gareshi yayi saurin tareshi yana fadin

    “Subhanallah, innalillahi wa inna ilaihi raji’un” sai ya fara neman dauki,wadanda ke kusa suka qaraso suka tayashi riqe abbas din daketa qoqarin daidaita numfashinsa ya kuma miqe ya tsaya da qafafunsa saidai abun yaci tura,sunqi sakinsa don sun tabbatar zai iya faduwa,dole aka dauko motar aiki aka sakashi a ciki suka wuce asibiti dashi.

    Ummu tafi kowa saninta da sanin wacece ita,hatta da mahaifiyarta ba zata gaya mata wacece ita ba,zamanta wajen ummun an dan samu ci gaba kadan,ta lalubo abubuwan da takeson ci ta saka latifa na tanadar mata su,a yadda ummun ta lura sai taga kamar qaramin ciki ke sake wahalar da widad din,koda ta gaya mata a gigice ta daga kai ta kalleta cikin tashin hankali gabanta na wani irin faduwa

    “Ciki kuma ummu?” Yadda taga hankalinta yayi mugun tashi saita saki murmushi

    “Wai hasashe na ne,amma ba lallai ya zamana shi din bane” tabar widad din a haka,don ta fuskanci sanin tana da cikin kamar zai sake zame mata wata qarin damuwa akan wadda take ciki,sai kawai taci gaba da kula da ita a hakan.

    Kwanansa biyu a asibitin yana jin jiki,a kwana na ukun yaji dama dama,ya kuma nemi sallama amma likitan yace bazai bashi yanzu ba,sai ya huta sosai,saboda stress yayi masa yawa,so yana buqatar ya samu hutu sosai.

    Daga wajen aiki sun bashi kulawa sosai,sun kuma saka an saka komai a gidan da aka bashi zai zauna a zaman aikinsa,koda suka gaya masa shi sai yaji duka wannan ba damuwa bace a wajensa.

    Ciki ikon Allah a kwana na ukun yaji ya fara damuwa da yanayin da yake ciki,zuciyarsa ta fara tuhumarsa,ko yaya widad take ba zaka iya zama da ita ba?,ya sadaukar da komai dominka fa. Maganar da wannan raunannan sashen na zuciyarsa ke gaya masa kenan,ya tuna wayarsu ta qarshe da muhsin,wadda daga ita bai kuma kiransa ba,ya kuma tuna yadda ya gaya masa abban ya dauki zafi,mutum me mugun karamci da kirki,sai ya miqe zumbur ya zauna saman gadonsa ya jawo wayarsa.

    Kai tsaye ya kira kawu hassan,bayan sun gama gaisawa ya fara masa bayanin biko yakeso suje masa

    “Ikon Allah,hafsatun abun yakai har da sake tafiya gida?” Kai ya girgiza yana jin zafi a ransa

    “Ba ita bace,widad ce”

    “Widad kuma?” Kawun ya tambaya cikin mamaki

    “Eh kawu” shuru ya danyi sannan yace

    “Allah ya kyauta,amma ya zama dole ka sake zama mai nisan haquri,su mata indai kace ba zaka dinga haquri ba,kowacce ma ba zaka iya zama da ita ba,ko ka auro saisun tafi,kuma zo mu zauna zo mu saba” ya danyi masa fada sannan yace zaiyi magana da ko sunusi ne sai su shiga kanon ko zuwa gobe ne,ya yiwa kawun godiya sosai,yace zai sanya a tura musu kudin da zasu sha mai

    “Don qaniyarka muba iyayenka bane,har sai ka bamu kudin mai banda alkhairin da kake mana” wani busashen murmushi ya danyi kawai,ya sake masa godiya ya ajjiye wayar.

    Shuru yayi ya jingina da gadon idanunsa a rufe,wata zuciyar na gaya masa ya kyauta,wata kuma tana tuhumarsa,kanme zai dawo da ita bayan babban laifin data aikata?,bata cancanci ya zauna da ita ba,ya rasa wanne matsaya yake a cikin biyun?.

    Sai da yayi sallar azahar hafsat ta fado masa a rai,ya dauki wayar yana duba ko akwai kiranta amma babu ko daya tsahon kwana ukun,mamaki ya kamashi,sai ya fara neman layinta.

    Sai data kusa da tsinkewa sannan ta daga,murya a daqile tayi masa sallama,ya amsa sa muryarsa mai laushi

    “Sai yau ka tuna damu,ni kamar ma mu ka kama a hotel din nan” ta fada cikin gatse,sai yayi shuru yana jinta ransa na masa zafi,batayi dogon nazarin taji sauyi a muryarsa ba ta dora

    “Duk masifar ta dawo kanmu,kwana uku kayi tafiya amma ka kasa neman matarka daka bari da yaranka” kansa ya girgiza yana jin ciwo a ransa

    “Ke bakisan ki kira mijinki kiji ya ya isa ba?,idan kinji shuru bakisan ki karashi kiji me yake faruwa dashi ba?,bani da lafiya ina asibiti kwana uku amma rashin kulawarki yasa bakisan da hakan ba,da irin wannan halin naki wataran sai an kawo miki gawata unexpected” sai kuma jikinta yayi sanyi,ta danyi shuru sannan ta fara magana

    “Ni wallahi bansan baka da lafiya ba,sannu Allah ya sawwaqe ya baka lafiya”

    “Ameen” ya amsa can qasa,duk wani karsashinsa babu,sai yaji baya buqatar dogon magana da ita,ya tambayi yara ta hadashi dasu.

    Kusan su suka debe masa kewa,yayi hira dasu mai tsayi sannan yasa suka kaiwa mamar tasu wayar,ta tambayeshi wanne asibiti yake,daya gaya mata ya dauka zatayi batun zuwa ganinsa,amma sai tace masa kawai Allah yasa kaffara,akan haka sukayi sallama,sai ya kashe wayar,widad ta fado a ransa,yayi imanin inda itace da yanzun haka ta rude masa gaba daya,ya mirgina kansa gefe yana jin zafin zuwanta hotel,sai yaji ko sunansa bayason ji.

    *********Sai da ya gama shirin fitarsa kasuwa sannan ya fito gaba daya,ya samu baqin da akace masa suna jiransa a falon saukar baqi na gidan.

    Sukayi gaisuwar mutunci sosai,ya shaida kawu hassan don haka bai buqaci sanin daga ina suke ba,haquri suka bayar kan su din basusan me yake faruwa ba sai daga baya,suka kuma gabatar masa da buqatarsu na abasu bikon widad din tare da alqawarin hakan ba zai sake faruwa ba.

    Gyara zamansa sosai abba yayi

    “To naji dadin zuwanku,don dama inata shawarar neman daya daga cikinku,batun ya sake faruwa ko kada ya sake faruwa dama bazai sake din ba,saboda a yanzun bana buqatar kowa ya nemi bikon widad,abinda nake buqata don Allah,ku gaya masa ya rubuta takardar sakin diyata ya aikomin da ita,ko ya turomin ni tunda yana da number ta,magana ta biyu kuma,ku gayawa ita abokiyar zaman tata mai shaida da shaidu cewa,ta shirya shiga kotu dani uban widad bisa qazafin zinar data yiwa diyata,zamu shiga kotu har sai gaskiya tayi halinta,walau gaskiyarta ko kuma gaskiyar tawa diyar” dukkansu sun girgiza sun kuma ji babu dadi,don basu zaci wannan hukuncin daga wajen abban ba,sai suka fara qoqarin bashi haquri

    “Ai baza’ayi haka ba alhaji”

    “Me zai hana ayi haka?,na gama magana kuyi haquri bana maimaici,ya bayar da takarda ita kuma ta shirya shiga kotu,’yata ba mazinaciya bace,ba kuma zata sake zaman zargi ba” daga haka ya musu sallama cikin girmamawa yabar musu falon.

    Dole bayan sun gama jimanta maganganun a tsakaninsu suka fito,kowa sai da ransa ya baci dajin cewa wai hafsat ce ta gaya masa anyi haka harda bashi shaidu,kawu hassan bai rufeshi da komai ba,ya kirashi yayi masa tatas,ya kuma bashi saqon abban ya kashe wayarsa abinsa.

    *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 39

    A Rubuce Take Book 2 Page 39

    Part 02

    Page 39

    Duk da kayanta ne na wancan gidan nasu amma gidan yayi bala’in burgeta,komai ya tsaru,an kuma shirya mata shi dai dai da ra’ayinta da kuma yadda takeson gida ya kasance,ta dinga satar kallon abbas tana mamakin yadda ya karanci komai nata,me takeso,meye bataso,walwala da damuwarta,sai taji zuciyarta ta karaya,ta samu kanta da addu’ar kada Allah ya kawo abinda zai sake rabasu ko ya saka shakka ko rudani a tsakaninsu har qarewar numfashinsu.

    Widad din mutum ce mai matuqar qoqari,a tsaye take kan hidimar gidanta,duk da komai a gyare yake amma sai da tayi goge goge,ta kuma samar musu da abinci duk da akwai taimakon abbas din yana kama mata,sannan suka sake wanka gaba dayansu suka shirya don wucewa gidan saukar yaaya bara’atu.

    Yana riqe da hannunta suka shiga motar tata

    “Inajin aminatu zanje na roqa abarmiki,wannan aikin yana miki yawa” dadi sosai ya kamata,ta murmusa tana cewa

    “Amma da ka kyautamin qwarai,inason yarinyar,tana da hankali,amma kuma ranka ya dade,naga kaman baka da ra’ayin daukan mai aiki” kallonta yayi sannan yayi murmushi

    “Wayon tsiya gareki,nasan me kikeso kice,na farko amintu ai bame aiki bace,qaramin qarfi garesu,daukotan zai zama kamar taimako,kamar yadda tasa aka dauko lawan yaso ya zame mana wani abu daban,na biyu kuma ina da tabbacin ko ire iren aminatu dubu zan cika miki gidanki dasu,ba zaki bari kowacce tayi hidimar mijinki ba,ba kuma zaki sakar musu hidimar gidanki gaba daya sai yadda sukaso suyi ba,munsan aminatu muna da tabbaci akan tarbiyyarta,ba zata batamin yara ba,kuma na tabbatar baki da sakaci da zaki kasa sanya ido a kanta,ko yaya motsinta ya canza nasan in sha Allah zaki kula,zaki kuma tsawatar” shuru tayi tana dan gyada kai,komai yayi wato yana sane,yana kuma da hujja akai

    “To Allah ya zaba abinda yafi zama alkhairi”

    “Ameen ya hayyu ya qayyumu” ya fada cikin nuna kulawa.

    Sai da ya ajjiyeta a qofar gidan sannan ya miqa mata key dinta yana jifanta da wani kallo,saika dauka sabon saurayi da budurwa ne

    “Drivernki ya gama aikinsa ranki ya dade” dariya ta tsuntsire da ita

    “Godiya nake,zan ninka maka salary dinka”

    “Da kuwa kin kyautawa dan marayan Allah” ta girgiza kai tausayinsa yana dan tabata

    “Allah ya jiqansu ya kyauta makwancinsu ya kyauta namu zuwan”

    “Ameen ya Allah,Allah yayi albarka” ta amsa da ameen ya fita a motar yana gaya mata zai qarasa gidan suraj da yake basu da nisa,idan sun shiga wata sabgar yasan zata iya maida kanta gida,idan kuma ya dawo da wuri sai ya maidata

    “Koka maidani dawowa zakayi,kasan dai kwanan waye ai” harara ya balla mata,tayi kamar bata gani ba ta wuce ciki tana qunshe dariya tana riqe da hannun affan da ya fara koyon tafiya,wannan yasa ta dinga takawa a hankali cikin kula da takatsantsan.

    Tun daga qofar gidan jama’a ne,ta dinga gaisawa da mutane sunayi mata sannu saboda ganin yadda tayi nauyi sosai da uban ciki a gaba,yan mata matan suka daukar mata affan din suka kutsa cikin gidan dashi ita kuma ta tsaya tana ci gaba da gaisawa da mutane.

    Hafsat din na tsakar gida anata rabon tuwon sauka,gaba daya ba cikin sukuninta take ba ganin yadda su mimi suka shiga sabgarsu cikin mutane,ko ta kanta basayi,yaran sunyi fes dasu sunyi haske sunyi qiba

    “La la la,da gani babu tambaya wannan yaron sir abbas ne” wata qanwar mijin yaaya bara’atu ta fada bayan an shigo da affan ciki

    “Tubarkalla ma sha Allah,yaro ya debo ruwa biyu,miqomin shi na ganshi” ta miqa hannu tana karbar affan dake fidda qamshi cikin navy blue din jeans da shirt dinsa.

    Sosai maganar taja hankalin hafsat,gabanta ya fadi ta waiwaya tana kallon yaron dake da yawan fara’a,abinda ya qara masa farinjini kenan,saita dauke kanta wani abu yana tsaya mata a wuya,shi da babansa sukazo lo shi kadai?, indai kuwa shi da babansa ne lallai abun abbas qara ta’azzara yakeyi,har yazo bauchi amma bata da mutuncin da zai gaya mata yazo din?.

    Bata gama wanann taraddadin ba widad ta danno kai,kamar kunna fitila cikin duhu haka ta haska gurin,da kyakkyawar shigarta me aji,dama tunda can din ita gwanar iya dressing ce,tunda quruciya ballantana yanzu data mallaki hankalin kanta,wata lafiyayyar atamfa ce a jikinta wadda tafi kama da material.

    Suna hada ido gaban hafsat din yayi Wani mummunar faduwa,faduwar da sai data rufe idanunta don tanajin sautin bugun zuciyarta har kunnenta,kamar ciki fa take gani a jikin widad din,ciki fa,cikin ma tsoho?,saita miqe tana laluben hanya,wanda banda Allah ya kare tayi hanzarin dafa bango da tuni ta timu a gurin ta fadi.

    Ba wanda ma ya kula da ita suna yiwa widad din maraba,kowa na qoqarin mata godiyar alkhairin da ya samu wannan karon daga wajen abbas din,wanda da yawansu sun tabbatar widad din ce sila,hakan yake kuwa,a wannan karon tayi shirin karbar soyayyarsu ne gaba daya,ribar kasuwancinta ta raba biyu,rabi ta dinga qarawa kowa akan abinda abbas ya saba bayarwar,har sai da suka qare,ita da fahad sukayi,batasan bakinsa bai iya shuru ba sai daya gaya musu,saboda shidai abun mamaki ya bashi,don koda wasa bai taba ganin hafsat din tayi musu haka ba,saidai tayi qoqarin ragewa ma.

    Mayafi da takalminta ta dauka ta sulale sai gidansu,tsananin bacin rai yasa da tashin hankali yasa ta manta da batun daukansu mimi da jiran zuwan abbas tayi masa kwance kwance ya bata yaranta.

    Tana shiga gidan ta dora hannu aka ta sakama maman nasu kuka,tayo wajenta hankali tashe

    “Wani cikinne da ita umma na shiga uku,ta kusa haihuwa fa?”

    “Ina fatan bakiyi wannan haukar a gabansu ba ko?” Ta fada cikin taraddadi,ta jinjina kai kawai don ta kasa cewa komai

    “Shikenan tashi muje ciki” yunqurin miqewa tayi amma sai jini ya soma bin qafafunta,ta fidda idanu waje ta qwala qara tana fadin

    “Wayyo Allah!…..cikina umma” sai kuma tayi baya luuuu ta sume umman tata ta tareta cikin tashin hankali.

    Kai tsaye asibiti suka wuce da ita,bayan an basu gado anyi gwaje gwaje aka tabbatar da zubewar cikin jikinta,kamar zatayi dan qaramin hauka koma ace qaramin haukan ta dinga yi a asibitin,har sai da haushi ya kama ‘yan uwanta.

    Ta ciwa cikin jikinta buri sosai,tasan abbas din da matuqar son yara,ta gama tsara yadda zai zame mata makamin da zata yaqi abbas ta kuma dawo dashi tsundum cikin rayuwarta.

    Ba abinda abbas din baiyi ba na hidimar asibitin,hatta da ruwan da yan dubiya zasu sha bai bari kowa ya siya masa ba,ko dama can shi din tsayayye ne,baya dorawa kowa lalurar iyalinsa.

    Ranar da aka sallameta ranar suke komawa bauchi,don haka duk wani plan dinta ya gama rushewa,umman nata tace kada ta damu,ta bari ta gama jinin biqin nan,sai su shirya ma komai da kyau.

    ********Shirin haihuwa sosai abbas yake yiwa widad din,siyayya yakema twince din da basuzo duniya ba kamar ba gobe,abun yazo masa akan gaba,saboda wani irin budi yake samu sosai,harkokin kasuwancinsa da yake gudanarwa a gefe kamar ana musu yayyafin alkhairi,haka ta fannin aikinsa,ya tsare gaskiya da amana,hakanan koda cikin yaransa ya kamaka da laifin karbar cin hanci ko rashawa to ka kade,dukkansu sun sani kuma suna kiyayewa dokokinsa.

    Already likita ya gaya mata,tana cika watanni takwas to zata iya haihuwa daga sannan,kasancewar cikin twince,kuma ba haihuwar fari bace,don haka kullum abbas din cikin shiri yake,tayita dariya saboda yadda yakeyi din,kamar lokacin za’a fara yi masa haihuwa.

    Ranar da zaije bauchi weekend kamar kada ya tafi,tace sam sai yaje,watansa guda kenan baije ba saboda cunkoson aiki anan katsinan,hakadai ya tattara ya tafin ya barta da aminatu da yasa akaje aka dauko mata ita kafin ya wuce,sai da ya dawo sannan hankalinsa ya kwanta.

    ********Tun kafin su gama cin abincin dare bayanta da mararta ke ciwo,amma take daurewa tana cijewa,suna gama cin abincin tasa aminatu ta dauki affan suka wuce dakinsu,sai itama tace kwanciya zatayi,don bayan sun gama cin abincin fita ta kama abbas din ta gaggawa,don haka suka rufe ko ina,yana da key din kowacce qofa tasan idan ya dawo zai bude.

    Tashinta uku xuwa wani irin fitsari da yake takura mata,a zuwa na hudunne ta durqushe a bakin toilet din tana riqe da mararta da bayanta saboda wani mugun murdawa da tayi

    “Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis” ta dinga maimaitawa,sai ta koma ta zauna sosai a wajen.

    Tun a can yaji jikinsa bai bashi ba,don haka ya katse meeting din,yabar mataimakinsa yace su qarasa,kome ake ciki su gaya masa.

    Yana buda qofar nishinta ya fara ji,a rude ya qaraso inda take yana tambayarta,amma babu baki,sai kawai ya fara sauko da kayan haihuwar data hadasu jiya jiya ya fidda cikin mota,ya kamata ya kaita mota,ya qwanqwasa dakinsu aminatu ta bude,ya gaya mata su kulle ko ina su kwanta,ya bata dukka keys din na gidan yace zasu asibiti,hankalin aminatun a tashe tayi musu addu’a ya fice.

    Kafin su isa ya kira daya daga cikin juniors dinsa,suka sameta a asibitin,bayan an dubata aka wuce labor room da ita.

    Addu’ar data dinga yi ba kadan bace,a wannan karon duk yadda ta zata ba haka bane,ana kiraye kirayen sallar asuba lokacin da abbas ya wuce masallaci cikin hukuncin ubangiji ta haife kyawawan twins dinta dukka maza.

    Yana kuma idar da sallar kira na shigowa wayarsa,ya daga yana sauraren bayanin da ake masa,tafiyar gaggawa ce ta taso musu shida matimakinsa da wanda abbas din ke bi,shine matsayar tattaunawarsu ta jiya,qarfe shida na safe,don dole ba yadda zaiyi haka ya amsa,don a qa’idar aikinsu ba sabawa umarni,ya baro masallacin yazo ya tarar da alkhairin da Allah ya saukar masa a wannan sassanyar asubar,baki da dukka zuciyarsa sun gaza daina furta godiya ga Allah,yaran kawai ya samu gani suma a gaggauce,haka yabar asibitin cike da kewar yaran da kuma mamarsu.

    Tun a hanya ya buga waya ya gayawa dukkan wanda ya dace ace ya sani,daga danginsa zuwa nata,gab da zai shiga gida ya kashe wayar don ya samu ya shirya,bai kunna wayar ba sai da suka dauki hanya.

    Yana kunnawa hafsat ya fara kira don ya fita hakkinta,ko basa tare indai zaiyi tafiya ya saba yana sanar da kowaccensu,bayan ya gama gaya mata tafiyar ya dora mata da batun haihuwar.

    Uffan kasa cewa tayi,saboda wani qaton abu da ya toshe mata qofofin maganarta,twince?,to maza ko mata?,ko Mace da namiji?,kai koma meye yarinyar ta haifa itakam ta shiga uku.

    Shurun da yaji yayi yawa sai ya mata sallama kawai ya katse wayar,ya amsa kiran yaaya bara’atu daya shigo masa.
    [25/05, 1:45 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 27

    A Rubuce Take Book 2 Page 27

    Part 02

    Page 27

    Yamma lis suka sauka a bauchi saboda gudun da yaron nasa ya tsula bisa umarnin ogan nasa

    “FAAZ hotels zaka kaini” ya fada a wani galabaice,kamar yau ya fara doguwar tafiya a mota

    “Yes sir” ya fada yana karya kan motar tasu ya dauki titin da zai sadasu da hotel din.

    Karon farko gabansa yayi mummunar faduwa sanda suka isa gaban hotel din,abind aya jima baiji ba kenan,duk irin hatsarin aikin da zai shiga kuwa,zuciyarsa ta dinga masa saqe saqen munana abubuwa,tana ayyana masa adadin xuwan widad wajen,kamar wanda allurarsa ta motsa ya zunkuda cikin zafin nama ya buda murfin motar ya fice,bayan ya yiwa yaron umarnin ya zauna cikin motar ya jirashi,yanzu zai dawo su wuce gida.

    Cikin rashin nutsuwa yake takawa zuwa makekiyar qofar hotel din,hannunsa cikin aljihun wandonsa yana qarewa qofar kallo,duk da irin qwarewarsa a wajen aiki,duk da qwarewarsa wajen iya bincike amma a yau kamar an bude kwanyarsa an kwashe dukka wannan qwarewar,komai ya kwance masa,a haka ya isa ga security din dake zaune daga bakin qofar.

    Sallama yayi masa ya bashi hannu suka gaisa,ya gabatar masa da kansa gami da nuna masa ID card dinsa,ya jinjina kai

    “To na shiga ciki ne na sanar da manager zuwanka?” Kai ya girgiza da sauri ransa yana masa suya,yau wai shine zai gwada aikinsa akan widad?,yau shine yazo bincike hotel akan widad?,halittar da duk duniya babu ta biyunta a wajensa?.

    “Ba buqatar haka,personal investigation ne,tambaya daya ce kawai zan maka,idan akwai buqatar shiga cikin sai na sanar maka”

    “To officer ba damuwa” .

    Wayarsa ya ciro daga aljihunsa yana rawa,ya buda hoton widad sannan ya miqa masa yana hadiye wani abu mai tauri a wuyansa,zuciyarsa kamar zata fashe

    “Zaka iya shaida wannan fuskar?,ina nufin ka taba ganinta a nan wajen naku?” Cira kai yayi daga kallon fuskar,ya shaidata sosai,matar da yayita jiya mamaki da yaji tana hausa,don bai zaci ta iya hausa ba

    “Tabbas jiya ma na ganta”

    “La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” ya furta yana saurin dafe qarfen qofar sanadiyyar jiri da yaji yana niyyar kayar da shi, idanunsa suka rufe na wucin gadi,da qyar ya samu ya daidaita kansa jin security din yana tambayarsa lafiyarsa lau?.

    “Na gode” ya fada yana karbar wayar daga hannunsa,sannan ya juya da wata irin tafiya yana nufar motar.

    Koda ya shiga sai ya saka kansa tsakiyar hannayensa yana jin kamar ana masa laguden tashin hankali,wani saqo can qasan zuciyarsa na gaya masa qarya ne,amma wani abu mai qarfi yana taso masa daga wani guri da baisan ina bane,yana gasgata masa abinda yake son ha zarga din

    “Idan hafsat kishiyace,bata qaunar ta,zata iya mata sharri,shi kuma wannan security din fa?,meye hadinsa da ita da zai mata sharri?,ga shaidu da suka tabbatar kuma da haka?”

    “Sir…….sai ina?” Muryar yaron ta kutsa tunaninsa

    “Kaini gida”ya furta ba tare da ya iya daga kai ya kalleshi ba.

    Farfajiyar gidan babu kowa,sai lawal dake zaune daga bakin gate yana yiwa hafsat CID din shigowar abbas din,ko karbar key din motar bai iya tsaiwa yayi ba ya wuce sashensa,yace lawal ya sallami yaron da kudi masu nauyi ya karba key din ya bayar cikin gida a ajjiye masa.

    Kansa a sama ya wuce sassan widad,hakanan yaji ko sassan nata bayason kallo bare ya hangeta.

    Da murnarsa ya kirga kudi ya bashin,ya karbi key din ya wuce sashen hafsat kansa tsaye baki har kunne,lallau yau ya warke,aljihunsa zai jiqe.

    Tana jin muryar sa ta fito da gudu gudu daga kitchen tana watsa hannaye idanunta a waje,irin na mutumin dake jiran wani kyakkyawan albishir

    “Ya ake ciki?” Dariya yadan saki

    “Da alama komai ya kankama fa,sassansa ya wuce yana tafiya da qyar,ga key dinsa nan”

    “Ma sha Allah,miqomin shi,ina zuwa” ta fada tana karbe key din,saura kadan ta fadi saboda yadda zaninta ke hardeta ya fice daga falon.

    Ba abinda ya iya cirewa daga jikinsa banda takalminsa,sassan fes wanda yake da yaqinin gyaran da widad din tayi ne randa zata fita a girki,abinda ya sake dagula masa lissafi,da qyar ya iya zama saman kujerar.

    Duk inda ya kwaso lissafin sai ya wargaje masa,yaji har cikin zuciyarsa yana qyamarta sosai,haske da tagomashin data samu cikin zuciyarsa wani qaqqarfan abu yana shirin tasowa ya lullubeshi fes!!! Ta yadda ko burbushinsa ba za’a samu ba.

    Sai data dan tsaya ta saita nutsuwarta a bakin part din nasa sannan ta tura qofar tayi sallama,bata ko duna yanayin shigarta ba dake a jikirce,wata rigar kamfala da sukayi anko ce ash color da aka yiwa dinkin half bubu,ta daura zanin atamfa a sama,sai dankwalin kamfalar a kanta data masa wani dauri kamar na ‘yan talla.

    Sosai kamfalar ta fidda duhunta,don dama daqyar tayita,don kala ce dake nuna baqinta,wannan yasa bata cikason abu ash ba.

    Da qyar ya bude idanunsa ya watsasu a kanta yana amsa sallamarta,sai yaji kansa ya sake sarawa,ya zuba mata ido harta iso gefansa hannun kujerar da yake kai

    “Sannu da zuwa daddyn mimi”

    “Yauwa sannuku”

    “Ya hanya?”

    “Alhmdlh ya yaran?”

    “Lafiya lau,sun gaji da jiranka sunyi bacci,yau kayi delay na dawowa,hala ka tsaya wani waje ne?” Kai ya girgiza mata,haka kawai yaji baiso tasan damuwarsa,tunda dama asalan basu saba haka da ita ba,batasan damuwarsa ba,shi daya yake cinye kayansa yayi solving dinta,saiko hajiyarsa Allah ya jiqan rai,ita kuma ba kowacce damuwa yake gaya mata ba,saboda kiyaye lafiyarta

    “Sokoto to bauchi kinsan tafiyar ba kadan bace” saita gyada kai

    “Ummmm,kuma fa hakane” daga haka shuru ya biyo baya a tsakaninsu,tanason taji ya sake cewa wani abu, tanason taji koda kalma guda daya daga bakinsa amma yaqi magantuwa,daga bisani ma sai ya miqe yana shirin shigewa bedroom dinsa

    “Baka buqatar komai?” Bayajin zai buqaci wani abun,amma kuma idan baice komai din ba bazata qyaleshi ya huta ba,a yanzun kadaice kawai yake buqata ko zai samu sararin yin tunanin mafita ga gagarumin ibtila’i ko musibar data afko rayuwarsa

    “Ki kawomin black tea”

    “In sha Allah” ta fada da wani yanayi da sam bata saba ba,hakan ya sanya ma abun bai wani karbeta ba.

    Ta gama shirya komai tsaf sai zaman jiransa da takeyi,tayi shiga irin wadda tasan yana tsananin so,tayi kewarsa kwana dayan nan kacal,ya shiga rayuwarta da yawa,ko yaya suka nisanci juna dukkansu saisun galabaita,ta samu wasu satar amsoshi da yawa a group dinsu na hanyoyin da zaki sake tsayewa mai gida a rai da takeson ta gwadasu a yau din,ita ta yarda da kanta,ta kuma yi imanin ta tsaya a rayuwar uncle din nata yadda ya kamata,amma kullum tunaninta da burinta shine taci gaba da tsaiwa a wannan matakin ba tare data cutar da abokiyar zamanta ba.

    Har aka idar da magariba tana sake gwada wayarsa amma still a kashe,sai abun ya soma bata tsoro,tayi Shuru saman abun sallah,cikin zuciyarta tana addu’ar Allah yasa lafiya,ta qiyasta wasu awanni,indai suka shude bai iso ba,bai kuma bude wayarba zata magantu,ba zata iya jurewa ba.

    Har isha’i shuru,don haka bayan ta idar da sallar isha din saita zura slipper dinta ta dora babban hijab saman qananun kayan jikinta sabbi fil data saka sabodashi,ta fito farfajiyar gidan tana neman fahad.

    Da motarsa ta fara yin ido hudu,mamaki ya cikata,sai taja burki kawai tana kallon motar,yaushe ya shigo?,shine tambayar da takewa kanta,amma saita bawa ranta qila tana tsaka da sallah ne yanzu yanzu shi yasa bataji ba.

    Muryar fahad taji a bayanta,saita waiwaya

    “Yaushe daddy ya shigo ne?”

    “Kai ai ya kusa awa biyu inajin”

    “Ok inajin ya leqo ina ciki” ta fadi yana qoqarin danne damuwa da mamakin nata dai,sai tayi gaba tana cewa yadan duba mata affan a falo kada ya tashi ya fara koke koke.
    [18/05, 6:54 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 35

    A Rubuce Take Book 2 Page 35

    Part 02

    Page 35

    Wannan shine babban damuwarsa kafin ya tunkari abinda yake gabansa.

    *******Qarfe daya na tsakiyar dare ya farka da wani irin mugun gumi da yake karyo masa,saboda riqewa da qirjinsa yayi da wani irin mugun ciwo,da qyar yake iya jan numfashi,ya laluba hannunsa ya kunna fitilar gefan gado,haske ua gauraye dakin nasa,shi daya yake kwana,bai taba takurata ko sau daya akan su hada makwanci ba,hasalima ta lafiyarta yake,ya sauko daga gadon ya fita waje don ya samu ruwa mai sanyi yasha ko qirjin nasa zai sake,ya tabbatar ciwon da yaketa dannewa ne yau yaci qarfinsa.

    Haki ya dinga yi sosai bayan yasha ruwan,ya samu hannun kujera ya zauna yana riqe da qirjinsa,a hankali ya fara kiran sunan Allah ganin ciwon yana neman yafi qarfinsa.

    Tana yawan fama da qishirwar dare,tsakiyar baccinta ta tasheta,ta farka a hankali tana mutsitsike idanu sannan ta zauna sosai tana kallon sashen da abbas din ya zauna dazun,wayam babu shi,ya zauna ne yana karanto mata wasu laifuka cikin system dinsa da wasu suka aikata ya kamasu ya kaisu kotu da hukuncin da kotu ta yiwa kowannensu,batasan sanda bacci ma ya dauketa ba.

    Ba ruwa a dakin,dole ta gyara farar hular data dora kan sassalkar sumarta ta zura bedroom slippers dinta ta fito.

    Da farko tsorata tayi jin alamun mutum cikin parlor din,amma kuma sai sautin muryarsa dake tashi can qasa ta gaya mata waye,cikin tashin hankali sosai ta iso gareshi.

    Gaba daya ta rude da yadda taga ya fita a hayyacinsa,tana ta son ta kira wani cikin mutanensu na nan amma ya riqe hannunta gam ya hanata motsawa,batasan sanda hawaye ya fara zaryar saman fuskarta ba,yanayin yadda yake riqe da qirjinsa ta tabbatar ulcer dinsa data jima bata tashi bace a yau ta tashi,kuma ko bai gaya mata ba ta tabbatar abincin data bashi ne yaci.

    Sosai hankalinta ya tashi,gani take kamar mutuwa zaiyi a daren,kamar bazai kwana ba,indai hakan ta kasance kenan itace ajalinsa?,abinda ya sake daga mata hankali ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai.

    Duk da cikin ciwo yake amma hakan bai hanashi jawota cikin jikinsa ba yana dan bubbuga bayanta

    “Kayi haquri daddy,ni na jawo maka”

    “Shshshsshsh” kawai yace da ita,sai tayi lamo cikin jikinsa,cikin ikon Allah zufar jikinsa ta fara raguwa,kasa sakinsa tayi,har zuwa sanda taji numfashinsa yana sauka a hankali da alama bacci ya fisgeshi.

    Har zuwa lokacin bata bar share hawaye ba,ta sake qanqameshi cikin jikinta tausayinsa ya kamata a karo na farko,hajiya ce ta fado mata,tayi imani inda tana raye ko meye zai faru bazaikai tsananin wannan ba,ta tuna maganarta ta qarshe akan abbas da affan

    “Allah ya baki ikon riqesu gaba daya” har maganar ta bawa widad din mamaki,ashe kusan wasiyya hajiyan ke bata.

    Dukkansu kukan affan ne ya tayar dasu,da tafiyarsa daya fara koya ya qaraso wajen,sai abbas din ya miqa hannu yana daga kwancen ya daukoshi cak ya azashi saman ruwan cikinsa yana kallon yaron fuskarsa dauke da murmushi

    “Am sorry son…..na hanaku bacci kai da mamanka ko?” Ya fada a karye,saita miqe ta zauna sosai tana masa sannu kafin ta kalli agogo,an riga an idar da sallar asuba,dole sai hakanan suka yita a makare.

    Yau din musayar aiki akayi,ta hanashi yin komai tayi dukkan wani aiki kamar yadda ta saba a baya,yana kwance yana binta da kallo,duk inda ta gifta sai wani abu ya motsa ransa,zuciyarsa bata masa dadi da yadda ya zargeta ya dasa bacin rai a ranta,ashe yaransa har biyu suna kwance a mahaifarta.

    Wuni sukayi ranar a tare,har bayan la’asar tana ta hidimar hada musu abincin dare,affan yana kwance saman cikinsa,tayi tayi ya dagashi saboda qirjinsa amma yace

    “Ki qyaleshi,yayi missing dina shima” tasan akwai magana a bakinsa amma ta shareshi.

    Cewa yayi tazo ta dauke affan din,tana isowa yasa hannu ya janyota jikinsa,sannan ya sauke affan a gefe,sosai ya sakata cikin jikinsa yana kallon fuskarta

    “Da gaske widad….bagarar dani kiketa yi,yau kwanaki nawa da dawowarki,da gaske bakiyi missing dina ba?,hala kin daina sona?” Ya fada murya a karye,hannu tasa tana ture fuskarsa daga tata,saboda wani nauyi yake sakar mata da manyan idanun nan nasa

    “Daddy bamu da lafiya dukkanmu,ka barmu mu warke cikin salaama” ido yadan lumshe sannan ya budesu ya zubesu fes kan fuskarta,saita janye idanunta tayi kamar bata ganshi ba

    “Alright…..jibi nakeso na wuce bauchi” ta daga kai a hankali ta kalleshi,ranta yadan quntata kadan da zuciyarta ta tuna mata da hafsat,wajenta zaije kenan?,kamar yasan me take rayawa sai yace

    “Wani aiki ne mai muhimmanci ya tasomin”

    “Amma daddy,su office din basusan har yanzu baka gama warkewa ba?”

    “Saun dauka na gama warkewa sumul,tunda sunsan ina da jarumar mata dake bani kulawar dake warkar da zuciya da gangar jiki,basusan wannan karon ta zama raguwa ba” kanta ta kawar kawai,tasan jan magana yakeso,ya saki boyayyen murmushi,wannan boyayyen fushin nata ya barta ne kawai,yana jiran lokaci,zai sauke mata shi tassss,a yanzun taci albarkacin abinda yake jikinta ne,amma itama ta sani,yasan lagonta fiye da yadda take tsammani,ya kauda shurun da ya wanzu a tsakaninsu

    “Aikin yana da muhimmancin da bazai iya jikirtuwa ba,saidai kiyimin fatan nasara kawai” ya fada yana lumshe idanu,yana tuna wayar da sukayi dazu da umar dinsa,wadda a qalla ta kwashesu kusan awa guda.

    “Allah ya bada sa’a ya kuma bada nasara”

    “Ameeen ya hayyu ya qayyumu”.

    Bayan ya kwantar da affan sai ya bita kitchen suka kama aikin tare,ba wata doguwar hira a tsakaninsu,amma lokaci lokaci tana kamashi yana satar kallonta,kallon da batasan na meye ba,daga bisani ya gaza jurewa,ya zagayo ta bayanta ya riqe qugunta sosai ya jawota cikin jikinsa, ya dora habarsa saman kafadarta

    “Wannan cikin yayi miki kyau fiye dana affan,ina fatan zaki bani baby girls masu kama dake this time around” murmushi ta saki tana jin saukar numfashinsa har cikin kunnenta,hakan kuma ya fara tayar mata da tsigar jikinta,saita zame a hankali

    “Eheeennnn…..gwara ma ka fadi gaskiyar ka,koda baby girls dinne masu kama dakai kakeso,ka dauka ba’a gayamin ba,sanda na haifi affan yadda ya deboka ya dinga maka dadi har baka iya jure fada” siririyar dariya ya saki,ya koma ya jingina da kitchen cabinet yana kallon kyakkyawar fuskarta

    “Bakisan kin fini kyau ba?,affan namiji ne,duk munina idan yayoni ba matsala,kinga kenan dama baby girls din ne yafi kamata su dauko ki ko?” Yadda ya kira kansa da mummuna ya sanyata dole ta daga kai tana sake dubansa da kyau,suka hada ido yayi wani kalar tausayi kamar ita zata zana masa yaran,sai dariya ta qwace mata.

    A sirrance ya sauka a bauchi,ba wanda yasan ya iso bauchi sai umar,ya kuma gana da manager din hotel din a ranar bayan ya kama daki a wani hotel na daban.

    Duk wani dauka na cctv camera dake hotel din saida yasa aka sauke masa,tun daga kwanan watan da kwanyarsa zata iya riqe masa na sanda suka fara zuwa weekend shi da widad,ya wuce dasu dakin hotel dinsa dasu.

    Sai da ya gama komai ya nutsu sannan ya fara bibiya,komai tiryan tiryan,bayan ya bawa umar wasu yace ya tayashi,amma ya tabbatar sai yana kebantaccen waje kamar haka.

    Aikin ba wani sabon aiki bane a wajensa ba,yana da kafiya da jajircewa akan aikinsa,idan yasa qahon zuqa akan abu sai ya ganoshi,saidai idan baiyi niyya bako bai sa kansa ba,wannan na daya daga cikin sirrin samun qarin girmansa akai akai,dom haka kuma zama bibiyat dukka motsin hotel din na watanni bai wani jigatashi ba,daren gaba daya ya sadaukar yayi wannan aikin,sai coffe kawai da yake makawa cikinsa.

    Ya tsaya ya jajirce yayi aikinne bawai don har a sannan akwai sauran zargin widad a ransa ba,a’ah,yayi hakanne saboda ya zamana shima yana da hujja kamar yadda tsarin aikinsu yake.

    Bai gama ba sai kusan azahar,zuwa sannan idanunsa sun kada saboda tsabar rashin baccin da kallon abu daya,amma duka wannan bai dameshi ba,sai wata nutsuwa data dinga saukar masa

    “Subhanallahi wabi hamdih,subhanallahil azeem” ya dinga maimaitawa yana lanqwasa yatsunsa,cikin tsakiyar kansa yana sake samun kansa da tuhumar kansa da kansa,tuhumar da tunda ya dawo hayyacinsa yakewa kansa,har yau kuma ya rasa dalilin da yasa ya fita hayyacinsa a wancan lokacin da har yau iya aminta da wannan mummunan zargin wa widad,wanda baisan me zaiyi da zai wankeshi ba,amma ya dora hakan bisa mizanin qaddara da jarrabawar rayuwa da rayuwar kowanne bawa bata rabuwa da ita.

    Ko kwana daya bai qara a hotel din ba ya hada kayansa gaba daya ya kira umar yace yazo ya kaishi gida,yawan baccin dake kansa bazai samu sakewa yayishi cikin dakin hotel din ba.

    Yana cikin mota ya kira Ezekiel,daya daga cikin yaransa dake bauchi,ya kuma bada umarnin ya hada yara suje su kamo masa lawal duk inda yake,amma bayason sunansa ya fito a ciki gaba daya,ko don saboda yaaya sa’id(mahaifinsa),ya masa bayanin kalar tuhumar da yakeso ayi masa,ya kuma aika masa da number wayar lawal din,yace kada su karbe wayarsa,muddin ya buqaci kiran wata me suna hafsat su bashi dama ya kirata,sannan ya kashe wayar,ya maida bayansa sosai jikin makarin kujerar yana karkata akalar tunaninsa kan next target.
    [22/05, 3:23 pm] +234 903 635 3539: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 32

    A Rubuce Take Book 2 Page 32

    Part 02

    Page 32

    “Hasbunallahu wani’imal wakil,ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis” itace ya samu kansa da maimaitawa,jujjuya kansa kawai yakeyi yanajin kamar zai zauce,kamar hankalinsa na shirin yin qaura daga gangar jikinsa ne,wasu irin muryoyi ne daga qasan zuciyarsa ke karanta masa abubuwa iri daban dabanya kama kansa da kyau ya riqe,sai yaji hawaye na shirin fita a idanunsa,kewar hajiya ta mamayeshi,ita daya ce yake iya jingina da ita a duk sand aya shiga matsanancin hali irin wanna,ita daya yake raba yaji snayi ya kuma samu mafita cikin sauqi,gaba daya kansa ya gama kwancewa,yanason yayi wani abu amma sai yaji kamar ana dannarsa,a wannan gabar abu daya ne kadai tunda ya darsu ya kasa barin zuciyarsa,yana son widad ta dawo,koma yaya ne yanason ta dawo,idan ta dawo koma meye sai yafi gabatar dashi a nutse,nesantarsa da tayi sainyakejin kamar bashi da sauran komai da ya rage masa a rayuwa,gaba daya maganin da likita ke bashi da sauran treatment da yake bashi ana bashine kawai badon suna wani amfani ba,a wannan rana da kansa ya kira yace ayi masa allurar bacci,saboda daina gane komai da yayi,kowanne sashe na zuciyarsa da abinda yake umartarsa da ya aikata.

    Cikin kwana uku ya gaza samun sukuni,gaba daya a rikice yake,yanatabyaqi da zuciyar dake umartarsa da nisantar widad da dukkan wani abu da ya shafeshi,ya dinga naci wa su kawu hassan da basu haquri,ba yadda suka iya,shi din mai alkhairi ne da maida damuwarsu tashi,haka suma suka dinga ziryar zuwa kano neman bikon widad din,zukatansu suma duka babu dadi.

    Tun abba yana saurarensu tare da jadda musu cewa,shifa takardar sakin widad yake jira bawai batun biko ba,har takai yama daina sauraron kowa a cikinsu,ba abbas da har yanzu yake kwance yana jinya ba,hatta dasu kawu hassan abun ya daure musu kai,don basu tsammaci samun hakan daga wajen abba ba.

    A yanzun har takai ta kawo baya saurarensu,sai yasa a kaisu dakin baqi suyita zaman jiransa,har sai sun gaji sun tafi.

    Yanayin da yake ciki na jinya a asibiti ne kawai ya hana su kawu zame hannunsu daga batun bikon widad din,duk yadda suke zaton al’amarin daga wajen abban ya wuce nan,dole suka yanke shawarar tuntubar tsoho mai ran qarfe alhaji salim,suna da yaqinin shi kadai ne zai iya masa magana yaji,shi daya ne zai iya sakashi yayi.

    *******K’arfe takwas na safiya ne,tana zaune saman kujerar dining din ummu tana kurbar tea mai dumi sosai,a yanzun ta zama wata acici,ita da abinci bai wani dameta ba,amma yanzun tun farar safiya take fara neman abinci,ita kuwa latifa bata gajiya da bata duk kalar abincin da takeso.

    Cikin kwanakin ta gama amincewa juna biyu ne da ita,bata buqatar zuwa asibiti su gaya mata,don dukkan wasu alamu sun nuna mata,a yanzun ba kamar lokacin cikin affan bane,babu quruciya sosai a kanta bare ta gaza fahimtar komai.

    Hankalinta a tashe yake sosai da fahimtar hakan da tayi,duka duka watan affan nawa?,sai taji tana shakka da d’ar d’ar na gayawa wani,a wannan situation dinma da take ciki?, yanayin da take ciki na zargin zina daga mijinta,mutumin da ya kamata ace shine mutum na farko da ya fada bata yarda?,sai ya zama shine mutum na qarshe da zai gasgatata?,iya wannan tunanin ya sanyata taji ta qoshi da tea din,ta ajjiye cup din gefe tana ta kokawar yage tunaninsa ta ajjiye gefe kamar yadda ta daukarma ranta,cikin kwanakin ta dan samu nutsuwa albarkacin addu’a da kuma karbar qaddararta da tayi,ta jawo wayarta ta buda tana duba saqonnin customers dinta,don har harkar business dinta ta dawo kai yanzu sosai.

    Sallamar abban nata ya sanyata daga kai da sauri,ta kuma miqe tana masa sannu da zuwa cike da mamkin fitowarsa da safe haka,saita samu kanta da faduwar gaba,amma ganin baice komai ba sun gaisa kamar ko yaushe yana tambayar abokinsa affan saita saki jiki,ummu ta fito ya tsugunna ya gaidata

    “Alhajin ya tashi?”

    “Eh kai yake jira ma,yace zaka kaishi dubiya”

    “Na iso, za’a sanar mas ako za’a min iso”

    “Bari na shaida masa” ummu ta fada tana komawa ciki.

    Ba jimawa ta dawo ta gaya masa yace ya jirashi,minti goma basu cika ba tsohon ya fito a shirye tsaf yana qamshi cikin farin kaya da farin rawani,shigar da yafiyi,ko gaisawa bai tsaya sunyi ba yace suje sa gaisa a mota,ummu da widad sukayi musu fatan dawowa lafiya suka fice yana takewa tsohon baya.

    Sai da suka dauki hanya sosai sannan tsoho yayi magana

    “Mamuda an kawo min qararka,surukanka sunce kaqi haquri ka basu bikon diyarka ko?” Nauyi yadan kama abba kadan,mutanen sun masa shigar sauri sunyi kuma mugun shammatarsa,sam hankalinsa baikai zasu nema alhajin ba,da tuni ya musu kandagarki ko ya yiwa tufkar hanci,so yake ya hukunta hafsatun harma da abbas din gaba daya,ta yadda a gaba koda wasa abu makamancin wannan bazasu bari ya sake faruwa ba.

    Ya muskuta ya dan gyara zamansa zai bada uzuri tsohon ya tari numfashinsa

    “Kanaso ayi amfani dakai a ruguza auren widad kamar yadda akeso ta faru ko?,wannan abun da kake shirin yi ba komai bane face hanyar cikawa maqiya burinsu,koma waye ya shirya wanna,ya shirya hakanne na tabbatar don yaga bayan auren yarinyar,to inason ka bawa mara d’a kunya,ka turawa koma waye aniyarsa ka maida widad dakinta,sannan ina me baka shawarar ka barwa Allah,duk yadda zaka hukunta wanda yayi mata wannan qazafin baikai hukuncin da Allah zaiyi masa ba,qarshenta kasa a daure maka shi ko?,to daurin da Allah zaiyi masa har yakai wanda zakayi masa?” tunda alhaji ya fara magana gyada kai abba yakeyi cike da gamsuwa

    “Hakane,in sha Allah za’a yi yadda kace alhaji”

    “To alhamdulillah,Allah ya tsare gaba,ya basu zaman lafiya dawwamamme,ya kauda sharrin maqiya da mahassada”

    “Ameeen ya hayyu ya qayyumu” abban ya amsa masa.

    Sai bayan sun gama harkokinsu da alhaji ya maidoshi gida sannan yasa aka kira masa widad,a sannan bata jima da gama sallar la’asar ba,tana saman abun sallah tana cin popcorn,wai yunwa takeji bayan duka abincin da taci,tana jira latifa ta gama gasa mata kifin da take sha’awar ci,ta ajjiye popcorn din ta miqe tsam ta fita a dakin.

    A falon baqi na gidan ta sameshi shi daya zaune

    “Shigo mana widad din ummu” ya kirata da sunan da ake yawan kiranta,wanda bata taba ji ya kirata dashi ba sai yanzu,ta qaraso kanta a qasa ta zauna gefe.

    “Allah yayi miki albarka,Allah yayi miki albarka,ya sake tsaremin ke”

    “Ameeen ya hayyu ya qayyumu abba,na gode”

    “Kinsan dalilin da yasa na kiraki?” Saita girgiza kai alamun a’ah

    “Inason ki gayamin gaskiyar abinda yake ranki,banaso ki boyemin komai”

    “To abba” ta sake fada tana bashi dukka hankalinta

    “Kinason ki koma gidan mijinki?” A wani mugun ba zata maganar tazo mata,har sai data daga kai ta kalli abban nata sannan ta saukar da kanta qasa,tun randa taji labarin zaryar da su kawu hassan keyi wajen abban nata,bata sake bari anyi zance makamancin hakan a gabanta ba,don zuwa yanzun ita din bata jin akwai sauran gurbin abbas a zuciyarta,ta soma sabuleshi daga rayuwarta.

    Har sau uku abba yana sake maimaita tambayar amma ta gaza amsa masa da komai,sai ana ukunne wasu hawaye masu zafi suka zubo mata,yadda abban yake nanata tambayar kamar yana alamta mata ya bada kai bori ya hau,su kawu hassan sun rinjayeshi

    “Ni bana buqatar komawa gidansa abba,bana so,amma indai kai kana da buqatar hakan,zan maka biyayya abba zan koma” ta qarasa fada kuka yana qwace mata.

    Sake saka mata albarka yayi sosai tausayinsa yana ratsata,ya dora da cewa

    “Ni bazan cuceki har abada,bazanso kuma ki shiga takura da damuwa ba,burina dukkanku ku rayu rayuwa ingantacciya me kyau,inaso ki koma gidanki,zan kuma maidaki ne saboda maqiya susan cewa basu isa su raba aurenku ba,kiyi haquri idan hukuncina baiyi miki dadi ba”

    “Kafi qarfin haka abba a wajena,ka isa dani ta kowavce fuska” tayi maganar siririn kuka yana qwace mata,don tuni ta fara shiryawa kanta yadda zatayi rayuwa ba tare abbas din ba.

    Maganganu masu dadi da kwantar da rai yayi mata gami da nasiha da jan hankali,har sai da kukan nata ya ragu sosai sannan ya sallameta,bayan ta fita kuma ya kira kawu hassan ya basu bikonta a bisa sharadan da idan ya amince dasu widad zata koma dakinta,idan kuma bai amince ba a shirye yake da karbar takardar sakinta.

    Na farko abbas din bazai sake hadasu zama gida daya ba tsakanin hafsat da widad,kowacce ta zauna gidanta daban,yace sam zamansu bazai yiwu ba,baya ga banbancin shekaru,irin wadan nan abubuwan da suka fara bullowa a tsakaninsu ba’a san gaba me ta dauki aniyar aikatawa ba,saboda bazai iya dauka da jurar abinda zata bullo dashi a gaba ba idan wannan sun barta da Allah sun qyaleta,na biyu ta kiyayeshi,koda wasa ya sake jin labarin ta aikata abu makamancin wannan to fa duk duniya babu mai tanqwarashi akan matakin da zai dauka dangane da ita,dukkansu sun aminta da wannan sharadin,sun kuma gode masa da har ya nuna dattako ya haqura yayi kawaici akan shariar da yace zasuyi,sun zaunar da hafsat kuma sun gaya mata komai,wadda tuni cikinta yayi bala’in durar ruwa sanda taji batun kai qara kotu,tana tsoron kada ballinta ya tashi,ta tabbatar idan asirinta ya tonu ta ba makawa wannan karon ba asiri ba,ko meye tayi abbas din bazai qyaleta ba,tanason taji cewar kotun za’a je ko an fasa?,amma ta rasa amsa daga wajensu,saboda batason ta matsa da tambayar da zata alamta musu bata da gaskiya,ta wajen abbas kuwa ta kasa jin komai,don ko wayarsa ta kira bashi yake dagawa ba, samuel ne ko wani cikin yaransa,kuma duk sanda zasu daga din zasu gaya mata ne cewa bacci yakeyi,sai suka barta cikin duhu,duhun da ya tafi da dukka nutsuwarta,dare da rana tana zulumin da tsoron ta ina ballin zai tashi?,abu daya yadan kwantar mata da hankali,kudaden data aikawa habiba tace ta koma wajen malamin nasu,ya kuma shaida mata magana ta mutu,har abada abbas bazai sake iya tada zancan ba,kai hatta da komen widad ma,yadda tabar gidan ta barshi kenan yadda yaro ke fita daga cikin mahaifiyarsa,wannan yasa ta saki jikinta taci gaba da sabgoginta.

    Tana kuka tana komai haka ummu ta gyara mata komai nata ita da anty deena,daban anty deena suka kebe da ita ita da anty madeena suka sake mata lecture kan wasu abubuwan masu amfani,wuni guda,itadai jinsu kawai takeyi tana binsu da idanu,gani take a yanzun tsakaninta da abbas ai sai kallo.

    A washegari lafiyayyar motar security tazo ta dauki widad tare da affan zuwa garin katsina,sabon muhallin da gurin aiki ya bawa abbas,tanata kuka ganin alhaji ya hana kowa yi mata rakiya

    “Ku barta ta tafi ita daya,hakan zai bata damar sasantawa da mijinta da wuri,tunda na fuskanci kamar har yanzu akan fushi take”.

    Tafiyar awa biyu da rabi ta sadasu da qofad kyakkyawan madaidaicin gidan,driver ya tsaya yayi hon aka buda qaramin gate din gidan ya saka motar a ciki,ya wuce qaramin parking lot na gidan da bai wuce yaci mota biyu ba ya tsaida motar

    “Rabbi anzilni munzalan mubarakan wa anta khairul munzilin” ta fada tana lumshe idanunta sannan ta budesu,bata taba zaton qaddara zata sake hadasu zama da abbas ba,hakanan a yanzu batasan wanne irin zama zasuyi dashi ba.

    Tana rungume da affan ta nufi qofar da ta tabbatar ta parlor ce,a hankali take takawa,sanye da wata irin doguwar riga ‘yar morocco mai sulbi da tayi masifar dacewa da fatarta data fara sheqi tun yanzu saboda qaramin cikin dake jikinta.

    Yaji shigowarsu sarai amma ya gaza motsawa,yana zaune cikin doguwar kujera hannunsa daya maqale da carbi counter,wanda a yanzun zama tare da shi ne kadai yake bashi sanyi da nutsuwar zuciya,daya hannun nasa kuma wayarsa ce yake duba news akan abubuwan da suka shafi katsina da kewayenta kafin ya gama warkewa ya fara fita aiki.

    Idanunsa qyar akan qofar sanda yaji an tabata,tana bude qofar idanunsu suka gauraya da juna,kowannensu sai yayi qoqarin janye idonsa daga kan dan uwanta,tayi sallama da siririyar muryarta daga can qasan maqoshinta,wanda banda Allah yasa ya saka kunne da kyau babu ta yadda za’a yi yaji abinda take fada.

    Amsa mata yayi yana qoqarin fita daga page din da yake karatun,ya aje wayar hannun kujerar da yake kai sannan ya miqe ya nufota.

    Batasan ya taho din ba,don tunda suka hada ido dashi bata sake marmarin kallonsa ba,ya rame sosai har hakan ya bayyana a fuska da jikinsa,to amma sai taji sam bata damu ba yadda ta saba ji a baya idan bashi da lafiya, taci gaba da takawa zuwa cikin falon,sai ganin mutum tayi yasha gabanta.

    [22/05, 12:28 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 43

    A Rubuce Take Book 2 Page 43

    Part 02

    Page 43

    Sake baki kawai tayi tana kallonsa,ya gama kasheta gaba daya,babu kunya ko kara a lamarin nasa?,sai ya kashe mata idonsa guda daya ya juya ya fice abinsa a falon hankalinsa kwance.

    Yana gama fita ta waiwayo ga hafsat din

    “Ki zauna sai…..”

    “Ba zama nazo yi ba,ga yara nan Allah ya karemin su ya kula dasu,idan kuma aka cucesu Allah ya isansu basu yafe ba” wani lafiyayyen murmushi widad din ta sakar mata hankalinta kwance,ta koma ta zauna saman kujerar ta dora qafarta daya kan daya tana kallon hafsat din

    “Ki kwantar da hankalinki,kowanne tsuntsu fa kukan gidansu yakeyi,mu namu kukan me dadi kyau da ma’ana ne,haka aka koya mana,yara kuwa sunzo gidan ubansu inda yafi dacewa dasu,inda zasu samu kulawar da suka rasa kaf iya tsahon rayuwarsu,na meye kuma zaki damu?,idan ka shuka alkhairi ai baka tsoron ranar girbi……oh……na manta,kina tsoron kada na maidasu ‘yan wanke wanke ba?,ko masu yimin shara ko wanki,ko kina tsoron kada na dinga basu wankin kashin su affan ko su sajjad?” Saita girgiza kai

    “Allah ya tsareni,banason ranar girbi na ta zamemin ranar kuka da nadamar baragurbin shukar dana dasa da hannuna,don haka kije kiyi baccinki harda minshari,zasu samu kulawar da ke kanki kika gagara basu,idan iya abinda ya kawoki kenan sai nace ki gaida gida,na gode da kyautar dan mutum sukutum da kikayimin har rai uku ba tare da nayi naqudarsu ba” saita qwalawa aminatu kira tace ta wuce ciki dasu.

    A karon farko hafsat tabar gidan jiki a matuqar sanyaye,kalaman widad sun bugeta qwarai,anya batayi gwaari ba data dauka yaranta duka ya danqa mata su?,sai shaidaniyar zuciyarta ta jaddada mata tayi dai dai,dole yaran zasu dameta,kuma shine kawai abinda zatayi ta baqanta musu rai,batasan wannan abun da tayi shine abu na farko data yi wanda ya faranta ran widad ba,don kuwa cikin kwana uku kacal yaran suka fara hawa saiti,farincikinsu ya qaru,dadi kamar suyi me babu ma kamar mimi da taji a duniya an gama mata komai,ta dawo waje antynta.

    Wannan kawo sun shi ya bawa abbas damar fara musu shirye shiryen tafiya america din gaba dayansu,ya kashe kudinsa sosai amma baiji komai ba,farincikinsa shine kasancewa da iyalinsa,sai a yanzu yakejinsa cikakken namiji kuma cikakken mutum,widad ta hada masa kan iyalinsa gaba daya,idan ka shigo gidan kai kanka sai ya burgeka,komai a tsare bisa doka da tsari,yaran sun soma samun wata cikakkiyar nutsuwa da kuma tarbiyya.

    Ranar da suka bar nigeria ranar hafsat din ta daura auren da ta dinga fatan abbas din yana nan zata daurashi,to baisan ta daura din ba don tuni jirgi ya lula dasu,koda yaji dinma babu abinda zai dameshi,don a duniya bayajin akwai wanda ya fishi farincikin rabuwa da ita,ya yadda KADDARARSA ce zama da ita,a yanzun kuma yana kyautata zaton yaci jarrabawar da Allah ya saukar masa,shi yasa yayi masa tagomashin rabuwa dashi.

    Rayuwarsu a america tazo da sabon tagomashi qarin wayewa da kuma budewar ido,don a nan ne widad tayi amfani da result dinta tayi course akan kasuwanci na shekara daya,don sun samu qarin wasu watanni shidan,a nan ta hadu da mutane sosai kala kala data qaru dasu,ta fannin gogewar Rayuwa mu’amala da zamantakewa, nau’in girke girke harma da gyaran kai gyaran jiki da kuma kula da iyali da miji gaba daya,ta samu experience na rayuwa me tarin yawa,bayan sun cika shekara suka tattara suka dawo,dukka yaran sun canza,sunyi dima dima sunyi fresh dasu,sai suka zama wasu ababen kallo,widad business dinta ya kankama,don tayi business sosai tacan,ta kawo kaya a shekarar kamar ba gobe,ta rabawa yan uwanta duka harda dangin miji,kowa ya samu alkhairi yayi murna,don sun qaru da ita,wasu har qaramin jarinsu suka tayar,hannunta me albarka ne sosai da komai ta taba sai ya siyu da tarin alkhairin ubangiji,ne yiwuwa zuciya me kyau da take da ita ne ya zame mata silar hakan.

    Kai tsaye suka sauka a tsohon gidansu da suka bari ana yiwa sabon gini,wani irin tsari aka yiwa gidan me matuqar jan hankali kamar a turai,masu sannu da zuwa da zuwa ganin sabon gida aka yita tururuwar zuwa, widad nata jin kunya tana boyen qaramin cikin data dawo dashi,a lokacin duka duka shekarar su sajjad daya da wata shida,ita a ganinta sunyi qanqanta da ayi musu qani,duk da sanda ta haifesu affan ma baikai haka ba.

    kuka ta dinga yi tace ita bataso

    “Ya kikeso yanzu ayi dashi”

    “Nidai a zubar”

    “What!!!” Ya fada da mugun qarfi

    “Eh lallai na yarda baki da hankali,kuma har yau baki girma ba,bari kiji abun Allah ya kiyaye Allah ya tsare,ko cikin shege nayi miki ai baki isa ki zubarmin da ciki ba” cikin wannan rigimar tasu suka iso nigeria,yana shareta tana shareshi,kowa yana ganin yafi dan uwansa gaskiya.

    Yau tunda ta tashi batajin dadin jikinta sosai,don haka koda safe ma tana jinsu suna sabgoginsu daga can babban falon gidan amma bata leqo ba,tasan aminatu zataji da komai,ga adda mimi kamar yadda tasa suke ce mata,yarinyar akwai qoqari,duk wani aikin zaka sameta tana taya aminatu,widad din bata taba hanata ba,saboda tana tuna wahalar data ci sanadiyyar rashin iya komai a aikin gida,duk da gatane na goyon kaka,tafison idan ta tashi aurar da mimi din kamar yadda take fata wanda duk zai auresu ya qare rayuwarsa yana shi mata albarka.

    Tana kwance abbas din ya gama shirinsa,yazo kanta ya tsaya,saita dauke kanta gefe,yakai hannunsa ya taba wuyanta,sai ya sauke ajiyar zuciya jin bawai zazzabin da yake takurata ne a jikinta ba,yana mamakin yadda ta iya shareshi da gasken tsahon kwanakin,sai yasa hannu yadan shafi fuskarta kadan yana fadin

    “Sai na dawo”

    “A dawo lafiya” ta fada ciki ciki,sai kuma tabi bayansa da kallo,bayan ya fitanbta lumshe ido tana fidda numfashi mai sanyi.

    Abbas miji ne na musamman,idan tace na musamman tana nufin hakan,duk yadda sukakai ga fada ko sabani da juna saidai iya kan harshe kawai,amma duk wata kulawa basa fasa baiwa junansu.

    Agogo ta kalla,qarfe daya saura,ta yunqura zata miqe ihun sajjad ya kawo mata har nan inda take,tasa hannuwanta ta toshe kunnuwanta

    “Allah ya yiwa aminatu albarka” ta fada idanunta a runtse,batason hayaniya kwata kwata,banda akwai aminatu da mimi da batasan yadda zatayi ba,dole yanzun ta fita,tasan filin dambe aka bude tsakanin affan sajjad da sajid,wataqila yusra na gefa tana tilliqa dariya,nawwara na qoqarin shigarwa affan mutuminta,saita sauko kawai ta shiga bandaki ta wanke fuskarta da bakinta ta fito ta zura wata sassalkar abaya a jikinta,already da wankanta dama,don bata iya kaiwa haka batayi wanka ba sam,ta zura wasu lausasan slipper kalar abayar ta fito tana daura siririn dankwalin rigar a kanta wanda bai rufe komai a gashin kanta ba.

    Falon kuwa ya kacame gaba daya,duk sun ruda aminatu kamar tayi kuka,dama gata gwanar sanyi,saida widad tayi musu tsawa sannan suka dakata da abinda sukeyi,sai kowa ya fara shiga taitayinsa,suka matso kowa yana gaidata

    “Maami ya jiki?” Suka dinga cewa,mamaki ya kamata,oh wato abbas yace musu bata da lafiya kenan?,zai hada mata case,yanzun idan suka dinga mata sannu har sai ta gaji,har sai an fuskanci abinda ke maqale a jikinta

    “Jiki alhmdlh,na warke ai”

    “Allah ya baki lafiya maami” mimi ta fada cikin damuwa da kulawa

    “Ameen mimi na” tattarasu duka tasa aminatu tayi waje daya,ta kunna musu cartoon din da sukafi so,sai aka samu salama kowa ya nutsu,sai sajjad da sajid da lokaci bayan lokaci ake fama dasu ana bari bari.

    Dining ta wuce ta duba abinda aminatu ta dafa musu,saita zauna daga can saman ta hafa baqin tea tana dan kurba kadan kadan tana kallon yaran,rai shida dukka yaran abbas,ga na bakwai a jikinta,kome zata haifa kuma Alla masani,cikin ranta ta samu kanta da addu’ar Allah ya raya mata su taga girmansu,ya bata ikon ci gaba da tarbiyyantar dasu.

    Qarar wayarta dake gefe ya katseta,ta duba wayar saita saki murmushi,ummunta ce,ta gyara zama ta daga wayar cikin shagwabar da har yau bata iya daina yiwa mutum biyu a duniya ita,suma kuma har yau bata girma a wajensu,abbas da ummunta.

    Ta sakankance sosai suna hirarsu kusan rabin awa,sai taga aminatu ta buda qofar falon ta fita,sai gata ta dawo,ta hauro inda widad ke zaune

    “Maami baquwa kikayi,to mai gadi ya hanata shigowa waisai an gaya miki” mamaki ya cikata,bai tana hana kowa shigowa ba muddin ya yarda dashi sai yau?,da yake qarin matsayin da ya samu yana da me gadi cikin qananun ‘yan sanda,hakanan an bashi driver da security

    “Koma wace a barta ta shigo” ta fada tana maida wayarta kunne,idanunta akan qofar falon har zuwa sanda labulen ya dage fuskarta data jirkice ta bayyana,saita zame wayar daga kunnenta tana cewa ummu

    “Zan kiraki ummu anjima”

    “To babu damuwa” ummun ta fada tana a gaida mata kishiyoyinta da masu gidan.

  • A Rubuce Take Book 2 Page 24

    A Rubuce Take Book 2 Page 24

    Part 02

    Page 24

    Kafin su gama hutunsu a bauchi ta tattauna da mutanen da suka zame mata tamkar fitila a rayuwarta,su anty deena hajiya sha’awa dasu hajiya fanna,anty deena tace

    “Kina ‘yar kano cibiyar kasuwanci ai baki da matsala,kaya kawai za’a yita kawo miki kina saidawa kina maido kudin ana sake miki sari” su hajiya fanna dake ‘yan kasuwa ne suma sukace ba matsala zasu dinga karba,ta zauna tayi shawara da tunani ta zabi kayan da zata dinga saidawa,bata bar bauchi ba saida kayan suka iso,ta raba wasu suka wuce kaduna da wasu.

    Abu kamar wasa saiga kaya sunata shiga ana hada mata kudinta,hakan yayi mata dadi sosai,a cikin lokaci qalilan ta fara gane amfanin sana’a ga mace.

    Ta maida kanta sosai ga kulawa da mijinta da yaronta dake shiga watanni takwas,gasu mimi da takejinsu kamar yaran cikinta,bata da sauran matsala sai godiya ga Allah.

    Watansu daya da dawowa ya dauki su mimi ya maidasu bauchi kan mamarsu ta dawo,bata wani damu ba tunda zuciyarta babu wani mummunan nufi a ciki,saidai bataji dadin tafiyar yaran ba,don hatta mimi taso a barta amma hakan bai yiwu ba.

    *R U B U T A C C I Y A R K’ A D D A R A*

    K’arfe hudu na yammaci,tana kitchen tana aikin abincin dare,affan yana goye a bayanta,don aminatu bata nan tana islamiyya,yau din ta dauko aiki me dan wahala,favourite foods na abbas din takeyi har guda biyu,don ma aminatu ta rage mata wasu ayyukan kafin ta wuce islamiyya.

    Knocking taji anatayi sosai,kamar za’a balla qofar,mamaki ya kamata,sam bata qaunar bugu me qarfi haka,taha tsaki ta share bugun ta qarasa juya miyarta sannan ta ajjiye ludayin ta nufi qofar tana tambayar waye da dan qarfi,saidai ba’a amsa mata ba har ta bude qofar.

    Tsananin mamaki ya kamata ganin abbas a tsaye,ya kafeta da ido kafin ya sanyo kai ciki,saita rabe gefe tana bashi hanya hadi da binsa da kallon mamaki,a hankali kuma ta taka ta bishi a baya jikinta na wani irin mutuwa.

    Sai da ya gama qarewa falon kallo tsaf sannan ya kalli wayarsa dake hannunsa ya maida dubansa gareta da murtukekkiyar fuskarsa

    “Ina kika je?”

    “Ni kuma?,ina zan fita ba tare da saninka ko izininka ba?,ina kitchen ina girki”

    “kina kitchen kuma?” Ya sake tambayarta cikin yanayi na rashin yarda sosai kwance a fuskarsa,abinda ya bawa widad mamaki sosai

    “Eh mana,uncle na taba yi maka qarya?”

    “Amma naketa kiranki baki dauka ba?,kamar kin fita ko kin tafi Wani wajen?” Idanu tadan zuba masa sannan ta sauke ajiyar zuciya mai qarfi,sai kawai ta kama hannunsa suka wuce zuwa bedroom dinta inda tabar wayar a ajjiye.

    Cak ta dauko wayar ta danqa masa a hannunsa,ya dubeta ya dubi wayar sannan ya bude

    “A silent take,ni na sakata saboda inason affan yayi bacci,kada kira ya shigo ya tadashi” wayar yadan juya a hannunsa kadan yana sauke ajiyar zuciya a jejjere,sai ya koma da baya ya zauna a bakin gadonta.

    A matuqar sanyaye ta fice,ta shiga kitchen ta bude fridge ta fiddo zobo me sanyi data hada masa da yaji kayan hadinsu abarba,daya daga cikin nau’ikan zobon data koya a class dinsu da deeja Berver (the best online class da na taba shiga da ya burgeni qwarai qwarai 0907 927 4454).

    Tason yana matuqar sonshi saboda taste dinsa na dabanne da ba ko wanne gida zaka shiga ka samu irinsa ba,shi yasa bata rabo da yi masa.

    Gabansa ta dawo ta durqusa ta soma zuba masa sannan ta miqa masa idanuwanta a kansa,bai musa ba ya karba ya kuma shanye tas ya miqa mata cup din,saita koma gefan gadon ta kwantar da affan sannan ta dawo gabansa ta zauna tana tattara nutsuwarta a kansa

    “Uncle,me yake faruwa?,kwanakin nan gaba daya idan ka kira wayata baka sameni ba sai hankalinka yayita tashi,sannan duka ka gaza nutsuwa a wajen aikinka,me yake faruwa?” Idanunsa ya lumshe yana kada kansa da yakejin ya masa wani nauyi,zuciyarsa kuma tana rabuwa gida biyu

    “I don’t know,kawai dai…….ina tsananin kishinki” shuru tayi tana nazarin maganarsa,a baya yana kishin nata amma ba ta irin hanyar da yanzu yakeyi ba,ya canza kwata kwata,wasu irin halaye yake mata da suke sakata shakku,kamar zargi zargi,to amma tunda ya bata wannan hanzarin bata da hurumin masa hukunci kai tsaye

    “Ka kwantar da hankalinka uncle,ni taka ce har abada” qaramin murmushi ya subuce masa wanda baikai har zuciya ba,ya waiwaya yana kallon affan dake bacci abinsa hankali kwance cikin cikakkiyar tsafta da kulawa.

    Bayan wasu kwanaki da yammacin wata litinin,a yau din ba ita keda girki ba,don haka tun bayan kammala sallar la’asar ta gama komai.nata tana zaune,sai kiran ummu ya shigo mata,suka shiga hirarsu sosai tana wasa da hannun affan dake zaune saman cinyarta yana wasa da teether.

    A qalla sun kusa awa guda,suna gamawa kuma kiran anty fanna ya shigo,suka hau hirar kasuwanci da lissafin kudaden kayan widad din da aka saida wadanda suke hannunta.

    Daga qofar falonta taji ana knocking,ta dauki excuse tace zata kirata ta aje wayar ta miqe tana bude qofar,aminatu ce sanye da kayan islamiyya,hannunta riqe da waya

    “Aah,har an taso?” Widad ta tambayeta

    “Aah anty,yau korar school fees akeyi” dan bata rai tayi kadan

    “Amma sau nawa zan gaya miki,duk sanda wata ya qare ki dinga tunamin ina baki?”

    “Mamace tace na qyaleki hakanan,wancan watan kin kawo kayan abinci,yanzu kuma……” Sai maganarta ta katse saboda ringing da wayar hannunta ta fara,duka suka kalli wayar a tare

    “Wayar waye wannan?”

    “Wani ne,da uniform irin nasu abban affan,yace sunanshi samuel,oga ne yace wai a kawo miki wayar zakuyi magana” ta gane komai a dan bayanin aminatun,amma sai mamaki ya kamata,tasa hannu ta karbi wayar,kafin takai ga dagawa ta yanke,saita saki qofar ta juya cikin falon jikinta a matuqar sanyaye,abun na abbas har ya fara kaiwa haka?,meye haka mai qarfi ya shiga zuciyarsa dangane da ita?.

    Tana shirin zama amintu ta sunkuya ta dauki affan tana masa wasa sai gashi ya sake kira,batayi qasa a gwiwa ba ta daga wayar ta sakata a kunne tare da yin sallama.

    Maimakon ya amsa sai ya fadata da fada,ta runtse idanunta tana jin kakkausar muryarsa har cikin zuciyarta,sai ta miqe tsam ta wuce daki riqe da wayar tabar aminatu da affan a nan.

    “Ke dawa kuke waya?” Ya tambayeta bayan ya gama fadan rashin daga wayar da wuri

    “Nida ummu,sai kuma anty fanna”

    “Shine har kusan awa daya da rabi?” Mamaki ya sake cikata,to meye a ciki?,yasansu kuma dukkaninsu dama idan tana waya dasu tana dadewa

    “Eh lissafin kaya mukeyi da ita,ummu kuma dama kasan hirarmu ai” Shuru ya danyi sannan yaja tsaki ya kashe wayar.

    Duk yadda taso danne zuciyarta amma ta gaza saida hawaye ya silalo mata,wai meye hakan?,me yake faruwa?.

    Sai data dan koka kadan zuciyarta tayi sanyi sannan ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta shafa farar powder sannan ta fito.

    Har yanzu suna falo ita da yaron,ta bata wayar tace ta maida masa,sannan ta zauna ta dauki tata wayar tana dubawa.

    Tex ta rubuta masa na ban haquri,duk da abun naci mata zuciya sannan ta tura masa,saita koma ta zauna jikinta gaba daya babu qwari.

    Falon shuru saboda aminatu ta fita da affan,zuzzurfan tunani ta shiga tanason gano ainihin abinda ya kawo wannan lamarin tsakaninta da abbas din amma ta gaza gano komai,cikin haka ta kwashe awa kusa biyu,ta daga idanunta tana kallon qofa sanda taji ansa key ana qoqarin bude qofar.

    Tasan waye,don shi kadai keda key din gidan,miqewa tayi cak da nufin shigewa bedroom dinta,motsinsa da taji kadai ya karya mata zuciya,bata kuma so tayi kuka a gabansa,saidai ta makara,bata kai ga isa dakin ba ya shigo,kuma ya ganta,yana dauke da affan,da alama ya tsaya ya karboshi ne.

    Daga nan inda yake ya tsaya bayan yayi sallama yana kallonta,ta amsa amma bata juyo ba,sai ya tako a hankali ya iso bayanta ya rungume ta ta baya,saita sake masa kuka kawai.
    [16/05, 5:20 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 29

    A Rubuce Take Book 2 Page 29

    Part 2
    Page 29

    A nutse ta bude k’ofar toilet din ta fito daure da babban towel fari sol,lallausar farar fatarta mai santsi da sheqi tana ta daukan idanu.

    Gaban dressing mirror din dake dakin ta isa,ta ja kujera ta zauna tana kallon fuskarta a ciki,gaba daya jin ranta da jikinta takeyi babu dadi,fuskarsa ke gilma mata cikin idanuwanta,sam jikinta bai bata ba,ta kasa nutsuwa gami da gamsuwa da wannan tafiyar da ya qirqirar mata bagtatan lokaci guda,tana tsaka da hidindimunta,tun daga yanayi fuskarsa da kuma yadda ya dinga tuqi daga bauchi zuwa katsina takejin kamar ba abbas dinta ba,tabbas akwai abinda ke faruwa,akwai wani muhimmin abu dake gudana,tayi tunani har babu iyaka,ta laluba dalilin tas tun daga randa ya sanya qafa ya fita daga gidan zuwa dawowarsa da kuma isowarsu katsina……tayi zagaye cikin tunani da abubuwan da suka wanzu kaf! Ta kasa gano abu guda daya farun.

    A iya saninta sun rabu suna masu kewa da kuma shauqin juna kamar ko yaushe,hakanan koda safiyar ranar sun jima ita dashi akan waya suna hira,wata irin hira irin wadda ke fallasa sirrin zuciyar masoyi zuwa ga dan uwansa,yana ta mata qorafin a takure yake acan din tare da mita tana lallabashi tana kuma masa dariya,har suka rabu kyawawan kalamai ne bisa fatar baki da zuciyar kowannensu,to amma me ya canza hakan?

    “AKWAI WANI ABU” ta fada murya qasa qasa tana motsa tausasan lips din bakinta tare da zare idanunta daga kallon da take qarewa fuskartata,ta dauki lotion dinta mai taushi da qamshi ta fara shafawa fatarta cikin kasala taraddadi da kuma damuwa.

    Duk bayan wasu mintuna saita kalli wayarta dake gefe tana tsammanin kiransa,saboda ta sani haka suka sabarwa juna,duk inda zashi cikin nigeria….. matuqar tafiyar mota zaiyi itace abokiyar hirarsa har ya isa inda zashi,idan kuma hakan bata kasance ba…..zaiyita kiranta har ya isa din,amma wannan karon ko gilmawar miscall dinsa bata gani ba bare kiransa,a qididdigen da tayi a yanzun kuma, tabbas koda baije gida ba yana gab da isa

    “Waishin meke faruwa?” Ta sake jefawa kanta tambayar wata irin damuwa tana tabata tun daga qasan zuciyarta.

    Cikin dauriya ta shirya kanta cikin doguwar rigar atamfa,ta fidda ainihin kyanta da surarta sosai,duk da yanayin da take ciki sai data tsaya gaban mudubi ta kalli kanta,lokutta da dama takan dubi kanta da kanta tana tuna WACECE ITA A SHEKARUN DA SUKA SHUDE,a yanzun sai taga kamar ba ita ba…..komai yana zuwa yana shudewa da wani irin sauyi mai ban mamaki.

    Lausasan slippers ta zurawa qafarta,sannan ta isa bakin qofa ta kama handle din ta bude tabi siririn corridor din da zai sadaka da ainihin falon gidan.

    Tun bata qarasa ba ta hangeta zaune cikin falon,halittace mai girman matsayi a wajenta,halitta dake sahun farko cikin halittu mafi soyuwa a wajenta,a duk lokaci irin wannan da zatayi balaguro ta taho takanas saboda kasancewa da ita…..duniyarta kan cika da farinciki,takanji a duniya yanayi irin wannan bashi da tsaara a wajenta.

    A jikinta taji tahowarta,saita dauke idanunta daga kan tv din da take kalla ta maida kanta,kusan lokaci daya suka sakarwa juna murmushi,ta kuma rigata magana

    “Wannan nauyin wankan naki dai yana nan,affan ya fara kuka har sai da aka fitar dashi” cikin karaya da rauni da takeji cikin gangar jikinta da zuciyarta ta qaraso dab da ita ta zauna,tana shirin amsa mata…..kamar me kiran yana jiran dai dai lokacinne kira ya shigo wayarta,a hanzarce ta daga wayar tana duba me kiran, zuciyarta cike da fata da burin ganin wanda ranta ke darsa mata.

    Batasan sanda murmushi ya subuce mata ba hadi da fitar siririyar ajiyar zuciya ba

    “Ina zuwa” tace da mommie,ba zata iya amsa wayarshi a gabanta ba,ita kadai tasan hottest words da suke gayama junansu,kuma muddin aka samu mishkila mommie taji daga ita har shi sun gama tafka abun kunya.

    Kai tsaye dakin ta koma,ta samu gaban madubin data tashi dazu ta zauna tana yunqurin daga wayar

    “Assalamualaikum” ta fada a shagwabe tana karyar da wuyanta gefe,abu mafi soyuwa kenan da tasan yana so tattare da ita,har yau kallonta yake cikin madubin da yake kallonta shekarun baya da suka shude,bata canza a idanunsa ba

    “Wa’alaikumus salam” mummunar faduwa gabanta yayi daka jin sautin muryarsa me taushi da sanyi da yake mata magana da ita koda yaushe ta juye zuwa wata iriyar murya,irin muryar da yake magana da cirminals a yayin da aikinsa ya biyo ta kansu…..irin muryar da yake magana da juniors dinsa a yayin da suke hurumin aiki……irin muryar da yake magana da ita a duk sanda ya shiga qololuwar bacin rai da fushi,muryar da bata taba jin yayi mata magana da ita ba.

    Kowacce gaba ta jikinta tayi sanyi,tayi namijin qoqarin tattaro nutsuwarta da juriyarta tace masa

    “Ka sauka lafiya?,ya kaje gida”

    “Me yasa zaki aikata min haka?” Ya fada muryarsa tana ninka ta da kaushi da ban tsoro,daga cikin wayar tana iya jin hucinsa,da alama a matuqar bacin rai da kuma fusata yake, tambayar tasa kuma ta dilmiyar da ita kogin tunanin ina ya nufa ne?,kafin ta lalubo amsa kunnuwanta sun fara isar mata da saqo mafi muni cikin rayuwarta,daga bakin halitta mafi soyuwa a gareta

    “Ashe haka kike?,ina miki kallon saliha ashe mayaudariya ce ke?,maciyar amana ce?,macuciya ce ke?,na baki dukkan yarda,na damqi miki rayuwata ashe zaki wasa da rai na da lafiyata?” Wani irin tashin hankali ne ya sauko mata,me abbas ke fada ne

    “Me nayi maka?,abban affan me ya faru?,kasan me kake fada kuwa?”

    “Na sani!,nace miki na sani, tsahon yaushe tsahon kuma wanne lokaci kika dauka kina cin amanata kina kuma ha’intata WIDAD?” Kasa zama tayi,ilahirin jikinta ya dauki tsuma,sai ta miqe tsaye qafafuwanta suna rawa

    “Kana cikin hankalinka kuwa abban affan?,a ins kake yanzu?” Ta tambayeshi don ta tabbatar da cewa he’s safe,ba gusar masa da hankali akayi ba yake gaya mata hakan

    “Har kinyi wayon fara bin maza?,ki kwana a hotel?,hakan bai isheki ba har sai kin dauko gardi kin kawomin gidana?,kin kuma kaishi har gadona na sunna widad?,wane laifi na aikata miki haka dana cancanci irin wannan hukuncin?” Yayi maganar ta qarshe muryarsa a wani mugun karye,saidai zafi da kaushin nan suna nan taf a muryarsa

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta fada a bayyane,qafafuwanta suka hau rawa,gabanta yayi wani irin bugawa da zuciyarta ta hasko mata abinda yake magana a kai.

    “Hotel kuma?” Ta tambayeshi muryarta na wata mugun rawa,irin rawar dake bayyanar da zallar daburce wa a sanda aka ritsaka bisa wani abu na rashin gaskiya

    “Bakije bane?,ko zaki shiryamin irin qaryar da kika saba?”

    “Naje,tabbas naje….amm……”

    “Ya isa!!!!” Abinda ya fada kenan a tsawace

    “Abinda nakeson ji kenan kuma naji,kije ke da Allah,bazan taba yafe miki ba,amanata da kikaci ubangiji ne kawai zaiyimin sakayya,Allah ya isa ban yafe miki ba!!!” Kit! Wayar ta katse

    “Abban affan,daddy!!!” Ta fada a gigice,saidai tuni ya katse layin

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta sake maimaitawa jikinta na wani irin kyarma tana yunqurin binsa,saidai a take kamfanin sadarwa suka gaya mata is switched off,saita saki wayar ta sulale a wajen tana sakin wani azababben kuka,wani abu mai tauri da zafi yana tokare mata qirji.

    “Waye ya ganta?,waye ya gaya masa?,waye???” Ta soma nacin gano daga inda maganar ta fita

    “Hafsah” taji an bata amsa daga can tsakiyar zuciyarta,kukanta ya tsaya cak na wasu sakanni,sai ta sake rushewa da kukan tana jin kanta yana sara mata,tana son miqewa amma ta kasa,idan tayi kamar zata tashi sai jiri ya maidata ya kayar,a haka aka turo qofar dakin,ta daga idanunta da taji kamar basa dauko.mata hoton komai da kyau ta tsurawa qofar idanu tanason tantance mai shigowar.
    [20/05, 8:46 am] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 28

    A Rubuce Take Book 2 Page 28

    Part 02

    Page 28

    Ba kowa a falon,saita saka kai zuwa bedroom dinsa,ta isa bakin qofar ta murdata ta tura tana saka kanta ciki.

    Dai dai sanda yake tsaye gaban madubu yana goge kansa da fuskarsa da qaramin towel,ya qurawa fuskarsa idanu da kyau,sai kace wanda yake karantar wani sabon abu daya tsiro masa a fuskar,saidai duka ba haka bane, zuzzurfan tunani da ya cika zuciyarsa fal.

    A hankali idanunsa suka sauka akanta ta cikin madubin dake gabansa,amma sai ya janye idon yayi kamar bai ganta ba yaci gaba da goge jikinsa.

    Ko sau daya a tsahon zamansu bata saba ganin haka ba,don haka bata kawowa ranta wai ya ganta ba,saita fara takowa cikin shagwabar nan tata data saba masa tana cewa

    “Ya da haka uncle?” Ta fadi tana kebe fuska kamar zata sakar masa kuka,duk kuwa da cewa ranta cike yake fal da wasi wasi.

    Bayajin zai iya kallon fuskarta a sannan,saboda wasu abubuwa da zuciyarsa ke sake saqa masa a kanta,sai ya barta bai tanka mata ba,har ta iso bayansa,ta rungumeshi tsam ta bayan,tana dora hannuwanta saman ruwan cikinsa.

    Qamshin turarenta da abaya yafi qaunar ji fiye da komai,a yanzun sai yaji dadinsa yana sauyawa zuwa wani abu da yafi qyama hadi da tsanar shaqa

    “Uncle?” Ta sake kiransa a shagwabe,kanta kwance a gadon bayansa.

    Ajjiye towel din hannunsa yayi saman madubin,sannan ya saka dukkan hannuwansa biyu ya zare hannunta dake saman cikinsa,har zata fara masa tabarar tata ya waiwayo suka hada ido,sai tayi sak tana kallonsa.

    Wani abu take gani yana wulgawa cikin qwayar idonsa, irin abinda bata taba gani atare dashi ba,wani irin kallo da ya sanyata jin ta muzanta gaba daya,kallon da ya sakata ta daburce ta kuma rude,sai kuma ya dauke kansa daga dubanta ya taka gaba zuwa wajen drower dinsa don ya fidda kaya,ta taka da hanzari ta cimmasa,ta kama murfin drower din da nufin budewa ta zaba masa kayan kamar yadda ta saba masa amma sai ya dakatar da ita da kakkausar muryarsa

    “Stop,bashshi kawai” abinda yayi mugun sanyaya mata jiki,yau me ya samu uncle?,me ta aikata masa yake zuwa da baqin halayen da bata taba ganin irinsu tattare dashi ba.

    Tsabar mamaki yasa tayi sakato tana kallonsa,har ya ciro kayan ya dawo gefan gado ya fara fidda na jikinsa don ya saka wadan nan.

    Har yau bata iya kallonsa naked don haka ta russunar da idanuwanta,amma jin muryar hafsat daga falo tana doso dakin ya sanyata zabura ta isa gabansa,ta dauki rigar ta fara ware masa fuskarta qunshe da murmushi tana jira ya gama saka boxer din ya karba,a haka idan ka kallesu saika dauka soyayya ake bugawa a lokacin.

    Sak hafsat din tayi wani idin abu na bugunta

    “Kan jar uba!,kada dai ace wannan plan din ma score zero point,” shine ya fara zuwa mata ka,da kuma irin kudaden xaga narka.

    kamar ta juya da tea flask din kuma saita fasa ganin ya ganta,ta tufa qofa ta shiga idonta akan widad da babu alamun akwai abinda yake damunta.

    Cikin son nuna bariki ta qaraso cikin daki

    “Gashi abban mimi,akwai wani abu da kake buqata kuma?” Kai ya girgiza mata,saita jinjina kai

    “Alright,idan akwai sai kayimin magana”

    “Thanks” kawai yace muryarsa can qasa, saita juya tana ficewa kamar babu abinda ya dameta dasu,saidai can qasan ranta tana jin kamar ta juyo ta dawo cikin dakin ta kora widad din.

    “Ehen……yauwa uncle,ni zan saka maka da kaina please,ka barni na samu wannan ladan” ta fadi a shagwabe da qarfi tana kallon bayan hafsat,dai dai sanda taga tana shirin ficewa a dakin.

    Aikuwa maganar ta daketa sosai,don da qyar ta iya cinyewa bata waiwayo ba,saita dan qara sauri cikin tashin hankali ta fice ta isa sassanta.

    Kallonta yake kai tsaye cikin idanunta,yasa hannu ya damqe rigar dake hannunta

    “Jiya ina kika je?” Gabanta ya fadi,wani tsoro da shakkar gaya masa ya kamata,saita saki murmushi

    “Jiya?,bako ina,ina gida” idanunsa duka ya lumshe

    “Ya Allah,ta tabbata……lallai ta tabbata”

    “Please do me a favor” ya furta idanunsa a lumshe ba tare daya bude ba,don bayason kallon fuskarta kwata kwata

    “Name uncle?”

    “Stay away from here,i need space” gaba daya sai jikinta ya hau rawa,to amma saita hanawa zuciyarta samun rauni

    “Ok shikenan” ta sakar masa rigar ta juya a sanyaye,harta kusa fita ta jiyo lallausar muryarsa yana cewa

    “Karki matsawa kanki,ki kwanta a sashenki kiyi baccinki” da qyar ta hadiye wani abu da ya taso mata,ta gyada kai ba tare data juyo ba ta fice da sassarfa.

    Sai daya tabbatar ya kulle sashen nasa sannan ya dawo ya zauna,wani baqinta na sake ninkuwa a ransa,zarginsa kuma na sake tabbata, widad da baisanta d qarya ba ko misqala zarratin yaushe ta fara qarya?,lallai akwai qamshin gaskiya a dukka abinda yake zargi.

    Wata baqar zuciya da baisan ta inda ta shiga qirjinsa ba ta dinga kambama abun tare da qara masa muni a idanunsa,wanda daga qarshe ta tayashi yanke mummunan hukunci akan widad din.

    Karon farko a rayuwar aurensu da Wani abu me suna bacin rai da batasan ta inda ya samo asali ba ya raba makwancinsu a ranar da yake girkinta ne,ranar da babu ranar da uncle din yake zumudin zuwanta irinta,ta rungume affan tsam a qirjinta tana ta juyi,ta lalubi bacci kaf a idanunta ta rasashi,ba irin tunanin da baizo kanta ba,amma saita taushi zuciyarta take gayawa kanta wata damuwa yake ciki wadda qila bayaso su sani,tunda a gabanta hafsat ma ta fice,amma bataso haka ba,batason ya dinga aje damuwa a ransa,tafison suci gaba da sharing problems dinsu tare suna samo solution yadda suka fara tun farko.

    Sai tsakiyar dare ta samu bacci ya dauketa,kiran sallar farko kuma ta farka a firgice saboda wani mafarki mara dadi da tayi,sanda ta idar da sallar asuba ta fuskanci saqo ya shigo wayarta,data duba saita saki murmushi,zuciyarta na saki daga damuwar data kwana cikinta,ranta yana mata fari sosai

    _ki shirya around 10 zaki rakani katsina,wani aiki ya tasomin,but basai kin shigo ba,idan kin shirya kawai ki fito gaba daya_

    Dadin da taji a ranta yasa ta miqe tun lokacin ta fara shiri,ta fara da hada masa lafiyayyen breakfast,farfesun kaza da yaji spice masu dadi,sannan ta masa hadadden spicy tea,gefe daya ga wani irin chips dake cakude da qwai,sannan ta gyara sashen,tayi wanka,sai a sannan affan ya farka, yaron yana da haquri sosai,ba kasafai yake hanata aiki ba,ta dagashi tana masa miqa hadi da karanta masa addu’ar tashi daga bacci sannan ta rungume shi tana kissing dinsa hadi da tambayarsa

    “Ka tashi lafiya uncle dina na kaina?,yau kaji baccin ka daban ko?,munyi missing daddy dukkanmu,karka damu,we have a trip tare da daddy,na tabbatar we will enjoy it in sha Allah” saita saki murmushi tana shafan kan yaron,sannan ta miqe dashi ta masa wanka a toilet suka hau shiryawa.

    Kayan data sawa yaron ya dace sosai sa shigar atamfar da tayi,atamfar tayi mugun karbarta kamar don ita aka bude kamfani atamfa,ita kanta sanda ta tsaya a gaban madubi tana kallon fuskarta a tsakiyar mayafin kanta ruwan zuma sai data burge kanta,ta saki murmushi tana jin dadin yadda kullum take sake zama cikakkiyar mace me iya dressing me fusgar hankalin mijinta, cikakkiyar macen da duk inda ta shiga za’a waiwaya a kalleta,ta tashi daga sakaltacciyar widad din ummu,ta zama classy madam din abbas turaki.

    Fahad ne ya shigo yana gaya mata

    “Uncle yace ki fito anty”

    “Breakfast dinshi fa,kace a kawo masa na gama”

    “Okay bari na gaya masa” sai ya juya ya fita,ba jimawa ya dawo ya gaya mata yace he’s okay,bazai iya cin komai yanzu ba,sai abun yayi mata banbarakwai,bata taba masa tayin abinci koda ba ranar girkinta bane ya tankwabar bare kuma ranar girkinta,don haka sai ta share wannan maganar ta shirya abincin cikin wani basket mai kyau da daukan hankali,na musamman ne da tasa akayi mata da dukka favourite colors na abbas din don saboda shi din, kome zatayi tana yin sa da colors ko yanayin da tasan zabinsa ne,bata taba duba nata choice din,wannan ya sake sawa ta kama zuciyarsa da kyau.

    Fahad ta bawa kwandon,ita kuma ta kulle sashen nata,ta saka affan a kafadarta ta fito.

    A seat din baya yasa fahad ya saka kwandon,karon farko da ya rasa duk wata sha’awa na cin abincinta,bama abincinta kawai ba,gaba daya yayi loosing komai da yakeji a kanta,sanda ya daga ido ya hangeta tana takowa,gaba daya ta haske farfajiyar gidan da wani irin kyau da qamshinta daya fara aika saqon tahowarta kowanne sashe na gidan,ita da yaron sunyi wani kyau na kusamman kamar fure,saiya dauke kansa ya maida gefe,yana jin zuciyarsa na masa matsanancin bugu kamar zaya fado daga qirjinsa,abubuwa hiyu suna gogayya cikin qirji guda daya lokaci guda SO YAYYA DA KIYAYYA,soyayyar nason tasiri,amma wani abu mai nauyi yana tasowa ya danneta yana baiwa qiyayyar damar wanzuwa a farfajiyar qirji da zuciyarsa,zuciyarsa na kwadaita masa ya sake kallonta,don ta fito a kamar da yakeso,amma tsananin haushinta ya danne wannan muradin da ransa ke dashi,don haka kafin ta qaraso ma ya shige cikin motar yana haki qasa qasa.

    Mamaki ya sake cikata,da kansa a irin wannan lokacin yake takowa ya karba affan daga hannunta ya bude mata motar ta shiga sanan ya miqo mata shi,jiki a sanyaye ta qarasa motar ta bude ta shiga ta zauna, qamshinta ya qarasa baibaye ilahirin motar

    “Ina kwana uncle” ta gaaidashi tana dan rusunawa,ya amsa a taqaice ya miqa hannu yana karbar affan,tsam ya rungumeshi a qirjinsa hana jinjina hukuncin da zai yanke wanda har yaron zai shafa,amma dai wannan shine maslaha a wajensa,don yana ji a zuciyarsa bazai taba iya zama da fasiqar mace ba

    “Why widad why?,ta ina na gaza?” Ya fada can qasan ransa yana jin wani ciwo,saiya sunkuya a sanyaye yayi kissing goshin yaron ya saka masa dariya kuwa,sai zuciyarsa ta karye,ya miqa mata shi ba tare daya sake kallon fuskarta ba,don kallon fuskarta na gaya masa wani fa ya taba tabata,wani ya taba rabar wanann jikin nata,wani ya taba kwanciya da ita yadda kakeyi,tunanin da yake sakashi jin kamar zaiyi bindiga.

    Duk yadda taso yaci abincin ya qiya,dole ta qyaleshi,tayita sako hira a hanyar tafiyar amma yana banzatarwa,ta jinjina kai tana mamakin wacce damuwa ce haka ke damunsa?,don kada fa takura masa daga qarshe sai tayi shuru itama, motar kamar ta kurame,tafiya mara dadi data fara yi dashi tsahon rayuwarsu dashi,har daga qarshe bacci ya dinga daukarta,dama yau din bata samu tayi baccin nata data saba ba.

    Lokacin da zasu gifta kano sai taji kamar ta sauka yaje ga ummunta,amma dole ta danne,koshi bata cewa komai ba,batason ta dameshi da magana,tunda ta fahimci a yanayin rashin son magana yake.

    Sai bayan azahar sannan suka isa magariba,ta ware idanunta sosai tana jin kewa da shauqin mommynta,tana jin dama ya ajeta wajenta duk da rakiyar aiki tayi masa,ga mamakinta sai taga ya dauki hanyar gidan nasu,ta kasa haquri sanda taga sun shiga unguwar su

    “Na gode uncle” kansa kawai ya daure ya gyada mata ba tare da yace komai ba.

    A qofar gidan yayi parking,cikin sa’a usama daya daga cikin qannenta maza da mamarta ta haifa a gidan ya fito,cikin zumudi da murna ya qarso wajen,suka gaisa da abbas sannan ya fidda mata kayanta

    “Kakaimin jakar kazo ka karbi affan” saboda yadda taji qafarta da mararta duka sun riqe mata gam.

    Yana shiga ya fito ya karbi affan din suka shige ciki suka barta,ta buda murfin motar,saidai har a sannan abbas din baice mata komai ba,sai ta dakata da fitar ta waiwayo

    “To sai yaushe kenan?,sannan a nan zaka sauka?” Kai ya girgiza mata alamun a’ah,ya bude bakinsa da yakejin kamar ya manne yace

    “Ki zauna kawai,sai lokacin dana gama aikin,zanzo na daukeki” duk da yanayin da yayi mata maganar yana saka mata rashin jin dadi a ranta,saboda ba yanayin daya saba mata mu’amala dashi bane,amma jin zata dan zauna a gidan ya mata dadi,tanason kasancewa sosai da mamarta,don tana jin dadin haka,uwa uba tana qaruwa da abubuwa masu yawa,sajta jinjina kai

    “Allah ya bada sa’a,yasa a gama lafiya, zamuyi kewarka nida affan” ta fadi a sanyaye da wani abu dake bugun zuciyarta wanda batasan meye ba

    “Ameen” ya fada muryarsa a qasa

    “Ba zaka shiga ku gaisa ba?” Tayi masa tayi,abinda bata taba ba kenan sai yau

    “Later” ya fada a gajarce,saita jinjina kai kawai,ta saka qafarta ta fice a motar jikinta a mugun sanyaye kamar wadda aka zarewa laka.
    [19/05, 7:12 am] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    Arewabooks:huguma
    A RUBUCE TAKE
    (k’addarata)

  • A Rubuce Take Book 2 Page 25

    A Rubuce Take Book 2 Page 25

    Part 02

    Page 25

    Kasa cewa komai yayi,sai zuciyarsa dake wani irin tsinkewa,sun jima a tsaye a haka har affan ya fara kuka,sai ya miqa mata yaron ya juya ya koma dakinsa yana jin wani yanayi mara dadi cikin ransa,yanason bata haquri ya kuma lallasheta ya kasa,sai bayan ya zauna cin abincin dare yake sake jadda mata

    “Ina tsananin sonki,ina kuma tsananin kishinki” bata da amsar bashi,amma batasan wanne irin kishi ko soyayya bane daya rikide yake son komawa ZARGI.

    Tun daga ranar data fuskanci haka saita daina doguwar waya don kada ya kirata bai sameta ba,hakanan ta daina nisa da wayarta,idan zaiyi kira dubu zata daga,don don kiyaye faruwar wata matsala da take gani kamar tana shirin kunno kai,da tayi hakan sai taga kamar abubuwan sun ragu,kira dai tana jurar dagashi,to amma ta barwa ranta hakan shine maslaharta.

    Ya koyi dawowa gida akai akai,sabanin baya da abincin rana kawai ke dawo dashi,a yanzu sai yazo gida sau hudu biyar kafin lokacin tashinsu a aiki yayi,tun abun yana mata wani iri har ya koma bata mamaki,tako ina ya koma wani irin tsauri da yake mata kama da ZARGI don yafi gaban kishi,amma tayi qoqarin dannewa,tare da bashi uzuri.

    Tafiya ta kamashi katsina ta kwana biyu,har sunyi sallama dashi kan aminatu zata dawo gidan ta zauna har sai ya dawo,amma bayan awa uku sai gashi da fahad,dan yayansa ne shima

    “Zai tayaki zama har na dawo” da to kawai ta amsa masa,don abubuwan nasa sun fada daure mata kai.

    A tafiyarsa ta kwanaki biyu ya dage da addu’ar Allah ya sassauta komai,ya kawo qarshensa,cikin sa’a daya dawo din sai taga abun ya ragu,satinsa daya da dawowar suka shirya zuwa weekend yadda suka saba,daga nan zasu maida fahad gida.

    *R U B U T A C C I Y A R K’ A D D A R A II*

    Shigar yammaci suka yiwa bauchin,sanda motarsu take shiga gidan duka yaran suna farfajiyar gidan suna wasa saman kekuna,hafsat na tsaye da wata baquwa da alama sallama takeyi tayo mata rakiya ne.

    Dukka yaran suka kwaso a guje sukayo kansu suna murna tare da kiran sunan affan,harda yusra dake rarrafe,duka tyai budu budu da jikinta da qurar dake farfajiyar gidan,widad bata barta ta qaraso ba ta isa gaban yarinyar ta dagata tana mata waqa

    “Allah rayan…..rayan ‘yar nan” sai kuwa ta bangale mata baki tana dariya,ta sanya yarinyar cikin jikinta itama tana dariya,duk da ajiqe jikinta yake,fitsari ne ko ruwa itama bata sani ba,yarinyar akwai fara’a sosai,shi yasa take sonta.

    Ga mamakin widad da hafsat ta dawo daga raka baquwar sai tayo wajensu

    “Sannu da zuwa daddy” ya daga kai da murmushi yana kallonta

    “Yauwa sannu da gida maman yara” ta saki murmushin jin dadi kadan,sai widad ta taka kadan ta gaidata.

    Ba yabo ba fallasa ta amsa mata sannan ta maida kanta ga mijinta suka fara hirarrakinsu,har widad taji tadan qosa da tsaiwar ta dauki qaramae jakarta ta cewa fahad

    “Shigomin da sauran kayan don Allah” sai tayi gaba ta barsu a wajen.

    Sai bayan kusan awa guda aka shigo mata da affan,a lokacin har tayi nisa wajen gyaran sashenta,ta karbeshi tana tambayar fahad ina duka yaran

    “Mamansu ta tafi dasu bagaren abbansu” saita gyada kai kawai tana cirema affan pampers dinsa,don ba kasafai take barinsa dashi ba don ba mai yawan fitsari bane.

    Ta kama kanta sosai game da lamarin hafsat dama tun ba yau ba,don sai ta gama zamanta a bauchi su koma bata bari hanya ta hadasu ba,to wannan zuwa hutun ma haka ya kasance,hatta dasu mimi ta janyesu,wannan bai damu widad ba,tunda koba komai itama Allah ya bata nata,affan ya isheta suyi sabgarsu a sassansu,ga kasuwancinta dake dauke mata hankali,wani lokacin saita share awanni tana lissafin kaya dana kudade.

    Uwa uba wannan zuwan ma da sukayi sai takejin jikinta duka babu dadi,yawan bacci da kasala gaba daya,ranar da ta karba girki washegari abbas din yana saman dining tana shirya masa breakfast yana riqe da affan yana masa wasa,ta kammala taja kujerar ta zauna ta fara saving dinsa,idanunshi a kanta harta gama ta daga kai suka hada ido

    “Lafiya yallabai?” Sai ya dage mata girarsa dukka biyun

    “Sonki nakeyi” maganar ta bata dariya har sai data murmusa

    “So na nawa kuma ranka ya dade?”

    “Na babu adadi,malala gashin tunkiya,ina sonki sosai,ina kuma kishinki widad,da ina da hali ko quda bazan bari ya sauka a kanki ba” ajiyar Zuciya ta sauke mai nauyi tadanyi rolling idanunta tana kallonsa,ta yarda kai idanma akwai abinda yafi yarda ta yishi akan irin soyyyar da abbas keyi mata

    “Amma jiya kinsan kinci bashi na,kikayi baccinki kina barni da kewa” murmushi ta sakeyi tana dan rufe bakinta

    “Amma yallabai,ina jinka fa ka rage zafi sosai fa” fuska yadan bata

    “Hakan bai gamsar dani ba madam…..bana wani ganewa rage zafi,na ji na kasance tare dake kawai shine magana,kwanan nan kin koyi lalaci da dogon barci,ko so kike na qara aure oho” ya fada yana dan shan mur kamar da gaske.

    Idanu ta fiddo,saita fara bubbuga masa qafa cike da shagwabar nan tata tana masa kukan qarya

    “Haka kace uncle?,haka kace?” Dariya ya saki

    “Wasa naki miki wuddu na” ya dora affan saman dining din yana cewa

    “Idan na biyewa mamarka bazan fita ba,ina da aiki masu yawa,gobe ma kuma sokoto zan tafi daurin aure,zai yiwu ma mu kwana can sai jibi”

    “Allah ya nuna mana”ta amsa tana qarasa tura masa sauran breakfast din.

    *W A S H E G A R I*

    Tunda wuri ta gama masa komai na tafiyan yana kwance yana bacci,hatta da breakfast da ruwan wanka,sai data kammala ta shiga dakin,suna cikin duvet shi da affan suna baccinsu hankali kwance,ta saki murmushi har qasan ranta tana jin dadi idan ta kallesu,su din sanyin idaniyarta ne,kamarsu kullum qara fitowa takeyi da juna,kana ganinsa basai ka tambaya ba kasan mahaifinsa ne,tadan dora hannunta saman pillow din da yake kai ta soma bubbugawa a tausashe,ya motsa kadan saiya dora hannuwansa saman kunnensa ya rufe.

    Murmushi ta saki,ta gane ya farka tashi ne bashi da niyyar yi,saita gyara zama ta zame duvet din gaba daya daga fuskarsa,ta kamoshi ya maida fuskarsa,ta sake zamewa,sai kawai ya cakumota gaba daga ya mirginata ya danneta da dukka qarfinsa,sannan ya kama fuskarta ya riqe a tafin hannunsa saitin tasa,ya fara bude manyan idanunsa da suka qara girma kadan saboda barci cikin nata qwayar idanun,suka kuma dan canza launi kadan.

    “Na meye zaki dameni da tashin sassafe,bayan ke kika gajiyar dani jiya?” Ya fada da muryar bacci wadda tayi mata dadi qwarai cikin kunnuwanta,saita saki murmushi tana girgiza kai

    “Banda sharri uncle,ka fadi gaskiya” girarsa ya daga mata

    “Wacce gaskiya ce da tafi wannan,ni wani irin zaqi naji kina…….”

    “Wayyo uncle,don Allah kada ka fada” ba shiri murmushi mai kama da dariya ya qwace masa,sai ya hade goshinsu waje daya

    “Don Allah ki barni na fadi irin abinda naji,da gaske nake widad,kullum sake dad……” Bata da zabi illa hade bakinsu da tayi waje guda,shi kuma hakan ya zamana kamar ta sake bashi dama ne,sai kuwa ya manne mata da kyau.

    Da qyar ta qwaci kwanta tana sakin numfashi,ta nuna masa agogo da yatsantsa

    “Lokaci yana tafiya, everything is ready” tayi tsalle ta fice daga bedroom din don kada ha biyota.

    Binta yayi da kallo yana murmushi,sai ya waiwaua gefan inda affan yake,sun tula masa pillows basu sani ba,ya gyara masa kwanciya sosai sannan ya fada toilet.

    Komai ita ta taimaka masa ya gama shi,yayi kyau cikin Wani lallausan yadi ruwan zama,wanda ya sake fitar da haibarsa da kwarjininsa.

    Widad dake tsaye tana qare ma kwalliyar tasa kallo,tana sake jinsa har cikin jininta tayi.magana qasa qasa,ya waiwayo yana dubanta bayan ya ajjiye tissue din da ya gama goge sauran maiqon abincin da yaci,saiya zube hannayensa a aljihun wandonsa ya fara takowa inda take idanunsa akan fuskarta

    “Me kika ce?” Dariya take qoqarin dannewa

    “Bance komai bafa” da wani irin zafin nama ya kamota ya sakata sosai cikin jikinsa yana sansanarta

    “Kayi kyau da kwarjini,idan ka fita kamar ba kai ba,kamar ba kaine ka gama danne ‘yar mutane dazu dazu ba,ko ba haka kikace ba?” saita zaro ido sosai,batayi tsammanin yaji abinda ta fada ba,girgiza kai ta fara yi

    “Don’t say no…..na riga naji” juyo da ita gabansa yayi

    “I love you,ina kishinki sosai” ido ta lumshe tana mamakin yadda yake jaddada maganar kishin nan koda yaushe

    “I love you too” ta amsa masa a sanyaye.

    Har gaban mota ya rakoshi,tana tsaye suka fice daga gidan bayan ya leqa ya yiwa hafsat sallama,ita din dama can batasan rakoshi ba,saidai idan wani abun zata amsa tayi mantuwa ta biyoshi,ko kuma abinda zata karba din yana cikin motar tasa.

    *B A Y A N A W A H U D U*

    Misalin qarfe hudu na yammaci,tana kwancw a falo tana chart,affan yana kwance saman cikinta yayi bacci kira ga shigo wayarta,data duba da kyau sai taga abubakar ne,dan uwa ga mahaifiyarta wanda yake kamar mazaunin uba a wajenta,yana da matuqar kirki,ya kuma dauketa kamar diyar cikinsa.

    Kwantar da affan tayi,ta zauna sosai tana amsa wayar,suka gaida dashi sannan yace

    “Muna garinku,amma bamusan inda zamu iso gidanki ba,don wannan shine shigowarmu ta farko bauchi” sosai dadi ya kamata,iya zuwan da takeyi wajen mummynta kawai ta fahimci yadda sukeson mommyn nata,bama ita kadai ba,har su da suka fito daga cikinta

    “Ta wanne guri kuke?”

    “FAAZ hotels”

    “Bansan gurin ba kawu,amma zan tambaya saina taho daku” ta fada cikin murna,karon farko wasu daga dangin mahaifiyarta zasu kawo mata ziyara gidanta.

    Suna gama wayar ta kira abbas din don ta gaya masa zata taho dasu,saidai cikin rashin sa’a dukka layukansa is switched off,ta kira rose tace ta yiwa samuel magana ko tare suke ya cewa ogansa ya kirata,to amma shima ba tare dashi sukayi tafiyar ba,ta kusa minti talatin tana kira bata sameshi ba,sai ta miqe ta gyara yafen mayafinta ta fito farfajiyar gidan.
    [17/05, 7:35 pm] +234 810 324 4136: *H U G U M A*
    *Arewabooks:Huguma*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)