Author: Novels

  • Arubuce Ta Ke 37

    Arubuce Ta Ke 37

    Page 37

    Cak ta tsaya sanda suka isa bakin part din nata,ta juya tana fuskantar sa,fuskarta a narke,tana wasanda yatsunta,da alama magana takeson masa,amma ta kasa sai motsa yatsunta da takeyi,shi kuma ya kafeta da idanu,ganin ta kasa magana sai yayi gyaran murya,ta daga idanu ta dubeshi,kafin yace wani abu ta magantu

    “Don Allah kada ka shigo” mamaki maganar tata ta bashi,sai ya kafeta da idanu yana neman ba’asi,bata gane ba,murya a narke tace

    “Kaji?” Saiga qwalla ta biyo bayan maganar,bai shirya ba amma dole ta sanya qaramin murmushi ya qwace masa,sai ya kauda kansa gefe na sakanni yana danne murmushin kafin ya dawo da dubansa gareta,ya gama gano abinda take nufi,don haka yace

    “Is okay” sai ya juya a hankali yabar wajen yana nufar sashen hafsat.

    Ajiyar Zuciya ta sauke tana binsa da ido,sai taji dadi a ranta da ya tafin,don idan da ya tsaya ba shiga zatayi ba,da wanne ido zata kallesu?,me zatace musu?,ta samu relief don haka ta juya tana dosar qofar falon nata.

    Kamar wata munafuka haka ta dinga rarraba ido tana rabewa a bango,jikin labulen bakin qofa ta tsaya tana leqen falon,inna laila ce saman dining ita da batulu,sai nujood zaune saman kujerar falon,Momma na zaune daga qasa,dukkansu kowa sanye da hijab,da alama tun tashin asuba ne basu koma ba.

    Tana daga tsayen ta hangi anty deena ta fito dauke da wata jaka ta ajjiye saman kujera,ta kalli nujood tana cewa ta tashi su sake gyara falon,latifa ta riga ta gyaro ciki,saita matso ta wajen bakin qofa zata dauka mopper dake ajiye a wajen.

    Motsin mutum ya sanyata waiwayawa ta dubi wajen,cikin mamaki take kallon widad

    “Ke kuma me kike yi a nan a tsaye ke daya?” Rau rau tayi da idanu,a yadda anty deena ta kafeta da idanu saita fara hawaye kawai

    “Meye haka widad?” Tambayar da ta sanya jikinta rawa,saboda tana ganin kamar anty deena din ta hangi abinda ya faru jiya,hankalin anty deena yadan dauko kadan,ta zaci ko wani abun ya gudana tsakaninsu,sai kuma taji hankalinta yadan kwanta kadan da taga yanayin tafiyarta bai canza ba,tana tausayinta,koda wani abun zai faru ma ta gwammace basa nan.

    Sai data mata da gaske tabar kukan ta shigo,momma dake zaune ta bita da harara

    “Ja’ira,zakiyi bayani ne” kasa hada idanu tayi da kowa,sai ta wuce ciki sum sum sum.

    Dakinta ta murda ta fada tana sauke ajiyar zuciya mai qarfi,sai a sannan ta nutsu,ta soma bin dakin da kallo. Sosai ya qayatar da ita,an gama shirya mata komai sai qamshin sabinta yakeyi,ta waiwaya ta dubi bandaki inda anty deena tace akwai ruwan zafi,ta shiga tayi wanka,ta kuma zabi kaya masu kyau ta sanya,ta juya zata shige sai aka turo qofar,anty basma da anty ramziyya da anty marwa suka shigo,kowanne riqe da yaronsa,marwa dince kawai mai ciki bata samu rabo da wuri ba.

    Nan bakin gadon suka zauna sunata tsokanar widad tare da da son jin me ya faru jiyan,kuka ta saki sosai

    “Ni wallahi ku daina banaso,bayan ummu ta hana,babu kyau,wallahi ba ruwana” haka ta dinga fada tana sharar qwalla,su kuwa ganin abun suke kamar almara,wai yau widad din ummu ce aka aurar?,a wata uwa duniya?,ta tafi tabar ummu duk qaunar dake tsakaninsu?,Allah ne ya kawo anty madina ta korasu,sannan ta kada kan widad zuwa wanka,bayan ta fito kuma ta shiryata da kyau cikin wani lace da yayi masifar karbarta,ya fidda kyau da hasken fatarta,ita kanta ta dade tsaye gaban mdubi yana kallon kanta,tana ta zuba shirmenta na kyan da tayi,anty madina na binta da murmushi gami da goge qwalla a fakaice.

    Daga bakin gadonta take zaune riqe da waya a hannunta,lokaci lokaci tana saka hannu ta share hawayen fuskarta,duk furuci daya da zatayi da anty ummee tana jin kamar zuciyarta zata tsinke saboda baqinciki bacin rai da zallar kishi kai daci

    “Har kusan qonewa nayi garin saurin na hada masa tea nakai masa,amma wallahi acan na sameta,namiji dan babansa……alamun dana gani ma sunsha dambene,saboda ko dankwalin kanta gashi nan watse a qasa,don Allah anty ummee mai zaiyi da wannan mitsitsiyar yarinyar,banda tsabar cin fuska?” Tayi maganar tana jin kamar zuciyarta zata fito ta bakinta.

    “Kinga ki ajjiye wannan a gefe,matuqar zakici gaba daga inda kika tsaya,zaki nuna komai ba komai bane…..hatta kusantar tata ma saikin hanashi gaba daya,meye a cikin ido ne banda ruwa?,ai nasara tana tare da jajircewa”

    “Wannan nasarar anya kuwa tana tare dani?”

    “Kin saare a dare daya kenan?” Anty ummeen ta tambayeta tana jinjina zallar gajen haquri irin na hafsa din

    “Shin ba’a gabanki komai ya dinga gudana tsakanina da amaryar abban sayyid ba?,yanzu tana ina?”

    “Banqi ta taki ba…..amma akwai nisan tazarar banbanci mai yawa tsakanin abbas dashi…..abbas anty…..yana da ra’ayin riqau kafiya da kuma magana daya,yana da wuyar sha’ani,yana da wuyar canza ra’ayi,idan yace eh…..tofa a haka zata yita tabbata”

    “Uhmmm,mace fa tafi gaban tunanin dukkan wani mai tunani,saidai idan ba zaki iya ba”

    “Zan iya” ta fada tana son sake bawa kanta qarfin gwiwa,ji take kamar ta rufe idanu ta kuma bude taga komai ya tarwatse,komai yazo qarshe,ta rufe idanunta kana ta budesu duk kusan lokaci daya sannan tace

    “Na rasa ta yadda abbas yaga yarinyar nan anty ummee……abbas fa?,mara damuwa da abubuwa masu yawa,wanda wani abun ma sai kinta cewa kalli….ko ka gani” ta jefawa anty ummeen tambayar da taketa damunta tare da yi mata yawo a kai,har yanxu kums bata samu amsarta ba

    “Namiji yafi gaban haka,kedai ki maida kai ga mission dinki…..”

    “Ina zuwa” ta fada da sauri tana sauke wayar daga kunnenta sanda fa jiyo alamun taku ana nufowa dakin,ta kuma san babu wanda zai shigo din sai shi.

    Da hanzari ta ajiye wayar,sannan ta fada bandaki ta maida qofar,da tattausar muryarsa yayi sallama ya tura qofar ya shigo,sai ya tsaya daga bakin qofa yana qarewa hargitsatsen dakin kallo,komai baya kan tsarinsa,baisan kuma sai yaushe zata gyara ba.

    Ajiyar zuciya ta sauke,ta matsa gaban babban madubin dake bandakin wanda ya cika da jirwayen ruwan wankan da ba’a wankewa,ta debi ruwa ta wanke fuskarta,saboda batason ya gane ruwan hawaye ya fita a idanunta,taja zaninta da tayi daurin qirji dashi saman t.shirt dinta ta gyara daurin,sannan ta goge fuskarta da towel ta fito.

    Suna hada idanu ta cika fuskarta da fara’a,sai ya dan lumshe idanunsa ya kuma budesu lokaci daya yana kallonta,qasan zuciyarsa kuma yana masa sanyi na yanayin da ya ganta a ciki,ba wata damuwa

    “Yanzu nake shirin fita mu gaisa da baqi,gashi ka tarar dani” ta sake fada tana murmushin da ita kadai tasan ciwon da yake mata.

    Agogo ya kalla kafin ya amsa mata

    “Kaman yayi wuri,gwara ki kwanta ki sake hutawaYou are very tired, you need a rest maman nawwara” ya fada yana sauke mata murmushi.

    Duk da cewa bata kalleshi ba amma tana jin saukar murmushin nasa har tsakiyar zuciyarta,murmushi ne da ita kadai tasan tsadarsa

    “To ya za’a yi,kamawa takeyi ai,gashi na kasa hada musu breakfast” ta sakeyin maganar tana zaqulo hijabinta cikin hargitsatsun kayan wardrobe dinta wadanda yana daga tsaye yake tayata kallon yadda suke a hautsine,haka suke koda yaushe,idan kayi magana tace su nawwara ne tana bacci suka aikata,ko kuma suna neman teddy dinsu ne

    “Ba matsala,kinyi qoqari sosai,zan saka a kawo musu breakfast”

    “Da dai yafi,na gaji da jegon jaka” ta fada qasan ranta tana zura hijabin a jikinta,sannan ta matso tana cewa

    “Bari naje mu gaisa kada suga rashin kyautawa ta,mun tashi gida daya ban leqasu ba” da kallo ya bita,duk da qoqarin sakewarta amma yana hangen wani.abu can qasan qwayar idanunta,zuciyarsa na alaqanta hakan da kishin da takeji a kansa.

    Hannayensa ya bude mata,cikin taushin nan nasa

    “Zaki wuce bamu gaisa ba madam” kallonsa tayi saita kauda kai tana qoqarin kawo murmushi kan fuskarta,tabbas idan tace zata shiga jikinsa a wannan yanayin kuka zata barke dashi,kukan kuma zai zame mata tonon silili ne.

    “Ina kwana oga?” Ta fada tana ci gaba da tafiya,sai ya maida hannayensa yayi folding nasu a qirjinsa yana kallonta,qaramin murmushi na sauka saman labbansa,irin gaisuwar da yafi qauna daga wajenta kenan,amma dama yasan zaiyi wahala ya samu yadda yakeso din

    “Alhmdlh madam,a dawo min da yarana mana?”

    “Zasu dawo dole yau” ta bashi amsa ba tare data juyo ba

    “Alright” ya amsa mata yana kallota ta cikin madubinta

    “Bari naje na dawo” ta fada tana jan masa qofar,tana so taje ta saje tantance widad din,yadda ta ganta a jiyan haka take ko idanuwanta ne da kuma sharrin dare?.

    Idanuwanta nakan dukka wani kayan qawa na falon,da qyar ta iya riqe kanta saboda yadda zuciyarta ke wani irin tsalle,ko ba’a gaya mata ba auren ‘yar gata ne daga dukkan alamu,saboda yadda aka shirya gami da qawata sassan nata gaba daya,babu ce kadai babu,jere mai aji da nutsuwa.

    Ta basu fuska sosai ta gaidasu inna laila dasu momma,har tadan zauna suna dan taba hira,tana ta baza ido taga ta inda widad din zata fito,saiga nujood,kamar inna laila tasan buqatar ta tace da ita

    “Kira widad,kice tazo ta gaida yayarta”

    “To” ta amsa tana okomawa ciki da mopper din hannunta data goge inda ruwa ya zuba.

    “Yaaa latifa” widad din ta fito tana fada,hannunta riqe da dankwalin lace din nata da yaqi dauruwa,anty deena dake wanka kuma tace lallai saita daura.

    Hankalin hafsa ya fara kaiwa wajen,tana tafe da dankwalin fuskarta a kwabe tamkar shagwababbun ‘ya’yan fari,gashinta dake wani irin sheqi da walqiya a daure cikin ribbon jelarsa na reto a bayanta, yanayin qirar jikinta kadai abar kallo ce,sai kace wata babbar budurwa,tun a yanzun coca-cola shape dinta ya fita sosai,kallo dayan data mata ya kusa tafiya da numfashin ta,ta dinga qoqarin riqe kanta da kyau,kada ballinta ya watse a wajen.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/2, 5:28 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 21

    Arubuce Ta Ke 21

    Page 21

    Sai da suka gama cin abincin ma sannan uncle muhsin ya shigo,ya zauna suka gaisheshi,widad ta miqe zata tattara kwanukan uncle muhsin yace

    “Dawo widad muyi magana,nujood debe kwanukan ke da musaddiq” da zumudinta ta dawo ta zauna,tana tunanin labarin tafiya gida zaiyi mata

    “Widadun ummu” uncle muhsin ya fada yana murmushi

    “Na’am uncle” ta amsa masa itama ta amsa masa murmushin,tun da tana son uncle muhsin sosai,kasancewar yana saya daga cikin jama’ar da suke nuna mata qauna da kulawa

    “Akwai wani abokina,sunanshi abbas,yacemin yana son yarinya mai hankali da nutsuwa zai aura,nasan widad dina nada hankali da nutsuwa,ina kuma alfahari da ita,wannan yasa nace masa yazo ya ganki kema ki ganshi” gabanta ne yadan fadi,saita dan rage fara’a kadan,uncle muhsin din ya karanci haka,don haka yayi murmushi

    “Kada ki damu,indai kika ganshi baiyi miki ba shikenan,babu wanda zai takura miki kinji ko?” Kai ta gyada

    “To uncle”

    “Yauwa,Allah yayi albarka widad”

    “Ameen uncle” ta amsa masa tana miqewa,jikinta yayi wani irin mutuwa,kamar zata daki sai kuma ta fasa tabi bayan nujood data tsaya a kitchen.

    Wanke wanke ta samu tana shirin yi,saita tsaya gefenta nujood din ta waiwayo

    “Menene?,na dauka zan ganki kina tsalle zaki gida,ko abban cewa yayi an fasa tafiyar?” Kanta ta girgiza

    “Wai wani abokinsa ne zaizo gobe ya ganni yanason yayi aure” murmushi nujood tayi

    “Ke wanne irin farinjini ne dake,amma abokin abba?,na sassan abokansa,wa yace miki?” Idanunta tadan juya alamar tunani na wasu sakanni sannan da sauri tace

    “Wai abbas”

    “What?” Nujood ta fada tana ajjiye plate din hannunta

    “Wai uncle abbas abba yake nufi?”

    “Oho,inajin shi dinne ko?” Ruqunqume widad nujood tayi,tana dan ihun murna

    “Wayyo widad,don Allah kada kice baki sonshi, uncle abbas yayi mugun haduwa,saima idan yasa uniform din nan nasa,ga miskilanci ga tsafta ga gayu,idan yazo gidan nan har ya tafi qamshin turarensa yana nan,don Allah kice kin yarda” ture nujood widad tayi tana tura baki

    “Dalla malama,ni ba wani nan,na barmiki ke ki cewa uncle kina so” dariya sosai nujood ta qyalqyale da shi tana cewa

    “Ni ai babana ne,banda haka ni abba zai bawa,tunda kika ga bai bashi ba kuwa babana ne din” ita dai widad bata sake cewa komai ba,sai ta hau saman kantan kitchen din ta zauna,tana sauraren nujood nata bata labarin uncle abbas din.

    Musaddiq ne ya shigo yayi kiran widad bayan kaman awa daya,yace tazo hajjaa nason magana da ita,ta sauko.tabi bayansa.

    A bedroom dinta ta sameta tana daga wasu kaya

    “Shigo mana widad” hajjaa ta fada ganin widad din ta dan rab’e,qarasa shigowar tayi,hajjan ta dan tsokanarta kan kayan tafiya kano take hada mata,don ta samu ta sake sosai tayi maganar da ta sanya aka kirata din dominta,ganin ta sake din sai tace da ita

    “Kinji abinda abbanku ya fada ko?” Kai ta gyada mata ba tare da ta amsa mata ba

    “Karki damu,abbas nada matuqar kirki,sannan shi din dan hajiya ne,hajiya dai wadda kuka zauna gidanta wancan satin” maganar data fada na cewa dan hajiyan ne ya sanyata sakin jikinta sosai,cikin dabara hajjaa keta janta da zance har ta saki jikinta,sai a sannan ta sallameta.

    Da yamma lis ta kama widad din duk rashin son kitso irin nata ta sake wanke mata kai,tana ta qi tana turjewa,sai data sanya su musaddiq suka dinga yi mata dariya ,tare da waqar me kukan kitso sannan ta nutsu,ta raba kanta tayi mata manyan kalaba da suka jelarsu masu tsaho zubo gefe da gefan fuskarta,saura kuma suka sauka a bayanta,kasancewar ba kasafai ta fiya kitso ba saboda qin da take masa,sai kalbar ta haska fuskarta tayi mata kyau sosai,hajjaa ta qawata qarshen kowacce jela da duwatsun kitso masu yawa da suka qarawa kalbar kyau suka taimaka kuma ta kwanta mata sosai a fuskar da bayanta.

    Itakam widad gaba daya murnar tafiya gida ya sanya ma bata damu ko ya dauki batun zuwan abbas da muhimmanci ba,siyayyar da uncle muhsin yayi mata taketa shiryawa abinta,tana ta zancensu Aafiya da sauran ‘yan uwanta,da wannan batun ta kwanta bacci.

    ************Washegari a gida yayi breakfast wajen hajiya,ya kuma shaida mata yau din suraj zai rakashi gidan muhsin din.

    Har cikin zuciya da ruhinta take jin farinciki,tayi addu’a sosai tare da fatan samun dacewa da albarka mai yawa cikin lamarin.

    Sai Azhar ya wuce gida bayan yayi salla a nan,yana komawa bacci ya kwanta,bai farka ba sai gab da la’asar,tun bai tashi daga kan gadonsa ba ya janyo waya yana sake lalubar number hafsa,saidai yau din ma har tayi ringing ta gama bata dauka ba,a qa’ida idan yayima mutun kira daya baya qarawa,amma wannan karon ita din sai daya kira sau uku bata dauka ba,sai ya maida wayar ya ajjiye ransa yana baci,ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala ya wuce masallaci.

    Yana dawowa dakin kira na shigowa wayar tasa,suraj ne yana dagawa ya soma zolayarsa

    “Sabon ango,Allah dai yasa ka shirya” ido ya lumshe yadan saki murmushi,surja badai zolaya ba

    “Haba duk zumudin na meye?,bayan la’asar fa mukayi dakai,kuma yanzun nan ma aka gama sallar” dariya suraj din yayi

    “Na qagu ne naga wacce mai sa’ar ce zata sake samunka,bama ni kadai ba,kaga zainab a nan ita kanta so take naje na dawo na gaya mata wacece”

    “Ita da hafsat kuwa”

    “To sai me?,kayi qoqari ka shirya,gani nan fitowa,abinci kawai zanci”

    “Saika qaraso” ya fada yana katse wayar,dole ya fidda hular da ya sanya ya aje,ya shiga bandaki ya don yin wanka.

    Yana tsaye yana tsane ruwan da yayi lumm cikin gargasar jikinsa yana duban madubi,karo na barkatai ya sake kallon wayarsa yana tuna adadin wayar da ya yiwa hafsat din bata dauka ba,sai ya jinjina kai yana qiyasta yadda zai fita daga bauchi jibi da sassafe zuwa kaduna.

    Ya gama shirinsa tsaf yana gaban mudubi yana kallon kansa,hannunsa riqe da hularsa yana karyata,yana jin wani banbarakwai,wai yau shine a karo na biyu zashi zance,zancen ma wajen wadda baisan wacece ba,ya dora hularsa sannan ya dauki sassanyan turarensa dake fallasashi a duk inda ya shiga ya feshe jikinsa dashi.

    Kiran suraj da ya shigo ya shaida masa isowarshi,saiya kara wayar a kunne ya tallafeta da kafadarsa saboda takalman da yake sanyawa a qafarsa bayan ya zauna kan dressing chair yana fadin

    “Ka qaraso ciki mana”

    “A’ah,ina cikin mota fito kawai” bai musa masa ba,ya zame wayar ya qarasa sanya wasu rufaffun takalma masu kyau da asalin tsada da wasu sake fidda shigarsa,ya dauki wayar ya mayar aljihu ya dauki keys din gidan suma ya saka sannan ya fito.

    “Kai mutumina,kamar yau ne zan rakaka wajen maman mimi?” Harara ya watsa masa bayan ya rufo murfin motar sannan yace

    “Kunna mota mu wuce,so nake muyi mu dawo,ina da wani uzuri”

    “Yanzu kuwa yallabai” ya fadi yana dariya,sai ya tada motar suka wuce.

    Suraj nata jansa da hira amma shi hankalinsa ya rabu kashi kashi,dubansa yayi sanda yaga yana qoqarin parking qofar wani qaramin mall

    “Bari mudan samo abinda za’a kai mata,ai bama shiga hannu rabbana ba”

    “Share kawai suraj mu tafi please”

    “A’ah,nikam ba za’ayi haka dani ba,ko banza fa ta zama matarka,tunda an riga an tambaya an kuma baka” maganar sai yaji tayi masa nauyi,bace komai ba har suraj din ya fice,bai kuma dade ba ya dawo da tarin alawoyi da chocolates masu tsada da dadi,ya ajjiye ledar ya kunna motar sukaci gaba da tafiya.

    ~~~~~

    “Kai,tubarkalla ma sha Allah,diyata din nan badai kyau ba” hajjaa ta fada bayan ta gama shirya widad,cikin wata sabuwar dark blue din super vilisco,dinkin doguwar riga,ta fidda jelar kalbarta tayi ta fito ta qasan daurin dankwalin data yi mata,ya zauna das a kanta,sannan ta bata siririn mayafi da ya dace da atamfar.

    Murmushi widad kawai keyi tana kallon kanta a cikin mudubin,badan badan ba da sai tace bata taba ganin tayi kyau haka ba,ummu ta tabo daa,bata iya zama tayi mata wadan nan qyale qyalen,saidai ko yaushe zaka samu widad din fes cikin tsananin tsafta da kuma sutturu masu tsada,saidai ita da kanta take zama tayi kwalliyarta wansa a wajensu Aafiya da yayyansu su ramziyya take kwaikwaya,ko latifa da take mutuniyarta ita dinma bawai ta yanzu bace,ba wani iyawa tayi sosai ba,amma da yake hajjaan gwanar ado ce,a yau din ta qawata widad din sosai,har abun yayi mata dadi ya kuma burgeta ita kanta,farincikin yadda taga tayi kyau yasa bata jin wani fargaba ko bacin ran zuwan baqon,Allah Allah ma take yazo ya tafi tazo hajjaa tayi mata hotuna masu kyau ta turawa daya daga cikin ‘yan gidansu su nunawa ummunta kafin ta isa gida.

    Musaddiq ne ya shigo dauke da ball a hannunsa yana gayawa hajjaa ga uncle abbas nan

    “Bude musu setting room,ka kunna ac kadan kada tayi yawa,sai kazo kakai musu ruwa” da to ya amsa ya juya yana ficewa.

    Sai da hajjaa ta tabbatar an kai komai sannan taja hannun widad ta zaunar da ita

    “Na sanki da hankali da nutsuwa,to ki qaro wata a kai,idan kin shiga ki gaishesu kinji?”

    “Tom” ta fada tana gyada kai,sai hajjaa ta kira nujood,ta sanyata ta saka hijab tace ta raka widad,har sun fita ta kirayeta

    “Karki ce zaki zauna,nasan halinku da shirme,kina rakata kuna gaisawa ki dawo ciki”

    “To” tace tana ficewa,suka rankaya kuwa ita da widad din zuwa setting room.

    Setting room din yabi da kallo,duk da ba baqonsa bane,don yawanci idan yazo a nan suke zama da muhsin din,kamar bazai zauna ba,haka kawai ya samu kansa da qaguwa na ganin wacece,wayarsa da aka kira ya duba kuma yaga ogansa ne ya sanyashi zama dole,don suna da wani irin respect na ga gaba dasu,ya fara amsa wayar cikin nutsuwa da kuma girmamawa.

    Suna cikin yin sallama da ogan nasa yaji suraj ya dan taboshi,sai ya maida dubansa ga suraj din don,signal yayi masa da ido yana masa nuni da hanyar shigowa setting room din,ya qarqare wayar yana ajjiyeta gefansa,sannan ya maida dubansa ga inda suraj din ke masa nuni.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/18, 12:43 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 29

    Arubuce Ta Ke 29

    Page 29

    Qarfe biyu na rana bayan sallar azahar aka daura auren asp abbas da amaryarsa widad mahmud salim akan sadaki naira dubu dari,dubban jama’ar da suka halarci wajen suka haida,labarin kuma ya kai har cikin gida ya fara yawo a tsakanin mata.

    Dai dai lokacin widad na zaune tsakiyar anty deena da anty warisha,sai sharban kuka takeyi,duk yadda sukayi da ita tayi shuru bare a samu ayi mata kwalliyar daurin aure taqi,sai suka sakata a gaba kawai suna kallonta.

    Anty madina ce tayi sallama ta tana turo qofar dakin,dakin da babu kowa sai su ukun kawai,warisha ta amsa sallamar anty dina dake danna wayarta kai kawai ta daga ta kalli anty madina

    “A’ah,na zata zanzo na tarar kun gama,an gama daurin aure fa,angwayen ma yanzun zasu shigo za’ayi hotuna”

    “Inafa akayi kwalliya,kin ganta nan ko kayan taqi ta saka ma,ni bansan me yake damunta ba” anty deena ta fada tana ajjiye wayarta a saman madubin dakin.

    “Ashsha,haba widad,mene hakan?” Hawayenta taketa qoqarin tsayarwa ta hanyar shareshi da hannuwanta amma hakan ya gagara,wani irin bacin rai tsoro da kuma takura takejin kanta a ciki,wanda ita kanta batasan dalili ba,kawai batason barin gida ne,hakanan shi uncle abbas din ta yaya za’a wani ce shine mijinta tana zaman zamanta?.

    Anty madina ce ta cewa su deena din su basu waje minti biyar kacal,nasu musa ba suka miqe,anty deena ta dauki mayafinta mahadin lace din jikinta ta fara yin gaba,don dama ta fara gajiya da zaman lallashin widad din,wadda bata da alamun daina kukan.

    Cikin mintuna goma sai ga hawayen ta tsaya tas,anty madina kuma ta shiryata da kanta,hatta da undies ita ta bata ta saka,tana jin kunya tana nonnoqewa,ta shiryata cikin wani lafiyayyen lace fari da ummu ta kashe maqudan kudade wajen siyansa,aka kuma shirya masa nutsatsen dinkin doguwar riga,gashinta da yasha gyara ta tufke mata,sannan ta qawata mata kanta da sarqa ruwan gold da aka sanyawa saman ka,wanda kusan al’adace ta asalin yarensu,hannayenta sun sha warware masu kalolin gold masu asalin tsada,haka yatsun hannunta kowanne zobe ne bibbiyu daga tsakiya.

    Fes widad din ta fito,asalin quruciya da qaranci shekarunta na sake bayyana kansu,wanda ya cakuda da qyallin amarcin da akewa kowacce mace feshinsa,komai kyau ko muninta,indai sunan nan na amarya ya hau kanta.

    Kiransu anty deena tayi sanda taji hayaniya ta fara cika gidan,muryoyin maza na tashi,alamu dake nuna tawagar angwaye ne suka shigo gaisawa da surukansu,daga inda take sai ta dinga jin kamar an daureta,gabanta ya tsananta faduwa,wani tsoro yana shigarta,kanta a qasa,nutsuwa ta musamman irin wadda duk wanda yasan widad din bai santa da ita ba ta saukar mata.

    Shi daya ne cikin motar kwance a seat din gaba,ya dage dukka baqaqen gilasanta,da hular da kuma babbar rigar duka ya ciresu ya jefa seat din baya,ta cikin motar yana iya hagen kai da kawon jama’a,ciki harda gungun abokansa da suka masa karar da ko auren farko bai sameta ba.

    Amatsayinsa na jimi’in tsaro,duba daya yayi musu yana daga kwancen ya fahimci shi suke nema,yasan zancan bai wuce ace su shiga cikin gidan,abinda sam bashi a tsarinsa kenan,saboda yana kallon haka a mazaunin keta haddin shari’a,tu dazu ya shigo ya kwanta,ya kuma gargadi Samuel kada ya gayawa kowa yana ciki.

    Idanunsa ya janye a hankali daga inda yake kallo sanda yaji ana knocking qofar motar,fuskar suraj yake hangowa wanda yayi wujiga wujiga saboda yawan al’ummar dake wajen,sai yasa hannu a nutse yana daga kwancen ya buda murfin motar,suraj ya sunkuyo yana sako kansa.

    Ajiyar zuciya ya sauke

    “Gaskiya baka kyauta mana ba,kaifa ake nema tun dazun,zaa shiga gaida iyaye da kakannin amarya,ga masu hotuna suna jira suma zasu wuce” kamar wanda baya son yin magana ya buda bakinsa

    “Duk da wannan uban jama’ar zamu kama mu shige musu gida suraj?”

    “To ya za’ayi,al’adace” kai ya girgiza

    “Ba dani za’ayi wannan aikin ba,idan ya zama dole ka sallamesu su tsaya iya waje,mu shiga koda mu uku ne muhsin yayi mana jagora iya sashen ummu kakarsa mu gaisa mu fito” dan hade rai suraj yayi,sai kuma ya saki dariya

    “Kai mutumina,anya ba kishin matarka ka fara ba?” Wani kallo ya watsawa suraj din

    “Waikai me yasa baka da girma saina jikinka,yarinyar da idan auren qauye ne na haifi kamarta?”

    “Allah yasa motsin gado ce,bar ganin allura,duk qanqantarta qarfe ce,any way…..banga laifinka ba,bari ina zuwa” ya fadi yana maida murfin motar ya rufe.

    Sai da yayi settling komai yadda abbas din yakeso sannan ya sanar dashi,hularsa ya dauka ya mayar saman kansa,ya riqe babbar rigar a hannunsa,yana jin ta masa nauyi,saboda rashin sabo da sanyata,tunda gaba daya aikinsa yafi alaqa da qananun kaya.

    Kamar jiransa maroqa da masu buga kakaki suke suka fara busarsu suna wasa shi,baisan a inda suka san muqaminsa da kuma muqaman da ya riqe a baya ba,duk da juniors dinsa da suke masa bodyguard hakan bai hanasu binsa da kide kidensu ba

    “Ka sallamesu don Allah” yace da suraj,saboda yadda yakejin kidan na haura masa har saman ka,sai da suraj din kuwa ya sallamesu da kudi masu tsoka sannan suka ja suka tsaya daga nan suna ci gaba da yagar rabonsu a hannun duk wamda suka fuskanci dan gaban goshin bikinne.

    Babban falon ummun cike yake da jama’a,saidai da yake yana da yalwa babu laifi ba’ayi cushewar da zaka fuskanci yawan jama’ar dake cikinsa ba.

    Duk da fargaba da kuma alhinin rabuwa da widad din tata hakan bai hanata qure ado fiye da duk wani bikin jikarta da za’a yi ba,ta cake cikin wani danyen lace purple color daya haska farar fatarta dake dan bayyana yanayin shekaru da suka soma hawa kanta.

    Muhsin ne ya gaya mata ga abbas nan zai shigo,don haka ta kira hauwa’u da batulu(matan baban widad) tace su rage mata jama’ar falon.

    Duk da jikinsu a mace yake saboda ganin irin hidimar da akeyi amma wannan aikin kam cikin karsashi suka yishi,saboda suma suna buqatar ganin mijin widad din sosai,cikin lokaci qalilan falon ya sake fili,ya zamana sai manya a cikin dangi suka rage,dai dai lokacin sukayi sallama suka shigo cikin falon su uku.

    Kamar yadda a tsarin zubi da halitta gami da kwarjini ya fita daban……hakanan adonsa da shaddar jikinsa ta banbanta data kowa,sai ya fito kamar wani wata a cikin taurari,qanwar ummu da sauran jama’ar dake wajen ke marabtarsu,har suka samu waje qasan carfet suka zauna bisa tsari na tarbiyya,sannan aka soma gaisawa.

    “Da gani babu tambaya,wannan na tsakiyar shine surukin namu ko?” Batulu da wani malolon abu ya tsaye mata a wuya ta fada,fuskarta kwance sa murmushin yaqe,kusan kowa a wajen sai da yaji banbarakwai,saboda ba ita ya dace tayi tambayar ba,ko banza ya kamata ace akwai kunya tsakaninsu,saboda a yanzun sune kamar copy na mahaifiyar widad.

    Murmushi suraj ya danyi,baisan dangantakar ta da widad ba,ya dauka abokiyar wasa ce,tunda suna irin haka,dalilin da yasa ya maida mata kenan cikin salo na wasa

    “Aah,nine fa,kingi batan dabo”

    “Allah ya sanya alkhairi,yasa anyi kenan,jikanyar tamu qaramar yarinya ce qwarai,sai anyi haquri da halayen quruciya da za’a yita gani,Allah ya bada zuri’a dayyi ba” qanwa ga ummu tayi hanzari katse doguwar maganar da batulu keson taja,falon sai ya game da addu’ar ameen ameen.

    Abbas din na shirin miqewa muhsin yashigo yana fadin ina widad din afito da ita,azo ayi musu hoto

    “Ya salam” yafada a ransa,me yasa muhsin zai masa haka,bashi da zabi illa yayi jiraye.

    Anty madina da anty deena ne suka fito da ita ta can backyard din gidan,basa so kowa ya tsaidasu bare kwalliyar tata ta baci,suna tafe anty madina na jaddada mata kada ta sake tayi kuka,zata bata fuskarta

    “Ke maison kwalliya,kinga yadda kikayi kyau kuwa widad,baki taba kyau irin na yau ba” takanji dadi idan akace kwalliya tayi mata kyau,musamman daya zamana ita din mai son kwalliyarce,to amma kuma bata samunta sai lokaci lokaci,yau din da anty madina ke cewa tayi kyau sai bata ji wannan dadin da takanji ba,ta daiyi qoqarin dakewa,tanason farantawa anty madina rai,saboda kirkinta da yadda take sonta.

    Sallamarsu cikin falon ya ja hankalin jama’ar dake falon,badawiyya abokiyar wasa ga widad din,wadda shigowarta kenan falon ta saki guda data ratsa falon gaba daya.

    “Ma sha Allah…..ma sha Allah,widad Allah yasa anyi a sa’a,Allah yasa mutu ka raba” bakunan masoyanta dake wajen ya cika da addu’a,yayin da kishi hassada da kuma qyashi ya cika zukatan wadanda ke qin jininta hakanan.

    Gaban ummu suka so kaita,amma saita musu nuni dasu ajjiyeta gaban abbas din ba tare da tayi magana ba,sun fahimta,saboda haka suka nufi gaban abbas din da ita,ganin haka yasa tun kafin su qaraso suraj da muhammad da suka masa rakiyar suka janye baya,suka basu fili sosai.

    A hankali suka tsugunnar da ita a gaban nasa,rabin fuskarta yana rufe,saidai hakan bai hana kayan adon dake jikinta bayyana ba,suka ja da baya,sai falon ya dauki hayaniyar abokan wasa da suketa yiwa juna tsiya tsakaninsu da uncle muhsin,abinda ya dan janye idanun mutane kenan daga kan abbas da widad din.

    Tana zama awajen wani irin qamshi ya soma fita daga jikinta,sassanyan qamshi mai fusgar hankali da kwantar da zuciya,irin qamshin dake saurin sakawa zuciya karaya da wani irin sassanyan yanayi,ya daga idanunsa a hankali,fararen hannayenta da suka jan lalle irin na asalin yamalawa su ya fara gani,a hankali yaci gaba da kallonsu kafin ya daga kai zuwa ga fuskarta,dai dai sanda itama ta daga kanta zuwa gareshi don ta gaidashi kamar yadda anty madina ta gaya mata,fuskarta ta fito tarwai da wani irin haske data qara

    “Ina yini” ta furta,bugun zuciyarta na bayyana har saman harshenta,ya kuma biyo ta sautin gaisuwarta ya sanya lafazinta fita a rarrabe,amma hakan sai ya qarawa sautinta mai cike da quruciya kyau,sai ya dan lumshe idanunsa kadan yana amsawa

    “Lafiya qalau” yana ganin fuskarta a yau ta sake zama ta manya fiye da ranar da ya ganta a gidan muhsin,a yau din ta dan sake zama babba kadan ba kamar ranar ba

    “Sir…..me hoton ya gama dauka,saura na tsaye da wanda za’ayi muku da hajiya ummu saboda tarihi ko?”

    Sam baima san zaman da tayi wai hoto akeyi ba,muhsin ya cuceshi,yanzun idan baiyi wasa ba kafin la’asar hoton ya riga rana fadawa cikin kafofin internet,ko a haka baisan yadda akayi labarin bikinsa ya karade duniya ba,ko ina ka duba tsakanin whatsapp twitter facebook da instagram zancan da akeyi kenan

    “Dagota mana please,yanzu yanzu aka gama baka amanarta fa suna kallonka” suraj ya rada masa,no more option sai bata hannunsa da yayi

    “Taso” ya fada yana kallonta,labbansa daya furta taso din take kalla,tsoro da mamaki fal idanunta,dama shima dan iska ne?,abinda take fada kenan a ranta,a gabansu ummun yake bata hannunsa?,bashi da kunya ashe shima?.

    Bata gama wannan tunanin ba taji ya kama lallausan tafin hannunta,ba shiri ta miqe ta kuma zame hannunta da sauri hawaye suka fara taruwa a idanunta,lallai saita gayawa ummu abinda yayi mata,so yake ta mutu?,bayan ummu ta hanata tsaiwa kusa da kowa ma?.

    _to masu karatu,gafa amarya widad mai cike da tarin wauta quruciya gata kuma goyon kaka,ba’a fara wasan bama,muje zuwa dai_😂😅👏🏽

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    O_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥

     

    [2/23, 1:39 PM] halimatuabidah: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 28

    Arubuce Ta Ke 28

    Page 28

    *********Washegari tana dakin yaran tana sauya musu kaya bayan tayi musu wanka taji ana sallama a falon nata,qaramin tsaki taja,ita gaba daya batason baqi a rayuwarta tun asali,bare a yanzu da take cikin wannan yanayin,mimi ta aika ta dubo waye?,sai ta dawo tana ce mata baquwa ce,tadan harari yarinyar,har yanzu taqi tayi wayo irin yadda takeso,irin wayon da zata iyayi mata bayanin duk abinda takeson ji,saita ajjiye kayan nawwara da bata kai ga sanya mata ba,ta miqe tana cewa

    “Bari muga wanne munafukinne” tayi waje yaran suna biye da ita.

    Tun kafin ta qaraso ta hangi wacece,rabi’atu ce,cousins suke da abbas din,takan jima bataga rabi’atun ba,bama ita kadai ba,danginsa ma yawancinsu ba wani zuwa sukeyi ba,saidai idan an hadu a wani sha’ani idan ta samu zuwa saisu gaisa,suna girmama ta dai dai gwargwado,amma ta dauki hakanne a mazaunin don anga mijinta yana da rufin asiri ne.

    Fuskarta kadaram kadaham ta qaraso ta samu kujera daya ta zauna tana dan satar kallon rabi’atun,saboda daga nesa taga yadda take satar kallon falon,zuciyarta kuma ta raya mata gyaran da akayi mata take kallo

    “Dangin miji irin jaraba” ta fada a ranta,babu dama suga sakakken abu a gida ko a jikinka sai sun nuna a fuska ko a kalaminsu(nace uhmmm,inama suka hadun ko sukazo gidan bare hakan ta faru?).

    Ba yabo ba fallasa suka gaisa da rabi’atun,sai kuma shuru yadan biyo baya,sai ita din da taketa qoqarin yiwa su mimi wasa,wadanda suka qi sakin jiki da ita saboda rashin sabo da basuyi da su ba.

    Kai rabi’atun ta dago tana cewa

    “Wai nan bayanku nazo suna,kinsan a nan qanwar mijina take aure”

    “Uhmmm,Allah sarki” ta fada a taqaice

    “Sai nace nari na qaraso mu gaisa,na kuma yi miki murna ko jaje zance,ashe kuma yaa abbas aure kishiya zai miki?,kuma a rasa wadda za’a rakito miki sai ‘yar wani garin,kuma ma yarinya qanqanuwa wadda a haife ya kusa haifarta” da fari cin mutunci hafsat ta shirya yuwa rabi’atun,amma jin ta fara bata hint akan abubuwan da batasan dasu ba saita maida wuqarta tana gyara zamanta

    “Ya kusa haifarta fa kika ce?”

    “Wallahi haka inna ke gayamin,tunda kwata kwata bata wuce shekara sha uku zuwa sha hudu ba” wani abu ne ya tsargawa hafsat,saita nema tashin hankalinta kaso talatin cikin dari taji babu shi,ta aro sakin fuska ta dorawa fuskarta

    “Kin ganta ne rabi’ah don Allah?” Kai Rabia ta girgiza

    “Ban dai ganta ba,amma inna tacemin ta taba ganinta gidan sau daya,badai ‘yar nan bace ‘yar kano ce” gabanta yadan fadi kadi jin abinda ta fada daga qarshe,ana wata ga wata,ko zakayi kishi yafi kayi da ‘yar garinku,kar tasan kar ne,bawai kayi da bare hayin wani gari ba,garin ma da tasha jin masu kishiyoyi daga wannan nahiyar suna qorafi,to amma ‘yar shekara sha uku zuwa sha hudu kishiya ce ko ‘yar raino?.

    “Ni irin wannan auren banda abin hajiyarsu,mutum na zaune da matarsa ya dauko aure,a kuma tsallake gida a tafi dawa?”

    “Da gidan da waje duk dai kishiya ce,ko daga dakinki aka fiddo miki da ita sunanta kishiya” hafsat din ta amsa mata rana dan hade rai,saboda tasan yadda ‘yan mata da yawa cikin familyn ke sonshi,kamar shi kadai ne namiji a family din nasu,sai data dinga murje idonta tana yanka musu rashin mutunci ta samu salama.

    “Gaskiya dai” rabi’atu ta waske ta hanyar fadin haka,bata jima sosai ba saidai hafsat din tadan samu wani haske akan lamarin,da yadda hajiyansa ke maraba da abun,daga qarshe sukayi sallama,ko pure water rabi’atu bata samu daga wajenta ba,haka tabar gidan tana tsine mata cikin zuciyarta,saidai duk da haka sudai suna adawa da wannan auren,tunda nasu basu samu ba ‘yan qannensu da suka zama ‘yammata gwara a bata goma daya bata gyaru ba gaba daya.

    Rabiah tana fita hafsat ta wuce daki cikin hanzari,ta dauko wayarta ta soma neman number din anty ummeee ta labarta mata labarin data samu,saidai duk saurinta ya zama nawa saboda babu kati a wayar tata,dole ta koma ta mobile app din bankin da take amfani dashi,ta saka card din dari biyu ta kirata.

    Sai data kusa tsinkewa anty ummee din ta daga,hafsat na daga tsaye ta gaza zama,sai kai kawo takeyi

    “Anty ummee….kina jina?” Ta fada da matuqar zaquwa,har kana iya jiyo haka cikin muryarta

    “Ina jinki hafsatu,lafiya?” Guri ta samu saman bedside drawer dinta ta zauna sannan ta soma magana

    “Yanzun nan rabi’atu cousin din abban mimi tabar gidan nan,kinsan yarinya qarama yaje ya dauko?,ko shekara sha biyar bata cika ba?” Ta qarashe maganar tana tabe baki,takaici yana cikata.

    Dariyar da anty ummee ke qyalqyalawa tayi kasake tana saurara,sai daga bisani tace

    “Kai haba?,kice raino ya dauko?,tirqashi,to ke ai ta fadi gasassa,babu kuma wani sauran kishi da tashin hankali daya rage miki”

    “Kamar yaya?,haba anty ummee,idan za’a maka kishiya ma ai sai ayi maka isassa,wadda zaku goga da ita,ba wata can qasan qasanka ba”

    “Tabdijan” anty ummee ta fada sannan ta dora da cewa

    “Amma bansan baki da hankali ba sai yau,ke!,kishiyar da zata shigo ta goga da ke ai masifa ce,me yayi miki zafi?,to idan baki sani ba bari na gaya miki,Allah sonki yake shi yasa ya hadashi da qwaila,a yanzun ne za’a fara wasan ma da kyau,dama dukka tana hannunki,idan kika dauki.maganganun da mukayi dake rannan kikayi amfani dasu da kyau to ina me tabbatar miki yadda zaki bawa su mimi da nawwara umarni itama haka ne,ba boka ba malam,komai zaizo miki da sauqi,kina daga kwance kina sarrafa gidan a hannunki,yanxu saurara nayi miki wani sabon karatu…….” Gyara zama tayi sosai tana bada hankalinta ga anty ummee din,tana hasashen qamshin gaskiya cikin msganganun anty ummee,sai taji ranta ya fara yin fes

    “Ina jinki” ta cewa anty ummeen……

    *********Can quryar gadon ummu take kwance abinta,ta duqunqune waje daya,duk kuwa da cewa gidan a cike yake da baqi jikoki da surukan gidan,wanda a baya duk lokaci irin wannan tana tare dasu sunata sabgoginsu,sabanin yau da gaba daya take jinta wani iri,musamman da aketa mata abubuwa daya banbanta dana ‘yan uwanta,aka kuma tsameta daga cikinsu.

    Tana daga kwancen tana kallon yadda ummu ita da warisha qanwar abbanta suketa hada kaya cikin manyan buhunhuna da kwalaye,wanda gaba daya kayan ummu tace nata ne,gidanta za’a kai mata ayi mata jeranta,itama ta samu nata gidan na qashin kanta,duk sanda ummu ta fadi hakan dadi takeji,amma yau gaba daya jikinta ya sanyaya,gwiwarta ta fara sagewa.

    Ana tsaka da wannan latifa tayi sallama ta shigo dakin ummun,ta tsaya daga bakin qofa yana gayawa ummu game gyaran jiki tazo,tunda widad din taji haka ta runtse idanunta tahau baccin qarya,ita kwata kwata batason wannan kwabe kwaben da aketa shafa mata yau wajen sati guda kenan,tana jin sanda ummun ta waiwaya tana qwala mata kira,amma sai ta sake lafewa cikin bargo tayi kamar bacci take,har ta gaji da kira ta juya ga latifa

    “Inaga kawai abar aikin nan haka,dama yau da gobe ne kawai ya rage”

    “To shikenan,bari na sallameta,yauwa……anty madina tace na gaya miki,kayan miyar ya za’a yi dasu,a markada gaba daya azubasu a freezer baya?”

    “Eh hakan yayi,don kada su lalace kafin jibin”

    “To shikenan” sai latifan ta juya ya fita,su kuma sukaci gaba da hada kayan,tana labe cikin bargo tana satar kallonsu,tana jin anty warisha na cewa

    “Banda abun ummu nawa ma jikin widad din yake,me ya sameshi ma da za’a mata gyara,ita da dama fatarta me kyau ce,a haka ma a karon banza daukan ido takeyi”

    “Wallahi madina ta matsa sai anyi mata,to ya na iya,itakam dama ta iya biyewa shirmensu,yanzu haka ta gama tsara musu komai,har kudi tasa muhsin ya karba musu wajen ango wai zasuyi walima” dariya warisha ta sanya

    “Kai,Allah mai iko,widad amarya” sai ummun ta murmusa kawai,don dauriya kawai takeyi batason aga rauninta.

    Tun tana labe tana kallonsu har baccin gaske ya dauketa,bata farka ba sai dab da la’asar,sanda ta tashi dakin babu kowa,sun gama aikinsu sun fice,bandakin ummun ta shiga ta daura alwala,ta shimfida abun sallar tayi sallarta,saita dan zauna tana jin hayaniyar su nabiha da sauran jikokin gidan,daga bisani ta gaza daurewa ta fito.

    Ido kuwa yayi mata caaa,mutane anata kiranta da amarya,saidai ta tura baki tayi gaba abinta,itafa shi yasa tunda aka fara baqin ma batason fitowa,a haka dai ta samu ta wuce sassan anty madina,a canne ta sake sosai abinta,harta manta da komai ma,har sai da anty madina tace lallai gobe za’a tsefe kai ayi kitso,a nan fa suka raba gaari da ita,saboda ta ambato maqiyinta wato kitso.

    *RANAR DAURIN AURE*

    Cikin jerin gwanon motoci na alfarma suka taso,tun daga garin bauchi zuwa cikin garin kano,qarqashin jagorancin jami’an tsaro da matakai masu tsauri,a ranar tamkar dai wani shugaban qasa,duk yadda ya dauki daurin auren sai ya wuce masa haka,tamkar dai dama ya dade da shiryama hakan,shi kansa cikin sabuwa dal din motarsa yake,yana seat din baya shi da suraj,sanye da wata danyar shadda wadda koda gari aka baka ka canki kudinta ba zaka ajeta nan kusa ba.

    Tunda suka taso fuskar hafsat ke masa yawo,tunda zancan ya tsiro bai taba jin tausayinta irin na yau ba,yana hangen yadda fuskarta ta sauya a sanda yake shiga motarsa cikin shigar dake jikinsa a yanzu,saidai zuciyarsa cike take fal da mamakin mene ya sauya hafsat?,me kuma ya kawo wannan sauyin?,yasan halinta ciki da bai,meye ya sanyata zub da makaman yaqinta?,wannan amsar ce har yanzu ya kasa lalubota,sai tarin wasi wasi da yake fama dashi kullum kwanan duniya.

    Tun daga titin farko zuwa abinda yakai layin da zao sadaka da ainihin gidan alhj salim mai fata cike yake tanqam da jama’a,idan akace maka jama’a ina nufin jama’a na gaske da zakayi tsammanin daurin auren wata hamshaqiyar budurwar data ci ta qoshi da karatu da wayewa akeyi,gaba daya unguwar a hargitse take sakamakon halartar daurin auren da manyan ‘yan siyasa gwamnoni da kuma qusoshin gwamnati da abbas yake hulda dasu sukayi,jama’a dake tsaye a gefe guda suna ci gaba da lissafa gwamnonin da sukaga suna shiga unguwar tasu,sai da suka lissafa shida casss!.

    “Bisa dukkan alamu wannan karon babban kamu akayi a gidan nan,lallai yau sun jawo babban kai,kai kaga motocin dake ta gilmawa kamar daurin auren ‘yar shugaban qasa?” Ire iren maganganun da matasa ‘yan zaman banza a bakin layi keyi kenan,sunayi suna ci gaba da dorawa a lissafin su.

    Daga can cikin gidan kuwa a shaqe yake da jama’a,ko ina idan ka kalla hada hada akeyi,zaka tsammaci an dauki shekaru ne ana yiwa bikin tanadi,saidai hausawa suna cewa,kowanne aure da arziqinsa yake zuwa,wanna haka yake,domin kuwa a lokacinne aka baje lefen widad wanda ya iso ne tare da ‘yan daurin aure,akwati mai sunan akwati,akwati na alfarma guda goma sha biyar,kowanne maqare da sutturu masu daukan hankali,duk wanda ya daga idanu ya kalla koda baiso magana ba sai bakinsa ya subuce ya furta

    “Ma sha Allah”mafi yawan mutane cikin family da wadanda ke cikin gidan dake zuba idon suga wani abun kaico ya bulla sai jikkunansu suka fara yin sanyi,musamman da labarin irin manyan mutanen da suka halarci bikin yajewa kunnuwansu……….

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/22, 2:49 PM] halimatuabidah: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 31

    Arubuce Ta Ke 31

    Page 31

    Maganar ta qonawa anty madina rai sosai ta kuma bata haushi,sannan sai taji.maganar kamar tayi girma a kunnen widad,tana girmama dukka faccalolin nata saboda dukkansu sun girmeta,ita kadaice qarama a cikinsu,shi yasa take musu kallon yayunta,don haka ta tattara wayar da kudin ba tare data gama saita wayar ba ta miqawa widad

    “Kaiwa ummu ta gani ta adana miki,anjima zan shigo saina qarasa gyara miki” karban kayanta tayi ba tare data ma fahimci maganar me momma takeyi ba,ko baqincikin dake manne a ranta ba ta qara gaba cikin doki da zumudi.

    Da kallo momma ta bita sannan ta tabe baki

    “Kinga yarinya sai rawar kai take,Allah yasa bai lasa mata zuma a baki ba ya barmu da…..”

    “Kai…..kai momma” anty madina ta fada tana kama kai fuskarta na nuna zallar rashin jin dadi

    “Wannan maganganun sunyi girma da yawa fa”

    “Wanne girma?,a wajen wa?, yarinyar da yanzu keda ita dukka matsayinku daya?,tabdijan,kina wasa da yaran yanzu,ni da rannan naji tana gaya musu zata tafi gidanta itama ta dinga girki irin nasu anty dina,tayi.bacci a gadonta?,to billhuwallazi kada ma kiyi mamaki idan akace miki ya gama lallatseta kafin ya tafi,ko ya fara buda hanyarsa”

    “To haka muke fata,aiba haram bane,me zan baki?” Tayi mai gaba daya saboda maganar ta soma isarta

    “Yauwa,mai zaki zuba mana,nawa ya qare gaba daya jiya suka zube shi a dambu” karbar robar tayi kawai ta miqe ta wuce store dinta dake manne a kitchen, cikin ranta tana tur da Ala wadai da irin wanna dabi:ar tata,banda abinta meye abun kishi da widad?,me za’a yiwa baqinciki akanta,yarinyar da bata da maraba da marainiya?,bata taka muku ba bata zubar muku ba amma kunbi kun qwarzabi kanku a kanta,batama san me suke ba,bata wani ganewa halinsu idan ba takurata sukayi da kyara ko hantara ba,shine zaka ga ranta ya baci saman fuskarta,ko kuma ta janye jiki daga gurin ba kuma zata dawo nan kusa ba.

    °°°°°°duk yadda take ta so ta tursasata kanta da zuciyarta…..ta tafi da zuciyar tata da ruhinta bisa doron shawarar da anty ummee ta dorata akai amma abun yana ta neman yaci tura,daga sanda labarin AN DAURA auren mijinta abbas sa wata gaba daya ta birkice,zuciyarta nata gaya mata anya mafita ce anty ummee ke bata?,ta tsaya kawai tayi masa hauka,tayi tawaye ta tada masa hankali har ya aje auren,wannan shine shawarar da mafi rinjayen sashe a zuciyarta ke bata,yayin da wani sashen yake gaya mata ta haqura taci gaba da tafiya a haka,saboda taga alfanun hakan,ta samu alkhairai masu yawa daga jikin abbas din.

    A ranar ita daya ce a gidan,ta tura yaran gidansu,ko wankan arziqi bata samu yi ba bare ta kintsa gidan,sai ta zauna dirshan,ta soma bin status din dukkan wanda tasan ya tafi kano daurin auren.

    Irin kyan da taga abbas yayi cikin dukka hotunan,da yadda taga fuskarsa shimfide da qayataccen murmushin nan nasa sake matuqar burgeta da daukar mata hankali sai taji ta sake birkicewa,saidai kaf hotunan bataga fuskar amaryar da taketa lalube ta gani ba.

    Jefa wayar tayi gefe tana rufe fuskarta da tafin hannunta,kuka ya subuce mata,abbas ya cuceta,kuma ko meye zaiyi mata bazai taba wanke kanshi ba,ba haka tasan abbas ba,bashi sa kallon mata ko kadan,bai shiga shirginsu kwata kwata,ya akayi wata mace ta gilmawa idanunsa har ya qyasa yaji yana son yin tarayya da ita?, macen ma yarinya qarama kamar yadda aketa bata labari?,ya zuwa yanzu ka ta fara tantamar anya yarinyar ce kamar yadda aka ce?,tasan tsarika da zabin abbas,ta yaya zai aura yarinya?.

    Wayar ta jawo da sauri ta cireta daga flight mode din data saka mata tun jiya,dai dai lokacin da saqon abbas ya fado wayarta bayan ya gaji da kiranta yana jin wayar a kashe,tsaki taja tayi fatali da saqon ta shiga duba number anty ummee.

    Bugu daya ta daga,kamar mai jiran kiran nata dama,kuka kawai ta saka mata,tayita yi har kudinta ya qare kiran ya katse,anty ummee daga can inda take zaune a falonta taja tsaki

    “Kuka ma yanzu kika fara,kishiya wasace,shegen son abun duniya irin naki,inda kin bada dama ‘yan uwanki sunzo gidan an dan zauna dake aida an debe miki wannan damuwar,amma don kada mutum yazo yaci abinci da nama kika hana kowa zuwa,kyaci takaicinki ke kadai” ta fada tana bin kiran nata daya katse.

    “Anty ummee anya zan iya?,wallahi bakiji abinda nakeji a qirjina ba” ta fada cikin muryar kuka

    “Ke dole ki daure fa,saboda ribar ciki tafi rashin ribar yawa,wannan ce kadai hanya guda daya da zaki zauna salamun salamun a gidan,kuma kowa yayi miki.biyayya ba tare daya shirya ba,wannan itace kadai hanyar da zaki tankwabar da auren ma gaba daya ba tare da kowa ya zargeki ba,amma fa saikin jure sai kuma kin daure,in kikai haka gaba zaki godemin” Shuru tayi tana nazarin maganganun a kanta

    “Ki kwantar da hankalinki,idan kin samu lokaci kizo zan sake shirya miki yadda komai zaici gaba da tafiya” ta sake gaya mata bayan sunyi maganganu masu yawa da suka dan saka hafsat din sake aro dauriya,duk da yadda take jin zuciyarta kamar wuta

    “Zanzo gobe ko jibi ma”

    “To shikenan,amma lallai lallai karki nuna masa wani banzan hali ko daya,kiyi kamar ba’ayi komai ba,zakiga yadda zai sake bude miki bakin aljihunsa”

    “To shikenan” ta amsa mata tana sake share sauran hawayenta.

    Suna gama wayar saita koma ta duba saqon daya turo matan,gaisuwa ce yana kuma shaida mata suna kan hanyar dawowa gida,wani mugun tsaki taja,kamar zata ajjiye wayar sai kuma ta tuna da zancansu da anty ummee,tayi ta maza ta danne zuciyarta ta kirashi.

    Bugu biyu ya daga wayar,dai dai lokacin da har sun fara yiwa kano nisa,suna bayan motar da ake tuqasu shida muhammad da suraj a tsakiyar escort dinsa,sai ya gyara zamansa yana kara wayar a kunnensa.

    Tun daga sautin muryarta ya fuskanci akwai damuwa,duk da yadda tayi namijin qoqarin boyewa,to amma a yadda taji ta masa magana ba wani mummunan lafazi sai yaji hankalinsa ya sake kwanciya,da ya tambayeta mai ya sami wayarta tun jiya yake kira a kashe

    “Kamar da gaske an damu dakai” ta fada a qasan ranta bayan tayi tsaki,amma a zahiri sai yace

    “Nawwara ce ta jefamin ita bayan freezer,ruwa ma ya tabata,yanzu nakeson bada ita game gyara”

    “Ya salam,shikenan,ki jira na dawo zan bayar a duba miki da kaina” tuni zuciyarta ta gama hasko mata abinda zatayi da wayar don haka tace

    “A’ah,ai yaronma yana waje jirana ma yakeyi na bashi wayar”

    “Is okay,yayi,saimun qaraso”

    “Ala tsare” ta fada tana gintse wayar,saita maidata flight mode din,gobe ko jibi idan zata gidan anty ummee zata biya ta saidata ta sake hade kan kudadenta,ya sake kashe wani kudin ya siya mata wata,don ba imani ko daga qafa yanzun tsakaninta dashi.

    Zuciyarta nata gaya mata ta shiga kitchen tadan samar masa wani abun da zaici,amma sai tayi fatali da wannan tunanin,taja tsaki ta miqe kan kujera abinta tana cewa

    “Bazan iya ba wallahi,wannan pretending dinma da nakeyi duka ya fara isata” ta sake jan wani tsakin tana rufe idanunta tanajin yadda ranta ke mata suya.

    Awanni kusan biyu tana zaune a wajen,sai data gaji don kanta,sannan ta miqe ta kom bedroom dinta,yanayin da jikinta yake ciki itama ya fara damunta,don haka ta hada ruwa ta shiga wanka,gaba daya hatta da yaran batason motsinsu ko bari bari da zasuyita sakata,don haka tun da safe ta aika gidansu dasu,wannan ne kadai zai bata damar zama tayi jinyar kanta da kyau.

    A nutse ya fita a motar bakinsa dauke da addu’o’i,samuel ya zagayo yayi saluting nashi sannan ya miqa masa key din cikin girmamawa,hannu yasa ya karba yana masa ban gajiya,sannan samuel din ya juya ya fita a gidan,zasu qarasa a ragowar motocinsu dake cikin layin.

    Jefa key din yayi a aljihun rigarsa,sannan ya juyo yana nufar gidan bayan ya sauke ajiyar zuciya,zuciyarsa na gaya masa ko me zaya tarar cikin gidan kuma?,sanin gaibu sai Allah,haka yaci gaba da takawa da kuzarinsa da qarfin gabban nan nasa da ya zama kamae signature dinsa.

    Da sallama a bakinsa ya yaye labulen falon yana qarewa falon kallon,as usual yana nan kamar kowanne lokaci,kamar yadda ya saba tarar dashi, matuqar sa’a ce zaici yayi wata tafiya ya dawo ya samu falon a kintse,har ya zame masa jiki,bawai ya dawo ya sameshi a hargitse ne abun mamaki ba a gareshi,babban abun mamakin ya sameshi neat,sai ya saki labulen ya kutsa kai zuwa ciki.

    Shurun da yaji yayi yawa sai ya dauka ko bacci yaran sukayi bayan ya kalli agogo,bakwai sa rabi na dare harda wasu mintuna,kansa tsaye ya tunkari dakinsu,amma daya tura sai yaga wayam babu kowa,dakin dai shima kamar ko yaushe,saiya maida qofarsa ya rufe ya sauya akalarsa zuwa dakinta.

    Tana tsaye bayan ta fito a wankan,daure da zanin jikinta wanda tayi masa daurin gaba(daurin qirji),tana ta qoqarin taje gashinta yana cije mata saboda taurin da yayi,ya turo qofar suka hada idanu,saita amsa masa sallamar ta maida kanta wajen taje kan nata,kamar ma batasan wayeshi ba.

    Kofar ya saka yana zare idanunsa daga saman gashinta yana takowa zuwa ciki,yasan kafin ya tafi ya ajjiye mata kudaden gyaran jiki da gyaran kai,yafi tsanar qazantar gashi fiye da qazantar komai,amma ita kwata kwata ba damuwarta bane,to ina takai kudin?,me kuma ya hanata zuwa gyaran kan?,jikinma baiga alamun an gyarashi ba, tun yana sanyata a gaba ya kaita har ya daina bata lokacinsa da kudinsa,tunda ya siya mata mota kudin kawai yake bata,cikin kaso goma kuma kaso biyu kacal take zuwa,kaso takwas din saidai ta adana kudinta,duk da shi baisan me takeyi dasu ba.

    Cikin juriya ya isa bayanta,ya kuma rungumota ta baya zuwa cikin jikinsa, hannayenta biyu ta saka da dukka qarfinta tana son janyeshi a jikinta,yasan zata aikata hakan,shi yasa bai mata qaramin riqo ba

    “Am sorry” ya fada da muryar da yasan tana matuqar tasiri wajen karya lagonta,turjiya da tijara takeson masa koda zata rage zafin dake danqare a ranta,mugun guguwar baqin kishin da anty ummeen tasa ta danneshi bisa salo na kissa,amma sautin muryarsa data sauka a kunnenta ta karya dukka lagonta,sai ta sakar masa kuka,kuka kuwa sosai wanda ke bayyana ftsananun zafin da zuciya ke fuskanta.

    Ya sani,kishi yana da zafi,don haka ya fara lallashinta cikin wani salo da yasan yana saukar da zafinta,a hankali sai ya soma birkice mata,abinda yaja hankalinta kenan ta soma zame masa tana tureshi,cikin ranta tana mita,sai an fara abun arziqi dashi sai kuma ya canza hanya,shi din babu dama a hada jiki dashi sai wani zance na daban.

    Sosai yayi mata riqon tsauri,baisan meye damuwarta ba,bata taba iya karbar damuwarsa hannu bibbiyu ta bashi hadin kai ya sauketa ba,kamar bata da wani feeling,kuma qarya ne!, tabbas tana dashi,saidai ta sanyama ranta wani baqin rai da girman kan banza.

    Duk yadda taso tayi avoiding nasa amma ta kasa,dole ta bada kai bori ya hau,duk da ba wani hadin kai ya samu ba,ya saba da hakan,har kusan ya zame masa jiki,bayan komai ya kammala kuma ta shiga quncinta kamar yadda ta saba,baibi ta kai ba,hasalima kafin tayi wanka sai daya tabbatar ta wanke kanta da kyau,ya hadata da hand drayer sannan ya fito,ya wuce sassansa don ya shirya.

    Ko da ya gama shirinsa ya fito kitchen ya duba saboda yadda cikinsa ya rarake kamar an masa yasa,babu alamun an girka komai,sai kawai ya dauki key ya fita don yi musu takeaway ba tare da ya tsaya jiranta ba,yasan ba abinda zata dafa a wannan lokacin,a hanya yayi kiran hajiyarsa,har kuma ya qarasa wajen sunata wayar,yace mata gobe zai shigo da wuri kafin ya wuce,don a gobe yakeso ya koma kaduna.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[2/25, 9:26 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 26

    Arubuce Ta Ke 26

    Page 26

    Koda ya shiga sassansa sai yaji dama dama,duk da cewa akwai qura data dan shishshigo masa amma kuma babu wannan dattin da annakiyar ta sassan hafsat,bai gaji sosai ba kasancewar tafiyar jirgi ta banbanta data mota,don haka ya ajjiye yaran saman kujera sunata masa hira,yahau kakkabe sashen nasa da goge goge,sai da yaga komai ya dauki haske,sannan ya hada ruwa yayi musu wanka da kyau,yana wasafa yadda zai samu lokaci yakai mimi a wanke mata gashinta.

    Sai da ya gama shiryasu sannan yayi nasa wankan,ya shirya cikin kayan barci saboda tara ta gota a sannan,kamar ya kirata yace ta kawo masa abincin nan amma sai ya fasa,ya tasa yaran a gaba suka koma can.

    Tana kitchen tana ta kaca kacar yadda zata hada masa koda coleslaw ne mimi ta shigo tace tazo inji daddy, saita maida.kayan hadin data debo din kawai,ta kwashi warmer da plate din ta biyo bayan yarinyar,tana dan hade ranta,wai koda hakan zai sanya yaji shakkar mata magana ko fada.

    Saidai kuma ya bata mamaki,saboda yadda yakecin abincin yana yiwa yaransa hira ba tare da yace da ita komai ba,can qasan ransa yana ji ne kamar ya furzar da abincin daga bakinsa,duka dai yana daurewa ne saboda muhimmiyar maganar da zaiyi mata.

    Koda ya gama cin abincin bai tashi a wajen ba,sunta hira da yaransa yana biyewa shirmensu,duk da hirar babu wani armashi,ita kuwa gogar tana zaune a gefa tana danna waya,abinda tafi kauri kenan,bata wani damu da hira da miji ba sam,lokaci lokaci takan dan sanya musu baki a hirar,a haka har nawwara dake saman cinyarsa tayi bacci,jimawa kadan mimi ma ta soma gyangyadi

    “Gwara ki kaisu daki ko?” Yace da ita yana dubanta,saita aje wayarta tana dan bata rai

    “Sai da nace ma mimi ta wuce daki idan ta fara jin bacci fa”

    “She’s too young da zata gane hakan ai” qarasowa tayi ta soma tashinta cikin hararrami,ya dakatar da ita cikin dabara ya daga yarinyar,ta kama hannunta suka wuce daki.

    Ba jimawa ya miqe,ya nufi kitchen don dafa tea,saboda ba wani sakin ciki yayi yaci abincin ba.

    Da kallo yabi kitchen din saboda uban wanke wanke da ya fara cin karo dashi,kana gani kasan ba iya kwanukan yau bane,saboda wasu ma sun fara bushewa wasu kuma sauran abincin ciki ya fara rubewa,kai ya girgiza takaicin na cinsa,ya matsa ya duba ma’ajiyar tukwanenta,cikin taimakon Allah ya samu wata wankakkiya,ya hada komai da komai ya tsaya ya jira ya tafasa ya juye ya dawo falon ya zauna ya fara kurba a hankali yana kallon labarai da ake haskowa a tashar alhadath,saidai sam ba ta nan hankalinsa yake ba,yana jiran jin fitowar hafsa ne,amma har ya gama babu ita ba dalilinta,wannan yasa ya miqe ya nufi dakin kansa tsaye.

    Yana tura qofar suka hada ido,tana kwance tsakiyar yaran,ya qarasa shiga ciki a hankali hannayensa zube a aljihun wandonsa yana nazarin dakin a fakaice,komai babu kintsi,ko ina ba’a gyare yake ba,sai ya kauda kai ya maida gareta

    “Zan wuce daki,wa zan daukar miki a cikinsu,coz na fara jin bacci,inason kuma muyi magana dake” fuska tadan yamutsa kadan

    “Kawai ka kwanta a nan mana,ni bansan me yasa bakason kwana a dakina ba,saidai ni kullum ina yawon binka?” Ta fada yau dai tana dan karya murya,jingina yayi da madubin dakin yana qoqarin controlling kanta,gaba daya dakin its not well organized,komai a birkice yake ba bisa tsari ba,duk sanda zai kwana a dakin komai sai ya nemi inda aka wulla masa,wannan dalilin ya sanya zaiyi wuya kaga wani abu nasa mai muhimmanci a dakin.

    Kafada ya dage
    “Well,zanje na shirya”

    “Yauwa,thank you”tafada tana dan jin dadi,saiya juya a hankali ya fice a dakin.

    Sai da yayi shafa’i da wutirinsa,ya kuma dauka duk abinda yasan zai iya buqata sannan ya rufe sashen ya koma,ya isa dakin ya dora kayansa saman madubinta yana fadin

    “didn’t you sleep?” Saita motsa kadan tana cewa

    “Uhmm”

    “Okay,tashi,dama muyi magana dake” dan muskutawa tayi kadan,sai kuma ta miqe a hankali ta zauna tana dan murza idanu,zuciyarta na bada Allah yasa samuwa ce tazo.

    Kujerar gaban madubi yaja ya zauna dab da ita,har gwiwoyinsu na gogar na juna,ya goye hannayensa a qirji yana duban fuskarta da manyan idanun nan nasa da suke saurin kassarata,tsahon wasu mintuna baice komai ba,har sai data qosa tace masa

    “Wannan kallon fa?,kana azamin nauyi fa,ka tasheni bakacemin komai ba” kai ya gyada siririn murmushi yana kufce masa,saiya saki hannayen nasa ya hade yatsunsa waje guda

    “Har yanzu motar da kikace min kinaso ita dince baki canza ra’ayi ba?” Wani madaukakin murmushi ya kubcewa hafsat din,abunda bata taba kawowa shi xai mata maganarsa ba,duk da dama abbas din ya iya bazata,ba daga nan ba

    “Eh itace” ta fada cike da zallar zumudi

    “Shikenan,nan da two to three weeks zata iso…..sannan kuma…..inaso ki duba kayan dakin da kikeson canzawa,ki turonsu ta watsapp,amma kada su d’ara 1mil,sai nasu mimi su kuma kada su wuce 50000k” wani irin mamaki da farinciki suka cikata,cikin muryar zumudi tace

    “Da gask kake abban mimi?” ta fada idanunta a waje tanason ta samu tabbaci.

    Kai ya jinjina mata yana sakin qaramin murmushi cikin bata tabbaci,hannunsa ta kama ya riqe da kyau tana dariyar farinciki gami da yi masa godiya.

    Hannayen nasu yabi da kallo,yadda ta riqe masa.hannun dama bata aikata hakan idan ba wani abun farinciki ya sameta ba,idan bai manta ba rabon data riqe masa hannun haka tun lokacin da ya shaida mata ya biya mata hajji,sai ya zame hannun a hankali yana cewa

    “Yauwa,dama nace zamuyi magana ko?”

    “Ai mun gama magana,irin wannan manya manyan albishir haka?” Ta fada tana washe baki,sai ya kada kai

    “Saura abu daya”

    “To ina saurarenka” ta fadi ba tare data bada wani muhimmin ba

    “Hafsa” ya kira sunanta,sai ta amsa tana murmushi

    “Komai muqaddari ne daga Allah ko?,hakanan rayuwarmu da dukka qaddarorinmu suna hannunsa,yadda ya tsara haka bawa zaibi,hakanan fadarsa ne daga qur’ani ku auri abinda yayi muku dadi daga mata bibbiyu uku uku da hurhudu…..” Statement dinsa na qarshe yasa fara’ar fuskarta taja baya,wani tunani kuma ya gilma mata,saita zuba masa idanu gabanta na wani irin faduwa,zuciyarta kamar zata fasa qirjinta ta fito

    “Hafsat,Allah ya nufeni da qara aure,wanda za’a daura shi cikin sati mai zuwa”

    “Meeee!!!” Ya fada da wata irin shaqaqqiyar murya,wadda tuquqin bala’i yasa ta gaza fita da kyau yadda ya kamata

    “Relax,calm down please,hakan ba yana nufin matsayinki ya canza daga yadda kike a zuciyata ba…..”

    “Wallahi qarya ne!……qarya ne abbas……qarya ne wannan” ta fada ya qaaraaji tana nunashi kamar wata mahaukaciya sabon kamu

    “Shine ka zaunar dani kana yimin wadan nan kyaututtukan?,to banaso,ka riqe kyaututtukan ka!,wallahi baka isa kuma ka qara aure ba!,ni kadai ce matarka!,ni kadai zaka zauna da ita duniya da lahira!!” Ta fadi da wani qaaraajin tana dubansa da idanunta da sukayi jazur suka kuma firfito kamar wadda aka shaqawa borkono.

    “Cool down,karki bari ranki ya baci kinji……zauna muyi magana ta fahimta dake” ya fada with softness yana yunqurin kamota ganin tana shirin miqewa,fusgewa tayi tana jifansa da wani mahaukacin kallo,ta bude bakinta cikin madaukakin sauti ta fara gaya masa dukkan maganganun da suka zo bakinta,miyagun kalamai na aibatawa da kuma tunzuri,sai ya koma kawai ya zauna,ya harde hannayensa a qirji yana kallonta a nutse.

    Ya sani ita aka tabo,kasancewa batun lamari na kishiya a wajen mace babban al’amari ne da ba kasafai suke iya daukan wannan mummunan labarin ba,wannan dalili ya sanya ya bata dama taketa fadin dukkan abinda taga dama ba tare da yayi yunqurin dakatar da ita ba,duk da kalamanta akwai wuce gona da iri da kuma zaqewa da yawa,amma yayi haquri ne ya jura saboda yasan wani ciwo ne da radadi daga zuciyarta,wanda shine ya dasa mata shi yanzu yanzu.

    “Shine ka zauna kana kallona?, wallahi abbas baka isa ba,wallahi nace bazaiyiwu ba” sai tayo kanshi,tana rarumo kwalaben turaren dake saman madubinta ya soma qoqarin jifansa dasu.

    Cikin qwarewa ya dinga sanya hannu yana cafe duk wadda ta jefo,ganin ko daya bata sameshi ba sai tayi kukan kura ta jawo bed lamp ta wurgota.

    Bai samu tareta ba,amma ta dakar masa hannaye,glass din jiki kuma ya yankeshi ba tare daya lura ba,saita tsugunna inda take ajjiye takalmanta ta fara daukansu suma daya bayan daya tana masa ruwansu.

    Miqewa yayi cikin zafin nama da mazantaka ya isa gareta,ya kama dukka hannayenta ya hade cikin hannunsa guda yana kallon fuskarta,ransa ya soma baci,ya dubi sashen dasu mimi ke a kwance,Allah yasa babu daya cikin abinda take wurgowa daya samesu

    “Ki nutsu hafsat!,ki nutsu!”ya fada shima da murya sa mai kaifi da zurfi,saita dakata din ta kece da wani irin kuka

    “Macuci azzalumi,Allah ya isa tsakanina da kai,kuma wallahi wallahi baka isa kayi wannan auren ba,idan ba haka ba sai na baka mamaki nima dakai da munafukar da zaka auro,ka fita ka barmin dakina,ka fita bana son ganinka!” Ta fada da mugun qarfi,saiya sakar mata hannaye,ya kuma taka a hankali zai fice,sautin amon muryarta ya dakatar dashi

    “Kazo ka kwashesu,suma bana son ganinsu,ka debesu daga gabana!” Dawowa yayi a nutse yadan tsaya gabanta yana kallon yadda ta birkice gaba daya,jikinta banda tsuma babu abinda yakeyi,yasa hannu ya kwashe dukkan yaran ya fita dasu.

    Ya jima yana mamakin baqin kishi it n na hafsat din,ashe abun ya wuce yadda take tsammani?,wanne irin hauka ne wannan?.

    Bai lura da hannunsa dake zubar jini ba sai daya kwantar da yaran saman gadonsa yaga stains na jinin a jikin blue bedsheet din nasa

    “Ya salam” ya fada sanda yake duba wajen,sai yaga ya yanke sosai,don haka ya koma dakin yaran dake sassanta don ya dauko first aid kit.

    Tun daga falonta yana iya jiyo gunjin kukanta,irin kukan da mutum yake zama dirshan ya bude dukka muryarsa yayishi,tausayinta sosai ya saukar masa a rai,sai ya kasa wucewa ya sake komawa ta dakin,sai biyu yana murda handle din yana jinsa a riqe da alama ta kulle ne daga ciki,ya sassauta murya yana kiran sunanta

    “Open the door please, don’t hurt yourself fa”

    “Ka tafi ka bani waje abbas,na tsaneka,banason kallon fuskarta,ka tafi nace tun ban bude na lahantaka ba!!” Duk yadda yaso ta bude din taqi,sai ma wasu miyagun kalmomin da zagi da yake antayo masa,hannunsa nata digar jini,dole ya haqura ya dauki kit din ya koma dakinsa ya gyara wajen.

    Daren ranar baccinsa ragaggene,haka yayita kai kawo tsakanin dakinsa zuwa sassanta,yasan halinta da muguwar baqar zuciya,yana fargabar kada ta illata kanta ita daya kulle a dakin,saidai duk sanda yaje din zaiji motsinta,wannan ke bashi ‘yar nutsuwa kadan.

    *Arewabooks: Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/21, 4:17 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 38

    Arubuce Ta Ke 38

    Page 38

    “Don Allah ki dauramin,na kasa wallahi” tayi maganar tana miqawa latifa dankwalin ba tare data lura da hafsa dake zaune a gefe ba,tana jin kamar ta mutu,abbas ya gama cutarta,yaje ya auro yarinyar data kusa haifa?, sannan kumata fita komai da komai na siffa?,duk da tana qoqarin qaryata kanta da kanta,tana qoqarin gayawa kanta idonta ne yake ganin hakan

    “Kawo,Allah ya gyara min ke,bansan sanda zaki koyi daura kallabi ba” dariya tadan saki

    “Ni nauyi Allah,banda anty deena ta takura”

    “Ga antynki nan baku gaisa ba” latifa ta fada bayan ta karba dankwalin tana lanqwasashi.

    A sakarce ta waiwaya ta dubi hafsa din da irin kallon da takewa kowa,ba tare da ta bawa matsayinta muhimmanci ko matsar dashi gaba daga matsayin da take bawa kowa data fara saninsa ba

    “Ina kwana?” Ta furta cikin girmamawa kamar yadda ta saba gaida dukkan wanda ya girmeta

    “Lafiya lau qanwata,ya kwanan baqunta?” Hafsat ta fadi da wani murmushi da takejin kamar na sossoka qayoyi ne cikin bakinta.

    Murmushi ta danyi tana maida dubanta ga latifa,saboda batasan amsar da zata bayar ba,don batasan amsar da ake bayarwa din ba,ta dan ranqwafa kadan latifa ta soma daura mata dankwalin.

    Cas ya zauna a kanta,ta daga kai latifan tana kallonta

    “Ehen…..yauwa,yanzu kikai dauri” latifa ta fada cikin tsokana.

    Idanunta hafsa takai kai,cikin sakanni taji ba zata iya ci gaba da zama tana kallon yarinyar ba,wani irin mugun kyau da kwarjini daurin yayi mata,saita miqe cak tana cewa

    “Bari na koma,yau jiki yayi nauyi ban samu dafa muku komai ba,kuyi haquri” murmushi inna laila tayi

    “Lah,babu komai fa,yaran ma suna gab da kammala dafa abun karyawan,ai ansha hidima wallahi,mun gode,Allah dai ya qara hade kanku,ya kade fitina,gata nan sai ayita haquri da ita,har yanzu akwai quruciya sosai a tare da ita,sai ana yi mata nuni,ana kuma gyara mata inda tayi kuskure,ayi haquri da ita don Allah” ta fada zuciyarta na danson naqaltar mata fuskar hafsatun

    “Aiba komai wallahi” ta fada a taqaice,can wani sashe na zuciyarta yana jin kamar ya zundumawa inna laila ashar,babu zancan quruciya uzuri ko daga qafa ga duk wadda ta aurar mata miji,koda kuwa widad din qyanqyasar yau ce,tunda har ta iya sanin meye so?,ta banbance tana sonshi,ta kuma iya sanin meye aure ai magana ta qare,babu daga qafa babu ragi babu kuma rangwame,haka ta dinga jefa qafarta zuwa sassanta idanunta basa gani sosai,fatanta Allah yasa abbas ya wuce sashensa,ya kamata ta rage kukan dake damunta a qirji.

    Cikin awannin da suka biyo baya suka sake shiga qalqale sassan nata da kyau,duk sauran abubuwan da ba’a gama kintsawa ba suka kammalasu,sun gama kuwa da wuri,saboda wadanda ke presidential lodge din da aka kaisu motoci sun kwasosu sun dawo dasu gidan,nan da nan sashen ya dan qara cika,anata hira da barkwanci,kusan kowa gidan widad djn ya tafi dashi,saboda babu ce kawai babu.

    Duk da wannan jikinta ya mata wani mugun sanyi,babu wannan hayaniya ko kazar kazar din,tana lafe a waje daya kusa da inna laila,itace ta zame mata kamar ummun nata,mugun kewar ummun take,gaba daya zuciya da jikinta babu dadi,duk da yadda suketa qoqarin janta da hira da kuma wasanni.

    Qarfe sha biyu har sun fidda jakankunansu harabar gidan,sun kuma fito waje,zuwa sannan idanun widad fararen nan sun fara kadawa suna tara ruwan hawaye,hakanan ta riqe hannun inna laila gam.

    Sanda suka fara shiga motocinsu dai dai lokacin ya iso,shi ya fara qarasowa wajen sannan hafsat wadda keta yashe baki tana sake binsu da murmushin yaqe.

    Cikin nutsuwar nan tasa yake tsaye gaban motocin,yana sanye da wani soft yard na maza gray color da yayi matuqar kwantawa a lafiyayyar fatarsa,jikinsa na fidda soft scent mai kwantar da hankali.

    Tsaf kowa ya shige,saura inna laila da latifa,a sannan tuni ruwan hawaye ya gama wanke mata fuska tsaf,zame hannunta da inna laila ta soma yunqurin yi ya sanyata fashewa da kuka sosai

    “Don Allah inna zan koma,karku tafi ku barni” ta fada tana sanya hannunta saman fuskarta,saita karya zuciyar kowa,inna lailan ta dubeta

    “Ga latifa nan widad,zaku zauna tare kafin wani lokaci,kiyi haquri” daga haka sai ta matsa gaba,ta kuma shige motar da sauri,gaba tayi zata matsa hafsat ta rigata,ta kuma riqota,a zuciyarta tana jin kamar ta rufe widad din da duka sannan ta hadasu su wuce kanon tare,amma sai ta shanye ta kuma hadiye wannan,cikin sigar lallashi tace mata

    “Haba mana widad,kiyi haquri,ai saiki karya musu zuciya,ba gani ba?,ga yayanki ma,sannan ga latifa an bar miki,kome kikeso ki gaya mana kinji,babu mai takura miki, kiyi shuru mana haba,yanzu inda su nawwara na nan ai sai su tsaya kallonki antynsu tana kuka” ta fada tana rungumota jikinta,ta rintse idanu tana jin kamar ta kara wuta ne a jikin nata.

    K’asa k’asa take kukan har zuwa sanda motocin suka gama ficewa a gidan,shikenan sun tafi sun barta…..shikenan sun rabata da ummun ta…… shikenan bata da kowa…..haka zuciyarta ta dinga gaya mata.

    Hafsat dince ta matsa gaba da ita wajen latifa tana miqa mata ita

    “Ki kaita ciki ta zauna ki lallasheta” sai latifa ta gyada kai tana kama hannunta tare da jawota jikinta suka fara barin wajen tana yiwa widad din magana qasa qasa,saidai da alama ba zata iya jurewa ba,saboda qarfi da kukan nata ya fara yi.

    Da kallo hafsat ta bisu har suka shige,tsinuwa da zagi kaka kala cikin zuciyarta akan widad din,sai data tabbatar sun shige din sannan ta matsa gaba inda abbas ke tsaye suna magana da rabi’u yaron gidan dake musu ‘yan aike aike da aikace aikace na filin gidan.

    Hannunsa zube a aljihun wandonsa har ta qaraso Inda yake tsayen,musayar murmushi sukayi,wanda murmushin dake kan fuskar hafsat din tasa ma’anar ta dabance

    “Sannu da qoqari madam” ya fadi har cikin ransa,don duk abinda je faruwa kan idanunsa ne yana gani,sai ta saki qaramin murmushi tana jin yadda zuciyarta keta mata ciwo

    “Yauwa sannu,amma kaima ya kamata ka shiga ka bata baki fa,kuka taketa yi,abun tausayi” ta fada tana canza yanayin fuskarta zuwa kalar tausayin.

    Da ido ya kalla sashen sannan ya maido kanta

    “Tunda kin rarrasheta aikin wakilceni” wani sanyi yadan sauka a ranta,ta juya idonta kadan

    “A’ah,ai matsayinka daban,inaga kaje din da kanka sai yafi” baice komai ba,sai ya kalla agogon hannunsa kawai sannan yace

    “Zan dan fita,inajin zan iya kaiwa magariba kafin na dawo,rabi’u zai kawo cefene komai da komai,ki duba abinda babu saiki gaya masa ya hado dashi” fuskar ta a wadace da fara’a,duk da sanda take ita daya ba haka takeyi ba,duk sanda yace za’a kawo cefene cikin bacin rai take,saboda tasan yana buqatar sauyin abinci kenan,zai kuma yita mata tsirfar kala kalar girki,tafi jin dadi idan cefanensu ya qare,zata girka abinda duk ranta yakeso babu wahalar da kai.

    Ita ta masa rakiya har bakin motarsa,ya shiga ya kunnata ya fice,ranta yayi mata dadi sosai,ganin ya share batun shiga sashenta

    “Wannan abun yana aiki,sai dan banzan wahala” ta fada a ranta,bata taba kawo zai fice bai shige ba,to amma auren soyayya ne kuwa hakan?,anya ba hadin hajiyar bane kamar yadda taketa jin qishin qishin tana qaryatawa?.

    Duk yadda latifa tayi kan widad tayi shuru amma abun ya faskara,yadda suke hanya suna ta cin kwalta har zuwa garin kano,haka ta lafe cikin kujerun ta ta dinga rera kuka,tun tana zaune tana aikin lallashi harta haqura ta zuba mata idanu,sallah kawai ta tashi tayi ta koma fa kwanta taci gaba da kukanta,koda latifan ta gama girkin rana wajen qarfe biyu da rabi na rana tayi mata maganar ta tashi taci qin tashi tayi,tayita lallabarta amma tayi funfurus,har akayi la’asar,ta sake lallabata amma taqi koda kallon abincin sai ruwan hawaye,bayan wasu mintuna ta gwada bata baki,saita tarar bacci yayi awon gaba da ita cikin kujerun

    “Gwara ma kiyi baccin kya samu salama,wanann kuka haka?” Ta fada tana jin tausayinta cikin ranta,saita samu dama ta shirya abincin dare mai rai da lafiya,tunda bata ga alamun girki daga wajen hafsat ba,tunda rana ma da jama’ar kano suka tafi bata sake jin duriyarta ba,tana sanya ran a nan zaici abinci indai abun ya tafi kamar yadda yake a tsare a shari’a,don haka ta tsara abincin da kyau.

    Dab da sallar magariba widad din ta motsa kadan,sai ta tsaya cak tana qarewa falon kallo tana daga kwance,kwanaki biyun nan mantawa take ba’a gida take ba,duk sanda tayi bacci ta farka saita zata zata farka ne ta ganta a dakin ummu.

    Tuna komai da tayi cikin yinin yau sai ta fara tara sababbin hawaye,sannan ta miqe daga kwanciyar tana zuro qafafunta qasa,dai dai lokacin latifa ta fito daga daya dakin da ta zabi zama a ciki
    “ai gwara da kika tashi,kwanciyar tayi yawa” ta fada tana qarasowa inda take zaunen,sai kuma ta dubeta

    “Aah,kukan dai widad?,to kiyi haquri mana,tashi kiyi sallah kizo kici abinci” kamar jiran me tanka mata takeyi wasu sabbin hawayen suka fara sauka,da qyar latifa ta lallabata ta shiga bayinta ta dauro alwala tayi sallar,amma qememe taqi daukan abincin ko cokali daya taci,sai dan banzan kuka da takeyi,abinda ya daga hankalin latifa kenan,tayi lallashin duniya amma widad din taqiyin shuru,tana kuma tsoron kira mata ummu taje ta birkice mata fiye da yanzu,a haka suka zauna ta sakata gaba har aka idar da sallah isha’i.

    Koda ya dawo a masallaci ya tsaya,sai da aka gama sallar isha’i sannan ya qaraso gidan,yau din shi daya ne,shi yayi driving abinsa,ya tsaida motar a parking lot na gidan ya kashe motar ya fito.

    Tsayawa yayi yana duban sassan guda biyu,baisan yadda akeyi ba,baisan wanne zai shiga ba,tsahon wasu mintuna kafin ya zare hannayensa daga aljihu,ya soma takawa zuwa sassan hafsa,tunaninsa ya bashi ya fara da babba tukunna.

    Yana tura qofar falon muryar mimi ya fara ji,sallamarsa ta ja hankalinsu,suka watsar da kayan wasan dake hannunsu suka nufoshi a guje,kowacce na kiran

    “Daddy oyoyo” dukka su biyun ya hada ya rungume a jikinsa,yana kallon yadda sukayi fes dasu suka canza,da alama suna samun kulawa da tafi ta mahaifiyarsu

    “Yaushe Kuka dawo?” Ya fad yana barewa nawwara chocolate

    “Dazu anty maamaa ta dawo damu” dai dai sannan hafsat dake kitchen tana ta faman yadda zata hada masa abinci me kyau da zai janye hankalinsa ta fito.

    “Sannu da zuwa” ta fada tana goge hannuwanta a jikin zanin jikinta,ya kalli zanin,kayan jikinta ne tun na safe,ya kuma tabbatar bata sake wani wankan ba,ya dauka zaiga canji ko yaya ne,amma ba wani abu daya canza,hatta da falonta a birkice yake,har da sauran maqalallun dattin yinin bikin da tayi da ba’a gama tsaftacewa ba,duk da haka ya danne shima,yana kallon yadda itama taketa qoqarin danne komai,duk kuwa da irin mugun baqin kishinta

    “Yauwa madam,kun yini lafiya ya yara?” Ya fada yana kashe mata ido,saita dauke kai tana jin wani zafi a ranta,duk sanda ta tuna akwai wata cikin gidan fa wai itama matarsa ce,sai taji kamar ta shaqeshi

    “Lafiya qalau” ta bashi amsa a gajarce tana nufar kitchen din

    “Bari na kawo maka abinci” ajjiye nawwara ya fara qoqarin yi,shekaru kusan bakwai ta kasa haddace me dame yakeso idan ya dawo

    “Noo,zan fara zuwa nayi wanka tukunna,kin kunna min heater dinne?” Da zaiyiwu ashar ya kamata ta qunduma,saidai tasan ko giyar wake tasha wannan shine kuskure mafi muni da zata aikata,me yakeson maidata?, baiwa?,wai da wanne ma zata ji?,da hidimar yara ko da ta kitchen ko kuma da tasa hidimar?

    “Ban kunna ba,banma shiga sashen ba yau kwata kwata” kai yadan kada,yanzun kenan yadda ya baro sashen haka zai koma ya tadda shi,babu shara ba komai,duk da cewa dama ya saba da hakan,sai ya sake kada kansa yana nufar qofa

    “Okay,ki shirya abincin,sai ki shiga ki kira qanwar taki kafin na fito” da harara ta bishi,sai taja tsaki bayan ya fice

    “To ubana,ga jaka tayi mata girki ko?” Buguzum buguzum tayi hanyar kitchen din tana mita hade da bala’i kamar zata fashe

    “Ni gaskiya na gaji,na gaji wallahi,dama hausawa sunce abun aro baya rufe katara,wannan attitude din dana ara ya fara isata,pretending din ya fara kaini bango” ta qarashe fada tana jan kwanon data gama hada coleslaw,bata kula ba santsi yasa ya subuce a hannunta ya fadi qasa ya tarwatse,abinda ke ciki yayi nasa guri

    “Innalillahi,kai jama’a” ta fada qwalla na cika idanunta,sai gasu kuwa sun gangaro,ta duqa a wajen ta fashe da kuka,dukka yaran da suka biyota sai sukayi carko carko suna kallonta.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/2, 5:28 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 24

    Arubuce Ta Ke 24

    Page 24

    Kai kawo ya dinga yi cikin dakin,ransa na masa suya,me zaiyi ya huce takaicin hafsa?,yasan dai tabbas bazai qyaleta ba,anzo gabar da dole ya koya mata lesson kamar yadda yasha fada.

    Idanunsa suka sauka akan wayarsa,sai ya jawota da hanzari ya fara kiran layin hajiya,bugu biyu ta daga

    “Abbas ya akayi?” Ta tambayeshi da mamaki,ganin bai wani jima da barin gidan ba,qoqarin dai daita muryarsa yayi,don bayason ta fuskanci akwai wata matsala ne ta tashi hankalinta

    “Lafiya lau hajiya,cewa nayi zai yiwu a gabatar da neman auren cikin satin nan?” Kai ta jinjina cike da mamaki,anya babu walakin goro a miya?

    “Eh to,saidai na nema kawunnanka naji”

    “Idan zaiyuwu hajiya kawai ayi,na shirya” tana saurin gano damuwa da kuma fushinsa,yadda yayi maganar a jikinta taji akwai damuwa,amma zata tambayeshi a hankali

    “Shikenan,zanyi magana dasu,duk yadda ake ciki zaka ji”

    “To hajiya na gode,gobe da yamma zan wuce,zan shigo ta nan kafin na wuce din in sha Allah”

    “To ba damuwa,Allah yakai mana rai” daga haka sukayi sallama.

    Cikin mamaki take sauke wayar,saidai kuma ta samu kanta da sakin murmushi tare da fadin

    “Alhamdulillah” zuciyarta na gaya mata wataqila akwai alkhairi mai tarin yawa a abun,shi yasa Allah ya kawo komai a kurkusa haka ya sauqaqe matsala da damuwa.

    “Tofa,ta samu kenan hajiya?” Faccalarta da suke tare a falon,ita da yayar abbas din mai suna mabruka suna hira ta fadi,wayar ta ajjiye gefe tana cewa

    “Aure ne ya tasowa danki” da mamaki ta kalleta

    “D’ana,wa kenan?”

    “Abbas mana” kallonta sukayi gaba daya cike da mamaki,abbas din da kowa yasan dabi’arsa,mutumin da ko auren hafsa dinma kamar bazaiyi ba saboda tsabar I don’t care manner irin nashi da rashin baiwa lamarin soyayya muhimmanci?

    “Abbas din yaushe har yaga wata yanaso?” Faccalar tata da yara ke kira da gwaggwo fanteka ta fada

    “Tayani tambaya gwaggwo,na dauka ma bashir ko yaya sa’id zata ce,ko kuma Sunusi” kai ta girgiza tana murmushi

    “Abbas ne” kai suka jinjina su duka,mabruka tace

    “Ya cancanci ya qara aure dama tuni,wannan rayuwar da akeyi a gidansa bata da ma’ana sam,naga qoqarinsa ma,ganin baida wannan ra’ayin yasa ban taba tuntubarshi da maganar ba,ga ‘yammata nan cike a dangi,ya zabi wata ya qara ko zai samu sassauci,haba abun na hafsa yayi yawa” kai gwaggwo ta gyada itama

    “Gaskiya dai,yammata kyawawa fa gasunan masu hankali,ita wannan din a ina ya samota?,cikin yan uwansa ne?,amma banji batun ba sai yanzu?” Gwaggwo ta fada cike da son jin wace?,tana fata ya zamana cikin yaranta ne,duk da tasan zaiyi wuya,don inda cikin nasu ne da tuni ta fahimta,amma rabonta da abbas a gidan tun sanda tayi wata rashin lafiya ya shiga ya dubata

    “Ba cikin dangi bane,wata yarinya ce diya take a wajen muhsin abokinsa,dukkanku ai nasan kunsan muhsin?” Ta fada tana kallon fuskokinsu, gwaggwo da tuni fuskarta ta sauya tace

    “Qwarai kuwa” sai hajiya ta dora

    “Yarinya ce ma,amma nutsuwarta da hankalinta ya bani abbas din xai samu nutsuwa a gidansa,zai kuma ce ayi ayi,a bari a bari”

    “Turqashi” gwaggo fanteka ta fada ba tare da tasan kalmar ta fita a bakinta ba,wani bacin rau na motsa mata,yaron da dukkan alamu suke nuna zaiyi arziqi cikin dangin nasu,taketa qulafucin ganin ta samu ta jogana diyarta,lokaci daya hajiyan ta wargaza fatanta da burinta ta dauko wata bare ta maqala masa?.

    “Banda abun hajiya ruqayya,gida bata qoshi ba za’a baiwa dawa?,gamu da yaran yammata duka sun tasa saiki dauko bare ki bashi?,duk da itama hafsan akwai alaqa amma ai baiyi alaqar sa da yaran kawunnansa ba ko?” Gwaggo fanteka ta fada tana dora murmushin yaqe kan fuskarta

    “Gaskiya nima wannan tunanin yazo min” mabruka ta fada tana gyada kai, murmushi hajiya tayi

    “Auren dangantakar ai bai amfana komai ba gwaggwo,gwara a gwada baren ko a nan za’a dace ko?” Kai ta kawar tana tabe baki,bacin rai iya bacin rai yana cikata,wanann babbar dama haka za’ayi asararta?,suna ji suna gani

    “Da dai kin sake tunani gaskiya,duk yadda bare yake da dadi ai baikai dadin dan uwa ba”

    “Hakane” ta amsa mata a taqaice,tasan halin gwaggwon da mita,ita kuma dama can bamaison dogon magana bace,gwggwon na daya daga cikin masu kushe aikin dan sanda a sanda abbas ya samu aikin

    “Dan sanda?,me na sama yaci ballantana ya baiwa na qasa?,kayan cin hanci da rashawa” wannan shine abinda taji tana fada sanda hajiyan taje gidan da kanta tana shaidawa kawunsa mijin gwaggwon cewa ya samu aikin,tun daga matakin constable saai yanzun da daukaka ta fara zuwa masa ake kwadayin hada zuri’a da ita?,duk haqurinta da kawaicinta ita din ba mahaukaciya bace.

    Hirar duka saita fita akan gwaggwo fanteka ta zama mara dadi,don haka bata jima ba ta miqe ta yiwa hajiyan sallama ta fice.

    *WIDAD*

    Sanda ta bude ido ta ganta qofar gidansu sai taga kamar wasa,kasa jira tayi drivern da uncle muhsin ya daukar mata shata har qofar gida ya fidda mata kayanta,ta sauka daga nan ta nufi gate din da gudu gudunta,ji take kamar zata bude ido ta ganta ta koma bauchi.

    Cikin sa’a kuwa tana buda gate din ummun ta hanga tsaye a farfajiyar gidan ita da kawunnanta,sanye da atamfa da kuma hijabi,hannunta riqe da carbi,da alama salla ta idar suka tasota,akwai zancan da sukeyi.

    “Ummunaaa” ta fada da qarfi sannan ta kwasa da gudunta,ta isa gabanta ta fada jikinta tana ruqungumeta.

    Sai da ummun tayi taga taga zata fadi kawu ya tareta

    “Ashsha,ashsha,zata kada mana uwa” sai ta saki dariya tana sakin ummun suka miqe tsaye dai dai ummun itama tana dariya idanunta akan fuskar widad din,kamar fa shekara bata ganta ba.

    “Ke dawa?,yanzu kike tafe?” Ummu ta fadi tana dubanta

    “Ni kadai yanzu yanzu na qaraso”

    “Iyeee,muhsin din barmin ke yayi ke kadai kika kamo hanya?,tabdijan ,zamu hadu dashi kuwa”kafin ta qarashe drivern uncle muhsin din ya shigo da jakankunanta,suka gaisa yace zai koma,ummu tace a’ah sai yaci abinci,suka wuce ciki ita da widad tace taje ta kawo masa abincin,su kawu kuma suka fice bayan an bashi wajen zama anan farfajiyar gidan.

    Zuwa wani lokaci sai ga sassan ummu ya dan cika da sauran yaran gidan,su Aafiya rafi’ah fareesa da sauran wadanda suke shekaru kusan daya,sun baibayeta tana ta basu labarin bauchi.

    “Kano fa tafi dadi Allah” ta fada daga qarshe tana yamutsa fuska,dariya sukayi mata

    “Daga baya kenan,bayan kin gama kwanakinki” dariya tayi tana cewa

    “Da gaske nake muku,bari kuga” sai ta wuce daki ta janyo jakarta,ta fidda jakar ledar kayan makeup din da hajjaa ta damqa mata tace inji abbas,tunda ta taho kayan suke daukan hankalinta,komai na ciki ya burgeta ya kuma yi mata kyau,harda takalmi me tsini irin nasu basma da aka sako musu a lefe,tayita maitar takalmin sai basman ta jefa mata harara

    “Ba baki zanyi bafa,kiyi addu’a kema Allah ya kawo me siya miki” fushi tayi tana tura baki tabar gurin,sai gashi ta sameshi sama ta ka,bayan shi harda mayafi da hand bag qarama mai matuqar kyau,a nan ta zazzage musu kayan,suka dinga santinsu,daga baya ta daukarwa kowa wani abun daga cikin kayan kwalliyar.

    *************

    Kwana biyu a tsakani tana kitchen tana cin abinci suna hira da latifa,ta ajjiye warmer din data zuba abincin alhaji a ciki tana cewa

    “Ashe dan bauchi kika samo mana kuma” kallonta tayi tana ci gaba da cin abincinta,don ita har ga Alla ma ta manta da wani batu

    “Dan bauchi?”

    “Eh mana,naji abba mahmudu yazo suna zancan da alhaji ai”

    “Auho,wai abokin uncle muhsin”

    “Shifa” sai widad din tayi shuru kawai,don batasan me zatace ba,itadai ba sanin soyayya tayi ba bare ta tantance tana sonsa ko bata sonshi,kawai dai taji bata damu ba bata takura ba kamar sands ake zancan mahfood da ma’aruf.

    Sosai ummu ta dinga juya zancan bayan da mahaifin widad ya zartar da cewa an bawa abbas widad don,amma bata taba kawo cewa zasu nema aurenta a nan kusa ba haka,taji abun sosai a ranta,a yadda ta lura kuma shi mahmudu din a shirye yake da auren diyarsa,tasan watarana komai tsahon zaman da zatayi da qaunar da takewa widad su rabu dole ta aurar da ita,so a yanzun bataga nata hurumin da zata hanashi bada auren ‘yarsa ba,tunda dukkan bincike da shaidu sun tabbatar da nagartar me neman auren kamar yadda musulunci yayi umarni.

    Amma babban abun shine,kishiya daya tabbata widad din nada ita,ta yaya yarinya kamar widad din zata iya fuskantar abu me wahala da zafi kamar kishi?,bata sani ba,saidai tana fatan ko mai zaizo da sauqi fiye da yadda suke zata.

    Kwanan widad din biyu da dawowa maneman auren abbas din suka iso kano qarqashin jagorancin uncle muhsin,sunga karamci irin na kanawa,duk da cewa su din ba kanawa bane usul,amma tunda an haifi ‘ya’ya da jikokinta suna amsa wannan sunan.

    Cikin girma da mutunci gami da karamci suka gabatar da neman auren abbas ga widad din,aka sake jaddada basu,suka nema alfarmar karbar kudin aurensu harda sadaki,take alhaji yasa aka karba komai,suka karbi roqonsu na daurin auren sati mai zuwa.

    A ranar zancan auren widad ya fara yawo a dangi,abinka da family house,kowa idan yaji zai gayawa na kusa dashi,bugu da qari widad din ‘yar gatan ummu,mai masoya da kuma tarin abokan adawa.

    “Uhmmm,sunje sun zaba mata miji ba,ai dama wannan yadda akaci buri a kanta nasan sai me abun hannu zasu bata” wannan shine abinda wasu suka dinga fada,musamman da suka samu labarin muqamin da ya riqe a gwamnatin bauchin,da kuma wanda yake kai yanzu,gani sukeyi uncle muhsin ya dauketa ne dama kawai don ya aikata hakan.

    Ita kuwa sam batasan ma me akeyi ba,don har ta koma islamiyya,wadda tun tafiyarta qaunar makarantar bata bar ranta ba,sanda ta koma din sai ta samu basu wani tsere mata ba,tunda ta dora daga inda ta tsaya a bauchin.

    **********Karfe shida saura na yamma suka iso gidan ita da Aafiya rafi’ah da widad din,bayan tasowarsu daga islamiyyar,gab da zasu shiga gate din gidan Aafiya ta kalleta

    “Nifa zancan bikinki naji ummanmu tana yi,wai nan da sati daya”

    “Nifa abinda yake hadani dake tsokanarki” widad ta fada tana watsa ragowar alawar data siya cikin jakarta

    “Wallahi nima haka naji,don kafin mu tafi islamiyya naji umma tana waya a karbo atamfofi akai mana wajen mai dinki”

    “Mahaukata,sai kuyi ai” widad din ta fada tana yin gaba abinta tana dan waqenta.

    Bata ma tsayasu ba ta zarce sassan ummu abinta,tana sallama a falon ta soma zare hijabinta daya dameta,gashinta mai santsi ya ware,don dama ita din ba ma’abociyar saka dankwali bace,tafi sanya hula,itama ba ko da yaushe ba,sai ummu tayita fama da ita.

    Ummu da anty halima ne a falon

    “Anty halima ina nabiha?,kikace idan zaki sake zuwa tare zaku zo?” Widad ta fada tana barewa alewan ta tura bakin yaron anty halima dake kan cinyarta.

    Da kallo anty halima ta bita,tana dan jin tausayin widad din

    “Oh ni sadiya?,wannan wacce irin amarya ce ummu?” Dan murmushi ummun tayi,ita kanta tausayin widad din takeji,har yanzu ma bata zauna tayi magana cikakkiya da ita ba kan auren da tasan widad din batasan meye shi ba,bata kuma da labari cikakke akan yinsa.

    “Au ina yini?” Ta fada tana dariya bayan ta tuna nata gaidata ba,ba kuma tare data maida hankali ga maganarta ta farko ba

    “Lafiya lau widad,nabiha zasuzo,sai satin biki in sha Allah”

    “Allah ya kaimu” ta fada tana gyada kai hankalinta kwance,saita dubi ummu a shagwabe

    “Yunwa wlh nakeji ummu,dazu banci abinci ba Aafiya ta matsamin na taho mu tafi”

    “ki wuce latifa tana kitchen ki karba”

    “Tom” ta fadi tana wurga jakarta ta zarce kitchen din,yayin da dukka su biyun suka bita da kallo.

    Ummu ce ta fara dauke idanunta tana sakin ajiyar zuciya,anty halima tace tana dariya

    “Wai,wa yaga widad amarya” kai ummu ta kada

    “Tausayinta nakeji halima,ban taba kawo rabuwarmu a nan kusa ba” tabe baki anty haliman tayi

    “Kaji ummu,to mu da aka rabu damu din tun bamu kai haka ba me ya samemu?,gamu ragal damu?,itama zata ware ne kamar kowacce mace” kai ummu ta girgiza

    “Ba zaki gane ba halima,dukkanku kunfi widad wayo sanda aka muku aure,kawai don lokaci yayi ne ba yadda zanyi,amma ban shirya kaita wani uwa duniya ba”

    “Tunda dai babanta ya bada ita,alhaji kuma ya goyi baya dole saidai ayi haquri,yanzu kawai yadda za’a tattarata akaita bata iya komai ba,kunbi duk kun shagwabata,bata iya komai ba,komai yi mata akeyi” anty halima ta fada tana mele baki,ta rasa wanne irin so ummun takewa widad?,tamkar ma ba mahaifin widad din ta haifa ba,ita ta haifa,ko ita diyarta ta cikinta bata jin tana mata son da takewa widad din.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

     

    *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 27

    Arubuce Ta Ke 27

    Page 27

    Washegari yaran da suka tashi suka gansu wajen babansu sam basu damu ba,murna suka dinga yi abinsu,shi ya dinga tiri tiri dasu,ya shiga kitchen da kansa ya hada musu breakfast mai kyau,da yake ya iya abubuwa masu sauqi hakanan cikin abinci,saboda yanayin karatun da yayi.

    Sunci kuwa sosai kamar ba gobe,sai ya zauna yana kallonsu,zuciyarsa na gaya masa basa samun kamarsa,duk da store dinsa cike yake da cima kala kala,wani abun har ya rube ko ya lalace batayi amfani dashi ba bata kuma bayar ba saboda baqar rowa,yayi nasihar yayi nasihar har ya koma fadan amma a banza,mutum ne shi mai bajintar wadata iyali tun samunsa baikai haka ba,tun rank dinsa bai kai haka ba,baya son iyalinsa suga wani abu a wani gidan da babu shi cikin gidansa,to amma kusan duk wannan qoqarin nasa a yawancin lokuta a banza yake tashi.

    Ruwan tea kawai ya iya sha bayan ya tabbatar sun qoshi,duk ransa a jagule in yake,saboda har sanann hafsat bata bude qofarta ba,yayi knocking yayi har ya gaji,ya ajjiye mata nata breakfast din bakin qofa amma baiga ta bude ta dauka ba.

    Bayan duka sun gama ya maida kwanukan kitchen,ya zage kamar yadda ya saba yawa yawan lokutta ya soma gyaran sassan nasa,yayi masa qal yadda yakeso,ya canza bedsheet da sauransu,ya hada duk abinda ya cire da kayansu mimi da yayi musu wanka cikin laundry basket,ya aje inda mai wankinsu zai dauka,sannan shima ya shirya kansa sannan suka dawo falon hafsat din,koda wai zataji motsinsu ta bude qofar.

    Saidai har suka gama zamansu ba ita babu dalilinta,a taqaice dai har zuwa azahar bata fito ba,yanason fita masallaci sallah amma kuma bazaiyiwu yabar yaran su biyu cikin gidan ba,don ita mimi din ma ba wani cikakken hankali ne da ita ba,dole ya hada kansu suka wuce sassansa,acan yayi sallar,sai la’asar daya dawo dora musu abinci yaga babu plate din daya ajema hafsat din,da alama yunwa ta korota,ta bude qofa ta dauka kenan,sai ya saki qaramin murmushi ya wuce kitchen din.

    Har dare suka kwanta babu wanda yaga qyallinta,a taqaice dai washegari kusan abinda aka maimaita kenan,don haka a kwana na ukun ya shirya yaran da kayansu ya wuce gidan hajiya dasu.

    Kallon farko data masa tasan hatsaniya ke tashi a gidan,ta kuma san bata rasa nasaba da batun aurensa,bata matsa da jin ba’asin kawo yaran ba,saboda tasan shi da zurfin ciki,zaiyi wahala ma ya iya zama yana fadin cikinsa,ta daiyi murna da zuwan nasu,don ba zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ta faru ba.

    Ya jima a gidan,sai yammaci sannan ya wuce,a sannan tuni nawwara tayi bacci a jikinta,ta baiwa muneera ta kwantar da ita,sai data dawo ta zauna gefan hajiyan

    “Hajiya da alama anty hafsat fa……”

    “Na sani muneera” hajiyan ta katseta,saita rausayar da kai

    “Shima uncle,ya haqura kawai hajiya suyi zamansu mana,irin wannan babu dadi fa don Allah” kallonta hajiya tayi,batasan ko taji abinda uwayenta ke fada ba,har mamaki suke bata yadda suketa goyon bayan hafsat akan auren nan,wanda tasan tsabar son zuciya ne,amma babu wanda baisan halinta ba da dabi’arta,idan sunce basusan yadda abbas yake samun careless daga wajenta ba wannan kam ba zata musa ba,don babu da wanda yake zancan,amma kuma sauran dabi’unta da abbas din ya dinga yaqi ta gyara fa?,ita hajiyan tasna wasu,saboda takan bashi shawari idan ta fuskanci yana cikin damuwa ne

    “Ke yarinya ce,ba zaki fahimta ba,sannan keba namiji bace,nan ma ba zaki gane komai ba” amsar da hajiyan ta bata kenan,sai tace

    “K’nnnn,ai shikenan” base on her experience tayi maganar,saboda taga halin da mamanta ta shiga sanda babanta yace zaiyi mata kishiya,a sannan hajiyan ce ta shiga batun(muneera ‘yar dan hajiyan ce),duk da.bai fasa ba anyi,amma abubuwan da sauqi,to amma yanzun hajiyan da kanta takeson ayima anty hafsat din?.

    Yayi tunanin zata kaishi qara wajen hajiya ko daya daga cikin yayunsa maza kamar yadda ta saba a duk sanda wani rikici data kasa jurewa ya hadasu,amma sai yaji shuru batayi ba,bazai iya tuna rana daya rak da ya kai qarar hafsat din ga danginta ba,duk da tarin matsaloli da laifukanta,shi wanann ba dabi’arsa bace kwata kwata.

    Kwanaki biyar hafsat din tana a haka,cikon kwana na biyar din Allah ya jeho qanwar mamanta ita da naty ummee,matar data jima rabonta da gidan,yanzun ma.suna sukazo ta bayan layin,anty ummee ta roqeta su biyo.

    Yana farfajiyar gidan shi kadai yana duba jarida,suka gaisa dashi suka wuce ciki,ba jimawa anty ummeee ta dawo

    “Don Allah yallabai ka duba mana,hafsatun tana ciki kuwa?” Jaridar ya ajjiye ya miqe tsaye yana gyara shirt din jikinsa,yasan tana ciki,kawai taqi budewa ne tana zaton shine yake bugun,kuma a yau ya yanke zai balle qofar zuwa dare muddin bata bude ba,sai ya gewaye anty ummin yayin cikin gidan,ta bishi da kallo tana jaddada miskilancin sa,har yanzu yana nan dai ba abinda ya sauya.

    “Ki bude qofar, ummee ce” ya gaya mata kai tsaye,bai qara minti guda ba sai ga motsinta,ta murza key dun data sawa dakin ta bude.

    Wani irin scent ne mara dadi ke fitowa daga dakin,saboda qarancin iska me kyau,duk da akwai ac da fanka ta cikin dakin,amma baya zaton tana kunnasu,jikinta tun kayan daya dawo daga kaduna ya sameta dasu ne,da alama har wanka ta yiwa yajin aiki,ta nan inda yake tsaye yana iya jin sauyawar yanayin jikinta,sai ganshin kanta dake cuccure waje daya da alama bata tajeshi,fuskarta gaba daya ta kumbure,kamanninta sun dan jirkita.

    Harara ta watsa masa sannan taja tsaki,tsakin da yakai har kunnen anty uwani dake falonta,tadan kama baki tanason tabbatar daga inda tsakin ya fito.

    Ya tsani tsaki a duniya,ta kuma san hakan,shi yasa ta bishi dashi,ko zata samu ta fanshe bacin rai da quntata rayuwarta da yayi kaso daya cikin dubu na abinda takejin yayi mata.

    Bacin ransa ya daure,ya juya yana barin wajen,saita biyo bayansa a hankali har ya fita a falon,ita kuma ta qaraso ciki,suna hada idanu ta zube a nan ta saki kuka,ciwon dake danqare a ranta ya motsa mata,don a kwanakin ita daya ke fama da baqincikinta cikin daki,kwata kwata basirar ta gayawa wani bata zo mata ba,hasalima wayar tana kashe tun ranar,saboda abbas din ta kashe,bataso yayi kiranta ma.

    “subhanallahi meye haka hafsatu?” Anty uwani ta fada cikin firgici tana dago hafsat din,sai ta dan dauke kanta kadan saboda abinda ke tashi a jikin hafsat din,ta jata ta zaunar kan kujera sannan ta zauna dan nesa kasan da ita

    “Lafiyarki kuwa?” Anty ummee itama ta jefa mata tambayar tana kallonta,cikin muryar kuka kamar wadda akace wa’adinta ya qarato ta soma magana

    “Na shiga uku na lalace anty ummee,anty uwani wallahi mutuwa zanyi,abbas ne yace zai qara aure” ta qarasa fada tana rushewa da kuka,haushi da takaici ya qume anty uwani,yadda taga hafsat din ta aza hannu aka ta zauna dirshan a wajen tana musu irin wannan kukan na tashin hankali

    “Mutuwa fa kike fada hafsatu,kinsan mutuwar kuwa?” Anty uwani ta fada tana harararta

    “Sai an bita a hankali ai anty uwani…..sannu yi haquri tashi ki daina kukan” anty ummee ta fada yana dagota daga zamewar da tayi daga kan kujerar.

    Da kallon takaici anty uwani ta bisu su duka,ta da jin labarin abinda hafsatun keyi a gidanta,qazanta baqar rowa,ga rashin iya mu’amala da mutane,kuma ko a yanzun ta sake shaida tabbatar qazantarta,saboda yadda jikinta yake tashi ba kowa ne zai juri xama kusa da ita ba,da alama kwana biyar din kenan batayi wanka ba.

    Tana jinta sanda take rattabowa ummee labarin yadda komai yake wakana,tasani wanda suka fita ma sun gaya mata ba daukan shawara takeyi ba,ko a yanzun ma tasan idan tace zata gaya matan bata baki ne,don haka sai ta miqe

    “Kin gama ko na wuce kya taho?” Dubanta anty ummee tayi

    “Aah ki bari mu wuce tare mana”

    “Um um,yi zamanki,nikam ina da uzuri,saikin taho,hafsatu sai a qara haquri,ki duba dukka iya kurekurenki da abubuwan da kikasan bayaso ki gyara tun yanzu,Allah ya bada haquri” badon tasan anty uwanin bata da wasa ba,bata kuma daukan wargi da ashar zata maka mata,amma hakanan ta hadiye bacin ranta tace mata ta gaida gida da shaqaqqiyar muryarta data ci uban kuka.

    “Yanzu me kika yanke ke?” Anty ummee ta fada bayan ta dawo daga raka anty uwani,ragowar hawayen dake fuskarta ta share,tana jin gaba daya rayuwarta ta juya mata baya cikin kwanakin nan

    “Babu wata shawara ko dabara da nake da ita,kawai dai abinda na sani,koda tsiya ko da bala’i wallahi bazan bar wata mace ta rabi abbas ba,bazan iya zura ido ina raye ba abbas ya auro wata mace da sunan matarsa ba” jinjina kai anty ummee tayi

    “Amma ina ganin wanann ba dabara bace,kwata kwata ragon azanci ne,kinfi kowa sanin halin mijinki,idan yace yes babu wanda ya isa yasashi yace no,tunda ya niyyata babu wanda zai hanashi…..”

    “Niko naci alwashin koda ta qarqashin qasa saina hana shi auren nan anty ummee” ta fada idanunta na sake kadawa suna kuma sake cika da hawaye.

    Ajiyar zuciya anty ummeen ta sauke,sannan tadan gyara zamanta

    “Niko sai nace wannan din ba hanya bace mai bullewa,face hanya mai wahala da kuma sanya kashe kudi,a matsayinki na mace,mai yasa ba zakiyi amfani da KISSARKI ba?” A hagunce hafsat din take kallon anty ummee,saboda bata fahimci me tafi nufi ba gaba daya,mafita kawai take nema,saboda haka tace

    “Kamar yaya kenan anty ummee???”

    **********Tun daga ranar bata sake kulle kanta ba,saidai kuma sabgarta takeyi kawai ba tare data shiga sha’aninsa ba,bai damu can can ba,don ko sanda suke shirin ma ba wani abu take dauke masa ko takeyi masa ba,kusan ya saba….fiye da rabin hidimominsa shikewa kansa,saidai ya dan samu nutsuwa,tunda aqalla bata sake tada wata fitina ba,har abun yaso ya bashi mamaki sosai.

    ********Karfe biyar na yamma tana kitchen tana hada abincin dare taji knocking,ta fito a kitchen din tana gyara daurin zaninta daketa kwancewa tun dazu,don bata daurin baya sai daurin gefe,a cewarta yana damunta ne.

    Tana bude qofar sukayi arangama da yaron gidan wanda ke musu aike aike,sai ya danja baya kadan cikin jin nauyi saboda ganinta babu mayafi

    “Madam oga ne yace a kawo,masu kayan gado ne da furnitures,zasu kwashe wadancan su saka sabbabi,yace muzo dasu suyi aikin” ta zuba masa ido ne taga zaiyin ko bazaiyi ba,duk da zancan kullum yana ranta dashi take kwana take kuma tashi,duk da ranta a bace yake matuqa har komai ma baya burgeta,to amma kuma tana son alqawaruran da yayi mata din.

    “Su bani minti goma ina zuwa” ta fada tana juyawa,ya rusuna cikin girmamawa ya amsa mata da to.

    Dakinta ta koma ta fara kwashe abubuwanta masu muhimmanci waje daya,aikin nada dan yawa,don sai ta shiga dakinsu nawwara ma ta hada nasu kayan,tanason ta samu dan tayi,to amma tasan a dai dai wannan lokacin koda tayi waya gida babu lallai a samu me zuwa ya tayata,saboda kowa yasan halinta da dna banzan rowa,saidai kayi mata wahala,dole ta koma kitchen ta kashe gas din girkin,dama ba wani girkin arziqi ta aza ba,tafi sati ma basa abincin saidai yayo musu takeaway,ita kuma ta nema wani abun taci.

    Sai da ta kusa awa guda sannan ta gama,duk ya hada gumi saboda ba maison aiki bace,sanann ta koma kitchen tana maida numfashi,su kuma suka shiga aikin gyara dakunan.

    Ana idar da sallar magariba suka gama kafa kayan gadon,da yake ba mutum daya ko biyu bane,sun kusa su biyar,suna fidda wadancan kayan ta fito

    “Su kuma wadan nan za’a kaisu?” Ta tambayi shazali yaran gidan

    “Yace a fiddasu compound a ajjiyesu” kai ta kada

    “Ka bawa masu kayan gadon idan suna siyan second hand,tunda wadan nan ba wani dadewa sukayi ba,kuyi ciniki su baka kudin ka kawomin” kamar yace ba haka oga yace ayi ba,to amma sai yaga meye nasa?,tunda kayanta ne,kuma matarsa ce?,don haka ya amsa mata da to yana ficewa,ita kuma ta juya ta shige dakunan tana jan tsaki a ranta,kudi takeso ta tara mai yawa daga jikinsa,ko banza ta rage wani radadin.

    Sosai dakunan sukayi mata kyau,dukka ya zaba favourite colors dinta ne,dakunan sun canza gwanin sha’awa,duk da ranta a bace yake amma sai data danji ta sauka kadan.

    Ba’a rufa awa ba kuwa ya dawo mata da kudin kayan cas,ta karba ta soke abinta taci gaba da sabgarta hankali kwance,ranar baya nan,yaje azare,zai kuma kwana sai washegari zai dawo,don haka hankalinta kwance ta gama tsara abinda zatayi da kudin,koda kuwa ya dawo ya tambayi yadda akayi da kayan,barema tasan halinsa,zaiyi wuya ya tambaya din,don bashi da wannan,amma koda yana da niyyar ma ta shirya abin fada masa.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[2/22, 2:45 PM] halimatuabidah: *H U G U M A*
    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 22

    Arubuce Ta Ke 22

    Page 22

    Nujood da widad dake tahowa yake nuna masa,baiji abinda yace ba,yadai ci gaba da kallonsu,suna sarqafe da hannun juna,widad din tana jin gabanta na faduwa ne gami da sanyin jiki haka kawai,yayin da nujood ke tsokanarta,har ta daga qafa zata dan bi nujood din da gudu sai kuma ta tuna taga qofar setting room din a bude,wannan yasa takai idanunta ciki,bata hango wadanda ke ciki tar,saidai ta tabbatar suna iya kallonsu.

    Da sallama suka shigo,suraj ne ya amsa musu fuskarsa da murmushi,nujood din na riqe da hannun widad suka qarasa cikin falon.

    Nujood dince ta fara gaida abbas,fuskarsa kadaram kadaham ya amsa,already ta san halinsa,bai fiya fara’a ba don haka bata damu ba,ta maida akalar gaisuwar ta ga suraj

    “Lafiya lau,ya karatu?” Ya amsa mata cikin fara’a da murmushi

    “Alhmdlh” tuna abinda hajjaa tace da ita ya sanyata miqewa

    “Saikin shigo” ta fada tana duban widad cikin salo na tsokana,wanda iya ita da ita ne kawai zasu fahimta.

    Maganar nujood din taja hankalin abbas harma da suraj,tunani iri daya ya darsu a ransu lokaci guda,kowanne dubanta yake,abinda ya sanyata taji kamar an aza mata wani nauyi,gaba daya ta jita kamar a daure,kallon da suke mata yana neman daburtata,tana takure a gefe tsakanin kujeru tana wasa da gefan mayafinta,saita nannadeshi ta wareshi,suraj ya fuskanci hakan,don haka yayi gyaran murya,cikin murmushi kuma yace

    “Barka da fitowa ‘yammata” muryar suraj din saita ankarar da ita mantuwar da tayi bata gaidasu ba,don haka ta daga kai in ta fara gaida suraj din,cikin sakewa da fara’a da kuma kulawa ya amsa mata,sa’annan ta koma ga abbas,idanu saika hada,take taji ya fiya kwarjini da yawa,tunda suka shigo kuma ta karanci fuskarsa bashi da yawan fara’a,sannan koda bata dade a wajen ba alamu su nuna yana da yawan shuru shuru,don ko daya bataji muryarsa ba tun bayan daya amsa gaisuwar nujood

    “Ina yini” ta fada tana kaida kanta,sai daya lumshe idanunsa ya bude sannan ya amsa mata,’yammatan daya fada sai abbas yaji kamar gatse ne yake masa,zaqin muryarta kuma me cike da zallar quruciya na zaga kwanyarsa

    “Kada dai ya kasance ita hajiya ta zaba masa?,anya kuwa?” Kamar suraj yasan tambayar dake yawo a ransa kenan,sai ya tsinceshi yana cewa

    “Allah yasa kece wadda hajiya tace muzo mu gani?” Kanta a qasa kawai ta gyada kanta,amsar data tilastawa abbas maida bayansa jikin kujera ya jinginar kawai idanunsa a lumshe.

    Yana iya jin yadda suraj keta janta da hira,tana amsa masa da qyar,muryarta cakude da kunya da kuma tsoro hadi da rashin sabo,tunda suraj din ya kalleshi ya karanci yanayinsa,wannan yasa ya karbe hirar abinsa ba tare daya sanyoshi ba,kamar ma shi abbas din ya yiwa rakiya.

    Jinnta take a takure kota ina,musaman idan ta waiwaya inda abbas din ke zaune abinsa ya sanya musu kunne

    “Wannan abokin nasa,ko me yasa yazo dashi?” Abinda tayita fada kenan a ranta

    “To widad mu zamu wuce,sai kuma wani jiqon?” Suraj ya fada yana duba agogonsa,maganar data yiwa widad din mugun dadi,don kafin ma ya miqe ita ta miqe tana cewa

    “Ku gaida gida” saita kada kai abinta tayi hanyar ficewa,a lokacinne abbas ya bude manyan idanunsa yana binta da kallo

    “Minti daya mana malama widad” suraj ya fada yana miqewa da ledar siyayyarsa a hannu yana yiwa abbas sign din ya tashi mana,sai ya kauda kai kamar bai gani ba,don haka ya taka ya isa inda take tsaye ya miqa mata ledar,cikin ransa yana fadin siyayyar kuwa ta dace da ita

    “Ga wannan ko babu yawa” sai data dora idanunta kan abbas dake zaune daga bayan suraj din taga ita yake kalla sannan ta saka hannu ta karba gabanta na faduwa

    “Na gode” ta fada tana ficewa a dakin da hanzari gabanta na wani irin faduwa.

    Da baya suraj ya dawo a hankali yana hararar abbas

    “Duk alamar da nake maka ka tashi ka miqa mata don ta fuskanci ma waye abbas din a cikinmu amma kayi banza dani?”

    “Wai kanason kacemin wajenta mukazo zancan?” Abbas din yayi tambayar hankalinsa kwance,sai haushi ya kama suraj,ya watsa masa harara

    “Ban sani ba,next time dama idan zaka zo kada ka sake ka kirani,idan kazo kai kadai zaka gane wajen wa kazo din,tashi mu tafi,ka barni ni kadai sai zuba nake”.

    Cikin mota gaba daya kansa ya kwance,me yasa hajiya ta dauko masa wannan?,ta yaya zai samu sauqi ko kulawa daga wajenta,kansa kada,gaskiya bazai iya sake zuwa zance ba,yaje yace mata me?.

    Yana jin suraj yana ta hirarsa amma bai saka baki ba,saboda gaba daya tunaninsa na ata wani waje,suffarta da kamanninta yaketa qoqarin maidowa idanunsa ya hadasu waje daya,babu qarya…..tana da kyau,ita din kyakkyawace ta gasken gaske,to ko kyawun hajiya ta gani?,sai ya sake girgiza kansa,yasan hajiyan,tasan abun qwarai sarai,bai gano me ta hango masa ba,amma ya tabbatar akwai abinda ta hanga din.

    Saida suraj ya ajjiyeshi a gida sannan shima ya wuce,abbas din ya masa ban gajiya da godiya

    “Ai babu wannan tsakaninmu,kawai dai next time ka tafi kai kadai,saboda ka samu ku fahimci juna sosai, she’s too young,dole sai kana janta a jiki da dabaru sannan zata saki jiki da kai,amma kuma ina me tabbatar maka indai aka samu shaquwa sabo da kusanci tsakaninka da ita,ina me tabbatar maka…..ina sake fadi ina mai tabbatar maka anan zaka fahimci komai basai an gaya maka ba” abinda suraj ya gaya masa kenan,wanda ya tsaya masa a rai,ya kasa fahimta kuma,da wannan maganar ya kwanta.

    Ita kuwa widad tana fitowa ta qara da dan gudu gudu,wani irin tsoro takeji da faduwar gaba sosai,don sai data tsaya a hanya tadan saisaita numfashinta tana dafe qirjinta da hannu,batasan me yasa batason wancan abokin nasa yana kallonta ba,to amma itafa wallahi mai wanna zubar maganar indai shine wanda uncle muhsin ya turo mata baiyi mata ba sam,saita tabe baki tana buda ledar daya bata,murmushi ya subuce mata da taga masoyiyar wato chocolate,saita zabura tayi cikin gidan tana qwalawa nujood kira.

    “Iyyeee,yammatan ummu,da alama ciniki ya fada tunda naga kin dade da yawa” hajjaa ta fada cikin salon tsokana tana murmushi,baki ta tura gaba tana ajjiyewa hajjaa ledar,kanta tsaye cike da zallar wautar quruciya tace

    “Ni gaskiya indai wannan mai surutun ne bana sonsa” dariya nujood ta sheqe da ita,kafin tace komai hajjaan da uncle muhsin ya bata aikin tuntubar widad din idan ta dawo aji ta bakinta tace da ita cikin tattara hankalinta

    “Saboda me?”

    “Ya cika siranta,kuma ya fiya magana” wannan karon nujood dariya harda fadowa

    “Bafa uncle abbas take fada ba,uncle suraj ne wallahi take nufi” sai hajjan itama ta saki dariya,tasan suraj din,duk da ba sosai ba,amma sai da nujood ta fada sannan ta tuna tabbas yana da kirki yana kuma da hira

    “To alhamdulillah,indai hakane uncle abbas yayi kenan?” Ta fada tana kallon widad,yadda suka tsareta suna jiran amsarta ya bata kunya,saita dauki filo ta cusa fuskarta a ciki tana dariya cike da jin kunya

    “Allah nidai hajjaa….”kunya ta sanyata tashi da gudu tayi dakinsu,sai suka bita da dariya,hajjaa taja chocolate din ta ajjiye da nufin idan uncle muhsin ya dawo ta nuna masa kafin su taba,ta kuma hada da gaya masa yadda sukayi da widad din.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/18, 12:43 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*