Author: Novels

  • Arubuce Ta Ke 40

    Arubuce Ta Ke 40

    Page 40

    Kuka sosai ta sakarwa ummun,da qyar ta samu ta shawo kanta,cikin hikima da dabara irin ta manya ta dinga lallabata,har sai data gamsu ta kuma ji alamun sakewa da tayi sannan ta fara tambayar ta inda wayarta take,sam ta ma manta da wani batun wayarta,sai a sannan ta tuna tun randa suka iso da nujood ta gama game da ita tace ta saka mata a bedside drawer dinta.

    Kusan awa guda suka shafe da ummu a waya,har alhaji ma ya karba,Aafiya da rafi’ah da suka shigo suma dukkansu suka karba,sai da kudin ummu ya qare tsaf kiran ya yanke da kansa.

    Maganganun da sukayi da ummu yasa ta samu sassauci,sai walwalarta kadan ta dawo,ta sauko daga saman gadon da wayar riqe a hannunta da niyyar kaiwa latifa.

    Tana shirin bude kofar dakin aka turo qofar,sai ta danja da baya tana kallonshi yana shigowa dakin,sanye yake da wani yadi mai taushi,a ido kawai zaka fahimci bashi da kauri,saboda kana iya hangen fara qal din vest din dake jikinsa.

    Baya ta sake ja tana rakubewa,gabanta kuma yana faduwa,har ya qaraso cikin dakin,ya taka a hankali ya qarasa gaban madubinta ya tsaya

    “Ina kwana?” Ta gaidashi tana dan russunawa,sai ya maida dubansa a kanta,gaba daya a darare take, baisan me yasa ba,amma ya gama karantar dabi’unta tsaf na rashin sakewa da jama’a,da alama tana da wuyar sabo,shikam tako ta ina baiga ta inda wannan hadin zai zama me alfanu ba,saidai ya sani cewa,abinda babba ya hango,yaro ko ya hau dala da gauron dutse bazai hangoshi ba

    “Lafiya lau,ya kwanan baqunta?” Ya fadi yana gyara daurin agogonsa,bata san ya zatace ba sai tayi shuru kawai ta sadda kanta,ita kawai Allah Allah take ya fita mata a daki,kada latifa tazo ta gansu su biyu.

    Sai daya gama gyara agogon sannan ya maida kallonsa a kanta

    “Shikenan babu wani abu da kuke buqata?” Kai ta gyada masa da sauri,sai ya jinjina kai,ya sanya hannu a aljihunsa ya fidda kudi ya ajjiye mata,don dabi’arsa ce,haka yakewa hafsan,koda suna da komai baya taba fita ya barta hannu babu komai.

    Ido ta bude sosai ta zarosu waje tana kallon kudin,har ya kusa fita daga dakin sannan ta ankara,da hanzari tace

    “Don Allah ka dauke,kada latifa ta gani,ni banaso” qaramin murmushi ne ya subuce masa duk da bai shiryawa hakan ba,ya waiwayo yana kallonta da manyan idanunsa

    “Ba zata komai ba koda ta gani din,daga yanzu duk abinda na baki babu wanda zai miki fada don kin karba,right?” Jikinta a sanyaye ta gyada kanta,don dai ita ta sani ummu na fada sosai gasu basma ma idan wani ya musu kyauta suka karba,tana kallonsa har ya fice daga dakin,sai ta matsa kusa da kudin tana kallonsu ba tare data taba ba.

    Ja baya tayi kadan jin an sake buda qofar an shigo,latifa ce,idanunta nakan fuskar widad din

    “Kun gama wayar ne?” Kai ta gyada mata

    “Eh tun dazu,kinga kudi wai ya bani” ta fada a shagwabe cike da sakarci tana dubanta

    “Kuma Allah bani na roqshi ba” ta sake fada qwalla na cika mata idanu,dariya kufcewa latifa,ta yarda widad bayan quruciya ma harda sangarta irin ta goyon kaka ke damunta,qarasawa tayi inda take tsaye ta kama hannunta ta riqe

    “Don ya baki kudi ba komai bane,mijinki ne kinji, komai zai baki hakanan kome zaiyi miki ba haramun bane kin gane?”, Kai ta gyada kawai bawai don ta fahimci me take nufi ba

    “Kuma ya akayi ya fita baki masa rakiya ba?”

    “Mu jera tare?” Ta tambayi latifa tana fidda idanu,saita jinjina mata kai

    “Eh mana,bakiga ummu na raka alhaji ba?” Shuru ta danyi tana tunowa,ta gyada kai a hankali

    “To daga yau kema haka zaki dinga yi masa kinji ko?” Fuska ta noqe,itadai wannan ai iskanci ne,batason irin wadan nan maganganun,haka dai ta gyadawa latifan kai,sannan ta sakata a gaba suka wuce kitchen.

    A ranar latifa ta fara gwada mata yadda zatayi wasu abubuwa cikin kitchen,kamar tsaftaceshi da inda zata dinga ajjiye komai a muhallinsa cikin kitchen din,yadda zata wanke kwanuka da sauransu.

    Da yammaci tana falonta a zaune bayan sun gama komai ta dinga jin hayaniyar yara,sai tayi mamaki don bata dauka akwai yara a gidan ba,daga nan ta yaye labulen falon nata,sai ta hangi su mimi suna wasa,tana son fita amma ita komai na gidan d’ari d’ari takeyi dashi,don haka taci gaba da kallonsu ta nan,har suka gama wasansu suka bar wajen.

    Tun qarfe shida ta gama lafta shinkafarta da miya,ta zubata cikin food flask,bata damu da jimawar da zaiyi kafin ya dawo ba,ko kuma gumin abincin da zai iya komawa cikin flask din ba.

    Fuskarta ta dauraye kawai,ta cire zanin jikinta ta nemo mahadin rigar ta saka,sannan ta tasa su mimi a gaba suka wuce sashen widad,tayi hakanne saboda ta hanashi dadewa acan,kada ya shiga yaje ya zauna,ko abinda ya faru jiya ya maimaita kansa,cikin ranta tana jin ko a jiyan ma kirsa ce kawai irin tata,ta sani cewa mace duk qanqantarta kaidi ne da ita,kada tazo tana tufka ta baya tana warware.

    Kan widad na saman cinyar latifa tana kitsa mata kalba tana warewa saboda santsin gashinta,sa’annan kuma ba wani kama mata takeyi da kyau ba,tana mata ne shigen yadda ummu ke mata idan tanason tayi baccin rana,latifan na bata labarun ban dariya,wanda ya sake sanyawa zuciyarta ta kuma saki.

    Koda tayi sallama hannu bibbiyu latifa ta karbeta,widad kuwa kamar ko yaushe binta tayi da kallo kafin ta zamo ta gaisheta kamar yadda take gaida dukan wanda ya girmeta,hakan kuma sai ya yiwa hafsat dadi,ta sake jin lallai itace a sama,ta dinga bin falon da kallo a fakaice,kafin ta koma satar kallon widad din,bata da matsala da komai,tana kuma jin komai zai tafi dai dai,damuwarta daya irin kyawun da yarinyar take dashi,tana tsoron kada wannan ya zama mabudin nasarar jan hankalin abbas…

    “Inaaaa,bazan bari ba” ta tabbatarwa kanta da kanta cikin zuciyarta,zatayi dukkan mai yuwuwa ta hana wannan kyan tasiri a fuska da idanunsa.

    Kusan da latifa suke hirar,ita widad ta maida hankalinta gasu mimi,kasancewarta mai son qananun yara,duka sai suka ja hankalinta,tana ta duban fuskar nawwara da taga tana mata kama da fuskarshi

    “Ke dawa kike kama?” Ta tambayi yarinyar tana dan murmushi,mimi tayi wuf tace

    “Da daddynmu mana,ni kuma da mommy na,wai shine su anty bara suke cewa ta fini kyau,wai daddy yafi mommy kyau” daga idanunta widad tayi ta dubi fuskar hafsat dake magana da latifa,eh itama taga wannan duk da qarancin shekarunta,amma dai tasan kyau

    “Eh wallahi,ya fita kyau” widad ta fada hankalinta kwance cikin yanayi na quruciya.

    Rigime mata mimi tayi ta soma qwalawa uwar kira

    “Mommy,kinji anty ma tace daddy yafiki kyau,kuma nawwara ta fini kyau?” Dariya latifa tadan saki tana kama baki,widad din tayi wauta,amma da alama ma ita a wajenta ba komai bane,yayin da hafsat ta kafe widad da idanu,wani abu mai kama da bacin rai yana motsa mata qasan ranta,sai kuma ta buge da murmushin yaqe

    “Tsokanarki takeyi,kuma ni nafi daddynku kyau,saidai ya nunamin manyan ido kawai” cikin murna mimi ta waiwaya tana duban widad

    “To kinji ko?” Dariya ta saki tana jawota jikinta

    “Wasa nake miki,kema kina kama da daddyn naki ai” kau da idanunta hafsat tayi daga kansu, zuciyarta na raya mata wani abu.

    Yau dinma kai tsaye sassan hafsat din ya fara isa,bai taras da kowa a falon ba,don haka ya sanya kai bedroom dinta,yana taka lallausan sabon carfet din daya sauya mata dab da bikin nan,amma har datti ya fara cikashi laushinsa ya ragu ainun.

    Dakin yaran ya fara budewa,komai a hargitse a zaune da duwawunshi,ash and baby pink ne color din dakin,amma pink din har ya dauki hanyar zama ash din shima,ya taka a hankali yana tattare kayan sawarsu dake watse a qasan dakin,sun cakude waje daya,ba zaka banbance wankakke da wanda baida wanki ko kuma guga ba,ya kwashe gaba daya,ya buda laundry basket dinsu da niyyar zubawa,sai ya sameshi a cike fam da kaya.

    Ransa ya sosu,baiga amfanin yaron da ya aje saboda ya dinga musu wanki ba,bayan duk wata sai ya ajjiye kudinsa,to kudin ake bashi a banza ko kuwa,ya daga kayan da niyyar zubasu a haka yaci karo da undies din hafsat din,harda brassieres.

    Kishinsa ne ya motsa,ransa ya sake baci fiye da dazu,sai ya watsar da kayan yaran gefe daya,ya soma birkito kwandon,nan ya dinga cin karo da undies dinta,ya dinga tarasu a gefe,har ya gama kwashesu tsaf,sannan ya zuba kayansu mimi din,ya buda toilet dinsu ya leqa,dole ya dawo baya da sauri,saboda abun babu kyan gani,mutum ne shi me masifar tsantsami,idan kanaso kaga fadansa to yaga qazanta.

    Dogon tsaki yaja kamar zai tsinke harshensa,yana dai tunanin me aikin da bayaso daga qarshe daqyar idan ba ita zai sa a daukowa hafsat din ba,ya gaji da ganin wannan qazantar gaba daya,to amma kuma hakan kamar daure mata qarqashi ne,kada ta sake sangarcewa ta miqe qafa,tun a baya yaqi a kawota dinne saboda gudun ta sake tabarbarewa,amma a yanzu dukka alamu suna nuna daukotan ya kusa zame masa wajibi.

    Dakin ya janyo musu ya wuce nata dakin,shima dai kamar dakin yaran,shikam natan harda tsami tsamin kayan wanki,bai saka kai da yawa ba ya dawo da baya yana ambaton sunan Allah,sai kawai ya juya ya fice daga sashen gaba daya.

    Duk da ransa babu dadi haka ya daure ya nufi sashen widad din,tunda dai itama matarsa ce kamar hafsat din,tana kuma da haqqi a kansa kamar ita.

    Sanda yayi sallama a falon yayi dai dai da sanda widad ke maimaitawa mimi karatun makarantar bokonta,yarinyar kuwa nata kamawa tana amsawa cikin jin dadi,don baqon abune a wajenta,mamarta bata taba tsayawa ko sau daya ta duba assignment dinta ko ta bibiyi karatunta ba,abbas din keyi mata assignment idan yana gari,idan baya nan kuma haka zata koma da litattafan ta, aunties dinsu sunsha rubuto letter suce ta kawo gida,hafsat ke karba,tana gama karantawa take yagawa,ta rubuta reply da cewa ayi haquri,mamanta ba mazauniya bace amma za’a gyara,har sun gaji da rubutun sun qyaleta,saboda suna ganin kudin ubanta ke tafiya,su basu da asara.

    Rige rigen zuwa yi masa sannu da zuwa sukeyi,widad ta bisu da kallo tana jin damuwarta da kewarta na raguwa,dan zaman awannin da sukayi dasu sun debe mata kewa matuqa.

    Tunda ya shigo din take bibiyar dukka motsinsa da idanuwanta,tana son taga shin ko zai kalli sassan da widad din ke zaune?,ko kuma zai saci kallonta ko sau daya ne?.

    *Arewabooks: Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[3/2, 10:44 AM] +234 802 297 0646: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 48

    Arubuce Ta Ke 48

    Page 48

    Tana cikin wannan mitar aka buga qofar falon

    “Waye na?” Ta fada cikin fada fada,ranta fal quncin mimin ta karya mata budget

    “Nine,sale ne”

    “Shigo” ta fada kanta tsaye bayan taja tsaki,duk da tasan abbas baison haka,don baya bari a shigo masa har inda iyalinsa suke kai tsaye.

    Da sallama yaron ya shigo yana sunkui da kai,don bai saba shigowar ba,ga hafsat din da daurin qirji,sauqinta akwai t-shirt a jikinta,a samanta taja zanin ta daura

    “Ina kwana hajiya”

    “Lafiya lau ya akayi?”

    “Eh dama me yiwa engine service ne yazo,za’a bada kudin a siya kayan aikin,sai mechanic din da zai dauki motar oga ya kaita garage za’a mata service itama” tsuke fuska tayi,don tasan kudaden daya wara ya bata saboda a duba motar da engine din suna da yawa

    “Bakaniken ya dauki motar,amma shi me yiwa engine service kace ya barshi kawai,sai mai gidan ya dawo”

    “To….amma engine din yana bada matsala fa,jiya ma…..”

    “Abinda nace kayi zakayi ko raayinka zanbi?”

    “Sorry madam” ya fada yana juyawa yabar falon,cikin ransa yana Ala wadai da dabi’arta,sarai yasan an bata kudaden,fitar dasu ne ba zata iya ba.

    Tsaki taja tana duban yaran

    “Ku wuce muje na dafa muku abinci” jin xancan abinci sai mimi ta ware,sukabi bayanta zuwa kitchen din,saidai tana ganin ta buda kwalin indomie yarinyar ta bata rai,ta gaji da ita,don jiya da daddare ma ita ta dafa musu

    “Indomie mommy?,bana ci nidai” cikin takaici ta kalla yarinyar,ubansu ya batasu da kala kalar abinci,ita kuwa ba zata iya dorama kanta wannan wahalar ba

    “Ba zakici ba ubanme zakici?”

    “Irin abincin gidan hajiya”

    “Meye abincin gidan hajiyan?”

    “Tuwo ko dambu”

    “Nabi tuwon da gudu,zakici ubanki wallahi,idan bakici ki zauna haka,yunwar cikinki” saita bare kwalin ta dauko guda biyu ta zuba a tukunyar.

    Kusan dai a gantale suka tsakuri taliyar,bata tsaya ta mata ma dahuwar arziqi ba bare darajar hakan ya sanya suci da yawa,daga qarshe ma.idan ta debo ta baiwa nawwara sai ta tankwabe hannunta,da yake ita din tafi mimi fada,sai ta tattarasu ta barsu ta shiga sabgarta,dole da yunwa ta ishesu suka dawo suka ci a haka bayan tayi sanyi.

    ¢¢¢¢¢¢¢¢¢ Hirar da suka sha da ummu da abbanta na kusan awa biyu ya sanya tajita tadan sake,sai kuma dan motsin da take jiyowa lokaci lokaci cikin gidan ya sanya bata matsu da yawa ba,ta dan saki jiki ta soma kade dakin da gyarashi kamar yadda latifa ta koya mata,sannu a hankali sai gashi ta gyara dakin fes,sadai fa tadan dauki lokaci,ta shiga toilet ta wanke fes,ta kama qugu tana dariyar farinciki na ganin yadda ta gyara dakin kamar ba ita ba,ta kama baki tana murna

    “Ashe dai na iya,amma ummu ke hanani,bari na kira umma latifa na bata labari” ta koma gefan gadon tana kaffa kaffa kada ta bata zanin gadon data d’ameshi da kyau,ta fara duba number latifa wadda basu jima da gama waya da ita ba itama,Latifa na daga wayar ta fara bata labari

    “Iyeee shalelen ummu,girma yazo,haka akeso,kiyita tsafta kamar ummunki,saura girki” dariya tayi tana sake bata labarin wahalar data sha,latifa na biye mata,ummu ja gefansu tana murmushi,duk da rabin hankalinta nakan shalelen tata.

    Wunin ranar bata wani ji yunwa ba,koda taji yunwa dinma tea ta hada tasha ta kwanta abinta.

    Kafin magariba tayi wanka,ta shafe jikinta da turarukan da latifa ta hado mata a kayanta,kusan sai data shafa kowanne turare,har ya soma yawa ya fara hawa ka,kowanne mai sanyi da dadin qamshi ne,amma yawan da yayi yasa ya jirkita,amma ita ko a jikinta,wata dubai abaya ta saka,ta dawo falo ta maqale jikin window tana leqen harabar gidan,gabanta yana dan faduwa kadan kadan,saboda ganin magariba ta gabato babu shi ba alamarsa.

    Ana qwala kiran sallar magariba motarsa tana shigowa cikin gidan,samuel ne ya kawoshi,shi ya koma shi kuma ya shigo ciki.

    “sannu da zuwa” ta furta tana jan dankwalinta daya zame saboda santsinsa daya hadu da sulbin gashinta,ta miqe tsoron nan nata yana bayyana,tanason karbar masa ledar daya shigo da ita kamar yadda ta saba duk sanda taga kaya hannun babba,amma tana shakka matsawa inda yake,a haka har ya qaraso ya ajjiye,ya zauna yana tube takalman qafarsa

    “Lafiya kika wuni?” Kai ta gyada masa,sai yadan lumshe idanu yana gyada kai,qamshin jikinta gaba daya ya cika falon,kamar anyi barin turare

    “Samomin ruwa nasha” hanyar kitchen din ta kalla,baiyi duhu sosai ba,don haka da sauri tayi hanyar,a nufinta tayi sauri ta dawo kada wajen yafi haka duhu.

    Binta yayi da kallo,ko yaushe ya kalletan sai ya dinga jin mamaki na shigarsa,wai matarsa ce wannan,ta dawo da ruwan ta russuna ta miqa masa kamar yadda ta saba yi tun a gida.

    Hannu yasa zai karba,yadda tayin yana burgeshi,duk da abub mamaki bane,duba da gidan data fito,muhsin kadai ya ishi a shaidesu,don ko cikin abokansu daban yake,wani abune da zai iya cewa baisan lokaci na qarshe da hafsat tayi masa ba wai don zata bashi abu.

    Sakin ruwan tayi da sauri sanda hannunsa ya sauka akan nata,jikinta ya dauki rawa,taja da baya tana yarfe hannu jikinta yana rawa,hawaye na shirin tarar mata a ido,shi bai kula bama,don ya duqa zai dauke ruwan bayan ya furta

    “Subhanallah” sanda ya dago harta samu waje ta rakube,ya bita da kallo yana mamakin yadda take matuqar tsoron tarayya dashi,kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya bude gorar ruwan ya fara sha,sannan ya miqe yana cewa

    “Zanje sallah,idan na dawo zaki shiga ciki ku gaisa da mutanen gidan,ga abinci nan a leda ki dauki naki” kai ta gyada masa gabanta na faduwa,bata samu nutsuwa ba har sai da yayi alwalar ya fice,ta bishi da kallo tana hararar hanya qwalla na gangaro mata,yanzu idan ummu ko mommy suka ga wannan abun da yakeyi fa?.

    A falo ya tsaya jiranta,ta fito yafe da mayafin abayar bayan ta cire hijabin da tayi sallar dashi

    “Koma ki samo babban mayafi,akwai mutane a waje” yayi maganar sanda yake dage labulen falon yana sake duba farfajiyar gidan,jikinta ta kalla,itadai bataga wani aibu a haka ba,amma sai batace komai ba ta koma ta lalubo mayafi cikin kayanta ta fito,suka jera zuwa cikin gidan.

    Babban gini ne,don yadan fi nasu girma da kayan alatu,sanda ta shiga ta samu matar gidan a falo,ta karbeta da fara’a,saidai tunda ta gaidata ta rasa me zata cemata.

    “Ban gane fuskar taki ba,ko kanwar amaryar abbas ce?” Qas tayi da kanta tana jin nauyi yana kamata,saita girgiza kai alamun a’ah

    “Ko amaryar ce da kanta?” Saita daga kai alamun eh,matar ta maida kanta sosai tana kallon widad din sosai,abbas data sani,abbas dake da.babbar mace kamar hafsat yaje ya auro wannan qwailar?,lallai Allah mai iko,sau tari mazan da suka fiya izza da kuma jin kansu daga qarshe haka suke qarewa,har gwara wannan din,kyakkyawa ce data amsa sunanta,komai nata mai ban sha’awa da daukan hankali,nan gaba kadan idan ta ida zama cikakkiyar mace lallai ba shakka sai an kalleta an qara,dole hankalin hafsat din ya tashi,amma a fili sai tace da ita

    “Ma sha Allah,Allah ya bada zama lafiya kinji amarya” bata iya amsa mata ba,sai shuru data sakeyi kawai kanta a qasa,gaba daya bata jinta a sake,tun asali dama ita din bamai saurin sabo bace,tana da wuyar sakewa da baqin fuska,don haka bata wani jima ba ta miqe tace zata tafi

    “To ina zuwa” ta fadi tana miqewa ta shige ciki,ranta da zuciyarta fal mamaki,ba jimawa ta fito da wasu kayan barci set uku ta bata,hannu biyu widad ta saka ta karba sannan ta fito.

    A inda ta barshi ta sameshi,ya sake mata jagora suka koma ciki,tana ta kallon gate,ji take kaman ta fita ta miqe qafarta,suna shiga falon ta miqa masa kayan kamar yadda takewa ummu a gida idan an mata kyautar abu

    “Gashi” ta fada tana ajjiye masa kusa dashi,dai dai lokacin da ledar ta zame,matan dake jikin takardar sanye da irin kayan baccin dake cikin ledar suka fito.

    Kusan tare suka dauke idanunsu shi da ita,taja baya da sauri qafafunta na sarqewa zata wuce ciki

    “Zonan” yayi kiranta yana karantarta,da baya da baya ta dawo,ita a lallai ba zata iya kallonsa ba,har abun yaso bashi dariya,ya dake da yanayin dakiyarsa da kuma miskilancinsa

    “Dauke abinki ki tafi dasu”

    “Banaso” ta fada kai tsaye tana maqale kafada,a mamakance yake kallonta

    “Bake ta bawa ba?”

    “Ni ta bawa,amma banaso,bana saka irinsu” dariyar da yaketa riqewa ta subuce masa,amma saita fita ta sigar murmushi

    “Zauna” yace da ita yanata kokawa da dariyar tasa,ta baya ta zauna har yanzu taqi yarda su hada ido dashi.

    “kinsan amfanin wadan nan kayan?” Fuska ta qara daurewa,tana sake tabbatarwa basu hada ido ba,kai ta girgixa masa ba tare da tayi magana ba

    “Oya….open your mouth,ban jiki ba”

    “Ban sani ba,kayan ‘yan iska ne fa” tayi maganar tana narke fuska,kamar zata saki kuka.

    Wannan karon duk yadda yaso boye dariyarsa sai data fidda sauti,yayi qoqarin daidaita kansa,da gaske ta jahilci aure,da alama aiki je jajur a gabansa a kanta,bai tsawwala sai ya samu komai daga gareta ba,amma aqalla ta gama sanin meye auren kansa,don da alama batasan meye shi ba.

    “Kwashesu ki tafi” ya bata umarni a taqaice,ta baya ta zuro hannunta ta jawo ledar zuwa gabanta,sannan ta miqe da sauri sauri tayi dakinta.

    Tana shiga ta jefa ledar saman sofa bed tana zumbura baki kamar zata fashe,ledar ta qarasa yayewa kayan suka fito sosai,bata gama kula da hotunan jiki bama sai yanzu,ta qarasa tana daga kayan saita jefar zuciyarta a a cushe

    “Lallai matar nan ma ‘yar iska ce ashe itama,don me zata bata wadan nan kayan?” Hadasu tayi ta cukuikuye ta jefa cikin sif,ta koma saman gado ta lafe a cikin bargo abinta,idanunta ta rufe,tana fata bacci ya dauketa tun tana iya jin motsinsa,basai waje yayi shuru ba.

    °°°°°°°°°Washegari ma haka ya fita,bai tsaya yin breakfast ba,yauma ita dinma kamar jiya,bayan ta gama ‘yan gyare gyarenta da zata iya,saita dawo bakin window din falon ta zauna,lokaci lokaci tana yaye labulen tana leqa farfajiyar gidan,abinda ya tayata zama kenan,duk da yace mata tana iya shiga cikin gidan ta zauna a can,kota debe kewa,amma kasancewarta mara saurin sabo taji gwara tayi zamanta a nan har zuwa sanda ya dawo gida.

    To tsahon kwanaki biyar kusan haka rayuwar ta dinga gara musu,da safe idan zaya fita aiki zai sameta ne a falo,sabida yafi dakinta haske,zatayi masa a dawo lafiya bayan ta gaidashi,ya ajiye mata kudi ya kuma tambayeta bata da matsala,sannan ya mata sallama,takan bishi da idanu tana jin kamar ta bishi,wani lokacin yana ankare da ita,wani zubin hankalinsa yayi gaba,zata gyara dakinta data fara sabawa dashi,ta gyara falo ta goge shi tasa,duk da cewa tana daukan lokaci kafin ta gama,amma yana kintsuwa,kyan sharar nata da gyaran nata yake gani,saboda tafi hafsat nesa ba kusa ba, at least ita bata barin qura ko datti,sabanin hafsat din da ko ina a birkice yake,duk da suna da komai a store,to amma bata taba dora girki ba,yana sawa a kawo mata abinci,idan ya dawo tana cikin falon,amma wata qurya ta daban,a can zata zauna ba um ba um um,tana kallonsa kawai,duk da tana buqatar hira da wanda zatayi hira dashi,sai idan yaga tana gyangyadi kota gaji zai rakata ta kwanta ya dawo falo yaci gaba da sabgoginsa kafin ya tattara shima ya wuce nasa dakin.

    Duk sanda tsautsayi yasa ta farka cikin dare kuwa da qyar da sudin goshi take komawa baccin,saboda dan banzan tsoro,a rayuwarta bata taba kwana daki ita daya ba sai a wannan karon.

    Bangaren hafsat kuwa kullum a rana saita kirata,ta tambayeta me ya faru a jiya,me yake faruwa a yanxu,amsa kawai take buqata,tana ji zata katse wayarta,saidai idan weedad dince tabi bayan kiran tace a bata su mimi.

    Zuwa sannan fa fara jin dadin wayarta,da kanta da kanta ta koyi yadda ake sarrafa abubuwa da dama a cikinta,ta dauko games kala kala da suke debe mata kewa sosai,wannan yasa dogon wunin kadaicin da takeyi ya ragu sosai.

    _wannan kenan_

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/7, 11:54 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 46

    Arubuce Ta Ke 46

    Page 46

    Space ya bata,ya zauna daga nesa yana kallonta har sai data gamsu don kanta ta tsagaita kukan,don ya fuskanci kukan da take harda na sakalci ma,sanann ya miqe yana duba dakin ko zaiga abincin da yace a kawo mata amma baiga alamunsa ba,waiwayawa yayi yana dubanta

    “Ina abincin da nace a kawo miki?” Baki ta tabe sosai irin na yaran da suka gwanance wajen shagwaba

    “Naji ana knocking,inajin tsoro ne bazan iya fita ba” dan qaramin bakinta me dauke da jajayen lips yabi da kallo,wannan da alama ba abinda ta sani sai sangarta da sakalci,ya janye idanuwansa yana laluba aljihunsa ya fidda wayarsa,a nan ya samu tarin miscall na wanda ya aika din,yana kiransa kafin yace komai ya gaya masa yayita bugu ba’a bude ba

    “Ba matsala,am back,zaka iya kawowa” ya fada yana nufar qofar dakin da zummar ficewa,saidai tun bai sanya qafarsa a falo ba ta miqe ta rufa masa baya.

    Tsayawa yayi bayan ya zame wayar daga kunnensa sannan ya waiwayo yana kallonta,saita dauke kanta gefe tana turo baki gaba gami da tabeshi

    “Ina zaki?”

    “Ni binka zanyi,Allah ba zan zauna a nan ba” saiga hawaye yana biyo bayan maganarta

    “Saqo zan karbo”

    “Zan bika” ta sake fada wasu hawayen na sake zubowa

    “Yanzu zan dawo,just a compound din gidan nan ne” wannan karon maqale kafada tayi saboda kuka ya riga da ya subuce mata

    “Oh god” ya fada yana dan lumshe idanunsa hadi da budesu duka lokaci guda,kafin ya sake cewa wani abu anyi knocking,sai kawai yayi gaba,ta kuwa take masa baya yana dauke qafarsa tana saka tata.

    Takeaway na abincin ya karba ya maida qofar ya kulle,daya juyo sai kuma tayi tsaye tana jin banbarakwai,ya tako taja baya hadi da yin gefe ta bashi hanya,ya isa tsakiyar falon

    “Dauko plate a kitchen da spoon” ya fada yana ajjiye ledar,hadi da zama saman kujerar sannan ya fara qoqarin cire agogon hannunsa.

    Jin shuru bata amsa ba,bata kuma motsa ba ya sanyashi dago kansa,tana tsaye ta marairaice fuska kawai tana kallonsa

    “Bakiji bane?” Ya tambayeta da kaurin murya

    “Tsoro….”

    “Subhanallah” ya furta a hankali,sai kawai ya miqe ba tare da yace komai ba,nan ma batayi qasa a gwiwa ba ta rufa masa baya,tana tsaye ya dauko plate din,ya hado da spoons da bottle water da drink na kwali guda daya sannan suka rankayo suka fito.

    Wannan karon a qas ya zauna sosai,ya bude ledojin ya hada komai da komai kowanne plates d’ai d’ai ya tura mata hade da ruwan da kuma lemon,ya sanyawa nashi palate din spoon ya fara diban abincin yana ci bayan yayi bismillah,hannunsa daya riqe da wayarsa yana dannawa.

    Shuru tayi tana kallon plate din nata,tun asali ita din bata saba cin abinci ita kadai ba,tun tasowarta,saboda ta taso mutum ce mara son cin abinci,wannan yasa kowanne lokaci da ummu sukeci,suna ci tana hilatarta har sai taci me yawa,idan kuwa tana azumine ko kuma tana makaranta taci kafin ta dawo wanda zaiyi wuya ma ta rigata ci din,saita hada mata da wani cikinsu Aafiya,ko ta tafi sassan anty madina taci cikin jama’a,shine fa take ci da dan dama,ko zuwanta bauchi kullum da latifa sukeci,to a yanzun saita kasa tabuka komai,har yayi nisa da cin nasa abincin.

    Bai kula ba sai da yayi nisa sosai,ya daga idanunsa ya kalleta,itama shi take kallo,ta narke fuska kamar wadda kukan da tayi bai isheta ba tana neman qari ne

    “Dauki kici” ya fadi yana mata nuni da abincin da ido,saita girgiza kai

    “Na qoshi” mamaki ya kamashi,baici ace bata jin yunwa ba,yasan tun sanda suka fito rabonta da abinci,saiya rasa yadda zai mata taci.abincin,don daga qarshe ma baya taja ta rungume qafafunta kamar wata marainiya.

    Ajiyar zuciya ya sauke yana ajjiye nasa plate din,shikam ya gamu da gamonsa,da alama rainon zaiyi da gaske,suraj da suke chart dashi a lokacin ya turawa gajeran saqon tambaya

    _”If you want a child to eat and he refuses, what will you do for him?,ina buqatar taimakon,its urgent please”_. Sai daya tura masa sticker din dariya sannan ya amsa masa

    _”yar rainon taka hala?,ka lallabata,malam ka kuma koyi magana,wannan ba hafsat bace,ita din ba zata gane shuru ba,be a child like her for a while,sannan ne komai zai daidaita”_

    _”thanks,i will tray_” ya amsa masa sannan ya kashe data dinsa ya ajjiye wayar

    “Oh God, give me courage” ya fada can qasan ransa yana kallonta

    “Let’s share the food,come closer” ya fada yans miqa hannu yaja plate din,makarantar da tayi mai tsada ce sosai,don haka ko a iya js data tsaya tana jin turanci fes tana kuma iya mayarwa,don haka taji sarai abinda ya fada,to amma fa ita tsironsa takeji,ta sani tun a gida cin abinci da maza ba abu bane me kyau,uwa uba hudubarta tana nan a kanta fes bata bace ba,ya zataci abinci da wani?,to amma kuma yunwa takeji,idan kuma bai tayata ci din ba tabbas tana iya kwana da yunwa

    “Uhnnn,bismillah” ya sake fada yana juya spoon dinsa a ciki,jiki a mace,a kuma mugun darare ta matso,nesa da plate din ta zauna,saidai tana kai hannu tana diban abincin,tana yi kuma tana satar kallonsa,amma sai taga sam shi hankalinsa baya wajen,wannan yasa ta dan sake sakewa ta soma cin abincin a nutse.

    Duk da ya qoshi hannunsa kadai ya zame amma bai tashi daga wajen ba,har sai da yaga ta cire nata hannun,takai goran ruwan mitsitsin bakinta ta fara sha,har cikin ransa yaji ya sauke nauyi,zuciyarsa tayi wasai,sanda ya dawo ya samu bataci abincin ba ji yayi kamar yaci amanar hajiya,ya kasa sauke nauyin amanar daya karba ya kuma dauka tun ba’a kai ga kwana ba.

    Zaman kurame sukayi a falon,shi yana aikace aikacen sa a waya,ita kuwa tana takure gefe daya duk da tv tana aikinta,saidai ita hankalinta ya kasu kashi biyu,duk wani motsi da taji saita waiwaya da sauri taga meye,shi kuwa ya zauna ne don ya debe mata kewa ya kuma rage mata dare,duk kuwa da yanason tashi,yana nan a zaune sai kiran hafsat ya shigo wayarsa,abinda ya bashi mamaki kenan,ya kuma yi hanzarin dagawa yana tunanin ko wani abunne ya faru?,qila ita ko wani cikin yaranne babu lafiya,saboda sam ba dabi’arta bace ta kirashi don yayi tafiya,komai nisan zangon da zaiyi,koda da nufin jin yadda ya sauka,saidai idan shi din ya sauka ya kirata ya shaida mata ya sauka lafiya,ta kuma bashi yaransa suyi magana,indai kaga kiranta to wani abunne ya faru,ko kuma wata buqatar ce ta taso.

    A tsanake ya daga wayar yana mata sallama da lallausar muryarsa data saukar mata da wani zazzafan kishinsa,zuciyarta nata ayyano mata kasantuwarsu da widad a dai dai wannan lokacin,duk kuwa da tana da wani yaqini da kuma qwarin gwiwa abinda ta dasa zaiyi tasiri sosai,saboda saran da tayi akan gaba.

    Muryar data amsa masa sallamar da ita ta sake sanyashi a mamaki,ya manta rabon da yaji wannan tune din daga gareta,tun wani zamani can baya,suka gama gaisawa yana jiran yaji ta kawo complain ko wani damuwa sai baiji wannan ba,sai hira da taketa qoqarin jansa dashi.

    To anan dai ya biye mata,don shima yana da buqatar irin wannan kulawar,yana yunwar samun kulawa irin wanann amma ta zame masa jidali a wajen hafsat din,ya kishingida kadan yana sauraren hirar da take masa,duk kuwa da cewa qarfin hali kawai takeyi,daga can harta gundura,bawai don ta gaji dajin muryarsa ba,muryarsa na daya daga cikin abubuwan da bata taba jin ta gaji dasu ba.

    “Wai ina qanwata ne?” Ta jefa masa tambayar fa tun dazun so samu ta zama ta farko,to amma he is very smart,zai iya sansano wani abu,shi yasa ta kaita tsakiyar zancansu

    “Bata mu gaisa mana,nayi mata ya gajiyar hanya?,ina fata ba zaka sake tara mata wata gajiyar ba” maida idanunsa yayi kan fuskarta da a yanzun ta bada hankalinta ga tv,saboda wani cartoon da suka juya haskawa,hasken tvn ya haske fara tas din fatarta da kyau,haka kawai zuciya ta d’arsa masa abinda hafsat din ta fada akan widad,ya danyi imagination akai na wasu sakanni,sai yayi sauri ya ture daga ransa yana fadin

    “She’s too young”

    “Hello” muryar hafsat dake tawa ta ratsa ta tunaninsa,saboda raya mata da zuciyarta tayi tana jikinsa ne yana debe kewa da ita

    “Ina jinki”

    “Tana ina?”

    “Bata kusa…..sai wani lokacin” haka kawai taji zuciyar ta bata yadda da abinda ya fada ba,don haka ta bishi da

    “Okay” taja qaramar keypad dinta ta soma trying number widad din,amma aka sanar mata a kashe wayar take,take tajin hankalinta ya tashi,abbas baya son barin waya a kunne a sanda suka kebe,haka yake,koda tata wayar karba yake ya kashe,yakance

    “I need a rest,ina buqatar kadaicewa da iyalina” bai fiya barinta kunna waya ba idan yana gida weekend a sanda suna tashen buga soyayyarsu.

    Haka kawai taji hirar duka ta fice mata a kai,don haka ta nema suyi sallama,bai matsa ba,don yaga qoqarinta,abun shekara da shekaru,shi yayi mata sallamar,yama rigata kashe wayar ya ajjiye,abinda ya sake saka mata zargi a ranta kenan,tayi jifa da wayar gefanta,ta koma da baya yaraf ta kwanta tana duban ceiling,dole ta kira yarinyar taji.me ya faru a yau,dole ta kirata ta dora mata bita.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/6, 3:13 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 35

    Arubuce Ta Ke 35

    Page 35

    Tun gari bai kammala wayewa ba suka tashi da aikin qarasa kintsa gidan,saboda suna son wucewa a ranar,saidai hakan bata samu ba,don abbas ya sake dakatar dasu yace su sake kwana,wannan ya basu dama suka buqaci mota,ya kira samuel daga office yazo ya kawo musu tare da yi musu jagora,inna laila,batulu anty deena anty halima da hajjaa suka sada widad da gidan hajiyan abbas.

    Fadin irin dadin da hajiyan taji bata baki ne,bata zaci zuwanta ba sam,saboda taga ba kasafai ake hakan ba,tunda ba unguwa daya suke ba,yadda ta dinga nan nan dasu zai baka mamaki,farincikinta ya gaza boyuwa,ta kirayi gwaggo fanteka donta tayata karbarsu.

    Duk abinda akeyi fantakea din da kallo take binsu,saidai ta saci ido ta tabe baki,idanuwanta qir akan fuskar widad

    “Ashe…..ba banza ba,ashe sadakar yalla ya kwaso,kai jama’a,kashin hafsatu ya bushe,ba abinda ba zata gani ba,idan Allah ya tsare ma bata fiddata gidan ba” wannan ta dinga maimaitawa a ranta tana binsu da kallo,musamman da taga kowanne a cikinsu daga yanayin fata zuwa halittarsu da sumar kansu batayi kama sam da hausa fulani ba.

    Duk da batasan da zuwansu ba haka ta cikasu da abinci kala kala,kasancewarta mace mai karamci,baka rasata da abubuwa irin wadan nan.

    Tun basu bar gidan ba ta kira abbas ta shaida masa,shima yaji dadin yadda suka karrama masa mahaifiya,yasan zasu fita,tunda muhsin ya gaya masa,don hajjaa tace ya gaya masa,amma baisan can zasu kaita ba.

    Sai yamma lis suka dawo gidan,a sannan hafsa tana daga jikin window dinta tanata leqe,har yanzu batakai ga ganin fuskar widad ba,sai giftawarsu data gani kawai.

    Dan kwalinta ta cire ta jefar,ta koma ta zauna jabar saman kujera tana fidda wani hucin azababben kishi dake cinta,tunda zancan nan ya bullo har kawo yau bata sukuni ko qanqani,gaba daya a birkice take jinta,hatta da yaran tace kada a dawo dasu sai gobe ko jibi,sai kawai tasa hannunta a fuska ta fashe da kuka mai cin rai,tana tsananin son abbas tana kuma kishinsa,batasan yadda zata jurewa wannan al’amarin ba,abu mafi dagula mata hankali shine sadakar yalla da akace ya auro,tana sane da yadda suke fidda mace da yaranta daga gidan,ta yaya zata kaucewa wannan?,saita tayi cikin bedrooms dinta gudun kada wani yaji gunjin kukanta,don kukan take da buqatar yi sosai.

    Su biyu ne a dakin ita da nujood,sun nutse abinsu saman gadon da yasha shimfida da lafiyayyen zanin gadon da yake tafiyayye tun daga yemen,sai hira suke abinsu suna dariya,babu abinda ya damesu,ita sam bata wani tuna wai amaryace,nan din gidan aurenta ne,zamansu a haka dasu anty madeena yana mata dadi,hankalinta kwance,bata tuna tafiya zasuyi su barta.

    Dai dai nan anty deena data gama hada kayanta tsaf ta tura qofar dakin ta shigo,saita saki baki kawai tana kallonsu,gadon da aka gama gyarewa aka sa masa zanin gado mafi tsada suka haye tsakiyarsa abinsu?

    “Qaniyarki nujood,sauko” anty deena ta fada tana mata daquwa

    “Gadon amaryar zaki kama ku haye?,ke baki mata fada ba ita batayi miki ba?” Nujood din tana dariya ta sauko,sai widad tayi tsam da ranta tana kallon anty deena,itakam batason ana nuna banbamcin nan sam,yanzu meye laifi don sunyi kwanxiyarsu ita da nujood din a nan

    “Ke kuma bakiji inna laila na kiranki ba tun daxu mijinki ya shigo kizo ku gaisa?” Kanta ta dauke sannan ta tura baki gaba,ita wannan miji da aketa cewa,ita an takurata fa da zancansa

    “Ni banji ba”

    “Bakiji ba amma na gaya miki ana kiranki a falo ko?” Nujood ta fada gudun kada tayi laifi

    “Ya isa naji,jeki falo nujood” anty deena ta fada tana wucewa ciki,ba musu ta miqe ta fice,ita kuma ta isa babbar wardrobe din widad,ta bude tana duba kayan dake ciki.

    Wata lafiyayyar gown ta atamfa ta dauko mata hade da mayafinta ta ajjiye mata,kusan duka kayanta a tsume suke da wani irin turaren kaya na itace mai matuqar qamshi da daukar hankalin duk wanda ya jishi,ta duba inda suka adana mata kayan ado ta fidda mata sarqa dan kunnen da abun hannu masu matuqar kyau,sannan ta dauko mata sabbin undies,saita juyo tana kallonta ganin wata guntuwar pad

    “Kin taba yin period ne?” Gaban widad ne ya fadi,saita daburce lokaci guda,saboda bada kowa take magana irin wannan ba idan ba ummunta ba,ganin ta rude sai anty deenan tayi murmushi

    “Ni kikejin kunya?,to ai kowa ma yana yi,kin taba yi ne?” Kai ta gyada.mata a hankali,sai anty deena din ta sauke ajiyar zuciya,duk sanda ta daga idanu ta kalli widad din sai taji fargaba da tausayinta,babu tabbacin zata yita zama a haka ba tare da komai ya hadasu ba,tasan halin mazan yanzu sarai wajen rashin haquri,duk da cewa yana da mata,amma sometimes masu matan sunfi fitina,saboda sunsan yadda abun yake

    “Sau nawa kikayi?,kuma yaushe ne yinki na qarshe?”

    “Sau biyu inayi,yau sati biyu” kai ta jinjina,saita koma gefenta ta zauna,cikin dabara take mata tambaya kan jinin haila da kuma wankan tsarki,cikin ikon Allah komai ta sani,saboda ba baya bace ita din wajen zuwa islamiyya,sannan ummu ta zauna da ita ta mata bayanin komai. Sosai anty deena taji dadin hakan,saita dubeta

    “Shiga bandaki ki sake wanka kizo ki shirya zaki je ki gaida mijinki,tunda mukazo baku gaisa ba,ko kun gaisa?” Bata kawo komai a ranta ba ta girgiza kai alamun a’ah,saboda dazun tana bacci ya shigo,sai fitarsa ta gani,yanzun kuma tana nan suna hira da nujood

    “Amma anty deena sanda zamu gidan hajiya fa nayi”

    “Wannan daban yake,duk sanda kikasan zaki wajensa ko kinyi wanka ki dinga sakewa kinji?,ki dauko kayan kwalliyar nan da aka kawo miki kiyi kwalliyarki ki saka sababbin kaya,maza tashi qanwata ta kaina” murmushi kawai tayi,ta tashin ta shiga bayi ta hada ruwa kamar yadda ta umarceta,tayi wankanta da kyau.

    Kusan ita ta shiryata,wani irin tururin qamshi na fita a jikinta

    “Muje na rakaki,amma zan dawo,kya taho ke kadai” kai ta gyada mata,bata wani damu ba,kawai tana jin dadin yadda tayi kyau abinta,suka jera da anty deena din tana mata wani karatu cikin hikima widad din na jinta.

    Daga dan nesa kadan da part din nasa ta juya,ita kuma widad din ta wuce tana dosar wajen.

    A darare,cike da baqunta da kuma tsoro,kasancewar a sannan sha daya kusan na dare ta murda handle din falon,saidai a kulle ta jishi,sai ta saka hannu tadanyi knocking,tana rayawa a ranta indai ba’a bude ba tafiyarta zatayi,to amma me zata cewa anty deena?,tunda tayi mata alqawarin zuwa,kuma bata iya qarya ba bare tace taje ta dawo ne.

    Dai dai lokacin da yake zaune qasan carfet,ya bude babbar farar takarda mai girma wadda ke dauke da map na garin kaduna,system dinsa na kunne hakanan akwai wani dan madaidaicin allo dake tsaye a gefe,yayi wasu zane zane da qananun rubuce rubuce da shi kadai yasan ma’anarsu,akwai babban aikin da yake tunkara,wanda yakeson gabatar dashi a sirrance,kamar yadda ya saba,kusan nasarar aikinsa kenan,a duk sanda zai gabatar da aiki na kama masu laifi da sauransu,yakan shirya komai a boye ne,dagashi sai amintattun sa irinsu samuel,sai lokacin gabatarwa yayi sannan.

    Idanunsa daya tsurawa takardar yana karantar map din ya daga yana duban qofa,yana tunanin hafsa ce,saboda ta kirashi taji ya dawo ba jimawa,to amma kuma knocking din ba irin nata bane,sai ya miqe a hankali ya juya allon,ya kuma kifa takardar,ya matsar da butar coffee din da yaketa sha a madadin abinci ya nufi qofar.

    Tuni fuskarta ta soma narkewa da tsoro,ta sake daga hannu cikin saarewa zatayi bugun qarshe ya buda qofar,iska mai sanyi da taushi dake kadawa a gurin ta yayibo dukka qamshin dake jikinta ta jefo zuwa hancinsa,dai dai sanda ya sauke kallonsa ga baby face dinta,fararen idanuwanta tarwai a haske wajen hadi da hasken falon daya sake haske fuskarta.

    Idanu ta zuba masa kamar zata saki kuka,shima idanun ya zuba mata,sai kuma ya janye gefe yana bata hanya,tsaiwa tayi kamar ba zata wuce ba,ta wurga idanunta ta gefensa tana hango cikin falon,tanaskn tava da mutum ko su kadai ne?,hango system dinsa da tayi sai ranta ya bata bashi kadai bane,wannan ya bata sukunin rabawa ta gefansa sosai ta wuce zuwa ciki,tun daga ranar da ummu ke gargadinta da kebewa da duk wani namiji ko kusantar inda suke bata qara bari sun hada inuwa da kowa ba,nan nan kusa kuma data sake tsawatar mata fiye da baya,watanni uku baya sanda ta fara period,ta sake jadda da mata batun.

    Wata ajiyar zuciya ce ta subuce masa,yayi tsaye a wajen kamar mai jiran wani,saidai yana shaqar qamshin ne da yayi masa dirar mikiya,hannunsa ya miqa ya maida qofar ya turata,widad dake zaune a darare a qasa tadan fidda ido waje kadan,kai…..ya zai rufesu su biyu?,saita tsirashi da idanu sanda yake takowa zuwa ciki,tana masa kallon tuhuma.

    Yana shirin zama suka hada idanu,farare sol din idanuwanta suka hadu da nasa manyan idanun,sai yadan lumshe nasa kadan,ya janyo computer dinsa gabansa yana cewa

    “Bakiyi bacci ba?” Kai ta gyada a maimakon ta amsa masa,sannan tace

    “Ina wuni?”

    “Kin yini lafiya?” Ya amsa mata yana daddanna system din ba tare da ya sake dubanta ba

    “Lafiya lau,dama anty deena ce tace nazo na gaisheka,wai bamu hadu ba dazu” yadda tayi maganar cike da quruciya da kuma sakalci shigen na yaran fari ya tilasta masa daga kai ya kalleta,suka sake hada idanu a karo na uku,qaramin murmushi ne ya subuce masa,kallonsa take kanta tsaye kamar mai masa kallon tuhuma,ya karanci me take nufi a cikin zancanta,amma yana sa yaqinin ita din bata fahimci komai ba,ta taho abinta ne gaba gadi

    “Anty deena ta kyauta,kinga ta fiki kirki,sai ita tayi tunanin kizo ki gaida mijinki” ya bata amsa yana sake maida hankalinsa ga system din nasa

    “Uhmmm” ta fada cikin rashin sabo da kuma baqunta.

    Coffee din gabansa ya tura mata yana sake kallonta,saita girgiza kai alamun a’ah,saboda ummu ta hanata karbar abun hannun maza,yana nan kuma daram a kanta bata manta ba,bai sake cewa komai ba sai kawai ya miqa hannunsa,ya jawo allonsa yaci gaba da aikinsa,abun da ya dauki hankalin widad kenan,ta dinga binsa da kallo

    “Dama malamin makaranta ne?,amma kuma nujood tace mata har bindiga ce dashi,to amma wa yake koyawa karatu bayan shi kadai ne a dakin?,inama zai dinga koya mata,tayi missing makaranta da karatu sosai,tanason karatu” ire iren wadan nan tunanukan ta dinga yi,har sai da taga aikinsa yakeyi sosai cike da qawa zuci,ta dan fara motsawa,so take ta koma,amma kuma tasan ba zata iya fita ita kadai ba,saidai ya rakata,amma kuma ta kasa buda baki ta gaya masa.

    Marker din hannunsa ya ajjiye yana fesar da iska daga bakinsa,yayi taku biyu baya a hankali,sannan ya duqa dab da ita,idanu suka sake hadawa,sai ya kauda kai ya soma zuge jakar dake aje a gefanta,wasu tsofaffin takardu ne da yasa samuel ya kawo masa su zai duba wani abu a jiki,yasoma zarosu,sai tsanya tayi tsalle ta biyosu har guda biyu,daya ta fada gefe dayar kuma kai tsaye ta fada jikin widad.

    Gigitaccen ihu data saki ya sanyashi watsar da takardun hannun nasa,kafin ya ankara tayo kansa tana tsalle gami da kiran wayyo Allah,wayyo ummu,taso rudashi amma ya tattara hankalinsa waje guda,saidai duk yadda yakeson dawo da ita nutsuwarta widad batasan yana yi ba,mayafi tuni ta cillar dashi,dankwali ma ya zame,lafiyayyen baqin gashinta dake fitar da qamshi ya tarwatse.

    Suciyarsa tayi wani mugun bugawa sanda ta shige jikinsa tana,sassalkan gashinta ya wanzu a fuskarsa,ihu take da zazzaqar muryarta dake cike da tsoro tana fadin ya cire mata

    “Calm down,ki nutsu,tsanyace fa kawai” ya fada muryarsa na dan rawa kadan,saidai ko daya bata jishi ba,tsoro ya cika kwanyarta a lokacin.

    *AREWABOOKS:HUGUMA*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/27, 10:37 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*
    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 45

    Arubuce Ta Ke 45

    Page 45

    “Barka da dawowa oga,tun wancan satin muketa zuba idanun dawowar ka,har mai gida yana tambaya” miskilin murmushi ya fita a fuskarsa

    “Naso dawowa,to amma ban gama shirye shirye bane,mun sameku lafiya?”

    “Lafiya sumul oga,ya hanya?,ashe an samu qaruwa?,to Allah ya sanya alkhairi,yasa abokiyar arziqi ce” bala mai gadi ya fada yana murmushi

    “Ameen”ya amsa masa a taqaice,sai ya zagaya da sauri ya soma budewa widad qofa yana fadin

    “Madam barka da rana” nauyi ya saukarwa abbas,da alama bala baisan qaramar yarinya bace yake gaidata,duk da ya bude motar bai damu ba yaga ta sake maimaita gaisuwarsa,sakato widad tayi cikin rashin sabo,wai yau ita ake gaisarwa?,ita da take gaida jama’a?

    “Ana magana” abbas ya fada yana cire belt seat dinsa,maimakon ta amsa saita maida masa gaisuwar,saboda rashin ganin dacewar ta amsa din,amsawa yayi ya kuma bisu da addu’ar zama lafiya da zuri’a ta gari,ita dai tana jinsa ba tare data amsa ba.

    Muqulli abbas ya miqa masa sannan yace

    “A shigo min da kayan qofar parlor bala”

    “An gama oga” ya fadi yana karba da hannu biyu

    “Muje” ya sake fadi yana duban inda widad taja ta tsaya,tana kuma bin gidan da kallon baqunta.

    Wata siririyar hanya suka bi,sai gasu qifar wata qaramar baranda mai kyau dake dauke da wata qofa mai dam fadi,yasa key ya bude qofar ya shige,ta bishi a baya,kamar za’a ce kettt ta zura da gudu.

    Madaidaicin falo ne amma ya qawatu matuqa,akwai qofofi guda uku a cikinsa na bedrooms guda biyu,daya qofar kuma ta kitchen ce sai dining area,sai qaramar qofar da zata fiddaka bayan gidan.

    Qarasawa yayi gaban daya daga cikin dakunan ya buda daya

    “Ki shiga nan kiyi wanka ki huta” bata iya amsa masa ba,sai gaba datayi zuwa qofar dakin tana raba idanu,turqashi,yau fa ake yinta,a wanann dakin zata zauna ta rayu ita kadai?,abinda yake nufi kenan?,ga gidan ta fahimci babu wadatar hasken rana,duk da cewa yammaci ne amma alamu sun nuna hakan,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta sanya kanta cikin dakin,dab da zata shige yace

    “Ki rubuta duk abinda kikeso,zan aiko a karba sai a kawo miki” sai a sannan ta samu daga masa kai,qwalla tana cika mata idanu,har yayi gaba ya dakata,ya juyo a nutse ya sanya idanunsa cikin nata

    “Me ya faru?”ya tambayeta yana kallonta,cikin jajircewa tayi qoqarin maida qwallar data cika mata idanu

    “Tsoro nakeji”ta amsa masa kai tsaye

    “Tsoron me?”ya tambayeta cikin mamaki, maimakon ta amsa masa saita maida dubanta ga dakin da ko qwan wutarsa ba’a kunna ba,saboda haka ya danyi duhu,gyara tsaiwarsa yayi,tana jin tsoro,to amma kuma baisan me zaiyi mata ba,hakan yana nufin saidai suyi sharing daki ita dashi?,kai ya girgiza kadan
    “NO” ya amsawa kansa,sai yanzu ya tuna da dan banzan tsoron da take dashi,ya manta the first time he saw her…ihun kyankyaso taketa yi,harda cire dankwali,takawa yayi ya matsa zuwa inda take tsaye,ganin ya nufota ta tuno da wani abu,tayi hanzarin jaa da baya a tsorace,har abun yaja hankalinsa,yadan dubeta kadan sannan ya dauke kansa,wannan bayan tsoron su kyankyaso hala harda tsoron mutane ma tanayi?.

    Qwan wutar dakin ya kunna,haske ua gaurayeshi,abinda ya rage mata tsoron dakin kenan,ya fita a dakin ya bata waje yana cewa

    “Sai anzo an share dakin,akwai qura” saboda sanda hafsata ta tashi tafiyarta a birkice ta barshi,shi kuma takaici yasa ko takan dakin bai sake bi ba tunda ta fita daga ciki.

    Sai data tabbatar yabar wajen sanann ta saka kai cikin dakin,ta tsaya tana duban komai,a hautsine yake,ji take yi ba zata iya zama ba,don kafin tafiyar latifa ta koya mata yadda ake gyaran bedroom xuwa falo,kuma babu laifi hannunta yadan fada,ta janyo jakarta zuwa tsakiyar dakin tayi mata waje.

    Zama tayi tana qarewa dakin kallo,idanunta fal hawaye,ta rasa qwarin gwiwar gyaran dakinma gaba daya,tana jin kamar an dauketa daga duniyar ta an kawota wata duniya ta daban.

    Bata tashi ba sai da aka kira magarib,ta miqe tana kame jikinta waje daya,saboda dakin ya mata datti,kasancewar bata taso ta saba zama cikin dauda haka ba,koda yaushe zaka samu sassan ummu qal qal,ko tsinke bata bari ya sauka,shi yasa basa shiri da jikokinta,don da zarar kazo ka zauna ta fuskanci kai dan bata guri ne yanzu zata koraka,widad dince kawai keyin yadda takeso a sassan ba tare data hanata ko tace mata komai ba.

    Toilet din ta shiga tayi alwala,tazo ta shimfida dankwalinta ba tare date nema abun sallah ba ta tada sallah,ko da ta idar tana zaune a wajen,har zuwa sanda aka turo qofar dakin,ta waiwayo a tsorace,saita zuba masa ido sanda yake shigowar,tsoro na kamata,a yanzun ya canza shiga,shirt da trouser ne a jikinsa da suka dace da jikinsa,suka fidda qirar jikinsa dake tafe da tsaho da murjewad jikin kadan,don ba zaka kirata qiba ba.

    Ido ta lumshe,tana jin dadin qamshin turarensa har qololuwar ranta

    “Kinyi sallah ne?” Kai ta gyada masa ba tare data iya kallonsa ba,sai ya dauke idanunsa daga kanta ya kalli agogon hannunsa

    “Zan dan fita…..” Tun kafin yakai qarshe ta daga manyan idanunta ta watsa a kansa,haka kawai yaji nashi idanun suna lanqwashewa zuwa lumshewa,kafin ya budesu ya azasu a kanta,har zuwa sannan manyan fararen idanunta suna kanshi,ta yaya zai fita ya barta a wannan gidan ita kadai?,duk da bata da tabbacin ita daya ce cikin gidan gaba daya,amma itakam ko dakin ummu bata yarda ta zauna ita kadai,inaga gidan gaba daya

    “Bazan dade ba zan dawo,za’a knocking za’a kawo abinci,saiki bude ki karba,idan kuma wani abu ya taso ki kirani a waya” wani mugun tsoro ne ya shigeta sanda ya juya yana ficewa,kuka sosai yazo mata,ta cure waje guda tana cusa kanta tsakanin qafafunta

    “Wayyo ummu”ta fada muryarta can qasa wadda ke cike da kuka,sun kawota inda bata da kowa,kamar basa sonta,itakam meye tayi musu?,sai taci gaba da rera kukanta a hankali,har zuwa sanda taji kiran sallar isha’i ta miqe ta bada farali,ta sake komawa yadda take.

    Tana jin anata knocking kamar yadda yace amma ko yunwa zata kasheta bata jin zata iya miqewa zuwa falon har ta bude,tana jinsu har suka gama bugunsu suka tafi,saita sake sakin kuka tana takurewa waje daya.

    Lokaci lokaci tana duban agogo tare da fadin

    “Allah kasa ya kusa dawowa” saita sake maida kanta tana sharar hawaye,har kusan awanni uku babu shi babu dalilinsa.

    A karo na barkatai ta sake daga kanta don kallon agogo,saidai hasken farfajiyar gidan ya hasko mata mage dake tsaye jikin window din dakin nata tana kada jela,wani mugun tsoro da razani ya shigeta,take jikinta gaba daya ya fara rawa,hawayen idanunta suka ninku,ta fara karanta ayatul kursiyyu a rarrabe saboda yadda bakinta yake rawa,a duniya babu abinda ta tsana take mugun tsoro irin magen,don saboda ita kowa na gidan ya haqura da ita,sabod koda ka kawota sai ummu ta sanyaka ka maidata inda ka daukota.

    A hankali magen ta soma kankarar glass din jikin window din kamar me neman hanya tana kuka mieeeuuuu mieeeuu,ba abinda yaxo kwanyar widad illa ga magen har ta shigo ta fada mata a ciki,take ta saki wata qara hade da kuka.

    Sautin muryarta yakai kunnuwansa sanda yake tsaye yana knocking qofar falon,kusan sau biyar kenan amma baiji motsinta ba,har ya fara tunanin ko tayi barci ne?,sai kuma saqon muryarta ya riskeshi.

    Sosai yaji hankalinsa ya tashi,to meye ya sameta?,cikin hanzari da kuma gaggawa ya fara laluben keys din dake aljihunsa,ya fiddosu ya fara gwadaw jikin qofar cikin hanzari da zafin nama,har sannan ihunta na tashi saidai da yake harabar gidan tana da yalwa,babu lallai wanda ke can nesa kamar malam bala ya jiyota.

    Cikin sa’a ya samu key din,ya bude ya tura sannan ya shige da sassarfa zuwa dakin nata.

    Motsin bude qofar dakin ya zake dagula kissafinta,ya kuma sakata ta sake gigicewa gaba daya,a nata zaton magen ce ta bude window din

    “Calm down mana,ki nutsu,menene?” Ya jefa mata tambayar yana riqe da dukka kafadunta,idanunta da suka jirkice ta daga ta kalleshi,batayi wata wata ba ta shige jikinsa ta qanqamesa kamar yadda ta saba yiwa ummu,sannan ta daga yatsanta tana nuna masa window.

    Mutuwar zaune yayi,a yadda ta shige masa jiki gaba cikin ba zata,wani irin sanyi ya sauka a gabbansa, tashin farko kamar an zare masa laka,don matasan tudun qirjinta gaba daya sun hade da nashi qirjinsa,yana iya jinsu sosai,ya daga kansa kamar mai ciwon wuya ya waiwaya ga window din,dai dai sanda magen tayi tsalle ta sauka daga window din,take ya fahimci ainihin dalilin rudewarta,sai ya dawo da dubansa kanta yana qoqarin zareta daga jikinsa,tare da fadin

    “Am beside you,calm down, mage ce fa,look there,she’s already gone” ya kuma fada yana qoqarin tsaida fuskarta tsakiyar tafin hannunsa tare da qoqarin lalubo qwayar idanunta don bata qwarin gwiwa.

    Sam taqi ganewa abinda yake fadi din,sai ya tuna abinda ya faru washegarin randa tazo gidan,don haka ya buda hannayensa ya sanyata cikin qirjinsa ya rufe,wata qatuwar ajiyar zuciya tana subuce masa.

    Dukka idanunta ta fidda waje kamar zasu zazzago,gabanta yayi mummunar faduwa,zai kuma?,irin ta ranar nan?,me yasa shi din dan iska ne?,take wata huduba data baro bauchi da ita ya fado mata,cikin dan qaramin qarfinta da bai taka kara ya karya ba ta saka hannayenta duka biyun tana qoqarin tureshi,ko kusa ko alama baiyi gezau ba,amma yaji abinda take shirin yi din,haka kuma yake buqata,sai yaja da baya yana kallonta.

    Kuka sosai ta fashe dashi,kukan takaici da baqincikin rungumeta da yayi,wannan wanne irin iskanci ne,haka kawai sai ya dinga taba ta?

    “Ya isa,ta tafi nace” ya fada calmly yana kallon yadda sumar kanta ta biyo ta gefan fuskarta,kamanninta suka fita sosai,fuskarta tayi jazur saboda kuka.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/6, 3:13 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 30

    Arubuce Ta Ke 30

    Page 30

    Anty deena ta ankara da yadda taketa narai narai da idanu,kadan take jira ta fara sakin ruwan hawayen nata,murya qasa qasa ta yadda ba wanda zaijisu tace

    “Haba mana widad,so kike ummu ta gani hankalinta ya tashi?” Kai ta girgiza tana kallon idanun anty deena da golden eyes dinta

    “Okay,maza hadiye,hadiye kinji qanwata” kai ta sake gyadawa,sannan aka fara daukan hoto.

    Gaba daya ji yayi ya qosa ayi a gama,murya can qasa yace da muhsin

    “Please muhsin,am tired wallahi” murmushi yayi,sau tari yana bashi dariya,bai taba ganin dan police wanda bai jure hayaniya ba irinsa

    “Okay” ya fada yana dagawa widad hannu,a hankali ta qaraso wajen tana kauda idanunta daga kallon abbas,haka kawai idan ta kalleshi sai taji gabanta ya fadi

    “Maza kusa ayi muku ku biyu” wani irin tsoro ya kamata,gabanta ya tsananta faduwa,sai ta narke cike da tsoro tana kallon uncle muhsin,wanda shi sam baima san me takeyi ba

    “Matsa widad lokaci na qure musu” anty deena ta fada,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta fara takawa zuwa kusa dashi,nesa kadan dashi ta tsaya,saida mai hoton yayita magana da taimakawar gargadin da anty deena ke mata da idanu ta sake matsawa aka dauka

    “Enough please” ya sake fada

    “Dama ai an gama” suraj ya amsa wannan karon yana dariya,sallama sukayi dasu ummu,akwai yiwuwar su kwana a kano,duk da babu tabbas, uncle muhsin keson hakan,saboda akwai walima daya shirya musu.

    Tun daga wannan lokacin gaba daya ta sake zama sukuku,ita gaba daya komai ya kwance mata,hakanan banbarakwai take kallon komai,daga qarshe dai a daki ta qule ta qarasa yininta,duk kuwa da sabgar da ake cikin gidan.

    Da daddare kuwa bata yarda ta kwana da kowa ba sai a bayan ummu,kowa tsiyar ai dole su rabu yake mata,wannan ya sanya zuciyarta karyewa ta kuma soma kuka sosai,da qyar ummu ta rarrasheta.

    ********Washegari tun da safe anty madina ta aiko kiranta,tana sanye da dogon hijab da ummu ta fidda mata,ganin cewa a yanzun wani nauyi ya hau kanta,kuma gidan akwai ‘ya’yan baffaninta maza,ga kuma baqi maza still ‘yan biki da basu kai ga tafiya ba.

    A kitchen ta taddata tana ta hidimar hada abincin safe,sai ta waiwayo tana kallonta

    “A’ah,ya haka?,bakiyi wanka ba dama?” Baki ta turo gaba a shagwabe tace

    “Anty madina duka duka yaushe garin ya waye?,kuma Allah an fara sanyi fa” rai anty madina ta bata sosai

    “A’ah,daga yau sai yau,kada na sake gani,idan akace mace tana da aure da wuri take wanka ta gyara jikinta kinji ko?,ta fidda kayanta tayi kwalliya sosai” kai ta gyada a sanyaye,ita dai komai sai ace aure aure,duk an takurata da kalmar nan.

    “Shiga dakina a hankali kada ki tada min abba,akwai turarenki da kika bari jiya saman mirror,ki dauka ki feshe jikinki sosai,sai kizo zan aikeki” amsawa tayi da to,don ita badai qauna da turare ba,ta wuce dakin anty madinan.

    Ba jimawa sai gata ta dawo,tana ta zanga qamshi kuwa,ta nuna mata wani baske tace

    “Dauki maza kikai sitting room din kawunnanki” ba tare data kawo komai a ranta ba ta amsa da to,ta dauki kwandon tayi ficewarta,tana tafe tana tsayawa magana da mutanen dake mata magana a hanya,cikin sauran baqi na gidan,har ta isa qofar setting room din.

    Jim tayi tana duban baqin half cover din dake qofar setting room din,wanda keta sheqi

    “Waye ma to a ciki?” Ta tambayi kanta,bata sani ba don haka ta tabe baki,cikin wannan d’arin d’arin nata da rashin sabo da maza ta saka kai ciki tare da yin sallama.

    A lokacin kansa yana duqe a qasa,yanata trying number hafsat ce,wadda tunda ya taho basuyi waya ba,duk kiran da zaiyi sai ace masa is switched off.

    A hankali ya daga kansa yana motsa labbansa tare da amsa mata sallamar,idanuwansa suka fada a kanta sanda take takowa kamar mai takatsantsan kada ta taka kwalba,baby face dinta dake tsakiyar blue black din hijab dinta ta fito fes,qananun gashinta masu santsi dake kwance gaban goshinta sun sake qawata fuskar,dan qaramin bakinta me red lips ta dan tsukeshi waje guda,fuskarta sam babu fara’a,sai ya lumshe idanuwansa kana ya maidasu qasa ga hannunsa inda wayarsa ke riqe,shidai baisan me hajiya ta hango ba data zabi ya auri qaramar yarinya har haka,kyau?….ko kuwa me hajiyan ta kalla?,shi kansa bai sani ba.

    Tazarar wasu inches ta bayar a tsakaninsu ta ajjiye kwandon,tana daga tsugunne ta gaidashi da siririyar muryarta

    “Ina kwana?”

    “Kin tashi lafiya?” Ya amsa mata yana sake daga kanshi gareta a karo na biyu,bata amsa masa ba sai miqewa da tayi tsaye ta soma shirin ficewa a setting room din,saboda gaba daya a tsorace take,already ummu tayi mata horon tsoron maza sosai da shan inuwa daya dasu,a yanzun kuma bata gama sanin muhimmancin abbas din ba

    Da kallo yabi bayanta,dariya ta taso masa can qasan ransa,ta yaya cikakkiyar budurwa mai shekaru da wayo ta aikata haka?,sai ya gyara zamansa kadan yana lalubo sunanta

    “Widad” ya furta a tausashe,tsayawa tayi cak gabanta yana faduwa,dama yasan sunanta wai?,ta tambayi kanta

    “Zo mana” ya sake fadi,abinda yasa ta waiwayo kenan,suna hada idanu duk wani kuzarinta yayi nasa waje,sai ta narke fuska

    “Ummu zata yimin fada idan na dade” kai ya girgiza yana lumshe idanunsa kamar yadda yake a al’adarsa

    “Ba zaki dade din ba,yanzun nan zaki tafi” kallonsa takeyi,sai ya jinjina mata kai alamun tabbatarwa,don haka ta dawo a hankali,ta samu nesa dashi ta zauna.

    Tattara dukka hankalinsa yayi ya zuba mata idanu,yanzun ta ina zai fara mata bayani ma?da wanne harshe zai mata magana ta fahimci abinda yake cewa quruciya duk ta baibayeta?,a qa’ida babbar budurwa ce yanzun zaune a gabansa,sai yafi sanin yadda zai dinga handling abubuwa har su saba da juna.

    Motsawa tayi kadan tana hade rai saboda yadda yake kallon nata ya sake takurata,ya fahimci haka sai ya aje wayar hannunsa,a bisa tilas ya arawa fuskarsa murmushi sannan ya fara magana

    “Ummu ta gaya miki an daura miki aure ko?” Kai ta gyada tana kallonsa

    “Good,daga yanzu na zama yayanki,na zama kuma abbanki,zamu tafi dake can zan kaiki gidana,zamu tafi tare,kema gidanki ne duka,zakiyi duk abinda kikeso a ciki,kina so?” Idanunta masu tsananin haske da ratsin gold color ta fara rarrabawa a tsakanin nasa idanun,sai ya kafeta da idanu sosai yana kallon yadda suke juyawa,yadda ta mele baki ta kuma tabe fuska hadi da lumshe idanunta,eye brows dinta masu tsayi suka hade waje guda sannan ta sake bude idanun warrrr a kansa yasa tsigar jikinsa ta zuba

    “Bazan dade ba zaka dawo dani wajen ummu?” Ajiyar zuciya mai nauyi ya sake yana dan murmushi kadan

    “In sha Allah,nima daga yau na zama yayanki ko?”

    “Uncle dina dai ko?,naji nujood na cewa sunanka uncle abb….” Kasa qarasa sunan nashi tayi,tana jin kada tayi abinda bata kyauta ba,murmushi ya subuce masa ba tare da ya shirya ba,har fararen haqoransa suna bayyana,ya fuskanci nauyin kiran sunan nasa take

    “Uhnnnn,uncle abbas” sai ta gyada kanta tana hade hannayenta waje guda,yakai duba ga hannun nata,tsararren jan lallen nan nata yana nan tas saman hannunta,ya zuba masa idanu kamar mai karnatar taswirar zane,lallai akwai hikima mai yawa ga masu yin lalle,har da suke iya tsara zane haka ya bada wani kala da nau’i mai kyau.

    Rai ta hada sosai ganin yana ta kallon hannun nata, saita zare hannuwan nata zuwa cikin hijabin tana sake qudundunewa waje guda,ya dauke kansa yana maidawa ga dan qaramin leda yar mitsitsiya daya shigo da ita,sai ya dauka ya tura mata

    “Wannan waya ce,ki cewa ummu a kunna miki,akwai komai a ciki,zan dinga kiranki,sauran kuma kudi ne,duk abinda kikeson siya ko kike son amfani dashi ki dauka a ciki,kada ki sake tambayar kowa yayi miki wani abu” murna farinciki da kuma mamakin bata waya da akayi ya lullubeta,to amma kuma tana tsoron kaiwa umnu kayan tace wani ne ya bata,duk yadda take zumudin wayar saita noqe

    “Wallahi ummu zata dakeni,zatace waye ya bani” murmushin dole ya sake subuce masa

    “Kice uncle abbas ne,idan ma bata yarda ba kice a kirani,bazata miki fada ba” sai ta matso kadan,ta dauki ledar tana cewa

    “An gode,Allah ya saka da alheri” girma yaji addu’ar tayi masa,sai ya bita sa kallo kawai harta fice,ya maido dubansa cikin falon yana sauke gauron numfashi,tsahon zamansa da hafsa bata taba fadin haka ba,duk girman kyauta idan yayi mata

    ‘An gode’ shine iya abinda ta iya fade kenan,bata buqatar cin komai,so yake kawai yaga sun dauki hanyar bauchi,to amma babu dadi su kawo suga baici komai ba,gashi ya baro baqi a masauki,don haka ya fidda qaramin flask din tea dake cikin kayan,ya hada tea.

    A gaggauce yake sipping,yana tsaka da kurba uncle muhsin yayi sallama

    “Aah ya haka bakaci komai ba?” Ya fada bayan sun gama gaisawa yaga abbas na ajjiye cup din

    “Sauri nake ne,ya kamata mu dauki hanya da wuri,saboda kamar gobe nakeson komawa kaduna,akwai gyare gyare da za’a yi acan,a office ma kuma ina da ayyuka da ban gama settling nasu ba bare na dora da nawa,ban taba aiki a kaduna ba sai wannan karon,kaga ina buqatar maida hankali na sauke nauyin al’umma dake kaina” kai muhsin ya jinjina

    “Gaskiya ne,to shikenan,muje kayi sallama dasu saimu fita tare,zaka saukeni a al-hamsad tower zan shiga wani shago akwai abinda nakeson dubawa,zuwa azahar an kammala walima in sha Allah saiku wuce kafin la’asar”

    Sai data gama nuqu nuqu da fargabar nunawa ummu kayan daya bata,da taga ba zata iya ba saita wuce sassan anty madina,ta sameta ta fito a wanka,don haka ta zauna cikinsu walid dake falo suna kallo harta gama shiryawa ta fito ta sameta

    “Widad,har ya tafi baqon?” Kai ta gyada tana miqa mata ledar

    “Wannan ya bani,sai da nace bazan karba ba ummu zatamin fada,yace wai ba zata min komai ba” dariya ta subucewa anty madina

    “Taso nan” tace da ita bayan ta karba ledar,suka matsa gefe can inda yaran ba zasu jiyosu ba,zama tayi ta zaunar da ita a gefanta

    “Shi wannan ai ba baqo bane yanzu,mijinki ne kin gane?,kamar ni da abban walid,kamar ummu da alhaji,kin gane?” Tadai jita,amma bata gane mai take nufi ba,ita kallon abban walid da anty madina takeyi a mazaunin yayanta ne,ummu kuma alhaji babanta ne

    “Bari muga me miji ya baiwa matarsa kyautar farko?” Ta fada tana dariya,ta zazzage ledar,kwalin kyakkyawar waya qirar samsung ta fado hade da sabbin kudi a miqe fil dasu

    “Lalalala,ah lallai wannan diya tamu da goshi take,tun yanzu?” Dariya ta kubcewa widad,haka kawia taji kunya ta kamata,saita sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta anty madina na tayata dariyar

    “Zankadi,bude idonki ki gani” saita bude idon da sauri,ba qarya wayar ta hadu,take taji murnarta ta qaru,qaunar wayar kuma ta shigeta,suna shirin kunnawa momma tayi sallama falon

    “Wa’alaikumus salam,qaraso momma,duk sun cika falon” anty madina ta amsa tana qoqarin tattare kudaden waje guda

    “Wannan sabbin kudi fa,ko na liqi ne da kikayi canji?,aisai ki adana abunki,bikin da babu ko kidan qwarya bare DJ,kamar wata amaryar buzuzu”

    “Uhmmm,momma kenan” anty madina ta fada tana dariyar yaqe

    “Albarkar aure ai ake nema,bare widad ma nawa take?,ina qawayen ma bare ace za’a zauna yi mata irin wannan bidi’ar?,ni ban canzo kudin komai bama,angonta ne ya bata hade da wayar?” Sai a sannan idanunta yakai kan wayar

    “Kai!” Ta fada cikin ranta,tasan wayar fes,irin wayar da deena tace yallabai(mijinta) ya kawo mata tsarabarta ne daga india a wannan satin daya dawo daga course daga can

    “Tofa,da gamo da kasawa,kada fa muna nan mun shanya baki muna kallonta yarinya qarama amma ace har tasan komai,kodai ta bada wani abune aka bata wannan tukuicin haka?” Momma din ta fada tana kama baki, zuciyarta cike fal da qyashi da baqinciki,don ko yanzu data baro sassanta maganar da suka gama kenan da batulu matar babanta da ‘yan uwanta da basu tafi ba,duka dai akan widad din,suna ganin komai anyi mata fiye dana ‘yan uwanta,ana kuma wuce makadi da rawa a kanta saboda tana da daurin gindin ummu,sun manta kowanne aure da irin nasa nasabin yake zuwa,labarin lefe data samu,manyan mutanen da suka halarci daurin auren da kuma kayan da aketa hadawa za’a tafi jere dasu kawai sukeyi,banbamcin da ake nuna mata akan nasu ‘ya’yan yayi yawa.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 90 16 59 91

    *Zafafa biyar kadai keda sinqin nau’ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci guda*🤝😄

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/23, 1:39 PM] halimatuabidah: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 36

    Arubuce Ta Ke 36

    Page 36

    Yadda ta shige masan tamkar zata koma cikinsa,gaba daya ta kasa gane me yake fada,sai kawai ya buda hannayensa,ya kuma rungumeta sosai a jikinsa,yayi mata riqon tsauri ta yadda ba zataci gaba da tsalle ba.

    A hankali ta fara samun nutsuwa,kukanta ya fara ja baya,sai a sannan kuma ta tuna ajikin wani take,tayi wani irin zillo ta zame daga jikinsa,cikin tashin hankali hadi da wani sabon tsoron,tunda take tsahon rayuwarta ko yatsarta ba wanda ya taba riqewa,amma yau gata a jikin wani?,ta shiga uku?,yanzu shikenan ta zama ‘yar iska?,idan ta samu ciki ta mutu fa?,bata kyautawa ummu ba,sai sabbin hawaye suka barke mata,jikinta har rawa yakeyi

    “Tafiya zanyi” ta fada bakinta yana rawa,kafeta yayi da idanu yanason gane me ya tsoratata kuma dai?,kafin ya gama wannan tunanin aka fara knocking qofar,ya maida kallonsa ga qofar,kafin ya bada izini an murda handle din an shigo.

    Hafsat ce dauke da jug da cup,da farki idanunta naga abbas,sai kuma sabon qamshin da taji ya baibaye falon yaja hankalinta,a hankali idanunwanta suka sauka kan widad dake tsaye tana tsuma,jikinta yana rawa,kanta babu dankwali bare mayafi,dukka suna watse a qasa,ga hawaye shabe shabe kan fuskarta,gabanta yayi wani mummunan faduwa,abubuwa biyu suka bugeta lokaci daya.

    Zallar madarar kyau data gani kwance saman fuskar widad din,duk da shekarunta qananu,da kuma tunanin daya darsu a ranta a take a lokacin,abbas ya nemi tarayya da widad din,tunanin daya kusa sanyata zubar da kayan hannunta,jikinta duka ya dauki rawa.

    A nutse ya amsa mata sallamar,ya dauke kansa ya maida ga widad data fara yin gaba zata fice,har yanzu tana hawaye

    “Dakata” ya fada cikin salo na umarni,cak ta tsaya amma har yanzu jikinta rawa yake,tasan tata ta qare,tana shiga su anty deena zasu gane wani ya tabata.

    Inda ta yasar da dankwali da mayafin ya qarasa,ya dauko mata ya tsaya gabanta ya miqa mata yana kallonta,sannan yace da ita

    “Daura” jikinta na rawa ta karba din,amma ta gaza daura dankwalin,sai mayafin ta yafa kawai

    “Muje na rakaki” ya fada sannan ya waiwaya ga hafsat wadda ta yiwa kanta mazaunin dole don kada ta fadi

    “Ina zuwa” yace da ita suka fice shida widad din.

    Kuka sosai ta fashe dashi kamar qaramar yarinya,da gaske abbas neman tarayya da yarinyar yayi?,har zuciyar abbas ta fara qawata masa ita?,duk qoqari da jajircewar da taketa yi kenan tana neman tashi a banza?,ya akayi tayi saken da har yarinyar tasan tazo sashensa?,ba shakka sanyata akayi,tunda ‘yan uwanta suna nan,tabbas ba zata ba haka ta sake faruwa ba,sai ta miqe tana barin flask din kawai ta fito ba tare data bi ta kansa ba,idanuwanta har basa gani sosai saboda tashin hankalin da takejin kanta a ciki,a daddafe ta dinga laluba hanya har takai kanta sassanta.

    A gaba ya sanyata yana biye da ita har suka isa sasssan nata,ita ta fara knocking,tayi tayi shuru ba alamun za’a bude,sai yace ta matsa shima ya shiga tayata,amma shuru kakeji,saiya waiwayo yana dubanta

    “I think duka sunyi bacci fa” kai ta langabe tana kallonsa,idanunta na fidda ruwan hawaye

    “To a ina zan kwana kenan?,don Allah ka tashesu mana” ido yadan zuba mata na wasu sakanni kafin ya kawar da kansa,quruciyarta ta gaske ce

    “Ki koma ki kwana a can,da safe saina rakoki,lokacin sun tashi ko?” Ya fada cikin sigar lallami,saboda yadda yakejin kansa yayi week,bacci ma dai a taqaice yaji yana saukar masa.

    “Amm…..”

    “Ba’a musu da babba right?” Ya fadi cikin sigar tambaya yana ritsata da kallonsa,karon farko taji idanunsa sun dan mata nauyi,saita sadda kanta qasa,ya sake sakata a gaba kamar dazu suka koma,jikinta duk a mace, hankalinta a tashe,anty deena ce ta jawo mata,ta yaya zata kwana daki daya dashi?.

    Yayi mamaki sanda ya dawo yaga babu hafsat din ba dalilinta,sai ya tsugunna ya tattara komai waje daya ya adana,har a sannan widad na zaune a takure a waje daya,ac din dakin ya kashe gaba daya,ya rage fitilun falon,saiya kalleta

    “Muje ciki ki kwanta” fuska ta tattare waje daya,tanason cewa a’ah amma kuma batason yaga kamar ummu bata koya mata cewa ba’a yiwa babba musu ba,tunda gashi dazu ya fada,haka ta miqe tana biye dashi har cikin bedroom din nasa.

    Da ido take kallon komai,bedroom din nada wani irin weather mai saukar da nutsuwa,sassanyan qamshinsa ya kama dakin sosai,komai fari ne qal,kuma komai yana kan tsari a killace,saita haye kan sofa bed ta dunqule,shi kuma ya wuce bandaki.

    A ciki ya shirya cikin wasu silk pyjama sky blue,yayi brush ya feshe jiki da bakinsa da turarukansu

    “Zaki canza kaya ne?” Ya fada yana dan duban gefanta,cikinta ne ya bada qululu saboda tsoro,yana nufin ta cire kayan jikinta ta sauya wasu?,a dakinsa?,saita damqe jikinta waje guda kamar wadda ya taho zai rabata da suturarta,ta jijjiga kai da qarfi

    “A’ah,wadan nan nakeso na jikina” dariya taso qwace masa amma ya danne,a yadda take acting yasan lallai batasan meye cikakken ma’anar aure ba,to amma me yasa take tsoro haka,sai ya rabu da ita,ya jawo wayarsa da nufin kiran hafsat din yayi mata sai da safe,duk da baisan me ya fiddata daga dakin ba,ya tsammaci zatace zata kwana kamar jiya.

    Sau uku yana kiranta tana katse kiran,abun yadan daure masa kai,amma saiya tattara ya watsar,dare yayi,hutu yake buqata

    “Ki koma gado ki kwanta” ya sake fadi,kamar dazun dai a firgice tace masa a’ah,sai da yayi da gaske sannan ta kuma taga ya yibi filo da bargo yana shirin bar mata dakin sannan taji ranta ya sake.

    K’ofar tabi da kallo sanda ya fita,sai kuma ta fara baza idanu,dan banzan tsoron nan nata ya dawo,ji tayi kamar ta bishi,amma ba zata iya ba,curewa tayi waje daya ta lulluba har kanta,saita saki kuka,anty deena ce…..duk ita tace sai tazo,gashi nan sun rufe mata qofa,bayan sunsan ta fita,kewar ummu ta taso mata,ta dinga hawaye ita daya cikin filo,har bacci barawo ya saceta.

    A hankali ya bude qofar dakin,duk da akwai qarancin haske amma yana iya hangenta a cure waje daya,sai ya kada kansa ya wuce bandaki.

    Alwala ya daura ya dawo dakin,ya feshe jikinsa da turare ya sauya jallabiyyar jikinsa,ya taka a hankali zuwa gefan gadon,hannu yasa ya bubbuga saman filon a tausashe,ta motsa kadan kamar zata tashi,sai kuma ta sake qudundunewa,cikin muryar barci tace

    “Don Allah ummu,ba’a idar ba,yanzu aka tayar” shuru ya danyi yana nazarinta,ta kwabe fuska gaba daya tana tura baki gaba a shagwabe,har kuma a hankali ta saki bakin nata,da alama ta koma bacci sosai.

    Kai ya girgiza kawai,bai hango komai ba banda zallar quruciya a tattare da ita,shikam baisan ya al’amuran zasuci gaba da tafiya ba,bai hango sauqi ba,sai nauyi daya sake hawa kansa,sai ya juya a nutse ya nufi qofa,yana kama handle din zai.bude ta bude idanunta a hankali, saboda yadda taji cikin jikinta ba’a gida take ba,saboda duk sanda tayi irin haka ummu saita takurata akan sai ta tashi koda ba’a tayar da sallar ba.

    Tana qyallara ido ta hangoshi,saita zabura ta miqe tana rarraba idanu,a nutse ya waiwayo ya kalleta,sai baice komai ba ya sanya kai ya fice.

    Sai data daina jin motsinsa sannan ta miqe a hankali cike da tsoro ta tura bandakin ta shige tayo alwalar itama ta dawo ta gabatar da sallar,har Allah Allah take ta idar ta fice zuwa wajensu anty madeena,tana idarwa bata ko tsaya addu’a ba tayo waje.

    Cak ta tsaya a qofar falon kamar zata saki kuka,ganin garin da duhu har yanzu,gashi dukka fitilun harabar gidan an kashesu,dan banzan tsoronta kuwa bazai barta ta wuce sashenta ba,saita koma.bakin qofa ta rabe tana maida qananun hawayen dakeson sauko mata,ba zata koma cikin dakin ba kuwa,a nan zata yita zama har sai gari yayi haske.

    Baiyi zaton zai sameta zaune a bakin qofa ba,don haka cike da kuzari da kuma hanzarinsa ya buda qofar falon

    “Subhanallah” ya fada da sauri yana kama murfin qofar ya riqe a hannunsa,sai kuma yadan dai daita yanayin fuskarsa yana kallonta

    “Me kikeyi a nan?” Mele baki tayi fuskarta a yamutse,da alama qiris take jira ta fashe

    “Ina kwana?,can zan koma,kuma wajen da duhu bazan iya fita ba” sai daya juya ya sake kallon harabar gidan,shi yasa aka kashe fitilun saboda yaron gidan yace sunata wasa da wutar kada su lalata qwayayen,qwayaye ne masu tsada da daraja

    “Basu bude ba suma,ki koma ciki sai rana ta fito” kai ta maqale a kafada,sannan ta miqe kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,ta koma saman kujera ta takure waje daya,bai sani bama ko hawaye take sharewa.

    Dakin ya wuce,bai jima ba ya dawo,ya haye saman doguwar kujerar daya kwana a kai,yaja bargonsa zuwa qugu ya rufe, lokaci lokaci yana dan daga idanu ya dubeta,yadda take curewa waje daya ta kwanta shine ke bashi mamaki,amma baice da ita komai ba.

    Wantsalowa tayi daga saman kujerar sanda agogo ya gama buga qarfe bakwai dai dai,suna hada idanu sai kuma ta koma dai dai ta zauna,fuska a narke take dubansa,cikin salo na roqo da magiya tace

    “Don Allah…..ka rakani,gari yayi haske fa?” Ido ya tsura mata na wasu sakanni yana kallonta,sai ya janye idanun nasa yana zame bargon jikinsa,daki ya sake shiga,bai jima ba ya fito yana gyara button na rigarsa

    “Muje” da saurinta ta sauko muryarta tabi bayansa,don kafin yakai qofa har ta kusa cimmasa,yadan sake binta da kallo sannan ya buda qofar suke fice.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/2, 5:28 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 41

    Arubuce Ta Ke 41

    Page 41

    Latifa ce ta fara gaidashi,sannan ta kauce ta basu waje,falon ya zamana iya su yasu.

    Cikin baqunta tadan motsa kadan tana gyara zamanta gami da hade jikinta waje daya,kamar yadda ummu ta koya mata duk sanda wani baqo ya shigo sassansu,koda kuwa cikin mazan gidansu ne yayyenta ‘ya’yan kawunnanta

    “Sannu da zuwa” itama fa fada kamar yadda su mimi suka fada,ba wani sakin jiki ko alamun sanayya a tattare da ita, yanayin da yayiwa hafsat dadi qwarai,ta kuma sake sanya idanu a tsakaninsu,tana kuma karantar yadda kowannensu ke nuna baqunta ga dan uwansa

    “Sannunki,kin wuni lafiya?”

    “Lafiya lau” ta amsa masa idanunta na a qasa,yayin da nasa hankalin yake kansu mimi,sai ya miqe dasu yana bare ma nawwara chocolate din daya shigo musu da ita.

    “Babu wani abu ko?” Yayi tambayar a wannan karon yana watsa idanunsa a kanta,ta girgiza kai da sauri

    “Ma sha Allah” ya fada yana kama hannun yaran,a sannan hafsat ta miqe,fuskarta fal murmushi

    “Amarya ki dinga sakin jiku mana kinji?,ba haka ya kamata ki marabci angon naki ba” sakato widad din tayi tana jin nauyin maganar hafsat din,zancan kuma yana mata girma

    “Ina zuwa bari.naje,ki shirya xamuci.abincin dare tare kinji ko?” Hafsat din ta fada tana danne dariya,yadda widad din tayi wuri wuri yayi mata dadi,bata amsa mata ba har ta fice.

    Sam batasan yana tsaye a wajen ba sai da tazo giftawa tana sauri don ta cimmasa saiji tayi an damqo hannunta,ya kuma jawota xuwa gabansa.

    Hannayensa ya sanya ya zage bayanta dasu,suka tsaya dab da juna suna ma juna kallon cikin idanu,ita ta fara janye idanunta,sabida bata fiya jurewa kallonsa ba,akwai wani irin kwarjini mai yawa cikin idanunsa,shi kuwa ci gaba yayi da.kallonta,irin wannan kallon yana tada masa feelings sosai a kanta,yana kuma karantar abubuwa masu yawa dake kwance a zuciyarta ta cikin idanun nata,saidai ya fuskanci ta koyi dabi’ar kaucema idanunsa din.

    Dan gyata tsaiwarsa yayi yana sake matsota kusa da jikinsa,duk da cewa ba irin wannan yanayin da scent din yake son samu daga jikinta ba…….zaya so ace tana fidda kalar launin qamshin daya daga cikin turarukan da yafi so,yake kuma siya ya ajjiye mata komai tsadarsu

    “Wai kin daina kishina ne?” Ya fada da wata irin cool voice,ita kadai tasan abinda ya saukar mata a zuciya,inda yasan yadda takejin zuciyarta a duk sanda yake magana kawai da wata macen,da wala’alla har ya mutu bazai sake kallon kowacce diya mace ba baya ga mahaifiyarsa

    “To amaryar taka ce naga bata iya komai ba,kaima kuma baka iya rainon da aka kawo maka ba” yadda tayi maganar yadan sansano sautin kishi a ciki,duk da yaso jurewa amma saida murmushi ya subuce masa,sai ya saketa kamar yadda taketa kiciniyar qwacewa daga hannunsa,yasan zata ce masa kada yara su gansu

    “Tunda gaki basai ki tayani rainon ba” baki ta tabe

    “Saboda ni ka aurowa ita?,yanzun ma……” Maganarta ta yanke sanda ta fuskanci gangancin da take shirin aikatawa,saita waske

    “Yanzun ma tausayinta nakeji,an aura mata tsoho” ta qarasa fada tana yin gaba,taku uku ya cimmata,sannan ya bata amsa

    “Tsohon ashe yayi.kasuwa,tunda har ya samo qaramar yarinya ko?” Cikin Zuciyarta sai taji kamar.magana ya gaya mata,don haka taja bakinta ga tsuke,bata sake saka.baki.akan magabar ba,gudun kada ta tafka shirme tana samu tana tsallakewa da qyar.

    Yana shiryawa yana mata magana cikin hikima akan ya kamata ra gyara dakin yaran dama nata dakin da kyau,baki ta tura,shi kome qoqarinka me yasa sai ya cika gyara?,sai yayi challenge naka?,duka ba hidimar dafa masa abinci ke cinye mata lokacin ba?,ita sai taji har ta qagu ya koma Kaduna,ta yadda zata samu ta miqe qafarta da kyau.

    Tana gama sallar isha’i ta shiga wanka saboda tuna alqawarin data daukarwa anty deena,data fito ta shirya cikin kayan bacci kai tsaye,wasu riga da wando ne kalan pink da suketa burgeta cikin kayan lefanta,dama Allah Allah take ta sakasu,tana gamawa ta maida hijab dinta tabi lafiyar gado tana hamma,yau ma a nan dakin zata kwanta tare da latifa,idan suka kwana tare sai tayita jin kamar ummu.

    Dai dai sanda take rufe bakinta sabida doguwar hammar bacci da taketa saki latifa ta turo qofar dakin,shigowarta kenan bayan ta maida kwanukan da sukaci abinci daki

    “A’ah,me zan gani?,yauma?” Ta fada tana kama baki,sai widad din ta waiwayo tana dubanta

    “Me nayi?”

    “Ke da zaki wuce ki tafi dakin mijinki?”

    “Dakin miji kuma umma latifa?,kamar wata ‘yar iska?” Tayi maganar tana maida kanta saman pillow ta dora da cewa

    “Yanzu da kanki kike cewa ma naje dakin wani” dariya taso qwacewa latifan,lallai da gasken gaske wauta da quruciya sun yiwa widad din yawa,saita qaraso gefan gadon ta zauna tana qoqarin fahimtar da ita.

    Sam widad din ta gaza kai hankalinta kan abinda take nufi,sai ma tubure mata da tayi kan babu inda zata,dai dai lokacin hafsat tazo kiranta tazo suci abinci,nan ma tace ta qoshi ba zata ba,ran hafsat din ya mata dadi,amma duk da haka a gaban latifa dashi kansa abbas din saita nuna bataso haka ba

    “Rabu da ita,yi serving dina” ya fada kansa tsaye sanda yake dan diban abincin kadan kadan yana baiwa nawwara a baki,wadda tayi dare dare saman cinyarsa,saita soma zuba masa abincin,amma bata rabu da zancan ba,don lallai ta nuna masa ita ba’a son ranta ba,har sai da yace

    “Will you keep quiet madam?,ko sai na saka gum dina na rufe miki bakin?” Ya fada yana jifarta da hararar wasa

    “Kai bakasan na fika farinciki da haka ba” ta fada cikin ranta,amma a zahiri bakin nata taha ta rufe,bata sake tashin zancan ba.

    *********sannu a hankali kwanaki suka fara tafiya,widad cikin gidan har a sannan tana matsayin baquwa,baquwar dake ganin kulawa da damuwa daga idanun hafsat,harma taje ganin matuqar kirkinta fiye dana ja’afar,yadda su mimi ke kiranta da mommy haka nan itama take kiranta dashi,tana mata kallon da takewa anty madina ne,tana kallonta a matsayin uwa ko wata babbar yayarta,gefe guda kuma sabo ne ya shiga tsakaninsu dasu mimi da nawwara,musamman mimin,a nan sassanta suke kusan yini.

    Idan ka samu widad din dasu mimi zakayi tunanin yayace da qannenta,kusan ko yaushe suna tare,sosai suke debe mata kewa,idan lokacin da zasu shiga kitchen yayi ita da latifa zasu shiga tare,to amma kusan fiye da rabin hankalinta yana kan yaran,don haka ba wani abun arziqi take tsaiwa ta koya ba.

    Ta bangaren abbas shima tana masa kallo daya ne,matsayin uncle muhsin take kallonsa,saidai wani bangare na zuciyarta haka kawai yake cika da tsoronsa,ta kasa sakewa dashi kwata kwata,babu fashi,a kullum zai shigo da safe yaji basu da matsala,ya sake dawowa da dare ya tabbatar da komai lafiya,zaman cin abinci dasu kuwa ko sau daya bata taba yarda ta zauna din ba,hakan yana yiwa hafsat dadi matuqa,yadda yarinyar je tattare kanta waje daya,take kuma dari dari da komai nasa,wannan shike haska mata lallai komai zai tafi mata a sauqi.

    To hakanan duk yadda latifa zata lallabata taje sashensa kona awa daya ne sai ta dawo taqi,sai tayi mata kamar bata ji ba,ta kwanta ta hau barcinta,tare suke kwana da latifa din a daki daya,gado daya,wannan yana debe mata kewar ummu qwarai da gaske.

    *******A nutse cikin takun nan nashi dake nuna zallar karsashi da lafiya da tsiyayyar qirar jikin da yake dashi yake takowa zuwa harabar gidan,kunnensa maqale da waya yana amsa kira,hannunsa daya riqe da key din motarsa.

    Sanye yake wani yadin kuftan mai kyau da daukar ido,anyi masa aikin hannu mai tsadar gaske,sosai kayan suka zauna masa,abbas din ba daga baya ba wajen iya saka manyan kaya,kowacce shiga daukansa takeyi,saika gaza tantance wadanne kaya ne suka fi masa kyau.

    A hankali ya zare wayar daga kunnen nasa yana katse kiran, hankalinsa yana kaiwa kansu, suna daga gefan farfajiyar gidan,mimi ce da widad,widad din na daga zaune gefan wata tukunyar fulawa,sanye take da wata doguwar riga mai santsi mai dogon hannu,tana hade da hula ne daga bayanta,bata saka hular ba,tadai saketa,lallausan gashinta mai santsi da tsaho yana matse cikin qaramin band,jelar ta buya ta bayanta,fararen qafafunta na slipper blue din slippers,color din dake matuqar fidda hasken fatarta.

    Mimi kedan garo mata ball,itama tana daga zaunen sai ta sanya qafarta ta maida mata,yau din tunda ta tashi bata da wani cikakken kuzari,shi yasa ma tace wa latifa ba zata shiga kitchen kallon girkin yamma ba,itama bata matsa mata ba,ta barta suka fito da mimi din,wadda hafsat ta tafi unguwa ita da nawwara,ta barta a nan,don qememe taqi binta,ba kasafai ta fiya damuwa da bin hafsat din unguwa ba,tafison zama da widad.

    Idanunsa ya janye dsga kanta ya nufi parking space,yana hangosu har sannan ta cikin mirror din,shi kansa a yau sai yaga babu wannan kuzari da kazar kazar din daya santa dashi,idanunsa ya kuma daukewa yana rufe motar ya tayar da ita ya fice daga gidan a hankali.

    A nutse yake tuqinsa kamar kullum,yana tafiya yana lura da abubuwan dake faruwa saman hanya,gidan hajiya ya nufa kai tsaye,don dama a yau din can yayi niyyar zuwa,sai dare kuma ya tsara zai fita daga unguwar.

    A hanya ya tsaya ya siyama hajiyan abubuwan da yasan tana sha’awa kamar yadda ya saba,sannan ya wuce,mintuna qalilan ya iso unguwar tasu.

    Tun daga farkon layinsu matasan da suka ankara da shigowar tasa suka biyo bayansa, mutum ne shi mai matuqar kirki tausayi da kuma taimako,wannan ya sanya masa farinjini sosai ga al’ummar unguwar,kamar ko yaushe,bai shiga gida ba sai da ya gama sallamarsu.

    A bakin qofar dakin hajiyan ya duqa ya cire Black cover shoes din dake qafarsa mai matuqar tsada da kyau,sannan ya yaye kyawawan labulayen falon dattijuwar bakinsa dauke da sallama.

    Su biyu suka amsa sallamar,hajiyarsa da kuma yayarsa yaaya bara’atu,fuskar hajiyan kwance da fara’a tayi magana

    “Tun dazu akacemin kana qofar gida,a raina nace qila jama’a ne suka riqeka” yana qoqarin zama a gabanta saman carfet yace

    “Sune hajiya,da qyar na qwato” ya qarasa maganar tsadadden murmushin sa kwance saman fuskar sa yana duban mahaifiyar tasa,saita jinjina kai

    “Ma sha Allah,mafi alkhairin mutane shine wanda yake amfanar da mutane,Allah ya qara tsare mana ku a duk inda kuke”

    “Ameen ya hayyu ya qayyumu” ya amsa,yaaya bara’atu tana tayashi.

    Sai da suka fara gaisawa da hajiyar sannan ya gaida yayar tashi,yana tambayarta mai gidanta,sannan suka shiga hira,kafin hajiya ta kira muneera ta kawo masa ruwa da lemo.

    “A qoshe nake hajiya alhmdlh,saidai kafin na wuce”

    “To shikenan muneera jeki”, tsaiwa tayi ta gaidashi cikin girmamawa,sannan ta koma kitchen taci gaba da aikinta.

    “Nace sai yaushe zaka koma kadunan ne ango?,ko cin amarcinne bai qare ba?” Yaaya bara’atu ta fada tana gyara zamanta sosai cikin lausasan royal chairs din hajiyar.

    K’aramin murmushi ya subuce masa,banda yaaya bara’atun babu wanda zasuyi irin wannan maganar dashi

    “Jibi nake saka ran wucewa,hutun da suka bani ya qare”

    “Sun kyauta ma ai, duka duka yaushe ka koma kadunan ma,Allah ya sanya albarka sun kyautata maka kam”

    “Sosai hajiya” ya furta yana gyada kansa.

    “Tafiya dai ta kama hafsat zuwa yanzu,tunda dai ai ba zasu tattare gaba dayansu su zauna anan kai kana can ba” anty bara’atu ta sake fadi tana dubansa,duk da bata da tabbacin samun cikakkiyar amsa daga gareshi,ta sani ba kasafai ya fiya son hirarraki irin wadan nan ba.

    Kaman hajiyan ta fuskanci bashi da niyyar yin magana din,sai tayi amfani da wannan damar ta isar da saqon da take ta son isar masa din

    “Hafsat ai dama bauchi ta zaba,widad itace abokiyar tafiya Kaduna,ita ta riga ta yankewa kanta hukunci,bana jin kuma zata janye” tsaf ya gama karantar saqon hajiyan,saidai can qasan ranshi yana tunanin yadda zai dauki rigimammiyar yarinyar da bata da maraba dasu mimi har zuwa wata uwa duniyar da sunan matarsa

    “Amma hajiya sai nakega ba zataji dadi ba,daga zuwan wata sai a tafi da ita ita kuma tana zaune?”

    “A’haaannn,to daa waye yayi mata?,ita ta yankewa kanta wannan hukuncin,ta kuma bada zabin ya samo mai zama dashi,meye laifi yanzun dukka a cikin wannan lamarin?” Shuru bara’atun tayi,sai ta dan jinjina kanta

    “Allah ya sawwaqe” .

    Shigowar fanteka ya tasheshi,ya miqe yana zuba hannayensa a aljihun wandonsa

    “Bari na danje bayanmu na dawo”

    “Allah ya kiyaye,sai ka dawo” hajiya ta fada kanta tsaye,tashin da yayi yayi mata,don batason wata magana sam a gaban fantekan,tunda ta karanci inda ta sanya gaba.

    Ba haka fanteka taso ba,amma saita rakashi da yaqe tare da addu’ar a dawo lafiya.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/2, 10:44 AM] +234 802 297 0646: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 33

    Arubuce Ta Ke 33

    Page 33

    Table guda ya kama shi kadai,sanye da fara sol din shirt me gajeran hannu,sai wani lafiyayyen trouser daya dace da boots din qafarsa,coffee kawai yake sha,duk da yana da buqatar abinci,loneliness yake da buqata,yayi hayaniya har baisan iyakar adadinta ba,abinda ba dabi’arsa bace,yana tsoron hakan ya haifar masa da ciwon kai,wannan yasa ya zabi ya kebe shi daya ba tare daya gayawa kowa inda yake ba idan ka dauke suraj.

    Tun jiya suke karbar baki,ko kusa ko alama bai dauka wani sabon bikin zasuyi ba,sai da yaje gidan hajiyarsa yaga yadda ta tashi gagarumin biki,ya koma gida bisa ga mamakinsa hafsat ta zauna tayi masa lissafi ta kuma karba kudade sosai daga hannunsa tana shaida masa itama taro zatayi

    “Ko yaya ma dai nakai ga qinta,tunda har an daura ta zama matarka,ina da ikon maida abinda ya faru ya zamana ba wanzajje ba?” Kai ya gyara cikin gamsuwa,ransa na masa dadi,yana sake samun nutsuwa,mamakinsa na sake daduwa akan hafsat din,fatansa da burinsa na dorewarta a haka na sake hauhawa,wanann abun yasa ba haufi ya ajjiye mata abinda ta buqata harda ma qari.

    Kusan komai mamaki yake bashi,auren yazo masa a hagunce,yanata kuma zuwa da abubuwan mamaki,bai dauka wani aure bane na azo a gani ba,amma sai gashi anata shirye shiryen daga kowanne bangare.

    Wayarsa dake yashe saman table din ta soma haske,saboda tuni ya maidata silent,idan kira ya shigo sai.ya duba ya tabbatar mai muhimmanci ne kafin ya daga,a yanzun ma suraj ne don haka ya danna green ya kuma maidata handsfree ba tare daya dauki wayar a hannunsa ba ya barta nan saman table din.

    “Baka dawo bane?,kana ta ina?”

    “I will be back……akwai damuwa ne?”

    “Babu,kusan ma an kammala komai,har presidential lodge din da za’a zuba sauran baqin ya zama ready”

    “Good,thank you suraj”

    “What are friends for” murmushi ya saka ya kashe wayar.

    Har ya daga coffee din zai sake sipping tunanin kiran Samuel yazo masa,ya lumshe manyan idanunsa kadan sannan ya budesu yana tuna yadda hajiya ke bashi amanar yarinyar,tun ranar da aka daura aurensu har yau din nan,ba ranar da zata fito ta fadi bata ambata masa cewa amana ce ta iyayenta ba,sannan amanace ta ita kanta hajiyan,farincikin da yaga hajiyar nayi da auren kawai ya isheshi shima,bashi da burin daya wuce ganin walwalarta,da kuma farincikinta,wannan ya qara masa qaimi ya danna number samuel din.

    Cikin girmamawa da kuma nuna respect yake amsa kiran ogan nasa,ya tambayeshi hanya yace komai lafiya,ya gaya masa a inda suke a yanzun,ya kashe wayar yana irga adadin mintunan da suka rage musu su qaraso bauchin,sai ya shanye sauram coffee dinsa ya miqe yana maida wayarsa aljihu,ya dauki key dinsa ya nufi parking lot na gurin shan coffee din.

    °°°°°°°Cike gidan yake da ‘yan uwanta da abokan arziqi har zuwa compound na gidan,wani abun mamaki ko kuma rashin sabo ga duk wanda yasan gidan ko kuma ya saba wucewa ta gaban gidan,ko gari banza da wahala kaga tayi baqo,don ita din mutum ce mai tsananin rowa da tsumulmula,rashin kyauta rashin faran faran da rashin iya tarbar baqo.

    Daga cikin gidan kuwa,cikin bedroom din,hafsat din ce zaune a gefan gadonta,sai anty ummee da tayi tsaye gaban cupboard dinta tana zaqulo mata kayan data saka,sai mita takeyi cikin masifa

    “Duk wannan uban suturar bansan me kike dasu ba,ke baki saka ba ke baki bayar ba,duk kayanki na fadan kishiya kuma bansan gidan uban da kika kaisu ba,kudin dinki da gyaran daya baki suma ina kika kaisu oho”

    “Don Allah anty ummee kawai ki dauko kayan da zaki dauko ki barni naji da abinda nakeji” hafsat ta dago kanta da takejin kamar zai cire ta fadawa ummee din,sai ta waiwayo ta dubeta,idanunta har sun kada sun canza kala,tabe baki tayi,ta juyo hannunta riqe da wani lace,wanda a ido yayi mata kyau sosai,tana kuma saka ran zai zaunawa hafsa din

    “Da wannan raunin naki da kuma rashin juriyarki bana jin zakici nasara maganar gaskiya,yau kawai…..tun bata kai ga shigowa gidan ba?,ina ga ta shigo?,ta wanzu a cikinsa?,zakici nasara kuwa?,wannan siradin ba na raguwar mace mai raguwar zuciya bane,hanya ce mafi sauqi ta mallakar kowa da komai……saidai…..tana yiwa yawa yawna mata wahala,ciki harda ke da alama”

    Hannunta dake dafe da kanta ta saki,ta sake daga kanta tana kallon anty ummee da kyau,muryarta a mugun karye,ita kadai tasan me takeji tsakanin zuciya da qirjinta

    “Wanne qoqari zanyi anty ummee bayan wannan?,kinsan me nakeji kuwa?,har na fara nadamar daukan shawararki,qila da ace abinda zuciya ta ke gayan nayi na aikata…..wala’alla da ban fuskanci zafin da nakeji a yanxu ba…..”

    “Da kuma kinyi biyu babu ba…..da baki samu darajar da kike ganinta a idanunsa ba,da nutsuwar da kike qaryatawa a yanzun a yadda kike ganin babu ita tayi qaura dake kwata kwata….. tashi kiyi abinda zai fishsheki,ki yiwa zuciyarki qarfa qarfa,kici galaba a kanta,don ki cimma muradinki” ta qarashe maganar tana watsa mata kayan data debo din,sannan ta juya ta fice tabar mata dakin don ta bata damar shiryawa.

    Bin anty ummee tayi da kallo harta fita,sanann taja gauron numfashi ta miqe ta soma daga kayan tana kallonsu,tana jin qirjinta na mata wani zafi,tana jin kamar ta cinnawa gidan wuta gaba daya,sauqi sauqi daya takeji a ranta,idan ta tuna qaramar yarinya za’a kawo mata,tana da ikon juyata duk yadda takeso,amma ta wani bangaren tana jin zafin yadda ya dauko yarinyar da ta kusa haifarta, tabbas banda gidansu ana zaman karatu ta haifi yarinyar,idan ta zauna ta lissafa shekarunta da nata.

    Bata damu da canza undies ba,tunda a nata ganin basa cikin abinda zaka damu da canzasu koda yaushe,ta riga data saba,sometimes abbas ke sakata canzawa,idan ta tarasu zaiyita fada sai ya tilastata ta wanke,idan kuma yana free ma baya jin qyashin wanke mata su.

    Tana gama shiryawa mimi ta shigo da gudu riqe da hannun nawwara,bin yarinyar tayi da kallo,tunda aka fara hidima a gidan taga jama’a taketa murna,rabonta da ganin mutane haka a gidansu tun haihuwar nawwara,a sannan kuma bata da wani wayau sosai

    “Anty jamila tace ki canza mana kaya,wai anty amarya tazo,yanzu motarsu ta shigo” gaban hafsat yayi mummunar faduwa,tabbas dirin motoci takeji daga harabar gidan,hakan yana gaya mata MUGUN IRIN ta shigo gidanta kenan,zuciyarta na wani irin zafi ta rufe mimi da fada

    “Anty amaryar ubanki,kike rawar qafa a kanta,ki cewa jamilan ba za’a canza miki kayan ba,tafi ki bani waje tun banyi ball dake ba” tsoro ya kamasu duka su biyun,bama kamar mimi da tayi tsilli tsilli da ido tana shirin saki kuka,dai dai nan anty ummeen tashigo,a bayanta kuma anty atika ce yayarta da suke uba daya

    “Yauwa,kin gama shiryawa ko?,maza fito gasu sun iso,fito” fuskarta tamkar wanda aka yiwa bushara da rasuwar wani makusancinsa

    “Na fita nayi musu me?” Kafin anty ummee ta amsa anty atika ta rigata

    “Ki tarbeta,ai haka akeyi” ta amsa mata tana shigewa toilet din hafsan,don fitsari ne ma ya shigo da ita,banda haka saitayi zuwa dari bata shigo dakinta ba,duk da dama bawai zuwan takeyi ba.

    Cikin wani madaukakin murmushi take takawa zuwa bakin motocin da sai yanzu suka gama tsaiwa,dai dai sanda anty deena ke tsaye a bakin qofar motar tana karantowa widad addu’o’i tana maimaitawa

    “Sannunku da zuwa,ma sha Allah” hafsat wadda ta lullube jikinta da kyakkyawan mayafinta kalar lace din jikinta ta fada,fuskarta wadace da fara’ar da takejin dai dai take da kukan mutuwa.

    Anty madina anty deena anty halima batulu da momma dake wajen dukkansu suka waiwaya suna duban inda maganar ta fito,hafsat din da mutum takwas dake tare da ita,anty ummee da anty uwani ne kawai ‘yan uwanta,sauran duka ‘yan uwan abbas ne

    “Yauwa sannunku”

    “Kun sha hanya barkanku da sauka” qanwar hajiyan abbas din mace mai yawan fara’a karamci da sanin ya kamata ta fada,don kwata kwata takun hafsatun bai mata ba,hausawa sukance wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi,sai ta matsa tana kamo hannuwan widad da anty madeena ta jawa mayafin ta lullubewa fuska sosai,banda kuma tayi mata hakan ita ba sanin anayi tayi ba,ba lallai ta kula da wannan ba

    “Lale maraba diyarmu,taso a hankali” ta sake fada tana tayata tasowar,ta cikin mayafi widad take mita ita kadai,kawai an qunshewa mutum kai?,wannan ai rashin gaskiya ne,ita me tayi daga zuwanta ba za’a barta bama taga hasken garin daga baya sai a rufe mata kan,da wannan tunanin tabi bayan gwaggwo mero qanwar hajiyan zuwa cikin gidan,duka sauran jama’ar suka bi bayansu.

    Kusan hafsatun ce a qarshe qarshe,tana biye dasu, idanunta da zuciyarta kamar zasu fado,sai data cewa anty ummee ba zata fito ba ta tilastata,ta fuskanci akwai munafukai cikin ‘yan uwan abbas dake murna da wannan auren,amma koma meye zatayi maganin kowa,bata ta yarinyar,don kallon farko tun bataga fuskarta ba ta tabbatar yarinyace din sosai kamar yadda akace.

    A babban falon hafsat da abbas yasa aka gyara mata shi duka don ya danni zuciyarta aka fara yiwa widad masauki,hafsat din ta shigo sai idanu sukayi kanta,wasu nason ganin launin fuskarta ne,yayin da wasu ke mamakin shigowar ta a qarshe,tayi ta maza ta aro dakiya da juriya tana sake musu sannu da zuwa da kuma sannu da hanya.

    Duk da cewa AKWAI WATA A QASA amma SANIN GAIBU sai Allah,hakan sai ya yiwa su anty deena dadi,ya kuma dan sanyaya musu zuciya,ko banza awajensu tayi abinda mata dubu suka gaza yi,a irin wannan lokacin wasu suke fara rabar da halinsu.

    Kanta tsaye ta wuce daura da inda aka zaunar da widad tana murmushi,tana zama sassanyan qamshin da fata da kuma sutturar widad din ke fitarwa ya ziyarci hancinta

    “Sannunku da hanya” ta sake fadar kalmar da tun dazu ita take maimaita wa,sannan ta dora

    “Sannu qanwata” idanunta nakan fuskar widad ta cikin mayafi,don har yanzu bata samu nasarar kallon fuskar tata ba,bata amsa ba kamar yadda bata motsa ba,anty halima data gama qarewa hafsat kallo a fakaice ta motsa,tace ayi salati ga annabi.

    ‘yan addu’o’i aka yi sannan suka gabatar mata da amanar widad din.

    Wani murmushi ta saki,inda ace ba akan plan take komai ba….ashar shine abu mafi dacewa ga wadda tace ta riqeta amana,amma babu komai,akwai lokaci,a juri zuwa rafi…

    “Ai Allah ne ya hada zamana da ita,ita din koda baku fada bama ai tamkar qanwa take a gareni,ai babu komai,in sha Allah,zaku yaba,Allah dai ya bamu aron rai” ta qarashe fadi tana kuma fadada murmushinta,cikin zuciyarta tana ayyana kwana nawa zata gudu da qafarta,ko su dawo su kwashe ragowarta.

    Addu’a aka sake rufewa da ita,sanann suka dunguma sassan widad,sassan da a lokacin aketa kaya kayan shigar da kayan jerenta,wanda motoci uku ne manya suka iya daukesu,irin kudin da ummu da alhaji suka fitar basu tana fidda makamancinsa ba akan bikin jika,gefe daya kuma ga abbanta shima da yayi tasa bajintar,abun da ya bugar dasu batulu sosai,suka kuma sake tabbatar da cewa hae yanzu yana qaunar fatima,daga yadda ya aurar da autarta cikin girma,saboda bai taba irin wanna hidimar ga sauran yaransa ba,da sukayi qorafi sai.ya gaya musu,ita din nesa za’a kaita,duka yaransa kuma babu wadda aka taba kaiwa nesa,bugu da qari duk wata dama da wani alfanu da mutumin dake kusa da gida zaya samu ita banda ita,sunyi mita sunyi qorafi har suka gaji suka godewa Allah.

    Babban falo ne dake dauke da dakuna guda biyu,sai kitchen dining area da kuma ventilation ta baya,ginin yayi kyau sosai gwanin qayatarwa,komai kuma a wadace babu matsi.

    Basuyi minti talatin ba hafsat tasa aka kai musu coolers din abinci da tasa akayi musu,suna fara ci kusan suka ajjiye,nujood wadda aka taho da ita tace kuma sai ‘yan kano zasu koma zata wuce gida ta ajjiye nata plate din itama

    “Nifa wallahi dana sani masauki nabi su na’eema,wannan abinci haka?” Ta fada tana yatsina fuska,harararta hajjaa tayi

    “Bamason abun magana daga zuwa baqunta malama,idan zaciki kici,idan bakici ki ajjiye musu kayansu”

    “To nima dai shuru kawai nayi,abun dai to…..” Latifa ta fada yana yatsina fuska,duk sai aka kwashe da dariya,ashe kowa shuru kawai yayi yake kaiwa cikinsa,kada ya fara magana aga gajen haqurinsa,musamman da yake inna laila qanwar ummu tana wajen,ita kuma ba kasafai ta fiya son ire iren wadan nan abubuwan ba.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[2/27, 10:37 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 32

    Arubuce Ta Ke 32

    Page 32

    Yana daga tsaye yake shanye tea din dake cikin cup din,yana yi yana hadawa da qonannen cake din da hafsat din tayi,dai dai sanda ita kuma ke sanye da kampala dinkin tea bubu,fuskarta a wanke tas babu digon kwalliya kamar kullum,hakanan fuskar tata a dinke take babu walwala sam sam.

    A duk lokacin data kalli abbas….ta kuma tuna a yanzun bawai ita daya ce mutum dake amsa sunan matarsa ba,sai taji kamar ta shaqe kanta,kota zauna tayita zunduma ihu har sai dukkan jama’ar dake kewaye da ita sun fuskanci irin zafi radadi gami da qunar dake cikin ranta,tsantsar bacin ran da babu halin nuna shi,baqinciki da tashin hankalin data zabi lullubeshi da kissa da kuma nuna halin ko in kula da lamarin aurensa,wanda ko kusa ko alama ba haka bane cikin ranta.

    Cup din ya dire saman fridge din yana furta

    “Alhmdlh” da Peace voice dinsa dake dauke da wani calmness da bai cika son hayaniya ba,idanunsa ya zube saman fuskarta yana kallonta,saita janye nata idanun daga kallonsa,batason zuciyarta ta karye ko sonshi ya motsa mata har tayi wani misbehaving,tsaki yana subucewa daga bakin nata,saidai Allah yasa baiji ba

    “Zan wuce” ya fada murya can qasa

    “Allah ya kiyaye hanya” ta amsa masa a taqaice tana folding hannayenta a qirji,matsawa gabanta kadan ya sakeyi yana rage kusancin dake tsakaninsu

    “Me da me kuke buqata?,ko kuma shikenan?,ba wani taro da zakiyi?” Kusan duk abinda takeso ya dire mata,ta wanki aljihunsa yadda ya kamata,to amma duk da haka batasi tace masa shikenan din, tunda zataje wajen anty ummee,batasan me zasu tattauna ba,don haka tace masa

    “Idan akwai wani abu zamuyi waya” kansa ya jinjina,ya sauke mata soft kiss a goshinta,sannan yaja da baya ya juya yana barin wajen,dole ta kama masa qaramar jakar tabi bayansa da ita tana qoqarin gyara yanayin fuskarta,don komai ya sake hawa kan saiti,ya kuma ci gaba da tafiya yadda suke tsarawar.

    Da murmushin yaqe ta bishi sanda yake waving mata hannunsa,motarsu tana fita ta koma ciki da sauri,ta dauki jakarta mayafi da key din motarta,har takai bakin qofa ta koma ta rage yawan kudin dake cikin jakar ta adana a locker dinta,cikin ranta tana raya

    “Kada bacin rana ya gifta ta kansu” duk kuwa da cewa gidansu zataje,acan zasu hadu da anty ummee din.

    Tunda ya tafi kusan ayyuka suka cunkushe masa,bashi da wani cikakken lokacin kansa bare na sauran abubuwan,haka ya dinga qoqarin handling komai,ga gida babu mace,idan ya dawo kusan wasi hidimomin da ya cancanci ace matar aurensa ce tayi masa kafin isowarsa gidan shi zai gabatar dasu,wanann ya sanya shi yanke hukuncin ajjiye widad a nan kadunan,ko babu komai gidan bazai zamana shuru babu dan adam a cikinsa ba.

    Yana daga nan ya sanya aka sake gyara part guda daga cikin parts din gidansu na bauchi,a nan kadunan ma yayi wasu qananun gyare gyare,mutum ne shi koda yaushe mai tsananin kyautatawa ga duk mutumin da Allah ya dashi zama dashi,hajiya tafi kowa sanin hakan,shi yasa zamansa da hafsa ya tsaya mata a rai qwarai da gaske,tako ta ina abbas din inda rubutawa bawa qaddararsa akeyi ya cancanci samun mace ta gari,wadda zata kula dashi matuqa gaya.

    ************K’arasa zuba jewel’s dinta data debo tayi cikin qaramar jakarta ta zuge,sannan ta dubi alhaji salim mai fata dake zaune kusan awa guda saman kujerar madubi dake dakin widad din

    “Alhaji na gama” ta fada tana murmushi

    “Da kyau jikata,sai tafiya kenan” kai ta gyada masa tana dariya

    “To muje na rakaki da kaina,kada ma mutsaya sauraren kowa su bata mana lokaci” sai ya miqe yana daukar mata jakar,yayin da ta lulluba mayafinta abinta,suka jera ita da kakan nata dake nuna mata zallar qauna hadi da kulawa kamar yadda tsohuwar matarsa ummu ke gwada mata.

    Hankali kwance alhaj salim ya bude mata gaban baqa wul don motar qirar range rover,daya daga cikin motoci mallakin ASP abbas muhammad bello

    “Shiga abinki ki zauna kafin su fito” sai a sannan ta kalleshi,tadan narke fuska

    “Amma alhaji,kace dakai da ummu duka kuna nan tahowa ko?” Kai ya gyada mata yana murmushi,saidai can qasan ransa kewa da kuma tausayinta ne fal zuciyarsa,farincikinsa guda daya zuwa biyu ne……sun aurar da widad din cikin aminci zuwa ga hannun mutumin da basu da haufi a kansa,nagartarta da ingancinsa sunkai,na biyu duk yadda suketa juya yadda za’a fidda widad din daga gidan salin alin bata tara musu taron jama’a ba,sai gashi da qafafunta ta fito zuwa motar da zata daga dasu bauchi,Allah ya bashi hikima da basirar da taketa shauqin tafiyar zuwa gidanta

    “Idan bamuzo ba waye zaizo?,kedai sha kuruminki,abinci zaki dafa mana mai dadi nida ita a kitchen dinki” murmushi ne ya sake kubce mata,itakam widad har ta isa macen da zata shiga kitchen tayi girkin baqi kenan,saita kama murfin motar ta kuma shige,alhj salim ya miqa mata jakar,sannan ya tsaya daga bakin motar yana mata hirar dake sake dauke hankalinta.

    A gajiye anty deena ta tura qofar dakin ummu tana sauke ajiyar zuciya

    “Allah ummu nidai nayi iya dubana banga widad bafa” cikin mamaki ta dubeta

    “Har wajen alhajin ku kin duba basa tare?” Kai ta girgiza

    “Ban duba ba”

    “Yi qoqari ki dubota,kinga kada suyi dare a hanya”

    “Gaskiya dai,nima banason muyi tafiyar daren nan saboda sanyi” tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin.

    Har zata gota jerin gwanon lafiyayyun motocin da aka shirya su saboda daukar widad din ta hangi alhajin tsaye jikin daya daga cikin motocin,saita dawo da baya,abinda ta gani ya sanyata kusan faduwa saboda dariya,widad ce zaune gaban motar ta qwame abinta,sunata hira da alhajin tana ta qyalqyala dariya,kome yake gaya mata oho,saita tsagaita dariyar tana kallonsu,murmushi na kubce mata,qasan ranta itama tausayin widad din na tsarga mata

    “Kuruciya me dadi” ta fada a hankali hawaye nadan tsatstsafo mata,ta tabbatar inda ace babba ce yanzun haka ake shirin tattarata zuwa gidan miji,gidan mijin ma wata duniyar ba duniyarta ba,ba duniyar data rayu a cikinta ba,ba shakka da tuni tana nan hankali tashe,saita juya kawai zuwa cikin gida don ta sanar musu,tafiya ta tabbata tunda amarya har takai kanta cikin mota,murmushi ya sake kubce mata.

    Dab da bakin falon sassan ummu sukayi kacibus da inna batulu momma

    “Har yanzu ba’a ganta ba?” Ta fada a fuska alhini ne fal,yayin da qasan zuciyarta wani fata ne na daban,ba tare da anty deena ta kawo komai a ranta ba tana danne dariyarta tace

    “Wa?,ai widad tuni tayi landing a mota” ido batulu ta zazzaro

    “Kamar yaya deena?” Dariyar da take riqewa ta kubce mata

    “Wallahi alhaji ya raka amaryarsa,kodan kishin nan ma bayayi,tana can tana jiran ‘yan kawo amarya” dogon salati taja tana tafa hannu,sai kuma taja burki ta juya da sauri har tana tuntube ta koma zuwa cikin falon,da kallon mamaki anty deena ta bita,saita take mata baya tabi bayanta itama.

    Tana shiga falon batulu na kwazawa ‘yan uwan abbas dake zaune a falon suna jiran fitowar widad din don su wuce

    “To ai bayin Allah zaman jira da qoqarin bikon da akeyi ya qare,amarya dai takai kanta cikin mota mu take jira” ran anty deena saiya sosu,duk da cewa akwai quruciya ga deena bai kyautu batulu ta kawo saqon a haka ba,fuskarta na nuna zallar alhini kamar ta aikata wani babban sabo a musulunce.

    Inna uwa qanwa ga hajiya ta tura wayar hannunta cikin jaka tana sakin dariya

    “La la la,lallai yaron namu badai farinjini ba,niko na godewa wannan diya tamu wallahi,ta hutashe shemu,saimu tashi shirin tafiya ta kammala” anty deena ce ta karbe cikin dariya

    “Aiko dai batason wahal daku biyan kudin biko,ai shikenan” dariya aka dauka a falon,kowa yana fadin albarkacin bakinsa,kusan yadda batulu taso a juya zancan ya zamarwa widad abun fada abun baizo a haka ba,kusan kowa dariyar quruciyar yakeyi.

    Sannu a hankali jerin motocin dake dauke da mafi yawan ‘yan uwanta suka fara barin farfajiyar gidan alhj salim mai fata,motar da take ciki itace mota ya qarshe,duk da a tsarin tafiyar zata kasance cikin tsakiyar motar securities din da zasuyi musu rakiya har zuwa garin bauchin.

    A hankali tasu motar ta fara motsawa,yayin da taketa dagawa su Aafiya hannu tana fadin

    “Sai kunzo,karku damu,alhaji yace kamar wancan lokacin da naje gidan uncle muhsin,wannan lokacin har zuwa zasuyi shida ummu saimu dawo tare,idan zai taho ku taho tare dashi don Allah” ta fada tana kallon afiya,tans jin ba dadi itama,zuciyarta najin wani irin yanayi wanda.bata saba jinsa ba,irin yanayin dako sanda zataje gidan uncle muhsin bata sanshi ba,wannan shi ake kira da yanayi na rabuwa……rabuwa da gida….. rabuwa da muhallin da qaddara ta wanzar maka a haifeka a ciki……rabuwa da bigiren daka rayu kayi kuma gwagwarmaya a ciki…..fadi tashi tsakanin masoya da maqiya,zuwa wani bigiren da RUBUTACCIYAR QADDARARTA ta zana mata……BIGIREN dake qunshe da tarin qaddarorin rayuwarta…..qaddarorin dake da tsananin zafi quna da kuma barwa rayuwa tabo me cin rai.

    Tun suna tafiya tana biye da hirar wadanda suke tare cikin motar wato anty deena,anty madeena anty madeeha da inna uwa,wani bangaren na zuciyarta kuma nata hasaso mata kayayyakin da dukka ummu ta nuna mata ta kuma shaida mata nata ne gidanta za’a kai mata,yadda zata sarrafasu ta more kayanta,irin yadda taga su anty deena anty ramziyya basma da sauran yayyunta keyi,zatayi iko irin nasu kenan itama,zata saka wasu wanke wanke idan sunzo gidanta,sai qaramar dariya ta qwace mata ita kadai,tana fasalta yadda zata saka su rafi’ah aiki,kuma dole suyi,saboda jiya jiya taji anty madeena na cewa ita din yanzu dukka ta girmesu,duk kuwa da cewa sun babbata wasu watanni.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/25, 9:26 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)