Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 28

Sponsored Links

Page 28

*********Washegari tana dakin yaran tana sauya musu kaya bayan tayi musu wanka taji ana sallama a falon nata,qaramin tsaki taja,ita gaba daya batason baqi a rayuwarta tun asali,bare a yanzu da take cikin wannan yanayin,mimi ta aika ta dubo waye?,sai ta dawo tana ce mata baquwa ce,tadan harari yarinyar,har yanzu taqi tayi wayo irin yadda takeso,irin wayon da zata iyayi mata bayanin duk abinda takeson ji,saita ajjiye kayan nawwara da bata kai ga sanya mata ba,ta miqe tana cewa

“Bari muga wanne munafukinne” tayi waje yaran suna biye da ita.

Tun kafin ta qaraso ta hangi wacece,rabi’atu ce,cousins suke da abbas din,takan jima bataga rabi’atun ba,bama ita kadai ba,danginsa ma yawancinsu ba wani zuwa sukeyi ba,saidai idan an hadu a wani sha’ani idan ta samu zuwa saisu gaisa,suna girmama ta dai dai gwargwado,amma ta dauki hakanne a mazaunin don anga mijinta yana da rufin asiri ne.

Fuskarta kadaram kadaham ta qaraso ta samu kujera daya ta zauna tana dan satar kallon rabi’atun,saboda daga nesa taga yadda take satar kallon falon,zuciyarta kuma ta raya mata gyaran da akayi mata take kallo

“Dangin miji irin jaraba” ta fada a ranta,babu dama suga sakakken abu a gida ko a jikinka sai sun nuna a fuska ko a kalaminsu(nace uhmmm,inama suka hadun ko sukazo gidan bare hakan ta faru?).

Ba yabo ba fallasa suka gaisa da rabi’atun,sai kuma shuru yadan biyo baya,sai ita din da taketa qoqarin yiwa su mimi wasa,wadanda suka qi sakin jiki da ita saboda rashin sabo da basuyi da su ba.

Kai rabi’atun ta dago tana cewa

“Wai nan bayanku nazo suna,kinsan a nan qanwar mijina take aure”

“Uhmmm,Allah sarki” ta fada a taqaice

“Sai nace nari na qaraso mu gaisa,na kuma yi miki murna ko jaje zance,ashe kuma yaa abbas aure kishiya zai miki?,kuma a rasa wadda za’a rakito miki sai ‘yar wani garin,kuma ma yarinya qanqanuwa wadda a haife ya kusa haifarta” da fari cin mutunci hafsat ta shirya yuwa rabi’atun,amma jin ta fara bata hint akan abubuwan da batasan dasu ba saita maida wuqarta tana gyara zamanta

“Ya kusa haifarta fa kika ce?”

“Wallahi haka inna ke gayamin,tunda kwata kwata bata wuce shekara sha uku zuwa sha hudu ba” wani abu ne ya tsargawa hafsat,saita nema tashin hankalinta kaso talatin cikin dari taji babu shi,ta aro sakin fuska ta dorawa fuskarta

“Kin ganta ne rabi’ah don Allah?” Kai Rabia ta girgiza

“Ban dai ganta ba,amma inna tacemin ta taba ganinta gidan sau daya,badai ‘yar nan bace ‘yar kano ce” gabanta yadan fadi kadi jin abinda ta fada daga qarshe,ana wata ga wata,ko zakayi kishi yafi kayi da ‘yar garinku,kar tasan kar ne,bawai kayi da bare hayin wani gari ba,garin ma da tasha jin masu kishiyoyi daga wannan nahiyar suna qorafi,to amma ‘yar shekara sha uku zuwa sha hudu kishiya ce ko ‘yar raino?.

“Ni irin wannan auren banda abin hajiyarsu,mutum na zaune da matarsa ya dauko aure,a kuma tsallake gida a tafi dawa?”

“Da gidan da waje duk dai kishiya ce,ko daga dakinki aka fiddo miki da ita sunanta kishiya” hafsat din ta amsa mata rana dan hade rai,saboda tasan yadda ‘yan mata da yawa cikin familyn ke sonshi,kamar shi kadai ne namiji a family din nasu,sai data dinga murje idonta tana yanka musu rashin mutunci ta samu salama.

“Gaskiya dai” rabi’atu ta waske ta hanyar fadin haka,bata jima sosai ba saidai hafsat din tadan samu wani haske akan lamarin,da yadda hajiyansa ke maraba da abun,daga qarshe sukayi sallama,ko pure water rabi’atu bata samu daga wajenta ba,haka tabar gidan tana tsine mata cikin zuciyarta,saidai duk da haka sudai suna adawa da wannan auren,tunda nasu basu samu ba ‘yan qannensu da suka zama ‘yammata gwara a bata goma daya bata gyaru ba gaba daya.

Rabiah tana fita hafsat ta wuce daki cikin hanzari,ta dauko wayarta ta soma neman number din anty ummeee ta labarta mata labarin data samu,saidai duk saurinta ya zama nawa saboda babu kati a wayar tata,dole ta koma ta mobile app din bankin da take amfani dashi,ta saka card din dari biyu ta kirata.

Sai data kusa tsinkewa anty ummee din ta daga,hafsat na daga tsaye ta gaza zama,sai kai kawo takeyi

“Anty ummee….kina jina?” Ta fada da matuqar zaquwa,har kana iya jiyo haka cikin muryarta

“Ina jinki hafsatu,lafiya?” Guri ta samu saman bedside drawer dinta ta zauna sannan ta soma magana

“Yanzun nan rabi’atu cousin din abban mimi tabar gidan nan,kinsan yarinya qarama yaje ya dauko?,ko shekara sha biyar bata cika ba?” Ta qarashe maganar tana tabe baki,takaici yana cikata.

Dariyar da anty ummee ke qyalqyalawa tayi kasake tana saurara,sai daga bisani tace

“Kai haba?,kice raino ya dauko?,tirqashi,to ke ai ta fadi gasassa,babu kuma wani sauran kishi da tashin hankali daya rage miki”

“Kamar yaya?,haba anty ummee,idan za’a maka kishiya ma ai sai ayi maka isassa,wadda zaku goga da ita,ba wata can qasan qasanka ba”

“Tabdijan” anty ummee ta fada sannan ta dora da cewa

“Amma bansan baki da hankali ba sai yau,ke!,kishiyar da zata shigo ta goga da ke ai masifa ce,me yayi miki zafi?,to idan baki sani ba bari na gaya miki,Allah sonki yake shi yasa ya hadashi da qwaila,a yanzun ne za’a fara wasan ma da kyau,dama dukka tana hannunki,idan kika dauki.maganganun da mukayi dake rannan kikayi amfani dasu da kyau to ina me tabbatar miki yadda zaki bawa su mimi da nawwara umarni itama haka ne,ba boka ba malam,komai zaizo miki da sauqi,kina daga kwance kina sarrafa gidan a hannunki,yanxu saurara nayi miki wani sabon karatu…….” Gyara zama tayi sosai tana bada hankalinta ga anty ummee din,tana hasashen qamshin gaskiya cikin msganganun anty ummee,sai taji ranta ya fara yin fes

“Ina jinki” ta cewa anty ummeen……

*********Can quryar gadon ummu take kwance abinta,ta duqunqune waje daya,duk kuwa da cewa gidan a cike yake da baqi jikoki da surukan gidan,wanda a baya duk lokaci irin wannan tana tare dasu sunata sabgoginsu,sabanin yau da gaba daya take jinta wani iri,musamman da aketa mata abubuwa daya banbanta dana ‘yan uwanta,aka kuma tsameta daga cikinsu.

Tana daga kwancen tana kallon yadda ummu ita da warisha qanwar abbanta suketa hada kaya cikin manyan buhunhuna da kwalaye,wanda gaba daya kayan ummu tace nata ne,gidanta za’a kai mata ayi mata jeranta,itama ta samu nata gidan na qashin kanta,duk sanda ummu ta fadi hakan dadi takeji,amma yau gaba daya jikinta ya sanyaya,gwiwarta ta fara sagewa.

Ana tsaka da wannan latifa tayi sallama ta shigo dakin ummun,ta tsaya daga bakin qofa yana gayawa ummu game gyaran jiki tazo,tunda widad din taji haka ta runtse idanunta tahau baccin qarya,ita kwata kwata batason wannan kwabe kwaben da aketa shafa mata yau wajen sati guda kenan,tana jin sanda ummun ta waiwaya tana qwala mata kira,amma sai ta sake lafewa cikin bargo tayi kamar bacci take,har ta gaji da kira ta juya ga latifa

“Inaga kawai abar aikin nan haka,dama yau da gobe ne kawai ya rage”

“To shikenan,bari na sallameta,yauwa……anty madina tace na gaya miki,kayan miyar ya za’a yi dasu,a markada gaba daya azubasu a freezer baya?”

“Eh hakan yayi,don kada su lalace kafin jibin”

“To shikenan” sai latifan ta juya ya fita,su kuma sukaci gaba da hada kayan,tana labe cikin bargo tana satar kallonsu,tana jin anty warisha na cewa

“Banda abun ummu nawa ma jikin widad din yake,me ya sameshi ma da za’a mata gyara,ita da dama fatarta me kyau ce,a haka ma a karon banza daukan ido takeyi”

“Wallahi madina ta matsa sai anyi mata,to ya na iya,itakam dama ta iya biyewa shirmensu,yanzu haka ta gama tsara musu komai,har kudi tasa muhsin ya karba musu wajen ango wai zasuyi walima” dariya warisha ta sanya

“Kai,Allah mai iko,widad amarya” sai ummun ta murmusa kawai,don dauriya kawai takeyi batason aga rauninta.

Tun tana labe tana kallonsu har baccin gaske ya dauketa,bata farka ba sai dab da la’asar,sanda ta tashi dakin babu kowa,sun gama aikinsu sun fice,bandakin ummun ta shiga ta daura alwala,ta shimfida abun sallar tayi sallarta,saita dan zauna tana jin hayaniyar su nabiha da sauran jikokin gidan,daga bisani ta gaza daurewa ta fito.

Ido kuwa yayi mata caaa,mutane anata kiranta da amarya,saidai ta tura baki tayi gaba abinta,itafa shi yasa tunda aka fara baqin ma batason fitowa,a haka dai ta samu ta wuce sassan anty madina,a canne ta sake sosai abinta,harta manta da komai ma,har sai da anty madina tace lallai gobe za’a tsefe kai ayi kitso,a nan fa suka raba gaari da ita,saboda ta ambato maqiyinta wato kitso.

*RANAR DAURIN AURE*

Cikin jerin gwanon motoci na alfarma suka taso,tun daga garin bauchi zuwa cikin garin kano,qarqashin jagorancin jami’an tsaro da matakai masu tsauri,a ranar tamkar dai wani shugaban qasa,duk yadda ya dauki daurin auren sai ya wuce masa haka,tamkar dai dama ya dade da shiryama hakan,shi kansa cikin sabuwa dal din motarsa yake,yana seat din baya shi da suraj,sanye da wata danyar shadda wadda koda gari aka baka ka canki kudinta ba zaka ajeta nan kusa ba.

Tunda suka taso fuskar hafsat ke masa yawo,tunda zancan ya tsiro bai taba jin tausayinta irin na yau ba,yana hangen yadda fuskarta ta sauya a sanda yake shiga motarsa cikin shigar dake jikinsa a yanzu,saidai zuciyarsa cike take fal da mamakin mene ya sauya hafsat?,me kuma ya kawo wannan sauyin?,yasan halinta ciki da bai,meye ya sanyata zub da makaman yaqinta?,wannan amsar ce har yanzu ya kasa lalubota,sai tarin wasi wasi da yake fama dashi kullum kwanan duniya.

Tun daga titin farko zuwa abinda yakai layin da zao sadaka da ainihin gidan alhj salim mai fata cike yake tanqam da jama’a,idan akace maka jama’a ina nufin jama’a na gaske da zakayi tsammanin daurin auren wata hamshaqiyar budurwar data ci ta qoshi da karatu da wayewa akeyi,gaba daya unguwar a hargitse take sakamakon halartar daurin auren da manyan ‘yan siyasa gwamnoni da kuma qusoshin gwamnati da abbas yake hulda dasu sukayi,jama’a dake tsaye a gefe guda suna ci gaba da lissafa gwamnonin da sukaga suna shiga unguwar tasu,sai da suka lissafa shida casss!.

“Bisa dukkan alamu wannan karon babban kamu akayi a gidan nan,lallai yau sun jawo babban kai,kai kaga motocin dake ta gilmawa kamar daurin auren ‘yar shugaban qasa?” Ire iren maganganun da matasa ‘yan zaman banza a bakin layi keyi kenan,sunayi suna ci gaba da dorawa a lissafin su.

Daga can cikin gidan kuwa a shaqe yake da jama’a,ko ina idan ka kalla hada hada akeyi,zaka tsammaci an dauki shekaru ne ana yiwa bikin tanadi,saidai hausawa suna cewa,kowanne aure da arziqinsa yake zuwa,wanna haka yake,domin kuwa a lokacinne aka baje lefen widad wanda ya iso ne tare da ‘yan daurin aure,akwati mai sunan akwati,akwati na alfarma guda goma sha biyar,kowanne maqare da sutturu masu daukan hankali,duk wanda ya daga idanu ya kalla koda baiso magana ba sai bakinsa ya subuce ya furta

“Ma sha Allah”mafi yawan mutane cikin family da wadanda ke cikin gidan dake zuba idon suga wani abun kaico ya bulla sai jikkunansu suka fara yin sanyi,musamman da labarin irin manyan mutanen da suka halarci bikin yajewa kunnuwansu……….

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
[2/22, 2:49 PM] halimatuabidah: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Back to top button