Author: Novels

  • Arubuce Ta Ke 42

    Arubuce Ta Ke 42

    Page 42

     

    Sanda ya dawo gidan babu kowa sai hajiyan tashi,nan yayi zamansa bayan ya fito daga sallar isha’i,yana cin abinci tana qara masa suna hirarsu

    “Nidai don Allah zan riqo alfarma guda daya a wajenka abbas” tayi zancan tana ajjiye dan bowl din data qara masa miya,sai ya tattara mata hankalinsa gaba daya,har yana ajjiye spoon din hannunsa

    “Hajiya badai alfarma ba,saidai umarni ko?”

    “Ko alfarma koma umarni,nidai burina ka cika……don Allah ka kula da yarinyar nan kamar yadda zaka kulaa da hadiyya da kuke fito ciki daya” kai ya jinjina,can qasan ransa yana jinjina tarin qaunar da hajiyar kema yarinyar

    “Na daukar miki alqawari hajiya”

    “To Allah ya taimakeka,yaci gaba da dafawa al’amuranka”

    “Ameen ya raheem,Allah ya qara lafiya da nisan kwana” sai ta bishi da murmushi kawai,kafin ta amsa masa da ameen.

    Yau din sassan Widad din ya fara isa,saidai latifa na bude masa qofa taja baya cikin girmamawa,har ya sanya kansa sai ya dakata

    “Kuna lafiya?,baku buqatar komai?” Ya tambaya,kai ta girgiza,tana tsananin yabawa da irin kulawar da yake nunawa akan widad din

    “Lafiya qalau alhmdlh,babu komai”

    “Itafa?” Ya tambaya kai tsaye

    “Tayi bacci tun dazu”

    “Lafiya dai ko?” Ya tambayeta yana dan ritsata da ido,kusan bai taba zuwa ya sameta tana bacci ba,yafi samunta a daki,data ganshi zata fara tattare jiki waje daya,ta kuma sanyawa bakinta kwado da linzami,har sai ya gana zamansa na mintu biyu zuwa uku sannan ya fito

    “Eh bata dan jin dadin jikinta ne wai”

    “Subhanallah,amma me yasa ba’a kirani an kaita asibiti ba?”

    “Ba zazzabi ko ciwon kai bane,kawai bata da kuzadi ne kamar yadda ta saba” sai yadan kada kai kadan

    “Allah ya sawwaqe,ammmm….. Please,koda akwai wani damuwa,a kirani ko ta wayarta ne”

    “In sha Allah” ta fada cikin girmamawa,cikin ranta tana yaba kulawa da sanin darajar dan adam irin nasa.

    Sanda ya shiga falon hafsa a zaune ya sameta,yaran na kwance a wajen saman carfet kowa d’ai d’ai,itama saman carfet din take a zaune,hannunta riqe da waya,plates din abinci ne da abincin da sukaci suka zuzzubar kaca kaca,saman kanta ba dankwali,gashinta dake samun qarancin kulawa qwarai da gaske daure a kyauro.

    Idonsa ya dauke daga kanta yana qarasawa wajen yaransa,saita janye qafafunta tana masa sannu da zuwa,qasa qasa ya amsa mata,yana dauke yaran daga qasa ya nufi dakinsu dasu.

    A hargitse ya samu dakin kamar ko yaushe,sai a gadon nawwara ya fara ajesu,ya karkade gadon mimi ya maidasu kai,sannan ya gyarawa nawwara nata gadon itama ya maidata kai,bayan ya duba cupboard dinsu ya canza musu wankakken zanin gado,ya tattara karikicen kayan wasansu dake tsakiyar dakin ya killace a drawer dinsu ya hade kayan wankinsu a laundry basket.

    Yana gab da kammala mopping na dakin ta turo qofar ta shigo,zuwa yanzu daurin dankwalin ture kaga tsiya ne a kanta,dinkin atamfa ce doguwar riga data bude sosai daga qasa,saidai idan ka kalli kayan sosai a jikinta zakasan ta dan sha jiki.

    “Ya daga shigowarka kuma dear?” Ta fada tana jin wani iri a ranta,shi ya fiya qaqale qaqale,banda hakan bataga wani shahararren datti da dakin yayi wanda zai hana mutum yin bacci ba,taga ko daxun kafin ta fita sai data tattare kayan wankin gefe daya,amma shi baima gani ba.

    Idanu ya aza mata kafin ya janye yaci gaba da qarasa goge wajen,sai jikinta ya dan mata sanyi daga kalar kallon da yayi mata,don haka ta saki qofar tana qarasowa ciki.

    Kafin ta qaraso ya gama,ya ajjiye mopping stick din,sannan ya goye hannayensa da tuni ya nade hannaun rigar xuwa sama yana kallonta,yadda ya aza mata kallon mayatattun idanuwan nan nasa duka sai taji nauyinsa ya sake kamata,don haka ta daburce gaba daya

    “Samu guri ki zauna” ya bata umarni kai tsaye,sai tadan ja tunga,gabanta yana faduwa,bata qaunar fadansa gaba daya,yanzun nan zai sanya ka ka rasa abun fadi,bayan tasan bata da kalar kowacce hujja da zata kare kanta da ita,dole ta samu gefan gadon nawwara ta zauna.

    Daya daga cikin kujerun dake hade da teburin karatunsu ya jawo,ya ajjiyeta dab ds ita ya zauna akai.

    Shuru ya ratsa dakin,tana ta kasa kunne taji me zayace da ita,yayin da shi kuma bai furta komai ba,sai kallo da ya ritsata dashi,kallon dake sake sanyata jin cewa da gaske ita din mai laifi ce

    “Hafsat” ya kira sunanta kai tsaye,wanda abune mawuyaci kaji ya kirata din

    “Na’am” ta amsa masa ba tare data iya kallon qwayar idanunsa ba

    “Ki gayamin me kika nema kika rasa a gidan nan,wanne nauyi ne nawa da bana sauke miki?” Motsawa tayi,kamar wadda ke zaune saman wuta,kasa bashi amsa tayi,har ya gaji da jiranta,sai ya sauke hannayensa qasa ya dafe kujerar da yake kai yana ci gaba da kallonta

    “A iya sanina babu wani abu da yayi saura wanda bana miki shi,ci sha suttura,kudin kashewa,hatta da lighter da za’a kunna gas a gidan nan alhmdlh ban bari ko yarda ki siya ba,me kika rasa hafsat?,amma kin kasa tsaida hankalinki ki tsaftace gidanki,ki kula da yaranki,ki sauke hakkina dake kanki,zaki iya tuna when last da kika kawo kanki gareni?” Ys jefa tambaya mafi girma da taketa tsoron yayi mata ita

    “Don Allah kada ka kawo wannan zancan,ka san dai ina iya bakin qoqarina ai……” Wani miskilin murmushin takaici ya saki

    “Well……am listen to you” da qyar ta tattaro dukka jarumta da qwarin gwiwar ta,duk da cikin ranta har yanzu bata jin kanta a matsayin mai laifi

    “Ina fa kwatantawa,ina qoqarina dear,aikin gida fa ba is not easy at all,sauqinta ma ace ina da ‘yar aiki,amma yanzun komai fa ni nakeyin abina,ga yara,ga makarantar mimi,dole wania abun fa sai ana haquri” ta fada tana dan tsuke girarta fuskarta qasa qasa,ita ala dole bataji dadin gyaran da yakeson mata ba.

    Shuru yayi kawai yana kallon fuskarta, reaction din da ta nuna saman fuskarta ya isa ya gamsar dashi cewa bata dauki kanta a tana aikata wani abu na ba dai dai ba,an dade hakan tana faruwa a tsakaninsu

    “Idan aiki ya hanaki gyara muhallin mijinki dana yaranki…..shi kuma kitchen da kika tara kwanukan wanke wanke fa?, harda na tuwon jiya?”

    “Yau ai fita nayi,kuma ka sani dear,ban zauna gaba daya a gidan ba,amma gobe in sha Allah da aikinsu zan tashi,idan na gyara gobe zaka ga kamar ba’ayi ba,ba shikenan ba?” A hankali ya lumshe idanuwansa gaba daya yana kiran sunan Allah,mata nawa ne keda nauyin da yafi nata amma zaka samesu su da gidansu da iyalinsu tsaf?,wannan muguwar qazantar baisan ta yaya zai raba hafsat din da ita ba,tafi komai ci masa tuwo a qwarya,ya yiwa qazanta wani mugu tsana da har baisan iyakarsa ba,abinda hafsat din har kwanan gobe ta kasa ganowa,mai aiki dai mai aiki dai…..shikam ba sakaran namiji bane da zai daukoma hafsat mai aiki,ya tabbatar daga qarshe ita zata koma yin komai.na gidan,qarshe harda abincinsa da zaya ci.

    Miqewa kawai yayi,ya zura hannayensa a aljihunsa

    “Duk abinda ya kamata nayi miki na miki shi,ya kamata ki canza for now…..yaranki suna girma,zasu kuma dauki jalar kowacce dabi’a daga wajenki,dama sau daya tak take zuwa ma mutum a rayuwa” yayi maganar yana daga yatsansa guda daya,sanann ya juya yana barin dakin.

    Gabanta ya fadi,binsa tayi da kallo har ya fice,to me yake nufi?,abbas din yana da wuyar fahimta wani lokacin,ta janye idanunta daga kallon qofar da tuni ya jima da wucewa,ta dawo da dubanta cikin dakin,komai yayi fea gwanin sha’awa,ta tabbatar koda ita tayi wannan gyaran bazaiyi kyau haka ba,to itadai bataga laifi ba,idan ma yayin ba duka yaransu bane shi da ita?.

    Taso sharewa itama,amma sai zuciyarta ta gaza nutsuwa da hakan,wannan dalilin yasa ta bashi kusan awa guda,sannan ta tattara kayan abincin tana ta mita a ranta na wahalar da ya bata na diban abincin tayi sashensa.

    Da sallama ta tura qofar bedroom din nasa,sassanyan qamshinsa ya fara mata maraba,babu wadataccen haske a dakin sosai,yana daga gefe saman dan table din da yake dora system dinsa yayi wasu ayyuka da suka shafeshi yana duba wasu takardu.

    Kallo daya ya mata ya maida kansa ga takardunsa,kallon da ya bata mata rai sosai taji kamar ta koma ita da abincinta,amma ta hadiye ta danne,tana da burika da yawa da takeso ta cimma,kuma anty ummee ta tabbatar mata sai ta iya mallakar kanta da kuma fushinta.

    Wani table qarami na glass ta jawo ta aza kayan a kai,tana shirin zama tace masa

    “Ga abincinka nan”

    “Am okay,ki kwashesu” ranta tadan bata,ta zumbura baki,kamar zatayi magana sai kuma tayi shuru,taci gaba da kallonsa,yayin da shi kuma ya aza dukka hankalinsa akan takardar dake dauke da wani zane mai kama da map,ya sani ba zata iya bashi haquri ba,abune mai wahala kaji kalmar haquri daga bakinta.

    Sai da ya gama abinda yakeyi ya ninke takardar sannan ya miqe

    “Jibi zamu wuce kaduna in sha Allah” ya fadi mata don ya fita hakkinta,gabanta yadan fadi

    “naji kace zaku wuce,kai da wa?”

    “Widad” ranar farko da ya fara ambatar sunanta,idanu ta qanqance cikin mamaki da ba zata tace

    “Na dauka a nan zaka barta ko”

    “Saboda ke ba zakije ba,kowa ma haka ne?” Wani tashin hankali ne taji ya ziyarceta,me abbas yake nufi?,ita zai barta a nan,ya tasa qanqanuwar yarinya a gaba su tafi garin da yake aiki?,ita tana nan tana me?.

    Sai da tayi yaqi da zuciyarta sannan ta hadiye maganganun da su taji sunfi dacewa ta gaya masa

    “Amma idan kun tafin me zata tsinana maka?,ka barta kawai a nan ta saba da dangi mu tafi tare” kai ya girgiza yana nufar wardrobe dinsa ya budeta sannan ya amsa mata

    “Ai bana magana biyu,kinfi kowa sanin hakan,zancan tafiya kaduna mun rufe wannan babin dake har abada,abinda yasa na gaya miki yanzun ma don na fita hakkinki,duk weekends zan dinga shigowa in sha Allah” wani abu ya taso ya tsaye mata a wuya,wannan karon taji ba zata iya shuru ba,ta yaya zai sanya yarinya qarama a gaba su tafi har wani gari,ita din tana jingine a gefe,sai qarshen sati sannan yazo mata?,me ma tayi kenan?,abinda take gudun afkuwarsa tabbas zai afku

    “Gaskiya ni ban yarda ba,saboda nice babba ni ya kamata ace na bika,ko ka bani zabi…..”

    “Wanne zabi zan baki?,ki manta tun kafin wanzuwarta kika yiwa kanki zabi?,hafsat kinga….. please bana son ciwon kai,zancan ya isheni haka…..ina underwears dina?” Ya jefa mata tambayar yana ritsata da ido

    “Ban wanke ba” ta amsa masa tana miqewa cikin hucin bacin rai

    “Good” yace da ita yana maida murfin wardrobe din ya rufe zuciyarsa na masa zafi,duk sanda yake da buqatar neat underwears saidai ya zauna ya wanke abinsa da kansa,ko kuma ya diba yakai mata,ya kuma jaddada mata amfani zaiyi dasu,wataran ta diba wasu daga ciki ta wanke masa,wataran kuma ta wanke duka idan taso.

    “Abban mimi….” Ta kirayi sunansa da kaushi, ganin bai qara bi ta kanta ba,ya nufi ma qofar toilet dinsa

    “Duk haquri da kuma kawaicin da nake maka hakan bai hanaka gaza yimin adalci ba ko?,to wallahi bazan yarda ina zaune a tauyemin hakkina ba” zuba mata idanu yayi sosai fiye da dazu yana kallon zallar ainihin rashin kunya daga wajen hafsat din,eh rashin kunya mana,banda haka ta manta abinda tayi masa

    “Tunda kika zabi zama a bauchi baki isa ki bini ko ina ba,kince na nema mai zama dani a kaduna kuma na samu fine….na dauka hankali kikayi kika fara gyaro kura kurenki,ashe ba haka bane,to a wannan karon ina mai gaya miki da kakkausar murya,kibi a hankali,don bazanci gaba da lamuntar halayenki ba,if not kuma…..mu zuba dani dake” daga haka yayi gaba ya bude qofar toilet din ya shige abinsa.

    Wasu qwalla masu zafi ne suka biyo kuncinta

    “Wallahi zankai inda za’a qwatar min hakkina,nima na gaji” ta fadi tana juyawa da gudu gudu ta fice daga dakin.

    Sanda ta gifta sassan widad dake kulle sai taji kamar ta koma ta shiga ta shaqeta ko zata rage zugi da radadin da zuciyarta ke mata,amma wata zuciyar ta hanata,ta wuce da sauri sauri zuwa sashenta tana kuka sosai.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/2, 10:44 AM] +234 802 297 0646: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 49

    Arubuce Ta Ke 49

    Page 49

    Awanni kusan hudu kenan tana abu guda,baya ga kitchen din data yiwa kaca kaca kota ina,kamar wadda ke girkin mutum ashirin,sannan daga bisani ta samu ta kammala tuwon shinkafa miyar kubewa iya yadda taga latifa tana yi,ta zuba cikin sabbin warmer masu kyau da aka hado cikin siyayyar cefanen da aka kawosu jiya.

    Dafe bayanta tayi bayan ta kammala gyare kitchen din

    “Shi tuwo dama haka yake da wahala?”ta fada tana yatsina fuska,duk da can qasan ranta farinciki ne fal,wai yau itace da yin girki cikin kitchen dinta,ba kwaba ba hantara babu bakiyi dai dai ba,ta juya ta soma diban warmers din takai saman dining,ta jeresu da kyau,tana kallonsu tana murmushi,har cikin ranta dadi take ji idan ta tuna wai yau ance tayi girki.

    Dakinta ta koma tayi wanka,ta shafa powder a kyakkyawan fuskarta mai santsi da sheqi dauke da tambari na quruciya,dubai abaya wine color da tasha adon duwatsu masu walwali ta fidda ta sanya,ta daura dankwalin saman kanta,ta kuma shafa turarukanta kamar yadda ya taba gwada mata yadda ake sanyasu,tun daga ranar kuwa ta dauke tsaf,yadda ya kwatanta matan haka take sakawa,ita kanta sai taji tafi jin dadinsu.

    Sosai abayan ta haska jar fatarta,kamanninta suka fito sak na ainihin tushen yankin data fito,ta koma gefan gadonta bayan ta dauko wayarta dake saman madubi,ta bude ta shiga wata game da taketa daukan hankalinta ta fara bugawa cikin qwarewa.

    Hankalinta yayi nisa sosai a game din,har bataji qarar motarsa zuwa shigowarsa cikin gidan ya kuma tura qofar dakinta ba,sai ya tsaya riqe da handle din qofar dakin,zai iya lissafa adadin shigowarsa dakin,idanunsa saman fuskarta,tattausan siraran labbanta sunata qyallin lips balm,tana ta juyi saman gadon,duk sanda taci game din sai tayi dan tsalle kadan na murna sannan taci gaba.

    Idanunsa ya dauke sannan yayi gyaran murya kadan ya hada da sallama,daga idonta tayi daga kan wayar zuwa kansa,saita aje wayar gefanta tana masa sannu da zuwa,sannan a dabarance tana laluba maballan gaban rigarta taji sun rufu da kyau?,ta kuma tsareshi sosai da ido taga ko.yana kallonta?.

    Sarai yaga abinda takeyi,amma sai ya kauda kai ba tare da yakai idanuwansa kan qirjin nata da yake ganin basu da maraba da qirgar dangi a wajensa ba

    “Tare da baqo nake,ki kawo abincin” kai ta gyada masa,ya saki handle din qofar ya juya zuwa falon,yana duba wayarsa daketa ringing.

    Ba kowa ke kiransa ba sai hafsat,tunda satin ya wuce taga baizo weekend ba hankalinta ya gaza kwanciya,gaba daya zuciyarta cike take da wasi wasi da kuma fargaba,duk kuwa da bayanin da yayi mata na cushewar aiki da ya samu a kaduna fiye da dukka garuruwan da yake zuwa aiki,amma zuciyarta ta kasa aminta da hakan,duk inda yake baya wuce satin nan dai baizo bauchi ba ko don hajiyarsa,sai wannan karon?,sai wannan lokacin daya tafi da wannan sadakar yallan?,anya ba holewarsa yakeyi ba?,anya bai samu wani abu bane daga gareta?.

    A kullum kwanan duniya kira uku zuwa hudu ne sai ta yiwa widad shi,ta tambayi ya suka kwana?,ya suka tashi?,ya suka yini?,ya dawo gida kuwa?,me ya faru a tsakaninsu?.

    Sam widad din bata boye mata komai,rashin wayo da qarancin shekaru yasa bata dsuki wannan din a mazaunin komai ba,face ma qauna soyayya da kulawar da mommy hafsa din ke nuna mata,wannan yasa ta sake ganin kimarta,ta kuma sake ganin girmanta,hakanan taji tana qaunarta,shi yasa dukkan abinda zata umarceta dashi take aiwatarwa kanta tsaye,wannan dalilin ne kuma yasa tayi riqo da hudubarta yadda ya kamata,don ya zame mata kamar tishi ne akan tarbiyyar ummu,sai faduwa tazo dai dai da zama,tana nisantarsa iyakar iyawarta,tana kuma qauracewa duk wani abu da tasan mommy hafsa ta gargadi akai.

    Ta sani ta kuma fuskanta,sam qarya bata cikin dabi’ar widad,da gaske haka take tun a gida,duk da samun wannan tabbacin,hakan bai sanya zuciyarta da ruhinta sun aminta sun kuma kubuta daga zargin abbas ba, don haka taketa kiransa,tanason taji yaushe zai zo din.

    Ajiyar zuciya ya sauke,yau inda ace buqata ce da hafsat din dole.ya ajjiye dukkan abinda yakeyi yaje ya sauke mata ita,to amma yafi kowa sanin wacece ita,tana iya share wata guda koma fiye bata buqaci komai daga gareshi ba,saidai shi din ya nema,a yanzun ma.ya tabbatar ba wani qwaqwaqwaran dalili ne da ita ba na kafewar ya taho din,ya bata dukkan wata dama da zata fadi uzurinta amma amsa daya ce

    “Kawai son ganinka nakeyi”

    “Kiyi haquri,indai ba babbar buqata ce dake ba……akwai aikin da nakeyi a nan din,banason kuma na matsa daga kaduna sai na kammalashi,aikin yana buqatar sirri kula da kuma takatsantsan” amsar daya bawa hafsan kenan,ta furzar da iska dgaa bakinta,zuciyarta na raya mata ta shirya ta tafi Kaduna kawai,to amma sanin girman laifin data aikata masa wanda yayi silar haramata mata Kaduna kwata kwata yasa ta sake jaddadawa kanta wannan ba mafita bace,zata bi ta hanyar da tasan dole yazo gida koda baiso ba.

    Sai data nema yalwataccen mayafi ta yane jikinta dashi sannan ta wuce falon,idanun abbas din a kanta,hakanan yaji abinda tayin ta burgeshi,bai gaya mata ta yafa din ba,amma tasan ya kamata,ta tsugunna har qasa ta gaida ameen abokinsa,sannan ta wuce ta soma dauko warmers din tana jera musu bayan ta shimfida table mat a qasan.

    Ta tsara komai yadda ya dace,har cikin ransa yaji abinda tayi ya burgeshi,ruwan sha dana wanke hannu duka akwai a wajen,abinda hafsat bata taba yi ba,dai dai da tissue daya dace ko yaushe a sameta saman dining sai ya nema,ita kuwa ta koyo hakanne daga wajen ummu,haka taga tana yiwa alhaji.

    Har ta juya zata wuce daki,sai taga ana hasko wani cartoon da take mugun so,fasa shiga dakin tayi,ta dawo ta zauna fuskarta cike da fara’a,kadan abbas ya waiwaya ya kalleta,kamar zaiyi magana saiya fasa,ganin irin excitement din dake kan fuskarta na ganin cartoon din,ya maida kansa ga warmer din,ya bude ya sanya hannunsa ya dauko malmalar tuwon farko.

    Tun baikai ga budeta ba ya fahimci an samu babbar matsala,duk da haka bai fasa ba,ya wareta yana sakinta saman plate,take kuwa tuwon ya dare biyu,suka hada ido da ameen din,sai abbas din ya basar,ya bude warmer din miyar,koriyar kubewa shar,wadda aka qarantawa kayan hadi ta bayyana,bama kayan hadi ba,harda kayan dahuwa,wake yayi tsuru tsuru yaja gefe,ga danyan manja a sama ya hade rai.

    Serving spoon yasa ya kwaso musu ita da qyar ya zuba akan plate din,ya maidata ya rufe ya saka musu cokula yana cewa da ameen

    “Bismillah” dukka dauriyarsa amee din ya gayyato,ya matso ya dauki cokalin,suka sanya lomar farko a tare da abbas din.

    Spoon din ya ajjiye sannan ya miqe yana duban abbas

    “Kasan nayi mantuwa a office,zan koma,daga can gida zan wuce” yadda ameen din keta rattaba bayani ya bawa abbas dariya,amma sai.ya qushe abarsa,gulma ce da ganin qarshen mutum tasa yace zaya biyoshi

    “Okay….sai na fito” ya amsa masa,sai ameen din ya juya yana cewa

    “Amarya,ni zan koma ko,ina godiya sosai,sauri nake.ban samu naci abincin ba,amma…… next time”

    “Ka gaida gida” ta furta a sanyaye sanda ta kalli abincin taga kamar babu abinda ya dandana,idanunta nakan plate din har ya fice a gidan.

    Dukkan alamu sun nuna.girkin nan nauyi dadi ko ma’ana ba sam,jikinta a sanyaye,ta tabbatar shima ajiye mata abincinta zaiyi,ba iya ci zaiyi ba,musamman data hangi yadda tuwon ya baje abinsa,ya koma kamar shinkafar da bata samu wadatacciyar dahuwa ba.

    A mamakance ta maida dubanta ga fuskarsa,sai kai abincin bakinsa yake,kamar babu wani abu da baiyi dai dai ba a girkin,karo na uku suka sake hada idanu tana masa kallon mamaki

    “Zonan” ya fada a tausashe yana yafitota da hannunsa,saita aje filon data dora saman cinyarta,ta miqe a sanyaye ta nufeshi.

    Idanunta na tara ruwan hawaye.

    Gabansa ya nuna mata,ta zauna a hankali tana sake ja baya kadan,qaramin murmushi ya subuce masa yana kallon qwayar idanunta,sannan ya tsame hannunsa daga abincin bayan yaci wani adadi mai yawa

    “Tuwo yayi fa dadi,gyaran kadanne” da farko shuru tayi tana dubansa,fuskarta dauke da alamun mamaki,daga baya kuma sai murmushi ya subuce mata,cikin wani irin zumudi da sakewar da bata tabayi dashi ba

    “Allah?,ashe dai na iya girki” ta fada cikin murna,kai ya gyada mata yana kallonta

    “Kin iya,amma na fiki iyawa ai” ido ta fidda waje tana dubansa

    “Namiji dama ya iya girki?” Ya jinjina mata kai qaramin murmushi na fita daga fuskarsa

    “Iyawa kai,ki shirya daga gobe zan fara koya miki irin nawa” sosai taji dadi da fadin hakan da yayi,ita din tanason taga ta iya girki irin na anty madina da anty deena.

    Cikin ransa yakejin dole haka zai samu lokaci cikin lokutansa ya ware ya koya mata wasu abubuwan kafin ya laluba makarantar koyon girki ya sakata,at least koda girkin ta iya zai rage wani abun.

    Washegari da safe shi yayi mata knocking ta fito,ta rusuna ta gaidashi tana sanye da kayan bacci masu kauri riga da wando da wando,tana biye dashi suka isa kitchen,ya sama mata kujera yace

    “Zauna a nan ki gani” murmushi ta sake tana kallonsa,sanye da wani wando na sojoji da farar shirt,ta zauna din sannan ta jefa masa tambayar dake cinta tun daxu

    “Wai kai police ne kuma soja ne?” Sai daya juyo ya kalleta da manyan idanunsa,sai tayi tsuru tsuru kuma tana dafe bakinta,tana jin kamar tambayar tayi yawa,kai ya girgiza yana sakin fuskarsa

    “Ni police ne me kama masu laifi” saita jinjina kai tana murmushi kawai.

    Cikin kitchen din taci gaba da zama,kome zaiyi sai ya nuna mata,saidai tana daga gefe tana d’ari d’ari dashi,bata bari tazarar dake tsakaninsu tayi kusa,ya lura amma dariya kawai take bashi,daga baya bayan ya gama hada komai,ya bata yanke yanke yace tayi masa tana daga zaune.

    Cikin awa daya da rabi suka hada breakfast mai kyau tare,ta dinga murna tana jin dadi,shi kam saidai ya bita da ido,bayan sun kammala yabar mata kitchen din ta gyara,shi kuma ya wuce dakinsa yin wanka,ta gyara ta kwaso komai ta kawo falon,saita zube saman kujera tana maida numfashi,don tadan gaji,sai data huta sannan ta wuce itama dakin don yin wankan.

    A ranar ma ya samu sauqin aiki,don haka da rana ya dawo gida,ganinsa a gida da rana ba qaramin dadi yayi mata,ashe mutum rahama ne,cikin zuciyarta ta dinga jin wani dadi,duk da babu abinda ke hadasu daga sannu da zuwa zai wuce dakinsa ne,bayan ya fito suka sake shiga kitchen tare,ta dinga murna da zumudin son ganin me zasu dafa,abinci sassauqa sukayi,itadai tana ta mamakin yadda namiji ya iya girki haka,bayan sun gama kowa yaci nashi ya sake shiryawa ya koma.

    To da daddare ma haka,sabon girki sukayi,duk abinda yakeyi idanunta na kanshi tana biye,haka ce taci gaba da kasancewa,cikin satin gaba daya aiki biyu ya dinga yi,yayi na office ya dawo gida ya koya mata abinda ya sawwaqa,wani lokaci idan bai samu dawowa da rana ba,to da daddare akeyi.

    Cikin satin sai gashi an samu ci gaba,ta riqe wasu abubuwan,da yake widad din badai kai ba,kuma tana da qaunar yin girkin,sai gashi a satin ta iya hada breakfast,hakanan abincin duk daya koya mata ta fara gwadawa,yana kuma yi,saidai hannun baikai ga fadawa sosai ba.

    Ranar wata alhamis bayan sun gama girkin dare ya fiddo foam yace ta matso ta bashi bayananta zai cike,foam ne na wata makarantar secondry ta ‘yammata daya samar mata zata ci gaba da zuwa,tsananin murna yasa ta fada jikinsa ta qanqameshi tana godiya,sai kuma ta sakeshi da sauri taja baya,jikinta nayin wani irin sanyi,kada fa mommy ta gane ta rungumeshi,tayi tsuru tsuru,har sai daya fahimta,ya dade da fahimtar wannan,koda a kitchen da suke ayyuka tare duk abinda zai kawo haduwarsu waje guda tana daga baya baya,ko abu zai bata sai ya ajjiye take dauka,hakanan suna gama komai take qulewa daki ta kulle abinta,shikam dariya take bashi,kamar yanzun,baisan me take tunani ba,shikam indai abinda take tunani ne idan yayishi yace yayi me?,saiya girgiza kai kawai yana boye murmushinsa cikin fuskarsa ya fara cike mata foam din,bayan ya gama ya miqa mata yana cewa

    “Idan zan fita gobe zan karba na fita dashi,and….ki shirya jibi zamu je bauchi” ta karba foam din jikinta a mace,sai taji inama ace kano yace mata zasuje?, tabbas da ranar ba zata iya bacci ba.

    *Arewabooks: Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 57

    Arubuce Ta Ke 57

    1. Page 57

    To tun daga wannan rana kwananta ya dawo dakinsa,saidai tana kammala sallar asuba take komawa dakinta ta shirya shirin makaranta,wani lokaci shike kaita,wani lokacin kuma samuel ko daya daga cikin yaran dake qarqashinsa.

    Aikin da yakeyi yasa a yanzun zamansa a gida yafi yawa,wannan ya fara haifar da shaquwa a tsakaninsu,duk da baya barin kowa ya rabi inda yake wannan aikin amma yawancin lokuta suna tare,badai hira sukeyi da ita ba,amma zata dauki littafinta ta zauna a wajen,ko ba komai tana jin motsinsa bata da kewa,lokaci bayan lokaci tana barin karatunta tadan zuba idanu tana kallonsa,idan sun hada ido kuma sai ta basar,murmushi kawai yakeyi ko yayi kamar bai gani ba yaci gaba da abinda yakeyi,aikin nasa ke bata sha’awa yake kuma burgeta,tanason masa tambaya amma kuma tana jin nauyi,don har yanzu bata gama sakewa dashi ba.

    A lokacin yayi qoqari matuqa ya koya mata abubuwa da dama,har ya fara sakar mata,don majority ita ke dafa musu abincin rana,kuma ya ciyu saboda gyaran bashi da wani yawa.

    Wannan karon ma bai samu zuwa bauchin ba sai bayan sati biyu,tanata hada kaya ta zaci da ita zaya je,sai yace a’ah,tayi zamanta,ta dinga masa kuka amma daga baya dole ta haqura,ya yiwa mai gidan magana matar gidan ta bata ‘yar tayin kwana suke kwana tare,friday ya tafi ya dawo sunday da magariba,saita samu kanta cikin murna da farinciki ranar daya dawo din,wanda ita kanta batasan dalili ba,tunda dai ya tafi taji gaba daya bata da sukuni.

    Zuwansa bauchi a yawancin lokuta bacin raine,yana zuwa ne kawai don ya sauke nauyin da Allah ya dora masa,ya kuma kwatanta adalci,amma baya ga haka baiga wani alfanu da yake samu ba,hafsat din ta yita mita da nunqufurcin bai taho da weedad ba,don ta tara ayyukanta jingim suna jiranta,gidan ya hada mugun datti da qura yadda ya kamata,to koda yaje ma kusan washegarin ranar a aikin kintsa gidan ya qarar dashi,daga qarshe sassan weedad din ya bude ya kwanta yayi baccin gajiya a falonta,ki sashen nata da babu dan adam baiyi wannan qazancewar ba,da yamma ya fice wajen hajiyarsa,wadda ta dinga jajjabin abinda yasa baizo da weedad din ba,a haka dai ya qare weekend din nasa a gantale babu wata kyakkyawar maraba.

    Haka kawai ta samu kanta da son masa gwaninta,yana fita sallar magariba din a gurguje ta shiga kitchen,ta hada masa simple spaghetti jallop,da murmushi yake kallonta sanda ta dire masa ita,taliya ba cimarsa bace,amma kuma sai yaji ta burgeshi dari bisa dari,ko babu komai tafi hafsat din wadda a qalla nata shekarun sun ninka na weedad din,amma ko irin hakan batasan tayi masa ba,don haka yaji bazai iya watsa mata qasa a ido ba,yaja taliyar ya soma ci,taste dinta sai ya bashi mamaki qwarai,har ya kasa jurewa

    “Yammata irin wannan abincin fa?,a ina kika koyo shi?” Sunan daya kirata dashi ya bata kunya,saita kifa kanta saman pillow tana dariya,batasan sanda suka fara irin wannan wasan dashi ba

    “Kaine ka koyamin” kai ya girgiza yana sakin murmushi

    “Wannan kaman ba aiki na ba” kuma ya fada dinne har zuciyarsa,saboda dandanon ya zarta yadda ya koya mata din.

    Daya tashi komawa bauchi da ita ya tafi saboda hajiyarsa dake ta tambaya,hakan ya yiwa hafsat dadi,ta sake miqa dukka wasu ayyukan gida ga weedad din,bata samun zama ko hutu saita gama dukka wasu aiki na sassan hafsat din,hakanan hidimar yaran gaba daya ta dawo hannunta,wankansu wanki cire pampers,basu abinci da sauransu,tun tana jin gajiya da wahala har ya soma zame mata jiki ta saba.

    Wani zuwa da sukayi,ranar asabar da azahar,tana kitchen din hafsat din tana gogeshi bayan ta gama wanke kwanukan da suka cika babban sink din kitchen din,cikin ranta cike fal da mamakin yadda take barin kitchen ya hada wannan uban datti da kayan wanke wanken kamar na gidan biki ko suna,mimi da nawwara na falon data gama gyarawa suna wasa,ta kadasu can don su barta ta gyara nan din a nutse,a dole ta sake qwarewa ta samu kuma experience sosai akan harkar kitchen da kula da yara.

    Sau biyu anty ummee na sallama sai surutansu mimi,har sai data bude qofar falon ta shigo,tabi falon da kallo zuciyarta cike fal da mamakin yaushe hafsta ta koyo tsafta?,yaran da suka ankare da shigowarta suka watsar da kayan wasan suka taho da gudu suka rungumeta

    “Ina babarku?”

    “Tana dakinta,ta kwanta tace kada a tasheta”

    “Babanku yana nan ne?” Kai ta girgiza

    “Ya fita a mota”

    “Muje cikin” ta fada tana kama hannunsu,har yanzu tana mamakin kintsuwar falon,duk da tazo kwana hudu da suka wuce amma ba haka ta samu falon ba.

    Tana kwance male male saman gadonta tana sana’artata wato chart,harta bude baki data ji an bude qofar zata hau masifa,a zatonta weedad ko yaran ne saita maida maganar dake cikinta tana murmushi ta miqe ta zauna saman gadon ganin anty ummee ce

    “Daga ina haka ba kira ba sanarwa?” Harara ta balla mata tana samun gefan gadon ta zauna

    “Kedai baki da hali,don zanzo gidanki saina gaya miki?” Dariya tayi

    “Allah ya baki haquri ba haka nake nufi ba” bedroom din nata anty ummen ta sake kalla

    “Nace ba,wai yaushe kika fara tsafta ne?,don nidai banga haka a jikinki ba” tafadi tana kallon jikin hafsat din,wadda ko brassiere babu,sai wata t-shirt data mata yawa da zanin atamfa,kanta kuma tsifa ce rabi da rabi.

    Fuska ta tsuke tana kallonta,tasan halin anty ummee idan ya motsa in ba cin mutunci tataba mata ba bata jin dadi

    “Ni dadina dake wlh cin fuska,aidai jikin nawa babu qazanta ko?”

    “Nima bance akwai ba” ta amsa mata tana boye dariya,sai hafsat din ta gyara zama tana cewa

    “Yarinyar nan ce sunzo weekend,ai na gayamiki indai sukazo bani da matsala,nima nawa weekend din nakesha”

    “Kina shan weekend dinki amma na ga kanki rabi da rabi,a haka mai gidan yazo ya sameki?” Kan nata ta shafo

    “To mene?,kitso naso azo ayimin kuma na kasa qarasa tsifar tun shekaran jiya”

    “Allah ya tsinewa qazantarki” anty ummee ta fada cikin ranta,amma a fili saita mirgina kai kawai,tasan kome zata gaya mata abanza,tunda ba yau farau ba,indai akan tsaftane

    “Amma dai ya kamata kiyi amfani da damarki duk sanda yazo weekend ya zamana kin qara kawo kusanci tsakaninki dashi”

    “Manta da wannan anty ummee,kome zakiyi masa baki taba burgeshi” baki ta tabe

    “Ai shikenan,Allah ya kyauta” daga haka ta maida kallonta ga dakin,ta fara bin ko ina da kallo tana neman abinda zata rabauta dashi,ganin haka sai hafsat din ta tsuke fuska da kyau,tasan yanzun zata rabata da wani abu,don haka ta zamo daga gadon tana daura zaninta

    “Muje falo anty ummee,kada a shigo gidan babu kowa a daukemin wani ita tana ciki tana aiki bata sani ba” ta fahimceta sarai,bata ce komai ba tadauki jakartata suka dawo falo,amma cikin ranta taci alwashin sai fa ta fita da wani abu daga gidan

    “A banza zan dinga baki shawari” ta fadi a ranta.

    “Nifa dadina dake rowa wlh,ko ruwa ki kasa bawa mutum?” Anty ummee ta fada ganin sunata zuba zance amma ko ruwa bata mata tayinsa ba,kusan wannan din dabi’ar hafsat ce,bawai wani abu bane a wajenta

    “Kai anty ummee,kedai kin cika qorafi wallahi”

    “Ahto ai gaskiya ce” daga nan inda take zaune ta qwalawa widad kira tace ta kawo ruwa,ajjiye mop stick din hannunta tayi,ta samu plate ta hado ruwa da kuma lemo babba da qarami me sanyi da cup,kamar yadda ta saba gani a gidansu ummu nayi,ta nufo falon.

    Idanun anty ummee a kanta harta qaraso,ta tsugunna ta ajjiye kayan sannan ta gaidata ta miqe ta koma ciki.

    Sai data koma sannan ta dauke idanunta daga kanta ta maida ga hafsat

    “Hafsatu,ya naga yarinyar nan tana girma ne?,kinga yadda take canzawa?” Baki hafsat ta tabe

    “Na gani,nima abun yana dan damuna,duk da dai nayi mata dashen dana tabbatar bazai barsu suyi kowacce irin sakewa ba,kai qarshe ma idan ya matsa nasan rikici za’a yi ba dan qarami ba,namiji kuwa kinfini sanin ba haquri gareshi ta wannan bangaren ba” kai ta jinjina

    “Eh da haka kam,amma dole mu sake lalubo wata hanyar kafin ta fahimci duk gaibu kike gaya mata” mugun tsaki hafsaa din taja

    “Kuma dai?,ni na fara gajiya,haka kawai kana zaman zamanka banda namiji matsiyaci ne ya dauko abinda zai hanaka sakewa,shi bai amfana ba kai baka sake ba,aikin banza kawai” ta sake fada tana jan mugun tsaki, idanunta har sun sauya launi,da kallo anty ummee ta bita tana fasa lemon da aka kawo mata,a baqin kishin hafsat dinma bata dauka za’a kai warhaka gayyar bata watse ba,saidai tana alaqanta dadewarta akan plan din da morar yarinyar da takeyi.

    Bayan ta shanye ta dauki dayan ta jefa a jakar hannunta,don tunda ta samu wannan damar ba zata barta ba,hafsat din kuwa ta bita da kallo cikin ranta tana fadin

    “Kwadayayya hadamammiya” yayin da anty ummee din ta waske da cewa

    “Karki damu,kafin lokaci ya qara turawa za’a samo wata mafitar”.

    Sannu a hankali rayuwa ta dinga juyawa,watanni suka fara shudewa,tsakanin widad da abbas yanzun akwai sakewa da sabo ba kamar baya ba,duk da cewa ba wata mai yawa bace,don bata bari ya kusanci inda take sosai,idan ka gansu zakayi tsammanin yaya ne da qanwarsa da yake matuqar bawa kulawa,zuwa sannan weedad din ta fara girma ita a karan kanta tana ganin wasu sauye sauye,ta fannin girki ta iya abubuwan da baza’a rasa ba,sosai kuma takejin dadin makarantar ta,ta fara sabo da mutane,ta kuma fara karantar rayuwa da yadda mu’amala take tsakanin mutane

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

    *_Arewabooks:huguma_*

  • Arubuce Ta Ke 51

    Arubuce Ta Ke 51

    Page 51

    Tun tana wanke wanken na marmari har ta soma ji gaba daya hannayenta sun fara mata zafi,sannu a hankali gajiya gaba daya ta saukar mata,hannunta yayi jazur saboda wankin kwanukan da kuma zafin detergent,tunda tunda uwarta ta haifeta bata taba wanke wanke mai yawan haka ba,da qyar ta samu ta kammala,ta gyara daurin dankwalinta daya sabule ta baro wajen.

    Babu kowa a falon,bama alamar suna nan,hakan yasa ta wuce zuwa sashenta kai tsaye,bayan ta ciro key din da ya bata a qaramar purse dinta.

    Idanu a narke ta shiga sashen nata,sai zuciyarta ta karaya,taga kamar zataga latifa,ta tuna wayon data yi mata ranar da zasu bar bauchi,komai yana nan a killace yadda latifa ta barshi,ba wani datti sai ‘yan qananun qura dake shiga wajen sanadin babu giftawar kowa,ta zube saman kujera tana share qananun qwalla,itakam tana jin kamar tsanarta akayi,kowa yana gida banda ita?,hakanan ta gaji da zaman,ba motsin kowa cikin gidan,ba alamun kuma zata samu wani abun da zata ci,ta miqe cike da shegen tsoron nan nata cikin sanda ta isa kitchen,ta duba store dinta ta fidda indomie,cikin tsoro da fargabar kada ta cabe irin ta rannan ta kunna wuta ta dora.

    A kitchen din ta zauna harta dahu,ta juye a plate,tasa fork ta debo ta dandana,sai murmushi ya subuce mata,tayi dadi fiye da yadda ta zata,har abun ya burgeta ita kanta,ta dauki plate din da hanzarin tayo hanyar falo,tana fitowa sai tayi turus da plate din a hannunta,ta manta ba’a kaduna suke ba,ta yaya zata wuce momy hafsat dake gargadinta koda yaushe ta tafi dakinsa?,saita koma ta zauna jiki a salube,ta sanya cokalin ta fara diban taliyar tana ci,ko TV ta kasa kunnawa saboda tsoro,sai taji kamar ana tafiya daga bayanta.

    Duk da ba’a nutse take ba amma hakan bai hanata jin dadin taliyar ba da gaske,tana ci idanuwanta suna mata nauyi,don haka kafin ma ta kammala bacci ya kwasheta a wajen,ko hannu bata samu wankewa ba.

    Daga yanayin da ya samu gidan yasan cewa babu wani abinci da zaya samu,don haka koda aka idar da sallar magariba bai shigo gidan ba sai da akayi isha’i,daga nan kuma ya dauki motarsa ya wuce yayi musu takeaway,bai bi ta halin hafsat din ba,don ko kaffara bazaiyi ba yasan ba wanda ya qoshi a gidan ciki harda yaranta,don haka ya hado dasu.

    Afalo ya sameta ta kammala mopping,tana ta fada dasu nawwara,fadan da bashi da dalili,yasan dai duka bazai wuce akan aikin sharar daya sanyata ba,yaran suka masa oyoyo ya daukesu yayi hugging dinsu,sanna ya ajjiyesu hade da ledar hannunsa yana cewa

    “Bari naje na dawo muyi dinner ko?” Suka daga kai cikin zumudi da jin dadi.

    “Ina kuma zaka je?” Ta tambayeshi cikin d’ar d’ar ganin ya kama hanyar fita da leda daya,waiwayowa yayi ya dubeta,bai bata amsa ba yaci gaba da takawa

    “Kawo nakai mata ka zauna kai kaci naka abincin” ta furta tana matsowa,saidai kafin ta iso ma ya fice abinsa,baisan me yake damun kanta ba,ita idan tayi laifi ma bata yarda tayi bare ta kamo hanyar gyarawa.

    Sau hudu yana knocking yaji shuru,sai kawai yayi amfani da spare key dinsa ya bude ya shiga.

    Sassanyan qamshin turarukan da latifa ta tsuma sassan dashi har yanxu yana nan,kamar ma a yanxun ake turara wajen,turaruka masu tsada da kama jiki na asalin shuwa.

    A yashe ya hangeta saman carfet ta cure waje daya,ya taka a hankali zuwa cikin falon,ya dauki remote ya sanyin ac din,ya ajiye remote din ya maida dubansa gareta,ko pillow babu a kanta,ya ajjiye ledar a hankali a gabanta,sannan ya durqusa yana tunanin yadda zai gyara mata kwanciya.

    Pillow din ya miqa hannu ya dauko,sannan ya zauna sosai,ya sanya hannuwansa duka biyu ya dagota,sumar kanta data baje ta watsu saman baby face dinta,sosai pink lips dinta suka dauki hankalinsa,bai taba kallonsu da kyau irin yau ba,wani irin sexy lips masu daukan hankali,girarta da suka kusa hadewa da juna ta sake qawata fuskarta da kyau.

    Ji yayi sunyi mugun kusanci da juna,kamar wanda aka sawa electric shock ya saketa da sauri,ta farka a firgice sanadin sakinta da yayi,jinta kusa da mutum kuma ya sake sakawa ta tsorata da gaske,saboda tasan dai already kafin ta kwanta ta rufe qofarta.

    Ihu ta sanya sosai a tsorace,yasa hannunsa da sauri ya rufe mata bakinta yana cewa

    “Ke….meye haka,it’s me” jin muryarsa ya sake kad’a mata cikinta,ta tattara qarfinta tana tureshi,dai dai lokacin da hafsa wadda ta saka zama ta biyo bayansa ta turo qofar falon da sauri ta shigo.

    Da yadda za’a fadi yadda taji a lokacin ya wuce haka,gaba daya ji tayi wani tashin hankali ya rufto mata,widad din a jikin abbas dinta?,sam batasan gabansu take nufa ba,har sai data isa,gaba daya zuciya ta gama gaya mata ta fincikota daga jikinsa ta rufeta da mugun duka ne,saidai tana isa din abbas din yana buda hannayensa widad din ta fice tana sakin dan qaramin kuka,gaba daya a tsorace take, jikinta sai rawa yakeyi tana kallon fuskar hafsat wadda ta ritsata da idanu,hantar cikinta ta gama kadawa kamar wadda aka kamata da kwarto,yanxun me zata cewa mummy?,duk yadda take kiyayewa da yin takatsantsan yau ta kamata a jikin wani.

    Mugun kallon data watsawa widad din ya sanyata cikin sauri da kuma rawar murya tace

    “Wallahi mummy ina cikin bacci,bansan ya shigo ba….” A nutse abbas dake tsaye ya waiwaya ya kalli hafsat din,da sauri ta dauke rikitaccen kallon da takewa widad ta maida ga abbas din cikin rudewa,yarinyar tana son balle mata liqin da tayi,sukayi kallon kallo na sakanni,kallon data hangi ayoyin tambaya masu yawa a idanun abbas din,ta hadiye wani yawu mai tauri,cikin qasa da second goma dabara ta fado mata,ta maida dubanta ga widad din

    “Ni Matsalata dake shegen tsoro,kinsan dai gidan nan babu wanda zai shigo,dagamu sai mu,ki dinga addu’a idan zaki kwanta kinji” tayi maganar cikin karyar da harshe,saita matsa tana zaunar da widad din sosai,amma qasan zuciyarta a mugun matse yake,kada fa ya zamana abbas ya fara latse d’iyar mutane,ta miqe sosai ta tsaya tana dubansa

    “Abban mimi…..ka dinga haquri,kaga dole ayi mata uzuri,akwai quruciya sosai a tare da ita” lumshe idanunsa yayi bisa fuskar hafsan,shi baima gane abinda take fada ba,gaba daya bugun zuciyarsa ne yake neman sauyawa,saiya maida dubansa ga hafsat din dake matsar qwalla

    “Ga dinner dinki nan,ki taso ki rufe qofar” ya furta yana juyawa cikin mutuwar jiki,sai hafsat ta biyo bayansa tana cewa

    “Kisa key ki rufe qofan falon kinji,saiki rufe ta bedroom din ma,sai da safe”

    “To Mommy” ta fada,cikin ranta tana jin tazarar son da hafsat din ke mata abbas din bai kama koda kwatarsa ba,haka tasa muqulli ta rufe qofar sannan ta dawo falon,tsoro ne fal ranta da zuciyarta,tana jin kamar ta bisu,amma kuma haushinsa takeji,don me zai dinga taba mata jikinta,a gurguje ta tattare komai ta wuce bedroom dinta,shima sai data saka key ta rufe da kyau sannan ta canza kayanta zuwa na barci ta haye gado,yau ko.wankan ma bata tsaya yi ba.

    Ta jima tana juyi ciie da tsoro, duqunqune cikin duvet,wannan gidan yafi na kaduna girma,hakanan gidan kaduna dakunan kusan a kusa da juna suke,tana jin kusancin abbas dake dakinsa a jikinta,sabanin wannan da kowa bangarensa daban,cusa kanta ta sakeyi cikin duvet din,hancinta na zuqo mata qamshin turarensa,wanda ya kama rigar jikinta radam,sai taja tsaki,haushi na cika mata zuciya

    “Dan iska” ta fada tana murguda baki.

    **********washegari bata bude qofarta ba har sai dasu mimi sukazo suna buga mata,taji dadin ganinsu,suka dinga wasansu a falonta,ita kuma ta shiga kitchen ta dafa musu jallop din taliya.

    Da dan gyare gyare cikin girkin,to amma da yake ba wani cimar kirki yaran suke ba sai abincin ya musu dadi sosai,suka zauna sukaci kaman ba gobe,itama cikinsu ta zauna,sunaci suna surutu tana tayasu,sai da suka qoshi sannan mimi tace

    “Mummy ce ta aikomu,tace kiyi mana wanka,bacci suke wai basu tashi ba” bata ji komai ba,don zamanta da yaran ita dadi yake mata,sannan ita kallon hafsat din take kamar anty deena,don haka ta kunna heater,ta tara ruwa mai dumi sosai,tayi musu wanka kuwa fes,ta shafa musu manta sannan ta dubesu

    “Ku karbo kaya wajen mommy din a saka muku” da gudu suka fella suka fita,saidai basu jima ba sai gasu sun dawo da kayansu a jikinsu

    “Mommy tace kizo” jikinta ta kalla,da da hali wanka zatayi kafin ta fita din,don gaba daya bata jin dadin jikin nata,saboda bata samu yin wanka jiya ba,amma kafin ta gama tunanin maganar mimi ta katse mata

    “Yanzu yanzu wai tace” mayafin doguwar rigarta ta zura tabi bayansu suka fice.

    Sallamar widad din ta sanyata ninke kudin da take irgawa ta daga bayan pillow dinta ta xubasu tana amsa sallamar,kudin da abbas din ya bata ne ta bawa widad din,anyi rasuwa yana sauri ya fita bai samu leqata ba.

    Sanda ta karba kudin kamar zuciyarta tayi tsalle ta fito,ita din gotai gotai da ita zai raba musu kudi dai dai da yarinyar da ta haifeta kota kusa haifar ta?

    “Badai ya fita din ba,meye abun damuwa” zuciyarta ta gaya mata,wannan ya sassauta fushinta,don tayi imanin sisin kwabo ba zata bata ba a cikin kudin.

    Har qasa ta tsugunna ta gaidata kamar yadda ta saba,saita koma gefe tayi tsaye a darare,ba tare data kalleta ba tace

    “Kitchen zaki shiga ki gyaramin,idan kin fito saiki fara da falo, bedroom dina kuma idan na gama abinda nakeyi zan miki magana saiki gyarashi,zan gyara dakin yaran da kaina” ta qarashe maganar tana debe kudinta,sannan ta wuce dakinta abinta.

    Hakanan widad ta zage ta cashi aikin da zata iya cewa bata taba kamarsa ba,ta gyara kitchen tayi wanke wanke,ta dawo falon ta gyarashi tsaf,sannan tayi knocking qofar bedroom din.

    Tana kwance abinta daga saman gado ta amsa da

    “Shigo” a darare ta shigo da sallama,a kashingide take tana chart

    “Mommy na gama”

    “Gyara abinda ya samu,idan na tashi kya gyara gadon,ko na gyara da kaina” cikin d’ararewa ta fara kwashe tarkacen dake zube a qasan dakin tana hadesu waje guda.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 39

    Arubuce Ta Ke 39

    Page 39

    Cikin girmamawa latifa dake zaune gaban widad wadda ke lafe cikin kujera kamar wata ‘yar mage tana hawaye ta amsa sallamarsa,idanunsa a kanta ya qaraso shigo wa,sai ya janye idanuwan nasa ya tsaya tsakiyar falon yana rungume da hannayensa.

    Gaidashi latifan tayi,ya amsa a mutunce sanann ya sake maida dubansa ga widad tare da tura tambayarsa ga latifa

    “Lafiya dai ko?,ba wani matsala?” Gyara tsaiwarta kadan tayi

    “Uhmmm,wallahi gata nan,tunda suka tafi take kuka,nayi nayi da ita amma taqi yin shuru,yau ko abinci bata ci ba”

    “Ya salam” ya fada yana lumshe idanunsa hadi da. Budesu lokaci guda

    “Matsala kan matsala” ya furta qasan ransa,saiya sauke hannuwansa ya fara takowa zuwa inda take kwance,ganin haka sai latifa ta juya ta nufi daki.

    Dab da ita ya tsaya yana dubanta,ita kuma saita cusa kanta cikin pillow tana sake sakin sabon kuka,batason ganinsa kwata kwata,saboda shi ya jawo mata,qila da tuni yanzu suna wajen anty madina suna hirarsu abinsu,qila da tuni yanzu suna falon ummu suna kallo da hirarrakinsu,da tuni yanzu ba cikin pillow take kwance ba,da tuni kanta yana kan cinyar ummu tana sosa mata kai,a hankali ya rage tsahonsa ya tsugunna a gabanta,saiya sarqafe hannayensa guri guda yana kallonta,ta takura sosai a kwanciyar da tayi,amma baisan ta yaya zai gyara ta ba,yana jin tashin sautin kukanta,amma baisan ta yaya zai fara lallashinta ba,idan nawwara ce ko mimi chocolate zai hadasu da ita,to amma ita din aita dara a rarrasheta da chocolate.

    Duk yadda ya kamo zaren lallashinta ya kasa daidaitashi da tunaninta,bayason qarya sam a rayuwarsa,kuma ba maqaryaci bane duk rintsi,amma a yanzun da aka hadashi da rainon yarinya dole sai ya hada da canza maganganunsa

    “Tashi muje” ya fada a hankali,abu na farko da yazo kanta shine gida zai kaita,don haka ta daga kanta da wani mugun hanzari,ta sauke manyan fararen idanunta da suka sauya launi saboda kuka tana dubansa

    “Gida zaka kaini wajen ummu?” Sai ya gyada mata kai,yana kallon yadda farar fuskarta tayi pink sosai saboda kuka,kafin ya gama tunanin sa tuni ta diro daga kan kujerar,ta nufi hanyar daki tana kiran sunan latifa ta dauko musu kayansu

    “Wait….zo mana kiji” ya kirata yana miqewa da sauri,saita tsaya cak,sannan ta saka hannunta tana maida gashinta baya,saboda ya rufe mata idanu bata ganinsa da kyau

    “Hijab kawai zaki dauko,kayan sai daga baya kinga suna da yawa,itama ki barta a nan zata biyomu”

    “To” kawai tace masa,saita qara wuta zuwa daki harda hadawa da sassarfa.

    Tafin hannunsa yasa ya dafe goshinsa,ya Allah…..a sanda kake buqatar ka huta……wannan wanne sabon raino ne ya sameshi?.

    Tunda latifa ta ganta afujajan ta kuma gaya mata me yace sai tayi murmushi kawai ta miqa mata hijab din tana cewa

    “Allah ya kiyaye hanya,saina taho” ta zura hijab din tayi gaba abinta.

    “Na shirya” ta fada a shagwabe tana karya wuya sanda ta dawo falon,kallon fuskarta sosai yayi,hijab din ya qara mata kwarjini,sai ya juya a hankali ba tare da yace mata komai ba ya soma ficewa,tuni tayi tsalle ta dafa masa baya,don kafin ya fice ma harta tarar dashi,jinta a gefansa ya sanyashi waiwayawa,dai dai sanda itama ta daga kai ta kalleshi,sai suka hada idanu,wani abu mai nauyi taji ya saukar mata,sai tadan dakata har sai daya gota mata da kusan taku uku sannan tabi bayansa.

    Da kansa ya bude mata seat din gaba ta shiga,sannan ya zagaya ya shiga shima ya tada motar,ta sauke ajiyar zuciya wadda ke hade da sheshsheqar kukan da tasha,sai taji hankalinta ya kwanta sanda suka hau kwalta,zata koma wajen ummunta.

    A hankali yake tuqin,ya rage speed na motar sosai,sai widad tayi relaxing sosai jikin kujera tana kallon yadda suke wuce titunan garin bauchi a hankali,kamar zata masa maganar cewa baya sauri,amma sai taga sannu sannu dai tunda sun fito zasu isa wajen ummun.

    Cikin nutsuwa da salo na janye hankali ya dinga bi tituna tituna da ita,tun tana zuba idanu taga sun dauki hanya dodar harta haqura taci gaba da bin unguwannin da suketa wucewa da kallo,wani waje ya burgeta,wani gurin taga kamar kano,wani gurin kuma taga kano tafi wajen kyau.

    Agogon hannunsa ya kalla,dai dai sanda ya nuna masa sha biyu saura na dare,saiya juya kan motar yayi reverse,ya koma asalin titin da zai maidasu gida.

    Tun tana zaune saman kujera tana chart su mimi na wasa a saman carfet,har bacci ya daukesu,sai a sannan ta lura da yadda lokaci yaja,to a ina ya tsaya?,ta tambayi kanta bayan ta gama kwantar da yaran,qirjinta ya buga sanda zuciyarta ta raya mata yana can da yarinyar yana neman hadin kanta qila kamar yadda ta samesu ran nan,tunanin da ya sanyata fara neman spare key din gefen nasa,wanda ta jima rabon da tayi amfani dashi,jikinta har rawa yake,bata ankara da rigar jikinta ta bambanta da zanin jikinta ba ta zaqulo muqullin ta fito da wani irin sauri.

    Cike da qwarin gwiwa ta sanya key din ta buda sashen nasa,wayam ba kowa a falon,wata zuciyar ta gaya mata suna can kan gadonsa yana cin amanarta,saita qara hanzari ta cusa kai bedroom din nasa,nan ma babu kowa,ta tsaya jim tana tad’i ita da zuciyarta,sai taji ranta yana raya mata qila yana sassanta acan suka yada zango,ta sake juyowa a birkice tana fita a sassan nasa.

    Tunga taja ta tsaya ganin alamun qofar falon na kulle ta ciki,wannan ya sake tunzurata,zarginta kuma ya fara hauhawa,ta fara bugun qofar da qarfi.

    Da hanzari latifa ta taso,wadda tuni bacci ya dauketa,gabanta ya dinga faduwa din irin qarfin bugun da akewa qofar

    “Allah yasa lafiya,Allah yasa ba wani abu bane ya faru” ta dinga fadi cikin zuciyarta sanda take kan hanyar zuwa ta bude qofar.

    Kallon kallo suka yiwa juna na sakanni kafin latifa ta tuna wace,saita sake fuska

    “Barka da dare” ta fada tana duban fuskar hafsat,bata amsa ba illa cewa da tayi

    “Tana ciki ne?” Kai ta girgiza

    “Sun fita,tun dazu kuwa,nima su nake tsimaye” saura kadan tayi subutar bakin sako ashar,Allah ya taimaketa ta danneta can qasan ranta,wani abu mai zafi da quna ya soma mata suya a qirji,wata mace abbas ya saka a gaban mota suka fita?,me yake nufi?,zai daidaita matsayinsa da yarinyar da ita take mata kallon bata da maraba da babu?,don cin fuska tana can tana zaman jiransa,bai gaya mata ma cewa ya fita din ba saidai taji a bakin wata?,saita juya ba tare da tace mata komai ba ta fara barin wajen,latifan ta bita da kallo ranta cike da tambayoyi,daga bisani ta maida qofar ta sakayata,ta koma falon ta zauna saman kujera tana hamma tare da duba lokaci,bataso ta koma bacci suzo kuma suyita bugu.

    Dab da zata isa sashenta qarar bude qofa da kuma hasken motarsa ya risketa,saita tsaya cak tana motar,kafin ta fara takawa zuwa wajen,tanason taga idanun abbas,da wanne baki zai mata bayani kuma?.

    Yana kashe motar tana isowa saboda saurin data kwaso,ya sauke Glass din motar a hankali yana dubanta kafin yace

    “Bakiyi bacci ba?,inata so na kiraki kuma saina sha’afa” hakan daya fada ba abinda yayi mata illa sake tunzurata,ya manta ma kenan da ita?,takai dubanta ga widad wadda jikinta ya gama yin la’asar,ta kwantar da kanta a seat din motar,bacci gaba daya ya cika mata idanunta,duk da haka ta hadiye

    “Qanwarki keta rigima nadan fita da ita” sosai tayi namijin qoqarin danne wani mulmulallen abun daya taso ya tsaya mata a wuya,bataso sam ya tabata da niyyar dagata ko taimaka mata ta fito,don haka tayi saurin zagayawa side din ta bude mata qofar tana cewa

    “Ayyah…..haba widad?,banda abinki da haka kowa yake sabawa, kowacce mace a matsayin baquwa take zuwa gidan aure,amma yau da gobe sai kiga ta saba” ta qarashe maganar tana bude murfin,tana jin kamar ta fincikota,amma hakanan ta tsaya harta fito din

    “Ka wuce ka huta,bari na rakata” ta fada tana kallonsa.

    Wani narkakken kallo yake binta dashi,gaba daya ta gama bashi mamaki ta kuma kwance masa kai,hafsat dinsa ta sauya fiye da yadda rai da zuciyarsa suke raya masa zata iya sassauta kishinta,kodon tana duba qananun shekarunta ne?,yana nan a tsaye har sukayi nisa,tana riqe da hannunta tana lallashinta da bata maganganu,saiya maida murfin motar ya rufe,ya sanya key din a aljihunsa ya soma takawa zuwa sashen sa yana jin gajiya nabin dukka gabbansa,babu abinda yafi buqata a yanzu irin ya watsa ruwa a jikinsa ya kwanta.

    Sai data tabbatar tayi nesa da widad daga inda abbas yake sannan ta fito tabar sashen,bayan ta gama mata lallashin qarya da nuna kulawa,wanda qasan zuciyarta cike yake fal da tsana da kuma qiyayyar yarinyar,tana jin kamar ta budi idanu taga babu ita kwata kwata cikin gidan.

    Latifa ce ta sakata a gaba kan sai taci abinci,da yake a gajiye take,kuma yunwar take ji da gaske saita zauna taci din,tana tsaka da cin ma baccin ya kwasheta ko.hannu bata wanke ba,sai tatifa ce ta gyara wajen ta kuma tasheta ta koma dakinta.

    Washegari tunda wuri latifa taga kiran ummu,bata yi jinkiri ba ta daga,don dama tana da niyyar kiran nata,bayan sun gaisa widad ta fara tambaya,bata boye mata ba ta gaya mata yadda suka wuni jiya,muryar ummun ta canza,da alama ita kewar widad din tata takeyi,sai tace takai mata wayar.

    Bacci takeyi amma sanda tace mata ummu ce sai gata ta wartsake sarai,ta karba wayar tana kiran sunanta hawaye na shirin balle mata,tausayinsu duka ya kama latifan,sai ta fice tabar mata dakin bayan taja mata qofar.

    *Arewabooks: Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 43

    Arubuce Ta Ke 43

    Page 43

    Gefan gadonta ta zauna hannuwanta rufe da fuskarta tana kuka sosai,me yasa abbas bazai fuskanceta su zauna lafiya ba?,yasha gaya mata zai bata mamaki,bata taba zaton irin wannan mamakin zai bata ba,ba ruwansa da harkar mata,kamar ma baida damuwa dasu,wannan yasa ta saki jikin cewa duk wani mataki da zai dauka a kanta bazai wuce ya qaurace mata ba,ita kuma bata da wannan damuwar,bata da yawan buqata,tasa buqatar ma damunta takeyi.

    Wayarta ta jawo dake gefan gadon ta soma laluba number kyawunta zatayi abinda ta saba wato kai qara,saidai tana kallon agogo taga dare yayi,wata zuciyar na ingizata ta kirashi,wata zuciyar na cewa tayi haquri ta barwa safiya,saita aje wayar,amma kuma yadda zuciyarta ta cika ta tumbatsa da bacin rai da kuma fushi,sai taji ba zata iya kwana ita daya da wannan baqincikin a cikin ranta ba,don haka ta sake daukar wayar ta kira number anty ummee.

    Cikin sa’a ta shiga,tana shiga din kuma ta daga

    “Ke lafiyarki a wannan tsohon daren?” Ta jefa mata tambayar jin ta fashe mata da kuka

    “Anty kaduna zai dauketa jibi su tafi”

    “Ita wa?,au amaryar taki?” Kalmar tayi mata ciwo,amma saita gyada kai kamar tana wajen

    “To sai kuma me ya faru?”

    “Na gaya masa ni.ban yarda ba,shine yake wani gayamin wai aini na zabi haka, mukayi fada dai dashi na baro masa dakin” wani tsaki anty ummee taja

    “Dadina dake wallahi baki da qwaqwalwa kwata kwata wani zubun hafsatu,ke da zaki nuna murna,kice hakan da yayi shine dai dai,zasufi sabawa da juna?” Ido hafsat ta zaro,kukanta ya tsaya cak

    “Anty?,suje su kebe su biyu wani abun ya faru kenan fa?,kaduna fa nake gaya miki,gidan da daga shi sai ita”

    “To ubanme ma zakije kiyi a garin da baki da ko kashi?,kibar kowa naki asalinki da tushenki a nan,suje sai sun dawo,sannan ma kuma sai akace miki haka zaki barta idan sun tashi tafiyar?,tsaya kiji,bude kunnenki da kyau” tarawa anty ummee nutsuwarta tayi,duk da tanajin babu wata mafita data wuce tayi masa bore,ko ya tafi da ita ko ya aje yarinyar a gida,saidai cikin minti biyar da fara sauraran anty ummee fuskarta ta washe da farinciki.

    **********Tun daren jiya bai kwanta ba sai daya tabbatar ya hada duk kayan da zaiyi tafiyar dasu ranar asabar din,idan da sabo kusan ya zame masa jiki,a shekarun da sukayi da hafsat zai iya irga sau nawa ta taba hada masa kaya wai don zaiyi tafiya ko zai koma bakin aiki.

    Bai kwanta ba sai kusan biyu na dare,a nan ma tunani ya hanashi sakat,yayita juyi from side to side,yanata bitar halayen hafsat,ya yarda matar aure ta qwarai dace ne,bai taba kawowa hafsat din zata sauya haka ba,bai taba kawowa cewa haka halaye da dabi’unta suke a zahiri ba,bai samu bacci ba sai wajen uku da rabi na dare,asuba nayi yayi alwala ya wuce masallaci.

    Bai shigo gidan ba sai wajen qarfe tara na safe,ya tsaya taron magidanta da akeyi a unguwar duk qarshen wata,kafin sannan hafsat takai ta kawo a sassansa ya kusa sau uku,so take ta aiwatar da shirinta tun da wurwuri,plan din anty ummee yafi kwanta mata fiye da nata plan din,saboda idan tanason barin garinta to tana qaunar mutuwarta.

    Sunyi sabani,tana komawa sassanta yana shigowa gidan,kamar ko yaushe a matsayin widad na baquwa sai ya fara da sashenta.

    Dai dai lokacin suna bedroom din widad din,latifa ta gama musu breakfast,harma sunci,don basa iya cin abincin hafsa,wanna yasa ma basa jiranta,itama kuma ana kwanaki biyar ta daina kawowa,saidai ta aiko a kirata tazo suyi dinner,sai akaci sa’a widad din mai wahalar sabo ce bata zuwa.

    Sabbin kaya latifa ke ware mata,saboda ta soma shirin komawa kano,amma dai bata bari widad din ta sani ba,don kada ta birkice mata

    “Wadan nan kayan dasu zakici gaba da kwalliyar,kinji dai abinda anty deena ta gaya miki?” Kai ta gyada

    “Bakiga kullum sai nayi abinda tace din ba”

    “Eh amma har yanzu baki qara zuwa wajen uncle din naki ba,kuma na gaya miki a can ake kwana” ido ta fiddo,waisu basa jin kunya suke mata zancan ta kwana da namiji?,bayan ummu ta gaya mata ko hannunta aka riqe ciki zatayi kuma mutuwa zatayi?,kafin tace komai anyi knocking qofar,latifan tasan ba wanda zai.shigo kansa tsaye saimai gidan,don haka ta zube kayan hannunta tana yiwa widad nuni da.hannu akan ta bude qofar.

    Itakam bata gane komai ba,ta sauko daga saman gadon,ta isa bakin qofar ya buda a hankali manyan idanuwansa suka fada cikin manyan fararen nata idanun,ta saki qofar cikin rashin sabo da d’ari d’ari taja baya tana cewa

    “Ina kwana?”
    “Lafiya qalau” ya amsa mata yana duban kayan jikinta,kayan bacci ne riga da wando masu taushi da kauri,wandon iyakarsa qauri,rigar ce ma mai dogon hannu,ya kauda ganinsa yana sanyo kansa cikin dakin,sai tahau raba idanu tana duban latifa dake jiran ya gama shigowa su gaisa ta basu waje,gabanta tana dan faduwa.

    Gaidashi tayi ya amsa,sai ta juya ta nufi qofa,widad din batayi qasa a gwiwa ba tabi bayanta zata fice itama cikin jin tsoro

    “Zo nan” ya kirata a hankali,saita waiwayo fuskarta a narke kamar zata saki kuka,ya kalli siraran labbanta jajaye data tabesu

    “Bari na dauko hijabi na” ta sake fada tana sanya jelar dankwalinta tana faman boyon na shanunta da suka fara bayyana kansu ta cikin rigar jikinta.

    Dariya taso bashi acan qasan zuciyarsa,ya fuskanci me take boyewa,ko me zasu sakashi ji wadannan qananun abubuwan oho,ya fada a ransa,saiya sanya hannu ya jawo hijabin da ya gani a gefansa ya miqa mata,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,tana ta faman cukuikuye gaban rigarta ta qaraso ta sanya hannu ta karba hijabin ta zura,sannan ya nuna mata waje ta zauna.

    “Kice ta shirya miki kayanki,gobe in sha Allah zamu tafi kaduna” da farko daya fara zancan hada kaya harta fara murna,ta dauka zaya ce gida zasu,amma sai taji yana kiran wata kaduna,ta fiddo manyan idanunta waje da suka fara hada hawaye

    “Kaduna?…..”sai ta kasa qarasa maganar,kai ya jinjina mata yana nazartarta,ta fiya tsoro, tsoronta yayi yawa,kuma ya lura maza kawai takewa haka

    “Eh,gobe da safe” shuru tayi tayi qas da kanta qwalla na zuba,bai lura kuka take ba,yamiqe yana cewa

    “Bakwa buqatar komai?” Saita jinjina masa kai kawai,ya taka a hankali ya fice,cikin ransa yana ayyana yadda zasuyi rayuwa a kaduna da ita ahaka a yadda take,itama din bata wuce raino ba.

    A haka latifa tazo ta tarar da ita,ta sata a gaba da tambaya,sai ta gaya mata,sannan ta dora da cewa

    “Ni gida zan tafi ba wani kaduna,wajen ummu zamu tafi” zama sosai latifa tayi tana kwantanta mata lamarin aure,ta kuma gaya mata gaskiyar ta taho kenan,ita da gida saidai ziyara,saita rude mata,ta dinga rusa mata kuka tana lallashinta,daga qarshe dai sai data kai ga kiran alhj mahmud.

    Cikin hikima irin ta d’a da mahaifi ya dinga bata baki,tare damata alqawurin zaizo can din,kuma ta fadi kome takeso zaisa a kawo mata

    “Ni banason komai,kawai komai a gidan,kullum shima sai ya tambayeni idan inason wani abu” wannan magana tata ta sake kwantar masa da hankali,ta kuma qarawa abbas martaba da bayyana asalin nagartarsa,abban nata bai barta ba har sai da ta sake sosai sannan sukayi sallama.

    Tsaf latifa ta hada mata kayan da dukka tasan ya kamata ta tafi dasu,itama ta faka nata kayan a boye.

    Bayan fitarsa sassan hafsat din ya wuce don yaga yaransa,a falon yayi sallama,sunata wasa da kayan bacci a jikinsu,babu alamun an musu brush da alwala ba bare wanka,fuskarsu duk jirwayen bacci da sauransu.

    Tana tsaye a dining area tana gyara kayan breakfast din data hada tun safe,bayan ta hana idanunta barci.

    Satar kallonsa takeyi,ya mata wani irin kwarjini da kyau,wani irin annuri ke fita daga fuskarsa,abinda ke qara mata soyayyarsa kenan da kuma kishinsa,kome ya sanyawa jikinsa karbarsa yakeyi.

    Cikin nutsuwar nan tasa ya duqa yana tarbar yaran nasa,suka shige jikinsa kowa a cikinsu yana son masa hira shi kuma yana biye musu,ta gaji da tsaiwa ganin baiko waiwayota ba,ta soma baro wajen zuwa inda suke tsugunne

    “Ina kwana” ta fada ranta yana suya,a dakeka a hanaka kuka?,wanne irin al’amari ne wannann

    “Lafiya”ya amsa a taqaice,ranta ya sake sosuwa,halin nasa ya motsa kenan,shi duk abinda ya faru kenan bai ga nasa laifin ba sai nata?.

    “Ga abincinka nan an gama”

    “Am okay alhamdulillah” ya bata amsa yana miqewa dauke da nawwara,sai itama ta miqe,zuciyarta na tafasa amma tana yunqurin danneta

    “Amma kada ka yimin haka,tun dazu na tashi saboda kai fa?”

    “Nace na qoshi” ya amsa mata bayan ya zube mata manyan idanunsa,abinda ya sage mata gwiwa ta koma baya ta jingina da kujera

    “Abinda ya faru jiya ne kenan har yanxu bai wuce ba?” Waiwayawa yayi yana sake kallonta,shi take ma tambaya kenan?,bai amsa mata ba sai ta baiwa kanta amsa

    “Kayi haquri,inasonka dole nayi kishinka,kishin ne ya sanya idanuna suka rufe,amma ya riga ya wuce,Allah ya tsare hanya” ta qarashe maganar tana jin kamar ta saki kururuwa,ita kadai tasan me takeji a zuciyarta,wani irin kisan mummuqe ne takewa zuciyarta,wadda bata saba da boye boye irin haka ba,komai nata gaba gadi take yinsa.

    Lokaci daya xuciyarsa yaji zuciyarsa ta karye,ta kuma sassauto,amma baiji gamsuwa akan lamarin hafsat din ba,ya santa,kamar hawainiya take akan wasu al’amuran,bashi da tabbacin ta fada din da gasken gaske

    “Kaji?,nace kayi haquri” ta kuma fada,a wannan karon duk yadda taso tare qwallar baqincikin dake idanunta sai da suka sulmiyo,abinda ya qarasa karyashi kenan,son sam baya qaunar kuka,sai ya sauke nawwara yacewa mimi taja nawwaran suje dakinsu su dauko brush dinsu.

    A tausashe ya sanya hannunsa ya jawota zuwa jikinsa,tun baice komai ba ta saki kuka mai nauyi,wanda ke dauke da saqonni da yawa da zuciyarta keson fesarwa,baki da ruhi sun gaza amintuwa da hakan saboda burin cikar wani buri.

    Baice komai ba sai hannu da ya sanya a bayanta yana dan bubbuga wa kadan kadan,har zuwa wani lokaci,ya dagata yana duban fuskarta

    “Is okay,wipe your tears” ya fada bayan ya miqa hannu ya yago mata tissue din dake kusa dashi,bata musa ba ta karba ta fara goge fuskarta ta,saidai zuciyarta har yanzu tana jinta kamar an fusgeta daga qirjinta an jefa gidan bread.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[3/6, 3:12 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 55

    Arubuce Ta Ke 55

    Page 55

    Da numfashinsa da idanunsa ya dauke lokaci guda sanda taja zanin nata sosai qasan marar tata,har jan pant dinta yana bayyana

    “Ya Allah” ya furta yana sake rintse idanunsa,har suka gama bai bude ba sai da yaji nurse din na magana

    “Zaki iya tashi?” Ta tambayeta,ya bude idanunsa a hankali ya maida kanta,sai ya taka a hankali zuwa gabanta,ya miqa mata hannunsa,idanunta a qas, karon farko da kunya tayi mata mugun kamu fiye da ko yaushe ta miqa masa hannun nata,ya dagota a tausashe.

    Sosai ta zauna saman gadon tana gyara daurin dankwalinta, likitan ya shigo yana qarasawa gaban computer scanning din yana duba scan din data bari a jiki

    “Ba wata matsala,zan rubuta mata magunguna,zata samu relief in sha Allah”.

    Koda suka fito dinma tana riqe a hannunsa,gaba daya ta narke masa,tana ta sharar qwalla,ummu take tunawa da yadda take kula da ita idan bata da lafiya,dan riqetan da yayi sai takejin kamar tana tare da ummun ne,don haka ta narke masa sosai kamar yadda takewa ummu.

    Tun a pharmacy din cikin asibitin ya siya magungunan,fruit kawai ya tsaya ya siya a hanya suka wuce gida.

    Dakinsa kai tsaye ya wuce da ita,ya shiga kitchen da kansa ya dauko gorar ruwa da cup,ya zuba abinci a plate ya zauna da kansa a gabanta yana dubanta

    “Kici abinci,magani zaki sha” kai ta girgiza,fuska yadan hade kadan,ya zama serious,ya debi abincin da kansa yakai bakin bakinta

    “Oya….karbi” haka ta dinga bude bakinta yana saka mata abincin,har yanzu hawayenta yaqi tsayawa,duk ta narke,kamar yadda takewa ummu,bai saba daukan shagwaba irin wanna ba,sai ya rasa ta inda zai bi da ita,a haka ya samu tadanci,ya balla mata magungunan ya bata tasha,sannan ya miqe yana kallonta

    “Ki huta kadan,sai na rakaki ki kwanta” ya fada muryarsa can qasa,saita gyada kai tana rintse ido,kawai yadda zata tafi dakin ta kwanta ita kadai take hasasowa.

    Toilet ya shiga,ya sauya kayansa zuwa jallabiyya mai sulbi saqar qasar india,ya daura alwala,ya dawo cikin dakin ya shimfida abun sallah yana dan duban sashenta,ta sanya pillow daga bayanta,idanunta na a lumshe,amma da alama idanunta biyu,sai ya juya ya kabbara sallarsa.

    Tun tana satar kallonsa da kadan da kadan har bacci ya soma rinjayar idanunta,tayita dagewa batason hawa gadon sosai,yana fusgarta tana qwacewa,har yaci qarfinta,ta kwanta riris saman gadon,bacci mai dadi yayi gaba da ita saboda sassaucin ciwon data samu.

    Da murmushi akan fuskarsa yake dubanta sanda ya idar da sallar yaga tayi bacci,ya qarasa addu’o’in sa ya sauya kayan baccin sannan ya matso dab da ita,ta ranqwafa saman kanta yana kallon fuskarta sosai da sukayi gab da juna,siraran tausasan labbanta masu kama da an shafa musu ban lebe suka dauki hankalinsa,ya miqa hannu a hankali ya dora saman lips din nata yasa yatsunsa ya shafasu kadan,saita motsa,ta turo baki gaba cikin shagwaba

    “Ummu na…..ummu don Allah fa ni….” Ta fadi tana yin juyi,abinda ya sake kawo kusancin dake tsakaninsu sosai har suka fara musayar numfashi,ta haye kusan rabin cinyarsa,ya kalleta yadda tayi relaxing a jikinsa,jikinsa ya bashi idan yace ma zai tasheta ne wata really rigimar ce,don haka kawai sai ya zame ya kwanta,hakan kuwa sai ya zamar mata kamar wata hanya data samu ta shige jikinsa sosai,harda curewa waje daya kamar kwanciyar yaro a cikin mahaifiyarsa,taja hannunsa kuma ta riqe gam tana cewa

    “Ummu……na….gode” ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke,da alama mafarki takeyi,hakanan ya samu kansa da sake kusanto da ita cikin jikinsa suna musayar dumin juna,ya lumshe idanunsa a hankali yana jin wani abu yana bin jinin jikinsa,zuciyarsa ta fara sauya tsarin bugunta,sannu sannu numfashinsa ya fara sauyawa,ya dinga fita a jejjere,mode dinsa ya canza gaba daya,yasan me jikinsa yakeso,amma bayajin wannan buqatar zata samu,ta yaya ma daga samun kusanci da yarinyar zuciyarsa zata bijiro da wannan babbar buqatar?,bashi da sauran zabi illa qoqarin zameta daya fara yi daga jikinsa,saidai ta riqeshi qam,daga bisani ma da yayi nasarar zameta din,juyi daya tak tayi ta dawo jikinsa,idanunta a rufe amma kukan shagwaba take saki,yayi shuru yana sauraren siririyar muryarta dake fidda wani irin kuka a shagwabe,wanda yake qara sanya tsigar jikinsa zubawa,ya sake rufe idanunsa da kyau yana sake qoqarin zameta a karo na barkatai,amma saita riqo hannunsa,ta kuma cusa kanta cikin qirjinsa sosai.

    Duk yadda yaso yayi controlling kansa ya kasa,komai na jikinsa ya gama amsawa,qwaqwalwarsa kuma ta dauki chargy fiye da kima,dukka hannuwansa ya sanya ya jawota cikin jikinsa,shi da ita suka sauke ajiyar zuciya a tare,a hankali ya nutsa hannunsa cikin sassalkar sumarta dake fidda qamshin man kitsonta mai hade da sinadarin menthol me sanyi,cikin sanyi taushi da nutsuwa ya fara yamutsa shi yana jin dukkan wata gaba ta jikinsa tana sake amsawa,abinda ya sanya widad sake sakankancewa cikin baccinta,zuciya da ranta suna bata tana tare da ummu.

    A nutse hannunsa ya biyo tsahon gashin nata daya sauka har zuwa gadon bayanta,yana kaiwa qarshe hannunsa ya zarce ta cikin rigarta dake da faffadan baya,lallausan tafin hannunsa ya hadu da fatar bayanta mai santsi da dumi,ya zura hannunsa a hankali yana shafota,idanunsa suna sake nauyi da kyau,zuciyarsa na sake dugunzuma da dokantuwa da samun biyan buqatar ransa,bai gushe ba yana ci gaba da murza fatar bayanta,duk inda yayi qasa da hannunsa zip din na bashi hadin kai wajen zugewa,har yakai can qasa,ya dora hannunsa numfashin sa yana sake gudu kamar wanda yayi tsere,wannan ya sake sanyashi matsa qaimi,ya birkitata a hankali ya soma sabule rigar tata,ya sake dora hannayensa saman wuyanta,hancinsa yana kaiwa wajen,sassanyan qamshin daya zamewa jikinta kamar dabi’a ya zuqa,qamshin da zai iya cewa tunda yake bai taba jin irinsa a jikin hafsat ba,sai yaji bashi da muradin daya wuce yayi sharing qamshin nata da tasa gangar jikin,don haka yasa fuskar sa sosai saman fatar wuyanta,ya kuma fara gangarowa ga qirjinta a hankali yana sauke wani irin birkitaccen numfashi.

    A hankali ya fara isowa ga tudun saman qirjinta,abinda ya sanya shi da ita sukaji tamkar an sanya musu wani irin electric shock,ya qanqameta da kyau yana sake zuqar qamshin turaren,yayin da ita kuma taji kamar ance mata tashi!!!,cak kwanyarta ta tsaya waje daya tana son rarrrabe abinda yake faruwa,sanyin daya fara ratsa fatar jikinta ta fahinci saura kadan rigarta ta sauka qasan qirjinta,yunqurin riqe masa hannu tayi cikun matuqar tashin hankali amma ta gaza,saboda yadda jikinsu take rawa gaba daya ita dashi

    “Don Allah…..don Allah” ta fara fada cikin mugun rawar murya da kuma kuka,cak ya tsaya kamar wanda aka sanyawa sarqa,ya zame hannunsa daga jikinta a hankali ya mirgina gefe yana fadin

    “Hasbunallahu wani’imal wakil” can qasan maqoshinsa,yayin ruf da ciki yana cusa kansa cikin katifar tare da qoqarin dawo da nutsuwarsa cikin jikinsa.

    Tuni takai bango,ta tattare dukka jikinta guri daya,tana riqe da rigarta a hannu qam qam,hawaye sun yiwa fuskarta ado,kuka take sosai cikin tsoro da kuma tashin hankali.

    Dakin ya dauki shuru na wasu sakanni,har yanzu kansa na cikin katifar,yana sauraren kukan da take rerawa,wanda ya dinga jinsa har tsakiyar kansa,wani tunani yazo mata,ta soma maida rigarta da sauri sauri,saidai ta gaza zuge zip din,sai kawai ta sauke qafafunta qasan gadon ta miqe ta nufi qofa.

    Cikin jikinsa yaji alamun takunta,ya daga rinannun idanunsa da har yanzu basu gama komawa dai dai ba yabita da kallo,duk da dakin ba wadatar haske amma kuma yana iya ganin bayanta daya bayyana sosai saboda rashin zuge zip din,wani irin baya dake dauke da wani shape mai jan hankali daya taimaka wajen fidda shape na mazaunanta da qugunta.

    Bayajin koda yayi magana zata fita daga maqoshinsa,don haka ya miqe kawai cikin wata iriyar kasala da mutuwar jiki,kamar wanda yasha abun maye,taku uku ya cimmata,ya isa jikin qofar,ya murza key sannan ya waiwayo ya zube mata idanuwansa gaba daya yana kallonta

    “Koma ki kwanta” ya fada da dakusashiyar muryarsa,saita janye gefe tana maqale kafada,bai sake mata magana ta biyu ba,illa hannuwansa daya sanya ya dauketa cak,bai direta ko ina ba sai saman gadon,ya kwantar da ita saman pillow,yaja mata duvet sannan ya sunkuya yana kallon qwayar idanunta sosai

    “Sleep……banason na sake jin kukanki,idan kuma kika sake tashi….tom” ya fada yana gyada kansa,alamun akwai abinda zai biyo baya,sai ya matsa yaja da baya,sannan ya juya ya shige bandaki.

    Runtse idanunta kawai tayi tana qoqarin danne kukan nata,wani haushinsa da tsanarsa takeji,ashe dan iska ne sosai haka?,tunda take ba wansa ya taba yi mata abinda yayi matan sai shi,boye kanta ta sakeyi sosai cikin duvet din tana share hawayen daketa bulbulowa daga idanunta.

    Ya jima cikin toilet din sannan ya kunna ruwan zafi dana sanyi ya daidaita temperature dinsu,ya sakarwa kansa shower,bai taba zaton yarinyar zata kunnashi haka ba,akwai wani irin magnet tattare da ita dake saurin jan zuciya da kuma gangar jiki,yayi shuru ruwan yana gangara a sassan jikinsa,yana tuna qamshi da dumin fatarta,da wani laushi kamar fatar jariri,irin yanayin da yakeso tattare da matarsa,irin yanayin daya jima yana fasaltawa,hannu yasa saman kansa ya sharce sauran ruwan da bai gama diga ba sannan ya fita daga qasan shower din ya samu babbabn towel ya daura ya fito daga bandakin.

    Koda ya fito turare kawai ya samu ya shafe jikinsa dashi ya sauya wata rigar,ya koma can daya side na gadon ya zauna yana kallonta yadda take nade waje daya,batayi motsi ba ko kadan,saidai duk da haka ya karanci bacci ya fara daukarta,saidai baccin baiyi nauyi ba,ya sauke ajiyar zuciya ya jingina bayansa da fuskar gadon yana sauke idanunsa kan agogon dake saman bedside yana duba time da date,yana buqatar zuwa bauchi lallai,saidai yau din Monday,zai iya jira har sai ran Friday kuwa?, tambayar da ta masa nauyi,kwanakin kuma yaji sunyi masa nisa da yawa,sai kawai ya jawo wayarsa,ya yanke bari ya kira hafsat din,at least ko hira da zata sake bashi nutsuwa ya samu daga gareta.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 47

    Arubuce Ta Ke 47

    Page 47

    Komai nasa ya tattare a falon,abinda yasa widad ta fahimci ya gama zamansa a nan kenan

    “Muje na rakaki daki,zan kwanta” jiki a sabule ta miqe din,yana gaba tana binsa a baya har zuwa dakin,tana zaune a gefan gado ya zuzzuge dukka glasses na window din sosai,ya kunna ac ya daidaita mata temperature dinta,duk abinda yake tana binsa da kallo,duka jikinta babu dadi,dan wankan da takeyi ma data yiwa anty deena alqawari bata samu yi ba,ta kuma riga ta saba da yinsa zuwa yanzu,ya tako a hankali yana ajjiye remote din acn sannan yace

    “Kin iya addu’ar kwanciya bacci?” Kai ta gyada masa

    “Da kyau,kiyi kafin ki kwanta” ta sake gyada masa kai,ba wannan bane a gabanta,tana qiyasta yadda abubuwan tsoro zasu kawo mata farmaki cikin dakin idan ta kwana ita kadai,babu abinda ranta da zuciyarta basu kawo mata ba,batasan sanda tayi wuf tabi bayansa ba sanda taga ya nufi qofa.

    Tsaiwa yayi yana kallon ta,hawayen nan da basu da wahala a fuskarta suna fita

    “Mene kuma?”

    “Tsoro nakeji”

    “A’ah….wai meye abun tsoron ne?” Kasa amsa masa tayi,illa d’ari d’ar da taketa yi,shuru yayi ya zuba mata idanu,yanason tuna abinda ya dace yayi

    “Yanzu me kike so?” Saita kalleshi da dara daran idanunta masu haske sosai,bakinta yana dan rawa,ta kasa cewa komai,ganin haka sai yace da ita

    “Muje dakina ki kwana” da sauri ta girgiza kai tana fidda ido waje

    “To ki koma dakinki ki kwana” ya sake bata second option,nan ma ta girgiza kanta da sauri.

    Ranshi ne ya baci,har yaja tsaki a fili,wacce irin yarinya ce ita?,duk option din da aka bata bai mata ba?

    “Ba zaki dakina ba,bazaki dakinki ba,to zaman gadinki zanyi?” Ya tambayeta emotion din fuskarsa yana sauyawa zuwa bacin rai.

    Maimakon amsa saita sakar masa kuka sosai,abind ya hasalashi ya sakar mata tsawa,tsawar data sanyata durqusawa a wajen tana kuma sakin wani kukan tare da kiran sunan ummu.

    A take jikinsa yayi sanyi,yaga kuma rashin kyautawarsa muraran

    “Sai ka dinga haquri da ita,kana kwatanta mata abubuwa,bata zama cikakkiyar budurwa ba,da quruciya har yanzu a tattare da ita,to zaka yita ganin yarinta,sai kayita haquri kana gyara mata,amma data gane abinda kakeso da wanda baka so,zakaji dadinta fiye da kowa” maganar da sukayi da hajiyansa ta qarshe ta dawo masa,wannan yasa temper dinsa ta sauka,ya tako a hankali ya tsaya a gabanta

    “Get up….tashi” ya fada a tausashe,saita miqe din tana sanya gefan dankwalinta tana goge fuskarta,duk da hawayen sunqi tsaiwa

    “Yanzu ya kikeso ayi?” Ya tambayeta yana narkar da idanunsa cikin nata,itama kallonsa takeyi,ya fuskanci ko a jikinta bata jin nauyin kallon qwayar idanunsa,ta gaza bashi amsa sahihiya,ya kuma gane tsoron hada daki takeyi kawai dashi,kamar kuma yadda take tsoron kwana ita kadai,tsahon wasu sakanni da shuru ya biyo baya sai ya gyada kai

    “Shikenan,ki kwanta a daki,zan zauna a falo har kiyi bacci” a hankali ta gyada kanta,hakan yayi mata,yafi ace ya koma dakinsa ya kulle ba kowa a kusa,duk da dakunan kusa da juna suke.

    A gaba ya sanyata har dakin nasa,ya dauki duk.abubuwan da zai dauka ya ajjiye a falon,ya maidata dakin ya tsaya harta kwanta sannan ya ja mata qofar ya dawo falon ya zauna saman kujera hadi da jingina filo bayansa da gefansa don yafi jin dadin zama,sannan ya buda wani qaramin littafi ya soma dubawa.

    Fakare tayi cikin bargon data lulluba har kanta tana rarraba ido,lokaci lokaci tana dan jiyo motsinsa daga falo,wannan ne ya sanya mata nutsuwa,har sannu a hankali bacci ya saceta ba tare data sauya koda kayan jikinta ba.

    Awa guda y bayar sannan y shigo dakin,ganin qarar qofar dakin bai sanyata ta motsa ba ya fahimci tayi bacci,sai ya koma da baya yana sake rufe mata dakin,ya koma falon ya kwashe kayayyakinsa ya wuce nasa dakin

    “Case closed” ya fada a ransa,amma yana tunanun haka zasu maimaita da ita gobe?,kenan wani sabon duty dinne ya sameshi

    “Ya rabb” ya furta yana furzar da iska daga bakinsa,ya ajjiye komai a muhallinsa y wuce bandaki don yayi wankan da rigimarta ta hanashi yi.

    Tunda gari ya waye ta dawo falon ta zauna,bayan ta dafa ruwan zafi kamar yadda latifa ta koya mata,ta hada da cup da tea flask din ta dora saman table,tun daxu take jiyo motsinsa cikin dakin,amma bata yi qoqarin shiga ba,saidai ta zubawa qofar dakin idanu tana qiyasta sanda zai fito.

    Yana taba handle din ta sake zubawa qofar idanu,ya fito a hankali cikin police uniform,sun masa wani irin kyau kai bakace uniform na ya sanya ba,haiba da kwajininsa sun fita sosai,tsayayyen namiji da siffar qarfi ke bayyana a halittarsa,qafafunsa saye cikin baqaqen boots,yana shirin rufe qofar ya lura da ita,sai ya waiwayo yana dubanta da mamaki kan fuskarsa,da yaji shuru yayi tunanin har yanzu tana daki baccin takeyi,dalili kenan da bai tasheta ba.

    Sosai ya sake mata kwarjini,wani tsoronsa ya sake shigarta,sai ta dauke idaninta ganin yadda yake kallonta,tura baki gaba, itafa duk wanda yake kallon mata dan iska ne a wajenta,ta sauke qafafunta qasa sannan tace

    “Ina kwana?” Bai amsa ba sai daya rufe qofar dakin,sannan ya tako zuwa wajen yace

    “Lafiya lau….” Ya fada yana duban kan dining din,sannan ya sake dubanta

    “Kinci abinci ne?” Kai ta girgiza

    “Akwai kayan tea a cupboard na kitchen din,zan fita anjima za’a kawo kayan cefane,ba wata damuwa?” Kamar jiya yauma fuskarta kamar ta fashe,yana nufin ita kadai zata wuni a sassan kenan?,wai Allah,ya zatayi,lallai zata mutu da tsoro indai yace zai sake kaiwa dare,ganin batace komai ba sai ya dora

    “Akwai mutane cikin gidan nan,zaki iya shiga ku gaisa,ko kuma idan na dawo saiki shiga” ya fidda kudi ya ajiiye mata

    “Sai na dawo” ya fada yana nufar qofar,binsa tayi da kallo,kamar ta zura da gudu ta bishi

    “Don Allah kada ka sake kaiwa dare irin na jiya” ta fada muryarta tana rawa,waiwayowa yayi yana kallonta,ba tare daya shirya ba murmushi ya subuce masa,shi kam ya jima baiga matsoracin mutum ba irinta

    “In sha Allah” yace mata sannan ya fita.

    Ta kusa minti talatin a wajen tana jin yadda gidan yayi mata shuru,sai da cikinta ya fara kiran yunwa sannan ta miqe,kana kallonta zakasan a tsorace take,duk da akwao motsi jifa jifa daga harabar gidan,kitchen ta shiga tana neman inda kayan tea din suke,tsahonta bazai kai ba,sai tasa kujera ta taka ta dauko ta dawo dining din ta doma qoqarin hada tea din,gana daya ta rude,saboda ummu ko latifa ke hada mata,koda ta gama hadawa ta dandana sai taji test din baiyi mata ba,ta bare baki kamar zata saki kuka,haka ta runtse idanu tana kurba har ta kusa shanyewa,dai dai lokacin da wayarta ta dauki tsuwwa,ta firgita da ringing din wayar daya soma fita,don a bazata yazo mata,saura kadan cup din hannunta ya subuce,ta ajjiye kofin ta nufi dakin da sauri.

    A can qasan gado ta gano wayar,a lokacin ana sake kira karo na uku MOMMY ta gani,shine sunan data sakawa hafsat,ta saki murmushi tana jin dadi,itace ta fara kiranta,cikin zumudi ta daga

    “Hello…..ina abban mimi?” Abu na farko da hafsat ta fara fadi kenan,ba tare data damu tayi sallama ba

    “Mommy ina kwana?,inasu mimi?” Ta maida mata da tambaya,ba tare data bawa tambayarta ta farko muhimmanci ba,saboda ba wannan bane damuwarta ba

    “Lafiya lau….ina abban mimi?”

    “Ya fita mommy”

    “Jiya a ina kika kwana?”

    “A dakina”

    “Shi kuma abban nasu fa?”

    “Ban sani ba,na rigashi yin bacci” gaban hafsat ya fadi

    “Da kika farka kenan a dakinki kika ganshi?” Kai ta girgiza kamar tana gabanta,gabanta kuma yana faduwa cike da fargabar kada ta karanci ya rungumeta,babban abun kunya kenan,tana kuma tsoron kada zancen yaje kunnen mutane a dauka ita din ‘yar iska ce

    “Daga dakinsa naga ya fito sai ya tafi office”

    “Karkimin qarya fa widad?” Kai ta langabe muryarta nayin sanyi

    “Allah ki tambayeshi ma” ta furta zuciyarta na addu’ar Allah yasa kada yace ya rungumeta idan ya tashi bata labari.

    Ajiyar zuciya ta sauke,hankalinta yana kwanciya

    “Shikenan,ina fata baki manta komai ba?”

    “Eh momy”

    “Da kyau,ki kula da kyau kinji ko?,ki kula”

    “To mommy…..mommy amma ki bani mimi ko….” Bata tsaya jinta ba ta gintse wayar,iya abinda takeson ji kenan,sauran koma meye ba damuwarta bane,ta aje wayar gefan gadonta tana furzar da iska

    “Shegiyar yarinya,kike cewa wani wai na tambayeshi,abbas din zan yiwa wannan tambayar?,ko ke ban isa na miki makamanciyarta a gabanki ba” sai kuma murmushi ya subuce mata

    “Anty ummee kinyi a rayuwa” ta fada a fili,ta duqa tasa qaramin muqulli ta bude drawer din jikin gadonta da take bawa kulawa ta musamman,kudade ne a ajiiye a ciki,ta fiddosu ta fara rigasu tana hade kansu waje guda,ranta na mata fari sol,yau sai taji gidan ya mata dadi,musamman idan ta kalli sassan widad din ra ganshi a rufe,sai taji kamar ta tafi kenan.

    Tana cikin maida kudin kira ya sake shigowa mata,ganin sunan mai kiran saita hade ranta,taja tsaki ta dauke kai,anty shafa ce yayarta,tasan kiranta baya rasa nasaba da zancan kudi,kullum zancanta na ta kawo wani abunne,ita kuwa kudinta bana tabawa bane,don haka ta maida wayar silent ta miqe tana kallon agogo.

    Sha biyu saura na rana,ko brush batayi ba bare ayi zancan breakfast shara ko gyaran gida,tana son abbas tana son ta kasance ko yaushe dashi,to amma idan suna tare irin wannan sakewar ce bata samu,shi yasa ba kasafai take damuwa da nisantar juna a tsakaninsu ba.

    Tunawa tayi tabar yara a falo,har tayi hanyar toilet saita sauya akalarta zuwa falon,tana addu’ar Allah yasa basuyi mata barna ba.

    Tun daga nesa ta hangi mimi tayi dafa’an a tsakar falon,ta fasa kwalin cornflakes ta cika madara kwano ta dama da ruwa tana ta durawa nawwara,tsawa ta kwaza mata,sannan ta fidda danu tana duban kwanon

    “Innalillahi” ta fada da qarfi,sannan ta nufi mimi da sauri, batayi wata wata ba ta gabza mata mari,gaba daya yarinyar ta jawo mata asara,kudin da ya bayar a siya wadan nan kayayyakin ta lankafesu,ta fitar da tsohuwar madarar daya taba siyawa yaran tasu tashan tea,ta ajjiye a dining tace suyi amfani da ita kafin ya dawo,yanzu ta daga madarar dukanta ta zazzage musu.

    “Uban wa yace ki taba?” Ta fada tana kama kunnen yarinyar,cikin kuka tace

    “Mommy,nawwara ce takejin yunwa” sai lokacin ta tuna bata basu komai ba ashe,ta saki kunnen nata tana huci

    “Ba sai kizo ki gayamin ba,kin tashi kin cuci mutane kin musu barna,matsa ki bani waje” haka ta sanya tsintsiya da ta gyara gurin,tana yi tana mita,yaran na rabe a gefe,mimi na hawayen murde mata kunnen da tayi.

    *Arewabooks: Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/7, 11:54 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 44

    Arubuce Ta Ke 44

    Page 44

    “Ma sha Allah” shine abinda latifa ta fada bayan ta gama feshe widad da turaruka masu taushin qamshi

    “Duba ki gani” ta fada tana matsar da ita gaban madubi,murmushi ne ya subucewa widad bayan ta kalli kanta da kanta ta madubin,tayi kyau irin yadda takeso,yau latifan tana da nutsuwar data mata ado haka

    “Gaskiya nayi kyau” ta fada tana dariya hadi da kallon latifa,sai dariya ta kama latifan

    “To sai a bani tukuici ai”

    “Duk kudin da uncle yake ajjiyewa ki dauka” ta fada tana murmushi,girgiza kai latifa tayi

    “A’ah,ba ruwana da kudin miji da mata,tashi kije qila sun fito,sai kun dawo” tana murmushin maganar da latifa ta fada da kuma farincikin yadda tayi kyau a saman fuskarta ta fita zuwa farfajiyar gidan.

    Dai dai lokacin da gafsat ke tsaye gaban motar abbas,sanye da baqar doguwar riga mai sulbi da jan mayafi babba data yafawa kanta,fuskarta kamar ko yaushe,babu alamun kwalliya ko d’is,sai maiqo maiqo da takeyi,don tana tsaka da barci mimi ta tasheta akan ta fito inji abbansu zasu wuce shopping.

    Sam bata ankara da widad ba sai data kusa gab dasu, qamshin ta dake kadawa cikin iska shine abu na farko daya fara jan hankalinta ta gane akwai baqo a wajen,sosai ta zuba mata idanu,sai taji gabanta ya fadi,wanne irin kyau yarinyar nan ke dashi?,ta tambayi kanta da kanta,take taji gaba daya ta muzanta,duk da cewa dama ba wani ado tayin ba,rigar da ita ta kwanta baccin,ganin bata jima da sanyata ba kuma a motar gida zasu fita su dawo yasa batayi wani sha’awar canzawa ba.

    Kafin ta dawo daga duniyar tunanin data lula widad ta iso wajen,sunata kakaci ita dasu mimi suna qyalqyala dariya abinsu

    “Ina yini momy” ta fada fararen jerarrun haqoranta suna bayyana,sautin siririyar muryarta ta karade kunnenta,ta kuma dawo da ita hayyacinta

    “Lafiya…..lafiya lau” ta fadi tana bude bayan motar da sauri

    “Ku shiga ku zauna,mimi ku shiga” ta fada tana duban idanun widad,kama hannunsu nawwaran tayi,ta fara saka mimi sannan itama ta shiga tana ci gaba da jansu da wasa.

    Wata ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke,har yanxu qirjinta bugawa yakeyi,kyawunta yana damunta,yana kuma son ya zame mata barazana,tafi yarda dari bisa dari kyawunta na daya daga cikin abinda ya fusgi hankalin abbas dinta,ta yaya zata gusar da wannan abu dake shirin zame mata barazana?.

    “muje ko” ta tsinci muryarsa dab da ita,sai ta dan bishi da kallo har sai daya kusa shigewa motar,ta taka jiki a mace ta isa gaban motar ta buda daya side din ta shiga.

    Wani baqon qamshi ne ya ziyarci hancinsa,ya soma shirin tada motar yana zuqar qamshin,sai daya tada ita sannan ya waiwaya ya kalli hafsat

    “Yaushe kika sayi wannan turaren?” Kishi ya kamata,bataso tace ba ita bace ya farga da yarinyar,idan kuma tace itace tayi qarya,duk da haka ta gwammace wa qaryar,sai tadan murmusa

    “Eh,cikin bikin nan na siya”

    “Yayi dadi sosai” ya sake fada yana dan waiwaya sashen da take,duk da baiji yana busowa daga nan ba,murmushin yaqe ta saki tana basarwa,zuciyarta na bugawa,tana addu’ar komai ya tafi dai dai.

    Sun dauki hanyan babban super market din suke siyayya lokaci bayan lokaci,motar shuru,bakajin komai sai muryoyinsu widad mimi da nawwara,a hankali muryarta ke shiga kunnensa,itama ta saje dasu abinta,zuciyarsa cike fal da tunanin ita din fa wai matarsa ce,sai kawai ya gyada kai qaramin murmushi yana qwace masa,saboda shi kansa yasan akwai jagwal,baisan kuma ya zata kasance masa ba.

    Murmushin da yaja hankalin hafsa,ta dan juya kadan tana kallonsa,sai shima ya kalleta ya basar yaci gaba da tuqinsa,ita sam irin hirar nan ta debe kewa don kana driving ma bata iyata ba,sai suyi tafiyar awanni amma saidai kowa yaci kansa,imma ya kunna radio imma ya zubawa hanya idanu kwanyarsa ta cika da tunane tunane har su iso inda zasu.

    Su suka fara yin gaba zuwa cikin super market din,cewa widad tayi ta tsaya dasu mimi zata dauko mata duk abinda ya dace,bata wani damu ba ta jasu gefe suka zauna,haka tayita zagaye,tana hada duk abinda ranta ya mata a kwandon data dauka,ba wani abun azo a gani take zaba ba,don ba iya zaben tayi ba,majority tare suke shiga da abbas din,shike zabar mata abinda yaga ya dace da ita,takanyi mita a fili da zuci

    “Wannan asarar kudine kawai,ni da kudin ka bani da yafi” dubanta kawai yakeyi

    “Abinda zaki sakamin din ko kimin amfani dashi na kalla naji dadinne asarar kudi?” Takan basar kawai,itama batasan tana wannan subutar bakin ba a wani lokacin.

    Sai data gama zane zabenta sannan suka hadu a wajen biyan kudi,yaga abinda ta diba,takaici ya hanashi cewa komai,ya biya kudin kawai suka fito,baisan yaushe zata koyi siyan abubuwa masu amfani ba,sa’annan kamar ita zata biya kudin,ta saka tsaiwa ta dauki kayan daya dace.

    Kai tsaye gidan hajiya ya wuce dasu,tunda hafsat taga titin da yahau tasan can zasuje,sai ta bata rai,amma dai batace komai ba,don batasan bata wasan nata.

    Yana tsaiwa a qofar gidan widad tayi zaraf ita dasu mimi suka fice,yadan bisu da kallo kafin ya dawo da dubansa kanta,itama shi take kallo,ranta ya sake baci,sai take ganin kamar widad din yake kalla

    “Amma zaka jiramu mu gama ne saimu wuce gida ko?,don inason nadan kwanta,bana jin dadin jikina yau” dubanta yayi kawai,tunda suka fito din batace masa bata jin dadi ba saida sukazo nan,saiya soma zare seat belt dinsa,har ya bude murfin motar sai kuma yace da ita ba tare daya waiwayo ba

    “You know what?…..idan zakaso saniya ka sota har qahonta,domin kuwa no matter what ba yadda za’a yi su rabu,mahaifiyata itace duniyata,silar nasarar rayuwata” a birkice ta juyo tana kallonsa,bataso ya fahimci emotion dinta ba,ta buda baki zata jefa masa tambayar rainin wayon ya buda motar ya fice ya barta a ciki.

    Katsam hajiya taga shigowarsu,farinciki ya cikata,murmushi ya wadaci fuskarta,tana marabtarsu tana duban widad,tare dason gano wani canji tattare da ita.

    Ta sake haske dai ta kuma sake fresh,amma girman da taso taga tadan qara babu shi,alamu dake nuna babu komai kenan daya wanzu tsakaninsu.

    Tana tsaka da wannan tunanin yayi sallama da muryarsa mai zurfi ya shigo,idanunsa suka sauka a kanta sanda take zaune gaban hajiyan hankalinta kwance kamar tana gidansu,fuskarta ta wadata da murmushin da zai iya cewa tsahon satin biyun da tayi gidansa bai taba ganinsa ba,ba wani alamun surukuta a tare da ita,yo ina ta gama saninta ma.

    “Maraba lale,saiga baqin yamma” hajiya ta fada sanda yake duqawa gabanta daura da widad din yana gaida hajiyan,dai dai sanda hafsa ta sanyo kai cikin falon,sai idanunta suka qara kusancin dake tsakanin widad din da abbas,bugun zuciyarta ya dadu,wani abu ya kama wuyanta,tayi ta maza ta kauda kanta tana zuqar numfashin wahala,sannan ta qaraso falon tana sakin sallama da shaqaqqiyar muryarta.

    “Ah,kacemin tare kuka?” Ta fada har cikin ranta tana jin dadin ganinsu gaba daya

    “Eh munje sunyi siyayya ne,saboda gobe in sha Allah zamu wuce”

    “To yayi kyau,ma sha Allah” hakanan ta duqa itama ta gaidata don ganin idanun abbas din,ba komai a fuska ko zuciyar dattijuwar ta amsa tana tambayar ta yara,bayan lafiya lau data ce bata sake cewa komai ba,taja gefe daya ta zauna ta tsuke bakinta,amma idanunta yana kan komai dake wakana cikin falon.

    Yadda taga hajiyan ta maida hankalinta gasu widad din ya qona ran hafsat sosai,ta yita mutsu mutsu cikin kujera cikin bacin rai,tana jin kamar ta tashi ta fice tabar musu falon,sauqinta daya harda yaranta take ja da wasa,don su mimi suna kan cinyarta suna ta harkokinsu,amma ita wannan sam baiyi mata ba,daga qarshe ta buge ta amsa waya ta fice harabar gidan.

    Huci ta dinga yi tana fidda iska mai zafi daga bakinta,zuciyarta kamar zata fito,bata iya jurewa ire iren wadan nan abubuwan,akan abbas zuciyarta na gaya mata komai zata iya yi.

    Ana idar da sallar magariba suka baro gidan,a hanyar komawa ma tamkar kurame,shi ya riga ya saba da irin wannan zaman,uwa uba kuma dama shi din ba mutum bane mai son magana,yayin da hafsat din keta cin daci,gaba daya zuciyarta babu dadi.

    Qaramar leda ta dauka ta debi wasu abubuwa d’ai d’aiku ta bawa widad,bata damu ba don ba damuwarta din bane,tasa hannu biyu ta karba tana godiya,shi kuwa baisan me ya faru ba,an masa total dai ya biya kudi,yana tsammanin kowa ya dauki abinda ransa keso.

    ***********Kuka take sosai tsahon awa guda cur da sukayi suna tafiya bisa hanyar bauchi zuwa kaduna,duk yadda zai mata tayi shuru yayin amma kamar ma bata san yana magana ba,har ransa ya baci ya shareta taci gaba da kukanta.

    Tun sanda motar samuel ta daga da latifa kano,su kuma tasu ta dauki hanyar kaduna ta birkice da kuka,bata taba tsammanin latifan tafiyarta daban da tasu ba.

    Sai data kusa rufe awa biyu sannan kukan ya fara ja baya,jikinta ya fara saki,sanyin yammaci gajiya da kukan data sha suka saukar mata ds bacci,a hankali ta langabe kanta gefe tana sauke ajiyar zuciya mai nauyin,alamun taci kuka ta godewa Allah.

    Dubansa yakai gareta kadan kafin ya dauke kansa yaci gaba da tuqinsa,cikin ransa yana sauke ajiyar zuciya,wannan aure ne ko rigima sabuwa ta sameshi?,ya tambayi kansa.

    Karo na biyu ya sake maida dubansa gareta,sai ya rage speed na motarsa ya gangara gefan titi ya tsaidata,ya miqa hannunsa a hankali ya sauke mata kujerar yadda zata ji dadin kwanciyar,ya koma seat dinsa ya zauna dai dai,sannan ya sake kunna motar suka ci gaba da tafiya.

    Yammaci lis suka shiga garin kaduna,kofar wani babban gida ya tsaya,ya danna hon,babu jimawa mai gadin ya iso ya bude gate din,fuskarsa cike fal da murmushi,da alama farincikin ganin dawowar abbas dinne,aiko yana sako hancin motar zuwa parking lot na gidan ya biyo bayan motar da sassarfa yana fadin

    “Barka da zuwa oga” qaramin murmushi ya saki,yana hangoshi ta madubin,mutum badai barkwanci,ya tsaida motar dai dai sanda ya qaraso gefan window dinsa.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/6, 3:13 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 34

    Arubuce Ta Ke 34

    Page 34

    Batulu dake zaune gefe tunda suka shigo gidan ta tabe baki,itakam ba haka taso ba,abubuwa da dama ta samesu ba a yadda take fata ba

    “To da alama dai uwar gidan nan tayi sake da yawa” ta fadi can qasan ranta,babu abinda take tunawa illa zamansu da fatima kafin su samu tabar musu gidan,koda yaushe mahmud ya tashi fatima dai…..fatima ce,basu samu salama ba saida tabar gidan,ko yanzun sun san cewa bawai tanar zuciyarsa bane gaba daya,rayuwarsa dai ta bari.

    Basuci da yawa ba suka ture abincin,can bayan awa daya saiga wasu sabbin coolers din,suna shigowa hajjaa ta gane daga gidan hajiyan abbas ne

    “Yanzu zakuci abinci ku ture” ta fada tana dariya sanda take bude coolers din,lafiyayyen abinci ne sosai,harda wani na daban tace na widad ne,sai ta miqawa nujood

    “Kai mata daki taci” nujood ta sutumi qawatacciyar warmer din dake fidda qamshi tun kafin ta bude ta wuce dakin da suka baro widad din. Su kuma a sannan suka sake sukaci suka qoshi.

    Saman katifa ta sameta,tana ta daddanna wayarta,wadda har yanzu batasan amfaninta ba idan ba game ba,dab da zata taho dai anty madeena ta saka mata numbers din mutane,ta kuma koya mata yadda zatayi wasu abubuwan

    “ga abincinki inji surukarki” nujood ta fada tana dariya,mayafin kanta tana gefe ta galla mata harara

    “Wai meye haka don Allah nujood”

    “Allah da gaske hajiya ce tace naki ne” ta zauna gefan widad din tana bude warmer din

    “Kedai kinji dadinki,kowa sai tattalinki yakeyi,kinga gidanki widad?,kinga kitchen dinki?,mtsewww,inda abbana zai yarda nima auren nan zance ayimin” kallonta kawai widad din keyi,ita kuma ji take dama itace su,tun sanda ummu ta fara mata fadan komai yace tayi tayi ta soma jin wani abu mai kama da takura ya sauka arayuwarta,kullum zancan ummu

    “Mijinki ne,babu musu a tsakaninku,ki girmamashi kamar yadda zaki girmama babanki da alhaji dani,ya fini matsayi yafi babanki matsayi” to wai banda abun ummu ta yaya zatace ya fisu matsayi?,idan tace tayi girmamashi tayi masa biyayya ta yarda da wannan,amma banda finsu matsayi (hankalinta baikai wajen ba).

    Tare suka soma cin abincin da nujood,tana ta bata labarin kayan da aketa jera mata, murmushi kawai takeyi,ita.mamaki abun yake bata,wai duk girman abu sai ace nata ne,har nan ma wai gidanta ne?.

    Koda suka gama saita labe ta cikin labule tana ganin yadda ake shirya falon,nujood na sake zugata ta tsaya ta kalla,har sai data gaji sannan ta koma ta zauna

    “Wallahi idan nice ko?, tabdi,sha’anina zansha babu takuramin” ta fada tana fadawa saman katifar,sai suka qyalqyale da dariya a tare.

    Da daddare aka sake kawo musu wani,muneer qanin abbas ya shigo da kansa bisa wakilcin abbas din,yayi musu sannu da zuwa,ya kuma tabbatar basa buqatar komai,sannan ya ajjiye musu kudi yace injishi.

    Sai wajen sha daya da rabi na dare ya shigo gidan,zuwa lokacin ya tabbatar kusan kowa yayi bacci cikin gidan,idan ma akwai wanda baiyi ba d’ai d’aiku ne,don haka kai tsaye ta wuce sashensa.

    Ya sameshi yadda yakeso,harma yayi mamaki,cike da tantama da kuma shakkar hafsa dince ta gyara ko sakawa tayi a gyara masa,bai sani ba,sai ya aje wannan tunanin,ya soma rage kayan jikinsa ya zubasu a laundry basket,ya wuce bandaki ya soma tara ruwa mai dumi sosai a bathtub,sai daya cikashi taf sannan ya fada ciki yana sauke ajiyar zuciya,bayan ya cikashi da turaren wanka mai sanyin qamshi.

    Luf yayi a ciki,idanuwansa a lumshe,yana jin hayaniyar daya wuni yana debowa tana sauka daga kanshi,sai daya kashe minti kusan talatin sannan ya wanke jikinsa daya tsumu da qamshin turaren wankan da kuma dumin ruwan daya jiqa kansa a ciki,ya zari daya daga cikin lausasan towels dinsa wanda qamshin shower gel da body mist dinsa suka kamashi da kyau,koda kuwa an wanke ya daura ya fito.

    A bakin madubi ya tsaya ya dauki wayarsa yana laluban layin hafsat,duk da bashi da hope kan zata daga,saidai cikin sa’a gab da zata katse ta dauka din

    “Ka dawo ne?” Abinda ta fara tambayarsa kenan,hakan kuma sai yayi masa dadi,saboda ya jima baiji magana cikin nuna kulawa kamar haka daga bakinta ba

    “Yeah,can u come to my room?” Ya fada da lallausar muryarsa da sauti can qasa

    “Why not?,gani nan zuwa” ta fada tana ajjiye wayar tata,sai ta miqe kanta tsaye ta soma canza kayan jikinta zuwa night gown,sannan ta shiga kitchen ta hada masa abinci ta kulle sassan nata,don taci alwashin yau din acan zata kwana ta fito.

    Duk da dare ne,hakanan babu cikakken haske a sassan widad din sai data zubawa part din nata harara,taja wani mugun tsaki kamar zata cire harshenta

    “Zakici ubanki da kyau,saboda tsaurin ido yarinya kamar wannan wai tasan soyayya?,tasan aure?,auren ma mutum kamar abbas,zaki gayawa aya zaqinta” ta sake fada tana jinjina kai tare da tabbatarwa da kanta hakan.

    Sanda ta shiga yana shafa mai ne,saita ajjiye abincin,fuskarta kadaran kadaham,ta koma gefan gado daga bayansa ta zauna,ya waiwaya kadan yana duban fuskarta,sai kuma ya dauke kai ya maida dubansa gabansa yana daukar body mist dinsa

    “Kinyini lafiya?,ya yaran” sai data dan yamutsa fuska kadan bayan ta tabbatar bazai ganta ba,tayi qoqarin saita muryarta,don tana jin kamar wani abu ya mata tsaye ne a hanyar shaqar numfashinta

    “Lafiya lau,yara kuma suna gida” ta cikin mudubin yadan dubeta kafin ya kawar da qwayar idanunsa

    “Har yanzu?,for now ya kamata ace sun dawo gida ko?,i missed them alort” baki ta tabe,bataga alamun hakan ba,ya shiga hidimar qara aurensa abunsa zai gaya mata haka?,da daa ne da tuni ya aika da mota ko kuma ya taka da kansa ya debo yaransa,amma yanzu saboda dalilin aurensa baiyi hakan ba,sai zancan a dawo masa dasu kawai yakeyi

    “Sai gobe idan Allah ya kaimu,zasu taho tare da nazeera,zata tayani hada abincin baqi” ajjiye body mist din hannunsa yayi ya waiwayo gaba daya yana kallonta,ya harde hannayensa aqirji,da gaske fa tana bashi mamaki,kamar ba hafsa na.

    Taji a jikinta sarai ita yake kallo,idanunsa ba normal idanu bane irin na kowa,zaiyi wuya ya kalleka dasu bakijisu har cikin qashinka ba,saita kauda kanta gefe,bataso su hada idanu,bare ya karanci komai ta cikin idanunta da wannan qwarewar aikin nasa da yake amfani dasu wani lokaci a kanta.

    Batasan tahowa yake ba sai da hancinta ya shaqi mayataccen qamshin nan nasa dake kashe mata jiki da zuciya,saman sofa bed ya zauna dab da ita,har gwiwarsa tana gogar tata,ya kamo hannuwanta sosai ya riqe cikin nashi,sai taji hawaye na shirin sauko mata,saboda yadda zuciyarta ta karye da tuna a yanzun abbas din sunan mijin mace biyu yake amsawa,so samu ta fusge hannunta,ta kalli idanunsa ta gaggaya masa magana,amma kuma hakan ya bata da tsarinsu,dole tayi laqwas,tana jin yadda azababben sonshi yake motsa mata.

    Da wata irin murya mai laushi yake mata magana,har yanzun bai saki hannunta ba

    “Idan nace miki banjin dadin wannan karamcin da kika yimin ba nayi qarya,kinyimin abinda babu wadda zaiyimin sai ke din,kin bani nutsuwar cikawa da sauke wannan nauyin,bansan da bakin da zan miki godiya ba hafcy” sunan da ya kirata dashi,wani suna ne mai dadadden tarihi a tsakaninsu,wanda ya jima bai kirata dashi ba,kuma kusan itace silar faruwar hakan.

    Dukka wadan nan maganganun da yake gaya mata gani take kawai rainin hankali da rainin wayo ne,maganganu masu zafi takeson gaya masa amma saita buge da janye hannunta daga nashi

    “Tunda dai ka samu yadda kakeso kuma ba shikenan ba?” Ta fada tana duqawa qasa ta soma serving dinsa,tasan idan ba haka tayi zata fallasa kanta ne kawai,saboda ta soma tsarguwa da irin kallon da taga yana binta dashi

    “Bismillah ga abinci nan”ta fadi tana matsawa gefe

    “Kiyimin alqawari zaku zauna lafiya ke da ita”

    “Banyi ba” ta fada a zafafe,saboda yadda takejin ta fara kaiwa maqura,haqurinta ya fara qarewa,ya zuwa sannan takai bango.

    Ita ta fara janye idanunta daga kallon qurillar da yake mata

    “Zanyi iya bakin qoqari na,zan mata yadda zanwa qanne na,amma idan ka taimakawa hakan ta hanyar nuna mata mutunci da kimata” ta qarashe zancan hawaye yana sauko mata.

    Karamin murmushi ya sake,sai ya bude mata hannayensa,with coolness yace

    “C’mon,is okay”.

    Yadda taso din hakance ta faru,a sassan abbas din ta kwana,ya sake tsumata da muguwar soyayyar nan tasa data sake dasa mata matsanancin kishinsa,ta kuma sake cin buri da alwashin hana kowacce diya mace lasar wannan tsadadda zuma daga gareshi.

    Tare suka kintsa sukayi alwalar asuba,abinda ya dade bai faru ba,shi ya sanya jallabiyya yadau hula da carbinsa ya wuce masallaci,ita kuma bayan ta idar ta maqale daga gefan gado,zuciyarta nata lasafta mata irin abubuwan da zasu ci gaba da biyowa baya cikin gidan bisa tsarinta da kuma yadda taso,tana jin bacci,tana kuma son komawa,amma tana son ta sake yin wani abun da zai qara wanke ta a wajensa,ya kuma share mata filin da zata aiwatar sa qudurinta hankali kwance.

    Sanda agogo ya kada shida saita miqe tana fita a sashen zuwa nata,ta kuma fada kitchen tanata qunquni da surutan hanata rawar gaban hantsi,tsahon rayuwar aurenta batajin ta tana shiga kitchen sau uku a irin wannan lokacin,koda abbas kuwa yana da fitar sassafe,saidai ya hadawa kansa komai,kafin ta tashi ma ya fice abinsa.

    Daga masallaci sai ya wuce sassan widad din don ya gaida baqi,yasan cewa dole akwai manya a cikinsu,duk da rabinsu suna masaukin da gwamnan bauchi da kansa ya bayar yace a sauki baqin.

    Yadda ya gaidasu cikin girmamawa da dattako ya qara shiga ransu inna laila,dukkan wata haiba da nutsuwa tasa gami da sanin darajar dan adam ta bayyana,widad ita da nujood da anty madeena suka kwana a dakinta,anty madeena tunda tayi sallah ta fito nan wajensu ta barsu a dakin,don haka cikin hikima inna laila tasa aka taso nujood a dakin,saura widad kawai.

    Har ya miqe zai juya inna laila tace dashi

    “Tana ciki ai” sam bai kawota cikin ransa ba,to amma ya kamata ya dubata,tunda yanzun dole tana qarqashin kulawarsa,bugu da qari kosa yaushe akwai wani sashe na zuciyarsa dake sake tunasar dashi muryar hajiya cikin sautin dake gaya masa amana ce ita a wajenka,ka riqeta amana.

    Da qanqanuwar sallama a bakinsa ya tura qofar ya shiga,qamshin sabbin furniture da turarukan wutan da aka ajjiye cikin dakin saman mirror suka cakuda suka bada wani kalar qamshi suka daki hancinsa.

    Sake maimaita sallamar yayi amma ba’a amsa masa ba,ya dan sake takawa zuwa ciki kadan,sai ya hangota daga gefan gadon,kwance saman lallausar sabuwar dadduma,ta qudunduna sosai cikin hijabinta jakar daddumar,da alama dasu tayi sallah,tana kuma idarwa baccin ya dauketa a wajen.

    Takawa yaci gaba da yi har ya isa gabanta,yadda ta cure sosai kamar maijin sanyi ko jariri a cikin mamarsa yasa ya fahimci kamar sanyi takeji,saiya waiwaya inda ac din dakin yake,sun qureta ne da yawa,ta kuma hadu da sanyin asuba,ya laluba remote saman bedside drawer ya kasheta,sannan ya maida dubansa ga fuskarta da rabinta ne kawai ya bayyana.

    Idanun nasa ya dauke,yaja da baya ya nufi qofar fita,dai dai lokacin da hancinta ya cika sa qamshin wani tutare na daban,saita buda idanunta da sauri,take ta hangi bayansa sanda yake ficewa a dakin,saita miqe da sauri ta zauna tana jingina bayanta da gado tana kuma raba ido

    “Me yasa ya shigo?,haka kawai tana baccinta” saita kalli jikinta
    “Allah ma dai yaso hijabine a jikina” ta fada tana sake jan hijabin tana rufe qafafuwanta,kamar ce mata akayi zai dawo.

    *AREWABOOKS:HUGUMA*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[2/27, 10:43 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)