Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 26

Sponsored Links

Page 26

Koda ya shiga sassansa sai yaji dama dama,duk da cewa akwai qura data dan shishshigo masa amma kuma babu wannan dattin da annakiyar ta sassan hafsat,bai gaji sosai ba kasancewar tafiyar jirgi ta banbanta data mota,don haka ya ajjiye yaran saman kujera sunata masa hira,yahau kakkabe sashen nasa da goge goge,sai da yaga komai ya dauki haske,sannan ya hada ruwa yayi musu wanka da kyau,yana wasafa yadda zai samu lokaci yakai mimi a wanke mata gashinta.

Sai da ya gama shiryasu sannan yayi nasa wankan,ya shirya cikin kayan barci saboda tara ta gota a sannan,kamar ya kirata yace ta kawo masa abincin nan amma sai ya fasa,ya tasa yaran a gaba suka koma can.

Tana kitchen tana ta kaca kacar yadda zata hada masa koda coleslaw ne mimi ta shigo tace tazo inji daddy, saita maida.kayan hadin data debo din kawai,ta kwashi warmer da plate din ta biyo bayan yarinyar,tana dan hade ranta,wai koda hakan zai sanya yaji shakkar mata magana ko fada.

Saidai kuma ya bata mamaki,saboda yadda yakecin abincin yana yiwa yaransa hira ba tare da yace da ita komai ba,can qasan ransa yana ji ne kamar ya furzar da abincin daga bakinsa,duka dai yana daurewa ne saboda muhimmiyar maganar da zaiyi mata.

Koda ya gama cin abincin bai tashi a wajen ba,sunta hira da yaransa yana biyewa shirmensu,duk da hirar babu wani armashi,ita kuwa gogar tana zaune a gefa tana danna waya,abinda tafi kauri kenan,bata wani damu da hira da miji ba sam,lokaci lokaci takan dan sanya musu baki a hirar,a haka har nawwara dake saman cinyarsa tayi bacci,jimawa kadan mimi ma ta soma gyangyadi

“Gwara ki kaisu daki ko?” Yace da ita yana dubanta,saita aje wayarta tana dan bata rai

“Sai da nace ma mimi ta wuce daki idan ta fara jin bacci fa”

“She’s too young da zata gane hakan ai” qarasowa tayi ta soma tashinta cikin hararrami,ya dakatar da ita cikin dabara ya daga yarinyar,ta kama hannunta suka wuce daki.

Ba jimawa ya miqe,ya nufi kitchen don dafa tea,saboda ba wani sakin ciki yayi yaci abincin ba.

Da kallo yabi kitchen din saboda uban wanke wanke da ya fara cin karo dashi,kana gani kasan ba iya kwanukan yau bane,saboda wasu ma sun fara bushewa wasu kuma sauran abincin ciki ya fara rubewa,kai ya girgiza takaicin na cinsa,ya matsa ya duba ma’ajiyar tukwanenta,cikin taimakon Allah ya samu wata wankakkiya,ya hada komai da komai ya tsaya ya jira ya tafasa ya juye ya dawo falon ya zauna ya fara kurba a hankali yana kallon labarai da ake haskowa a tashar alhadath,saidai sam ba ta nan hankalinsa yake ba,yana jiran jin fitowar hafsa ne,amma har ya gama babu ita ba dalilinta,wannan yasa ya miqe ya nufi dakin kansa tsaye.

Yana tura qofar suka hada ido,tana kwance tsakiyar yaran,ya qarasa shiga ciki a hankali hannayensa zube a aljihun wandonsa yana nazarin dakin a fakaice,komai babu kintsi,ko ina ba’a gyare yake ba,sai ya kauda kai ya maida gareta

“Zan wuce daki,wa zan daukar miki a cikinsu,coz na fara jin bacci,inason kuma muyi magana dake” fuska tadan yamutsa kadan

“Kawai ka kwanta a nan mana,ni bansan me yasa bakason kwana a dakina ba,saidai ni kullum ina yawon binka?” Ta fada yau dai tana dan karya murya,jingina yayi da madubin dakin yana qoqarin controlling kanta,gaba daya dakin its not well organized,komai a birkice yake ba bisa tsari ba,duk sanda zai kwana a dakin komai sai ya nemi inda aka wulla masa,wannan dalilin ya sanya zaiyi wuya kaga wani abu nasa mai muhimmanci a dakin.

Kafada ya dage
“Well,zanje na shirya”

“Yauwa,thank you”tafada tana dan jin dadi,saiya juya a hankali ya fice a dakin.

Sai da yayi shafa’i da wutirinsa,ya kuma dauka duk abinda yasan zai iya buqata sannan ya rufe sashen ya koma,ya isa dakin ya dora kayansa saman madubinta yana fadin

“didn’t you sleep?” Saita motsa kadan tana cewa

“Uhmm”

“Okay,tashi,dama muyi magana dake” dan muskutawa tayi kadan,sai kuma ta miqe a hankali ta zauna tana dan murza idanu,zuciyarta na bada Allah yasa samuwa ce tazo.

Kujerar gaban madubi yaja ya zauna dab da ita,har gwiwoyinsu na gogar na juna,ya goye hannayensa a qirji yana duban fuskarta da manyan idanun nan nasa da suke saurin kassarata,tsahon wasu mintuna baice komai ba,har sai data qosa tace masa

“Wannan kallon fa?,kana azamin nauyi fa,ka tasheni bakacemin komai ba” kai ya gyada siririn murmushi yana kufce masa,saiya saki hannayen nasa ya hade yatsunsa waje guda

“Har yanzu motar da kikace min kinaso ita dince baki canza ra’ayi ba?” Wani madaukakin murmushi ya kubcewa hafsat din,abunda bata taba kawowa shi xai mata maganarsa ba,duk da dama abbas din ya iya bazata,ba daga nan ba

“Eh itace” ta fada cike da zallar zumudi

“Shikenan,nan da two to three weeks zata iso…..sannan kuma…..inaso ki duba kayan dakin da kikeson canzawa,ki turonsu ta watsapp,amma kada su d’ara 1mil,sai nasu mimi su kuma kada su wuce 50000k” wani irin mamaki da farinciki suka cikata,cikin muryar zumudi tace

“Da gask kake abban mimi?” ta fada idanunta a waje tanason ta samu tabbaci.

Kai ya jinjina mata yana sakin qaramin murmushi cikin bata tabbaci,hannunsa ta kama ya riqe da kyau tana dariyar farinciki gami da yi masa godiya.

Hannayen nasu yabi da kallo,yadda ta riqe masa.hannun dama bata aikata hakan idan ba wani abun farinciki ya sameta ba,idan bai manta ba rabon data riqe masa hannun haka tun lokacin da ya shaida mata ya biya mata hajji,sai ya zame hannun a hankali yana cewa

“Yauwa,dama nace zamuyi magana ko?”

“Ai mun gama magana,irin wannan manya manyan albishir haka?” Ta fada tana washe baki,sai ya kada kai

“Saura abu daya”

“To ina saurarenka” ta fadi ba tare data bada wani muhimmin ba

“Hafsa” ya kira sunanta,sai ta amsa tana murmushi

“Komai muqaddari ne daga Allah ko?,hakanan rayuwarmu da dukka qaddarorinmu suna hannunsa,yadda ya tsara haka bawa zaibi,hakanan fadarsa ne daga qur’ani ku auri abinda yayi muku dadi daga mata bibbiyu uku uku da hurhudu…..” Statement dinsa na qarshe yasa fara’ar fuskarta taja baya,wani tunani kuma ya gilma mata,saita zuba masa idanu gabanta na wani irin faduwa,zuciyarta kamar zata fasa qirjinta ta fito

“Hafsat,Allah ya nufeni da qara aure,wanda za’a daura shi cikin sati mai zuwa”

“Meeee!!!” Ya fada da wata irin shaqaqqiyar murya,wadda tuquqin bala’i yasa ta gaza fita da kyau yadda ya kamata

“Relax,calm down please,hakan ba yana nufin matsayinki ya canza daga yadda kike a zuciyata ba…..”

“Wallahi qarya ne!……qarya ne abbas……qarya ne wannan” ta fada ya qaaraaji tana nunashi kamar wata mahaukaciya sabon kamu

“Shine ka zaunar dani kana yimin wadan nan kyaututtukan?,to banaso,ka riqe kyaututtukan ka!,wallahi baka isa kuma ka qara aure ba!,ni kadai ce matarka!,ni kadai zaka zauna da ita duniya da lahira!!” Ta fadi da wani qaaraajin tana dubansa da idanunta da sukayi jazur suka kuma firfito kamar wadda aka shaqawa borkono.

“Cool down,karki bari ranki ya baci kinji……zauna muyi magana ta fahimta dake” ya fada with softness yana yunqurin kamota ganin tana shirin miqewa,fusgewa tayi tana jifansa da wani mahaukacin kallo,ta bude bakinta cikin madaukakin sauti ta fara gaya masa dukkan maganganun da suka zo bakinta,miyagun kalamai na aibatawa da kuma tunzuri,sai ya koma kawai ya zauna,ya harde hannayensa a qirji yana kallonta a nutse.

Ya sani ita aka tabo,kasancewa batun lamari na kishiya a wajen mace babban al’amari ne da ba kasafai suke iya daukan wannan mummunan labarin ba,wannan dalili ya sanya ya bata dama taketa fadin dukkan abinda taga dama ba tare da yayi yunqurin dakatar da ita ba,duk da kalamanta akwai wuce gona da iri da kuma zaqewa da yawa,amma yayi haquri ne ya jura saboda yasan wani ciwo ne da radadi daga zuciyarta,wanda shine ya dasa mata shi yanzu yanzu.

“Shine ka zauna kana kallona?, wallahi abbas baka isa ba,wallahi nace bazaiyiwu ba” sai tayo kanshi,tana rarumo kwalaben turaren dake saman madubinta ya soma qoqarin jifansa dasu.

Cikin qwarewa ya dinga sanya hannu yana cafe duk wadda ta jefo,ganin ko daya bata sameshi ba sai tayi kukan kura ta jawo bed lamp ta wurgota.

Bai samu tareta ba,amma ta dakar masa hannaye,glass din jiki kuma ya yankeshi ba tare daya lura ba,saita tsugunna inda take ajjiye takalmanta ta fara daukansu suma daya bayan daya tana masa ruwansu.

Miqewa yayi cikin zafin nama da mazantaka ya isa gareta,ya kama dukka hannayenta ya hade cikin hannunsa guda yana kallon fuskarta,ransa ya soma baci,ya dubi sashen dasu mimi ke a kwance,Allah yasa babu daya cikin abinda take wurgowa daya samesu

“Ki nutsu hafsat!,ki nutsu!”ya fada shima da murya sa mai kaifi da zurfi,saita dakata din ta kece da wani irin kuka

“Macuci azzalumi,Allah ya isa tsakanina da kai,kuma wallahi wallahi baka isa kayi wannan auren ba,idan ba haka ba sai na baka mamaki nima dakai da munafukar da zaka auro,ka fita ka barmin dakina,ka fita bana son ganinka!” Ta fada da mugun qarfi,saiya sakar mata hannaye,ya kuma taka a hankali zai fice,sautin amon muryarta ya dakatar dashi

“Kazo ka kwashesu,suma bana son ganinsu,ka debesu daga gabana!” Dawowa yayi a nutse yadan tsaya gabanta yana kallon yadda ta birkice gaba daya,jikinta banda tsuma babu abinda yakeyi,yasa hannu ya kwashe dukkan yaran ya fita dasu.

Ya jima yana mamakin baqin kishi it n na hafsat din,ashe abun ya wuce yadda take tsammani?,wanne irin hauka ne wannan?.

Bai lura da hannunsa dake zubar jini ba sai daya kwantar da yaran saman gadonsa yaga stains na jinin a jikin blue bedsheet din nasa

“Ya salam” ya fada sanda yake duba wajen,sai yaga ya yanke sosai,don haka ya koma dakin yaran dake sassanta don ya dauko first aid kit.

Tun daga falonta yana iya jiyo gunjin kukanta,irin kukan da mutum yake zama dirshan ya bude dukka muryarsa yayishi,tausayinta sosai ya saukar masa a rai,sai ya kasa wucewa ya sake komawa ta dakin,sai biyu yana murda handle din yana jinsa a riqe da alama ta kulle ne daga ciki,ya sassauta murya yana kiran sunanta

“Open the door please, don’t hurt yourself fa”

“Ka tafi ka bani waje abbas,na tsaneka,banason kallon fuskarta,ka tafi nace tun ban bude na lahantaka ba!!” Duk yadda yaso ta bude din taqi,sai ma wasu miyagun kalmomin da zagi da yake antayo masa,hannunsa nata digar jini,dole ya haqura ya dauki kit din ya koma dakinsa ya gyara wajen.

Daren ranar baccinsa ragaggene,haka yayita kai kawo tsakanin dakinsa zuwa sassanta,yasan halinta da muguwar baqar zuciya,yana fargabar kada ta illata kanta ita daya kulle a dakin,saidai duk sanda yaje din zaiji motsinta,wannan ke bashi ‘yar nutsuwa kadan.

*Arewabooks: Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
[2/21, 4:17 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Back to top button