Hausa NovelsMatar Makaho Hausa Novel

Matar Makaho 86-87

Sponsored Links

Page8⃣6⃣&8⃣7⃣
Babane tsaye akan kafarsa yana gyara yayin dake kan bukkar sa, da mamaki Al’ameen yace ikon Allah baba menake ganin nan?

Da sauri baba ya juya da mamakin ganin Muhammad ya dawo daidai lokacin nan, Alhalin ba lokacin ake tashi aiki ba, lafiya ka dawo yanzun?

Kai zan tambaya dai baba, na ganka tsaye akan kafafunka, kaida ka karye?

Zoka zauna muhammad muyi magana?yace yana zama akan taburma.

Ba musu Al’ameen ya zauna a kusa da baban.

Muhammad ina fatan kaga abinda nake so ka gani koh?

Da sauri Al’ameen ya warware rawanin sa, kamar ya baba kuma me kakeso na gani?

Muhammad Abinda yasani yin haka badon kome bane, illah don naga kaje da kanka gidan sarkin nan, tunda na ganka jikina ya bani wani abu, kamar dake tsakanin ka da muhibbat da muwaddat ya baci sosai, haka sarki ma duk da rabona dana ga fuskar sa, bazan iyya tuna ranan ba Saboda dadewar da nayi bana gani, Amma fa ka sani nasan sarki tunkan yahau mulki, yanda kaga fuskar ka, haka fuskar sa yake sai dai ka nuna masa yaranta?

Me kake nufi baba bangane ba, wai sarkin da naga fuskar sa a rufe kana nufin yana kama da yara biyu dana gani innan?

Kwarai muhammad duk da dai akan samu mutum, ya samu mai kamar sa a duniya Amma kaman ku dasu Akwai alamun jini.

Baba ni bani da kowa a nijar fa bansan kowa a nan ba.

Toh Amma kaman nin ku, ku hudun nan yayi yawa muhammad?

Bamu hudu bane mu biyar ne, da kanwa ta.

Muhammad niba yaro bane, Amma tunda kace haka shikenan, amma dai zaka cigaba da zuwa aiki har lokacin da na yanke akan zancen kafata, tunda ba kariyar gaske nayi ba baikamata na koma ba yanzun?

Shikenan baba zan cigaba da zuwan,har randa zaka koma aikin, ina su gidado ne tunda na shigo ban gansu ba?

Sunje kasuwa yi mana sayayyan kayan abinci.

Tashi muhammad yayi ya ibi ruwa ya shiga band’aki wanka yayi ya shige d’aki ya kwanta, tunanin duniya ya dame sa, duk sanda ya lumshe idanunsa yaran nan yake gani wanda baba yace masa muwaddat da muhibbat wai suna kama da sarki, kenan suna kama dashi, kai shikam bai gane kan Al’amarin nan ba, wani zuciyar na kawo masa wani tunani, amma kokarin tunkude sa yake don yasan abune da kamar wuya.

Yana kwance har gidado da badaru suka dawo kasuwa, yana jinsu suna ta girki da jido ruwa Amma bai koh fita ba.

Har suka kammala aikin dare abinka da gidan gauraye, bayan sunci abinci suka wuce masallaci.

Daren nan sukutum muhammad baiyi bacci ba, sai kusan asuba bacci ya d’auke sa.

Washe gari muhammad yaje aiki kamar jiya bayan sun gama shayin safe, yaukam had’a masa akayi da yawa a tire, ya wuce dashi falon , da sallama ya tura kofar falon ba kowa a falon sai kamshin turare dake tashi aka tsakar falon, wucewa falon maimartaba yayi a hankali ya tura kofar da sallama.

Sarauniya ce cikin Alkimba a zaune akan kujera hannunta dauke da kumshen lalle ja abinka da farar fata sosai yayi kyau, sai sarki dake kujeran sa na special kamar kullum fuskar sa a rufe, sai muwaddat da muhibbat dake zaune akasan kushin sai tsohowar nan dake zaune a kujera tana magana da nabila, ke nabila nafa fahimci babu wanda ya bata ku sai lawiza(sarauniya) ace mutum ya dage sai yayi turanci abinda bama amfani muke dashi anan ba?

Kai mahmah karfa ki manta a abroad nake karatu kuma ashan basu san wani abu wai French koh buzanci ba, da turanci kawai ake Amfani kinga kuma nan gaba muwaddat da muhibbat suna gama secondary suma chan zasu, shiyasa nake saba musu tun a gida mahmah, nabila tace.

Murmushi sarauniya lawiza tayi tana kallon mijinta da kwata kwata hankalinsa baya wajen su, hankinsa bama a wajen su yake ba, hawaye ne ya cika mata ido, ta rasa yaushe ne ita da yaranta zasu samu lokacin sa? abu tsawon shekaru abu d’aya, tun yaransa na kanana suke korafi har yanzun sun girma har yabi jikinsu, Abban muwaddat……bata karasa ba sukaji sallamar muhammad.

Amsa masa mahmah tayi, ya karaso cikin falon yana gaidasu da turanci lawiza da su muwaddat ne suka amsa sarki kam koh d’ago kansa baiyi ba bare Amsa gaisuwa, mahmah kam baki ta kama sai kuma tayi shuru batace kome ba.

a kan table ya aje shayin ya siyaye a kofuna yazo ya aje musu, yana kokarin tashi saiga wasu zaratan maza sun shigo falon cikin sallama, maza ne guda biyu d’ayan zaikai shekara 40 d’ayan kuma zaikai 33 zama sukayi akan kujerun falon suna gaida mah mah da buzanci bayan ta amsa suka juya wajen sarki sauka gaidashi hannu kawai ya d’aga musu.

uncle Ango, nabila tace tana dariya

Hararan ta mai shekara 33 yayi ke wallahi bana wasa dake? zan saba miki fa.

Dariya muwaddat ta sake kai uncle jiya mafa aunty Amarya tazo school namu, ta kawo mana special Anko in mu na yaran Ango.

Ganin bakin yasa muhammad siyaye musu shayi suma, don shidai duk hiran da suke baji yake ba, kasancewar da yare suke magana, yazo ya jera musu a gaba, har zai mike kawai kafarsa ya taka na nabila,

ai da sauri ta mike cikin masifa, kai wallahi kaji na rantse maka ka fita idanuna, kai wani irin masifa ne,haka kawai kabi ka sani a gaba da fitina tunda ka fara aiki a gidan na kake takalata tun jiya?

Kiyi hakuri don Allah bada sanina bane, muhammad yace da sauri yana matsawa gefe duk da sumayya ta masa rashin mutunci a farkon zamansu, Amma bata taba masa a cikin mutane ba, koh zata masa masifa sai insun kasance su biyu, amma wannan a gaban sarki take masa zagi haka bataji kunyar mulki ba? a take yaji wani irin tsanar yarinyar.

Ke nabila matsalata dake kenan rashin hakuri da rashin kunya, d’aya daga cikin mazan ya fad’a yana mamakin rashin kunyar nabila

Gaskiya nabila halinki sai Allah ace ke a rayuwar ki rashin kunya ne baya baki kunya a gaban Abba kike irin wannan tsewar kamar ba sarki bane a gaban ki?

Kunya ne ya kamata da sauri ta sunkuyar da kanta kasa, cikin sanyin jiki ta fita a falon, muhammad ma hakuri ya kara basu ya fita, yana fita yaga nabila tsaye alamu dai shi take jira.

Wallahi wallahi in baka fita idanuna ba zan maka rashin mutuncin da ba’a taba maka ba, matsiyaci kawai shashasha duk cikin turanci take maganar.

Kala muhammad baice mata ba ya nufi kofa, sai masifa take Amma shi koh juyowa baiyi ya kara ganinta ba, yana gaba tana baya har suka fitoh a flat in sarki ta shiga nasu, muhammad kuma ya wuce sashen shayi.

*****************
Sumayya na bude kofar falon khadija ta gani tsaye da kaya a hannu, da mamaki tace”tsayuwar me kikayi a nan kuma, kika kasa shigowa koh rashin gaskiya ne”?

Ah ah aunty yanzun nake kokarin shigowa.

“Aiko kwara ki shigo inkam” tace tana koma ta zauna a kan katifa.

A hankali khadija ta karaso falon kayan dake hannunta ta kai d’aki, sai kuma ta makale taki fitowa gabaki d’aya fargaba ne a Ranta, ganin fuskar sumayya a hade.

“Khadija wai tsayuwar me kike a bakin kofar nan ne da bazaki shigo falon ba”?

A hankali ta shigo falon tana rabe-rabe a jikin falo a nesa da sumayya ta tsaya.

“Waike khadija meye haka? zama zakizo kiyi muyi magana”

Kiyi hakuri Aunty wallahi ni bansan da maganar wayar nan ba, kawai sai naga ya bani shine fa danaki karba ya shigo falo.

“Nidai bance kome ba nace kizo ki zauna muyi magana”

A hankali ta matso ta zauna a bakin katifar.

Kallonta sumayya tayi “menene tsakanin ki da kalamu-wahid”?

Wallahi Aunty babu kome a tsakanin mu dashi kawai fa mutunci muke, kuma aunty koh soyayya zanyi sai nayi da d’an yaron nan?

“Oh yaro koh lalle kam waya gaya miki ba’a auren yaro ai da ba’ayi da bazan aure yayanki ba”

Kai Aunty yayana fa ya baki shekaru 4 rus fa, Amma kalamu bazai girmeni da 2 years bama.

“Kwadaiji dashi wallahi ina nan ina zuba ido, kuma ga wayar taki saiki rike, tace tana mika mata kwalin wayar”

Amsa khadija tayi da sauri ta ruga d’aki da gudu tana murmushi don wallahi ba karamin son waya take ba.

“Khadija dawo nan”

Jin abinda sumayya tace yasa khadija dawowa ta zauna.

Kinga khadija waya a zamanin nan cikin kaso goma ya kwashe kaso 7 na hanyar lalacewar yara, sauran 3 nan sune ake amfanuwa, ki kula da wayar nan ban baki ita don kiyi abinda ranki yake so ba, kinga waya sirrin mutum ne wani bazaka taba tunanin koh yatsa aka saka masa a baki zai tauna ba, Amma in aka amshe wayarsa abinda za’a gani bamai kyau bane?na barki ki rike wayar nan ne saboda kalamu Amma ki rufamin asiri ki ji tsoron Allah ki kiyaye shiga inda bai dace ba”

Insha Allah aunty zan kiyaye.

“Yauwa sannan zaki iyya hawa online Amma ban yarda ki d’aura hoton ki ba sam banaso”

in Allah ya yarda Aunty

“Toh tashi ki tafi d’akin”

D’akin khadija ta shiga ta had’a wayarta daman oready ya saka mata wayar a cherge, ya saka mata sim suka, tana kunna wayar aiko ta shiga latsawa, ya sauke mata facebook whatsApp da instagram harda telegram duk ya bubbude mata account, call ne ya shigo wayar da sauri tayi picking ganin rubuta daya bayyana Nurul-Qalbi a screen in, tana d’agawa taji yayi sallama hade da kiranta da kanwar sa.

da masifa ta fara magana, Allah ya sauwaka ka zamo yayana wallahi wane kai kaji na fad’a maka.

Shuru yayi bai mata magana ba, jin baiyi magana ba yasa ta dawowa hayyacinta cikin kunya ta Amsa sallamar, tana masa godiyan waya daya bata.

baiyi magana ba har lokacin, ita ma shuru tayi kamar yanda yayi,sai da yayi minti biyu yace mata ta hau whatsApp ya mata messenge.

Kashe call in tayi ta hau whatsApp ganin akwai enough card a wayar.

Khadija kamfa gabaki d’aya yau waya ya d’auke mata hankali sosai, tana gama girkin ta, ta nuke a d’aki sai hira suke da kalamu, Abin har yaso bawa sumayya dariya daga zaran khadija taji motsen zata shigo d’akin saita kifa wayar ta kama baccin karya, Amma batace mata kome ba tunda yanzun hutun makaranta suke, sai kalamun yazo zata masa fad’a maganar karatunsa karya biye shashanci.

Ranan fa khadija a d’aki tayi shimfida a kasan tiles ta kwanta da waya a hannu, sumayya ita kad’ai ta kwana a falo.

***************
Yau kwanar muhammad 25 yana zuwa aiki gidan sarauta, zuwa yanzun ya fara fahimtar Halin mutanen gidan sosai, especially nabila ba karamin haushin yarinyar yake jib, bad’an kad’an ba, yau tun Asuba yayi wanka yabar gidansu, kasancewar yaune za’a fara bikin kanin sarki(Ramadan) kamar yanda yaji ana fad’a, shiyasa tun asuba zasu tafi aiki, don shirya shayi mai yawa da zai d’auke mutanen biki zasu wuni sha, duk lokacin da aka nemi shayi a samu kar ya kasance babu, aiko hakance tun safe da sukaje basu zauna ba daman har yanzun ba’a sakar ma muhammad hannu ya girka shayi shi kad’ai ba, anfi sashi ya rarrabawa mutane.

yau haka ya wuni aiki saiya kaiwa flat innan yana dawowa a bugo telephone in kitchen ace yakai shayi, gabaki d’aya yayi mugun gajiya.

Haka muhammad sukayi ta fama da aiki har na tsawon kwana 4, sai yau aka d’aura aure, da misalin karfe 4 na yamma liyafa aka had’a a tsakar farfajiyar gidan, manyan sarakuna da manyan kasa ne makil a ciki, masu kudi da shuni, tunda aka fara bikin sarki bai hallaci koh wani liyafa ba sai d’aurin aure da wanda yanzun ake, muhammad ne ya karaso filin yana raba shayi koh wani table yana aje musu nasu dayake taron na mazane da mata, kuma tarone na manya yasa Al’ameen yake bin kome sannu sannu karyayi kuskure koh laifi, kwala masa kira nabila tayi ganin ya wuce table nata da suke xaune da kawayen ta, bai aje musu shayi ba zai tafi next table, kai malam bazaka kawo mana namu shayin ba!!

Cikin haushi yazo zai dongora mata shayin a gaban table inda suke, by mistake kafarsa ta harde da cafet inda aka shimfid’a a kasa, kawai shayin ya watsale sai jikin kawar nabila, ihu kawar ta saka wanda yaja hankalin jama’a, ai nabila na ganin haka batayi wata-wata ba ta tsinke muhammad da mari.

Kafun ta sauke hannunta muhammad ya bata wasu tagwayen mari hagu da dama, masu masifar zafi ihu da sake cikin azaba don a tsawon rayuwar ta bazata iyya tuna lokacin da aka bugeta da wayon taba.

Yayan nabila dake gefen su ne ya mike cikin zafin nama ya d’aga hannu zai wanke Al’ameen da mari, da sauri Al’ameen ya cafke hannunsa cikin matsanannin cin bacin rai ya nuna mustapha da yatsa, jikinsa har rawa yake cikin kakkauran murya yace karka kuskura ka tabani..

Ai bai karasa maganar ba Ramadan(Ango)daya karaso wajen don abin sosai yajawo hankalin jama’a ganin mai aikin gidan sarauta ya mare yar gidan, cakumo kwalar muhammad yayi cikin zafin nama hade da kai masa naushe a fuska, da sauri Muhammad ya kauce a zafafe wanda yayi sanadin yagewar kwalar rigansa da ramadan yake rike dashi.

A take Ramadan ya ja da bawa tare da kwalo ido waje, jikinsa har rawa yake yana nuna wuyan Al’ameen, sai kuma cikin sauri yasa hannu akan rawanin fuskar sa zai…………

✨Ruqeenjalal✨

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
🧑‍🦯 *MATAR MAKAHO* 👨‍🦯
~ Na ~

🍃 *Rukayya* *Ibrahim* 🍃

Back to top button