Hausa NovelsMatan Ko Mazan Book 1

Matan Ko Mazan Book 1 Page 5

Sponsored Links

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 5️⃣
Ummi kwata kwata takasa runtsawa koyaya ta kulle ido ganin lokacin da Alhaji ke kallonta take, da yanda ya kula da ita dazun dinnan the same way yake handling su Aman that’s yanda yayi handling nata, abun yaki fita daga zuciyanta, the entire scene ya narkan da zuciyanta sosai dan har yanzu kamshin turarenshi takeji yanda yazo dab da ita, she can still feel dadin kamshin iskan bakinshi lokacin daya hura mata, mirginowa tayi daga dan katifan datake kai zuwa kasan tiles, sanyin tiles din yawani kara tsuma zuciyanta ta bude idanunta tana kallon POP sama fuskan Alhaji take gani wlh Alhaji akwai karisma da haiba dawani irin kyau ahankali tace “inama ya aureni” dawani kalan sauri tadaura hannunta saman bakinta kaman irin wacce tafadi taboo din nan, tayi aiki agidaje 4 wannan ne na 5 bata tabajin kaman mijin ko Alhajin gidan datake aiki ya aureta ba sai wannan sabida yanada mugun kirki, gashi da sanyin zuciya, sannan yanada natsuwa, yanada daraja mutane sannan yana son yaranshi sama da komi kawai mata ce baiyi sa’a ba wlh inda itace matanshi ko zaiga gata dan miji irin Alhaji da baida matsala hakan nan wlh kula zatayi dashi sama da yanda yake kula dasu Amal ma kula zatayi dashi kaman wani jariri tana bashi duk abinda yakeso aduniya, ahaka bacci yayi awon gaba da ita da tunanin Alhaji aranta.

Wuraren 1 yashigo gidan da kanshi ya kwaso duka kayan daya sayo dazu na cefene yakai kitchen ya ijiye komi sannan yawuce sama dan kwanciya.

As usual biyar yafito sanye da jallabiya tunda yabude kofanshi kamshi ya daki hancinshi ahankali yake sauka daga staircase harya karasa sauka kasa wutan ko’ina akasan akashe wutan kitchen ne kawai akunne ga kofan kitchen din abude wajen dinning yaje ya tsaya yana kallon kitchen din Ummi yagani tana girke girke daban daban ga su lunch bag na Aman da Amali akan island yau zasu school, tana sanye da Riga da skirt yana ganin kayan yagane su kayan Hadiza ne tun tana yammata sun kode sosai amman dudda haka sunma Ummi kyau that means tayi wanka kafin tashigo kitchen folding hannunshi yayi yana kallonta tundaga kan slippers green dake kafanta zuwa kanta dake daure da dan kwalin atampan jikinta, tanada tsayi sannan tanada hips dudda ba sosai ba but sunada curve irin yaran nan ne da suna samin kula zasu cicciko yanzu wahala ne yasa suke looking haka ma, dan lumshe idanu yayi yabude ya tsare fuskanta da kallo ahankali Yatambayi kanshi am I falling for this girl? Dan ijiyan zuciya yasauke yajuya yawuce yafice zuwa mosque yana deep tunani shiba yaro bane yasan when zuciyanshi keson abu.

Wuraren 7 nasafe yashigo gidan Hadiza yagani a dinning taci gayu sosai cikin wani exclusive atampa ta buga dauri tanacin lafiyayyen breakfast chips da pepper soup sai shayi agefe, itakuma Ummi na tsugunne a tsakiyan falo tana feeding Amal a baki Aman na kusa da su daduk ta shiryasu cikin kayan makaranta suna ganin babansu da gudu sukai wajenshi. “Daddyyy Assalamu Alaykum Dady ina kwana” murmushi yayi yadauki kowannensu yamusu peck yashigo dasu falon yace “ku karasa breakfast yanzun nan school bus zaizo” basuyi musu ba suka koma, anatse Ummi da kanta ke kasa tace “ina kwana Alhaji” batare daya kalleta ba yace “fine” sannan yadau remote yana chanza tasha 8 zai fita hakan yasa kawai ya ijiye remote din yawuce sama ko kallon HADIZA baiyiba itama bata kalleshi ba saima karasa cin abincinta datayi tawuce tadauki car key tace “ki dafamin couscous da daddare ke” ahankali Ummi tace “to Anty, saikin dawo Allah bada sa’a” yatsine fuska tayi bata amsaba tawuce tafita tashiga motanta tabar gidan, bata dade da fita ba motan su Amali yazo Ummi takaisu suma suka wuce tafito tana gyara wajen taje dinning ne ta gyara inda Hadiza taci abinci sannan tawuce tana duba girkin datake ma Kakan su Amal dazata zo, tana cikin tuka tuwon Alkaman taji kamshin turare dasauri ta juyo hada ido tayi da Nura daya shigo kitchen din yasa wani blue gizna shadda wlh yayi kyau na bugawa a jarida faduwa gabanta yayi dasauri ta dauke kai ta saki muciyan a tukunya zata duka yace “cigaba da abinda kikeyi” batai musu ba tacigaba saikuma tadan juyo hada idanu suka sakeyi ahankali bakinta nadan rawa tace “kana bukatan wani abu ne Alhaji”? Dan girgiza kai yayi yaja daya daga cikin kujerun dake gaban island din yazauna yace “me kike tukawa”? Atsanake tajuya takalli tukunyan tace “tuwon Alkama, kace Hajiya da safe zata iso saisa nake mata nasan basuyi kari ba suka shiga hanya, itakuma sister ka zan dafa mata abu daban” yana kallonta yace “nikuma fa” dan kallonshi tayi ga mamakinta murmushi yasakan mata dasauri tace “breakfast dinka nakan dinning amman idan kanason wani abu daban ne zaka iya fadamin namaka yanzun nan” “hmmm!” Yasauke ijiyan zuciyan dashi kanshi baisan karanta yafito ba maganan yatabamai zuciya dan wannan ne abinda matanshi bata tabamai ba just look at yanda yarinyar nan tabashi girma da daraja da kima kome yakeso yafadi zatamai that king treatment shitake mai, kawai saiya dago yakalleta yace “dafamin shayi mai kayan kamshi” dasauri tace “to” zare muciyan tayi daga tuwon tadan diga ruwa ta rufe tarage heat din tawuce ta wanke hannunta tashiga hadamai shayi shikuma yaciro wayanshi yana tabawa dan kawai tasaki jiki amman wlh kusan kome takeyi idanunshi binta suke, nan da nan tahada shayin tadauko wani hadadden flask jug tazubamai tasaka a tray tadauki cup da spoon da sugar kaga yanda take plating zaka dauka taje culinary school ne nan ko tsabagren experience ne a aikatau, tadauko tray din tazo har gabanshi ta ijiye sannan ta duka tace “nazuba maka?” Ahankali yace “yes” mikewa tayi yana kallon hannunta farcenta farare kal dogaye masu kyau tazubamai tace “sugar cubes nawa zansa ko asa zuma?” Kaman wani yaro dan he’s just enjoying the way take neman permission nashi for komi this is luxury da baya samu yace “zuma” dasauri tajuya tafita daga kitchen din taje dinning tadauko zuma takawo ta zubamai sannan tajuya tadauki cup din tadaura kan tray nashi tajuyo tabashi kallon fuskanta yayi sannan yasa hannu ya amsa yace “thank you Ummi” wucewa tayi takoma wajen tuwon tashiga kwashewa kaman daga sama taji yace “waye Mudin kauye?” Juyowa dasauri tayi takalleshi hada ido sukayi yana kurban tea juyawa tayi tacigaba da kwashe tuwon tana mamaki a ina yatabajin takira sunan Mudi saikuma ta sauke ijiyan zuciya tace “tsohon miji na ne” dasauri Nura yakalleta yace “kin taba aure”? Gyadamai kai tayi tace “eh amman an dade tun ina shekara sha uku-sha hudu aduniya” yana kallonta yace “meya rabaku”? Tsayar da kwashe tuwon datakeyi tayi saikuma ta kalleshi yanda ya tsareta da ido yasa ahankali tace “dukana yake, kullum kullum duka, hakanan kaman idan bai dakeni ba bayajin dadi rayuwanshi, shine…..” takasa maganan tai shiru takai hannu ta goge hawayen dasuka zubo mata dasauri tajuya tacigaba da kwashe tuwo Nura yace “shine meya faru”? Ahankali tana kwashe tuwon tace “shine rannan dayamin wani bakin duka saida na haifo bakwaini, inada cikin wata shidda lokacin, amace yafito yaron, saida nayi jinya na kusan shekara daya inata fama da yoyon fitsari, Gwaggo na ta hadashi da mai anguwa akan saiya sakeni kuma abimini hakkina dan ya illata mata jika tun bayan haihuwan dole dayasa nayi ban warkeba, to da kyar yasakeni amman dudda ina rashin lafiyan yakan biyoni har gidanmu yamin duka har suma inayi, ko baizoba kullum cikin fargaba nake zaizo, Maman mu tarasu Gwaggo mu ce kadai garemu kuma batada karfi ta tsufa, ahaka dai na warke but ina cikin tsoro kullum, saisa dataji wata mata dake zuwa kauyenmu kwasan yara aiki taje ta roka da kyar akace za’a daukeni, to aboye aka fitar dani daga kauyen mu kada Mudi yaganni, tundaga nan nazo birni tun ban gane abubuwa harna gane yanzu nima, amman inaso nakoma kauyenmu naga Gwaggo na da kannina Salamatu tai aure harta haihu Maimuna da Ikilima ne za’ayi bikinsu kwanan nan kuma inaso naje amman Gwaggo na bataso nazo tsoro take kada nakoma kauye Mudi ya kasheni, yanzu ance yafi da zama takadiri ya gagari kowa, tsoron shi ake har mai gari, amman nayi kewan garinmu da gidan mu da Gwaggo na da kannina sosai bansan ya Allah zaiyi dani ba bansan kozan kara sa kafa a kauyenmu ba” tai maganan tana kai hannunta saman fuskanta duka biyun tadanyi sheshekan kuka mara sauti, shiru Nura yayi yana kallonta tabashi tausayi sosai ahankali yace “kinaso nakaiki kauyenku kiga yan uwanki”? Dasauri tazare hannayen ta dagakan fuskanta takalleshi da rinannun idanunta yanda ya tsareta da idanu yasa gently ta gyadamai kai, murmushi yayi yace “I promise zan kaiki kauyen ku, and namiki alkawari ba Mudi ba ko mudari yake bai isa yamiki kallon banza bama balle ya dakeki kinji” gyadamai kai tayi ahankali, murmushi yadan mata yace “kada ki kara kuka bayama fuskanki kyau” akunyace tai murmushi shima murmushi yayi yace “idan Hajiya tazo dazaran nagama kata katan asibitin ta zan kaiki gida ko” gyadamai kai tayi dasauri, tashi yayi yakalli agogon hannunshi yace “bari natafi daukosu nasan jirginsu yatashi yanzu kafin nakai airport sun sauka, kinason nasayo miki wani abu”? Yamata tambayan da saida ta kalleshi da mamaki ganin ya tsaya yakuma tsareta da ido tace “Amali tadameni tun jiya zatasha yoghurt babu yoghurt agida” jinjina kai yayi irin yaji din nan yace “ke me kikeso”? Sunnar da kanta kasa tayi akunyace tace “slippers wannan yakatse dazu na naneshi da wuka mai zafi saisa na iya sawa” yanda takejin kunyanshi na burgeshi sosai, anatse yace “to” yajuya zai wuce dasauri tace “Nagode Alhaji Allah kara girma, saika dawo Allah ya tsare” juyowa yayi yace “Ameen Hajiya Ummi” dasauri takalleshi wucewa yayi yafice yana murmushi mota yashiga, saida yafara tsayawa a super market yayi sayayya harda cream da shower cream mai kyau yasa mata da su turaruka da wasu abaya daya gani a super market din da idanu ya gwada tsayinta haka yabiya kudi yafito, haryakai airport labarin Ummi yake tunani yaushe kauye zasu dainama yara Auren wuri ne haka, yanzu sabida wani katon mugu aka koro yarinyar nan aiki, yayi traumatizing nata tun tana 14, small girl fa, hmmm Allah ya kyauta.

Daidai yana parking awajen parking wayan Amina nashigowa fitowa yayi daga motan yana daukan wayan yace “okay ku jirani a arrival din gani nan zuwa” wucewa yayi tun kafin su ganshi ya hangosu, wata tsohuwa ce fara mai zanen kalangu a fuskanta zaune kan wheelchair dawata budurwa da akalla zatai tsaran Ummi ke gungurawa ga akwatinan su kan cart a gefe tareda mutumin dake turawa, ahankali tsohuwan matan tadago idanunta dan taji alamun danta ajikinta hakan yasa sai waige waige take, ta baya yazo yahada idanu da Amina daya mata alamun kartai magana sannan yataho kawai Hajiya ganinshi tayi agabanta ya tsaya bai damu da airport sukeba tsugunnawa yayi yasa guiwowinshi akasa yana kallon fuskan mahaifiyar tashi data washe baki ganinshi tace “me haka tashi tashi kayanka zasu baci, yanzu kasan banda karfi balle na wanke maka” ahankali yakai duka hannayenshi yatallabo fuskan mahaifiyan nashi yace “bance kada ki kara ciwo ba eh Hajiya?” Cikin barkwanci tace “ai dazai tasomin saida nace kai rashin lafiya ka manta kashedin da Nura yamaka ne kakeso kadawo kuma” dan murmushi yayi duk rashin lafiyan Hajiya bakinta is always there baya fatan tai rashin lafiyan dazai hanata magana har abada In sha Allah. Rungumeta yayi ahankali yace “barka da zuwa Mamana, Allah yabaki lafiya Hajiya, Allah yasa kaffara ne” bayanshi ta shafa tace “Ameen Ameen ai naji sauke Amina ai bata kyautamini ba banso ta tadamaka da hankali ba wlh, tashi daga kasa kaga jama’a sai kallemini d’a suke yasa guiwa akasa” batare daya saketa ba yace “albarkan mahaifiyata nake so” murmushi tayi tace “Allah maka albarka Nura, Allah ya lura dakai kaman yanda kake lurada ni, Allah yasa yaranka sumaka yanda kamini Nura, yanzu tashi mutafi kaji dan albarka” anatse yace “to Hajiya” sannan yadago yabama mai cart hannu suka gaisa sannan yakalli Amina hannu yabude mata dasauri ta rungumeshi tace “Yaya ina yini” kanta yashafa yace “lafiya lau Autan Hajiya” wheelchair ya karbe yashiga tura Hajiya da kanshi har mota saida ya zaunar da Hajiya tazama comfortable sannan ya sallami mai cart suka shiga mota suka tafi, Hajiya sai kallonshi take ta madubi tanamai hira tace “amman kai rashin lafiya ne ko Nura? Naga kafada sosai”? Dan murmushi yayi yace “aiki ne wlh Hajiya” ijiyan zuciya tasauke tace “to Allah yabaku sa’a kadinga hutawa kanacin abinci akai akai kaji ko” “to Mamana” ya amsa yana murmushi, tace “nataho maka da danderu” baki yabude yadan juyo zai kalleta dasauri tace “kul maida hankali tuki kake” dan dariya yayi yace “Meenah ya akayi akabar Hajiya tawuce da danderu”? Dan dariya tayi tace “ba anga batada lafiya ba babu wanda yayi musu da ita” murmushi kawai yayi yace “inason Mamana Ameena sosai” Hajiya data washe baki tace “nima inason d’ana sosai” Ameena ta turo baki tace “Hajiya nifa” dan dariya Hajiya tayi tace “Inason ku duka akwai wanda ma yasamu soyayyata irinki Auta na” ahaka suna family hira sukakai gida Nura yace “specialist danai consulting yace zai ganmu by 12 yanzu zakici abinci kihuta anjima saimuje asibitin ko” yayi maganan tareda yin Parking yafito da ita sabida dakali da kafanta tayi tafiya tana rikeda shi suna tafiya ahankali Ameena biye dasu tana kallon hadadden gidan, bude kofa sukayi suka shiga ciki wani lafiyayyen kamshi yamusu sallama dasauri Ummi tafito daga kitchen tazo har tsakiyan falon ta duka tace “sannu da zuwa Mama, ya hanya ya jiki, Allah yabaki lafiya Mama, Allah yasa kaffara ne” washe baki Hajiya tayi tana kallon Ummi tace “waye wannan yarinyar mai ladabi ba irin su Auta ba da basu gaida mutane da kyau, ga iya addu’a, waye ita”? Dan murmushi kadan Nura yayi yace “Ummi sunanta” daidai Hajiya na zama, Hajiya tasauke ijiyan zuciya tace “jiki Alhamdulillah Ummi, sannu kinji Allah miki albarka tashi tashi ki zauna, ina Hadiza? Nasan jikoki na ana makaranta ina Hadiza?” Hajiya takara tambayan da zuciya daya tana waige waige neman Hadiza, cikeda hikima Ummi tace “tadanje tadawo wani uzuri yakamata amman tace na kula dake da kyau kome kikeso namiki” sosai Nura ke kallon Ummi yanda yarinyar keda hikima baitaba sanin zata iya fadan magana hakaba, dariya Hajiya tayi tace “ayyooo” kallon Amina data shigo da jaka Ummi tayi gateman biye da ita da kayansu da sauri ta tashi tace “kawo nakai miki daki jeki zauna kihuta kinsha hanya” murmushi Meena tayi tace “thanks” kai kayan sukayi sama sannan Ummi tadawo tashiga kitchen a tray tajera abincin Hajiya da ruwa a bowl mai kyau na wanke hannu tafito takawo har gaban Hajiya, Hajiya tace “Ayyah sannu da aiki Ummi, Allah dai yasa cimata ne dan yanzu bakomi nakeci ba, cuta batayi ba” tai maganan tana bude kulan ganin tuwon Alkama da miyan zogale dayaji ganye yasa Hajiya tace “laaaaaaa Hadiza tamin girkin nan kafin tafice” dasauri Ummi tabude baki zatace eh Nura yace “Ummi ta dafa miki Hajiya” kara kallon Ummi Hajiya tayi saikuma ta nunawa Meena Ummi tace “kinga girkin sa’onninki ko ke sai shegen kiwuya, wai wannan kamshi haka bari naci abincin nan akasa zan zauna ma” da taimakon Nura tazauna akasa ta wanke hannu takai abincin baki saita kalli Nura takuma kalli Ummi takara kallon Nura again tace “Ummin nan dai danake gani tai girkin nan”? Gyadamata kai Nura yayi sai kawai Hajiya tace “Allahu Akbar wlh tayi girkin yanda nakeso, kaga ba gishiri ba magi, sannan bata sakamin jan nama ba hanta da Koda kadai ne amiyan, cimata tamin kuma yanda nakeso, bani jakana Meena kigani” bata jakanta Meena tayi Nura ya karba, dasauri Hajiya tace “ciro duka kudin dake purse dina” murmushi yayi ba musu yaciro dubu goma da dari biyar ne ta karba tamikama Ummi tace “ga tukuicin ki dan kin dadada mini rai kinsa natuna na diyata Aisha mai bin Nura tana aure a eygpt ita kadai kemini abinci irin wannan taste din wannan tarban da akamin bazan taba mancewa da ita ba, nagode ko Ummi amshi kudinki” akunyace tace “Mama kibar shi ni nadafa miki ne kawai wlh” Hajiya tace “laaaa ungo amshi nace” dan satan kallon Nura tayi shima kallonta yake ahankali yace “bazaki amsa kudin Hajiya ba kinsan kalan makon Hajiya kuwa? Ba kasafai akecin kudinta ba, ke kinyi sa’a tabaki” dariya duka sukayi harda Ameena, Hajiya tace “atoh dan haka karbi abinki” gently Ummi tasa hannu ta amsa ahankali tace “nagode Mama Allah ya ninka miki dubun su” Hajiya tace “Ameeen Ameeen” Ummi na murmushi takalli Ameena tace “nadafa miki shinkafa dafa duka dakuma taliya na manja wanne zan kawo miki” dasauri Ameena tace “taliyan manja” harzata tashi saikuma tadan kalli Nura dake kallonta kasa kasa tace “Alhaji mezan kawo maka bakayi breakfast ba kaima” abincin Hajiya yakalla yace “zanci abincin Hajiya” gyadamai kai tayi tawuce kitchen karaf akan idanun Hajiya yanda Nura ke kallon yarinyar amman batace komi ba, saida sukaci sukai kat Ummi takawo mata juice na cucumber kadai data mata Hajiya tasha sosai sannan Nura yakaita sama dakinsu dakin dake kusada na Hadiza inda Hadiza ta kwana ranan ta gyara Hajiya ma sai complain take ita batason sama Nura yace yafiso ta kwana inda zai dinga jin motsinta hakanan ta hakura.
Wuraren 12 suka fice asibiti Ummi tasake gyara gidan.

Sai wajajen shidda saura suka suka shigo gidan da gudu daga Aman har Amal sukazo suka rungume kakansu abinci Ummi takawo, tama Hajiya unripe plantain porridge datasa shuwaka da bushashen kifi da daddawa aciki shima ba maggi ba gishiri sai kamshi daddawa da kifi sun bama abincin taste, tayi jellof rice da naman rago ma sauran mutane, duk suka baje harda Nura za’aci abinci anan falo, Ummi takoma gefe ta duka Hajiya tace “kema taho nan kici, an taba haka ki mana girki saiki koma gefe, tahonan” dan satan kallon Nura tayi shi harya faracin faten Hajiya ma, da idanu yamata tazo nan, hakanan taje tashiga cikinsu suka faracin abinci, ita da Ameena da su Aman shinkafa sukeci, tunda tafara aiki yaune rana na farko data ji kaman tana gidansu Hajiya ne Gwaggon ta Amina kuma yan uwanta, sai hayaniya su Amal keyi anacin abinci, no wonder Alhaji keda kirki mahaifiyar shi batada matsala at all. Nura yace “Hajiya dan ban juice din cucumber dinki nasha” jug din Hajiya ta kalla tace “kai Nura na tsammaka na tsammaka harna gaji da sammaka wai kaine mara lafiyan nan ne”? Dariya akayi Ummi itama dan boye dariya ta tayi ganin yanda Hajiya keda barkwanci, takalli Nura tace “inje inmaka kaima Alhaji”? Batare daya kalleta ba yace “a’a kihuta zansha na Hajiya” kofi Hajiya ta dauka ta tsiyaya mai rabi ya karbe ita ta shanye rabin tace “Allah miki albarka Ummi zaki koyama wannan shashashan Autan nawa kafin mu koma” gyadama Hajiya kai tayi, Hajiya tace “Auta dukta cinye ke bakici komiba” dasauri Ummi tace “naci sosai wlh” kashigo falon ji zakayi inama haka farin ciki zai dawwama agidan, Nura yana lura da yanda bini bini Ummi kecin abincin tana duba Amal da Aman, chan kuma saita debo tai feeding Amal da mostly wasa take da abincin at this point bazaiyi karyaba yarinyar ta shiga ranshi sosai barinma dayaji labarinta dazu, yaji ta taba aure har ta haihu dudda pre matured birth tayi amma saiyaji yakara natsuwa da ita, wato saisa takeson yaranshi kuma saisa takeda hankali koba komi tanada experience, baison yayi mu’amala da yara masu danyan kai that knows nothing akan aure koba komi tasan menene aure kuma tayi zaman aure, tayi rainon ciki, sannan tayi nakuda, hakan is perfect for him.
Sake lura da yanda yake satan kallonta Hajiya tayi daidai nan aka bude kofa aka shigo dukansu suka dago kai cikeda fara’a Hajiya tace “oyoyo oyoyoo, sannu da dawowa Hadiza” tundaga inda Hadiza ke tsaye tabi kowa na falon da kallo da yanda falon yayi kacha kacha dudda bawai kacha kachan yayi ba kayansu ne jaka da gyaluluwa dasuka zuba akan kujera dan dawowansu kenan Ummi ta taresu da abinci sai abincin da Amal da zuzzubar a falon rice din, daidai nan idanunta yasauka akan Ummi dake cin abinci tareda Amina dakuma yaranta akasa tana kokarin bama Amal abinci abaki hankalinta kwance dan akasa take zaune technically batayi laifi ba yau. “Ke menene aikinki? Jibi yanda gidana yayi kacha kacha zama kikayi kinacin abinci? Kina yar aiki waya gayamiki kinada darajan zama inda mijina yake kici abinci eh”? Yunkurawa Ummi tayi jikinta yayi sanyi zata tashi dasauri Hajiya tace “dakata Ummi” takalli Hadiza dake tsaye awajen da taje tace “ninace taci abinc……” “Hajiya dan Allah kidakata badake nake magana ba” Hadiza tayi maganan rai abace dasauri daga Nura har Ameena suka juyo suka kalleta da mugun mamaki itama Hajiya tayi tsuri tana kallonta dan batasan haka Hadiza tazama tasan ta dai da rashin son aiki ko sunzo babban salla Kano dama ba zama take agidanta ba saidai ta gudu gidansu so bata wani zauna da Hadiza one on one na dogon lokaci ba, ganin abun zai zama wani kala yasa dasauri Ummi ta tashi zata juya strictly Nura yace “dawo ki zauna kicigaba da cin abincin ki” cikeda tsoro Ummi takalli Nura gabanta na faduwa tadan kalli Hadiza dake kallonta rai abace ahankali takoma ta zauna abun ya mugun mugun yima Hadiza ciwo dan yaune rana na farko daya nuna bata isaba agaban yar aikin yawanci ba agaban idanunta suke tsiyansu ba, zuciyanta wani kalan baki yayi takalli Nura tace “muzuba nidakai badai anzo har cikin gidana ana nema ajuyamaka kai ba tun yanzu an fara kulla kisisina da shairi ko da sunan rashin lafiya amman bakin mutum rass yazauna yana zakalkalan abinci to wlh muzuba dani dakai” Ameena jitayi kirjinta na tafarfasa badan Ya Nura na zaune wajen ba da wlh saita durama Hadiza ashar wucewa tayi fuuuu tayi sama kunyan duniya rufe Nura yayi abinda matarshi tama Hajiya jiyayi ma abincin ya isheshi kowama hatta yaran jisukayi abincin ya ishesu Hajiya ta kalli Ameena tace “tashi keda Ummi ku gyara wurin” kunya yasa Nura yamike yama kasa kallon kwayan idanun Hajiya yajuya yace “bari nazo Hajiya” baima jira amsanta ba yafice dasauri Hajiya tabishi da kallo saitaji dan nata yabata tausayi.
Kayan daya sayo dazu yasa mai gadi ya kwashe yakaima Ummi sannan yaja mota yabar gidan.

 

Abin yama Hajiya ciwo sosai, ya sosa mata rai, ta haifi yaran dasuka girmi Hadiza, yaranta mata uku biyu sunyi aure saura daya, ita Hadiza zatama rashin kunya haka. Dawowa daga kitchen Meena tayi ganin ba Yayanta awajen tazauna kusada Hajiya tace “Hajiya Hadizan nan yar iska ce kuma wlh wlh ta ijiye iskancin ta a inda tasabayi let her not try that nonsense da ke inba hakaba ni kadai na isheta wlh dan idan nakira su Ya Aisha har gida zasuzo sumata shegen duka ba Egypt ba Ya Aisha zata iya barin ko’ina take aduniya tazo muma duk wacce ta zageki shegen duka……” hannu Hajiya tadaga mata tace “banson maganan nan Auta, Matar yayanki ne” cikin fushi Meena tace “koma waye dama nasha gayamiki halinta tunda kika fara rashin lafiya sau daya bata taba kiranki taji yajikinki ba, yar iska kawai mahaukaciya wacce batasan darajan iyaye ba idanma kinci abinci na kanin ubanta kikaci kona danki, okay saitaga kina shurin mutuwa ne zatasan baki da lafiya dakikiya kawai” Hadiza dataji duka maganganun Meena dan saukowa tayi zataci abinci takoma sama saikuma gobe, takarasa saukowa takalli Ameena dabama ta lurada itaba tace “did u just call me dakikiya Ameena”? Dasauri daga Hajiya har Meena suka juyo suka kalleta Meeena zatai magana Hajiya taja hannunta cikeda hikima irin na manya tace “a’a badake takeba Hadiza wani labari take bani daya faru a kano” kwafa Hadiza tayi tace “gwara dan wlh dasaita bar gidan nan yanzun nan kema kibita” fizge hannunta Meena tayi daga hannun Hajiya tamike tsaye tai wajen Hadizan dan rainin wayon ta yayi yawa ta nunata da hannu tace “an kiraki dakikiya dake nake Hadiza idan baki koreni daga gidan nan ba baki cika yar halas ba” Hajiya datake daga zaune tahau yunkurin tashi tana kwalama Meena kira itama Ummi tafito daga kitchen da gudu tazo wajen yaran ma haka daidai Hadiza na nuna Hajiya tace “kinga dakikiya chan not me” Meena batai wata wata ba ta daurama Hadiza mari abaki jikake tasss!!!! Haba sai jini Hadiza ta kurma ihu tadaura hannunta kan bakinta dataji lema lema tacire hannu taga jini ahaukace tace “ni kika mara”? Ta chakume gaban rigan Meena da karfi, dambe sukahauyi ba kama hannun yaro Hajiya tafashe da kuka sosai Ummi tashiga rabasu amman ina basa rabuwa, dukan juna suke sosai bana wasa ba, Meena ta fizge ribbon din gashin nan taja gashin kaman zata cire mata su daga tushen kwakwalwa, da gudu Ummi tayi waje Mai gadin su takira yazo da kyar aka iya rabasu aiko Meena ta bala’in lallasa Hadiza bakinta sai jini yake ta yayyakusheta a wuya da hannu, dudda itama Meena ta daku a hannun Hadizan amman bata sami any ciwo ba kaman yanda tama Hadiza kowa sai nishi yake, shiga tsakaninsu gateman yayi Ummi tarike Meena tace “dan Allah kuyakuri” cikide zuciya Meena tace “kada kice na yakuri Ummi ba’a haifi wacce zata zagan mini uwa agabana banyi wani abu ba, am I even my mother’s daughter idan agabana za’ahau zagin Mamana nai yi shiru eh? Is she mad? Ba’a bata tarbiya agidan su bane? Idan ba’a bataba ni I will give u, dagayau kowace uwa kika tashi zagi zaki tuna diyar wata ta taba miki duka dakika zagan mata uwa, you are very very very stupid to insult Hajiya kinji, shegiya mai halin matan da iyayensu sukama baki” cikin ihu da kururuwa Hadiza tace “wlh, wlh, wlh yau saina kulleki a police station na rantse da Allah, ni kika daka kin san wacece ni anan Abuja? Number one, the most successful business owner anan Abuja, kinsan award guda nawa ke cikin office dina? BBC waye waye duk anyi hira dani, nizaki zo har gidana ki daka? Wlh wlh u are a small girl yau zan nuna miki your place” tana maganan tayi kofa bayan ta fincike key nata awajen tray na car key ta shiga motanta tafice dasauri Ummi tasaki Meena tayi wajen Hajiya dake kuka shikuma gateman yace “ayi hakuri ayi hakuri” yawuce yafita.
Dukawa Ummi tayi takai hannunta tana sharema Hajiya fuska tace “Hajiya kiyakuri” da kyar Hajiya ke iya magana tace “Ummi kiramini Nura gobe goben nan zan koma gida Meena batajin magana nasha gayamata zuciya batakai mutum ko’ina, kowani zagi Hadiza tamini sai mene ita ta zaga basaita bartaba akanme zatai dambe da Matar yayanta eh akan mene daga zuwa na garin nan yau yau din nan? To ko warakata na nan nahakura kiramin Nura idan akwai jirgi yanzun yanzun nan ma komawata zanyi kano” yanda Hajiya ke kuka tana bama Ummi wayanta yasa takira Nura, yana dauka yace “Hajiya” ahankali tace “nice kazo gida Hajiya na nemanka” hakanan jikinshi yabashi wani abu daman baiyi nisa ba duka duka yana ta gaban estate nasu fruits yaje saya yasan yanda Hadiza tadawo saitai rashin mutunci saisa baiyi nisa ba at all dasauri ya katse wayan, ijiye wayan Ummi tayi tadauki Amal dake kuka sosai ta goya Aman ma ta lallasheshi dan duk kuka suke sunga anci uwar Maman su, taje wajen Meena dake wajen dinning zaune akasa yanda Hajiya ke kuka yasa she’s feeling so guilty dan yanzun nan hawan jininta zakaga yatashi, yana isowa gidan ko parking baiyi da kyau ba yafito yashigo gidan Hajiya yagani tana kuka sosai yaranshi suma kuka Ummi sai jijjiga Amal take ga Meena akasan dinning idanunta sunyi jazur kayanta ya chukurkude kaman wani abu yafaru dasauri yayi wajen Hajiya ya duka yace “subhanallahi hajiya menene haka?” Cikin kuka tace “kaga Ameenatu yarinyar chan bazata taba daina jamini bala’i aduniya ba, duba jirgi yanzun nan idan an samu mukoma kano nahakura da asibitin Nura bazan iyaba bazan iya da tashin hankali ba” rungume Hajiya yayi yace “ya isa Hajiya ya isa daina kuka muje ki kwanta gobe da sassafe saiki koma” yay maganan trying to just calm her down, yace “ya isa ko I’m here now, everything is gonna be fine”.

Sama yakaita yana zuwa wani allura yamata a hannu da Dr yace adinga mata idan anga hankalinta yatashi nan da nan bacci yadauketa yasauko kasa yazo inda Meena take zaune yace “Meya faru?” Baki tabude zatayi magana saikuma tafashe da kuka cikin kuka tafada mai duka abinda yafaru batai karyaba zaiyi magana daidai an bugo kofa an shigo Ummi ce dawasu yan sanda guda biyu ta nuna Meena tace “officer ga tachan” tashi da sauri Nura yayi yana kallon Hadiza da yan sandan guda biyu wanda ganin Nura yasa basu karasa shigowa falon ba duk suka tsaya anan mini parlor dasauri yakaraso inda suke ya mike musu hannu yace “officer lafiya”? Mutumin yace “Madam dinka ne tashigar da kara kan mother Inlaw ta da sister Inlaw sunzo har gidanta sun mata taron dangi anmata duka, kuma munga shaida bakinta da wuyanta saisa muka biyota muyi arresting sai amusu sulhu a police station” ijiyan zuciya yasauke yajuyo yakalli Ummi dake faman jijjiga Amal tana kuka tarike hannun Aman yace “ku tafi sama keda Meena dakin Hajiya ku rufo kofa” dan yasan Hadiza zata iya kamasu da duka kuma, gyadamai kai tayi tawuce takama Meena duk sukai sama, Hadiza tace “ba sama ba ko lahira kukaje sai anyi arresting naku yau wlh” officers din duk suka kalli Hadiza Nura yace “bismillah ku muje waje” binshi sukai waje Hadiza tabiyosu officer da kanshi yace “ki barmu maza muyi magana mana Madam” tsayawa tayi saikuma ta buga tsaki takoma daki, explaining komi Nura yamusu yama nuna musu some magungunan Hajiya dake motanshi yabasu hakuri kan kada suyi arresting kanwarshi, ganin kamalan shi da natsuwan shi duba kuma da babban mutum ne, a well known businessman anan Abuja kuma ba yaro ba sannan sunga yanda Hadizan keyi itama borkonon kanta ce yasa sukai Na’am dudda haka saida suka amshi 20k a hannunshi kafin su tafi, suna tafiya ya tsaya ya jingina da mota yadan sauke ijiyan zuciya baiso ya yanke decision cikin fushi yakai 5min awajen sannan yakoma ciki afalo yaga Hadiza jikin window tana ganinshi ta taho tana ihu tana tafi tace “u bribe them and send them away sabida kar ayi arresting sister ka da Maman ka ko? To rest assure wlh wlh I will so deal with them, wlh saisun barmin gida, babu wani mahaluki dazai shigo gidana and snatched my peace of mind for me to menene amfanin karatun danayi? Ina zaman zamana wata Maman miji ta dawo gidana da zama is that even fair? Ba manyan asibitoci ne a Kano? Why here why Abuja? Let’s be fair fa Nuri, lokacin da Maman ka ke gidan mijinta mother inlaw dinta tazo ta tare mata agida? Then why me? Kuma ace ban isa nayi complain ba? Still sun shigo ur sister nada taurin zuciyan ta daken ni? Ni Hadiza? Wlh u have to choose one koka tattarasu kaje ka nema musu hotel ko ka maidasu kano, this house belongs to me and you Nuri aure yabani gidan nan, dan haka wlh sai sunbar gidan nan” girgiza mata kai Nura yayi, cikin kakkausan murya yace “wlh saidai ke kibar gidan nan not my mom! ki tattara kayanki kibar gidan nan don’t sleep in my house Hadiza, Na Sake Ki SAKI DAYA!”.

 

The foundation of Marriage is built on trust, respect, biyayya and love which I think Hadiza broke all awajen Nura, now do you all support sakin daya mata? Or do you think he should’ve done something entirely different???

Now the major abu da matan aure fears dayasa basason yan uwan miji suzo is because Men always tends to take side din yan uwansu and neglect side na matan su tambaya na anan shine Nura shima yadauki side din yan uwanshi kenan?? Or kuna tunanin he should’ve done better???

As a woman can you stand kiga an zagi mahaifiyarki data haifeki? Do you support action din Meena or not? Dan two things are involve Hadiza matan yayan tane sannan Hadiza ta girmeta far far and surprisingly Nura bai cema kanwarshi Meena anything ba….hmmmm share your two cents on this😞

Now overall tambayata is kuna tunanin basics na mata akan basason yan uwan miji suzo gidansu uhmmm to some extend sunada gaskiya dan maza always takes side na family su gaskiya ne???
How should a family Man dazai sami kanshi a tsakiyan conflict tsakanin relatives nashi da matanshi address the matter??

See y’all Saturday 💃
[9/18, 9:17 PM] +234 706 542 1229: 💫 MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

 

Back to top button