Blog

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 9

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 9

    Book 2

    *Episode 9*

    Uk

    ….wurgi yayi da ita kasan dutsen ya juya abun sa,ya shiga mota chike da tsanar hiyana ya ja motar da gudu ya bar wajen dai dai lokacin lokachin motar Khalid ya iso wajen yana kashe motar suka fito da sauri, a sukwane Fahad ya chiro wayar sa dake aljihun sa tare da balle agogon diamond dake hannun sa ya miƙawa yaya Khalid yayi tsalle ya faɗa kasan dutsen ya ce bi bayan hiyana, ta sauri yaya Ahmad ya karisa wajen yana kokarin faɗawa yaya Khalid ya riƙe sa yana faɗin “muje mu sauka kasan dutsen mu tare su a chan, a tare suka koma chikin mota yaya Khalid ya jasu juya kan motar yayi suka bar waje.

    Suna karisawa kasan dutse daga bakin rafin suka ga motar yaya Yusuf a wajen, kashe motar yaya Khalid yayi a tare suka fito suka nufi wajen da yaya Yusuf yayi parking motar sa, da mamaki suke bin motar da kallo, ga mota dai motar Yusuf ne amma baya chiki, ɗaga kai sukayi suka fara dube dube ta in da zasu ga Yusuf, amma basu ga ko mai kama da Shiba, almost 5mins suna tsaye sunyi shiru sai karan tsuntsaye da ke tashi da sautin zuban ruwa.

    Chan suka hango Fahad saɓe da hiyana a saman kafaɗar sa yaya Yusuf na biye dasu a baya dukkan su sunjiƙe sharkaf ruwa sai zuba yake daga jikinsu, hiyana kuwa ko motsi bata yi, da sauri yaya Khalid da yaya Ahmad suka karisa wajen su, a hankali Fahad ya kwantar da hiyana a kasa ta gefen rafin, zuba mata ido sukayi, fiskar ta yi falau ta kara haske sosai

    hannu Fahad yasa ya chire face mark dake fuskantar ta ba karamin razana sukayi da ganin yadda tayi haske sosai kamar babu jini a jiki ta, kasa kasa Fahad yace “daman haka kamannin fuskar ta yake? Ai wan nan ba in da ta bar yaya prince a kamanni, wlh tama fishi kyau” dogon tsaki yaya Khalid yaja chike da ɓachin rai ya fara magana “wai kai Fahad ta fuskar ta ma kake ko? Baka tunanin abun da Bgs ya mata bai kyau taba kashe ta fa yaso yayi ba dan Allah yasa muna nan ba” “No yaya Khalid wlh ni ina da tabbacin dan yaya prince yasan muna nan ne kuma yasan bazamu taɓa barin ta mutu ba shiyasa yayi hakan amma wlh da yasan babu kowa ba zai mata haka ba, ai shi ba mahaukaci bane, yasan me yake yi” da sauri yaya Yusuf ya karɓi zanchen da chewa “kana da gaskiya Fahad wlh idan Bgs yasan bamu nan ba zai yi kuskuren jefata chikin ruwan nan ba, tabbas yana da zuchiya kuma yana za zafin rai sosai kuma ya tsani mace amma ai shi ba mahaukaci bane ya san idan ya kuskura wani abi ya sami sister wlh Ammi zata iya tsine masa akan hakan, yana sane da duk abun da yake, inaga fa ya mata hakane domin gobe karta sake kwatan ta kashe kanta da kanta” chiki tsawa yaya Ahmad yace “dalla kuma mutane shiru koma me kusani idan da wan nan abun da yayi wa sister yazo da karan kwana da ta mutu ku ɗaga kan ku fa ku kalli daga in da ya jefota wlh idan da wata mai karamin zuchiyar ne tun kafin ta iso chikin ruwan nan zata mutu dan tsoro, than God sister iya suma tayi” chike da confidence yaya Khalid ya fara magana “kana da gaskiya Ahmad wlh ya zama dole yau mu gwadawa Bgs kuskuren sa ai dan yaga muna tsoran sa sosai ne shiyasa yake duk iskanchin da ya ga dama kuna gani fa yana jefata ya juya ya shiga mota abun sa da bamu zo da wuri bafa wlh mutuwa zatayi amma dan baku san gaskiya kun tsaya kuna wani chewa yana son gwada mata kuskuren tane, toma duk abun da sister tayi ba shi ya ja tayi ba yanzu me laifin sister da Bgs zai tsane ta saboda Allah dai ku gayawa kan ku gaskiya haka kwanaki ya zabgawa friend ɗin Aunty farida nan da take saudiya mari a gaban ɗan mijin ta,haka kuka take gaskiya ku ka che wai matan ne tayi laifi, me laifin ta dan ta masa nasiha akan ya rage zafin rai? to yau dai ko shine ya aifi zuchiya sai mun faɗa masa kuskuren sa” “yaya Khalid kai da waye zakuje faɗa masa kuskuren nasa!? Chewar yaya Ahmad yayi Maganar yana zaro manya manyan fararen idon sa ” ku mana ai ni ba zan tun kare sa ba ku zaku je” da sauri yaya Yusuf yace “wlh ban da ni sai dai Fahad” Mikewa tsaye Fahad yayi yana faɗin “kai idan kun ganni a lahira kai ni akayi me haɗina da yaya prince ba shiyasa nache muku abun da yayi, yayi dai dai ba ba wai dan yayi dai dai ɗin bane yasa nace hakan ai, kawai dan kar akai ga zanchen tun karar sane amma sai da kuka ja akazo wajen to ni kunga tafiya ta babu ruwana daku”

    Tsaki yaya Khalid yaja kafin yace “to sai ka ɗauki ta mu tafi ai, duƙawa yaya Ahmad yayi yasa hannu zai ɗauke ta chikin sauri yaya Khalid yace “aa Ahmad ka bari dai Fahad ɗin ya ɗauke ta” da mamaki Ahmad ya ɗago yana kallon Khalid irin kallon nan na karin bayani nikeso “kana da gaskiya Khalid na farko ita matar Aure ce kuma koba matar Aure ba daman Fahad ɗin ne ya dace daya ɗauke ta dan shine muharraminta” chewar Yusuf yayi maganar yana kokarin wuchewa ya shiga motarsa, dawowa Fahad yayi ya ɗuƙa ya ɗauki ta chak ya saɓa ta a kafaɗar sa ya nufi motar, Yusuf

    A gidan baya ya kwantar da ita san nan ya shiga gidan gaba, Yusuf ya shaga mazaunin driver, Khalid da Ahmad suka shiga nasu motar a tare suka tayar suka bar wajen suka nufi gida

    Suna shiga gida tun basu gama parking ba yaya Khalid ya fito chikin sauri ya faɗa chikin gida yadda suka bar su Zahra haka ya shigo ya same su sai kuka suke, suna ganin sa suka miƙe tsaye da gudu Zahra ta nufoshi a ruɗe take tambayar ina hiyana “yaya Khalid ina Aunty Hiyana” riko kafaɗar ta yayi yace “Auta kiyi shiru sister tana lfy kinji yanzu dai ina yaya prince ya dawo ne? “Eh yana ɗakin sa” “ok to ku jirani ina zuwa yayi maganar tare da sakin ta ya nufi stair ɗin.

    Ko da ya kisha ɗakin Bgs kwanche ya isko shi saman katafaren gadon sa, yana waya da Ammi shiru Khalid ya tsaya har sai da ya kammala wayar chike da ɓachin rai da jin haushi ya fara magana “yanzu dan Allah abun da kayi wa yarinyar nan ka kyau ta? Karka manta fa amana aka baka ita ai wlh kamata yayi ache kafi kowa tausayin yarinyar nan da kuma kaunar ta, saboda kasan Ammi ba abun da takeso a duniyar yanzu daya wuche ƴaƴa ɗan uwan ta ɗaya tilo, yara ba uwa ba uba sun taso chikin ukuba da wahalar rayuwa amma duk da kasan haka babu ko ɗan ɗigon tausayin su a rayuwar ka, anya Bgs kai mutun ne kuwa? Kai ni dai gaskiya na fara tantama a kan chewa kai mutun ne, koba mutun ba, to idan ma kai mutunne na fara tantama akan musulunci ka, domin duk wani chikakken musulmi yana da imani da tausayi, amma kai ko kaɗan babu,
    A waje ɗaya mukayi rayuwa da kai bare nache ko zama chikin turawane yasa tausanyin ka da imanin ka suka ragu amma gaskiya ya kamata ka gyara wlh ko dan neman lahiran ka, ni ko zaka kasheni sai na faɗa maka gaskiya dan ina son ka ina kaunar ka inason mu shiga aljanna tare bayan mun mutu” dakatawa yayi da Magana yana kallon BGS da idon sa ke lumshe,

    hayewa saman gadon yayi tare da ɗan bubbuga kafaɗar Bgs waro manya manyan green eyes nashi yayi kan face ɗin Khalid, chike da izza yace “au har ka gama surutun ne ai na ɗauka kwana zakayi kanayi” dunkule hannu Khalid yayi chike da jin haushi ya kaiwa Bgs naushi da sauri Bgs ya riƙe hannun sa yana faɗin “a lallai yau Khalid ka fusata sosai wai ma to me ya fusata kane? Tsaki Khalid yaja tare da gyara zaman sa a gefen Bgs dan ya lura idan mutun yace zai bi wa Bgs ta karfi tofa babu abun da zai sauya gwara subi shi ta lalama

    “prince dan Allah ka rage zafin zuchiyar nan taka kaji ko? da kasa mu farinciki wlh kana yawan jefamu chikin tashin hankali da damuwa, ni nasan kana sanmu kuma nasan haka halinka yake amma pls karinƙa sassautawa dan farinchikin mu zakayi hakan” dogon numfashi yaja tare da sauƙe ajiyar zuchiya kafin yace “duk abun da ka faɗa Khalid naji from A to Z so i will try my best amma ina son kasan wani abu ni ba wai nayi niyar kashe yarinyar nan bane na mata hakane dan gobe kada tayi ganganchin kokarin kashe kanta yanzu kaga ta ɗan ɗani yadda akeji idan akazo mutuwa, gobe ba zata sake yunkurin kashe kan taba “aa prince yanzu da bamu je wajen bafa mutuwan gaske fa zatayi “ai nasan dole zakuje wajen ne shiyasa na jefata “to amma lokachin da ka jefata bakayi tunanin kafin ta isa kasa zata iya buguwa da jikin dutsen ba? “Haba Khalid ya kake min tambaya kamar ba da Brigadier General Safras kake magana bane ni da idan na kalli abu sau ɗaya to zan iya rufe ido komai nisan abu in sai ta shi in harbeshi da gun, kuma ya harbu, karka manta dukka wani wanda yake riƙe da wata mukami a chikin sojoji ko mai girman mukamin to a karkashin Brigadier General yake daga mukami na babu wani kowani soja a kasana yake to kana tunanin a banza na taka wan nan matsayin ne, na san ta yadda zan jefata, kuma idan ka lura a mun rigaku isa wajen amma ban gefata da wuriba sai da na tabbatar kun kusa isowa san nan na kefata ina faɗa maka hakan ne ba dan na kare kai na ba sai dan kuyi farinciki kuma ku dai na dangan tani da mara imani”

    “eh hakane amma dai duk da hakan ka rinƙa rage zafin zuchiyar taka” “ka san me yasa na tsaya nake magana da kai Khalid? Girgiza kai Khalid yayi alamar a’a “to ina magana da kai ne dan naga yau kaɗau zafi dayawa duk chikin mu kai ne kaɗai wanda baya ɓata rai baya fushi kullun kana chikin farinciki kullun fiskar ka ɗauke da murmushi So ba zan so ganin face naka babu wan nan farin ciki ba gaskiya that why na tsaya nake maka wan nan dogon bayani amma yanzu zaka iya tafiya ka chigaba da farinchi ki” “Maganar bata kare ba ai Bgs bare kache na tafi” “ok to ina jinka saura me kuma” “me yasa kayi blocked na Aunty farida? “Wan nan bai shafeka ba Khalid tsanina da ita ne! “Ok naji bai shafeni ba amma zan rokeka wata alfatma dan girman Allah idan kamin hakan ka gama min komai aduniya” zubawa Khalid green eyes nashi yayi batare da yayi Magana ba “pls my Brigadier General dan Allah ban che ka ansa sister a matsayin mata ba ka ansheta a matsayin sister, ka dai na tsoratata ka daina daka mata tsawa pls idan ta gaishe ka karinƙa amsawa idan ta kawomaka abinci ka bari tarinka zuba maka pls wan nan alfarman kawai nake nema” “ok i will try my best, shike nan kaji daɗi? Murmushi Khalid yayi kafin yace “naji daɗi sosai shiyasa nake son ka my blood” “da kasan ka chucheni ba dole kace kana sona mana” dariya Khalid yayi ya sauka gadon ya nufi hanyar fita yana faɗin “ba wata chuta ya za’ayi na chuchi my blood ai hakan ba zai yuwu ba, ya kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin ya nufi palon kasa.

    Saman duguwar kujera mai zaman mutun 3 Fahad ya kwantar da hiyana dake jike sharkaf, da sauri su Zahra suka matso kusa da ita, ko motsi batayi da alama ta sha ruwa sosai, a hankali Fahad yasa hannu ya fara danna mata kan chikin ta, kaɗan kaɗan ruwa na fitowa daga bakin ta, har ya fara fita sosai kuka su Zahra suke sosai yaya Ahmad na basu hakuri, chike da jin haushi kukan nasu Fahad yace “zaku min shiru ne ko sai na kakkarya ku” tsit sukayi suna goge hawayen.

    Sai da hiyana ta amayar da ruwan chikin ta gaba ɗaya san nan ta fara tari, ganin ta farfaɗo ne yasa Fahad ya chire hannun sa daga kan chikin nata ya nufi ɗakin su dan chanza kayan jikinsa. Matsowa su kayi baga ɗayan su kusa da ita har da su Yusuf dai dai lokacin yaya Khalid ya sauko kasa ya fito daga ɗakin Bgs, wajen su ya kariso suka zubawa hiyana ido.

    a hankali ta waro blue eyes nata da suka sha ruwa suka koma jaa sosai, yunkurawa tayi zata mike zaune da sauri Zahra ta sa hannu ta tai maka mata suna mata sannu, kuka mai tsuma zuchiya ta fashe da shi.

    zama yaya Khalid yayi kusa da ita yana rarrashin ta chikin kuka ta fara magana “yaya khalid dan Allah ka faɗamin shin kaga wani abune ajikina wadda zai sa kowa ya tsaneni duk in da naje baa sona, a kauyen mu kowa ya tsaneni a gidan Ammi, Abba da Ammi sai kai da yaya Ahmad da Aunty Zahra Aunty Farida ne kaɗai kuke sona dan Allah ni me nayiwa mutane ne kowa bai sona” “ya isa haka sister kowa yana son ki kinji ki chigaba da hakuri zaki chi riba yanzu kije kiyi wanka ku shirya kuzo muje shopping domin saya muku kaya da wasu abubuwan da zaku bukata, karki damu da kowa mujema na saya miki waya ki fita harkan kowa kiyi abun dake gaban ki kinji? Dawo da kallon sa yayi kan Zahra “auta tai maka mata ki kai ta ɗaki tayi wanka bari na ɗauko mata jallabiyar Bgs, waro ido waje hiyana tayi chike da tsoro tace “wlh bana so bana son duk wani abu da ya shafi yaya prince Allah bana son ko sake kallon face nashi a rayuwa ta” matsowa Yusuf yayi kusa da ita chikin sanyin murya ya fara magana “sister na san ke macece mai ilimin addini kuma wadda take amfani da ilimin ta kin yarda da kaddara ko ba hakaba? Dan haka kiyi hakuri ki daure ki chigaba da yakin da kika fara gaba ɗayan mun nan har da su Abba da Ammi muna bayan ki kuma muna tayaki da addu’a, ina son ki sani sarkin yawa yafi sarkin karfi bi izzinillahi taala zamuyi na sara akan Bgs, ina son ki sani gaba ɗaya mu har da su Ammi mun dora yakinin mu a kanki ne mun sa ran ata da lilinki Bgs zai iya sauyawa, kada ki watsa mana kasa a ido pls sister mun miki alkawarin kome zai faru ba zamu taɓa bari Bgs ya chutar da keba ki yar da damu ki chigaba da hakuri kina masa duk abun da ya dache a matsayin sa na mijinki kinji? Shiru tayi ta sunkuyar da kai kasa dan gaskiya ba zata iya yiwa su Yusuf musu ba ko ba komai sun gwada mata halacci kuma Yusuf shine mutun na farko da ya fara share mata hawaye a duniya bazata taɓa mantawa da kyautatawar sa agare taba, murya na rawa yaya Ahmad ya fara magana dan shi har gobe yana son hiyana kuma yana tausayin ta sosai amma ba yadda zai yi “sister ki kara hakuri kinji? karki yanke kauna da samun rahman Ubangiji kiyi abun da muka chemiki zakiyi nasara In Sha Allah” ba karamin kunya hiyana ta jiba ache yanzu kamar su yaya khalid suke rukanta abu kai yazama dole tayi musu koda hakan zai zama sanadiyar rasa rayuwanta, ɗago kanta tayi chikin nitsuwa da sanyin muraya ta fara magana “na muku alqawarin zanyi iya kokarina a matsayina na ya mace ko da kuwa hakan che zatayi sanadiyar mutuwa ta to zanyi kuma zanyi alfahari idan na mutu ina bautawa miji daga yau zan ɗaura ɗamaran yaki da jiji da kan yaya prince” har suna haɗa baki wajen faɗin “good sister Allah ya dafa miki” kasa kasa ta amsa da “Amin” “Auta tai maka mata ki kaita ɗaki sai ki dawo ki je daki kema ki shirya .

    A tare suka mike gaba ɗayan su har da su amrat Lamrat kuwa tana mikewa ta fara ihu dan azaban zafin da take ji dazun ma da kyar ta iya mikewa taje ɗakin hiyana to yanzu ta manta da chiwon shiyasa ta mike da karfin ta “sisters meke damun ki? Chewar yaya khalid shiru tayi ta sunkuyar da kai kasa karisowa in da take Yusuf yayi ya duka ya saɓeta a kafadar sa ya nufi part nashi da ita yana faɗin “ai daman ke bai kamata ki bisu ba kamata yayi mu tafi ɗaki naje na miki wanka na shiryaki da kai na, kinsu da kallo Khalid yayi a zuchiyar’sa yana faɗin “kai amma gaskiya Yusuf baka da dama yanzu ka kasa hakuri kabar yar mutane ta huta, shine ka rigani lallai nima ba zan yar daba am sorry Auta gaskiya a yau ba sai gobe ba zaki karɓi bakon lamari, dan ba zan yarda Yusuf ya rigani samun baby ba” yayi nisa cikin tunanin sa sai yaji an taɓashi firgigit yayi yana kallon ta “yaya Khalid me yasa ka tsaya a nan? Wai gawa yayi yana faɗin “Auta ina Ahmad dake tsaye a nan “yaya Khalid ai lokachin da na shigo palon nan babu kowa sai kai kaɗai “ok to jeki ɗaki ina zuwa bari naje na ɗaukowa hiyana jallabiyar Bgs in kawo miki ki kai mata idan tayi wanka ta sanya” bai jira amsar taba yayi sama ya nufi ɗakin Bgs ita kuma ta wuche part nasu.

    Zaune gaban mirrow ya same sa yana faman haɗa wani allaura suna video call da Aryan gefen sa yazo ya tsaya yana karewa Aryan kallo, lokachin guda yaji wani mugumugun tausayin Aryan ya kara dira masa a zuchiya gaba ɗaya Aryan ya sauya kamar ba shiba yayi baki ya rame, daga chikin wayar Aryan yace “Khalid ya Auta? Kakalo murmushi Khalid yayi yace “Auta tana lfy ya karfin jiki? “Jiki Alhamdulillah” Khalid yana son ya tambayi Aryan lbr diyana amma yana tsoron kara tayar masa da hankali dan haka sai yayi shiru

    Ɗaure hannun sa Bgs yayi yana neman jijiya dan yayiwa kan sa alluran da ya haɗa “me zakayi kake ɗaure hannun ka haka ko dai baka da lfy ne? Aryan ya tambaya yana karewa Bgs kallo, shiru Bgs yayi bai tanka Aryan ba, zuba masa ido Khalid yayi yana jiran yaji amsar da zai bayar, dago alluran yayi zai yiwa kansa Aryan na ganin Alluran da Bgs ke kokarin yiwa kansa chikin sauri yace “haba Bgs bai kama ta a che har yanzu kana ɗirkawa kan ka wan nan alluraba, yanzu fa kana da mata pls my blood ka bari haka kar yaje ya taɓa lfy kafa ka rungumi matar ka kawai a wuche wajen, ɗayan hannun sa Bgs yasa ya katse Video Call ɗin tare da wurgawa Khalid harara ta chikin mirrow, juyawa Khalid yayi yana guntse dariya ya nufi dressing room nashi, bakar jallabiya ya ɗauko ya fito ya fice daga ɗakin.

     

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 4

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 4

    Episode 4*

     

    KANO

    washe gari tun karfe 7 Aunty farida Aunty salma Aunty mardiya suka shiryawa su hiyana ɗakin su da duk wani abun da mace zata buƙata an shirya musu, super market Aunty farida taje tayiwa hiyana sayayyan kanana kaya masu kyau da tsada Akwati 3 chike da kananan kayan ta kawo mata da kanta ta shirya mata a sip sosai tasake saka Hiyana a gaba tana bata shawara da kuma yadda zasuyi dan su samu su shawo kan Bgs, ba musu hiyana ta bawa Aunty farida goyan baya tare da mata alkawarin zata yi yadda tache ba karamin daɗi Aunty farida ta ji ba sosai ta sake karfafawa Hiyana guiwa tare da mata alkawarin zasu rinƙa waya kuma zata rinƙa taya ta yaki daga nata ɓangaren, Sallama sukayi dan yau zata koma Maiduguri, kuka Hiyana ta farayi dan tana ganin kamar idan Aunty farida ta tafi shike nan Yaya Prince zai kasheta, rarrshin ta Aunty farida ta shiga yi har ta hakura tayi shiru san nan Aunty farida ta tafi

    Yau ta kama Monday Hiyana na zaune a ɗakin ta dan tun da aka kawota ko palo bata lekaba saboda tsoron kar ta haɗu da yaya prince, tayi light make up sanye take chikin doguwar rigar abaya baki ta yafa gyalen rigar a kanta, tayi tagumi ta zauna shiru tana tunanin ina diyana ta shiga awani hali take yanzu shin ta chi abinchi kuwa? Tayi nisa chikin tunanin da take sai taji an buga kofar ɗakin nata, wani miguwar faɗuwa gaba taji chikin sauri ta miƙe ta nufi kofar, batare da ta tambayi wanene bane ta murza key ta buɗe kofar wani dum dum taji gaban ta ya faɗi ganin Bgs a tsaye ya juyawa kofar baya ya zura hannu a aljihun kallon sa ta baya ta farayi from head to toe sanye yake chikin wando sojoji 3cuter da farin t-shirt mara nauyi zubawa gashin kan sa ido tayi ya tara ya ɗaure a baya sai sheki gashin yake sauko da blue eyes nata tayi kan wuyar sa, wani bakin lallausan gashi ne kwanche awaje har kusa da farkon bayan sa sai wani fitinannen kamshin yake zubawa kamar anyi ɓarin turare ajikin sa dawo da kallon ta tayi kan ɗamtsen hannun sa dake chike kamar zasu fasa hannun rigar aranta tana faɗin idan yaya prince ya daki mutun da hannun nan tofa wlh ba zai tashi ba chikin sauri ta tsugunna kasa murya na rawa tace

    “Yaya prince ina kwana shiru bai amsa ba kuma bai yi wani motsin da zai tabbatar maka da yaji gai suwar ba, tunani ta shigayi na mai mai ta gaisuwar ne ko kuma nayi shiru to idan nayi shiru kuma bai ji gaisuwar da nayi da farko bafa? Idan kuma na mai mai ta zai iya hukun tani kai bari dai nayi shiru ai ya ji fitowa ta bari naga me zai che shiru shiru Almost 5mins tana tsugunne, shi kuma yana tsaye ya bata baya yana kallon palon kasa, shiru shiru Hiyana har ta fara gajiya da tsuguno kafarta ta fara yimata zafi sai wani ash take faɗi, shi ko yana tsaye ko motsi bai yi ba

    Juyawa yayi ya fara tafiya batare da ya kalli in da take ba sai da ya ɗan yi tafiya mai nisa ba tare da ya juyo ba yace “Abba na kiran ki a palon sa yanzu, yana kai karshen maganar ya sauka kasa ya nufi hanyar fita palon kasa cikin sauri Hiyana ta miƙe tana kallon sa sosai ta zuba masa blue eyes nata tana kallon yadda yake tafiya, sai da ya fice daga Palon san nan ta sauke ajiyar zuchiya a file ta fara magana “kai gaskiya yaya prince yana da kyau sosai Ni wlh ma gashin kan sa na burgeni ga hannun nan na sa shima burgeni yake sosai, ɗakin ta ta koma ta ɗauki hijabi babba har kasa ta sanya san nan ta fito ta sauko kasa ta fice daga palon ta nufi palon Abba

    A bakin kofar shiga part ɗin Abba ta samu Bgs tsaye yana latsa waya, tunani ta shigayi to me ya tsayar da shi kuma a nan? Karisowa tayi wajen da yake ta sake sugunnawa tace “yaya prince ina kwana, ba tare da ya ɗago da fuskar sa daga kan wayar tasa ba ya daka mata wani mugun tsawa chike da izza yace “ke Ni zaki tsayar ina jiran ki!!? Chike da tsoro da karyewar zuchiya murya sai kerma yake tace “kayi hakuri yaya prince ban san Ni ka ke jira bane, dogon tsaki yaja tare da shigewa chikin part na Abba chikin sauri ta miƙe tabi bayan sa

    Gaba ɗaya family sun haɗu a table ɗin chin abinchi

    Abba na ganin Bgs da Hiyana sun shigo a tare ya fara murmushi yana faɗin “haka nake son ganin ku kowa ya shigomin shi da matar sa a tare shi yasa nache kuzo a tare, wani kululun ɓakin chiki Bgs yaji tazo masa har wuya jiyake kamar ya shake yarinyar nan ta mutu kowa ya huta wai ma ni ban ga abu da ya sanya Abba yake son dan gan tani da yarinyar nan ba

    karisa wa wajen Table ɗin su kayi kujerar kusa da Aryan Bgs yaje ya zauna tsayuwa Hiyana tayi tama kasa zama dan tsoro, sai kallon su Zahra take ɗaya bayan ɗaya kowache tana zaune kusa da mijin ta ba karamin kyau hakan ya mata ba ji tayi itama tana bukatar zama kusa da mijin ta

    hannu Abba yasa ya mata nuni da kujerar dake gefen Bgs ɗin yana faɗin “zo ki zauna kusa da mijin ki, jiki ta har rawa yake saboda tsoro gaba ɗaya palon sunyi shiru suna kallon ta ita kuwa zulaihat kallon Bgs kawai take tana yaba kyan sa chike da ɓachin rai Bgs ya miƙe yana faɗin “Abba ka dai na min hakan bana so! No need ma na ji dalilin da ya sanya ka kiramu na fasa yin 3 month ɗin yau jirgina zai ɗaga zuwa London” tun da ya fara magana gaba ɗaya family suka nitsu suna kallon sa yana kai karshen maganar ya juya zai fita chikin sanyin murya Ammi tace “Prince dawo ka zauna a sukwane Bgs ya juyo dan Ammi bata taɓa yi masa magana da sanyin murya haka ba kuma bata taɓa kiran sunan saba sai dai tace masa kai, lallai yau dole nayi abun da kike so my Ammi nan take yaji zuchiyar sa tayi sanyi juyawa yayi ya koma kujerar da ya tashi ya zauna, shi dai Aryan duk wan nan abun da ake bai ma san ana yi ba dan kwata kwata hankali sa baya tare dasu ya sunguyar da kansa kasa da alama tunani yake

    “Hiyana zo ki zauna kusa da mijin ki chewar Ammi chikin rawar murya hiyana tace “Ammi ni bana jin yinwa zan iya komawa ɗaki? Gaba ɗaya su Abba sai da suka tausaya mata ban da zulaihat da Aunty amarya dake ta jin daɗi nuni da hannu Abba yayi mata akan tazo, ba musu ta karisa kusa da shi zata tsugunna yayi saurin dakatar da ita tare da kamo hannun ta ya zaunar da ita a saman kujerar dake kusa dashi “Abba wai me yasa ka kiramu ne chewar Yusuf dake zaune kusa da Baby Lamrat nashi, gyaran murya Abba yayi san nan ya fara magana

    “Daga yau idan ba nawa matan ba karwan da ya sake zuwamin palo chin abinchin kowa matar sa ta rinƙa kai masa ɗakin sa, da sauri Yaya Ahmad yace “Abba ni da Umar da Haidar fa “eh ku ma ai na kusa yin naku bikin amma kafin nan kurinka zama a ɗakin ku mai Aiki tana kawo muku” Umar yayi sauri chewa “Abba dan girman Allah karka yimana irin Auren da kayiwa su yaya prince kabari mu samo matan m.. bai karisa maganar ba yayi shiru sakama kon wani mugun kallo da Bgs ya wurga masa dariya ne yaso kub chewa Zahra Amma sai tayi saurin damme wa hakan ya haifar mata da tari, tari take sosai chikin sauri Khalid ya ɗauko ruwan dake gaban Abba ya fara bata abaki yana faɗin “sorry my wife yana ɗan bubbuga mata baya

    Wani kunya Ammi taji ya lullɓeta ji take kamar ta make Khalid, shi ko Abba sai murnushi yake ba karamin daɗi yaji ba ganin yadda Khalid ke kula masa da autar sa

    wani dogon numfashi yaya Aryan yaja tare da miƙewa yace “Abba zan koma Maiduguri an jima amma a yau zan dawo, bai jira amsar Abba ba ya fice da sauri saboda harara da Aunty Amarya ke wurga masa, miƙewa Bgs yayi ya nufi hanyar fita “Hiyana tashi kije ki shiryawa mijin ki breakfast nashi ki kai masa ɗaki chewar Abba yayi maganar yana kallon Hiyana kamar zatayi kuka haka ta miƙe jiki ba kwari ta bi bayan Bgs chikin fushi da ɓachin rai Aunty Amarya ta miƙe ta bar palon

    Kai tsaye ɗakin ta ta nufa sauri take sosai tana shiga ta ɗauko wayar ta dake saman drawar gefen gadon ta shiga contact ta fara kiran layin hajj sadiya bugu ɗaya Hajj sadiya ta ɗaka babu ko sallama Aunty amarya ta fara magana “Hajj sadiya ina kike? Daga ɗayan ɓangaren Hajj sadiya tace “me kuma ki ke nema na yanzu ba da kin che kekam kin tuba ba dan kawai ɗanki ɗaya ya rasu “dan Allah Hajj sadiya ki dai na wan nan magana ai lokachin gani nake kamar ni che nayi sanadiyar mutuwar tasa saboda kinga mumukasa gagarabadau ya yiwa Ahmad asiri to kingani kuma sanadiyyar rashin lfy Ahmad Aiman ya fara samun matsala kuma sanadiyar jin an che Ahmad ya rasune yasa zuchiyar Aiman ɗin ta buga ya mutu idan kikayi lissafin zaki ga kamar ni che na kashe ɗa na da hannu na “aa Hajj Hajara ba wan nan magana ba ke kika kashe Aiman ba lokachin sane kawai yayi kawai idan zaki tashi ki san me kike gwara ki tashi ki samu ki kama gidan ki a hannun ki dan yanzu fa ba’a zama motsawa ake ta ko ina” “to Hajj sadiya naji yan zu dai ni wlh ko 20m zai iya badawa in dai za’a min maganin ranan wajen Aishan nan domin suna neman haukatamin yaro “wai wasu yara kuma bayan an riga an gama Aiki” “aa Hajj sadiya ai iya diyana kawai Aikin ya kama ita hiyana wlh ko chiwon kai bata yiba haka itama karamar ko chiwon kai bata yiba ɗan gara Lamrat maganin ya kayar da itama kuma har yanzu tana cikin chiwo amma fa ba wani sosai bane” “to yanzu dai kin ga gagarabadau aikin farida yake yi idan ya gama sai mu sake yi masa maganar yaran muji me zai che “to shike nan Hajj sadiya pls ki kara himma ya maganar zulaihat kuma? “Karki damu da zanchen zulaihat na kusa kammala komai yanzu dai ki san yadda zaki rinƙa haɗa zulaihat da shi Safras ɗin saboda ta hakane maganin zai fi yin Aiki “tab lallai Hajj sadiya wlh baki san halin Safras bane bashi da kirki ba wace ta isa ta shiga part nashi kuma shima baya shiga part na kowa a gidan nan sai part na Abba da uwar sa sai kuma Aryan shi kenan “to Hajj Hajara in dai hakane mu gwada tura zulaihat taje part nashi a matsayin yar Aikin da zata rinƙa yiwa wan chan shegiyar matar tasa Aiki kinga daga nan zamu samu abun da muke so “eh hakane wlh hajj sadiya kin kawo shawara haka ko za’ayi barima naje tun yanzu na shirya hakan, bari na samu zulaihat na faɗa mata yadda zamuyi kin gama chikin ruwa sanyi zulaihat zata chi uban yarinyar” wani dariyar mugun ta Hajj sadiya tayi kafin tace “kai kawata shiyasa nake bala’i son ki “ni ma Ai ina bala’i son ki hajj sadiya domin duk wata matsala da na shiga ke kaɗai kike bani mafita yanzu dai bari muje mu fara shiri akan hakan, daga nan sukayi sallama Aunty amarya ta ajiye wayar ta miƙe sai murna take ta nufi waje

    Washe gari

    Amrat che kwanche saman katafaren gadon yaya Fahad sai juyi take tana murkusoso ta dafe chikin ta da hannu ɗaya wasu siraran hawaye masu ɗumin gaske ne suke bin gefe da gefen kumatun ta Takai Almost 11mins a awan nan yanayin

    Turo kofar toilet Fahad yayi ya fito ɗaure da towel fari tas mai laushi da kyau a ƙugun sa gashin kansa sai ɗigar da ruwa yake alamar wanka yayi, gaban mirrow ya nufa batare da ya kalli in da Amrat take ba yace “ke jeki fitarmin da kayan set ɗaya” shiru shiru Amrat bata amsa ba dan bazata iya magana ba jin kuka kasa kasa ne yasa Fahad ya ɗan waigo ganin halin da take chiki ne yasa shi ajiye perfume dake hannu sa da sauri ya karisa gaban gadon yana faɗin “ke lfy kike kuwa? Ganin ta kasa amsa masa ne yasa ya haye kan gado tare da sa hannu ya riko hannun ta dake dafe da chikin nata chikin sanyin murya yace “chikin kine ke miki chiwo? Shiru Amrat bata amsa ba, addu’a ya fara karan to mata kamar haka “*ya hayyu ya kayyumu bi rahmatika astagisu aslili shanin kullahu wala takil illa nafsi ɗar fata ain wa laila ahdin ninan nas* yana kai karshen Addu’ar ya tofa a hannun sa chikin nitsuwa ya kai hannun nasa kan maran ta da nufin ya shafa mata addu’a wani irin shock yaji lokachin da hannu sa ya taɓa lallau san fatar marar ta, da sauri ya zame hannun sa yana kallon face nata, ba ƙaramin kyau ta masa ba mu samman idan chikin nata ya murɗa yadda take tsuke bakin nata ba karamin kyau hakan yake masa ba ya shagala da kallon ta sai gani yayi tayi wani miƙa sai kuma ta saki ji ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nepa
    Chiki sauri yasa hannu yana ɗan shafa kumatun ta yana kiran sunan ta “Amrat Amrat” shiru bata ko motsi hannun sa ya ɗora saman kirjin ta, da sauri ya ɗauke hannun nasa ganin alamar suma tayi ne yasa ya kwanto da kan sa dai dai fuskar ta a hankali ya ɗan girgiza kan nashi ruwan da ya wanke gashin kan nashi ya zuba mata a fuska kamar yayyafi dogon numfashi taja tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya Slowly ta buɗe idon ta a kan face nashi domin kuwa fiskar sa na dai dai sai tin tata fiskar ya zuba mata ido yana kallon irin kyawun halittar da Allah ya mata

    Da sauri ta mai da idon ta ta rufe kasa kasa yace “chikin naki ya dai na chiwo ko? Da kyar ta iya buɗe ɗan ƙaramin bakin ta chike da shagoɓa tace “Allah yaya Fahad bai dai na ba yana min amma ya rage ba.. ba ta kai karshen maganar ba sai jin fuskar sa tayi akan nata ya haɗe fuskokin su waje guda yana kallon idon ta dake rintse wani irin yana yake ji yana shigar sa wadda shi kansa ba zai iya misilta wani irin yana yi yake chiki ba, chikin dashewar murya yace “in baki magani ne? Batare da ta buɗe ido ba chikin sauri tace “Eh yaya Fahad dan Allah ka bani nasha ko Allah zai sa chiki na ya dai na chiwo “kin shirya an san maganin nan kuwa? “Eh yaya Fahad wlh na shirya “to idan dai kin shirya buɗe idon ki dan maganin baa bawa mai rufeffen ido” tun bai kai karshen maganar ba ta waro idon ta chikin nashi, murmushin gefen fuska ya saki tare da matso da bakin sa dai dai kan tata har bakin nasu na gogan na juna wani irin yana yake ji ji yake gaba ɗaya tsikar jikin sa na tashi kasa kasa yace “ashe da gaske kina son ganin first shikarun ki nawa yanzu “13 years nake yanzu ta bashi amsa tana mai da kallon ta kan ɗan karamin red lips nashi

    “To kallon me kuma kike wa lips na ko dai ya miki kyau ne? Chikin sauri ta kawar da idon ta gashi ba halin ta rufe ido kar yache ba zai bata magani ba “eh mana yaya Fahad bakin ka na da kyau sosai” murmushi gefen fuska ya saki kafin yace “to in baki ne? “Eh yaya Fahad idan zamuyi chanji ina son wlh kabani naka in baka nawa” bata gama rufe baki ba ya haɗe bakin su waje guda a hankali yake kissing lip nata na kasa mutuwar kwan che Amrat tayi gaba ɗaya jin wani sabon yanayi tayi ji take kamar ba ita ba runtse ido tayi ta kame jikin ta waje guda

    Fahad kuwa jin sa yake a sabuwar suniya sai wani numfashi yake fitar wa da kyar da kyar

    Almost 10mins yaya Fahad na kissing ɗin amaryar sa a hankali ya zame bakin sa daga nata yana kallon face nata da sauri ya yunkura zai mike sai kuma ya dawo a sukwane sakama kon towel dake jikin sa ya kwanche, rumfa ya mata da faffaɗar kirji sa da kyar ya iya buɗe baki ya fara magana muryan sa har sarkewa yake “girma ne yazo miki kuma gashi na kin ɓatamin bet shit, ki rufe idon ki idan na shiga dressing room sai ki tashi ki shiga toilet ki gyara jikin ki ki dawo ki chire bet shit ɗin ki shin fiɗa wani kinji ko? Kai ta gyaɗa masa tare da chewa “to”

    A hankali ya yunkura tare da chafko towel nashi da sauri ya karisa miƙewa ya nufi dressing room nashi

    After 15mins

    Amrat ta fito daga toilet ɗaure da towel a kirjin ta wadda ya sauko har guiwar ta kamar zatayi kuka ta kariso tsakiyar ɗakin zaune a bakin gado ta samesa yana latsa waya jin fitowar ta ne yasa ya ɗago ido yana kallon ta

    “Lfy Amrat na gan ki a birkiche haka? “Yaya Fahad wlh jini na gani a jikina kuma na wanke amma ya sake fitowa” kallon ta Fahad ya shigayi from head to toe ya fahimci Amrat bata san komai ba dan haka sai ya ajiye wayar sa a saman drawer ya miƙe ya nufi in da su Aunty farida suka shiryawa amrat ɗin kayan ta walldrop ɗin ya buɗe ya zaro pant ɗaya daga chikin san nan ya buɗe ɗayan ɓangaren ya shiga dubawa sosai ya wasa kayan dake chiki gaba ɗaya chan kasan kayan ya ga Always a jere, ɗauko leda ɗaya yayi ya koma bakin gadon sa ya zauna ajiye pant ɗin yayi a gefe san nan ya buɗe ledar Always ɗin ya zaro ɗaya ya sanya mata a chikin pant ɗin ya mika mata tare da faɗin “ansa kije kisa sai kizo na koyamiki yadda akeyi lokachin period” ganin hakan yasa ta fahimci abun da yaya Fahad ke nufi sai ta sunkuyar da kai kasa saboda kunya tama kasa ko motsawa daga wajen

    Ganin haka yasa Fahad ya miƙe ya nufeta hannu yasa ya ɗago haɓarta runtse ido tayi tana tsuke baki, bai san san da ya saki wani cool murmushi ba “kunyata kike jine? Shiru tayi bata che masa ko mai ba sakin haɓar tata yayi ya kama hannun ta ya sanya mata pant ɗin a chiki tare da shafa fuskan ta da ɗayan hannun sa yana faɗin “to amma kunyar taki zai barki ki iya shiga toilet ɗin ko? Ko dai shima toilet ɗin sai na kai ki da kai na”? Jin hakan yasa Amrat ta kwasa da gudu ta koma chikin toilet ɗin yar dariya yaya Fahad yayi wadda yasa wushiryar dake tsakanin fararen hakoran sa na gaba ta bayyana

    Juyawa yayi ya koma gaban gadon ya sa hannu ya yaye bet shit ɗin dake shinfiɗe a gadon ya nufi wajen ajiye kayan wanki ya ajiye san nan ya ɗauko wani bet shit ɗin ya shinfiɗa ya haye gadon ya kwanta tare da jawo wayarsa ya cigaba da latsawa

    Masu karatu sai mun hadu gobe idan mai dukka ya kaimu

     

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    *💫STAR LADY💫*4

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 13

    Book 2

    *Episode 13*

    …….sai 6pm Hiyana ta lallaɓa ta zagayo ta koma chikin gida a babban palon kasa tachi karo da yaya khalid, zai koma part nasu, sugunnawa tayi har kasa “yaya khalid ina wuni” “me ya fitar dake waje sister? Shiru ta ɗanyi tana tubanin abun da ya dace ta faɗa masa “Bgs ne ya miki wani abun ko? Dan naga hawaye a face naki” Chikin sauri ta girgiza kai tana faɗin “aa yaya Khalid ba shi bane” kallon ta khalid yay fara yi from head to toe, kawar da kai gefe yayi chike da bakin chiki yace “ok jeki yi wanka ki chanza kaya kizo part nawa ki sameni kuma kizomin da wayar ki” sai lokachin ta tuna ashe tana da waya, jiki ba kwari ta mike ta haye sama, tana tafiya tana tunani, wai shi yaya prince ai na ya keson na sa rai nane ya kashe ni ma ya huta kawai na gaji nagaji sa irin azabtar dani da yake wayyo Allah dan isar ka ya Allah ka kawomin ɗauki, da wannan tunanin ta shiga palon su, zaune saman sofa mai zaman mutun 3 ta samu Fahad yana sanye da jallabiya fara yana latse latse a waya, tsugunnawa tayi har kasa “yaya Fahad ina wuni” sai lokachin ya ɗago ido kallo ɗaya ya mata ya kauda kan shi gefe chike da bachin rai ya mike har wani huchi yake kamar wani zaki ya nufi betroom na Bgs batare da yache da ita komai ba.

    kwanche saman gadon ya same’sa idon sa a lumshe, kallo ɗaya Fahad ya masa ya gane bai yi barchin ba, chike da fushi ya fara magana “yaya prince ka dubi girman Allah ka tausayawa sister wai dan Allah me ta maka ne da har ka tsaneta haka pls ko dan farincikin Ammi da Abba ka rinƙa tausayin sister, ina kakeson yarinyar nan ta sa ranta dan Allah dai, ko so kake watarana zuchiyar ta ta buga ne? ba ni kakewa ba amma duk sanda kayi mata wani abun jinake zuchiyara kamar zafa fashe, ji nake kamar zan mutu, nasan kana son mu baka son ɓachin ran mu kana kauchewa duk abun da zai samu bachin rai, to kasani fa wlh idan kayiwa sister wani abun gaba ɗayan mu ji muke kamar zamu mutu dan ɓachin rai, mu muna sonta muna kaunar ta, munason farinchikin ta kamar yadda mukeson na Auta, karka manta fa wlh ina da tabbacin Ammi tafi son Hiyana sama da yadda take son Auta, wlh ko dan Ammi dole naso yan uwana, lokachin da aka aura min Amrat ban son ta amma dana fahimchi yaran nan sune farincikin Ammi, sai na hakura na rungumi matata Allah da ikon sa kuma chikin ƙanƙanin lokachi ya dasamin son ta a rai na, dan Allah yaya prince ka bawa sister kulawa ko dan Ammi, da Abba ina da tabbacin hakanne kawai burin da ya rage musu a rayuwa pls yaya prince ba dan kowa ba dan Allah.

    Ba tare da ya bude ido ba yawa Fahad alama da hannu akan yazo, ba musu yaje ya zauna a gefen sa
    Wani wawan mari ya sakar wa Fahad ɗin a kumatu tare da mikewa zaune ya wato idon sa waje, chike da ɓachin rai ya fara magana “kayi girman da zakazo ka tsaya a kai na kanamin magana haka ko? Chikin sanyin murya da danasanin Fahad yace “kayi hakuri yaya prince bachin rai ne yasa hakan amma am so so sorry ba zan sake ba” shiru Bgs yayi bai sake magana ba “yaya prince dan Allah ina neman wata alfarma” zuba masa ido kawai Bgs yayi batare da yayi Magana ba, “dan Allah yaya prince kabar sister ta dawo ɗakin ka wlh ban son ganin ta a palon nan kuma kaga tana da tsoro sosai” shiru yayi na tsawon 2mins kafin yace “me ya samu ɗakin na ta? Da sauri Fahad ya kara juyowa da kyau yana fuskantar shi dan jin yadda Bgs ɗin yayi magana chikin sanyi murya da alama zasuyi nasara “yaya prince ai ton lokachin da ta kalli snake a ɗakin take tsoron shiga” zuro dogayen kafofin sa kasan fadon yayi ya miƙe batare da yace da Fahad komai ba ya nufi wajen hutawan sa dake chikin ɗakin, shiru Fahad yayi yana addu’a a chikin zuchiyar sa Allah ya ɗora su a kan Bgs Allah ya sa ya yarda hiyana ta dawo ɗakin sa, Almost 30mins yana zaune daga ƙarshe dai ya mike ya fice daga ɗakin chike da sa ran zasu iya yin nasara awan nan karon dan, yadda yaji yaya prince yayi magana a hankali.

    Zaune saman sofa a palo ya samu hiyana ta takure waje guda da alama sanyi takeji, “sister tashi kije ɗakin ki ki chanza kaya” chikin rawar murya tace “yaya Fahad wlh tsoron ɗakin nake ji bazan iya shiga ba” shiru yaɗan yi kafin yace “ok ɗauki kayan naki muje na rakaki part ɗin yaya Aiman sai kiyi wanka a chan ki chanza kaya” ba musu ta mike ta ɗauko wasu riga da sket masu shegen kyau black colour, ta nufoshi gaba yayi ta bishi a baya, har part na Aiman.

    Zama Fahad yayi saman sofa a palo san nan yayiwa Hiyana nuni da betroom din yace taje tayi wanka yana jiranta a nan, dan ya lura tsoron part ɗin take.

    Jikinta sai kerma yake ta shiga betroom ɗin Aiman wani makeken hoton’sa ta fara chin karo da shi a gefen gado yana sanye da jeans da t-shirt ya ɗaura rigan aikin sa a sama kayan yana ɗan murmushi, ganin hoton Aiman ba karamin tayarwa Hiyana hankali yayi ba, nan take hawaye suka fara zarya akan fuskanta, tana kuka tana bin ɗakin da kallo karaf idon ta ya sauka kan wani makeken Frame mai kyau gaske wadda ke ɗauke da hoton Bgs yana tsaye da kakin sojoji ya rike Ak47 a hannun sa, ba karamin kyau yayi ba fiskar nan tashi kamar kullun babu alamar annuri ko kaɗan,kurawa hoton ido tayi tana ta kallon sa tana goge hawaye ta, 15mins ta ɗauka tana kallon hoton kafin ta wuche ta nufi toilet a gurguje tayi wanka ta fito, shiryawa tayi chikin riga da sket din ta nufi gaban mirrow ta tsaya tana kallon kanta

    Ba karamin kyau kayan suka mataba sun fito mata da ainihin suran jikin ta,

    kai kallon ta tayi kan kirjin ta gaba ɗaya rabin boobs nata awaje kasan chewar wuyar rigan babban ne sosai gashi kayan sun manne da jikin ta sun matse ta sosai, tsaki ta ja ta sanya hannu ta tara kyakkyawar lallausan bakin gashin kan ta a tsakiya ta daure ta kitse bindin gashin ta watsa shi baya wadda ya kai har karshen bayan ta, kunyan fita hakan take ji gashi hijabin Amrat ya jike kuma yayi datti sosai, shiru ta tsaya a ɗakin almost 10 mins tana tunanin yadda zata fita da kayan nan a hakan ma wai ta zaɓo kayan masu ɗan fasali kenan, data ga dai tsayuwa ba zai tsinana mata komai ba sai ta, dauki kayan ta da ta chire ta kare kirjin ta dasu ta kama hanyan fita tana tafiya gaba ɗaya a takure take har ta fito palon

    Yadda ta bar Fahad haka ta fito ta same’sa yana zaune yana latsa waya, jin Sallamar tane yasa ya ɗago kai kallo ɗaya ya mata ya kau da kai tare da mikewa yayi gaba yana faɗin “to muje” bayan sa tabi hannun ta rike da kayan da ta chire ta kare kirjin ta dasu, part nasu suka koma.

    Yana shiga palo ya wuche betroom na su ita kuma hiyana ta zauna saman sofa, ta kame jikin ta waje guda, dan ji take kamar babu kaya ajikin ta a haka har barchi ya fara ɗaukan ta gyarawa tayi ta kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba da ita

    KHALID

    wunin yau gaba ɗaya Zahra ta wuni ne tana kuka khalid yayi rarrashi har ya gaji taki yin shiru taki chin komai tun safe ga zazzaɓi da ya rufe ta, Sosai Khalid ya shiga damuwa, ya rasa meke masa daɗi
    ……..zaune yake gefen gado yayi tagumi ya rasa meke masa daɗi, Zahra na kwanche saman gadon tana kuka kasa kasa, chikin shesshekar kuka tace “yaya Khalid” chikin sauri ya juyo tare da haurawa saman gadon ya karisa in da take, hannun ta ya kama chikin nashi murya kasa kasa Kamar mai raɗa yace “am sorry my wife kiyi hakuri kinji? Chikin dashewar murya tace “yaya Khalid ka dai na damuwa kaji bana son ganin ka kayi shiru kana tunanin nan” “my wife in dai baki dai na kukan nan ba baki chi abinchi ba, ba zan dai na damuwa ba” “to yaya khalid kamin tausa dan ko ina chiwo yake min idan na samu sauki zan chi abinchin kaji? Chikin sauri ya fara yimata tausa yana faɗin “yanzu nan ma ina gama yimiki tausan nan zaki samu sauki sai na baki abinchi da kai na ko? Kakalo murmushi dole Zahra tayi ga hawaye na bin gefe da gefen fuskar ta tace “to amma iya tea kawai zan sha” “ok to ko tea din ma yayi bari na kawo miki” batare da ya jira amsar taba ya sauko daga gadon ya nufi, waje.

    Jim kaɗan ya shigo hannun sa ɗauke da kyakkyawar cup, mai ɗauke da tea mai zafi gefen gadon ya zauna tare da ajiye cup ɗin a saman drawer gefen gadon, hannu yasa ya ɗago ta ya ɗaurata kan chin yar sa, ya ɗauki tea ɗin ya fara bata a baki, a hankali hankali take dan sha har ta shanye “in karo miki wani ne? “Aa yaya Khalid ya isa haka wannan ma da kyar fa na shanye” batare da ya sake magana ba ya ajiye cup ɗin a saman drawer, san nan ya miƙe tare da ita a jikin sa suka haura saman gadon.

    Kwanchiya yayi, tana manne a kirjin’sa, a hankali yake shafa bayan ta yana mata raɗa a kunne tun Zahra na share sa har ta fara biye masa suka chigaba da zubawa juna kalaman love.

    Maiduguri Nigeria

    Ahzan ne zaune saman karfet a betroom din mum ɗin sa yayin da mum ke saman gado suna hira
    “Ahzan kana ganin hakan shine dai dai? “Eh mum ya kamata mu taimaka mata” “amma Ahzan abun ne da ban mamaki anya Dr walid bai yi kuskure ya baka result na wata ba, a mai makon na Ummi dan ni dai ban ga alamar Ummi na bukatar aure ba” “mum baki ji Dr yace yanzu ne abun ya fara kamata ba idan ta kara 1 week ba tare da an mata aure ba, shine abun zai bayyana karara kuma kinga idan hakan ta faru ba zanji daɗi ba” “Ahzan Hanan fa zata girmi Ummi sosai dan yadda nake ganin Ummi ba zata wuchi 16 years ba kawai tana da wadatatchen halittace, ni anawa ganin idan ma hakane to chiwon hanan ya kamata ya fara kamawa ba Ummi ba” “mum kowa da kike gani a duniyar nan da irin tasa kaddarar, ai wanna chiwon bai bi ta shekaru ba” “hakanne Ahzan kana da gaskiya to shikenan zanyiwa dadyn ka salim magana” “to mum amma fa karki sanar da kowa batun chiwon nata dan kar su fara magana akai” “ai wannan abun kunya ne baki ba zai iya faɗi ba” “yauwa my mum san nan kinji Dr yace kar a wuche 1 week baa mata Aure ba idan aka wuche za’a samu matsala, ba ƙaramin tausayi yarinyar ta bani ba shi yasa ma na yanke shawarar Auren ta kawai, dan in shere mata hawayen rashin iyaye” “In Sha Allah zaka samu ladan hakan” “Allah yasa my mum, amma mum yana ga baki shirya zuwa wajen aiki ba jiyama fa baki jeba lfy” “wlh Ahzan gaba ɗaya jikina a mache ne bana iya komai sai kwanchiya kawai” shiru Ahzan yayi yana tunani a ranshi “kai gaskiya maganin na aiki da kyau am sorry mum ba zaki iya komai ba kwakwalwan ki ma bazata yi aiki ba bare kiche babu irin wan nan chiwo a duniya, dole sai abun da na tsara miki shi zaki yi, bazaki iya fita ko nan da tsakar gida ba har sai an ɗaura Aure na da Ummi dan karki bata min shiri nasan kina fita zaki samu lbr ana neman Ummi dan haka babu in da zakije sai bayan Aure, shima dady salim yanzu zanje nayi maganin sa dan idan yazo kawai ya amince da zanchen Aure na da Ummi, babu wan da zai zo gidan nan da sunan yazo biki salon suga Ummi, su tonamin asiri Auren sirri za’ayi
    “Ahzan tunanin me kake? Da sauri ya dago kai tare da mikewa ya nufi hanyar fita daga ɗakin yana faɗin “babu wani tunanin da nake mum ina tausayin yarinyar ne kawai” ya kai karshen maganar tare da ficewa daga ɗakin, gyara kwanchiyar ta mum tayi a saman gadon ta ta lumshe ido ta chigaba da barchinta da ta fara.

    KANO

    da sallama ɗauke a bakin sa Aryan ya shigo fada, kallo ɗaya Abba dake zaune kan kujerar sarauta ya masa ya kau da kansa gefe dan bai san ganin Aryan a chikin wannan hali kwata kwata, saman kujerar kusa da Abba yaje ya zauna “Aryan yaushe ka dawo? “Yanzu na dawo Abba” “to ya ake chiki Allah dai yasa diyanar ce” “aa Abba ba ita bace, wadda suke magana a kanta wai mahaukachiya che wani ya buge da mota to kaga ita kuma ai ba mahaukachiya bace shiyasa ban ma bi ta kan maganar tasu ba ina jin hakan nayi dawowata kawai” “eh lallai Aryan na yarda kana chikin matsananchin tashin hankali wadda yasa baka iya tantanche abubuwa” juyowa Aryan yayi da kyau yana kallon abba kafin yace “Abba me yasa kace haka? “Eh mana Aryan idan ba kana chikin tashin hankali ba, ai da ka daɗe da gano in da diyana take” da sauri Aryan ya kara waro idon sa waje yana kallon Abba “ta yaya kenan Abba kamin bayani” “lokachin da farida ta kira tana sanar mana da diyana ta bata kai kayi picking call din amma tashin hankali ya hanaka kaji bayanin da farida tayi kafin ɓatar diyanar” “Abba pls tell me wani bayani kuma tayi!? “Chemaka tayi diyana ta tafi babu ɗankwali babu mayafi babu ta kalma ta bar wajen, to kaga bazaka nemi diyana a chikin masu hankali ba sai dai a dubata a sawun marasa hankali, idan kayi tunani mai yuwuwa wayan chan mutanen suna da gaskiya domin babu yadda za’ayi suga hoton diyana su che itache kai kuma ka che ba ita bace ko da blue eyes nata zaka iya ganeta chikin sauki kawai dan ayanzu baka da nitsuwa ne, shiyasa Amma abun da nake so da kai yanzu ka tattara nitsuwar ka waje guda, ka dawo asalin Kga da na sani kayi aiki da kwakwalwan ka dan samun nasara ina taya ka da addu’a tare da fatan awanan karon kayi nasara”

    a sukwane Aryan ya miƙe ba tare da ya sake magana ba ya nufi hanyar fita fada, taku yake da sauri sauri, wayar sa ya chiro, ya kunna hasken screen ɗin ya duba time 7pm contact ya shiga sauri sauri ya fara kiran layin Shahram, kira ɗaya Shahram ya ɗaga chike sauri da bada umarni Aryan yace “ka sanar da commissioner ya rikemin wayan nan mutanen, san nan ka shiryamin tafiya gobe karfe 7 ina son tai mana a Maiduguri” yana gama faɗin hakan batare da ya jira amsar Shahram ba ya katse kiran part na Ammi ya nufa

    Da sallama a bakin sa ya shiga betroom na Ammi zaune take saman Throw pillow tana shan fura ganin shi yasa ta ajiye furar a gefe chike da kulawa ta amsa masa sallamar tare da tambayar yaushe ya dawo, sauri sauri yace mata “yanzu” Ammi zata sake magana ya rigata da chewa “Ammi ina son ganin drowar sa kayan yarinyar nan “diyana? Ammi ta tambaya tana kallon sa sosai “Eh ita inane wajen sa kayan ta yake? “Yana ɗakin su kayan na chan yadda suka bari ba a taɓa ba” tun Ammi bata karisa maganar ba ya juya ya fice ya nufi ɗakin su Hiyana, jakar da ya bawa diyana lokachin da ya dawo saudia ya ɗauka ya fice daga ɗakin, kai tsaye Part nashi ya koma

    Yana shiga betroom nashi ya ajiye jakar saman mirrow ya nufi toilet dan yin wanka

    Uk

    8pm dai dai hiyana ta fito part nasu ta nufi kitchen already jourfree ya gama shirya abinchin Bgs dauka kawai tayi ta komo part nasu gaba ɗaya a takure take dan ji take kamar tsirara take tafiya kayan sun kamata sosai, da sallama ta shiga betroom ɗin yana zaune saman sofa yana waya da wajen aikin su ga dukkan alamu magana yake akan sojojin su da yan ta adda suka kama yana chikin bachin rai sosai, saman table dake gaban sa ta ajiye masa abinchi chikin sauri ta juya zata fita dan kar ya ganta ba hijabi muryan sane ta katse ta yace “ke zonan!? Chikin sauri ta dawo ta tsugunna a gaban sa ta sunkuyar da kai kasa dan kunyar kayan jikin ta takeji, alama ya mata da hannu akan tayi sarving nashi, da mamaki ta ɗago tana kallon sa, taga bama ita yaƙe kallo ba, chikin sauri ta ɗauko plate ta fara zuba masa abinchin tana gama zubawa bata lura da hannun sa dake saman hannun kujerar ba ta ɗora plate din awajen saman hannun nashi, wani wawan mari ya sakar mata, tare da binta da harara chikin tsawa yace “get out” da gudu ta miƙe ta fice daga ɗakin tana kuka, katse wayar da yake yayi ya ajiye wayar a gefe, chike da ɓachin rai ya miƙe ya fice daga ɗakin ya nufi waje, Hiyana na ganin fitar sa ta dawo ɗakin ta kwashe kayan abinci gaba ɗaya ta mai da kitchen tana dana sanin abun da tayi yau itache rana ta farko da yaya prince zai fara chin abun da ya fito daga hannun ta amma gashi saboda zumuɗi ta bata hakan, dawowa tayi saman doguwar kujera ta kwanta ta lumshe ido tana tunani har barchi yayi awawon gaba da ita

    12:30Am

    Bgs ya dawo chikin gidan kai tsaye part nasu ya nufa, dai dai zai shiga betroom nashi yaji mutun na numfashi da kyar da kyar kamar wadda aka shake, gashi palon akoi duhu wutan a kashe yake, kunna wutar wayar sa yayi haske ya gauraye wajen, juyawa yayi ya nufi in da take kwanche ta takure waje guda, sai rawan sanyi take, a hankali ya kai hannun sa saman wuyar ta jikin nata yayi zafi sosai kamar wuta hannu ɗaya yasa ya dauke ta chak, ya nufi betroom nashi da ita

    Jin mutun ya dauke tane yasa ta waro manya manyan blue eyes nata da kyar dishi dishi ta fara gani ta kasa gane wanene ya dauke ta kokarin kwache kanta take ta fara fisge fisge da iya karfinta, chike da jin haushin hakan ya…..

     

    Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu🤪🤪

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 8

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 8

    Book 2

    *Episode 8*

    …….After some minutes Yusuf ya ɗago kai a razane ya miƙe ganin halin za lamrat ke chiki, chike da tashin hankali da danasani ya kariso wajenta “subhanallah shine abun da ya furta lokachin da idon sa ya sauka akan aika aikan daya aikata yayi dana sani sosai, ya ruɗe ya rasa ta ina zai fara taɓa ta tunani ya shigayi gashi gaba ɗaya likitoci dake dubasu maza ne kai shi ko mace ba zai iya bari taga jikin matar shiba bare namiji yanzu ne ya kara jin zafin rasuwar Aiman, da yanzu Aiman na nan sai yaje ya tambayoshi abun da ya dace ya mata, yaya Aryan shine mai ɗan saukin kai shima baya nan ko kwaya ya sha bai isa ya tinkari Bgs da maganar nan ba, ya shiga matsanan chin tashin hankali da danasani ko dai na sanar da yaya Khalid girgiza kai ya shigayi yana faɗin “No No” ba zan iya sanar da kowaba” chan kuma wata dabara ta faɗo masa chikin sauri ya diro daga kan gado ya ɗauki short na shi ya mai da jikin sa ya fara laluɓar wayar sa chan gefe ta karshen gadon ya hango wayar, chikin sauri ya ɗauko tare da kunna hasken screen ya duba time karfe 11pm contact nashi ya shiga kan number Aunty farida ya danna kira, wayar tayi ringing har ta katse baa ɗaga ba, sake kira yayi sai a karo na uku Aunty farida ta ɗaga da murya irin na mai barchi tace “Hello Yusuf” shiru ya ɗanyi yana tunanin ta yadda zai fara sanar da Aunty farida aika aikan da yayi “yaya Yusuf bakaji nane? “Aa Aunty farida ina jinki Ykk? “Lfy lau ya London? Ya Amarya Lamrat? “Uk Alhadulillah” “lfy kakirani a wan nan daren? “Eh Aunty babba lfy ba lfy ba” chikin sauri Aunty Farida ta miƙe zaune tana faɗin “subhanallah ba lfy ba kuma to me yake faruwa baka da lfy ne? Ko dai Lamrat che bata da lfy? Ko kuma sauran yan uwan namu dan yanzu prince yayi block nawa bana samun sa awaya” “Aunty farida ki kwantar da hankalin ki mana irin wan nan jero tambayoyi haka dukkan mu muna chikin koshin lfy daman” sai kuma yayi shiru ya kasa karisawa “dama me Yusuf? Kayi magana mana ko so kake ka bugamin zuchiyata ne haba mana” “no Aunty farida ki bari zan rubuta miki tex kawai” batare daya jira amsar taba ya katse kiran chikin sauri ya shiga rubuta mata massage, yana gamawa ya tura mata ba afi 2mins ba sai ga kiran ta ya shigo wayar sa,ji yayi kamar kar ya ɗau call ɗin saboda kunya amma ba yadda zai yi dole ya ɗauka dan ga Lamrat nata zubar da jini, jiki ba kwari chike da jin kunya yayi picking tare da manna wayar a kunnen sa

    “Kana jina Yusuf yanzu kasa ruwa mai zafi wadda hannu zai iya shiga chiki sai ka mata wanka ka gasa mata jini amma ka zuba detol a chikin ruwa san nan ba sau ɗaya ba idan ruwan ya ɗan yi sanyi sai ka sauya mata wani mai zafin, zai taimaka mata sosai amma ya zama dole ka kaita asibiti domin kaga lamrat karaman yarinya ce tayu ka jimata chiwo tun da ba waje ɗaya muke ba bare nazo da kaina yanzu kayi mata wanka sai ka shirya ta kuje hospital” tun Aunty farida bata karisa magana ba ya katse kiran chikin sauri ya shiga Toilet ya haɗa mata ruwa mai zafi tsabar ruɗewa yama manta Aunty farida tace ruwan da hannu zai iya tsayawa

    Dawowa chikin ɗakin yayi ya ɗauki Lamrat chak kamar yar baby ya koma chikin toilet ɗin da ita, chikin baf ɗin wanka ya sanya ta, da sauri ta damke hannun sa dan zafin da ruwan yayi masa, wani irin ihu azaba ta saki tare da kankame hannun sa da karfi, kawar da kansa gefe yayi dan bai san ganin tashin hankali dake kan face nata, sosai lamrat ke masa kuka, jin kukan nata yake har chikin ranshi amma ba yadda zai yi dole ya nema mata lfy, sau uku yana chanza mata ruwa kafin nan ya mata wanka sarki ya saɓota a kafaɗar sa sudawo chikin ɗakin saman sofa mai zaman mutun 3 ya kwnatar da ita yaje ya ɗauko bargo ya rufe ta saboda rawan sanyi da take, komawa yayi wajen gadon gaba ɗaya ya kwashe gayan dake kan gadon, kama daga bargon bet shirt fillows gaba ɗaya ya kwashe su ya kai wajen ajiye kayan wanki ya dawo ya shiga dressing room ya ɗauko wani set na bet shirt da blanket, yazo ya shinfiɗa da kansa, ya koma ya ɗauko ta ya dawo da ita kan gadon sai kuka take, a hankali hankali idan ba ka kasa kunne sosai ba bazakaji kukan nata ba dan voice nata baya fita sosai, shiru yayi yana tunani wani kaya ya kamata ya sa mata dan bata da kaya ko set ɗaya a gidan nan basu ɗauki komai ba sai da safe daman zasuje shopping su saya musu kayan sawa, komawa chikin dressing room ɗin yayi jim kaɗan ya fito rike da jallabiyar sa a hannun, hayewa gadon yayi ya ɗagota ya zura mata jallabiyar tallaɓota yayi da kyau a kirjin sa chike da so da kauna ga wani mugun tausayin ta da ya dira masa a rai kasa kasa ya fara “my baby am so so sorry pls ki dai na kukan nan kinji idan kinayi har chikin raina nakeji pls kiyi shiru kada kanki yayi chiwo kinji? Ko kallo in da yake lamrat batayi ba ta chigaba da kukan ta mai tsuma zuchiya, dafe kai yayi yana kara dana sanin abun da ya kai kata mata, wayar sa ya ɗauko yana kokarin kiran yaya Aryan, sai ga kiran Khalid ya shigo, kwantar da lamrat yayi ya miƙe ya koma gefe dan kar Khalid ya ji kukan lamrat, picking call ɗin yayi tare manna wayar a kunnensa ya fice daga ɗakin ya koma Palo “Hello yaya Khalid” daga ɗaya ɓangaren Khalid yace “Yusuf ka fito muci Abinci mana tun ɗazun muke jiran ka “No yaya Khalid kuchi kawai ni bana jin chin abinchi gaskiya” yana gama faɗin hakan ya katse ba tare da ya jira amsar Khalid ba dan baya son ya jefo masa wata tambayar da ba zai iya amsawa ba.

    layin yaya Aryan ya fara kira, kira ɗaya Aryan ya ɗaga, chikin dashewar murya yace “Yusuf kun sauka lfy? “lfy lau yaya Aryan ya karfin jiki? “Alhamdulliah” “yauwa yaya Aryan pls alluran barchi nake son yiwa Lamrat” “akan wani dalili zaka mata Alluran barchi” shiru yayi yama rasa amsar da zai bawa yaya Aryan “Yusuf kana jina koma me dalilinka kasani dai alluran barci yana da illa ba kasafai akewa mutun ba sai idan ya zama dole, ka rabu da yar mutane karka sa mata wani chuta “to yaya Aryan wani magani ya kamata na bata domin ni gaskiya bana son kai ta asibiti kasan yadda tsarin kasar nan yake basu da Addini sosai” shiru yaya Aryan yayi yana nazari kuma yana son ya gano dalilin Yusuf na neman magani dan shima bai son tambayar Yusuf ɗin tun da yaga sai wani kauche masa Yusuf ɗin yake alamar bai son asan meke damun matar tashi, amma dole dai ɗayan biyu ne ko dai ta fara period ko kuma, yau ta karɓi bakonchin Yusuf “yaya Aryan ya kayi shirune? “Yusuf matar taka ta fara period ne? “Aa yaya Aryan ba period bane fa kawai” sai kuma yayi shiru, murmushi gefen fuska yaya Aryan ya saki dan ya gano me Yusuf ke ɓoyewa “zan tura maka message ɗin drugs da ya dache ka bata” “ok kawai Yusuf yace tare da katse kiran ya koma chikin ɗaki.

    Gaba ɗaya sun haɗu a babban palon kasa domin chin abinci ban da Yusuf da Lamrat sai Bgs da baya nan shima, abinchi suke chi chikin kwanchiyar hankali chike da tausayi da tunanin me zai biyo baya Khalid ya dubi Hiyana ya fara magana “sister tashi kije ki kaiwa yaya prince abin chin sa ko” kallon Khalid yaya Ahmad yayi ya buɗe baki zai yi magana, cikin sauri Khalid ya ɗaga masa hannu yana girgiza kai yace “bana bukatar maganar kowa wan nan umarnin Abba ne dan haka dole abi ko ana so ko baa so” jin haka yasa yaya Ahmad yayi shiru ita kuma Hiyana ta mike jiki ba kwari ta nufi kichin nasu, already jourfree mai Aikin su ya gama shirya abin chin yaya prince a chiki wani haɗaɗɗen katowar trey da kyar hiyana ta iya ɗaukan trey ɗin ta fito ta nufi ɗakin nashi, tafiya take Kamar wadda kwai ya fashewa a chiki

    Da sallama ɗauke a bakin ta tashiga ɗakin nashi yana kwanche saman katafaren gadon sa yana latsa waya daga shi sai short wannan haɗaɗɗiyar suran jikin nashi dake rikita mata da maza awaje lallausan bakin gashin kan nan nashi ya kwanto masa har kan fuska, kasan chewar bai ɗaure ba kuma gashin na da tsawo sosai dan zai iya kai kusan tsakiyar bayan sa, ɗamtsen hannun san nan kuwa kamar zasu fashe saboda karfi da samun horo mai kyau baki lallausan gashin dake kwance saman faffadar kirjin san nan kuwa sai kyalli yake, ga wani gashi mai tsantsi da taushi kwanche a chinyoyin sa har zuwa yatsun kafar sa haka ta sama ma gaba ɗaya hannun sa baki lallausan gashin me mai kyau da sheki ne kwanche awajen har kan yatsun sa na hannu,

    saman table dake tsakiyar ɗakin Hiyana ta ajiye trey ɗin, ta karisa Wajen gadon ta sugunna tare da sunkuyar da kai kasa, murya na rawa tace ” yaya prince ina wuni” shiru bai amsa ba ko kallon in da take bai yiba latsa wayar sa kawai yake “yaya prince ga abin chin ka chan na kawo maka”shiru kamar bai san da shigowar mutun a ɗakin ba, jiki ba kwari hiyana ta miƙe ta fice daga ɗakin, tana fita wani kukan bakin chiki ne ya zo mata da gudu ta wuche ɗakin ta tafaɗa kan gado ta fara rera kukan ta, chikin kuka take faɗin “ni me nayiwa yaya prince yamin irin wan nan tsana haka sai kache ba musulmi ba ya Allah idan yaya prince ne alkhairin a gareni Allah ka kawomin mafita ta yadda zan samu kansa idan kuma shi ba alkhairi bane a gareni ya Allah ka gaggauta chiremin son sa a raina dan isar ka da karfin mulkin ka ya Allah nasan ba wan da ya isa ya bani abun da baka bani ba haka zalika ba wanda ya isa ya kwachemin abun da ka bani ya Allah ka dafamin, ya Allah kasan ina son sa ina kaunar sa tun farkon gani na da shi ya Allah ka dafawa rayuwata, kukan da yachi karfin tane yasa tayi shiru ta dai na magana ta chigaba da kukan ta mai tsuma zuchiyar mai sauraro har barchi yayi awon gaba da ita.

    Yola Nigeria

    A hankali Inna ta waro idon ta wani haske ne ya kashe mata ido da sauri ta runtse su

    sake buɗewa ido tayi a hankali, bin in da take kwance da kallo take sai wani jujjuya ido take sama, karaf idon ta ya sauka kan yaya Bello dake tsaye a Kanta ya harɗe hannu a kirji yana kallon ta, chike da mamaki tace “bello kai ne? Ina ne nan kuma? Waye ya kawoni? Ajiyar zuchiya yaya bello ya sauke tare da saukar da hannun sa kasa ya kariso in da take kwanche ya zauna a gefen ta burman nata ya fara magana “eh goggo habiba nine, nan kuma wajen mai magani ne, kuma ni na kawoki” yun kurawa tayi zata tashi amma ta kasa komawa tayi ta kwanta “yanzu Bello duk irin takurawa rayuwan ku da nayi bai sa kaki taimako na ba” “aa goggo habiba ki daina faɗin haka ko ba komai uwa ɗaya uba ɗaya kuke da Bappan mu kuma ni duk abun da nakeyi inayin sane dan Allah ba dan wani ba” kuka mai tsuma rai Inna ta fashe dashi chikin kuka take faɗin “Allah mai iko dan Allah Bello ku ya femin “goggo habiba kiyi shiru kinga yanzu kina chikin chiwo ni na yafe miki duniya da lahira Allah ya yafe mana tare” Shiru sukayi sai kuka kasa kasa Inna take, yaya Bello na rarrashin ta.

    KANO

    slowly zulaihat dake kwanche saman sofa ta tada kai da chinyar Aunty Amarya ta buɗe ido, da murna Aunty amarya ta fara faɗin “alhamdulliah alhamdulliah Allah mun godema ta farfaɗo” Ammi dake zaune a gefe guda ta taso ta nufo wajen tana faɗin “masha Allah” dogon tsaki Aunty amarya taja kafin tace “karki zo nan munafuka ba duk ɗan ki bane yaja ai wlh da ya kashe yar mutane zai gane kurenshi” shiru Ammi tayi ta dakata da nufar tasu da take, Ummi dake zaune saman sofa mai zaman mutun 1 ta mike ta kama hannun Ammi ba tare da tayi magana ba suka fice daga ɗakin sukayi part nasu.

    Washegari Uk

    Kwanche Lamrat take kan gado ta tada kai da chinyar yaya Yusuf sai kuka take,
    Da kyar yaya Yusuf ya iya shawo kan ta ta dai na kuka kwata kwata taki chin abinci ita dai dole ya mai data wajen Ammin ta tun da kasheta yake sonyi, “my baby kiyi hakuri na miki alkawari ba zan sake miki hakan da zafi ba” waro ido waje Lamrat tayi chike da jin haushi tace “au daman yaya Yusuf zaka sake yimin hakan kenan? “My baby dole na sake yi maki mana idan ban miki ba taya zamuyi mu samu baby’s” “nifa yaya Yusuf bana son baby’s ɗin na hakura kawai ka mai dani wajen Ammi na” “haba my baby idan na mai daki wajen Ammi ni kuma fa dawaye zan zauna kenan? “Ka zauna kai kaɗai mana ai daman kai kaɗai kake zaune ba da ni ba “to shike nan tun da haka kika che yanzu dai zan mai daki wajen Ammi ni kuma sai na samo wata baby na Aura ta aifamin baby’s masu kyau” kuka mai karfi Lamrat ta fashe dashi a razane yaya Yusuf yace “my baby lfy kukan me kuma kike “ni yaya Yusuf ka kaini wajen Aunty hiyana ta wlh ni yanzu bana son ka tun da dai wata mata zaka aura” dariya mai karfine ya kwache masa, dariya yake sosai har da rike chiki, ganin yana mata dariya ne yasa ta kara sautin kukan ta sosai, ba shiri ya dakata da dariyan da yake “sorry my baby tuba nake ni ai ke kaɗai kin ishe ni ba ruwa na da wata mace ni kam wasa nake” “ni dai yaya Yusuf ka kaini wajen Aunty hiyana tun jiya fa ban ganta ba”tana magana tana shesshekar kuka “to kiyi shiru idan kina son zuwa wajen su nima yanzu zanje na shirya na je wajen aiki sai karfe 2 na rana zamu dawo sai mu kai ku wajen shopping dan ku zabi kayan da kuke bukata” “to nayi shiru ka kai Ni” mikewa yayi batare da ya sake magana ba ya kwantar da kanta a saman gadon ya sauko kasa ya shiga dressing room jim kaɗan ya fito hannun sa ɗauke da jallabiya baki ya dawo kan gadon ɗagota yayi ya zura mata jallabiyar san nan ya miƙe ya ɗauke ta chak ya nufi waje da ita, a babban palon kasa ya samu su Zahra gaba ɗayan su suna zaune suna hira hiyana ce kaɗai bata wajen, saman sofa mai zaman mutun 3 ya direta chike da jin kunya lamrat ta fara gai da Zahra, shi ko juyawa yayi chikin sauri Zahra na gai da shima bai bi ta kan taba ya haye sama.

    Da sallam hiyana ta shiga betroom ɗin Bgs sanye take chikin doguwar hijabi har kasa fari tas, hannun ta ɗauke da katon trey mai ɗauke da kayan breakfast nashi, tsaye yake gaban mirrow sanye da uniform na sojoji yana kokarin ɗaure gashin kansa ta baya, kasa kasa hiyana ke satar kallon sa ba karamin kyau kayan suka masa ba kamar dan shi akayi su, sai wani fitinannen kamshin da yake zubawa kamar anyi ɓarin turare ajikin sa, sosai take shakar kamshin turaren nashi

    table ɗin tsakiyar ɗakin ta nufa da niyyar ajiye masa abincin, turus ta tsaya ganin abincin da ta kawo masa jiya da daddare ma ko taɓawa bai yi ba, shiru ta tsaya tana tunani shin na ajiye masa breakfast ɗin ko zai chi ne ko kuma dai na haɗa har da na jiyan na mayar kitchen tun da ba zai chi ba, tayi nisa chikin tunanin da take, sai ganinshi tayi ya wucheta ya nufi kofar fita, chikin sauri ta tsugun na kasa murya na rawa tace “ina kwana yaya prince” ko kallon in da take bai yiba ya fice daga ɗakin, shiru tayi ta kasa miƙewa dan ji tayi gaba ɗaya jikin ta ya mutu, yanzu ya zatayi da abincin nan, da ƙyar ta miƙe ta fice daga ɗakin ta mai da breakfast ɗin kitchen san nan ta dawo ta ɗauki na jiyan ma ta mai da kitchen chike da ɓachin rai ta koma ɗaki ta kwanta

    Misali karfe 2pm gaba ɗayan su suna zaune a palon kasa suna hira wayar Zahra dake hannun Lamrat ya fara ringing, chikin sauri Lamrat ta miƙawa Zahra wayar, ansa Zahra tayi ganin sunan Aunty farida ne ya bayyana a kan screen ɗin yasa ta yin picking da sauri ta sanya wayar a hand-free dan su hiyana su gaisa da ita gaba ɗaya, daga ɗayan ɓangaren Aunty farida tace “Auta ykk? Ya Uk? “Aunty farida muna lfy ya junior? “Junior yana lfy ina Hiyana? “Gatanan Zahra tayi maganar tana miƙawa hiyana wayar, chikin sanyin murya hiyana ta fara magana

    “Aunty farida ina wuni” “lfy lau my Hiyana ykk y mijinki? “Muna lfy ya junior” “yanzu dai bar zanchen wani junior mu fiskanchi abun dake gaban mu, kinga yanzu mijin ki yayi blocked ɗina, waro ido waje Hiyana tayi “yau Aunty farida ke da kanki yaya prince yayi blocked? “Eh my Hiyana nima na sha ruwan mamaki amma wan nan duk bashine matsalar ba kinaji kyalesa idan ya huche zai buɗe Ni, yanzu dai kina yin abubuwan da na tsara miki ne? ko kuma dai kin chigaba da zama shiru shiru “Aa Aunty farida inayi jiya ma na kai masa abinchi yau ma kuma na kai masa” “good my Hiyana abu na gaba da zan faɗa miki ya kamata ki rage tsoronsa kuma na faɗa miki ki daina sanya manya manyan hijaban nan da kike sanya wan kina jina ko? Zan sanya yaya Khalid ya sai muku waya gaba ɗayan ku dan mu rinƙa waya sosai kinji ko? Hiyana zatayi magana sukaji diran motochi su Bgs a chikin gidan alamun sun dawo daga wajen Aiki, chikin ruɗu hiyana tace “Aunty farida gasu yaya prince sun dawo aikin” “good my hiyana yanzu yana shigowa ki bishi ɗaki nasan yana shiga ɗaki zai zauna saman sofa yaɗan huta to yana shiga ki bishi ki chire masa takalmi da socks kinji? Shiru Hiyana tayi tana tunanin ta yarda zata fara tunkaran Bgs har ta chire masa shoe “my Hiyana kimin alkawarin zaki min hakan kinji? “Aunty farida na miki alkawari zanyi tana magana wasu zafafan hawaye na bin kunchin ta, hannu Zahra tasa tana gege mata hawaye chike da tausayin ta, katse kiran tayi ta ajiye wayar a gefe ta rike hannun Zahra tanan kokarin fara magana kenan, sukaji takun tafiyar su Bgs nan take suka nitsu ɓoye fuska hiyana tayi chikin chinyoyin ta dan hawayen nata sunki tsayuwa kuma bata son su yaya Yusuf suga tana kuka.

    Bgs ne a gaba ya shigo kafin Zahra ta ɗaga masa gaisuwa ma ya haye sama abun sa, miƙewa Hiyana tayi chikin sauri ta bi bayan sa, a tare su Khalid suka shigo gaba ɗayan su suka baje a palon kowa ya zauna kusa da matar sa, chike da so da kauna suke gaisawa da juna “ke Amrat tashi kije ɗaki ki ɗauko min laptop di na” chewar yaya Fahad, da gudu Amrat ta miƙe ta haye sama

    A ɓangaren hiyana kuwa

    Tana zuwa bakin kofar ɗakin yaya prince ta tsaya ta goge hawayen ta, san nan ta shiga ɗakin da sallama yana zaune saman sofa mai zaman mutun 2 ya ɗan jingina da jikin sofan ya lumshe ido, a nitse ta tako zuwa gaban sa jikin ta har rawa yake, ta sungunna, ta kai hannunta kan takalmin sa, da kyar ta ita sai ta hannun ta ya dai na rawa, igiyar ta kalman tafara kwanchewa, da kyar ta iya ɗan ɗaga kafar tasa ta zame ta kalmin haka ta zame ɗayar ma, ɗan ɗaga kafar wandon nasa sama tayi ta kama bakin safar kafar tasa ta zame ta a hankali, zubawa kafar tasa ido tayi, ba karamin kyau dogayen yatsun kafan sa suka mata ba, ga wani bakin lallausan gashi a kwanche a kan yatsun, farchen (kunba) kafar sa farare tas sai kyalli suke bata san lokachin da ta kai hannun sa saman yatsun nashi ta shafuso su ba wani gigitachen mari ya sakar mata a kumatu wadda yasa ta mikewa tsaye ba shiri tare da fasa wani razanannen ihu chikin tsawa yace “get out” a guje ta fice daga ɗakin ta nufi nata

    Tana shiga ɗakin ta ta chire hijabin jikin ta, ta sanya karfi ta yagashi gida uku chikin sauri ta ɗauko face Mark ta sanya a fuskar ta ɗaukan hijabin nata tayi ta taka saman gadon ta ta ɗaura hijabin a jikin Ac tanayi tana kuka mai suma rai, daure hijabin nata tayi sosai chikin kuka tace “banga anfanin rayuwata ba wlh Bappa ya rasu Inna ta rasu diyana ta ɓata yaya prince da yake matsayin mijina ya tsane ni to me kuma ya ragemin sosai ta gyara face Mark dake fuskantar ta yadda zatayi saurin mutuwa kar numfashi ta ya fita ɗaure wuyar ta tayi da kyau san nan ta sauka daga kan gadon kafar ta na lilo a tsakiya sai karkarwa take ta zaro blue eyes nata waje sosai saboda shake wuyar ta da hijabin yayi,

    Amrat na fitowa daga ɗakin su rike da laptop ɗin yaya Fahad, daga ɗakin hiyana taji wani irin numfashi da take da sauri ta nufi ɗakin tana nura kofa taga hiyana na kokarin mutuwa dan gaba ɗaya har jikin ta ya fara saki, wani razanannen ihu Amrat ta saki wadda ya dira a dodon kunnen kowa dake gida, gaba ɗaya su Khalid suka miƙe a tare suka hauro dai dai lokacin Bgs ma ya fito daga ɗakin sa dan jin irin ihu da Amrat ta saki, kusan tare suka shiga ɗakin Hiyana.

    Bgs na ganin halin da Hiyana ke chiki yaja wani dogon tsaki tare da karisawa chikin ɗakin da hannu ɗaya ya damki kafafunta tare da chire hijabin da ta ɗaure wuyarta ya sauko da ita kasa sai wani tangal tangal taka alamar ta jigata, wuyar ta ya damko ta bayan ya fara janta har suka fito waje, chike da bachin rai Khalid yace “haba Bgs menene haka? Bai bi ta kan kowa ba yayi waje da ita chikin bayan motar sa ya jefata ya shiga gidan gaba yau da kansa ya ja motar da gudu suka bar gidan, a razane Fahad yace “ina key ɗin ɗayar motar nan dole na bisu dan nasan halin yaya prince yanzu wani abun zai mata, tun kafin Fahad ya karisa maganar yaya Khalid ya shiga motar sa ya tayar da sauri Fahad da Ahmad suka shige chikin motar da gudu suka bi bayan Bgs

    sai kuka su Zahra suke suna addu’ar Allah ya kuɓutar da hiyana daga hannun Bgs

    Wajen saman wata gatuwar dutse dake zubar da ruwa kasa Bgs ya tsayar da mota fita yayi ya buɗe gidan baya ya damko wuyar Hiyana ya jata har zuwa bakin dutse kallon kasan dutse Hiyana tayi katuwar rafine awajen a tsorace ta dawo da kallon ta kan shi, so take ta chire face mark dake fuskantar ta masa magana amma kafin ta ɗago hannu ya daga mata tsawa chikin tsawa yace “ba mutuwa kike son yi ba to ga hanyar da zaki mutu chikin sauki, yana gama faɗin hakan yayi wurgi da ita kasan dutsen ya juya abun sa…..

     

    Masu karatu Bgs fa ya buga min kai yau sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu naso na muku 2 page amma bani da charji shiyasa na muku long page Ashe karatu lfy azo a bani hot comments

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 5

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 5

    Book 2

    *Episode 5*

    …..da wani matsanan chin ihu jabir ya farfaɗo daga doguwar suman da ya shiga sakamakon bugun da bgs ya masa a baya, da sauri daddyn sa ya miƙe daga saman kijeran da yake ya nufi gadon da jabir kwache kiran sunan shi dadyn sa ya farayi yana ɗan tattaɓa sa da kyar jabir ya nitsu tare da waro idon sa kan dadyn na shi, wani dogon tsaki yaka tare yun kurawa yana kokarin mikewa hannu dady’n sa ya sa yatai maka masa ya miƙe zaune chike da rashin kunya da tsaurin ido jabir yace “dadyn kada ka sake taɓani pls “jabir what are saying ne? “Abun da kaji shi nake faɗe dady” “oh sorry my lovely son nasan nayi laifi amma amin afuwa ko” “dady idan kana son namaka afuwa to wlh sai ka kamomin Hiyana na mata fyaɗe kuma sai ka kamo wan da ya bugenin nan kasa yaran ka su ɗaure sa na koya masa hankali yana maganar yana kwaɓe fuska “oh my lovely son wan nan kawai bukatar ka to ka kwantar da hankalin ka ka sa a ranka tamkar hiyana take ko wacece to kasa dai a ranka tamkar tana ɗaki tana jiran ka kaji? Shi kuma wanchan ko dan gidan uban wayene sai an nemo sa zan baza yarana kai har da yaran mum ɗin ka zan haɗa sai an kamo shi koma ai na yake, karka damu da hannun ka zaka masa hukuncin” murmushin jin daɗi jabir yayi kafin yace “to dadyn na ngd shiyasa nake Son ka amma ina mum ne? “Mum ɗin ka tana ɗaki taje wanka, yunkurawa jabir yayi yana faɗin “dady’n ya kamata na je school ban san ko rana ɗaya ya wucheni ban je school ba, shiru dady yayi yana mamakin wato shi jabir bai ma san ya kai 2 weeks a sume ba kenan sauka jabir yayi daga gadon ya nufi toilet dan yin wanka, miƙewa dady yayi ya fice daga ɗakin ya nufi ɗakin sa.

    YOLA

    Ihu inna habiba take kamar ranta zai fita sai murkusoso take a tsakiyar ɗaki tana dafe da chikin ta, ga kwaryar magani a gefenta da alama wani abun tasha, gaba ɗaya kauyen babu wan da ya kawo mata ɗauki mafi yawan chin jama’ar garin suna jiyo ihun ta amma babu wan da ya ko kalli gidan ta kallon mitunchi ma bare a sa ran akoi wadda zai kawo mata agaji, kuka take tsakanin ta da Allah tana juyi tana faɗin “na shiga uku na!! Mutuwa zanyi wayyo Allah!! Ahmadu ka dawo ka ya femin, wayyo Ummi na san na chutar dake ki dawo ki ya femin shikenan ni kam nan take wasu manya manya kuraje (kurji) suka fara fito mata a jiki ta ta ko ina har kan ido chikin hanchi chikin bakin ta ga bala’i zafi idan kurjin yazo fitowa tun tana iya ihu har ta kasa takoma fitar da nishi kawai tana ji tana gani jikin ta duk ya lalace da wayan nan kuraje masu bala’i zafi da kuma wari dan idan kurjin ya fito bayan 10mins sai ya fashe ya zama kamar kunan wuta sai wani ruwa mai wari ya fara fitowa daga wajen haka dai inna tayi ta juyi a chikin ɗakin ta ba wan da ya kawo mata ɗauki har numfashi ta ya ɗauke ɗiff

    A ɓangaren buba kuwa ba laifi yana samun sauki dai dai gwargwado dan yanzu ya dai na buge buge da fisge fisge sai dai ya kwanta shiru ba um ba umm shiru baya magana, yaya Bello yana bashi kulawa sosai da sosai

    A ɓangaren hasana kuma laulayin chikine gadan gadan take fama dashi yaya Bello ba ƙaramin ko kari yake ba duk abun da chikin hasana yake so tofa koman dare bawan Allah n nan sai ya fita ya nemo mata koda kuwa karfe 1 na dare ne idan ma mangoro tache take so tofa ko mai dare sai ya fita ya hau bishiya mangoro ya chiro mata.

    Innar buba na samun sauki sosai domin ba karamin kulawa take samu wajen yaya Bello da Innar saba yanzu kunburin kafar nata ya ragu sosai harma tana iya ɗan takawa a hankali,ba karamin daɗi yaya Bello ya jiba ganin Buba da Innar sa suna samun sauki.

    Duk da ɗawai niyar dake kan yaya Bello hakan bai hana shi kula da amanar da Ammi ta bashi ba na kulawa da dabbobin su hiyana ba yanzu haka kusan shanu 20 ne suka Aihu shanu fa sai daɗa yawa suke abun baa magana gashi suna samun kiwo mai kyau suna koshi sosai sai girma suke karawa.

    Maiduguri

    A hankali yarinyar da Ahzan ya kaɗe da mota ta fara waro manya manyan idon ta, bin ɗakin da kallo ta fara yi ganin ta buɗe ido ne yasa Ahzan dake zaune kusa da mum ɗin sa da wata yar budurwan yarinya miƙewa chikin sauri ya nufo gadon da yarinyar ke kwanche bai kai ga karisawa bakin gadon ba yaja birki da sauri a ɗan tsorace yake kallon yarinyar chike da mamaki mum tace “Ahzan lfy kuwa? Baya baya ya ɗan yi kaɗan a hankali yace “mum zo kiga yarinyar nan shin da gaske ne abun da nake gani ko kuma dai ido nane, tasowa mum tayi ta nufo shi, turus itama ta tsaya ta kasa karisawa bakin gadon, chike da tsoro tace “Ahzan anya ba aljana ka buge ba kuwa? domin ni kam a bil adama dai ban taɓa ganin mutun mai kyan yarinyar nan ba, kuma ka dubi kwayar idon ta kwata kwata ba irin na mutane bane”
    “No mum akoi mutane masu kwayar ido blue irin nata sai dai basu da yawane kuma baa Chika samun su a nan gida Nigeria ba sai dai kasashen turawan nan, Ni kyawun nata ne da ta buɗe ido shine ya tsoratani nake ganin kamar ba mutun ba

    tasowa yar budurwan dake zaune a bayan su tayi itama ta nufo su tana faɗin “mum menene? Hannu mum tasa ta mata nuni da yarinyar dake kwanche kan gado tana faɗin “hanan kalli yarinyar da yayanki ya buge ne ta farfaɗo, kai kallon ta hanan tayi kan gadon da yarinyar ke kwanche tana kallon saman, chike da murna hanan tace “wow mum kinga yarinya mai kama da Aswariyya raj na kasar India sai dai blue eyes ne kawai da ya bambam tasu ta kai karshen maganar tana nufar gadon da yarinyar ke kwanche gefen ta ta zauna tana faɗin

    “Sannun ki ya jiki? Dawo da blue eyes nata yarinyar tayi kan hanan, sosai take kallon hanan “zaki iya yimin magana? chewar hanan, shiru yarinyar tayi batace komai ba karisowa wajen Ahzan da Mum su kayi “hanan jeki kira likita ki che masa yarinyar ta farka” chewar Ahzan yayi magana yana kokarin zama a gefen gadon

    “Yammata ya sunan ki mum ta tambaya tana kallon yarinyar shiru yarinyar bata yi magana ba sai binsu da ido da take “mum ina ganin mu kyaleta tukun nan ko? tun da kinga yanzu ta farfaɗo kila sai anjima idan ta sake samun nitsuwa zatayi magana” “eh hakane Ahzan amma gaskiya yarinyar tana da kyau sosai, shiru Ahzan yayi dan yama rasa me zai che domin kyan yarinyar ya gama ruɗar da shi

    Dr walid ne ya shigo ɗakin da sallama ɗauke a bakin sa hanan da Nurse biyu suna biye da shi a baya, zuwa yayi ya fara mata yar gwaje gwaje sa da zaiyi yayi yar dube duben sa, san nan ya dawo da kallon sa kan su Ahzan da gaba ɗaya sun zuba masa ido suna sauraron suji me zai che “Alhadulillah yarinya dai ta samu sauki amma akoi yar matsala bazata iya yin magana ba yanzu wata kila gaba zata iya chigaba da magana sai kurinƙa sata a addu’a, shiru sukayi ba wan da ya sake magana, Dr walid ya kwashe kayan aikin sa ya nufi waje

    KANO

    Khalid da Yusuf ne zaune a palon Abba suna hira “amma yaya Khalid kana ganin Bgs zai so yarinyar nan kuma ya zauna da ita a matsayin mata kuwa? Murmushi Khalid yayi kafin yace “inaga duk gidan nan ba wan da ya kai Ni sanin halin Bgs, ko Aryan bai kai Ni sanin halin saba domin Aryan baya shiga abun da baa shigar da shiba ni kuma ko da Bgs bai shigar da niba in dai naga abun da bai min ba sai nayi magana shiyasa nafi Aryan shiga jikin Bgs sosai wlh kaji na rantse maka ko? Ko Bgs zai so yarinyar nan tofa inaga sai mun haɗu gaba ɗayan mu mun dangana da ɗakin gaba mu ɗauki shekara ba barchi dare mu kwana muna sallah muna masu addu’a idan ba haka ba abu mai wuyar gaske ne Bgs yaso sister shifa da mace da namiji duk ɗaya yake kallon su ba shi da wani shauki baya jin wani filling shifa bai ma san kyau ba bare muche idan yaga kyan sister zai iya ruɗe wa yace yana son ta, to bai ma san kyau ɗin ba shi idan ba kyan bindiga boom da kuma bullet ba bai san kyan komai ba, kai in ta kai che maka ma idan kaga Bgs ya ɗaga ido ya kalli sister to wlh a rashin sani ne sai kache baka ma san shiba kake min irin wan nan tambaya mutumin da ko Aryan baya ɗaga ido ya kalla ka dubi yadda suke da Aryan ɗin nan fa, kuma wlh ba wai Bgs baya son mu bane ni nasan yana matikar son mu shi yasa duk wani iskilancin da zai min bata damu na nariga da nasan haka halin sa yake ina da tabbacin idan ba mu da muke tare da shi ba sai kuma Abba da Ammi tofa ba wan da a gidan nan zai che ga kalan voice ɗin Bgs kai a gidan nan ma akoi wayan da basu taɓa jin voice nashi ba bare ma su riƙe kalar ta” dakatawa da magana Khalid yana kallon Yusuf da ya sunkuyar da kai kasa kamar mai tunani

    “Yusuf tunanin me kakeyi kuma? Ɗago kai Yusuf yayi tare da sakin murnushin mugunta yana kallon Khalid “lfy kake irin wan nan murmushin haka Yusuf? “Kasan me yaya Khalid wlh idan na tuna wata rana sister zata fito ɗauke da chikin Bgs sai abun ya rinƙa bani dariya zan ga wan nan lokachin kuma wani irin iskanci zai mana shin zai chi gaba da chewa kallo ɗaya yakewa wace da namiji ne ku kuma alokachin zai fara bamban tasu” “amma gaskiya Yusuf baka da dama wlh wai daman tunanin baby Bgs da sister kake ko to sai kayi kokari ka dage da yi musu sallar dare kana rokon Allah daya sanya soyayyan da tausayi da imani a zuchiyar Bgs dukka dan wani lokaci idan Bgs yayi wani abun ni tunani nake anya yana da imani kuwa “aa yaya Khalid dolefa wata rana Bgs zai hakura ya rungumi kadda ya kama matar sa domin dai kaji me Abba yace ko mutuwa yayi bai yadda Bgs ya saki hiyana ba to kaga zama da ita ya zama masa dole” “eh hakane Yusuf kana da gaskiya zama da ita ya zama masa dole amma yanzu ta yadda sister zata juri zama da shine abun dubawa domin wlh zata sha wahala ba kaɗan ba gashi baya magana baya kallon mutane idan ka masa magana ba zai am saba idan kayi tunanin bai ji bane ka mai mai ta ya daka maka tsawa kai duk wani abun da zakayi ka burge ɗan adam idan ka yiwa Bgs hukun taka zai yi shikam babu wani abu a duniya dake burge sa inaba Gun da bullet ba mutun ne bazaka taɓa gane hagun sa ba bare dama”

    “Ai yaya Khalid kai baka ma sani bane wlh gaba ɗaya wajen aikin mu kama daga manya har kananun sojoji masu tasowa da zarar an ambaci sunan Bgs kowa jikin sa rawa yake Hmmm ai a gida ma yana muku sassauci sai kaje wajen aikin mu watara zaka sha mamaki dan akoi wata rana da wani soja yayi laifi yaya Aryan yace Bgs ne zai masa hukuncin wlh sojan nan yana jin anche Bgs ne zai hukunta tashi yasa bindiga ya harbi kansa ya mutu, kai bama wani ba ko ni da kai na idan misali yanzu nayi laifi a che Bgs ya hukun tani to ina mai tabbatar maka harbe kai na zanyi na mutu dan da Bgs yamin hukun chi gara na mutu na huta dan hukunchin sa ba kyau ba zai kashe ka ba amma zaka gwanmachi mutuwa idan ya fara hukun taka, kana gani gaba ɗaya faɗin London idan aka ambaci sunan shi sai kasar ta girgiza daga manya manya masu faɗa aji a kasar har kananan yan siyasa mutuwar tsoron sa suke koda super market kaje chikin wasa ka amince sunan sa nan take zakaji jama’a sun nitsu ba zaka rasa masu furta kallamar shahada a chikin su bama”
    “To ai Yusuf wan nan dalilin ne yasa nache maka wani lokaci idan Bgs yayi wani abun sai naga kamar bashi da imani mu dai yanzu sai dai mu dage mu taya sister da addu’a” dariya Yusuf yayi kafin yace “ba dole na taya sister da addu’a ba domin idan Allah ya dai dai ta komai ɗan da zasu haifa ba karamin kyau zai yiba madara da madara ne suka haɗu kyau iya kyau baa magana shiyasa na yanke hukunci first born na Bgs nawane awaje na zai zauna, amma Allah yasa ya ɗauki blue eyes na sister” tsaki Khalid yaja san nan yace “wlh Yusuf kai dai baka da aiki wato har ka tsara yadda ɗan su zai kasan che ko to in ban da kai ma da wani zanche Ai da Bgs da sister kaman nin fuskar su ɗaya basu da wani banbanci idan ba na kalar ido ba” Yusuf zai yi magana kenan idon sa ya sauka a kan Abba dake tsaye a bakin kofar Betroom nashi ya harɗe hannu a kirji ya zuba musu ido yana kallon su

    chikin sauri Yusuf ya miƙe ya kama hanyar fita yana faɗin “my baby na kirana miƙewa Khalid ma yayi batare da ya lura da Abba ba ya bi bayan Yusuf yana faɗin “to ai nima sis love ɗina na jirana binsu da ido Abba yayi har suka fice daga Palon sauke nauyayyar ajiyar zuchiya yayi kafin ya fara magana

    “Na tabka babban kuskure arayuwata nayi da na sanin haɗa Bgs da hiyana ido na ya rufe bani da burin da ya wuche in samo wa ɗana mace ta gari batare da na yi la’akari da halin da ita yarinyar zata shigaba, gaskiya da baa ɗaura Auren nan ba da ba abun da zai hanani in aura wa Ahmad ita ni da kaina na jefa rayuwar marainiyar Allah a chikin kunchi da damuwa innalillahi wa inna ilaihir rajiun Ya Allah kana gani ban yi hakan da nufin chutar da itaba ban yi hakan da nufin kun tata ma rayuwar taba,nayi hakan ne da kyakkyawar niya da kuma yakinin wata rana zai sauya ban san chewa abun nashi ya kai har haka ba daga chewa Bgs ne zai maka hukunci kawai sai ka harɓi kanka da bindiga to inaga yarinyar da aka haɗasu dole kuma anya bazan raba auren nan ba kuwa kai dole nayi magana da Aisha tun abu bai yi nisa ba musan abun yi, ya Allah ka kawo min agaji Allah ka kawowa hiyana mafita yana kai karshen maganar ya juya ya koma chikin betroom na shi

    Kwanche yake a saman katafaren gadon sa yana latsa waya kiran Aunty farida che ta shigo wayar sai da wayar ta kusa tsin kewa san nan yayi picking tare da manna wayar a kunnen sa, daga ɗayan ɓangaren Aunty farida tace “Hello Prince Ykk Y gida? Shiru ya ɗan yi na yan sakanni kamar ba zai yi magana ba “lfy Ykk?ya faɗa a takaice yayi maganar yana kawar da fiska gefe kamar yana gaban ta “Ina lfy dan Allah prince magana nake son yi da hiyana kuma kaga bata da waya pls ka kai mata wayar ka muyi magana” ta karisa maganar chike da fargaban abun da zai biyo baya, Aunty farida na gama magana batare da ya bata amsa ba ya katse kiran tare da yin block na number Aunty farida yayi wurgi da wayar gefe guda, wani dogon tsaki yaja tare da miƙewa ya fice daga ɗakin ya nufi part na Aryan

    Kwanche saman sofa mai zaman mutun 3 ya isko Aryan ya ɗora hannun sa ɗaya a saman fuskar sa dai dai sai tin ido ɗayan hannun kuma ya ɗora a kan chikin sa yayi shiru, shiru Bgs ya tsaya a bakin kofa yana kallon yadda Aryan ya rame sosai yayi baki ya sauya gaba ɗaya ya fita hayyachin sa kamar ba shi ba nan take wani mugun tausayin Aryan ya dira masa a rai

    a hankali ya zuro kafafun sa ya shigo chikin palon saman sofa mai zaman mutun 1 ya zauna kasa kasa ya fara kiran sunan Aryan “Aryan Aryan” ɗauke hannun sa Aryan yayi daga kan fiskar sa slowly ya waro Ash eyes nashi da suka sauya yanzu sun kara girma saboda raman da yayi sunyi jaa sosai gaba ɗaya jijiyoyin idon nasa a tsai tsaye suke kallo ɗaya yayiwa Bgs ya kawar da kan sa gefe guda tare da yun kurawa ya tashi zaune “Aryan ka tashi ka shirya dan ina ga yau zamu wuche mu koma bakin aiki ba zan iya zaman Naija ba” chikin kasalalliyar murya Aryan ya fara magana “Bgs ka tafi kawai ni ba zan je ko ina ba tare da matata ba idan kaga na bar Naija to tare da ita ne” “what!!? Aryan kasan me kake faɗe kuwa mace fa kace ni ai na ɗauka duk damuwar da kake chiki saboda rasuwar Aiman ne” “No Bgs zafi biyu ne a lokacin guda suka haɗun min ina rokon Allah daya bani ikon chin wan nan jaraba da ya jarab cheni da shi, wlh zuchiya ta ta fara karaya kwata kwata ji nake duniya ta ishe ni na rasa ina zan saka kaina” “Amin amma yanzu dai katashi kaje ka shirya mu tafi, ka dai na yawan tunani addu’a Aiman ke buƙa ba wani abu ba”
    “Bgs nafa faɗa maka babu in da zanje ba tare da matata ba “wai ni kam Aryan kana da lfy kuwa kasan me kake chewa kuwa Aikin naka fa “bgs lfy na kalau aiki kuma idan ba zaka iya ɗaga min kafa har Allah yasa naga matata ba to zan rubuta maka later barin aikin sai kasa hannu domin idan babu my d a rayuwata rayuwar tawa bata da sauran wani amfani, shiru Bgs yayi ya zubawa Aryan green eyes nashi yana kallon sa from head to toe ya san dai iya gaskiya Aryan ke faɗa domin duk wani maganar da zasu yi da Aryan tofa basa saka wasa a chikin ta “Aryan mace kuma kai ina ba gaskiya kunne na ke faɗamin ba “no bgs gaskiya kunnen ka ke faɗama ba karya bane ina son matata ina kaunar ta fiye da rai na tun ranar da na fara ganin ta a duniya na kamu da matsanancin Son ta idan har na bika London yanzu ba tare da ita ba tofa ba zan kai labari ba dan haka ka kyaleni a nan kawai har ta Allah ta kasan che idan Allah ya ƙaddara zan ganta tofa zaka iya dawowa ka sameni idan kuma babu rabon na ganta tofa zaka dawo kasamu gawata yana kai karshen maganar ya miƙe da kyar ya shiga betroom nashi, wani irin bakin ciki ne ya tokarewa bgs makoshi jiyayi ya kara tsanar mace a rayuwar sa yanzu yasake tabbatar wa kan shi mace halittace mai rauni kuma duk lokacin da ta raɓeka kai ma zaka zama mai rauni dobi duk jarumtar Aryan da izza da kuɗi da mulkin da yake da shi jibi yadda ya dawo saboda mace, macen ma yar karamar yarinya no ba zan taɓa bari hakan ta faru da niba wlh mikewa yayi jiki ba kwari yanufi hanyar fita har yakai bakin kofar fita sai kuma ya juyo dan ba zai iya barin Aryan a halin da yake chiki ba bin Aryan yayi chikin betroom ɗin

    Zaune a gefen gadon ya isko Aryan ya dafe kansa da hannu ɗaya sai wani huci yake yana murza sai tin zuchiyar sa da hannu ɗaya, karisowa in da yake Bgs yayi gefen sa ya zauna yasa hannu ya chire hannun Aryan da ya dafe kan sa dashi chike da tausayin ɗan uwan nashi ya fara magana “Aryan pls ka daina damuwa kasan dai ba zan iya jure ganin ka a wan nan yana yin bako zan baka hutu har tsawon lokaci da zaka gane matar taka san nan ai na ta ɓata? Chiki rau’nanniyar murya Aryan yace “a Maiduguri ta ɓata” “ok to nama alkawarin in dai tana chikin Maiduguri bata fitaba to In Sha Allah bazata kara kwana biyu bata dawo gareka ba, kayi waya headquarter kace ni na bada izinin abaka sojoji mota 20 naso na taya ka neman ta da kaina amma ba lokachin all the best my blood amma dai ka dai na shiga damuwa dan in kana chikin damuwa nima dole na shiga damuwa kuma ba zan samu kwanchiyar hankali ba” juyowa Aryan yayi ya rungumi Bgs yana faɗin “nagode da ka fahimci ni nagode ɗan uwana” hannu Bgs yasa yana ɗan bubbuga bayan Aryan awan nan yanayin Fahad ya shigo ya same su

    Zama yayi a gefen Bgs yana kwaɓe fuska sakin Bgs Aryan yayi yana faɗin “Fahad lfy na ganka haka, sai lokachin Bgs ya dawo da kallon sa kan Fahad ɗin “yaya Aryan pls wani magani ya kamata na bawa Amrat bata da lfy ne? Dogon tsaki Bgs yaja tare da miƙewa ya fice daga ɗakin

    “me yake damun ta Fahad? Shiru Fahad yayi ya sunkuyar da kai dan bai son ya faɗawa yaya Aryan amrat ta fara period “to Fahad lfy ko dai chiwon nata baa faɗa ne? “Aa yaya Aryan kawai irin chiwon sun nan ne na matan kuma chikin ta yana chiwo sosai tun safe takemin kuka” duk da tashin hankali da Aryan ke chiki hakan bai hana shi yin murmushi ba dan Fahad ya bashi dariya eyee su Fahad ma an girma har da mata yanzu kam “tashi gaje ka ɗauko min box bari na baka maganin da sauri Fahad ya miƙe ya nufi wajen da ake ajiye wa ya ɗauko ya kawowa yaya Aryan magani kala uku Aryan ya bashi tare da faɗa masa yadda zai bata chikin sauri Fahad ya ansa tare da faɗin ngd kana ya fice daga ɗakin binsa da kallo Aryan yayi har ya fice san nan ya karisa hayewa kan gadon ya kwan ta ya lumshe ido

    KHALID

    ” Yaya Khalid dan Allah ka barni naje wajen Aunty hiyana mana” chewar Zahra dake kwanche saman sofa ta tada kai da chinyar Khalid “eyeee Auta wato yanzu ba kya tsoron yaya prince ko!? “aa yaya Khalid ina tsoron sa sosaima amma dai gaskiya zanje wajen Aunty hiyana dan wlh ina kewar ta sosai” “to yau she kika fara kiran Hiyana da Aunty kuma?Yayi maganar yana tura hannun sa chikin rigar ta, ɗan buge hannun sa Zahra tayi chikin shogoɓa tace “Kai yaya Khalid jiyama da ka shamin wlh zafi suke min ni ka kyaleni” sunkuyo da kansa yayi dai dai sai tin face nata chike da so da kauna yace “gaskiya ni da kayana ba zan bari ba bazan iya dai na sha da kuma matse suba” rufe ido Zahra tayi ta turo baki tana faɗin “Allah to sai na koma ɗakin Ammi na” yar dariya yayi kafin yace “ai da yafi domin a part ɗin Ammi ma zai fi daɗi abun kinga jiya dan ina sha kika rinƙa min kuka wai zafi to idan a part ɗin Ammi ne ko zan shanye dukka ba zakiyi kuka ba dan kina tsoron wani yaji kuma kin san ni kam ba ruwana ko agabab Ammi zan.. bai kai ga karisa maganar ba Zahra ta rufe masa baki da hannun ta tana faɗin “ai nasan zaka iya to ni babu in da ma zanje yanzu dai pls yaya Khalid ka barni mana naje na ga Aunty hiyana” “to naji idan na barki kikaje kika dubo hiyana in kin dawo me zaki bani? Da sauri Zahra tace Allah ka barni zaje duk abun da kake so zan baka” “kin tabbatar? “Eh yaya Khalid na tabbatar “ok to tashi kije amma karki daɗe minti 30 na baki kawai “yauwa yaya Khalid nagode” chikin zumuɗi ta muƙe

    fisgo ta yayi ta dawo ta faɗa saman kirjinsa a tare suka furta ash zafi “yaya Khalid me kuma na maka ka barni na tafi mana pls” “ba zaki tafi baki min kiss ba” turo baki Zahra tayi tana faɗin “to ka rufe ido ka” “aa ban yarda ba gaskiya haka jiya ki kamin ni dai ido na a buɗe zaki min in ba haka ba afasa zuwa wajen Hiyana nan” dukan wasa ta kai masa a kirji bam tana faɗin “Allah yaya Khalid kai ko “amin hot kiss ko kuma afasa zuwa wajen Hiyana ɗago kanta tayi a hankali ta haɗe fuskokin su tare da runtse idonta a hankali ta kamo lips nashi na kasa tafara tsotsa kamar jira yake daman ya tura hannun sa chikin rigar ta ya fara wasa da breast nata sai wani nishi yake Zahra data ga abun nashi ya fara yawa chikin dabara ta shammache sa ta kwache kanta da gudu ta miƙe ta fice daga Palon kwafa yayi yana faɗin “wlh zan kamakine yau bazan ɗaga miki kafaba, ita dai Zahra bata bi ta kansa ba tayi waje abun ta kai tsaye part ɗin Bgs ta nufa gaban ta na dukan uku uku

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 2

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 2

    Book 2

    *Episode 2*

    ……sosai Aunty amarya take kuka kamar ran ta zai fita sai rarrashin ta Ammi da Ummi suke chikin nitsuwa Abba ya fara magana “ku tashi muyi musamu mu kai Aiman ma kon chinsa, ku kuma Aisha ku tashi ku tafi kowa tayi part nata, kukan ya isa yanzu ba abun da Aiman ke bukata face Addu’a, kuma ina son sanar daku chewa ban yar ku sanar dasu farida yanzu ba ku bari sai bayan kwana biyu domin idan kuka sanar dasu yanzu tofa dole Aryan da Ahmad zasu samu lbr kuma kunsan me zai biyo baya idan suka sani a yanzu, yana kai karshen maganar ya miƙe ya fiche daga ɗakin miƙewa su Ammi ma sukayi gaba ɗaya suka fice sai kuka Aunty amarya take kamar ranta zai fita.

    After 8 days da rasuwar Aiman, gaba ɗaya family sun haɗu a palo Abba, harda su Aunty mardiya Su Aunty farida gaba ɗaya family Abba sun haɗu A nitse Abba ya fara magana

    “Duk kan ku ina mai baku hakuri da rashin da mu kayi san nan ina rokon Allah da ya baku hakuri da juria rashin ɗan uwan ku, a tare suka haɗa baki wajen chewa Amin, sun kuyan da kai kasa Aryan yayi sai furzar da iska mai zafi yake daga bakinsa chigaba da magana Abba yayi

    “Safras Khalid Fahad Yusuf Aryan duk da chewa kai Aryan matar taka bata nan Amma In Sha Allah zamu gano ta, to ga amanar ƴaƴana nan na baku ku kulamin dasu idan ni bana ganin ku to kusani Allah na ganin ku musamma Safras Aryan Yusuf Fahad kusani marayu kuka Aura idan kuka chutar dasu wlh Allah ba zai kyale kuba.

    Chikin rashin fahimtar Aunty amarya tace ranka ya dade ban gane me kake son kace ba wai wasu ya’yan naka kake maga kuma amanar wasu ƴaƴan ka basu? Dawo da kallon Abba yayi kansu ya chigaba da magana

    “Kamar yadda kuka ji na faɗa hakane gaba ɗaya yaran nan na musu Aure nan dai Abba ya basu labarin yadda ya haɗa Auren nasu da kowa da matar sa, chike da tashin hankali da ruɗu hiyana ta ɓoye fuskantar a chikin chinyoyin ta saboda wani kukan bakinchiki da yazo mata shike nan na shiga uku na yaya prince ne mijina wayyo Allah ni nasan rayuwata tazo karshe kenan.

    Chikin ɓachin rai Aunty amarya ta fara magana “wlh ban yar da ba tayaya za’ayi a haɗa ɗana da wanchan kazamar yar kauyen, dawo da kallon ta tayi kan Aryan dake zaune ya sunkuyar da kansa kasa yana kukan zuchi dan tun lokacin da ya samu labarin rasuwar Aiman kullun chikin kukan zuchi yake ya koma shiru baya magana bayama fitowa waje kullun yana kwanche a ɗaki

    “Kai Aryan idan har na isa da kai to ka saki yarinyar nan yanzu dan ni bazan haɗa zuri’a da masu kiwon shanu ba, chikin jin haushi Aunty Maryam tace “haba Aunty amarya dan Allah ki kyale yaya Aryan yaji da abun da yake ji mana” “zaki min shiru ne ko sai na zabga miki mari wlh yau idan kunga Aryan bai saki diyana ba tofa mutuwa nayi tana magana tana huchi kamar wata zakanya

    “Ba yau ba yanzu zan rubuta wasiya idan kika kuskura koda mutuwa nayi ki ka sanya Aryan ya rabu da matar sa tofa sai kin fuskanchi hukunchi mai tsanani gaske” chewar Abba
    Chike da izza Aunty amarya tace “wlh babu wan da ya isa yasa na bar ɗana ya zauna da wan chan kazamar yarinyar, rai a matukar ɓache Bgs ya miƙe tare da miƙar da Aryan ya riko kafaɗar sa suka nufi waje tun lokachin da Aryan yasan Aiman ya rasu kullun yake chikin rashin lfy bai da wani kuzari sai yawan tunani

    Miƙewa Aunty farida tayi tare da faɗin “ku tashi mutafi tayi magana tana kallon su hiyana, a tare suka miƙe gaba ɗayan su har da su Aunty Maryam suka nufi waje.

    Palon ya rage daga Abba Ammi Ummi sai Aunty Amarya, shiru sukayi suna jin yadda Aunty amarya ke surfa ruwan bala’i dole sai Aryan ya saki diyana,Abba batare da yayi Magana ba yasa hannu a aljihun sa ya chiro wayar sa, ya shiga contact ya fara kiran wata number wadda akayi saving da My Brother.

    Kira ɗaya a ka ɗaga sanya wayan a hand-free Abba yayi chikin girmamawa ya fara magana “Assalamu alaikum, daga ɗayan ɓangaren aka amsa da wa’alaikumus salam jin muryan wadda ya amsa Sallamar yasa Aunty amarya tayi sauri kwache wayar a hannun Abba ta katse kiran tana faɗin “dan girman Allah kayi hakuri karka sanar wa yaya wlh in dai Aryan ne na barshi yaje ya chigaba da zama da matar sa har abada Allah ya basu zaman lfy Allah yasa a gane ta” tana kai karshen maganar ta miƙe tare da ajiyewa Abba wayar sa a gefen sa ta nufi waje da sauri tana faɗin Allah na tuba kayafi min, duk bachin rai da raɗaɗin rasuwar Aiman dake damun Abba hakan bai hanashi yin ɗan murmushi ba dawo da kallon sa yayi kan Ammi da Ummi ya fara magana

    “Aisha kije ki sanar wa farida nache ta shirya hiyana ta mata duk abun da ya dache ta kai ta part ɗin mijinta, ita kuma salma ta shirya Zahra itama ta kai ta part na mijinta, ke kuma hauwa’u ki sanar da mardiya akan ta shirya lamrat da amrat suma ta kai su part na mazajen su, suyi sauri yana kai karshen maganar ya miƙe ya nufi betroom nashi.

    Kallon Ummi Ammi tayi chikin fargaba da tsoro abun da zai biyo baya tace “ki tashi muje mu isar da sakon ko? “To kawai Ummi tache a tare suka miƙe suka bar palon

    After some hours

    Aunty farida da Hiyana ne zaune a bakin gadon a ɗakin su hiyana Aunty farida ta tsara mata make up sosai

    hiyana tayi kyau sosai kamar ka sache ta ka gudu da ita, sanye take chikin wata danƙareriyar lace pink colour ta yafa mayafi fari a kanta, chikin nitsuwa Aunty farida ta fata magana

    “My Hiyana na san baki son Yaya prince Amma kiyi hakuri wan nan itache kaddarar ki kuma kisani hakan kamar jarabawa che Allah ya jarab cheki to kiyi kokari ki chinye jarabawar ki, kuma awan nan karon mu zaki tai makawa kinji ko? ina mai rokonki da ki daure nasan kina da hakuri sosai kuma nasan zaki iya to ki kara hakuri nasan zaki sha wahala zama da yaya prince amma ki daure In Sha Allah zamuyi nasara a kanshi kinji ko? kuma In Sha Allah kema zaki fara son shi yanzu zan faɗa miki ta yadda zamu fara yakar sa
    abu na farko duk da nasan baya san ganin mace a kusa da shi amma ya zama dole kirin ƙa kasanche kusa dashi koda kuwa baya so

    Abu na biyu ki dai na saka hijabin da kike sawa ki koma saka kananan kaya idan kin san yana gida, na uku zan roki maki alfarma a wajensa ko da yake ma koban roke saba nasan Abba zai che ke zaki rinƙa kai masa abinchi, kinga a nan ma zamu iya yin nasara, san nan idan ya dawo daga wajen aiki kiyi kokari ki saba masa da chire masa takalmi da socks da kan ki, nasan zaki sha wahalan hakan Kuma nasan zai iya chewa baya so to amma ko yache hakan karki dai na kirin ka yimasa kinji koh?

    Kuka Hiyana take sosai kamar ranta zai fita rungumota Aunty farida tayi sosai tana bubbuga bayan ta tana bata hakuri awan nan yanayi Ammi ta shigo ta samesu “feeda Abban ku fa yace kiyi sauri ki kai Hiyana part na mijinta tun ɗazun fa su salma suka kai su Zahra” “to kawai Aunty farida tace tare da miƙewa ta kamo hannun Hiyana suka sufi wajen

    Wani hawayen farinchiki Ammi taji ya zo mata burinta ya chika hiyana ta zama matar ɗan ta, sai dai awani ɓangare na zuchiyar ta kuma tana tausayawa hiyana sosai dan tasan Hiyana ba karamin wahala zata sha a wajen Bgs ba amma ta ɗauki kudirin taya hiyana yaki ta kowani hali

    Maiduguri

    ɗankareriyar mota kirar marcedes Benz che ta shararo a guje gudu mai motar yake sosai kamar zai tashi sama,ji kake kiiiiiii mai motar ya kwashe wata mahaukaciyar yarinya da ta zo tsallaka titi, wata mahaukachiyar birki yaja chikin sauri ya buɗe kofar motar ya fito kyakkyawa ne sosai fari tas dashi, chike da tashin hankali ya nufi inda yarinyar ke kwanche a saman titi ko motsi batayi kamar ta mutu ga jikin ta duk jini kanta ya fashe sosai, wani dogon salati yayi kafin ya karisa in da take juyawa yayi gabas da yamma babu kowa a kan hanyar, dawo da kallon sa yayi kan yarinyar, zuba mata manya manyan fararen idon sa yayi yana kallonta, gani yayi hannunta ya ɗan motsa alamar bata mutuba chikin sauri ya duka ya ɗauke ta ya nufi mota da ita gidan baya ya buɗe ya kwantar da ita ya rufe kofar ya buɗe gidan gaba ya shiga da sauri ya kunna motar yaja ta da gudu ya nufi asibiti da ita

    Yana yin parking a chikin asibitin ya fito ya ɗauke ta chak ya nufi chikin asibitin da ita, kai tsaye office na Babban Dr ya nufa, batare da yayi Sallama ba dan tsabar ruɗewa shiga office ɗin yayi kai tsaye, Dr na zaune yaga an shigo masa office chikin sauri ya miƙe yana faɗin “Ahzan lfy!? subhanallah wan nan fa!? Yayi maganar yana nuna yarinyar da Ahzan ɗin ke ɗauke da ita chike da tashin hankali Ahzan yace ” Dr walid ka taimake ni wlh yanzu shigowata garin nan ke nan ina sauri na karisa gida na buge yarinyar nan

    Hannu Dr walid yasa yana masa nuni da gadon dake chikin office ɗin yana faɗin “ka kwantar da ita tun da Allah yasa kai ma babban police ne yanzu zamu fara dubata, Ahzan bai jira Dr walid ya karisa maganar ba ya nufi gadon da sauri ya kwantar da yarinyar, chikin sauri Dr walid ya fara shirya kayan aiki

    Fitowa waje Ahzan yayi ya zauna saman wata kujera tare da chiro wayar sa daga aljihu kira ya danna tare da manna wayar a kunnen sa, kira ɗaya akayi picking, chikin rawar murya Ahzan ya fara magana “eh dady na shigo amma fa akoi matsala” chikin tsorata dady yace “wani matsala kuma Ahzan? “Accident na samu na buge wata mahaukachiyar yarinya che yanzu haka muna asibiti” “subhanallah ka turomin address ɗin Asibitin da kuke ganin nan zuwa” to kawai Ahzan yace tare da katse kiran ya shiga massage turawa dady address din asibitin yayi san nan ya mai da wayar aljihun sa ya dafe kan sa da hannu biyu….

    Dan girman Allah kumin afuwa jiya nache zanmuku page 2 to ina baku hakuri da rashin chika alkawari da nayi wlh ban samu charji bane sai wuraren 4 shiyasa amma In Sha Allah zuwa gobe zakuga sako masu zafi amin afuwa

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    *💫STAR LADY💫*3

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 1

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 1

    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

    Book 2

    *Episode 1*

     

    Ni gaskiya Abba na sak.. bai kai ga karisa maganar ba Abba ya daka masa tsawa chikin fushi da bachin rai ya fara magana “wlh Safras ko bayan rai na kasaki hiyana ban yafe maka ba itace zaɓin da na maka itace nake son gani a matsayin matar ka, ni ko kishiya ban yar da ka mata ba.

    Dafe kai Bgs yayi da karfi ya damki lips nasa na kasa da hakoran sa ya datse da karfi kan kache me jini ya fara zuba gaba ɗaya ya fasa lallausan lips nashi hannu biyu yasa ya samki kansa wani irin gigitachen kara ya saki kafi Su Abba su farga ya zube kasa wanwar ko motsi bayayi da alama ya suma, da gudu rundunar jibga jibgan sojojin sa su kayo kansa shi kanshi Abba ya tsorata da ganin halinda Bgs ɗin ya shiga na dama ya fara yi a zuchiyar sa “me yasa ma tun farko na haɗa Aure nan yanzu gashi abun yana son yafi karfi ina da tabbacin wlh hiyana zata sha wahala san nan mawuyacin abu ne Safras yaso ta, innalillahi wa inna ilaihir rajiun ba zan iya barinka ka saki hiyana ba domin idan nayi hakan na chutar da ita idan kuma na barka da ita tofa idan abu yazo da karar kwana zaka iya kasheta, ya Allah ka kawomin mafita Allah ka taimake ni ka kawomin ɗauki amma nayi nadama gaskiya kuma bayi kuskure

    Sojoji uku ne suka ɗauki Bgs suka kai shi mota, san nan suka dawo suka ɗauki Aiman shima suka kai shi mota, fitowa Abba dasu Khalid sukayi kowa ya koma chikin motar da yazo da gudu motochin suka fita Masallaci a jere, kai tsaye gida suka nufa

    tun daga nesa suke ta faman danna horn chikin sauri jibga jibgan sojojin masu tsaron gate ɗin suka wangale musu, kutsa motochin chikin gida sukayi kai tsaye parking space suka nufa, suna kashe motochin wasu jibga jibgan sojoji masu jini a jiki ƙo sassu masu ji da lfy, suka kariso wajen su biyu suka ɗauki Bgs zuwa babban palon Abba wasu sojoji biyu suka ɗauki Aiman shima sukayi chikin palon Abba, nan take Abba yayi kiran gaggawa akan gaba ɗaya family su hallara a Palo sai lokachin Abba ya lura da Aryan da Yusuf basa nan da mamaki Abba yace

    “ina Aryan da Yusuf Chikin sanyin murya Ammi tace “Yusuf dai yana ɗaki tare da lamrat shi kuma Aryan ban san ina yake ba” chikin faɗa Abba ya fara magana “me Yusuf kuma yake wajen lamrat yanzu duk tashin hankali da muke chiki bai isa yasa ya tsaya kusa damu ba” “a’a ranka ya dade lamrat fa Allah ya mata rasuwane”chewar Ammi, a razane Abba ya ɗago tare da faɗin”what!? Me ya samu lamrat ɗin daman bata da lfy ne!? “Aa lfy ta kalau tana tsaye kawai ta yanke jiki ta faɗi “subhanallah kai Umar jeka kira Yusuf ɗin kace ya tawo da lamrat, kai kuma Khalid kiramin layin Aryan muji ai na shi kuma ya tafi” da sauri Umar ya juya ya fita shi kuma yaya Khalid ya chiro wayar sa ya fara ne man layin Aryan.

    Dogon salati Khalid yaja lokachin da ya kammala waya da Aryan gaba ɗaya mutanen palon suka ɗago suna kallon sa “menene ya faru kuma Khalid!? Chewar Abba “Abba diyana ce aka sace yanzu haka Aryan ya tafi Maiduguri gaba ɗaya jama’ar palon suka ɗau salati har da Aunty amaryan

    Wani razanannen Ihu hiyana ta saki wadda yasa Bgs farfaɗo daga sumar da yayi yanke jiki tayi ta faɗi kasa sumammi ya, da sauri su Ammi su kayi kan ta suna kiran sunan ta chikin tashin hankali “hiyana!!! Hiyana!!! Amma ina shiru ko motsi batayi

    Chikin tsawa Bgs yace “kai dalla kuma mutane shiru Allah yasa ta mutuma kowa ya hu..bai karisa maganar ba green eyes nashi ya sauka chikin idon Abba dake aiko masa da sakon harara miƙewa yayi a fusache ya nufi hanyar fita, kamar daga sama yaji yo muryan Aiman yana sambatu da alama ya farfaɗo juyowa Bgs yayi chikin takun sa irin na jaruman maza ya nufi kujerar da Aiman ke kwanche sai faman sambatu yake

    “Abba kada kamin haka wlh ba zan iya jure wa ba ba zan iya hakura da diyana ba zafi zuciya ta kemin pls Abba ka tausaya min mutuwa zanyi dai dai lokacin Yusuf ya shigo ɗauke da gawar lamrat idon sa yayi jawur sosai kamar wuta gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun miƙe sai wani huchi yake kallo ɗaya zaka masa kasan yana chikin matsanancin bachin rai da tashin hankali

    “Kai Aiman kamin shiru wlh ko na tsine maka dan tsabar rashin zuchiya yarinyar nan zakache kana so” chewar Aunty amarya tayi magana chike da bachin rai da bakin chiki, dafe sai tin kirjin sa Aiman yayi yana juyi kamar zai mutu

    Nan take Bgs yaji zuchiyar na masa zafi chike da ɓachin rai ya ɗago green eyes nashi ya sauke su kan Aunty amarya chikin tsawa da ɗaga murya ya fara magana “wlh idan kika sake magana a palon nan babu abun da zai hana ni kakkarya ki, kashe shi kike son yine yaji da wanne yaji da raɗaɗin chiwon da yakeji ne ko kuma yaji da bala’i in ki!? Shiru Aunty Amarya tayi tana zare ido dan tasan hali Bgs tsab zai iya aikata abun da yace, Ba karamin daɗin abun da Bgs yayiwa Aunty amarya Abba yaji ba duk da tashin hankali da yake chiki sai da yaɗan yi d
    Murmushin jin daɗi

    “Yusuf Ai lamrat bata mutuba tashin hankali ne ya hana ka kane hakan baga hannun ta na motsi ba” chewar Khalid dake tsaye ta bakin kofar shigowa, a sukwane, Yusuf ya kai kallonsa kan hannun lamrat dake ɗan motsi chikin sauri yace “haidar bani ruwa, kasa kasa Bgs yace “karka zuba mata ruwa ka kyaleta ta farka da kanta, ba karamin daɗi Abba yaji ba da alama Bgs ya fara saukowa

    Da gudu Umar ya dawo chikin palon chikin ihu yake faɗin “Abba Allah yayiwa yaya Ahmad chikawa yaya Ahmad ya rasu yanzu shigana ɗaki na samesa ya rasu wani gigitachen tsawa Bgs ya dakawa Umar “akoi wanda ya tambaye kane!!? Yana maganar yana kallon Aiman dake kwache, wani irin juyi Aiman yayi ya kankame kirjinsa da sauri sauri numfashi sa ke fita sai murkusoso yake yana juyi chikin rawar murya da kyar maganar sa ke fita yace “Ahmad ya rasu wayyo Allah wani miƙa yayi nan take hannun sa suka juya

    da gudu Abba ya dawo kusa da shi yasa hannu ya danne kirjinsa ya riƙesa da kyau yasa ɗayan hannun Sa ya kamo kumatun Aiman ɗin ya fara karanto masa kalmar shahada sosai Abba ya sake danne kirjin Aiman ɗin da karfi dan yana son Aiman ya karɓi kalmar shahada, duk dauriya irin na Khalid sai da yayi kwalla da kyar Aiman ya fara karɓan kalmar shahada da Abba ke ta mai mai ta masa, bai kai ga karisawa ba rai yayi halinsa, chikin karyewan zuchiya Abba ya saki kumatun Aiman tare da zame hannun sa daga kan kirjin Aiman ɗin yayi baya baya ya koma ya zauna a gefe duk kokarin da Abba yayi ya danne hawaye sa amma abun ya chi tura nan take kwalla ya fara bin kumatun sa wani na bin wani, gaba ɗaya mutanen palon kuka suke ban da Bgs wadda idon sa suka sauya sukayi jaa sosai kamar wuta ya sunkuyar da kai kasa yana kukan zuchi

    Mutuwar yara biyu lokachi guda wannan azaba dayawa take wai yau me ya shiga gida na ne Alhadulillah Allah na godema chewar Abba Khalid Yusuf duk kwalla suke sun kasa magana, sunkuyar da kai kasa Fahad yayi saboda kwallan da ya chika masa idon, bakajin sautin komai a palon sai sautin kuka da shessheƙa

    Abu ɗaya Bgs yake tunawa shine Aryan, yaya Aryan zai ji lokachin da ya samu labarin rasuwar ɗan biyun sa da kuma Ahmad tabbas Aryan zai shiga tashin hankali mara misaltuwa.

    Kutashi kuje ku shirya asamu a musu sutura mu kaisu gidan su na gaskiya, chewar Abba yayi maganar yana goge kwalla tun Abba bai gama rufe baki ba Bgs ya miƙe chikin sauri ya fice daga palon ya nufi part nashi

    chikin rawar murya Khalid yace “Abba bazan iya zuwa ba bazan iya ganin yadda za’a saka Ahmad da Aiman a chikin kabari ba, bani da wan nan jaruntar ɗago green eyes na shi Yusuf yayi zai yi magana kenan sukaji sallama daga bakin kofar shigowa palon

    Nan take kowa ya daka ta da kukan da yake

    aruɗe suka kai kallon su bakin kofar shigowa kasan chewar sunji irin voice na Ahmad ne, zubur Abba ya miƙe chikin zafin nama Yusuf ya kwantar ta lamrat a kasan kapet ɗin shima ya miƙe, muryan sa har kerma take wajen furta Ahmad daman baka mutu ba!?

    Murmushi yaya Ahmad yayi tare da ƙarisowa chikin palon yace “ban mutuba Yaya Yusuf ina raye Allah ya raya ni kuma ya tai makeni sana diyyar hiyana, gaba ɗaya jama’ar palon suka zubawa Ahmad ido suna juran karin bayani, nan ya fara basu lbr yadda hiyana ta taimaka masa har izuwa yau da ta bashi ruwan addu’a ya sha bayan na sha ruwan adduar da ta bani ɗazun ne sai naji gaba ɗaya jijiyoyina sun rike basa motsi nan take naji numfashi na ya ɗauke daga nan kuma ban sake sanin komai ba sai yanzu nan dana farka naji ni garau kamar ban taɓa chiwoba.

    Alhamdulliah Alhamdulliah kawai mutanen dake chikin palon ke furtawa chikin sanyin murya Abba ya fara magana “yanzu mace mai irin wan nan halinne Safras zai che baya so lallai kuwa da ɗazun ka saki hiyana da ka tapka babban kuskure arayuwar ka” “Abba me kake shirin faɗane wache hiyanar kuma ba dai hiyana da tamin addua ba Abba nifa yanzu ma da kaga nazo palon nan, nazo sanar da kai chewar ina son hiyana ne ina son ta kuma zan Aure ta,

    tirkashi chike da tashin hankali Khalid ya fara magana “Ahmad sai dai kayi hakuri domin hiyana dai matar Bgs che yanzu, kai in ta kai che maka gaba ɗayan mu yau Aka ɗaura auren mu, chikin tashin hankali Ahmad yace “yanzu shike nan hiyana tayi Aure innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunalluhu wani mal wakil, shikenan ba komai nasan haka Allah yaso wai ina Aiman da Aryan da Bgs ne? A sukwane Abba ya ɗago yayi saurin chewa Aiman baya nan yana Maiduguri wajen Aunty farida, juyawa Ahmad yayi yanufi hanyar fita yana faɗin zuwa Maiduguri ya kamani a yanzu nan kenan dan ina matikar son naga ɗan uwana kuma shima nasan yayi kewana sosai zai ji daɗi sosai idan ya ganni yana kai karshen maganar ya fice daga palon ba tare da ya lura da yanayin fuskokin su Ammi ba Allah ma yasa Aiman na kwanche a kujerar bayan ne shiyasa Ahmad ɗin bai ganshiba, dafe kai kawai Abba yayi yana addu’ar Allah ya kawo masu mafita dago ido yayi chikin bada umar ya fara

    “Kar wanda ya kuskura ya sanar da Ahmad rasuwar Aiman yanzu ku kyalesa ya tafi Maiduguri dan musamu muyi jana izar Aiman ɗin, idan ɗaya daga cikin ku yayi kuskuren sanar dashi yanzu tofa za’ayi gawa biyu kunga yanzu ya tashi daga chiwo dan haka ku kyalesa, Abba ya karisa maganar dai dai lokacin da hiyana ta farfaɗo

    Sambatu ta fara yi tana faɗin “wayyo Allah na lamrat ta mutu diyana ta ɓata na shiga uku na dan Allah wadda ya sace diyana ya dawo da ita ya ɗauke ni ko kashe ni ma yake son yi ya kasheni ni dai ya dawomin da yar uwa, wayyo Bappa na Inna ta” gaba ɗaya palon ba wanda bai tau sayawa hiyana ba harta Aunty Amarya wadda yanzu mutuwar Aiman yasa tafara na damar rayuwar ta da abun da tayi

    miƙewa Abba yayi ya koma kusa da ita hannun ta ya kamo chikin nashi murya kasa kasa ya fara magana “hiyana kiyi hakuri kinji jarabawa che Allah ya jarabce mu gaba ɗayan mu kiyi kokarin muchi jaraban nan kinji? Kuma ita lamrat bata rasuba doguwar suma tayi zata farfaɗo nan ba da jimawa ba, diyana kuma zamu gano ta kinji ko? Jin abun da Abba yace yasa hiyana miƙewa zaune da sauri tana faɗin “yanzu lamrat na raye wayyo Allah Alhadulillah Alhamdulliah Allah na godemaka, shiru Abba yayi yana kallon ta tunani yake
    ya wan nan marainiyar Allah zataji idan ta samu lbr yanzu matar Safra che ita mutumin da ya nuna mata tsantsar tsana da kiyayya agaban idon ta, gakiya nayi na damar haɗa wan nan Aure dan nasan mawuyachin Abune Safras yaso yarinyar nan tun da ya furta da bakin sa ya tsaneta gaskiya nayi ganganchin sauri haɗa Auren nan.

    To masu karatu bari mu leko yaya Aryan kuma muga wani wai nar yake toyawa tun da munji yadda Aunty amarya tafara karɓan hukunchi abubuwar da ta aikata hakkin mutane ya fara bibiyan ta

    Maiduguri

    Gaba ɗaya chikin birni da kauye Aryan ya baza sojojin sa ta ko ina an rufe hanyar shige da fice duk in da yake tsammanin zai ga diyana awajen an duba babu ita babu lbr, yashiga tashin hankali mara misaltuwa yama rasa ina zai sanya kanshi bayaji baya gani haka ya baza sojoji ta ko ina anyi sanarwar a gidan redio jaridu gidan Tv amma shiru babu diyana ba lbr Aryan kamar zai zauche wani azaba da raɗaɗi yakeji a zuchiyar sa sai jin faɗuwar gaba yake time to time kuma yana yawan jin voice na Aiman a kunnen sa yana faɗin “ɗan uwana ina kaunar ka ina matikar son ganin farinchi kin ka gaba ɗaya Aryan ya rasa meke damun kwakwalwa sa da take ta tariyo masa voice ɗin Aiman

    To masu karatu dan Allah kumin afuwa wlh ina hanyane shiyasa kuma bani da charji amma idan na isa gida na samu charji to gobe zaku sammu sakon zafafan page har 2 yanzu dai ayi kuskuren baki da wan nan ina ganin addu’oe ku ina godiya

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    *5,YA FITA ZAKKA*
    by(mum Sayyid)

    *Baby*
    By (Mhiz innocent)

    *💫STAR LADY💫*2

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Gidan Aunty Book 1 Page  71-72

    Gidan Aunty Book 1 Page 71-72

    BOOK 1

    Not edited

    Page 71-72
    🔚
    Tunanin abunda ta gani cikin pillow ne ya fi komai d’aga mata hankali, yanxu gabaki d’aya hankalinta ya karkata kanshi, so take tasan ko yana lapiya , wayarta ta soma dubawa ganin batanan ne yasa tayi saurin barin d’akin har zata hau sama sai ta fasa ta sakko kasa , Wanda ta gani akasanne ya bata mamaki bata yadda da hakan ba shiyasa ta ‘kara matsowa dan tabbatarwa kanta ,tabbas ,”shine” ta kara nanawata, da Sauri ta karasa inda yake , a hankali ta kai hannunta kan goshinsa , sanyi goshinsa yayi hankali a tashe ta soma jijjigashi, kuka ta fara ganin abun kamar a mafarki gashi ko motsi ya kasa yi , gabaki d’aya ta rasa abunyi, ruwan da ta gani tayi saurin ‘balle murfin tare da yayya famasa ruwan amma gabaki d’aya kamar ba mutum take yayyafawa ba , rud’ewa ta karayi ga wani irin murd’awa dataji cikinta ya soma yi mata , salati kawai ta soma hannunta d’aya dafe da mararta yayin da d’aya hannun nata yake kan fuskarsa, kuka kawai Tahee take da iya ‘karfinta ganin ko motsi bayayi,rubutun da dada ta batane ya fado ranta da Sauri ta mi’ke duk da tsananin murd’awa da cikinta yake mata , fridge d’inta na sama ta hau cikin Sauri sauri gudu gudu , tana bud’ewa Kuwa ta ganshi, da Sauri ta dauko ko kallan gabanta bata yi, Daidai inda yake ta nufa , cikin Sauri ta ‘balle murfin robar ta soma yayyafa masa kafun ta bud’e bakinsa ta saka masa ruwan kad’an, tari ya fara sosai wani ba’kin ruwa ya fara fitowa daga bakinsa, adduar da oumma ta koya mata ta soma kafun ta fara tofamasa, gabaki d’aya fuskarsa tayi zufa duk da sanyin Ac dake ratsa ko ina na falon, ruwan adduar ta kara saka masa ,yanxu ma tarine ya sarkesa jijiyoyin kansa gabaki d’aya sun fito waje, ta d’au kusan 20 minutes tana masa addua kafin ya soma ajiyar zuciya , gyara masa kwanciya tayi yanda zai ji dadin sakewa . Tsawan lokaci Tahee ta d’auka tana bin kyakkyawar fuskarsa da kallo, a zuciyarta kuwa addua take faman yi masa , dabarace ta fad’o mata, babbar plasma Tvn ta ta kunna tayi connecting, suratul Bakara ta kunna ta saka volume dadda zata dunga ji daka kitchen, kafun ta kulle kofar shigowa part d’in gabaki d’aya , cikin d’auri ta shiga kitchen dan ta Sama musu abunda zasu ci, chips tayi masa tare da pepper chicken , sai omelette din da ta kara yi masa , amaimakon ta had’a coffee yau hakanan zuciyarta bata yadda da kayan coffe din ba shiyasa ta d’ona ruwan tea me cike da kayan kamshi,Lokacin data duba a gogo almost 10:30 tayi , a dinning ta jera musu breakfast d’in kafun ta dawo inda yake , fuskarsa ta soma shafawa a hankali, kusan tsawan 2 minutes kafun ya d’an saki a jiyar zuciya, idanuwansa da sukai masa nauyi ya bud’e a hankali bakinsa d’auke da addua, zuba mata narkakkun eyes d’insa yayi itama shidin ta ke kallo, temaka masa yayi ya zauna kafun ya kalli inda yake da mamaki, kokarin tuna abunda ya faru yake amma ya kasa ,” me yasa na ke kwance anan” ya furta cikin sanyin murya , kallansa Tahee tayi na ‘yan sakanni kafun ta furta “ ka gajine shiyasa bacci ya d’auke ka , ynxu ka tashi kayi Wanka sai muci breakfast “, a gogon hannunsa ya kalla ganin lokaci yayi saurin mikewa tsaye tare da ita a jikinsa, dining din ya nufa dakansa yayi serving abincin a plate, jinsa yake kamar an cire masa abu me nauyi a kirjinsa ga bakinsa kwata kwata ba appetite din abinci,batare da yace mata komai nan ya soma bata abincin abaki har saida ya tabbatar ya isheta, zata bashi yayi saurin kawar da kansa gefe , “ I lost my appetite, and inaso nayi wanka “, kamar zatayi kuka ta kallesa “ ko na dafa maka wani abunne “ murmushi ya sakar mata sosai da ya dad’e beyi kamar saba “ don’t worry bari na fara wanka , okay ?”, a sanyaye ta furta “okay”, wayarsa ya mika mata kafun ya furta “ used it “, tana kar’ba ya juya ya nufi upstairs,kallan wayar tayi na ‘yan seconds hakanan yau take dan taga abun cikin wayar, da pin ajiki abun mamaki tana saka hannunta pin d’in ya bud’e take a wajan hotan ta ya bayyana lokacin da take part d’in Ammey, da Sauri ta shiga photos gabaki d’aya babu hotunansa a ciki sai hotunanta da ita kanta bata san lokacin da aka d’auke ta ba, wasu hotunan bacci take aka d’auketa , hatta lokacin da ta Samu matsalar kai, da ta fara shigowa part d’insa akwai hotunan a ciki, hawaye ne ya fara tarar mata a ido tayi saurin sharesu, soyayyar mijinta na kara shiga cikin zuciyarta , a hankali ta cigaba da kallan hotunan ita kadai tana murmushi.

    ********
    *********** A cikin part d’in Ammey kuwa a zuciye ta fasa wani babban glass d’in jug, gabaki d’aya idanuwanta sun canza Sabida bala’in da yake cinta , sai faman zagaye inda aka kawatashi kamar wajan iska take ko tsoran a ganta bata yi, daga gefe d’aya wannan mutumin da yake yawan zuwa d’akin amrah shima zaune, dukda ba a ganin fuskarsa a yadda idanuwansa sukai ja mutum zai gane yana cikin tsan tsan tashin hankali da bacin rai, a fusace Ammey ta jiyo kan mutumin, “kace mun kasaka kwalbar ban inda ya dace Garin ya akai komai zai lalace lokacin da burinmu yake gab da cika, bazan d’auki a sara ba , bazan d’auka ba , na dad’e da tsara rayuwata , babu Wanda ya isa yace zai lalatamin,zan kashe sa , sannan na kashe duk Wanda yayi run’kurin ruguzamun shiri, kamar ydda nayi rantsuwa da dodo , bazan sa’ba ba dole burina ya cika ,yau ba sai gobe ba zan fara aikina dole na basa babbar kyauta da zai ‘kara ruguza farincikin sa har abadah”, ta karasa zancanta tana sakin wani d’an iskan dariya , taso wa mutuminnan yayi daga zaunan da yake , inda Ammey take ya nufa tare da kamo hannunta d’aya yana shin shinar wuyanta, tsaki Ammey taja tana turesa , a zuciya ta furta “ wannan ba lokacin da ya dace bane , raina a bace yake karka kara batamin, kaje wajan waccan karuwar yarinyar tukunna me zubin arha banza da kasaba latsawa, komai ina sane dashi”, da karfi ya matse hannunta guda d’aya , cikin wata kausash shiyar murya ya furta “ ke baki isa ki hanani jikin kiba sabida ked’in mallakina ne , dole na kashe mijinki dan naga alama yana kokarin shigar mun hanci da kudun duni, yanxu zan barki sabida raina a ‘bace yake , akan duk da haka yau zan kawar da aikina akan d’an talikin can, sannan karki manta dole ki fara aikin boka yanxu, bazan taba yadda jinin da ke cikin waccen shed’aniyar ya fito duniya ba , zuwan shi duniya kamar ruguzama shirin da muka dad’e munayi ne ,inaso a salwantar Dashi cikin ‘kan’kanin lokaci, dan wannan karan bana bu’katar kuskure , kafun na koma kan yan iskan yarancan da suka dawo, suma rayuwar su tana cikin gangara “, ‘karar fad’uwar glass sukaji da Sauri suka juya dan ganin ko wanene, babu kowa a wajan da Sauri Ammey ta nufi inda glass d’in ya fashe , nan ma babu kowa a wajan sai glass d’in sai kuma labulen da aka d’an bud’e da alamun mutum ya tsaya a wajan, cikin tashin hankali Ammey ta ‘kara dubawa babu wa kowa a wajan gabaki d’aya , a’bangaran mutumin kuma yana jin fashewar abu ya d’auki wani Jan zobe ya saka a hannunsa tare da soma karanta wasu abubuwa marada a dad’in ji take a Wajan ya ‘bace gabaki d’aya. Da Sauri Ammey ta shiga cikin falon ta nan ma ba kowa a jan, cikin bacin rai ta d’auki wani d’an karamin aban kifi fari tas Dashi ta buga a kasa tare da caka masa ‘karamin wu’ka ko tsaran azo Atarar da ita bata yi, a kausashe ta soma magana “ inaso a kasheta , sannan aka she mun abunda ke cikinta , sanadin hakan inaso zuciyar mujinta ya buga” sai kuma ta fara ‘kyal’kyalewa da dariya tare da nufar d’akin ta na sa azuciyarta tana ayyana duk Wanda yayi gangancin saurarar magan maganinsu na d’azu to ya kawo kansa Halaka dan sai ta kashe koma wanene “.

    ✨✨✨✨✨✨

    Apart d’in Tahee kuwa har yanxu karatun Alkuranin da ta saka bata kashe ba sai ma ‘kara volume da tayi da Zata hau sama , Hakanan take jin ranta babu dad’i lokaci zuwa lokaci sai ta ta’ba cikinta ,intatuna halin da mijinta yake ciki sai kuma taji zuciyarta na bugawa haka kurum, dakin da yake ta shiga lokacin harya shirya cikin shigar’kananan kaya da kullum yake futo da ‘kyansa da kwarjininsa, ‘kura masa ido Tahee tayi hakanan take ji bata so ta dena kallansa , har ya ‘karaso inda take bata sani ba sai daddad’ar iskar bakinsa me ‘kanshin mint da ya hura mata a fuska,nunfashi ta sauke tare da ajiyar zuciya “ wannan kallan fa ,kamar kina missing d’ina”, bata san lokacin da hawaye suka fara sakko mata a ido ba da ita kanta bata san na Menene ba , cikin tashin hankali ya ri’keta a rud’e ya soma tanbayarta “ me ya faru?, me kikosa?, baki da lapiya ? Cikin ki? Baby…..”, bai ‘karasa ba ta had’e bakinsu waje d’aya , sosai take kissing dinsa kamar me jinyunwar haka , kokarin raba bakinsu yake ta kara had’e lips dinta cikin nashi yau da kanta take basa hot kisses d’in da yake neman zautar dashi,be hanata ba sai ma ‘kara gyara mata tsayuwar ta yayi, tana sakin bakinsa ta soma sunbatar face d’insa ta ko ina, kafun ta rungumeshi tana sakin wani saban kukan,” ya ilahiiiiiiii, please banasan kukan nan yana ta’bamun zuciya please kiyi shiru karki d’agan hankali”, gyada masa kai tayi kafun ta soma share hawayen , kallanta yayi sosai kafun ya furta “ me yasa ki kuka “ ajiyar zuciya Tahee ta sauke , kafun ta bud’e bakinta da yayi mata nauyi “ Nima ban sani ba , kawai banaso ka fita ne yau” murmushi ya saki me d’au sauki yana jan hancinta,” am sorry kinji akwai operation d’in da zanyi wa wani a zuciya , but zan i promise insha Allah zan dawo dawuri,okay ?”, kamar zatayi kuka ta d’aga masa kai ,”oya smile “ ya fad’a yana kara sakar mata wani murmushin, a hankali ta murmusa dukda har zuciyar batajin dad’i sam, “please kaci abinci kafun ka fita “,d’an risina mata yayi kafun ya furta “ duk yadda madam tace “, bata san lokacin da murmushi ya su’buce mata ba sai da ta murmusa, har sukaje wajan dinning hannunsu na sar’ke da na juna , da kanta tayi feeding d’insa a baki har lokaci kuma bata dena binsa da kallo ba , wayarshi da ya bata d’azu ta mika masa , kiss yayi mata a kumatu ka fun ya d’auki main wayarsa dake kan dinning d’in , ko a bakin kofar fita daga falon nasu ‘kin sakinsa tayi har hakan yaso bashi dariya da Alama yau rigima takeji, da ya juya zai fita sai ta ri’kosa ko tace “ zawj amma babu Wanda zaiyi operation din sai kai “, hannunta biyu ya kama kafun ya mayar da ita cikin falon ya dur’kusawa, “ zan dawo ba da dad’ewa ba , yau naga alama rigima kikejii, take care of you and my baby, I love you “, a sanyaye ta furta “ I love you too, kafun ta soma masa adduar data saba yi masa idan zai fita “ har zuciyarsa yaji dad’in adduar da tayi masa haka kurum yaji kamar ya fasa fitar shima sabida kewarsa da yaji ya soma yi lokaci guda Amma ba damar hakan sabida operation d’in da zaiyi.

    A kan kujerar da ya zaunar da ita anan ta kwanta, ita kad’ai ta dungajin kad’aici na damunta , Addu’ar neman tsari ta soma yi a cikin zuciyarta tare da yiwa mijin ta adduar dawowa gida lapiya,tana zaune akan kujerar wani wahalallan bacci mara dad’i ya d’auke ta .

    ✨✨✨✨

    🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

    ABUJA

    A ‘bangaran zarah da khaleed wata irin soyayya suke wa oumma , duk Wanda ya gansu tare da oumma babu me cewa ba Itace ta haifesu ba , sosai Hutu da kwanciyar hankali ya bayyana a jikin oumma ta zama babbar hamsha’kiyar mace , a yanxu Dady ya bud’e mata babban super market da ya zama mallakinta komai na ciki a ‘kasar waje ake kawo mata musamman da dady ya had’a ta da wata matar abokinsa da take zaune a London ita da yaranta, a tsakaninsu sosai Amin ta ya shiga tsakaninsu har ya zam to sun zama ‘kawaye sosai duk da har yanxu hajiya madina bata taba zuwa nigeria sun had’u ba saida ko kaya za a kawo akwai Wanda take sawa ya kawowa oumma da ynxu ake wa la’kabi da Hajiya maryam.

    A yanxu ma shirye shiryen tafiya BUNKURE suke da dady yace zasu kai wa ziyara kafun su wuce saudiya, da farko oumma ta so ‘kin zuwa amma dady ya zaunar da ita tare da yi mata nasiha akan tawakkali da hakuri, duk da yasan macece me hakuri da juriya dan ko shi saida ne. Gabaki d’aya gidan tare zasuje hatta hajiya da itama tace da ita za ‘ayi tafiyar , A kano zasu fara sauka ta jirgi kafun su bi ta mota zuwa BUNKURE .

    Sanye zahra take cikin shigar doguwar Abaya pink colour tare da small fashion bag d’inta fara da shoe din ‘kafarta me d’an tsini shima white colour , tayi rolling da mayafin abayar da ya kasance shima pink colour , babbar wayar ‘kirar iPhone 13 promo max d’inta ita bayn kwabar pink colour ne me d’antan barin barbie, sosai kayan sukai mata kyau, dukda ba wani makeup ne a fuskartaba amma sosai tayi kyau, d’ayan hannunta kuma janye yake cikin medium size trolley bag d’inta. Khaleed ne ya fito shima cikin shigar ‘kananan Kaya d’aya hannunsa shima janye da trolleys guda biyu bayansa hajiya ce itama taci uban adonta na tsofaffi har da ba’kin glass a idanunta. Oumma da dady ne suka fito suma sosai shigarsu ta ‘kayatar, dady sanye yake cikin wani Boyel d’in manyan kaya blue colour da suka ‘karawa fuskarsa dattako da annuri, oumma kuma sanye take cikin wani tsadajjen material pink colour sai adansa flowers me blue da yake jiki, ta kalmin kafarta da Jakarta sai ya kasance blue colour yayin da mayafinta ya kasan ce pink colour , ita kadai sai walwali take , duk inda ta motsa sarkar wuyanta da stone Suma sai sun ‘kada,kallan juna zahra da khaleed sukai , kafin zahra ta karasa wajansa tana masa rad’a a kunne, shima khaleed kamar ‘karamin yaro yayi mata rad’a a kunne suka ‘kyal’kyale da dariya, cikin had’a baki suka furta “ Oumma Wlh kunyi matching sosai 100%”, sun kuyar da Kai oumma tayi cikin jin kunya ganin hajiya a falon tarasa Yaushe zarah zata dena ‘barin bakin nan nata , itama hajiya da ta fuskanci oumma taji kunyar maganar zarah sai tayi shiru batare da tace komai ba , Dady kuwa kanshi kawai ya girgiza aranshi yana tunanin lokacin da zahra zatayi hankali. Basu ‘bata lokaci ba suka d’au hanyar NNAMDI AZIKIWE INTERNATIONAL AIRPORT, cikin sa’a da suka je Airport d’in ma basu zauna ba jirginsu ya tashi zuwa Garin Kano Ta dabo.

    Hour 1 d’aya da mintuna 10 ne ya kawo su Garin Kano , kai tsaye manyan motocin da suke jiran su a Airport d’in aminu Kano Suka shiga , Dadyn da zahra sai khaleed motar su d’aya , oumma kuma ta zauna tare da hajiya, a maimakon su nufi Gidan su na G.R.A kai tsaye hanyar da zata kaisu Bunkure suka nufa , gabaki d’aya oumma sai ta kasa sakewa tuna abubuwan da sukai mata,fahimtar hakan yasa hajiya cikin dattako ta rike mata hannu” karki damu babu abunda zai faru sai Alkairi”, gyada mata kai oumma tayi, mamakin yanda suke bin hanyar tayi wani wajan duk angyarashi ba kamar daba , lokacin da aka shigo layinsu saida gabanta ya fad’i ga Taheer d’inta da ya fad’o mata arai, tun daga layin shiga unguwarsu aka soma bin motocin su da kallo, wasu rayan na bin motar har aka zo bakin kofar gidan su , labari har ya kai cikin gidan cewa ga mutanan Birni sunzo da manyan Mota.mazan cikine kawai suka fito dan sosai rayuwa ta canza musu, suma su kawu sule shida rabi’u kowa yayi jugum jugum Suna jiran abinda zai faru, Dan duk atunaninsu anzo kama d’aya daga cikin sune, su Dady ne suka fara fitowa , tsakanin Rabi’u da kawu sule har yar rigen du’kawa sukai wajan gaishe da Dady, da fara’a a fuskarsa ya amsa musu, su oumma ne suka fito daga mota suma , gabaki d’aya babu Wanda ya gane oumma a cikinsu , kamar yanda suka gaishe da Dady haka suka gaishe da su oumma kafin cike da fargaba kawu sule ya furta “ Allah yasa ba kamamu kukazo yi ba Dan girman Allah kuyi hakuri”, kallan mamaki oumma ta bishi dashi, abunda bata ta’ba gani ba kenan wai magana cikin salama , cikin sakin fuska dady ya furta “ ko zamu iya shiga daga ciki”, d’an shiru sukayi kafun Rabi’u ya furta “ bari na yiwa yan gidan magana “, tun kafin dady ya amsa masa har yashiga gida , cikin ‘kan’kanin lokaci kuma ya dawo” Bismillanku “, su oumma ne suka soma yin gaba kafun su khaleed suka bi bayansu, suna shiga suka tarar da anshin fid’a musu doguwar tabarmar da gaba d’aya ta fita a hayyacinta duk ta zare , bin gidan oumma tayi da kallo gabaki d’aya ya canza mata yanxu babu wannan ‘kazantar, batare da wani ‘kyan ‘kyami ba suka zauna nan tabarmar, ragowar yan gidan kuwa gabaki d’ayansu cun kushewa sukai waje guda a ‘kasa kowa ka gani abun tausayi ba kamar suba, da d’ad’d’ai da d’ad’d’ai suka soma gaishe da su oumma har lokacin kuma babu Wanda ya gane ta a cikinsu, kaka ta bawa ce ta fito cikin d’akinta sai faman d’ingisa ‘kafa take, kallan Oumma ta tsaya yi kamar zatayi Magana kuma ta fasa itama zata tsugunna Oumma tai saurin ru’kota, a hankali oumma ta furta “ kaka tabawa”, itama kaka tabawa cikin dafe ‘kirji tayi saurin furta “Maryama”, gabaki d’aya ‘yan gidan kallan kallo suka fara a tsakaninsu suna tunanin wace maryama ake nufi,murmushi me ciwo oumma ta saki kafun ta furta “Na’am “, ai ba shiri kaka tabawa ta fashe da kuka tana neman yafi yar oumma , abinda bata ta’ba tsammani ba , ‘ko’karin dur‘kusawa take duk da ciwon da ‘kafarta take mata amma oumma ta hanata hakan batare da ‘kyan’kyamiba oumma ta rungumeta a cikinta, suma ‘yan gidan sai alokacin suka gane wacece, gabaki d’ayansu ko wannensu neman yafi yar oumma yake ita dai babu abunda take yai sai murmushi, ta lura Dije da Bintalo basa cikinsu amma bata ce komai ba , saida komai ya lafa kaka tabawa ta soma basu ha’kuri akan basu da abunda zasu basu, sukuwa sai murmushi kawai suke sakarmusu, ‘kara neman yafi yar oumma kaka tabawa tayi kafun ta soma labarta mata irin neman ta da suka dungayi da neman Taheer da har yanxu basu ganshi ba, sannan da irin cin zalin da Dije take gana musu, cikin kuka taka tabawa ta ‘karasa da “ maryama nasan Alhakin kine yake bibiyar mu, na ro’ke’ke da Girman Allah, ki yafe mana , mun gane kuskuren mu”, itama oumma cikin kuka take furta “ Na yafe muku gabaki d’ayanku ,” itama a ta ‘kaice ta basu labarin barowarta gida da Auran ta, abunda yafi baba oumma mamaki yanda suka nuna tsananin farincikinsu babu Hassada, nasiha sosai dady yayi musu da jan hakali cikin hikima da dattako, koda ya kammala hajiya itama sai data ‘kara yi musu nasihar su so junansu da hakuri da juna”, Tashi khaleed yayi, ba dad’ewa aka soma shigo da manyan kayan Aminci tun daga kan shinkafa, makaroni da mai da manja har dasu Dankali da doya da kwai sai da aka ajjemusu, sosai akai musu siyayya hatta oumma siyayyar taso bata tsoro, cikin kuka kaka tabawa ta soma yi musu Godiya da addua , daman tun safe babu abinda suka ci, Dije ta tattara komai na anfanin gidan ta siyar Dashi, hatta gidan tayi ‘ka’karin siyarwa Allah be bata sa’a ba , ta ibi wasu kayanta a cewar ta zata shiga yawan samo kud’i, har lokacin kuwa Bintalo ba a ‘kara ganin ta acikin unguwar ba.

    Gabaki d’ayansu saida Dady yabi ya rarraba musu kud’i akan su ja jari, wasu dubu hamsin wasu talatin, kaka tabawa kuwa dubu d’ari ya bata cif cif . Babu Wanda baiyi nadamar abunda yayi wa oumma ba gashi a sanadinta, mijinta ya temaka musu, itama oumma tsarabar da tayi niyar basu tasa aka rabasu, Atampopi mazan kuma shadda, hatta hajiya kaka sai data bawa kaka tabawa tsarabar kujerar makka , so kaga farin ciki wajan mutanan gidan kamar su akai wa albishir, itama oumma sosai taji dad’in canzawarsu ko ba komai an zama ‘yan uwa yanxu, ko da zasu tafi har bakin ‘kofa suka rakosu suna yi musu addua , ba ‘karamin dad’i oumma taji ba harda hawayenta da zasu rabu, aranta kuma tana Adduar Allah yasa shima Taheer yana cikin ‘Koshin lapiya a duk inda yake, basu d’au dogon lokaci ba suka kama hanyar komawa Kano dan gobe da sassafe jirgin su zai tashi zuwa ‘kasa me tsarki.

    ✨✨✨✨✨✨✨

    1:29pm Tahee ta farka a firgice sabida mummunan mafarkin da tayi, da Sauri ta janyo wayarta tare da dialing number d’insa amma abun mamaki switched up ake ce Mata abun da bai ta’ba faruwa ba , ‘kara dialing number tasa tayi the same abinda ake ce mata kenan, ajiyar zuciya ta sauke data Tuna cewa zai may be ko yana cikin theatre har yanxu, ganin lokacin sallah na tafiya ne yasata mi’kewa ta nufi d’akinta.
    Tana idar da sallah wanka tayi cikin material d’in me rawa black colour , ganin babu Wanda ya shigo part d’in harsu ihsan yasa ta saka wayarta kawai a aljihun kayanta , tare da rolling d’in mayafinta da niyyar zuwa part d’in Dada.

    Lokaci d’aya gabanta ya yanke ya fad’i, ga wata irin iska data soma ratsa mata zuciya kamar ana cire mata wani sassa na jiki, hannunta dafe da zuciyarta ,gabaki d’aya yau ta rasa me ke damunta lokaci zuwa lokaci Babynta na fado mata arai ganin haryanxu be kira taba .

    A ‘bangaran king kuwa a hanyar dawowansa
    Gida ,lokacin da yake driving dan yau shikad’ai yafita dan dakansa yake driving yau, hatta zaki yau be fita dashi ba ,Daidai Lokacin da ya yanki kwanar Area d’in babban titin da zata sadashi da banana Island wata babbar trolley data ‘bullo tayo kansa gadan gadan, ‘ko’karin Jan burki yayi amma sai burkin ya kwace take a Wajan babbar trolley d’in tayi sama da motar da King yake ciki tare da fad’owa duk ta rugurguje. Driver ciki na ganin hakan yayi saurin d’aga wayar sa dake ringing kafun ya furta “Angama sir “ sai kuma yayi saurin Jan trolley d’in da gudu ganin a ‘ko’karin tsayar dashi.

    Wasu matasa biyu da akai abun kan idan su ne sukayi saurin ‘karasowa inda motar king take kafun su kira jami’an ‘yan sanda ,ganin yadda motar ta lotse , wani card da d’aya daga cikin samarin ya ganine ya d’auka kafin yayi dialing number , Daidai lokacin dasu Abeey suke zaune a falon dada kiran matashin ya shigo wayarsa , haka kawai zuciyarsa ta tsinke kamar ba zai d’aga ba sai kuma ya d’auka , tun kafin yayi magana Matashin saurayin ya sanar dashi Accident d’in king duk da be tabbatar da alakarsu ba , “ babu abunda Abeey ya ke furtawa face Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, cikin gaggawa ya bada umarnin akaishi NAHYAN hospital ko sauraran su dada dake tanbayar me ya faru be yi ba , cikin tashin hankali suka nufi asibitin lokacin har manyan likitocin asibitin sun shiga da shi Emergency Room, tsaro sosai Abeey ya sa a saka a cikin asibitin gabaki d’aya , dai dai lokacin da uncle musaddiq da uncle saleem suka karaso cikin tashin hankali suma , sun fi 2 hours tsaye a bakin emergency room har lokacin kuma likitocin da suka shiga basu fito ba sai abubuwan da nurse ke ta faman d’akkowa. Umarni ya bama uncle saleem da yaje ya d’akko su Dada amma kar a fada musu condition d’in da king yake ciki sai sunzo. Hakan kuwa akayi yana zuwa ya tarar dasu ashirye hakanan komai ummey asanyaye take yinsa , ga wata iska da take ratsata kamar lokacin data rasa Moha d’inta ,ga baki d’aya da mutanan gidan aka tafi ban da tafi dake fama da fad’uwan gaba lokacin.

    Suna shiga asibitin saura kadan jiri ya kwashe ummey, Ammey kuwa sai faman murmushi take saki a fakaice da mutum ya kalleta kuma zaiga Tsantsan tashin hankali akan fuskarta . Lokacin da suka samu labarin accident gabaki d’aya mutuwar tsaye sukai, ummey kam yau ta kasa daurewa tazo zata fad’i Abbey yayi saurin ri’ke ta hakan kuwa ba karamin bacin rai ya saka Ammey, gabaki d’aya ita sai ta nuna tafi shiga zamuwa Dan har faduwa kasa saidatayi gabaki d’aya kowa hankalinsa ya tashi, ganin babu Tahee a cikinsune Dada ta bata umarnin Mamy Matar uncle musaddiq suje su d’akkota, Aunty kam yau itama ta shiga damuwa ko ba komai ba shi ta tsana ba Tahee ta tsana, yan matan gidan ma kowa sai faman kuka take a cikinsu .

    ****A ‘bangaran Tahee jitayi gabaki d’aya zaman gidan ya isheta babu abunda takeso kamar tajita a waje ,da Sauri ta zabura cikin Sauri ta nufi hanyar fita daga part d’inta , babu inda take kalla sai hanya duk da duhu ya farayi, abun mamaki har tazo gate d’in farko babu security Sabida lokacin sallah yayi, a gate na biyu ne yake da tsaro amma duk cikin su babu Wanda ya hanata fita harta fice daga gidan mutane biyu ne sukayi run’kurin tsayar da ita amma babu Wanda ta kula a ciki, tana ganin ta Fita daga gidan kuma lokaci guda ta saka gudu , gudu kawai take abunta ita kanta batasan hanyar da take biba. Su mamy na zuwa suka samu wannan mummunar labari, gabaki d’aya an duba gidan bata ciki, har layin gidan kwata kwata babu Tahee babu alamarta , Gabaki d’aya bincike aka soma , lokacin da d’aya daga cikin masu tsaran ya fad’awa zaki abunda sukayi take a Wajan ya dakatar dasu daga aiki gabaki d’ayansu mutane kusan goma sannan yasaka wasu tsaran da suka fi wanda ya bari, sosai a ka shiga binciki.

    Su mamy na barin hospital d’in wani doctor Armeen ya fito daga cikin ER sai faman had’a gumi yake , ba Wanda be san Abeey ba shiyasa dakansa yayi wa abeey jagora zuwa office d’insu, cikin girmamawa ya soma bawa Abeey hakuri kafun ya sanar dashi King ya shiga COMA, alokacin kuma Mamy take sanar dashi neman Tahee da akai aka rasa, gabaki d’aya kuma sai kowa ya ‘kara har gitsewa musamman ummey da Ammey da suka yanke jiki suka fad’i lokaci guda, dada ma kuka kawai ta saka babu abunda take cewa sai Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, cikin gaggawa Abeey yasa a binciki duk inda take anemota kafun ya sanar wa da commissioner da kansa akan abincika masa duk inda take anemo ta cikin gaggawa , shima gabaki d’aya ya shiga damuwa , yana tsoran halin da King zaishiga idan yasamu labarin ‘bacewar matarsa

    ******
    SHIN KING YANA TASHI DAGA COMA?
    GA TAHEE DA TAKE DA CIKI TABAR GIDA KO INA ZATAJE?
    SHIN ZASU KARA GANINTA ?
    INA TAHEER ?
    INA DIJE DA BINTALO?
    WANENE MUTUMIN DA YAKE MAGANA DA AMMEY?
    WANENE YAJI ZANCANSU LOKACIN DA SUKE TATTAUNAWA?
    SHIN SU OUMMA ZASU KARA HADUWA KUWA ?
    INA YAYAN OUMMA DA AKACE YA BAR GIDA?

    Alhamdulillah anan na kawo karshen littafin GIDAN AUNTY BOOK 1 .
    Ina rokan Allah kamar ydda na fara littafin nan a sa’a ya bani ikon kammala shi.
    ALHAMDULILLAH
    ALHAMDULILLAH
    ALHAMDULILLAH…

     

     

     

  • Gidan Aunty Book 1 Page  61

    Gidan Aunty Book 1 Page 61

    BOOK 1
    Page 61

    Tsayawa yayi a inda yake gabaki d’aya hankalinsa ya gama tashi ganin ta da wuka a hannunta, kalaman dazu take ta kara maimaitawa,gyada mata kai yayi shima “ ok zamu rama muma amma bani wukar nan tukunna”, kin bashi wukar tahee tayi saima fashewa da wani saban kukan tayi, jikinshi har rawa yake dan ya gane ba ita kadai ce ba, tsoransa karsu cutar da ita, sunan dazu da ta kira ne ya fado masa kafun ya kalli yanda take faman hada gumi duk da sanyin Ac dake fitowa, bayanta ya kalla kafun ya furta “NONNA”, da sauri ta juya tana sakin wukar hannunta, yana gani ta juya taku biyu yayi ya damki Dan tsan hannunta, kara ta sakar masa sai faman fusge fusge take ita kadai, wata iriyar gigitacciyar tsawa ya daka mata yana hade fuskarsa kamar bashi ba, “ki nutsu”, ya furta cikin kausashshiyar murya , nutsuwar kuwa tayi tana sun kunyar da kanta, “ ya sunanki “, shiru tayi tana kara sunkuyar dakanta, “karki bari na sake maimaita tawa “, cikin shashsheka ta furta “sunana LOLA”, dan kallanta yayi jin tayi magana da wata iriyar murya”wacece ke , me yasa kika shiga jikin mata ta”, yanxu ma shiru tayi masa, bece komai ba kafun a cikin dan daga murya yayi Bismillah, rawa jikinta ya fara ,” ah ah zanyi magana ka bari dan Allah “ ta fada cikin rikicewa, banza yayi mata kafun ya fara karatun alkuranin, yanxu kam ihu ta sa masa tana rokonsa karya konata, zaunar da ita yayi kan kujera har yanxu hannunsa na rike da nata kafun ya dakko wani bottle water da ke gefensa ya ajje mata a gabanta, da sauri ta saka hannu zata dauka ya matsar da ruwa nesa da ita “ ruwa , ruwa “ ta fara fada , “zakisha”, ya furta , bata jira ba ta amsa masa da Sauri” zan baki ruwa idan kin gama amsamun tanbayoyina, sabanin hakan kuma zan kona kine “, wacece ke, me yasa kika shiga jikin matata”, cikin wata iriyar murya ta fara kuka , “ ba cutar da ita nake ba, te makonta nake, suna san Kasheta ne kamar yanda suka kashe mun ahalina”shiru yayi na yan sakanni kafun cikin kausashshiyar murya ya furta “Menene hadinki da matata, sannan menene alakar ku da matata da zaki shiga jikinta”, ina bata kariyane kamar yanda Nima ta taba temakona a lokacin baya,ni ba muguwa bace, suna harin rayuwar tane”, su wanene” da mugun firgici ta kallesa , zasu kasheta kamar yanda suka kashe shi, bazan iya va”,wani irin rawa jikinta ya fara,”ruwa !!ruwa!!”, ruwan ya dakko kamar yanda ta bukata amma be bata ba,”banasan jin wannan tatsuniyar taki, kar na sake ganin ki a jikin matata, idan va haka ba zan konaki da ayoyin uban giji, ki gaggauta fita daga jikin matata yanxun nan”,kanta ta daga masa tana rike makoqwaranta, ruwan ya mika bata da mugun sauri ta fara sha, saida shanye duka kafin ta fara sakin ajiyar zuciya,”zan fita daga jikinta, Kai ma nagode da yanda kake kular mun da ita,nasan kana kula da ita amma ka nunkashi sabida kokarin kasheta da suke yi, ganin komai nasu ya fara lalacewa,ka kula da ita “, tana gama fadar hakan tahee tayi atshawa me karfin gaske,kafun ta sulale ta fado kan king da yayi saurin tarota, cikin zafin nama ya dauke tare da kaita cikin bedroom, kallan yanda take bacci peacefully yayi, kokarin kawar da tunanin yun kurin kashe masa mata da akace yake, iska ya furzar a hankali kafin ya furta “ it’s a lie”. System dinsa ya dauka bayan ya canza kayan jikin sa, ya jima yana operating a kanta,lokaci zuwa lokaci yana kara dubata duk da yana kusa da ita, kiran sallah la’asar ne ya tayar dashi, kan gadon ya karasa har yanxu bacci take peacefully abinta, goshinta ya danyi pecking kafun ya bar dakin.

    Mintuna 15 da futarsa ta fara motsa idanuwanta kafun ta budesu gabaki d’aya, mamakine ya kama ganin ta kwance akan gado, wayar da akayi mada da text message ne kawai ya fado kanta, duk yanda zata tuna zuwan ta kan gadon ta kasa, sakkowa tayi daga kan gadon bakinta dauke da addua, agogon dakin ta duba, 4 ta wuce da sauri tashiga toilet kafun ta fito ta kabbara sallah , tana Idarwa azkar dinta tayi kafun ta mike , kara kallan agogo tayi mamakinta har yanxu be dauke ba ganin be dawo gida ba, dan karamun bakinta ta turo waje kafun ta bar dakin, shima falon shiru alamar ba kowa a ciki,3rd floor ta hau nan ma shiru sai ac da kamshin turaran da ke buso dakin,dacin da bakinta ya somane yasata nufar fridge din data gani, tana budewa kuwa idanuwanta ya sauka kan kayayyakin ciye ciye dake shake a ciki, fiye da saurin fridge din, wani abun ma bata taba ganin saba, strawberry ice cream din data ganine yafi daukar hankali, janyoshi tayi tana sakin wani murmushin jin dadi, waje ta samu akan gado tana shan ice cream din, tana sha tana sakin dariya sabida yanda dadin ke ratsa mata kwakwalwa, idanuwanta ne suka sauka kan wata yar karamar roba dake kan bedside dinsa, ajje Ice creams din tayi tana janyo robar “ANTI DEPRESSANT” shine abunda aka rubuta jikin robar, har zata mayar sai kuma ta fara karanta abunda ke jikin robar, da wani irin shock ta mike tsaye, tana karanta abunda ke jikin robar, wasu hawayene suka fara sakko mata kawai ta fada kan gadon ta fashe da kuka , saida tayi me isarta kafun ta mike dauke da robar a hannunta, zata bar dakin kenan shikuma yana shigowa da sallama a bakinsa kasa kasa, cikin zuciyarta ta amsa sallamar tasa fuskarta kwata kwata ba fara’a, kallan yanda fuskarta ta dan tashi yayi kafun cikin sauri yayi yunkurun nufar inda take”what’s wrong with my baby”, hannunta d’aya ta nuna masa alamar ya dakata karo na farko a rayuwarta, da wani irin expression yake kallanta, be gama tunani ba ta dago robar drugs din dake hannunta, “ Menene wannan”, ta fada tana zuba masa idanuwanta da suka kara haske sabida kukan da tayi,wani irin harbawa zuciyarsa yayi” sam ya manta daya sha drugs din ya barshi a fili”, cikin dan daga murya kamar ba ita ba ta furta “ maganin Menene wannan kakesha “, kokarin matsota yake ta kara dakatar dashi” please calm down, am sorry I will explain”, bata san lokacin da ta buga robar a ‘kasaba maganin ciki ya zube” me yasa , me yasa , I thought Dagaske kake da kace kana sona, i though da gaske kake da kace kai dady nane, kana shan wancan pills din dukda kasan illar su, u’re a doctor, I thought ka d’auke ni a matsayin matarka, Aushe nayi kuskure ba haka bane, you’re taking this drugs to…. to…”, ta kasa karasa zancan nata sabida wani saban kukan da yake kokarin zuwan mata tana dannewa, wani irin shock ne ya dake shi, jin kukanta yake kamar ana kara cakarshi da maki a zuciya gabaki d’aya ya rikice , cikin sanyin murya ya furta “ please don’t be angry, I will explain “, manyan eyes dinta ta zuba masa hawaye na sauka akan idon nata” bana bukata” kawai ta furta tare da barin dakin, wani irin jirine yaji yana neman kayan dashi yayi saurin samun waje ya zauna , ga baki daya hannayensa ya tusa cikin gashin kansa yana ya mutsasu “ I’m in a big mess , she’s more angry than ever”, ya rasa Wana irin tunani zaiyi , bayaso koka d’an tayi fushi dashi dan bazan iya daukan fushinta ba, da sauri ya mike ya nufi bayanta, yana shiga ya tarar da bata cikin bedroom dinta, ragowar bedroom din second floor ya duba , shima duk bata ciki, muryar da ya fara ji sama sama a falon kasane yasashi nufar falon kai tsaye, TAHEE ce a falon tare da su sumayya da suka zo falon, wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana binta da kallo , adaidai lokacin da ta daga idanuwanta itama, tana ganinshi ta d’auke idanuwanta fuskarta a dan hade kadan ta yanda su Ihsan bazasu gane ba.” Oh my god “ ya furta cikin zuciyarsa har yanxu ya masa dauke idanuwansa akanta, su firdausi na ganinshi suka kara gaishe ganin yanxu yana amsa musu gaisuwarsu bakamar daba, kanshi ya dan daga musu alamar amsawa dan kwata kwata ba shi yake bukata ba,so yake ya rungumeta, ya lallasheta ko zata dena fushi dashi, he want to feel her warm , he can’t take it”, satar kallansa ihsan tayi ganin yanda ya tsaya gabaki d’aya hankalinsa na kan tahee dake dannawa waya,murmushi ta saki kafun ta kalli tahee,” sister yau dai bari na cika miki alkawarin Pam cake din ki”, bata jira amsar tahee ba ta mike ta nufi kitchen, firdausi da sumayya ma duk sun ankara dashi dan haka da sauri suma suka mike “muma bari mu tayaki” dukansu basu jira jin amsar taba sukayi saurin guduwa , bece komai dan Hakan yake bukata, ganin ta tashi zata bi bayansu yayi saurin shan gabanta, hannunsa biyu yayi hade alamun pleading, dauke kanta tayi daga kansa zata wuce yayi saurin riko hannunta, fisge hannun tayi kafin ta furta “ don’t touch me again “, tana gama maganarta tayi upstairs, waje ya samu ya zauna kansa na sara masa, gabaki d’aya launin idanuwansa ya canza Sabida yanda yaji xuciyarsa na masa zafi, ya dau tsawan lokaci zaune a kan kujera kamar ya bita amma yana tsoro karta kara wani fushin, ganin lokacin sallah yayi ne yasashi barin part gabaki d’aya .

    Aban garan su ihsan kuwa suna shiga cikin kitchen din suka kulle kofar, kwai kwayar yanda suka ga king na kallan tahee suka fara, “wayaga Romeo and juliet “ cewar ihsan , dariya suka saki gabaki d’ayansu, kan kujerun dake kitchen suka zauna suna dasa saban hira , daman space suka basu kar king ya koresu, sun dade suna hira abunsu kafun su fito falo, ganin babu kowa ne yasasu sakin ajiyar zuciya , da Sauri ihsan tayi hanyar kofa ,kallanta sumayya tayi alamun karin bayani” kun manta pan cake mukace zamuyi mata, tana fitowa kara zaunar da mu zatayi , ni kuma ban shirya shan masga ba Wajan yaya”,ga baki daya basu yi wannan tunanin ba, gudun karta fito tazo ta samesu sukayi saurin barin part din.

    Tahee kuwa tana shiga daki wani saban kukan tayi kafun ta shiga ban daki, Wanka tayi ganin ana kiran sallah tayi alwalarta, ta kabbara sallah bata bar daddumar ta ba sai da akayi isha’i, wasu English wears ta saka masu daukar hankali blue colour , cikakken gashin kanta ya sakko har bayanta duk da hular da ta saka, wani irin masifaffen kyau tayi na musamman amma fuskarta har yanxu a cin kushe take, Fararan hannunta da yan yatsunta sun fito fes da masu musamman da kunshin hannunta ya kara fito da farinsu,Daddadan kamshin turaran princess ne ke tashi a cikin dakin ta ko ina, message din data gani akan wayarta ne ya sata sakin baki “ sorry sis karkizo kiga bamanan ummey ce ta kiramu”, ba kowa bane ya tura mata text din face ihsan, hararar wayar tayi kamar suna gabanta,kafin ta fito daga dakinta, karo suka ci da king da gaba daya yanayinsa ya canza, kallo daya tayi masa kafun ta d’auke kanta “ sannu da zuwa “ ta furta zata bar wajan, ya rungumota ta baya yana sakin ajiyar zuciya, cikin disashewar murya kamar mara lapiya ya furta “ I can’t take it any more , please am so sorry, bayanda Kike tunani bane,” raba jikinta tayi da nashi kafun ta furta “ your dinner is ready”, am not hungry, ya furta yana binta da kallo, bata kuma ce masa komai ba tayi wucewarta kan dining, apple ta dauka guda daya ita ma, ta wuce dakinta, zuciyar ta na raya mata ta kallesa amma ta danne, tana barin Wajan ya dafe kansa dake sara masa, tayi masa kyau sosai yau , and he don’t like her frowning face, cikin sanyin jiki ya nufa dakin shima , yana kallan yanda take shan apple dinta cikin kwanciyar hankali, bece mata komai ba yace toilet,ya dade a ciki bayan ruwan sanyin da ya sakar wa kansa, ganin zazzabin nasa na kara yawa ne yasashi kashe ruwan, shima wasu kayan bacci ya dauka white colour masu kauri sabida yanda yake jin sanyi, turare kawai ya fesa ya fito, yana fitowa yatarar da fitula aka she sai lamp din da aka dan kunna, sai tun zuciyarsa ya rike yana cije lips ,sallar da ya saba yake so yayi amma ya kasa sabida ynda yake jin jikinsa, a tunaninsa tayi bacci ne shiyasa ya na hawa bed din ya janyota jikinsa yana sakin ajiyar zuciya,kara rungumeta yayi kamar wacce za a kwace masa ita, tun lokacin da ya rungumeta ta bude idanuwanta ga zafin jikinsa dake ratsa nata jikin,tausayi ya bata kamar tayi magana sai kuma tayi shiru har bacci ya dauketa, “ am so very sorry “ yake fada a cikin zuciyar sa….

    Mss Lee 💖

    GIDAN AUNTY
    07041879581

  • Gidan Aunty Book 1 Page  70

    Gidan Aunty Book 1 Page 70

    BOOK 1

    Page 70

    Lallashinta yayi har tayi shiru bayan ya gama dressing din kwalbar da ya shigar mata kafa, wayansa ya dauka da niyar kiran Ammeey tayi saurin dakatar dashi ,bata san lokacin da bakinta ya furta me zaka mata, d’an kallanta yayi shima na ‘yan second kafun ya furta yaja hancinta kad’an “ wani kunun ayar zansa a kawo mana”, ita kanta bata san lokacin da take wani abun ba “ No kabari gobe zanyi maka wani kajiii babyn? Ynxu bari na fara temaka maka kayi wanka sai kaji abinci ,okay? Kanshi ya d’aga mata alamar toh kafun ya kuma cewa “ but bari na saka a kawo mana wani kunun aya , Kema ai naga kina san kunun Ammeey” no kaji ka fara yin wanka already na hada maka another juice please ni yunwa mukeji nida babyn ka fa “,cikin ya ta’ba kafun ya saki wani ajiyar zuciya “ toh ayiwa dady hakuri yanxu zakuci abinci” yana kai karshen maganar sa yashi ya nufi kofar da zata sadashi da ban dakinsu, ajiyar zuciya Tahee ta sauke cikin zuciyar ta kuwa cewa take “ Allah ya tsare na karacin abincin shaid’aniyar iblisarcan, Wanda naci a baya ma a rashin sani ne , muguwa me kama da kwarkwata, ta Allah ba taki ba “, gudun karya sakko ya tarar da abun kunun yasa tayi saurin fita daga d’akin, Daidai inda kunun ayar yake ta nufa , a bun mamaki amaimakon ta samu kunun ayar sai wani ‘bakin ruwa da ta samu, addua ta soma yi cikin xuciyarta, kafun taje ta dakko Mopper ma gabaki d’aya ruwan kunun ayar ya kuma komawa ba’ki , karfin adduarta ta soma tun tana yi a zuci haka ta cigaba dayii ita kanta bazatace ga adduar da take karantawa ba, da Bismillah ta fara goge ba’kin ruwan harta kammala, tare da kunna karatun alkurani yanda bazai damesu ba , tana cikin Kimtsa falon ya sakko ‘kasa shima cikin shigar kayan bacci blue colour masu Taushin gaske , serving Dinsu abincin tayi atare suke feeding din junansu har suka kammala , a kan 3sitter ya zauna ita kuma ta kwanta akan cinyarsa tana wasa da sajanshi “ babyn” ta kira sunansa a hankali kamar me rad’a , kallanta yayi alamar na’am duk da ne bud’e baki yayi magana ba “ wacece Ammey a wajan ka “ wani lallausan murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa da ya kara kawata kyawun fuskarsa har hakan yaso bata mamaki, mi’kar da ita yayi zaune tare da kamo hannunta Suka nufi d’akinsa ta lipter , zaunar da ita yayi akan sofa kafun ya bar d’akin , mintuna kad’an kuma ya dawo hannunsa d’auke da wani karamin white box’s,budewa yayi take a wajan wasu hotunan Suka bayyana duk da darewarsu amma babu abunda ya samesu,” sorry laifina ne da har yanxu baki gama sanin Tarihin mijinki ba,nasan kinsan full name dina , amma still zan kara fad’a TAHNOON ZAYED AL_NAHYAN, mumu 4 ummey ta haifa Akheee moha shine babba Allah ya masa rasuwa ,sai ukhtiii next tomorrow itama zaki ganta , sai ni sai kuma auta zoya , tun ina ‘karami na nake ‘bangaran Ammey sabida yanda take nunamun soyayya da wata shakuwa ta musamman komai ta samu ni zata fara bawa kafin ta bawa kowa na gidan har hakan ya kara sha’kuwa a tsakaninmu, soyayyar da take munne yasa sau da dama mutane sai su dunga d’aukar cewa ita tahaifeni sabida wani irin shakuwa da yake tsakanina da ita, part d’in ammeey na dawo cikin abinci, komai nawa a part din Ammeey nakeyinsa, hatta kwana a part d’in ammeey nake yi har lokacin tafiyata waje karatu, acan turkey na kammala karatun likitancina, har na kammala at time moment…” sai kuma yayi shiru yana runtsu idanuwansa , itama kallansa tayi sabida wani irin tausayinsa da ya mamayeta, tabbas ba karamin cutar dashi Ammeey tayi ba , hannunta d’aya ya dam’ke cikin nasa ,” At That moment, mukayi accident da Akhi , and at the same time motar da muke ciki ta kama da wuta , duk yanda nayi kokarin cecensa na kasa , ina jin zafin hakan every single day idan na tuna na kasa cetan best brother , I can’t save him, na kasa cetansa , agaban idona wuta ta ‘konashi” ya karasa zancansa kamar nunfashinsa zai d’auke , rungumeshi Tahee tayi tana fashewa da wani irin kukan tausayinsa , tabbas idan Ammeey zata iya ‘kona mutum da ransa toh tabbas zata iya yin kome tace ,a zuciyar ta kuwa fad’i take “Ammey kin cuci rayuwar mu, kin rusa mana farincikin , tana zan iya sanar Dashi kece kika kashe masa d’an uwa, kika rabasa da mahaifiyarsa”, shafa bayanta yake a hankali cikin rad’a rad’a ya furta “ banasan kukan nan naki idan ba so kike Nima nayi ba , duminki kawai nakeso,zuciyata ba dad’i inasan farin cikin matata “, ya karasa kalmar matata Tahee ta had’e bakinsu waje d’aya, duk yanda taso tsayar da hawayen fuskarta ta kasa , wani irin deep French kiss take basa, gabaki d’aya ta mantar dashi abunda ke damunsa, light din dakin king ya kashe kafun yaja bargo ya lullu’besu sabida sanyin da yake busosu…..

    After 2 hours kwance take a jikinsa gabaki d’aya taki yarda su hada ido, “ a ina kika samo wannan karatun, I like it please kunyarnan ta tafi haka tana cutana fa “bugun kirjinsa tayi a hankali amma dukda haka saida yace ouuuush, yana kara rungumeta a jikinsa , lumshe idanuwanta tayi kamar me jin bacci Amma sam ba baccin take ba , tunanin yadda zata tona wa Ammey asiri kawai take a cikin ranta, tana cikin tunanin bacci ya d’auketa, forehead d’inta ya sumbata kafun ya ‘kara rungumeta a jikinsa, abubuwanda Suka faru tsawan shekarune suka dawo yawo akansa, babu inda ya fi tsaya masa arai kamar mutuwar d’an uwansa, ganin yanda jijiyoyinkansa suke ‘ko’karin ta shine yasa ya soma adduar tsari cikin zuciyarsa , ya d’ad’d’e yana addua kafun yayi nafila akan rokan Allah ya sassauta masa abun da yake ransa kafun shima ya kwanta yana kara rungumota a jikinsa.

    ********
    ✨✨✨✨✨

    WASHE GARI king yana tafiya masallaci itama Tahee ta Tashi tayi sallarta, bacci take ji sosai shiyasa ta koma zata kwanta, a side d’in hagun da king ya fi kwanciya a gefen ta kwanta , hannunta d’aya ta zura ta karka shin pillow sa yanda zataji dad’in kwanciya sai taji abu kamar yana tokararta, gyara kwanciyar ta tayi yanda zata fi jin dad’in baccin nata amma still tanaji kamar abu na sukarta, ni’kewa zaune tahee tayi tare da yunkurin canza pillows din, hannunta ne ya sauka akan tsakiyar pillow d’in hannunta , da Sauri ta janye hannunta tana karantar addua, wajan ta kara ta’bawa amma still tanajin kamar akwai abu a wajan, cikin rashin tsoro ta kara kai hannunta wajan still har yanxu tana jin abinda takeji, rigar pillow d’in ta yi saurin zazzagewa kafun ta kara taba wajan, still dai abun na Wajan, cikin Sauri ta dauki pillow d’in ta nufi d’akin ta dashi, reza ta fara nema cikin sa’a kuwa ta samota, bakin pillown ta farka duka kafun ta zazzage abinda yake ciki, ‘karamar kwabace ba’ka ta bayyana a cikin abin cushion d’in, bakinta d’auke da Bismillah ta bud’e kwalbar, wani haya’kine ya fito daga cikin kwalbar ba’ki’kirin da shi ,Addua Tahee ta fara da ‘karfi cikin ‘kan’kanin lokacin kuwa haya’kin ya bace gabaki d’aya . A Daidai lokacin da wannan kwalbar ta fad’o a daidai lokacin kan king yayi mugun sara masa , ga wani jiri jiri da ya soma d’aukarsa, part d’in ammey zaishi amma ya fasa ya nufi nashi part d’in, yana shiga cikin falon sa ya fad’i kasaaaaa..

    #MANAGE
    GIDAN AUNTY
    07041879581
    MSS LEE 💖

    MAI BUKATAR KARANTA GIDAN AUNTY HAR KARSHE YA TUNTUBENI TA NUMBER TA .