Blog

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 22

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 22

    Book 2

    Page 22

    Uk 1am

    Tana kwance saman katafaren gadon sa ta kasa barci duk bayan minti ɗaya sai ta duba time shiru shiru Bgs bai dawo ba tun abun baya damun ta har ta fara shiga damuwa miƙewa tayi zaune saman gadon tana tunanin ina ya tafi Allah dai ya sa lfy tun da sukazo gidan nan bai taɓa wuce 12:10am a waje ba shin me ya daɗar da shi yau, gajiya tayi da zama ta miƙe tsaye ta fara kai kawo tunawa tayi ɗazun ta kalli waya a saman table ɗin da yake ajiye ta kardu da system nashi da sauri ta nufa wajen tana addu’ar Allah ya sa akoi sim a chikin wayar,hannun ta har karma yake wajen ɗaukar wayar ta kunna haske screen ɗin,wani Cool murmushi ta saki lokacin da ta ga akoi sim a chiki already ta haddace number sa a kai chikin sauri ta shigar da number ɗin sa chikin wayar burinta kawai ta kira shi batayi tunanin me zai je ya dawo ba, sau biyu tana kiran wayar sa bai ɗaga ba sai a na uku ya ɗaga tattara nitsuwar ta tayi gaba ɗaya chikin sanyin murya tace “ina wuni yaya Prince” shiru yayi na ɗan lokacin kafin yace “me menene!? “Babu komai daman naga baka dawo bane har yanzu shine nace…. Bata kai karshen maganar ba ya daga tar da ita ta hanyar chewa “kawomin black tea ɗakin bincike” “yaya Prince ban san ɗakin ba ai”guntun tsaki yaja kafin yace “ki fito palo awajen da ake ajiye remote ki duba zakiga farin remote ki ɗauka ki sai ta sama ki dan na open stair case zai sauko sai ki haura ina wajen” yana gama faɗin hakan ya katse kiran, murmushi ta saki kafin ta ajiye wayar ta fice daga ɗakin

    Kitchen ta nufa ta haɗa masa black tea kamar yadda ya buƙa ta ta dawo palo kamar yadda ya sanar da ita haka tayi, tasha ruwan mamaki lokacin da ta ga wani ɗan siririn stair case na saukowa bayan ta danna remote,mutun ba zai taɓa zaton akoi wani abu a saman nan ba wai shi stair case tsoro hawa taji dan kar ta hau ta makale amma da ta tuna yaya Prince ɗin ta na wajen sai ta samu kwarin guiwa,
    Chikin zafin nama ta haye saman stair tana hawa stair case ɗin ya naɗe kansa da kansa

    wani katafaren ɗaki ne awajen mai chike da computers da na urori da ban daban gaba ɗaya ɗakin gauraye yake da hasken computers, yana tsaye gaban wata makekiyar desktop ya sanya wata na’ura a idon sa kamar glass sai aiki yake tika,tsayuwa tayi tana bin ɗakin da kallon kafin ta mai da kallon ta kansa sanye yake da yar gakeren wando wadda ta ɗame sa sosai babu riga a jikin sa da alama wandon ma dolece ta sanya ya sa dan kallo ɗaya zaka masa ka gane haka asalin kyakkyawar suran jikin sa ta bayyana gaba ɗaya hannayen sa da chinyoyin sa baki lallausan gashi ne a kwance awajen sai sheki yake kai kallon ta tayi saman ɗamtsen hannun sa daƙe murɗe dama dama wani mugun farinciki take a duk lokacin da ta kalli kyakkyawar bakin gashin dake kwance a saman faffaɗar kirjin, Cool murmushi ta saki lokacin da idon ta ya sauka a kan haɗaɗen bakin gashin kansa wadda ke baje har bayan sa kasan chewar bai ɗaure gashin ba ya sake ta har baya
    duk da sanyin Ac dake ɗakin hakan bai hana shi zufa ba saboda Aikin da yake tika kusa da shi tazo ta tsaya tace “sannu da Aiki yaya Prince” bai an sa ba kuma bai juyo ba aikin sa yake sosai da alama aiki ne mai muhimmanci

    Tana tsaye shi kuma yana ta aikin sa almost 10mins da zuwan ta sanna ya chire na’uran dake fuskar sa ya juyo kallon ɗaya ya mata ya ɗauke kai kayan barcine riga da wando a jikin ta fari tas masu laushi sai ɗan karamin hijabin da bai wuce kirjin ta ba ta sanya a kanta baki

    ansan cup ɗin hannun ta yayi ya ɗora saman wasu takar du dake wajen chikin sanyi murya yace “wayace ki ɗauki waya har ki kirani? Banche duk wanda zaki kira sai kin sanar da ni ba!? Baya baya ta farayi tana girgiza kai tana addu’a a zuchiyar ta Allah ya sa kar ya bugeta,takowa ya farayi a hankali yana bin ta tana baya baya, “ba dake nake mana bane? Kasa magana tayi ta chigaba da yin baya tana girgiza yana bin ta kai har suka kure bango,runfa ya mata da faffaɗar kirjin sa chikin tsawa yace “bazaki bani amsa ba sai na ɓallaki”slowly ta ɗago kanta tana kallon saitin wuyar sa ta fara magana “daman naga baka dawo bane shi ya sa na kiraka amma kayi hakuri ba zan sake ba” har chikin ran sa yaji daɗin amsar ta dan duk yan uwan sa ba wanda ya taɓa damuwa ko ya kirasa awaya idan ya wuce lokacin dawowarsa ɗan garama Aryan daman shi duk abun da suke a tare suke duk kuma in da zasuje tare suke zuwa for the first time yau sister sa ta damu da bai dawo ba har ta kirasa awaya wow wanan abu yayi,afili kuwa ɗaure fuska yayi sosai chike izza yace “idan kika saƙe ɗaukan waya kika kira sai na hukun taki!” Ɗago kai tayi sosai dan ya fita tsawo sosai idan suna tsaye tana son kallon face na shi sai ta ɗaga kai sosai kwata kwata tsawon ta bazata wuche kirjin sa ba da kanta da komai

    Kallon face na shi tayi kafin tace “In Sha Allah ba zan sake ba amma dan Allah idan ba zaka dawo da wuri ba ka faɗamin kafin ka fita” abu guda ɗaya ne ke burgesa da yarinyar nan koda batayi laifi ba idan ka mata faɗa tana ansan laifin tace kayi hakuri bata damuwa wajen dole dole sai ta sanar da kai ba tayi laifi ba da tayi da bayayi ba zatache kayi hakuri bazata sake ba kuma tana kokarin taga ta kiyaye abun da kayi magana a kai, yana sane ba ita take faɗawa Ammi yana mata mugun taba amma da yace idan tasake faɗa sai ya bugeta duk da ba ita ɗin che ta faɗan ba bata nuna ba ita ɗin bace hasalima hakuri ta bashi ta ansa laifin da ba tayi ba

    Shiru suka tsaya yana kallon face nata, sunkuyar da kanta kasa tayi tana jiran taji me zai che da ita gaba
    saukar hannun sa taji saman kanta zame mata ɗan karamin hijabin jikin ta yayi a jefar kasa shafa gashin kanta ya shigayi tare da jawota jikin sa, jin abun tamkar mafarki Hiyana take, sun daɗe a haka yana shafa gashin kanta kafin ya zame hannun sa daga kan nata ya ɗago habar ta suna kallon juna matso da face nashi yayi dai dai nata chikin sauri ta runtse ido kirjin ta na dukan uku uku kasa kasa yace “ki shirya gobe zan sanya a kira muku masu gyaran gashi” yana kai karshen maganar ya sake ta tare da juyawa ya koma wajen aikin sa ya ɗaukk tea ɗin da ta kawo masa ya koma saman sofa dake a ɗakin ya zauna,ya fara sha chikin nitsuwa

    Juyawa tayi zata fita sai ta tuna da massage ɗin yaya Khalid in da yake chewa idan ya saura kamar kwana biyu alluran ya sake sa kirin ƙa yawan zama kusa da shi kina yawan yimasa magana ko da ba zai amsa ba domin awan nan lokacin duk karfin alluran ya ragu yana gab da karewa ne gaba ɗaya alokacin zai ɗan fara jin feeling kaɗan kaɗan,tuna hakan ya sanya ta koma wajen sofan da yake zaune ta na kokarin tsugunnawa kasa ya nuna mata gefen sa da hannu ba tare da yayi magana ba, nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauƙe kafin ta zauna kusa da shi tana satar kallon sa ta kasan ido, kaɗan ya sha tea ɗin ya ajiye ya miƙe ya koma bakin aikin da yake yana miƙewa ta kwanta a wajen dan daman ta fara jin barci tana kwanchiya ba jimawa barci yayi awon gaba da ita

    2am ya kammala aikin da yake gaba ɗaya ya kashe duk wani kayan wuta dake ɗakin nan take duhu ya gauraye ɗakin haske wayar sa ya kunna kasa kasa yace “tashi muje” shiru bata amsa shi ba tsaki yaja kafin ya nufi wajen da take kwance hannu ɗaya ya sanya ya ɗauke ta chak ya saɓata a kafaɗa ya nufi hanyar fita da ita sai da ya kai tsakiyar ɗakin ya danna remote stair case ɗin tayi kasa ya sauka yana sauka stair ta koma kai tsaye bedroom ya wuce,saman katafaren gadon sa ya shin fiɗe ta ya wuche ya nufi toilet wanka yayi chikin sauri yayi shirin barci dan dare yayi sosai, saman gado ya dawo ya haye tana kwance yadda ya kwantar da ita gefe ya kwanta ya karanto addu’oe in barci ya shafa sannan ya lunshe ido

    Kamar jira take yana lumshe ido yana lumshe wa ta mirgino ta faɗo jikin sa slowly ya waro green eyes na shin karaf sai saman face nata, zuba mata ido yayi yana kallon ta barcin ta take chikin kwanchiyar hankali yauche rana ta farko da ya karewa face nata kallon, shafa nashi face ɗin yayi kafin yace “haka ne fa kamannin mu ɗaya da yarinyar nan” dawo da kallon sa yayi saman ɗan karamin bakin ta ya zuba mata ido zuchiyar sa na ingizashi akan ya sunbacheta ɗayan ɓangaren na zuchiyar sa yace “idan ka sunbace ta ka sunbaci wa keman?” da sauri ɗayan ɓangaren yace “ka sunbaci sister ka kuma zaka iyayin komai da ita a matsayin ta na sister ka, kawai ka ɗauke ta a matsayin abun rage kewar ka,shiru yayi sai tunaninnuka daban daban yake a zuchiyar sa amma ya rasa wanne ɗaya sai kama ji yayi ba zai iya jure kallon lallausan lips nata ba batare da ya sumbata ba

    slowly ya kai bakin sa saman nata da niyar ya sumbace ta amma sai ya zarce ya fara kissing nata ba tare da ya sani ba, sosai yake kissing nata tare da kara jawota jikin sa sosai duk abun da yake mata tana jin sa dan daman batayi barci ba da gangan ta faɗo jikin sa yaya Khalid ne ya rubuta mata a massage kar ta yarda ta rinƙa barci ba a jikin sa ba tarinƙa nuna masa kamar barci take ta mirgino jikin sa ta nuna kamar bata san ta faɗo jikin na shi ba,kara matse ta yayi sosai a jikin sa yana bata hot kiss tula tulan breast nata dake sokin sa a kirjin sane ya fara damun sa ɗan sassauta rungumar da ya mata yayi dan ya samu su ɗan raba jiki, kaɗan kaɗan yake jin feeling akan ta sai da yayi kissing nata mai isar sa sanna ya zame bakin sa daga nata tare da raba jikin su ya ɗan juya ya lumshe ido shi duk a tunanin sa tana barci bata ji me ya mata ba ita kuwa mutuwar kwanche tayi dan gaba ɗaya ya gama kashe mata jiki ya ruɗar da ita dannewa kawai take tunani ta shigayi anya zata iya biyewa shawarar yaya Khalid da yaya Aryan kuwa? Gaskiya wanna aiki ne mai wahala ba zata iya ba gaskiya sai dai su kawo wani shawarar da wanan tunani barci yayi awon gaba da ita, kusan tare barci ya ɗauke su

    KANO NIGERIA

    Auty Amarya na kokarin fita bedroom nata dan lokacin chin abinci yayi tasan yanzu gaba ɗaya su Abba sun haɗu a palo dai dai zata fita wayar ta dake bedside drawer tafara rigging kamar bazata je ta ɗauka ba sai kuma ta fasa ta koma taje ta ɗauki wayar sunan hajj sadiya che ta bayyana saman screen ɗin wayar zama tayi a bakin gado kafin tayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen ta

    Daga ɗayan ɓangaren hajj sadiya tace “Hello hajj ya hajara Ykk”dogon numfashi Aunty Amarya taja kafin tace “lfy Ykk” “Alhadulillah daman nakira na sanar da ke ne yanzu gagarabadau ya mutu sai dai na kaiwa malamina dake bayalsa ya yi mana aikin Farida da Aisha” miƙewa tsaye Aunty Amarya tayi tare da dafe kirji chike da raza na tace “yaushe ya mutu!? “Yanzun nan gani nan ma a kofar gidan sa yanzu baafi minti ɗaya ba”komawa Aunty Amarya tayi ta zauna gaba ɗaya jikin ta ya mutu tama rasa me zata che wa haj sadiya “haj ya hajara ina zulaihat ne? Tun shekaran jiya bata kirani awaya ba itama malamin mu na Niger ya kusa kammala aikin ta tsakanin ta da Safras”tsaki Aunty Amarya ta ja kafin tace “zulaihat bata koma wajen ki ba ai ni tun shekaran jiya da na ganta da safe ban sake ganin taba na yi tunanin ta gaji da zama da nine ta koma wajen ki ai” “aa zulaihat bata dawo waje naba kai amma wanna yarinyar yanzu a gidan naki ma sai data fita yanzu tana chan kila wani saurayin nata tabi yarinya kwata kwata bata jin magana ni Allah yasa malamin nan ma ya gama aikin nan da wuri mu sa mu ayi auren nan kila idan ta shiga gidan Safras ɗin ta rage yawon banzan nan,barima na kira layin ta dan uban ta koma ina take ta wuce ta dawo” guntun tsaki Aunty Amarya taja dan ita gaba ɗaya yanzu haushi ma suke bata daga zulaihat ɗin har Haj sadiyar “haj sadiya sai munyi waya yanzu zanje palo muyi breakfast ne kowa ya hallara saura ni zamuyi waya anjima” tana gama faɗin hakan ta katse kiran ba tare da ta jira amsar haj sadiya ba mayar da wayar tayi saman drawer gefen gadon ta miƙe ta fice daga ɗakin tana mai bakin ciki mutuwar gagarabadau

    Da sallam ɗauke a bakin ta ta shiga palon Abba gaba ɗaya wayan da suka rage a gidan suna zaune saman table diyana na zaune kusa da Aryan ɗin ta tayi shiru ta kasa chin abinci zama Aunty Amarya tazo tayi a kujerar kusa da Abba tana harara Aryan da diyana

    “my diyana kici abinci mana” chewar Abba yayi maganar yana kallon diyana,sai lokacin Aryan ya ɗago kai tare da ajiye wayar sa a gefe saman table ɗin ya jawo plate na abincin nata ya ɗauki spoon ɗin ya ɗibo chips ɗin ya kai mata bakin ta, shiru tayi bata buɗe baki ba kuma bata ɗago ba tana kallon kasa, mai da spoon ɗin yayi chikin plate ɗin ya ɗan rungumota da hannu ɗaya yana faɗin “my jidda menene kuma….bai karshen maganar ba yaji ta sake masa jikin ta gaba ɗaya a jikin sa kokarin faɗuwa take dan bai riƙe ta da kyau ba chikin zafin nama ya rikota da kyau yana faɗin “my jidda lfy me ya faru” miƙewa Abba yayi yana faɗin “suma fa tayi Aryan” tun Abba bai gama rufe baki ba Haidar ya miƙe da sauri ya nufi fridge ya ɗauko ruwa, ɗaukan ta Aryan yayi chak suka koma tsakiyar palo ya shinfiɗe ta saman karpet Haidar ya miƙo masa ruwa, chikin sauri ya balle bakin robar ruwan ya tarbo a hannu ya fara shafa mata a face nata gaba ɗaya su Ammi sun kewaye su suna jiran farfaɗo war ta zama saman sofa Abba da Aunty Amarya su kayi Ammi da Ummi kam sun kasa zama suna tsaye Omar Haidar suma suna tsaye,sai kwaɓe fuska Aunty Amarya take

    Sau uku Aryan na zuba mata ruwa amma shiru bata farfaɗo ba sai a na huɗun ne taja dogon numfashi tare da sauke ajiyar zuchiya tun bata buɗe ido ba ta fara sambatu “Aunty farida yaushe ne jirgin mu zan tashi wlh na kosa na ga su hiyana ina kewar yaya Aryan kin san me Aunty farida ina zuwa gida Ammi zan fara runguma sai yaya Aryan sai kuma hiyana da Aunty Zahra aa na manta Ammi ce first sai Abba tukun nan yaya Aryan” shiru palon yayi suna sauraron sambatun diyana Allah sarki wato shine maganar ta na karshe tana cikin hayyacin ta lokacin guda Abba yaji idon sa ya chiwo da kwalla ba karamin tausayi diyana ta basu ba,mutun ya zauna chikin fitar hayyaci ba karamin abu bane, amma Alhadulillah dan da alama ta dawo hayyacin ta tun da har tana iya sambatu da sunayen yan gidan

    Ji Aryan yayi ba zai iya chi gaba da jin sambatun nan nata ba tana tayar masa da hankali hannu ya sanya ya shafa fuskar ta tare da matsowa kusa da ita ya riƙe hannun ta ɗaya chike da kaunar ta ya fara magana “my jidda buɗe idon ki kallemu ai tun ɗazun jirgin naku ya iso gida” jin muryan Aryan ya sanya ta waro blue eyes nata da sauri tare da miƙawa zaune tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya miƙewa tayi da sauri ta rungumi Ammi tana murmushin tana faɗin “Ammi nayi kewar ki daman na faɗawa Aunty farida muna isa ke zan fara runguma” sosai Ammi ta rungume itama tana faɗin “my diyana nima nayi kewar ki sosai amma yanzu dai duk bamu ya kamata ki fara runguma ba mijin ki ya kamata ki fara nunawa farimcikin ki dan ya fimu bukatar ganin hakan” turun diyana ta tsaya chike da mamaki tace “Ammi miji kuma yaushe na samu miji” Abba ne ya ansa zanchen da chewa “Eh my daughter mijin ki” sakin Ammi tayi ta kariso wajen Abba tana faɗin “Abba wanene kuma mijin nawa? Da hannu Abba ya Nuna mata Aryan dake tsugunne ya kasa mikewa dan gani yake kamar har yanzu bata dawo dai dai ba a wani bangare na zuchiyar sa kuwa farincike yake yana godewa Allah da dawowar matar sa hayyacin ta

    Kallon sa diyana tayi kafin ta ɗago ta kalli sauran jamaar palon chikin nitsuwa tace “Abba ni yaya Aiman nake so ba yaya Aryan ba da yaya Aiman mukayi alkawarin Aure ba yaya Aryan ba” tirkashi gaba ɗaya zuba mata ido jama’ar palon sukayi Aryan jin kalaman nata yake tamkar ana zuba masa garwashi a zuciya ashe Aiman yayi gaskiya shi diyana ke so chije lips nashi yayi lokaci guda idon sa ya sauya jijiyoyin kansa suka miƙe huci ya fara yi kamar wani zaki diyana ta haɗa masa zafi biyu lokaci guda na farko ta tuna masa da Aiman na biyu tace ba shi take so ba zuciyar sa zafi yake masa jiyake tamkar zata fasa kirjin sa ta fito waje,chikin zafin nama ya miƙe yana kokarin barin palon da sauri Abba ya dakatar da shi ta hayyar riko hannun sa yana faɗin “koma ka zauna” ba musu ya koma saman sofa ya zauna tare da dukar da kai kasa umarni Abba yayiwa su Ammi akan su zauna zama sukayi gaba ɗayan su, saman sofas

    “Kai Omar kaje ɗakin Aryan zakaga wata jaka baka mai ɗan girma ka kawomin” chewar Abba da sauri Omar ya juya ya fice daga palon
    Dawo da kallon sa Abba yayi kan diyana dake zaune kusa da Ammi ya fara magana “my daughter kiyi hakuri da Auren da na miki ba tare da na tambayeki ba, abu na gaba Allah ya yiwa Aiman rasuwa inason ki anshi Aryan a matsayin miji domin da Aryan da Aiman duk abu ɗaya ne kuma Aryan ya riga Aiman fara son ki kema kuma Aryan ki ka fara so ba Aiman ba nasan kinche Aiman kike so ne ba dan komai ba sai dan alkawarin da kika masa akan zaku yi Aure nasan da kin san Aiman ya rasu ba zaki che hakan ba,ina jinjina miki da kokarin chika alkawari da ki kayiwa Aiman duk da ba shi kike so ba” shiru palo yayi ba abun da kakeji sai kukan diyana kuka take sosai kukan da take ne ya sanya Aryan ɗagowa baya san kukan ta ko kaɗan idan tana kuka zuciyar sa zafi yake masa

    Chikin kuka tace “Abba dan Allah ka chemin wasa kake yaya Aiman bai rasu ba wlh na yarda yaya Aryan nake so ba yaya Aiman ba pls kucemin wasa ne yaya Aiman na ɗakin sa” kuka take sosai kakar ranta zai fita kasa jurewa kukan nata Aryan yayi ya miƙe ya dawo kujerar kusa da tasu ya zauna chikin kulawa ya fara magana “my jidda ya isa kukan nan kiyi shiru” “yaya Aryan kai ma ka yarda yaya Aiman ya rasu kenan? “My jidda dole na yarda dan ba’a wasa da mutuwa yanzu dai ki dai na yin maganar kinji idan ba haka ba zaki sanya zuciya ta ta fashe” rage sautin kukan nata tayi dai dai lokacin Omar ya shigo hannun sa ɗauke da jakar da Aryan ya bawa diyana tsaraba lokacin da ya dawo makka

    Ansar jakar Abba yayi ya buɗe ya fido da abubuwan dake chiki wayan nan Box guda biyu da Aryan ya ɓuye bai nunawa diyana ba Abba ya ɗauko ɗan babban ya fara buɗe wa, wani dangareren sarkan gold ne wanda ya ansa sunan shi gold ne awajen,mai matukar kyau da tsada sai ɗaukan ido yake ɗago kai Abba yayi ya kallin diyana da ta kwantar da kanta jikin Ammi tana kuka kasa kasa “my daughter ga sadakin ki 100m shine kuɗin sadakin ki daga mijin ki” hannu Ammi ta sanya ta ansa ta sanyawa diyana a tafin hannun ta tana faɗin “an sa ki gani my diyana” kuka kawai take taki kallon sarkan buɗe ɗayan kwalin Abba yayi ya miƙawa Aryan ansa Aryan yayi ya fito da wasu kananan Fararen box masu bala’i kyau daga chiki buɗe ɗayan yayi dan kareran diamond ring ne wadda ya amsa sunan sa diamond sai kyalli yake yana ɗaukan ido ring ɗin ɗauke yake da harafin A ajikin sa ta tsakiya ajiyewa yayi a gefe ya ɗauko ɗayar box ɗin ma ya buɗe shima ring ne irin ɗaya da wan da ya buɗe da farko komai nasu ɗaya sai dai wanan ɗauke yake da harafin D a jikin sa ɗago kai yayi ya kalli diyana dake ta faman kuka kasa kasa yace “my jidda tashi ki zo”tashi tayi tazo gaban sa ta tsaya dan saman sofa mai zaman mutun ɗaya yake zaune hannu ya sanya ya nuna mata saman chinyar sa akan ta zauna satar kallon su Abba tayi kasa kasa yana kallon chikin idon ta miƙewa Abba yayi yana faɗin “zama chikin turawa ya ɓatamin ƴaƴa basa kunya ta yanzu kwata kwata” ya kai karshen maganar tare da fice palo chikin sauri su Ammi suka bi bayan sa taɓe baki Haidar yayi ya fice shi da Omar suna mamakin yaya Aryan

    Aryan Kamar jira yake su Abba su fita ya jawota jikin sa yana faɗin “my jidda ya isa kukan nan haka kwantar da kanta tayi saman kirjin sa kasa kasa tace “yaya Aryan kukan ne ai yaki tsayawa” hannu ya ɗaura saman face nata yana goge mata hawaye yana faɗin “to ya isa karki bari hawayen ya sake fitowa kinji? Gyaɗa masa kai kawai tayi ta kara lafewa a kirjin sa hannun ta ya riƙo ya sanya mata diamond ring mai tambarin harafin A sanan ya miƙa mata mai tambarin harafin D yace ta sanya masa ansa tayi ta sanya masa a ya tsan sa na kusa da karamin ba karamin kyau ring ɗin ya musu ba kamar dan su akayi shi
    Kasa kasa da murya kamar mai raɗa yace “my jidda tashi muje na baki abinci” maƙe kafaɗa tayi chikin shagwaɓa tace “aa na koshi yaya Aryan” jan karan hanchin ta yayi chikin wasa yana faɗin “idan baki chiba zan miki Allura” chikin sauri tace zanci to amma kaɗan” ba tare da ya sake magana ba ya miƙe ya saɓata a kafaɗar sa tana faɗin “yaya Aryan dan Allah ka sauke ni zan tafi da kafana” bai tan ka taba ya wuche ya ɗauki Box na sarkan sadakin ta da sauran kayan ya fice daga palon kai tsaye part na shi ya wuce

    Masu karatu mu damalmale da ku a soyayyar Habibi da jiddan sa gobe idan mai dukka ya kai mu su habibi yau abun nema ya samu 😹😹

    Ina muku fatan alkhari masoyana masoyan Duk Karfin Izzata fatan Allah ya chika muku burin ku na alkhari

    Ina miko gaisuwa da jijjina gare ku

    Aunty Asma’u
    Aunty Hauwa’u
    Maman Twins
    My mum
    Dr Aisha
    Aisha
    Hauwa’u yar adamawa jinin yola
    Sister Halima
    Sister Deeja
    Aunty Amira
    Nana farida
    Deenat Ahmad
    Maman Amir
    Hafsat Rabi’u Abubakar

    Da duk sauran wayan da ban samu daman kiran sunan su ba ina godiya ina ganin comments na ku ya sanyani farimciki da nishaɗi yana rage min kishin hiyana da nake ki dan na lura hiyana ta fara shisshigewa masoyina 🥲

    Pls a bani hot🔥 comments

    💋Duk Karfin Izzata 💋

     

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Maman Shureim gaba ɗaya wanan page ɗin na kine more love 🥰

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 19

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 19

    Book 2

    Page 19

    Jabir

    _________dady wlh ni dai ba zan yar da ba koma yaya ne dole ni dai akawomin hiyana na rinƙa kwana da ita har sai na gaji” miƙewa dad yayi daga saman nashi kujerar ya dawo kusa da jabir ya zauna tare da ɗan rungumosa ya fara magana “am sorry my son kasan dai ko ba ka che hakan ba dole na hukun ta wanda ya taɓamin kai,bani kaɗai bama bakaji yadda mum ɗin ka ma ta ɗau zafi ba, munnemi yarinyar nan har mun gaji sai daga bayan nan na samu lbr basa kasar nan ashe ma yar gidan abokin gaba nane Abubakar saraki,yanzu kasani gaba biyu ne ba ɗaya ba bazan taɓa barin family Abubakar saraki su zauna lfy ba kayi hakuri yarinyar na shigowa kasar nan zamu kawo maka ita” chikin jin haushi jabir yace “dad why baza kuje har kasar da take ku kamota ba!? “Jabir calm down mana ina son kasani bamu isa mu shiga Uk mu kama yarinyar nan ba kai ko hanyar gidan da take ba mu isa mu bi ba kasan awani gida take kasan su wanenen yan uwan ta? Turo baki jabir yayi kafin yace “ni dad ina ruwa da in da take ni dai kawai ina son in ganta a gadona koma ta yaya ka kawomin ita “jabir you are watching news everyday an you knew who is Brigadier general Safras an You knew Lefternal general Aryan an general Yusuf, kai fa da bakin ka kake sanar dani irin haɗarin dake tattare da mutanen nan amma shine yau kuma kake chewa naje gidan su na ɗauko maka yar uwar su sokake na mutu ne ina son kasan shifa makiyi baa fuskantar sa gaba da gaba sai dai ayakesa ta bayan page” chikin tsawa jabir yace “dad it’s ok ni ka mutuma idan ka ga dama amma dai ka tabbatar ka kawomin hiyana kafin ka mutu” yana kai karshen maganar ya miƙe fuuuu ya shige betroom nashi ya banko kofa ya burza key,jiki ba kwari dad ya miƙe ya bi bayan sa murɗa cofar betroom ɗin yayi yaji a rufe alamar jabir ya murza key

    Chikin muryan rarrashi dad ya fara magana “my son ka buɗe min kaji ko? i promise that zan kawo maka ita ko da zan mutu hakan yayi maka” daga chikin ɗakin jabir yace “dad pls leave this place I don’t want to talk to you again if you want to talk to me then you should go an bring hiyana for me first if not I will not come out from this room again I will die here” dafe kai dad yayi sai yanzu ya fara dana sanin me ya sa ya shagwaɓa jabir why yanzu gashi bai isa yayi masa magana ba duk abun da yake so zai yi,yana bala’l son jabir shi kaɗai ne ɗan da Allah ya bashi ba zai iya ganin bacin ran saba kuma yasan halin jabir idan yace zai yi abu tofa sai yayi, yanzu zai iya zama a chikin ɗakin kamar yadda yace idan baa nemo masa hiyana ba bazai fitoba,

    chike da damuwa dad ya kuma cewa “ok my son yanzu zan tafi kuma na maka alkawari zan dawo maka da yarinyar amma pls idan mum ɗin ka ta dawo daga wajen aiki ka fito kuyi hira kaji haba my lovely son” “dad naji ni dai yanzu ka tafi kawai kuma karka dawo ba tare sa hiyana ba”murnushi dad yayi dan yaji daɗi jabir ya fara saukowa “ok my son yanzu kuwa zan tafi amma fa kai ma ka fito kaji” “dad pls leave ai naji ko dai sai ka sake batamin rai ne idan baka tafi ba ka sake wata magana Allah ba zan fito ba kuma ba zanchi abinci ba sai dai na mutu a nan” jin abun da jabir yace ne ya sa dad yayi saurin barin waje ya fice daga palon ya shiga motar sa ya bar gidan gaba ɗaya yana saka yadda zai ɓullowa family Abubakar saraki.

    YOLA

    Gaba ɗaya iyalan gidan su bellon yau suna zaune a tsakar gida innar buba da innar yaya bello suna gyara ganyen rama da zasuyi miyan dare,hasana na zaune gefen su,sun hanata aikin komai saboda chikin ta buba na zaune kusa da innar yaya bello yana gyara musu kifi, inna habiba na kwance saman tabar ma a gefe daga ɗan nesa dasu kasancewar har yanzu ita jikin nata bai gama warwarewa ba
    Da fara’a yaya Bello ya shigo gidan hannun sa ɗauke da yan kananan buhu guda biyu, gaban inna habiba ya ajiye mata buhu ɗaya ɗayan kuma ya wuce da shi ya miƙa wa matar sa,zama yayi a tsakiyar innar sa da innar buba chike da farinciki ya fara magana
    “inna mun yi waya da Ammi tace ranar Litinin zata turo mota ya ɗauke mu da ni da ke da ita” yayi maganar tasa ta karshe yana nuna hasana ba zai iya kiran sunan ta a gaban ta ko a gaban innar sa ba,hakan a chewar su rashin tarbiyya ce,chikin nuna damuwa innar yaya bello ta fara magana “aa Bello kuje dai kai da ita ni zan zauna da su habiba dan kaga dukkan su basu gama samun lfy ba” chikin sauri innar buba ta tari numfashi ta da chewa “aa innar Bello ku tafi dai karki damu In Sha Allah zamu kula da kanmu bamusun sanadiyar mu ki rasa jin daɗin ki” hmmm larai kenan ai na riga na gama magana babu in da zanje ya ɗauki matar sa suje yaje yaga yanayin wajen idan wajen yayi masa sai ya dawo musan shawarar da zamuyi” ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta ɗauki kwaryar ganyen da suka gyara ta bar wajen ta shege kitchen

    Dawo da kallon sa yaya bello yayi kan innar buba,hannu innar buba ta sa tana shafa kansa alamar kar ya damu yabi abun da innar tashi tace,jiki ba kwari ya mike ya nufi ɗakin sa yana tunanin ta yadda zai yi wanan tafiya ba tare da innar sa ba, anya zai iya barinta a nan kuwa? Chike da zulumi ya kwanta saman gadon chiyawar su

    Alama innar buba tayiwa hasana da hannu akan ta miƙe ta bi yaya bello dan ta lura gaba ɗaya ya sauya da innar sa tace ba zata bishi birni ba,chikin jin kunya hasana ta miƙe tabi bayan mijin ta.

    KANO

    8am Aryan ya tsaka da barchin sa mai chike da daɗi da mafarkin diyanar sa,
    a chikin barchi ya jiyo ihun ta har tsakar kansa babu shiri ya waro ash eyes nashi masu chike da barchi sunyi jaa saboda barchin bai ishe sa ba hannun sa ya ɗora gefen sa yana lalubar ta bata awajen chikin sauri ya miƙe zaune, da mamaki yake kallon ta zaune a tsakiyar ɗaki ta wargaza gashin kanta ta harɗe hannayen ta a guiwowin ta ta dunkule waje guda, kawar da kansa gefe yayi ya sauko daga gadon ya nufeta yana zanchen zuchi yau kuma kalar iyashegen da tazo masa da shi kenan

    Sugunnawa kan yatsun kafar sa a kusa da ita ya sanya hannu yana kokarin chire hannayen ta data murɗe a guiwowin ta yana faɗin “my jidda wai me ya sa kin chika rigima ne? Yanzu me ya zaunar da ke awajen….bai idasa magana ba yaga tayi wani kukan kura ta hankaɗesa har sai da yayi baya ya faɗi, da sauri ya runtse idon sa ya kuma buɗe wa domin ya tabbatar wa kansa ba mafarki yake ba, ɗago kan sa yayi yana kallon yana yin garin tabbas karfe 9 zatayi yanzu,ya kamata a che lokacin karewar karfin maganin da Ahzan ke bata yayi, mamaki ne ya sake kamashi tuna irin turesa da tayi tabbas wanan ba karfin ta bane domin yana da tabbacin ko hannun sa idan ya sakar mata nauyin bazata iya ɗagawa ba, tuna hakan yasa ya miƙe tsaye chikin sauri yana yan waige waige bata a chikin ɗakin da sauri ya nufi kofar fita daga shi sai wando zuwa guiwa da singlet fari tas a jikin sa, bata a palo ficewa yayi waje yana mamaki, jin abun yake tamakar mafarki, tsayuwa yayi a harabar gidan ya rasa wani part zai shiga neman ta,ba zai iya komawa ɗaki ba tare da ita ba dan yadda ya gantan nan bai ga alamar mai lfy ba wani zuchiya nace masa ya nufi part na Ammi wani zuchiyar kuma nace masa ya nufi part na Abba, ya rasa wanne ɗaya zai ɗauka yayi nisa chikin tunanin da yake yaji wani razanannen ihu daga part na Aunty Amarya,chikin zafin nama ya nufi part ɗin

    Abun da bai taɓa zato ba idon sa yayi tozali da shi turus ya tsaya a bakin kofar palon yana ganin ikon Allah, Aunty Amarya na dafe da goshin ta jini na zuba,ga Omar da diyana na tikar dambe duk karfi da kasancewar Omar namiji amma diyana ta faffasa masa jiki, sai kokarin take ta karisa wajen Aunty Amarya shi kuwa Omar duk chiwon da ta jimasa hakan bai sa ya kyaleta ta karisa wajen ba, sai faɗa suke Omar ya kasa da katar da ita dan jin karfi take kamar doki, mutuwar tsaye Aryan yayi yana kallon abun kamar Tv yana kasa motsawa daga in da yake.

    Chikin ɗagawa war murya Omar yace da Aunty Amarya “Aunty Amarya ki gudu ɗaki wlh yarinyar nan ba wanda zai iya tare ta, tunkan ta illatamu mu dukka ki gudu” ya kai karshen maganar dai dai lokacin da gaba ɗaya Family suna iso ban da yan Uk dasu Aunty farida dake gidan mazajen su, “subhanallah subhanallah” abun da Abba ke faɗi kawai chikin sanyin murya Ummi tace “diyana lfy wai meke faruwa ne? Omar na kokarin yin magana diyana tayi kukan kura ta damki wuyar sa ta ɗagashi sama tayi wurgi dashi gefe,a fusace Haidar ya kariso wajen bai yi wata wata ba ya ɗauke ta da mari yana faɗin “ke wani irin kwaya kika sha yau? Ba zato ba tsammani Haidar yaji ta tanki wuyar sa da hannu ɗaya ta ɗagashi sama sai kokarin kwace wuyar nashi yake amma abun ya chi tura zaro ido ya farayi waje alamar ya ji shaƙa, ihu Ummi ta fasa tana faɗin “zata kashe Haidar ku kai masa ɗauki Ammi kam tana tsaye ko motsi ba tayi ba domin kallon ɗaya tayiwa diyana ta fahimci an haɗatane da manya manyan sheɗanun aljanu masu ji da karfi da mugunta kuma duk wan da ya tinkare ta idan bai yi Sa’a ba to zai iya mutuwa, gaba ɗaya su Abba sun ruɗe tashin hankali ya bayyana karara a kan face nasu

    Chikin zafin nama Aryan ya kariso chikin ɗakin hannu ya sanya yana kokarin chire hannun diyana daga wuyar Haidar, amma ji yayi kamar kwaɗo akasa aka haɗe wuyar da hannun ta akan datse ko motsa hannun nata ya kasa ga Haidar gaba ɗaya ya gama gala baita numfashi sa na gab da ɗauke wa, karasowa wajen su Abba yayi chikin sanyin murya yace “dan Allah bai war Allah ki yi hakuri ki sake sa zai iya mutufa, Abba bai gama rufe baki ba Aryan ya furta “No” da karfi tare da hankaɗe diyana da iya karfin sa suka tafi gaba ɗayan su kasa ji kake dam karar harbin bin diga builet ɗin ya wuche ya fasa bango, gaba ɗaya mutanen dake chikin ɗakin suka chure waje guda ba karamin tsorata Abba yayi ba chike raunaniyar murya yace “Aryan wanna arbin bin diga fa daga ina? Dai dai lokacin Aryan ya mike zaune yana faɗin “bgs yayi harbin” “bgs kuma? Abba ya faɗa da mamaki a kan face nashi “eh Abba shine yayi harbin kuma nasan hakan zata faru tun danaga Haidar ya galabai ta” “amma Aryan Ina chewa Prince baya nan ta ina to yayi harbin?chewar Ummi tayi maganan da mamaki sosai a face nata mikewa tsaye Aryan yayi ya nufi diyana dake kwance a kasa kamar ta mutu yana faɗin “eh Ummi baya nan akoi wani Gun da ake baiwa manyan manyan sojoji da na ura gun ɗin take aiki, gaba ɗaya gidan nan akoi Camera sirri da muka sanya to idan kana son harbin wani daga chikin gidan nan tachikin Cameran da muka sanya zakayi amfani da motsin mutun sai ka sai ta nauran wanchan gun ɗin ka shigar da Cameran dake gidan nan ka sanya motsin wadda kake son harba sai ka sai tashi kawai ka danna Don shikenan, to daman kafin ka harbi mutun idan aka sai tashi da gun ɗi zaki ga alamar wata jan wuta a jikin sa, shi ya sanya dana gani na turesu” chikin faɗa da ɓachin rai Abba ya fara magana ” hauka Safras yake ne da zai harbeta wato kashe ta yake son yi baya ganin ba a hayyacin ta take ba ne?” chikin sanyin murya Aryan yace “kayi hakuri Abba bai da zaɓine dolece ta sanya ya sai ta harbin nata ku masa uzuri kunga baya nan ta chikin Camera yake kallon mu kuma da kuke nan ya ku kaji da ku kaga Haidar na gab da mutuwa a gaban ku bare kuma shi” ya karisa maganar lokacin da ya tsugunna kusa da diyana, tsaki Abba yaja kafin yace “wanna ba hujja bane ai rai bai fi rai ba… Abba bai gama rufe baki ba yaga diyana ta tamko wuyar Aryan,tare da mikewa zaune tana zaro ido,chikin zafin nama Aryan y ɓalle hannun ta daga wuyarsa ya haɗe hannayen nata dukka biyu ya rike yana faɗin “sa idon ki chikin nawa” wani kukan kura tayi tare da murɗewa waje ɗaya ta dakarkare ta kaiwa masa bugu da kafar ta wadda ya sanya shi yin baya baya ya faɗi dan daman bai tsugunna da kyau ba akan yatsun kafar sa ya tsugunna, miƙewa tayi, ta nufi Aunty Amarya,

    a guje Aunty Amarya ta wuce bayan Abba ta buya, chikin zafin nama shima Aryan ya miƙe ya nufeta ta baya ya damko ta yayi yayi ya ɗagata saman amma jin ta yayi kamar dutse ko motsata ya kasa, juyawa tayi tana kokarin kokawa da shi akan ya sake ta kamar daga sama sukaji wata gigitatchiyar tsawa da basu taba jin Voice irin taba “ke Khadijah ki nitsu!!! a razane gabaɗayan su suka juya suka kai kallon su in da sautin tsawar ta fito, ba karamin razana su kayi ba lokacin da suka ga Ammi ce tayi wanna tsawar tana tsaye kamar gunki kusa da ita Abba ya matso kasa kasa yace “Aisha kina lfy kuwa? Ba tayi magana ba kanta na kallon kasa, lokacin guda diyana ta saki Aryan ta duka kasa chikin wata iriyar Voice mara daɗin ji ta fara magana

    “Kayi hakuri oga ba laifin mu bane” chikin tsawa Ammi tace ta fara magana da muryan maza “ba laifin ka bane laifin wanene menene ya kawoka jikin ta? Ba su Abba ba har shi kanshi Bgs dake kallon su ta Camera ya tsorata ganin mahaifiyar sa na magana da muryan maza, kara matsowa Abba yayi kusa da Ammi ya sanya hannu ya na kokarin zaunar da ita, yanke jiki tayi ta faɗa jikinsa chikin sauri Aryan ya kariso ya dauke ta daga jikin Abba ya shinfiɗe ta saman doguwar kujera umarni Abba yayi wa kowa dake chikin palon akan su zauna ba musu kowa ya samu waje saman sofa ya zauna da kyar Haidar ya iya miƙewa ya zauna saman sofa shiko Omar ko motsi bayayi yana baje a kasa alamar ya suma

    Ido a rufe Ammi ta fara magana da muryan maza kamar ɗazun “baka bani amsa ba menene ya kawoka jikin ta!? Chikin Voice mai bada amo mara daɗin ji diyana ta fara magana “turomu akayi akan mu haukatata ta dawo ita ba mutun ba kuma ita ba aljana ba” “waye ya turoku ashe akoi wanni daga chikin ku dake chin gashin kansa ashe bakujin maganar mai martaba babana” kuka mai sauti diyana ta fasa chikin kuka take faɗin “izirail kayi hakuri karka sanar da sarki Ni yanzu ma zan fita daga jikin ta amma fa ko na fita kasani ba zata samu lfy ba domin gaba ɗayan ta ogan mu ya riga ya sanyata a chikin kwalba, rayuwar ta na hannun shi ta yuwuma idan na fita a jikin ta ya kashe ta idan na fita zata dai na buge buge da duk wani abu kamar mahaukaciya amma fa bazata samu lfy ba kullun zata kasance chikin chiwo domin oga ya rufe komai na jikin ta har magana ba lallai ta iyayi ba, zaɓi biyu kuke da shi na farko ko dai ku chigaba da bata maganin da kuke bata daga 1 week baya zuwa shekaran jiya domin maganin kamar yana chan zatane gaba ɗaya komai nata zai chanza zaɓi na biyu kuma ko dai ku tinkari oga da kanku domin ya warware aikin shika ɗai zai iya warware Aikin” chikin tsawa Ammi tace “wanene ogan naku? Waye ya turoku? “Ka idar Aiki kasan bamu faɗa amma zan iya faɗa muku in da yake” “ai na yake?” “Garin yola yake” yana kai karshen maganar diyana ta yanke jiki ta faɗi kasa alamar aljanin ya fita

    chike da bada umarni Ammi ta nuna Aryan da hannu ba tare da ta buɗe ido ba ta chigaba da magana “yanzu Khadijah ta zama nauyinka hakkine a kanka ka nema mata lfy sai ka shirya ya je ka nema mata magani idan kuma zaka iya zama da ita to zaɓi ya rage gareka” chikin sanyin murya Aryan yace “amma ya akayi ka kirata da Khadijah ba diyana ba ko dai har yanzu aljanin na nan ne bai fita ba kuma shine mai suna Khadijah” “ai Khadijah ne sunan ta ba diyana ba, da sunan Khadijah aka yanka mata rago, Khadijah na da bukatar abubuwa da dama daga gareka kayi amfani da matsayin da kake da shi ka nemo mata wasu ɓangarori na rayuwar ta” chikin sauri Aryan yace ban fahimta ba ɓangarori na yaruwar ta kuma kamar me kenan? Shiru sukaji Ammi ba ta sake magana ba sai ma wani attishawa da ta buga mai karfin gaske, shikenan sai barchi mai nauyi ya ɗauke ta

    “Tirkashi to Aryan ka dai ji aikin da ke gaban ka ko” chewar Abba shiru Aryan ya ɗanyi kafin yace “Abba amma ya akayi sunan yarinyar nan ya sauya? ba tare da sanin kowa ba kuma ya akayi ko ita kanta bata san sunan ta ba? kuma wani ɓangarori yake magana kenan? ina son sanin asalin tushen yaran nan” miƙewa Abba yayi yana faɗin “sai dai ka nemi sanin asalin su ta fannin ma haifiyar su bata mahaifin su ba ta mahaifin su kam su Safras ne tushen su dan idan ba Aisha ba Bappan su bai da wasu yan uwa” shiru Aryan yayi na ɗan mintuna kafin ya miƙe ya saɓi diyana a saman kafatar sa ya fice da ita ya nufi part nashi, umarnin Abba ya bawa su Aunty Amarya akan su wuce ɗakin duba marasa lfy Aryan zai zo ya duba su, ba musu Aunty Amarya da Haidar suka wuce Omar dake sume kuwa Aryan ne bayan ya kai diyana ya dawo ya ɗauke sa, Abba da Ummi suna zaune kusa da Ammi suna jiran ta farfaɗo.

    Uk

    fitowa yayi daga ɗakin computers nashi bayan ya gama kallon su Ammi kai tsaye wajen hutawar sa na ɗaki ya nufa yana tafiya yana latsa wayar sa, zaune take a saman ɗaya daga chikin kujerun wajen sanin ba wanda yake zuwa wajen ne ya sanya tayi baje warata dan duk tunanin ta baya nan kuma ba zai dawo yanzu ba sai dare, sanye take chikin wasu shegun riga da wando sun matse ta sosai rigar yana da babban wuya kusan rabin tula tulan boobs nata awaje gashi ko breziya bata sanya ba hips nata kamar zasu fasa wandon ta baza gashin kan nan nata ko ɗan kwali bata sanya ba yau kam bare hijab dan tasan ba wanda zaizo wajen,ba karamin kyau tayi ba kamar yar india,tana riƙe da wayar ta tana buga game, ga wani haɗaɗen cofin glass dake saman table ɗin kusa da ita ta zuba ruwa mai sanyi a chiki idan tayi game ta gaji ta ɗau ruwa ta sha.

    Jin tayi gaba ɗaya ta tsargu kamar wani yana kallon ta, slowly chikin tsoron abun da zata gani ta ɗago blue eyes nata, karaf idon ta ya sauka chikin nashi yana tsaye wajen ɗan karamin pool dake wajen ya harɗe hannu a kirji ya zuba mata ido, a tsorace ta miƙe jiki na kerma tazo ta raɓa gefen sa zata wuce hannu ya sanya ya damko gashin kanta da karfi ya jawota baya ya dawo da ita ta gaban sa suna fuskantar juna, tsuke fuska tayi dan ba karamin zafi jan gashin ta da yayi ya mata ba calmly da sexy Voice na shi ya fara magana “me ya kawoki nan? Bakin ta har bari yake lips nata sai kakkarwa suke tace “kayi hakuri yaya Prince bazan…. Bata karisa maganar ba ya ɗaura yatsa ɗaya a saman lallausan lips nata yace “shiiiiiii” shiru tayi shima yayi shiru ya zubawa tsoratachiyar face nata ido ita kuwa ganin ba zata iya kallon chikin gwayar idon sa bane ya sanya ta runtse idon ta, Almost 3mins suna tsaye a haka da kyar ta iya buɗe baki lips nata sai kerma yake tace “yaya Prince dan Allah kayi hakuri wlh zafin gashin yake min” kasa kasa yace “open your eyes now” chikin sauri ta waro blue eyes nata a kan face na shi tana jiran taji me zai che da ita “wai me nake miki ne da kike yawan kirana da mugu? Kara zaro idon ta waje tayi tana mamakin yaushe yaji tana zagin sa kuma “ba dake nake magana bane” da sauri tace “kayi hakuri yaya Prince ba zan sake ba”
    “Nifa ba chewa nayi zaki sake ko baza ki sake ba chewa nayi me nake miki da har kike kirana da mugu kuma kika tsaneni” runtse ido tayi chikin tsoro hukuncin da zai mata idan ta faɗa masa ta fara magana

    “kana kyamata kace baka sona baka son ganina komai na taɓa baka so,baka kaunar hanya ta haɗa ka da ni ma bare har jikin mu ya haɗu, ban san me na maka ba kamin irin wanan muguwar tsana duk da tsanar da kamin hakan bai hanani in sauke hankin ka dake kai na ba,hakan baya hanani kyautata maka amma komai nayi maka ba dai dai nayi ba….bata kai karshen maganar ba ya jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjin sa da murya kamar mai raɗa yace “shikenan abun da ya sanya kike chemin mugu?har kike ikirarin kin tsaneni? Kasa magana tayi dan ji take kamar ba aduniya take ba,chi gaba yayi da magana “ok yanzu mun haɗa jiki kuma bana kyamar ki sai ki dai na kirana da mugu, because kalmar batamin daɗi” nan ma ahiru tayi ta kasa magana,hannu ya sanya ya ɗago habarta ya zubawa face nata ido, idon ta a lumshe dan gaba ɗaya kunyar sa take ji “open your eyes” slowly ta buɗe idon nata a kan face na shi “what is your name? Chikin sanyin murya tace “hiyana”shiru yayi bai sake magana ba sai hannun sa da ya ɗago ya ɗaura saman kanta a hankali ya shiga shafa lallausan bakin gashin kan ta, ya zagayo da ɗayan hannun sa ta bayan ta ya ɗaura saman kugun ta, kwantar da kai hiyana tayi saman kirjin sa ta lafe tana tunanin anya ba aljanin bane wannan ɗayan bangaren zuchiyar tane ya bata amsa da chewa idan ma aljani ne yau dai ba kin kwanta saman kirjin aljani mai kama da mutumin da kika fi so a rayuwar ki ba,tuna haka yasa ta kara lafewa a jikin sa tana shakar daddaɗar kamshin perfume na shi almost 10mins suna tsaye haka, kasa jure tsayuwar hiyana tayi dan ta lura Bgs ko shekara zasuyi a tsaye ba zai damu ba, kokarin zamewa take kasa dan kafofin ta sun gaji jin hakan ya sanya ya sunkucheta da hannu ɗaya ya koma da ita wajen kujerun dake rufar wajen, kwanchiya yayi da ita a saman faffaɗar kirjin sa kwantar da kanta tayi saman kirjin na shi tana ɓoye fuska,chi gaba da shafa lallausan bakin gashin kanta yayi, lokacin guda ya fara fita hayyacin sa dan daman shi mutun ne mai tsananin sha’awa, shi ya sanya dan ya kare kansa daga faɗawa neman matan banza yake allura,

    ɗayan hannun sa ya ɗaura saman bayan ta yana shafawa a hankali, mutuwar kwance hiyana tayi ita har yanzu ganin abun take tamkar mafarki ne ko kuma aljanine yazo mata a suffar yaya Prince, tayi nisa chikin tunani bata ankara ba sai gani tayi ya juya da ita ta koma saman sofar shi kuma ya mata runfa da faffaɗar kirjin sa, waro blue eyes nata tayi waje ba shiri, tana kallon sa, lokaci guda tsoron sa ya dira mata a rai ganin yadda idon sa suka sauya zuwa jaa sosai chikin tsoro lips nata na kerma tace “yaya Prince in tafi ɗaki? Bai yi magana ba sai ma haɗe fuskar su yayi waje ɗaya a hankali ya kamo lips nata na kasa ya fara kissing, gaba ɗaya duk wani kofa da iska ke shiga a jikin ta ya buɗe domin ansan sakon da yaya Prince ke aika mata duk wani jini dake gudu a jikin ta sai da ya tsaya chan,ya baiwa sakon yaya Prince hanya ya wuce, sosai yake kissing nata tare da shafa gashin kan ta da hannu ɗaya, almost 10mins yana kissing nata kafin ya sake ta tare da miƙewa zaune chikin da sarke war murya yace “jeki kawomin abinci” tun bai kai karshen maganar ba ta miƙe da gudu ta barwajen

    Masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

     

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Wanna page ɗin nakine Hauwa’u jidda maman Abba ina godiya da comments naki ina matikar farinciki da jin daɗi Allah ya bar zumunci

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 17

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 17

    Book 2

    Page 17

    Kukan da take ya hanashi barchin sai juyi yake chikin tsawa yace
    “kimin shiru!!

    Chike da jin zafin zazzaɓi ga azabar zafin da kirjin ta yake mata tace

    “gaskiya yaya prince baka da imani sai yau na kara yarda da hakan, baka da tausayi kai mugune wlh duk abun da kamin sai Allah ya sakamin tun da ba abun da na maka, komai mutun ya maka aduniyar nan bai yi dai dai ba mutun baya taɓa gane gaban ka bare bayan ka, natsane ka wlh natsani ganin ka kwata kwata kai ba mutun bane, dan girman Allah ka kasheni ka huta na gaji na gaji da wanan bakar wahalar rayuwar, tun da na taso a rayuwata ban san komai ba ban da hawala, ina rokon Allah da ya sanya ya samu dacewa a lahira” tana magana tana juyi kamar zata mutu da alama bata a chikin hayyacin ta,

    a sukwane ya mike zaune yana kallon ta, da alama bata chikin hayyachin ta kwata kwata batama san me take faɗe ba, abun da yake zuchiyar tane ya fito bakin ta ba tare da sanin ta ba,

    Shiru yayi yana kallon ta yama rasa mai zai che mata domin yasan ba a chikin hayyachin ta tayi maganar ba, so bai kamata ya hukun tataba abun dake zuchiyar tane ya fito fili bata shirya ba

    Da karfi ta dafe mararta tafara juyi tana faɗin
    “wayyo Allah na ya Allah kasa karshen wahala tace tazo Allah kasa mutuwa zanyi a yau, na mutu na huta da wanna bakar wahalar wayyo diyana pls ko aina kike idan kin dawo ki kula da su amrat sosai, kar ki bari su shiga ukubar rayuwa irin nawa, ko mutuwa zaki yi ki tabbatar kin share musu hawaye, wayyo Allah na”
    shiru tayi da surutan saboda azabar chiwon maran nata ya karu,

    yana zaune ya zuba mata ido karo na farko da ya fara jin tausayin wani ɗan adam a rayuwar sa, ya kasa motsawa daga in da yake

    wani miƙa tayi lokachin guda kuma sai ta saki, ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nepa

    da sauri ya matso kusa da ita Slowly ya ɗaura hannun sa saman wuyar ta, a hankali ya gangaro da hannun nasa saman saitin tsakiyar kirjinta,da sauri yae ɗauke hannun sa, matsowa bakin gadon yayi ya zura kafar sa kasa ya miƙe, ya nufi, palo

    Ruwa mai sanyi ya ɗauko ya dawo ɗaƙin ya haye saman gadon.

    Buɗe ruwan yayi ya tarbo a hannun sa, ya shafa mata a fuska, shiru bata farfaɗo ba, sake ɗeban ruwan yayi ya shafa mata nan ma shiru bata farfaɗo ba, kura mata ido yayi sosai a hankali ya kai fuskar sa saitin tata har dogon hanchin su na gogan na juna, kara matso da face nashi yayi sosai ya haɗe fuskokin nasu, har bakin su na gogan na juna, hannu ya sanya ya matse ɗan karamin bakin ta sannan ya ɗora nashi ya shiga hura mata numfashi sa a hankali
    bai chire bakin sa ba har sai da yaga alamar ta fara numfashi chikin sauri ya chire bakin sa tare da sakin nata bakin ya koma gefe guda yana kwaɓe fuska.

    A razane ta farka tare da miƙewa zaune, tana bin ɗakin da kallon, zuba mata ido yayi yana kallon ta da kyau dan ya tabbatar ta dawo normal ne ko dai har yanzu bata chikin hayyachin ta, lokachi guda kuma ya kawar da kansa gefe yana kwaɓe fuska.

    Bata lura da shi a chikin ɗakin ba ta miƙe tana takawa a hankali ta nufi toilet, yana zaune ya kasa komawa ya chigaba da barchin sa.

    Wanka tayi ta fito ɗaure da towel, batare da ta lura da shiba ta nufi wajen trolley ɗin ta wasu shegun riga da wando ta ɗauko, rigan mai siririn hannu fari tas mau laushi na roba, wandon kuma baki ne mai ɗan ratsin fari daga ta kafar, ta ɗauko always ta zari pant ɗaya ta sanya Always ɗin a chikin pant ɗin,
    ta miƙe ta sanya pant ɗin a jikin ta, zame towel na jikin ta tayi, ta ɗora saman trolley ta ɗuki rigar nata tana kokarin sanyawa karaf idon ta ya sauka a kan face nashi, a razane ta fasa ihu tare da sakin rigar nata ya faɗi kasa ita duk a tunanin ta aljanine mai kama da shi, dan a iya sanin ta by this time ya tafi wajen Aiki.

    Watsa tayi ta gudun gaske ta nufi hanyar fita ɗakin tana ihu, tsaki yaja ya miƙe taku biyu yayi ya damko kugun ta ta baya, tsabar tsorata yau aljani ya taɓata ne yasa numfashi ta ya ɗauke, ba tare da ya lura ta sume ba chikin tsawa yace

    “a haka babu kaya zaki fita? Shiru yaji kamar an ɗauke wutar nefa kallon face nata yayi yaga alamar ta sume, tsaki yaja ya saɓeta a kafaɗar sa ya koma da ita wajen gadon, wurgi yayi da ita da karfi saman gadon ya juya ya nufi toilet, a gurguje yayi wanka ya fito sauri sauri ya shirya chikin wandon jeans blue da t-shirt ash, bai bi ta kan taba ya fice daga ɗakin, ya tafi wajen Aiki

    KANO NIGERIA

    gaba ɗaya family Abba suna zaune a palo sai wayan da basa nan, diyana na zaune kusa da Aryan dan taki yarda da kowa a gidan gani take kamar zasu chutar da ita gyaran murya Abba yayi ya fara magana.

    “Alhamdulliah Alhamdulliah Allah ya dawo mana da diyana lfy sai dai tana da matsa likitoci daban daban sun dubata babu abun da ke damun kwakwalwar ta, munyi magana da Aryan yace yana son matar sa a haka abar masa kayan sa, da kai shi zai koya mata komai, baya buƙatar yan aiki ko wani abu makamancin haka, zai kula da ita da kan sa idan tana da rabon samun sauki zai chiba da mata addu’a Allah ya bata lfy, sannan Aryan gareka nayi magana da ɗan uwan ka ya sansar da ni yana bukatar ka awajen aiki dan haka sai ka shirya komawa, ya karisa maganar yana kallon Aryan, “sannan magana ta gaba Monday zanje Uk kuma ban yarda wani daga chikin ku ya kirasu ya sanar da su ina zuwa ba, ina son inje in ga irin zaman da suke ne, dan na tabbatar da aiki na a matsayina na uba, ga marayun Allah bayin Allah, akoi mai Magana?

    Mikewa Aryan yayi yana faɗin
    “Abba zamu wuce tare on Monday ɗin”
    yana gama faɗin hakan ya nufi hanyar fita daga palon,

    da gudu diyana ta miƙe ta bi shi hannun sa ta rike chike da shagwaɓa tace
    “shine zaka tafi ka barni ko? Tsayawa yayi da tafiyar da yake ya juyo suna fuskantar juna chikin sanyin murya ya fara magana

    “bazaki zauna da su Ammi bane, suma ai yan uwan kine” make kafaɗa tayi tana girgiza kai tana faɗin

    “aa ni dai tsoron su nake ji” ta karisa maganar kamar zatayi kuka

    “to shike nan ba sai kin min kuka ba, amma kina jina ki dai na tsoron su, Ammi itace ta haifeki kin ji? Itace mamanki ba abun da zata miki karki ji tsoro kije ki zauna da ita an jima sai ki dawo ɗaki muyi hira”

    gyaɗa masa kai kawai tayi tare da sakin hannun sa, ta nufi wajen su Ammi dake zaune kusa da Abba gaba ɗayan su sun zuba musu ido suna kallon ikon Allah yau diyana ce ta dawo hakan,

    “Aa Aryan ku tafi tare da ita tun da tafi sakewa da kai” chewar Abba

    “to Abba ke zo mu tafi”
    tun bai gama rufe baki ba ta juyo a guje ta dawo wajensa ta kama hannun sa, juyar da hannun nasa yayi ya rike nata suka fice daga palon

    “Kai wai daman sunan ka Aryan? Ta tambaya lokachin da suƙe ficewa daga part na Abba”

    “eh sunana kenan sunan bai yi bane?

    “Aa yayi amma ina ji kamar na taɓajin sunan kuma inaji kamar na sanka kamar na taɓa ganin ka, da wanchan mutumin yace Aryan sai naji zuchiya ta buga da karfi kamar na taɓa jin sunan,

    a sukwane ya juyo yana kallon ta lokachi guda farinciki tamamaye zuchiyar sa
    “Alhadulillah Alhamdulliah ya fara furtawa ko ba komai diyana ta fara jin sunan shi a zuchiyar ta In Sha Allah nan ba da jimawaba zata dawo dai dai ashe Dr yayi gaskiya.

    Tsabar farinciki yasa ya duƙa ya ɗauke ta chak ya karisa da ita chikin part nashi

    “Aryan kasan me? Allah ina son shan sweet”

    kasa kasa yace
    “ba Aryan zaki rinƙa kirana ba kinji? Yayi maganar dai dai lokacin da suka karisa chikin betroom nashi

    “to wani suna zan rinƙa kiranka da shi kenan?

    Sauke ta yayi a saman katafaren gadon sa yana faɗin

    “daga yau sunana habibi”

    “to habibi nache maka zan sha sweet irin wannan sweet da Aunty Hanan ke bani kullun da safe”

    “ok bari nayi wanka na shirya idan zanje wajen D P O sai na sawomiki, yakalan sweet ɗin yake?

    “Sweet ɗin fa yana nan kamar wani abu haka yana da ɗan wasu abu farare kamar kasa a chikin sa yana da danko sosai, kuma….bata karisa maganar ba ya dakatar da ita chikin sauri

    “ke waya ke baki irin wannan abu kuma idan suka baki keda waye kuke sha!?

    “Ni kaɗai nake sha idan nace Aunty hanan ta sha sai tace yaya Ahzan ya hana kowa sha sai ni kaɗan”

    da sauri ya dawo in da take hannun ta ya kama yana kallon kwayar idon ta, yayin da itama shi take kallon tabbas yanzu ya kara tabbatar da zargin sa akan su Ahzan domin kuwa gashi karara abun ya bayyana a chikin idon ta shi yake bawa diyana abun da zai sanya ta rinƙa mantawa da rayuwar ta na baya, duk lokacin da tasha ba zata tuna komai na rayuwan ta na baya ba sai dai wadda take yanzu shi ya sanya take manta kome ta dawo kamar wadda tayi loosing memory lallai idan kuwa haka ne Ahzan tashi ta kare.

    Sosai yake kallon chikin idon ta duk da ba karatun likita yayi ba a iya sanin sa dai wannan magani baya wuche 24h ajikin mutun karfin maganin yake karewa mutun ya dawo dai dai wannan shine dalilin da ya sanya Ahzan ke sanya hanan kowani safiya ta baiwa diyana guda ɗaya.

    A fusace Aryan ya sake hannun ta ya juya ya nufi hanyar fita yama fasa wanka gaba ɗaya idon sa ya rufe baya ji baya gani burinsa kawai ya isa ga Ahzan ya masa bugu ɗaya wadda zata sadashi dasu walakiri.

    Har ya kai bakin kofar fita sai kuma ya tsaya chak a hankali ya juyo tana zaune yadda ya ajiyeta tana kuka kasa kasa ga hayaye sharɓa sharɓan akan face nata ganin kukan nata ya sanya yaji zuchiyar sa ta ɗanyi sanyi chikin sanyin murya yace

    “menene ya faru kike kuka?

    “To ba kai ne zaka tafi ka bar ni ba” tayi maganar chikin kuka da shahsheka

    hannu kawai ya buɗe mata ba tare da yayi Magana ba, da gudu ta miƙe ta taho ta faɗa jikin sa tana dariya kamar ba itace mai kuka yanzun nan ba, rungumeta yayi sosai ya sanya hannu ya ɗago habar ta ya manna mata kiss a goshi

    “habibi bafa a goshi akeyi ba na gani awayar Aunty Hanan a baki akeyi”

    shiru ya ɗanyi kafin yace
    “ok zan miki a baki idan mun dawo amma yanzu dai muje sauri nake”

    “ni dai Allah habibi ban yar da ba idan bakamin a baki ba ba zan tafi ba”

    chije lips nashi yayi da karfi Ahzan ya chuche sa baya son yayi kissing nata bata chikin hayyachin ta ya kamata first kiss nasu ya kasance gaba ɗayan su suna chikin hayyachin su kuma suna shaukin abun

    “kiyi hakuri muje mota sai nayi kissing naki a chan ko kinga sauri nake yanzu”

    kukan shagwaɓa ta farayi tana buga kafa a kasa, dukawa yayi ya ɗauke ta chak yayi waje da ita dan ya lura idan ya biye mata bazasu tafiba kuma shi gaskiya ba zai iya ɓata first kiss na shi ba ba zai iya kissing nata bata a cikin hayyachin ta ba.

    Gudu Shahram yake da mota ga motochin sojojin su biyu a gaba uku a baya, diyana na kwance a jikin sa sam taki yarda ta sake shi sai satar kallon su Shahram yake ta chikin mirrow motar tana ta zuba shagwaɓan ta shi kuma yana biye mata.

    “Habibi ka manta baka min umm yama sunan abun, shiru ta ɗanyi ta ɗaga kai sama kamar mai tunani yauwa bakamin kiss ɗin ba,

    wani wawan birki Shahram yaja wadda ya sanya su gaba ɗaya tafiya luuuu suka bugu da kujerar gaba na motar, ji kake kiiii motochin jibga jibgan sojojin dake baya sun taka birki har sai da motar baya na karshen ta ɗan daki na kusa da ita, dan birki taki jawuwa da wuri.

    Chikin tsawa Aryan yace

    “are you mad!!? Wani irin birkine haka muna tsaka da gudu”

    chikin rawar murya Shahram yace
    “am sorry oga nima ban san ya akayi na jaa birkin ba.

    Kukan shagwaɓa diyana ta saki dawo da kallon sa Aryan yayi kanta chikin sanyin murya yace
    ” Me ya faru kuma?
    “Habibi ba kai na bane ya bugu da wajen nan tayi maganar tana nuna jikin kujerar motar.

    Hannu sa ya sanya saman goshin nata in da ta dafe da nata hannu tana turo baki, dai dai lokachin Shahram ya tada motar suka chi gaba da tafiya.

    Shafa saman goshin nata ya shigayi yana faɗin
    “Am sorry kin ji zai dai na yimiki zafi.

    Kwantar da kanta tayi saman kirjin sa, tana ɗan wasa da rigar sa yana jin yadda take gangaro da hannun ta ta kasan marar sa, yana son ya hanata amma yana tsoron rigimar ta dan yanzu yana hanata yasan kuka zata sa masa to gwara ya kyaleta kawai.

    Bai an karaba sai jin hannun ta yayi saman mararsa ta zura hannun ta chikin rigar sa, wasa ta farayi da chibiyar sa ta sanya yatsan ta awajen tana ɗan jujjuyawa.
    lokachi gudu ta birkita mishi tunani wani mugun sha’awar tane ya taso masa, ji yake tamkar, ya chika aiki kawai a chikin motar nan wani zir zir yake ji a gaban sa,

    Ɗora hannun ta tayi saman gaban sa ta dafa wajen tana kokarin gyara, kwanciyar ta a jikin nashi dan ta ɗan zamo kaɗan.

    Ji yayi gaba ɗaya duniya juya masa take, yama rasa me zai yi wata muguwar kasalane ya da bai baye sa lokaci guda, ba zato ba tsammani kwatsam yaji tana tattaɓa wajen tana faɗin
    “Habibi menen wannan kuma naji kamar an chusa wani abunne awajen ga mugun tauri abun.

    Dariyar da Shahram ke gumtsewa ne ta kubche masa dan tun ɗazun yake kallon su ta chikin mirrow motar,
    chikin sauri Aryan ya ɗago ido yana kallon Shahram, dake ta famar ɓoye dariyar amma abun ya chi turo da sauri Shahram ya chire idon sa daga kan mirron, harara Aryan ya watsa masa yana kokarin yi masa magana muryan diyana ta kuma katse sa

    “Habibi ya ake buɗe wajen nunamin zan buɗe ne dan naga me kasa awajen, idan ya min kyau nima zaka samin”
    Ta karisa maganar dai dai lokacin da sukayi parking a chikin police station

    Nauyayyar ajiyar zuchiya Aryan ya sauke tare da fita motar da sauri dan bai san diyana ta sake jefo masa wani tambayar, sosai ya sake jin haushin Ahzan dan shi ya mai da ta haka amma wlh sai ya gwammaci da bai zo duniya ba.

    Chikin sauri diyana ta fito tabi bayan sa, tana faɗin
    “Habibi ka jirani mana”

    chak ya tsaya bai san ya zai yi da ita ba yanzu idan yace ta jirashi a mota kuka zata masa, shi kuma da yaji kukan ta gwara a harbesa da bindiga baya son ko ɓachin ran ta bare kuka idan kuma yace zai shiga da ita chiki sai ta sa shi a gaba akan ya faɗa mata menene a chikin wandon sa, bashi da amsar da zai bata bai sana ya zasu kare ba gashi bata mantuwa ko kaɗan.

    Domin sanin ya rikichin Aryan da diyana zai kasan che a chikin office ɗin D P O ku kasan che da Princess teema Star Lady mu haɗe daku masoyana masoyan diyana page na gobe nakune ku da diyanar ku 😹

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    Masoyiya gidan Aunty wanna page ɗin na kine kyau ta na baki dan page ɗin na manya ne daga yau har next week pages ɗin dukka nakine 😹😹

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin bDuk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 10

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 10

    Book 2

    *Episode 10*

    UK

    A nitse hiyana ta chire jikakken kayan jikin ta ta dauki farin towel mai kyau da laushi dake gere awajen drawar ajiye kaya ta ɗaura a kirjinta zuwa dai dai chinyar ta towel ɗin ya tsaya kwanche gashin kanta tayi subhanallah hiyana tafi diyana gashi nesa ba kusa ba domin ita gashin ta ya kai har karshen bayan ta gashi bakin kirin mai laushi da tsantsi sai sheki da kyalli yake, a hankali take tafiya kamar bata san taka kasa duk in da tayi taku ɗaya sai jikin ta ya girgiza, tafi diyana halittar komai akoi ta da manya manyan boobs ga hips nata kamar zasu fashe in dai fannin shap ne baa magana hiyana karshe che, kai tsaye toilet ta shiga, kokarin kwanche towel dake jikin ta take karaf blue eyes nata ya sauka kan ɗan karamin machijin dake ta yawo a chikin baff ɗin wanka tsantsi ya hana shi fita ya gudu, wani ihu ta saki tayi waje da gudun gaske, tama manta babu kaya a jikinta daga ita sai towel, dai dai tsakiyar palon part nasu tayi karo da Bgs kankame shi tayi sosai a ruɗe take faɗin “yaya prince machiji wlh machijine a toilet na” chikin tsawa yace “ke sakeni!!” a razane ta ɗago kanta tana kallon face nashi, da mamaki yake kallon razananniyar face nata tunani ya shigayi wacece wan nan kuma ko dai itace matar da aka kakaba min, shiru yayi, yana kallon yadda take juya idon ta chikin tsoro tace “wlh yaya prince yau ko kasheni zakayi bazan sake kaba sai dai ka kasheni wlh tsoron machijin nake” runtse ido yayi chikin tsawa yace “ki sakeni nace ko!! kara kankame shi tayi da kyau ta chusa kanta chikin faffadar kirjin sa ta fashe da kuka tana kuka tana magana “wlh yaya prince ba zan sake ka ba” a fusache ta damko wuyar ta da nufin yayi wurgi da ita, a razane ta ɗago blue eyes nata da suka fito waje sosai saboda shakan da ya ma wuyar nata tana kallon sa, a hankali ya zame hannun sa daga kan wuyar ta kasa kasa yace “sake ni” sake harɗe sa tayi ta rikesa sosai, bashi da wani zaɓi dole ya mata abun da takeso, tsaki yaja tare da saɓa ta a kirjin sa tare da tallaɓo bayan ta ta kasa ya nufi ɗakin nata, sosai hiyana ta shiga jikin sa, kai tsaye toilet suka nufa.

    Chikin dabara yasa hannu ya damki kan machijin, ya juya ya nufi waje tana makale a saman kirjin sa, dai dai tsakiyar palon part nasu, kasa kasa yace “ke sauka na chire machijin” dago kai hiyana tayi karaf blue eyes nata ya sauka kan machijin dake hannun sa a reke ihu ta sake ta kankame da karfi nan take kuma ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nepa, ji yayi tana kokarin zame wa daga jikin sa ta faɗi kasa chikin sauri ya kankame ta da kyau, tsaki yaja ya juya ya nufi betroom nashi da ita saman katafaren gadon sa ya kwantar da ita san nan ya fito ya nufi waje, Abdol ya mikawa machijin ya koma chikin gida.

    yana shiga ɗakin sa call ɗin Ammi na shigowa wayarsa a nitse ya chiro wayar daga aljihun sa, ganin sunan Ammi ne ya bayyana a kan screen din wayar hakan yasa shi yin picking da sauri manna wayar yayi a kunnensa tare da faɗin “Assalamu alaikum” daga ɗayan ɓangaren Ammi ta amsa masa da “wa’alaikumus salam” “my Ammi y kuke y gd? “lfy lau ya yan uwan ka? “Suna lfy” “ina son yin Magana da Hiyana ne ka bata wayar” sai lokachin ya ɗago ido ya sauke su saman gadon sa, kwanche take kamar yadda ya kwantar da ita ko motsi bata yi “Ammi tana barchi amma idan ta tashi zan kiraki sai na haɗa ku” ba ƙaramin daɗin jin hakan Ammi tayi ba “to amma idan ka fita ka saya mata waya mai kyau kawai dan idan na tashi magana da ita ba sai na kiraka ba” chikin sauri yace “ok za ayi yadda ki ka che” “au shine ka amsa da wuri dan kar na che karinƙa haɗa mu ko? Wato muna takura maka ko? “Aa Ammi kawai maganar che tazo da wuri” “to shikenan ba zan gaji da tunatar da kai ba, kasani duk abun da kayiwa Hiyana na chutar wa idan mu bamu gan ka ba Allah na ganin ka, ina kara rokan ka dan Allah ka kulamin da marainiyar Allah nan kada ka bari tayi kuka idan tayi kuka to tamkar ni nayi idan ka sanya ta kuka tamkar ni ka sanya” ɗaure fuskar sosai yayi ji yake kamar ya katse kiran ita Ammi nan kullun ta kira mutun wa’azi wa’azi, to mutun yace bai san yarinya amman an kakaba masa dole san nan yanzu kuma arinƙa takurawa mutun da zanchen hakki hakki ni gaskiya abun nan ya isheni “au yanzu ina maka ma shiru kamin ko? “Ammi ba shiru nayi ba karki damu ina iya bakin kokarina” “to ka kara kokari kaji? “Ammi pls bari nayi picking call ɗin wani” yana gama faɗin hakan ya katse kiran batare da ya jira amsar taba yayi wurgi da wayar saman sofa tare da jan dogon tsaki ya nufi saman gadon sa, gefen hiyana ya kwanta tare da lumshe ido ba jimawa barchi yayi awawon gaba da shi

    A chikin barchi yaji mutun na numfashi da kyar da kyar kamar wadda aka shake, Slowly ya waro green eyes nashi mai chike da barchi alamar barchin bai ishe sa ba, kan Hiyana ya sauke su, kallon ta yayi from head to toe tsaki yaja kafin ya zame hannun sa dake kan chikin ta yana ɗauke hannun nasa ta miƙe chikin sauri tana bin jikin ta da kallo da gudu ta fice daga ɗakin tsaki yaja ya mai da idon sa ya lumshe

    Har ta kai tsakiyar palo kuma sai ta juyo a kuje ta koma ɗakin sa, jin mutun ya shigo yasa ya waro green eyes nashi akan ta ji tayi kamar ta nitse kasa dan kunya gashi kuma tana tsoron ɗakin ta dan tun da taga snake tofa bazata iya zama a ɗakin ba ko kasheta za’ayi bazata zauna a chan ba

    Chikin tsawa yace “me ya dawo dake ɗakin nan” murya na rawa ga masifaffen kunyar sa da takeji tace “ya ya yaya prince wlh tsoron ɗakin nake ji nake kamar akoi wani machijin a chiki” mai da idon sa yayi ya lumshe batare da ya sake magana ba kalaman Ammi ne kawai ke masa yawo a kwakwalwa sa yana matikar son Ammi baya son ɓachin ran ta san nan baya son hanyar da zata haɗashi da yarinyar nan kai ba ma itaba baya son hanyar da zata haɗashi da mace kwata kwata, dan har yau yana kan bakarsa na chewa duk wadda mace ta raɓa tofa ya zama mai rauni, shi kuma kwata kwata bai san mutun mai rauni

    Sai rawan sanyi hiyana take kasan chewar Ac ɗakin a kunne, gashi babu kaya a jikin ta, almost 15mins tana tsaye shiko yana kwanche idon sa a lumshe kasa kasa hiyana ta fara kuka dan sanyi da yayi mata yawa, tana son ta je ta ɗauki blanket nashi ta rufu amma tana tsoro tun tana sa ran zai mata magana har ta chire rai ta chigaba da kukan ta kasa kasa tana rawan sanyi
    Almost 20mins ta kara kan 15 na ɗazun, gajiya tayi da tsayuwa ta lallaɓa ta koma saman sofa mai zaman mutun 1 ta zauna ta takure, duk wani motsin da take achikin kunnen sa take dan ba barchi yayi ba ya dai lumshe ido ne yana jinta, kasa kasa yace “ki shiga toilet na kiyi wankan” ba karamin razana da girgiza hiyana tayiba tunani take anya ba karya kunnen ta ya jiyo mata ba, to idan ma ba karya bane gaskiya ba yaya prince bane yayi maganar nan sai dai idan aljani dan ita bata taɓa jin yayi magana da mutun a nitse haka ba kullun chikin yiwa mutane tsawa yake, daman ya iya magana a hankali? tunawa tayi yace ta shiga toilet nashi tayi wanka chikin suri ta mike dan kar tayi laifi ta nufi toilet ɗin.

    “Yaya khalid naje ɗakin Aunty hiyana fa ban ganta ba”chewar Zahra dake tsaye tana rike da jallabiyar da yaya khalid ya ɗauko wa hiyana a ɗakin Bgs “Auta mata da mijin ta kuma kike tambayar ina take wata kila tana wajen yaya prince” “haba yaya Khalid kasan dai bazata je wajen sa bakam” “ok to kije ɗakin nashi mana ki dubota sai mu tabbatar” da sauri Zahra ta wuche ta ajiye jallabiyar a saman sofa tana faɗin “kai aa tayi zaman ta ako ma ina take” dariya Khalid yayi kafin yace “to saiki ɗauki hijabin ki muje ai tun da kin ki zuwa ki dubo mana ina sister take su Yusuf suna jiran mu a palo” “to yaya Khalid yanzu kenan zamu tafi ba tare da Aunty hiyana ba? “Eh to mata tana wajen mijin ta zamuje muche tazo muje ne? ki kyaleta idan munje sai ki zaɓa mata kawai idan kuma da wani abun da take bukata sai mu koma gobe” ” to kawai Zahra tace san nan ta ɗau hijabin ta Khalid ya riko hannun ta suka nufi waje

    A babban palon kasa suka sami su Yusuf, sun gama shiri suna jiran su “ina Hiyana kuma? chewar Yaya Ahmad” “muje kawai ba zata jeba” chewar khalid, tare suka jera ba wadda ya sake magana suka fita waje, mota 5 sukayi ɗaya Khalid da Zahra ɗaya Fahad da amrat ɗaya Yusuf da Lamrat ɗayan kuma Ahmad, shi kaɗai ɗayan kuma jibga jibgan sojoji yan rakiyar sune a chiki, da gudun gaske suka bar gidan

    Chike da jin kunya hiyana ta tafito daga toilet ɗaure da towel ɗin Bgs a kirjin ta wadda yazo mata har guiwa kamar yadda ta barshi kwanche lumshe da ido haka ta fito ta same sa, saman sofa ta koma ta zauna sai rawan sanyi take, jingina kanta tayi da jikin kujerar har barchi yayi awon gaba da ita a haka

    Maiduguri Nigeria

    A yaune aka sallami su Ahzan daga hospital suka koma gida ba laifi jikin yarinyar yana samun sauki sosai sai dai har yanzu bata magana sai dai kallon mutane kawai take.

    Misalin karfe 4pm yarinyar na zaune a palon gidan su Ahzan tayi shiru tana kallon kasa, sanye take da doguwar riga abaya baki wadda mum Ahza ta bata, Ahzan da mum nashi suka fito daga ɗakin mum suka fito palon saman sofa ɗaya suka zauna, a nitse mum ta fara magana “bai war Allah gashi bamu san iyayen ki ba amma ina fatan zaki iya zama damu? a chikin gidan nan ko, abun mamaki sai yarinyar ta amsa da “eh zan iya” a razane Ahzan ya miƙe chike da mamaki yace “daman kin fara magana? Gyaɗa masa kai tayi alamar eh Ahzan da Mum har suna haɗa baki wajen chewa “Alhadulillah Alhamdulliah” “baiwar Allah ya sunan ki? Chewar mum shiru yarinyar tayi kamar mai tunani chan kuma ta fara girgiza kai tana faɗin “ban sani ba” kallon juna Ahza da mum sukayi wayar Ahzan ya fitar daga aljihun sa ya shiga kiran layin Dr walid, bugu ɗaya Dr walid ya ɗauka

    “Hello Dr ya Aiki? Daga ɗayan ɓangaren Dr yace “lfy lau Ahzan ya mai jiki” “jiki da sauki dan ita ma na kira yanzu “ok to me ya faru? Ajiyar zuchiya Ahzan ya sauke kafin ya fara magana “Dr yarinyar nan ta fara magana amma abun mamaki mun tambayeta sunan ta tache bata sani ba shin daman ta samu matsala a kwakwalwan tane? “Aa Ahzan ba wata matsalar da kwakwalwan yarinyar nan ya samu lfy lau take kila ta shiga ruɗani ne ku barta ta kara hutawa zata dawo dai dai In Sha Allah” “to shike nan Dr nagode sai munyi waya, yana gama faɗin hakan ya katse kiran ya dawo da kalon sa kan mum, chikin nitsuwa yayi mata bayanin yadda sukayi da dr, addu’a samun lfy mum tayiwa yarinyar, amin Ahzan ya amsa da shi shiru suka zauna ba wan da ya sake che da ɗan uwan sa kala

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 14

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 14

    Book 2

    *Episode 14*

    …….Chike da jin haushi hakan ya yakacheta daga jikin sa zaiyi wurgi da ita, kalaman Fahad suka fara masa yawo a kwakwalwa kalman Ammi ta karshene ta dira masa a rai in da take chemasa idan har ya kuntata wa hiyana to yasa a ranshi tamkar ita ya kuntatawa, tuna hakan ne yasa ya mai data jikin sa ya rike ta da kyau chike da bachin rai ya daka mata tsawa “zaki min shiru ne ko sai nayi wurgi dake! Jin voice na shi yasa ta nitsu tsit dan ita bata taɓa tunanin shi bane tayi tunanin wanine yazo sache ta shi yasa take kokarin kwache kanta.

    saman ka tafaren gadon sa ya kwantar da ita tare da mikewa ya ɗauko Box ya dawo saman gadon, magani zazzaɓi ya fitar ya ɓalli guda biyu, chikin sanyin murya yace “gashi an sa ki sha” jikin ta na kerma ta sa hannu zata ansa zubawa hannun ta ido yayi da mamaki yake kallon yadda hannun nata ke kerman tsoro, ɗaugo idon sa yayi ya fara kallon ta from head to toe gaba ɗaya jikin ta kerma yake hannun ta ya kasa tsayawa waje guda ba lallai idan ya sanya mata maganin a hannun ta ta iya kaiwa bakin ta ba, mikewa yayi ya koma falo ya ɗauko ruwa mai sanyi tare da glass cup ya dawo ɗakin a gefen gadon ya zauna ya balle bakin roban ruwan ya zuba a glass cup ɗin, zama yayi da kyau ya sa hannu ɗaya ya ɗagota, kasa kasa yace “buɗe bakin ki” da kyar ta iya sai ta kerman da bakin na ta keyi ta bude masa, sanya mata maganin yayi sannan ya kafa mata glass cup ɗin a bakin ta, sosai ta sha ruwan sai da ta shanye dukka, san nan ya chire mata cup ɗin a baki ya mai da ta ya kwantar, ya mike ya mai da cup ɗin da roban ruwan saman table ɗin tsakiyar ɗakin, toilet ya nufa.

    Wanka yayi ya fito ɗaure da towel a kugun sa, a gurguje ya shafa mai tare da fesa perfume nashi mai bala’i kamshi da daɗi, dressing room ya nufa, jim kaɗan ya fito sanye chikin kayan barchi masu kyau da tsada ga laushi fararen tas riga da doguwar wando, saman katafaren gadon sa ya haye, ya kwanta hannu yasa saman drawer ya ɗauki remote ya kashe wutan ɗakin ya mai da remote ɗin ya ajiye, ya kunna wutan gefe da gefen gadon masu bada haske blue da green, addu’ar barchi yayi ya shafa, sannan ya juyo ya ɗan kalli in da hiyana ke kwanche yadda ya kwantar da ita ko motsawa ba tayi ba, hannun sa ya kai saman goshin ta ba laifi jikin nata ya fara sanyi, dauke hannun sa yayi ya juya ya bata baya yana fiskantar gabas ya ja blanket zuwa saman chikin sa, tare da lumshe ido, asuba ta gari.

    1:30am hiyana ta farka daga barci dishi dishi ta fara gani goge idon ta da kyau tayi domin ta tabbatar wa kanta shin muryan mutun take jine ko dai aljani ne mai wannan karatun dan ita dai a chikin bil adama kam bata taɓajin voice mai daɗin wannan ba, mikewa tayi zaune a saman gadon, tafara bin ɗakin da kallo.

    mamaki ne ya kamata yaushe ta zo ɗakin nan kuma? Waya kawota? Dan ita jiya kwata kwata batama san in da kanta yake ba, yan waige waige ta fara yi tana neman ta in da take jiyo wannan kira’an Alqur’ani mai bala’i daɗin, karaf idon ta ya sauka kan shi yana zaune saman dar duma yana rike da Alqur’ani mai girma yana karatu, tasha ruwan mamaki wai daman yaya prince ɗin nan ya iya karatu? wai da gaske ne daman yana da imani? Ashe yasan Allah? Ashe yasan in da gabas take? ai na ɗauka shikam in ban da bindiga ba abun da ya sani, da wani zuchiyar sa kamar na Abu lahabi, duk girma da kima da mutunci da fiyayyen halitta manzon rahma yake da shi sai da abu lahabi, ya rinka kokarin kashe sa, to haka yaya prince ka ke duk mai mutunchi da imani da kima wadda Allah ya ɗaura maka responsibility sa a kanka komai kyaytatawar da zai maka sai ka nemi ka masa rashin mutunchi kai mutun baya taɓa kyau tata maka ko mai aka maka laifi ne, tayi nisa chikin tunani da take kamar daga sama har tsakiyar kanta taji voice nashi “ke sauka kije ki kawomin Black tea mara sugar! Chikin sauri ta diro daga gadon ta nufi waje mai da kanshi yay kan karatun da yake ya chigaba.

    Jim kaɗan sai gata ta shigo rike da Cup mai shegen kyau gefen sa tazo ta tsugunna murya na rawa tace “gashi nan yaya prince” ko kallon in da take bai yi ba, shiru shiru sai zuba kiraar karatun qur’ani kawai yake tun hiyana na sa ran zai ansa har ta chire rai ta gaji da tsugunno gashi ba wani isshen lfy ke gareta ba, Almost 30mins tana tsugunne a wajen har barchi ya ɗan fara ɗaukan ta, slowly ya sa hannu ya ansa cup ɗin, da kyar ta iya mikewa sai kuma ta kasa komawa saman gadon nashi ta kwanta, gani take kamar idan ta hau zai mata tsawa yace ta sauka, shiru tayi tana tunanin ta haune ko dai ta koma Palo, dan bata son tsawan nan da yake mata ko kaɗan, daga karshe dai ta yanke shawarar komawa saman sofa set dake chikin ɗakin dan tana ganin hakan ne ɗan dama dama.

    Saman doguwar kujera ta kwanta ta lunshe ido, har barchi ya fara ɗaukan ta sanyi mai karfi ne taji ya fara ratsa gaba ɗaya jikin ta, takurewa tayi waje guda, sai rawan sanyi take, har karfe 2:45am ba abun da kakeji a chikin ɗakin sai karan hakoran ta dake kakkarwa suna haɗuwa da juna
    mikewa yayi ya mai da Qur’an mazaunin sa bayan ya gama karatun dawo yayi ya naɗe daddumar ya nufi gadon sa, hayewa yayi ya kwanta yaja blanket zuwa dai dai chikin sa, ƙaran sautin haɗuwar da hakoran ta keyi ne suka takura masa, chikin tsawa yace “ke zaki dai na damuna ne ko sai na ɓallaki!? Da sauri ta sanya hannu ta toshe bakin ta ta dungule waje gida, rmt ra ɗauko ya kara gudun Ac sosai ya mai da ya ajiye, ya ɗan kara hasken din light dake gefen gadon ya lumshe ido ba jimawa barchi yayi awon gaba da shi.

    Hiyana kuwa barchi ya gagara, sai juyi take saman kujera sabon zazzaɓi ne ya rufe ta tun tana iya hakuri har ta fara kuka kasa kasa, gashi yace bai san jin karan sautin hakoran tama bare kuma kuka sosai ta toshe bakin ta, ta rasa in da zata sa ranta, shiko sai sharara barchin sa yake a haka har asuba, bata yi barchiba tayi kukan ta kasa kasa har ta gaji tayi shiru, tana jin sa ya tashi yayi wanka ya shirya chikin jallabiya fara ya fice ya nufi masallaci, yana fita ta chire hannun ta daga bakin ta, ta saki wani marayan kuka da kyar ta tashi ta nufi toilet na shi sauri sauri tayi wanka da ruwa mai zafi sosai, ta fito ɗaure da towel nashi ta nufi Palo, kamar zatayi kuka lokachin da take duba kayan da zata sanya dan tayi sallah gaba ɗaya babu kayan arziki, daga rigar da wando masu kama da 1 sai doguwar riga mara hannu, ji take kamar taje ta dauko Zahra ta mata mugun duka dan haushi, da kyar ta samu wani bakin wando da rigarsa fari mai hannu ɗaya, hannun ɗayan ma ɗan siriri da shi da babu duk ɗaya ne, komawa tayi chikin ɗakin sa da sauri ta sanya kayan ta ɗauki blanket na shi ta rufa a jikin ta daga kanta har kasa ta shin fiɗa daddumar tayi Sallah, tana idarwa ta mai da blanket ɗin ta naɗe daddumar, ta ɗauki Cup da yasha black tea da daddare ta fice daga ɗakin ta mai da kitchen, tunani ta shigayi shin yauma naje na gyara masa ɗaki ne ko dai na kyalesa kar yazo yamin hukunchin irin na jiya.

    Da wannan tunanin ta koma betroom nashi, gadon ta nufa ta chire bet shirt ɗin ta nufi waje ajiye kayan datti ta ajiye ta dawo ta shiga dressing room ta ɗauko wani dankareren bet shirt fari tas mai bala’i kyau da tsada ga laushi kai ka che audigane, sauri sauri ta shinfiɗa gadon ta sauko ta nufi toilet ta wanke masa fes ta gyara ko ina a chikin ɗakin, ta sanya turare mai bala’i kamshi, shiru ta tsaya tana mai da numfashi tunani take in koma palo in zauna ne ko dai in zauna a nan kar kuma na zauna a nan ya dawo ya fara faɗa, dan shi bazaka taɓa gane menene idan ka masa dai dai da kuma ba dai dai ba, yanzu na samu ya fara ansan abu daga hannu na bai kamata nayi masa wani laifin da zai sa ya dai na hakan ba, jiki ba kyari ta fito palo ta zauna saman sofa, tayi shiru tana tunanin chan ta tuno ashe tana da waya, mikewa tayi chikin sauri ta ɗauko wayar a chikin akwatin ta, ta kunna babu charji, mikewa tayi ta sanya wayar a chaji ta dawo ta zauna.

    Karfe 6 Bgs ya shigo palon yana waya betroom nashi ya nufa har ya kai bakin kofa sai kuma ya juyo kallo ɗaya ya mata ya kauda kai tare da chere wayar daga kannun sa, daga in da yake tsaye ya sai ta ta da wayar alamar tazo ta ansa, chikin sauri ta miƙe ta garisa gaban sa ta sugunna ta ansa watar juyawa yayi ya shige chikin betroom ɗin.

    Manna wayar tayi a kunnen ta, chikin sanyi da girmamawa duk da batasan wanene ba tace “Assalamu alaikum ina kwana” daga ɗayan ɓangaren Ammi tace “lfy hiyana Ykk y gida? Chike da farin chiki da zumuɗi tace “Ammi ina lfy ya gida yasu Abba wlh ina kewar ku dukkan ku” “sunanan lfy muma muna kewar ki” “ayya Ammi ki sa a dawo dani gida kinji na gaji da nan banason kasan nan ko kaɗan” jin abun da hiyana tace ba karamin ɗagawa Ammi hankali tayi ba hakan ya tabbatar mata da Bgs baya kula da hiyana idan yana kula da ita bazata yi wan nan furuchin ba, wani irin bakin chikine ya tokarewa Ammi makoshi awan nan karo gaskiya bazata kyale Bgs ba ya isa haka “Ammi ya naji kin yi shiru ko dai kin kashe wayar ne? Muryan hiyana ta katse mata tunani da sauri tace “aa ban kashe ba, kina jina hiyana yanzu zan sanya yayan naki ya sai miki waya yau ɗin nan anjima sai muyi magana da wayar ki yanzu kam ki bashi wayar sa” Ammi ai jiya yaya Khalid ya sai mana waya dukkan mu nawa babu charji ne yanzu nasa a charji idan yayi charji zan ansa number ki ko wajen Aunty Zahra ne sai na kiraki” mamaki ne ya kama Ammi lallai ba karamin abu Bgs kewa hiyana ba tun da gashi shine mijin ta amma batace zata ansa number na awajen Shi ba sai dai wajen Zahra yarinya kwata kwata bata so ayi mata zanchen sa, amma bari na ɗan tambaye ta “Hiyana ina yayan ki? “Yana ɗakin sa Ammi” “to naga lokachin tafiyar su wajen aiki ya kusa kije ki tayashi shiryawa mana zamuyi waya anjima” “kai Ammi! Shiryawa kuma kinason ya….sai kuma ta yanke maganar tace “to Ammi bari naje” hmmmm kawai Ammi tace dan ta rasa me zata che da Hiyana, chikin karyewar zuchiya tace “to hiyana ki je ki kai masa wayar In Sha Allah daga yau kasar zata fara yimiki daɗi kinji? “To kawai hiyana tace tare da mikewa ba tare da ta katse kiran ba ta nufi betroom nashi

    da sallama a bakin ta ta shiga yana tsaye gaban mirrow yana shafa mai, gaban sa dazo ta tsugunna chikin sanyin murya tace “yaya prince ina kwana ga wayar” shiru yayi bai ansa mata gaisuwar ba kuma bai ansa wayar ba, aikin gaban sa kawai yake, Almost 10mins tana sugunne shi kuma ya gama shafa mai yana gyara gashin, chike da tsoro tace “yaya prince dan Allah ka ansa wayar mana wlh ji nake kamar zan faɗi kai na na chiwo sosai” shiru kamar baya wajen duk wannan abun da suke Ammi na jin su dan bata katse kirar ba, sai da ya gama abun da yake san nan ya ansa wayar ya wuche dressing room dan shirin zuwa wajen aiki, sauri sauri Hiyana ta miƙe ta fito ta nufi kitchen already jourfree ya gama shirya breakfast na bgs ɗauka tayi ta nufi betroom nashi.

    Tana shigowa dai dai lokacin ya fito daga dressing room ya shirya chikin haɗaɗɗadiyar suit ash colour, da alama wani meeting zai je ba ƙarin kyau kayan suka masa ba, sun kara fito masa da ainahin suran jikin sa, kyawun sa ya kara bayyana sosai, ya ɗaure lallausan bakin gashin kan nan nashi, sai wani haske da ya kara, fiskar nan tashi a ɗaure take sosai kamar wadda akayiwa wani abun, dan yanzu da yake tsaye gaban mirrow fiskar a ɗan sake, daga shigan sa dressing room ya fito fiskar sa ta sauya sosai, ɗamtsen hannun san nan kullun kamar kara hurasu ake sai kara chika suke kamar zasu fasa hannun rigar,
    sosai hiyana ke satar kallon sa ta kasan ido tana addu’ar Allah ya dai dai ta tsakanin su, kwata kwata bata son ya fahimci tana son shi shiyasa bata taɓa yarda tayi gigin kallon face nashi kai tsaye sai dai ta rinƙa satar kallon sa ta sanya wa ranta ko mutuwa zatayi da son sa bazata taɓa bari ya fahimci tana son nasa ba.

    Saman table ta ajiye masa abincin, ta tsaya awajen tana jiran shi yazo tayi sarving na shi

    Sake feshe jikin sa yayi da perfume nashi mai bala’i kamshi da daɗi sannan ya nufi saman sofa ya zauna, chikin sauri ta fara haɗa masa tea ta miƙe masa, sai da ya ɗauki tsawon 2mins kafin ya ansa cup ɗin, a hankali ya kai cup ɗin sai tin dan karamin bukin sa ya fara sha tea ɗin, kasa kasa hiyana ke satar kallon yadda yake shan tea ɗin kamar bai san sha, zuba masa chips tayi a plate tare da soyayyun kaji, ta dora saman table ɗin ta matso masa da table ɗin, komawa gefe tayi ta zauna tana jiran ya kammala ta kwashe kayan.

    Muryan sane ya daki gogon kunnen ta yana faɗin “kije ki ɗauki magani a drawar chan ki sha guda biyu bayan kinchi abinchi, san nan idan kika sake magana ta da Ammi kin san sauran” murya na rawa tace “kayi hakuri yaya prince bazan sake ba” shiru yayi bai sake magana ba yachi gaba da shan tea ɗin sa mikewa tayi ta nufi drawer ta ɗauko maganin ta fice daga ɗakin ta nufi kitchen

    abinci kaɗan ta zuba a plate ta dawo palo ta zauna, a nitse ta chi abin chin ta ta sha ruwa sannan ta sha maganin tana kokarin mikewa ta nufi ɗakin, shi kuma yana fitowa, kasa kasa chikin tsoro tace “adawo lfy Allah ya tsare” a’sukwane ya juyo ya kalleta nan take taji numfashi ta ya tsaya duk wani jini dake gudu a jikin ta sai da ya tsaya chak addu’a ta shigayi Allah yasa ba laifi tayi ba faɗin hakan da tayi, juyawa yayi ya chigaba da tafiya ba tare da yayi Magana ba bin bayan sa tayi da kallo har ya fice, yana fita ta sauke nauyin ajiyar zuchiya tare da miƙewa ra nufi betroom ɗin

    Kwashe kayan abin chin tayi ta maida kitchen ta dawo ta kara kyara ɗakin ta shiga toilet na shi tayi wanka a gurguje ta fito ɗaure da towel nashi wadda yazo mata har kasan guiwa, fitowa tayi ta nufi betroom nasu Fahad, sallama tayi a bakin kofar, Amrat na daga chiki ta amsa tare da faɗin “Aunty Hiyana ki shigo mana yaya Fahad baya nan” “aa Amrat ni bazan shigo ba ki kawomin hijabi idan akoi a chikin kayan ki” “Aunty hiyana hijabin ɗan karamin ne fa bai wuchi ya tsaya zuwa kirjin ki ba” “eh kawomin” bata karisa rufe baki ba amrat ta fito rike da wani haɗaɗɗen dan karamin hijabi mai stone a jiki, pink colour ta mika mata, chikin sauri hiyana ta ansa ta sanya a jikin ta ta juya batare da ta kara Magana ba sauko palon kasa tayi, ta nufi part na su Zahra.

    dai dai zata shiga part ɗin Zahra na fitowa karo suka kusayi baya hiyana tayi tana hararan Zahra “lfy kike harara ta Aunty hiyana? Zahra ta tambaya tana guntse dariya dan tasan batun hijabi ne ya kawo hiyana “yanzu Aunty menen hakan dan Allah ki bani hijabi idan kina da shi wlh yau da blanket ɗin yaya prince na rufa nayi sallah” “dan Allah Aunty Hiyana da gaske kike yi yau da blanket na yaya prince kikayi Sallah” hararan wasa hiyana ta wurga mata kafin tace “eh mana” dukawa kasa Zahra tayi tayi sujudur shukur tana ɗagowa ta rungumi hiyana tana faɗin “Alhadulillah Alhamdulliah ya Allah na godema da ka nunamin wannan rana ya Allah ka dauwamar min da yar uwata chikin farinchiki ya Allah kasa yaya prince ya so ta sosai” “ke Aunty Zahra waya che miki sona yake, baya nan fa na ɗauki blanket na shin kema ai kin san da yana nan ban isa ba” “Aunty Hiyana ke dai karki damu jiya kwana nayi ina sallah ina miki addu’a Allah ya juyo da hankali yaya prince gareki” “hmmmm ko kuma kwana kikayi kina zubawa yaya Khalid iya shege ba” “kai Aunty hiyana to duk ma ba wan nan ba yaya khalid ne yace daman naje na sanar dake ki shirya zamuje yanzu nan ya mana registration zamu koma school” “da farinchiki Hiyana tace “kai Alhadulillah Alhamdulliah daman na gaji da zaman gidan nan, yanzu dai Aunty Zahra dan girman Allah ki bani hijabin ki da kika sanya da zamu zo nan kina ga fa ko hijabin sallah bani da shi” “kimin alkawarin iya sallah zaki rinƙayi da shi kawai” “Aunty Zahra na miki alkawari iya sallah kawai zan rinƙa yi sai kuma idan zan fito palon kasa ya miki? “Eh ya min kije ki shirya zan kawo miki hijabin yanzu” to kawai hiyana tace ta juya ta koma part nasu Zahra kuma ta koma ɗaki

    8pm dai dai Khalid ya ɗauki su hiyana suka tafi registration yaje ya musu sannan suka wuche wajen sayyaya saya musu duk wani abun da zasu bukata na makaranta yayi sai karfe 1pm dai dai suka dawo gida kowa ya wuche part nashi.

    Hiyana na shiga part nasu kai tsaye wajen da ta ajiye trolley kayan ta ta nufa dan ta sanya kayan school nata a chiki, da mamaki take bin wajen da kallo, gani babu trolley ɗin awajen lallaɓawa tayi ta leka betroom ɗin ta tagani ko yaya prince yasa an kai su chan, gani tai basa chiki, juyowa tayi ta nufi betroom nashi, da mamaki take kallon yadda jourfree ya shirya mata trolley ɗin ta a chikin ɗakin tunani take to waye yace jourfree ya kawo mata kayan ta nan kar yaya prince yazo ya hukun tata yayi tunanin ko ita ta kawo su ɗakin, jiki ba kwari ta nufi trolley, zuge zip ɗin babban tayi ta zuba kayan makarantar nata a ciki, ta miƙe ta wuche toile

    sauri sauri tayi wanka ta fito gaban mirro taje ta tsaya chike da tsoro ta fara shafa man shafawar sa tanayi tana tunanin karfa yaji kamshin man shi ajikin na ya hukun tani, hannu ta kai zata ɗauki perfume nashi sai kuma ta fasa ta juya taje ta ɗauko wasu sheɗanun riga da wando kwata kwata rigar babu hannu, ita kuwa wando crazy che duk an tsastsaga ta a dai dai chinyoyin, sosai kayan suka matse ta, chinyoyin ta kamar zasu fashe, ɗaure gashin kanta tayi ta ɗauki hijabin Zahra ta sanya, ta fito ta nufi kitchen, already abin chin Bgs na shirye ɗauka kawai tayi ta koma part nasu, saman table da ta saba ajiye masa a nan ta ajiye ta kara gyara masa ɗakin ta nufi wajen turaren ɗaki dake gere chikin wani box glass mai ɗan girma wani haɗaɗɗen turare ta zaɓo mai bala’i kam shi ga daɗi, gaba ɗaya lungu da sakon dake chikin ɗakin sai da tabi ta feshe air freshener nan ta kara gudun Ac ta fito ta zauna a Palo, ta ɗauko wayar ta, ta kunna ta shiga massage dan ta duba massage ɗin da yaya Khalid yace ta duba, tana kokarin fara karan tawa sai taji takun sa alamar yana shigowa da sauri ta ajiye wayar, ta nitsu ta kame jikin ta waje guda

    Kasa kasa yayi sallma kafin ya shigo, kafin ta buɗe baki ta gai da shima har ya shige betroom nashi, chikin sauri ta gyara hijabin jikin ta, ta miƙe tabi bayan sa, zaune saman sofa ta same sa ya jingina kai a jikin sofan yana kallon sama, gaban shi tazo ta tsugunna chike da tsoro ta fara chire masa ta kalmin kafar sa tana faɗin “sannu da dawuwa yaya prince ina wuni” chikin sanyin murya tayi maganar shiru yayi kamar ba da shi tayi maganar ba, bata damu ba dan bai amsa mata gaisuwa ba idan da sabo ta saba, zame masa safar kafan sa tayi, zubawa kafan sa blue eyes nata tayi ba Karami kyau yatsun kafar sa ke mata ba, ba abun da ya faɗo mata a rai sai marin da ta sha ranan akan taɓa kafar sa da dayi tuna hakan ne yasa tayi saurin kawar da idonta gefe tare da mikewa ta ɗauki ta kalman da safan ta mai dasu wajen da ya dace

    Gaban shi ta dawo ta sugunna ta ɗauko goran ruwan faro mai sanyi daga chikin try abin chin da ta kawo masa, dauko glass cup tayi ta balle bakin roban ruwan ta zuba a chikin glass cup ɗin, ta ɗago ido tana satar kallon sa chikin sanyin murya tace “yaya prince ga ruwa” sai lokachin ya ɗago daga jinginan da yayi a jikin sofan, ba tare da kalli in da take ba yasa hannun ya ansa cup ɗin, a hankali ya kai cup ɗin sai tin dan karamin bakin sa ya fara shan ruwan, wani nauyayyar ajiyar zuchiya ta sauke wadda yasa shi ɗan kallon in da take chikin sauri ta fara kokarin zuba masa abin chi, hannun ya ɗaga mata kasa kasa ya furta “no need am ok” yana kai karshen maganar ya miƙe, da sauri ta miƙe itama ta dan duka ta anshi cup ɗin hannun sa, wuchewa yayi ya nufi toilet ita kuma ta kwashe kayan abin chin tayi waje dasu, sai murna take yau yaya prince ya bari ta chire masa ta kalma lallai yau ba zata manta da wannan rana ba, Allah dai yayiwa Ammi albarka daman ta faɗa mata daga yau yaya prince zai sauya mata to kuma gashi nan zan chen Ammi ya fara tabbata, kitchen ta mayar da kayan abin chin ta dawo palo ta haye doguwar kujera ta kwanta tare da jan hijabin jikin ta ta rufe har kafanta, ta lumshe ido kamar mai barchi.

    Maiduguri Nigeria

    Da matsanan chin gudu sosai motar su Aryan ta shararo akan mikakkiyar hanyar da zata sadasu da titin gidan Aunty farida, dai dai zasu shiga kwanan da zata sadasu da hanyar gidan Aunty farida, lokachin motan Ahzan ya danno kai, a sukwane ya taka birki, da da sauri motochin su Aryan ma suka taka birki wani wawan birki Shahram yaja wadda yasa Aryan dake zaune a gidan baya kan shi ta bugu da kujerar gaba na motar saura kaɗan motar sojojin dake gaban ya bugi motar Ahzan, chike da bachin rai Aryan yace “wani irin birki ne wannan Shahram? Murya na rawa Shahram yace “sorry sir bamusan mota na zuwa a gaban mu bane Shiyasa Allah ma ya tsare” shiru Aryan yayi bai sake magana ba ya dukar da kan sa dake matsanan chin sara masa, zuchiyar sa na bugawa da sauri sauri ji yake gaban sa na faduwa sai mai mai ta innalillahi wa inna ilaihir rajiun hasbunalluhu wani mal wakil a chikin zuchiyar sa

    A ɓangaren Ahzan kuwa chike da jin haushi ya kama marfin motar zai fita Hanan dake zaune a gidan baya kusa da Ummi tace “yaya Ahzan karka fita dan Allah kana ganin wayan nan manya manyan Sojojin daga ganin fiskar su basu da imani” “haba hanan sufa suka so buge ni, ko ina mukaje sune masu laifi dan baa shiga kwana da irin wannan gudun da suka shigo yanzu da mun samu haɗari fa? Dole doka tayi Aiki a kansu duk da suke sojoji ai sun karya doka su kaya, juyawa yayi yana kokarin buɗe kofar motar sai ji yayi ana buga glass ɗin motar, fasa buɗe motar yayi ya sauke glass ɗin, da sauri ya runtse ido yasa hannu yana goge idon na shi dan ya tabbatar wa kan sa ba mafarki yake ba kuma ba karya idon sa ke gane masaba, wani jabgegen sojane tsaye awajen fiskar sa babu annuri chikin tsawa da karfin murya sojan yace “kai ka jaye mana motar kan nan ka bamu hanya!! Nan take jikin Ahzan ya fara rawa hannun sa sai kerma yake da kyar ya iya tada motar da gudu ya bar wajen, komawa chikin mota sojan yayi suka tayar suka bar wajen da gudun gaske.

    UMMI

    “Aunty hanan ji nake kirjina na bugawa da karfi zuchiya ta sai tsinkewa take kamar wani abu zai faru dani, Ahzan dake zaune a mazaunin driver yana tuki ya ɗan kalleta ta chikin mirrow motar yace “haba Ummi kawai kin tsoratane saboda haɗarin da muka kusa yi, ba wani abu da zai faru dake ki chigaba da faɗin hasbunalluhu wani mal wakil kinji? Gyaɗa masa kai Ummi tayi alama to, suka chigaba da tafi suna hiran irin sayayyan da zasu idan sun karasa shopping ɗin, “amma fa ba zaku shiga shopping ɗin nan ba jira zakuyi a mota ni zanje na sayi komai ba dan kun matsa ba ma da ba zaku bini ba” Hanan zatayi magana ya ɗaga mata hannu dai dai lokacin da yake shiga gate ɗin super market ɗin.

     

    To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    Wannan page ɗin sadaukar wane gareki masoyiya Gidan Aunty ya Allah ya baki lfy Allah yasa kaffara ce

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 7

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 7

    Book 2

    *Episode 7*

    9pm jet ɗin yaya prince yayi landing a kasar London United Kingdom, ba tare da ɓata lokachi ba Bgs ya miƙe ya nufi hanyar fita, wasu jibga jibgan rundunan sojoji masu ji da karfi da lfy a gere daga farkon in da jet ɗin yake har wajen motochin da akan tana da domin ɗaukan su Bgs zuwa gida layi biyu suka geru ga wani haɗaɗɗen farin karfet da aka shinfida daga farkon jet ɗin har zuwa wajen motochin

    A hankali Bgs ya sako kafar sa wajen jet ɗin nan take wayan nan rundunar sojojin masu ji da lfy da karfi suka fara ɗaga hannu suna sara masa tare da buga kafa ga dubbannin yan jarida dake chike awajen suna son suzo suyi hira da Bgs amma suna tsoro dan shi kullun fuskar sa babu alamar wasa kullum a ɗaure take tam,ganin hakan yasa suka saita Camera kawai suna ɗaukan sa hoto batare da yayi Magana ba, bai bi ta kan kowaba ya fara taku irin na jaruman maza ya sauko ya fara tafiya kan wan nan farin karfet da aka shin fiɗa masa, duk in da yazo wuchewa sai sojojin sun ɗaga hannu sun sara masa, bai tanka kowa daga chikin suba kai ko kallon in da ma suke bai yiba, ya nufi motar tun bai karisa wajen motar ba Abdol ya buɗe masa kofar motar yana ƙarisowa ya shiga ya zauna hannu Abdol ya ɗaga ya sara masa tare da rufe kofar motar.

    A tare Yusuf da Khalid suka fito rike da hannun matan su gaba ɗaya sojojin sun sha ruwan mamaki ganin Yusuf da mace, dan sun san halin sa ƴaƴan manya manyan yan siyasar dake kasar sunyi ta bibiyar Bgs Aryan da kuma Yusuf amma ko ɗaga ido su kallesu basu ɗaba yiba kuma har yanzu akoi wasu da suka nache su dai dole sai Bgs, gaba ɗaya yan jaridun dake wajen suka dakata da daukan Bgs suka komar da Camera kan Yusuf da Khalid dan sun sha ruwan mamaki ganin su da mata.

    Fahad Ahmad tare suka fito suna yar hira sama sama nan dai suma yan jarida suka fara ɗaukan hoton su kowa jira yake yaga fitowar tager Aryan amma shiru shiru daga karshe hiyana tare da amrat suka fito, dai dai tsakiyar karfet ɗin nikaf na hiyana ya kwanche, ya gangaro ya rufe mata ido hannu tasa ta chiro nikaf ɗin gaba ɗaya, ta rike a hannun ta, nan take kallo ya dawo kanta manya manyan Generals na sojoji da manya manyan yan siyasan da su kazo tarban su Bgs sai wani kallonta suke suna lashe baki da mamaki sojojin dake wajen ke kallon hiyana ɗaya daga chikin yan jaridan ne ya matso kusa da ɗayan yace “kai kaga wata hurul ai, mai kama da Brigadier General Safras anya wan nan ba kanwar sa bace dan kaman nin nasu yayi yawa? “Kai john wlh ka iya bakin idan ba haka ba yanzu zaka jika a bakon waje, shiru sukayi suka chigaba da bin hiyana da Camera suna ɗaukan ta gaba ɗaya jama’ar dake wajen kallon su ya dawo kan hiyana da Amrat chike da jin haushin hakan Fahad yace “wai sister’s ba zakuyi sauri ba!? Da sauri suka kariso wajen

    motar da yaya Ahmad ya shiga shi suka shiga a tare motochin suka bar Airport ɗin suka nufi gida

    Motochin na parking a chikin gida Bgs ya fito ya nufi chiki gaba ɗaya su Fahad ma suka fito suka bi bayan sa, a babban palon kasa suka zauna, Bgs da Fahad kuwa part na Bgs suka wuche basu tsaya a palo ba, kallon Yusuf Khalid yayi san nan ya dawo da kallon sa kan hiyana dake sunkuye da kai kasa ya fara magana

    “Sister ki tashi ki bi mijin ki part na shi kije kiyi wanka ki huta idan kin shiga palon, zakiga kofofin guda uku a chiki to ki shiga ɗakin gefen hagu kinji shine ɗakin ki na tsakiyar kuma ɗakin yaya prince ne” ya karisa maganar yana nuna mata part ɗin Bgs da hannu “to kawai Hiyana tace san nan ta miƙe jiki ba kwari ta haura sama bin ta da kallo sukayi har ta karisa haurawa ta shiga part ɗin Bgs, dawo da kallon sa Khalid yayi kan Amrat yace “kema sister Part ɗin da Hiyana ta shiga nan zaki je domin da alama mijinki a part ɗin Bgs zai zauna ina tunanin yana ɗakin gefen dama, kije kema kiyi wanka ki huta sai anjima idan mun haɗu wajen chin abinchin” to Amrat tace tare da miƙewa itama ta haye sama, hannun Zahra ya kama tare da miƙewa yana faɗin “sis love muje ko, tsaki Yaya Ahmad ya ja kafin ya miƙe ya nufi part nashi yana faɗin “nima dai na kusa Auren nan, dariya Yusuf yayi tare da miƙewa ya ɗauki Lamrat chak kamar yar baby ya nufi Part na shi da ita

    Da sallama Amrat ta shigo ɗakin da yaya Khalid yace taje,ɗaki ne mai girman gaske ɗauke yake da wani katafaren gadon mai shinfiɗe da White bet shit ba ƙaramin kyau gadon yayi ba, ga wasu haɗaɗɗun sofa set 1 Brown da milk a tsakiyar kujerun akoi wani haɗaɗɗen sofa table daga gefen dama kuwa wasu tagwayen kofofi guda biyu ne awajen da alama ɗaya kofan toilet ne ɗayan kuma dressing room ne ta shagala da kallon haɗuwar ɗakin sai ji tayi an sunkucheta chak sai kan gado.

    A hankali ya kwantar da ita chike da kulawa yace “tsoron ɗakin kike ne? “Aa kawai ina kallon ɗakin ne” “ya miki kyau kenan? “Eh mana yaya Fahad ɗakin yayi kyau sosai” “ok to tun da ya miki kyau a nan zamu zauna daman so nake mu koma Part na yaya Aiman amma bari mu zauna a nan kawai tun da kina so ɗakin” shiru tayi batayi magana ba kallon fuskanta yake sosai ji yake kamar ya mai data chikin sa, kasa kasa da murya kamar mai raɗa yace “tashi muje na miki wanka” dariya tayi wadda yasa dan siririn wushiryar dake tsakanin fararen hakoran bayya, chike da yaranta tace “yaya Fahad ai na iya wanka ni ba sai kamin ba “eh ai nasan kin iya tun da kullun ke kikeyi amma yau ni zan miki da kai na” zatayi magana yayi sauri haɗe bakin su waje guda sosai yake kissing nata sai da yayi kissed nata mai isar sa san nan ya saketa yana kallon face nata, turo ɗan karamin bakin ta tayi chike da yarinta ta fara magana “yaya Fahad wai kai sai ka rinka shawa mutun baki kuma fa yana min zafi” murmushin gefen fuska yayi kafin yace “ai ba bakin ki bane na wane kuma sha kam yanzu na fara muje na miki wanka sai mu dawo na chigaba da sha” “to yaya Fahad baki na ɗin yana maka daɗine? “Sosai ma kuwa ai bakin ki yafi zuma daɗi amma kefa ba ki faɗamin ba nawa bakin akoi daɗi? “To ai ni ban taɓa shan naka ba kullun kai kake shan nawa” “ok to yanzu kema ki sha nawa sai ki faɗamin akoi daɗi ne ko babu” yayi maganar ya kara haɗe fuskokin su sosai, chikin nitsuwa Amrat ta kamo lip nashi na kasa tafaɗa sha kamar yadda yake mata, wani irin shock yake ji bai ma san lokachin da ya rungumeta gaba ɗaya ya maido ta kirjin saba wani irin salon kiss ya shiga yi mata, lokachin guda ya ruɗe sai wani numfashi mai zafi yake fitarwa, kuka Amrat ne ya dawo dashi daga duniyar da ya faɗa, a hankali ya zame jikin sa daga nata ya ɗan koma gefe

    da kyar ya iya buɗe bakin sa chikin dashewar murya yace “me ya faru ki ke kuka? Chikin shesshekar kuka tace “ba kaine ka danne niba kuma kirji na yana min zafi ga baki nama zafi ya kemin” “oh sorry to tashi ki je kiyi wanka dan yanzu gaba ɗaya jikina ya mutu ba zan iya ɗagaki ba” yun kurawa tayi ta miƙe ta sauko daga kan gadon ta nufi toilet, binta yayi da ido har ta shige chikin toilet ɗin shafa kansa yayi tare da sauke ajiyar zuchiya, kasa kasa yace “wai me ke damu na ne Fahad? Me yasa duk lokacin da naga yarinyar nake kasa samun kwanchiyar hankali har sai ta kasan che kusa dani, kwanchiya yayi tare da lumshe ido yana jiran fitowar ta

    Kwance yaya Yusuf yake saman katafaren gadon sa yana latsa waya, jin an buɗe kofar Toilet ne yasa ya ɗago yana kallon ta ɗaure take da towal a kirjita ta sanya hijabi zuwa guiwa murmushi yayi kana ya mata nuni da hannu akan tazo ba musu taje kusa dashi ta zauna hannu yasa ya chire mata hijabin dake jikin ta sunkuyar da kanta kasa tayi “kunya ta kike ji ne my baby? Shiru tayi batayi magana ba, hannu yasa ya ɗago haɓarta “ya jikin naki? Kasa kasa kamar wadda bakin ta ke chiwo tace “da sauki” jawota yayi ta faɗa kan kirjin sa ya juya da ita ya mai data kan gadon ya mata runfa da kirjinsa “me yasa kike jin kunyata my baby? Runtse ido tayi tace “babu komai yaya Yusuf kawai dai ina jin bazan iya haɗa ido da kai bane” “mmmm amma zaki iya haɗa baki da ni kam ko? Da sauri ta waro idon ta waje tana kallon sa “kunyar ya tafi ne kuma? naga kin buɗe ido Hannu tasa ta rufe fuskar ta tana murmushi, “my baby ni ki faɗamin wai kin samu sauki ne dan nifa inason ki haifa mana baby masu kama dake da wuri, zame hannun ta tayi daga kan fuskar ta chike da zumuɗi tace “yaya Yusuf nima wlh ina son baby’s dayawa pls” kara matsowa kusa da ita yayi har dogon hanchin su na gogan na juna kasa kasa yace “kin shirya ansan baby yanzu ne? “Eh yaya Yusuf ni ko yanzu aka bani ina so kuma ko guda 12 za’a bani inaso” “to waye zai bakin? “Ni ma ban sani ba ina chewa a asibiti ake bawa mutun idan yaje” murmushin kaɗan yayi chike da so da kauna yace “aa duk duniya ni kaɗai ne zan iya baki baby” “yauwa yaya Yusuf to dan Allah ka bani yanzu kaji pls “kin shirya na baki yanzu? “Eh Allah na shirya kawai ka bani inaso amma biyu zaka bani sai na kaiwa Aunty hiyana ɗaya” “ok yanzu kuwa zan baki yan uku ma ba yan biyu ba” zatayi magana ya haɗe bakin su, waje guda waro ido waje lamrat tayi tana kallon sa hannu yasa ya rufe mata ido ta saman kanta, sosai yake kissing nata chikin dabara ya kwanche towel dake jikin ta ɗayan hannunsa ya kai kan breast nata ya shiga shafasu yana ɗan murza yan kananan bakin, zame ɗayan hannun sa yayi daga kan face nata ya zura shi ta bayan ta ya tallaɓota da kyau ya shiga murzata ta ko ina.

    Lamrat da taga dai ba zai chire bakin sa daga chikin nata ba sai ta gabza wa harshen sa chizo ba shiri ya same bakin sa daga nata yana kallon face nata ganin ido a runtse tana murmushin ne yasa ya fahimci da gangan ta chijesa kwafa yayi yace “zanyi magana nin ki yanzun nan kuwa, kafin ta buɗe ido ya mai da bakin sa kan Nipple nata,wani irin shock sukaji gaba ɗayan su chike da shagwaɓa tace “yaya Yusuf pls kayi hakuri wlh akoi zafi shiru yayi kamar bai ji me take faɗe ba ya chigaba da socking na breast nata yana murza ɗayan da hannun sa lokachi guda ya fita hayyachin sa sai wani gurnani yake fitarwa tun lamrat na rokansa akan ya kyaleta a hankali har ta fara yi masa kuka, amma ina yaya Yusuf baya chikin hayyachin sa baya jin kukan nata, chikin dabara ya zame wandon dake jikin sa tare da shot ɗin gaba ɗaya, kafin ramlat ta ankara sai taji wani azaban zafi ya ziyarche ta lokachi guda wani ihu azaba ta saki tafara kokarin ture’sa tana faɗin “dan Allah yaya Yusuf kayi hakuri wlh ba zan sake chizon kaba na tuba wlh akoi zafi wayyo Ammi kizo ki checheni yaya Yusuf zai kashe ni, duk wan nan ihun da lamrat keyi yaya Yusuf baya jin ta bai ma san tanayi ba socking nata kawai yake, yagushin chizo babu wan da lamrat bata yimasa ba duk ta ya gushe masa fuska tun tana iya ihu da karfi har voice nata ya dai na fita, Yaya Yusuf dai bai bartaba sai da ya mai data chikakkiyar mace san nan ya sauka daga kanta ya kwanta gefen ta yana mai da numfashi, ita kuwa gaba ɗaya bata chikin hayyachin ta sosai tasha wuya

    Amin afuwa yau naje anguwa sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu

     

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 12

    Book 2

    *Episode 12*

    KHALID

    ……wai dan Allah yaya khalid me yasa bazaka bar mutun ya yi barchin sa bane? “Gaskiya aa sis love ni ban hana ki barchi ba karki min sharri, ki yi barchin ki abun ki” “wai to taya mutun zai yi barchi kana taɓa shi? “Gaskiya sis love surutun ki ya fara yimin yawa dan kin samu yau na ɗan kyale miki bakin naki ya sha iska ko?” turo baki Zahra tayi chikin shagwaɓa ta dan buga kirjin sa tana faɗin “ni wlh yaya khalid dakin Aunty hiyana zan kwana gobe” dariya khalid yayi kafin yace “ai inaga sai dai Aunty hiyana nan naki tazo ta tayaki kwana gobe ba dai ke kije ba dan ba zaki samu kafar zuwa bama” zatayi magana yayi saurin haɗe bakin su, dan surutun Auta ta fara yimasa yawa, Sosai suke missing junan su yana yi tana taya shi, chigaba da murza kan nipple nata yayi yana shafa bayan ta da hannu ɗaya.

    Da kyar Zahra ta iya kwache bakin ta daga nashi da taga alamar bai da niyar sakin ta, kamar jira yake ta raba bakin nasu ya chapko Nipple nata ya shiga tsotsa kamar jariri, tun Zahra na kokarin hana shi har ta kyalesa dan gaba ɗaya ya ruɗa ta, a hankali ya zame hannun sa dake kan Nipple nata ya mai da gaban ta chikin dabara ya zame pant ɗin dake jikin ta ya shiga wasa da wajen, lokachin guda ya fita hayyachin sa, sai wani irin nishi yake yana fitar da numfashi da karfi karfi, zame Short ɗin jikin sa yayi batare da Zahra ta ankara ba, matso da bakin sa yayi dai dai sai tin kunnenta chikin wata irin yar murya dake fita da kyar yace “am sorry am so so sorryyyyyyy sis love” ɗago kai Zahra tayi tana kokarin tambayar sa sorry for what, sai taji wata iriyar azaba ya ziyar cheta lokachi guda, ihu ta fasa tare da sa hannun ta bibbiyu saman kirjin sa tana kokarin turesa daga kanta, amma ina ko motsashi ta kasa yi, ihu take tana faɗin “wayyo Allah na shiga uku Ammi na ina kike Ummi yaya Khalid zai kashe ni Abba kazo ka checheni, wayyo Allah yaya khalid wlh bana sonka mugu ka mai dani gida zan mutu wayyo Allah!! Shiko Khalid baya ma jinta socking nata yake da karfi karfi dan baya chikin hayyachin sa yana sambatu “wash my wife Allah ya miki albarka kin biyani ash Allah wai gaskiya Yusuf baka kyau tamin ba da ka rigani dan ɗana wan nan daɗin” da karfi Zahra ta gabza masa chizo a kirji amma ina bai ma san tana yi ba ya tafi duniyar sama jannati, lokachi guda Zahra ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nepa, gaba ɗaya bakajin komai a dakin sai nishin khalid.

    Sai da ya samu nitsuwa san nan ya sauka ya kwanta gefen ta yana mai da numfashi, bai ma lura da Zahra bata numfashi ba, da haka barchi ɓarawo yayi awon gaba da shi

    To masu karatu bari muleko su Inna a Yola Nigeria muga wani wai nar suke toyawa wata kila kafin mu dawo su yaya khalid ya dawo hayyachin sa shima

    YOLA NIGERIA

    sosai inna take samun sauki sai kuma wani azababben laulayin chiki da take fama da shi bata son ganin komai bata chin abin chi da zarar taji kanshin abin chi zata fara amai, abu ɗaya take iya chi shine gawayi, shine abin chinta idan ba gawayi ba babu wani abun da chikin nata ke yarda ya ansa haka zatayi ta gabzan gawayi tana shan ruwa, tun yaya Bello na mamaki har ya daina yanzu kullun idan zai zo dubata wajen mai magani sai ya sawo mata gawayi na 200 kafin gobe ta chinye.

    A ɓangaren buba kuwa ba laifi sauki ya samu sosai dan yanzu abubuwa dayawa shi yake yiwa kansa amma har yanzu kwakwalwa tasa akoi ɗan sauran matsala dan gaba ɗaya ya manta da suwaye diyana da hiyana ma.

    A ɓangaren Innar buba kuwa ta samu lfy sosai yanzu tana iya takawa da kafar ta ta fito tsakar gida, sai dai bata iya tafiya mai nisa sosai take gajiya

    Hasana matar yaya Bello kuwa baa magana yanzu laulayin chiki nata ya ragu sosai sai wani kiba da haske da tayi, ta kara kyau ta chika ta ko ina, kullun yaya Bello yana makale da matar sa yana matikar ji da chikin nan nata, duk da haka baya hana shi bawa su inna kulawa da duk abun da ya dace.

    Washegari jumma’a misalin karfe 7am Allah yayiwa bappan su yaya Bello rasuwa, ba karamin tashin hankali suka shigaba yaya Bello duk jarumtar san nan sai da yayi kwalla lokachin da ake sanya bappan sa a rami, sosai buba ma yayi kuka, da kyar aka samu jama’a suka iya lallaɓa yaya Bello ya dawo gida da yace shi ba zai iya barin kabarin bappan sa ba, a kofar gidan su jama’a ke zaman makokin bappa, Inna ko tana chan wajen mai magani tana fama da laulayin chiki bata da masaninyar bappan su Bello wato ya’yan ta ɗaya tilo a duniya ya rasu, bayan rasuwar bappa yaya Bello yazo wajen ta har sau uku amma yaki sanar da ita dan kar ta kara chiwo kan chiwo.

    Wan nan kenan tun da munji halin da mutanen yola ke chiki sai mu koma London dan muga ne ake ciki

    Uk

    Sai kusan asuba Khalid ya farka daga nauyayyar barchin da ta ɗauke sa, chikin sauri ya miƙe tsaye kai kallon sa yayi kan Zahra dake kwance ko motsi bata yi, a razane ya haura saman gadon hannu yasa ya ɗagota amma sai yaji jikin ta a sake ga wani mugun zafin da jikin nata yayi alamar zazzaɓi mai zafine ya rufe ta, maidata yayi ya kwantar chikin ruɗu ya sauko daga gadon ya nufi tailet jim kaɗan ta fito ɗaure da towel, saman gadon ya hau ya ɗauke ta chak ya nufi toilet da ita, Almost 45mins san nan ya fito da ita naɗe a towel, sai kuka take kasa kasa, zaunar da ita yayi saman sofa ya dawo gaban gadon da kansa ya chire bet shirt ɗin ya ɗauko wani ya shinfiɗa, ɗauko ta yayi ya dawo da ita saman gadon, san nan ya sauko ya koma toilet dan yin wanka lokachin an fara kiraye kirayen sallar asuba, yana fitowa wayar sa dake masan drawer gefen gadon ta fara ringing, batare daya nufi wayar ba ya wuche dressing room, dan yasan Yusuf ne ke kiran shi su rafi masallaci, sauri sauri ya shirya chikin jallabiya baka ya fito, har lokacin kuka Zahra take, yanaso yaje ya rarrashe ta Amma, babu lokachi dan an tada kabbara a masallacin su kuma yana da tabbacin Bgs ya tafi dan shi baya jira sai dai a jirashi, dan haka sai ya kyale Zahra chikin sauri ya fice daga ɗakin ya nufi waje

    Tsaye ya samu khalid a palon kasa, ba sai ya tambayi ina Bgs da Fahad ba yasan sunyi tafiyar sune, tare suka gera shi da Yusuf suka nufi waje.

    Karfe 5:20am Hiyana ta farka chikin sauri ta sauko kasa daga kujerar, mikewa tsaye tayi ta fara sanɗa kamar wata ɓarauniya, ta leka ɗakin Bgs dan taga yana nan ko baya nan, tana ganin baya nan tayi sauri ta koma palo ta buɗe trolley ta ɗauki wasu kayan ta shige ɗakin sa, toilet ta nufa a gurguje tayi wanka ta ɗauro alwala, ta fito ɗaure da towel nashi rike da kayan da ta chire a hannun ta, sauri sauri ta sanya kayan da ta ɗauko, ta zura hijabi a nitse ta shin fiɗa daddumar sa tayi sallah.

    tana gamawa ta naɗe ta mai da masa mazaunin sa, har ta juya zata fita idon ta ya sauka kan gadon sa dake watse a yamutse ajiye kayan hannun ta tayi ta haye gadon ta fara gyara masa, tanayi tana surutu “yanzu ni ya kamata na rinƙa gyara gadon nan ba mai aiki ba gaskiya, kai bama gadon ba har ɗakin gaba ɗaya amma idan ya tafi aiki zan rinƙa zuwa ina gyra masa dan na rinƙa samu ladan yiwa miji hidima dole na san yadda zan yi na dakatar da mai Aikin nan da shiga ɗaki nan” tana ta surun ta har ta kusan kammala gyara gadon.

    tana ɗago blue eyes nata karaf sai kan face nashi yana tsaye a bakin kofar shigowa ɗakin yana latsawa waya, chike da ruɗu da tashin hankalin ta diro kasa daga gadon ta sungunna, murya na rawa tace “ina kwana taya price, shiru kamar bai ma san da mutun awajen ba sai latsa wayar sa yake, Almost 15mins yana tsaye yana latsa waya ita kuma tana sugunne.

    Chikin tsawa yace “in my room!! On my bed!! Chikin rawar murya tace “kayi hakuri yaya prince wlh ba zan… Bata kai karshen maganar ba ya daka nata wani uban tsawa wadda yasata mikewa ba shiri “shoot up!! Oya fara frog jump, daga yanzu har na dawo aiki! yana kai karshen maganar ya karisa shigowa chikin ɗakin bai ko kalli in da take ba, ya wuche toile

    tsallen kwaɗo hiyana ta fara, tun tana yi da sauri sauri har ta fara a hankali hankali, kuka kasa kasa ta fara dan ta gaji gashi yace daga yanzu har karfe 2pm idan ya dawo aiki, gashi mutun ne da idan yayi magana baya sauyawa dan haka No need ta bashi hakuri dan kota bashi bata bakin ta zatayi idan ma batayi Sa’a ba ya kara mata da wani hukunchin.

    Wanka yayi ya fito ya shirya chikin wandon jeans blue da t-shirt ash, ya gyara lallausan bakin gashin kannan nashi ya watsa a baya ba tare da ya ɗaure gashin ba, booth blue ya sanya a kafar sa ya ɗaura wata danƙareriyar agogo diamond a hannun sa, wayar sa ya ɗauka ya nufi waje yana jin hiyana na kuka tana tsallen kwaɗo amma ko ajikin sa kamar ba mutun che ke kuka ba yayi fuchewar sa.

    A harabar gidan ya sami Fahad na tsaye ya harɗe hannu a kirji shima ya shirya chikin wandon jeans blue da t-shirt fari, yana ganin Bgs ya fara ɗaga masa gaisuwa, ba tare da ya amsa gaisuwar ba kasa kasa yace “yauma bina zakayi? Ya kamata ka fara Aikin ka fa, “yaya prince to ai kai ya kamata ka samomin aikin ko? “Aiki kam ai yana zaune yana jiranka duk time da ka shirya kuma duk matsayin kujerar da kakeso yanzu dai ina Yusuf da Khalid? “Basu fitoba” batare da ya sake magana ba ya wuche ya nufi waje motochin sa, Fahad ya bi bayan sa, dai dai lokacin Yusuf ya fito shida Lamrat ta rakosa har waje suna rungume da juna, ganin Fahad da Bgs yasa Lamrat kwache jikin ta da sauri ta fara gaidasu, Fahad ne kawai ya tsaya yana amsa gaisuwar tata shiko Bgs ko kallon in da suke bai yi ba yayi wuchewar sa.

    Fahad na gama ansa gaisuwar lamrat shima ya ɗagawa Yusuf gaisuwa, da fara’a Yusuf ya amsa tare da tambayar “ina yaya khalid? “Bai fitoba” Fahad ya bashi amsa lokachin da yake wuchewa ya nufi wajen Bgs, juyowa Yusuf yayi yana fuskantar Lamrat, ya fara magana “my baby ki koma chiki sai mun dawo” “yanzu yaya Yusuf da gaske ba zaka tsaya kayi breakfast ba? “My baby na faɗa miki sauri muke akoi rundunar da yaya prince zai je ya sanya hannu a kan takardun su zasu tafi yaki da yan kunan bakin wake, jiya sun kama mana manya Manyan sojojin mu to shine za’a tura runduna 2 suje su yake su su kwato mana sojojin mu, baki ga gaba ɗaya jiya ran yaya prince a bache ba, kinga har yanzu ma ransa a ɓache dan haka bari nayi sauri karya hukuntani shi baya son jira sai dai a jirashi” kiss lamrat ta masa a kumatu tana faɗin “to a dawo lfy Allah ya tsare mani kai ya kareku da kariyar sa” “eyeee my baby yau ba fullanchin kenan ba jin kunya har da kiss na samu wow i can’t forget this day” sunkuyar da kai kasa tayi tace “amma ai yaya Yusuf ba da kai zaa je yakin bako? Murmushi yayi tare da kama hanyar tafiya wajen Bgs yana faɗin “ba da ni za’a jeba ki koma chikin gida” “to kawai lamrat tace tare da juyawa ta goma chikin gida

    Chikin motar Bgs ya isko Bgs da Fahad zaune nashi motar ya shige ya zaune.

    “Kai Fahad kiramin layin Khalid” chewar Bgs yayi maganar yana kokarin chiro wayar sa daga aljihu dan yaji tayi kara alamar shigowar sako, yana kunna hasken screen ɗin sai yaga sakon khalid ne, chere pin na wayar yayi ya shiga massage “kai Fahad kyale batun kiran khalid ɗin nan muje kawai” “to yaya prince amma shi yaya khalid ɗin yau lfy ba zai je wajen aikin sa ba? Shiru Bgs yayi kamar bai ji me Fahad yace ba, umarnin ya bawa sojojin sa akan sutafi, da gudu suka kunna mitochin suka bar gidan.

    Tun hiyana na iya kuka har ta kasa sai dai numfashinta dake fita da sauri sauri, sai wani wahalallen nishi da takeyi, tun asuba har zuwa karfe 8am tana frog jump.

    Tun tana iya ɗaga kafarta har ta kasa ta yanke jiki ta faɗi kasan karfet ɗin sumammiya

    Maiduguri Nigeria

    Kwanche Ahzan yake saman gadon sa yana waya, “Umar wlh ba zaka gane bane ina son ta ina kaunar ta wlh ban taɓa ganin yarinya ta shiga rai na lokaci guda ba sai ita, so bazan iya mikawa iyayen ta itaba gaskiya dan naga alama yadda ake nunata a duk wani tasha ta gidan Tv da zaridu gidajen redio da sauran su, ni nasan ba daga ƙaramin gida ta fitoba, to kaga in dai hakane, in na miƙa ta ga iyayen ta bazasu taɓa bani auren taba gara kawai na lallaɓa na chigaba da ɓoyeta har nayi na saran chusa mata sona idan yaso bayan munyi Aure na kai ta wajen iyayen ta dan kaga lokachin ba yadda zasuyi dole su kyalemu, da nayi tunanin sata school ma amma gaskiya na fasa zan rinƙa samun lokachi ina karantar da ita da kaina kaga a haka zan samu sona ya shiga zuchiyar ta, daga ɗayan ɓangaren Omar ya fara magana “amma Ahzan kana ganin hakan ba rashin adalci bane? ni a nawa tunanin idan kayiwa yarinyar nan haka baka kyau ta mataba, to duk bama wannan ba kana tunanin mum zata yarda ka Auri yarinyar da bakusan asalinta ba? “Umar mum zata yarda ni nasan ta in da zan bi mata ta yarda,
    ………….. da dai daddy na raye ne sai inche ba zai yiwuba, amma dan mum bani da wata damuwa wai kai Umar wlh idan kaga yarinyar nan sai kache nayi kokari ma dana iya hakuri na kyaleta sai an mana Aure, “kai Ahzan duk kyau ɗin ta ta kai diyana tace, wlh idan kaga diyana kai zakache ita tayi kanta yarinyar nan amma haka wanchan ban zan yayan nata ya mun duka ya raba ni da ita, amma wlh ba zan hakura ba ina samun sauki duk in da zanshiga, sai na shiga dan na samu diyana” “wai Umar ni kam aina ka samu wannan diyanar ne da kullun kake takuramin da zanchen ta? Haba kilama ko kyan gani bata da shi, ni dai yanzu zan lallaɓa daddy ya yiwa Ummi waliyi nan da next week a ɗaura mana Aure dan ma kar na ja lokachin har yan uwanta su gano tana nan, wai kasan ma awajen aiki daga manyan mu na sama aka turomana hoton ta akan mu nemota, na sa yarana suna ta yawo a gari bayan na ɓoyeta a gida kai daga ganin yadda ake neman yarinyar nan a garinnan kasan ba yar karamin mutun bane” “kai haba Ahzan karfa kaje ka jefa rayuwan ka chikin hatsari wlh gwara ka fitar da yarinyar nan ka mikata ga iyayen ta in yaso kaje ka nemi aurenta a wajen su idan sun baka to Fine idan ma basu baka ba sai ka hakura, nifa ina ganin kamar ma daddy salim ba zai yarda da batun auren ba, dan daddyn salim da Allah jikan rai dadyn ka halin su irin ɗaya, dama dai daddy Auwal ne” “lallai Umar baka da lfy daddy Auwal fa kace tab hmmm ai ban isa in tinkari dady auwal da wannan magana ba, kai dai bari yau ma dadyn kam ya wuche Us kuma har Chan zan bi shi nasa ta yadda zan ɓullo masa, zai yarda ai yadda nake son yarinyar nan ma koda daddy’na na raye sai na san yadda zanyi nasa ya yarda da abun da nakeso ɓare daddy salim kai dai kawai kazuba ido ka tayani da addu’a” “to Ahzan Allah ya shige mana gaba” “amin Omar ngd amma kasan me Omar? “Aa ban sani ba sai ka faɗa” “jiya danaje office ɗin commissioner naji suna magana wai left kanal general Aryan yazo, nasha ruwan mamaki wlh sai Allah kaɗai yasan wajen wani mai Sa’a yazo, ina masifar son ganin guy ɗin nan ba kaɗan ba da zan samu Allah ya taimake ni wani yamin hanya ba samu ganin sa koda sau ɗaya ne arayuwa ta, to dana sanya wannan ranar a chikin ranakun tarihin na wayan da ba zan taɓa mantawa dasu ba” “wai daman Ahzan kasan Kga? Ni wlh sunan sa kawai nake ji in burin naga koda hoton sane ba face Mark” “kai ina da wani hoton sa guda ɗaya wadda na taɓa turawa a wayan Commissioner, zan turoma ka ganshi amma ya sanya face mark, sai dai kaga jikin sa, da kaga jikin nashi kaga chikakken jarumin namiji, ai wlh da Allah zai nunamin Bgs da kga arayuwata ko da a mafarki ne shikenan nikam burina ya gama chika a duniya” “kai Ahzan bari ina rabaka wlh ka kiyayi kan ka domin ko shugaban kasa wuyar gani Bgs da Kga zasu masa kai dai ka bar kan ka a in da Allah ya ajiyeka” “kai dai Omar bari ai addu’a nayi kuma karkasha mamakin Allah ya haɗamu wata rana” “to Allah ya haɗamu da su ta hanyan alkhairin, dan wlh da mu haɗu da su ta hanyar sharri gwara mu mutu tun kafin lokacin” “kai Omar amin dai ka haɗu da su da alkhairin ma yaya bare da sharri yadda nake jin ana lbr su a gidajen Tv da jaridu, tab basu da wasa” “nima dai ina mugun son naga wannan Bgs ɗin sai dai duk hotunan su da ake dorawa a gidan Tv zaka samu sun sanya face mark ban san me yasa basu son barin face nasu a buɗe ba” “ai kasan wasu mutanen haka suke sun fi son a sansu ta aikin su ba ta suna ko fiskar su ba” “hakane Ahzan kana da gaskiya to Allah dai yasa mu dace” “amin Omar sai munyi waya” yana gama faɗin hakan ya katse kiran tare da sauke nauyayyar ajiyar zuchiya ya miƙe ya fice daga ɗakin.

    UK

    misalin karfe 1:30pm jourfree ya shigo ɗakin Bgs da nufin ya gyara masa ɗakin, ganin Hiyana a sume ne ya bashi mamaki, da sauri ya koma kitchen ya ɗauko ruwa ya dawo ɗakin, kusa da ita ya tsugunna ya zuba mata ruwan, a razane ta mike tana faɗin “yaya prince kayi hakuri wlh ba zan sake ba na tuba” “what are U saying madam? Jourfree ya jefo mata tambaya, dawo da kallon ta tayi kansa chikin sauri ta mike tsaye tana gyara hijabin jikin ta, kasa kasa tace masa ” “as from today i don’t want to see U here again, pls get out” chikin tsoro jourfree ya juya ya fice a ɗakin dan ba zai iya jayayya da maganar hiyana ba kuma bai san ya zasu kwashe da Bgs ba lallai akoi dirama.

    Aiki hiyana ta shigayi tama manta ya sata frog jump, yace karta tashi har sai ya dawo aiki, duk da zafin da kunburin da kafarta suke hakan bai hanata ta fara tikar aiki ba wanke masa toilet tayi tas ta shinfiɗa masa gado ta gyara ko ina ta sanya masa turaren ɗaki mai daɗin kamshi, karfe 1:55pm ta kammala aiki ta ɗauki kayan ta ta nufi hanyar fita ɗakin har ta kai bakin kofa sai kuma ta juyo, tace “kai yau dai tun da baya nan wlh sai na je wajen hutawan shin nan nagani, dawowa tayi ta nufi kofar glass dake kusa da toilet, a hankali ta tura ta shiga wajen

    wani iska mai shegen daɗi ne ke kaɗawa awajen saman kujera taje ta zauna tana bin wajen da kallo, mikewa tayi ta ɗauko ruwa da glass cup ta dawo ta zauna ta zuba ruwan a cup ta fara sha sanyin ruwan na ratsa ta sai wani lumshe ido take, tana sauke Ajiyar zuchiya, Almost 15mins tana zaune awajen har barchi ya fara ɗaukan ta, alamar tafiyan mutun da tajine yasa ta miƙe chikin sauri tana karanto duk addu’ar da tazo bakin ta, dan neman Allah ya tsareta daga faɗawa hannun Bgs.

    dai dai zata fita shi kuma yana shigowa a razane ta ja da baya, chikin fushi da bachin rai fuskar shin nan kamar hadiri a daure tamau ya damko wuyar ta ya jata zuwa karshen wajen, chikin tsawa yace “ke bana che karna sake ganin ki a daki na ba shine zaki shigomin har nan” tsabar tsorata hiyana ta kasa magana, ta kasar ido ya kalli kasar benen, san nan ya dawo da kallon sa kanta, sai faman girgiza masa kai take ta kasa magana, wurgi da ita yayi kasan benen chike da ɓachin rai ya juya ya koma chikin ɗaki, wayar sa ya ɗauka ya kira jourfree, chike da izza da bada umarni yace wa jourfree yana bukatar a chan za masa komai dake wajen shakatawar sa na chikin ɗakin yana gama bawa jourfree umarni ya wuche cikin toilet…..

    Hiyana kuwa tana fadawa chikin katon pool dake wajen, da kyar ta iya sai ta numfashi ta Allah ma yasa ta iya ruwa tun a kauye dan tun suna yara suke zuwa rafi, da kyar ta iya fitowa, kasa tafiya tayi ta zauna a bakin pool ɗin tana kuka kasa kasa dan sautin kukan nata ma baya fita sosai

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 11

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 11

    Book 2

    *Episode 11*

    Maiduguri

    misali karfe 1 na rana gaba ɗaya gidan ba kowa sai yarinyar da Ahzan ya buge da mota, hanan ta tafi school
    Mum tana wajen aikin ta a babban hospital

    zaune take a palon mum Ahzan tana chin pop corn, tana kallon film a chikin makekiyar Tv dake manne a bango.

    jin motsin mutun a kantane yasa ta ɗago kai, kallo ɗaya ta masa ta kauda kanta dan taga alamar bai yi kama da mutanen kirki ba, shiru tayi tana tunani anya wan nan ba shine yaya deen ɗin da Aunty hanan ta taɓa bata lbr ba kuwa, dama Aunty hanan tace min ɗan iskane ashe da gaske ne kaga wani gashi kamar shekan tsuntsu.

    Chike da iskilancin deen yace “ke chika yaushe kika zo gidan nan? Baa faɗamin nazo na latsaki ba irin wan nan kaya ai sai ni, wai ma wacece ke? Waya kawo ki ko dai ke yar uwar wanchan matar ne? Shiru yarinyar tayi kamar ba da ita yake ba ta chigaba da chin pop corn nata “ke chika wai ba dake nake bane!? Ko kallon in da yake batayi ba, hannu ya kai zai taɓata chikin sauri ta mike tsaye tare da yar da roban pop corn ɗin chike da izza tace “wlh idan ka kuskura ka taɓani sai na sharara maka mari! “Wow kai kaji wata voice mai shegen daɗi, gaskiya ne ke barikiji tun da kika zo gidan mu tofa taɓaki ya zama dole, idan ma zaki saki jiki gwara ki saki jiki idan kuma kinki to zaki sha wahala “kai har ka isa ka bani wahala ni bari kaji mutumin kirki ma bana tsoran sa bare mutumin banza Allah kaɗai nake tsoro” wani wawan mari ya sakar mata a kuma wadda yasa ta fasa ihu kwashe kafafunta yayi ta faɗi kasa, chikin tsawa yace “ni zaki chewa ɗan iska to wlh yau sai kin gwammachi da baki zo gidan marigayi Alhaji Abbas ba” sake dungule hannu yayi zai kai mata bugu charaf Ahzan ya rike hannun sa ta baya chike da jin haushi ya wanka wa deen wani wawan mari chikin tsawa Ahzan yace “me ya kawo ka part ɗin nan!? Chike da rashin kunya deen ya fara magana “tambaya kake ko neman sani wai shin Ahzan ko ka manta Alhaji Abbas ne ya gina gidan nan ba kai ba to idan ka manta na tuna maka kuma kamar yadda kake ɗan shi nima haka nake ɗan shi har Alhaji Abbas ya bar duniya bai taɓa yiwa wani iyaka da shiga wani part a chikin gidan nan ba kuma koda yayi ma kasan dai ni bai isa ya hanani ba” afusache Ahzan ya sake ɗaga hannu zai mari deen chikin fushi deen ya rike hannun nashi yana girgiza kai “bari kaji Ahzan ko ɗazun da ka mare ni bansan zaka kawo marin bane shisaya har ka samun daman marin nawa, yanzu lokachin ka bugeni na barka ya wuce, dan ni ba yaro bane! Kwache hannun sa Ahzan yayi chikin fushi ya fara bugun deen, damko kafar sa yayi, yayi wurgi da shi, chiro belt nashi yayi ya fara bugun deen ɗin kamar Allah ne ya aiko sa, ihu deen yake yana faɗin “mugu azzalumi kawai dan kaga kafi karfi na ko to ai baka fi karfin Allah ba, duk zaluncin da zakamin wlh tarawa nake idan ya chika sai na rama, wani naushi Ahzan ya kai wa deen a baki dan yayi shiru amma ina yaki yin shiru, gaba ɗaya Ahzan ya fasawa deen baki sai jini ke zuba, da gudu yarinyar ta miƙe ta bar palon ta nufi ɗakin hanan tana kuka.

    Sosai Ahzan ya bugi deen amma duk wan nan budu daa deen yasha hakan bai sa bakin sa tayi shiru ba daga karseh hakuri kawai Ahzan yayi ya kyalesa, ya juya ya bi bayan yarinyar, deen kuwa bajewa yayi a kasa awajen ya cigaba da ihun sa yana surutai.

    Kwanche saman gadon hanan ya same ta tana kuka, saman drawer gefen gadon ya zauna a nitse ya fara magana “ya isa haka kukan kinji? Ɗago kai tayi tana ganin sa ta mike zaune tana goge hawayen “yaya Ahzan wai daman a gidan nan yaya deen yake kuma wai daman kanin kane, ni kullun idan Aunty hanan tana bani lbr sa, ina tunanin ko ba’a nan yake ba ban ma taɓa tunanin ɗan mum bane, yanzu gashi saboda ni ka da kesa a banza” tana magana tana shesshekar kuka “look ya isa haka deen kani na ne baban mu ɗaya amma ba mum che ta aife sa ba maman shi daban ina ga tun da kikazo gidan nan baki fita waje bane, amma da kin fita tsakar gida zakiga gate na shiga part nasu, daga gefen hagu, ki daina damuwa ba dan saboda ke na bugi deen ba kisani baa taɓa yin sati ban bugi deen ba na rufesa a station na bashi horo amma duk da haka a banza baya jin magana ga shaye shaye da bin abokan banza, idan na hukun tashi kullun sai mum nashi tayi ta faɗa bata son laifin sa ko kaɗan, dan haka babu ruwanki da shi idan ya shigo ya sameki a palo ki tashi ki koma ɗaki ki bar masa palon kinji ko? Gyaɗa masa kai tayi tare da faɗin “eh naji” “munyi magana da mum tun da har yanzu baki tuna sunan kiba zamu rinƙa kiranki da Ummi kinji” “to yaya Ahzan Nagode” “ki dai na min godiya kinji? ni yayan ki ne kuma kin chan chan chi na miki hakan, yanzu dai ya kamata ki shiga school kafin Allah yasa muga iyayenki ko? Da sauri ta mike zaune ta goge hawayen fuskarta ta fara murmushi “yaya Ahzan yanzu nima zan rinka sa uniform irin na Aunty Hanan? zan rinka zuwa in da take zuwa? Zan rinka rubutu a takarar da kamar yadda take? Kasa bata amsa ma yayi ya zuba mata ido kawai yana kallon yadda take murmushi chike da farinchiki, shi kanshi bai san lokacin da ya fara murmushi ba “yaya Ahzan yaushe zaka kai ni to? “Ranar Monday In Sha Allah” saukowa tayi daga gadon ta dawo gaban sa ta sungunna tace “Nagode yaya Ahzan” mikewa yayi ya nufi waje yana faɗin “ki dai na yimin godiya ni yayan ki ne mai kaunar ki dan Allah” yana gama faɗin hakan ya fice daga ɗakin, da murna Ummi ta mike ta koma kan gado tana ta farin ciki ta kwata ta lumshe ido kamar mai barchi

    KANO

    Kwanche Ammi take a saman gadon Abba ta tada kai da chinyar sa, tana wasa da yatsun hannun sa ɗaya, chikin nitsuwa Abba ke shafa gashin kanta da ɗayan hannun sa “Aisha an gama ginin gonan kun nan fa saura mu ɗauki ma aikata sai a kwaso dabbobi a zuba aduba abubuwa da ya kamata a kara awajen, amma wani suna ya kamata a sanyawa gidan gonan? Gyara kwanchiya Ammi tayi tana kallon face nashi da kyau ta fara magana “ni har ga Allah na barwa su hiyana rabon nawa gadon nariga da nayi kyauta da wadda zanyi sauran kuma a chigaba da kula musu da shi ka zaɓi duk sunan da ya dache ka sanyawa gidan gonar, amma ina neman wata alfarma, idan ba damuwa “wace alfarma che wan nan Aisha? ” Ina son idan anje ɗauko dabbobin nan a ɗauko har da bello dan bello ba mutunne na yarwa ba, ya mana halak chi ya chanchan chi muma mu kyautata masa, ina gidan da ka sayawa Ahmadu lokachin da mukayi mukayi ya dawo nan yaki to kabawa Bello gidan ya zauna da matar sa” “Aisha wan nan shawara ce mai kyau kinga daman yasan kan dabbobi sosai sai mu bashi aiki a gidan gonar yanayi duk wata muna biyan shi Albashi ko? “Eh hakane kaga yaransa zasu samu karatu zasuyi ilimi kuma zai sanya matar sa ma a makarantar tun da itama ba wani girmane da itaba kwata kwata bazata wuchi 18 to 19 years ba, shi kan shi Bellon ma bai wuchi 25 years ba zai iya shiga school ai” hakane kina da gaskiya Aisha Allah dai ya dafa mana zanyi magana da Aryan dan muga sunan da ya dache musawa gidan gonar.

    “Yauwa niko ɗazun banga Aryan awajen breakfast ba naje part nashi baya nan na kira layin sa bata shiga” “Aryan fa baya nan ya tafi Maiduguri dan an kirashi jiya da daddare akoi wadda ya kalli diyana, shine yaje ya duba ko itace” zubur Ammi ta miƙe chike da farinchiki sai murmushin take tace “Allah yasa itace ko Aryan ya samu kwanchiyar hankali bawan Allah wlh kullun sai na tayashi da addu’a, duk lokacin da na tunashi sai nayi hawaye yana matikar Son diyana sosai gashi abun ya haɗe masa rasuwar Aiman batar diyana” Abba da ya lura yanayin Ammi ya fara sauyawa ta fara shiga bakin chiki da ta tuna diyana, sai ya matso kusa da ita chike da so da kauna ya rungumota tare da ɗago habarta yace “ai yadda nake son ki yafi yadda Aryan ke son diyana” hararan wasa ta wurga masa tana faɗin “gaskiya Aryan yana bala’i son diyana sosai” kara rungumota sosai Abba yayi yana kokarin mantar da ita maganar diyana dan yasan yanzu zata fara kuka, kwan chiya yayi da ita a jikin sa, yana shafa bayan ta a hankali, shiru sukayi har barchi ya ɗauketa.

    UK

    karfe 6pm hiyana ta farka a hankali ta waro idon ta, da kyar ta miƙe zaune a hankali chike da tsoro ta kai idonta kan katafaren gadon sa, ganin tayi Bgs baya nan chikin sauri ta fara jujjuya blue eyes nata tana duba ta ina zata gan shi, amma ina ko alamar sa babu a ɗakin mikewa tsaye tayi jiki ba kwari, tana son fita waje amma babu kayan sawa, a hankali ta taka ta fito palon su, ta rasa ya zatayi gashi daman da hijabi ɗaya tazo kuma ta yaga hijabin tana son ta shiga ɗakinta domin ta ɗauki kayan da ta chire ta mai da tun da bata da wani amma tana tsoro gani take kamar akoi wani machijin, tayi nisa chikin tunani sai ji tayi an taɓa ta firgigit ta ɗago ido ganin Amrat che yasa ta sauke ajiyar “Amrat jeki kawomin hijabin ki, in sanya ina su Aunty Zahra kuma? “Aunty Zahra suna palo yanzu muka dawo daga wajen shopping nima zanje na ajiyewa yaya Fahad kayan shine a ɗaki kizo muje palo kema kiga kayan da Aunty Zahra ta zaɓi miki” “to jeki kawomin hijabin ki tukun nan” to Amrat tache tare da wuchewa ta shiga ɗakin su Amrat na wuchewa sai ga Bgs, chikin sauri Hiyana ta sugunna kasa tace “ina wuni yaya prince” ko kallon in da take bai yiba ya wuche betroom nashi jim kaɗan ya fito ya fice waje, da alama wani abun ya ɗauko, tunani hiyana ta shigayi anya yaya prince zai iya sauyawa kuwa shi kwata kwata ma ba zaka taɓa gane in da ya dosaba baka gane daman shi bare hagun sa, mutunne kamar ba mutun ba, amma zanyi magana da Aunty Farida da kuma Ammi kila su karamin wani shawara amma gaskiya ina da babban aiki kuma da alama na dauki alkawarin da ba zan iya chikawa ba, tana duke a wajen har Amrat ta fito mata da hijabin ta.

    “Aunty Hiyana ga hijabin” mikewa hiyana tayi ta ansa hijabin ta sanya iya guiwa hijabin Amrat ya tsaya mata tare suka jera zuwa palon kasa, nan suka samu Zahra da Lamrat sun baza kaya a gaba sai surutu suke, saman sofa mai zaman mutun 1 Hiyana ta zauna tare da ɗagawa Zahra gaisuwa, fiska ɗauke da fara Zahra ta amsa tare da faɗin “Aunty hiyana wayan chan trolley guda ukun nakine ki duba kayan idan akoi wani abun da kike bukata wadda baa sa a chiki ba yaya khalid yace ki faɗamin sai gobe mu koma wajen ki zaba da kan ki idan ma kayan gaba ɗaya basu miki ba sai muje gobe ki zabo da kanki.

    Saukowa kasa karfet din Hiyana tayi batare da tayi magana ba ta fara bubbuɗe trolley tana duba kayan, gaba ɗaya trolley sai da ta buɗe su ta duba chike da jin haushi ta ɗaugo blue eyes nata tana kallon Zahra ta fara magana

    “Aunty Zahra menene wan nan? Ai wan nan ba kaya bane shirme dai kuma naga babu hijabai da irin abayan nan da sauran manyan kaya na Musulunci a chiki sai dai shirmen irin kayan da diyana ke so” chike ta tsokana Zahra tace “Aunty hiyana yaya prince ne yace wa yaya khalid irin kayan da zai saya miki kenan kuma kada ki kuskura ki rinƙa sanya hijabi a chikin hidan nan dan nan ba gidan hijabi bane gidan kashe miji da love ne wai ma Aunty Hiyana ba Aunty farida ta hanaki sanya hijabi ba? Kina son in faɗa mata chewa baki jin maganar ta ko? “Aunty Zahra waye ya tsara miki maganar da zaki faɗamin haka? dan dai na san wan nan ba maganar ki bane sai dai idan wani ne ya tsaramiki “ni Aunty hiyana babu wan da ya tsaramin iya Gaskiya na faɗamiki” “naji iya gaskiya ne to amma Aunty Zahra me yasa kuke son haɗani da mutumin da baya ko san ganin fuskata? “Au yanzu Aunty Hiyana kin manta alkawarin da kikayiwa su yaya khalid ɗazun nan na chewa ki kayi fa kin ɗaura ɗamarar yaki da jiji da kan yaya prince? “Ban manta ba Aunty Zahra ina sane” “to ai saboda mu taya ki yaki da jiji da kan na shine yasa yaya Khalid yace in zaɓa miki irin kayan nan san nan yace ga waya na baki akoi sakon massage a chiki ki karanta” ta kari maganar tana mikowa hiyanar waya kiran i photo 14 promax, murmushi hiyana tayi tasa hannu ta ansa wayar tana faɗin “wow amma gaskiya wayar tayi kyau ki tayani yiwa yaya khalid godiya” “eh to yanzu dai ki duba massage ɗin dake chiki first” “aa Aunty Zahra zan duba amma sai na koma ɗaki yanzu bari na kwashe kayan na kai ɗaki tukun nan, dan bansan ganin waje a watse” shiru Zahra tayi bata sake magana ba miƙewa Hiyana tayi tare da ajiye wayar a hannun kujera ta fara kwashe kayan nata da ta watsa tana mayarwa chikin trolley

    “Aunty Zahra yanzu da baku sayamin hijabi ba dame kuke son na rinƙa yin sallah? “To baki da hijabi ko nayin sallah ne daman? Ina wadda kika sanya da za mu zo” “ai shi na yaga dazun yanzu ko ɗaya babu” “to inaga sai dai ki rike na Amrat dake jikin kin nan dan a garin nan ba’a sayar da hijabi” shiru Hiyana tayi ta chigaba da kwashe kayan dan tasan karya Zahra ke mata akoi kasar da ba’a sai da hijabi ne amma bata son yin jayayya da maganar Zahra dan haka sai tayi shiru ta chigaba da kwashe kayan

    Babban trolley ta fara za zuwa part nasu tana shiga ta tsaya turus a Palo tunani ta shiga yi aina zata ajiye kayan nata dan wlh ko kasheta za’ayi bazata koma ɗakin taba dan ita bata yarda da ɗakin ba gani take akoi wani snake ɗin a chiki, da taga ba abun da tunani zai kara mata idan ba zafin kai ba sai ta nufi bayan sofa mai zaman mutun 3 ta ajiye trolley haka ta kwaso sauran dukkan ta ajiye su a bayan sofa, buɗe trolley tayi ta ɗauki wasu riga da wando masu ɗan hankalin ta lallaɓa ta leka ɗakin yaya prince dan taga ko ya dawo bata sani ba, tana ganin baya chiki tayi sauri ta shige chikin ɗaki ta chire hijabi jikin ta sauri sauri ta sanya kayan data ɗuko tare da mai da masa towel nashi toilet ta fito da sauri har tana haɗawa da gudu

    Sai da ta fito palo san nan ta sanya hijabin Amrat a jikin ta ta fice daga palon nasu ta sauka palon kasa

    Tana zama saman sofa mai zaman mutun 1 su yaya khalid na shigowa shi da yaya Yusuf kusa da Zahra yaya Khalid ya zauna, shi kuma yaya Yusuf kusa da Lamrat ya zauna, chikin nitsuwa da girmama Hiyana ta gai dasu, da fara suka amsa mata tare da tambayar ta ya karfin jiki sunkuyar da kai kasa tayi tace “naji sauki”

    “Amma sister kin kaiwa Bgs abin chi kuwa? Chewar khalid yayi maganar yana kallon ta “eh yaya Khalid tun kafin ku dawo wajen aiki naje na shirya masa abin chin sa a ɗaki amma bai Chiba, daman kuma nasan ba chiɗin zai yiba dan jiya ma da na kai masa bai Chi ba” chike da ɓachin rai Khalid ya miƙe ya nufi waje yana faɗin “ina zuwa, kai tsaye wajen hutawa dake gefen dama a chikin gidan Khalid ya nufa

    Waje ne mai matikar kyau da tsaruwa kewaye yake da furanni masu kyau da tsada sai kamshi suke, daga tsakiyar wajen kuma wasu tsadaddun kujeru masu numbashine a wajen an sanya runfa mai kyau a dai dai saitin kujerun san nan aka kewaye kujerun da glass aka sanya karamin table a tsakiya, ga wasu yan kanan box glass masu kyau suna ɗauke da ruwa da wasu irin kifaye (fish) masu kyau sai yawo suke a chiki an kewaye wajen gaba ɗaya da box glass na kifin sai wasu tsadaddun fitilla masu bada haske mai tambarin Bgs, komai na wajen ɗauke yake da tambarin Bgs, kallo ɗaya zaka wa wajen kasan wajene na musamman kuma mai mallaki wajen mutun ne na musamman.

    Zaune saman kujera yana latse latse a system dake kan chinyar sa Khalid ya iskoshi sanye yake chikin wando 3cuter da yar riga mara nauyi, chike da bachin rai khalid ya shigo wajen amma yanayin arba da face ɗin Bgs nan take yasha jinin jikin sa dan yaga babu alamar wasa a face nashi, jiki a mache ya zauna kusa da shi har yar shakewa voice nashi take ya fara magana

    “Haba Bgs ba kamin alkawarin idan sister ta kawo maka abinchi zaka chi ba? Why yau baka chi ba? Shiru Bgs yayi kamar bai san da zaman mutun a kusa da shi ba, idan da sabo khalid ya saba yasan idan kayiwa Bgs magana wani lokaci ma yana ɗaukan 10mins kafin ya baka amsa idan sauri kake ma to sai dai ka tafi, dan wannan abun ya zamo masa jiki, wani lokaci sai ka chire rai da samun amsar Bgs tukun nan sai kuma kaji ya baka amsa wata zubin har sai ka manta da maganar da kayi masa ma, kafin ya baka amsa, to awan nan karon ma hakane sai da Khalid yayi zaman 15mins san

    Batare da ya dogo idon sa daga kan system ɗin ba ya fara magana “ni fa Khalid ban maka alkawarin hakan ba kawai nache maka zanyi tunani ne, so naga ma no need nayi wani tunani dan nasan ba zan iya chin abun da yarinyar nan ta taɓa da hannun taɓa kyama take bani ban so, ɗazun ma dana che zanyi tunanin kawai dan naga kaji bachin rai sosai ne shiyasa na maka hakan dan ka sauko amma yanzu ka tashi ka bani waje dan nima raina a bache yake yanzu!! Ba musu khalid ya miƙe ya bar wajen dan ya lura tabbas Bgs na chikin bachin rai idan ya tsaya yache zai masa wani magana to zai iya sumar da shi awajen

    Chikin gida ya koma kai tsaye ya wuche part nashi mikewa Zahra tayi ta bi bayan sa dan taga fiskar sa kamar babu annuri.

    11pm Amrat che kadai zaune a palon kasa tana shan complex su Zahra sun tafi part nasu, a tare Fahad da Bgs suka shigo palon kai tsaye part nashi Bgs ya nufa, Fahad kuwa tsayuwa yayi yana kallon Amrat dake ta faman shan complex nata “ke me kike yi a nan har yanzu baki kwnata ba? “Naga baka dawo ba ne yaya Fahad kuma sai na fara jin yinwa shine na fito na haɗa complex, karisowa in da take yayi yasa hannu ya ansa cup din, debo complex ɗin yayi a spoon ya kai bakin sa ya sha zama yayi kusa da ita, ya fara shan complex ɗin sosai yana sha yana bata a baki gwanin sha’awa, a tare suka shanye complex ɗin bayan sun gamane ya ajiye cup ɗin a gefe, ya dawo da kallon sa kanta matso da fukarsa yayi kusa da tata har suna iya jiyo numfashi juna harchen sa ya kai kan ɗan karamin bakin ta la lashe ragowar madarar complex dake wajen, wani dogon numfashi Amrat taja tare da runtse ido kasa kasa yace “numfashi me kike ja kuma? Ko kinyi tunanin bakin naki zan sha ne? Girgiza masa kai tayi tana faɗin “aa” “to ai garama kiyi tunanin hakan dan yanzu kuwa zan fara shan kayana” buɗe baki Amrat tayi zatayi magana yayi saurin haɗe bakin su waje guda, sosai yake kissing nata chikin dabara ba tare da ya zame kabin sa daga nataba ya duke ta ya ɗorata kan chinyar sa tare da mikewa da ita ya nufi ɗakin su, yana shiga palon part nasu yachi karo da hiyana kwanche saman doguwar kujera tana barchi, ɗaure fuska sosai yayi a hankali ya zame bakin sa daga na Amrat tare da sauke ta kasa chike da bachin rai yace “Amrat jeki ɗaki ina zuwa, batare da ta lura da hiyana ba ta wuche ɗaki

    Karisowa yayi wajen Hiyana yasa hannu ya ɗan bubbuga jikin kujerar yana kiran sunan ta, da kyar ta iya waro blue eyes nata waje sunyi jaa almar barchi bai ishe taba, “sister me ya kwantar dake a nan? Me yasa baki shiga ɗakin ki ba? Mikewa zaune Hiyana tayi chikin muryan barchi ta fara magana “yaya Fahad wlh ɗazun machiji na gani a ɗakina to na roki yaya prince ya chiremin shi amma har yanzu wlh tsoron ɗakin nake ji bazan iya shiga chiki ba” “machiji kuma!? a chikin gidan nan kai anya kin gani da kyau kuwa sister to wai ta yama za’ayi machiji ya shigo gidan nan har ɗaki” “wlh yaya Fahad na gani da kyau machijin gaskiyane, ka tambayi yaya prince kaji shi ya chire da kansa” “Gaskiya abun da abun mamaki a che snake a gidan nan amma dai ina zuwa” yana kai karshen maganar ya miƙe ya shiga ɗakin Bgs.

    Gaban mirrow ya samu Bgs yana shafa mai da alama wanka yayi gefen gado Fahad ya zauna chike da jin haushin abun da Bgs yakeyi wa mutane ya fara magana “yaya prince dan Allah ka bar sister tazo ta kwana a ɗakin nan ko da saman kujera ne, dan tana tsoron ɗakin ta, kaji pls? Shiru yayi kamar bai san da shigowar Fahad dakin ba sai da ya gama shafa mai ɗin sa, ya feshe jikinsa da perfume masu bala’i kamshi da tsada, slowly ya juyo ya sauke idon sa a kan Fahad dake zaune ya zuba masa ido alamar yana jiran amsa “get out Fahad!! Ya furta cikin tsawa, mikewa Fahad yayi ba musu ya fice

    yana fita bai bi ta kan hiyana ba dan bashi da wata amsa da zai bata wuchewa ɗakin sa kawai yayi.

    Bgs kuwa dressing room nashi ya shiga jim kaɗan ya fito sanye da kayan barchi masu kyau da tsada farare tas masu laushi, saman gadon sa ya haye ya kwnata tare da jan kyakkyawa kuma lallausan blanket nashi zuwa kan chikinsa ya lumshe ido ba jimawa barchi yayi awon gaba dashi.

    Ranan dai a palo hiyana ta kwana, ta takure waje guda kallo daya zaka mata ka gane ba karamin tsoron palon ta keji ba, shiyasa ta takure waje guda, fiskar ta duk hawaye a bushe…

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 3

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 3

    Book 2

    *Episode 3*

    Da sallama ɗauke a bakin ta Aunty farida ta shigo chikin palon Bgs rike da hannun Hiyana daketa faman sharara kuka dan ita gani take shike nan kwanan ta ya kare, kai tsaye betroom nashi suka nufa ita kanta Aunty farida fargaban shigar betroom ɗin take

    Zaune yake a bakin katafaren gadon sa sanye da jallabiya baka ya dafe kansa da hannu biyu yana kallon kasa da alama wani tunani yake, jin Sallamar Aunty farida che ya sa ya ɗan ɗago kai kaɗan, batare da ya kalli in da suke ba kasa kasa ya Amsa sallamar, ƙarisowa chikin ɗakin sukayi jin shesshekar kuka yasa ya ɗago idon sa kallo ɗaya ya musu ya kauda kansa gefe yana kara yamutse fuska gefen gadon Aunty farida ta zauna tare da zaunar da Hiyana a gefenta, Chike da So da kaunar ɗan uwan nata tafara magana

    “Prince ina ne ɗakin Hiyana? Shiru yayi kamar bai ji me Aunty farida tace ba “Prince Magana nake maka fa nache inane ɗakin Hiyana!? Ta karisa maganar tana ɗan kwaɓe fuska alamar bataji daɗin shiru da ya mata ba, shiru dai Bgs bai yi magana ba kamar ma bai san da shigowar mutane ɗakin ba, shiru Aunty farida tayi bata sake yi masa Magana ba dan a tsorache take da shi Almost 10mnt suna zaune shiru chikin muryan rarrashi Aunty farida ta fara magana

    “Haba prince dan Allah ka bani amsa mana nasamu naje na kaita ta kwanta ta ɗan huta” shiru shiru kamar bai san da zaman su a ɗakin ba ganin hakan yasa Aunty farida ta miƙe ta kama hannun Hiyana ta nufi waje da ita ɗakin dake kusa da nashi Aunty farida ta shiga rike da hannun Hiyana, komai na chikin ɗaki iri ɗayane da nashi sai dai ban ban chin colour domin komai na ɗakin sa farine tas na hiyana kuma sky blue, a bakin katafaren gadon dake chikin ɗakin Aunty farida ta zaunar da Hiyana ta juya batare da tayi magana ba ta nufi waje gaba ɗaya ji tayi jikin ta yayi sanyi wani mugun tausayin hiyana ne ya sake dira a ranta, tunani take tana tafiya lallai Prince ya tabbata baya son hiyana ko kaɗan Allah sarki bai war Allah, ɗakin Bgs ta koma

    Da Sallama tashigo ɗakin kamar yadda ta barshi haka ta dawo ta same sa gefen sa ta dawo ta zauna chike da fargaban abun da zai biyo baya ta fara magana

    “Kayi hakuri Prince na san ba’a kyau ta maka ba amma idan ka daure kayiwa iyayen mu biyayya zamuyi nasara arayuwa kaji? shiru Bgs yayi bai yi magana ba da alama bai da niyar magana kwata kwata, chigaba da magana Aunty farida tayi “pls ɗan uwana kaji tausayin yarinyar nan marainiya che ba uwa ba uba kuma kana sane da irin wahala da ta sha arayuwar ta to dan Allah ko da ba zakuyi zama a matsayin mata da miji ba ina neman alfarma da ka ɗauke ta kamar yadda ka ɗauke ni dan Allah idan kamin hakan ka gama min komai pls” wani iska mai zafi ya furzar daga bakin sa kafin ya fara magana

    “Pls Aunty babba zaki iya tafiya!!” chikin sauri Aunty farida ta ɗago tana kallon sa shima ita yake kallo ba karamin razana tayi da kallon yadda green eyes nashi suka sauya izuwa jaa sosai ga jijiyoyin kan san nan duk sun tashi duk da A.c dake ɗakin hakan bai hana shi zufa ba chikin murya irin na rarrashi Aunty farida tace “dan Allah prince ka saurare ni nasan baa kyau ta maka ba amma kasani ba laifin Hiyana ba che wlh bata san komai ba yarinya bai war Allah ita kanta yanzu kukan dana sanin zuwan ta duniya gaba ɗaya ma take, ta sha wahala a rayuwar ta pls my blood ka karɓi Hiyana a matsayin kanwa ba mata ba kaji? ta karisa maganar kamar zata yi kuka kawar da kansa gefe yayi chikin nitsuwa ya fara magana

    “Naji zan yi tunani a kan hakan zaki iya tafiya”wani nauyayyar ajiyar zuchiya Aunty farida ta sauke dan tasan halin Bgs idan yace zai yi abu to zai yi ne addu’a take Allah ya ɗora su a kan shi, da wan nan tunanin ta miƙe ta fice daga ɗakin, wani dogon tsaki yaja tare da miƙewa ya kwanta yana kwaɓe fuska

    A ɓangaren Khalid kuwa

    Aunty salma rike da hannun Zahra wadda ke ta kuka suka shiga palon sa, kwanche suka same sa saman sofa mai zaman mutun 3, yana ganin su ya miƙe zaune yana faɗin “sannu ku da zuwa” murmushi Aunty Salma tayi tana mai farin chikin yau ɗan uwan ta yayi Aure kuma abun farin chikin ma Autan su ya Aure

    Gefen sa Aunty salma ta zaunar da Zahra san nan ta koma gefe ɗaya ta tsaya chike da farinchiki ta fara magana “to ga amanar kan wata na baka ka kulamin da ita sosai fa” da murmushi a kan face nashi yace “gaskiya na karɓi wan nan Amanar hannu dubu dubu In Sha Allah zan kula da sis love na sosai kamar kwai a kan bajejjen faranti” dariya Aunty Salma tayi kafin tace “oh Allah ko kunya ta bakaji ba ko? Sunkuyar da kansa kasa yayi chikin raha yace “to Aunty babba gashi nan naji kunyar taki” tsaki Aunty salma taja chikin wasa tare da nufar kofar fita tana faɗin “ai, Ni ban soma Abba ya baku matan naku yanzu ba so nai ya bari sai nan da wata 2 masu zuwa” tana kai karshen maganar ta fice daga ɗakin

    Dawo da kallon sa Khalid yayi kan Zahra dake ta faman sharɓan kuka, hannu yasa ya goge mata hawaye chike da so da kauna yace “my wife kukan me kuma ki keyi ne? Shiru Zahra tayi bata tan ka shi ba kuma bata dai na kukan ba, murmushi Khalid yayi tare da miƙewa ya naɗe hannun rigan sa ya duƙa ya ɗauke ta chak kamar yar baby ya nufi betroom nashi da ita

    A tsakiyar katafaren gadon sa ya zaunar da ita tare da zama daga ɗan gefen ta ya kwan to da kan sa kan chinyar ta kasa kasa ya fara magana

    “My wife wai kukan menen hakan? Baki san zama da nine? Sunkuyar da kai kasa Zahra tayi ta chigaba da kukan ta, “oh my god Khalid ya furta tare da miƙewa zaune yasa hannu ya ɗago haɓarta, chike da so da kauna yasa harche ya lashe hawayen nata tas tare da haɗe fuskokin su yana kallon chikin idon ta “now zaki yimin magana ne ko kuma dai sai na chiji ɗan bakin nan naki? Chike da shogoɓa tace “Ni Allah yaya Khalid bana so ka mai dani part ɗin Ammi na” murmushi yayi kafin yace “au shine dalilin kukan naki? Gyaɗa masa kai tayi alamar eh “ok to bari zuwa gobe zan mai dake kinji amma yanzu tashi muje na miki wanka na shiryaki muje na baki abinchi a baki” turo ɗan bakin nan nata tayi chike da shagoɓa tace “ni na iya wanka da kai na ai”
    “Aa ni gaskiya ban yarda ba kizo kawai muje na miki idan ke kikayi bazaki fita sosai ba, bata san lokachin da dariya ya kubche mata ba zuba mata ido yayi yana kallon yadda take dariya sai da tayi mai isar ta san nan ta raba fuskantar da nashi tana faɗin “to ai ni nake wankana tun dama chan kuma ina fita sosai ai a haka ma ka ganni kache kana so” ta karisa maganar tare da rufe fuskar ta da hannun biyu “eyeee a lallai my wife ta girma babu zan chen ɗaga kafa kenan” “ɗaga kafan me kuma dama ai ni ban che kaɗaga kafaba” “au haka kika che? “Eh mana yaya Khalid ni ban che ka ɗaga kafa ba to ma idan ka ɗaga kafar ka kai ta ina

    Fisgota yayi da karfi ta faɗa kan kirjin sa, rungumeta yayi sosai yana faɗin “ai ko ba zan ɗaga kafar ba” ɗago da fuskan ta tayi daga kan kirjin nasa chike da shogoɓa tace “yaya Khalid ka kusa karyamin hannu fa Allah” “sorry my wife to muje na kai ki toilet kiyi wanka ko?tun da bakya so na miki, Ba tare da ya jira Amsar taba ya miƙe ya ɗauke ta chak ya nufi toilet da ita.

    A ɓangaren Yusuf kuwa Aunty Mardiya na fita ya matso kusa da Amaryan sa kasa kasa yace “my baby ya jiki? Kan ta a sunkuye tace “da sauki amma har yanzu kai na na min chiwo sosai” eyya sorry kinji In Sha Allah zai dai na yimiki chiwo yanzu dai ki kwanta ki huta bari naje wajen Abba a fada ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi waje ita kuma lamrat karisa hayewa saman gadon tayi ta kwanta ba jimawa barchi yayi awan gaba da ita

    A ɓangaren Fahad kuwa

    Koda Aunty mardiya ta shigo tare da Amrat shiru palon babu kowa kai tsaye betroom nashi suka shiga tare da sallama babu kowa a ɗakin sai dai karan ruwan dake tashi daga toilet da alama wanka yake
    Karisawa su kayi chikin ɗakin a bakin gado Aunty mardiya ta zaunar da Amrat tace ” amrat ki zauna kijira mijin ki yana wanka ne zan koma ɗakin Ummi kinji? Batare da tajira amsar amrat ba ta juya ta fice daga ɗakin.

    Almost 20mnt Amrat na zaune shiru tana sunkuye da kanta kasa tana wasa da yatsun hannun ta, jin An buɗe kofar Toilet ɗin ne yasa ta ɗago kai tana kallon kofar tana jiran taga mai fitowa dan ita kwata kwata batama san wanene mijin nata ba

    Ɗaure da farin towel mai laushi da kyau a kugun’sa ya fito bai ma lura da mutun a ɗakin ba kai tsaye gaban mirrow ya nufa, ganin sa haka yasa Amrat fasa ihu dan ba karamin tsorata da ganin halittar jikin sa tayi ba, A’sukwane ya juyo yana bin in da akayi ihu da kallo, da mamaki yake kallon razanan ne fuskar ta a nitse yace “ke wacece ke? Sai lokachin Amrat ta dawo chikin hayyachin ta da sauri ta miƙe tsaye ta kwasa da gudu ta nufi hanyar fita daga ɗakin taku biyu Fahad yayi ta damko kugunta ta baya tare da ɗaga ta sama ya dawo da ita chikin ɗakin wurgi yayi da ita a saman gadon chikin tsawa yace ” wacece ke!? Me ya kawo ki ɗakin nan!?

    Amrat ta gama tsorata murya ta har rawa yake ta fara magana “Aunty mardiya che ta kawo ni” ” wacece ke!? “Sunana Amrat” shiru yayi yana tunanin chikin ran shi yana mai mai ta sunan Amrat tabbas na taɓajin sunan Amma na manta ko ai nane “to naji sunan ki Amrat me kika zo yi a ɗakin nan!? “Aunty Mardiya che ta kawo ni kuma tace na zauna na jira miji na ya fito sai yanzu Fahad ya tuno in da ya taɓa jin sunan lokachin da limamin babban masallacin juma’a yake faɗin an ɗaura Auren Fahad Abubakar Saraki da Amrat Ahmad guntun tsaki yaja tare da juyawa ya nufi gaban mirrow ya fara shafa mayu kan sa masu kamshi da tsada, Amrat kuwa shiru ta kwanta a saman gadon nasa ta runtse idon ta tana jiran taji me zai sake che mata

    “Ke tashi ki shiga dressing room na ki ɗauko min kayan da zan sa dan ni yar Aiki aka kawomin da sauri Amrat ta miƙe chikin sanyin murya tace “yaya ina ne wajen kayan naka kuma yaya sunan ka, da mamaki ya ɗago yana kallon ta ta cikin mirrow wai yarinyar nan ko sunana ma bata sani ba amma Abba ya san yadda ya shiga ya fita ya haɗa mu Aure nan take kuma yaji wani irin tausayin yarinyar ya kama shi chikin sanyin murya yace “sunana Fahad ki buɗe wan chan kofar ki shiga zakiga kayan na awajen ki kawomin set ɗaya, chikin sauri Amrat ta nufi dressing room ɗin

    Jim kaɗan ta fito hannun ta ɗauke da kayan nashi gaban sa ta dawo ta sungunna chikin nitsuwa tace “yaya Fahad ga kayan nan shiru yayi kamar bai jita ba, shiru ita matayi ta sunkuyar da kanta kasa tana jiran ya amsa kayan, sai da ya gama gyara gashin kansa san nan ya goma gefen gado ya zauna tare da miƙa mata hannu alamar ta kawo masa kayan, miƙewa tayi tana tafiya a hankali kamar bata son taka kasa, sugunnawa tayi a gaban sa tare da miƙa masa kayan, bin kayan yayi da kallo ba tare da ya ansa ba

    “Waye ya koya miki zaɓen abu mai kyau? “Babu kowa ni da kai na na iya, shiru yayi bai sake magana ba yasa hannu ya Ansa kayan, shiru tayi ba tare da ta miƙe ba tana ɗan satar kallon sa “tashi ki zauna a saman gadon mana, ya faɗi hakan tare da miƙewa ya shiga dressing room ɗin bin bayan sa da kallo Amrat tayi har ya shige room ɗin san nan ta miƙe ta koma gefen gadon ta zauna.

    Maiduguri

    “Ahzan ai na ka buge wan nan kyakkyawar yarinya haka? Kuma ina iyayenta da yan uwan ta suke? “dady wan nan yarinyar fa mahauniya che bata da hankali” ” aa Ahzan wan nan yarinyar ba mahaukachiya bace ka dubi jikin ta mana ka kalleta da kyau zaka gane hakan” “to dady Ni dai a yadda na ganta sai naga kamar mahaukachiya che “To mu bari ta farfaɗo tukun nan sai muji daga bakin ta ko? Yanzu dai bari naje na sanar da mom ɗin ka sai mu dawo gaba ɗaya dan ta chigaba da kula da yarinyar” to kawai Ahzan yace miƙewa dady yayi ya fice daga ɗakin, dawo da kallon sa Ahzan yayi kan yarinyar dake kwanche bata ko motsi sosai ya zuba mata ido chikin ran shi yana yaba irin kyawun yarin yar…..

    To masu karatu sai mun haɗu gobe idan Allah ya kaimu

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    P*💫STAR LADY💫*4

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai

  • Duk Karfin Izzata Book 2 Page 6

    Duk Karfin Izzata Book 2 Page 6

    Book 2

    *Episode 6*

    Saɗab saɗab Zahra take lallabawa kamar ɓarauniya ta shiga part ɗin Bgs sai waige waige take tana tafiya tana juyowa ta kalli bayan ta karaf sai ji tayi tayi karo da mutun chikin tsoro da tashin hankali ta ɗago kai ganin Aunty amarya ne tsaye a gaban ya sa ta sauke nauyayyar Ajiyar zuchiya tare da faɗin “ina wuni Aunty amarya “lfy lau Auta me ki ka zo yi a nan kuma kika bar ɗakin mijin ki? “Wajen Aunty hiyana nazo” jin Zahra ta ambaci sunan hiyana yasa Aunty amarya ta ɗaure fuska cheke da ɓachin rai tasa hannu tawa Zahra nuni da ɗakin Bgs dan mugunta tache hiyana na chikin nan” “to” kawai Zahra tace san nan ta wuche ta haye saman stair case ɗin ta nufi ɗakin yaya prince ɗin

    Aunty Amarya kuma sai murmushin mugunta take ta nufi hanyar fita daga palon

    A hankali Zahra ta tura kofar kamar wadda bata da gaskiya ta shiga yana tsaye gaban mirrow jikin sa sanye da kayan sojoji yana gyara lallausan kuma bakin gashin kan sa, jin anshigo masa ɗaki ne yasa ya ɗago green eyes nashi ta chikin mirrow yana kallon Zahra dake ta yan waige waige alamar bata ganshiba zuba mata ido yayi sosai
    ya kalleta san nan ya kalli kanshi ba shakka Auta tana kama dani sosai, why nake kaunar Auta sosai har hakane? Yayi wa kansa yambayar da ba shi da amsar ta “zo nan ke!!”ya faɗa tare da juyowa yana kallon ta da kyau, chikin tsoro da tashin hankali Zahra ta karisa gaban sa ta sugun na kasa murya na rawa tace “ina wuni yaya prince” “me ya shigo dake part nan!!? banche karna kara ganin ku a nan ba!!? “Kayi hakuri wajen Aunty hiyana nazo, jin an ambaci sunan hiyana yasa ya ɗaure fuska sosai chikin tsawa yace “tashi ki fita ko nayi ball dake!!! Da gudu Zahra ta miƙe ta fito a bakin kofar ɗakin nasa ta waje ta tsaya tana tunanin ina ne ɗakin Hiyana dan ni dai gaskiya ba zan tafi ba har sai na ga hiyana ta

    Tayi nisa chikin tunanin da take ne sai taji shesshekar kuka a ɗakin dake kusa da na Bgs kuma muryan Hiyana che ke wan nan kukan, chikin sauri ta tura kofar ɗakin ta shiga turus ta tsaya ganin hiyana a duke tali nill down ta daga hannu sama tana kuka ga zulaihat tsaye a kanta rike da bulala chike da bachin rai da fushi chikin tsawa Zahra tace “ke zulaihat me hakan!! Chike da izza zulaihat tace “ina ruwanki ko kimin shiru ki fita a ɗakin nan ko kuma in haɗa dake, karisowa chikin ɗakin Zahra tayi dai dai gaban hiyana taje tasa hannu ta ɗago ta tare da mai da ta kan gadon chikin fushi ta juyo ta zabgawa zulaihat wani wawan mari ta kwasa a guje tayi waje, a guje zulaihat ta bi bayan ta a dai dai tsakiyar palon kasa ta damko gashin Zahra ta baya da karfi ta ja ta baya wani ihu azaba Zahra ta saki hankaɗata kasa zulaihat tayi ta faɗi ta buge goshin ta a kasa wani razanannen kara ta saki gadan gadan zulaihat ta nufeta a zafafa ta ɗaga hannu zata kaiwa mata naushi a chiki, chak daji a damki hannun nata da karfi kafin ta ɗago taga wanene ya kwashe kafafunta ta faɗi kasa wani wawan mari ya wanke mata fuskar ta dashi wadda yasa gaba ɗaya ta daina gani, baiyi wata wata ba ya sa kasa yayi ball da ita ta tafi luuuu saboda tsantsin wajen ta bugu da jikin stair case wani ihun azaba ta saki lokachin guda kuma ta ɗauke diff kamar an ɗauke wutan nepa

    Dawo da kallon sa kan Zahra yayi tare da miƙa mata hannu alamar ta kama hannun sa ta miƙe chike da tsoro da mamaki Zahra ta kama hannun sa jawota yayi ta faɗa kan faffadar kirjinsa da ɗan tsawa yace “ba nache ki bar part din nan ba me ya hana ki tafiya kuma wacece wanchan? Chikin shesshekar kuka Zahra tace “kayi hakuri yaya prince wlh ina son ganin Aunty hiyana che shiyasa amma yanzu zan tafi” ” wacece wan chan? “Yar uwan Aunty amarya che” “me ya kawota part nan har zata bugeki? Yayi Maganar tare da raba ta da jikin sa nan dai Zahra ta bashi labari yadda ta shigo ta samu abun da zulaihat kewa Hiyana, tsaki yaja tare da juyawa ya koma betroom na shi

    Haurawa sama Zahra ma tayi ta koma ɗakin Hiyana suka bar zulaihat sume awajen

    In da ta bar hiyana a wajen ta dawo ta same ta sai kuka take gefenta ta zauna chike da bachin rai tafara magana “yanzu Aunty Hiyana yar zulaihat ɗin nan zaki bari ta bugeki dame ta fiki eh? To wlh tun wuri idan zaki tashi ki dai na zama shiru shiru ki kwatar wa kan ki yanchi gwara ki tashi, wlh ki ajiye ustazan chinkin nan yanzu lokachin fafata yaki ne to bari kiji in faɗa miki ma zulaihat tazo gidan nan ne domin ta samu soyayyar yaya prince shiyasa na tsaneta ranan na shiga part ɗin Aunty amarya na jisu suna shawan yadda zasu bullowa yaya prince ita da Aunty amarya to kinga yanzu tashi zakiyi ki ɗaura ɗamarar yaki ki kwachi mijinki” chikin shesshekar kuka hiyana ta fara magana “Aunty Zahra ai Aunty amarya che tazo tache komai zulaihat ta sani in rin ka yi idan ban yiba sai ta kusan kashe ni shiyasa kuma Ni fa yaya prince ba sona yake ba ya tsane ni bai son gani na dan haka ba ruwana da shi nima, kuma ba wani yaki da zanyi a kansa” Zahra zatayi magana sukaji an buga kofar ɗakin

    Da sauri Zahra ta miƙe ta nufi kofar tana faɗin “Allah yasa ba yaya prince bane dan yace na bar part din nan juyowa hiyana tayi ta zubawa kofar ɗakin blue eyes nata, chike da tsoro Zahra ta buɗe kofar ɗakin ganin yaya Khalid ne yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuchiya “my wife zo ki wuche kije ki ɗauki duk abun da kike bukata nan da 10mins jet ɗin yaya prince zai tashi zamu koma London ɗan leko da kansa ɗakin yayi chike da kulawa yache “hiyana tashi kema ki shirya yanzun nan muna palon Abba muna jiran ku yana gama faɗin hakan ya juya ya nufi hanyar fita

    Juyowa Zahra tayi ta kallin Hiyana chike da farinchiki tace “to Aunty Hiyana yaki da su zulaihat ya kare kiyi sauri ki shirya “Aunty Zahra taya zan tafi ba tare dasu diyana ba? ina diyana na take? wani hali take chiki yanzu? shin tana raye ne? ko ta mutu? “Aunty Hiyana kiyi hakuri kisani Abba ba zai taɓa barin rayuwar diyana ya salwanta a ban za ba zasu nemota In Sha Allah yanzu dai ki tashi ki ɗauki abun da kike so kiyi sauri dan kinsan halin yaya prince baya son jira “to Aunty Zahra, da sauri Zahra ta bar wajen ta sauko kasa ta fice daga palon ta nufi part ɗin mijin ta sauri sauri Hiyana ta mike itama tafara shiri

    Gaba ɗaya family sun haɗu a palo Abba ana jiran Hiyana da Lamrat da yaya Yusuf

    Rike da hannu lamrat yaya Yusuf ya shigo gwanin ban sha’awa saman sofa mai zaman mutun 2 ya zauna tare da zaunar da Lamrat kusa dashi, sukayi shiru suna jiran Hiyana, sai kwaɓe fuska Bgs yake ba dan Ammi dake wajen ba da ba zai zauna ba

    a hankali take takowa zuwa chikin palon tana sanye da hijabin ta har kasa fari tas ta sanya nikaf baki kusa da Ammi taje ta zauna gyaran murya Abba yayi ya fara magana “to ku bani hankalin ku gaba ɗayan ku, nitsuwa sukayi gaba ɗayan su suka zubawa Abba ido suna kallon sa banda Bgs daya sunkuyar da kai kasa chigaba da magana Abba yayi
    “Safras ya bukachi da ku koma bakin Aikin ku yau to naji kuma na barɓi hakan amma ban da Aryan domin ya sanar dani ya bawa Aryan hutu zuwa lokacin da zamu gane diyana, tare da matan ku zaku koma kuma zaku tafi tare da Fahad saboda amrat dan idan kuka tafi da yan uwan ta bazata ji dadin zama ita kaɗai a nan ba, ba zan gaji da yimasu nashiha akan ku kula da hakkin marayun dake kanku ba kusani yanzu kune uwan su kune uban su basu san kowa a chan ba sai ku, ina haɗa ku da Allah karku bari yaran nan suyi kukan marai chi”

    miƙewa Aryan yayi chikin dashewar murya yace “Abba ina ganin No need na zauna a wajen nan saura 30mins jirgi na ya tashi zuwa Maiduguri ya karisa maganar kamar zaiyi kuka, jiki ba kwari ya fice daga Palon, wani irin mugun tausayin Aryan ne ya dira a zuchiyoyin gaba ɗaya jama’ar dake Palon, shiru Abba yayi yama kasa chigaba da magana

    Miƙewa tsaye Bgs yayi yace “Abba na wuche “aa Safras ka same a ɗaki zanyi magana da kai kafin ku wuche yana kai karshen maganar ya miƙe ya nufi betroom na shi bin bayan sa Bgs yayi

    kutashi muje ko chewar Yusuf miƙewa sukayi a tare Yusuf ya riko hannun Lamrat Khalid ya riko hannun Zahra Ahmad da Fahad sukayi gaba Amrat ta rike hannun hiyana sukayi waje Umar da Haidar suka rufa musu baya, palon ya rage Ammi Ummi da kuma Aunty amarya

    “wai ina zulaihat ne bata fito ba? chewar Ummi guntun tsaki Aunty amarya taja kafin tace “tana ɗakin ta mana kin san ita bata son hayani yane” shiru sukayi ba wanda ya sake magana

    A harabar gidan jikin motochin da sojojin bgs suka jera musu domin tafiya Airport suka tsai tsaya suna jiran Bgs

    Fitowa Bgs yayi Abba na biye da shi a baya yana musu fatan alkhairin, taku irin na jaruman maza bgs yake kallo ɗaya zaka yiwa face nashi ka fahimci yana chikin bachin rai sosai, sai wani huchi yake yana furzar da iska mai matukar zafi daga bakin sa, da gudu jibga jibgan sojojin sa sukayo wajen su bubbuɗe musu kofar motochin, bgs bai bi ta kan kowa ba ya shiga mota ya zauna Khalid Yusuf mota ɗaya suka shiga tare da matan su Motar da bgs ya shiga shi Fahad yaje ya shiga hiyana na rike da hannun Amrat sunyi shiru sun rasa wani mota zasu shiga

    “Sister zo mushiga motan nan kinji? Chewar yaya Ahmad yayi maganar yana nunawa hiyana motar da zasu shiga ba musu hiyana ta bi bayan sa rike da hannun Amrat suka shiga mota ɗaya da yaya Ahmad, kwata kwata Abba bai ji dadin hakan ba amma baya son yayi magana dan yanzu ma da kyar ya shawo kan Bgs akan ya yarda hiyana ta rinƙa shirya masa abin chi idan sun koma London kuma da kyar ya lallaɓa shi akan karya rinƙa daka mata tsawa dan bawani koshin lafiya ne da itaba da zarar abu ya tsoratata sai suma shiyasa Abba ya lallaɓa bgs akan karya rinƙa mata tsawa.

    Da gudun gaske motochin suka bar gidan kai tsaye Airport suka nufa, juyawa Abba yayi ya koma chikin gida chike da tunanin ya zaman Bgs da hiyana zai ka san che a London Amma yayi wa kansa alkawarin yimusu zuwan bazata nan da 2 week’s dan yaga meke tafiya

    Karfe 2 dai dai katafaren haɗaɗɗen jet na Bgs wadda ke ɗauke da tambarin sunan sa kamar haka PRINCE SAFRAS ya ɗaga zuwa London United Kingdom

    To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu akoi chakwakiya fa shine yaya zaman hiyana da bgs a London? ina diyanan yaya Aryan take? Su Aunty amarya zasuyi nasara kuwa? Shin mutuwa zulaihat tayi ko suma? Inna habiba ta mutune ko suma tayi? Shin Aryan yana ganin diyana ku koma taɓata kenan? Yaya Aunty amarya zatayi idan ta samu lbr abun da bgs yayiwa zulaihat? To domin samun amshoshin ku ku chigaba da bibiyar princess teema Star lady 💃💃

    NEW TEAM💖
    💖THE TALENT TROUPE WRITER’💖

    *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*
    👇👇👇👇

    *1,DUK ƘARFIN IZZATA*
    by(Star Lady)

    *2,GIDAN AUNTY*
    by(mss lee)

    *3,SARKI SAMEER*
    by(xeemat….love)

    *4, JINI DAYA*
    by(mrs bbk)

    💖The Talent Troupe Writer’s 💖

    *DUK ƘARFIN IZZATA*

    💖Story And Written💖
    ⬇️
    *Star lady*

    Duk mai buƙatar littafin Duk Karfin Izzata daga farko har ƙarshe to yamin magana ta wan nan num ɗin 09162620621 ban da kira iya whatSapp kawai