Amatulmaleek Hausa NovelHausa Novels

Amatulmaleek 1

Sponsored Links

[11/8, 3:00 PM] +234 816 839 8310: Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

1
BismillahirRahmannir Raheem

Shiru tayi tana sauraron yanda muryar kawunta ke tashi sbd yanda yake daga sautinsa cikin fushi da bacin rai,
Fushi da bacin rai ne sosai tareda gajiyawa bayyane a fuskarsa datake a hade Babu sauki ko rahama ko kadan,

Duk wannan fushi da bacin ran tareda daga sautin mahaifiyarta Dake zaune tana sauraronsa yakewa,

Daga ita maaman har ita ‘yar tata datai girman da ciwo takeji sosai aranta a duk lokacinda aka zaunar da mahaifiyarta ana mata irin wannan fadan takeji Babu Wanda ya dago acikinsu ya kallesa bare tankawa fadan dayaketa tada jijiyar wuyansa Yana yi,

Shi kansa kawu bellon akoda yaushe ransa tsananta Kuna da Baci yakeyi a duk lokacinda zaizo ya ringa zazzaga kwandon masifarsa a gabansu Amma Babu Me tankawa acikinsu Seya gama maama din ta bisa da yayi hakuri kawai,ita JANNAT ko kanta Bata dagowa bare tai magana.

Wannan Karan fadan nasa da maganganun nasa sunyi tsauri akansu Dan haka idanuwanta Dana maama din duk sun ciko da kwallan da Babu dayansu dakeson yaga hawayen Dan uwansa.

Zufan goshinsa ya share da babbar rigar jikinsa cikin maimaitawa maaman kalman karshe yace

“Tabbas idan Abdulhameed ya sake zuwa makarantar bokon Nan aka kawo min qararsa wlh tallahi almajiranci zan Kaisa bazan iya da baqin ciki ba ‘dan uwana ya mutu be barmun komaiba Se lalurarku,
Idan bazaki tsaya inda Allah ya ajiyeki ba keda yayanki to ki tattara ko qara gaba bazamu iya ba”.

Juyawa yayi yabar gurin batareda ya Dena masifa da fadan da yake yi din ba harya bar kofar qaramin sashen nasu da Tin bayar rasuwar mahaifinsu suke su kadai cikinsa.

Numfashi maamah din ta sauke batareda Kalli gefen da AmatulMaleek din take zaune ba itama tana cigaba da dinkewa Abdulhameed wandonsa Daya barke da allura duk Bata Wani iyaba sbd shekarunta Basu Kai ta iya din sosaiba.

Dukkaninsu Babu Wanda yace komai sbd AmatulMaleek din tsananin zurfin cikinta yayi yawa duk da yarintarta Amma sosai ta iya danne abu ta boyesa a ranta.

Maamah datasan AmatulMaleek din ba magana zatai ba sai kawai ta hadiye hawayenta sbd kada ma AmatulMaleek din ta Gani ta miqe daga zaunen datake ta nufi kayan wankin data fitar masu shegen yawa tafara yi.

Satar kallanta AmatulMaleek tayi tareda ajiye allura da zaren hannunta tana zubawa maamah din fararen idanuwanta batareda tace komaiba,

Abu Daya ne koyaushe yake yawo aranta shine idan har Mommy ‘yar uwar maamah dince meyasa koyaushe Se dai a Turo musu kaya da abinci Amma takasa rabasu ta daukesu daga wannan azabar rayuwar wulaqanci da tozarcin da suke ciki a hannun dangin mahaifinsu,

A duk lokacinda abincinsu ze qare qaninta dayake qanqani sosai bara yake zuwa yayo ya samo abinda zaici su kuwa Se dai su wuni su kwana ahakan Kokuma maamah tayiwa matan gidan aikin abincinsu na dare idan ta gama a San mata Wanda zataci da ‘yayanta.

Babban mamakinta a duk ranar da aka kawo musu kayan abinci daga gurin mommyn a ranar ake taruwa a rarrabe komai abarsu da Wanda iyakacinsu kwana biyu ya qare sun koma cikin tsanani..

A rayuwar dasuka taso gidan dayake dauke da iyayensu Maza yanne da qannen mahaifinta kowannen da iyalinsa daga me mace biyu sai me mace uku harma dame hudu Dan haka gidan yake na taro,

Kowa acikin gidan kansa ya sani sai iyalansa,
Babu me iya taimakawa Wani sbd kowa nauyin dayake kansa ma yafi karfinsa Dan haka kusan rayuwar kowa tasa ta fishesa akeyi.

Su biyar ne manyan gidan Maza Kuma kowannensu Yana cikin gidan da nasa iyalan Babu Wanda ya bar gidan duk kuwa da zaman matsuwa da akeyi a gidan,

Babanta shine qaraminsu gaba Daya Kuma shine yayi karatun Boko Kuma shi kadaine yake aikin gwamnati a primary school din Dake qauyen nasu wanda Babu yanda baayi dashi yabar kauyen yaje abasa Wani aikin Amma yakasa tafiya anan yake vice principal har manyanci yaxo ya rasu yabar matarsa da ‘yarsa Daya AmatulMaleek dakuma jaririn qanin Amatun Wanda aka mayar masa sunan mahaifinsa Abdulhameed.

Kafin rasuwar Babah rayuwarsu acikin gidan ahalinsu me suna Sanda Fulde rayuwa ce data bambamta da duk ahalin gidan sbd gata da kulawa da Babah ke Basu itada mahaifiyarta,
Babah baitaba raayin Kara aureba sbd matsi da rayuwar gidan take ciki dakuma ganin yanda tarbiya ma Neman gagara takeyi ga Yan uwansa sbd yawan iyalai duk da kusan da yawa yaran gidan shine yake dauke da lalurarsu sbd nasu iyayen bazasu iyaba ba hali Kuma ahakan bawai sun Dena haihuwar bane.

AmatulMaleek itace hasken idon mahaifinta sbd burinsa da buqatansa na son kebantar da tarbiyarta daga sauran yaran gidan da tarbiyarsu takeda qaranci duk da Yana iya kokarinsa gurin Basu tarbiyar Amma Yana yi ne iyayensu na warwarewa Dan haka ya tsayu sosai Akan tasa ‘yar wadda yake burin tata rayuwar ta ingantu dama sauran kannanta da zasuzo Dan haka baiyi qasa a gwiwa ya Sakata karatu Wanda kaf gidan a mata ita kadaice ta shiga karatun bokon.

Ya rufe idanuwansa tareda kunnuwansa ga duk abinda zaa fada akan ‘yarsa da rayuwar Daya zabar mata Dan haka ita kanta AmatulMaleek din ta taso tamkar miskiniya Bata Hulda ko iya shiga mutane sosai hakama Bata iya fita daga sashensu zuwa kowane sashe agidan sbd sunyi yawan sosai a gidan da kusan daga Wani bangaren idan zaka Wani bangaren sai Wani acikin mazan gidan ya tare yarinya ya lalatata a hanyoyin gidan dasukeda duhu wasu lokutan,
Da yawa yaran gidan wasunsu sun lalace ne a tsakaninsu Wanda haka ake rufe idanuwa ana daura musu aure da junansu.

Wannan shine Mafi girman abun Dake daga hankalin Babah da maamah akan rayuwar AmatulMaleek data fita daban a cikin yaran gidan Dan haka Sam Babu inda Amatun ke fita idan ba tareda mahaifinta ba Koda kuwa aike ne to tabbas hannunta na riqe dana mahaifinta.

Akwai tsautsayin Daya taba kusan afkuwa ga AmatulMaleek din Wanda shine abu na farko Daya daki zuciyar Babah ya Sakar masa ciwon zuciyar Daya zamar masa ciwon jiki Wanda daga karshe kusan shine ajalinsa.

Daga Aiken Amatun can kuryar gida Wani babban Dan kawunta ya dafeta cikin soron gaba ya rufe mata Baki batareda ya bari ta gansa ba yaso illata rayuwarta batareda laakari da shekaruntaba.

Babah ne da kansa ya riski wanna mummunan kaddarar data Saka Yanke jiki ya Fadi Allah yasa Babu abinda ya faru din AmatulMaleek din ta tsira Dan haka ya tattara masu kayansu itada mahaifiyarta zuwa Abuja gurin ‘yar uwar Kuma Aminiyar maamah sukai zamansu acan sai bayan kusan watanni masu tsayi suka dawo.
Bayan dawowansu zuciyarsa Bata taba samun nutsuwa ko kwanciya ba da rayuwa acikin gidan Kuma ba Dan haka ya kama haya a kusa da gidan ya koma da iyalansa,

Acan rayuwarsu ta inganta hankalinsu ya kwanta a lokacin ne AmatulMaleek tafara wayon sanin alaqar mahaifiyarta da ‘yar uwarta Mommy abeeda wadda gabaki daya rayuwarta data maamah ta bambamta Kuma bambamci me girman gaske.

Da farko Bata taba sanin ba uwa Daya Uba dayane ya haifesu sai daga baya idan sunje gidan mommyn Taga yanda mahaifiyarta ke aiki cikin masu aiki tafara fahimtar tabbas ba uwa Daya ce ta haifesu ba Amma har lokacin tana Saka ran Uba Daya ne ya haifesu.

Kafin rasuwar Babah babu abinda yake daga zuciyarsa tareda cizonta da girmamman kunci irin yanda rayuwa zatayi da AmatulMaleek da mahaifiyarta a cikin Yan uwansa.

Wannan dalilin ya Saka ya Yanke hukuncin karban aikin da ASH TALBA ke bibiyansa dashi tin tini.

Bayan ya karbo offer ta aikin da muhallin zama acan Allah beyi zaiyi aikin ba ciwo ya kwantar dashi Wanda ya zama ajalinsa.

Da farko bayan rasuwarsa Babu yanda Madame abeeda bataiba ta tafi ‘yar uwarta musamman sbd haihuwar datai ko suna baayiba Babah din ya rasu Amma Sam dangin Babah din suka qi yarda sbd Dan abinda yabari sukeso aci dasu Dan haka dole madame ta barta a cikinsu tareda AmatulMaleek wadda take tsarar tata ‘yar qwalli Daya itama.

Rayuwa a gidan da Babah yabarsu tayi musu nauyi sbd qarin kulawa da suke buqata Dan haihuwar maamah din da basuda me kulawa dasu ga ciwo Daya shigeta sosai itama na rashin Miji da haihuwa Amma Babu me kulawa dasu.

Hayarsu ta qare Dan haka tini suka tattara suka koma cikin gidan zuria da suka fito Allah yasa ma Babu Wanda ya shiga bangaren nasu Dan haka suka gyara sukai zamansu.

Tin bayan rasuwar Babah madame tabar qasar tareda mijinta da Daman ba’a qasar yake zaune ba sai dai suzo su koma.

Madame tabar qasar Bata San halinda yar uwarta da ‘yayanta suke ciki ba na qunci da tsananin buqata Kuma Daman kaf itace kadai ke kulawa da Aminiyar tata sbd sune danginta.

Maamah ta taso ne a hannun kakarta Amma mahaifin madame Abeeda ne yake dauke da nauyin duk wata lalurarta sbd mahaifinta kafin ya rasu shine babban yaronsa.

Itada abeeda baitaba bambamta tsakaninsu ba sbd daukansu matsayi Daya a ransa Kuma haka ya tsaya tsayin daka ya Saka musu tsananin so da kaunar juna suka taso tamkar Yan biyu sbd tsananin kaunar dasukewa juna tareda daukan junansu Wani bangaren na rayuwarsu.

Abeeda ma marainiya ce mamanta ta rasu Dan haka a hannun matar mahaifinta ta taso,
Duk Wani karatu tare sukai har matakin secondary Wanda suna shekarar karshe alhaji mahaifin Abeeda ya rasu Wanda Hakan ya kawo rabuwarsu Badan sun dena kaunar juna ba sai Dan lokacin rabuwar da yayi.

Maamah wadda sunanta na Yanka yake Asmau ta koma kauye tareda kakarta inda acan riqonta ya koma hannun dangin mahaifinta itama.

Bayan karatun secondary Wanda Bata qarasa ba Babu Wani cigaba daya sake kusanto rayuwarta har Allah ya kawo Babah Akai mata Auren kauye Wanda ya sake durqusar da rayuwarta gaba Daya zuwa qasa danma Allah yasa ta samu Miji me kaunarta da kulawa kamansa sai rayuwar ta Dan yi mata sauki.

Abeeda kuwa bayan rasuwar alhaji dangin mahaifiyarta itama karbanta sukai da gadonta me tsananin yawa suka bar garin gabaki daya da ita zuwa porthcrt inda acan akaci gaba da inganta rayuwarta cikin gata da kulawa tareda tarin arziki me yawa.

Abeeda ta wuce Malaysia acan tayi karatunta Wanda a daidai lokacin Kuma Asmau tana cikin zuriar Sanda Fulde tana ganin rayuwar Auren da Babu komai acikinta sai hakuri da jarabawa bayan jarabawa.
##MAMUH
Regular 700
Vip 2k
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
[11/8, 3:00 PM] +234 816 839 8310: Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#

AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar

2
Nisan dayake tsakanin Asmau da abeeda Bai taba rage kauna ko girman junansu ba a zuciyarsu,
Babu dawowar da Abeeda zatai Nigeria Bata zo har kauye ta ziyarci Yar uwar tata ba Dan haka kusan kaf dangin mijin asmaun Babu Wanda baisan girman alaqarta da kaunar Dake tsakaninta da Abeeda ba,

Duk wata sutura da abincin datake ci Daya bambamta Dana Yan kauyen duka abeeda ce ta tsaya Mata akansu Koda Bata qasa ko tana qasar duk lokaci bayan lokaci sai an aikowa da Asmau abinci da suturar datake sakawa.

Acan dangin mahaifiyar abeeda Babu Wanda Bai gama sanin matsayin kaunar Dake tsakaninsu ba Dan haka Babu Wanda yayi yunkurin hanawa saima tsayuwa da sukai akan inganta rayuwar asmaun duk da tana kauye Dan haka itama asmaun Bata da tamkarsu.

Nisansu Bai hanasu zama abokan sirrin juna ba Dan kuwa Babu matsalar Asmau da abeeda Bata saniba kamar yanda asmaun Babu damuwar abeeda da Bata saniba.,

Rashin samun haihuwar Asmau da wuri yasaka Abeeda ta samu Samar dauko asmaun ta tafi da ita ganin Wani likita a porthcrt,

Da farko hankalin Asmau Bai tashi ba da rashin haihuwarta ba Amma ganin yanda abeeda ta damu ta kwallafa Rai Akai sai hankalinta ya tashi Wanda yasaka dole aka tsaya aka ringa yawon asibiti da asmaun.

Kamar yanda hausawa sukace ita dai kaddara yashi ce ko an dunkulata Bata dunquluwa, Abeeda ta tsaya da karfi da dukiyarta an nemawa Asmau lafiya Bata samu nutsuwa da Kwanciyar hankaliba Saida Asmau ta wayi gari ta samu ciki a jikinta.

Cikin Asmau nada wata biyu Aka kulla Auren Abeeda da Wani ‘dan babban Aminin mahaifinta Aleeyu Muh’d Talba Wanda dagashi har ita bawai suna son juna bane Amma dayake Auren na connection ne Basu damu ba.

Auren Abeeda da Aleeyu aure ne na fitowar Rabon haihuwa kawai Wanda Allah ya kaddaro a tsakaninsu sbd Auren da wata uku Allah ya karbi ransa sanadin jinyar ciwon cikin kwana Daya kacal.

Bayan rasuwarsa ranar da Abeeda ta fita takaba ranar Asmau ta haifi AmatulMaleek wadda taci sunan Abeeda Amma suke kiranta da AmatulMaleek din sbd shine sunan da mahaifinta yafiso din Dan haka take amsa sunan AmatulMaleek din Amma a rubuce Abeeda AmatulMaleek ne sunanta.

Abeeda Bata samu zuwa haihuwar AmatulMaleek ba sbd itama tana fama da tsohon ciki me tsananin wahala Wanda ya Sakata shiga ciwo sosai.

Asmau duk da jegonta bata zaunaba haka taxo ta zauna jinyar abeeda harta samu sauki itama ta qarasa watanninta ta haifi ‘ya mace itama take aka Saka mata sunan ASMAU Amma ana kiranta da Husnah.

A ranar da akai sunan Husnah a ranar aka daura Auren Abeeda da ASHRAF MUH’D TALBA ‘dan uwan Aleeyu Wanda suke Yan biyu batareda sun taba ganin juna ba Amma hakanan zuciyar abeeda tafi kamuwa da son Ash Talba akan Aleeyu sedai Kuma halin Aleeyu ya bambamta sosai da ASH Dan haka zamanta dashi yafara Bata wuya ta bangarora da dama.

Wanna shine damuwar data fara Sako Auren Abeeda a gaba sedai Kuma Asmau ta tsaya sosai gurin Bata qwarin gwiwa Dan ta fuskanci aurenta ta tsaya ta riqe mijinta da kyau.

ASH baida raayin Auren mace biyu Bai taba shaawan Hakan ba Dan haka a zuciya da gangar jikinsa ya amshi abeeda dari bisa dari sedai rashin fuskantar halin juna da sanin juna yanda ya kamata yake azabtar da Auren nasu Amma Kuma kasancewar sunada ilimi dukkaninsu ya Saka Basu taba nunawa junansu gajiya ko gazawa da zamanba bare juna ba,

Matsalar datafi quntatar da Auren nasu shine rashin iya kulawa da soyayyar Auren Abeeda wadda Sam ta kasa yanda zata iya shiga zuciyarsa ta mallakesa ta hanyar kauna ko soyayyarta.

A idanuwansa tana iya hango tsananin girmamawa ne kawai yake mata Babu wata soyayyarta bayan Hakan Dan haka ta dage sosai dan ganin ta mallakarwa kanta zuciyarsa da Babu kowa a cikinta.

A duniya da yawa basusan ba Ash ne mahaifin Husnah ba kaman yanda Babu Wanda yasan matar Ash din bashine ya fara aurentaba.

Zamansu me dadi da Kwanciyar hankali da wayewa suke rayuwar aurensu Dan haka ya dauketa daga kasar suka tafiyarsu inda yake rasuwarsa tareda mahaifiyarsa da kanwarsu qwalli Daya wadda ta kasance tana gida bayan auranta Daya mutu ta fito da saurayin ‘danta Wanda ya girma sosai Yana karatu Shima.

Duk Nisan da Asmau tayi da Abeeda Hakan Bai Hana ASH yiwa Asmau farin sani ba sbd shaquwa da kusancinsu hakama da kansa ya fahimci irin girman junansu a zuciyarsu Dan haka yake respecting Asmau sosai tareda Mai gidanta Wanda yaso ya taimakawa sosai Amma Babah din yaqi yarda da Hakan Dan haka sai kawai mutunci da kusanci suka ya shiga tsakaninsu duk da Hakan ya taimakawa babah din sosai.

 

Bayan shekaru sunja sosai a rayuwar kowannensu Abeeda tayi nasarar shiga zuciyar ASH sedai batada tabbacin ta mamaye zuciyar ne duka Amma ko a iya inda ta samu din a zuciyarsa tanada tabbacin babu Wani guri da wata zata samu shiga sbd ita kanta gurin data samu a zuciyar tasa sai data share shekaru a cikin auren kafin ta samu wannan gurin a zuciyarsa Dan haka ta tabbatarda zuciyar ASH ba guri me saukin samu ga kowace mace ba.

Baida raayin mata kaman yanda baida Wani raayi ko time na abubuwan dasuka danganci soyayya bayan ta matarsa Abeeda wadda yake ganin iya sonta da ita din ta ishesa a rayuwarsa Bata buqatan Qari sbd baida Wani gurin bawa wata macen a rayuwarsa kwata kwata.

Rayuwar Abeeda ta sauya ne ta tashi daga arzikin mahaifinta ta koma arzikin mijinta Wanda ya take ya rufe arzikin mahaifinta datake ganin yanada ta gado,
A familyn ASH kusan shi kadaice me irin wannan arzikin duk da mahaifiyarsu ma nada arzikin Amma ba kamar na mahaifinsu da suka gada ba.

ASH da Aleeyu mahaifinsu daban Wanda bayan rasuwarsa mahaifiyarsu tayi aure ta haifi Aysha wadda ita mahaifinta daban dasu Amma dai mahaifiyar tasu Daya ce.

Sune masu arziki sosai sbd mahaifinsu shine me arziki sabanin Aysha da nata mahaifin baida Wani abun bayan rufin asiri.

Da wannan qyashi da Jin zafin Aysha ta tashi a cikinsu har Allah yasa Akai mata aure ta haihu ta fito daganan aurenta uku tana fitowa karshe dai ta hakura da auren sbd takasa samun masu iri arzikin ‘dan uwanta ASH dashi kadaine yanzu ya rage mata hakama ummansu ta rasu Dan haka ta tattara itada ‘danta NAUFAL ta suka dawo karkashin ASH tamkar shine Uba mahaifin Naufal duk Wani gata da Jin dadi Babu abinda basa samu a gidan karshe dai kusan gidan ya dawo hannun mom Aysha kaman yanda ake kiranta da girma yazo mata sbd ta girma Abeeda sosai ba laifi Dan haka kusan gidan idan aka cire Mai girma me gidan the grt ASH TALBA mom Aysha itace me fada a ji Dan kusan kamar matsayinsu Daya agidan Ash itada abeeda.

Rayuwar mom Aysha a cikinsu ya Saka duk yanda kusancin Asmau da abeeda yake yafara raguwa sbd mom Aysha Asmau ce macen datake Jin har cikin zuciyarta Bata kaunar kusantuwarta da Yan ahalin gidan Dan haka tsauri da kaidojin mom Aysha akan Asmau yasa taji Bata shaawan zuwa gidan Abeeda Koda suna gari Dan haka da wannan kusancinsu yafara raguwa dakuma manyanci Daya zo musu dukkaninsu.

Bayan haihuwar husnah Abeeda Bata sake haihuwa ba Saida manyanci yaxo musu ta haifi ‘da namiji Wanda ya kasance a gurin ASH TALBA shi kadaine jininsa Amma Kuma a zuciyarsa haydar din da Husnah matsayinsu Daya Dan kuwa ita kanta Husnah duk da ta girma batasan ba ASH TALBA mahaifin Daya haifetaba.

AmatulMaleek tanada shekaru goma sha uku a duniya maamah ta sake haihuwar ta haifi qaninta Abdulhameed Wanda harya girma baisan mahaifinsa ba tinda kafin sunansa Babah ya rasu yabarsu cikin halin qaqanikayi.

Rayuwarsu ta zama me Wani irin babban gibine da basusan tayaya zamu cikesaba ko samun me cike musu shi,
Qunci da wahala da yunwa da azaba tareda hantara suke rayuwa acikinsa har Abdulhameed ya girma yayi wayo,
Tunda tagama primary karatunta ya tsaya,
Abdulhameed kuwa karfi da yaji ya zama kamar almajiri sbd ko suturar da zai Saka basuda ita sai abinda Allah ya Basu kawai suke Samu.

A gidan kaf Babu Wanda yake iya Basu abincim da zasuci sbd kowa ta kansa yakeyi kowa na fama da rashi.

Madame abeeda wadda a yanxu matsayinsu da sunansu ya zarce na Baya sbd matsayin da ASH yake dashi a gurin Al’ummar Dake tsananin son ya tsaya musu a matsayin gwamnan jahar Amma baida raayin siyasa duk da Hakan jamaa sosai sukeyinsa Dan haka kusan Babu Wanda baisan the grt ASH TALBA ba.

Rayuwarsa data iyalansa kwata kwata baa qasar yake yinta ba sai dai yakan Fi iyalan nasa zuwa Dan haka jamaa sukeyinsa sbd taimakon dayake bayarwa kaman baisan zafin dukiyar ba Dan haka manya da yawa mutanensa ne hakama talakawan ma mutanensa ne hakama masu kudin Dan haka kowa yinsa yakeyi duk da da yawa baisanma sunayi ba Amma Kam sosai aketa Daman gwagwarmaya da rigimar shi akeso amma Sam Baya raayi.

Ta bangaren matarsa Abeeda kuwa wadda duniya ke kira da Madame abeeda Talba tini rayuwarta data ‘yayanta ta zama abin kallo daga nesa sbd tsaron da ake Basu bana wasa bane sbd ASH Bai hadasu da komai nasa ba Dan haka a yanzu tsakaninta da maamah aike ne kawai Shima sai can idan lokaci me tsayi yaja Dan haka itama maaman ta hakura ta rungumi marayun ‘yayanta.

 

*****Bayan rasuwar Babah da shekara biyu kawu bello ya aure Maamah din wadda bayan wahala da ukubar data ringa sha a hannun kishiyoyi Babu abinda suka Qaru dashi itada ‘yayanta
Ahakan suka ringa Shan kuncin rayuwa har kawun ya gaji ya saketa sbd yace bazai iyaba lalurar tai masa yawa Dan haka dai anan cikin gidan Akai auren anan Akai sakin taci gaba da gwagwarmaya itada ‘yayanta Wanda tanaji tana Gani Abdulhameed yakoma almajiri AmatulMaleek kuwa haka take zaman gidan Bata taba barinta fita ba Koda zuwa cikin gidan sbd yanda gidan yake sake zama hadari sosai ga duk Yan matan gidan da Yara qanana ma Dake tasowa duk da yawa sun lalace a tsakaninsu batareda sanin iyayensu ba.

AmatulMaleek tinda tafara wayo rayuwarta ta zama tamkar kurma sbd rashin magana tinda basuda abin magantuwa akansa Dan bayan tarin kunci Babu komai a rayuwarsu Dan haka ta taso a miskilar gaske Wanda Hakan yafiwa maamah dadi da farin ciki sbd kullum kukan maamah a gaban Allah shine yanda zata bawa ‘yayanta kariya daga masifar gidan musamman AmatulMaleek datake mace.

AMATULMALEEK
Regular 700
Vip 2k
0022419171 Access bank Maryam sani
09033181070

#MAMUH#
#LA HOT
#LIFE
#ASH TALBA
#AMATULMALEEK
#NAUFAL TALBA
#MEERAH HERBS
#ABOKIYAR NISHADI TV CHANNEL

Leave a Reply

Back to top button