Duk Karfin Izzata Book 1Hausa NovelsHausa Novels

Duk karfin Izzata Book 1 Page 19

Sponsored Links

Episode 19*

 

Lafayar da Aunty farida ta kawo musu ta ɗauko, Aunty farida da kanta ta ɗaura mata baƙaramin kyau tayiba ga kitso guda biyu a gaban goshita, kamar wata amarya ga lallenta ja da baki ” wow my diyana kin haɗu iya haɗuwa yanzu muje wajen flowers ɗin garɗing muyi hotan koh zaifi kyau ” to Aunty farida amma sai na ɗaukoh takalmi a ɗakin Ammi ” ina takallamar dana kawo muku ” aa shikam sai gobe zansa yanzu high heel nakeso ” murmushi Aunty farida tayi tare da jan hannunta tana faɗin to muje ” fitowa palon sukayi nan suka isko su Zahra suma sun sha kwalliya sosai sai dai su dukkansu hijabi suka’sa dan zuwa sallar idi ” Aunty farida ina zakuje Zahra ta tambaya ” hoto zamuje muyi a garding, ko zakuyine kuma ” aa nikam banso chewar Zahra ” to kufa tayi maganar tana nuna su lamrat “har suna haɗa baki wajen chewa aa bamusu ” da kyar hiyana tamike dan sarawar da kanta ke mata tana faɗin Aunty farida muje kimana tare ni kam ina so ” riko hannunta Aunty farida tayi dan yadda taga yanayinta kamar zata faɗi da kyarma take tafiya” a harabar gidan suka tsaya san nan Aunty farida tace my diyana kije ki ɗauko ta kalmar naki kinji, kiyi saurifa dan kinga hiyana bazata iya tsayuwa sosaiba ” da sauri diyana ta juya tanufi bangaren Ammi ” Shahram na ganin’su yazo wajen da sauri ya gaida Aunty farida san nan ya tambayeta ko fita zasuyi’ne ya kaisu ” aa tace masa ” juyawa yayi yakoma bakin gate ” suna tsaye har diyana ta dawo kwas, kwas, kwas, take tafiya, a nitse take zuba takunta da yanga ” daga nesa Aunty farida tafara ɗaukarta video sai faɗin wow take, sai da ta iso kusa dasu tukun nan Aunty farida ta tsai da video, suka nufi chikin garding ɗin ” hotona sosai, tamusu a tare san nan tawa diyana ita kaɗai kala kala, bayan sun gamane suka nufi chikin gd Aunty farida na faɗin to my diyana sai kije ki ɗaukoh hijabinki muje masallachi koh ” to diyana tace tare da wucewa ɓangaren Ammi ” Aunty farida da hiyana kuma suka nufi ɓangaren Ummi

SAUDIA

Tsaye yake a gaban mirrow ɗaure da towel a kugunsa da alama wanka yafito, yana shafa mayukan’sa masu kanshi da tsada’ bayan ya gamane ya gyara gashin kansa ya sake feshe jikinsa da turare mai kanshi da tsada, trolley’sa ya jawo ya buɗe ya ɗaukoh farar jallabiya, ya juya a jikinsa yayi kyau kamar balarabe,tsayuwa yayi a gaban mirrow yana kallan kansa, wayarsa dake kan gado tayi kara alamar kira yashigo, a hankali yake takawa kamar yana tsoran taka kasar ya isa gaban gadan,hannu yasa ya ɗauki wayar my blood ne ya bayyana a kan screen ɗin wayar, da sauri yayi picking call ɗin tare da manna wayar a kunnen’sa ” hello ” daga ɗayan ɓangaren DON yace jirginmu zai sauka 9:30 dai dai “ok by the i will be they ” thanks ya faɗa tare da katse kiran’ Aryan zai ajiye wayar ke nan yaji tasake kara alamar shigowar sako, ganin my lovely Aunty yasa ya buɗe sakon,
da sauri ya zauna a bakin gado tare ta kara waro ash eyes nashi a kan’wayar,Sosai yake kallan wayar kamar zai chinye, wow dole Aunty farida ki ruɗe irin wan nan kyau haka,yarinya kamar wata aljana, yayi maganar yana manna wayar a kirjinsa, jinake kamar jibi yamin nisa jinake tamkar ranakun tsawo suke karawa, kusan 10 mnt yana zaune yana surutai, san nan a hankali ya miƙe yanufi hanyar fita,wayar na manne a kirjin’sa

Kai tsaye ɗakin khalid ya nufa nan yasami Yusuf ma a chan dukkan’su sun shirya chikin fararen jallabiya bakaramin kyau sukayiba ” muje koh lokachin sallama yakusa ae chewar Aryan” Khalid yace wai Aryan ina DON ne tun shekaran jiya nake tambayar’ka kakemin wani kauce kauce koh ” nafaɗama’ka Khalid yana nan kawai yaje chikin madina ne ” lallai Aryan to karyan ma bai dace da kaiba, baka sabayi’ba shiyasa ma dakayi yanzu, karyan bata zauna ba ” dogon tsaki Aryan yaja tare da faɗin inkun gama kusameni a masallachi nayi gaba tun da naga baku da niyar tafi, yana gama faɗin hakan yayi waje ” kallan Yusuf dake zaune ya zuba musu ido Khalid yayi”muje koh ” hmmmm kasan’me Khalid wlh DON baya kasar nan wani lokachi sai Aryan yarinƙa magana kamar ba tare muka tasoba ina da tabbachin DON yana London zai wani chemana yana madina shi ko karyan ma bai iyaba ” kaga Yusuf kafita maganar Aryan da DON kazo mutafi masallachi kar murasa sallah, yakai karshen maganar yana nufar hanyar fita ” mikewa Yusuf yayi yabi bayan’sa ” suna fita waje suka samu gaba ɗaya family sun haɗu amma banda Aryan ” Khalid ina Aryan da Prince Ummi ta tambaya tana kallan fuskarsa ” sunyi gaba Ummi ” to muma ae sai muje koh dan kar lokachi yakure ” tare suka jera dayake masallachi kusane da masaukin’su ” suna isa suka rabu su Ammi sukayi ɓangaren mata su Abba kuma sukayi ɓangaren maza

Nigeria

Zaune suke a palon Ummi diyana yau baƙi ya buɗu ta tasa fruits a gaba sai chi take ” hiyana na rike da littafin addu’oe tana karatu ” lamrat na game a waya Zahra ” amrat na kallo a wayar Aunty farida ” Zahra kuwa ta kwanta ta tada kai da chinyar Aunty farida sai hira suke kamar saannin juna ” da sallama Aunty Maryam ta shigo palon ” Aunty farida ta amsa mata fuska ba yabo ba fallasa ” zama tayi a saman sofa mai zaman mutun 1 tare da faɗin, ina wuni Aunty farida anyi sallah lfy ” lfu lau ykk “lfy Alhadulillah ta faɗi hakan tana mikewa ” inakuma zakije kitsaya muci abinchin rana tare mana tun da lokachin yayi chewar Aunty farida ” aa bana buƙata a inda,na fitoma akoi abinchi dama dai kawai nabi dokar gd nanne nazo na gaisheki kuma namiki barka da sallah a matsayinki ta babba, SO no need na tsaya yin wani abun, tana gama faɗin hakan tayi waje ” Allah ya shiryaki Maryam Allah yasa ki gane.. bata garisa maganar’ba sukaji diran manya manya motochi a gd ” da fara’a Aunty farida ke faɗin oyoyo Aunty salma oyoyo Aunty mardiya” tun Aunty farida bata karisa magarba Zahra tamike a guje tayi waje, mikewa Aunty farida ma tayi tabi bayan Zahra suka bar su diyana a ɗakin ” hiyana ta dubisu diyana” kukam bazakuje kumusu oyoyo bane ” ni kam bazanjeba dan bansan’suba kilama halinsu irin na Aunty Maryam ne chewar diyana” lamrat da amrat ma sukache muma bazanjeba ” baki hiyana ta taɓe tana kallansu zata yi magana sai gasu Aunty farida sun shigo” Aunty farida rike da hannun Aunty Salma “Aunty mardiya rike da hannun Zahra da wani baby boy mai kyau dashi mai kama da yaya khalid,saman sofa suka zauna ” da sauri hiyana tafara ɗaga musu gaisuwa” wow Aunty farida wayan nan ƴa’ƴan larabawan fa kodai sune ƴaƴa Abba da ya faɗamin yasamu wasu ƴaƴa daga Allah Chewar Aunty salma ” eh wlh salma sune ” kai gaskiya bari Abba yadawo ya taimaka yabani wanchan da wan nan tayi maganar tana nuna hiyana da diyana ” tab ae kuwa wayan nan yaran nan gani nan bari, inji Abba dan tun farkon zuwar’su nida mardiya mun roka ya hanamu ” aa ae ni nace masa zanyi wlh har sai yabani ” to Allah yaba da sa’a chewar Aunty farida ” ameen Aunty salma ta amsa tare ta chewa ya su nanku ɗaya bayan ɗaya suka faɗa mata su nansu sai wow nice name kawai take faɗi ” kutashi kuje kuyi wanka kuzo muchi abinchi ” a tare Aunty mardiya da Aunty salma suka mike suka nufi dakinsu ” inakuma zakuje Aunty farida ta jefo musu tambaya ” ɗakinmu mana ” wani ɗakin ae sai dai kuje ɓangaren Ammi dan kuwa ɗakinku yazama ɗakin Yan mata’na har sai randa Ammi ta dawo zasu barmuku ɗakin sukoma nasu ” to ae danan da chan duk ɗayane badamuwa chewar Aunty mardiya tayi maganar tare da juyawa tanufi hanyar fita, bin bayanta Aunty salma ma tayi ” Auta ki kiramin masu aiki suzo ku shirya mana abinchi ina zuwa mikewa tayi tanufi ɗakinta ” Zahra kuma tasa hannu ta anshi wayar ta a hannun lamrat, tafara kiran layin binta, bugu binya ta ɗaya Zahra tabata umarni tazo ta shirya abinchi tana gama faɗin hakan ta katse kuran tamikawa lamrat wayar

SAUDIA

abinchi sukechi chikin nitsuwa shiru palon babu mai magana ” Abba me zai hana mutafi gobene dole sai jibine, Chewar Aryan “a sukwane DON ya ɗago yana kallan’sa, shi ko ajikinsa saima latsa wayar’sa yake ” meyasa kakesan mutafi gobe Aryan kodai ƙasa mai tsarkinne bakaso chewar Abba ” aa Abba bawai bansan kasan bane wlh nagajine inasan inkoma gida ” Khalid ya ɗago ya sachi kallan Yusuf sai murmushi suke ” Aiman kuma ya kalli Khalid san nan yajuya ya kalli Yusuf yana girgiza kai a zuchiyar’sa yana faɗin muna fukai asirinku yakusa tonuwa ae idanma wani abu kuke shiryawa ɗan uwana to kanku zai dawo ” Ahmad kam abinchin’sa kawai yake chi hankalin’sa kwan’che ” haidar ya matso kusa da Umar yafara masa magana katsa katsa anya yaya Aryan lafiyar’sa kuwa “umar ya ɗago kai zaiyi magana karaf idon’sa ya sauka chikin na Fahad dake gurga musu mugun kallo ” to shike nan Aryan tun da haka kakeso kukira’su farida ku faɗamusu gobe zamu dawo chewar Abba yayi maganar tare da mikewa yanufi hanyar ɗakin’sa ” mikewa Ammi da Ummi sukayi sukabi bayan’sa “Aunty amarya kuma tamike tanufi nata ɗakin ” kallan Umar da haidar DON yayi yana faɗin me kukejira ae tun bai kai karshen maganar’ba suka mike suka nufi waje, dawo da green eyes nashi yayi kan Fahad, tun baiyi magana’ba Fahad yamiƙe shima yayi waje ” green eyes nashi ya jubawa Aryan sosai yake kallansa” Aryan nasane da kallan da DON ke masa amma yaki ɗago kai dan bai da amsar tambayar da DON ɗin zai masa ” bazan sake tambayar meke damunka ba dan nalura kaima bakasan meke damun nakaba binchike mai kyau zanyi kawai a kan hakan ” sai loakchin Aryan ya ɗago yana faɗin da ka taimakamin bro dan koba komai zaka daina tunanin chewa ina ɓoyemaka wani abu ” ajiyar zuchiya ya sauke san nan yamiƙe yana faɗin to sai kuje kushirya ae tunda komawa gobe yakamamu gashi yanzu kusan karfe 4, da ɗai ɗai suka miƙe suka bar palan

Yola Nigeria

Inna tachi wankan ta tasa wata atampha da bappan, bubu ɗinka mata mayafi ta ɗauka tayi waje, kai tsaye gidan’su buba tanufa, da sallama tashiga gaba ɗayan’su suna tsakar gd ” inna sannu da zuwa chewar buba” yauwa buba ya kafar taka ” naji sauki ae yanzukam ina ɗab iya takawa batare da sandaba ” to alhamdulillah Bappa ina wuni” bappa dattijon arjiki halinsa iri ɗaya da bello mutumin kirki yace lfy habiba anyi sallah lfy ” lfy lau bappa inna larai mushiga daga chiki koh” inawuni inna chewar bello ” yamutse fuska inna tayi kafin ta amsa da lfy, san nan tawuce ɗaki da sauri dan karma wani ya gaisheta, bello ma albarkachin bappa yana nanne shiyasa ta amsa gaisuwar” miƙewa innar buba tayi tabi bayan inna, innar bello dai dake zaune kan tabarma ta taɓe baki tai tana kallansu har suka shige ɗaki a zuchiyar’ta tana faɗin Allah ya kare mutun daga sharrinku dan kuwa wayan nan idan suka haɗu ko sheɗan suransu yake ”

Lfy inna chewar innar buba” lfy ba lau’ba kinga anyi sallah yau yakamata gobe mukoma wajen malam koh dan asamu ayi aikin nan dawuri ” aa to mezai hana muje yanzu chewar innar buba ” to me zakice wa bappan buba idan zamu fita ” aa ae yanzu zai fita dakin ɗan tsaya kaɗan’ma bazaki samesa’ba yanzu dai mujira fitar’sa ” to shike nan bari naje gd na ɗaukoh kuɗin nadawo,bata jira amsar innar buba ba tayi waje ” da sauri sauri ta shiga gd ɗakinta tanufa tana shiga ta ɗaga yar katifar chiyawar’ta ta ɗauki kuɗin ta kirga sauran 5k ,ta juya tanufi waje, a dab da bakin kofa tayi karo da bappan buba zai fita, matsa masa tai tana faɗin Allah ya kiyaye hanya adawo lfy ” amsawa yayi fiska bayabo ba fallasa yayi waje da sauri ” ita kuma tayi chikin gd

Tare suka fito da innar buba sai sauri suke zubawa suka nufi hanyar kungurmin dajin nan tafiya mai tsawo sukayi, kafin su kai wajen duwatsun chikin kogon suka shiga, zaune yake kan wata ƙatuwar dutse ga tukunyar hayaki a gaba sa ” da baya baya su inna suka karisa wajen dan dokar wajenne shiga da baya baya

(ma’anar shiga da baya baya kuwa shine kajuyawa Allah baya kajuyawa alkibla baya kabar halak ka kama haram kabar Allah ke nan ka fiskanchi boka, ya Allah ka tsare mana imanin’mu ya Allah duk halin da zamu shiga ka tausaya mana kabarmu da imanin’mu)

Kan wani jar shinfiɗa suka zauna, wani mahaukachin dariya bokan nasu yayi ha, ha, ha, san nan yace kuɗin da kika rike ko warware tsarin jikin’su bazai yiba bare har aje gamaga nagaba ” to don Allah alagafarta malam..” ke dakata banace baa kiran su nan Allah a nan’ba ko ance maki aikin Allah muke a nan, sheɗan kawai zaki kira mana dan kuwa aikin’sa muke ” kayi hakuri to kataima’kamin ina chikin damuwane idan yaran nan na raye ” zan iya taimakawa na kunce tsarin dake jikinsu ke kuma sai kinemo kuɗin aikin daza’a amusu amma da sharaɗi ” menene sharaɗin komanene zanyi” to farko dai ajiye kuɗin dakikazo dashi, na biyu kuma zaki bani kanki ” to inna tace tare da ajiye kuɗin chikin wata kwarya, idon ta yarufe bataji bata gani” boka kuwa ganin inna ta aminche yasa ya umarchi innar buba da taje waje, ba musu ta tashi ta fice ” nanfa boka yafara biyar bukatar’sa da inna sai dai abun da bata saniba shine ta baya bokan zai nemeta, ba karamin wahala ta shaba tayi ihun azaba shiko ko ajikinsa bukatar’sa kawai yake biya bayan sun gamane, ya umarce’ta da taje gd bayan kwana uku ta dawo ” da kyar inna tamike tana hawaye, tanufi waje nan tasamu innar buba zaune a kan wani dutse ” innar buba na ganinta ta mike da sauri tanufeta, tana faɗin sannu, jerawa sukayi suka nufi gida dan yamma tayi sosai ” yanzu shike nan zai mana aikin chewar innar buba” aa wan nan abun damukayi iya warware tsarin jikinsu kawai zaiyi nikuma sai nasamo kuɗin aiki ” to yanzu ae na zaki samo kuɗin ” nima wlh ban saniba amma koma sata zanyi wlh sai na nemo kuɗin ” to shike nan amma nawa yace maki kuɗin aikin ” 15k yace ” tab lallai to Allah dai ya dafa’mana

(nikoh nace aikin Allah kukene dazakuce Allah ya dafa muku)
inna sai ɗingisa kafa take har suka isa, inna tayi gidanta innar buba ma tayi gida

KANO

Misalin karfe 8 na dare zaune suke a kan table ɗin chin abinchi, Aunty farida ta ɗago tana kallansu tafara magana ” Abba yakirani ɗazun yasanar dani gobe damisalin karfe 5 na yamma jinginsu zai sauka a airport” chike da murna Aunty mardiya ke faɗin alhadulillah alhadulillah ” ae chanake sai jibi zasu dawo Koh chewar Aunty salma” eh daman dawowar’su jibi ne bansan meyasa Abba yace sudawo gobeba Aunty farida tabata amsa tana kokarin goge bakinta ” to kunga yakamata muje mu kwanta dawuri dan mutashi dawuri saboda aiki shirye shiryen chewar Aunty Salma ” eh hakane yanzu mardiya keda salma kutafi bangaren Ammi nikuma zamuwuce nida sister’s ɗinna kamar yadda muka saba, kutashi muje my diyana ” ba musu suka mike gaba ɗayan’su sunai’wa juna sai dasafe

Washe gari tun da sukayi sallar asuba basu mai da barchiba “Aunty farida ta shirya ta tsab chikin a tanfa mai tsadar gaske blue colour wuyarta da hannunta shaƙe yake da manya manya gwala gwala mai kyau da tsada tayi simple make up, plat shoe baki tasa da mayafi baki wayar’ta da ATM kawai ta ɗauka tayo waje, a palo tasamu su diyana” diyana sarkin kwalliya kullun tana chikin kwalliya tana saye da doguwar riga ash colour tayi rolling gyalen rigar a kanta, tayi kyau sosai ” Aunty farida ina zakije diyana ta tambaya” shopping zanje kozaki rakanine ” eh zanje” to duk wadda zataje tazo muje ” diyana da lamrat ne suka mike, suka nufi Aunty farida” Aunty farida na ganin hakan ta juya tayi waje, suka bi bayanta yau ma dai kamar kullun Shahram ne ya jasu da matsakai’chin gudu yafita gidan

Sai karfe 4:30 su Aunty farida suka dawo, su Aunty mardiya gaba ɗayan’su sunyi kwalliya sunyi shirin tarban’su Abba ” a gurguje Aunty farida ta tanufi ɗaki dan yin waka itama tana faɗin my diyana kuyi sauri ku shirya kuma, tana gama faɗin haka tayi ɗakinta “ɗakin Aunty mardiya diyana da lamrat suka nufa a gurguje sukayi waka dan kar a tafi tarban’su Abba a barsu, diyana dai duk saurin datake sai da ta tsaya tayi make up” gida yachika da jama’a sosai karfe 5:10 dankara dankaran motochi masu numfashine suka jero guda 20 “guda 5 suka fito daga gidan Abba suka tadda 15 afarfajiyar babban get jerawa sukayi suna sharara gudu dan sunyi latti da 10 mnt, gudu suke shararawa sosai chikin ƙanƙanin lokachi suka isa airport, lokachin har jirginsu Abba ya sauƙa sai dai basu fara fitowaba,

Fitowa daga motachin, su Aunty farida sukayi suka jingina da jikin motar suna jiran fitowar su Abba gaba ɗayan’su, sun kurawa jirgin ido
Abba ne yafa saukoh wa a nitse yake takawa Aunty amarya na biye dashi sai Ummi da Ammi a baya ” da gudu Aunty mardiya tayi wajen Abba ta rungumesa ita kuma Aunty salma wajen Ummi tanufa, Aunty Maryam kuwa wajen Aunty amarya tanufa, su diyana kam wajen Ammi suka nufa suka rungumeta itama rungumesu tayi tana hawaye ” Aunty farida kam tana tsaye jikin mota ko motsawa batayi’ba
Rike yake trolley a hannunsa yana taku irin na jaruman maza ya saukoh daga jirgin sanye yake da jeans da t-shirt bakake yasa p-cap baki, fiskar nan kafar an aiko masa da mutuwa,Aryan na biye dashi a baya shigarsu ma iri ɗayane basubi ta kan kowaba sukanufi wajen da motochin ke tsaye,” da sauri security dake tsaye a awajen ya buɗe masu kofar ɗaya daga chikin motochin san nan ya anshi trolley hannunsu, ” Aunty farida naganinsu tayi gunsu da sauri ” DON zai shiga motar ganin Aunty farida na zuwa sai ya ɗan dakata ya juyo tare da buɗe mata hannu, da sauri tafaɗa jikinsa, tana faɗin Wellcome my blood ” rungumeta yayi yana faɗin mun sameki lfy”sakin’sa tayi ta juya ta rungume Aryan dake tsaye tana faɗin, lfy ya hanya ” nayi kewarki lovely Aunty chewar Aryan ” nima nayi kewarku sosai wlh ta karisa maganar tana sakin Aryan,
Chikin motar suka shiga gaba ɗayansu ukun, sukasa Aunty farida a tsakiya ” DON yabawa driver umarnin yawuche dasu gd ” ba musu driver yata da motar da ma tsakaichin gudu yabar airport ɗin ” mamakine yakama Abba har yake faɗin kai Allah ya shiryamin Safras da Aryan da farida, wato ita farida tunda taga yan uwanta shike nan batada wata damuwa to Allah ya kara haɗamin kanku, Amin dukkan jama’ar wajen suka amsa dashi san nan suka ranƙaya gaba ɗayan’su suka shiga motochin lokachin har anfara kiraye kirayen sallar mangariba,
A jere kuma a nitse motochin suka bar airport ɗin suka miki titin gida
A dai dai bakin katafaren babban gate motochin suka rage gudun nan take security suka wage musu gate ɗin, suka kutsa chikin gd, 15 daga chikin motochin sukayi parking a harabar wajen 4 daga chiki kuma suka kusa garamin gate suka shiga chikin gd gaba ɗaya,kai tsaye parking space sukanufa ” suna kashi motochin da sauri security suka fito suna bubbuɗe kofar motochin ” Su Abba suka fito, Abba ya dubesu yana faɗin kuyi sauri kuyi alwala gashi har za’a tada sallah, yana gama faɗin haka yajuya yayi ɓangaren’sa da sauri ” Ammi ma ɓangaren’ta tanufa rike da hannun amrat da lamrat dayana hiyana da Zahra na biye da ita a baya ” Ummi kuwa rungume da salma tana rike da Aunty mardiya da ɗayan hannun’ta suka shiga ɓangaren’ta “Aunty amarya rike da hannun, Aunty Maryam suma suka nufi nasu ɓan garen” su Khalid kuwa kowa yanufi nasa ɗakin

Ammi nashiga palo ta saki hannun’su tana faɗin kuyi sauri kuyi alwala koyi Sallah sai muje palon Abba mu gaisa koh tana gama faɗin haka ta nufi hanyar ɗakin’ta suma kowa tayi ɗakinta hiyana diyana dakuma Zahra suka nufi ɗakinsu, Amrat da lamrat ma sukayi nasu ɗakin

Bayan sunyi sallah sungamane gaba ɗayan’su suka nufi palon Abba already Ammi tariga da tatafi chan ” da sallama suka shiga gaba ɗaya family suna zazzaune kan table ɗin chin, abinchi ido kowa ya ɗaga yana kallan’su banda DON dayake duke yake latsa wayar’sa ” a hankali Aryan ya dago ash eyes nashi yana kallanta still dai da light make up face ɗin ta ɗan karamin bakin nan yasha lips’gloss, kasa ɗauke kansa yayi daga kallanta sosai ya zuba mata ido sai taunan chingom take ” yusuf ne ya dawo dashi hayyachin’sa dacewa oyoyo my baby ku karaso mana, wajen table ɗin suka karisa gaba ɗaya ba wanda ya lura da chiwon goshin hiyana dan dasafe anchire mata ban dejin
Zama sukayi ” Aunty farida tabawa masu aiki umarnin su zuba musu ferfesu kayan chikin SA da chips ” sannu da dawowa Abba ya hanya chewar hiyana ” Ammi tace kibari mana sai angama chin abinchi sai ayi gaishe gaishen Koh ” aa Aisha karki takurawa ƴa’ƴana yayi maganar yana kallan Ammi, dawo da kallansa yayi kan hiyana lfy ya….. Bai karisaba maganar ba idonsa daya sauka kan goshinta, subhanallah hiyana meyasameki a goshi haka a razane yayi maganar ” gaba ɗaya idon mutanen palon yadawo kanta har shi kanshi DON sai daya ɗago kai dan jin yadda Abba yayi maganar ” sunkuyar da kanta kasa tayi tana wasa da yan yatsun hannunta,” Abba faduw… Bata karisaba tajiyo,” diyana na faɗin Aunty Maryam che tamana bugun mutu har sai da aka kaimu asibiti ” nan take ido jama’ar palon yadawo kan diyana lbr tashiga basu dalla dalla kamar antam bayeta” what? Abba yafada yana mikewa ” shiru palon yayi ba mai magana, Abba zai sake magana ke nan sai sukaji sallama a bakin kofar palon, amsa sallamar Abba yayi tare da faɗin shigo mana ” ɗaya daga chikin security ne kasa ya duka yana faɗin yallaboi kana da baki a waje ” ok nasan da zuwan’su gani nan zuwa yana gama faɗin hakan yakama hanyar fita ” Abba nafita Ummi ta dubi Aunty Maryam dake zaune hankalinta kwanche tace haba maryam me yaran nan suka miki zaki musu irin wan nan bugun ” dogon tsaki Aunty Maryam taja san nan ta ɗora dacewa na tsanesu ne shiyasa na bugesu ko zaki rama musune” gaba ɗaya palon kallon Aunty Maryam suke ” me yasa kika tsanesu Maryam, laifinme suka miki Ammi ta tambaya a nitse ” ke Aisha badake nakeba banzo kankiba tu kun nan tsanar dana ke mikine ae tasha fesu ” a fusache DON ya mike ya ɗaga yasu biyar zai zabga mata mari green eyes nashi ya sauƙa chikin na Aryan dake zaune ya zuba musu…✍️✍️

Yau nayi kokari namuku long page to ina buƙatar more comments

Iya comments iya read more amma jiyama kunyi kokari kunmin comments dayawa ina godiya 🙏

*💫STAR LADY💫*

 

*DUK ƘARFIN IZZATA*

_💖Story And Written💖_
⬇️
*Star Lady*

*

 

 

Leave a Reply

Back to top button