Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 41

Sponsored Links

Khadijah ta shiga hali na damuwa sosai bayan tafiyar sudais, bata da aiki sai na tunani da xubda hawaye bata taba xaton rabuwa da Sudais a lkcn ba, da ba don Nanny dake gidan tana kwantar mata da hankali ba da abun ya mata yawa, gani take kamar sudais xai dawo kullum jiran tsammani take amma shiru wasa wasa har sati biyu, ta rame ba kadan gashi kullum cikin jin ciwo take a kirjinta, ciwon da ta fi shekara bata ji sa ba sai gashi ya dawo mata da karfinsa, hakan yasa Nanny ta tilastata suka shirya suka tafi asibiti don ko baccin kirki bata iya yi da daddare, khadijah bata yi mamakin abinda likita yace game da ciwon da take yawan ji a kirji ba, at anytime xata iya kamuwa da ciwon xuciya, yini biyu tayi asibitin under medication, nanny tayi ta kai kawo da twins xuwa asibitin, da yamma likitan ya sallamesu ya kuma bata shawarari da dama kan abinda ke janyo ciwonta da yanda xata yi preventing tashin ciwon, A hanyarsu ta dawowa cikin Napep da damuwa Nanny tace “Yanxu Mum twins da kike sa ma kanki damuwa haka idan abu ya same ki yaran ki fa? Ko don su baxa ki hakura ki rufa masu asiri ki kwantar da hankalin ki ki rungumi kaddara ba, kar fa ki manta ko wani bawa da irin tasa kaddarar, so why not just accept urs a yanda ya xo maki” Khadijah ta goge hawayen dake xuba idonta a hankali tace “Ban san ya xan yi ba” Nanny ta kwantar da murya tace “Cire komai xa ki yi a ran ki, kiyi facing sabuwar rayuwar da xa ki fara da yaran ki, bawan Allahn nan ya tafi, ya kuma ya maki duk abinda ya kamata kafin ya tafi yanxu the ball is in ur court, sai kiyi abinda ya kamata ki kuma rike addu’a sai komai ya xo maki da sauki, as a mother nake baki shawara Khadijah… For the sake of ur boys ki yi hakuri ki cire ma kan ki damuwa don Allah” a hankali khadijah tace “Toh nagode sosai” suna isa gida Khadijah ta sauka ta ba mai adai daitan kudi, xata karbi shureim hannun Nanny ya makalkaleta ya ki yarda, jikinta yyi sanyi tana kallon yaron, Nanny tayi murmushi ta fito da duk yaran biyu, khadijah ta karasa ta bude gate din sannan suka shiga gidan, ba laifi ta dau shawarar Nanny ganin shi kadai ne mafita a gareta sai dai hakan bai sa fara’arta ya dawo ba, she is always sad, bata taba xaton Sudais xai bar ta so early a rayuwa ba, kusan kullum sai ta yi tunaninsa, magungunan da take sha ya taimaka ya rage mata ciwon xuciyar da take fama da shi duk da baya tasar mata ma sai da daddare taji kamar xata mutu, ba karamin kokari take yi na ganin ta ja su little sudais a jiki ba amma sun ki yarda ko da yaushe cikin gudun ta suke kamar dodo, hakan na kara sa ta shiga damuwa Nanny ta dinga nuna mata a hankali xa su sake da ita kar ta damu, a ranan da yaran suka cika shekara daya a duniya Nanny ta raka Khadijah tayi enrolling kanta a ss1 na wani makaranta dake nan anguwar ta su, idan ba ita ta gaya maka tana da yara har biyu a gida ba in xa a shekara ana gaya maka baxa ka yarda ba, a lkcn kuma shekarunta sha bakwai a duniya, kana ganinta kasan she is a teenager, a hankali khadijah ta fara kokarin yakice tunanin sudais a ranta domin tayi concentrating a karatun ta, idan ta fita tun safe sai hudu take dawowa gida, sannan ga islamiyyar da ta shiga na yamma, hakan yasa still babu wani interaction tsakaninta da yaranta tun da ba xaman gidan take ba, amma har ga Allah yanxu ji tayi tana son abun ta duk da tsoronta da suke ji har lkcn. Haka rayuwa ta ci gaba da kasance ma khadijah har ta gama ss1 lafiya, xuwa lkcn abu uku ne ke damunta a xuciya, Rashin Ummanta, gudun ta da yaranta suke sai kuma ciwon xuciyar da ya sa ta gaba abu kamar wasa kusan ko da yaushe hanyar asibiti take wanda hakan ke sa ta fashin makaranta don ma tana da kokari, Sudais kam ta rufe sa a babin rayuwarta sai dai duk sllh sai tayi masa addu’ar Allah ya saka masa da alkhairi abinda yyi mata a rayuwarta da yaranta. Yau lahadi suna parlor, Nanny na feeding Sudais da shureim da yanxu shekarun su biyu da yan watanni a duniya indomie ta dafa masu take basu, yaran sun yi wayo sosai babu inda basa xuwa sai dai fa da ka gansu kaga Aliyu barin sudais komai na Abban nasa ya dauko, sau da yawa sai Khadijah tayi ta kallonsu, wani lkcn tayi murmushin takaici, wani lkcn kuma tayi hamdala ga Allah da ya bata yan biyun, Nanny ce ta katse shirun dake tsakaninsu tace “Mum twins to ya xa ayi da cefanen, wa enan ba yarda xa su yi in tafi in bar su ba, kuma wahala kawai xa mu je mu sha idan muka tafi gaba daya” Khadijah ta ajiye novel din hannunta tace “Nanny kawai da wayo xa ki tafi ki bar su” a tare yaron suka kalleta, Nanny ta kyalkyale da dariya tace “Toh ai kin tona, wa yace maki basa ji, sarai sun ji abinda kika ce” murmushi khadijah tayi tana mamakin sharpness din twins din, tuni shureim ya kara matsawa kusa da nanny, Khadijah ta tabe baki tace “Toh bari ni in je” Hijab har kasa ta daura kan kayan jikinta sannan ta dau kudin ta yi ma Nanny sallama tana daga ma boys din hannu ta nufi kofar fita su ma suna daga mata, jikinta yyi sanyi ganin in dai uwa xata fita yaranta sun dingi kuka kenan xa su bi ta, but why is her own case different, ko a jikin yan biyun dake cin Indomie da nanny ke basu har ta fita, to ita bata san kuma ya xata yi yaran nan su saki jiki da ita ba, iyakar kokari tana kokarin kwatanta masu abinda sudais yace Kafin ya bar su amma sun ki sakewa da ita, tana tsaye bakin titi tana jiran abun hawa a ranta kuwa tunani take ko dai abinda sudais ya fada kan nonon da bata basu ba gaskiya ne, kenan haushin ta suke ji? Ji tayi da ma basu girma ba ta basu nonon yanxu, tsabar yanda jikinta yyi sanyi bata lura da motar da har ya wuce ta da farko ya fara reverse a hankali yana dawowa ba, tana ankarewa ta dauke kai da sauri hade da tsuke fuska don hakan ma yasa bata son fita, tana mamaki da jin haushin me yasa in dai xata fita sai an tsayar da ita, ita ba wannan ne gabanta ba kuma bata jin xuciyarta xai kara kula wani d’a namiji har ta bar duniya, ganin mai motar ya fito daga motarsa ta bar wajen da sauri tana tafiya fuska daure ba tare da ta damu ta kallesa ba, ji tayi ance “Khadijah?” ta juyo da sauri suka yi ido hudu da shi, ya dinga kallonta kamar me son kara tabbatar da ita ce ko ba ita bace, ita din ma kallonsa take da mamaki, yace “Baki gane ni ba Khadijah?” Jikinta yyi sanyi lkci daya tayi murmushin da ya bayyana fararen hakoranta tace “Na gane ka, am just trying to be sure ko kai ne ko ba kai bane” ya wara yace “Maa sha Allah, Imagine we met after 3 good years” murmushi ta kuma yi tana kara kallonsa da kyau ganin yyi mata tsayi fiye da yanda ta san sa a da tace “Sure, to ya bayan rabuwa” ya rike chin dinsa yace “Waow kin girma Khadijah, just look at how calm you are now, kin tuna lkcn da kike yawo ba Hijab da jikakken kaya?” dariya ya bata ta rufe fuska tace “Har da tsokana” yace “Am serious, a Abuja dama ku ke?” Tace “Ehh wllh, ya su mama fa” yace “Suna kt, nima ban dade da fara aiki a nan ba, just 7 months back” Khadijah tace “Allah sarki, toh Allah ya taimaka” d’an shiru yyi yana kallonta, kafin a hankali yace “Ko kin yi aure ne Khadijah?” Kallonsa ta tsaya yi ita ma, lkci daya ta samu kanta da girgixa masa kai tace “Aure kuma, A’a ina karatu ne” yyi murmushi yace “That’s good, kar in tsaya ina ta tsurutu da matar aure ban sani ba” murmushi kawai khadijah tayi a xuciyarta kuwa mamakin yanda aka yi ya fara magana ta yi don a lkcn da ta san shi da wuya yake magana sai dai danna waya, lkci daya jikinta yyi sanyi tuna abinda yyi mata a lkcn da take walagigi a katsina cikin yunwa, muryarsa ya katse ta yace “Ina xaki yanxu?” Ta kallesa tace “Kasuwa” yace “Toh shiga in yi dropping din ki” d’an xaro ido tayi tace “Kai da ba d’an gari ba?” Yace “Wata na 7 kice min ba d’an gari ba” murmushi tayi tace “Toh naji kai d’an gari ne” yace “Toh shiga muje” motar ta bude tana murmushi ta shiga, ya xaga ya shiga maxaunin driver suka bar wajen, yana driving yace “So ya rice and stew, and Irish with egg? Kuna nan kuna damawa koh?” Dariya sosai Khadijah tayi ta rufe fuska, yana murmushi yace “Yarinyar nan ta kashe min kudi a lkcn da abincin yan gayu gashi sai Abba ya bani nima lkcn” Khadijah ta dago a hankali tana kallonsa tana murmushi tace “Ae yanxu babu abinda bana ci har tuwo da miyar kuka, da ma kunu da kosai” ya wara ido yace “Da gaske? Anya xan yarda kuwa” ta gyada masa kai tace “Serious…” yace “Hmm that’s surprising amma” ta turo baki tace “Baka yarda ba kenan?” yace “Toh ai ban ce komai ba Khadijah” suna isa kasuwa bbu yanda Khadijah bata yi da shi ya tafi ba yace xai jira ta, bbu yanda ta iya haka ta siya abubuwan da tasan xa su bukata a lkcn daga baya sai ta dawo ta siya sauran don bata son ta bar sa yyi ta jiranta, yana parking kofar gidan da ta nuna masa yace “Nan ne gidanku?” Ta gyada masa kai ta bude motar ta fita, yace “Toh ki gayar min da su mama da mutan gida” a sanyaye tana kallonsa tace “Xa su ji nagode sosai” daga haka ta juya xata shiga gate, yace “Wait Khadijah baki ban number ki ba mu dinga xumunci” dawowa tayi ta kira masa numberta yayi saving yana kallonta yace “It’s nyc meeting you once more Khadijah” ta kirkiri murmushi ta daga masa hannu ta shiga cikin gida, Nanny na kitchen su sudais kadai ne xaune parlorn ta sa masu cartoon, khadijah ta ajiye ledan hannunta ta isa kusa da su ta xauna tana kallonsu, su ma kallonta suke, ta yi murmushi ganin irin kallon da suke mata ta yi masu kiss gaba daya, Sudais ya goge bakinsa shureim na ganin haka shi ma ya goge nasa, jikinta yyi sanyi sosai tana kallonsu, bata san lkcn da hawaye ya kawo idonta ba ta mike ta wuce daki da sauri, Nanny ce ta shigo dakin ganin khadijah kan gado tana hawaye da mamaki ta karaso da sauri tace “Mum twins me ya faru kuma?” Cikin rawar murya tace “Wai don na masu kiss shine suke goge bakinsu” dariya sosai Nanny tayi kafin tace “kai Khadijah shine har da kuka, to kyalesu xan yi maganinsu” daga haka Nanny ta juya ta koma parlor, taso keyar boys din tayi suka taho dakin, kusa da khadijah ta ajiye su duk suka shiga kkrin sauka daga kan gadon Nanny ta daure fuska tace “C’mon, duk wanda ya sakko xan xane sa, ita ce uwar ku ba ni ba” Kuka suka fara yi kuma basu sauka kan gadon ba, Nanny na kallon khadijah dake ta kallon kyawawan yaran nata tace “Yanxu abinda xa mu yi shine xa su dawo kwana nan dakin, ke xaki dinga masu wanka ki shirya su, ke xaki dinga ba su abinci hakan kadai xai sa su saki jiki da ke” a hankali khadijah tace “Toh” Nanny tace “Don haka duk safe kafin ki tafi school sai kin masu wanka kin shirya su ni kuma in hada masu breakfast sai in baki ki basu” kai kawai Khadijah ta gyada don har ga Allah bata son gudun ta da yaran suke, haka Nanny ta fita ta bar su suna kuka xa su bi ta, amma da yake suna jin magana bbu wanda ya sauka daga kan gadon kamar yanda tace masu, suka gama kukansu suka yi shiru suna kallon khadijah, Sudais yyi tapping dinta yana nuna mata kofa yace “Nanny…” Murmushi Khadijah tayi ta jawo sa jiki tace “Nima Nanny ce ai” hakura yaran suka yi suna ta xaune dakin kusa da ita har bacci ya dauke su, Nanny na ganin lkcn tashin su ya kusa misalin karfe biyar na yamma ta dama masu custard ta dafa masu indomie ta kawo ma khadijah dakin ta fita ta rufe masu kofa, a lkcn kuma suka tashi, duk suka yi jigum suna kallon khadijah, ruwan wanka ta hada a bathroom dinta tayi masu gaba daya sannan ta fito ta shafa masu mansu dake dakin ta sa masu singlet da pant ta xaunar da su kan carpet ta shiga basu custard din suna karba, har ranta ta ji dadin hakan suna gama sha kuma ta fara basu indomie da egg din, shureim na koshi ya fiddo wanda ta sa mashi a baki ya mike ya kai mata bakinta, murmushi tayi ta bude bakinta ya xuba mata abincin ta shiga ci a hankali. Sai kusan karfe shidda Khadijah ta fito parlor da yan biyun nata, cartoon ta sa masu parlorn duk suka xauna kan kujera suna kallo basu bi ta kan Nanny ba, da daddare a kan gadon ta ta shimfide su bayan sun yi bacci, ta gama shirin kwanciya kenan ita ma wayarta ya fara ring, ita dai bbu mai kiranta a waya ban da Nanny sai wata classmate dinta Aisha dake sonta sosai, ta dinga kallon number kafin ta daga, sallama yyi mata jin muryar hankalin ta ya dan kwanta sai dai bata san dalilin kiran ba ta amsa masa sallamar ta gaishesa yace “Ko kin fara bacci ne?” Ta girgixa kai tace “A’a yanxu dai xan yi” yace “Ohk, ya mutan gidan?” Tace “Lafiya lau Alhmdllh” yace “Maa sha Allah” shiru ta yi bata ce komai ba, a hankali yace “Kawai sai kika bar garinmu ba sallama Khadijah” tayi murmushin karfin hali tace “Ummata ce ta xo ta dauke ni ai” yace “Allah sarki, but dama me ya kawo ki gidan tun farko” khadijah da taji kamar kar tace komai kawai ta yi murmushin takaici tace “Ai yayan Abbana ne” yace “Are you serious?” Tace “Uhn” yace “Waow, to me yasa basu baki abinci” ta wara ido tace “Suna bani fa, ni ce ban iya cin abincin ba lokacin” murmushi yyi yace “Allah sarki, kwanaki ma ai kawun naki yyi accident kin sani koh” Khadijah ta bude ido sosai tace “Haba dai, ban sani ba, basu gaya mana ba” Sadeeq yace “Ehh amma da sauki yanxu ina jin ya samu lafiya ma” A hankali khadijah tace “Toh Allah ya kara kiyayewa” yace “Ameen” shiru ne ya biyo baya kafin yace “Kin taba ba Umma labarina” Khadijah da taji jikinta yyi mugun sanyi a hankali tace “Kowa ma ina ba labarin ka, cos you fed me when I was in need of food” Sadeeq yace “Noo I did that for the sake of Allah, not for you to tell everyone” murmushi kawai khadijah tayi a sanyaye, shi ma murmushin yake yace “Sure, yaushe xa ki hada ni da Umma mu gaisa ko kuma in xo har gida in gaisheta, ko baki son mu yi xumunci sosai?” gabanta ne yyi mugun faduwa and she was totally lost of words, a hankali yace “Hello, Khadijah are you there?”

Back to top button