Author: Novels

  • Noor Al Hayat 14

    Noor Al Hayat 14

    By khaleesat Haiydar_📚✍🏻

    14…..

    Tsayawa yyi yana kallonta ta shiga parlorn sannan shima ya shiga, kan kujera ta nufa ta xauna, ya karaso bayan ya kulle kofar ya ajiye ledan hannunsa kan center table, sannan ya shiga daki, jinginar da kai tayi da kujera tayi xurfi cikin tunanin da take taji yana kiranta, dagowa tayi da sauri ta gansa tsaye gefenta ya rungume hannunsa, a hankali yace “Na hada maki bathing water a bathroom” sunkuyar da kai tayi, ta mike yana gaba ta bi bayansa xuwa dakin, towel ya dauko ya mika mata, ta karba murya can kasa tace “Thank you” ya juya ya fita dakin, da mouth wash na Listerine ta wanke bakinta, tayi wanka da shower gel, sai kusan bayan minti talatin ta fito daga bayin, bayan tayi ta tsayuwa bakin kofar bathroom din tana tunanin fitowa da towel, bbu kowa dakin sai Hijab dinta da ta gani kan gado, mamaki ya kama ta tayi ta kallon Hijab din, karasawa tayi ta dauka ta koma bathroom din, wanke kayan da ta cire tayi sannan ta sa hijab din ta fito da kayan da ta wanke a bucket, xaune ta gansa a parlor yana rike da remote, kallo daya yyi mata ya dauke kai har ta shigo parlorn, yace “Why did u wash, u still under medication” bata ce komi ba, yace “Na bude maki kofar….” Tace “Da gaske?” Yace “Ehh, ki tafi ki shirya” murya can kasa tace “Nagode” sannan ta wuce tana rike da Hijab din. Sai da tayi sllh snn ta wanke masa towel din a bayinta ta fito ta shirya ta tafi shanya kayan da ta wanke da towel din nasa, kwanciya tayi daki bayan ta gama lkci daya bacci ya dauketa. A hankali ta bude ido jin kamar ana tashinta, ta mike da sauri tana kallon sa, yace “I’ve been knocking and calling since, but…. Taso mu je ki ci abinci” ta girgixa kai tace “Am not hungry bacci nake ji” yace “Noo, baki ci komai ba yau, kuma kinga xa ki sha magani, you have to take something….” Daga haka ya mike yana kallonta, sauka tayi daga kan gadon ta bi sa suka fita parlor, xuba mata abincin yyi ya mika mata ta karba ta fara ci, wayarsa yake ta dannawa har ta ajiye abincin tana yamutsa fuska tace “Na koshi fa” ya kalli abincin sannan ya dau ledan maganin ya ballar mata drugs din ya taso ya mika mata da goran ruwa ta karba, ta sha maganin tana kallon sa yace “Allah ya sauwake” bata iya ta ce komai ba, yace “To ki je ki kwanta, sleep without thought plss” ta gyada masa kai sannan ta tashi ta shiga daki. Bata tashi ba sai kusan biyu da rabi na rana, ta shiga bayi tayi alwala ta fito tayi sllh, tana idarwa ta sake kwanciya. Knocking kofar dakin taji ana yi cikin bacci, ta mike xaune ta sa hijab sannan ta bude kofar, yana tsaye bakin kofar, yace “Have u prayed zuhur?” Ta gyada masa kai, yace “Abinci fa” tace “I am not hungry” ya girgixa kai yace “You are, fito ga abinci na kawo maki sai ki sha magani” daga haka ya juya ya bar wajen, bin sa tayi, yana daga tsaye ya nuna mata abincin kan table, ta karasa ta dauka, tuwon shinkafa ne da miyar vegetable ta gani da ta bude, ta daga kai tana kallon sa, ya daga kafada yace “Yea, a frnd of mine ce ta yi…” Tace “Kai baxa ka ci ba?” Ya girgixa kai da sauri yace “Noo I don’t take heavy foods, I don’t take swallow” murmushi tayi ta dauke kai, ya shafa kai yace “Sbda ke na karbo” tace “Toh ngd” yace “No thanks” plate taje ta dauko a kitchen ta debi abincin, shi dai har lkcn yana tsaye, ta kallesa a hankali tace “Baxa ka xauna ba” shiru ya d’an yi, sai kuma ya karaso ya xauna kan kujerar dake kallon nata yace “So u care” bata ce komai ba ita dai, a hankali ta dinga cin tuwon, duk lkcn da ta daga kai sai sun hada ido, daga karshe bata sake yrda ta dago ba har ta gama cin tuwon ta dau magani ta sha, sai a snn ta sake kallon sa taga kallonta yake still, hade rai tayi ta dauke kai, yyi murmushi yace “Who is Aliyu?” Kallon sa tayi da sauri, kamar yanda shi ma yake kallonta har lkcn, can ta tsuke fuska tace “Ban gane ba” bai sake cewa komai, bayan kusan minti biyar yace “don’t pretend… Is he ur Husband?” xuciyarta na bugawa tace “Nooo” Yana mata wani kallo yace “Ur Ex Husband?” Hade rai tayi sosai cike da masifa tace “Noooo” sai kuma ta mike tana masa wani kallo tace “I know nothing about what u are saying” ya d’an yi murmushi yace “You passed out yesterday at the hospital with the name Aliyu in ur Mouth” shiru tayi tana kallon sa a sanyaye, lkci daya hawaye ya cika idonta, can ta juya ta bar masa parlorn da sauri, kiran ta ya dinga yi har ta shige daki ta xauna kasa ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka, bin ta yyi cikin dakin, ya karaso gabanta ya durkusa a hankali yace “Ohk, I am very sorry Khadijah, may be I shouldn’t have say anything about that, but dole xan yi magana, Billah da xan ga Aliyun nan… Sai na sa ya d’an dani abin da kike ji, I guess he broke ur heart kuma yake kokarin dawowa rayuwar ki yanxu saboda may be selfish reason dinsa, he will regret that duk ranan da muka hadu face to face…. I vow!” ita dai bata ce masa komai ba sai kukan da take, duk jikinta yyi mugun sanyi, mikewa yyi ya fita dakin. Har dare khaleel bai shigo ba, tun da tayi magrib take hade abubuwan da tasan xa ta kai gida, don bata jin xata kara kwana a kasar, gaba daya xaman kasar da karatun ya fice mata a kai, hawaye kawai take duk jikinta a sanyaye, Sudais has always wanted her to be a doctor, ta xo ta samu kan ta a bangaren pharmacy, wanda a yanxu bata jin ma xata ci gaba, domin kuwa ta hakura da karatun, may be some other time she wil be d doctor Sudais wants her to be, to ko ta xama likitan ma what is that adding to her life, wanda take son yi dominsa ya tafi ya bar ta a lokacin ta fi bukatarsa a rayuwarta, baxa ta ce ya gujeta ba, but what’s the difference? Kusan duk daya…. Ta share hawayen idonta ta fito parlor a sanyaye, tsaye tayi tana kallon Khaleel da shigowarsa knn a hankali ta sauke idonta kasa wasu sabbin hawayen na xubo mata, ya karaso kusa da ita yace “Ina xa ki?” Ta juya masa baya tana kkrin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba, a hankali yace “Khadijah” cikin rawar murya tace “Am going back to Nigeria” ya juyo da ita ya xaunar gefen kujera yana kallonta, ya bar ta tayi kukan me isarta, ta hade kai da gwiwa tana sauke ajiyar xuciya, cikin sanyin murya yace “Tell me about you Khadijah” Ta dago tan kallon sa hawaye na sakko mata, sai dai kuma tayi ma kanta alkawarin bayan Sudais bbu wanda xai ji ita wacece, muryarsa ya dawo da ita tunanin da take, yace “I still don’t deserve to know you koh?” Ta sunkuyar da kanta tana goge hawayen dake sakko mata, a ranta kuwa tunani take anya xata iya fadi ma Khaleel ita wacece kuwa, a hankali ta xamo kasa daga xaunen da take kan kujera, ya sakko k’asan shima yana kallon kwayar idanuwanta da suka rine, kife kanta tayi da kujera cikin sanyin murya tace “Ka daina kallona da idon ka” ya d’an yi jim sai kuma yace “Why?” A hankli tace “Bana son irin su” murmushi yayi yace “Da gaske” taki cewa komai, a hankali yace “Toh na daina kallon ki” dagowa tayi suka kara hada ido tayi saurin mayar da kanta jikin kujera, dariya ta basa sai dai bai yi ba ya shafa kansa yana murmushi, murya can kasa yace “Am all ears Khadijah” ta dago kanta tana wasa da dogayen yatsun ta tace “Ohk…..” Wayarsa ya da ya fara ring ya ciro aljihunsa, ta kalli screen din kamar yanda shi ma yake kallo, Jawaheer ne jikin screen din… Yyi silencing wayar ya ajiye a hankali, Tsura ma lallausan carpet din da suke xaune kai ido tayi ko kiftawa babu, cikin sanyayyan muryarta tace “I am an only child… I was raised from a very rich home, I was raised by only my Dad don kuwa ina da shekara uku kachal a duniya mahaifiyata ta rasu….” D’an murmushi tayi wasu sabbin hawaye na taruwa idonta tana kallon Khaleel da ya kafeta da nasa idon….

    Who is Khadijah?

  • Noor Al Hayat 28

    Pharmacy Aliyu ya tafi ya siyo mata drugs ya dawo gidan, bedroom din mumy ya shiga ya bata ledan maganin tace “Toh ni nasan prescription dinsu Aliyu, ka tasheta ka bata mana” yace “Ohk” sannan ya fita xuwa dakin baby, baby na xaune kan study table din ta tana solving mathematics din, Ya karasa kusa da gadon yana kallon khadijah, kallon baby yayi yace “Je ki tambayi mai aiki a downstairs ko ta ci abinci” Baby ta fita ba a dau lkci ba ta dawo rike da plate din abincin ta ajiye a kasa tace “Tace bata ci ba” Yace “Tell her to make a cup of tea” baby ta juya ta fita, da cup din shayin ta dawo ya karba ya ajiye sannan ya tada khadijah, mikewa xaune tayi tana murxa ido ya dau shayin ya mika mata, ta girgixa masa kai tace “Am not hungry” yace “I know you are not Hungry, kafin in dawo kin shanye shayin nan” daga haka ya fita, Baby ta taho da sauri tace “Kawo in taya ki sha kafin ya dawo” khadijah ta mika mata, baby ta fara shan shayin don ba xafi sai da ta yi rabi ta mika ma khadijah, ta bata fuska tace “It’s till plenty” baby ta sake kafa kai bata sauke ba sai da ya rage mitsitsi, ta mika ma khadijah ta karba, ta bar gun da sauri tana goge baki ta ci gaba da abinda take yi a study desk dint, khadijah ta shanye sauran ta ajiye cup din, xata kwanta sai ga shi ya shigo yana kallon cup din dake ajiye, hade rai yyi baby sai satan kallonsa take ya juya direction dinta tayi saurin dauke kai, kallon khadijah yyi yace “Shayin kika bata ta shanye kenan” ko rufe baki bai yi ba baby ta fice daga dakin da gudu, ya bi ta da ido, daukan cup din yyi ya mika ma khadijah yace “Tafi ki kai a sake hada maki wani da kanki” kamar xata yi kuka tace “Ni ba yunwa nake ji ba” ya wani hade rai yace “Tashi ki fita” ta mike da kyar ta dau cup din xata fita yace “Ina jiran ki fa” Rabin cup ta sa kyauta ta hada mata shayin ta dawo dakin yana tsaye ta shanye sannan ya bata magungunan da bottle water, da kyar ta shanye su har da kukanta, ya wani hade rai, xata kwanta ya hanata ya dauko textbook din da baby take assignment yace “Solve it now ba sai kin kwanta ba” karba tayi a hankali yana kallonta ta fara solving maths din, yace “Idan kin gama ki kawo min downstairs” tace “Toh” sannan ya juya ya fita, dinning ya koma ya xauna, saleem dake xaune parlor bai ce masa ba shi ma bai ce masa ba, bayan kusan minti sha biyar khadijah ta sakko rike da textbook da note book din baby, gun Aliyu ta nufa ta ajiye tace “Na gama yayanmu” ya dau book din yana kallon abinda tayi, after sometime yace “Good, shine kike son a sa ki jss2” ta d’an yi murmushi ce “A jss2 nake ai, it’s just that lesson teacher dina back then at home yana koya min karatun jss3” Aliyu bai ce komai ba ya rufe books din, ganin tana ta tsaye ya daga kai yana kallon idonta da suka rine yace “Toh tafi” juyawa tayi xata tafi dakin kyauta ya kirata, ta dawo yace “Tafi dakin baby kiyi kwanciyar ki” Sama ta kalla tayi shiru, yace “Tafi na ce” juyawa tayi ta nufi stairs din, saleem ya bi ta da kallon gefen ido, tana kwanciya dakin baby bacci ya dauketa. Tun daga wannan lokacin khadijah ta koma dakin baby da kwana ba don kyauta ta so ba, baby da kanta tace ma Mumy ta gaya ma kyauta ta dauko kayan khadijah a kawo ta saka a cikin press dinta akwai space, duk wannan abun Anty khadijah na nan ta sa masu ido abun na cin ranta wai khadijah ce har sama dakin baby… tabdii, sai dai bata ce wa kowa komai ba da yake har lkcn bata magana da Aliyu, Mumy ma ko shiga dakinta ta daina yi, yanxu saleem ne nata da siyama da Aneesah a gidan, sai dai fa ita kadai tasan kudurin dake ranta, kusan a dakin Anty Khadijah Saleem ke yini, da yake ba wani shiri suke yi da Abbansu Aliyu ba bata fara ce masa komai kan khadijah ba, tun da ta ki xaman aure domin kuwa aurenta yyi uku ko ga maciji basa yi da shi idan ba yanxu da ta ja6e a gidansa ba take gaishesa don dole, idan ta ga yanda yake faram faram da khadijah sai taji abu ya makale mata a makogwaro, a haka daddy ya koma germany bayan sati daya shi kadai ba tare da saleem ba, Kusan kullum sai Iklima ta tsokani khadijah a gidan har da xagi tamkar dai uwarta ke sa ta, Amma ko sau daya khadijah bata taba kulata ba, tun da mumy tace kar ta sake ta kulata, hakan yasa fadanta yawanci da baby take yi, wani lkcn har da dambe, wanda ba haka Anty khadijah ta so ba, ta so ne ace da khadijah iklima ke wannan abun toh da bata samu fuskar su yi fadan gun khadijah ba yasa ta makale ma baby suke fadan, gashi baby ta nakada mata duka hakan bai sa kuma ta daddara, islamiyya mumy ta sa saleem ya kai Iklima, sanin ikliman ba gaida Aliyu take ba har sannan yasa Mumy bata ma sa shi ya kai ta ba, Ranan litinin da asuba mumy ta kira saleem ta basa cash na kudi tace “Gashi anjima idan yara xa su makaranta, ku tafi tare da Iklima kayi mata registration, ita ma tace jss3 take” Saleem yace “Toh Mumy, har da uniforms?” Tace “Eh Abbanku ne ma ya bada kudin” fita yyi dakin bayan ya amshi kudin ya kirga. Mumy ta bude kofar dakin Anty Khadijah don tare suke kwana da ‘ya tata da take ji kamar ta mayar ciki, tun da ta ga Khadijah na kwana dakin baby ta hana iklima shiga dakin, Anty khadijah ta dauke kai ganin yayarta hade da daure fuska, Mumy ta tabe baki tace “Sai ki tashe ta daga baccin ta shirya xa su makaranta tare da su Siyama” daga haka Mumy ta rufe masu dakin. Aliyu na bedroom dinsa yana shiryawa da safen ranan baby ta shigo sanye da Uniform tana turo baki tace “Yayanmu kaga wannan ikliman mai shegen tsokanar mutane mumy tace xata fara school din mu yau kuma same class muke da ita da Iman koh, yaya a schl ma tsokanata xata dinga yi ni bana son ta xo schl dinmu Allah” yana karashe buttoning shirt dinsa yace “Toh ki je ki gaya ma Mumy mana” ta turo baki tace “I told ya Saleem yace xai mare ni, he is always supporting the dirty girl” Aliyu ya tabe baki bai ce komai ba, Baby ta karasa gun sa ta nuna masa takardan hannunta tace “Yaya…. Iman ce tayi solving din math din nan, I told her it’s wrong ta ki ta yarda” karba yyi ya juyo yana kallon book din, ya langwabar da kai yace “Where is she?” Juyawa baby tayi sai ga ta sun dawo tare da Khadijah, khadijah ta tsayema bakin kofa ita ma tana sanye da uniform tace “Yayanmu ina kwana” yace “Lafiya lau, where u sleeping when solving dis?” Ta xaro ido tace “Aa idona biyu” ya mika mata yace “Toh it’s wrong” karasowa tayi ta karba tana kallon baby, tace “but I told her to solve it let’s see kuma taki yi fa, and tare muka yi wannan” Aliyu yace “Don’t worry ku yi submitting haka, learn not to be afraid of failure…” Khadijah tayi murmushi tace “ohk thank you” daga haka ta fita baby ma tace masa thank sannan ta bi bayanta. Tun dawowarsu makaranta iklima ke ta ba uwarta labarin makarantar da ta fara ranan, Anty khadijah dake saurarenta fuskar nan a yamutse tace “Yanxu ajin ku daya da annobar can kenan?” Iklima ta tabe baki tace “Ehh mana, class din mu daya, kuma ko wani tambaya aka yi a class din ita ke bada amsa, Iman ma ake kiranta a class, she is always bragging she knws everything, in the afternoon ya Aliyu ya xo school din ma….” Katse ta Anty khadijah tayi da sauri tace “Wajen wa?” Iklima ta kara tabe baki tace “Water colour naga ya kawo mata da Math set, may be she told him since yesterday, lokacin muna break ma ya xo” Anty khadijah da ta wangale baki tace “Haba….” Iklima tace “Wllh, kuma yyi kamar bai gan ni ba har bin wajen motarsa nayi” kamar xata yi kuka ta kare maganar, Anty khadijah da idonta ya kankance tace “Ita kadai ya kawo wa ko har da baby??” Iklima tace “It seems baby tana da shi, ita kadai naga ya kawo ma” shiru Anty khadijah tayi tana naxari iri iri a ranta, can tayi kwafa hade da murmushi. Baby ce tsaye a class tana kyakyata dariya har da rike ciki, Khadijah dai murmushi kawai take tana kallon sheet dinta na quiz da suka yi ranan over 20 both math and English gaba daya kuma ta cinye, Wata yarinya ta karbe script din baby dake ta kyalkyale dariya taga 15 gare ta, Baby ta sake satan kallon iklima dake can gefe tsaye tayi keeping strong face ta linke script dinta ta boye, baby ta kara rushewa da dariya har da kwanciya, har sanusi ya xo daukansu ranan baby da ta saci kallon iklima sai ta kwashe da dariya, Siyama da ke kusa da iklima ta kalli baby tace “Dariyar me kike ke kuma” Baby tayi keeping innocent face tace “Nothing” a nan ne ta fiddo script dinta a jaka tana murmushi ta mika ma Siyama tace “Quiz da muka yi daxu a class, I got 15 over 20, Iman kuma scored 20/20” Aneesah tace “Iklima fa?” Baby ta danne dariyarta tace “I don’t really knw” Siyama ta kalli Iklima tace “Ke meye score din ki” Iklima ta tsuke fuska tace “16” wani kara baby tayi tana xaro ido tace “Wllh karya take she scored 3 over 20 I saw it with my two naked eyes” Iklima ta cakumota ta kunduma mata xagi tana huci tace “Ke kika ban 3 din, munafuka shegiya” kokuwa suka fara yi cikin motar har sai da Sanusi yyi parking, Siyama ta fito da baby daga cikin motar, sai da Sanusi ya sa baby ta dawo gaba sannan fadan ya lafa, amma sai xage xagen juna suke baby na kiranta olodo har suka isa gida, Iklima ta fice daga cikin mota ta shige gida da gudu ta rushe da kuka tana kwala kiran Uwarta, Da gudu Anty khadijah ta fito tana tambayarta menene da yake Mumy na gun aiki bata dawo ba, cikin kuka Iklima tace “Su baby ne ke ta tsokanata suna kirana olodo tun a school mumy bana son same class with dem, gwara a mayar da ni jss2…” Baby ta shigo parlorn tana turo baki Anty Khadijah tace “Baby me ya hada ki da ‘yar uwarki, uban waye ya shiga tsakanin ku har yake neman raba min kan ku?” Baby tace “Anty ita ce take dambe da ni a mota, just because she scored 3 over 20, ni bani nayi marking din ba da take fada da ni” Anty khadijah bata ce komai ba ta ja Iklima xuwa daki ta kulle kofar tace “3 over 20 iklima garin yaya” iklima ta turo baki tace “Toh the questions where very hard” Anty khadijah ta bude baki tace “Toh ita babyn me ta ci?” Iklima ta tabe baki tace “Wai 15” Anty khadijah tace “kina me iklima, to ita shegiyar yarinyar can fa” Iklima ta kara turo baki gaba tace “She scored everything, mumy kuma na ji suna cewa xa su nuna ma ya Aliyu xai siya masu wani abu” hawaye cike idonta ta kare maganar, Anty khadijah tace “Ba kwa xuwa makarantar ne a can gida!” Iklima tace “Ina xuwa” Anty khadijah ta dungureta tace “Amma kin kunyata ni Wllh, yanxu da wani ido xan dubi yan gidan nan, yar iskar can xata iya cinye duka quiz din ke me kike da baxa ki iya ba” Iklima sai matsar kwalla take, Anty khadijah tayi shiru tana cixan yatsa, can tace “Tafi kije dakinsu ki dauko min script din shegiyar da sauri” da gudu iklima ta fita dakin, ta je dakin baby tayi sa’an ba kowa ta bude jakar Khadijah ta dau takardan quiz dinta ta fita ta kai ma Anty khadijah, yayyage papern Anty khadijah tayi ta bude window ta watsar tace “Tafi kiyi wanka ki je ki karbi abincin ki” cike da murna Iklima ta wuce bayi. Da daddare babu irin neman da Khadijah bata yi ma takardanta ba baby na taya ta xa su kai wa Ya Aliyu, Baby tace “Ni nasan Iklima ce ta sace maki script, she openly showed she is jealous tun a schl,” daga haka ta fice ta tafi ta gaya ma ya Aliyu dake dakinsa, shiru yyi yana kallonta.

  • Noor Al Hayat 18

    Noor Al Hayat 18

    A hankali khadijah dake kallonsa tace “please” ya dago ya kalleta kafin yace “Sai in gan ki a ina in baki abincin?” Shiru ta yi kamar me naxari, can tace “Ohk, ae akwai flowers a kusa da gate din, to ka dinga ajiye min a wajen idan na fito sai in dauka” murmushi yyi yace “Koh?” Ta gyada masa kai, yace “Ohk” ta kara matsowa gaban sa tace “Promise u will do that plss” yace “I will” ta wara idonta ta hade hannayenta tace “Thank you very much, may Allah reward you, byeee” daga haka ta juya da sauri ta bar wajen ta nufi gida ya bi ta da ido, bbu wanda ya bi ta kanta ta ajiye sakon a kan kujera ta fito ta ci gaba da wanke wankenta Happily, sai kusan karfe biyar ta gama ta shigo ciki, Hajiya Maimuna ta hada ta da uban kayan yaranta ta linke su ta xuba a cupboard, sai kusan magrib ta fito ganin kowa na alwala ita ma taje bakin tap tayi alwala ta dawo tayi sllh, tana rakube jikin kujera aka fara kiran kowa ya je kitchen ya karba abinci, ita ma ta tashi sanin Hajiya Maimuna na iya kunduma mata xagi idan taga bata shigo ba, tuwo ne da miyar karkashi aka yi ranan, ta fito bayan an dungura mata nata tana kallon cikin tuwon, xaunawa tayi ta kai hannu cikin miyar dake turiri ta dangwala ta kai baki, ta kasa hadiyewa ta shiga satan kallon mutanen parlorn trying very hard to keep her face normal, kowa hankalinsa na gun kallon Hausa film da ake yi a TV, ita da yake can gida basa kallon Hausa film ko bin ta kan kallon bata yi ba, sulalewa tayi ta fita waje rike da kwanon tuwon ta ajiye nan verenda ta nufi gate da sauri, a hankali ta durkusa gun flowers din bakin gate tana addu’ar Allah yasa ya ajiye mata abincin, ta bude flower din a hankali tana dubawa ai kuwa ta ga leda fari, ta dauka da sauri ta bude taga takeaway ne da goran five alive, ajiye ledan tayi ta doka uban tsallen murna sannan ta dau ledan har tana tuntube ta shiga cikin gida, backyard ta nufa da sauri ta nemi wani lungu ta xauna ta bude abincin taga jollof rice ne da naman kaza da plantains sai sauce a gefe, Cike da murna ta fara cin abincin tana ci tana gyada kai har da lumshe ido, sauri sauri ta cinye abincin ta bude drink din ta sha kusan rabi sauran ta kasa shanyewa, ta mike ta boye goran drink din sannan ta dau takeaway din ta fita gate ta jefar cikin katon abinda ake xuba shara ta dawo ciki tana goge bakinta, sai da ta tsorata ganin tuwon da ta ajiye ta kauda kai da sauri kamar ta ga mugun abu ta daukesa kamar wani shara tana yamutse fuska ta fita waje, almajiri ta samu ta juye ma sannan ta dawo gidan ta tafi gun tap tana wanke kwanon sajidah ta leko da alamar sai lkcn aka lura bata parlorn, yarinyar ta juya ta koma Khadijah ta bi bayan ta da sauri rike da kwanon da ta wanke, Hajiya salaha tace “Daga ina kike?” Ta nuna mata kwanon tace “Naje wanke wa ne” salati ta saki tana tafe hannu tace “Yanxu abincin kika je kika xubar khadijah?” A tsorace tace “Wllh mama ban xubar ba” Hajiya Maimuna tace “Karya kike, kece xa ki ci tuwon nan har ki cinye?” Ta marairaice tace “Amma ban xubar ba wllh” Hajiya salaha tace “Toh ya kika yi da shi?” A hankali tace “Na ba almajiri” cup Hajiya Maimuna ta dauka ta jefeta da shi tace “Allah ya isa” Khadijah tayi kofa da gudu ta fita ganin Hajiya salaha ta mike, can bakin gate ta tafi ta tsaya a tsorace, yau ma dai kamar jiya kawu ne ya shiga da ita parlor, bayan ya duddungureta yyi gorin iya son ransa sannan ya juya kan iyalansa cike da fada yana nanata masu indai suka janyo ma khadijah malaria sisin sa baxai yi ciwon kai ba sai in su xa su kai ta asibiiti, bbu warce ta tanka sa cikinsu, ya gama bambamin sa ya shiga ciki. Washegari sai da kowa ya tafi makaranta khadijah ta fara wanke wanken kwanukan jiya, kamar xata yi kuka take yi don duk sun bubbushe, tayi kusan awa daya bakin tap din ta bar sauran kwanukan ta shiga ciki, Hajiya tace “Kin gama ne munafuka” ta girgixa kai tace “Na kai halve” koranta tayi taje maxa ta gama, khadijah ta fito tana kallon agogo ta ga karfe tara ya wuce har da rabi, cikin sanda ta nufi gate ta bi anguwar da kallo ta ga ba kowa da yake silent anguwa ce, bude flower tayi dai dai wajen jiya taga farin Leda, ta washe hakora ta dauka da sauri ta shiga ciki, backyard ta nufa tana waige waige kamar munafuka, ta samu inda ta xauna jiya ta xauna ta bude ledan ta fiddo takeaway din, fried potato ne na turawa da uban kwai a ciki, ta lumshe ido tana murmushi, ta fito da wani water bottle karami da ke ledan ta bude tana kallon ciki taga shayi ne yaji madara da Milo, ta wara ido tace “Wowwww” har wani rawa hannunta yake ta kai bakinta tana yi a hankali kar ya konata taji bbu xafi sosai, tun da ta kafa baki bata ajiye ba sai da ta ga bayan shayin, ta ajiye bottle din ta rufe tana lullumshe ido ta dau fork din cikin ledan ta soma cin dankali da kwan, da kyar ta gama cinyewa don ta koshi kuma bata son xubar da abincin, ta tashi a hankali tana leke leke ta fita da gudu ta jefar da takeaway din a bola, ta dawo bakin tap ta wanke bottle din ta sa a Leda ta koma jikin flower ta bude ta ajiye sannan ta shigo ciki ta ci gaba da wanke wanken, bayan ta gama ta shiga ciki Hajiya Maimuna ta nuna mata kunu a cup da aka rufe a walakanci da wani bushashen bread a leda tace “Idan kin ga dama gasu can, don bawa baxae biye ta halin ki ba tunda yana da baya” Khadijah ta girgixa kai ba tare da ta sake kallon direction din kunun ba tace “Ni na koshi mama” sakin baki Hajiya Maimuna tayi can tayi murmushin mugunta tana gyada kai tace “Toh maa sha Allah” xaunawa khadijah tayi a favourite position dinta, daga karshe Hajiya Maimuna ta mike ta wuce ciki, kwanciya khadijah tayi don ji tayi cikinta ya mata nauyi nan da nan kuwa bacci ya dauketa. Yau ma dai da rana shinkafa da mai da yaji aka girka, tana gani suka xubo ma baki da suka yi ita ko oho sai ma wankin socks da panties din yara da aka tula mata bakin tap abinda bata taba ba, sai shafa socks din take tana turo baki gashi ta fara jin yunwa da wajajen karfe uku ne, kalle kalle ta fara yi kafin ta mike kamar mara gaskiya ta fita wajen gate, bude gun flower tayi a hankali taga farin leda sabo, ta wara ido ta dauke ledan taga bbu na bottle din da tasha daxu, ta shiga ciki da sauri ta wuce backyard, snack ne a ledan da roban five alive. Nan da nan ta ci da sauri ta sha drink din sannan ta fita ta xubar da ledan a shara taje ta ci gaba da wankin ta. Sai kusan la’asar bakin suka tafi, Hajiya salaha ta fito ganin wankin da Khadijah tayi, kuka ne kawai bata yi ba, amma har kumfa bakinta yake don fada da xage xage ita dai Khadijah na tsaye jikin bango tana kallonta tana wasa da flower din gown din jikinta, sai da Hajiya salaha ta mayar da gaba daya kayan cikin bucket ta xuba omo xata sake wankewa, Allah ya isa kam Khadijah ta sha sa na barnar omon da tayi mata, daga karshe Hajiya Maimuna ta kirata kamar ta ji shawarar da mai kanti ya ba khadijahr ta dungura mata takarda dauke da abubuwan da xata siyo mata ta bata kudin ta je kanti, Khadijah na isa kantin bayan ta basa takarda ta sa ya bata fallen takarda da Biro, yana mika mata ta xauna shi kuma ya ci gaba da hada mata kayan Aiken da aka yi mata a Leda, rubutu tayi kamar haka “Assalam, I am soo happy you fulfilled ur promise, I am no longer hungry anymore, I love the foods, may Allah reward u abundantly, I like you.” Ta tsura ma neat writing dinta mai kyau ido tana murmushi, can ta linke takardar ta mayar ma mai kanti biron sannan ta karbi kayan ta ta wuce da sauri, cikin flowers ta bar takardan yanda xa a gani sannan ta shiga gida, Hajiya Salaha dake ta wanke ta jefa mata kallon tsana tace “Shi yasa fa kayan ki can a kwandon kayan wanki har sun fara tsutsa maga uban da xai wanke maki, ba dai duk kin saye kayan ba” Ita dai bata ce komai ba ta shiga ciki ta kai ma Hajiya Maimuna sakonta. Karfe biyar da rabi yara suka dawo gaba daya, aka xuba ma kowa abinci amma banda ita, ko kallon inda abincin su yake bata yi ba banda kallon da take har kowa ya gama cin abincin ya kai kwanuka waje, Hajiya salaha ta shiga kitchen gun kishiyarta dake girki tace “Maman Hafsa kinsan yarinyar can daxu bata karya ba gashi yanxu ma ko damuwa bata yi tace ina abincin ta ba?” Hajiya Maimuna tace “Wallahi ina lura da ita, ke dai na mu ido, ranan yanke jikinta ta fadi ya kusa xuwa, ni dai baxan roketa ta xo ga abinci ba idan ma ba ta ci ba auki xai ma yaran mu” Hajiya Salaha ta fita tana cewa “Toh ni kinga ina bi ta kanta” Da daddare yau dai macaroni dafaduka aka yi ta manja, Khadijah ta ki xuwa kitchen ta karbi abincin sai kallo take, Tsawa Hajiya Salaha ta mata tace “Toh maxa tashi ki fita ki wanke kwanukan daxu da aka 6ata, ba dai kina xaune kina jiran a kawo maki abinci ba…” Khadijah ta mike ta fita da sauri daga parlorn Hajiya ta bi ta da kallon mamaki don a tunaninta xata shiga kitchen ne, wanke wanken taje ta d’an yi kafin ta fita gate da sauri ta bude flower sai ga wani ledan, tayi murmushi ta dauka ta dawo ciki ta wuce favourite position din da take xama ta bude take away din taga shinkafa ce da miya sai nama kusan yanka biyar ta wara ido cike da jin dadi ta fiddo goron five alive ta ajiye sannan ta fara ci, cikin few minutes ta gama saboda saurin da take ta koshi ba kadan ba don har ta kasa shan drink din gaba daya, ta boye a inda ta saba boyewa sannan taje ta jefar da ledan ta dawo ta ci gaba da wanke wanken tana gyangyadi tsabar koshin da tayi, da kyar ta karasa ta shiga ciki wajen karfe tara tana shiga kuwa isha tayi suna ta kallonta su ji ta ce ina abincinta amma sai ji suka yi tace xata je kwanta daga haka kuma ta tafi tayi kwanciyarta. Haka nan Khadijah ta ci gaba da rayuwa gidan har na kusan wata biyu bbu ranan da ya taba fashin ajiye mata abinci gashi tun haduwar da suka yi a kanti ta bukaci ya dinga ajiye mata abincin basu sake haduwa ba, duk kwana biyu sai ta ajiye masa note din godiya cikin flowers, Bbu abinda ke daure ma Hajiya Maimuna da Hajiya salaha kai irin yanda suka ga Khadijah ke ta kiba tana kyau gashi fa sai ta kai har washegari wani lkcn bata ko bi ta kan abinda suka girka ba, ga uban aikin xa take narka kullum a gidan, ranan dai abun ya ishi Hajiya Maimuna tace “Ni kam yarinyar nan ko dai akwai gun da take xuwa cin abinci ne ba mu sani ba, dubi fa ko bin ta kan abincin gidan nan bata yi ko da an xuba mata sai ta ki ci, gashi lafiya lau sai ma kiba da na ga ta yi kamar” Hajiya Salaha tace “Nima abun na daure min kai kuma kema kinsan bbu inda take xuwa sai gun mai kanti kuma bata dadewa take dawowa gida” Hajiya Maimuna tace “Yanxu dai kawai mu sa ma duk movement dinta ido sosai” Da rana Khadijah na ta xaune parlorn tana jiran su tafi su kwanta taje ta dau abincin ta a flowers, kallon wani Hausa film suke, taga basu da niyyar shiga ciki, ta mike ta dauke few plates dake parlorn duk da tayi wanke wanken safe tace “Mama in je in wanke” Hajiya Salaha tace “Toh sai kin tambaya, ko ba aikin ki bane” fita tayi da sauri don dama abinda take nema kenan, tana ajiye plates din ta fita gate, tuni su Hajiya suka fito suna lekan compound suka ga bbu ita, hakan yasa Hajiya Salaha xata nufi gate Hajiya Maimuna ta rike tace “Jira kamar ga kafafuwanta can a tsaye” ko rufe baki basu yi ba sai gata ta shigo da leda suka yi saurin makalewa da bango, ko lura da su bata yi ba ta wuce inda ta saba xama da sauri, ta bude soyayyen kwai da indomien dake turiri kenan ta ajiye five alive a gefe, sai ga su a kan ta, tsuru tsuru tayi tana kallonsa kamar yanda su ma suka saki baki suna kallon abincin, salati suka saki a tare, Hajiya Maimuna tace “Uban wa ta baki wannan abincin Khadijah” Khadijah da tayi mugun tsorata xata mike ta gudu Hajiya Maimuna ta cafketa tace “Gun ubanwa kika karbo?” Jikinta na rawa tace “Ku yi hakuri” Mari Hajiya Maimuna ta xabga mata tace “Dama shi yasa kika daina bi ta kan girkinmu a gidan nan, karuwanci kika fara ba mu sani ba? To yau sai kin fiddo wanda ke baki abincin nn” cikin kuka tace “Gidansu yana can mama” janta suka yi suka fita ko warce ta yafe dankwalinta a kai ana huci suka ce “Mu je gidan”

    Kuka kawai Khadijah take a tsorace tana biye da su Hajiya Maimuna na janta har suka isa kofar gidan, Cikin rawar murya tace “Nan ne gidan….” Hajiya Maimuna ta xaro ido tace “Nan kike xuwa?” Ta girgixa kai da sauri tace “Mama sau daya na xo, mutumin ne ke kawo min abincin ya ajiye cikin flower, ku yi hakuri don Allah” kwankwasa gate Hajiya salaha ta dinga yi da karfi mai gadi ya bude, tace “Ina masu gidan nan” Mai gadin yace “Daga ina?” Bin gefensa tayi a fusace ta shiga tace “Xaka ji da munafurcin ka, ni din ce xaka ce baka taba gani ba” Hajiya Maimuna ta bi bayan ta tana jaye da Khadijah suka isa parlorn gidan suka bude, Hajiya Maimuna ta rafka sallama kamar tashin duniya, Wata yar budurwar ce ta fara fitowa tana kallonsu ta gaishesu, a takaice suka amsa suka tambayi uwarta, ta juya kenan xata je kiranta sai ga ta ta shigo parlor, har ta karaso kallonsu take da mamaki, Hajiya Maimuna ta hade rai tace “Hajiya Amina mun wuni lafiya?” Hajiya Aminar tace “Alhmdllh, in ji lafiya” Hajiya Salaha tace “Ba lafiya ba, ina d’an ki yake?” Da mamaki tace “Da na kuma?” Cike da jaraba Hajiya Salaha tace “Kwarai, ya fito ya gaya mana menene tsakaninsa da yarinyar nan, ya fito yanxun nan” Hajiya Amina tace “Kar ku min hayaniya a gida don Allah, ku gaya min meye ya faru?” Hajiya Maimuna tace “Hayaniya kam dole, don wannan case din sai ya iya kai mu har kotu, tunda batanci yake yi da ‘yar mu” bude baki Hajiya Amina tayi tana kallonsu, haka ma ‘yar ta… Khadijah dai sai matsar kwalla take jiki na rawa, Dai dai nan kuwa sai ga shi ya fito parlor, tsaye shi ma yyi yana kallonsu da mamaki, Mahaifiyarsa da ranta ya gama baci tace “Sadeeq, what’s between you two” ta fadi haka tana nuna masa khadijah, kafin yace komai Khadijah tayi saurin cewa “Nothing ma, kawai yana kawo min abinci yana ajiyewa cikin flowers ne in dauka in ci…” Buge mata baki Hajiya Maimuna tayi ta kunduma mata xagi tace “Kece sadeeq? Makira yar iska? Ke ta tambaya?” Sadeeq dai na tsaye yana kallon ikon Allah ya kasa cewa komai, mahaifiyarsa tace “Magana nake maka malam” ya juya ya kalleta yace “Mum I don’t think I have time explaining my self to any of this women, ni dai nasan the girl told me about how hungry she was ba’a a bata abinci a gidan, and I volunteered….” Uwarsa ta xaro ido tace “Volunteered what Sadeeq?” Ya d’an hade rai yace “She requested in dinga ajiye mata abinci a flowers din kofar gidansu thats all, sannan tun ranan bamu sake haduwa da ita ba cox dama gun wancen mai kantin muka hadu, sai kuma yanxu da take tsaye a nan, ashe dama taimako na xama laifi, kuma da ba su barta da yunwa ba har xata ce in dinga ajiye mata abinci she’s always hungry? Ba komai kuma yasa nake ajiye mata abincin ba sai don nasan bbu illar da ya kai barin ‘ya mace da yunwa, bana son ta shiga wani hali shi yasa, if not what’s my connection with her da har xan dinga bata 3 daily meals?” Tunda ya fara magana su Hajiya suka saki baki suna kallon Khadijah da ta sunkuyar da kai, Hajiya Maimuna tace “Toh kayi na farko kayi na karshe, dauki 3 daily meals din naka ka kai gidan almajirai ko marayu, kada ka sake xuwa mana kofar gida da abinci, ita kuma yanxu xa mu koma gida mu ji wanda yake barin ta da yunwa da tace she’s always hungry” Hajiya Salaha tace “Sai ma kin fada, kuma wllh Allah ya isa tsakaninmu da ita tunda mu ta ke bi gida gida a anguwar nan tana cewa muna barin ta da yunwa, bbu abinda xai hanani yi mata jina jina yau” Daga haka ta ja ta xasu fita, khadijah ta hade hannunta tana kallon sadeeq cikin rawar murya tace “I am very sorry” Rankwashi Hajiya Salaha ta kai mata da karfi ta ja ta suka fice gidan, Hajiya Amina ta kalli d’anta tace “Daga this very moment na raba ka da abinda kake yi” Hajiya Maimuna tace “Da dai ya fi maku” daga haka ta bi bayan su. Duka da xagi kam khadijah ta sha shi ranan, duk ta fita hayyacinta sai kiran Ummarte take, don Kansu suka kyaleta daga karshe, indomie da kwan kuma suka dauke suka juye a plate suka cinye. Tun daga ranan sadeeq bai sake ajiye mata abinci ba, kafin kwana biyu ta rama duk ta xama wata iri har lkcn ta ki kwantar da hankali ta ci abinci da suke girkawa, sai taji yunwar xae sumar da ita take tura abincin ko yaya shi ma wani lkcn har da amai sai tayi, tafe take kamar iska xai kadeta tsabar weakness dake tartare da ita, ta isa gun mai kanti ta basa takardar da aka aiketa ya karba yana tsokanarta kamar yanda ya saba, ita dai bata ce komai ba unlike before da xata fara masa turanci, kiranta taji anyi ta juya da sauri jin muryar, ta ga Sadeeq tsaye bayan ta, ta yi murmushi tace “Good evening” a hankali yace “How you?” Tace “Fyn” kallonta ya dinga yi ganin yanda ta rame, ta juya ta karbi sakonta tace “Bye” yace “Khadijah” ta juya da sauri tana kallonsa, yace “You are always hungry koh?” Shiru ta yi hawaye ya cika mata ido, yace “I am sorry I cant help it” ta ce “Don’t worry, I appreciate the one you did before…..” Hannu ya sa a aljihu ya Ciro kudi ya kirga dubu biyar ya mika mata yace “Toh gashi ki boye wannan ko biscuits da doughnut sai ki dinga siya kina ci a nan kinji?” Shiru ta yi ya kamo hannunta ya sa mata yana murmushi ya gyada kai yace “Yeah” rike kudin tayi ya sake hannunta yace “See you some other time” ta daga masa hannu hawaye cike idonta tace “Thank you” hanya daban daban suka bi tana isa gida ta boye kudin, tana son fita ta siyo abinda yace da daddare ta kwanta amma tana tsoro, hakan yasa ta sha ruwa kawai ta kwanta cikinta na kugi don wake da taliya aka yi daren ranan. Bayan kwana biyu tana xaune ita kadai tsakar gida tana tankaden uban garin masaran da Hajiya salaha ta hada ta shi, duk kayan jikinta ya koma fari kamar warce ta yini a kusa da injin nikan, ga hawaye da ya bubbushe fuskarta, a kan tankaden nn tun safe Hajiya Salaha ke dukanta da tayi sai tace bai yi ba, hakan yasa take yi a hankli ynxu bayan ta ci kukanta ta koshi, bude gate aka yi ta daga kai ta ga Ummarta, still tayi rike da rariyar, kamar yanda ita ma Umma ta tsaya kallonta ko kiftawa bbu, hawaye ya cika idon khadijah ta mike da gudu ta nufeta ta rungumeta tace “Ummata” sosai Umma ma ta rungumeta duk jikinta yyi sanyi, can ta janyeta jikinta tana kallonta daga sama har kasa, hawaye ne ya cika idonta ta mata alamar ta dauko takalmarta, khadijah ta koma ta dauko takalman da duk sun tsinke ta sa su haka, Umma ta ja ta suka fice daga gidan, Khadijah dake ta bin ta tace “Ummata tafiya xa kiyi da ni?” Hawaye na sakkowa idonta tayi tambayar, Umma ta gyada mata kai kawai don ta kasa cewa komai, suna isa dai dai gidansu Sadeeq khadijah dake murmushin farin ciki tana rike da hannun Umma gam tace “Umma I have a frnd here, can I just go and bid him goodbye, he is more than kind” Umma ta kalleta for d 1st time ta bude baki cikin sanyin murya ganin hawayen dake ta sauka idon khadijar, tace Some other time dear, khadijah ta gyada mata kai har suka wuce kofar gidan, da sauri Umma ke janta har suka isa main road ta tsayar da adai daita, direct sai motor park, ta biya masu kudin mota bayan yan mintuna motarsu ya tashi xuwa garin kano, bacci Khadijah ta dinga yi jikin Umma don tun asuban fari aka tasheta a can gidan, har suka isa kano bacci take yi, Umma ta tasheta, ta bude ido a hankali, suka sauka cikin motar Umma na rike da ita suka fito bakin titi ta dau adai daitan da xae kai su har gidan da take aure. Ba laifi babban tsakar gida ne compound din mai dauke da small building har hudu, ko wani building na da parlor da daki a cikinsa, sai babban kitchen dake tsakar gidan, da kuma bayin wanka biyu da toilet ma biyu, a gefen kitchen kuwa ga rijiya a rufe, gidan da Umma ke aure kenan, tana kuma auren d’an kasuwa ne mai mata biyu, yara ne su kusan biyar ke ta wasa tsakar gidan da yake da yamma ne kuma ranan alhamis ba islamiyya, da wasu yan mata uku dake xaune kan tabarma suna danne dannen waya, umma ta amsa gaisuwar da yara kananan ke mata ba tare da ta sake kallon gun da yan matan suke va ta fiddo key ta bude part dinta, khadijah dai na tsaye sai kallon yaran take kamar yanda su ma ke kallonta, can ta kalli yan matan taga su ma kallonta suke, Umma ta kalli direction din kitchen jin kamshin girki suka yi ido hudu da Shafa kishiyarta dake lekosu ta cikin kitchen din, suna hada ido kuwa tayi saurin dauke kanta, Umma ma ta dauke nata kan, can ta hango uwar gidan mai gidan nata ita ma tana lekota ta windown parlornta ita ma suna hada ido tayi saurin dauke kai, Umma ta bude kofar ta ta ja hannun Khadijah suka shiga ciki ta dage labule ta daura kan kofar kasancewar parlorn ya dau xafi.

  • Noor Al Hayat 10

    Noor Al Hayat 10

    10….

    Hadarin da ta gani garin ya kara mata kwarin gwiwa ta tashi da kyar tana layi kmr warce ta tashi ciwo ta samu taxi bayan ta fita haraban mall din, sai da suka dau hanya kafin ta iya bude baki ta gaya masa inda xa ta, kanta ta daura a kafarta har suka isa, tana jin yana ce mata sun kawo amma ta kasa dagowa, har sai da ya fito da sauri ya bude bayan motar yana cewa “Madam, are you okay” mugun karfin hali tayi ta dago tana dubansa da idanuwanta da suka yi jajur, yace “You look sick…” Da taimakonsa ta fito taxin, bai karbi kudi ba ya ce taje ta sha drugs ta gyada masa kai ta shiga gida tana hade hanya, Ikon Allah ya kai ta bakin kofar flat dinta ta fadi dai dai kofar Khaleel tana dafe da xuciyarta da take jin kamar an caka mata mashi, bugu daya ta ma kofar ta hade kanta da kasa, bude kofar aka yi, Khaleel ya d’an ja baya yana kallonta da mamaki, saurin durkusawa yyi yace “Subhanallah, Are you okay….” Ta dago da kyar hawaye na sakko mata ta nuna masa kirjinta ya rikota da mamaki yace “Me ya same ki” girgixa masa kai ta dinga yi ta kasa cewa komai, tun tana ganin sa dishi dishi a hankali kuma bata kara ganin komai ba. A hankali ta bude idanuwanta da suka mata nauyi tana bin dakin da take da kallo, dai dai nan aka bude kofa wani matashi ya shigo Khaleel na biye da shi a baya, mutumin ya karaso inda take ya duka ya d’an yi murmushi yace “Hello….” Kallonsa kawai take, yace “How are you feeling now?” Tayi shiru, yace “Sannu, Allah ya sauwake, babu inda ke maki ciwo yanxu koh?” A nan ne ta gyada masa kai, ya juya yana kallon Khaleel dake rungume da hannunsa yana tsaye bakin kofar, likitan yyi murmushi yace “Quack MD do you mind coming over” d’an murmushi Khaleel yyi ya karaso kamar bai son tafiyar ya isa kusa da ita idonsa a kanta a hankali yace “ina ke maki ciwo yanxu?” Shi ma dai bata ce masa komai ba, likitan dake kusa da shi yace “Xa ki ci abu yanxu, sai yyi maki allura ya baki magani kin ji” kallonsa nayi ban dai ce komai ba, ya kara min fatan samun lfya sannan ya nufi kofa yace “Dr I will take my leave…..” bin bayansa Khaleel yyi suka fita waje, da damuwa Dr Ahmad yace “But… Tayi k’ank’anta da wannan matsalar, naga kamar she is in her early 20’s….” Khaleel ya sauke ajiyar xuciya yace “Probably it’s an inheritance….” Ahmad yyi dariya yace “Kai kuma ina mamakin wani irin Dr ne kai wani lkcn wllh….” Dakatar da shi Khaleel yyi yace “No you ought to have known me for long, I don’t treat people that are close to me, ban iya bane…” Dr Ahmad yace “Close to you? Yanxu kana nufin yarinyar nan is close to you? A ina ka santa” Khaleel yace “Noo ba haka nake nufi ba malam” Ahmad yace “Seriously you need to get rid of that behavior Dr, Allah ya bata lfya, ka sama mata abinda xata ci yanxu sai ka mata alluran ko shi ma baxa ka iya ba?” Khaleel ya hararesa yace “Wa ya sani….” dariya Ahmad yyi yace “Toh shknn ni dai bari inje in d’an yi karatu kai kam nasan tun ba yau ba ka gama, abun ka da manya” Khaleel ya shafa kai yace “Xan dai yi, tnx for ur care frnd” daga haka suka yi sallama Khaleel ya koma ciki, a hankali ya tura kofar bedroom din nasa, har lkcn tana xaune ta dago kai tana kallonsa, yace “What will you eat Khadija?” Bata ce komai ba, ya d’an yi jim yana kallonta, juyawa yyi ya fita, ba a dau lkci ba kuma ya dawo rike da cup din shayi, da kyar ta yarda tasa hannu ta karba shayin da yake mika mata ganin yanda ya kafe ta da ido, ta dinga sha kamar magani don bbu wani xafi, xaunawa yyi gefen gadon, bayan wani lkci ta mika masa sauran shayin hawaye cike idonta, ya tsura mata manyan idonsa, murya can kasa yace “Meye matsalarki Khadija, tell me what ur problem is” girgixa masa kai kawai tayi, ya mike ya fita da shayin ya dawo, allurorin ya shiga hadawa har ya gama sannan ya dawo gefenta yace “Let me inject you sai ki sha magani you will be relieved soon in sha Allah” ganin jiranta yake ta d’aga rigar a hankali ta kwanta yyi mata sannan ya dauko mata magungunan da goran ruwa ya ballar mata su ya mika mata ta karba ta sha, tashi ta shiga kokarin yi tace “Ina son xan yi sllh” ya nuna mata bathroom, ta kusa minti daya bata tashi ba bata ce komai ba, can ta mike ta shiga ta dauro alwala ta fito, Fita yyi xuwa apartment dinta don dauko mata Hijab, a hankali ya tura kofar bedroom, idonsa ya fara sauka kan enlargements dake dakin na hotuna, a hankali ya karasa dakin yana kallon cute twins dake hoton da ita kanta, sun rungumeta gaba daya tana murmushi, ya sake mayar da dubansa kan daya enlargement din da suka manna mata kiss gaba daya, dauke idonsa yyi ya dau Hijab da ya gani linke kan gadon ya fita dakin, kan gadonsa ya ajiye mata Hijab din sannan ya fita. Ta jima xaune kan darduman bayan ta idar da sallahn magrib da isha, ido ta kafe ma wani hotonsa dake gaban mirror yana sanye da farin labcoat da stethoscope rataye a wuyarsa, a hankali ta sauke idonta daga kallon hoton, can tayi wani murmushin ta mike da kyar tana dukkan kokarin ganin bata yrda hawayen dake makale idonta ya xubo ba, ta linke masa lallausan pray mat dinsa ta ajiye sannan ta dau dankwalinta dake kan gadon ta yafa ta nufi kofa kamar mai counting steps dinta ta fito parlor, xaune ta gansa kan kujeran parlorn idonsa a kan wayarsa dake hannunsa yana operating, ya daga kai ganinta yace “You want something?” Girgixa masa kai tayi tace “No, am going to my apartment, thanks for ur care” daga haka ta nufi kofa yace “But….” Juyowa tayi tana kallonsa yace “Are you sure you will be okay all alone” tace “Yea sure” karasawa yyi kusa da ita ya mika mata makullin hannunsa ta karba ta bude kofa ta fita ta rufe masa. Bedroom dinta ta wuce direct ta fada kan gado, sae a sannan wani kuka ya xo mata, kukan da ta kasa yi tun daxu, Allah ya sani ta samu relief sosai kukan da tayi domin kuwa taji saukin abinda xuciyarta ke mata, har lkcn ta kasa gaskata wanda ta gani, why all of a sudden. Bata wani rintsa ba daren ranan don da baccin ya dauketa xata farka a firgice, daga karshe ma hakura tayi da baccin ta dauro alwala ta yi ta sllh sae dab da asuba wani bacci me nauyi yyi awon gaba da ita.

    A hankali Aliyu ya bude idanuwansa jin kwankwasa kofa da ake ta yi, ya tashi xaune yana kallon kofar yace “Who’s there?” Muryar small mum dinsa yaji tana cewa “Are you okay Aliyu? Baka fito sllh yau ba” a hankali yace “Nayi a nan Anty… Was having a slight headache ne” tace “Toh Allah ya sauwake, ka fito kayi break sae ka sha magani” daga haka tayi wucewar ta, mikewa yyi yana dafe kansa da yayi masa nauyi ya nufi window ya tsaya, lkci daya ya dawo ya xauna gefen gadon ya rike kan yace “Noo, nasan ba ita bace, ba Iman bace, it’s her look alike…. But….” mikewa yyi da sauri cike da damuwa da confusion yace “Why did she run then, me yasa ta gudu?? Does it mean ita ce? Ya Allah….” Jingina yyi da bango ya runtse ido, ya kusa minti ashirin a haka aka sake bubbuga kofa, ya bude ido a hankali cikin sanyin murya yace “Who’s there?” Muryar Maryam cousin sis dinsa yaji tace “Yaya ni ce” yace “Ya aka yi” bata ce komai ba, hakan yasa ya karasa ya bude kofar tace “How was ur nyt?” Ya dauke kai yace “T’was good” Tace “Mumy wai ka fito ka yi breakfast” yace “Ohk” daga haka ya rufe kofar ya koma gefen gado ya xauna, kallon agogo yayi ganin takwas ya tashi ya shiga bathroom, wanka yyi ya fito, ya fi minti sha biyar kwance jin kamar xaxxabi xai rufesa, can yyi ta maxa ya mike ya shirya ya dau makullin motarsa ya fice gidan ba tare da ya bari Small mum dinsa taga fitarsa ba. Mikewa xaune Khadijah tayi da sauri daga baccin da take ta dalilin bell da aka danna, ta tashi a hankali jin jiri na dibarta, ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta wanke baki sannan ta fito ta dau hijab ta sa ta fito parlor ta bude kofar, har lkcn yana tsaye gun, yana kallonta a hankali yace “Bacci kike na tashe ki?” Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace “Na tashi” yace “How are you feeling now?” Tace “Alhmdllh, ina kwana” yace “Lafiya lau” jin yyi shiru ta dago kai suka hada ido, saurin sauke idonta tayi, yace “You cried!” Ta girgixa masa kai kawai, yace “Noo you cried malama” lkci daya hawaye ya kawo idonta ta kasa ce masa komai, shiru yyi bai sake cewa komai ba, bayan wani lkci yace “Shiga ciki” ba musu ta juya ta koma ciki ya rufe kofar, daki ta koma ta kife kai da pillow wasu hawayen na xubo mata, duk taji ta tsani xaman UK din, ta tsani karatun, dago kanta tayi da sauri ta dalilin *SUDAIS* da ya fado mata, bata san lkcn da tayi murmushi ba kawai taji kamar an yaye mata bakin cikinta, tayi tagumi a sanyaye…. Ta fi minti sha biyar a haka, ji tayi duk duniya bbu wanda ta tsana… tsanar da bata da iyaka irin wanda tayi tozali da jiya a mall, taji an bude kofa ta dago da sauri, jin shiru ta mike ta fito parlor tana goge idonta, xaune ta gansa kan kujera yana hada allura, ya dago ya kalleta, lkci daya ya hade rai , bata yrda sun sake hada ido ba, ya ajiye alluran hannunsa ya mike yace “Are you alright? under this condition stil xaki dinga xama daki kina kuka haka, dama kuka na magani? idan ma damuwa gare ki baxa ki sa Allah ran ki ba” bata iya tace komai ba bata kuma yrda ta dago ba, ya koma ya xauna, bayan kusan minti uku ya nuna mata cup din shayi da bread dake ajiye kan table yace “There” ta karaso ta dau shayin yace “With d bread” girgixa masa kai tayi ta fara shan shayin, murya can kasa yace “Look…” ta dago idanuwanta ta kallesa ya nuna mata kujera, a hankali ta karasa ta xauna, ajiye cup din tayi bayan ta sha shayin, yace “ur injection” tashi tayi ta wuce daki ta daura xani cikin Hijab din jikinta ta fito, nan parlorn yayi mata alluran ya bata maganinta, yace “You go get some rest now, ki yi bacci da yawa kin ji” yyi kasa da murya yace “And please kar sake kuka ur condition isn’t encouraging, always remember Allah xaki samu natsuwa sosai…” Bata ce komai ba ta mike ta wuce daki ya bi ta da ido, tashi yyi ya dau cup din ya fita. Sai bayan azahar ta farka daga baccin da tayi, sosai taji xuciyarta ya mata saukin xafin da yake mata don ta samu bacci da yawa, kuma taji ddin drugs din, yunwa taji na dawainiya da ita, ta tashi ta shiga bathroom ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, shafe shafe tayi ta dau gown mara nauyi da tsayi ta sa ta shimfida darduma ta saka hijab har kasa ta tada sllh, tana idarwa ta cire Hijab din ta linke sannan ta fito parlor don dafa ko da indomie ne ta ci, still tayi ta juya baya da sauri a parlorn ganinsa da tayi dai dai center table ya ajiye ledan hannunsa da alamar shigowarsa kenan, Bata jira ta ji abinda xai ce ba ta nufi daki da sauri ta rufe kofa, xama tayi kan gado ta hade kai da gwiwa duk taji kunya ya kamata, ta fi minti goma a haka, can dai ta mike a hankali ta saka Hijab din da tayi slh ta fito parlorn, bbu kowa ciki ta karasa gun ledan ta bude taga abinci ne da drink, kadan ta ci ta fara gyaran gidan, dab da la’asar aka danna bell, ta kasa xuwa ta bude, can dai taa isa gun kofar tace “Who’s there?” Yace “Koh” bude kofar tayi ta juya ta dawo parlorn ya shigo ya tsaya daga bakin kofa yace “Sorry….” Da sauri ta katse sa tace “Ohh bakomai” yace “Bakomai me?? ai baki jira kin ji abinda xan ce ba malama” ta d’an kallesa, sai taji kunya, ya buda ido sosai yace “Dama cewa xan yi, sorry… me yasa kika gudu daxu?” Bata ko kallesa ba balle tace komai, yyi murmushi yace “Toh kin ci abincin” kai kawai ta gyada, yace “How you feeling now” tace “Naji sauki” duk wannan abun bata yrda ta juyo ba sai gyare gyare take, yace “Alluran ki…” Da sauri tace “No naji sauki, xan sha maganin” shiru yyi na kusan thirty seconds, yace “Malama” sai a sannan ta juyo suka hada ido, jallabiya ce Milk colour jikinsa da ya fiddo da ainahin kamanninsa na larabawa, shi ya fara dauke kansa sai kuma yace “ohk… Ki sha maganin” daga haka ya fita ta bi sa da ido har ya rufe kofar.

    *Haske writers association*💡

    ✨ *Noor-Al-Hayat*✨

  • Noor Al Hayat 19

    Noor Al Hayat 19

    NOOR-AL-HAYAT*

    Khadijah ta xauna kan kujera tana kalle kallen parlorn tace “Umma nan ne gidan ku koh?” Umma ta bude fridge xata dauko mata ruwa tace “Ehh” Karban ruwan tayi tace “Umma yunwa nake ji ban ci komai ba” Umma tace “Toh me xa ki ci yanxu?” Murmushi tayi da ya bayyana fararen hakoranta ta langwabar da kai tace “Indomie Ummata” Umma ma ta yi murmushin ta juya ta fita, Khadijah ta dinga bin madaidaicin parlon da kallo kai kana ganinta kasan she is just happy, muryar Umma taji tana kiranta daga waje ta fita da sauri ta sa takalminta tace “Gani Umma” Umma ta mika mata ruwa a buta tace “Gashi ki fara yin alwala kiyi sallah” tace “Toh” sannan ta durkusa tana alwala tana yi tana kallon yaran dake ta kallonta har da matar dake girki a kitchen, Umma ta shiga kitchen din ta dauko indomie daya ta fito ta kai parlorn ta sannan ta dawo rike da naira dari tana mika ma wani yaro da baxai wuce shekara biyar ba tace “Mudassir je kanti ka amso min kwai biyu” yaron ya karba ya wuce waje da gudu, Karamin tukunya Umma ta daura kan electric madaidaici dake parlorn ta bayan ta shimfida ma Khadijah darduma, khadijah na idar da sallahn Umma tace “Kin fara xuwa school a can gidan” girgixa kai tayi tace “A’a, kin san me Umma ta” Umma tace “Bari ki ci abinci” soya mata kwan da yaron ya kawo Umma tayi sannan ta ajiye mata a gabanta da ruwa a cup ta mayar da wani tukunyar ta sa mata ruwan wanka, Umma tayi tagumi tana kallon yanda take cin abincin, kana ganinta kasan yunwa kawai take ji, kafin ta gama Umma ta juye mata ruwa ta kai bayi da sabulu, ita ta rakata bayin sannan ta koma parlorn, khadijah na gama wankan ta fito daure da xanin da Umma ta bata, Shafah dake girki daga cikin kitchen ta bi ta da wani kallo hakan yasa tace “Ina yini” dauke kai tayi kamar bata ji ba, khadijah ta wuce cikin parlorn Umma tace “Wannan matar dake girki na gaisheta bata amsa ba” Umma tace “Kar ki sake gaisheta” daga haka ta cire hular kanta bayan ta kawo mata man shafawa, sakin baki tayi tana kallon gashin don tun kalaba shidda da ta yi mata kafin kawu ya tafi da ita kasancewar gashinta na da tsayin bala’i kuma bata son ana taba shi, Umma bata dai ce komai ba, ta dau gyalenta tace “Ban ce ki fito ba ki jira ni har in dawo” khadijah tace “Toh” daga haka Umma ta fita, bayan kusan minti ashirin ta dawo rike da Leda ta sake labulen parlorn ta bude ledan ta fiddo wasu dinkakkun riga da skirt kana ganinsu dai kasan taje ta karbo su ne tace “Tashi ki sa, gobe xan je kasuwa in siyo maki kaya kinji” khadijah ta sa kayan tace “Umma in kunna TV?” Umma tace “Ban ce ba” kwanciya tayi kan kujera bbu bata lkci bacci ya dauketa, Umma ta xuba ma jikinta ido ganin shattin duka, tagumi tayi tana kallonta tana tausaya ma marainiyar. Khadijah na tsugunne tana alwala tsakar gida da magrib bayan Umma ta tasheta tayi sllh taji an fixge butar daga hannunta ta daga kai tana kallon yarinyar da baxata wuce ta ba, Yarinyar ta murguda baki ta tafi ta kara ruwan ta fara alwala, mikewa khadijah tayi tace “Are you okay?” Yarinyar ta balla mata harara tace “Ki fadi wanda xan ji mana” khadijah bata sake cewa komai ba har yarinyar ta gama sannan ta wuce da butar parlornsu, khadijah ta xaro ido sai kuma ta juya ra wuce gun Umma dake parlor ta tsaya bakin kofa a hankali tace “Umma wata yarinya ta karbe butan ta tafi da shi” Umma ta fito tace “Wace yarinya?” Nuna mata parlorn da yarinyar ta shiga tayi, Umma ta kama hannun ta suka je har kofar parlorn ta bude labule tace “Wacece a ciki” Khadijah ta dinga bin yara kusan biyar dake parlorn da kallo sannan ta nuna mata yarinyar, Umma tace “Rahmah dalilin me kika karbe buta tana alwala?” Yarinyar da ta tsuke baki tace “Toh Anty namu ne ai” Umma tace “Kar ki sake, idan ko ba haka ba sai na bata maki rai” daga haka ta ja hannun Khadijah suka bar wajen ba tare da ta bi ta kan Uwarsu Hasana dake xaune parlorn ba, Umma ta dauko buta parlorn ta ta bata, Wata yarinyar ce ta shigo parlorn da abinci a er warmer ta ajiye ta juya ta fita, Umma ta daga kan khadijah dake kafarta a kwance tana bata labarin abubuwan da aka dinga yi mata gidan Kawu sannan ta mike ta jawo warmer din, shinkafa ce da miya sai nama biyu da salad a gefe, iya cin ta ne abincin, ta daura dankwali ta fita xuwa kitchen din ta dau wani plate ta bude tukunkya xata debi abinci sai ga Shafah da sauri tace “Amma dai Amina kinsan ba ke ce da kitchen ba, don haka baki da hurumin shigar min kitchen” Umma ta kalleta tace “Ae kin gan ni da bakuwa kika yarfo min er shinkafa a cooler kamar mayunwaci, don haka ke ma baki da hurumin hana ni debar mata abinci” Shafah tace “Bakuwa? Kin gaya min xaki yi Bakuwa in sa girki da ita ne, to wllh kin yi kadan ki kara diban wani abincin don na almajirai ne” Umma ta Debi shinkafar kusan cikin plate ta xuba miya kai da nama biyu tana kallonta tace “In ji duka” daga haka ta fice daga kitchen din Shafah tace “Ai kuwa ni da ke shege ka fasa Amina, mu xuba” tsaye Umma ta ga Hasana bakin nata parlorn tana lekosu tana ganinta ta shige ciki da sauri Umma tayi tsaki ta shiga ciki ta ba Khadijah abincin hannunta. Da yake khadijah tayi baccin rana har karfe goma idonta biyu tana ta ba Umma da tayi tagumi tana saurarenta labarai iri iri, Yar Shafa ta farko fadila ta bude kofa tace “Abba yana kiran ki” daga haka ta juya ta bar gun, mikewa Umma tayi ta fita tare da Khadijah tana rike da hannunta suka tafi turakar mai gidan, ba wani babba bane mai gidan don baxai wuce 48 ba, Shafah na xaune kan kujera da Hasana a gefenta, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah k’asa ta xauna ita na, Gaishe da shi tayi, khadijah na kallonsa tace “Good evening Sir” idonsa a kanta yace “How are you” tace “I am fine” Shafah da Hasana aka kyabe baki, mai gidan da suke kira da Abban Fadila yace “Wacece wannan Amina?” Umma tace “Kayi hakuri na so kiran ka tun kafin in iso kano daxu sai da bani da charge, duk da mun yi da kai gobe xan dawo kawai kuma na fasa, wannan ‘er marigayin tsohon mijina ce Khadijah, na taho da ita ba tare da ixinin ka ba, kayi hakuri ban ji dadin yanayin da na same ta bane shi yasa na daukota bbu shawara da kai” shiru yyi bai ce komai ba, can ya jinjina kai yace “Toh Allah ya kyauta” Su shafa aka kwalalo ido ana kallon khadijah jin wai er kishiyarta ce da ta rasu, Abban fadila yace “Dalilin ki na shiga kitchen ba ke ce da girki ba daxu nake son ji? Shi yasa ma na aika a kira ki” Umma tace “Ehh toh, sun ganni da yarinya mun dawo Abban fadila, sai da aka tashi xubo min abinci da magrib sai aka xubo dai dai wanda ni xan ci a yar cooler” yace “Shine aka ce ko shiga ki diba? me yasa baxa ki nemi izini gun mai girki ba ko kuma kice ta k’ara maki kina da bakuwa, ke ce kadai me karya min doka a gidana fa Amina” Umma tace “Watana kusan uku gidan nan yaushe da yaushe na karya maka doka Alhaji?” Hasana sai wani blushing ake Shafa na taya ta, Abban fadila yace “Toh tashi ki je” mikewa tayi ta daga khadijah da su Hasana aka bi da harara ta fice parlorn ta koma nata, daki ta nuna ma khadijah ta tafi ta hau saman gado ta kwanta, khadijah tace “Toh Ummata” sannan ta shiga dakin ta kwanta hade da lumshe ido don har ta mance Rabon da ta hau gado har tayi bacci a kai. Washegari da asuba Umma ta tada Khadijah taje tayi sallah bayan ita ta idar, khadijah ta fita tsakar gidan rike da buta tana mitsika ido, yara ne kusan biyar ko wanne na alwala tana kokarin shiga bayi tayi fitsari taji an fixgota ta juyo da sauri a tsorace, yarinyar da ta kawo ma umma abinci jiya ce, tana kallo yarinyar ta shiga bayin, ta ja gefe a hankali ta tsaya tana jiranta, bata gaya ma Umma abinda ta sake yi mata ba, bayan ta idar da sallah ta koma daki ta kwanta ta ci gaba da baccinta. Gari na fara wayewa Umma ta kuma tashinta daga baccin ta kai mata ruwan xafi bayi da sabulu da soso, ba a dau lkci ba khadijah ta dawo tana wasa da yatsunta a hankali tace “Umma wata yarinya ta fitar min da ruwan ta sa nata ta rufe bathroom din” fita umma tayi ta tafi kofar bayin da sauri tana kallon xanin waye kafin tayi kwafa ta nuna ma Khadijah kujera tace “Xauna nan ki kyaleta kawai, idan ta fito ki shiga” khadijah ta xauna tace “Toh” umma ta koma ta ci gaba da sharanta, yarinyar na fitowa khadijah ta mike ta shiga da ruwan da kyar ta juyo xata dau sponge case wata ta sake fitar da ruwan nata ta hankadota waje ta shiga ta rufe kofa, tsaye khadijah tayi baki bude tana kallon bayin, dai dai fitowar Umma da abun kwashe shara da tsintsiya, karasawa tayi da sauri ta tura kofar ta janyo ruwan waje ta fiddo sabulun yarinyar sannan ta dau na Khadijah ta saka tana kallonta tace “Xo ki shiga” yarinyar ta fashe da ihu tana buga kafa, khadijah dake kallonta baki bude a hankali tace “Why are they behaving like this” Umma ta shigar da ita bayin tace “Maxa ki fara wanka” Hasana ce ta fito da sauri jin ihu da kukan yarta, tana kallonta a gigice tace “Walida ya aka yi, me ya faru” cikin kuka walidar tace “Xan shiga inyi wanka shine Anti ta fiddo min ruwana ta fito da ni ta saka yarinyar da ta kawo cikin bayin” Hasana da tayi mitsi mitsi da ido tace “Toh Allah ya isan ki, kuma mu xuba da su a gidan nan xan ga ko agolarta xata samu gun xama, ita ma da take a dosane ta ji da kanta mana, tsabar munafurci da neman kugun xama taje ta jajibo yar kishiyar da kilan ma ita ta kasheta ta kashe ubanta, shege ya fasa mu da ita a gidan nan” Umma bata ko kalleta ba ta shiga share kofar parlorn ta, Shafa ta fito tace “Ya aka yi ke kuma da sassafe, ke da wa?” A fusace Hasana tace “Ki rabu da yar kaxa kaza, wai Walida ce xata shiga wanka shine ta fiddo mata da ruwan ta ta saka na shegiyar da ta kawo mana mai kama da aljanu” Shafah ta rike ha6a tace “Ikon Allah Walida da xata makaranta? Ita kuma agolar da take gida, Mutum dai bashi da aiki sai neman fitina, banda jakanci ma ina aka taba dauko agola ace xa a takura ma masu gida dominta” Hasana tace “Ke fa kika san jakanta, amma ni nasan maganinsu wllh, kuma xa mu sa kafar wando guda da su” daga haka ta kalli yar ta tace “In ta fito ki kwara ruwa bayin ka fin ki shiga, Allah dai ya tsine duk mai son takura ku gidan ubanku ehe” daki ta shiga tana ci gaba da kumfar baki, Shafa ta bi bayan ta tana cewa “Amin dai, Allah kuma ya kawo mana karshen bala’in nan, muna xaman xamanmu dai” Khadijah bata fito ba duk da ta gama wankan, sai leken tsakar gidan ta kofar bayin take taga ko sun tafi, ganin Walida ce kadai xaune tsakar gida ta fito tana gyara daurin da tayi ma Xanin jikinta ta ta nufi dakin Umma da sauri, taji Walida tace “Shegiya kawai” kallonta khadijah tayi tace “Back to sender” sannan tayi saurin shigewa dakin ummanta. Kafin karfe bakwai da rabi duk yaran gidan an shirya wucewa makaranta, jin muryar Abban fadila a waje, Umma ta kalli khadijah tace “Go outside and greet him. Come back immediately after that” khadijah ta fita waje ta gansa tsaye ya shirya alamar xai fita kasuwa yana sauraren yaransa mata biyu da suke requesting kudin wani littafi da xa su siya a boko ga iyayensu tsaye bakin kofa, Khadijah ta karasa kusa da shi ta durkusa a hankali tace “Good morning sir” ya kalleta yace “Morning yar turawa, how was ur nyt?” Ta washe hakora tace “It was splendid” yace “Good, ina mamar taki?” Ta kalli kofa tace “Tana ciki” yace “Kira min ita” Shafa da Hasana da lkci daya mood dinsu ya canxa suka kalli juna, juyawa khadijah tayi taje kiran Umma suka fito a tare, Yace “Naga baki shigo gaisheni ba” Umma tace “Bayan nayi sallah I just slept off” yace “Ohk, anjima sai ki je ki mata registern islamiyya ko xuwa next week sai a samu boko a sata” Umma tace “Toh nagode, Allah ya kai mu” Naira Dari ya Ciro ya mika ma khadijah yace “Gashi ki siya biscuit” xaro ido tayi ta kalli Umma, Umma tace “Amsa” ta karba da hannu biyu tana murmushi tace “Nagode uncle” daga haka Umma ta ja ta suka shiga ciki ba tare da ta yarda ta kalli inda kishiyoyinta dake cika suna batsewa suke ba, Shafa tace “Toh Abban Fadila kudin kitso da na tambaye ka tun jiya fa?” Hasana tace “Ni tun shekaranjiya nake ta bi ya sa min kati amma kinga wani gwaninta a nan” Tuni ya isa kofa bayan ya sallami yaransa mata dake turo baki kudin bai ishesu ba, sai da ya fita gidan, Hasana tace “Toh wllh abinda baxai yiwu ba kenan, ya gama ji da nasa yaran mana, har xa a kara daura masa nauyi bayan wanda ke kansa, ko ita yarinyar bata da dangin uba ko uwa ne sai karere??” Shafah tace “Ke fa kika San karere, ita nan gwaninta take a idon duniya ko, toh kuwa xata sha kunya in har bata mayar da yarinyar nan gun dangin ubanta ba, sai yarinyar nan ta ja mata masifa da bala’i sai kuma ta dauko mata abun kunya muna nan dake, sai dai idan ba ni ce nan Shafa’atu yar gidan Sanusi jikar Yakubu na bude baki na yi magana ba” Hasana tayi shewa tace “In sha Allahu kuwa” Umma dake ta jin su ta girgixa kai tana murmushi a ranta tana masu addu’ar samun sauki, sai bayan da duk suka gaji suka shiga ciki ta dauko kibiya da comb xata tsefe ma khadijah gashinta, Tuni khadijah ta fara matsar kwalla tun kan ta kama kan din right from Beginning idan ana son tashin hankali toh a taba gashinta, sosai ta ba Umma wahala ta dinga rusa kuka tana ihu, har dai aka gama tsefewa ta bata Hijab ta sa suka fito don xuwa saloon a wanke mata gashin, da ido su Hasana suka bi su har suka fita.

    Sai kusan azahar suka dawo gida, Idon khadijah ya kumbura don kuka, Hasana na xaune tsakar gida tana jajjagen tafasasshen nama da alama dai dambunsa xata yi, Shafah kuma na daga xaune bakin kofa suna ganin shigowarsu suka yi shiru daga xancen da suke ko wacce ta hade rai, Umma ta bude kofar ta ta ja khadijah suka shiga ciki, xaunawa khadijah tayi kan kujera Umma na harararta tace “Duk kika tsefe kan nan ke kadai xaki saloon din baxan iya wahala ba, dubi idanuwanki kamar warce aka yi ma duka, ke ba yarinya ba ki dinga ma mutane ihun kitso” Khadijah ta kwanta kan kujera bata ce komai ba, Umma ta fita ta shiga kitchen ta dau indomie biyu ta fito, Hasana ce tace “Gaskiya Abban fadila ya dawo ya kasa ma kowa indomie ya ajiye a dakinsa tun jiya ake ta shiga ana daukar indomie abinda yaran gidan ma sai su yi sati basu ci ba, wnn ai mugunta ce” Umma tayi yar dariya bata ce komai ba ta shiga ciki, dama da kwai hudu ta dawo gidan, don haka ta girka indomien a daki ta dafa kwan ta tada khadijah da ta fara bacci ta bata nata sannan ta fita yin alwala, Da daddare yau ma kamar jiya a karamar cooler shafah ta aiko ma Umma abinci, Tea ta hada da yake tana da kayan shayin a daki ta fita da kanta ta siyo bread ta ba khadijah ta ci ba tare da ta bi kan yan gidan ba. A can katsina kuwa neman duniya kawu da matansa sun ma khadijah amma bbu ita babu labarinta, gidan da suka fara xuwa kuwa gidansu sadeeq ne, nan mahaifiyarsa ta nuna masu the other side of her don har sai da suka tsorata kuma tace kada warce ta sake shigo mata gida, har station kawu yaje da gidan radio, bai taba kawo wa cewa Umma ta san gidansa ba balle ta xo ta dauke khadijah, Duk da ba wai abun ya wani dame su Hajiya salaha da Hajiya maimuna ba amma ganin yanda mai gidan nasu ya dage yana nemanta yasa su ma suka xage, har shawara Hajiya salaha ta bada su kai karar Hajiya Amina da d’anta, kawu ya gwaleta cike da masifa yace “Kinsan waye uban yaron?” Hajiya Maimuna tace “Alkali” Kawu yace “Shine xata dinga magana kamar mahaukaciya?” Ita dai Hajiya Salaha bata ce komai ba. Washegari da safe Umma ta fita tare da Khadijah don sama mata islamiyyan da xata fara xuwa, bata yrda ta kai ta wanda yan gidan ke xuwa ba ta kai ta wani dake gaba da shi sosai, bayan ta biya komai ta wuce kasuwa tare da ita don yankar mata uniform daga can tayi mata siyayya kananun kaya. Da yammacin ranan Umma ta amshi girki, tuwon shinkafa da miyar vegetable take girkawa, Khadijah na xaune kan tabarma bakin kofar Umma tana cin gyadar da Umma ta siya mata a hanyarsu ta dawowa, da ta bare sai ta jefa ma wani kadangare dake tsakar gidan yana yawo bawon gyadar, tsawa taji an mata ta waiga da sauri Hasana da fitowarta kenan tace “maxa tashi ki tsince su don baki da bawa mai shara a gidan nan” Umma kallo waje tayi daga kitchen din bata dai ce komai ba ta ci gaba da girkinta, mikewa khadijah tayi ta isa gun da ta ke ta jefa bawon ta shiga tsince su tana xubasu a shara har ta gama, Hasana ta nuna mata wasu bola dake kusa da kofar Shafah wai taje ta tsince, Umma ta fito tace “Wannan kuma ne baki isa ba” kujerar da ke kusa da kofar kitchen ta nuna ma khadijah tace “Sit here” khadijah ta karasa da sauri ta xauna, Hasana ta rike ha6a tana kallon Umma bata dai ce komai ba. Umma bata bar khadijah ba sai da ta tabbatar ta yi bacci sannan ta tafi bangaren Abban Fadila, bata yi mamakin ganin kishiyoyinta ba a xaune parlorn, da kuma alamar yana shigowa suka bi sa don bai jima da dawowa ba, har Umma ta ajiye tray din abincin hannunta kallonta yake, ta xauna ta gaishesa, bai amsa ba yace “Dama kin taho da yarinyar nan ne don ki ci xarafin mutane Amina?” Umma ta kallonsa tace “Ban gane ba” yace “Toh daga yau kar ki sake nuna iko a kan ta Idan ba haka ba ki mayar da ita dangin ubanta, banda janyo yaro ya raina babba don me Hasana zata sa ta aiki ki hanata, akan me? Meye amfanin xamanta gidan idan baxa a ci moriyarta ba!” Umma dake saurarensa tayi murmushi tace “Tun da na shigo gidan nan cikin yaransu akwai warce na taba sa aiki ta min? Babu…. domin kuwa duk sun hanasu amma na taba kai maka kara? Ni wllh matan ka basu isheni kishi ba Alhaji, banda kaddara ba lallai su gan ni cikinsu ba balle su sa ni gaba, ina ce ni ka fara sani ma kafin su? Wllh basa gabana balle inyi kishi da su, marainiya ce dai na daukota sae dai bakin ciki ya kashe su tunda ba a kansu xata xauna ba” Tana kai wa nan ta fice daga parlon idan sun fita sai ta dawo. Ka’ida ce duk safiya a gidan su Fadila ne ke yin wanke wanken safe da sharan tsakar gida ko ma wacece ke girki kafin su tafi makaranta, yau kam suna tashi da safe wanka suka yi ko wanne ta tafi ta saka uniform, Umma bata ce masu komai ba tana ta soya dankalin irish da xa ayi breakfast da shi a gidan, Khadijah na durkushe kitchen din sai dai ta bude babban cooler a Umma ta xuba wanda ta soya, Umma ta gama soya Irish din da ta fere gaba daya ta soya kwai, kananun yaran gidan ne suka dinga tahowa karban nasu duk ta basu ko wanne sa cup din shayi da ta hada, Khadijah dake ta kallonsu tace “Umma why are they so plenty?” murmushi umma tayi tace “Just as the one ur uncles home” Khadijah ta langwabar da kai tace “Noo, they are nt as much as this” Fadila ce ta taho kitchen din tace “Anty ina kwana, ina dankalina” Umma ba tare da ta kalleta ba tace “Idan kin gama wanke wanken can xan xuba maki” juyawa tayi ta wuce sai ga Shafah ta fito, “Amina ban gane baxa ki ba Fadila kalachi ba, meye dalili” Ko tanka ta Umma bata yi ba, ta hau masifa tayi mai isarta daga karshe tace “Bar ta ita ce mayunwaciya Fadila, ta hada da Wanda ta ajiye ma kanta da agolar da ta kawo su cinye, mu je in baki kudi ki siya kosai da bredi a hanya, wanke wanken su shekara nan, in dai baxa ta ba ma agolarta tayi ba” daga haka ta wuce ciki Fadila na biye da ita a baya, daga Hasana har Shafah bbu warce tayi kalaci da girkin da Umma tayi, duk wainar shinkafa suka aiki almajiri ya siyo masu a makwabta, Umma kam ko a gyalenta, wanda ya rage ra kira almajirai ta basu ta hada kayan wanke wanke xata yi, Khadijah tace “Umma na iya wanke wanke fa yanxu xan yi” da kyar ta amince ta bar ta, Ganin yanda ta fara jika kayan jikinta Umma ta karbi kayanta ta shiga yi tace mata ta tafi daki ta kwanta. Da rana cous cous umma ta girka gidan d’an dai dai, daga ita sai khadijah a gidan don tun misalin goma su Shafah da Hasana suka fita basu dawo ba, ta dibar ma kananun yaran gidan a warmer ta kai can dakinta da miyar ta ajiye bayan ta xuba ma Khadijah, ta dawo ta tsaftace kitchen din ta wanke tukwanen da tayi amfani da su da utensils sannan ta koma ciki. Sai kusan karfe Uku su Shafa suka shigo gidan Hasana na cewa “Wash wajen nan ba dai nisa ba Maman fadila, na xata bai fi tafiyar minti talatin ba fa” Shafa tace “Nima farkon xuwa na na sha wahala sosai, ga hanyar bbu kyau mutum na mota kamar ya hau jaki duk jikina ciwo yake…” Shiru Umma taji sun yi suna kallon kofar ta, ita ke ganin su ta labule amma su basa ganinta, suka kalli juna basu dai ce komai ba, kitchen Shafah ta wuce, can sai ga ta ta fito tana kallon Maman walida tace “Ke kamar fa bata yi girki ba” Maman Fadila tace “Bata yi girki ba kuma? Kin ga uban yunwar da nake ji ga shi bani da kosisi kudin sun kare a kudin motar” Daga labulen Umma Maman walida tayi suka yi ido hudu, d’an kame kame ta fara da farko, sai kuma tace “Ba a da niyyar yin girkin rana ne yau a gidan nan ga yara su kusa dawowa” Umma tace “Ehh” sake labulen tayi ta bar wajen Maman fadila ta bi bayan ta, tana jin Shafah na jajjage a kitchen xa su dafa indomie, ita dai tana xaune inda take. Uku da rabi yaran suka dawo kuwa, nan Umma ta xuba ma kowa abincinsa ta ajiye masu tsakar gida, Shafah dake kan tabarma ta kalli kishiyarta dake bakin kofar ta ita ma a xaune, yaran suna gama ci suka fara shirin tafiya islamiyya, Umma ta sa Khadijah ta shirya cikin dinkekken uniform din da tela ta kawo mata daxu, sai murna take har ta gama shiryawa, har bakin makarantar umma ta rakata na ranan kadai sannan ta dawo gida. Umma na kitchen tana girkin dinner ta dinga jin kamar kukan khadijah, ta mike da sauri ta nufi kofar fita, su Shafah da Hasana dake xaune kusa da juna suka bi Umma da ido, a bakin kofa ta kusa cin karo da Khadijah ta riko hannunta tana kkrin cire Hijab din da ta rufe fuskarta tace “Me ya faru?” Cikin kuka tace “Umma wannan yarinyar dake gidan nan ne ban mata komai ba na gansu a hanya, she just slapped my eyes and pushed me na fadi a kan wani dutse” Umma da ranta ya gama baci tace “Wace yarinya kenan?” Dai dai nan walida ta shigo fuskarta tsuke, Khadijah ta nuna mata ita tana shessheka, fixota Umma tayi ta wanka mata mari ta ja kunnenta tace “Don uwarki kika sake taba min ‘ya sai na cire maki hakori wallahi, muguwa kawai mai halin banxa” daga haka Umma ta hankadata, walida ta fasa wani ihu kamar xata tsaga gida tana kiran uwarta. Mikewa Hasana tayi baki bude tace “Amina??? Ita walidar kika mara??” Umma ta juya tana facing dinta tace “An mareta, ki taho ki rama mata, d’a ya fi d’a ne, ai wllh duk shegiyar da tace ‘ya ta baxa ta xauna lafiya ba gidan nan sai dai ita ta rasa xaman lafiya, me marainiyar ta maku? Ko ba a cin arxiki dama a duniya, kishin naku ya tsaya iya kai na mana, toh wllh duk ku ja ma ‘ya yan ku kunne, duk wanda ya sake ko da yi ma khadijah kallon banxa ne, sai nayi masa abinda bai yi xato ba” tana kai wa nan ta tafi daki da Khadijah ta tura ta ciki tace “Maxa ki canxa kaya” daga nan kuma ta dawo kitchen ta ci gaba da abinda take rai bace, daga Hasana har Shafah haka suka bude baki suna kallonta bbu wanda ya iya cewa komai cikinsu. Da daddare Abban Fadila ya dinga kwalo ma Umma dake xaune kan darduma kira, ta mike ta fita don bata ma ji shigowarsa ba amma tuni har ya shiga parlon sa, bin bayansa tayi ta shiga parlon tana masa sannu da xuwa, bai amsa ba ta xauna ba tare da ta yarda ta kalli kishiyoyinta dake xaune parlorn ga Walida a durkushe a kasa, Abban Fadila yace “Amina, so nake xuwa gobe ki mayar da yarinyar nan dangin ubanta da kika daukota, I agree zan yi sponsoring dinta ko tana can din, idan ya so duk bayan watanni uku ko hudu sai ki je ki dinga dubata, I think that will better, I didn’t buy d idea of her staying here anymore….” Tun da ya fara Umma ke kallonsa a sanyaye, Hasana da Shafah da aka wani hakikance kan kujera kamar wasu Hajiyoyi xa a iya ganin murnar dake shimfide fuskarsu, trying hard to control her tears Umma tace “Saboda me kace haka Alhaji? Kada ka mance yarinyar nan marainiya ce ba ta da kowa, tun tana yar shekara biyu mahaifiyarta ta rasu, mahaifinta kuma bai mata gatan nuna mata dangin mahaifiyarta ta ba, da na sansu da can xan kai masu ita baxan kawo ta ba gidan ka Alhaji” Abban fadila yace “Kiyi hakuri iyakar taimakon da xan ma yarinyar kenan, ko nawa ne kudin karatunta xan biya idan ya kama ma da feeding expenses duk xan ba da, kawai dai gidana ne baxata xauna ba, kuma baki min kara ba da har xaki daga hannu ki mari diyata a ido don abun su can ya hada su, so tafiyarta xai fi, I think that’s all… Gobe ki hada kayanta ki maida ta inda kika dauko ta” Umma da hawaye ke xuba idonta a hankali tace “Ina jin da ka sauwake min kawai in tafi da ita xai fi don ni baxan mayar da ita dangin mahaifinta ba” yana gyada kai yace “Kema xa ki iya sauwake ma kanki ai Amina ba sai na sauwake maki ba” mikewa Umma tayi ta fita ta koma bangarenta, ta shiga daki tayi kukanta mai isarta, duk tausayin khadijah ya cika xuciyarta, to yanxu ina xata kai marainiyar nan, ita ba ta da kowa mahaifiyarta ta rasu da sai ta kai ta gun ta tasan xata rike mata ita, bata da wani abun hannu don duk cutar ta yayyin mahaifin khadijah suka yi a rabon gado bayan ya rasu, domin kuwa kafin a ankare sun boye abubuwa da dama cikin dukiyarsa, banda haka da ko boarding sai ta kai khadijah, har gari ya waye Umma bata ritsa ba tana ta tunanin inda xata kai khadijah domin ta ma kanta alkawari first thing da safe xata fitar da ita da gidan, yayarta warce suke uba daya dake Kaduna ta fado mata ta yi shiru tana naxari.

    Daukar waya Umma tayi ta shiga kiran layin step sister dinta Yakumbo amma baya shiga alamar dai wayar a kashe yake, da safe bbu abinda ta girka ma mutan gidan a madadin breakfast, ta dai hada ma Khadijah tea ta siyo mata bread ta bata, Karfe takwas ta shiga bangaren mai gidan nasu ta sanar da shi xata mayar da Khadijah gida, ya kirgo dubu biyar ya mika mata yace “Gashi ku yi kudin mota, idan kin dawo sai a san yanda xa ayi batun makarantar nata in ji ko nawa ake biya” Umma ta girgixa kai tace “A’a ka bar shi mun gode Alhaji, muna da kudin mota” Yace “Shi kenan, Allah ya tsare” mikewa tayi ta fita dakin, a cikin wata karamar jaka Umma ta hada ma Khadijah d’an kayan da ta fara siyo mata, suka fito parlor ta sa ma kofar kwado bayan ta rufe, khadijah dake sanye cikin doguwar riga da karamin Hijab tace “Umma ina xa mu?” Umma ta kasa kallonta tace “Xa mu d’an yi tafiya ne khadijah” daga haka ta kama hannunta suka nufi kofa, tana jin su Shafah da Hasana na dariya suna cewa “Toh a sauka lafiya, sai a kara gaba can da ita” ita dai bata tanka su ba har ta fita. Tasha suka tafi cikin a dai dai ta, can suka samu motar Kaduna, bayan wani lokaci motar ta cika suka yi set off xuwa Kaduna garin gwamna… Ko barin kano basu yi ba khadijah tayi bacci jikin Ummanta, har suka isa Kaduna bata tashi ba, suna isa kawo bayan driver yyi parking kowa ya fara alighting daga cikin motar, Umma ta tada khadijah suka sauka su ma, sai kalle kalle khadijah take tace “Umma where is this?” umma tace “Kaduna” Khadijah tace “Wow I’ve heard of Kaduna in school” Umma ta samar masu napep suka yi ciniki sannan suka shiga xuwa hayin rigasa Unguwar da yakumbo take, tafiya ce mai nisa kafin su iso rigasa, da yake Umma sunan layin kadai ta sani ba wai ta wani san gidan yakumbo bane a bakin layin tasa mai napep din ya sauke su ta basa kudinsa tana rike da hannun khadijah suka shiga layin umma na bin ko wani gida suka xo wucewa da kallo don ta haka kadai xata gane gidan yayarta kasancewar ta jima bata xo wajenta ba, sun fi minti talatin suna bulayi a layin, Khadijah sai tambayarta take “Umma where is this, everyway is dirty, they are smelly gutters everywhere” Umma tace “look I don’t want to here ur mouth again” shiru khadijah tayi, daga karshe dai wata mata da ta gansu suna ta yawo ce ta tambayesu gidan da suke nema, Umma tayi shiru tana tuna sunan da aka fi sanin yakumbo da shi, can tace “Kulu mai waina” Matar tace “Ikon Allah, yo ai ga gidan can kun wuce” Umma ta juya tana kallon gidan da matar ke nuna mata, matar tace “Wancan gidan mai keke a gaban sa” Umma tayi murmushi tace “Kin ga kuwa sai yanxu na gane, gaskiya na nagode sosai” daga haka suka juya khadijah na biye da ita a baya, tsallake gutter din dake kofar shiga gidan Umma tayi Khadijah ma ta yi haka sannan suka shiga xauren gidan, gida ne ginin kasa duk ya kwarabe, Khadijah ta xaro ido tana bin gidan da kallo, Yakumbo ce xaune tsakar gida tana hura icce duk hayaki ya cika ko ina, Umma tace “Yaya” dagowa yakumbo tayi ta xaro ido tace “Aminatu” karasawa Umma tayi ta rungumeta tace “Rai kan ga rai yaya” cike da farin ciki Yakumbo tace “Sannu da xuwa Amina, daga ina haka? ya mai gidan naki?” Umma tace “Wllh daga kano Yaya, yana nan lafiya yace duk a gaida ku” Yakumbo tace “Maa sha Allah sai dai kin rame kan lokacin bikin, wacece wancan” Yakumbo ta fada tana nuna Khadijah, A hankali Umma tace “Yar marigayin mijina ce Alhaji Muhammad” Yakumbo ta rike haba tace “Ikon Allah gashi ta kusa xama budurwa, sun hakura sun baki ita kenan?” Umma tace “uhn, labari ne me yawa yaya bari dai mu yi sallah” Yakumbo tace “Gaskiya ne bari in kawo maku ruwa” tabarma ta fara shimfida masu kafin ta tafi debo ruwan alwala, Umma ta xauna ta nuna ma khadijah dake tsaye gefenta, khadijah ta karaso tana tsattsallake bololin dake watse tsakar gidan, Umma tace “yaya ina mutan gidan?” Yakumbo tace “Toh jikokin nawa sun fita wasa, tun safe rabona da su, yaran makwabtana kuma duk sun tafi talla, iyayensu kuma aikatau suke na yini, Ladi ce kadai ta shiga makwabta daxu, nima anjima xan fita suyan wara da dankali a bakin titi” shiru Umma tayi jikinta yayi mugun sanyi, yakumbo ta kara da cewa “Ai Allah ma yyi ban tashi a gidan nan ba kika xo, don duk mai gidan ya ba mu notice xai rushe gidan wai, to gida ne duk ya rube” Umma ta kalleta da sauri tace “Ina xa ku koma yaya?” Yakumbo tace “Oho dai har yanxu ina lalube ne, kudin kama wani gidan ma ai xaune yake da kugunsa, talauci yyi yawa ta ko ina, ko daxu na fita duba gida don sati daya ya ba mu xai watsar mana da kaya waje” Umma tace “Ikon Allah” Yakumbo tace “Ai ke dai kawai sai du’a’i duniyar ta xama abinda ta xama” Yakumbo ta kalli khadijah da ta takure gu daya tace “ke yar nan tashi ki fita waje gun mai kanti ki siyo min farin maggi” Umma tace “Yaya ai bata san ko ina ba” Yakumbo tace “Ka ji ki, nan nan ga masu kanti kamar jampa a jos ta ko ina a anguwar nan, tana fita duk inda ta bi akwai mai kanti” daga haka Yakumbo ta kunce kullin xaninta ta fiddo wani naira ashirin dake a dunkule ta jefa ma khadijah, mikewa khadijah tayi ta karasa ta duka ta dau kudin tana kallon Yakumbo tace “How much own” yakumbo ta d’an bude ido tace “Eh??’ Umma tace ” twenty naira” khadijah ta juya ta fita, yakumbo tace “Sai na ji kamar yare tayi” Umma tayi murmushi tace “Turanci tayi” Yakumbo tace “Au tohhh abun na manya ne Ashe” ita dai Umma bata ce komai ba ta mike taje tayi alwala ta dawo tayi hau kan tabarman ta tada sallah, jin shiru shiru Umma na idarwa ta bi bayan khadijah, a bakin xaure suka kusa cin karo Umma tace “Ina magin kuma me ya sa kika dade?” Khadijah tace “Umma I’ve forgotten the one she mentioned” Umma ta hade rai tace “Bani kudin” mika mata khadijah tayi ta umma ta koma ta dau dari a Jakarta ta fita, farin magin hamsin ta siyo mata da maggi star saba’in sannan ta dawo gida, garau garau na dafaduka Yakumbo ta girka masu, ta xubo a faranti. Umma kadai ce ke cin abincin a sanyaye tana tausayin khadijah dake tsintar shinkafar, yakumbo kuwa na ta yankan warar da xata fita soyawa kamar yanda tace suna yi suna hirar xumunci da yar uwarta, la’asar nayi Yakumbo ta kira almajiri ya kai mata kayan bakin titi gun da take suyar, Tana kokarin saka Hijab dinta da yyi dukun dukun tace “Toh Amina xan fita kasuwa, idan kun ji yunwa ku kara deban abincin, sai ki d’an taimaka ki share min daki ki fiddo kayan wanke wanken ki ajiye su bakin kwararon can ko yarinyar nan ki sa tayi” Umma tace “Toh yaya, amma fa har yanxu yaran basu dawo ba” Yakumbo tace “Rabu da gantalallu suna makwabta na sani, idan yunwa ta kwakulesu xa ki ga sun dawo da daddaya da daddaya” daga haka yakumbo ta fita rike da roban dake dauke da dankali a ruwa, Umma ta bi ta da kallo, Khadijah ta yatsine fuska tace “Umma the food is somehow” Umma ta hade rai tace “Haka nan xa ki ci, ko ni ma baki ga hakan na ci ba” Khadijah bata ce komai ba, Umma ta mike ta shiga d’an karamin dakin yakumbo, har wani wari dakin yake gashi bbu ventilation don windown dan karami ne, ga kaya ta ko ina, plastern dakin duk ya faffashe gashi ko leda babu, jikin umma yyi sanyi ta daga dan karamin katifar da tayi bakikirin ta shiga gyaran dakin ta fidda duk kwanukan da har da funfuna jikinsu sannan ta fara sharan dakin. Ko da ta fito bayan ta gama bacci ta tarda khadijah na yi, ga shinkafar ta bar sa, Umma ta tada ta ta bata Dari biyu tace “Kije kantin da kika je daxu ki karbo Nutri milk da biscuit din hamsin ki xo ki ci” Karba khadijah tayi ta fita. Sai kusan karfe biyar jikokin yakumbo uku suka dawo gidan sun yi dukun dukun da dirty, duk kanana ne yaran, Umma ta masu wanka da sabulun wankin da ta gani, ta xuba masu abinci, Khadijah dai na xaune sai kallonsu take da wani expression, nama Umma ta fita ta nemo a anguwar ta xuba masu kan abincin ko khadijah xata ci, nan ta tsince naman ta bar mata shinkafar wai ta koshi, sai dab da Isha yakumbo ta shigo gidan tare da Almajiri da ya dauko kayan suyanta, Sannu ta dinga ma su Umma, Umma ta mike ta taya ta karban kayan…. sha dayan dare bayan su khadijah sun yi bacci Umma ta shiga yi ma Yakumbo bayanin abinda ya kawo ta da Khadijah, bayan yakumbo ta gama saurarenta tace “Ikon Allah, mugunta fa yyi yawa a duniyar nn yanxu ki kuluwa” Umma tayi shiru bata ce komai ba, Yakumbo ta kyabe baki tace “Toh ni wannan ai ba matsala bace, don dai in rike marainiya, bakomai wllh” Dubu 30 Umma ta kirgo ta ba yakumbo tace “Wannan sai ki siya kayan abinci da indomie ki ajiye yaya” makaranta kuma ayi mata Register da ta gwamnati idan Allah ya hore min sai in canxa mata, dubu ashirin ta kuma bata tayi ma khadijah siyayyar makaranta, yakumbo ta dinga godiya kamar ita ta ba kudin, sai kusan karfe daya suka kwanta bayan yakumbo ta gama tsine ma matan mijin Umma, da su kawu. Washegari da safe Umma ta dau hanyar kano bayan ta rubuta ma Yakumbo lambarta kan cewa duk inda suka koma ta sanar da ita in case xata dawo duba khadijah, dubara aka ma khadijah aka aiketa daga nan Umma ta samu ta bar gidan duk jikinta a sanyaye, da Khadijah ta dawo ta kyallara ido taga ba umma ta dinga ihu tana kuka a gidan tana cewa a kai ta gun ta, Bakin yakumbo a leko ta dauko muciya tace “Kin ga wannan abun hannu na? To wllh da shi xan fasa maki kai idan kika ci gaba da tona min asiri a anguwa, kaji min katuwar banxa, maxa ki tafi tare da Fauxiyya ku siyo min ice da xan yi tuyan awara anjima” Jikin khadijah na bari suka fita, matan gidan dake ta kallon ikon Allah suka ce “Yo ke kulu da kike jiran fauxiyya ta kara wayo ki kai ta aikatu kina samun kudi don me baxa ki kai wnn budurwar da aka kawo maki ba? Ai wannan da ganinta bbu aikin da baxata iya ba har wanki” Yakumbo tayi shiru tana kallonsu.

    Ko da suka dawo gidan firewood kwara biyu kadai khadijah ta riko a hannu, fauziyya kuma ta rike ya kusa shidda, daga matan gidan har Yakumbo sakin baki suka yi suna kallon Khadijah da ta ajiye tana haki, yakumbo tace “Meye wannan din kika dauko?” Da kyar khadijah tace “Firewood, it’s too heavy, and it’s pricking me all over” a fusace Yakumbo tace “Kin ma uwar ki Amina turanci ba ni ba, kuma ke kadai xaki koma ki kwaso duk wanda ga rage fauziyya baxa ta je ba tunda ba ki da mutunci” korata Yakumbo tayi ta fita ta na share hawayen dake sakko mata, mai firewood din ganin yanda take hawaye kuma kana ganinta kasan baxata iya dauka ba ta dauko wani rabanta ta xuba mata su a ciki ta daura mata a kai tace “Kina kai wa ki dawo min da roba na kin ji” a hankali khadijah tace “Toh nagode” A haka ta isa gida tayi ta tsayuwa da roba a kai wai bbu ke sauke mata inji Yakumbo, daga karshe ladi ta kike ta sauke mata tana cewa “Idan ka xa ki kama jiki ki kama jiki ki daina ma mutane kamar mara laka a jiki” Khadijah dai bata ce komai ba, bayan ta juye iccen tace ma yakumbo xata mayar da roban, ko kallonta yakumbo bata yi ba ta juya ta fita kai ma mai iccen robar ta. Yakumbo ce tsaye tsakar gida bayan kwana uku da xuwan su Umma, tafi minti talatin banda kumfar baki da masifa bbu abinda take, ga matan gidan da yaransu a xaune babu mai bata hakuri sai ma xugata da suke, khadijah kuma na tsaye bakin xaure duk tayi wani duhu ta rame sosai, idonta duk ya kumbura don kuka ga shatin bulala a jikinta, Ladi tace “Yo da kinsan haka ne tun farko kema ai baxa ki fara daukarta ba, meye amfanin yaron da baxa ka amfana da shi ba sai shegen son jiki da iyayi, ai kadan ma kika mata da kin hada kin fasa shegen bakin turancin da take xagin mutane da shi a gidan nan” Yakumbo na huci tace “Ai Amina ta cuce ni, ta yaudare ni… Tasan haka shegiyar yar take xata kawo min ita tun farko, gode gode da yarinya bata iya komai ba wanke wanke duk ta jika kayan jikinta tayi awa da awanni a bakin kwararo, shara duk a gantale, gyaran daki gwara ka da fauziyya mai shekara biyar, aike sai kayi yyi sau uku, har yau ta kasa iya hura icce, girki dama ba a maganar sa, wa ennan yan mitsimitsi yaran idan na sa ta tayi masu wanka ta shaka masu sabulu a hanci ko a ido, ni dama tun farko abinda ya sa na karbeta na yi xatan xan amfana da ita ne, banda haka me xai kai ni kowa na ta kansa a rayuwar nan gashi gobe ko jibi xa a xo a fitar mana da kaya har ynxu ban kama wani gidan ba, ni wllh wllh da nasan gidan Amina sai in yi kudin mota in mayar da ita ta bani kudi na don baxan iya kayan tsiya ba, dama can Aminar ma ba wani kyautata min take ba uba ne kadai ya hada mu” Salamatu tace “Ai irin yaran nan kyansu aikatu wllh, a can xa a horasu su ladabtu….” Katse ta yakumbo tayi tace “Yar da har yanxu bata iya shara ba xan kai aikatau, ai koramu xa ayi daga ni har ita” Ladi tace “Yo ke nuna masu xa ki yi bbu abinda bata iya ba ai, a can xa su gyara mata xama ta iya komai, mutanen da basu san darajar d’an Adam ba, ai tuni wahalar da xa su dinga mata xai sa ta xage a nan kuma xata koyi komai, wannan d’an abincin da kike bata ma take kin ci take yawo da yunwa can nema xata yi ta rasa, hakan xai ladabtar da ita wllh” Yakumbo ta ja kujerar tsugunno ta xauna tace “Kai amma fa kun kawo shawara, amma….” Sai kuma tayi shiru ta kalli khadijah dake kallonsu, tsawa tayi mata ta ce “Fita ki ban waje kije gun mai kanti da hamsin di ta dake gunsa ki amso min barkonu” juyawa khadijah tayi da sauri ta fita gidan, Yakumbo ta mayar da dubanta gun su Ladi tace “Toh Amina fa? Kunsan baxa ta yarda ba” dariya Ladi tayi tace “Ka ji ki, sai ki gaya mata, barin ma yanxu tashi xa ku yi Ku bar anguwar, shawara a nan shine kada ki kuskura ki gaya ma ko inda kika koma a anguwar nan, kawai cewa xa ki yi ba ki ma samu gidan ba gidan wata yar uwarki xa ki kafin ki samu, ke kuwa kije shanono abun ki ki kama ko daki daya ne bbu wanda yasan inda kike, dama ba waya gare ki ba, har ki tara kudin da xa ki tara da yarinyar daga nan idan ma mayar da ita gun Aminan xa ki yi sai ki ja mata kunne ki mayar da ita” Yakumbo tayi murmushi tace “Dadina da ku akwai shawara mai ma’ana, amma fa har da kudin da xan sa yarinyar a makarantar gwamnati ta bani, yanxu haka ma da kudin xan je kama haya a shanonon, dubu hamsin kuma jari xan ja na su omo da sabulu ina siyarwa, ita can na kai ta gun aiki ana biyanta dubu uku misali, kun ga ni ban ma kai da nisa ba….” Ladi tace “Toh gaskiya sai kin ba mu dubu dai dai mu da muka kawo shawarar Ashe ma kudi gare ki har haka” yakumbo ta hade rai tana da ta sanin gaya masu, rai a bace tace “Dari bibbiyu dai” daga haka ta mike ta shiga cikin akurkin dakinta, sai ga ta ta fito da sauri tace “Toh yanxu wa xai min hanya in kai ta gidan aikin, don ni gaskiya baxan tare da ita a sabon gidana ba, ko yau aka samu gun aikin ba don yamma yyi ba kai ta xan yi, don haka gobe da safe xan kai ta….” Ladi tace “Akwai wata kawata Habiba dillaliyarsu ce, xan baki lambarta… Ko kuma ki sa katin dari a wayata mu kirata, in sha Allah nasan baxata rasa inda xata kai maki ita ba” hakan ko aka yi Yakumbo ta sa kati ladi ta kira Habiba, suka ci sa’a number ya shiga, bayan ladi ta gaisa da kawartata tace “Bibalo dama wata yarinya ce da ake son kai ta gidan aiki to shine muke son ki yi taimako” Bibalo tace “Kai yanxu haka Ina hanyar dawowa daga kauye na mayar da wasu yara, amma gobe da safe xa ki gan ni duk da bani da wa enda ke son masu aiki yanxu, amma nasan kawata Abu baxata rasa ba don ta ma fi ni sanin gidajen manya” daga haka suka yi sallama ladi ta katse wayar tana kallon Yakumbo don ba sai ta mata bayani ba tunda a handsfree tasa ita ma ta ji komai, Yakumbo tace “Toh Allah ya sa a dace, ni wllh ko dubu biyu ma xa a dinga biyanta na yarda” tagumi tayi tace “Allah gani gare ka, kasa a karbi yarinyar nan ni kuluwa” Washegari da safe kuwa sai ga Bibalo tare da kawarta da ta fada Abu, Yakumbo dake ta washe hakora ta gaishesu suka amsa aka xaxxauna kan tabarma ladi ma ta fito akurkin ta tana masu sannu da xuwa, bayan sun gaisa Bibalo tace “Toh kinga ni bni da inda xan kai ta amma Abu tace kawarta ta taba hadata da wata Hajiya mai neman mai aiki, da xata dinga share share da goge goge sannan wanke wanke, akwai ma wata babbar mai aiki dake girki a gidan, to Abu taje gidan ya fi sau uku ba a bude mata gate, yanxu ma gwada sa’a xa ayi kuje har da ke kika wajen, idan sun dauketa to, idan kuma sun ce A’a sai ki jira har a bukaci mai aiki a wani gidan sai in kai ta” Yakumbo tace “A’a mu je kawai mu gwada sa’ar mu” Bibalo tace “Toh ki sallame ni ni xan wuce” Yakumbo ta hade rai tace “In sallame ki? Me kika min da xan sallame ki” Bibalo ta bude baki tace “Au haka ma xa ki ce, shi kudin motar da nayi da kuma bata lokacina da na yi na xo nan tare da kawata har xa ki ce min me na maki” mikewa Yakumbo tayi rai a bace ta shiga ciki ta fito da dari biyu tana cewa “Ko daukar yarinya ba ayi ba xaki wani ce in sallame ki idan ba hadama ba” dungura mata dari biyun tayi a gabanta rai a bace, Bibalo ta dauka ta mike tace “Ya fi babu ai” daga haka ta yi ma Ladi sallama da Abu tayi ficewarta, Abu tace “Toh inji kinsan mu dubu daya ce sallamar mu?” Yakumbo ta hade rai tace “Idan an dauki yarinya ba” Abu tace “Toh gwara da kika san haka don ni baxan tsaya cacar baki ba, yanxu Ina yarinyar take?” Yakumbo ta nuna mata khadijah dake ta fama da wanke wanke, kwalalo ido tayi tace “Warcen da ta fi minti ashirin tana d’an wanke wanken can, tun shigowar mu fa take wanke wanken kamar ayi kamar baxa ayi ba” yakumbo ta marairaice tace “Haka take Abu, akwai iya aiki amma ba sauri ne kawai, amma tana xuwa can nasan xa su gyara mata xama ta xama mai hanxari” Abu ta tabe baki tace “Toh unguwar da nisa, don can Gra ne, kuma wllh gidan babban mutane ne, ni dai Allah ya sa su dauketa, yanxu sai ki tashi ku shirya ta hada kayanta ina jiran ku mu kama hanya” Yakumbo ta mike da sauri ta shiga ciki tana cewa “Toh bamu minti biyar kacal” tana shiga dakin ta kwalo ma khadijah kira, khadijah ta mike ta shiga da sauri. Yakumbo ta jawota tayi kasa da murya tace “Dijangala ta mai gari, ba auren talaka ba” tana washe hakora ta fadi haka, ita dai khadijah kallon ta kawai take, Yakumbo tace “Kinsan inda xa mu yanxu kuwa?” Girgixa kai khadijah tayi, Yakumbo tace “Gidan da xa a dinga biyanki kudi mai yawa in tara maki in sa ki a boko, kai har in maki aure ma” khadijah tayi shiru bata ce komai ba, yakumbo ta marairaice tace “Don haka muna xuwa kice kin iya aikin komai, sai ki bada himma idan an saki aiki ki yi da sauri da sauri, sannan don Allah Idan mun je gidan khadijah kar ki masu wannan yaran naki na turanci kin ji koh? Kawai Hausa xa ki masu, idan kuma baki san Kalmar da xa ki fada da hausa ba sai kiyi shiru abun ki ba sai kin yi turancin ba” yanxu maxa canxa kayan Ki bari in tusa maki wa encan a jaka tunda basu samu wanki ba idan kin je can ko ba ki iya wankin ba ki tsoma su a ruwa ki xuba omo ki shanya” daga haka Yakumbo ta shiga tusa kayanta a wani karamin Ghana must go, don har ta siyar da jakar da Umma ta kawo mata kayanta ciki, karfe tara da kusan rabi su yakumbo suka bar gidan tare da Abu bayan ta yi ma yan gidan sallama suka dinga yi mata Allah ya bada sa’a, tana rike da hannun khadijah suka isa bakin titi, Abu tace “Amma kinsan ke xa ki biya kudin abun hawa dai koh?” Yakumbo ta tsuke fuska tace “A kan me?” Abu tace “A’a mayar da wukar ae dai naga ba xuwan kai na xan yi ba gidan don hka idan kinsan gidan ke sai ki kai ta, yakumbo ta rikota da sauri tace “Naji, mu je ya na iya, daga yau ai babu wanda xai xo yace in biya masa kudin napep dai koh?” Ko tanka ta Abu bata yi ba ta shiga napep din da ta tsayar, Yakumbo ta shiga ta daura khadijah a cinya. Tafiya ce mai nisa kamar yanda Abu tace masu, tun da suka bar hayi dama Yakumbo ke addu’ar Allah ya sa a dau khadijah gidan aikin idan ba haka ba asirinta ya tonu don ta sa rai da kudin da xa a dinga biyan khadijah, tun da suka shigo anguwan Yakumbo ta saki baki kamar yawu xai dalalo tana kallon gidaje na alfarma, Abu ta dinga nuna ma Mai napep din inda xai bai, har suka iso wani cool silent anguwa mai cike da shuke shuke a ko wani gate, ga bakin kwalta a shimfide daga farkon layin har inda yakumbo ke tunani karshe ne, bakin wani gate Abu ta sa mai napep din ya tsaya, yakumbo ta wage baki tana kallon jibgegen gidan da aka yi ma ginin xamani kamar ta sure ta gudu, gidan ya hadu ne kawai don ita a ganinta duk ya fi sauran gidajen dake layin haduwa, suka sauka sai kuma Yakumbo aka tsuke fuska da ta tuna kudi xata bada yanxu, ta dungura ma mai napep din kudin da yace lkci daya kuma tana hararan Abu, Abu da ko lura da ita bata yi ba tace “Toh Allah ka bamu sa’a don kwanaki da na xo haka na sha xamana bakin gate rana yayi maganina ban samu shiga gidan ba… Yakumbo tace “Yana da kyau mutum ya dinga fadin alkhairi ko yayi shiru, yanxu me ya kawo wannan xancen, in sha Allahu ma sai mun shiga don haka ki mana shiru” daga haka Yakumbo bta kwankwasa gate din a hankali kamar me tsoron kada ya fashe don ita fa gani take kamar glass ne a kauyancinta, ta kwankwasa ya kai sau hudu kafin wani da alamar mai gadi ne ya bude yana kallonsu, Yakumbo ta durkusa har kasa ta gaishesa, yace “Wa ku ke nema?” Yakumbo ta mike tace “Matar gidan muke nema ce mana tayi mu samo mata mai aiki yarinya karama, to cikin ikon Allah gashi mun samo mai haxaka, shine muke hadaka da Allah yaro ka bar mu mu shiga, mu gabatar mata da aiken da ta mana” ya girgixa kai yace “Ai akwai mai aiki yanxu haka a gidan don haka ban ji xa a bukaci warce xa ku kawo” Bakin yakumbo ya fara rawa tace “Wllh xa su bukata dubeta fa kaga bbu abinda bata iya ba, sannan Hajiyar da kanta ta sa mu ko daxu mun yi waya da ita tace sai mun xo, haba yarona ka duba tsufana mana gashi daga hayin rigasa muke wllh” Mai gadin yace “Toh yanxu ma ku kirata idan tace ku shiga toh shkkn” daga yakumbo har Abu aka hadiye yawu da kyar don babu mai waya cikinsu, Yakumbo tayi karfin halin cewa “Wallahi wallahi na mance wayar a gida kaji rantsuwar musulmi” Abu ta saki baki jin rantsuwar da Yakumbo tayi alhalin taji Bibalo tace bata da waya.

  • Noor Al Hayat 12

    Noor Al Hayat 12

    12…

    Da asuba tana kitchen ta gama goge goge xata hada breakfast taji muryarsa ta waje yace “Morning” da sauri ta kalli direction din window taga bata hangosa ba, ta leka a hankali taga gym yake, ta bar gun da sauri ta ci gaba da hada ingredients din da xata soya eggs din da xata yi toasting da bread kasancewar bata yi da raw eggs, bayan wasu mintuna tace “How you feeling now?” bai amsa ba shi ma, hakan yasa ta juya ta kalli window direction, dai dai lkcn da ya iso kusa da window din kenan suka hada ido ya karyar da kai yana kallonta daga sama har kasa, juya baya tayi da sauri don rigar bacci ne jikinta, yace “Uhn… You look cute in that…” mamaki ne ya cikata ta kasa juyowa, ya ce “Ki shirya xaman gidan ya isa haka ki tafi makaranta yau koh” daga haka ya bar wajen, ko bai fada mata ba dama tayi niyyar tafiya makarantar yau. Karfe tara ta fito cikin shirin tafiya makaranta, fitowa yyi ya tsaya bakin door dinsa yana kallonta yace “Makarantar xa ki tafi yanxu?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Yeah” yace “Alright you wait for me” daga haka ya koma ciki, k’asa wucewa tayi tana ta tsaye wajen har ya fito rike da makullin motarsa, as usual kananun kaya ne jikinsa, kallo daya tayi ma wandonsa ta dauke kai a ranta tace aiki, yace “to mu tafi” parking space ya nufa ta bi bayansa, sai da ta jira yyi warming motar sannan ta bude ta shiga. Haka kawai gabanta ke faduwa ta rasa dalili, idonsa na kan titi yana driving yace “Do you have problem with anybody here?” Ta kallesa da sauri, shi ma ya kalleta, mayar da dubansa yyi kan titi, tana girgixa kai tace “I don’t think it’s any of ur concern” shiru ya d’an yi kafin yace “Ohk then” bai sake ce mata komai ba har ya isa makaranta, bata yarda sun hada ido ba ta bude motar ta fita tace “Thanks” daga haka tayi wucewarta. Tafe suke da course mates dinta bayan sun fito lectures din karfe goma da suka shiga, cafeteria suka nufa ita kuma tace masu xata je library karatu, bayan sun rabu bata je library din ba, kawai she want to be alone ne dama, guri me shiru ta samu ta xauna ta tsura flower dake wajen ido, ta kusa minti talatin a wajen kamar ance ta dago suka yi ido hudu da khaleel dake xaune d’an nesa da ita da wata baturiya dake karatu ita ma, mikewa yyi bayan sun hada ido yana kallon baturiyar yace “Stephanie c yah later” mikewa khadijah tayi ta riga sa barin wajen. Da safe misalin karfe takwas ta fito apartment dinta, yau dai kam ta makara sosai, tsaye ta gansa parking space waya kare kunnensa, suna hada ido ya dauke kai, ita ma bata sake kallonsa ba har ta fita daga gidan a xuciyarta tace “Can ta matse maka” Ita kadai ce xaune Cafeteria bayan sun gama lectures din ranan, Vanessa tuni ta bi saurayinta suka tafi tun bayan da suka gama cin abinci, ita kanta ta rasa me yasa ta ki barin gun har lkcn gashi tana son wucewa, chatting take da kawarta Salima dake Nigeria a WhatsApp kanta a duke, kamar ance ta daga kai tayi still ganin wa enda suka shigo Cafeteria din, a hankali ta saki wayar hannunta ya xame ya fada kan cinyarta, da sauri ta kauda kai xuciyarta na mugun bugawa, table dake gefen nata ya xauna kan kujerar shi da Baturen da suka shigo wajen tare, cikin sanyin muryarsa yake cewa “I don’t have intentions of coming here frank, let be fast” baturen yace “Yeah, they will be here soon…” baturiyar dake tsaye kansu ta mika masu takardar list din abinci dake hannunta, muryarsa ya kuma dakan codon kunnenta da accent din turawa yace “Number 6 content for my frnd, just table water for me…..” Kamar ana tilasta sa yyi maganan, a hankali khadijah ta mike kamar an xare mata abu a ciki, tana boye gefen fuskarta da mayafin kanta ta nufi kofar fita sum sum tana hade hanya, satan kallonsa tayi suka yi ido hudu don bin ta da kallo yyi, lkci daya ya mike ya xaro ido yana kallonta, tana ganin haka ta kwasa a guje, bin ta yyi da sauri yana cewa “Imannn….. Imannn plss wait, Iman…..” hankalinta bai gama tashi ba sai da taga bin ta yake tsakaninsa da Allah gashi ya kusa kamo ta, ta jefar da takalman kafarta da jaka ta fashe da kuka sosai, gudu take kamar her life depends on it, tana yi tana waiwayowa a tsorace, Gani tayi wasu wanda da alaman Africans ne sun rikesa suna tuhumarsa me yasa yake bin ta, hakan ya kara mata kwarin gwiwan gudun, taxi ta samu ta shiga tana waige waige muryarta na rawa tace “Bridge street” tuni mai cab din ya ja suka dau hanya, lumshe ido tayi hawaye masu xafi na sakko mata, tana son fashewa da kuka ko xata ji dadi amma tayi controlling kanta ganin inda take, number gidan ta gaya masa bayan sun kai yyi parking ta bude motar ta fita, tunawa tayi bbu kudin da xata basa, tana kallonsa a sanyaye tace bari ta shiga ta dauko masa kudi, a hankali take tafiya compound din tana goge hawayen dake sauko mata, dai dai fitowar Khaleel part dinsa rike da makullin mota da wasu takardu, tsayawa yyi yana kallonta daga sama har kasa mamaki dauke fuskarsa, hade rai tayi sosai ta turo baki ta dauke kai ta kuma ki motsi daga inda take, taku daya biyu ya iso gabanta tayi saurin barin gun, fixgota yyi ta fashe da matsanancin kukan dake cin ta tun daxu, da mamaki yace “What’s wrong with you, me ya faru? where are you coming from?” Kin cewa komai tayi sai kukan da take yi sosai, damuwa ne sosai fuskarsa yace “Talk to me plss, me ya same ki?” Ta hadiye kukan da kyar tana share hawayen idonta cikin rawar murya tace “Ban ba mai Cab kudi ba….” Kallon gate yyi, can ya sake ta ya fita, Durkushewa gun tayi ta dinga rera kuka xuciyarta na mata xafi, a haka Khaleel ya dawo ya sameta, ya hade rai yace “malama tambayar ki nake where r u coming from” mikewa tayi tana share hawayen idonta har lkcn bata daina kukan da take ba xata bar wajen ya rikota yana mata wani kallo a d’an tsawace yace “Me aka maki nace, where r u coming from?” Ganin ba magana xata yi ba yana rike da hannunta ya wuce part dinsa da ita, xaunar da ita yyi kan kujera a parlor ya duka gabanta yana kallonta cikin sanyin murya yace “Now tell me what happen” cike da karfin hali tace “Nothing” ido ya xuba mata bai sake cewa komai ba, can ya mike ya koma bayan kujera ya rungume hannu ya tsaya yana kallonta, ta gama cin kukanta ta jinginar da kanta da kujera, tafi minti sha biyar a haka bbu kalan tunanin da bata yi ba har bacci ya dauketa. Shi kam yana tsaye har lkcn bayan kujera yana kallonta yana mamakin irin taurin kanta, sai da ya ga bacci ya dauketa sannan ya xagayo ya iso gabanta ya durkusa kusa da ita, shi dai ya san tausayinta kawai yake ji har ransa, though he don’t know her that much but he knows she’s pained, coz she looks so, lumshe ido yyi ya bude yana kallonta, Khadijah is just the definition of cool Beauty, tall…. fair…. Slim with a perfect shape, Best of all she have got d most sexiest lips and eyes, her nose….. Kauda tunanin yyi, a xuciyar sa yace not as beautiful as Jawahir, a hankali ya mike ya dafata da xumar yace mata ta kwanta, a firgice ta farka tace “Aliyuuu….” Ja baya yyi yana kallonta. Da kyar ta karashe bude idonta da yyi mata nauyi ta daga kai tana kallon sa, xamowa kasa tayi a hankali, ya mike ya rungume hannayensa yana kallonta a ransa yana nanata sunan da ta kira, tashi tayi ta runtse ido ta juya xata fita parlorn, murya can kasa yace “Malama” sake juyowa tayi, yace “Where are u coming from” bata iya ta kallesa ba cikin sanyin murya tace “School” yace “Me ya same ki a can?” Tace “Am not feeling fine” bai sake cewa komai ba ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita. Magungunan ta ta dauka ta sha lkci daya kuma bacci ya dauketa, bata farka ba sai da asuba shi ma ta dalilin yunwa, ganin lkcn sllh bai karasa ba ta shiga kitchen don neman abinda xata ci, motsi ta dinga ji a waje ta leka a hankali, gym ta gansa yana yi jikinsa sanye da 3qtr kadai, suka yi ido hudu tayi saurin barin gun, parlor ta koma ta dauko Hijab ta sa sannan ta dawo kitchen din, har ta gama abinda xata yi bata sake leka waje ba, ta koma parlor da Indomien ta, tun da tayi wanka bayan tayi sllh gabanta ke ta faduwan xuwa schl gashi tana da test, hawaye ta dinga yi duk xuciyarta tayi rauni, gaba daya xaman kasar ya isheta taji gida take son komawa, to karatun fa, shekara bai kai biyu ya rage mata ba, danna bell aka yita mike a d’an tsorace, don ynxu kam gaba daya a tsoracen take, hijab ta saka ta fito, a hankali tace “Yes?” Yace “How you” bude kofar tayi ta gaishesa, yace “Baxa ki schl din bane yau?” Kamar xata yi kukatace “Ban sani ba” kallonta kawai yake bai ce komai ba, bayan yan sakwanni yace “Toh ki shirya, I am waiting for you” daga hka ya juya ta rufe kofar. Har dept ya ajiye ta, kowa ya ganta a lkcn yasan a tsorace take, yace “Yaushe xa ki gama lectures din?” Tace “Quiz ne” yace “Shi kadai?” Kai ta gyada masa, yace “ohk am around I will call ltr in ji ko kun gama” buda masa hannu tayi tace “Jakar ya fadi jiya ai” Kallonta ya tsaya yi, can ya ciro waya aljihunsa ya mika mata yace “I will call” ta karba tana gyada masa kai, daga hakata fita motar, shi ma ya fito yace “I think I will leave the car here” bin satayi da ido har ya wuce kafin ita ma ta bar wajen da sauri.

    *Haske Writers Association*💡

    ✨ *Noor-Al-Hayat*✨

  • Noor Al Hayat 8

    Noor Al Hayat 8

    8……

    Sai a sannan Khadijah suka gaisa da Nanny tana tambayarta hanya da Umma, kitchen Nanny ta nufa xata daura masu ruwan wanka khadijah tace “Na riga na sa ruwan Nanny, bari xan masu” daga haka ta mike ta ja boys din xuwa Bedroom dinta. Wanka ta yi masu ta wanke masu baki ta sa duk suka yi alwala sannan suka fito, ta saka masu kayansu ta sa suka yi sallah, a tare suka ci abincin da tayi serving dinsu, Nanny da ita ma ta kintsa a daya bedroom din ta fito ta tarda su parlor ta dau abincinta da Khadijah ta rufe mata, nan su Shuraim suka dinga bata labarin abubuwan da ya faru a makaranta, ita dai ta tallabi chin dinta tana kallon kyawawan yaran with interest, Nanny ta shiga ciki ta kwanta ta bar su a parlorn, Shiddah saura Sudais ya 6ata fuska yace “Anty ba mu ci indomie ba fa yau” dariya tayi tana kallonsa sanin irin soyayyarsa da indomie gashi har da speaking din Hausa, which is rare kaji sun yi, ta mike tace “Toh bari in dafa maka Prince, in yi maka frying egg din or I shud cook it” yace “Cook” tace “Toh” Shuraim yace “No i prefer fried egg” tace “Alryt duk xan maku” daga haka ta wuce kitchen ta bar su suna kallon cartoon a parlorn, ta gama dafa indomien kenan tana xuba masu a plate kamar ance ta kalli waje ta tagar kitchen ta hango Shuraim tsaye kan study table din khaleel, khaleel din na tsaye gaban sa yana murmushi yana kallon sa, shuraim kuwa sai demonstrating yake da hannunsa yana masa magana, ta wani hade rai ta bude kofar kitchen din ta fita a tsawace tace “Me kake a wajen nan Shuraim, with whose permission ka fita” sosai yaron ya tsorata ya shiga kkrin sauka kasa, Khaleel ya saukesa ya juya yana kallon ta calmly yace “With my permission madam” ta wani kara hade rai, Shuraim ya nufo ta da sauri kamar xai yi kuka yace “Kiyi hakuri Anty” hanyar kitchen din ta nuna masa tana kallonsa sternly, ya shiga ciki da sauri, Khaleel ya shafa beard dinsa yace “Toh sannu me k’anni.. sai ki jira ki haifa naki tukun” ko kallonsa bata yi ba ta shiga ciki ta rufe kofar ta ta dau plates din indomie din ta fita parlor, duk a tsorace Shuraim yake, ta ajiye abincin hannunta tace “Zo nan” tasowa yyi ya nufota yace “Kiyi hakuri” tace “Wa yace ka fita?” ya girgixa mata kai yace “Ball nake nema” ta kara hade rai strictly tace “Ka taho da ball ne?” Nan ma ya girgixa kai a tsorace tace “Toh me mutumin yake gaya maka?” Yace “He is asking me my name and Sudais name, shine kuma yace wani class muke” kamar xai yi kuka ya kare, tace “Idan ka sake fita gidan nan I will flog you mercilessly, why can’t u be like ur brother Sudais?” Sudais dake kwance yace “Na ce masa kar ya fita but he refused, I don’t knw what’s wrong with him” Ta ce “Ka dai ji me nace maka, ka sake fita kaga abinda xan maka” ya gyada mata kai, ta dau indomie dinsa ta basa sannan ta dau na Sudais ma ta mika masa. Ana magrib ta ja su suka wuce daki bayan sun gama waya da Umma, suna yin isha duk suka kwanta saman gado suna ta mata labari tana biyesu har bacci ya daukesu gaba daya, tayi murmushi sanin karfin hali ne irin na yaro kawai banda haka uban tafiyar da suka yi tun yamma ya kamata su yi baccin ma. Washegari bayan sun yi sllh brush kawai ta masu suka fito parlor da pyjamas dinsu misalin karfe goma ta kunna masu cartoon, tana kitchen tana girka breakfast taji duk suna kiranta, ta fito parlorn da sauri jin irin kiran, khaleel ta gani tsaye parlon ya daga Shuraim dake turjewa yana kiranta tare da d’an uwansa dake kkrin ganin ya sakkosa duk da hannunsa bai kai ba, Shuraim yace “Anty kinga xai tafi da ni, nace masa A’a….” Khadijah ta daure fuska ta dai rasa abinda xata ce, Daya hannun Khaleel ya sa ya dauki Sudais da ke jan sa ya sauke masa d’an uwa shi ma ya daga sa sama ya juya ya nufi kofa da su suna kwala mata kira, Nanny ma ta fito tana kallon ikon Allah, har ya fita da su Khadijah bata ce komai ba, Nanny tayi murmushi tace to fa sai kace dole, ita dai khadijah na tsaye har lkcn, bayan wani lkci taji duk sun yi tsit, komawa kitchen tayi ta ci gaba da abinda take bbu walwala. Ta kalli agogo yafi a kirga don kusan awa biyu kenan da ya tafi da su har yanxu shiru kuma ko motsinsu bata ji, kasa daurewa tayi ta mike ta yafa mayafinta ta fita waje, a hankali ta murda kofar parlorn, xaune ta gansu gaba daya a parlor sun sa shi a tsakiya yana game a laptop, Shuraim na kwance kusa da shi bakin nan har kunne yana cin Burger yana nuna masa direction din da xai bi a game din, Sudais kuma na daga gefensu yana cin indomie da kwai yana kallon game din shi ma, duk suka juya suna kallonta, Shuraim ya bata fuska ya mike da sauri yana cewa “Antyyyy…. Ya ki ya bar mu mu wuce” Sudais ya jefa masa wani kallo a hankali yace “Stop lying pls” Hauri Shuraim ya kai masa da kafa yace “u re calling me a liar” Sudais ya ajiye abincin hannunsa ya mike kamar jira yake, Khaleel yyi saurin janye Shuraim, hakan kuma bai hana Sudais kai masa naushi a baki ba, tana ganin haka ta karaso da sauri a rude ta durkusa tsakankaninsu ta rike Sudais tace “Fadan xa ku fara yanxu…” Cikin kuka Sudais yace “He started 1st, why will he kick me” Shuraim dake nasa kukan shi ma yace “Why calling me a liar” Kamar xata yi kuka take kallonsa tace “Ba kai ka fara kick dinsa ba shuraim” Duk wannan abun Khaleel dake rike da Shuraim din yana kallonta, bai san lkcn da yyi murmushi ba ya jawo Sudais yana kallonsu a hankali yace “Toh ku yi hakuri” Duk suka ki cewa komai sai kuka, ya rungumesu gaba daya yace “Ohk, I don’t want to hear u both cry anymore” Sudais ne ya fara yin shiru sannan Shuraim, khaleel na kallonsu yace “To waye senior cikin ku?” Sudais ya nuna masa Shuraim, yace “Good, tell him u are sorry now” a hankali Sudais yace “I am sorry” Ya kalli Shuraim yace “Say it also” yana kumbure kumbure yace “But ai shi ya fara” Khaleel ya hade rai yace “Ba shi hakuri yanxu” a hankali Shuraim yace “Okay kayi hakuri” Khaleel yace “Good….” Kallon Khadijah yayi yace “You can’t just come into my apartment babu notice bayan ke ma ba son a shiga naki kike ba malama” wani kallo tayi masa ta mike ta fice daga parlorn. Har yamma tana ta xuba ido ta ga shigowarsu amma shiru, ta rasa yanda xata yi, Nanny ta tura ta dauko su wai xa su yi wanka, ba a dau lkci ba Nanny ta dawo tace “Kinji wai sun yi wankan” shiru Khadijah tayi don ta rasa abun cewa. Tana kitchen tana girkin dinner ta hango boys din a waje gun da yake xama yayi karatu da alama tare suka fito ya koma ciki shi, don ga textbooks dinsa da eye glasses a ajiye, kofa ta bude da sauri ta fito tana masu wani kallo tayi masu alamar da su xo su shiga ciki, tahowa suka yi ta shigar da su kitchen gaba daya sannan ta shiga ita ma ta kulle tana hararansu, Shuraim ya nuna mata wayar hannunsa a hankali yace “Anty na shi ne” kwacewa tayi tace “Maza ku wuce daki, bana son ganin ku ko a parlor” obediently suka wuce kamar yanda tace, ta bude kofar ta fita don ajiye masa wayarsa, dai dai lkcn da ya fito waje, ta ajiye da sauri xata bar gun ya jawota, xaro ido tayi jin ta a jikinsa ta kalli kitchen dinta da sauri tace “Meye haka kake yi malam ka sakeni” a hankali yace “Me yasa kika kora su ciki” taki cewa komai, ya juyo da ita tana facing dinsa, kin yarda su hada ido tayi don ko kadan bata son idonsa, ta shiga kokarin kwace kanta, ya jinginar da ita da bango yana kallonta, turasa tayi da karfi tayi kitchen dinta da gudu ta tura kofar ta rufe, jingina tayi jikin kofar gabanta na faduwa, a xuciyarta tace “Wannan mutumin fa dan iska ne da gaske” Fita tayi kitchen din, ta sa Nanny ta karasa mata girkin, ta dawo ta xauna gefen gado a bedroom tana kallon yaran dake ta hada puzzles xaune kasan carpet din dakin, kallonsu take ko kiftawa bbu, lkci daya ta tafi duniyar tunani iri iri a xuciyarta, bata san sanda tayi wani murmushi ba wanda xa a iya kira da na takaici hawaye ya xubo idonta, ko kadan bata san yaran sun ga hawayen ba, duk suka taso Shuraim ya kamo hannunta da damuwa yace “Anty are you sick?” Da sauri ta girgixa kai tana share idonta tace “Noo, idona ke ciwo” Sudais da har idonsa ya kawo ruwa yace “Toh Anty me yasa” jawosu tayi jikinta jin wasu hawayen sun taho mata, ta rungumesu trying very hard to control her self tace “I will be okay soldiers, xae daina yanxu” shiru suka yi gaba daya, bayan wani lkci ta janyesu a hankali ta mike tace “Xan yi alwala” daga haka ta shiga bathroom tayi kukanta me isarta har taji xuciyarta yyi sanyi sannan ta fito, ganin duk sun yo kanta tace “Ku je kuyi performing ablution” ba musu duk suka shiga bayin. Da wuri duk suka kwanta bayan sun ci abincin da nanny ta kawo masu har dakin. Washegari da ya kasance Saturday, bata tashi da ko wani damuwa ba kafin karfe tara har sun yi breakfast ta yi ma su sudais wanka, ita ma ta shirya don so take su fita xuwa gidan Vanessa ta dau motarta ta xaga da su gari kamar yanda ta yi masu alkawari jiya kafin su yi bacci, tana parlor tana goge veil dinta aka bude kofar parlorn, ta dago tana kallon direction din, tsaye yyi bakin kofar ya rungume hannayensa idonsa a kanta, tayi saurin kauda kanta, ganin ita kadai ce parlorn yasa ta fara kame kame gashi kananun kaya ne jikinta, kofar kitchen ta kalla tuna su Shuraim da tayi, sai a sannan ta tuna tun daxu suka je ajiye cup din cornflakes da suka sha a kitchen shiru shiru basu fito ba, Nanny dama tana daki, ya karaso cikin parlon cikin tafiyarsa ta kasaita, ta mike da sauri xata shiga kitchen yyi hanxarin preventing dinta, ta daure fuska tace “Meye haka ni ka kyaleni” yana kallon lips dinta da lumsassun idonsa yace “You’ve got cute lips” xaro ido tayi xata fixge hannunta ya jawota jikinsa a hankali yace “Tafiya na xo yi da twins” ta hadiye abu da kyar cikin rawar murya tace “Stop it pls ka sakeni, ni bani kadai bace a gidan nan” yace “In tafi da su?” Kai ta gyada masa, duk da haka ya ki saketa, taji ta kasa tsayuwa, kamar xata yi kuka ta rufe ido tace “Ni ba yar iska bace na hadaka da Allah ka daina min irin haka” A hankali ya saketa yace “Nima ba d’an iskan bane, just living a free life, ko kin taba kamani da wata?” daga haka ya nufi kitchen ta bi sa da kallo xuciyarta na bugawa, Tare ya fito da su Shuraim, bai kuma yarda ta hada ido da su ba, don sai kakkaresu yake, su ma basu yarda sun kallo inda take ba sai shigewa jikinsa suke har suka fita ya kulle kofar, duk da bacin ran da take ji hakan bai hanata murmushi ba, tana jin fitar motarsa daga gidan ta tabe baki ta dau veil dinta ta wuce daki tayi kwanciyarta.

    *Haske Writers Association*💡

    ✨ *Noor-Al-Hayat*✨

  • Noor Al Hayat 9

    Noor Al Hayat 9

    9……

    Sai kusan karfe biyar din yamma Khaleel ya dawo da boys din, da kayan wasa suka shigo mata ko wannensu baki har kunne, kana ganinsu kasan they are just happy, ta ajiye handout din hannunta tana kallonsu ta nuna masu hanyar bedroom alamar su wuce ciki, basu mata musu ba suka wuce, mikewa tayi ta isa kofa ta sa makulli sannan ta bi bayansu, tsaye ta samesu sun yi tsuru tsuru, ta hade rai tana kallonsu gaba daya tace “Ku gaya min daxun da ku ka je ajiye cup a kitchen me ku ka tsaya yi?” Duk suka ki cewa komai ko wannensu a tsorace, tace “Ba magana nake maku ba?” Sudais ya kalli Shuraim sannan yace “Anty mun ga uncle a waje shine ya xo wajen window yace mu fito, ni nace A’a, sai Shuraim yace xa ki mana duka” daga haka yayi shiru, ta kalli Shuraim strictly tace “Sai me ya far kuma?” Shi ma kamar xai yi kuka yace “Shine sai ya tambayemu inda kike sai Sudais yace kina parlor” shiru yayi shi ma, ta rungume hannayenta ta kalli Sudais tace “What now happened after that?” A hankali yace “He told us to remain in the kitchen he will come pick us…. And, shine kawai muka gansa ya shigo ya tafi da mu” tana kallonsu da kyau tace “Good… Next time baxa ku sake xuwa wajena ba kuma xan fadi ma Mumy duk abinda ku ka yi tunda bakwa ji” hawaye su ka fara yi suna bata hakuri, bata bi ta kansu ba ta yi fitowar ta parlor. Ranar lahadi Khadijah na kitchen tana dama masu custard kamar yanda suka bukata taji an danna kararrawa, kusan a tare da Nanny dake masu wanki a bathroom suka fito, ganinta Nanny ta juya ta koma, ita kuma ta sa hijab ta iso gun kofar, a hankali tace “Waye…” Yace “Kin sani” k’in bude kofar tayi tace “How can I help you?” Yace “In bude kofar kenan da kaina” shiru ta yi na ‘yan sakwanni kafin ta bude kofar, da sauri ta bar bakin kofar ganin shigowa xai yi kuma bai damu da cewar sai ya bugeta kafin ya shigo ba, yace “Where are they” ta hade rai bayan ta bar gun tace “Breakfast xa su yi” lkci daya duk suka fito daga dakin suka tsaya cirko cirko, sakin baki tayi tana kallonsu, arms akimbo ya tsaya kallonsu shi ma yana murmushi, can a hankali yace “Good morning boys” suka washe baki a tare suka ce “Good morning Uncle” yace “We’ve got 2 more places to go… So…” A hankali Shuraim yace “Noo we won’t make it up” ya buda ido yace “Why” duk suka kalleta, Khaleel ya kalleta shi ma sannan yace “What about her?” a hankali Sudais yace “Aunt was angry at us yesterday, she promise not to let us come over again for holidays” Buda baki tayi tana kallonsu, Khaleel yace “Ohk, haka kika ce masu” ta hade rai ta kallesa tace “Ni bance masu haka ba, they misunderstood me” yace “Ohk to fahimtar da su abinda kike nufi ynxu” ta kallesu tace “Oya ku bi sa ku tafi” Shuraim ya kamo hannunta yace “Sure Anty?” Ta dake tace “Yeah” rungumeta suka yi gaba daya da murna suna ce mata thank you aunt, Khaleel ya kama hannunsu suka fita yana murmushi, banging kofarta tayi bayan fitarsu rai a bace. Ba su tashi dawowa ba sai da daddare don ita har ta kwanta sbda takaici gashi gobe xa su koma, wato ba gunta twins din suka xo yin hutu ba wannan karan kawai, Nanny ce ta shigo daki da uban ledoji ta mike xaune tana kallon ledojin, rungume ta boys din suka taho suka yi da gudu ko wannensu na kokarin expressing kansa ya bada labarin abubuwan da ya faru, sai kuma suka sauka kasa suna bude mata ledojin, mamaki duk ya cikata ganin uban abubuwan da ya siya masu har da kaya da abubuwan makaranta, haka ta saki baki tana kallon ikon Allah, Nanny kam sai yabawa take tana shi masa albarka, ita dai bata samu bakin cewa komai ba har Nanny ta ja su ta masu wanka, bayan ta shirya su xuwa rigunan baccin su tayi masu tayin abinci suka ce sun koshi, daga haka suka kwanta bbu bata lkci bacci yyi gaba da su, Nanny ta wuce dakinta, sae a snn Khadijah ta samu kwarin gwiwar sakkowa daga saman gado tana kallon tsaraban cike da mamakin yanda ya san gobe xa su koma, bata kwanta ba sai da ta gama hada masu duk kayansu da za su koma gida da, taji har ta fara jin kewan yaran gashi bata samu lkcn su yanda take so ba. Washegari kafin karfe takwas har ta gama shiryasu nanny ma ta shirya, tana kokarin fita kira masu taxi aka danna bell, lkci daya kuma ya bude kofar yana mata kallon cikin ido a hankali yace “Morning” sauke kanta tayi wondering anya yasan abinda yace kuwa, don gaisuwa bai taba hada su ba, “Same to you” ta mayar masa, a takaice yace “Yaushe xa su wuce airport din” tace “Yanxun xa mu wuce” yace “Alryt, ina jiran ku” ta bi sa da ido bayan ya juya. Shi ya kai su har airport din a motarsa duk da bata so hakan ba amma twins suka gwaleta, suna isa duk jikinta yyi sanyi, yanxu fa komawa yaran xa su yi su bar ta, su kansu sai bata rai suke suna shisshige mata, shi ya rakasu daga karshe don ita kam kasawa tayi, sae d’aga mata hannu yaran suke, kasa daurewa tayi bayan tafiyarsu ta hade kai da gwiwa a inda take xaune, bayan kusan minti goma Khaleel ya dawo, muryarsa taji yace “Heyy” ta dago kanta a hankali, ya d’an bude ido yace “Waow, kuka kike?” da sauri ta goge idonta don bata san ma tana yi ba, yyi murmushi yana shafa kai yace “Su ma kinga kukan suke, Ashe sun ji a jikinsu kina kukan ne” tashi tayi da sauri tace “Kuka suke?” yace “Yea but I made sure sun yi shiru before I left, the bond between u and ur Siblings is really amazing….” daga haka ya fara tafiya yace “let get home” bin bayan sa tayi a sanyaye har suka isa gun motar sa, a hankali ta sa hannu ta bude front seat ta shiga, babu wanda yace komai cikin su yana driving, tsaki yyi bayan wani lkci ya jawo wayarsa dake ta ring tun fara driving dinsa yyi silencing wayar ya ajiye, ita dai tayi nisa tunanin da take na su Shuraim, yana gama parking a gida murya can kasa tana wasa da yatsunta a hankali tace “Thank you very much, Allah ya saka da alkhairi” kamo hannunta yayi yace “For?” Ta fixge hannunta hade da galla masa harara daga haka ta bude motar ta fita ta nufi flat dinta ya bi ta da kallo ta madubi. Tun da ta shiga bedroom dinta take bacci har azahar, biyu da rabi ta tashi ta shiga bayi ta wanke baki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana gabatar da sllhn zuhr ta shiga kitchen don neman abinda xata ci, ko ba a fadi mata ba tasan ita kadai ce gidan coz everywhere was very silent, ta gama cin abinci ta dau materials din karatunta don rabonta da karatun tun xuwan kids din, gashi yau ma tana da lectures bata je ba, sai sha biyu saura na dare ta hakura da karatun ta kwanta don gobe da safe take da lecture. Washegari takwas saura ta fito xata wuce makaranta, dai dai fitowarsa shi ma, suna hada ido tayi saurin dauke kai ta kara pace dinta, kafin kuma ya fito da motarsa har ta hau taxi abun ta. Karfe uku da wani abu suka fito school tare da Vanessa da Angela, sauraren Vanessa dake mata korafi ta gama yi kafin tayi ‘yar dariya da halshan turanci tace mata ba wai ta fasa xuwa bane xata dawo gidan nata amma sai during weekend, ko da wasa bata nuna mata su shuraim sun xo ba balle ta sake jin haushin rashin kawo su da tayi, juyawa Khadijah tayi tana kallon direction din da Angela da Vanessar ke kallo, sai a snn ta ga motar da ya tsaya gefensu dai dai lkcn da kuma ya sauke glass, hannu ya daga ma su Vanessa a hankali yace “Hi” suka mayar masa da “Hello” Ya kalleta yace “Are you heading home?” Tunani ta fara yi shi kuma wannan yaushe suka fara yin haka da shi, wani kallo tayi masa tace “Noo thank you” wani murmushi yyi yana shafa millionaires belt dinsa yace “Ohk a gaban kawayen naki xaki ce min A’a” Tace “Ka saba daukata ne?” Yace “Xan fara yanxu, shiga mu je” tabe baki tayi bayan few seconds ta kalli su Vanessa tace “Alryt, see you girls tomorrow” daga haka ta xaga ta bude front seat ta shiga ta kulle kofar, daga masu hannu yyi ya ja motar suka bar gun, basu yi tafiya me nisa ba yace “Twins sun isa lafiya?” Ta gyada kai tace “Sure” wayarsa dake ajiye kusa da ita yyi haske ta sauke kai tana kallon screen din, “Jawahir” sunan dake saman screen din kenan ta dauke kanta, bayan seconds kusan biyar ya dau kiran yace “Am driving baby, xan kira ki when am home” daga haka ya katse wayar ya mayar ya ajiye, suna isa gida yyi parking ta bude motar ta fita ta rufe ta nufi apartment dinta, xaro ido yyi ya bi ta da kallo.

    Washegari Tuesday da yamma ta shirya bayan ta dawo makaranta don xuwa shopping mall ta yi shopping din turarurruka da man shafa, karamar jakarta ta sakale kafadarta ta fito ta rufe apartment dinta, ganin motarsa a parking space yasa ta gane yana nan don tun da ya ajiyeta jiya rabon da su hadu, babban shopping complex ne wajen ta gama daukan mayuka da turarukan da xata dauka, tayi deciding hadawa da disinfectant da antiseptics, Dettol babba ta dauka bata lura da mutumin dake bayanta ba kamar yanda shi ma din da alamar bai lura da ita ba don backing din juna suka yi, lkci daya suka juyo kusan a tare suka ci karo, pack din Sabulun dettol dake hannunsa ya fadi kasa, da sauri suka durkusa kusan a tare again ta rigasa daukan sabulun kafin ya kai hannunsa tace “Ohh sorry pls, I…i…” dai dai sanda suka mike tsaye ido cikin ido, shekaru kusan hudu kenan rabon da ta ji abinda taji a xuciyarta lkcn, a hankali ta saki dettol din hannunta tana kallonsa bbu kiftawa, wani kallo shi ma yake mata da wani expression, yana son magana amma da alama words din sun kasa fitowa, lkci daya words din yyi escaping lips dinsa cikin wani yanayi yace “IMANN….” Juya masa baya tayi tana ganin turawan da ke d’an nesa da ita doubled doubled, kawai ta nufi kofar fita complex din, tana jin yana kiranta da alamar bin ta yake ta kara saurinta, cikin sarkewar murya tace ma baturen gun ta mance ATM card dinta a gida yana bude mata kofa ta fice fittt without thinking twice ta nufi bayan mall din kamar xata tashi sama, ta xauna nan kasa jikin bango ta kai hannu dai dai kirjinta ta runtse ido, ta fi minti sha biyar wajen xaune, ji take kamar an mata alluran tsayar da Adrenaline ne don komai na jikinta gani take ya daina aiki kamar ba nata ba.

    *Haske Writers Association*💡

    ✨ *Noor-Al-Hayat*✨

  • Noor Al Hayat 6

    Noor Al Hayat 6

    6……

    *Nigeria*

    Ajiye fork da knife din hannunsa yyi ya tura abincin gabansa lkci daya ya fuzar da iska ya dau tissue yana goge bakinsa ya mike ya bar dinning din, mum dinsa dake xaune parlor ta bi sa da wani kallo tace “Barin abincin kayi sbda xancen da nake maka Aliyu?” Kallonta yyi da sauri yace “Noo, not at all Mum, xan je sallama da Granny ne coz am leaving as early as possible tomorrow” daga haka ya dau makullin motarsa da ya ajiye kan Center table ya nufi kofa yace “Sae na dawo mum” tagumi mahaifiyar tasa tayi ta bi sa da kallo cike da damuwa har ya fita, ya fuzar da iska bayan ya shiga motarsa ya jinginar da kai jikin kujera hade da lumshe ido yace “Ba ta taba barin in ci abinci in koshi Mum, always with a particular complain” ya bude ido a hankali snn ya tada motar yyi horn mai gadi ya bude gate ya fita rai ba dadi, bai yi minti goma yana tafiya a Independent way ba wata 206 dake gabansa ya taka wani burki da har sai da ya kusa bugesa ba dan shi ma yyi saurin preventing hakan ba, wanda hakan kuma ya janyo motar dake bayan tasa motar ta buge sa, Kilan rudewa ya sa me 206 din ya juye kan steering wanda hakan yasa ya buge motar gefensa shi ma da karfi, everything just happened all of a sudden, lumshe ido Aliyu yyi ya bude yana kiran Allah a xuciyarsa bayan komai yyi still kamar ba ayi ba, sai a sannan ya lura da wani bike ne ya shigo ma mai 206 din yyi kkrin avoiding da ya janyo faruwan slight accident din, Aliyu ne ya fara fitowa daga motarsa daga nn kuma kowa ma ya fara fitowa, ya nufi 206 din da har driver din ya fito da sauri ya bude back seat, kukan yara ke tashi a motar, jin hakan Aliyu ya karasa da sauri gun motar, identical twins ne bayan motar da baxa su wuce shekaru biyar ba, Aliyu ya fiddo su duk biyun daga motar yana kallon yaran dake sanye da uniform din makaranta ya durkusa a hankali yace “Hey boys are you okay??” Dayan kadai ne ya gyada masa kai a tsorace, dayan kuwa banda kuka babu abinda yake yana kiran Anty, kallon yaran kawai Aliyu yake ko kiftawa bbu, muryar mutanen da ke tsaye gun kowa na fadin albarkacin bakinsa yasa shi mikewa a hankali yana shafa kansu yace “Sorry Boys, Allah ya tsare gaba” Wani mutumi ne ya dinga tambayarsu inda ke masu ciwo duk suka girgixa kai, Aliyu ya daga kai jin abinda mutumin da ke gefensa ke ce masa yana kallonsa, “Allah dai ya kiyaye gaba ka tafi da yaranka gida kawai, Allah kyauta na gaba” cewar mutumin kenan, wani mutumi ma ya sake fadin makamancin hkn, murmushi yyi yace “No, ni ban san su ba” mutumin karshe da yyi magana ya kalli yaran sannan Aliyu, kada kai yyi yace “Ikon Allah….” bude bayan motar Aliyu yyi ya shigar da yaran yana kallon Drivern yace “Ka ajiye su gida, Allah ya kiyaye gaba” godiya Drivern yyi ma mutanen wajen ya shiga motar ya tada ya hau kan titi ya bar wajen. Aliyu ya koma gun motarsa ya shiga har lkcn cute twins din na ransa, bai kuma damu da kallon da wasu suka bi sa da shi ba. A waje yyi parking ya shiga gidan grandmum dinsa da sallama bayan sun gaisa da masu gadi, wata budurwa ce da baxata wuce shekaru ashirin da daya ba kwance kan kujera dake parlon tana danna waya, sau daya ya kalleta bai sake kallon inda take ba ya wuce dakin grannynsu da suke kira da yaya, sllh ya sameta tana yi ya kalli agogo sanin Magrib bai yi ba, ya tabe baki ya dawo parlon ya xauna ko sallan me take, ba a dau lkci ba ta biyosa tace “Mijin ka xo kenan” ya gaisheta ta amsa da fara’a tana tambayarsa ya hanya, yace “Alhmdllh” ta kalli budurwar dake kan kujera tace “Ke koh Salmah kun gaisa da yayan naki” yarinyar ta gyada mata kai idonta a kan waya, ya kalleta fuskarsa daure yace “Uban wa kika gaida?” Ba ta ko kallesa ba tace “Yaya ni ki ce ya daina xagi na plss” Mikewa grandmum din tasu tayi tace “A’a ni dai gaskiya ba a gidana ba yau, ku je can gidan iyayen ku ba ruwana, kai kuma naga ai ba dole bane sai an gaisheka, ke kuma sa’an ki ne shi din da baxa ki gaishesa ba” mikewa yyi ya nufi kofa, kakar ta bi bayan sa da sauri tana cewa “Ina kuma xaka Aliyu” bai juyo ba yace “Sallama dama na xo maki gobe xan wuce Uk….” da sauri take bin sa ganin yaki tsayawa tace “Toh baxa ka tsaya ba ina ma magana” yace “Mu yi waya” bata fasa bin sa ba tana cewa “Da kai fa nake Aliyu…” juyowa yyi yace “Don Allah yayah ki rabu da ni dama sallama na xo maki kuma gashi na maki dai ko” rike ha6a tayi tace “Yo ni me ya sha min kai da sallamar ka da rashin sa, magana ce dai baxan fasa maka ba tunda ba tsoronka nake ba, baka kuma isa inji tsoron ka ba, kum maganar dai da baka so ce xan maka wato maganar aure, Aliyu sa’annin ka daga me d’an shekara biyar sai mai d’an shekara shidda kai har bakwai akwai, yanxu kai baxa kayi ma kanka fada ba kasan inda ke maka ciwo d’an nan, ga mahaifin ka ya xuba ma na mujiya ya kyaleka ya fita lamarin ka, me kake son mayar da rayuwar ka ne, idan ma lafiya ce baka da ba sai ka mana bayani ba ko ni in kai ka asibiti amma ka mayar da mu shashashai….” tsaye yake yana saurarenta sai dai bai juyo ba har ta kai karshe sannan ya juyo yana kallonta yace “Allah kawo lkci yayah” daga haka yyi ficewarsa daga gidan, ya jima xaune mota ya kasa barin anguwar, ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido a hankali ya bude cikin sanyin murya yace “Can I ever get her? Then Where?” Lkci daya idonsa ya kada ya hade kansa da steering, ya fi minti goma a haka kafin yyi karfin halin dagowa ya tada motar ya bar gun jikinsa a sanyaye, yana hawa independent way yaran daxu suka fado masa, ya d’an yi murmushi loving to see them once more and their parents. Bai yarda ya wuce gida ba a lkcn kawai ya wuce gidan abokinsa kuma amininsa Farouq, ganin Magrib tayi sai da ya fara shiga masallacin dake anguwar don gabatar da magrib bayan yayi alwala, ana idarwa kuma suka fito tare da Farouq, gaisawa suka yi Farouq yace “D’an rashin kirki kace min xaka dawo ranan kasa Madam tayi serving har da kai amma kaki dawowa, ina ta xuba ido, I called kuma you refused picking saboda kasan baka da gaskiya koh” Aliyu ya shafa kansa yana murmushi yace “Na ma mance me ya hanani dawowa wllh” har suka shiga gida mitan xancen Farouq yake, suka karasa har parlor, Boys din Farouq suka taho da gudu don gaida abokin dad din nasu, Aliyu ya rungumesu yana tambayar su ya school suka ce masa “Alhmdllh” Wara ido yayi yace “Toh ban ga “Baby Fiddausi ba” Ahmad yace “She’s upstairs with mum” yace “Alryt maxa ku je ku ce masu Ina gaishesu” Ahmad me shekara shidda da kaninsa takwaran Aliyu suka wuce daki da sauri. Farouq dake ta kallon Aliyu yyi kasa da murya yace “Doctor….” Kallonsa Aliyu yyi da sauri, Farouq yace “I don’t knw, may be am nt worth ur best…” Aliyu ya d’an bude ido yace “Ban gane ba Umar” Farouq ya girgixa kai yace “Kullum tambayata why did you prefer living as a bachelor ka ki bani answer, what’s ur problem Aliyu, am I not worth knowing ur problem, I would love seeing ur kids Frnd duk clique dinmu kai kadae ne Bachelor har ynxu, tell me why… I beg you…” Kallonsa kawai Aliyu yake can yyi murmushin karfin hali ya kauda kai yace “Xan yi Farouq, lkci ne kawai” a d’an fusace farouq yace “Na gaji da jin haka Ali.. For good six years this is always ur reply, kudin gashi kana da su Alhmdllh, yan matan gasu kawo maka hari suke ta ko ina…. Toh meye kuma yayi saura??” Aliyu dai bai ce komai ba sai danna wayarsa da ya fiddo yake, farouq na masa wani kallo yace “Ko Iman din dai kake jira har yanxu, I mean aljanar nan taka…” Aliyu ya dago da sauri hade da yin murmushin da ya fiddo da ainahin kyansa na fillo ya karyar da kai yace “Yeah” tsaki farouq ya ja yana girgixa kai cike da takaici, Aliyu ya dafe shoulder dinsa a hankali yace “Look frnd, wllh ba aljana bace mutum ce kamar ka, ka bar ce mata aljana” Farouq yace “Toh wai ni abinda ban gane ba a nan shine ita ta san ka?” Aliyu ya sauke manyan idanuwansa daga kallon abokin nasa a hankali yace “Yea may be tasan ni, may be kuma bata san ni ba” Wani dariya Farouq yyi har da kyakyatawa yace “Wllh baka da hankali Haiydar, wato bata ma san ka ba?” Murmushi kawai Aliyu yyi yana shafa cute beard dinsa bai dai ce komai ba, Farouq yace “To what if tayi aure? Ko kuma tana da aure?” Murmushin fuskar Aliyu ya bace lkci daya ya mike a fusace yace “Billah sai ya saketa ko ma waye shi… Na rantse da sarkin dake busa min numfashi xan iya kashe ko ma waye ya aureta” sakin baki Farouq yyi da mamaki yana kallonsa, yana kikkiffta ido yace “Aliyu are you alright kuwa, wani irin rantsuwa da threat ne haka, anya kana right sense din ka kuwa” Ko kallonsa Aliyu bai yi ba ya nufi kofa, Farouq ya mike da sauri ya rikosa yace “Habaa, Toh Allah baka hakuri, let eat plss, In sha Allah ma Iman bata yi aure ba duk da ni dai billahil azim ban yarda ba aljana bace” yana magana ne yana satan kallon Aliyu da har lkcn fuskarsa ke daure, da kyar dai ya samu ya lallabasa ya dawo ya xauna, Aliyu ya lumshe ido yace “In kaji wacece Iman din nan xa kayi mamaki Umar” Farouq yace “Toh don Allah ka gaya min wacece” A takaice Aliyu yace “Noo baka santa ba, bata sanka ba, kilan ni kadai na santa” dariya sosai Farouq yyi yace “Ko da yake gogan ma bai san ko ta san shi ba balle ni, wllh you look confused Aliyu, Allah ya yaye maka wannan bala’i” Aliyu ya kallesa yace “Plss xancen Iman da muke ya tsaya iya nan kar ko da wasa wataran kaje can gida kana cewa Iman” Farouq yace “Why, ko sun santa?” Aliyu ya girgixa kai yace “A’a kawai dai kar ka sa a daukeni mahaukaci ne” Farouq ya jingina kai yana murmushi yace “Hauka kam ka jima da fara sa ai frnd”

    *Haske writers association*💡

    ✨ *Noor-Al-Hayat*✨

  • Sakayyah Book 2 Page 27

    Sakayyah Book 2 Page 27

     

                        By

    *GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2… Page 27*

     

            Na

    *Aysha Aliyu Garkuwa*

     

    Ido suka zuba kan gadon
    dake hargitse ga jini dake kai sai rigar baccin Khausar da suka gani
    gefen pillow.

    Sai kuma suka kalli juna da mamaki gami da tausayin,

    Ummi kama tuni hawaye ya cika mata ido a hankali tace.

    “Toh ina take?.”

    Da sauri Aunty Hajara ta rumtse idanunta ganin yadda beshid ɗin
    ya ɓaci da jini, musamman wannan farin ƙyalle mai  heart dake tsakiyar gadon.

     

    Da sauri ta jujjuya kanta sai kuma ta ta kalli ƙofar
    Bathroom ɗin sabida jiyo mgn can ƙasa-ƙasa
    da sauri tace.

    “A’a Ummin Jameel kinji fa kamar mgn a cikin Bathroom
    dinsu”.

     Sai kuma duk sukayi
    kasake alamun kasa kunne cikin mmki Ummin ta sauƙe numfashi tare da cewa.

    “Ai kamar ma muryar Babane a ciki”.

     

    Shi kuwa Modibbo da duk saurin Didi ya rigasu, iso kuma da
    suka zo basu shiga cikiba iyakar Jakadiya ma falo, shiyasa basu san ya dawo ba,
    a zatonsu yana Masallaci kamar yadda haka al’adarsu take kafin ango ya dawo
    salla biyu daga cikin ƴan uwanta da dole al’adar masarautarsunce in an kawo
    amarya ma sai an bar mata biyu, masu maidawa iyayen yarinya tukuici in ta kawo
    budurcinta da kuma kai hatimin mulki da za’a mallakawa mata shaidar
    kasantuwarta Gimbiya kenan.

     

     Toh koda ya dawo
    kawai ciɗak ya ɗagata ya nufi Bathroom da ita, yana shiga ya direta cikin ruwan
    ɗumin daya haɗa mata, tun kafin ya tafi.

     

    Jin yadda zafin ruwan ke ratsata ne yasa take yayyarfa
    hannunta tare da sakin raunataccen kuka murya adisashe.

    A hankali ya ɗan tallaɓe kanta tare da mannawa da ƙirjinsa
    cikin sanyi mai cike da bayyanar asalin matsayinta dake cikin zuciyarsa yace.

    “Sannu kiyi haƙuri ki zauna zakiji sauƙin ciwon sosai”.

    Ya ƙare mgnar da dan ƙara zaunar da ita cikin ruwan ɗumin,

    wani raunataccen ƙara ta kuma saki wanda yasa har Jakadiya
    da Didi dake falo suka jiyota, cikin sauri Jakadiya ta kalli Didi tare da cewa.

    “Inaga sun ɗagata bari mu ɗauko ƙyallen tarihinmu da zanin
    gadonmu”.

    Kai kawai Didi ta gyaɗa mata.

     Allah yasani ji take
    kamar ta shiga to amman ba dama tunda Ita dai surkuwa ce.

     

    A can cikin ɗakin kuwa Ummi da Aunty Hajara kam bushewa
    sukayi a tsaye kamar wasu sakarkaru, suke kallon ƙofar Bathroom ɗin fuskoki
    cike da mamaki.

     

    Da sauri suka juyo suka kalli ƙofar jin a buɗe Jakadiya da
    yanzu ta shigo, kwaryan dake hannunta ta miƙa Ummi tare da cewa.

    “Gashi ta zauna ciki ammafa kada ta wuce 2 minute”.

    Toh Ummi tace tare da amsa kana ta ajiye ƙwarya, sai kuma ta
    kalli Aunty Hajara dake ruggume da hannun.

    “Inaji mafa kamar tana tare da mijinta ne a Bathroom ɗin.”

    Aunty Hajara ta faɗa.

    Murmushi Jakadiya tayi tare da cewa.

    “Ato shike nan ai ni bari in na ɗe…”

    Sai kuma suka kalli ƙofar Bathroom jin kamar an buɗe, shi
    kuwa Modibbo jin alamun surutaine yasa ya ɗan miƙe tsaye kana ya buɗe ƙofar dan
    yaji surune da gaske akeyi a ɗakin.

    Da sauri yayi ƙasa da kanshi ganin Ummi.

    Ita kuwa Ummi cike da kunya ta miƙa mishi kwaryar nan da
    Jakadiya ta bata tana mai kauda kai tace.

    “Gashi ta zauna ciki, Amman kada ta wuce daƙiƙu biyu”.

    Cikin tsaanin kunya yayi ƙasa da kanshi tare da amsar
    kwaryar, ya juya cikin Bathroom ɗin da sauri ya maida ƙofar ya rufe ba tare da
    yace komai ba kana bai bari sun haɗa idoba.

    Itama Ummi cikin
    kunya ta kama hannun Aunty Hajara suka fita.

    Jakadiya kuwa murmushi mai cike da jin daɗi tayi, tare da
    shimfiɗa wani farin leda mai taushi a gefen gadon zai kuma ta ɗan jawo  wannan farin ƙyalle mai zanen heart ta
    sanyashi cikkn ledan kana ta maida shi ta liƙe ya zama kana iya ganin duk jinin
    dake jikin ƙyallen sai kuma ta sa hannun ta ɗauko wani ɗan bugeggen katako  mai zagaye da gold a jiki, kana an yishi da
    marfin glass daga saman an Rubuta MRS Aleeyu
    Mouleey, da manyan baƙin larabci.

    Sai a ƙasan kuma aka rubuta. Lalla Khausar.

    Cikin ta shimfiɗa ƙyallen tare da maida marfin glass ɗin ta
    rufe, sai ya zama tamkar abun aje hoto, sai kuma daga ge da gefensa da ke ɗauke
    da tambarin masarautar Mouley ɗin.

    Cikin sauri-sauri ta naɗa beshit ɗin kana ta zaro wani fari
    mai ɗauke da alamun zanen masarautarsun ta shimfiɗa tare da sa rigunan pillow
    da blanket.

    Sai kuma ta ɗaukesu tare da fitowa falo da sauri.

     

    Tana fita Lalla Khadijah na isowa da kaskon turaren wuta,

    Da sauri ta miƙa wa Didi wannan furem ɗin ƙyallen da kuma
    sanin gadon, cike da jin dadi Didinta amsa ita kuwa Jakadiya, amsa kaskon
    turaren wuta  tayi ta koma ɗakin ta
    ajiye.

    Gefen gado kana ta jawo ledan nan, ta fito da wata dandatstsiyar
    Alƙyabbata irin ta matan masarautar Mouley ɗin, sai kuma wata tattausar riga
    mai gajeren hannun, dukansu kolon tutar masarautar sune sai fararen ondis.

    Turarukan data kawo tajera gefen kayan.

    Sai kuma ta juya ta koma falo bayan ta ƙarasa kimtsa ɗakin.

     

    A nan cikin Bathroom kuwa, cikin wani irin fitinennen kallo
    Modibbo ke kallon Khausar da ta tura lip inta na kasa tare da kwaɓe fuska, har
    lau hawaye na tsiyaya, cikin sanyi ya ɗan tallabo kanta  da hannunsa duka biyu, manyan yatsunshi yasa
    tare da fara goge mata hawayen, murya cike da taushi, tausayi, gamin da jinƙai
    yace.

    “Kiyi haƙuri ko, kin yafewa Yah Mu’allim dinki ko?”. Cikin
    Shesh-sheƙan sabida jin yadda zafin ruwan ke ratsa mata jiki, ga wani irin
    fitinennen zazzaɓi da ciwon kai da sukayi mata taron dangi, murya a disashe
    tace.

    “Allah zai saka min”. Da sauri ya kauda kanshi gefe jin
    murmushi na gaba da subce mishi, ita kuwa kuka ta ɗan saki tare da cewa.

    “Ai dama na gayawa Ummi haka zakayi ta cin zalina amman suka
    ki yarda, Allah zai saka min”.

    Cikin sanyi ya ɗan tsuke fuska kana yace.

    “Zo nan, zo ki shiga cikin wannan inji Ummi”.

    Da sauri ta rumtse idanunta jin ya tallabota ya ɗagota, sai
    kuma yayi saurin ruggume ta, jin yadda ta saki wata ƙara mai cike da alamun
    galabaita.

    A hankali ya zaunar da ita cikin kwaryar.

    Da ƙarfi ta saki ƙara tare da cakumo wuyanshi ta matseshi
    gam a jikinta da yake rawa kar-kar sabida zafi gami da raɗaɗin da jininta ya ɗauka.

     

    Rumtse idanunsa yayi da ƙarfi dan ba ƙaramar shaƙa tayi
    mishi ba, sai kuma ya fara sauƙe ajiyan zuciya jin ta fara sassauta cacumar da
    tayi mishi, ido ya zuba mata jin yadda take ta sauƙe ajiyan zuciya a jere a
    jere, sai kuma wani irin fitinennen zufa daya keto mata tako ina a jikinta.

     

    Lumshe idanunta tayi tare da jingina kanta da ƙirjinsa.

    Tana mai ci gaba da sauƙe numfashi, a hankali yace.

    “Da sauƙi ko?”.

    Bata kulashi ba, sai idanunta dake rufe domin duk abinda
    yake mata bata buɗe idanunta ba.

    Sai yanzu da taji ya ɗagota cak daga cikin kwaryar da sauri
    ta buɗe idan, sai kuma ta rufesu ganin shima ita yake kallo, ɗan murmushin
    gefen baki yayi tare da cewa.

    “Toh kiyi niyan wankan tsarki”.

    Bata kulashi ba, shi kuwa a hankali ya koma gefen bakin
    bathtub din ya zauna.

    A hankali ta buɗe idanunta tare da ɗan kallon ƙofar fita,
    sai kuma tayi saurin cewa.

    “Ni ka daina kallona kuma, ka fita zanyi wanka”.

    Bakinshi ya ɗan motsa bata dai ji me yaceba, ta daiga ya
    rufe idanunshi alamun bazai fita ba kena, ganin haka yasa tayi niyan wankan,
    tare da fara yin wonkan a suffatul ijjiza, kawai ruwa ta sakarwa kanta.

    Daga zaune ta gama wonkan, kana tayi al’wala, a hankali ta
    yunƙura ta tashi tsaye ga mamakinta kaso 65 ɗari na zafin da takejin ya tafi.

    Zafin da takejin ya tafi har wani tsukewa taji jikinta yayi.

    Sai kuma tayi saurin da hannunta ta kare ƙirjinta ɗaya
    zubawa idanu, da sauri kuma ta maida hannun nata ƙasa ganin yadda ya tsura
    wurin ido.

    Shi kuwa towel ya jawo tare, da rufe matashi kana ya dauketa
    suka fito.

    Bisa bakin gado ya ajiyeta, sai kuma ya jawo kujerar dressin
    mirror d mai a fabanta ya zauna.

    Tare da lakatan mai ɗin ya murza a tafin hannunsa kana a
    hankali ya fara shafawa ƙafarta.

    Ita kuwa cikin sanyi da rawan jiki tace.

    “Yunwa nakeji”.

    Yana mai ci gaba da shafa mata mai ɗin yace.

    “Toh acici kazar birni, ai ni ya kamata inyi kukan yunwa
    nida kika kwana ƙwaƙulewa”.

    Cikin mamaki ta zuba mishi ido tare da mgnr zuci.

    “Motar sherri”.

    Ga mamakinta sai ji tayi yace.

    “Ni ne motar sherri”.

    Da sauri ta jujjuya kai, tare dacewa.

    “A’a da kaina nake”.

    Hannunta ya kamo ya shafa mata mai ɗin kana ya juya ya gaban
    dressin mirror yana mgna cikin ranshi.

    “Komai ma ki, kirani zan amsa, tunda nayi laifi”.

    Da sauri ta dauki pant ɗin dake gefenta ta saka.

    Sai kuma ta jawo tattausar doguwar rigar nan.

    Ta zura, hannunshi yasa ya jawota tsaye, tare da ɗaukar
    alƙyabar nan.

    Ya zira mata.

    Sai kuma ya dawo ta gabanta tare dasa hannunshi kan caɓullenta
    ya ɗan matsa a hankali da sauri ta rumtse idanunta.

    Sai kuma ta fara jujjuya kanta jin abinda yace.

    “Yau ma suna miki ƙaiƙayin ne, in sosai miki”.

    Murmushi ya ɗanyi ganin yadda gaba ɗaya jikinta ke karkarwa.

    Turarrukan ya fesa mata kana yasa mata hulan rigar sai kuma
    ya jawo hulan alƙyabar ya rufe mata kanta.

    Bisa sallaya ya jawota.

    Ita kuwa idanunta ta rumtse da karfi sabida yadda in ta daga
    ƙafarta zafin ke ɗan tsargarta.

     

    A hankali ya dawo bakin gado tare da cewa.

    “kiyi salla”.

    Ya ƙare mgnar yana dafe kanshi da hannun bibbiyu da shima
    zazzaɓin yakeji da ciwon kan da yasan rashin baccine ya jaza mishi.

    A hankali ta miƙe tsaye bayan ta idar da sallan

    Dai-dai lokacin kuma Jakadiya tayi sallama, ɗan tsaki yaja
    tare da amsa sallamar kana ya mata izinin shigowa.

     

    A gefe ta rusuna cikin girmama ta gaidashi ba tare da ya
    kalleta ya amsa.

    “Bisa umarnin Didi tace Lalla Mouley tazo mu tafi wurinsu
    Ummin Jameel”.

    Ta fadi tana kallon Khausar, tare da tura kaskon turaren
    wutan da ta shigo dashi a hannunta da kuma wata ƴar ƙaramar kwalba dake cike da
    turaren wutan tsuguno na musamman.

    Shi kuwa Modibbo. Cikin tsuke fuska yace.

    “Uhm”. Ita kuwa hannun ta miƙa Khausar tare da cewa

    “Ki tsuguna ki turara jikinki da turaren wutan nan, sai mu
    tafi.

     murya na rawa Khausar
    tace.

    “Bazan iyaba”.

    Da sauri Jakadiya ta juya ta fita jin Modibbo yace.

    “Kije zan kawota”.

     

    Tana fitowa falon ta gaya musu yadda sukayi hakan ne yasa,
    duk suka fita Ummi da Aunty Hajara suka koma masauƙinsu, Didi da Jakadiya da
    Lalla Khadijah kuma suka nufi kasan.

     

    Dai-dai lokacin kuma Lalla Hafsat da Rahama dake kitchen da
    kansu suka shiryawa Khausar breakfast mai rai da lfy, wanda natane ita kaɗai,
    sai kuma na Abualeey da Modibbo da suka shirya da ban sai kuma nasu duka.

     

    Shi kuwa Modibbo a hankali ya miƙa tare da kallonta jin tana
    cewa.

    “Zan faɗi”.

    Hankali ya jawota jikinshi ya ruggume mata tsam, cikin sanyi
    ya cusa kanshi a wuyanta yana mai shaƙan daddaɗan ƙamshin jikinta,

    Bakin gado ya ajiye ta, kana ya dawo ya ɗauki kaskon da
    turaren wutan, ya ajiye gefenta ta inda zai zauna tattare jallabiyar jikinshi
    yayi ina ya zauna, hannunshi yasa ya kamo nata tare da jawota gaban shi, cikin
    karkarwa da rawan murya tace.

    “Ƙafafuna rawa suke bazasu iya ɗaukata ba“.

    Kanshi ya ɗan ɗago ya kalleta sai kuma ya ɗan sunkuyo
    turaren wutan ya danga mai ɗan yawa ya zuba a cikin kaskon, sai kuma ya jawota
    gaban shi sosai tare da sa hannun ya ɗan buɗa sawunta, da sauri ya yawota gaban
    shi sosai hannunshi ɗaya yasa ya tallabo ƙugunta, kana ya manna kanshi da
    cikinta yayi mata Garkuwa Da kyau dan ya lura zata iya faɗin.

    Da sauri ta rumtse idanunta tare dasa hannunta ta kamo
    hannunshi ɗaya da taji ya zira cikin rigar ta yana jan pant ɗinta yanayin ƙasa
    dashi.

    Jin yadda ta riƙe mishi hannun ne yasashi ɗan jujjuya kanshi
    murya a tausashe yace.

    “Ki bari in cire shi, hayakin zaifi shiga jikinki da kyau
    yayi miki aiki“.

    Ya ƙare maganar da yin ƙasa da shi baki ɗaya.

    Sai kuma yasa sawun shi duka biyu tsakanin nata sawun.

    Wanda haka yasa dole ta zare ƙafarta ɗaya, sai kuma ta saki
    ƙara da ƙarfi jin ya ware sawun nashi da yasa dole ta zauna kan cibiyoyinsa,
    manna kanta tayi da ƙirjinsa tare da rufe udanunta hawaye na kwaranyo mata
    sabida zogin da takeji.

    Shi kuwa Modibbo cikin sanyi ya ɗan sunkuyo tare da gyara
    zaman kaskon sautin jikinta sai kuma ya tattare rigar nata ya buɗashi ya
    bazashi bisa guiwowinshi ya zamana ta zama ba komai a jikinta ta ƙasan, sai
    kuma ya ƙara ɗanƙo turaren wutan ya saka a ciki.

    Ai ko kai tsaye kan jikinta hayakin ke tashi, a take ta fara
    sakin numfashi da ajiyan zuciya sabida wani irin daɗin da taji a jikinta sai
    kuma ta lumshe idanunta sabida jin yadda jikinta ke mata wani irin daddaɗan
    ƙaiƙayi alamun ciwon na workewa ne, bisa ƙarfin magungunan dake cikin turaren
    wutan.

    Numfashi mai sanyi ta fesar tare da ɗan buɗe idanunta.

    Idonta ta ɗan zubawa lips inshi da yake ɗan motsawa alamun
    mgn yake sonyi, kuma mishkilanci ya hanashi, fahimtar hakane yasa ta ɗan tura
    baki tayi tare da hararanshi ta ƙasan ido.

    Da sauri ta kalleshi jin yasa hannunsa duka biyu bisa
    ƙugunta ya riƙe da kyau kana murya can ƙasan maƙoshinsa yace.

    “Anya kuwa kina son ki rabauta, ki samu jannatul firdausi”.
    Cikin kwaɓe fuska sabida yanayin yunwa wahala da bacci tace.

    “Ina so mana”.

    Kamar cikin raɗa yace.

    “Kin san dai sai na ɗaga ƙafa zaki shiga ko?”.

    Ya ƙare maganar cikin wata iriyar murya mai nuni da shima
    zazzaɓin ne a jikinsa kana ya tsareta da matattun idanunsa, ita kuwa Khausar
    cikin sanyi tace.

    “Eh nasi”.

    Kanshi ya ɗan manna da ƙirjinta a saman lips inshi yake

    “Toh bakya son shiga kenan?”.

    Ya ƙare maganar yana shafa sajenshi kan haɓarta.

    Cikin sanyi tace.

    “Toh bazaka ɗaga min in shigaba kenan?”.

    “Eh in baki bar tura min baki da jujjuya fitinannun idanun
    nan naki ba kam bazan ɗafaba”.

    Da sauri tace.

    “Kayi haƙuri bazan ƙaraba”.

    Kanshi ya ɗan jujjuya tare da cewa.

    “Naƙi”.

    Cikin zubda hawaye murya na rawa da alamun tsoro tace.

    “Ai dama na sani baka sona ka tsanane kai zakama fi son in
    shiga wuta”.

    Murmushi mai cike da jin daɗi yayi kana a hankali yace.

    “Sorry yi shiru in dai kina min duk abinda nakeso, to zan ɗaga
    miki, ki shiga ba ke ba wuta jinki ko Minha”.

    Ya ƙare maganar tare da manna fuskarshi da tata, a hankali
    ya ɗan zaro harshensa cikin sanyi ya fara lasar hawayenta tare da shaƙan
    ƙamshin jikinta.

    Allah ya sani so yake suyi bacci, amman ya lura tana cikin
    galabaita, ga jikinta zafi kana ko muryarta bata fita, gashi tun ɗazu take
    ƙorafin yunwa, kuma ga umarnin Didi.

    A hankali ya ɗago kanshi ya kalleta jin tana cewa.

    “Yunwa nakeji, kamar zan faɗifa kaina ciwo bayana ciwo,
    ƙuguna ciwo, idona ciwo”.

    cikin wata amintacceyar murya yace.

    “sorry Minha vidaa Bazaki faɗiba bari in kaiki kici abinci
    mu tafi asbiti”.

    Sai ya ɗan tsaida ita tare da sa mata pant ɗin kana ta gyara
    mata rigartan.

    Sai kuma ya sunkuyo.

    Cak ya ɗagata tare da mannata da ƙirjinsa,  sassayan numfashi ya fesar tare da fitowa da
    ita ya nufi Side ɗinsu Ummin.

     

    Dai-dai lokacin ɗin da suka iso ƙofar falon dasu Ummin suke
    tace.

    “Ka sauƙeni a nan zan ƙarasa da kaina”.

    “Naƙi”. Yace yana mai kutsawa cikin falon.

    Da sauri ya sunkuyar da kansa dan kusan duk su Ummi suna
    falon cikin wani irin fitinennen kunya
    ya direta bisa 3 sitter kai a sunkuye yayi musu gaisuwar ƴan kasuwa tare
    da juyawa ya fita.

     

    Yana fita yaci karo da Didi da Lalla Hafsat da Jakadiya, a
    hankali ya raɓa jikin gini tare da sosa ƙeyarsa.

    Cikin kauda kai Didi tace.

    “Kaje ƙasa Khadija ta baka abinci”.

    Cikin sanyi yace.

    “Toh”. Sai kuma ya nufi ƙasan.

     

    Ita kuwa Khausar yana fita ta kife kanta bisa cinyar Ummi da
    tazo ta zauna kusa da ita, cikin rawan jiki da muryar data disasha yasa bata
    fita sosai tace.

    “Ummi yunwa nakeji, kaina ciwo zazzaɓi nakeji”.

    Sai kuma ta saki sabon kuka.

    Dai lokacin kuma Didi suka shigo.

    Da sauri ta matso gabansu shafa kanta tayi cike da kulawa so
    da tausaya take mata sannu tare da tambayar Ummi me  ke damunta.

    Kai ta jinjina jin abinda Ummin ta gaya mata, kana cikin
    kulawa tace.

    “Hafsat sauƙa kije ki cewa Ibraahim yaje ya ɗauko Dr
    Jameel”.

    Da sauri tace to kana ta juya ta fita.

     

    Ita kuwa Ummi a hankali tacewa Khausar.

    “Tashi kici abincin to”.

    Cikin rawan jiki ta tashi zaune da taimakon Aunty Rukayya
    dake jera mata sannu.

    A hankali suka kalli gefen da Hajia Bunayyah take sabida jin
    wani dogon tsakin da taja tare da juyawa ta bar falon.

     

    Cikin zubda hawaye Khausar ta kalli Asma’u dake ta sakin
    murmushin tare da sune kanta.

    Sai kuma ta kalli Dija ta kuna kalli Aseeya.

    Cikin muryar kukan tace.

    “Ummi ki ganifa dariya su Asma’u kemin”.

    Da sauri Asma’u da Dija suka nufi cikin ɗaki sabida daƙuwar
    da Ummi tayi musu, Asiya ma bayansu tabi.

    Hajja Nana kuwa cikin dariyar mugunta a fili tace.

    “Yar nema ba cewa kikayi Ni Modibbo nake so”.

    Cikin Shesh-sheƙan kuka murya na rawa tace.

    “Wallahi na fasa, ni dai Wlh ku maidani wurin Mommy na ta
    kare mgnar da iyakar gskyar zuciyarta”.

    Dariya ce ta kubcewa Aunty Hajara da Rukayya Hajja Nana da
    Innayi kuwa tafa hannu sukayi.

    Ummi kuwa da sauri ta jawota jikinta.

    Didi kuwa tea mai zafi ta fara haɗa mata.

     

    A can ƙasa  kuwa
    kwance kan 3sitter Lalla Hafsat ta samu Moddibo
    jikinsa cike da zazzafan kasala gaba ɗaya yayi so weak baki ɗaya bashi
    da kuzari saboda yayi abinda bai taɓa yi ba a tsawon rayuwarsa duk jikinsa
    amace yake ga wani fitinennen zazzaɓi da yakeji yana ratsa ƙasusuwan jikinsa,
    yayinda cinyoyinsa kuwa gaba ɗaya jinsu yake kamar ba nasaba, a hankali ya
    kishingiɗa da jikin Kujera yayin da ya manna kansa da jikin Kujeran yasa
    hannunsa duka biyu ya riƙe sabida zazzafan zazzaɓi yake ji wanda yasa har
    jikinsa ke rawa ga kuma ciwon kai wanda alamun kukanda yayi tayine da rashin
    bacci suka haifar masa da ciwon kan.

    Cikin kula ta isa wajen tare da ɗaura hannunta na dama kan
    goshinsa jin hannunta agoshinsa ne yasa ya buɗe Idanunsa dake lumshe ya
    kalleta.

    Cike da kulawa tace.

    “Jikin ka zafi,Zazzaɓi kake jine?”.

    Kai ya gyaɗa tare da maida idanunsa ya lumshe.

     Cikin kulawa ta kalli
    fuskarsa tare da cewa.

    “Subhanallah Sannu”.

    Sai kuma ta juya ta kalli Ibraahim da yanzu yake shigowa
    tare da cewa.

    “Yawwa Ibraahim dama yanzu Didi tace in faɗa maka kaje ka
    kira Dr Jameel yazo ya duba Khausar bata jin daɗi.

    Shima Aleeyu gashi yanzu naji duk jikinsa da zafi ga yanda
    ya zama wani so week haka nan!”.

    Jin abinda ta faɗa yasa Moddibo buɗe Idanunsa ahankali tare
    da faɗin.

    “Dr Jameel kuma?.”

    Kai ta gyaɗa mishi alamun eh.

    Cikin ɗan rawan sanyin zazzaɓin yace.

    “Ba Dr macene? Bana so Dr Jameel ya dubata, a nemi mace”.

     

    Kai Ibraahim ya gyaɗa kana yace.

    “Toh Shikenan bari naje na taho da Dr Jameel,Da Dr Isha in
    yaso Dr Jameel sai ya duba ka ita kuma
    sai mace ta duba ta”.

    Kai Moddibo ya gyaɗa kana Ibraahim ya juya ya tafi…

     

    Acan ɓangaren su Didi kuwa sauri Didi ta Sanya hannunta ta
    karɓi plate ɗin da Khausar ta ke miƙawa Hajja Nana mata alamar ta ƙoshi ita
    kuwa Hajja Nana harara ta watsa Khausar tare da cewa, nicema zan karɓi ragowar
    yunwarki ai shi daya jinyataki sai shi zaiyi jinyarki, Ni ko sannuma zaki samu
    a wuri nane,.

     

    Murmushi Ummi da Didi sukayi, cikin kulawa Didi tace.

    “Ki hutama Hajia ni zanyi jinyar ɗiyata”.

    Murmushi suka kumayi baki ɗaya.

     

    Ita kuwa Khausar a hankali ta koma baya tare da jingina
    kanta da jikin Kujeran ta lumshe manyan idanunta da suke ɗan kumbure kana sunyi
    ja saboda yawan kuka da rashin bacci.

    Sai kuma ta fesar da sassayan numfashi sabida cikinta yayi
    mata tib saboda yanda abincin ya mata daɗi taci sosai musamman ma naman ya dahu
    yayi lugun gashi yayi yaji yadda take so.

    Anutse Didi ta sake miƙa mata kofin tea mai kauri tare da
    cewa.

    “Karɓi ki shanye”.

    Sunkuyar da kanta tayi kana tace.

    “Cikina ya cika”.

    Ummi dake gefenta tace.

    “Karɓi ki shanye ki kafa kai kawai ki shanye”.

    Cikin lumshe idanu ta karɓa tare da kafa bakinta ta shanye
    tass.

    A take zufa ya shiga tsats-tsafo mata tako ina.

    Cike da kulawa Ummu ta kalleta tare da faɗin.

    “Sannu”.

    Kai ta gyaɗa tare da lumshesu so take ta gyara zamanta amman
    tsoron yadda zata motsa take, sabida har yanzu tanaji zogi.

    Gajiya da zaman ne yasa ta ɗan kishingiɗa.

    Ummi na gyara zamanta tace.

    “Kwanciya kike sonyi?”.

    Langwaɓar da kai Khausar tayi kamar za tayi kuka ta gyaɗa
    mata kai tare da faɗin.

    “Eh jikina ba ƙarfi,Ummi baki daya jikina amace”.

    Numfashi Ummi ta fesar ganin yanda take ciccije baki alamar
    tana jin ciwo ajikinta tace.

    “Toh ki kwanta”.

    Kai ta gyaɗa tare da kwanciya.

     

    Zama Didi ta gyara tare da kallon Hajja Nana dake cewa
    Innayi.

    “Dan Allah nikam Innare yau dai kam ki faɗa mana meye ne
    sirrin Al’amarin tafiyar ku gari ya garire kuka je kuka zauna har wancan
    ƙasar”.

    Kallon Didi Innayi tayi alamar kin amince in basu labari.

    Kai Didi ta Jinjina tare da faɗin.

    “Ki faɗa musu”.

     

    Zama Innayi ta gyara tare da juyawa ta fuskancesu baki ɗaya
    kana ta fara basu labari kamar haka…

    Masarautar Mouley ta kasance Masarautace mai girma da ƙarfin
    iko kana da matsayi a yankin Africa baki ɗaya, sannan su su Abualeey sarki
    Youseep kenan su goma ne acikin Mahaifin su suna da ƴan Uba su kuma su huɗu ne
    kaɗai acikin Mahaifiyarsu maza biyu mata biyu Sarki Youseep Muhammad Mouleey
    sai Haroon Muhammad Mouley, sai Salma Mouley da kuma yar autarsu mahaifiyar Dr
    Jameel.

    Sannan Mahaifiyarsu ta kasance itace Uwar gida mahaifinsu
    tun yana da rai yayii Murabus aka ɗauki mulki aka bawa Sarki Youseef kasancewar
    shine babba sai suka fara fuskantar ƙalubale ƴan Uba sukayi ca akansu bayan
    yayi Aure dai duk abin bai bayyana sosai ba, saida suka fara haihuwa, aihuwarsu
    ta forko aka samu, Lalla Khadijah lafiya lau aka raineta har aka yayeta. Kana
    aka haifi Lalla Hafsat lafiya lau itama aka yayeta, amma tunda aka fara haifan
    ƴaƴa maza sai ya zama duk Namijin da aka haifa baya wuce kwana arba’in a duniya
    tun yana kwana talatin zuwa arba’in ɗin ake sace yaro, baya wuce kwana uku sai
    a tsinci gawar yaro a tsakiyar fada, an kashe shi.

    Masarautar Mouley gaba ɗaya ta shiga ruɗanin wannan
    al’amari, sai da Gimbiya Didi ta haifi ƴaƴa maza uku duk ana kashe su kafin ta
    haifi Moddibo da aka haifi Moddibo kuma dai-dai lokacin Mahaifin Moddibo ya
    kamu da ciwo ya zama kamar irin Kiɗimamme haka ya rasa gane Ainihin abinda ke
    damunsa har aka ɗauki Sarauta aka maida ita hannun Ƙaninsa.

    Ƙanin shine ayanzu yake kwance kusan shekaru ashirin da
    biyar bashi da lafiya.

    Sanin danayi ana haifar yara basa wuce kwana arba’in ake ɗauke
    su yasa nayi niyya taimakon uwar ɗakina da uban ɗakina da kowa yasan yanayin
    jikinsa akwai alamun sa hannun magauta.

    Kasan cewa nice Jakadiyar Didi yawan zama da ita da yaranta
    da take musu fulatanci yasa na iya yaren sosai tunda alokacin ma munyi kusan
    shekaru goma sha uku tare, dan a lokacin shekarun Lalla Khadijah 12 cib Hasfat
    10. Haka yasa nayi niyyar ɗaukesa naje wani waje nayi rayuwa dashi ya zama
    zakaran gwajin dafi kafin na dawo dashi shiyasa na rubuta wasiƙa sannan na ɗauki
    sandarsa wanda tsarin Masarautarne duk Amaryar da aka aura ranar da akayi First
    night ɗin ta idan aka sameta cikakkiyar budurwa za’a bata wannan sandar Amma
    sandar za’a ajiyeta aɗakin Tarihi na Masarautar inda ake ajiye ƙyallayen budurcin
    matan masarautar da sarautar ke hannunsu, sai randa ta haifi ɗa Namiji ya kai
    shekara ɗaya aduniya za’a ɗauko shi akawo mata shi matsayin sandan godon
    sarautar, dan haka ne na ɗauki sandar sannan na shiga ainihin ma adanar
    masarautasu kasancewata amintacciyar Jakadiya yasa nasan duk shiga da fitan
    Masarautar shiyasa na shiga na ɗibi Silalllan Gwal ɗinna kafin na rubuta wasiƙa
    da yi musu cikekken bayanin ba sace ɗansu akayiba ni na ɗauleshi na tafi dashi
    kuma in dai yana raye ina raye wata rana zan dawo dashi.

    Na basu cikekken tabbacin Cewa zan dawo musu da ɗansu in Sha
    Allah su kwantar da hankalin su nayi musu alkawarin zan kula dashi sannan zan
    bashi tarbiyya za kuma yi mishi duk abinda uwa da uwa zasuyiwa ɗan su bazaiyi
    kukan rashinsu a kusaba susa aransu zan dawo musu da ɗan su lokacin da yafi
    ƙarfin magautan su a kuma lokacin da sukafi buƙatar sa kusa dasu…

     

    Nan’nauyan ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe sai kuma ta juya ta
    kalli Hajja Nana dake cewa.

    “Sai kuma ki rasa inda zaki je sai garin mu”.

    Murmushi Innayi tayi kana tace.

    “Eh saboda lokacin da aka kawo Didi ƴar Nigeria ce jahar
    Adamawa sheik Jabeer ya kasance Aminine ga Sarki Mohammed Aliyu Mouley shiyasa
    suka haɗa Auren ƴaƴan su.

    Shiyasa dana tashi na tafi Nigeria naje na zauna ta yankin
    dake magwabtaka da yankinsu kuma shiyasa nake hana Modibbo zuwa Adamawa, sai a
    sace yaje sau ɗaya nanma da naji nai ta kuka haka yasa yayi min alƙawarin bazai
    sake zuwaba Marocco ma nice ke hanashi zuwa da tuni yazo, niko nasan duk wanda
    yasan iyayensa to dole in ya ganshi gane ɗansune”.

    Murmushi kawai Didi keyi tana sake jin ƙaunar Innayi aranta
    ta yanda ta riƙe mata amanar ɗanta ta kuma bashi tarbiyya.

    Innayi kuwa idanunta akan Hajja Nana ta cigaba da cewa.

    “Daga nan kuma ban san meya faruba a masarautar Mouley bayan
    tafiyata ba”.

    Numfashi suka sauƙe kowa yana sake jinjina girman ikon Allah
    aransa da yanda al’amarin ya kasance kana suka haɗa baki wajen cewa.

    “Ikon Allah rabo nefa.

    Rabon Aurensa da Khausar ne ya jasu”.

    Amintaccen murmushi Didi ta Saki kana tace.

    “Aikam Al’amarin Ubangji ya wuce wasa sai godiya”.

    Sai kuma ta ɗan kalli Innayi tare da cewa.

    “Bayan tafiyarku da wata biyu Sarki Muhammad Mouley ya rasu,
    kana a ranar Unclee Haroon ya cika shekaru biyu a karagar mulki ƙanin Abualeey
    kenan. kasancewar jinyar Abualeey gaba gaba kawai takeyi, to shekarunsa huɗu a
    kan mulki yayi haɗari shida Baban Jameel da kuma Mamin Jameel ɗin.

    A lokacin Yusuf ɗinshi ƙaramine, haka yasa dole aka bawa
    Unclee Yazidu. Shekaransa ɗaya rak bisa mulki, a lokacin kuwa wannan dokin Rinƙas
    yana tsaka da ƙuruciya, abin mamaki dokin nanne ya kasheshi har lahira a
    tsakiyar fada, bayan rasuwarsa aka ɗaura ƙaninsa Zarid, shima shekararsa ɗaya
    dokin ya kasheshi irin kisar da yayiwa ɗan uwansa zuwa lokacin kuma Allah ya
    bawa Abualeey sauƙi duk larurar dake tare dashi haka yasa akace shi zava
    maidawa mulki, shi kuwa yace shi baya buƙatar mulki a lokacin jinyar ɗan uwansa
    shine a gabanshi mu kuma Alhamdulillah an haifi Ibraahim an raine shi lfy haka
    yasa,

    Yace a bawa ƙanin Zarid Isman abin mamaki ba yadda ba’ayu da
    isman ya karɓi mulkin nanba fir yace shi baya so, da aka matsa mishi sai cewa
    yayi kawai shifa bazaiyi mulkinba tunda sauran yayunsa duk wanda aka bawa
    mutuwa yakeyi, kawai sai ya rinƙa faɗin duk abinda sukayiwa Abualeey yace sune
    suka so haukatashi kuma sune suke kashe mun yarana uku duka, kuma sunema suka
    kashe mahaifinsu daga nan ya zama mahaici yanzu haka shi yana raye ko yaushe
    yana tsakiyar fada ranar da Aliyu yazo ma Allah ne ya tsaresa dan Aliyu da
    dokin ya kashisu dan shi ya kashe mahaifiyarsu ma Lalla Adir tohfa haukacewarsa
    da sirrinsu da yake ta tonawa ne yasa muka gane cewa Rinƙas yanayi mana faɗa da
    magautanmu ne, duk da ƙanensu mata da suka haɗa uban su dai kamar ba a’lamun
    cutarwa haka yasa aka matsawa Abualeey akan ya amshi mulki.

    bisa dole dai, ba don yasoba aka sake daurashi kan mulkin
    Alhamdulillah yanzu dai masarautar Mouley babu wasu bayyanannun magauta sai dai
    ɗan abinda ba’a rasaba wanda tsoron yasa suka bari daga forko dai tsoron Allah
    bai sa sun tubaba, sai tsoron rinƙas da yasa suka rusuna amman zuwa yanzu sun
    gane cewa Allah shine abin tsoro zuƙata sun tsarkaka ko nida abokan zamana bamu
    da wata matsala asalima Gimbiya Sahra ita ke shirya komai na Khausar saidai ita
    batama taɓa haihuwaba sai ta ukun mu kuma ƴaƴanta duk matane, ta hudun kuma
    ƴaƴanta yarane amman ita duk mazane mu dai Alhamdulillah”…

    Sai kuma duk suka sauƙe nannauyan numfarfashi Khausar kuwa
    ido cike da alamun bacci da ciwon ta lumshesu

     

    Dai dai lokacin kuma Dr Eshaa da Lalla Hafsat suka shigo wacce
    bisa duk kan alamu tayi mata bayani.

    Shogowan sune yasa suka rufe maganar tare da yi mata sannu
    da zuwa amsawa tayi tare da gaishe su cike da ladabi.

    Cikin kulawa ta zauna kusa da Khausar tare da ɗan shafa
    gefen fuskarta.

    “Sannu Allah ya sauƙa”.

    Amin Ummi da Didi suka amsa.

    Hajia Bunayyah kuwa baki ta taɓe a ranta tace.

    “Allah shi ƙara”.

    Ita kuwa Dr Isha cikin kulawa ta muƙawa Didi

    Magunguna tare da faɗin.

    “Lalla Hafsat tamin bayani, a bata magungunan tasha yanxu In
    Sha Allah duk wani zugi ko zazzaɓi da ciwon kai zata daina jinshi”

    Amsa Didi tayi tare da fara ɓalla kana tace.

    “Ai yanzuma kuwa zan bata”.

    Gyaɗa kai Dr Isha tayi tare da sallamansu ta fita.

    Didi kuwa maganin ta bawa Khausar tasha kana ta miƙe tabi
    bayan Dr Isha da bata tsaya duba ko Khausar ta samu rauni ba, dan tasan ko ta
    samu rauni tsumin tsarin masarautar da turaren wutan zasu haɗeta…

     

    Acan Falon Didi kuwa Dr Jameel ne  ya bawa Moddibo magunguna kana ya koma gefe
    yana amsa kiran da aka masa daga asibitinsu.

    Ahankali Moddibo ya miƙe ya nufi ƙofar da sai kashi Side ɗin
    su, dai-dai lokacin kuma Didi ke dawowa daga Side ɗin su Khausar.

    Kallonsa tayi tare da cewa.

    “Ina zaka je?”.

    Cikin yanayin zazzaɓin da yake ji ya fesar da numfashi kana
    ya motsa laɓɓansa tare da cewa.

    “Zanje In kwanta ne”.

    Tsayuwarta ta gyara kana tace.

    “A’a muje dai kaje kaci abinci tukunna”.

    Ba musu ya gyaɗa kai kana ya nufi dining tana biye dashi
    zama yayi tare da ɗan rumtse idanunsa.

    Gefensa ta zauna kana tayi serving ɗin sa,

    Sai kuma ta kalli Dr Jameel tare da cewa yazo suci abinci.

    A hankali Modibbo ya kalleshi jin yana cewa.

    “Didi Azumi nakeyi”.

    Kai Modibbo ya ɗan jinjina dan zuwa yanzu dai ya fara
    gamsuwa da sauyawar Dr Jameel, musamman yadda ya dage da azumi dan daƙushe
    sha’awarsa.

     

    Ita kuwa Didi kai ta jinjina sannan ta sawa kanta  suka fara cin abincin, yana ganawa ya miƙe.

    Da sauri tace.

    “ina kuma zakaje, kasha maganin ne?”.

    Dai-dai lokacin Dr Jameel ya iso wurin kujera yaja ya zauna
    yana cewa.

    “Eh Didi yasha”. Sai kuma ta juyo ya kalli Modibbo tare da
    cewa.

    “Amman fa kamar ba zazzabin kawai ke damunsa ba na lura yana
    yawan miƙa kamar wanda jikinsa ke masa ciwo, bini bini ya dafe ƙugunsa”.

    Da sauri Didi ta miƙe tare da turawa Dr Jameel ɗin womers ɗin
    abinci gabansa kana tayi cikin falon dan tasan ba ƙaramin aikin Dr Jameel bane
    yayi ɓaram-ɓarama, a gabanta haka yasa ta ma mance yace yana azumi.

    shi kuwa Modibbo wani irin harara ya rabkawa Dr Jameel tare
    da cewa.

    “Ace mutum shi bakinsa baya iya shiru”.

    Murmushi Dr Jameel yayi tare cewa.

    “Na lura baka taɓa sanin maceba, da alamu jiya kuma kayi
    yaƙin fatauci shiyasa ƙugu da jinyoyi suke ciwo, ah aini da na ɗauka kai kam ba
    abinda zakayi da mace yadda kake wasu abu kamar waliyi, shine tun ba’aje ko
    inaba kaje kai ta karya ƙugu ka kwashi Gara, yanzu kuma jiki magayi dan na lura
    baka sararawa yar mutaneba”.

    Sai kuma yayi saurin dage kansa tare da sakin kara jin yadda
    Modibbo ya kaiwa bakinsa bugu.

    Dariya ya fashe dashi tare da bin Modibbo da ido kana ya
    dawo tsakiyar falon.

     

     A hankali ya nufi
    Side ɗin sa saboda wani irin bacci da yake ji ga zazzaɓin ya fara masa yawa
    alamar maganin ya fara kokawa da Zazzaɓin yana shiga ya kwanta bisa 3 sitter…

     

    Jakadiya kuwa kai tsaye ɗakin Tarihin Masarautarsu takai
    ƙyallen budurcin Khausar.

    anan aka ajiye wannan frame ɗin kana ta ɗauko sanda da
    Jigidan Zinare mai tambarin Masarautar Mouley sai chain na ƙafa shima na Zinare
    ne  kuma munduwa mai tambarin Masarautar,
    da dai  wasu kaya masu masifar kyau da ɗaukar
    hankali kai tsaye sashen Didi ta shiga kana ta kalli Didi dake zaune kan 2sitter
    daga ƙasa Carpet ta zauna tare da faɗin.

    “Yawwa Didi gashi an gama haɗawa”.

    Sanyayyan Murmushi Didi tayi hakan ganin abin sai ya tuna
    mata da lokacin da aka kai mata nata cikin sauƙe ajiyar zuciya tace.

    “Toh shikenan mu tafi mu nunawa Niyna daga nan mu tafi da
    ita”.

    Miƙewa Jakadiya tayi suka nufi Side ɗin Niyna daga nan
    kuma  suka shiga sashin abokan zamanta
    suka nuna musu kana suka wuce wurinsu Ummi.

    Hajja Nana, Innayi da Hajja Umma suka samu azaune suna hira.

    Yayin da Ummi Khausar Asma’u Dije da Asiya ke bedroom.

    Zama Didi sukayi kana suka sa aka kira su Ummi,Hajiya
    Bunayya,Aunty Ruƙayya, Aunty Hajara duka suka fito falon Jakadiya ce tayi musu
    bayanin cewa.

    “Ga wannan Sandar amma yanzu dai an nuna muku ne saboda
    tabbacin cikekken tukuicin da aka samu daga Masarautar Mouley ce”.

    Wani irin farin ciki ne ya mamaye baki ɗaya ilahirin
    zuciyoyinsu saɓanin Hajiya Bunayya da take jin wani sabon kunci da tashin
    hankali aƙahon zuciyarta.

    Jakadiya kuwa cike da alfahari ta cigaba da cewa.

     “Kuma yanzu za’a sake
    mai dashi cikin karagar masarautar tarihin gefenta sai sanda aka samu ɗa namiji
    ya cika Shekara ɗaya ranan za’a mallaka mata sandar ahannunta saboda sandar
    shine zai nuna shaidar Lalle gadon Masarautar a ɗakinta yake”.

    Cike da matsanancin farin ciki Innayi tace.

    “Alhamdulillah abinda ake ƙi dai shi ya tabbata in  Allah yaso Sarauta dai tana nan ta tabbata a ɗakin
    Lalla Didi”.

    Niynah kuwa murmushi take tare da faɗin.

    “Alhamdulillahi burin magauta bai cika ba”

     

    Acan ɗaki kuwa Asma’u ce ta kalli Khausar tare da ƙyalƙyalewa
    da dariya kana tace.

    “A’a manya gari yane duk bakinki ya mutu. Yah Moddibo yayi
    aiki kenan”.

    Kallonta Khausar tayi tare da tura baki cikin yanayin jin
    bacci saboda magungunan data sha ta harareta da kumburarrun idanunta sai kuma
    ta murguɗa baki.

    Ware idanu Asma’u tayi tare da faɗin.

    “Eh lallai yarinyar da sauran ki har yanzu Yah Moddibo bai
    ladab tar dake ba tunda har kika samu idanun harara da bakin tsiwa”.

    Wani kallo Khausar tayi mata cikin dishsheyar murya mai cike
    da sanyi da rauni alamun ko yanzu tana iya kuka a hankali tace.

    “Hmmm Ladabtuwa na nawa kuma, sai dai kuma in kasheni ya
    rage yayi”.

    Sai kuma ta lumshe idanunta hawaye masu zafi suka zubo
    ahankali ta taune lips ɗin ta na ƙasa tare da cewa.

    “Naji azabar da tunda Uwata ta haifeni ban taɓa ji ba, salon
    mugunta kuwa babu wanda Yah Moddibo bai haddace ba bayan makarantar Hadda da
    yaje ina ga har da na koyon mugunta da zalumci yaje yayi Mater’s ya iya salon
    mugunta iri da kala, Ni dai Allah ya sani ba abinda zance sai Allah ya saka min
    kuma inyi ta Addu’a Allah ya tsareni da sherrin muguntarsa”.

    Ta kare mgnar murya na rawa, da kuma iyakar gskyar
    zuciyarta.

     

    Wani sabon dariya Asma’u ta ƙyalƙyale dashi harda riƙe ciki
    kana tace.

    “Uhm lallai su Fattanah anji maza wato har Master’s Yah
    Moddibo yayi a fannin mugunta”.

     Cikin kauda kai
    Khausar ta runtse idanunta tare da cewa.

    “Ayyah am Asma’u kiyi dariya son ranki kema kwana nawa ne
    zaki zo irin wannan Matsayin?”.

    Murmushi Asma’u tayi tare da miƙa mata wayar kana tace.

    “Gashi naga Mommy ke kiran”.

      Tana karɓan wayar ta
    fashe da kuka.

    Shiru Mommy tayi tana jin shesh-sheƙan kukanta kusan minti
    biyu ta ɗauka tana kukan kafin cikin rawan murya tace.

    “Momy ina kwana”.

    Ajiyar zuciya Momy ta sauƙe tare da cewa.

    “Kin gama kukan?”.

    Kamar jira take sai kuma ta sake fashewa da sabon kuka cikin
    sauƙe numfashi Momy tace.

    “Meyesa bakya girma ne Mamana. ai rayuwar nan da kike gani
    hakuri ake musamman mace dole abubuwa suzo maka ayanda ba kayi zato ba, ki koyi
    dauriya Khausar agaban surkunan ki kike fa, kinga za’a barki agarin da babu
    kowa naki ki iya dauriya ke macecefa wata rana ma haihuwa zakiyi”.

    Kuka ta kuma fashewa dashi cike da rauni tare da cewa.

    “Wallahi Mommy ni nafasa Auren zan biyosu in dawo wallahi ni
    na fasa bazan zauna ba zan biyosu bazan zauna a garin nan ba kasheni zaiyi”.

    Sai kuma taja ajiyar zuciya tare da cigaba da faɗin.

    “Dama shi mugune sannan kuma an kawo ni inda ba kowa nawa
    zai cigaba da yimin mugunta”.

    Cikin sauƙe numfashi Momy tace.

    “Kul kada In sake Jin kin faɗi haka abakin ki bana so, ce
    miki akayi aure wasa ne,  ina Umminki?”.

    Cikin Muryan kuka tace.

    “Tana falo”.

    Kai Mommy ta gyaɗa tare da faɗin.

    “Toh bawa Asma’u ta kai mata”.

    Miƙawa Asma’u wayar tayi ta karba kana ta fice ta kaiwa
    Ummi.

     

    Bayan sun gaisa da Ummi fuska ɗauke da yalwataccen farin
    ciki Ummi tace.

    “Kai Alhamdulillah Momyn Khausar yau muna cike da farin ciki
    in Sha Allah gobe zamu dawo, zamu dawo da tukuici mafi tsada da daraja na
    munduwar masarautar Mouley shaidar yarmu ta kawo budurcinta ”.

    Wani banzan kallo Hajiya Bunayya ta watsa mata Ummi kuwa
    cikin farin ciki ta cigaba da cewa.

    “Khausar ɗin mu ta kai budurcinta gidan miji sannan Sarauta
    wanda muke da yaƙinin in Sha Allah aɗakin Khausar zai kasance”.

    A wannan karon ƙwaffa mai ƙarfi Hajiya Bunayya tayi ta
    sunkuyar da kanta ƙasa yayin da idanunta suka kada sukayi Jawur cike da takaici
    bakin ciki da hassada tace.

    “Uhmm ai duk gaggawar asara ta dai jira samu”.

    Da kallonta suka bita sabida su dai fulanine ba wata
    cikekkiyar hausace garesu ba dan haka basu wani fahimceta ba bare su damu.

     

    Mommy kuwa cikin hayaniyar da take jiyowa tace.

    “Naji kamar kina cikin mutane”.

    Kai Ummi ta gyaɗa tare da faɗin.

    “Wallahi ina cikin mutane farin cikine ya hanani in haɗiye
    abun da zamu tattauna”.

    Mommy na murmushin Farin cikin tace.

    “Toh ki bari sai kin nutsu zamuyi waya amma ya jikin ƴar
    taki?.”

    Zama Ummi ta gyara tare da faɗin.

    “Jiki da sauƙi anzo an bata magunguna yanzuma ina ga bacci
    zatayi su Asma’u ne suka hanata bacci da surutu”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin.

    “Toh shikenan Allah ya ƙara sauƙi”.

    Ameen Ummi ta amsa kana sukayi sallama.

     

    Acan gadon Khausar kuwa ganin ta samu bacci ne yasa Asma’u,
    Asiya Dije fitowa.

    Fitowar su yayi daidai da ɗaga wayar Lalla Hafsat ta manna
    akunnenta maganar minti biyu tayi kana ta janye tare da kallon Asma’u da
    shigowanta Falon kenan tace.

    “Asma’u kizo mu tafi kina da baƙo A Side ɗin Didi”.

    Kai ta gyaɗa tare da kallon Ummi batare data bita ba.

    Ummi data fahimci tsayuwar da take yasa tace.

    “Kije mana”.

    Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da bin bayan Lalla Hafsat da ta
    fara ta fiya tana isa Falon ta saki ɓoyeyyen ajiyar zuciya ganin Dr Jameel dake
    zaune kan 3sitter Lalla Hafsat kuwa direct bedroom ɗin Didi ta wuce.

    Cikin tsira mata ido da tarin ƙaunarta dake ratsa duk wani
    magudanan jinin jikinsa wanda yake uzzura jabarsa ɗaya danne yayi alƙawarin
    tsakaninsa da Allah bazai ƙara kusantar zinaba, ganinta ya sashi sauke numfashi
    mai sanyi tare da lumshe idanunsa kana ya buɗe su akanta tare da cewa.

    “Ƙaraso ki zauna anan”.

    Ya faɗa yana nuna mata gefensa cikin wani irin yanayi mai
    tattare da kunya ta nufi gefensa ta zauna kana ta gaishesa amsawa yayi yana mai
    tsira mata idanu tare da shaƙar daddaɗan ƙamshin hunran data shafa Cikin sauƙe
    numfashi yace.

    “Albishir My Asmeey”.

    Idanunta aƙasa ta motsa laɓɓanta tare da faɗin.

    “Goro”.

    Yana binta da wani sihirtaccen kallo yace.

    “Fari ko Jaaaaa”.

    Murmushi ne ya subce mata asaman laɓɓanta jin yanda yaja
    kalmar Jaaa ahankali tace.

    “Fari ƙall”.

    Zamansa ya gyara fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi dake
    bayyana farin cikin dake ciki yace.

    “In sha Allah gobe, da Abualeey, Galadima, Waziri da Abban
    Zakariyya da ƙanin Abbanshi zaku tafi, saboda za’a je ayi tambayar Aurenmu”.

    Tafin hannunta ta sanya ta rufe fuskarta kana ta saki
    murmushi mai ɗauke da kunya kafin ta ɗago kanta tare da cewa.

    “Allah ya kaimu Allah kuma ya mana zaɓin abinda yafi
    Alkhairi”.

    “Ameen ya hayyu ya ƙayyum amma dai kinyi farin ciki ko?”.

    Kai ta gyaɗa still hannunta na saman Fuskarta.

     

    Cikin son janta da hira ya gyara zamansa tare da cewa.

    “Kuma harda batun Asiya da Zakariyya ma duk za’a yi tambayar
    kinsan shi Zakariyya ya riga ya koma Indi’a amma in Sha Allah yace bazai daɗe
    ba zai dawo saboda yana so ayi abin cikin ƙanƙanin lokaci in Allah ya yarda”.

    Ahankali tace.

    “Ayyah Allah dai ya mana zaɓi mafi Alkhairi”.

    Cikin tarin ƙaunarta yace.

    “Ameen nan suka ɗan ci gaba da hira”.

     

    Lalla Hafsat da Lalla Khadijah kuwa, duk suna ɗakin Didi
    hadimai na shirya musu kayansu dan yau da dare Lalla Khadijah zata koma
    gidanta. Lalla Hafsat kuwa ƙarfe shida na safe na safen gobe jirnsu zai tashi
    zuwa Mexico.

     

    Su Ummi kuwa ƙarfe sha daya zasu tashi.

    Wanda kuma da pravate
    jet zasu tashi so kai tsaye Adamawa jirginsu zai sauƙesu, wanda tunima
    sun samu amincewa da sahalewar sauƙansu a Yola international airport, kassn
    cewar abune na manya ga kuma su Sheykh Jabeer da sune masu Jihar.

     

     

    Acan ɓangaren Khausar kuwa bacci ne mai nauyi mai cike da
    gajiya takeyi.

     

     Yayin da aɓangaren
    Moddibo ma hakan ne ya kasance sosai yayi bacci kiran sallar la’asar ne ya
    tashe sa yana tashi yaji jikinsa yayi sakayau alamar zazzaɓin ya sauƙa, cikin
    jin daɗi yasa hannunsa bisa mararsa yana shafawa jin maransa tayi sakayau wani
    makirin murmushi ne ya subce mishi sai kuma ya lumshe idanunsa wani irin farin
    ciki yake ji mara misaltuwa gami da nitsuwa salama kwanciyar hankali da
    cikekkiyar lafiya sai kuma zazzafan shauƙi.

    Da Zaran ya tuna wasu abubuwa da suka gabata sai ya saki
    murmushin.

    A fili yace.

    “Wai Wayyo Didi zai kasheni Yah Mu’allim zan mutu”.

    Sai kuma ya ɗan jujjuya idanunsa tare da cewa.

    “Farar kura ba, *Minha Vidaa* ga tsoro ga ban tsoro, ga
    tsiwa ga raki ”.

    ahankali ya shiga toilet ya sakaraa kanaa ruwan ɗumi kana ya
    daura alwala ya fito cikin wani tattausan yadi fari ƙall ya shirya kana ya
    feshe jikinsa da turarukansa masu daɗin ƙamshi a bedroom ɗinsa yayi sallan
    azahar daya riskeshi yana bacci, kana ya wuce masallaci yana mgnar zuci.

    “Sai na hukuntaki da sani makarar samun jam’i da kikeyi
    kuwa”.

     

    Khausar kuwa kafin akira La’asar ta farka tana tashi Ummi ta
    sake bata abinci taci kana tace.

    “Toh tashi kiyi wonka kiyi salla”.

    Kai ta gyaɗa tare da miƙewa tsaye ga mamakinta sosai ciwon
    yayi sauƙi sai kaɗan-kaɗan da takeji alamun mgni yayi aiki.

    Bayan tayi wanka ta sauya kaya tayi sallan azahar da la’asar
    ɗin.

    Tana bisa sallayar Ummu ta ɗauko mata Magungunan _Aunty
    Aysha Aliyu Garkuwa_ ɗan bokatjn wata gumbar madara mai haɗe da kwakwa ta miƙa
    mata, ba musu Khausar ta karɓa ganin yadda Aunty Hajara ta tsareta da idanu.

    A hankali ta fara ci tana haɗawa da kwakwar gumbar nada ɗan
    karen daɗi shiyasa ta ci mai ɗan yawa.

     Sai kuma ta amshi
    gorar da take miƙamata wanda na tsumin riɗine da kuma tsimi zuma a cup ta haɗa
    mata su.

    Cikin tura baki tace.

    “Ayyah Aunty Hajara cikina ya cika fa”.

    Da sauri ta ɗan sa cup ɗin a baki sabida hararar data watsa
    mata.

    Ajiye kofin tayi bayan ta shanye.

    Sai kuma ta kalli Ummi dake cewa ki shiga Bathroom na haɗa
    miki ruwan ɗumi ki zauna a ciki, kai ta gyaɗa kana ta shiga.

     

    Toilet ta tayi tsarki da ruwan ɗumi kana ta shiga cikin
    wanda Ummi ta haɗa matan.

    Wanda yaji turaren tsarki
    ta fito.

    Tana baza ƙamshi ita kanta in ta ɗan sunkuyo da kanta sai ta
    Lumshe idanu sabida yadda take baza ƙamshi ga kuma kullacar sirri da yafi komai
    mata daɗi, shiyasa take nace masa wurin shafawa ganin ba kowa a ɗakin ne yasa
    ta fita falon tana jin zazzaɓin ya sauƙa kana zugin da ƙasanta ke mata ma ya
    ragu sosai.

     

    Haka dai yinin wannan ranan Khausar da Moddibo sukayi yinin
    jinya kuma Alhamdulillah jiki yayi sauƙe…

     

    Moddibo kuwa yana dawowa masallaci part ɗin Didi ya wuce.

    Allah ya sani so yake ya ganta yaga yanayin jikinta amman ya
    rasa ta yadda zai nematan haka yasa ya miƙe da nufin zuwa side ɗin dasu Ummin
    suke kuwa sai ya sauya hanya tare da komawa side ɗinsu Allah ya sani kunyasu
    Ummi yakeji, kuma tsoron wannan tsohuwar mai Shegen baki yakeji kada ta
    kunyatashi.

     

    Bayan sallan isha akazo aka ɗauki Lalla Khadijah ta koma
    gidanta.

     

    Misalin ƙarfe tara da kwata, Ummi ta kalli Khausar dake
    kwance gefenta tace.

    “Khausar kada kiyi bacci
    anan fa, tashi ki tafi dakin mijinki”.

    Cikin tsinkewar zuciya ta zazzaro idanunta waje, tare da
    saurin kallon Ummi tana mai girgiza kai kana tace.

    “Na shiga uku Ummi dan Allah, ki barni in kwanan ni bazan
    koma canba wlh anan zan kwana”.

    Kai ummi ta girgiza tare da faɗin.

    “Nan kuma Khausar bayan gacan ɗakin mijinki a’a bazai
    yiwuba. maza tashi ki tafi”.

    Da sauri Ummi ta zuba mata ido jin ta fashe kuka tsakaninta
    da Allah kuwa take kukan. dashi tana yarfe hannu tace.

    “Ni dai dan Allah Ummi ki barni mu kwana anan, wlh tallahi
    bani da lafiya dan Allah ki barni in kwana kusa dake”.

    Asma’u dake gefe tayi murmushi tare da gyara kwanciyar ta.

    Ummi kuwa ganin yanda take kuka da faɗin baza ta je bane
    yasa tayi shiru…

    Sai kuma ta jinjina kai jin Innayi na cewa.

    “Ba komai Ummin Jameel barta ta kwana a nan ɗin, gobe ina
    zata ganku”.

    Ita kam Khausar ido ta rufe tana mgnar zuci.

    “Yoh ai tarema zamu tafi dan wlh ni dai bazan zaunaba”.

     

    Zuwa lokacin karfe goma harda kota….

     

    Washe gari da asuba ana fita masallaci Aka kai Lalla Hafsat
    da Hakim Airport.

    Bayan ta sallami su Ummi.

    Bakwai dai-dai jirginsu ya ɗags zuwa Mexico.

     

     Abujan Nigeria, karfe
    takwas dai-dai Unclee Naseer ya bar gidan.

    Tun fitansa kuwa Amina ke konce a tsakiyar falon bisa
    Carpet.

    A hankali take sauke numfashi sabida ɗan baccin ɗaya fara
    fizgarta.

    Cikin baccin da ya fara nisan, ta rinƙa jin hucin macijin
    nan, sai kuma tayi saurin buɗe idanunta sabida jin sanyin jikin macijin yana
    ratsa cikinta yana ɗan jujjuya kanshi tare dayin sama da kan nashi da ya shigar
    ta ƙasar ƴar rigar dake jikinta.

    Wani irin fitinennen karkarwa jikinta ya fara, tare da
    zazzaro idanunta baki ɗaya lokacin da taji macijin nan ya manna bakinshi kan
    nimple dinta na hannun dama yayiwa nimple din wani irin damƙa da karf….

     

     

    *Littafin Sakayya dai na kuɗi ki biya  karanta cikin aminci da salama ba haƙƙin kowa
    a kanki 1k ne kacal 0661110170 gtbank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min
    shaidar biyanki ta wannan number 09097853276 in tura Miki ki karanta cikin
    aminci*