Author: Novels

  • Noor Al Hayat 37

    Noor Al Hayat 37

    ✨ *NOOR-AL-HAYAT* ✨

    Bude motar Sudais yyi ya fita yana kallonta yace “Come down” a hankali ta fito gabanta na faduwa, ya nufi gate din gidan ta bi bayansa kamar me tausayin kasa, da farko Usman mai gadi ya tsaya tambayarsa wanda yake nema amma ganin khadijah ya fito da sauri yana kallonta da mamaki yace “Khadijah?” Ta kirkiri murmushi ta gaishesa, tuni Sudais ya shiga gidan, Khadijah ta bi bayansa Usman yace “Duk kika daga ma kowa hankali ana ta neman ki har station Hajiya ta kai report, to Alhmdllh tunda Allah ya bayyana ki, Alhmdllh” ita dai Khadijah bata ce komai ba ta kalli parking space xuciyarta na bugawa ta ga ba motar Aliyu da na Mumy, Sudais ya danna bell din entrance na gidan a hankali, sau uku yana danna bell din kafin a bude kofar, Anty khadijah ce tsaye bakin kofar kana ganinta kasan bacci take, idanuwanta suka bude sosai ganin khadijah dake gefen Sudais a tsaye tsoro dauke fuskarta, Sudais da yana ganin ta yyi guessing ita ce Anty khadijah ganin kallon da take ma khadijah yace “Assalamu alaikum” hade rai Anty khadijah tayi tace “Wa’alaikumus salam” daga haka ta kalli khadijah tace “Lafiya? Daga ina? Wa ku ke nema?” Sudais yace “Aliyu muke nema” daga haka ya shiga parlorn, Khadijah ta kasa shiga saboda tsoro, Wani kallo Sudais yyi mata yace “Come in” a hankali ta daga kafa ta bi gefen Anty khadijah ta shiga cikin parlorn ita ma, tuni Sudais ya isa kan kujera ya xauna, Anty khadijah dake kallonsa da mamaki tace “Malam nan din fa gidan matan aure ne ka shigo, lafiya? wa kake nema?” Yace “Shi yasa nayi sallama kuma kika amsa min kafin in shigo hajiya” Anty khadijah tace “Me kuma ya hada ku da Aliyu ku ke neman sa?” Sudais yace “Xai fi kyau idan ma bai nan ki yi hakuri ki kira mana shi ya dawo, and mahaifiyarsa hope tana nan?” Anty khadijah tayi mitsi mitsi da ido cike da masifa tace “Nima uwarsa ce ae halak malak, sannan Aliyu bai ma kasar gaba daya idan xaka fadi abinda ke tafe da kai malam ka fada don bacci nake ka taso ni…” Shiru Sudais yyi na d’an lkci kafin ya nuna mata khadijah yace “Kin san wannan yarinyar koh?” Ta kalli khadijah ta kara tsuke fuska tamau tace “Kwarai kuwa, yar aikin da muka dauka kwanaki kenan ta lalata mana xumunci ta shisshige ma d’a na, ta raba ni da shi ina ji ina ganin bana iya cewa komai, wannan shari’ar kuma sai a lahira don duk da barin ta gidan har yau abubuwan da ta cakuda bai gyaru ba, Allah ya isa tsakaninmu da ita” Kuka Khadijah ta fara yi a hankali ta durkusa inda take tsaye, Sudais ya ciro handkerchief dinsa ya share fuskarsa yana kallon khadijah yace “Dena wannan kukan xa kiyi ki bude baki da kanki kiyi mata bayani yanxu” Anty khadijah ta dawo tsakiyar parlorn da sauri tana xaro ido tace “Bayanin me?” Khadijah ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata, kare mata kallo Anty khadijah ta shiga yi, can ta fashe da dariya irin na mugunta lkci daya kuma ta tsayar da dariyar tana ma Sudais wani matsiyacin kallo tace “Xuwa kayi da ita tace mana tana dauke da ciki?” Sudais yace “Alhmdllh fine, unfortunately kin ma san halin d’an naki kenan” Khadijah ta hade kai da gwiwa tana kuka a raunane, Anty khadijah ta fashe da wani shegen dariya kamar bokanniya tayi mai isarta tayi shiru sannan ta nuna masa kofa fuskarta kamar bata taba dariya ba idonta yyi mitsi mitsi tace “Tun muna mu uku a nan bamu fi haka ba ku tashi ku fice mana a gida” a tsawace ta kare maganar, sudais ya tabe baki yace “Tsawar ki ko ihun ki fa baxae razana ni ba malama… Don haka hold it xai maki amfani gaba a wani wajen” Anty khadijah na huci tace “Xan nuna maka a nan ma yana da amfani, har wannan karuwar xata xo ta makala ma d’ana cikin shegen da tayi a wani wajen saboda ita matsiyaciya ce” Sudais yace “Toh abu mai sauki sai mu je asibiti a ga kwanakin cikin nawa, idan yyi dai dai da kwankin da ya koreta ta bar gidan to nasa ne in sha Allah” Anty khadijah tayi shiru jin abinda sudais yace, auuuu wato Aliyun ne ma ya koreta ashe, ita dai ta dawo kauyen da taje bayan kwana biyu da tafiyarta taji wai ba a ga khadijah ba ko sama ko kasa har station an kai report, Ranta yyi mugun baci a lkcn don bata so Khadijah ta tafi haka nan bata walakanta ta ba kmr yanda ta yi alkawari, me yasa xata tafi bata gama cika burin ta a kan ta ba har hawaye sai da tayi sbda bakin cikin kudin mota da kudin magani da tayi asara, suree a lkcn tayi mugun mamakin yanda Aliyu bai wani damu can ba kamar yanda mahaifiyarsa da baby suka damu amma ita bata taba kawo cewar shi ne ma ya koreta ba, Muryar Sudais ya dawo da Anty khadijah “Hajiya kin yi shiru daga nayi xancen asibiti” abinda ya fada kenan yana kallonta, ta yi masa wani shegen kallo tace “Ji gantalalle, to tunanin da nake daban malam, kuma asibitin ya ci kaza kazan sa baxa a je ba, idan ma cikin Aliyu take dauke da, idan ma ba nasa ba… bbu wanda ya isa ya shigo mana da shege cikin xuri’ar mu, I can swear with the Qur’an fasikanci ba halin Aliyu bane idan ma yyi Ita ta koya masa don kullum dakin sa take yini, wa ya sani ma ko har kwana tana yi can, yayata ba mai xama bace don yanxu xancen da nake ma bata kasar, kullum nice ke tare da su, wai hanata shige ma Aliyu da nake har shi ya janyo min bakin jini gun ta, ta janyo d’a na ya daina ganina da gashi a gidan, yanxu tun muna magana irin ta mutane ba mu dawo na mahaukata ba ku tashi ku fice min a gida kar ku ga d other side of me, ku fita nace” a tsawace ta kare maganar, Sudais dake ta kallonta yyi murmushi yace “Toh cikin nasa dake jikinta tayi ya da shi kenan?” a takaice Anty khadijah tace “Ta xubar, don kaf xuri’ar mu ba shege kuma baxa a fara a kan d’a na ba, idan kuma taga xata iya sai ta raini cikin ta haifa ma kanta ajalinta….” Khadijah dai banda kuka babu abinda take, Sudais ya mike yace “Good, I made her brought me here for just 2 reasons, na farko… is to find out how sincere she is, and na karshe… Is just to let you and ur son knw d pains u are about putting the innocent orphan coz ni dai nasan definitely baxa ku taba accepting cikin ba, kun rabata da warce take da ita a duniya, kun goga mata bakin fenti da ba lallai ya gogu ba har karshen rayuwarta, amma Hajiya ina son ku sani, kamar yanda marainiyar nan tayi bankwana da farin ciki to wallahil azeem kuma hakan ne xai same ku a a xuri’ar ku barin shi Aliyun, He will know no peace da hakkin marainiya a kansa, who knows tunda tace likita ne shi signs na pregnancy din ya gani ya koreta, in sha Allahu sai kun yi da kun sanin abinda ku ka aikata ma yarinyar nan” yana kai wa nan ya karasa gabanta ya ciro ID card a gaban rigarsa ya nuna mata yace “Barrister Aliyu Umar, or just sudais.. we might meet some other time in sha Allah…. Or probably not” ya fadi hakan yana gesturing da hannunsa, khadijah da gabanta yayi mugun faduwa ta dago da sauri tana kallonsa wasu hawayen masu xafi na xubo mata, wani dariya Anty khadijah tayi tana tafe hannu tace “Are you threatening us?” Ya girgixa kai yana murmushi yace “Noo, not at all, kilan idan kika gaya masa aika aikan da yyi xai iya biyota, here is my complimentary card…” Ya ajiye card din gefen kujera, dauka tayi ta yayyage ta xubar nan kasa a gabansa tana huci tana kallonsa, yayi murmushi ya kalli khadijah yace “Tashi mu je” khadijah ta mike a hankali ta bi bayan sudais da har ya isa kofa, tana goge hawayen ta har ta iso gun motarsa, shi ya bude mata motar ta shiga ya rufe ya xaga ya shiga maxaunin driver, har suka hau titi bai ce komai ba ta hade kai da gwiwa tana rera kuka ko xata ji saukin tukukin da xuciyarta ke mata, A bakin hanya sudais yyi parking ganin masallaci ya fita don yin sllh da bottle water ya dawo motar, bayan ya sha ruwan ya ci gaba da driving dinsa, ya hade rai yace “Will you stop those tears and start thinking of how to face reality” ba shiri tayi shiru tana shessheka ya ci gaba da tukin sa. Dab da isha suka shigo kano, direct ya nufi hotel bayan yyi parking yace “Gobe da safe xa mu je gidan Step mum dinki” a tsorace take kallonsa, ya bude motar ya fita yace “Ki fito” daga haka ya wuce reception, daki biyu ya amsar masu, ya siya masu abinci a nan reception din sannan suka wuce sama, yana tsaye daga bakin kofar dakin da ya bude mata ta shiga na hotel din yace “Make sure you try and pray, ki daure ki ci abinci kiyi wanka sannan ki kwanta” spare ki ya cire yace “Don’t leave the key jikin kofar” daga haka ya juya ya shiga nasa dakin, wanka kawai yyi, yyi sallah abincin ma bai iya ya ci da yawa ba ya kira mami, bayan sun gaisa ta tambayesa ya hanya, yace “Alhmdllh mami gobe xan dawo in sha Allah” tace “Toh maa sha Allah, in ji anyi nasara” yace “In sha Allah mami” tace “Toh Alhmdllh” a hankali yace “Am very tired mami xan kwanta” tace “Toh Allah huta gajiya” yace “Ameen” daga haka ya kwanta nan da nan bacci me nauyi ya daukesa, bai farka ba sai karfe uku, mikewa yyi xaune da sauri ya dau shirt dinsa ya sa ya dau spare key dinta da ya cire ya fita dakin ya nufi nata, saka makullin yyi ciki yana addu’ar Allah yasa ta cire makulli jikin kofar, yana murdawa ya bude ya tura kofar dakin, xaune ya ganta ta jinginar da kanta jikin gado, ya karasa da sauri ya durkusa gabanta yace “Kin samu kin ci abincin kuwa Amira?” Shiru yyi yana kallonta ganin yanda idonta ya kumbura, ya sauke idonsa kan ledan abincin da ya ajiye mata jiya da daddare, bude ledan yyi yaga bata taba abincin ba, ya wani hade rai yace “What’s wrong with you, tun dare kike kuka har yanxu?” Ta girgixa masa kai da sauri muryarta na rawa ta nuna masa kirjinta tace “Yana min ciwo” sauke ajiyar xuciya yyi murya can kasa yace “Kin yi wankan?” Ta girgixa masa kai, yace “Sallah fah?” Nan ma girgixa masa kai tayi, mikewa yyi ya shiga bathroom da ke dakin ya hada mata ruwan wanka ya fito yace “Tashi ki je ki yi wanka, you will feel more better” a hankali ta tashi ta wuce bathroom din, yana ta xaune har ta fito da kayan ta da Hijab ta kwanta kan gado ta dukunkune waje daya, ya mike ya rufa mata bargo, ba a dau lkci ba ya ga alamar bacci ya dauketa, tashi yyi ya kashe wutan dakin ya nufi kofa ya fita ya rufe. Da asuba bayan sudais ya idar da sllh ya koma dakinta yaga har lkcn bacci take ya koma dakinsa shi ma ya kwanta. Da safe ya fita hotel din don nema mata kunu, wani almajiri da ya gani kan hanya ya ba kudin ya tafi gun masu siyar da kosai ya siyo masa kunu, yana ta jiransa gaban wani store har yaron ya dawo da kunun a cikin leda, karba yyi yyi masa godiya ya bar masa canjin dari takwas din don na Dari biyu yaron ya siya, ya mike ya amshi ruwa bakin store din da yake ya dawo kan bench ya xauna ya bude bottle water din ya sha kadan ya xubda sauran sannan ya juye kunun ledan a ciki ya mike ya koma hotel din, tashinta yyi daga baccin da take ganin tun jiya bbu abinda ta ci, ta tafi bayi ta kuskure bakinta kamar yanda ya ce mata, da alwala ta fito yana ta xaune yana jiran ta gama sallah, duk ta galabaita kafin ta idar, ya dawo kusa da ita ya mika mata bottle din kunun bayan ya bude yace “Gashi ki sha ko ba yawa kin ji” kai ta gyada masa ta karba ta kai baki a hankali har wani rawa hannunta yake, kusan rabi ta sha kunun ta ajiye ta jinginar da kanta da gado, yace “Ki daure ki kara kadan” ta girgixa kai da sauri tace “A’a xan yi amai idan na sha kuma” rufewa yyi yace “Toh ki kwanta kafin in yi wanka xa mu je can gidan step mum dinki” shiru ta yi ta bi sa da kallo har ya fita dakin, da yake ba ya rabo da spare clothes a motarsa can ya tafi ya dauko kayansa yana gama wanka ya canxa. Ko da ya dawo dakin idon Khadijah a lumshe yake duk da ba bacci take ba, tausayin kanta kawai take don bata san wani irin rayuwa xata fara yanxu ba kuma, ita da ba kowa gareta ba a duniyar, muryarsa da taji ya sa ta bude ido da sauri don bata ji shigowar sa ba, ta mike xaune yace “Let go, it’s almost nine yanxu” tashi tayi ta sauka daga kan gadon, ya dau ledan abincin jiya da bata ci ba ya fita tana biye da shi a baya, nan reception ya bada makullan dakin ya nufi wajen hotel din xuwa Parking lot, ya bude mata front seat ta shiga sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, sai da ya hau kan titi yace “Ina ne gidan step mum din naki yake?” Kamar xata yi kuka tace “Wllh tsoro nake ji kuma tace kar in kashe mata aure, I don’t want to be the cause of that” yana kallon titin gabansa yace “Kar ki damu you will remain inside the car, while we talk” kai ta gyada masa a hankali hawayen dake makale idonta ya sakko, yace “Clean those tears now” da sauri ta goge idonta, tana ta nuna masa hanyar gidan bayan sun shigo anguwar, ganin sun kusa a hankali tace “Plss ka tsaya da motar a nan kaga gidan can” ya tsayar da motar ya na kallon gidan da take nuna masa, kashe motar yyi yace “Ya sunan step mum din ki?” Tace “Hajiya Amina” bude side dinsa yayi ya fita, ta bi sa da kallo ganin yanda yake tafiya har ya isa kofar gidan ya tsaya, wani yaro ne ya fito gidan dake kusa da gidan ya kirasa, yaron ya taho sudais ya duka yana kallon yaron yace “Big boy… shiga gidan nan kace ana sallama da Hajiya Amina” yaron yace “Toh” sannan ya shige gidan da sauri, ba a dau lkci ba sai ga Shafah da Hasana sun fito ko wacce daga mai riga a kai a matsayin mayafi sai mai wando, Sudais ya dinga kallonsu daga sama har Kasa, Shafa dake ta kallon sudais tace “Sannu da xuwa bawan Allah” yace “Ina kwanan ku” a tare suka amsa masa, ya shafa lallausan gashin kansa da ke kara masa kyau yace “Dama Hajiya Amina nake son gani” a tare suka hade rai Hasana tace “Yar uwar ka ce?” Ya girgixa kai tace “Halan kudi xaka karba gunta? Toh Allah sa dai ba yawa, don kuwa Amina xamanta ya xo karshe gidan nan tun shekaranjiya don kuwa Alhaji ya saketa, yanxu haka ko tsinkenta babu a gidan” Kallonsu Sudais yake a sanyaye, Hasana tace “Atoh, ban da mugunta ki tura yar mutane karuwanci don ba ke kika haifeta ba yarinya marainiya bata da kowa duniyar nan banda Allah, dama an ce idan mutum xai gina ramin mugunta yyi ta yar karama…. To ita kam da xurfi tayi sa gashi ta afka ciki” Sudais da ko kadan bai san ma abinda suke cewa ba yyi karfin halin cewa “Toh don Allah kun san garinsu?” Shafah tace “Halan kudin da yawa, matar da har gorin cin bashi take mana ashe a boye take nata” Hasana tace “Mun dai ji kishin kishin a gari ta siyar da duk kayan dakin nata wai xata koma kasarsu, ka san 6are ce ba yar Nigeria ba” Sudais yace “Ina ne kasar ta su?” Shafah tace “Wai ko Ethiopia ko morocco ko Sudan oho dai… amma nan Africa ne, mu dai Allah ya raba mijinmu da alakakai” juyawa sudais yyi ransa a dagule ya nufi motarsa yana shiga ya hade kai da steering yana tunanin ta ina xai fara, ya xai yi da yarinyar nan da kowa ke kira da marainiya, khadijah da ke ta kuka tun bayan fitarsa cikin rawar murya tace “Ummata na fushi da ni har yanxu koh?” Dago kansa yyi yana kallonta da idanuwansa da suka sauya kala.

    Tada motar sudais yyi bai ce komai ba suka bar layin, ban da kuka babu abinda khadijah take har da shessheka, duk a tunaninta Umma ta ki hakura ne ta kori sudais, yana driving a hankali yace “Bana son wannan kukan da kike cika min kunne da shi plss, if you are in pain it’s better you pray, plss kukan ki yana damuna da yawa” a hankali khadijah ta hadiye kukan tana share hawayenta a sanyaye, bayan wani lkci sudais yayi breaking silence din cikin motar a hankali yace “Ur step mum is gone Amira” da sauri khadijah ta kallesa xuciyarta na bugawa sosai tace “To where?” Yana ci gaba da driving dinsa yace “Dama ba Nigerian bace Ita?” Khadijah na kkrin mayar da wasu sabbin hawayen da ke taruwa idonta tace “She told me she is not a Nigerian… I don’t knw her country” ya lumshe ido ya bude yace “Toh ta koma kasar su in ji Co wives dinta, since the day before yesterday ta wuce” cikin rawar Khadijah tace “Me yasa?” Kallonta yyi ya dauke kai bai ce komai ba, sai dai baya son gaya mata aurenta ya lalace kamar yanda su Hasana suka gaya masa, Bayan kusan minti biyar murya can kasa yace “Look, you just have to face reality Khadijah, keep all those tears and crying aside, don’t cry any longer it has no use” kai kawai take gyada masa kuka na cin ta amma bata yarda ta yi ba, nan ko shi ma hankalin sa a tashe yake kamar yanda nata yake a tashe amma yayi kokarin boye hakan yana lallashinta ita, bai san yanda xai yi da ita ba, bai san inda xai kai ta ba, bai san inda xai ajiyeta ba, bai ma san ta ina xai fara ba, tunanin hakan yasa yace “Ya Allah” bai san ya fito fili ba sai da khadijah dake ta share idonta ta kallesa, ya shafa kansa yana ci gaba da driving dinsa, Nearest filling station ya shiga domin kara Fuel kafin ya dau hanyar Damaturu, tun da suka shigo station din xuciyar khadijah ke tashi jin warin fetur, ta dai rufe fuskarta da Hijab din jikinta a hankali, Sauke glass yyi yana fadi ma mata mai siyar da man na nawa xata xuba masa, tana fara xuba man khadijah ta fara kkrin bude mota ya juya yana kallonta da mamaki yace “What?” Ganin yanda ta toshe baki yyi saurin bude lock din motar ta fita, tana fita kuwa ta shiga kwarara amai nan kasan wajen, sudais ya dafe kai a hankali a ransa yace Ai shi ya shiga uku…. Ganin wata mata ta fito daga motar dake bayan nasa yasa shima ya bude motarsa a hankali ya fito, matar ta riketa tana mata sannu kamar yanda kowa na gun ke yi mata, sudais ya xagayo ya tsaya ya ma rasa abinda xai ce, mai siyar da fuel din ta tafi gun siyar da drinks a filling station din ta karbo ruwan gora daya ta dawo matar da ke rike da khadijah ta bude ta mika mata khadijah ta karba da kyar tana wanke fuskarta da ruwan, mijin matar dake rike da khadijah ya fito shi ma yana ma khadijah sannu, matar ta kalli Sudais tace “Bari ta shiga motar sai ku wuce” barin wajen sudais yyi matar ta taimaka ma khadijah ta shiga motar sannan ta rufe, mai siyar da mai ta debo kasa tana xubawa wajen aman, Cike da karfin hali sudais yace “Toh mun gode kwarai” matar tace “Ayya ba komai, Allah ya sauwake, ya kuma raba lafiya” Sudais ya juya da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Ameen mun gode” daga haka ya xaga driver seat ya kara yi ma mai siyar da mai da mutanen wajen godiya ya shiga ya tada motar suka bar filling station din, Har suka hau kan titi bai ce komai ba tunanin da yake a ransa daban, can ya saci kallonta yaga idonta a lumshe ta jinginar da kai da kujera, kwantar mata da kujerar yyi ta bude ido da sauri, sai a sannan murya can kasa yace “Sorry” Bata iya ta amsa masa ba ta mayar da idanuwanta ta rufe daga nan bacci ya dauketa. Buga kujerar motar da take kai taji ana yi cikin bacci, ta bude ido a hankali Sudais dake kallonta yace “Come down” kalle kallen inda suke ta shiga yi taga kamar gidan Sudais ne, ganin har ya fita yasa ta bude motar a hankali duk jikinta ba kwari ta fito ta bi bayansa, yana tsaye parlor yana jiranta bayan ta shigo, ya nufi wani bedroom ba wanda ta fara xama ba ya bude ya juyo yana kallonta yace “Go inside xan kawo maki bedsheet yanxu ki shimfida sai ki kwanta ki huta” daga haka ya wuce ba a dau lkci ba ya dawo da bedsheet din ya bata sannan ya fita ya kulle kofar, yanda yace tayi haka tayi ta kwanta a gajiye ga baccin da ke idonta, nan da nan bacci ya sake dauketa, sai kusan azahar ta farka da kyar ta dalilin sanyin da ta dinga ji alamar xaxxabi, cike da karfin hali ta mike ta shiga toilet din dakin ta dauro alwala ta fito tayi sallah, tana idarwa ta jinginar da kanta da gado hawaye na sakko mata, ta dau lkci me tsayi a haka aka yi knocking kofar, da sauri ta dago kanta tana goge hawayen idona, jin an kara bugawa ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, tsaye ta gansa bakin kofar rike da leda babba da karami, bai ce komai ba ya shiga dakin ta bi bayansa, sai da ya ajiye ledan hannunsa yace “Tun daxu kike kuka kenan?” Kai ta gyada masa, yace “Good, kukan me kike?” Kamar ya dada tunxurata ta kuma fashe masa da kuka sosai ta durkushe wajen har da shessheka, cikin raunin murya tace “Ni bani da kowa yanxu, I don’t knw if I have any use, i….” Ta fashe da wani matsanancin kukan, ya durkusa kusa da ita shi ma a hankali yace “Noo, you have use Amira, kar ki sake cewa baki da kowa, or don’t you have trust in Allah?” Ta kallesa da sauri tana share hawayen idonta cikin rawar murya tace “I do” ya d’an yi murmushi yace “Then have faith in him” ledan da ya ajiye ya nuna mata yace “Ki yi wanka ki canxa kaya, take some fruits after that sai kiyi sllh ki kwanta ki huta sosai” daga haka ya mike ya fita ya kullo mata kofar, ta fi minti goma a durkushe yanda ya bar ta daga karshe ta tashi ta bude ledan taga sabulu har da toothpaste da brush, sannan ga inners da dogayen riguna uku da hijab, duk jikinta yyi sanyi, ta mike ta shiga bathroom din ta yi wanka ta fito, Apples kadai ta iya ci cikin fruits din bayan ta gama shiryawa sannan ta kwanta lkci daya kuma bacci ya sake dauketa. Buga gefen gadon taji ana yi cikin bacci ta bude ido a hankali, ganinsa gefenta ta mike xaune da sauri, yace “Ur temperature is running high, are you feeling pain anywhere?” Ta girgixa masa kai tace “A’a” yace “Ba ki yi sllh ba…..” Kallon agogo tayi taga karfe bakwai ya wuce, ta kallesa da sauri tace “Dare yayi?” Yace “Yea, you slept all day ai” sunkuyar da kai tayi, yace “Me kike son ci yanxu?” Shiru tayi kamar me naxari, yace “Say it” a hankali tace “Kila gyada” ya d’an bude ido yace “What? Groundnut?” Shiru tayi tana kallonsa, da wani expression a fuskarsa yace “Ina xan samo gyada da daddaren nan?” A takaice tace “A titi” kauda kansa yayi, khadijah dake ta kallonsa bayan kusan minti biyu a hankali tace “Ka barshi kawai bana jin yunwa tunda dare yyi, am not even hungry…” wani kallo yyi mata ta gefen ido ya mike ya nufi kofa kamar xai tashi sama ta bi sa da kallo har ya fita, a hankali ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka nmta wanke baki sannan ta dauro alwala ta fito, tana ta xaune kan darduma bayan ta idar da sllh, yanda xata koma kan gado ne ta kasa tashi duk jin jikinta take kamar ba nata ba, gaba daya bbu karfi tattare da ita, har bacci ya fara daukarta a xaunen taji an bude kofa, ta dago da sauri, karasowa yyi kusa da ita ya ajiye ledan hannunsa ya koma gefen gado ya xauna, Kallonta kawai yake yace “Ga gyadar, after I’ve gone round of d whole of damaturu” Khadijah ta wara ido tace “All the round of damaturu?” Bai ce komai ba ya hade girar sama da ta kasa, a hankali tace “Nagode” bude ledan tayi taga dafaffen gyada ce da Wanda aka gasa a wani ledan daban, dafaffen ta fara ci, da ta juya xata ga ita yake kallo, duk sh was uncomfortable na kasa cin gyadan, can dai ta sake kallonsa tace “Bismillah” bai ce komai ba, can ya sakko ya xauna kusa da darduman, ya dau gyada daya ya bude, haka ya dinga bude su har suka yi yawa sannan ya mika mata ta karba tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace “Eat” ba musu ta fara ci, ya kuma bude mata wasu masu yawa, ya mika mata, haka ya dinga mata har tace masa ta koshi, yace “Are you sure?” Tana yatsina fuska tace “Kamar amai xan yi” hade rai yyi sosai yace “Don’t try dat malama, kinsan garin da naje na samo gyadar nan” khadijah ta ja baya tana nodding masa kai, can ya shafa kai a hankali murya can kasa yace “Just relax xaki daina jin aman” ta kuma gyada masa kai ta jingina da jikin gado ta lumshe ido, ji tayi aman xai taho mata, ta toshe bakinta da hannu biyu tana girgixa masa kai kamar xata yi kuka tace “Wayyo xuwa xai yiii” tashi yyi da sauri ya shiga bathroom ya debo ruwa, ya dawo ya durkusa kusa da ita ya cire Hijab din jikinta, ya watsa mata ruwan a fuska da gashinta, har ranta taji sanyin ruwan ta koma baya da sauri tana sauke ajiyar xuciya, a hankali yace “Sorry” wani ajiyar xuciya ta kara saukewa jin aman ya d’an lafa mata, ta kallesa da kyar tace “Xan kuskure baki” table water dinsa da ya shigo da ya mika mata ta tashi ta wuce bathroom da sauri, bata fito bayin ba sai da ta amayar da gaba daya gyadar da ta ci, ta fito da kyar ta xube nan tsakiyar dakin tana satan kallon sa tana mayar da numfashi, wani kallo ya dinga mata Daga inda yake xaune, bata sake kallonsa ba ta lumshe ido, lkci daya kuma bacci ya dauketa, gashin kanta taji ana gyara mata ta bude ido da sauri ta gansa durkushe gefenta yace “Ki rufe gashin ki ki hau saman gado” ba musu ta mike xaune ta hade uban gashinta waje daya ta tufke, xata mike tsaye jiri ya kwasheta ta koma da sauri ta xauna yace “Be careful” gyada masa kai tayi ta kuma tashi ta koma kan gadon ta kwanta, ac dake dakin ya rage yace “In kashe maki wutan?” Ta girgixa masa kai, yace “Sai da safe” daga haka ya fita ya kullo mata kofar dakin. Kafin asuba Sudais ya shigo ya fi sau biyar duba ta don da ya bude kofa xata farka, gaba daya ya kasa bacci tunanin yanda xai yi da khadijah ya damesa gashi mami Bata san ya dawo ba ma, shigowarsa na karshe ne ya rufe ta da blanket don xaxxabi ne sosai jikinta, da asuba da ya shigo tashinta tayi sllh amai tayi ba kadan ba kafin ta dauro alwala ta fito, ruwan wanka ya hada mata bayan ta idar da sllhn, da kyar ta yi wankan ta fito, ta kasa shiryawa ta kwanta nn kan gado ya lullubeta da bargo, bayan kusan minti sha biyar ya dawo gefenta yace “Daure ki tashi ki shirya mu tafi clinic” bata ce komai ba don har fuskarta ta rufe, ya cire bargon suka hada ido, sauke idonsa yyi yace “Tashi ki shirya” daga haka ya fita dakin, har ya dawo bata tashi ba, yace “Ke fa nake jira” cikin sanyin murya tace “Ni baxan iya ba” yace “Toh ni xan sa maki kayan?” Bata ce masa komai ba, yace “Look bana son in dawo in gan ki cikin bargon nn it’s better ki daure ki tashi kiyi abinda xa kiyi” juyawa yyi ya fita, cike da karfin hali ta mike xaune hawaye cike idonta, kamar ynda yace mata haka ta dinga daurewa har ta sa kayan a nan inda take kan gadon, tana gama sa wa ta koma ta kwanta, bayan kusan minti goma ya dawo dakin, tsayawa yyi kusa da gadon yace “Toh tashi mu je” rasa abinda xata ce masa tayi, can dai ta mike xaune a hankali tana sauke numfashi, Wayarsa ce ta fara ring, ya daga yana kallon screen din kafin ya xauna da sauri ya daga ya kai kunne tare da sallama yace “Good morning Mami” murmushi yyi yana shafa gashin kansa a hankali yace “Ku yi hakuri Mami ban kira ba, amma in sha Allah yau xan taho, am done with what am doing” bayan wani lkci yyi mata sallama ya mayar da wayar aljihu, yana kallon khadijah yace “Tashi mu je” daga haka ya nufi kofa, a hankali ta sakko da kafafuwanta kasa tayi karfin halin mikewa, har suka isa compound din gidan bai juyo ba, sai da ya isa gun motarsa ya juyo yana kallonta, can ya bude motar ya shiga, ta karasa ta bude front seat ta xauna ta lumshe ido don ji take kamar wani aiki me wahala tayi, wani babban private asibiti suka tafi, bayan yyi parking ya juyo yana kallonta da kyau yace “Har mu bar clinic din nn bana son jin bakin ki, am nt asking for ur opinion or anything, I am doing wat I think is right, am I clear?” A hankali ta gyada masa kai, yace “Good” da yake da safe ne ba su wani dde ba suka samu ganin likita bayan ya biya kudin kati, ta xauna daya daga kujeran dake kallon likitan, ya xauna shi ma yana facing dinta, hannu ya ba likitan suka gaisa, likitan na kallonta murmushi dauke fuskarsa yace “How you madam, though u look sick” khadijah tayi murmushin karfin hali, likitan yace “Allah ya sauwake, ya raba lafiya,” kallon Sudais dake shafa beard dinsa yyi yace “Drugs xan rubuta maku yanxu da xata dinga sha, there is nothing more I think…. She will get better gradually” Sudais ya ce “Ba abinda ya kawo mu ba kenan Dr, though I knw it might look wrong, but… she got pregnant by mistake, it’s just some weeks old, so plss I want u to get rid of it….” Tunda ya fara maganan likitan ke kallonsa da expression din mamaki, Sudais yyi kasa da murya yace “Yes plss” likitan yace “Sorry we don’t do that hear sir, xaku iya tafiya wani asibitin” kallon Sudais khadijah take kamar idanuwanta xa su fito, Sudais yyi kasa da murya sosai ya marairaice yace “Yeah, I knw it’s very wrong Dr… But she is my…. Wife, the last pregnancy wasn’t funny, and.. She’s breastfeeding an eight month old baby now” kamar ana forcing dinsa yyi magana, likitan sai kallon khadijah yake, Sudais ya ciro handkerchief ya share goshinsa don har xufa ya keto masa yace “Plss Dr, ka taimaka for d sake of d eight month child” Likitan ya girgixa kai yace “I think xai fi a daina breastfeeding babyn, she shud take care of d one she’s carrying now, sai kaga Allah ya taimaka komai ya xo da sauki” Sudais yace “Nooo Dr, don Allah ka cire mata I will pay what ever amount u request for plss” likitan ya mike ya nufi show glass dake office din ya dauko wani allura da syringe, ya dawo yace “I will give her this injection sauran drugs din kuma xan rubuta maka kaje pharmacy ku siya” Sudais ya sauke ajiyar xuciya yace “Thanks very much Dr, nagode sosai” Lkci daya khadijah t fashe da kuka ta mike tace “Nooo, ni bana son a cire min don Allah ku yi hakuri” bude baki Sudais yyi yana kallonta da mamaki, ta hade hannuwanta tana girgixa masa kai hawaye na sakko mata a hankali tace “Don Allah kayi hakuri, I don’t want to abort d pregnancy, Allah will be angry with me plss” Likitan ya ajiye alluran ya rungume hannuwansa yana kallonta yace “Ba mijin ki bane kenan?” Hawaye na ci gaba da sakko mata ta gyada masa kai alamar eh, Sudais dake mata wani irin kallo ya mike yace “Sae ki san inda dare yyi maki kuma daga nan” daga haka ya fice daga office din kamar xae tashi sama, a hankali take kuka tana kallon likitan dake kallonta yana girgixa kai, can ta nufi kofa cikin sanyin jiki ta fita, babu motarsa a parking space, ta fita gate tana share hawayen da ya ki tsaya mata.

    Har Khadijah ta isa bakin titi kuka take bata damu da mutanen dake kallonta ba, ta ma rasa inda xata bi gashi ko sisi bata da shi, all this while Sudais na cikin motarsa yyi parking motarsa ya dinga bin ta da kallo har ta d’an yi nisa, ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido yana kiran Allah a xuciyarsa, he is just confuse, a hankali ya ci gaba ya fara driving motar har ya iso dai dai inda take ya tsaya ya wani hade rai cikin tsawa yace “Ina kika san xaki tafi yanxu?” Ta juyo a tsorace tana kallonsa ta tsaya bata ce komai ba, yace “Shigo mu je” fuska daure yyi maganan, A sanyaye ta xaga ta bude motar tana kallonsa ta shiga, bai ko kalleta ba ya ja motar, har ya isa gidansa bai ce mata komai ba, ita ko tayi nisa cikin tunanin da take ya bude motar ya fita ta bi sa da ido, Juyowa yyi ganin bata fito ba Yace “Should I bring u down?” girgixa kai tayi ta fito ya kulle motar ya nufi entrance din gidan ta bi bayansa, kana ganin yanda yake tafiya kasan a gajiye yake, xaune ta gansa parlor ya jinginar da kansa jikin kujera bayan ya xauna ya lumshe ido, a hankali ta xauna kasa ta takure waje daya sbda sanyin parlon, bude ido yyi bayan wani lokaci ya kalleta, suna hada ido ya dauke kai, khadijah dai sai kallonsa take, yanda ya tsura ma ac dake aiki a parlon ido yasa xaka gane tunani yake, a hankali khadijah tace “Xan yi wanka…” sai a snn ya juya ya kalleta, a takaice yace “In kai ki bayin kenan?” Ta girgixa masa kai, yace “Toh tashi ki tafi” mikewa tayi ta wuce dakin da ya saukar da ita, wanka tayi ta fito ta shirya ta sa Hijab, yana nan yanda ta bar sa, har ta iso kusa da shi kuma bai sani ba, duk jikinta yyi sanyi ta durkusa nan kusa da shi cikin sanyin murya tace “I knw I am a burden, u don’t knw where to start from, and u don’t want to send me away cos you’ve got a good heart… You look so responsible to keep me in ur home, you have parent and elders that won’t take it likely…. I don’t want to be d beginning of ur problems, sbda haka nake rokon ka don Allah ka taimakeni ka kai ni gidan marayu kamar yanda na roka a baya, I will cope there in sha Allah, I will take care of the motherless there, but I want u to do me the favour of coming to see me, even if it’s just once in a year plss, I want to feel I have somebody in this world, don Allah kar ka mance ni bani da kowa” tana kai wa nan hawayen dake makale idonta ya sakko, kallonta kawai sudais yake, can ya runtse ido ya bude ya mike ya fice parlorn, hade kai tayi da gwiwowinta tana kuka a hankali tana me tausayin rayuwarta, sai bayan kusan minti talatin sudais ya dawo parlorn, duk da ta ji shigowarsa bata dago kanta ba, muryarsa taji yace “tashi ki shiga daki kiyi kukan da kyau” ba musu ta tashi ta wuce cikin dakin, tayi kukan kamar yanda yace mata har ta gaji ta kwanta ta takure waje daya, bude kofar dakin yyi ya shigo, ta daga kai tana kallon sa har ya iso inda take yana tsaye yace “Good, am hoping all the tears you where planning to shed while in this house kin yi su yau kin gama, cos I am nt gonna tolerate that, clear? Better ki barni in ji da daya” Mikewa xaune tayi ta gyada masa kai tana share guntun hawayen idonta, yace “Me xa ki ci?” Ta girgixa kai tace “Bana jin yunwa” ganin kallonta yake a hankali tace “Toh xan ci apple” yace “Not apple, I mean food” ta d’an yi shiru, can ta dago tana kallonsa a hankali tace “Wainar flawa” wani kallo yake mata yace “Meye shi?” Taace “Da flour, albasa, tarugu, maggi, gishiri and man gyada ake yin sa, Anty Kyauta tayi mana a can gidan” da mamaki yace “A ina xan samo maki shi?” Tayi shiru bata ce komai ba, ya fi minti biyar a tsaye, can ya tabe baki ya fiddo wayarsa a aljihu yayi dialing number ya kai kunne, ba a dau lkci ba ya amsa sallaman da aka yi masa yace “Rabi’ah am on my way now, pls ina son ki min….” Juya ido yyi kamar me son tuno sunan abun, can ya cire wayar a kunne da sauri ya jefa ma khadijah wani kallo yace “Meye sunan ma?” A hankali tace “Wainar flawa” ya mayar da wayar kunne yace “Wainar flawa” Khadijah na jin yarinyar na dariya ya tabe baki ya katse wayarsa ya mayar aljihu ya fice a dakin. Khadijah na nan yanda ya bar ta ya dawo dakin, yana kallonta yace “ermm, ohk let me say Amira, you see xan je gida yanxu, but baxan dade ba xan kawo maki abincin, xa ki iya tsayawa ke kadai ai koh?” Ta gyada masa kai yace “Good, I will be right back now” kashe ac din dakin yyi ya kunna mata kayan kallo daga haka ya nufi kofa khadijah tace “Allah ya tsare” juyowa yyi ya kalleta yace “Amin” daga haka ya fita ya kulle mata kofar. Kwanciya tayi duk da sonta da kallo ta rufe idonta. Tun da sudais ya shiga gidansu yyi parking gabansa ke faduwa ya bude motar a hankali ya fita ya wuce cikin gidan, jin ana soye soye a kitchen ya karasa kitchen din, Rabi’ah ce tsaye tana soya wani abu da bai taba gani ba yace “What’s this” wara ido tayi ganinsa tace “Sannu da xuwa yaya, wainar da kace mana” yace “Dama kamar kwai yake?” Ta gyada masa kai tana yar dariya ya tabe baki yace “Mami fa?” Tace “Tana bedroom da su Anty Maryam” bai ce komai ba ya haura sama yyi sallama kofar dakin maminsa, Kanwar mami da kanninsa biyu dake Dakin ne suka amsa masa ya shiga ciki, kallon uban kayan dake jibge a kasa ta ko ina a dakin, ga boxes masu tsada dake ajiye su ma, dukawa yyi ya gaida mami ta amsa da fara’a tana masa tambayar ya hanya, yace “Alhmdllh” sannan ya gaida Anty Maryam ta amsa da murmushi tace “Welcome barrister” sai a sannan ya amsa gaisuwar kanninsa ya mike ya koma can karshen gado ya xauna, Mami tace “Ka ga sai yau Maryam ta karbo sauran akwatunan xa a xuba kayan ciki yanxu” a hankali yace “Ohk” Mami tace “ka gama gyaran da kace a can gidan naka” ya gyada kai yace “Eh Mami” Mami tace “Toh maa sha Allah” Yana ta xaune har suka gama jera gaba daya kayayyakin a akwatunan, kanninsa su Humairah suka fita dakin ya rage daga shi sai Mami da kanwarta, Mami tace “Lkci na ta tafiya sudais yaushe ka ga ya kamata a kai kayan” tasowa yyi a hankali ya dawo kasan carpet ya xauna kansa a kasa murya can kasa yace “Mami…” Mami dake ta kallonsa kamar yanda Anty Maryam ma ke kallonsa tace “Ya aka yi sudais?” Kasa dago kansa yyi yace “Mami ina son a dakatar da kai kayan nan yanxu ne….” Mami dake masa kallon mamaki tace “Ko saboda me Aliyu?” Ya girgixa kai yace “Mami a dai dakata kawai” Anty Maryam tace “Ko Jiddahr ta yi maka wani laifin ne sudais?” Shiru yyi bai ce komai ba, Mami tace “Toh ni dai abinda xan ce maka a nan shine idan dai kasan ba shiririta bane, ba wani concrete laifi bane ka ajiye wannan shashancin da kake fadi aside, idan kuma kaga laifi ne babba to shkkn” Anty Maryam tace “Ka fada mana me tayi, wani laifin ka kama ta da shi Sudais, Kar mu xama kananun mutane” ya girgixa kai a hankali yace “A bar xancen kawai mumy” Mami tace “Toh Allah rufa asiri” yace “Ameen” mikewa yyi yace “Xan fita in dawo yanxu Mami” daga haka ya nufi kofa Mami ta bi sa da ido har ya fita, Anty Maryam tace “Kar ki tilastata masa don Allah Mami tun da kika ga haka ba karamin laifin ya kamata da shi ba, kin dai san halin sudais da xurfin ciki ko xaki shekara kina tambaya ba fada xai yi ba” Mami dai bata ce komai ba. Sudais na fita ya shiga kitchen ya tarar Rabi’ah ta gama wainar ta xuba masa a warmer, ya bude warmer din yana ta kallon abincin kafin ya tabe baki ya dauka ya fito parlor, da mamaki tace “Yaya ba a nan xaka ci ba?” Yace “Ehh ni da frnds dina xa mu ci, sai na dawo” daga haka ya fita gidan ya hau motarsa ya wuce. Sai da Sudais yyi azahar a masallacin layin gidansa sannan ya shiga gidan misalin karfe daya da rabi, jin an bude kofa Khadijah dake bacci ta bude ido da sauri, karasowa yyi yana kallonta ya ajiye warmer din hannunsa yace “Tashi ga abincin” ta xauna ya bude mata warmer din, ba don tsare ta da yyi ba da daya ma baxata cinye ba amma haka ya dinga forcing dinta har ta cinye biyu, sai dai duk she was restless don amai kawai ta dinga ji, ya hade rai sosai yace “Look idan ki ka yi aman nn I will nt bother my self about ur food again am telling you” hawaye cike idonta tace “Kayi hakuri wllh ba ni bace” ya xauna gefen gadon yace “Toh nayi, amma ki daure kar ki yi…. Just try” ta gyada kai ta koma xata kwanta ya ce “Toh ai hakan xai sa ki yi aman” dagowa tayi da sauri ta xauna, toshe baki tayi tana girgixa kai, ya wani hade rai kamar bai taba dariya ba yana kallonta, a hankali tace “Wllh amai xan yi kayi hakuri” daga haka ta mike ya fixgota har sai da ta kusa fadawa kansa, yace “Am serious baxa ki yi ba” bai rufe baki ba ta kwarara masa aman gaba daya a jikinsa da bedsheet, wani kallo ya dinga mata yana yamutse fuska, can ya runtse ido har ta gama aman, Khadijah ta kasa kallonsa sae sauke numfashi take, wani tsaki da bata taba jin irinsa ba ya ja a fusace ya mike ya shige toilet, hawaye ya dinga sakko mata a sanyaye ta hade kai da gado, bayan kusan minti goma ya fito, ita dai tana nn yanda take, taji ya dafa ta ta dago da sauri, singlet da 3qtre ne jikinsa, ya sauke idonsa yace “kije kiyi wanka na sa maki ruwa” ta girgixa masa kai tace “Baxan iya ba ynxu” yace “No ki daure” daga hka ya sa ta tashi ta wuce bayin, Tana fitowa taga har ya shimfida wani bedsheet din ya cire na da, ta kwanta tana rawan sanyi, ya shiga bayi da xanin gadon, bai fito ba sai da ya wanke da shirt dinsa ya fita dakin.

    Daga wannan rana Khadijah ta fara laulayi me tsanani kamar baxa ta yi ba, tausayinta Sudais yake har ransa, duk ta rame ba kadan ba ga yawan complain din ciwon kirji da take, idan aka ga yanda sudais ya damu sai a rantse ya taba sanin Khadijah, hakan bai hanasa trying best dinsa gun ganin Maminsa bata d’ago komai a rashin dawowa gida da baya yi da wuri da fitan da yake yi da sassafe ba, yawanci duk khadijah ke cinye masa time dinsa, ya kai ya kawo sai ya fi kwana biyu bai karbi case ba tunda he is always by her side kwana ne kadai bai yi gidan nasa, karfe sha daya idan tayi bacci yake barin gidan ana idar da sllhn asuba kuma kafin ya shiga gida sai ya taho gidansa dubata yaga ya ta tashi, Dr Yusuf ke xuwa bata medication kusan kullum da safe da yamma tun daga allura xuwa drugs duk da biyansa Sudais yake, A haka har Khadijah ta cika sati biyu ciff a gidan. Da safe misalin karfe sha daya Sudais yaje can clinic gun Yusuf, bayan sun gaisa Yusuf ya tambayesa jikin khadijah, ya shafa kai yace “Toh ga ta can dai, am just tired Yusuf, wai why not baxa ka taimaka ka cire mata cikin nan ba frnd, am talking to you about this for the 3rd time don Allah ka cire mata ko nawa ka bukata xan baka, plss Yusuf” Yusuf ya girgixa kai yace “My reply will always be the same, I don’t abort pregnancies and I will not, nace ka kai ta wani asibitin ni dai baxan yi ba ka ki ganewa” Sudais ya marairaice yace “Nasan baka cire ciki amma ita wannan case dinta daban ne, she was raped… beside she is too young da ciki dubi fa yarinya ce karama, gashi sai wahala take sha ko don haka ka tausaya mata mana Yusuf” Yusuf dake rubuce rubucensa yace “Ae sai kuma ka yi Barrister” Sudais ya d’an hade rai yace “Haba Dr, ya kke son marainiyar tayi da yaron da xata haifa yanxu, ta ina xata fara rainonsa don ni dai ba dauwama xata yi tare da ni ba na har abada, har ynxu ina tunanin taimakon da xan bata ta tafi ta inganta rayuwarta but nt when she is this sick everyday, dubi fa jiddah gani take kamar na yaudareta ne, but ba hka bane idan aka yi auren ina xan sa ta, kasan it won’t make sense ina da gida in kama haya, dole Mami xata so sanin dalili, infact she will be suspicious, Yusuf don girman Allah ka rufa min asiri ka cire mata jaraban nn ta kama gabanta plsss” Yusuf ya tabe baki yace “xa ma ka gama dadin bakin ka” jin Sudais yyi shiru yana kallonsa ya ajiye pen din hannunsa yace “Sae in har in rubuta maka kaje can pharmacy ka siya nasan baxa ka rasa iya allura ba, duk sai kayi mata da kanka” ban da hararansa babu abinda Sudais yake, Yusuf yace “yes, or you buy her just drugs shkkn amma ni dai ba da hannu na ba” Sudais ya dake trying hard to hide his anger yace “Rubuta min” Takarda Yusuf ya jawo yyi rubuce rubucensa ya mika masa Sudais ya fixge ya nufi kofa Yusuf ya bi sa da kallo yana murmushi, Gida ya nufa bayan ya je garage din mota amso sakon Mami da ta aikesa tun safe, Xaune ya same Mami parlor, tun da ya shigo take kallonsa ganin ramar da yyi har ya karaso ya xauna kasa kusa da ita yace “Ina yini Mami” tace “Lafiya lau, sannu da xuwa” ajiye mata ledan hannunsa yyi yace “Ga sakon Mami” Bata ce komai ba ganin haka ya daga kai yana kallonta, tace “Aliyu ni ban fa gane nufin ka ba kayan akwatunan da kasa nayi jere da shi a daki ka hana a kai, toh Abbanku ya sa in xaunar da kai ka sanar da ni ko fasa auren kayi, wannan ai iskanci ne da kokarin mayar da mu kananun mutane da kake, idan ma da matsala ne ai sai ka yi mana bayani, babu mai maka dole tun da kai ka kawo yarinyar nan kana so ba wani ya kawo maka ita ba, yanxu ni ka gaya min ma’anar cewa da kayi kar a kai kayan a dakata” Sudais da har xufa ya fara keto masa ya shafa kai da kyar yace “Mami ba wai na fasa bane, kawai dai akwai matsala… ina son a min alfarmar ce masu su d’aga ko xuwa sabon shekara da xa mu shiga, idan kuma sun ga baxa su iya dagawa ba to gaskiya na hakura, Allah bata wanda ya fi alkhairi a kai na” Mami dake masa wani kallo tace “A daga a kan wani dalili?” Ya kasa dago kai yace “Kiyi hakuri Mami ayi min yanda nace pls, I just want to figure out the problem, Mami kin fa san aure ba don kwana daya ko ‘yan watanni ake yin sa ba na har abada ne, Mami I don’t want to make marriage mistake in my life don ni bani da burin xama da mace fiye da daya so I want to have the best marriage, ku taimaka ku ce masu a daga har lkcn, idan sun ga yyi masu tsayi to na hakura gaskiya I don’t want to cheat my self” Mami tace “Toh shi kenan, Allah sa mu dace, xan yi ma Abban naku bayani” Sudais ya dan yi murmushi a hankali yace “Nagode Mamina, xan je in dawo yanxu” Mami na kallonsa da kyau tace “Wllh ban gane fitar nan da kake kamar me talla ba kwanan nan sudais, da sassafe ka fice baka dawowa sai kusan sha daya, what’s wrong with you?” Ya dago yana kallonta a hankali yace “Mami wani case ne ya shige min duhu, so ina bincike ne shi yasa kika ga haka” kallonsa kawai take can ta tabe baki tace “Though I knw when you are saying the truth and when u are lying, and duk da nasan karya kake coz I saw it in ur eyes, ni kam sai dai ince Allah tayi jagora, ya kuma yaye maka abinda ke damun ka, wnn ramar kuma da kayi, kayi kkrin ganin cire ko ma ke damun ka plss, it’s better you pray to ur God” Sudais ya dauke kansa daga kallonta da yake ya mike a hankali yace “Toh nagode Mami sai na dawo” tace “Allah ya tsare” daga haka ya fita. Pharmacy ya tsaya ya siya magungunan da Yusuf yyi masa prescribing sannan ya siya fruits kafin ya wuce gidansa, har wani faduwa gabansa ya shiga yi bayan yyi parking cos bai son xuwa ya ga khadijah in pain, ya dai dake ya shiga gidan, kwance ya sameta kamar ko da yaushe a daki idonta a rufe, yawanci duk haka yake xuwa ya sameta kuma ba bacci take ba, yana tsaye a hankali yace “Amira” ta bude idanuwanta a hankali tana kallonsa, yace “Ya jikin” kai ta gyada masa ya durkusa yana bude ledan apples da banana da ya siyo mata yace “Ga Apple nan” ta girgixa kai da sauri tace “Anjima” yace “Toh kin yi sllh?” Gyada masa kai tayi, ya d’an yi shiru sai kuma ya mike yace “Toh tashi ga magani na kawo maki ki sha, you feel more better idan kin sha” kamar xata yi kuka tace “Xan yi amai ni nafi son allura” kallonta ya tsaya yi, can yace “Baxa ki yi ba kawai guda uku ne fa” daga haka ya fiddo magungunan a leda sai kuma ya fita xuwa ya debo mata ruwa, har ya dawo tana kwance ya d’an hade rai yace “Toh tashi mana” mikewa tayi da kyar ya bude maganin gudu uku kamar yanda yace ya bata a hannu ya mika mata ruwa a cup, ta karba tana bata fuska xata yi kuka, ya daure fuska yace “Ki sha Ki ban cup yanxun nan” wayarsa ne ya fara ring ya ciro a aljihu tana ganin haka ta watsa maganin a bayanta tayi saurin kai ruwan baki tana sha dai dai lkcn da ya maido dubansa kanta, da sauri yace “Kin sha?” Ta mika masa cup din tana yamutse fuska, ajiyar xuciya ya sauke a hankali, kokarin amai ta shiga yi da sauri yace “Noooo, don’t ko in bata maki rai” ta koma baya a hankali kar ya xagayo ya ga maganin ta jingina da gado yace “Good girl” daga haka ya fita ya kira Yusuf dake kiransa, da sauri ta kwashe magungunan ta watsar a bayan gado tana turo baki, Sudais ya hade rai bayan ya kai wayar kunne yace “Ya aka yi?” Yusuf yace “Ya ta sha?” Sudais yace “It’s nt ur concern” dariya Yusuf yyi yace “In dai ka tabbatar ta sha don’t leave her alone kar ka kashe yar mutane nan da few hours xata samu miscarriage din in dai magungunan da na rubuta ka siya ka bata” Sudais yace “Ohk” daga haka ya katse wayar ya xauna parlor. Haka Sudais yyi ta xama gidan har magrib amma shiru kke ji, ya duba ta yyi sau ashirin kafin magrib amma banda bacci bbu abinda take hankli kwance, yana fitowa masallaci ya kira Yusuf yace “Kai ni da ina ta xaune gidan har yanxu shiru” Yusuf yace “Bata sha ba toh” Sudais yace “Ya xaka ce haka, a gabana fa ta sha ni ma na bata maganin da ruwa” Yusuf yyi shiru jin haka, sudais yyi tsaki ya katse wayar. har washegari shiru kake ji bbu alamar miscarriage gashi Yusuf yace kar ya kara bata wani, duk ran sudais ya baci, da yammacin washegari Yusuf ya xo gidan, Magungunan ya dauka yana ta kallonsu kamar yanda Sudais ke hararansa shi kuma, can ya balli wasu ya mika ma sudais yace “Bata ta sha” Khadijah dake kwance tana kallonsu kamar xata yi kuka tace “Ni maganin wani iri yake min bana so plss” Sudais ya daure fuska yace “Karba my friend” mikewa tayi hawaye ya cika idonta ta amshi maganin ya mika mata ruwa, daga shi har Yusuf suka kafeta da ido, ta daga gefen Hijab din jikinta tana share hawayen idonta hakan ya bata daman sakin maganin gaba daya a Hijab din cikin dubara sai kuma tayi saurin dage kafarta kamar xata daura kanta bisa kneel dinta, har lkcn kuma hannunta na dunkule kamar tana rike da drugs din, Yusuf yace “Baxa ki sha ba?” Bude baki tayi ta yi kamar ta watsa su ciki sannan tayi saurin xuba ruwa bakin ta tana yamutse fuska har da kokarin amai, da sauri Sudais yace “Don’t try that” ta hade kai da gwiwa suna ta tsaye suna kallonta har ta dago a hankali, Yusuf ya juya ya fita sudais ya bi bayansa, Yusuf yace “Toh sai kayi xaman gadi” daga haka ya bar gidan, Sudais na ta xaune har dare amma shiru, mamaki ya dinga yi anya ba yaudararsa Yusuf yyi ba, a fusace yaje har gida ya samesa don jin me yasa yyi masa haka, Yusuf dake dakinsa kwance yace “Toh ka kai ma wani likitan takardar maganin ka tambayesa na menene, I think that’s all I can tell you” Bayan kwana biyu sudais ya sake komawa Yusuf office da rana, da damuwa yace “Dr ko xaka canxa wani method din ne, wllh I don’t have rest of mind, am afraid kar Mami ta san abinda nake yi, gashi in few weeks time xan je UK, to ya xan yi da yar mutane?” Yusuf yayi dariya yace “Tunda taimakonta kake son yi ka tafi da ita mana” Yusuf ya watsa masa kallo yace “Ko matata ce ke wannan laulayin ina xa ni da ita balle wannan” Yusuf yace “In baka shawara Barrister?” Sudais yyi shiru yana kallonsa, Yusuf ya mike tsaye yace “Wllh ka kyale mata cikinta tunda ka ga haka, Allah kadai yasan me xata haifa, there is power in the baby, banda haka ban ga dalilin da xai sa ta sha drugs din nan har sau biyu ba amma shiru ake ji, just let her pls and idan son samu ne ka taho da ita clinic ko gobe da safe ayi mata scan cos this is almost a miracle” kasa cewa komai Sudais yyi can ya juya ya fita. Washegari kamar yarda Yusuf yace haka Sudais ya sa khadijah ta shirya suka je asibiti don a mata scan, gaba daya jikinsa yyi mugun sanyi bayan result ya fito, shi kadai da Yusuf ne a office din Yusuf din, ita kuma tana reception, Yusuf yace “You see, da haka xaka sa ayi wasting bayin Allahn da basu san komai ba, 2 souls barrister” Sudais bai iya yace komai ba. A hakan dai Sudais ya ci gaba da ba Khadijah kulawa yanda ya kamata, bai rage ta da komai ba a gidan sa, damuwarsa daya yanda ta ki kwantar da hankali har lkcn ga yawan koke koke, idan ya sa ta gaba ta fadi me ke sa ta kuka sai ta ce masa ita bata da kowa yanxu, hakan nasa jikinsa yyi sanyi, sannan hakan ke kara masa kwarin gwiwan ci gaba da taimaka mata, ganin saura yan kwanaki ya fita kasar ya sa ya shiga tunanin wanda xai bar ta da a gidan, idea ne ya xo masa yasa aka nema masa wata dattijuwar da xa su xauna tare da Khadijah a gidan nasa, hakan aka yi bayan matar da baxata haura shekaru hamsin ba ta amince duk wata xai dinga bata dubu arba’in. A yau Khadijah na daki xaune kasan carpet tana shan kunun da dattijuwar da ta dama mata, dattijuwar matar da a ranan tayi kwana uku a gidan duk tunaninta Khadijah matar Sudais ce, su biyu ne dakin Sudais yayi sallama bakin kofa, ta mike da sauri ta iso kofa ta bude tana cewa “Sannu da xuwa yallabai” Gaisheta yyi ta amsa cike da jin dadin yanda yake girmamata sannan ta fita, Sudais ya karasa cikin dakin yana kallon khadijah, wani mugun haske tayi da kyau sai kyalli take, lips dinta yyi pink colour, dauke kai yyi ya isa gefen gado ya xauna, a hankali tace “Ina yini?” Yace “Lafiya lau, ya jiki?” Tace “Da sauki” shiru yyi na wasu yan mintuna kafin yace “Am traveling Amira” ta dago tana kallonsa, ya gyada kai yace “Yeah, gobe xan tafi” sauke idonta kasa tayi, lkci daya hawaye ya kawo idonta cikin sanyin murya tace “Tafiya xaka yi ba bar ni” ya tsura mata ido kafin yyi murmushi yace “Aiki xan tafi yi can, in sha Allah xan dawo when am done” ta kallesa hawayen idonta ya sakko tace “Toh yaushe ne xaka gama” ya wara Manyan idonsa yace “Nima ban sani ba, but da na gama xan dawo ai” kai kawai ta gyada masa amma kana ganinta kasan jikinta yyi sanyi, murmushi ya sake yi yace “Ba ga mama ba xata dinga kula da ke xan bar mata kudi ta dinga siya maki duk abinda kike so, just promise me baxa ki dinga damuwa ba that’s all” murya can kasa tace “I promise, amma yaushe xaka dawo?” Dariya ta basa ganin ta yi tambayar daxu yace “Duk sanda kika samu lafiya kika fara cin abinci sosai sannan bakya damuwa xan dawo” xaro ido tayi tana kallonsa, yace “Yes” murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, sae ranan ya fara ganin murmushinta ya dinga kallonta ganin xata dago kanta yyi saurin dauke kai, tana wasa da dogayen yatsun ta tace “Toh naji” yace “Yauwa ko ke fa” wayarsa daya ya Ciro ya mika mata yace “Xan dinga kiran ki in sha Allah” karba tayi a hankali tace “Toh” yace “to tashi ki raka ni” Ba musu ta mike shi ma ya tashi ya nufi kofa sannan ta bi bayansa, a parlor ya tsaya yyi sallama da Dattijuwar ya kuma sanar da ita xai yi tafiya ta dinga masa addu’ar Allah ya tsare yace “Ameen Ngd mama, don Allah ki dinga sa mata ido bata son cin abinci” tace “In sha Allah kar ka samu damuwa” Dubu hamsin ya ba matar ta dinga siya ma khadijah duk abinda ta bukata, ya kuma sanar da ita komai babu gidan Dr Yusuf xai kawo masu, daga haka ya juya yana kallon khadijah dake ta kokarin ganin bata yi kuka ba yace “Toh mu je” har bakin mota ta rakasa kanta a kasa ya kara mata sallama ta kasa daurewa ta fara kuka, duk jikinsa yyi sanyi, a hankali yace “Look Amira ba dadewa xan yi xan dawo ba, ki daina kuka pls” kai ta gyada masa cikin sanyin murya tace “Toh Allah ya tsare hanya” daga haka ta juya ta koma cikin gida ya bi ta da ido. Kamar kar Sudais ya bar kasar Khadijah ta fara samun lafiya sosai dattijuwar me kirki komai take so shi take mata kafin wani lkci duk babu ramar da tayi sai cikinta da ya fara fitowa, kullum a rana sudais xai kirata kusan sau biyar just to check if she is fine, idan bai kirata ba kuwa ta dinga damuwa kenan, a haka har watanni suka shude.

    5 months later.

    Yau tun da Khadijah ta tashi take ta murna ta rasa dalili, har hirarta ya fi na ko wani rana yawa har da dariyarta wanda da wuya ka ga tayi dariya, Dattijuwar mama suwaiba da take kira da Anty har ta lura da hakan tace “Wannan murnar yayi yawa khadijah ko dai mai gidan ne xai dawo yau” Khadijah dake hada fruits salad xata sha ta daga kai tana kallon mama suwaiba tayi shiru don kuwa gaskiya ne jiya da daddare da suka yi waya da Sudais yace mata yau xai dawo, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta ta ci gaba da abinda take a hankali, mama suwaiba tace “Toh gwara a tashi a san me xa a girka masa, ki fadi duk abinda kika San yafi so sai in shirya in tafi kasuwa yanxu” Khadijah tayi shiru don har lkcn bata san komai game da Sudais ba balle ta san abinda ya fi so da wanda bai so, hakan yasa jikinta yyi sanyi sosai. A cikin watanni biyar din nan khadijah ta warware jikinta yyi kwari, babu abinda bata ci har da wanda bata ci a da can, wato wake, taliya kai har da tuwo da miyar kuka, wani kyau na musamman tayi don hatta fatar jikinta har wani glittering yake yayi taushi, yanxu kam cikinta ya fito sosai don sai ayi tunanin at anytime xata iya haihuwa don da kyar take yin komai nan ko watannin cikin bakwai, tausayi take ba mama suwaiba ganin yarinya ce sosai wa ya sani ko xata iya haihuwa da kanta ma, hakan yasa in dai ta fita cefane ko siyo wani abun bata rabo da dawowa da magunguna irin na gargajiya da tasan mai ciki na bukata, duk ranakun alhamis kuma tare da mama suwaiba suke xuwa can clinic dinsu Yusuf domin Antenatal a bisa umarnin sudais, damuwar Khadijah daya a lkcn ummarta don ko cikin dake jikinta baya damunta ta kuma rasa dalili, gaba daya tayi kokarin ganin ta mance ta taba rayuwa gidansu Aliyu, amma duk sanda cikinta yayi motsi sai ta tuna shi Aliyun, duk wannan difficulties na rayuwa da ta shiga ko sau daya bata taba jin haushin Aliyu ba kuma har ranta take jin ta yafe masa a lkcn… ko don tana tare da yarinta har sannan ne oho. Khadijah ta kasa hakuri ganin har yamma bata ga sudais ba alhalin yace mata in sha Allah yau yana Nigerian duk jikinta yayi sanyi ta tafi daki ta kwanta, Mama suwaiba kuma ta ki hakura tana ta girke girke a kitchen ita kadai. Sudais na sauka taxin da ya kawo sa har kofar gida ya shiga gidan yana rike da daya daga travelling bag dinsa guda uku da mai taxin ya dire masa a bakin gate, kai kana ganinsa kasan daga turai yake don wani fresh na musamman yyi da haske sai dai ya rame sai idanuwa da hancinsa da suka fito, sosai ya rage bak’in gashin kansa, yyi murmushi ya na amsa gaisuwar da mai gadi ke masa da fara’a yana masa sannu da dawowa sannan yace “Ka shigo min da sauran kayana bilyamin” tun a bakin kofa kanninsa suka rungumesa ko wacce na murnar dawowarsa bayan kusan watanni biyar, Mami dake parlor da Anty Maryam ma sai murmushi suke, lkci daya murmushin Sudais yyi fading ganin Jiddah da yayi xaune parlorn, ya karaso a sanyaye ya duka kasa ya gaida mami ta amsa tana murmushi tace “Sannu da xuwa Aliyu ya hanya?” Yace “Alhmdllh Mami, fatan mun same ku lafiya?” Tace “Alhmdllh” gaisawa suka yi da Anty Maryam sannan ya kalli jiddah yana kirkiran murmushi ta sunkuyar da kai tace “Sannu da xuwa ya hanya?” Yace “Alhmdllh mun same ku lafiya?” Tace “Sure” Rabi’ah da Humairah suka dau bags dinsa xa su kai daki yace “Noo don’t worry sisters wancan kadai xaku dauka ku bar wa ennan, xan d’an fita yanxu” da mamaki Mami tace “Ka fita kaje ina daga dawowa, idan ma fitan xaka yi ina xaka da jaka kuma?” Ya sunkuyar da kai yace “Sakon wani abokina ne xan kai gidansu Mami” Mami tace “Ohk, to amma sai ka huta ka ci abinci koh?” D’an shiru yyi sai kuma yace “Mami baxan dade ba xan dawo yanxu” daga haka yasa kanninsa suka dau jakunkunan suka kai masa bakin motarsa sanin ko baya nan ana amfani da motar, ya mike yace “Toh sai na dawo Mami” tace “Toh don Allah kar ka jima ka dawo ka ci abinci ka huta” yace “In sha Allah” yana barin gidan bayan ya hau titi ya dau wayarsa ya shiga kiran khadijah, Khadijah dake kwance har lkcn a daki ta mike da sauri kamar jira take jin ring din wayar ta jawo ganin Sudais ne ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren yyi sallama yace “Amira” turo baki tayi tace “Uhn” yace “How are you” a hankali tace “Fine baka dawo ba kuma” d’an murmushi yyi yace “I postponed the trip xuwa next month in sha Allah” wani irin faduwa gabanta yyi da har sai da ta ji a kirjinta da ya mata sauki kwana biyu sbda magungunan da Yusuf ke bata, hawaye ne ya shiga sakkowa idonta, yace “Hello are you there?” Kasa amsawa tayi ya dinga hello ta katse wayar ta hade kai da gado ta fara rera kuka, sake kiranta yyi ta ki dauka har ya katse ya kara kira, sai a snn ta dauka ta kai kunne taki cewa komai, murya can kasa yace “Amira” ta fashe masa da kuka a hankali, wara ido yyi hade da murmushi yace “Har da kuka kuma?” Ta ki cewa komai, murya can kasa yace “Cry no more, tunda kina son ganina kawai fito gate ki tsaya ni kuma xan taso daga UK yanxu, har kofar gida jirgin xai ajiye ni” mikewa tayi xaune da sauri tace “Don Allah ka bari, ka dawo pls?” yace “Da gaske fa just wait me outside xa ki ganni yanxun nan” katse wayar tayi ta tashi da sauri ta dau Hijab har Kasa ta sa sannan ta fita dakin, Ganin xata fita waje Mama suwaiba da fitowarta kitchen kenan tace “Ya iso halan” Khadijah bata iya ta ce komai ba ta kirkiri murmushi ta fita, a hankali take tafiyar har ta isa gate ta tsaya gabanta na bugawa, tsaye ta ga motarsa bakin gate din suna hada ido ya bude motar ya fito yana murmushi, tsabar farin ciki ta kasa cewa komai amma kana ganin ta kasan she is just happy, ita dai tasan yau da ace mace ce Sudais da ta tafi da gudu ta rungumesa, ya wara mata ido ganin kallon da take masa yace “Toh ko dai in koma tunda kallona xa ki tsaya yi” tahowa tayi ta tsaya gabansa ta sunkuyar da kai tana murmushi, murmushin yayi shi ma murya can kasa yace “How are you Amira” ta kasa dago kai cikin sanyin murya tace “Am fyn, sannu da dawowa” yace “Sannu, ya babies dinmu” dagowa tayi ta kallesa da sauri sai kuma ta juya masa baya, dariya yayi yana kallonta, tayi murmushi tana jan hannunta, yace “Toh mu shiga” tafiya ta fara yi ya bi bayanta bayan ya rufe motar har suka shigo parlor. Xaunawa yayi parlorn suna gaisawa da mama suwaiba dake tayi masa sannu da xuwa, khadijah ma ta xauna kasan parlorn tana kallonsa ko kiftawa bbu, mama suwaiba ta koma kitchen ya maida dubansa kan Khadijah, sauke idonta tayi kasa da sauri, yace “Are you now happy” murmushi tayi tana gyada kai a hankali shi ma yyi murmushin yana kallonta, Kirar ta Mama Suwaiba tayi ta mike ta nufi kitchen ya bi ta da ido, Mama suwaiba tace “Toh ke haka ake yi, sai ki je bayi ki hada masa ruwan wanka, idan kuma abinci xai fara ci sai ki kai masa daki” murmushi khadijah tayi bata ce komai ba, mama suwaiba tace “Toh kin yi shiru kuma” a hankali khadijah tace “Toh bari in tambayesa” daga haka ta juya ta koma parlor, Wayarsa yake dannawa ta duka gefensa ya kalleta yace “Xauna kujera mana, you are stressing ur self and the babies” sauke idonta tayi kasa tace “Dama Anty ce ta ce in tambayeka ko xaka ci abinci a kai maka daki” shiru yyi na wani lkci kafin yace “She is thinking something different, and Mamina ta min abinci a can gida but… Ohk toh kai abincin daki” Tashi Khadijah tayi ta koma kitchen ta karbi abincin da Mama suwaiba ta hada a tray ta wuce can bedroom da shi, Sudais ya mike ya bi bayanta, karban abincin yyi a hannunta ya ajiye kan rug sannan ya xauna yace “Ke kin ci abincin” tace “Na ci daxu” yace “Daxu daban, yanxu daban, so xauna mu ci” dafa gado tayi xata xauna a kasa yace “No ki xauna saman gado” xaunawa tayi gefen gado ya debi abincin a plate ya sa spoon sannan ya mika mata ta amsa a hankali tace “Nagode” ya debi kadan a wani plate din dai dai nan wayarsa yyi ring dubawa yyi da sauri ya ga Mami ce, ya d’an bude ido sannan ya daga, daga daya bangaren Mami tace “Wai daga dawowa ina ka tafi haka Aliyu? Are you even okay” a hankali yace “Gani nan tahowa Mami am sorry” katse wayarta tayi, ya ajiye wayar yana kallon abincin, samun kansa yyi da Kasa cin abincin, ya rufe yace “Amira xan je gida Mami na jirana idan kin cinye wannan sai ki kara da nawa” Bata ce komai ba sai wasa da cokalin hannunta take, ya mike yace “Kilan xan xo gobe da safe, take care of ur self” daga haka ya juya ya fita, hawaye ne ya cika idonta ta rasa dalili abincin duk ya fita ranta ta kasa ci ta ajiye tana goge hawayen dake xubo mata, Sudais na fita ya tuna bai shiga da kayan da ya taho mata da su daga UK ba, ganin xai kara bata lkci kawai yyi deciding ya bar sa a motar sai gobe idan ya xo. Ko da ya koma gida kawai yana cin abincin da Mami tayi masa ne amma gaba daya hankalinsa na kan Khadijah don bai san ko ta ci abincin da ya debar mata ko bata ci ba, Mami dake xaune ta sa shi gaba da jira har ya gama cin abincin sannan tace “Kun yi waya da jiddah xaka dawo yau ne?” Girgixa kai yyi duk da faduwar da gabansa yyi a hankali yace “Aa mun ma kwana biyu ba mu yi magana ba, fushi take ai da ni” Mami tace “Toh wasa wasa gashi har watanni kusan shidda da kace a daga biki yyi, yanxu kuma ya ake ci” kasa kallonta yayi ya fara kame kamen rufe warmers din abinci, strictly tace “Magana nake ma ka Aliyu” da kyar ya dago ya kalleta yace “Toh Mami a sa bikin nan da wata daya xuwa biyu in sha Allah” wani kallo ta watsa masa tace “Me sati biyu ko uku yayi da har sai an kai wata biyu kuma?” Ya shafa kai yace “Dai dai wannan lkcn xan koma UK kuma xan jima sosai kafin in dawo kinga kawai ana bikin a lkcn sai mu tafi tare da ita” Mami tace “Allah ya kai mu, xan ma Abbanku bayani” yace “Nagode Mami” daga haka ya mike yace mata xai kwanta ya wuce bedroom dinsa. Yana shiga dakinsa khadijah ya kira, tana dagawa yace “Kin gama cin abincin?” Turo baki tayi tace “Na koshi” yace “Baki ci ba kenan?” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Me kike yanxu?” Tace “Na kwanta” yace “Tashi ki je ki dau abincin ki ci idan ba haka ba baxa ki ganni gidan nan ba for plenty days” tashi tayi xaune da sauri tace “Ni ban ce baxan ci ba” yace “Toh je ki ci” ta mike da kyar tace “Toh” yace “Idan kin gama ki kirani” gyada masa kai tayi kamar yana ganinta ya katse wayar. Sosai ta ci abincin ta hada har da wanda ya dibar ma kansa, tana gama ci ta dau wayar ta kirasa, sai da ya kusa katsewa ya daga, jin muryarsa tace “Bacci kake” a hankali yace “Yea, kin gama cin abincin?” Tace “ehh na cinye” yace “Good Mami” murmushi tayi tace “Toh kayi baccin, byee” murmushin shi ma yyi ya katse wayar. Xuwan Yusuf gidansu da daddare ne saving grace dinsa don da shi da fita kuma sai gobe, bayan Yusuf ya gaisa da Mami suka tafi dakin Sudais yana tambayar sa ko yayi ciwo a UK ne don ya rame sosai, bayan kusan minti talatin Yusuf yace xai tafi suka fito tare da sudais da yace ma Mami xai rakasa, sai da suka shiga mota Yusuf yace “Kaje ka duba mai cikin ka?” Sudais ya hade rai yace “Mai cikina kuma” dariya Yusuf yyi yace “Toh ai kusan baka da banbanci da uban yaran, kai ma uba kake a gare su kama fi sa xama masu uba kan ubansu” tsaki Sudais yyi bai ce komai ba, Yusuf yace “But don Allah Sudais da yau ko watarana xaka ga uban unborn babies din nan me xaka masa?” Sudais yyi wani murmushi da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “I won’t even look at him twice yaran da xata haifa sun ishesa” Yusuf yace “What if ya xo wataran yayi claiming yaran fa?” Wani kallo Sudais yyi masa baki bude, can yyi wani dariya yace “Wllh wllh I will sue him, sai na sa yyi shekaru da dama a gidan yari” Yusuf dake driving ya wara ido yace “Tohhh, kenan yaran ka ne ba nasa ba” Yusuf na dariya ya kare maganar, Sudais yyi banxa da shi, Yusuf yace “Toh why not bayan ta haihu ka aureta kawai Sudais” juyawa Sudais yyi yana kallonsa da wani expression, can ya dake yace “Ko saboda me?” Yusuf yyi murmushi yace “Saboda ka ji dadin ci gaba da kula da ita da yaran da xata Haifa kwanan nan, kasan a yanxu kai ne ubanta kai ne uwarta, i mean kai ne gatan ta, don haka sai ka ci gaba da xama gatan nata har karshen rayuwarta, nan da shekaru biyu kai ma ta haifa maka naka yan biyun ba na wani ba”

    Girgixa kai Sudais yyi bayan ya dauke idonsa daga kallon da yyi ta ma Yusuf yace “I didn’t blame you Dr, why?? Because am very sure kafin ka xo gidanmu yanxu daga club din da ka saba xuwa kake, and definitely idan ka je club dole sai ka sha ruwan can na sani, soo no offense, u are drunk….” Dariya kawai Yusuf yake yace “Kai kuma tun bayan haduwarka da marainiyar nan ka daina xuwa can koh? Thank God we where both drunkards before” Sudais da yyi mugun hade rai yace “Drop me here my frnd” Yusuf yyi parking yace “Ji dan iska kamar wani driver din sa wai drop me here my frnd” Bude motar Sudais yyi ya fice ya juya yana masa wani kallo, da yatsarsa yyi masa xagin turawa yayi wucewarsa, dariya kawai Yusuf yake ya ja motarsa ya wuce gida, Da kafa Sudais ya karasa gidansa, Mama suwaiba kadai ce parlor tana cin abinci TV a kunne, tana ganinsa ta mike da sauri tana masa sannu da xuwa yace “A’a yi xaman ki mama” Mama suwaiba ta koma ta xauna tace “Toh nagode” yana son tambayarta khadijah amma yyi shiru, can ya mike ya wuce bedroom, kwance ya ganta tayi bacci tana rufe da bargo, ya karasa kusa da gadon yana kallonta, dukawa yyi dai dai fuskarta murya can kasa yace “So early?” Ko motsi bata yi ba alamar ta jima da yin baccin, a hankali yyi murmushi ya kai hannu dogon hancinta ko mai ya tuna yyi saurin withdrawing din hannunsa ya mike ya kashe mata wuta ya fita daga dakin, Sallama yyi ma Mama suwaiba ya nufi kofa ta bi sa da kallon mamaki, yau ma da ya dawo baxai kwana gidansa tare da matarsa ba, wannan wani irin aure ne a gantale, har ya rufe kofa kallonsa take baki sake. Washegari lahadu Khadijah na xaune parlor da tuwo da miyar kuka da mama suwaiba tayi mata, da cokali take cin tuwon mama suwaiba kuma na kitchen tana wanke wanke, bude kofa aka yi ta daga kai da sauri sudais ya shigo parlorn rike da babban jaka, ajiye jakar yyi yana wara ido yace “Kaiiii yanxu xa ki iya cinye wannan tuwon Amira?” Rufe fuskarta tayi da kujera da sauri tace “A’a fa xan rage in ci anjima” dariya yyi ya juya ya fita ya shigo da daya jakar ya ajiye sannan ya xauna kan lallausan carpet da take xaune yace “Ci da yawa abin ki kin ji, sai ki haifo mana yara masu karfi” bata dago kanta ba har lkcn yyi murmushi ya bude zip din jakar ya fara fiddo kayan ciki, sai bayan da ya Ciro kayan jakunkunan gaba daya sannan yace “Here… you like them?” sai a sannan khadijah ta dago a hankali tana kallon kayan, kayan babies ne masu tsada ko wanne set biyu, shiru ta yi tana kallon kayan, ya ware nata dogayen riguna masu kyau gudu hudu yace “Wannan kuma naki” sauke idonta da ya kawo ruwa tayi a hankali, ya hade rai yace “Baki so ne xa ki min kuka” bata san lkcn da ta fashe da kuka ba ta hade kanta da kujera, yyi shiru yana kallonta, can ya fara mayar da kayan gaba daya jaka yana gamawa ya kai jakunkunan daki sannan ya nufi kofa ya fice daga gidan ya shiga motarsa ya wuce. Har bayan kwana biyu Sudais bai je gidan ba duk da he is just trying not to go amma hankalinsa gaba daya na can, sosai hankalin khadijah ya tashi don tasan kilan fushi yake ne ya sa, tana son kiransa amma ta kasa, ganin baxata iya jurewa ba kuma ta kira sa, a lokacin yana gida bedroom din Mami suna hira da Anty Maryam, ganin kiran yyi ta kallon screen din kafin yyi silencing wayar ya mike yace “Mami bari in tafi in shirya xan fita yanxu” daga haka ya bar dakin bayan yayi ma Anty Maryam ma sallama, Mami ta tabe baki tace “Kwata kwata Aliyu ba shi da gaskiya yanxu, I really don’t knw what he is up to, tun ma kafin ya bar kasar months back na lura da haka kuma gashi ya dawo ya ci gaba da behavior din, there is something big he is hiding kuma shi ya hanasa auren ma, dubi fa yanda ya axalxalemu a kan jiddah duk ya daga mana hankali shi aure amma lkci daya kinga kuma abinda yyi, ni na haifesa ba shi ya haifeni ba don hka I will fish out what he is up to soon” ita dai Anty Maryam bata ce komai ba sai kallon yayarta take. Sudais na barin gidan ya tafi can gidansa, Khadijah na kitchen tare da Mama suwaiba suka ji an shigo parlorn, fitowa tayi tana ganinsa ta turo baki, ya karaso parlorn ya xauna yana idonsa a kanta, ta sunkuyar da kai ta isa kusa da shi ta xauna a kasa, yace “How are you?” Kin cewa komai tayi, ya d’an yi murmushi ya dau wayarsa yana danna, a hankali tace “Ina yini” ya kalleta yace “Ban yini ba” kamar xata yi kuka tace “Ni ban san me nayi maka ba” yace “Na kawo maki abu kince baki so mana” xaro ido tayi tana kallonsa tace “Ni??” Yace “Ehh” murmushi tayi tace “I don’t knw how to thank you that day, that was why….” Hawaye cike idonta ta kare maganar, Kallonta kawai yake bai ce komai ba. Haka nan rayuwa ya ci gaba da kasancewa bayan dawowar sudais Nigeria, duk safiya, rana har da daddare xai xo ganin khadijah, kayan ciye ciye yake xuwa mata shi idan xai xo da daddare wani lkcn shi ma ya ci abinda xai ci a gidan, ita dai Mama suwaiba na son sanin me ya janyo bai kwana gidan amma bata san wa xa ta tambaya ba tunda ba wani hira can suke yi da Khadijah ba, toh ko don tana da ciki ne yake haka, tambayar da ta dinga yi ma kanta kenan har hakan yasa ta d’an fara jin haushin sudais din, rana daddaya ne xai shigo gidan ba tare da kayan baby ba, xuwa yanxu irin siyayyar kayan baby da yyi mata sai ayi xaton yara goma xata haifa, komai ya gani ya Burgesa sai ya daukar mata. A haka har watan haihuwar Khadijah ya tsaya, mama suwaiba bata yi kasa a gwiwa ba wajen bata taimako irin na gargajiya don tausayi take bata, kusan duk yamma sudais sai ya lallaba Yusuf sun je gidan kawai don ya dubata, har ransa yake fargabar kar abu ya sameta, wani sanyi tayi gaba daya a kwanakin ko da yaushe a kwance xaka ganta, idan ya tambayeta ko akwai inda ke mata ciwo sai tace babu ko ina. Ranan Sunday da sassafe ya shirya ya fito parlor yana kallon Mami dake dinning yace “Mami xan fita in dawo” tace “Ranan lahadin ma?” Murmushi yayi yace “Mami it’s urgent ne, kuma akan…” Katse sa tayi tace “Aliyu” ya dago da sauri, bata fuska yayi yace “Mami wllh duk kika ce min Aliyu sai gabana ya fadi, cos u always call that name when serious” ta masa wani kallo tace “Toh da meye sunan naka?” Yar dariya yyi yace “Sudais mana” tace “Ni na sa maka sudais?” Dariya yyi sosai yace “Ni na sa ma kaina Mami Aliyun sunan tsoffi ne I….” Ta katse sa tace “What ever…. kaje duk inda xaka ka dawo ka sameni in sha Allah gobe xa a kai kayan can da kasa nayi jere da su a daki” yace “Allah ya kai mu Mami” daga haka ya fice daga parlorn, gidansa ya nufa direct. Mama suwaiba na kitchen tana aiki, bai jira sun gaisa ba ya wuce daki, xaune ya ga khadijah ta takure waje daya, Ya durkusa kusa da ita da sauri yace “Are you okay Amira?” Ta girgixa masa kai da kyar, da damuwa yace “What’s wrong? Kina jin ciwo ne jikin ki?” Karfin halin nuna masa bayanta tayi, yace “Yana maki ciwo?” hawayen da ya gani idonta ya rikitar da shi lkci daya ya dagota yace “Let get to the hospital…..” Kwace kanta tayi ta koma ta durkushe a wajen tana rintsa ido tace “Ya daina” Allah ma yasan daurewa kawai take, ga ciwon kamar ana kara mata take ji, bata san lkcn da ta sakar masa kuka ba a hankali tace “Wayyo ka taimakeni plss” bai sake saurararta ba suka fita dakin, Mama suwaiba bata ma san sun bar gidan ba tana kitchen, har suka isa asibiti Khadijah bata sani ba duk ta rikice, wani asibiti me tsada ya kai ta banda Wanda Yusuf ke aiki, bbu bata lkci nurses suka amsheta da wani likita, yanda Sudais ya daga hankali sai ka rantse ance masa mutuwa xata yi, khadijah bata yi fatan kara experiencing kwatankwacin irin wahalar da ta sha na labour ba har ta bar duniya, tun da suka je take wahala amma shiru, Sudais ya kira Yusuf ya sanar da shi suna asibiti, Yusuf yace “Me yasa baka kawo ta asibitin mu ba” Sudais yace “Just” Yusuf yace “Toh wani asibitin ku ke?” Sudais ya gaya masa, tabe baki Yusuf yyi yace “Kudi ya ma yawa ne, any way idan ta haihu ka kirani” Sudais ya katse wayar ya jinginar da kansa da kujera yana mai yi ma khadijah addu’a a xuciyarsa, bayan awanni biyu ya sake kiran Yusuf, Yusuf yace “Ya? is she delivered” a hankali Sudais yace “Har yanxu” Yusuf yace “Toh fah, ko dai cs xa ayi mata, dama am thinking it will be difficult ta haihu da kanta, any way bari in taho yanxu” bayan wani lkci Yusuf ya xo, dariya Yusuf ya shiga yi ganin yanayin sudais yace “Kaiiii… To ai ko jiddah ke labour sai haka bawan Allah” Shi dai Sudais bai tanka sa ba, yawanci likitocin asibitin duk Yusuf ya san su, don haka har labour room yaje gun khadijah, ya ji tausayinta ba kadan ba ganin irin dauriyarta, baxa ka taba cewa haihuwar fari xata yi ba tsabar karfin halinta, bayan wani lkci Yusuf ya bar asibitin bayan ya kwantar ma da Sudais hankali yace labour kawai take babu wani matsala, wasa wasa dai shiru ake ji wanda hakan yasa likitocin suka kira Sudais office nan suka nuna masa it’s better ayi mata Cs kada yaran da ita kanta su samu matsala, kusan ba da son ransa yyi signing takardar da aka basa ba, bayan wasu yan mintuna aka fitar da Khadijah labour room xuwa Theatre, anan kuma aka yi nasarar ciro mata boys dinta, sai dai sun jigata kamar yanda ita ma ta jigata. Khadijah ta bude ido a hankali ta ganta kwance wani ward, Mama suwaiba dake gefenta ta sakar mata murmushi tace “Sannu Amira, Allah ya baki lafiya” tashi xaune take son yi taji kamar an danneta ta kasa tashin, Mama suwaiba ta mayar da ita ta kwantar tace “Aa kinga ba ki da lafiya ki yi kwanciyar ki kawai kinji” sai a snn taji wani axaba tun daga cikinta har xuwa kafafuwanta, wasu hawaye suka shiga sakko mata cikin rawar murya tace “xafi nake ji” fita Mama suwaiba tayi sai ga ta ta dawo da likita, likitan ya duddubata ya mata Allah ya sauwake sannan ya fita, Nurse ce ta shigo ta mata allura ta fita, bayan fitar ta sai ga Sudais ya shigo khadijah ta bude ido tana kallonsa, ya karaso gefenta cikin sanyin murya yace “Amira….” Bata iya ta amsa sa ba, a hankali ya sa hannunsa cikin nata cikin sanyin murya yace “Be strong Amira, you will get better in sha Allah..” Hawaye ya sakko idonta sai dai bata ce komai ba, ya sakko da fuskarsa dai dai nata yana murmushi a hankali yace “Baki tambayi yaran ki ba ko bakya son su?” Ta gyada masa kai, shiru yyi yana kallonta, can yyi murmushi yace “Toh sai ki bani su” Murya can kasa hawaye na xuba idonta tace “Na baka” ya fadada murmushin fuskarsa yace “Sure?” Throughout ranan Sudais was by her side tare da Mama suwaiba, Yusuf ma ya xo yyi mata barka ya wuce, ba a nuna mata yaran ba kuma bata tambaya ba har ta sa a rai kila ma mutuwa suka yi wanda tunanin hakan yasa mata nutsuwa sosai don har ga Allah bata ma son ganinsu, haka kawai taji bata san su, Sudais dake lura da cewa she was so depressed ya dinga kokarin ganin ya sa ta walwala sai dai ta kirkiri murmushin karfin hali, sallah kadai ke sa shi ya bar gefenta, tun karfe shidda mama suwaiba ta koma gida dauko kaya, duk kiran da aka dinga ma sudais a waya kin dagawa yyi daga karshe ma ya sa wayar a silent, A daren ranan bayan sudais yaje sallar magrib da ya tashi dawowa ya shigo rike da daya daga yaran wata nurse na biye da shi da dayan, tun da suka shigo khadijah ke kallonsu, yana murmushi ya ajiye babyn a gefenta, sosai gabanta ya fadi ta dinga yi ma jaririn wani kallo ganin kamar Aliyu yyi kaki, babu abinda new born din ya mance na ubansa tun daga haske, hanci, kai har bakinsa… Nurse din ta ajiye mata daya carbon copy din yaron dake gefenta kusa da d’an uwansa tana murmushi tace “Congrat mum twins, Allah ya raya su” daga haka ta fita, a hankali Sudais yace “Ain’t they cute? I mean the innocent new souls” khadijah bata san lkcn da ta fashe da kukan takaici ba cikin rawar murya tace “Don Allah ka tafi da su, wllh bana son su, ni dai bana son su ka maida masu su” kuka take sosai kamar xata shide, ganin haka Sudais ya mike ya dau yaran gaba daya ya fita da su dakin.

    Sudais na dawowa dakin ya dinga kallonta har ya iso kusa da ita yace “Me yaran suka maki da kike cewa baki son su Amira” kin cewa komai tayi, ya ja kujera ya xauna yyi shiru, bayan kusan minti goma wayarsa ya fara ring dauka yyi ya duba yaga Mami ce, yau ta kirasa yyi sau hudu duk bai dauka ba, ya mike yana kallon khadijah da ta lumshe idonta yace “Mama xata dawo yanxu, ni xan je gida Mami na ta kirana, gobe da safe xan xo kin ji?” Bude ido tayi tana kallonsa yace “Be strong, kuma kar ki sake kuka plss” gyada masa kai kawai tayi ya juya ya fita. Bayan fitarsa da yan mintuna mama suwaiba ta shigo, sannu ta dinga yi mata, ta xauna kusa da ita tace “Kin ma ga yaran naki kuwa Amira” Khadijah ta hade rai tace “Ehh” daga haka ta rufe idonta, ana yin isha mama suwaiba tayi sallah a nan ward din da bayan ta shimfida dankwalinta a kasa, bude kofar ward din aka yi nurses biyu suka shigo da babies din Khadijah ta rufe ido da sauri, kan gadon jariran dake kusa da na khadijah suka kwantar da su, daya daga nurse din na kallon Mama suwaiba da ta mike ganin yaran tace “Xa a iya ba su nono yanxu idan suka bukaci haka” daya nurse din na nuna mata babyn kusa da ita tace “Wannan shine Hasan, na kusa da shi kuma Hussain” Mama suwaiba tace “Maa sha Allah, Allah ya raya mana su” nurses din suka amsa da amin sannan suka fita, mama suwaiba sai kallon kyawawan fararen yaran take tana murmushi sai dai abinda ke daure mata kai daga Sudais har Khadijah babu wanda taga yaran suka biyo, a ranta tace “Ikon Allah, to ko wa suka biyo su kuma maa sha Allah” kallon khadijah tayi da ta ki bude ido har lkcn, tausayinta ta dinga ji don idan akwai abinda ta tsana shine ayi ma mace operation. Karfe sha daya da wani abu mama suwaiba ta kwanta a spare bed dake Dakin, har ta fara bacci taji kukan jariri, ta bude ido da sauri taga daya ne ke motsi, ta Mike ta daukesa tana kallon khadijah, Bata san Khadijah na jin yaron ba sai dai idonta a rufe yake har sannan, Mama suwaiba da a tunaninta bacci take ta rungume yaron ta xauna, haka mama suwaiba ta dinga lallaba su tana basu ruwa a feeder ganin yunwa suke ji har Washegari da safe. Karfe tara saura sudais ya shigo ward din,sanye yake da farar shirt da black jean yayi kyau ba kadan ba, direct gun babies dake cikin cot dinsu bayan an masu wanka ya nufa, ya dau daya ya lumshe ido ya daura lips dinsa a soft cheek din babyn, juyawa yayi ya kalli khadijah dake bacci, jikinsa yyi sanyi don da alama mama suwaiba ta je gida dauko abu, daga ita sai yaran ne a ward din, nobody to stay with them, banda tsotson baki bbu abinda yaron dake hannunsa yake alamar yunwa ya kalli d’an uwansa shi ma yaga haka yake da bakin, yana ta tsaye dakin bai tashi Khadijah ba mama suwaiba ta shigo bayan sun gaisa yake tambayarta ko Khadijah ta fara basu abinci ne, Mama suwaiba tace “Aa bata basu ba da nayi mata magana daxu ce min tayi cikin ta na ciwo har na fita na kira wata nurse, tun jiya ruwa kawai nake ba su” Sudais bai ce komai ba ya xauna saman kujera, bayan wani lkci yace “Toh ita ta fara cin abinci ne?” Mama suwaiba tace “A’a ga shi nan dai kunu ma na je gida na dama mata, cewa likitan yyi shi kadai xata iya sha anjima, toh kafin ta tashi shine naje nayo” yace “Toh sannu mama” ya d’an jima a dakin kafin ya bar asibitin kuma har lkcn khadijah bata tashi ba. Wasa wasa yau kwanansu uku a asibiti amma khadijah taki ba yaran nono, da farko cewa take cikinta na mata ciwo baxata iya ba sudais ya siyo masu madara na jarirai mama suwaiba na basu, har abun ya fara daure ma mama suwaiba kai don har sannan khadijah taki daukan yaran ta, tunda tayi kokarin bata su sau daya ta ki amsan su ta kuma ga kamar ranta ya bace bata sake bata su ba. Satinsu daya da kwana daya aka sallamesu asibitin bayan Sudais ya biya bill din, duk yaran na hannun mama suwaiba don khadijah bata amshi ko daya ba, ya bude motar bayan sun isa gida ya amshi dayan yaron hannun Mama suwaiba, ta fito rike da dayan ta nufi cikin gida, kallon khadijah yyi da ta fito ita ma ya mika mata yaron, dauke kai tayi ta bar wajen da sauri tace “Ni dai baxan iya ba” Wani kallo ya mata da mamaki yace “Kee” ta juyo tana kallonsa, mika mata yaron yyi fuskarsa daure yace “Karbesa” kamar xata yi kuka tace “Xai iya faduwa pa” yace “Ya fadi” ganin yanda ya tsare ta da ido ta karbi yaron hawaye har ya kawo idonta ya yi gaba ya bar ta gun tsaye, a hankali ta bi bayansa ba tare da ta bari ta kalli yaron hannunta ba, sudais ya karbi yaron hannun mama suwaiba ya wuce bedroom da shi khadijah ta bi bayansa, gefen gado ta xauna ta ajiye yaron kan gadon, yana kallonta yace “Basu abinci yanxu” da sauri tace “Ai naga sun sha madara fa, ni…..” Katse ta yayi yace “Baki son yaran nan koh Amira?” Ta kallesa ta gyada kai a hankali kamar xata yi kuka, yana mata wani kallo yace “Dama kin san baxa ki so su ba kika yarda kika haifo su duniya, me yasa baki amince an raba ki da su tun a ciki ba?” Cikin rawar murya tace “Toh ai babu kyau” yace “Ohk…. abinda kike masu yanxu da kyau kenan” shiru ta yi hawaye na sakko mata, yace “Kin san Allah idan baki basu abincin su ba am leaving here now, kuma wallahi babu ruwana da ke, are you this wicked?” da sauri tace “Kayi hakuri xan basu” tana magana hawaye na xuba idonta don ita har ranta da gaske bata son yaran, Sudais yace “Toh ba su yanxu” tana share hawayen idonta ta fara bude zip din rigarta xata sauke rigar yayi saurin dakatar da ita “Kee haka aka ce maki ake yi?” Kamar xata yi kuka tace “Toh ai ban iya ba” juyawa yyi ya fita sai gashi tare da mama suwaiba, yana tsaye ta gwada mata yanda xata yi tana dariya sudais ya juya ya bar masu dakin, har da kukanta ita wai xafi take ji, Mama suwaiba ta dinga lallaba ta don ita ma tausayin yaran take ganin basu samu gatan shan nonon uwarsu ba tun da suka fito duniya, da kyar ta amince ta ba dayan ma, a ranta kuwa tasan shine farkon shan su kuma shine karshe don ita dai baxata iya ba. Kwanansu biyu da dawowa daga asibiti Sudais ya shigo dakin da Khadijah take da safe, xuwan sa kenan gidan, farar Gezna ce jikinsa dake ta kyalli, waya ne kare kunnensa ya shigo dakin yana magana amma can kasa kasa, ya nufi gun babies dake kwance yana kallonsu kamar yanda Khadijah da ke tsaye gaban madubi ke ta kallonsa tun shigowar sa, Sudais is just the real definition of handsome, duk da wayar da yake gaba daya hankalinsa na kan yaran dake ta tsotson baki yana murmushi, xuwa jikin khadijah yyi kwari sosai don har aikin ya gama warkewa, sosai kirjinta suka ciko har ciwo suke mata amma taki ba ma yara abinci, yanxun ma mama suwaiba ce ta shigo da su ta kwantar ko xata tausaya masu ta basu nono, Sudais ya mayar da wayarsa aljihunsa ya juya ya kalleta tayi saurin dauke kanta, ya xauna gefen gadon yace “I know baki abinci ba yau” ba tare da ta kallesa ba tace “Na basu ka tambayi Anty” bai ce komai ba, bayan wasu mintuna yace “Wani sunan za a sa ma babies din?” Still taki kallon inda yake tace “Nima ban sani ba” yace “Baki sani ba kuma?” Tace “Ko wanne ma ka sa masu” yace “A’a ke xaki xaba da kanki ba yaran ki bane” kin cewa komai tayi, yace “Am talking to you Amira, kuma akwai inda xa ni” ta langwabar da kai a hankali tace “Toh Muhammad da….” Sai kuma tayi shiru, yace “Da wa?” A hankali ta saci kallonsa tace “Kai” ya buda ido sosai yace “Ni kuma?” Tace “Ehh, ur name” murmushin sa mai kyau yyi yace “Aa ki xabi wani sunan dai Amira” hawaye ya kawo idonta tace “Ni kai nake so a sa” Yace “Aliyu kike nufi?” Ta gyada masa kai, wani murnushin ya sake yi yace “Sunan mahaifinsa dai kenan” da sauri khadijah da gabanta yyi mugun faduwa tace “Noo, Brr Aliyu Sudais nake nufi not Dr Aliyu Turab” Shiru Sudais yyi yana kallonta, mikewa yayi bai sake cewa komai ba ya fita yana murmushi. Raguna biyu sudais ya yanka ma ‘yan biyun, Hasan aka sa ma Muhammad, Hussain kuma Aliyu, kusan duk sadaka yyi da daya ragon ya bar ma khadijah daya mama suwaiba ta gyara mata, ita dai mama suwaiba kanta ya gama daurewa taga babu me xuwa barka tun dawowarsu, shiru kuma ba xancen taron suna gashi har an gyara rago, Yusuf kadai ya xo gidan a ranan, nan xuciyarta ya fara wani tunanin anya wa en nan ma’aurata ne ma kuwa, don ga dukkan alama wnn dai ba aure bane domin kuwa tun xuwanta bata taba ganin Sudais ya kwana gidan ba, amma meye tsakaninsu? Sudais na bedroom dinsa a can gidan Abbansa da yamma, shigowarsa gidan kenan tun safe da ya fita, Anty Maryam ce ta shigo dakin ya juya yana kallonta sannan ya gaisheta ta amsa da murmushi tace “Kasan an kai ma jiddah kaya kuwa Aliyu, and sati biyu aka sa bikin from today” kasa ce mata komai yyi da farko baki bude, can yace “Amma dai ni babu wanda ya gaya min, sati biyu kuma Anty, what’s d rush for, ni Wllh jiddar nan maganar gaskiya ta fitar min a kai, don Allah ni dai Anty….” Dafe kansa yyi yace “Ohh God, sati biyu fa ku ka ce?” Tabe baki Anty Maryam tayi ta juya ta bar masa dakin, zaunawa yyi gefen gado yana rike da kansa, can ya dago ya tashi ya fita, dakin Mami ya shiga ya sameta tana waya ya tsaya ya jira har ta gama sannan ya marairaice yace “Mami Anty Maryam ke ce min….” “Saura sati biyu bikin” Mami ta karasa masa tana masa wani kallo, tsaye yyi yana ta kallonta can ya juya ya fice a dakin, Mami ta fito ita ma ganin dakinsa ya koma ta fita compound, gun drivern gidan ta nufa, ya gaisheta da ladabi ta amsa masa tace “Musa, ina son ka min wani d’an aiki ne don Allah” with respect yace “Toh Hajiya aikin me xan yi” Tace “Ina son idan sudais ya fita gidan nan ka bi sa ka gano min ina xa shi, ko yanxu ko anjima ko da daddare” da mamaki yace “Barrister?” Tace “Shi” yace “Toh in sha Allah Hajiya” Har ta fara tafiya ta juya tace “And be very very careful you knw who you are dealing with”

    Sorry it’s nt much, long chappy ltr in sha Allah.

  • Noor Al Hayat 20

    Noor Al Hayat 20

    Not edited.

    Mai gadin ya girgixa kai yace “Toh ku yi hakuri gobe sai ku je ku dawo, amma ku tabbatar kun taho da wayar da xa ku yi communicating da ita” xai rufe gate Yakumbo tayi saurin saka kafarta daya ciki tace “Don girman Allah kayi hakuri ka bar mu mu shiga, wllh mun kashe kudin mota yayi dubu daya, kuma ni na biya, ka ji tausayina d’an nan” kamar xata rushe masa da kuka ta kai karshe, ya tsaya kallonsu da mamaki, can yace “Toh shkkn, amma har ni nasan sai kun janyo min fada wllh, amma bakomai akwai Allah, ku shigo” Yakumbo ta durkusa har kasa tana masa godiya suka shiga cikin makeken compound din gidan, uwa idonta xai fito yyi magana ta dinga bin gidan da kallo da motocin dake parking lot, Abuu ko idan da sabo ta saba shiga gidaje haka kai yara masu aiki, don haka ita ke biye da mai gadin yakumbo kuwa nata kalle kalle, bbu abinda khadijah tayi ma kallo biyu a compound din, don bbu bakonta a ciki. Karkashin wani artificial tree mai gadin ya nuna masu su jira sa, ya isa main entrance din shiga gidan, ya kusa minti biyar tsaye bakin kofar bayan ya danna bell aka bude kofar, Mai aikin gidan ce warce baxata wuce shekara ashirin da bakwai ba tana sanye da apron da hularsa alamar daga kitchen take, ganin warce ta fito yayi murmushi yace “Kyauta mun tashi lafiya?” Tace “Lafiya lau Usman, Ashe kai ne ma, ya aka yi?” Ya d’an sosa kai yace “Hajiya ce tayi bak’i ina fatan dai ta tashi bacci?” Kyauta tayi kasa da murya tace “Gata can parlor xaune ma” Muryar Hajiyar gidan suka ji tace “Waye kyauta?” Kyauta ta yi saurin barin bakin kofar tace “Hajiya, Usman mai gadi ne wai kin yi baki” Hajiyar dake gyara farcenta da nail cutter ta kalli agogo tace “Baki kuma?” Kyauta tace “Eh Hajiya” tace “Toh su shigo, amma ni bani da wasu baki da nake expecting da safen nan, da akwai ai da na gaya masa” Usman da ya ji abinda ta fada ya nufi gun da yakumbo suke yace “Allah ku daina karya bashi da amfani a rayuwa, yanxu gashi tace ita bata da wasu baki da take expecting da safen nan ku kuma har da ce min kun yi waya” yakumbo ta yi kasa da murya tace “Mu dai don Allah tunda har muka samu muka shigo gidan nan ka rufa mana asiri mu karasa idan ma ta kore mu shi kenan sai mu fita haka Allah yayi” ya nuna masu kofar shiga ya koma can bakin gate yana mamakin wasu ‘yan Adam. Da yake a bude kyauta ta bar masu kofar, da sallama Yakumbo ta kutsa kai cikin parlorn tana dudduke kai ga wani daddadan kamshi dake tashi ta ko wani angle… Abuu na biye da ita a baya, Sai da duk suka shiga khadijah ta tura kofar a hankali ta rufe sannan ta bi bayansu, Hajiya Fatima matar gidan ta dinga kallonsu da mamaki har suka xauna kasan lallausan carpet din tsakar makeken parlorn, sanyin Ac yasa yakumbo ta fara rawan Dari, Hajiya tace “Sannun ku da xuwa” Yakumbo tayi saurin cewa “Yauwa ina kwana shugaba?” Ba Hajiyar kadai bace xaune parlorn ita da wata ce wanda ga dukkan alama kanwarta ce tsabar kamanninsu, matar xa kuma ta yi shekaru talatin da ‘yan kai a duniya, Hajiya ta kalli kanwarta kamar yanda ita ma take kallonta, Amsa gaisuwar yakumbo Hajiyar tayi tace “Daga ina?” Yakumbo tayi gyaran murya kafin Abuu tace komai tace “Dama Hajiya da daddewa mun ji kina neman mai taimakon ki, shine ga yarinyata ganin irin haxakarta da hanxari yasa nace in rako Abuu dillaliya mu kawo maki” Hajiyar tace “Ayya ai kam ina da mai aiki bayin Allah gata can ita ta bude kofar ma….” Yakumbo ta katse ta tace “Ayya wannan d’an share share da goge goge xata ke maki Hajiya, wancan naga ai babba ce, ni ko baxa ki biya kudi mai yawa ba ki dauketa Hajiya don wllh daga waje me nisa muke ga uban kudin mota da muka kashe, ki taimaka fisabillilahi Hajiya” Abuu ta kara da cewa “Ki taimaka Hajiya wllh takanas saboda ke muka kawo yarinyar” Hajiya da tayi shiru tana kallonsu tace “Toh wacece mai aikin?” Da sauri Yakumbo ta nuna khadijah dake kallo so engrossed a katon plazma dake parlorn tana murmushi, Yakumbo ko lura da hakan ba ta yi ba, sai kallon Hajiya take ta kara jin abinda xata ce kan khadijah xuciyarta na bugawa, Hajiyar na duban khadijah tace “Ke ya sunan ki?” Inaa khadijah ana can duniyar kallo wannan karan har da dariyarta don film din ya mata dadi, yakumbo ta hadiye abu da kyar ganin irin kallon da Hajiyar ke mata, ta wani mitsileta a boye da sauri khadijah ta dawo, a fusace Abuu tace “Ba ke ake ma magana ba” khadijah ta kalli Hajiyar dake kallonta har lkcn tayi kasa da murya tace “Sorry ma’am, pardon?” Daga Hajiyar har kanwarta dake xaune kusa da ita bude ido suka yi suna kallonta sosai, Khadijah tayi kasa da manyan idanuwanta tace “I am sorry” Mikewa Yakumbo tayi jin fitsari ya taho mata, shi kenan khadijah ta cuce ta sai da ta buga masu turancin, ta nufi kofa da sauri tana cewa “Bari in d’an xaga Hajiya ku yi hakuri” Abuu ma sai kallon khadijah take baki sake jin fa kamar wani yare ta yi maimakon Hausa, Hajiya dake ta kallon khadijah tace “Alright, what’s ur name!” Khadijah ta kalleta tace “My name is khadijah Muhd” Hajiyar tace “From where” khadijah tace “I am from kano, I lost my mum and dad… My step mum brought me to Kaduna 4 days ago and she left me….” Tana magana ne har hawaye ya kawo idonta, Hajiya dake kallonta keenly tace “And… Who is this woman that left to ease her self now?” Khadijah tace “My stepmum told me she is her senior sister..” Shigowar yakumbo yasa khadijah tayi shiru, Yakumbo ta shiga kalle kalle kamar munafuka ta xauna amma kuma ta kasa cewa komai tana jiran jin hukuncin Hajiya, ta ma san kawai Hajiya fasa daukar khadijah xata yi don ita tunda take bata taba jin an dauki mai aiki yar boko ba, sai ayi tunanin wani mission ya kawo ta gidan, Hajiyar na kallon Yakumbo tace “Nawa ne kudin aikin?” Xuciyar Yakumbo yyi mugun sanyi ta gyara zama tace “Wallahi ko nawa Hajiya, ko nawa Allah ya hore maki babu damuwa barin yanxu da kudi yyi wahala” Hajiya tace “Dubu uku xan bayar, yanxu kuma xan ba da na wata uku kamar yanda nake ma duk mai aiki idan na dauka” Yakumbo dake ta godiya kamar marokiya tace “Wallahi ba damuwa Allah ya bi ya maki bukatunki na alkhairi, nagode nagode nagode” Kanwar Hajiya mai sunan Khadijah dake gefenta ce tace “Why House maid again bayan kyauta Mumy? Beside I don’t think this little girl will be capable, you just look at how engross she is with the TV….” Ko kadan khadijah bata ma san abinda ake cewa ba don gaskiya ne gaba daya hankalinta ta mayar kan kallo, yakumbo da babu abinda taji baya ga kyauta a xancen da Anty khadijah tayi ta marairaice tace “Kiyi hakuri baiwar Allah bbu abinda yarinyar nan ba ta iya ba wllh” Hajiya tace “Toh idan naga bbu abun kirki in sha Allah nan da kwana uku xa ku dawo ku dauki yarinyar, idan ya so sai ki mayar min da dubu shidda nah, ki rike dubu uku” Yakumbo tace “In sha Allah Hajiya, nagode nagode nagode” Hajiya ta katse ta daga godiyar da take yi tace “Toh ta wani number xa a same ki?” Yakumbo tace “ni ki ban naki idan na koma gida sai in kira ki Hajiya, na bar wayar a gida kuma ban san number ba” Hajiya ta sa kyauta ta kawo takarda da Biro tana cikin rubuta number aka bude kofar, duk suka juya kallon bakin kofar banda ita dake rubuta number, dogo ne tamkar dai khaleel din wasu can Lol… Irinsa shi ma ake kira da gentlemen, sanye yake da farar T-shirt da bakin wando, shigar ya kara haska farin fatarsa, iyakar kyau dai kam Alhmdllh Allah ya masa, tuni turarensa ya gauraye ko ina na gidan, har ya iso cikin parlorn idanuwansa na kan mahaifiyarsa dake rubuta sunanta kan number da ta rubuta a takardan hannunta, ya xauna gefenta yana murmushi ya mata side hug a hankali yace “Good morning mum” Sai a sannan ta kallesa hade da turasa tace “Morning…tashi kusa da ni sai warin asibiti kake dalla” Xaro ido yayi yana shinshina kayansa yace “Kai mum warin asibiti kuma duk kamshin nan da nake” tace “Ae kamshin daban warin asibitin daban” ya d’an yi murmushi yace “Ba dai warin asibiti ba sai dai kice kamshin magunguna mum…” Ya kalli Small mum dinsa yana shafa kai yace “Good morning small mum” tabe baki tayi tace “Allah ya kara…. ina ce nan ka tsallakeni ka tafi can gashi an gwaleka” rike kansa yyi yana d’an murmushi can ya dago a hankali yace “Mum kin ji koh” Sai a sannan ya kalli su Yakumbo, tayi saurin cewa “Ina kwana Alhaji” yace “Lafiya Alhmdllh” Hajiya da har ta bata paper din tace “Toh shkkn, yanxu saura in baku kudin ina sauraren kiran ku” kallon D’an ta dake xaune har lkcn a gefenta tayi tace “Aliyu akwai cash tare da kai yanxu?” Ya sa hannu aljihun sa, tace “10k xaka ban” dubu goman ya fiddo ya mika mata ta karba ta ba Yakumbo, Hannu bibbiyu ta karba tana jero godiya, Aliyu yyi saurin dauke kai yana kallon small mum dinsa da wani expression yace “Who are they?” Anty khadijah ta tabe baki tace “Wai house help” yace “House help kuma, did mum dismissed the one available?” Anty khadijah tace “Ina fa, duk biyun xata hada ina ga” ya yatsine fuska yace “Which means ta ba ma su Siyama daman su kara relaxing kenan” Anty khadijah ta tabe baki bata ce komai ba, yace “Which among them is the house help” Anty khadijah ta nuna masa khadijah dake rakube gu daya ana ta kallo happily, lekata ya dinga yi baki bude, can ya dago da sauri yace “Which help will this little girl render?” Anty khadijah tace “Kai ma dai ka gani” bai sake cewa komai ba ya fiddo wayarsa dake vibrate a aljihu, Su Yakumbo suka tashi xa su tafi har lkcn tana ma Hajiya godiya ko bin ta kan Khadijah bata yi ba ta fita tana kara dunkule kudin hannunta Abuu na biye da ita, Hajiya ta kalli Khadijah tace “Tashi ki dau cups din nan ga kitchen can ki kai su” ko kadan khadijah bata ji mai Hajiya ke cewa ba, har sai da Anty khadijah ta mata tsawa, ta dawo daga kallon da take a firgice, Hajiya ta nuna mata cups din tace “Ga kitchen a can ki kai su” tashi khadijah tayi tana neman cups din ta gansu can kusa da Anty khadijah, tana kallon Tvn da wayo ta nufi gun cups din, xaro ido Aliyu yyi jin yanda ta take kafarsa ya fixgota a mugun fusace yace “Baki da hankali ne” Hajiya tace “Bata sani ba fa ina ji Aliyu….” Khadijah dake ta kallonsa tayi kasa da kai a hankali tace “I am sorry, I didn’t notice ur leg”

     

  • Noor Al Hayat 27

    Noor Al Hayat 27

    Har bakin daki kyauta ta kawo ma su Anty Khadijah breakfast din, Mumy ta taso ta karba ta dawo ta ajiye ta xauna tana sauraren ‘yar uwar ta, Anty Khadijah tace “Toh fa kin ji Anty fati, kuma in sha Allahu da daddaya xan dauke yarana gaba daya a gidan, a kan wani dalili ina raye, dubi yanda iklima ta koma, mata muguwa axxaluma kawai duk ta gama da ubansu, tana neman kashe min ‘ya ya ni wllh da ba dan bana ra’ayin Salisu ba da bbu abinda xai hana ni fitar da matar nan in koma gidan” Mumy dake ta kallonta tace “Ta ya?” Anty Khadijah tayi kwafa tace “Lallai kina wasa da ni Anty” Mumy bata sake cewa komai ba sai bin iklima take da ta fito wanka da kallo, Anty Khadijah ta sauka ta shiga hada mata shayi tace “Yi maxa ki shafa mai ki taho kiyi breakfast Pretty” Mumy tace “Toh Allah ya kyauta, Allah kuma ya shiryi masu irin halin ta, Allah ya raya mu tare da yaranmu” Anty Khadijah tace “Ameen fa” Mumy tace “shi yasa na ke nuna maki masu aikin nan ki rabu da su lafiya, tsakaninki da su gaisuwar mutunci wani hantara da nuna isa duk ba shi bane” dakatar da ita Anty Khadijah tayi da hannu ta daure fuska tace “A’a kar ki fara Anty kar ki bata min, dangin uwa ko na uba da xan dinga gaisuwar mutunci da su su rainani, ni ba gashi yarana basu ji ba basu gani ba ana walakantasu suna wahala, don haka ki kyaleni nayi ma kowa ma haka” Mumy ta tabe baki tace “Ka ji xancen banxan, to ai wannan a rubuce yake duk abinda kayi ma ‘ya yan wasu sai an ma naka abinda nake ta nuna maki kenan kin ki gane wa” rai bace Anty Khadijah ta mike tana kallon Mumy tace “Ni dama tun da dadewa nasan ba so nake kike ba kawai kina xaune ne da ni dole don 6are ma sun fi ni k’ima a idon ki, Anty fati dole ne sai na xama so dangi kamar ki? Me ya hada ni da ‘ya yan wasu? Don Allah ki kyaleni in yi rayuwata yanda nake so, ke kije can kiyi ta kwashe kwashen mutane har sai kin kwaso warce xata fiddo ki a inuwar da kike ta tura ki rana, muna nan da ke kuma” Tashi Mumy tayi ta nufi kofa bata sake tanka ta ba, Anty Khadijah ta bi ta da harara tace “Ke so dangi… To mutanen nan su ne xasu raba ki da farin cikin ki idan ba ki yi hankali ba” Saleem dake ta xaune a dakin bai tofa nasa ba tun daxu ya girgixa kai bayan fitar Mumy, Anty Khadijah tace “Kai ka ji fa saleem, dole ne sai na ja mutane gantalallu da xa su daura min wahala a rayuwa a jiki? In ji da yarana da kai na mana, Ita taga xata iya ne halinmu ba daya ba kuma baxai taba xuwa daya ba in dai a kan wannan ne, gwara ta kyaleni, kuma duk shegen da bai gallaza ma ‘ya yana ba bai haifu cikin uwarsa ba… Mutum ne idan ban son sa ban son sa har abada babu me canxa min ra’ayi” Saleem yace “Ni Anty ban san me yasa Mumy take haka ba wllh, yau wannan gobe wancan, dubi fa kwanaki da kyar ta mayar da fitsararriyar yarinyar nan kauyensu ga shi yanxu ta jajibo wata ita wannan har boko naga an sa ta saboda matsayi” Anty Khadijah ta juyo tana facing dinsa a hankali tace “Wani bokon?” Saleem yace “Essence wllh” kasa rufe baki Anty Khadijah tayi tana kallon Saleem xuciyarta na bugawa, can ta nufi kofa fuuu ta fita, k’asa ta sauka gun kyauta, Kyauta dake ta aiki a kitchen tana wake wake tayi shiru ganinta ta risina tace “Har kin samu fitowa Hajiya” Anty Khadijah bata saurareta ba da wani expression tace “Kyauta ina yar uwar ki mai aiki nan” kyauta tayi kasa da kai tace “Toh Hajiya, jiya madam ta sa a kai ta makarantar bokon su baby, yanxu haka ma tana can” Anty Khadijah ta saki salati bata sake saurarenta ba fuuu ta wuce sama ta bude dakin Mumy, daga bakin kofa tana huci tace “Anty ita mai aikin kika saka a makarantar su siyama?” Mumy ta daga mata hannu tace “Khadijah ki tafi ki ban waje kar ki sake bata min rai don Allah, da kudin ki na sa ta bokon ko da ajiyar da kika bani?” Wani murmushi Anty Khadijah tayi tace “Ko daya, amma wllh kinyi making babban mistake a rayuwar ki, ita mai aikin kika sa a boko koh? Tam Allah ya taimaka, aje xuwa” daga haka ta fice daga dakin, parlor ta koma ta xaune tana girgixa kafa xuciyarta na kuna, can ta dau wayarta ta shiga kiran Aliyu, Aliyu dake xaune office ya dinga kallon wayar ganin mai kiransa har ya kusa katsewa sannan ya daga ya kai kunne hade da sallama, ko amsa sallamar bata yi ba cikin daga murya tace “Yanxu Aliyu kana gidan nan ka bari Anty ta sa mai aikin nan a makarantar da ku kayi?” Tabe baki yyi bai ce komai ba har lkcn wayar na kare kunnensa, tace “Ko da yake its a mistake ma kiran ka da nayi don duk bakin ku daya da Anty, kai ne ma munafukin… amma ina son ka sani wllh ta dauko ma kanta dala ba gammo ne, sai tayi mugun da ta sanin sake ma 6are da take yi kwanan nan ba sai an dade ba, sai ta xo ta sameni har daki tace Ashe abinda kike yawan gaya min gaskiya ne Khadijah, ni kuma a lokacin xan mata dariya, kai kuma ka ci gaba da biye ma gurgayen shawarar da take yi da kai har kai sai ya shafa muna nan baxa a dade ba in sha Allah, ita yarinyar da ku ka sa a makarantar sai ta ma sharrin da har jikoki baxa ka mance ba, sai ta goga ka bak’i a idon duniya” daga haka ta katse wayarta, Aliyu ya tabe a baki a xuciyarsa yace Allah ya shirye ki, daga haka ya ajiye wayar ya ci gaba da abinda yake. Da yamma bayan su Khadijah sun dawo tana bathroom ta shiga wanka kyauta kuma na fiddo mata kayan da xata sa sai ga Anty Khadijah ta shigo dakin ‘yar ta Iklima na biye da ita a baya, Ko rufe kofar bata yi ba tana ma kyauta matsiyacin kallo tace “Ina tsinanniyar take?” Kyauta ta rasa abun cewa ta fara kame kame sai ga Khadijah ta fito daure da towel, kin karasowa dakin ta yi ganin Anty Khadijah, kai kana ganinta kasan tayi mugun tsorata, Anty Khadijah ta karasa ta fixgota da karfi tace “Kina da gadon mutanen gidan nan ne da kika yarda suka sa ki a boko?” hawaye ya cika idon Khadijah cikin rawar murya tace “Ki yi hakuri Anty” kife ta tayi da tafin hannunta da karfi ta gwara kanta da bango tana hade hakoranta tace “Sai kin lalata tsafin da kika shigo mana gidan nan da har aka sa ki a boko don kaza kazan ki” Khadijah ta rike kanta tana kuka sosai tana kallon kyauta da ta tsaya a gefe idonta ya kada, dukanta Anty khadijah ta dinga ta ko ina tana cewa “Barin gidan nan ya kama Ki don kaza kazan ki” Muryar mumy suka ji tana cewa “Zo nan Khadijah” Anty Khadijah ta dago tana huci tuni Mumy ta juya ta bar wajen, Rankwashi ta kuma kai mata ta sake gwareta da bango tace “Da bakin ki xaki ce masu baki son makarantar idan ba haka ba in kashe ki, kuma ki kama hanyar kauyen ku” daga haka ta fita dakin fuskarta a murtuke, sama ta iske mumy a tsaye, mumy na kallonta rai a bace tace “Khadijah idan har baxa ki iya xama da ni da mutanen dake tare da ni ba ki tattara ki bar min gidana nan ba da dadewa ba, ai ban hanaki xaman gidan mijin ki ba, a kan wani dalili duk xaki bi ki takura ma bayin Allah a gida, ina fa sane da duk abinda kike ba wai ban sani ba, ina ruwanki da bokon da na sa ta? Kudin ki ne ko kudin wani naki, ki fita harkata a gidan nan wallahi, banda mugunta yayi maki katutu me yarinyar ta maki xaki je kina dukanta haka alhalin daxu kika gama nuna rashin jin dadin ki a kan yanda ake treating din naki yaran a gidan ubansu, wlh na fara gajiya dake da halinki, komai na harkan gidana ki cire idonki a kai ki jira idan kina naki gidan in kin so yan Adam ma su kwanta ki dinga tattakesu wannan matsalar ki amma baki isa ba a gidana tunda ba tsoronki nake ba, lastly bbu ruwanki da wannan yarinyar Khadijah, tsakanina da ke daban tsakanina da ita daban, ki yi ta kanki a gidan nan” daga haka mumy ta shige dakinta. Anty Khadijah tayi kuka har ta gode Allah, har ta hada kayanta da na ‘yar xa ta bar gidan wata xuciyar tace mata wato ma kenan yarinyar har ta isa da xaki bar mata gidan, ki tafi saboda ita, Inaa ai sai dai Ita ta bar maki, kyale Anty fati kawai kina xaune xata xo ta sameki, tunanin hakan yasa ta hakura da tafiyar duk da ba wai tasan inda xata bane, a ranta kuwa jin tsanar Khadijah take fiye da komai a duniya har kishiyarta ta kuma dau kudirin sai ta 6ata ta gun Mumy da kowa na gidan kafin a koreta. Tun da Aliyu ya dawo misalin karfe biyar yake xaune dinning, bai damu da rashin amsa gaisuwarsa da Anty Khadijah da ke xaune parlorn tayi ba, ya gama cin abinci ya hau danna laptop, iklima sai kai koma take a parlorn sun hada ido ya fi a kirga bata gaishesa ba shi ma bai ce mata komai ba, dinning taje ta dau ruwa suka sake hada ido ya hade rai yace “Sai na fasa idanuwan nan da kike kallona da shi a wajen, a gidan ku ba a koya maki gaisuwa ba ai sai kallon mutane kamar bakauyiya” turo baki tayi ta dauke kai ta bar wajen, Anty Khadijah da taji komai ta mike kamar jira take tace “Ae da ka fasa idon, tunda kai ka hallitar mata su, kuma bakauyiyar ce uban waye ba daga can ya fito ba? Idan ba munafurci da borin kunya ba ka nuna ka san ta ne balle ta gaisheka, ina ce kai ne ya kamata kace A’a iklima ce… ashe kun xo, yaushe ku ka xo ya hanya, amma kayi gum da baki tunda ba tarkacen da uwarka ta saba kwasowa bane, to wllh iklima ita ce dolen ka ba su ba, kuma baxa ta yi gaisuwar ba, ni din ma ba a walakance ka gaisheni ba kake jiran ‘ya ta ta gaisheka kawai don kun ga mutum na xaune gidan ubanku, bari ka ji…. yau sai uwarka ta rabu da ku amma ni muna makale ko min wuya don nice dolenta ba ku da ta samu a gidan nan ba, uwan mu daya ubanmu daya da ita, tun kan ku xo duniya muke tare, munafuki kawai” daga haka ta ja hannun iklima dake tsaye kusa da ita ta wuce sama tana cewa “I can’t wait ranan da tarkacen da ku ke debowa da har suke neman haddasa mana matsala xa su kunyata ku a gidan nan, wllh sai na xuba ruwa a kasa na sha don farin ciki, ke kuma iklima ko da wasa kar ki gaishesa ya fasa idon mu gani tun ance masa kwai ne” Aliyu ya tabe baki ya mayar da dubansa kan laptop din gabansa, baby ta karaso dining tana kallon Aliyu tace “Anty Khadijah can just shout for African ehennn, I don’t even like that her daughter that is eying me since, it seems she even used my sponge to bath this morning coz it wasn’t d way I left it” shi dai bai ce komai ba, ta bude masa textbook din math dinta tace “Yaya koya min assignment don Allah” ya kalli book din sannan yace “Ki je ku yi da Classmate din ki mana” Baby tace “Iman?” Yace “Yes” ta ce “She told me she is not feeling fine, kayi mana sai in kai mata ta yi copying nawa, she is even lying down now” yace “Me ya sameta?” Baby ta bude hannu tace “I don’t knw, or may be it’s because Anty Khadijah ta doke ta daxu, kasan duka tayi mata daxu fa” yace “Duka? Why? A ina ta doke ta?” Baby tace “Dakin can ta shiga ta mata dukan shine ni kuma naje na gaya ma Mumy a sama ta sakko downstairs tayi ma Anty Khadijah fada sosai, har sai da Anty Khadijah tayi kuka, I even saw her packing her load but I don’t knw what made her Change her mind kuma” yace “Kira min ita” ta ce “Iman?” Yace “Ehh” tace “Noo daxu da naje tana bacci na tasheta, shine kyauta tace kar in kara tashinta tace mata kanta yana ciwo sosai, kuma kamar Anty Khadijah ce tayi causing din ciwon kan coz she hit her head on the wall many times” Tashi Aliyu yyi yace “Mu je wajen ta” baby ta mike ta bi sa suka tafi dakin kyauta, kwance take kan gado kyauta ta rufe ta da bargo bayan uban rub da ta shafa mata a jiki, ya isa kusa da gadon Baby na biye da shi, sosai lebbenta yyi ja kana ganinta kasan ta ci kuka ba na wasa ba, ya kai hannu forehead dinta ya ji har ya dau xafi, baby ma ta taba tace “Kaji jikinta da xafi koh, Anty Khadijah ce tayi causing din komai” juyawa yyi ya fita ya wuce dakin Mumy, yana tsaye har mumy tayi hanging kiran da take tana kallonsa tace “Ya aka yi Abuturrab?” Yace “For God sake abinda Anty Khadijah ke yi a gidan nan is getting out of hands, why will she just best someone’s child the way she did” Mumy tace “Na fa yi mata magana nasan baby ce da gulma xata gaya maka, wllh ni kaina nayi mamakin abinda nayi mata daxu cos gaskiya I am nt happy” yace “Toh yanxu da ta sa ma yarinyar xaxxabi fa?” Mumy tace “Toh sae in ce Allah ya saka mata, don yarinyar dai bata mata komai ba” juyawa yyi ya fice daga dakin ya harari saleem da fitowarsa daga dakin Anty Khadijahr kenan ya sauka downstairs ya koma dinning ya xauna, mumy ce ta sakko ta shiga dakin kyauta, jin xafin jikin khadijah ta tada ta ta wuce sama da ita xuwa dakin baby, baby da ta biyo su ta xauna kusa da khadijah da mumy ta kwantar saman gadonta tace “Mumy let her be staying in my room sae mu dinga assignment tare ba sai ina xuwa dakin kyauta ba” Mumy tace “Tafi ki kira min yayanku” juyawa baby tayi ta fita ba a dau lkci ba ta dawo tace yana xuwa, mumy na ta jiransa har ya shigo da sallama tana kallonsa tace “Ko xaka samo mata magani don Allah Aliyu” ya karaso gadon yana kallon khadijah, mumy ta mike tace “Ae ita ma ga nata can ana gallaza masu kuma bata yarda don tana ma ‘ya yan wasu bne” daga haka ta fita Aliyu ya bi bayanta, baby kuma ta xauna tana ta kallon khadijah.

  • Noor Al Hayat 21

    Noor Al Hayat 21

    Littafin Noor-Alhayat na siyarwa ne kindly patronize ur writer and read happily_

    Aliyu ya d’an bude ido ya kalli Mum dinsa sannan small mum da ta hade rai, mumy tace “Toh ka ji, she didn’t notice” karasawa khadijah tayi ta dauke cup din ta nufi kitchen da aka nuna mata tana yi tana kallon TV har ta isa bakin kofar shiga, kin shiga tayi ta makale da bango tana kallon TV din, haka Mumy ta saki baki tana kallonta, ta kusa minti daya sai kuma ta juyo a hankali ta saci kallonsu, hada ido suka yi da Aliyu dake kallonta kamar yanda mahaifiyarsa ke kallonta ita ma, boye fuskarta tayi da hannunta da sauri tana yar dariya ta shige kitchen din, mikewa Aliyu yyi ya tabe baki yace “Lallai” sannan ya wuce sama, small mum dinsa ta mike tace “Kai fa kasan lallai, ni ban san me yasa Anty fatima take jajibe jajibe haka ba, ni abun ya isheni wllh” daga haka ta bi bayan Aliyu, Mumy dai bata ce komai ba, khadijah na ajiye cup din ta fito ta taho gun mumy ta durkusa gefenta a hankali tace “Anty naga remnant din fried potato and egg, and I am very hungry please can I take it?” Mumy ta gyada mata kai kawai tana kallonta, murmushi khadijah tayi tace “Thank you very much ma” daga haka ta mike ta wuce kitchen din cike da murna, ta dau dankalin da kwai ta xauna a nan kitchen din ta tankwashe kafarta ta fara ci tana lullumshe ido, a nutse take cin abincin kar ma ya kare ta fi minti goma a haka taji an shigo kitchen din, daga kai tayi tana kallon waye ta ga mutumin daxu ne, tun da ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba ya nufi gun da mugs suke a ajiye, Khadijah ta bi sa da kallo tace “Are you a medical Dr?” Juyowa yyi da sauri ya kalleta, ta wara masa manyan fararen idonta tana cin dankalin bakinta, ya daure fuska yace “Am I ur mate that u are asking me dat?” Ta girgixa kai da sauri tace “Not at all…. I just…” Sai kuma tayi shiru ta debi kwai ta kai baki, coffee ya hada ya xuba madara da sugar cube daya, tana ta kallon mug din ganin xai fita tace “Please can you give me some of ur tea” Juyowa yyi fuska daure yana kallon ta, tayi saurin sunkuyar da kanta tace “Ohk ohk sorryyy” har ya isa kofa sai kuma ya dawo ya dau wani cup ya xuba mata kusan rabi ya bude coffee powder ya debi rabin tea spoon ya kara xubawa a nata ya jujjuya sannan ya dauka ya mika mata yace “Here” wara ido tayi ta karba tana murmushi tace “That’s kind of you, thank you” ko kallonta bai yi ba ya fice daga kitchen din, haka tayi ta hura shayin tana jira ya d’an huce ta sha, tana sipping din kadan ta mike a gigice tana neman kofar fita jin daci sosai, wani kofar da ta gani ta bude ta fita da gudu, bakin tap ta ga kyauta tana wanke kayan ciki, ga kifi ta gama wankesu a gefe, har da naman kaza a ajiye, khadijah ta tofar da ruwan shayin bakinta tana yatsine fuska ta nufi gun tap din tace “Dan Allah Anty xan sha ruwa kadan” matar ta kalleta fuska daure tace “Me kike yi a kitchen?” Khadijah na ci gaba da yatsine baki tace “Ina cin potatoe and egg ne” sake wukan hannunta kyauta tayi tace “Uban wa ya baki?” Khadijah ta bude hannu tace “Antyn dake parlor tace in dauka in ci, har na kusa cinyewa ma” Kyauta ta tsuke fuska tace “Mayya, wuce ki ban wuri, kuma kafin in shigo ki wanke kayan wanke wanken dake kitchen din nan, da gani a yunwace kika xo dama” Khadijah ta juya ta bar wajen ta koma kitchen, karasa cinye dankalin tayi ta ajiye plate din da cup a sink, coffeen kuma ta rufe sannan ta fito parlor, Mumy dake xaune har lkcn ta nuna mata jakar kayan ta tace “Ki dau jakar nan ga daki can ki kai ki ajiye” Mumy ta fada tana nuna mata dakin dake parlorn, khadijah ta xaro ido tace “Anty kayan fa sun yi datti sosai they are not washed, they are even smelling” Mumy tace “Me yasa baki wanke su ba toh?” Ta langwabar da kai tace “Ni ban iya ba Anty, I only use to wash plate” mumy dake ta kallon ta tace “Toh dauka ki kai su can waje ki ajiye” tace “Ohk ma” daga haka ta dau jakar ta fita da shi can waje, ta dawo, xaunawa jikin kujera kusa da Mumy tayi tana kallon wani program da Mumy ta sa, a hankali tace “Anty bakya kallon cartoon?” Kallon ta mumy tayi, tayi murmushi kafin ta canxa channel din xuwa cartoon, happily khadijah tace “Thank youuu” Mikewa mumy tayi ta wuce sama, Khadijah ta gyara xaman kallon cartoon, a haka Kyauta ta fito daga kitchen ta ganta, daure fuska tayi tace “Ke dan kaza kazan ki ba wanke wanke kwanukan dake kitchen nace kiyi ba kika taho nan kina kallo?” Khadijah ta bata fuska tace “Plss xan yi, ina son in gama wannan cartoon din ne, I have never watch it before” Kyauta ta bude baki da mamki, tana son kara tabbatar da anya ta ji xancen su yakumbo da Hajiya sosai daxu kuwa, ita dai kamar ji tayi ance aiki yarinyar nan xata yi, ko dai bata ji dai dai bane? Khadijah ta turo baki ganin Kyauta taki tafiya, ta nufi kitchen din tace “Toh naji xan wanke” daga haka ta bi gefenta ta shiga kitchen din, kyauta tayi kwafa ta fita don ba ma driver sakon da xai siyo mata na farfesun da xata yi, Khadijah na wanke cups din a kitchen cikin sink trying hard bata xubda ruwa kasan kitchen din ba a hankali take wanke wanken, Aliyu ne ya shigo rike da mug din daxu, tana ganinsa ta tsuke fuska, shi kam bai kara kallonta ba ya ajiye mug din xai fita tace “Wait” da kamar baxai tsaya ba sai kuma ya tsaya ya juyo, cup din da ya bata coffee daxu ta dauko ta cire murfin ta taho gabansata daga kai tana kallonsa tace “You didn’t tell me that it was medicine u made…. I wouldn’t have ask for some” kallonta ya tsaya yi, xata kama hannunsa ta sa cup din da sauri yace “Ke xan mare ki fa” turo baki tace “Toh ni nace baxan sha ba is it by force” mika masa ta kara yi, ya dauke kai yyi murmushi yana shafa beard dinsa, kallon sink yyi yace “Toh xubar” ta xaro ido tace “How? Why? For what reason? Why shud I throw it away? Ummata told me that they are consequence of throwing food away” shafa kansa yyi ya karbi cup din ya karasa sink xai xubar ta rikosa da sauri ya buge mata hannunta, ta bata fuska xata yi kuka, kusan rabi ya xubar ya nufi inda kayan shayi suke, ya kara madara ya xuba Milo da sugar cube uku ya kara ruwan xafi a ciki ya juya sannan ya mika mata, ta wara ido da sauri tace “For me?” Ya hade rai tayi saurin karbewa cike da murna tace “Thank you very much” dai dai nan kyauta ta shigo kitchen din, tayi kasa da kai tace “Sannu da xuwa yallabai, ina kwana” yace “Lafiya lau” daga haka ya fice kitchen din, khadijah ta nemi waje ta xauna ta tankwashe kafa ta fara shan shayin idonta lumshe, muryar kyauta taji tana cewa “Kee shine ya baki shayin nan?” Ta bude ido da sauri tace “Ehh” kyauta ta hade rai ta karasa ta ja kunnenta tace “Idan kina shisshige ma yan gidan nan sai na ci kaza Kazan ki shegiya kawai” khadijah ta ci gaba da shan shayin ta bata ce komai ba. Kyauta ce ta karasa wanke wanken tana gunguni khadijah sai lekota take ta cikin cup ta take shan shayin ta, Mumy ce ta shigo kitchen din tana kallon kyauta tace “Kin bada sakon da nace kyauta” cike da ladabi kyauta ta bar wanke wanken tace “Ehh Hajiya” Mumy tace “Ohk, ina yarinyar nan take” kyauta ta nuna mata khadijah, Mumy tace “Ohk, idan ta gama ki turo ta ta xo ta amshi sabulu a sama tunda akwai omo a nan ki nuna mata yanda xata wanke kayan ta ga su can a waje wai masu daud’a ne” Kyauta tace “Toh Hajiya” daga haka Mumy ta wuce, Kyauta ta balla mata khadijah harara tace “Maxa ki gama kije ki amso, ni dai bbu wanki da xan maki” khadijah ta karashe shanyewa ta nufi gun sink ta ajiye cup din xata fito kyauta ta fixgota tace “Maxa wanke ni xan wanke maki?” Turo baki khadijah tayi ta fara wankewa a hankali kyauta ta kwace cup din tace “Tafi sama ki karbo min sabulun bbu abinda kika iya wllh” Khadijah ta juya ta fita ta wuce sama, tsaye tayi corridor tana kallon doors dakunan, ko wani daki na da taxara sosai daga na kusa da shi, aka bude wani kofa sai ga Anty khadijah, tana ganin khadijah ta hade rai tace “Ke me kike yi a nan, maxa sauka ance maki masu aiki suna hayowa nan ne” a hankali khadijah tace “Am sorry, Anty ce tace in xo….” Tsawa Anty khadijah ta mata tace “Maxa sauka shegiya” Mumy ce ta bude kofa ta leko tace “Ohk ni nace ta taho ta karbi sabulu khadijah” Anty khadijah ta hade rae tace “Kai Anty ki daina haka wllh ba shi da amfani ina kika taba ganin ana haka ma dai tukun, baki ganin yanda kawayenki suke da masu aiki ne, shegun ka ja su jiki su cuce ka kawai” mumy bata ce komai ba ta shiga ciki ta fiddo wasu sabulu masu tsada ta mika ma khadijah tace “Ki kai ma kyauta” khadijah ta karba ta juya, Anty khadijah tace “Ko da wasa kika sake hayowa nan wllh sai na mareki ko da kuwa Hajiya ce ta aike ki….” Khadijah dai bata ce komai ba har ta sauka, Kyauta ta kwace sabulun suka fita, bakin tap ta xuba duk kayan a roba tana yatsine fuska ta xuba ruwa da omo tace “Maxa taho ki wanke tsummokaran ki shegiya” Khadijah ta xaro ido tace “Kai Anty ban iya wanki ba fa” dagowa kyauta tayi da sauri tace “Toh uban wa xai maki” khadijah ta bude hannu alamar bata sani ba, kyauta ta dinga masifa tana jaraba ta shiga wanke kayan khadijah na tsaye tana kallonta, tas ta wanke su gaba daya tayi ta dauraya, khadijah dake ta tsaye tace “Anty in je in dinga yin shanya?” Kyauta tace “Ja can, warce bata iya wanki bace xata iya shanya” khadijah dai bata ce komai ba, kyauta tace “Ni dai da ki tafi ki ban waje in daina ganin ki” Khadijah tace “Toh Anty” daga haka ta wuce ciki da sauri taje ta ci gaba da kallonta, xaune ta samu Anty khadijah a parlor Aliyu na xaune kusa da ita sanye da 3qtr da farin riga yana nuna mata abu a laptop, tana ganin khadijah ta yi mata alamar da ta koma inda ta fita fuskarta daure, ganin Anty khadijah tayi shiru Aliyu ya daga kai yana kallon inda take kallo, dai dai lkcn da khadijah ta juya da sauri ta koma kitchen din, Anty khadijah tayi tsaki tace “Gayyar tsiya” shi dai Aliyu bai ce komai ba yana ci gaba da danna laptop dinsa, Komawa gun kyauta Khadijah tayi, kyauta ta hade rai tace “Dawowa kika yi?” A hankali khadijah tace “Wannan Aunt din ce ta koreni” Kyauta ta tabe baki tace “Wannan aikin ai sai khadijah baxawarar gidan, warce ta fi matar gidan xakewa, ta ki xaman aure ta xo nan duk ta gallabe mu da su Usman, ai sai ki je ga dakali can ki xauna ya kika iya” tafiya khadijah tayi ta xauna tana kallon kyauta dake ta daurayan kayan ta.

    Kyauta ta gama shanyan kayan ta dau sabulun da ya rage ta mika ma khadijah dake ta xaune a gun da ta nuna mata tace “Kina shiga parlor xa ki ga wani kofa, maxa ki shiga ki ajiye sabulun nan saura kuma ki min tabe tabe nasan yanda na ajiye komai na” tashi khadijah tayi ta karbi sabulun ta wuce ciki, ta kusa minti daya tsaye bakin kofar kitchen tana lekan parlorn don har lkcn Anty khadijah na nan, tun xuwanta wajen Aliyu ya ganta, da sun hada ido sai ya dauke kansa, can dai small mum din tasa ta mike tace “Xan tafi in kwanta Son” yace “Alright” daga haka ta wuce sama, sai a sannan khadijah ta shigo parlorn tana taku a hankali ta shiga kofar da kyauta ta ce mata, kare ma dakin kallo ta dinga yi, komai fes fes kamar ba dakin mai aiki ba har da gado a dakin, khadijah ta ajiye sabulun tsakiyar dakin sannan ta juya ta fito, gun Aliyu ta nufa ta tsaya kusa da shi tana kallon laptop din kafarsa tace “Kasan me?” Ko kallonta bai yi ba idonsa a kan laptop din, tace “Nima ina da laptop da Abbana ya siyo min ah….” Shiru tayi tana kallon sama tana son tuna sunan kasar, ta langwabar da kai tace “May be it’s china! kuma na iya operating laptop din amma kawu ya amshe min” kamar xata yi kuka ta kare maganar, ya dago kai ya kalleta yace “Na tambaye ki?” Dariya ta yi har da rufe fuskarta tace “A’a kawai gaya maka nake yi” yace “Toh juya ki bar nan” Dai dai shigowar kyauta parlon, ganin Aliyun tayi kasa da kai tace “Sannu yallabai” yace “Yauwa sannu da aiki” Kyauta ta shiga dakinta, ya kalli khadijah yace “Wuce ki ban waje” ta buda ido tace “Ohk” daga haka ta bi kyauta dakinta, kyauta dake kokarin ajiye sabulun da khadijah ta yasar mata a tsakiyar dakin ta juya ganinta ta rufe kofar dakin, sannan ta ja kunnenta tace “Ba nace ki daina ma mutan gidan nan shisshigi ba, ke wani irin kunnen k’ashi gare ki, me ya hada ki da likitan har xaki je ki tsaya gabansa?” Khadijah ta turo baki tace “I was just telling him about my laptop” sake baki kyauta tayi tana kallonta, can ta dungureta tace “Sannu baturiya, you dey tell am about ur laptop koh? Wai ma ina iyayenki?” A hankali khadijah tace “They are late?” Kyauta tace “Wa ya kawo ki gun aiki?” Khadijah ta langwabar da kai tace “Wata mata ce, she is very wicked” kyauta ta rike ha6a tana kallon khadijah, muryar Hajiya taji tana kiranta a parlor ta juya da sauri ta bude kofar ta fita khadijah ta bi bayan ta, Hajiya dake tsaye tace “Kyauta white rice kawai xa ki yi da miya for lunch, pepper soup din da xa ki yi kuma na dinner ne idan kinga xaki iya yi yanxu kiyi, idan baxa ki iya ba ki bari da yamma” kyauta ta risina tace “Toh Hajiya” Mumy ta juya ta koma sama, Aliyu dake parlorn har lkcn yace “Mumy baxa ki aiki ba yau” Tace “A’a sai gobe” Kyauta ta shiga kitchen Khadijah na biye da ita, Ruwan shinkafar ta daura kan gas, duk inda ta bi a kitchen din sai khadijah ta bi ta, gajiya da karon da suke ci Kyauta tayi ta fixgota ta nuna mata kofar fita kitchen din tace “Tafi ki ban waje baki min ko wani amfani a nan” da sauri khadijah ta fita kitchen din, bbu kowa parlorn haka yasa ta dau remote da sauri ta canxa xuwa cartoon, ta rakube kasan kujera tana kallo, kafin karfe daya Kyauta ta gama shinkafa da miyar ta fito parlor, dai dai sakkowar Anty khadijah downstairs, tun a stairs ta bude baki tana kallon khadijah da gaba daya hankalin ta na kan TV, kyauta na ganinta tayi kasa da kai xata koma kitchen ta kwalo mata kira, sai a sannan khadijah ta mike da sauri, cike da isa Anty khadijah tace “Ba ki gaya ma yarinyar nan rules din gidan nan bane kyauta?” Kyauta tace “Ban kai ga gaya mata ba Hajiya, tun daxu ina kitchen ne da na san nan ta xauna kallo da baxan barta ba kiyi hakuri Hajiya” Anty khadijah ta kalli khadijah fuskarta daure tace “An ce maki nan din gidan ubanki ne da kika taho kika hakikance a parlor kina kallo a matsayin ki na mai aiki da aka dauka yau” khadijah tayi shiru bata ce komai ba, a tsawace Anty khadijah tace “Ba magana nake maki kike kallona da shegun idanuwanki ba” Kyauta tace “Kiyi hakuri Hajiya hakan baxai kara faruwa ba idan Allah ya yarda” Anty khadijah tace “Halan baki san ita ma aiki aka dauketa ba da xaki bar ta tana kallo ke kuma kina ta aiki a kitchen, ina ce tare ya kamata ku yi aikin ba?” Kyauta ta risina tace “Kiyi hakuri naga yarinya ce Hajiya” Wani kallo ta jefeta da shi tace “Yarinya? Ai iyayen nata sun san yarinya ce suka kawo ta gidan aiki, maxa idan akwai wani aikin ki bata ta tafi taje tayi yanxu, daga yanxu kuma bana son sake ganin kina aiki ita tana xaune” kyauta ta juya da sauri tace “Toh Hajiya” bin bayan ta khadijah tayi, Anty khadijah ta dakatar da ita tace “Daga yau na sake ganin ki xaune cikin parlorn nan wllh sai na lahira ya fi ki jin dadi gayyar tsiya kawai” A hankali khadijah tace “Am sorry maa” daga haka ta bi bayan Kyauta da sauri. Kyauta ta fixgota bayan sun shiga kitchen din ta ja kunnenta tace “Kin ga xaki fara ja min matsala koh? Da nace ki wuce daga kitchen ce maki nayi kije kiyi kallo??” Khadijah ta girgixa mata kai kamar xata yi kuka, kyauta ta nuna mata can wani gefe tace “Tafi ki je ki xauna wawiya kawai, dole ne sai kin yi kallo har wancan baxawarar xata dinga maki gori bata san at times condition ke sa crayfish yyi bend ba, banda haka uban me xai kawo mu gidan nan” khadijah tayi dariya har da kyakyatawa tace “Anty is crayfish bent?” Hararata kyauta tayi ta juya ta ci gaba da abinda take, a dinning kyauta ta jera lunch din duk me son ci a can xai je ya diba, ta dau wani katon roba ta kusa cika sa da shinkafa nama yayi takwas ta fita parlor tana leke leke, dawowa tayi da sauri ta mika ma khadijah tace “Maxa maxa tashi ki kai dakina da sauri ki ajiye a bayan kofa ki rufo dakin” khadijah ta mike ta karba abincin ta fita da sauri, har xata shiga daki ganin Aliyu ta tsaya, sai kuma ta nufesa har gun stairs tana nuna masa abincin ta tabe baki tace “Kaga Anty mai girki tace in kai mata abincin nan daki da sauri, may be she fetched all the food kila har da kai ma baxa ka samu ba, cos there is nothing left in the pot, I even saw when she was pouring water inside” Aliyu ya rungume hannunsa ya hade rai yace “Where did u knw me from?” Tana rike roban abincin da kyau saboda tiririn da yake innocently tace “In this house mana, I….” Turata yyi baya da sauri har sai da ta kusa faduwa shi ma ya koma baya ganin ta sake roban hannunta gaba da uban shinkafa da miyar da nama suka tarwatse kasan tiles har kan stairs, ta xaro ido ta toshe baki kamar xata yi kuka tace “Shikenan ka xubar… wllh bani bace ba kai ne ka xubar, ka xubar ma Anty mai girki abinci….” Kyauta ta fito da gudu daga kitchen jikinta na rawa jin karar faduwar roba kamewa tayi gun ganin khadijah can bakin stairs ga tulin shinkafa a xube kasa, xata koma kitchen suka yi ido hudu da Aliyu ta sake dawowa da gudu bakinta na rawa tace “Subhanallahi ta xubar, ban san baxata iya ba dama nawa ne da nata da nasu Usman…” Khadijah ta daga hannu da sauri tace “Noo Anty mai girki bani bace ba fa, shine ya turani baya kawai abincin ya fadi a hannuna” Aliyu ya tsallake abincin ya bar wajen, Kyauta ta koma kitchen da gudu ta dauko wani karamar roba ta dawo ta dinga kwashe shinkafar tana xubawa a babban roban, khadijah tace “Hope u are nt eating this any longer?” ko kallonta kyauta bata yi ba ta gama kwashe abincin ta kai dakinta da gudu ta fito ta shiga kitchen ta fito da sweeper, cikin yan mintuna ta gama gyaran gun ta goge, sai a sannan ta mike tana hararan khadijah tace “Ae yau sai dai yunwa ya kashe ki gidan nan, ba dai ni kika yi niyyar toxartawa ba? Yanxu da baxawara ce ta sakko ba bawan Allahn nan ba ya xan yi da raina?” A hankali khadijah tace “Kiyi hakuri” kunnenta ta ja tace “Baxan yi ba, sai kin gaya ma yan garin ku da yunwar cikin ki yau, little brat kawai” daga haka kyauta ta koma kitchen da sauri, khadijah ta langwabar da kai ta bi ta da kallo. Da kyar khadijah ke cin shinkafar tana yi tana kallon shi da kyau ko xata ga dirt a ciki, kyauta sai hararata take tana ci hankali kwance, Khadijah tace “But Anty mai girki me yasa baki xuba mana wani ba?” Kyauta tace “Kika sake ce min Anty mai girki sai na kalla maki mari, Anty mai girkin gidan ku, nace idan baxa ki ci ba ki dau naman ki tashi ki ban waje ni xan iya cinyewa, kila ma gidan da kika baki samun irin wannan xaki xo nan kina min iyayi” Khadijah ta xaro ido tace “The woman is always cooking concoction there, bata taba irin wannan abincin ba” Kyauta tace “Toh ki rufe min baki ki ci abinci yanxu yaran gidan xa su dawo daga makaranta” khadijah tace “Ohk” Jin shigowar mota kyauta ta bar ma khadijah sauran abincin ta mike da sauri tace “Toh gasu can… Idan kin cinye ki fito da roban kika kai kitchen” daga haka kyauta ta fita, yara uku ne suka shigo parlorn sanye da kayan makaranta daya kamar khadijah take tana jss3, daya kuma na ss1, babban cikinsu na ss2, khadijah ta fito rike da sauran abincin ta tsaya bakin kofa tana kallon yaran, Gaba daya dinning suka nufa ko wacce na cewa “Yaya ina yini?” Aliyu dake xaune gun ya amsa masu gaba daya, bbu warce ta gaida kyauta dake ta masu sannu da xuwa duk suka wuce sama, banda yar karamar cikinsu sa’ar khadijah, Kyauta ta washe baki tace “Yauwa sannu Anty khadijah ya makarantar?” Yarinyar da ita ma sunanta khadijah tace “Alhmdllh, kyauta who is that girl staring at us?” Kafin kyauta tace komai khadijah ta turo baki tace “I am not staring at you…” daga haka khadijah ta shige kitchen da roban hannunta, duk wannan abun Aliyu na kallonsu daga dinning, yarinyar ta juya da sauri ta tafi gunsa tace “Ya Aliyu who is she?” Ya kamo hannun Kanwar tasa yace “Ask mumy” yarinyar tace “Ohk” daga haka ta wuce sama kyauta na cewa ta na cire uniform tayi sallah ta xo ta karbi abincinta, kyauta ta bi khadijah kitchen ta jawota fuskarta daure tace “Ke fa ba ruwanki da yaran gidan nan naga har kin fara masu fetsara, ki tsaya a matsayin ki idan ba haka ba baxawara ta ishe ki”

  • Noor Al Hayat 26

    Noor Al Hayat 26

    Shirin tafiya islamiyya suka yi bayan sun ci abinci, tun da Khadijah ta fito sanye da uniform din islamiyya Siyama ke ta harararta, kyauta da ta lura da hakan ta ja Khadijah kitchen tace “Kafin su gama iskancinsu da harare harare tafi gun Sanusi ki jira a gun motar” Khadijah ta fita ta tafi gun da motar yake ta tsaya, Aliyu ne ya fito baby na biye da shi a baya ita ma ta shirya, Baby tace “Yayanmu kenan baxan je mu taho da Daddy ba?” Yana bude motarsa yace “Ai islamiyya xa ki baby” ta bata fuska tace “Yaya yau kadai xan yi fashi fa” yace “Bulalan da xa a maki fa?” Tace “Ae cewa xanyi bani da lafiya sai ka rubuta min medical report in kai” yace “C’mon wuce ki shiga mota ku tafi makaranta my frnd… Bakin ki kamar medical report” Juyawa tayi kamar xata yi kuka ta tafi gun Khadijah dake kallonsu, ya shiga motarsa ya bar gidan. Karfe shidda da ‘yan mintuna suka shigo gidan daga islamiyya, wani saurayi ne xaune parlorn shi kadai yana danna laptop, ba can suke kama da Aliyu ba amma kana ganinsu kasan yan uwan juna ne, su siyama suka yi kansa cike da murnar ganinsa, siyama ta rungumesa tace “Wllh nayi kewarka ya salim, wai don Allah yaushe Yaya Aliyu xai tafi duk ya takura mu gidan nan, the house is just boring with him, idan Abba xai koma ya tafi da shi ya bar mana kai plss, Allah ya Aliyu is a problem in this house ko irin d’an birthday din frnds da party ya hana mu xuwa daga boko sai islamiyya” kamar xata yi kuka ta kare maganar, shi dai saleem sai uhn, uhm yake ta cewa yana sunkuyar da kai, sum sum Aneesah ta wuce sama, hakan yasa siyama ta bi parlon da kallo ta ga ya Aliyun xaune dinning yana kallonta, dauke kai tayi da sauri ta toshe baki tana xaro ido tace “Na shiga uku” Saleem ya dinga dariya kasa kasa har da kyakyatawa ba tare da ya kalli direction din Aliyu ba, Khadijah dake tsaye ita ma ta rufe fuskarta da Hijab ta wuce dakin kyauta tana murmushi, bin ta da wani kallo saleem yyi da wani expression yace “Who’s this?” Siyama ta yamutse fuska tace “The new housemaid after kyauta….” ya buda ido yace “What” tabe baki tayi ta mike tana satan kallon Aliyu tace “Sannu da gida yayanmu” kallon fork din gabansa yyi ya dauka tana ganin haka da gudu ta wuce sama tana turo baki, Saleem yyi murmushi ya mike ya isa dinning din yace “Big bro duk ka takura masu koh” Aliyu bai tanka sa ba ya dau Apple din gabansa ya fara ci. Bayan isha duk yan gidan suka hallara a dinning kasancewar in dai Daddy na garin duk a tare suke yin dinner a dinning area, Last cooler din kenan na soyayyen kaji kyauta ta dauka xata kai masu dinning din kasancewar ta mance Daddy ya hango Khadijah da ita ma ta fito daga kitchen xata shiga dakin kyauta rike da plate din abincinta, yana kallon Mumy yace “Kun yi baki ne?” Mumy ta kalli direction din Khadijah kafin ta shiga dakin ta kira ta, Juyowa Khadijah ta yi ta dawo, Sau daya Aliyu ya kalleta ya ci gaba da cin abincinsa kansa a sunkuye, Mumy tace “Yarinya ce aka kawo min riko daddy, kayi hakuri ban sanar maka ba yau satinta kusan uku, dama ina jiran sai ka dawo ne” yace “Riko kuma, daga ina” mumy ta yi yar dariya tace “Marainiyar Allah ce nan da ka gani” Saleem ya juya yana kallo Khadijah dake tahowa, Siyama ta tabe baki tare da tura abincin gabanta, Khadijah na isa wajen tana kallon Daddy a hankali tace “Good evening sir” da fara’arsa yace “Evening how are you” Khadijah tace “Alhmdllh, hw was the trip?” Ya kalli Mumy yana murmushi yace “It’s great” Shiru Khadijah tayi daddy ya nuna mata kujeran dake kusa da Saleem yace “Have ur sit ke ma” Ta gefen ido Saleem ke kallonta, Khadijah ta buda ido tace “Noo uncle I will love eating alone” daddy yyi murmushi yace “Alright then, do what pleases you” a hankali tace “Thank you” daga haka ta juya ta wuce, Daddy ya dau cokalinsa yace “She is sharp, haka nake son baby ta xama but baby is too meek” baby ta turo baki, Mumy tayi dariya tana kallon Baby da ta bata rai, kyauta ta bar wajen tana washe hakora a ranta tace “Har da mai gidan ma turanci take tsabar iya turancinta” sai da Daddy ya bar dinning area din sannan Saleem yyi facing Mumy yace “Wai mumy wacece yarinyar?” Aliyu ya ajiye cup din hannunsa yace “Did you have any business with her” Siyama ta hararesa ta gefen ido tace “Ya saleem na gaya maka house maid ce ko baka yarda bane, xan ma karya ne?” Mumy ta kalleta tace “She is a house maid or other wise thats nt ur problem, kuma kada ki sake kiranta da haka, yar rainin wayo kawai” jefar da cokalin hannunta tayi ta bar dinning din da sauri Aliyu ya bi ta da wani irin kallo, mikewa saleem yyi yace “Akan wata banxa can xaki bata mata rai mumy, for what….” Daga haka ya bar dining din shi ma, Aneesah ma ta tabe baki ta mike ta bi bayansu, Mumy ta bi su da kallo kafin tace “Allah ya kyauta” shi dai Aliyu bai ce komai ba, can mumy ma ta mike ta bar dining din, Baby ta bi abincin da suka bari ta kwashe naman kai ta sa a nata, Aliyu dake ta bin ta da kallo yyi murmushi yace “Glutton of the house” washe baki tayi tace “I don’t want it to waste yayanmu” yace “Then go and share it with Iman” mikewa tayi rike da plate din ta wuce dakin kyauta, ba a dau lkci ba ta fito ta ajiye plate din kan dinning tace “Na bata yayanmu, xan je wajen mumyna” daga haka ta wuce sama, yana ta xaune dinning din Khadijah ta fito rike da plate xata kai kitchen, tsayawa tayi ganinsa sai kuma ta nufesa tana murmushi ta buda dara daran idonta tace “Yayanmu thanks for the school bag I love it” kallonta yake yace “Wa yace maki sunana yayanmu” tayi dariya tace “Na ji baby tana kiranka haka, Anty kuma tana ce maka Aliyu, su Anty siyama kuma yaya Aliyu” bai ce komai ba ta juya xata wuce sai kuma ta dawo tace “But did you buy the bag with d name iman or you where d one dat place it there?” Yace “I don’t knw” wara ido tayi tace “Okay” sannan ta wuce kitchen, ganin kyauta ta fito gyaran dinning din ya mike ya wuce sama. Kafin Khadijah tayi bacci baby ta shigo mata da tsaraban da Daddy ya kawo tun daga kan chocolates, teddy bears, novels, takalma, rigan sanyi da ribbons na gashi sai kaya kala daya, kai kana ganin tsabar kasan na baby ne Mumy ta raba ta bata ta kai ma Khadijah, kyauta ma baby ta kawo mata nata tsaraban tana ta godiya baki har kunne. Kyauta na kitchen bayan su Khadijah duk sun wuce makaranta taji muryar saleem yana cewa “The great Aunt, ko minti goma ban yi da cewa xan kira ki inji yaushe xaki dawo, don duk gidan ba dadi ashe dai kina hanya” Anty Khadijah dake shigo da jakunkuna tace “Wllh kuwa, don ma d’an iska tsinannen mai mota muka samu, shi yasa na so Anty fati ta bani motar ta da xan tafi ta ki, banda haka wani banxan ne ya isa ya bata min rai a titi” Saleem dake taimaka mata shigo da kayan yace “Ae sai a hankali bin motar haya Anty da baki fara ba” Kyauta ta kwalalo ido ta jingina da kofa tace “Asshaa… Baxawara an dawo” Muryar Anty Khadijah taji tana cewa “Toh baxa ki shigo bane iklima ko kin kasa cire takalmin ne” kyauta ta leka a hankali suka yi ido hudu da Anty Khadijah, fitowa kitchen din tayi baki har kunne tace “Lale marhaba, Hajiya ashe ku ne, sannun ku da isowa” babu yabo babu fallasa Anty Khadijah tace “Ki hado ma iklima breakfast bata karya ba muka taho” sai a sannan yarinyar ta shigo parlorn, baxa ta wuce su baby ba a shekaru amma kana ganinta kasan cikin wahala take, ga tabo duk jikinta, kyauta ta karasa kusa da ita da gudu ta rungumeta tace “Yau ga iklima na gani ashe kece, yar kyakkyawa maa sha Allah, sannu da xuwa iklimatu” Anty Khadijah tace “Dalla ki cikata ki tafi ki nema mata abun k’ari, dangi uwa ko na uba” da sauri kyauta ta juya ta nufi kitchen, iklima ta bi ta da harara tace “Ashe ma house maid ce, kawai xata shafa min datti a jiki” Saleem yace “Iyye kaji Iklima manya, wato datti xata shafa maki koh, to ina su Yusuf?” Ta turo baki tace “Ai basu san mun taho ba” Anty Khadijah da ta yi hanyar stairs da jaka tace “Kafin ta gama maki breakfast din taho in sa maki ruwan xafi kiyi wanka, Saleem ku kuma saukan yaushe” Saleem yace “Jiya muka dawo Anty” tace “Daddy na part dinsu kenan” Saleem yace “Ina ji” bin bayanta yyi da sauran kayan, sai da suka isa dakinta tace “Aliyu fa?” Ya ajiye jakar hannunsa yace “Ya fita aiki.” Mumy ce ta fito jin muryar yar uwarta ta shiga dakin ita ma.

  • Noor Al Hayat 24

    Noor Al Hayat 24

    Da washegari har baby suka wuce makaranta bata yarda ta kalli inda khadijah take ba, ba Anty khadijah ba, har Mumy ta tambayeta me ya sami idonta tace babu komai, har daki Anty khadijah ta kai kan ta gaya mata ko an mata wani abu ne amma baby taki gaya mata komai, khadijah kuwa tunda ta shiga kitchen safiyar ranar jin muryar Anty khadijah ta makale ta ki fitowa, Allah ya gani ko matan kawu ba ji tsoron su kamar yanda take tsoron Anty khadijah ba, babu kalan xagin da kyauta bata yi ma Anty khadijah ba jiya a daki bayan Khadijah ta gaya mata abinda ya faru, har tsine mata sai da tayi, daga karshe rub ta shafa ma khadijah a bayanta da jikinta sannan ta sa ta ta kwanta ta dungureta tace “Gobe kya tsaya kallon shegen tv dinsu ke ma mayya” ita dai khadijah bata ce komai ba, wannan dalili ne ma yasa tun da khadijah ta shigo kitchen kyauta bata sa ta ko da dauko cokali ba, tana dai tsaye gefe tana kallonta, kyauta ta fita kai ma Anty khadijah dake xaune parlor Lipton a cup, mumy tace “Ban ga khadijah ba kyauta, ko bata tashi bane?” kyauta tace “Tana kitchen Hajiya, tare muka fito” Anty khadijah ta tabe baki tana kai Lipton din hannunta baki, kyauta na komawa kitchen tace “Kin min tsaye a kai tun daxu, ki tafi ki gaida Hajiya” Khadijah tayi shiru tana kallonta, turata waje kyauta tayi, hakan yasa khadijah ta turo baki ta wuce parlorn, Mumy na kallonta da mamaki tace “Me ya samu fuskarki?” Girgixa kai tayi tana sauke idonta kasa tace “Ba komai Anty” mumy tayi shiru tana kallonta hakan yasa ta durkusa kasa tace “Ina kwana” Mumy tace “Lafiya lau, kira min kyauta” Khadijah bata tashi ba sai da ta gaida Anty khadijah da ta amsa da kyar tana jifanta da wani kallo sannan ta wuce kitchen tace da kyauta Anty na kiranta, mumy na kallon kyauta bayan ta xo tace “Kyauta me ya sami khadijah fuskarta ya tashi haka?” Kyauta tayi kasa da kai tace “Hajiya nayi tambayar duniyar nan taki gaya min, haka nima naga fuskar kamar an mareta har ma da jikinta duk mintsili ne, nayi nayi da ita ta ki gaya min” Mikewa Mumy tayi ta wuce gun khadijah da taki fitowa daga kitchen, tana dubanta da kyau tace “Akwai wanda ya doke ki a gidan nan ne khadijah?” Khadijah ta girgixa kai da sauri tace “A’a Anty” Shiru mumy tayi tana kallonta, can ta juya ta fita kitchen din ta wuce sama gaba daya, Anty khadijah ta bi yayar tata da harara, da sauri kyauta ta shige kitchen tun kan su hada ido. Driver ne ya kai su kyauta da khadijah kasuwa misalin karfe sha daya domin yi ma khadijah siyayyar da mumy tace, Kyauta ta daukar mata duk wani abin da ta san xai amfaneta, har kayan sa wa, sai da kudaden suka kare sannan ta hakura suka koma gida, khadijah na ta lekan kayan daga cikin ledan kyauta ta kai mata rankwashi ta daure ledan da kyau. Xaune suka tadda Aliyu da abokin sa Farouq a parlor, kyauta ta gaishesu ta wuce daki, Khadijah ta kalli Aliyu da bai kalli inda suke ba tace “Good evening” yace “Evening” daga haka ta bi bayan Kyauta, Farouq na tambayarsa wacece ita bai taba ganinta ba. Ranan asabar mumy tasa khadijah ta shirya su je islamiyyar da su Siyama ke xuwa ayi mata register, saukin abun Anty khadijah na can daki tana ta bacci kamar matatcciya bata san abinda ake ciki ba, Da farko mumy driver tace yaje yyi mata komai a makarantar, amma ganin Aliyu ya shigo gidan daga clinic tace “Abuturrab tunda ka dawo ko xa ka taimaka kai ta ayi mata register?” Ya d’an hade rai yace “Noo Sanusin dai yaje ni yanxu shiryawa xan yi in tafi daurin aure zari’a” Mumy tace “Zaria? Sai ka dawo yaushe?” Yace “Anjima in sha Allah” tace “Toh shkkn” daga haka ya wuce sama, dole Sanusi ne ya tafi da su gaba daya makarantar khadijah dai na xaune daga jikin kofar motar su Siyama ko kallonta basu yi ba sai ma hade rai da suke ta yi, ko wace bata son jikinta ya taba nata don kuwa taxara sosai ne tsakaninsu a cikin motar, a ajin baby aka sa khadijah bayan anyi mata interview, nan Sanusi ya biya duk kudin ya karbar mata form ya koma gida don a cike mata, a ranan kuma mumy tasa ya je kasuwa ya yankar mata uniform da Hijab, kyauta sai murna take tayi mata bayan sun dawo da yamma, khadijah kuwa sai washe baki take tana bata labarin yanda islamiyyar yake, can kuma kyauta ta hade rai tace “Toh ni me yasa basu sani islamiyyar ba” khadijah ta xaro ido ta rike kugunta tace “Kaji Anty mai girki bayan kin girma?” Ranan lahadi bayan sun dawo islamiyya da yamma mumy ta sa Sanusi ya kai su saloon kasancewar duk lahadi suke gyaran gashi, tun da khadijah ta ji Mumy tace aje da ita hankalinta ya tashi, ta tafi ta kwanta kamar mai bacci a dakin kyauta, kyauta ce ta shiga ta korota waje ta rufe dakinta, haka dai suka tafi saloon khadijah kamar an aiko mata mutuwa duk ta daga hankali. Siyama aka fara gyara ma gashin sannan Aneesah sai baby, aka xo kan Khadijah tuni ta fara hawaye tace “Mai saloon ni gashina bai yi dirty ba ki duba ki gani” Mai saloon din ta saki baki tace “Toh bai yi datti ba me kika xo yi” cikin rawar murya tace “Anty ce tace sai na xo” Mai saloon na ganin xata tada mata hankali tace su wuce kawai bayan an bada kudin su siyama. Shiru Mumy tayi da mamaki tana kallon khadijah dake matsar kwalla bayan sun dawo, can tace “Sai kace yarinya khadijah, yanxu gyaran gashin ne kika ki tsayawa a maki?” Anty khadijah dake xaune tana ta girgixa kafa tana tabe baki cike da masifa tace “Ai maganinki kenan Anty Fati, gwara da ta kunyata ki ba ke sodangi ba” Mumy ta kalleta tace “Toh kika san ko tana da matsalar scalp ne?” Aliyu dake xaune dinning ya bar abincin da yake ci ya fito parlorn rike da makullin motarsa yana kallon khadijah yace “Mu je saloon din” xaro ido tayi ta nufi daki da gudu tace “Anty kice masa gashina bai yi ba datti wllh, mai saloon din ma ta duba tace mu tafi” ya hade rai yace “Xan xaneki idan kika shiga dakin nan….” Anty khadijah ta mike da mugun mamaki tace “Yau nake ganin ikon Allah… to ina ruwanka Aliyu? Meye damuwanka da gyaran gashinta da rashinsa har xaka zakalkale haka” Ko saurarenta bai yi ba ya sake ce ma khadijah ta fita kar ya xo ya sameta inda take, da gayya Kyauta ta kora masa ita waje tana satan kallon Anty khadijah, Ya bi bayan su bayan yasa baby ta biyosa, Kasa cewa komai Mumy tayi ta bi su da kallo, baby ce ta xauna gaba, Khadijah ta xauna a baya tana share hawayen da ya kawo idonta, kyauta ta rufe motar har da risinawarta tana daga ma Aliyu hannu tana masa Allah ya tsare hanya. Da kyar mai saloon ta gama gyaran gashin khadijah me tsayi bana wasa ba, sae sheki yake, ga gashin da uban laushi, khadijah tayi kuka har ta gode Allah, haka kowa ya saki baki yana kallonta a saloon din, babu sunan wanda bata kira ba bayan ummanta har da Anty mai girki da Mumy, shi dai Aliyu na tsaye yana kallonsu yana son yin dariya amma bai yi ba, baby ma na tsaye kusa da shi tana kallon khadijah, ba don shi ba da babu abinda xae sa khadijah ta tsayar da kanta har mai saloon ta samu daman gyarawa, dubu uku Aliyu ya ba mai saloon din tana ta godiya, yana ma khadijah wani kallo yace “Get up my friend” make kafada tayi wasu sabbin hawayen na xubo mata, kujera ya sa mu ya xauna yace “kiyi mata kitson kawai madam” da gudu khadijah ta fice a saloon din, baby ta kyalkyale da dariya mutanen dake cikin saloon din na taya ta, khadijah dake tsaye jikin mota ta dinga leka saloon din ko matar ta biyota, yana fitowa ya dagata yyi cikin saloon din ta rirrikesa tana ihu tana basa hakuri, mai saloon dake dariya tace “Ta tuba babban yaya ayi mata hakuri” baby ta rufe baki tana dariya har da kyakyatawa, bude bayan motar yyi ya saka ta ciki ya rufe ba shiri tayi tsit kirjinta na heaving, ya harareta ta madubi yace “Xan yi maganin ki ne” Bayan sun koma gida har daki Anty khadijah ta bi Aliyu, Ta rufe kofa tana masa wani kallo tace “Aliyu akan wani dalili ka tafi da yarinyar nan saloon daxu, ban gane me hakan ke nufi ba, ka taba sanin ta ne da can ko kuwa shisshigi ne da hali irin na uwarka ya motsa? Kai ma sodangin xaka koma” Aliyu dake ta kallonta yace “Meye a ciki don na kai ta saloon Anty, Kina fa ji Mumy ce tasa ta bi su Siyama kuma ta ki yarda ayi mata, to make my mum talk less shi yasa kawai ni na kai ta da kaina kuma ba gashi ta tsaya ba” Anty khadijah tace “Eh lallai ni kake gaya ma bakar magana ko Aliyu? Babu damuwa, xan yi maganinka” daga haka ta fita, Aliyu ya tabe baki ya mike ya rufe kofar sa don a bude ta bar masa. Yau khadijah ta cika sati biyu gidansu Aliyu, babu abinda Mumy ta rage ta da shi a gidan, duk yanda ta yi da su siyama haka take mata ita ma banbancin kawai shi ne har lkcn a dakin kyauta take, kusan dai kyauta ce kadai mai aikin gidan don ko kadan kyautan ma bata takura khadijah tayi aiki sai dai fa tana nuna mata abubuwa da yawa ko kadan ne tana barinta tayi har goge gogen, ranan da khadijah ke da sati daya a gidan Anty khadijah ta tafi Abuja ganin yaranta, hakan yasa hankalin khadijah kwance har na sati biyu yanxu, Tunda baby ta ci duka gun Aliyu ko kallon banxa bata sake ma khadijah ba, sai ma note da take bata wani lokacin ta kwafar mata na boko ita dai Mumy bata ce masu kala don kuwa rubutun khadijar ma ya fi na baby kyau, har assignment khadijah na kwatanta yi ma baby, su siyama dama ba wani interacting suke da ita ba, don haka babu ruwansu da ita, A yau da ta cika sati biyu ne mumy na bedroom dinta da yamma Aliyu ya shigo, Gaisheta yyi tace “Halan ka fita nyt duty ne?” Yace “Tun three days back yanxu morning xuwa yamma nake yi” tace “Ohk, kun yi waya da Abbanku” Aliyu ya shafa kansa yace “Ehh ai gobe xai taho in sha Allah” tace “Nima haka yace min daxu” yana fiddo wayarsa a aljihu yace “Wai yaushe Anty xata dawo mumy?” Mumy tace “Toh nima dai ban sani ba wllh, amma jiya da ta kirani kamar akwai damuwa kilan su Iklima na cikin wani hali….” Yace “Toh Mumy wai me yasa iklimar baxata dawo nan gidan ba, su Ahmad maxa ne bbu damuwa sosai amma ita macen da ta dawo nan” Mumy tace “Ai ubansu baxai yarda ba ne matsalan sai dai ta taho da ita ba tare da ya sani ba” Aliyu ya girgixa kai yace “Allah ya kiyaye” mumy tace “Ameen dai” Shiru yyi bai sake cewa komai ba, Mumy tace “Ya aka yi kamar kana son yin magana koh?” Murmushi yyi don sure yasan mum dinsa ta gama karantarsa gaba daya, yana facing dinta yace “Mumy dama ba komai bane a kan Mai sunan Anty ne” tunda khadijah ta shigo gidan bai taba kiran sunanta ba saboda Anty khadijah, Mumy ta kallesa da sauri tace “What about her?” Yace “Noo, kawai mum naga da ki taimaka a sa ta a boko…” Katse sa tayi tana kallonsa da kyau tace “Ko saboda me?” Ya d’an bude ido yace “Noo Mumy naga kawai she isn’t an illiterate, its just anyi depriving dinta right dinta ne, from all indications she was born with a silver spoon, you knw… it’s just condition mum, ina tausayinta ne wllh, kin dai ga har coaching Baby tana kokarin yi, she is very intelligent, Allah will reward you idan kika taimaka mata mumy” murmushi mumy tayi tace “Kasan me Ali?” Ya girgixa kai da sauri yana kallonta, strictly tace “Abuturrab ko da wasa, I mean ko ba a cikin hankalinka ba, kayi making mistake din ce min kana son yarinyar nan wataran I will show u my other side, because it will and will neva be possible, that is just it” da mugun mamaki yake kallonta, a hankali yace “Sonta kuma mum?” Ta gyada kai tace “Yes” yyi shiru na few seconds kafin yace “Mai ya kawo wannan xancen mumy?” Ta hade rai tace “Kai ka kawo sa, for I see no reason har xaka damu In sa ta makaranta kai ka kawo min ita gidan?” Ya girgixa kai kawai, tace “To be careful, yes xan sa ta makarantar boko amma wllh wllh ko a mafarki ka cire ran akwai aure tsakanin ka da yarinyar nan, period” Ya kalli Mumy a hankali yace “But.. Ko saboda me” strictly Mumy tace “Hakan nake so ya kasance, or are you querying me” yace “Amma mumy ni ai ba ce maki nayi ina son ta ba, boko kadai nace ki sa ta for the sake of Allah, meye ma xai sa kiyi tunanin nan mumy, ni kuma in rasa warce xan ce ina so sai karamar yarinyar nan? Wallahil azim ban taba kawo hakan a raina ba, gaskiya I am nt happy mum” daga haka ya mike ya fita a dakin.

  • Noor Al Hayat 23

    Noor Al Hayat 23

    Washegari thursday Kyauta xa ta kasuwa tare da Khadijah bayan Mumy ta fita aiki, Anty khadijah kuma ta fita anguwa, Aliyu kadai suka bari gidan kasancewar night duty yake yanxu, da ido ya bi su har suka fita parlorn, Driver da xai kai su kasuwar ya tada motar ganin sun fito, Daya daga dogayen riguna Umma ta siya ma khadijah ne jikinta sai hula da Kyauta ta sa mata ta bata karamin mayafi ta daura a kan, Khadijah ta karbi list din abubuwan da xa su siyo ta dinga karanta su kyauta na jifanta da hararan wa ya sa ta? Driver Sanusi yace “Wai wannan yarinyar madam tace mu je tare da ke ayi ma siyayya?” Kyauta tace “Ehh ita ce” Drivern yace “Kin ga shi kenan sai ayi mata gaba daya koh? Daxu ta bani dubu ashirin da biyar kafin ta fita” kyauta tace “Ka ji sanusi da wani xance, cefane fa xa mu je yi ba kasuwar kaya ba” Sanusi yace “Toh shkkn, gobe sai mu je kasuwar kayan” sai kusan karfe daya Kyauta ta gama duk siyayyar da xata yi suka dawo gida, babu kowa gidan har Aliyu ma ya fita, nan ta daura girki a gurguje Khadijah kuma ta tafi yin sallah kamar yanda tace mata tana idarwa taki fita tayi kwanciyarta. Karfe Uku da rabi su Siyama suka dawo gida, kyauta ta xuba masu abinci gaba daya ta kwashi uniform dinsu ta kai gun wanki, baby kadai ce parlor ta sa cartoon tana kallo da plate din abincin a hannunta da yake bbu islamiyya, su Siyama kuma suna can kan dining, khadijah ta fito daga daki tashinta daga bacci knn ta makale jikin bango tana kallon Cartoon din da baby ke kallo, Baby na ganinta ta kashe tvn da remote ta hade rai, shiru khadijah tayi bata ce mata komai ba, su Siyama suka fara dariya suna kallon khadijah dake tsaye, bude kofa aka yi duk suka juya Aliyu ya shigo parlorn Baby ta kallesa tace “Yayanmu sannu da xuwa” ya karaso parlor ya ajiye makullin motarsa saman table ya xauna tare da jinginar da kansa da kujera yace “Ya school, yau ba islamiyya sai kallo koh” baby bata ce komai ba ta kai fork dake dauke da taliya bakinta, ya kalli TV yace “Wa ya kashe television din” Baby ta nuna masa khadijah tace “Ko ba ita bace take kallon cartoon din da nasa, tell her to get away” kwace remote din yyi ya kunna tvn yana hararanta, Tayi shiru bata ce komai ba, yace “Wawiya kawai” daga haka ya mike yyi wucewarsa sama, baby ta hade kai da gwiwa xata yi kuka, juyawa khadijah tayi ta wuce kitchen, su Siyama suka bi ta da harara. Khadijah na ta tsaye kitchen tana kallon naman da kyauta ta daura yana ta soyuwa a cikin mai kyauta kuma na can waje, jin an shigo kitchen din ta juya da sauri taga Aliyu ne, cup ya dauka ba tare da ya kalleta ba yace “Have you eaten?” Kai ta gyada masa ita ma bata kallesa ba, sai ga kyauta ta shigo kitchen din, ganin Aliyu tayi saurin cewa “Sannu da xuwa yallabai, in kai maka abinci” ya juya ya nufi kofa yace “A’a nagode” khadijah tayi narai narai da ido tace “Wallahi anty mai girki ni ban kulasa ba shi ne yyi mun magana ki tambayesa ma ki ji” da sauri kyauta ta tura kofar kitchen din ta rufe ta daura hannu a ka tana xaro ido tace “Na shiga uku ni kyautar Allah, yanxu ‘yar nan me nace maki xaki ja min salalan tsiya?” Khadijah tayi shiru tana kallonta, kyauta ta bude kofar kitchen din ta turata waje tace “Tafi ki ban waje ni dai” turo baki tayi ta juyo taga Aliyu xaune parlor da baby dake sulking har lkcn, ta wuce daki tana ci gaba da turo baki. Da daddare khadijah ta fito wanka tana daure da xanin da kyauta ta bata ta dinga wanka, kyautar kuma na tsaftace kitchen aka bude kofar dakin, Anty khadijah ce ta shigo baby na biye da ita a baya, kana ganin Khadijah kasan ba karamin tsorata tayi ba ganinta, Anty khadijah ta riko duk hannayenta biyu da hannu daya fuskarta kamar bai taba ganin ruwan alwala ba tace “Don kaza kazan ki kinsan matsayin yarinyar nan a gidan nan?” Ta fada hakan tana nuna mata baby, Khadijah da ta gama tsorata gaba daya cikin rawar murya tace “Anty kiyi hakuri” mari Anty khadijah ta sauke mata, lkci daya tayi saurin daura hannunta a lebbenta alamar kar tayi kara, hawaye ya shiga sakko mata ta dinga girgixa mata kai, kalle kallen dakin Anty khadijah ta dinga yi ko xata samu wayar wuta amma bbu, hakan yasa ta kuma kai mata wani mari, Cikin kuka khadijah tace “Anty don Allah kiyi hakuri ban mata komai ba” da hannu Anty khadijah ta dinga dukan bare skin dinta tana mintsilinta ta ko ina tana cewa “Toh wllh ko kallon baby kika sake yi a bisa kuskure cikin gidan nan sai na sumar da ke shegiya balle ki mata kallon banxa, gayyar tsiya arna a idi, kuma daga yau kika sake tsayawa cikin parlor ba kitchen ba koh cikin dakin nan sai na kashe ki in kashe banxa” wani Marin tayi mata ta rankwasheta ta hankadeta sannan ta kama hannun baby suka nufi kofa tana cewa “Banda Anty fati hau ya fada mata ina ita ina dinga yi ma shegun mutane abinda take yi yanxu, ai sai dai idan bana gidan nan amma duk sai na sa an sallameki har tsinanniyar kyautar, ni kadai raina ma xan iya aikin gidan nan gaba daya idan Allah ya yarda, shegu kwadayayyu yan maula” Kuka kawai khadijah take har da shessheka rabonta da irin wannan kukan tun tana gidan kawunta, fita tayi dakin ta wuce kitchen gun kyauta tana kuka sosai, nan taga kyauta bata kitchen ta bude kofa ta fita can gun da kyauta ke cewa ta xauna ta xauna nan ta dinga kuka kamar ranta xai fita, Aliyu ya mike daga xaunen da yake yana aiki a laptop ya leka kasa, juyawa yyi ya bude kofa ya fita, tsaye yyi kanta yana kallonta, ganinsa ta hade kai da gwiwa tana ci gaba da kukanta, ya durkusa yace “What happened?” Dagowa tayi tana kallonsa amma ta kasa cewa komai saboda kukan da ya ci karfinta, yyi shiru bai ce komai ba, ya kyaleta don kanta ta daina kukan a hankali sai ajiyar xuciya da take, yace “Me aka maki?” Cikin rawar murya ta nuna masa cikin gidan wasu hawayen na sakko mata tace “Wannan Antyn nan ce ta min duka” shiru yyi yana kallon tafin hannun dake kwance saman fuskarta da yyi ja, yace “Wace Anty?” Kasa cewa komai tayi saboda wani sabon kuka da ya taho mata, yace “Don’t cry again, ki fada min wace Anty ce ta doke ki” ta buda masa hannu muryarta na rawa tace “Ban san sunanta ba” Fiddo wayarsa yyi a aljihu ya shiga gallery ya nuna mata hoton kusan yan gidan gaba daya yace “Wacce a ciki?” Ta goge hawayen idonta tana kallon hoton da yake nuna mata da kyau, a hankali tace “The one wearing blue” sake kallon hoton yyi yaga Anty khadijah ce, yace “Me kika mata” wasu sabon hawayen suka taho mata tace “May be wannan yarinyar ce tace mata ina kallo a parlor…..” yace “wacce yarinya?” Shiru ta yi bata ce komai ba hawaye na taruwa idonta, Ya sake shiga gallery ya nuna mata hoton daxu ta nuna masa baby, dauke kai yyi bai ce komai ba can ya kalleta yace “Toh ina kayan ki?” A hankali tace “I just took my bath shine ta shigo daki” rushewa ta kuma yi da kuka yace “Don’t cry, ki jira ni a nan” daga haka ya mike ya wuce ciki, ba a wani dau lkci ba ya dawo rike da hannun baby dake kallonsa a tsorace, Ya iso gun khadijah da ita yana kallon khadijar yace “stand up” mikewa tayi, ya mayar da dubansa kan kanwarsa yace “Me ta maki kika yi reporting dinta gun Anty, kuma if you dare lie to me you are in big trouble” kamar xata yi kuka tace “Yayanmu am sorry” ya hade rai sosai yace “I will give u a dirty slap idan baki yi answering question dina ba” Muryarta na rawa tace “I only told aunt that….” Yace “That what?” Hawaye ya cika idonta tace “Don Allah yaya kayi hakuri” kalle kallen gun ya fara yi, ta fashe da kuka tace “Wayyooo yayana kayi hakuri” ya buge bakinta ya mata alamar da ta yi shiru, ta toshe bakinta da hannu daya tana hawaye, ya isa gun wani flower ya karya branch din ya dawo yace “Kawai saboda ke muguwa ce kika je kika sa Anty ta mata duka koh” a rikice ta dinga girgixa masa kai tace “Aa wllh, yaya kayi hakuri baxan kara ba, let me tell her sorry now plss” hannunta ya fixgo yace “Kika kuskura kika min ihu idan na dauke ki daga nan wllh asibiti xa mu tafi” daga haka ya shiga tsula mata bulalan yanda yasan xai yi mugun shigarta yayi hakan kusan sau biyar tana tsalle tana son kwace kanta amma ta kasa gashi ba daman ihu, sai da yaga hannunta yyi ja sannan ya saketa tana tsalle hawaye na sakko mata, ya hade rai yace “Tafi ki bata hakuri” da sauri ta isa gun khadijah dake kallonsu cikin rawar murya tace “Don Allah kiyi hakuri” Khadijah tayi kasa da idonta tace “ke ma kiyi hakuri” Fixgota Aliyu yyi tana kuka tace “Yaya wllh na bata hakurin” yace “Tell her you two are now frnds from this moment” ta kuma kallon khadijah da sauri tace “We are now frnds from dis moment” a hankali khadijah tace “You are welcm” ya sake kanwarsa yace “Maxa goge idonki kije tap ki wanke fuskar ki tafi ki kwanta, if I shud hear pimm, you will spell doom, I mean idan kika kuskura kika gaya ma kowa abinda ya faru sai na kusa cire maki kunne” da sauri ta je ta wanke idonta ta goge fuskarta sannan ta wuce cikin gidan, ya kalli khadijah da ta bi ta da kallo yace “Ke ma good nyt” ta kallesa ta gyada masa kai a hankali tace “Bye” daga haka ta shiga ciki ita ma.

  • Noor Al Hayat 17

    Noor Al Hayat 17

     

     

     

    Karasowa parlorn dattijuwar matar tayi har lkcn tana kallon khadijah tace “Where are you coming from?” Khadijah ta dago a hankali tace “Just 3 houses away….” Matar tace “Gidansu Hajiya Salaha kenan?” Khadijah ta gyada kai, matar tayi shiru tana kallonta, can tace “An aiko ki ne?” Ta girgixa kai tace “A’a kawai abinci nake son ci” kallon d’an ta da ke xaune matar tayi, khadijah ta ci gaba da cin abincin gabanta, shi dai bai ce komai ya mike xai bar parlorn, mahaifiyar sa ta bi sa da ido tace “Kaje to Sadiya ta xuba maka wani abincin koh” ya juyo yace “Noo dama it’s not as if ina jin yunwa mum, anjima xan ci” daga haka ya wuce ciki, matar ta dinga kallon khadijah dake cin abincin sanyi sanyi, can ita ma ta juya ta bar parlorn, jawo remote khadijah tayi ta kunna TV ta gyara xama tana facing tvn, tana cin abincin amma gaba daya ta ba tv attention dinta, bayan kusan minti talatin taji ance “Wai ke baxa ki gida bane? Ba kin gama cin abincin ba” Ta juyo da sauri ta kallesa sai kuma ta marairaice tace “Plss ina son in gama kallon nan” sakin baki yyi yana kallonta ga plate din abincin ta gama, bai dai ce komai ba ya fita rike da makullin mota, ba a dau lkci da fitarsa ba sai ga yan mata uku sun shigo gidan sanye da kayan islamiyya, tun da suka shigo suke kallonta ita kam ko sanin sun shigo bata yi ba, Muryar matar daxu taji a parlorn tace “Ke baxa a nemeki gida ba” khadijah ta dago da sauri, sai kuma ta bata fuska tace “Anty bana son xuwa gidan” Matar ta buda ido tace “Baki son xuwa kuma?” Shiru ta d’an yi kafin tace “First… They are so dirty and unkept, and I don’t like their dishes…. I don’t just like the house” matar dake kallonta da mamaki tace “Toh ba gidan ku bane” khadijah ta girgixa kai a hankali tace “Noo uncle dina ne ya kawo ni” matar tace “Maza tashi ki tafi kar ayi ta nemanki kin ji” kallon agogo tayi taga karfe shiddah ta ce “plsss ma… am I always welcome here?” Matar ta d’an yi murmushi tace “Sure” khadijah ta kwashe plate da cups da ta ci abinci tace “Where can I find d kitchen” nuna mata matar tayi ta kai ta fito sannan ta dau ruwan goron da d’an ta ya ajiye tace “In tafi da shi?” Matar ta gyada mata kai, murmushi tayi ta risina tace “Thanks ma” daga haka ta nufi kofar fita matar ta bi ta da ido, tana fita gidan gaba daya ta hango mutane tsaye bakin gate din gidan kawunta, tafiyar minti kusan shidda tayi ta isa gidan, tsaye ta tadda su Hajiya Salaha da yaransu gaba daya ga makota ana ta surutu, Sajida ce ta fara ganinta tace “Lahhh mama kun ganta” sai aka juyo gaba daya ana kallonta, Hajiya Salaha ta isa inda take da sauri ta fixgota tace “Daga ina kike?” Khadijah dake bin kowa da kallo tace “Just few houses away…..” Bata rufe baki ba Hajiya Salaha ta sauke mata mari, wani ihu ta fasa tana rike da fuskarta tana jin duniyar na juya mata, tunda take ba a taba kai hannu jikinta ba bare fuskarta sai ranan, iyaka a sa ta tayi kneel down ta daga hannu, har tsadadden bokon da take xuwa a kano ma ba a duka, Hajiya Salaha na huci ta shiga kunduma mata xagi tana cewa “Allah ya isa yawon da kika sa muka dinga yi muna nemanki kamar gantalallu, sai Allah ya saka mana… Kuma bari Alhaji ya dawo wllh xaman ki ya kare gidan nan ya je can ya kai ki gun talakawan dangin uwar ki…” Kuka kawai khadijah take tana rike da fuskarta, hakuri mutanen wajen suka dinga ba Hajiya Salaha suna cewa ai yarinya ce, Hajiya maimuna da ganin Khadijah ya sa ta shiga parlor ta fito da wayar wuta ta nufo ta, wata mata ce tayi saurin janyeta tace “A’a don Allah ki bari Maman Hafsa, ayi mata hakuri” wata mata ma ta rike wayar tana ba Hajiya Maimuna hakuri, Hajiya Salaha tace “Ku bar ta ta ci mata mutunci crook ce wannan yarinyar da ku ke gani haka, wa yasan gidan uban da taje” Matar da ta ja Khadijah ta duka dai dai fuskarta tana kallonta tace “Ina kika je ake ta neman ki yan mata” Khadijah na shessheka tace “I was hungry and I had to…..” Kasa ci gaba tayi ta rushe da kuka, Matar ta d’an kwalalo ido tace “Tohhh bata jin Hausa ne?” Hajiya Maimuna tace “Iskancin fa?? Tsabar shakiyanci ne da iyayi da kinibibi ita er mai kudi, toh wai ma ina mai kudin yake yau? Ku ce min yana kabari, toh idan ma xata sauke kai ta yi rayuwa yanda ko wani talaka ke yi ya rage nata, uwar me suka tsinana ma mutane banda tsoron Allah har Alhaji xai daukota ya ajiyeta a gidansa, wai I am hungry… To kafafuwar uwarki xan dafa maki in baki banda abinda aka girka kika ki ci” Hajiya Salaha tace “Ae komai ya xo karshe, ya dawo yasan yanda xai yi da ita, wnn ‘ya sai ta kashe aure, taje can inda xa a dinga dafa mata indomie da kwai a bata shayi mai kauri da custard ta sha, mu ba rainon tea da bread muka ma yaranmu ba” daga haka tayi shigewarta ciki, Matar dake rike da Khadijah tace “Ke me yasa kika fita baki sanar masu ba? Komai aka baki kuma bata sai ki ci ba khadijah” Khadijah ta kasa cewa komai sai kuka take, jin kiraye kirayen magrib duk aka fara watsewa ana ma su Hajiya Allah ya kyauta, wasu kuma na tausayin khadijah domin kuwa suna ganin iyayenta basu mata adalchi ba in har abinda su Hajiya ke fada gaskiya ne a kanta, ba a san yanda rayuwa xata kaya ba don haka iyaye ya kamata su dinga koya ma ‘ya yansu both the right and left side of life, yau idan an ci na masu kudi gobe a ci na talaka bawan Allah, wannan xai sa yaro yyi adapting a duk situation da xai tsinci kansa. Khadijah ce kadai tsaye tsakar gidan duk sun shige ciki da yaransu, ta share idonta a hankali ta bude kofa xata shiga, a tsawace Hajiya Salaha tace “Ki shigo ki mana me? Maxa koma sai Alhaji ya dawo gidan nan, maxa fita kar in sumar dake annamimiya kawai” juyawa tayi da sauri ta bar wajen bayan ta rufe masu kofa ta nemi wani waje ta xauna ta daura kanta bisa kneels dinta, har aka kira Isha tana wajen ga sauro sai cixonta suke, Kawunta bai dawo gida ba sai wajen karfe goma, bayan ya gama parking xai shigo ciki ya ga kamar mutum a wajen ya haske waya, tana nan yanda take bacci ya dauketa a hakan, da mamaki yace “Ke!!” Firgit ta farka ta mike tsaye da sauri, yace “Me kike a nan” tana kallonsa da idonta da yyi bulu bulu yyi jajir, shatin hannun Hajiya Salaha a gefen fuskarta hankali tace “Aka ce in tsaya a waje” yace “Saboda me?” Tayi shiru bata ce komai ba, shiga gidan yyi ya tarar da su gaba daya da yaransu ana xaune parlor ana kallo ana shewa, duk suka fara cewa “Abba sannu da xuwa…” Bai bi ta kansu ba yace “Me wancan yarinyar take yi a waje?” Hajiya Maimuna ta tabe baki tace “Xaman jiran ka dawo” Hajiya Salaha ta kara da cewa “Tun kafin la’asar ina jin yarinyar can da ka gani ta fita muka dinga bin layi layi muna nemanta da makwabta ba ita ta dawo gidan nan ba sai dab da magrib, duk ta Daga mana hankali daxu gidan nan ba masaka tsinke” yace “Shine xa a bar ta xaune waje cikin sauro a jawo min abinda xai sa in kai ta asibiti?” Hajiya Salaha tace “Toh xan iya mata abinda raina ke raya min Alhaji shi yasa nace tayi ta xama a waje” yace “Toh kada warce ta sake turata waje war haka ko uban me tayi… Na gaya maku” juyawa yyi ya kalli Khadijah dake tsaye ta rakube a fusace yace “Xo nan” karasowa tayi da sauri ya wani hade rai yace “Ina kika je?” Hawaye ya cika idonta ta nuna masa waje da hannunta jikinta na rawa, fixgota yyi ya turata ciki yace “Gobe ki kara, saurayen da suka cije ki ma kadai sun isheki” daga haka ya wuce ciki yana cewa “Sai ku bata abincin idan xata ci idan kuma baxata ci ba ta kwana da yunwa” daki ya wuce, Khadijah ta xauna kasa jikin kujera bata yarda ta hada ido da su Hajiya dake ta 6alla mata harara ba, a wani kwanon da yyi tsatsa aka xuba mata tuwo da miyar kubewar da aka girka, ta jawo abincin a hankali tana kallonsa, miyar ta kai baki ta d’an yamutse fuska, ganin kallonta Hajiya maimuna take tayi saurin saita fuskarta, ta tsura ma TV ido tana kallo kamar yanda duk occupant din parlorn suka yi, ji tayi Hajiya Maimuna tace ma Hafsa taje ta dauke kwanon abincin ta kai kitchen, Khadijah bata damu ba don dama ba yunwa take ji ba, sai waje karfe sha daya da rabi kowa ya tafi makwancinsa ita ma ta kwanta a kan tabarmar da aka nuna mata ta dinga kwanciya a dakinsu Sajida wai katifar baxai dauke su su dukka ba. Bayan kwana biya Khadijah na xaune tsakar gida da yamma tana uban wanke wanken da su Hajiya suka tula mata, su kuma suna ciki da yaransu kasancewar ranar Friday ce bbu islamiyya, yi take kamar baxata yi ba tana turo baki an hanata kallo, wanda a kansa kusan kullum sai ta sha mazga amma ta ki hakura, ita dai tayi kallo, duk ta rame ta kanjale, kana ganinta kasan akwai yunwa sosai da wahala tare da ita, ga rashin sabon aiki, ba laifi yanxu tana d’an wanke plates din su fita sai dai ta kan fi awa biyu kan kwanukan wanke wanken, kayan jikinta kuwa yanda aka san ta shiga rafi tsabar jikewar da yake idan tana wanke wanken, yanxu an ma daina sa ta sharan gaba daya tsabar kawai bata iya ba sai dai wanke wanke da jan ruwa wani lkcn a waje idan bbu wuta, tun ranan da ta fita har yau bata sake fita ba sai dai idan an aiketa gun mai kanti ko kuma xata debi ruwa a er karamar bucket da take dauka, har yau bata sake cin abinci mai dadin gidan da taje ba, abincin gidan kawu daga taliya sai tuwo da shinkafa da wake da mai da yaji, gashi duk bata son su hakan yasa take tare da yunwa sosai, Hafsa ta fito ta jefa mata kudi tace “Khadijah wai Mama tace ki je gun mai kanti ki siyo sabulun wanki da Hypo leda biyu, sai ki siyo maggi mai tauraro na hamsin” Khadijah ta turo baki bata ce komai ba, tashi tayi bayan Hafsah ta wuce sanin Hajiya na iya lekowa taga ko ta wuce, ta shiga parlor Hajiya Salaha tace “Aiken fa” ta kalli kayan jikinta tace “Mama xan canxa kaya” dakuwa tayi mata tace fita Ki ban guri, shashasha sshe da gangan kike jike kayan wajen wanke wanke kenan kin san abinda ya kamata” juyawa tayi ta fita, ta sake kallon kayan dake a jike tun daga saman gwiwanta har kasa, gate ta nufa kanta sanye da hula don gaba daya Hijabs dinta yaran gidan sun gaje, tafiya ce me nisa xuwa gun mai kanti, tana tafe tana wasa da d’an karamin iccen hannunta, har ta wuce gidan da taje ta ci abinci idonta na kan gate din gidan amma ba daman shiga, tana isa gun mai kanti cikin aiken da aka mata maggi kawai ta tuna, gida ta koma da sauri ta shiga parlor tana kallon Hafsa kamr xata yi kuka tace “Me da me kika ce ma” Hajiya Salaha tayi wani murmushi ta na kallon kishiyarta tace “Me na fada maki” Hajiya Maimuna tace “Kin ji na maki musu? Ko an taba aikenta bata dawo tambayar me aka aiketa ba dama” Hajiya Salaha ta ce “Wllh Ubanki ya cuce rayuwar ki, kishiyar uwarki kuma kiri kiri ta nuna bata son ki tunda har ta sangarta ki haka ta lalata ki saboda ba ita ta haife ki ba, banda haka wannan xabgegiyar budurwa godai godai kullum aka aike ki sai kin dawo wai kin mance, sai shegen turancin iyayi…. ni dai wllh tunda yarinyar nan ta xo gidan nan nake fama da surutu abinda yaran da na haifa ma basu sa ni ba, Allah dai ya isa wllh” Hajiya maimuna ta tabe baki tace “Ke kika ga xa ki iya, ni kinga ina yi? Ai sai dai duka” Kabir ne ya sake nanata ma khadijah Aiken da aka mata ta fita da sauri tana maimaita abinda yace a ranta har ta isa gun mai kantin sannan ta fada masa, yana dariya yace “Ke yar fari ce ko?” Ta wara ido tace “I don’t understand” dariya yyi yace “Aa ni ba bature bane, don nema maki saukin kai wa da dawowa idan an aikeki kawai kice a dinga rubuta maki sakon a gida kinji” tace “Ohk then” muryar da taji yana cewa a bashi kati ya sa ta juyawa da sauri, suka hada ido ta washe fararen hakoranta tace “Good evening” daga sama har kasa ya kalleta yace “How you?” Ta langwabar da kai tace “I shud say fine” yana gyada kai yace “Good” karban card din da mai kantin ke mika masa yyi yace “Doguwa dake baki sa Hijab idan xa ki fito” a hankali tace “Bani da Hijab yanxu” bai ce komai ba yana loda card din kafin yace “Toh me yasa kika jika kayan ki” tace “Wanke wanke nake yi tun da rana” yace “Ina ne gidan ku?” Tace “Our home is 3 house’s away from u people’s” ya kalleta yace “Gidan Alhaji Jibril?” Ta gyada masa kai, yace “Ke yarinyarsa ce” ta girgixa kai a hankali, yace “Yaushe kika xo gidan!” Ta kalli sama kamar me naxari sannan tace “10 days ago” ya gyada kai bai ce komai ba, ta amshi ledan sakonta da canji tana kallonsa kafin tace komai yace “Ya sunanki?” Tace “Khadijah” yace “Good” a hankali tace “Ina son in xo in ci abinci gidan ku amma an hanani, kuma I can’t eat the food they are cooking, it’s just concoction” a hankali ta karashe maganar, yace “Me yasa aka hana ki?” Tace “Su mama sun ce xa su kashe ni idan na sake xuwa ko ina kuma ina jin tsoro” ya kalleta bai dai ce komai ba, ta matso kusa da shi a hankali tace “Ko xaka dinga kawo min abincin gidan ku da kanka?” Ya buda ido yace “Ina?” Tace “Gidanmu mana, sai in dinga boyewa a backyard ina ci” tana magana ne hawaye cike fararen idonta, jin yyi shiru ta ci gaba tace “I am always hungry….” Ya sauke idonsa daga kanta bai dai ce komai ba.

  • Noor Al Hayat 15

    Noor Al Hayat 15

    Shekaru shiddah baya…..

    A hankali ta karashe shanye shayin dake hannunnta ba tare da ta bi ta kan soyayyen kwan dake gabanta ba ta ajiye cup ta mike tace7 “Umma to idan Kawu ya tafi da ni baxan sake dawowa ba?” warce ta kira da Umma dake duke tana goge mata takalmanta masu tsada tana xuba su a wani jaka ta juyo da rinannun idonta tana kallon ‘yar yarinyar warce da kadan ta haura shekara sha uku tace “Xa ki dawo Khadijah in sha Allah” Khadijah bata sake cewa komai ba tana dai tsaye, tsadaddun ready made ne jikinta da cover shoe mai kyau sai kyalli yake, da farin hijab karami, kunnuwanta dauke da dankunnen zinari ‘yan kanana, Khadijah tace “Toh Umma me yasa ke baxa mu je da ke ba” Umman bata kalleta ba tace “Nima gidanmu xan je Khadijah” Khadijah ta durkusa kusa da ita a hankali tace “Umma ni bana son gidansu Kawu ki tafi da ni gidanku don Allah” Umman bata ce komai ba har ta gama rufe jakar ta daura kan babban jakar dake dauke da kayan Khadijah, jin Umma bata ce komai ba Khadijah ta dau remote xata kunna TV, Umma ta jefa mata wani kallo tace “Xaki fara ko, ni dai na gaya maki kar kije gidan mutane kina masu irin wannan kallon da kike kamar wawuya, kashe TV din nan yanxun nan” Khadijah ta kashe tvn ta koma ta xauna kan kujera, dai dai shigowar kawunta, kuma wan mahaifinta, har ya karaso parlon idonsa na kan soyayyen kwan da Khadijah ta bari a plate, ya dau plate din ya xauna yace “Tsabar almunbazzaranci dubi abinda aka yi ma lafiyayyen kwai, karshen komai ya xo in sha Allah” ita dai Umma bata ce komai ba ta wuce daki don fiddo nata sauran kayan da ya rage a gidan, Kawu ya dinga cin kwan kamar his life depends on it, har dai ya gama daga karshe ya ajiye ya na kallon Khadijah dake ta kallonsa yace “Toh ki tashi ki fita ga adai daita can ki shiga ki jirani a kofar gida” ta xaro ido tace “Kawu ba da mota xa mu je ba” dakuwa ya mata yace “Tashi ki ban waje” mikewa tayi tayi hanyar kofa tana waigosa, shi kuma ya dau katon jakar ya bi bayanta, Umma ta fito da nata kayan waje ta dau plate da cup ta shiga kitchen ta wanke su ta ajiye, ta kuma sake tabbatar da komai a kashe yake sannan ta bi bayansu, Khadijah na tsaye jikin adai daitan Umma ta jawo ta, a hankali tana kallon eyeballs dinta tace “A duk inda kika tsinci kanki ki xamo mai hakuri kin ji Khadijah, nasan ki da shi, komai kuma aka sa ki kiyi, sannan most important of all banda kallon TV don Allah…” Khadijah tayi murmushi da ya bayyana beauty point dinta tace “Umma I can’t do without watching tv fah” Umma ta hade rai tace “So u won’t heed to what am saying koh?” A hankali ta sauke idonta tace “Am sorry mum” Umma ta ja kumatunta tana murmushin karfin hali tace “That’s my girl” a hankali kuma a sanyaye ta kara da cewa “And always pray for daddy, kullum kika yi sallah ki masa addu’ar Allah ya masa rahama” Khadijah ta gyada kai tace “Toh Umma” Umma ta shigar da ita adai daitan tace “Safe trip dear, I will always pray for you” Khadijah ta gyada mata kai trying hard to control her tears, Tuni Umma ma ta juya ta nufi main road da jakarta ba tare da ta bi kan kawu Jibril dake kokarin maka ma gidan kwado ba, Khadijah ta bi stepmother din ta da kallo hawaye na sakko mata, a haka kawu ya shigo adai daitan, yana mata wani kallo yace “Kukan uwar me kike ma mutane” cikin rawar murya tace “Umma ta” Dungurinta yyi yace “Uwar ki ba Ummar ki ba” Khadijah ta sunkuyar da kai, mai adai daitan ya dau hanyar park, hannu Khadijah ta daga ma stepmum dinta ganin sun wuceta, ita ma ta daga mata tana goge hawayen idonta. Tasha mai adai daitan ya kai su, kawu ya sauke kayan Khadijah ya bai ma mai adai daitan kudi sannan ya biya masu kudin mota xuwa katsina, da kyar ya yarda ya biya seat biyu wai xai dauketa a kafa, sai da yan motar suka sa baki, bayan kusan minti goma motar ta cika suka dau hanyar katsina, tunda Khadijah take bata taba shiga motar haya ba, rabonta kuma da katsinan tun tana da shekara bakwai da suka je tare da Abbanta, kai kana ganinta kasan she is restless, matar da ke kusa da ita tace “Yarinya me ya faru?” Kamar xata yi kuka tace “Amai….” Kawu ya kwalalo ido yace “Me?” Tace “Amai” dungurinta yyi yace “Ke yarinya ce xaki ce ma mutane kina jin Amai cikin mota” matar tace “Haba bawan Allah, sai yara ke Amai idan suna tafiya” dakatar da ita yyi yace “Ke… Learn to mind ur business while in public, ‘yar ki ko tawa” matar tace “Aa ba yar ka bace wllh, don da yar ka ce baxa ka yi mata abinda kayi mata ba yanxu” Bala’i kawu ya fara kamar mace a motar, ana haka Khadijah ta toshe bakinta jin aman xai taho mata, matar bata bi ta kan kawu ba ta sa driver ya tsaya, ta sauke Khadijah, nan kuwa ta dinga kwara Amai, matar na tsaye kanta, shi ko kawu yana cikin mota sai fada yake yana kumfar baki, kowa ya xuba masa na mujiya bbu wanda yace ci kanka, wani mutumi a motar ya ba matar ruwa ta mika ma Khadijah, ta wanke bakinta da fuska sannan suka dawo cikin motar ana mata sannu, wata mata ta bada leda ta rike a hannu idan ta ji wani aman, har suka isa katsina kawu bai yi shiru ba, Khadijah tayi Amai yyi sau biyar, dunguri kam ta sha sa gun kawu duk da ba a kusa da shi take ba, bbu wanda yace masa ci kanka cikin passenger din motar, a dai dai ta ya samu da xai kai su har gidansa.. Karfe biyu da kusan rabi suka shigo gidan, bungalow ce mai kyau, wanda Abban Khadijah Alhaji Muhd ya mallaka ma yayan nasa a lkcn yana da rai, sai dai ba lallai wanda ke nan lkcn da aka ba Kawu gidan ya yarda Cewar gidan ne a ynxu ba, don yyi mugun tsufa ga dattin bala’i, kuma dudu gidan bai yi shekara shidda ba, Duk matan Alhajin guda biyu suka fito jin shigowar mai gidan nasu suna masa sannu da xuwa, kawu dake kokarin bude jakar kayan Khadijah bayan ya xauna parlor yace “Toh ga ta nan, gida kuma ni da Isiyaka mun rufe an sa a kasuwa, ga ta nan ban san gun warce xata xauna ba cikin ku” Matarsa ta fari Hajiya Salaha tace “Toh ni dai yara sun yi yawa a gu na, ban san dai ko Maimuna ba” warce ta kira da Maimuna tace “Ni kuma sai nace maki yaran basu min yawa ba koh?” Kawu yace “A’a bbu xancen tada jijiyoyin wuya taje dakin ki Maimuna kayanta kuma a kai dakin salaha, shkkn” daga haka ya dinga fiddo da tsadaddun kayan Khadijah, daga shi har matansa bbu mai cewa komai sai kallon ikon Allah suke, Kusan set takwas ya cire ya ajiye gefe yace “Wannan siyar da su xa ayi in sha Allah, domin kuwa baxata xo nan ta dinga saye sayen kaya ba kamar wata er gote ta janyo ayi tunanin shi gareni…” Takalman ma duk ya ware kusan biyar, golds dinta na dankunni da awarwaro kuwa dama suna aljihunsa, Khadijah dake ta tsaye jikin kujera tana waiga ko ina na parlorn da idonta tana neman remote ta kunna TV amma bata gani ba, ganin kawu xai xuba duk kayan da ya ware a wani jaka ta karaso da sauri tace “Kawu ina son wannan takalmin, da shi nake xuwa makaranta” Dungurinta yyi da karfi ya kunduma mata ashar, ta koma baya a tsorace yace “Ki shiga hankalinki da ni fa xan xane ki wllh” xata mike ya fixgota ya cire dankunnin kunnenta, Hajiya Maimuna tace “Toh idan ba fitsara ba ita har xata gaya maka abinda xaka yi” mikewa yyi ya dau jakar yace “Ku shiga da sauran, ni na tafi kasuwa kan yamma yyi” daga haka ya nufi kofa” bayan fitarsa Hajiya salaha ta sake fiddo kayayyakin ta dau kusan kala biyu da panties da kayan bacci, Hajiya Maimuna ma ta jawo jakar ta dau huluna da kaya kala daya da dogon rigar kanti da safunayen hannu da kafa, Hajiya salaha xata sake jawo jakar Hajiya Maimuna ta rike tace “Tsiyace jakar xa ki yi” Hajiya salaha ta jefa mata wani tace “Ke ai arxiki kike karama jakar, abu baxa ayi sa da hankali ba, ita sai ta sa uwar me?” Hajiya Maimuna ta rufe jakar ta tura tana kallon Khadijah dake ta tsaye tana kallonsu tace “Dauka ki kai dakin can dake kusa da wancan kofar, kin wani tsaya ma mutane kememe” Khadijah ta karaso da sauri ta dau jakar ta bi hanyar da Hajiya Maimuna ta nuna mata, kafin ta fito sun dau takalma kala daddaya ta dau jakar takalmin ma ta kai dakin. Uban wanke wanken dake tule gun pampon da aka tanadar don yin wanke wanken Hajiya salaha ta nuna mata taje tayi, a hankali Khadijah tace “Ina jin yinwa” Hajiya salaha tace “Can baki ci abinci bane kafin ki taho, ki je bakin pampon akwai tukunyar taliyar da ta rage ki ci sannan kiyi wanke wanken” Fita khadijah tayi xuwa gun pampon, ta yi kusan minti daya tana kallon taliyar da kudaje ke bi, ta turo baki ta rungume hannayenta, Dawowa parlon tayi kamar xata yi kuka tace “They are flies perching all over the food, ni baxan iya ci ba” sakin baki suka yi gaba daya suna kallonta, can suka kwashe da dariya Hajiya Maimuna tace “Toh baturiyaa jikar mongo park….” Hajiya salaha tace “Kin wuce kin ba mutane waje ko sai na mike.. Ina ruwan ki da k’uda idan ba rainin wayo ba, ki bar abincin kar ki ci, kuma maxa ki tafi ki wanke kwanukan yanxun nan” juyawa khadijah tayi ta bar wajen, Hajiya Maimuna tace “Idan ba ma tsoron Allah ba har Alhaji xai yarda ya rike er Muhammad, uwar me ya tsinana sa yana raye” Khadijah dake ta turo baki ta dau omon da ta gani da sosan wanke, tsaye tayi ta rasa ta inda xata fara wanke wanken, can dai ta dauko babban bahon da ta gani ta tari ruwa ya kusa cika sannan ta xaxxage d’an omon, muryar wata mata da shigowarta gidan kenan taji tana cewa “Ke ya haka, da uban ruwan nan xaki kada kumfa?” Khadijah ta kalleta kamar xata yi kuka tace “Toh ban sani ba” matar ta karaso baki sake, nan ta rage ruwan ta kara mata omon sannan tace “Haka ya isa” parlor matar ta shiga wajen su Hajiya tana cewa “Ku kuma ina kuka samo wancan Ajebon” Karfe kusan hudu da rabi Hajiya Salaha ta fito bayan tafiyar bakuwarta, sakin baki tayi tana kallon Khadijah dake durkushe bakin pampo har lkcn, kwanuka ta ko ina, duk ta hade gumi ta jike kayanta jagab, kai kana ganinta kasan bata taba ba ne, Hajiya ta kwalo ma kishiyarta kira ta fito da sauri, ita ma ta xaro ido tace “Me xan gani ni Maimuna, wanke wanken awa biyu?’ Khadijah dake kallonsu kamar xata yi kuka tace ” plates din sun bushe, ya ki ya fita” Hajiya Maimuna ta rike ha6a tace “Ehh lallai muna da aiki, yanxu tsalelliyar budurwa kamar ki baki iya wanke wanke ba shekara sha uku sa’ar Murjata” Hajiya Salaha da ita ma ta bude baki ta kalli kishiyarta tace “kina da aiki dai, don ba ni aka kawo ma ita ba, mutum yaji da nasa ‘ya yan mana, shima Alhaji wllh, da ba sai ya bar ta gun kishiyar marigayiyar uwarta ba” Juyawa Hajiya Maimuna tayi tace “Toh Allah ya kyauta” daga haka ta shiga ciki, Hajiya salaha ta mata tsawa tace “Tashi mana kan kwanuka yar banxa kawai, ke ga yar masu kudi ko, to xa ki ci kwakwa a gidan nan don bbu shegen da xai dau iskancin ki, kawai kin bi kin ma mutane asarar omo, maxa kuma ki dau tsintsiya ki tattare gaba daya gidan nan idan shima kuma baki iya ba sai in ga” khadijah da ta bata fuska xata yi kuka ta karasa ta dau tsintsiyar da take nuna mata ta fara sharan, takaici ya rufe Hajiya ganin gwara ma ta shekara a tsugunne bakin pampon da wannan sharan da take na yan iska, juyawa tayi ta bar gun daga karshe tana cewa “Xaki san inda kika xo yarinya” da daddare Khadijah na rakube jikin kujera gaba daya hankalinta da soul dinta na kan kallon cartoon da kananun yaran kawu Jibril suka sa a TV, an kirata ya fi sau uku amma inaa, hauri Sajida er Kawu ta biyu ta kai mata tace “Yau naga mayyar kallo ana magana bata ma san ana yi ba” a firgice ta mike sai dai har lkcn idonta na kan TV, Hajiya Maimuna dake lekosu daga kitchen don ita ke kiran khadijar ta xo ta karbi abinci, ta karaso a fusace ta kai mata dundu, firgita ta juyo Hajiya Maimuna ta murda kunnenta tace “Gafara shegen kallon nan xai maki ne hala, ka ji min yar kaza kaza” sunkuyar da kai khadijah tayi kamar xata yi kuka, Hajiya Maimuna ta turata kitchen tace “Ga tuwon ki can a kitchen ki dauka, gayyar tsiya kawai” tafiya kitchen din tayi tana yi tana waiwayo TVn ta dauko tuwon a wata yar roba an ya6a masa miyar kuka koriya shar, sai kallon miyar take kamar idanuwanta xa su fito, ta dawo parlon ta xauna cikin yara dake cin abinci su ma ta ci gaba da kallonta Hajiya Salaha ta shigo parlon tace “Wato kinsan idan mutum ba ayi masa tarbiya ba sai na kallo, kinga saura kadan ta xubar da tuwon tana kallo” da sauri khadijah ta kalli tuwonta taga ba daidai ta ajiye sa ba, Hajiya salaha ta fixgota a fusace ta juyar da ita tana kallon kofar kitchen tace “Duk kika sake juyowa sai na kashe ki” Khadijah dai bata ce komai ba ta kai hannu a hankali cikin tuwon ta mintsili kadan ta kai baki, yamutsa fuska tayi tana hadiyewa da kyar sai kuma ta kalli Er Kawu ta uku mai suna Rabi tace “Anty akwai indomie?” Yarinyar ta fashe da dariya sannan ta gaya ma Uwarta Hajiya Salaha, Hajiyar tace “Ehh akwai wanda ubanta ya kawo mana daga kabari” Khadijah dai bata ce komai ba, haka tayi ta kallon tuwon ta kasa ci, daga karshe haka ta mike ta kai kitchen ganin kowa na kai kwanonsa can, Hajiya Maimuna ta kwalo ma kishiyarta kira ta nuna mata tuwon da ta bari tace “kin dai ga koh? To wllh har in fita girki sai dai yunwa ya kashe yarinyar nan”

    *Haske Writers Association*💡

    07087865788 Contact me here.

    ✨ *Noor-Al-hayat*✨

  • Noor Al Hayat 16

    Noor Al Hayat 16

    Washegari talata Khadijah na ta share tsakar gidan da aka sa ta tayi tun asuba har lkcn bata gama ba Kawu ya fito cikin shiga ta alfarma da daya daga kayan mahaifin Khadijah, matansa sun rakosa xuwa balcony ana yi masa Allah ya tsare hanya, ganin Khadijah da yayi ya juya yana kallon matan nasa yace “Gobe er can ta shirya da safe xa a kai ta makarantar boko” Hajiya Maimuna tace “Wanda su Sumayya ke xuwa?” Wani kallo yyi mata yace “Ke xa ki biya, ko ina naga kudin biyan wannan makarantar, makarantar da yaran Bala ke xuwa xa a kai ta, ina jin ko a Jss2 aka ce take ko one” Khadijah ta mike tace “Aa jss2 nake Abba” Wani shegen kallo yyi mata yace “Kun ga irin rashin tarbiyar ko, kun gani ko, to yanxu wa ya sako bakinta, dama na samu labarin an baki tuwo ki ci jiya da daddare kin ki ci tunda kin taho da abinci daga gidan marigayi Muhd, to wllh xa ku yi aiki hand in hand da yunwa in har baxa ki ci abinda ya sauwwaka ba, baxa ki taho gidana kina min sangarta ba” daga haka ya nufi daya daga motocin dake tsakar gidan, Khadijah ta ci gaba da sharanta na yan koyo da take yi. Throughout haka ta dinga aikin da ba ta iya ba bata taba yi ba a gidan, duk ta gaji amma ko kadan bata ce haka ba sai turo baki da take ta yi, Hajiya Salaha ta kai mata dundu yyi sau biyar daga karshe ta gaji da bin ta tana mata dundun ta kyaleta, Hajiya Maimuna kuwa ta surfa mata xagi ya fi a kirga, duk wnn abun sai dai ta turo baki ko ta bata fuska daga nan kuma shkkn, kunu da kosai a gantale aka bata a cup, ita ma ta ci a gantale ta bar masu abinsu don ba saba ci tayi ba, sai da suka yi baccin rana sannan ta samu tayi sallahn zuhr ta lallaba ta kunna TV ta rage volume ta xauna tana kallo happily, dauke wutan da aka yasa ta turo baki, a hankali ta kwanta nan kasan parlon nan da nan kuma bacci ya dauketa don tun tashin asuba. Ko abincin rana ba a bata ba wai sai yaran gidan sun dawo, basa kuma dawowa sai karfe biyar, suna dawowa kuwa da yamma aka xuba ma kowa shinkafa da wake da mai da yaji da Hajiya Maimuna ta girka, Hajiya Salaha ta sa Sumayya ta xuba ma Khadijah don ita Hajiya Maimuna rantsuwa tayi baxata bata ba, khadijah ta tsura ma shinkafa da waken ido da aka barbada ma yaji, a hankali ta kai hannu ta dinga tsince waken tana ajiyewa a kasa gefenta, Hajiya Maimuna dake ta kallonta ta mike ta karbe kwanon abincin ta kai kitchen ta rufe, abincin da ba ta ci ba kenan har aka yi magrib sannan isha, tana ganin aka ba kowa shinkafa da miyar da Hajiya maimunar tayi amma ban da ita, bayan ta idar da sllh ta samu Sajida dake waya ta duka gefenta a hankali tace “Anty ni ba a ban shinkafar ba” ta mata wani kallo tace “Toh ni na dafa ki samu su Hajiya mana” mikewa tayi ta wuce dakin Hajiya salaha, ta samesu xaune da yaranta ana assignment, kallonta tayi tace “Lafiya??” ta girgixa kai tace “Ni ba a bani abincin ba ina jin yunwa” tsawa tayi mata tace “Fita ki ban waje, ba dai shayi da soyayyen kwai kike jira ba yunwa xai kashe ki gidan nan” a hankali Khadijah ta juya ta fita, ta tafi gun kwanciyarta ta rakube hade da rufe ido tana tuno Ummarta. Washegari kamar jiya da asuba aka tasheta, har gari ya waye tana shara, sai da duk yaran suka wuce makaranta sannan Hajiya maimuna tace idan ta ga dama ta wuce tayi wanka ta shirya, tsaye khadijah tayi a bathroom dake tsakankanin dakunan su Hajiya, soson wankan ta da Abbanta ya siyo mata daga Kasar waje ya xama na kowa da kowa hadda sabulunta mai tsada, ta turo baki ta dau sabulun kadai ta yi wanka da shi ta fito cike da kyankyanin bayin, tun da ta fito parlor Hajiya Salaha ke kallon kayan jikinta, khadijah ta durkusa gefenta a hankali tace “Na gama” tabe baki Hajiya salaha tayi ta nuna mata cup din kunu tace “Gashi can ki dauka, kosan ya kare” Khadijah ta leka cup din da sauri a xaton ta shayi ne, a hankali ta mike ganin ba shi bane ta isa gun cup din kunun ta dauka, Hajiya salaha tace “Ko yau ma baxa ki sha ba” bata ce komai ba ta dinga shan kunun da yyi mata tsami a baki tana d’an yamutsa fuska, sai hararanta Hajiya salaha take tana kwafa, daga karshe kadan ta sha ta ajiye ta mike tace “Na koshi” duk da uban yunwan da take ji cikinta na kugi, Hajiya Salaha tace “Toh ki hutar da kanki tafi ki juye a flask ki hada duk kwanukan ki wanke, kuma ki min irin na ranan in fasa maki jiki da wayar wuta” ita dai khadijah bata ce komai ba ta mike taje yin yanda tace nata. Wani almajirin Kawu ne ya taho kai ta makarantar, shegen nisa ce da makarantar kuma almajirin me suna musa yace da kafa xata dinga xuwa kullum don haka gwara ta dinga kallon hanyar da kyau, tunda suka shiga makarantar Khadijah ke kalle kallen ko ina, don ita dai bai yi mata kama da schl ba, gashi ko plaster ba ayi ba, yaran ma basu da yawa, Musa ya shiga gun wani wanda da alama shugaban wajen ne, ita tana tsaye waje, tana jin mutumin na ce ma musa ai lesson ne wa yaran da basa gane karatu, kuma na shekara daya ne kafin yaro ya shiga boko, musa ya tambayesa nawa ne yace dubu uku da dari biyar, nan take musa ya basa kudin, ita kuma aka kira wata daliba ta kai ta ajin karshe musa ya wuce, su kusan goma ne a ajin, ita dai tunda ta shiga ajin take kallon malamin dake ta koya sentence making, “The boy was tall…” Shine abinda malamin ke ta nanatawa yaran na fadi su ma, khadijah dake ta kallon sa tace “Excuse me, but you said present tense sir?” Malamin yace “Yes” tagumi tayi tace “Sorry but that’s past tense class master” kallon board din yyi da sauri sannan ya kalleta, bai kulata ba ya ci gaba, nan ma kuma sai da ta sake masa gyara, hade rai yyi yana kallonta, can ya basu classwork ya koma ya xauna, sai bayan kusan minti sha biyar ya karba sannan ya fara koyar da Multiplication a board, sai da ya gama tas, sannan ta kai masa gyaransa a littafi tana nuna masa, fita malamin yyi xuwa gun shugabansu, ba a dau lkci ba ya kirata, tana tsaye yace “Ke tunda baki da kunya kar ki sake xuwa makarantar nan daga yau, tunda kin iya abinda ake koyarwa ki xauna a gidan ku ko kuma a kai ki school ga kudin ku” karba tayi tace “Ohk, in tafi yanxu” yace “Tafi” juyawa tayi ta fice daga uncomplete building din, gano gida bai mata wahala ba saboda sharpness dinta, su Hajiya salaha dake xaune parlor suna hira suka saki baki suka ce me kika dawo yi, tace “Ba abinda suka iya fa a wajen, they are just teaching rubbish, ni bana son wajen school nake so, am in jss2” Hajiya maimuna tace “Shine kika dawo” gyada mata kai tayi ta mika mata kudin hannunta, ta tafi jikin kujera ta rakube ta xauna, duk suka bi ta da kallo baki sake. Yunwa sosai take ji amma bata ce komai ba, Kawu ne ya fito a shirye xae fita wajen karfe goma da rabi, ganinta yace “Wannan yarinyar musa bai kai ta makarantar bane” Hajiya salaha tace “Uhn gata nan ya kai ta ta dawo wai bbu abinda suka iya kilan mai tsada take so” ya juya da sauri yana kallonta yace “Me ya dawo da ke?” Tace “Abba they are teaching rubbish there, kuma ina ta correcting dinsa, ban san whether he reported me bane, sai aka kira ni wai in tafi kar in sake dawowa, har da kudin ma an bani na dawo da shi” Kawu ya gyara tsayuwa yana gyada kai yace “Ohhhw haka aka yi kenan, toh kin ma kanki, Alhmdllh Muhd baxae gan ni da ko wani laifi ba don na kai ki makarantar kika gudo, don haka sai kiyi ta xama gidan” daga haka yyi ficewarsa, ita dai bata ce komai ba, Hajiya Maimuna tace “Wato ke isassa kin raina makarantar shine kika je kina ma malaman fitsara ko, uban wa ke da kudin asaran da xai kai ki irin makarantar da ubanki ya sa ki tun farko?” Khadijah dai sai kallonta take, Hajiya Salaha tace “Ni da nace xan fara awaran siyarwa xan dauko mai aiki wllh da Alhaji xai yarda da sai ta dinga kai min can bakin kasuwa, kinga ai ba talla bane wnn, xama waje daya xata yi” Hajiya Maimuna tace “Ae ko da xai yarda nima sai in hada mata da Omon siyarwa na” Hajiya salaha tace “Toh bari ya dawo dai mu ji” suka gama dai hirarsu duk suka shiga dakunansu domin kwanciya suka bar ta ita kadai a parlorn ga yunwa dake dawainiya da ita, da rana yau kam taliya da wake suka girka, gashi ita bata cin wake tun tana karama, Hajiya salaha ta dan yarfa mata a kwano ta bata, kamar xata yi kuka tace “Ni ban iya cin wake ba” Hajiya salaha tayi er dariya ta mayar da abincinta cikin tukunya ta fito kitchen din, sai a sannan khadijah ta fara hawaye don tunda take bata taba jin yunwa irin wannan ba, ita shinkafa da miya take so, tsakar gida ta tafi ta xauna tana share idonta, har wani rawa jikinta yake don yunwa, tashi tayi ta fice gidan gaba daya, ta shiga gidan dake kusa da na kawunta, gidan shigen na kawunta ne, taga wani yaro xaune tsakar gida yana cin tuwo da koren miya, fita tayi da sauri har tana tuntube, gidan dake kusa da wannan ta tura ta ji a kulle, haka na kusa da shi ma, a gida na hudu ta tsaya tana kallon babban gidan don ya fi duk gidan anguwar, tura gate din tayi taji a bude ta shiga tana kallon mai gadin ta gaishesa yace “Wa kike nema?” Ta nuna masa cikin gidan sannan tayi wucewarta, har ta isa balcony kallon karen dake cikin cage a gidan take, ta murda kofa a hankali ta shiga parlorn, tsaye tayi bakin kofar ganin wani matashi da baxai wuce shekara ashirin da shidda ba yana xaune parlorn da plate din abinci a hannunsa idonsa a kan tv, yana kallonta da dan mamaki yace “Wa kike nema” ta kalli abincin hannunsa kamar xata yi kuka a hankali tace “Nobody, I am just hungry” ya buda ido kamar ya ji mugun abu, a hankali tace “Please” ajiye plate din hannunsa yyi yace “Take” ta karaso ciki da sauri ta xauna kan kafarta tana kallon shinkafa da miyar da naman kaza sai coslow dake gefe murya can kasa tace “Thank you” daukan spoon din tayi ta kai abincin baki ta fara ci, ya kafeta da ido irin kallon mamaki, muryar wata dattijuwa taji tace “Who’s this?” Ya juya ya kalleta kafin yace komai Khadijah tace “Good afternoon ma.. I am khadijah” matar ta kasa cewa komai, ta kalli yaronta dake xaune kamar yanda shi ma yake kallonta, Khadijah ta dau kazar abincin tana ci tana kallon matar.

    *Haske writers association*💡

    ✨ *Noor-Al-Hayat*✨