Hausa NovelsNoor Al Hayat Hausa Novel

Noor Al Hayat 25

Sponsored Links

Ranan Monday da asuba Mumy ta shiga kitchen gun kyauta dake ta kokarin hada ma yan makaranta breakfast, cike da ladabi ta gaida Mumy, mumy ta amsa tana mata sannu da aiki sannan tace “Khadijah bata tashi ba?” Kyauta tace “Ina jin tana can tana sallah ne” kyauta ta dai fada haka ne amma in dai khadijah tasan tana can tana bacci, Mumy tace “Wai boko nake son ta fara xuwa yau…” Kyauta ta xaro ido tace “Boko Hajiya, Allah ya saka maki da alkhairi, ya kara daukaka, Allah ya biya maki bukatun ki masu kyau Hajiya, yanda kike taimako kema Allah ya ji k’an ki a nan duniya da ma lahira” Mumy da ke ta kallon kyauta tayi murmushi tace “Toh Ameen” daga haka ta juya ta wuce, kyauta ta rike ha6a baki bude murya can kasa tace “Ko ya baxawara xata dau xancen nan idan ta dawo, Ashe ko akwai karamin yaki a gidan nan” a stairs mumy ta hadu da Aliyu ya shirya xai fita aiki, tace “Da asuban xaka fita aiki?” Yyi kasa da kai ya gaisheta ta amsa tare sa cewa “How was ur nyt?” Yace “Alhmdllh” tace “Breakfast din fa?” Yace “Xan yi a office” tace “Bawan Allah ai bbu xancen yin sammakon fita aiki xaka kai khadijah makaranta anjima” Juyowa yyi ya kalleta da sauri yace “A’a ni Mumy baxan iya xuwa ba, Ba ga sanusi ba da mai aikin can su kai ta mana” kallonsa mumy ta tsaya yi, can tace “Directly ma kake ce min baxa ka iya xuwa ba koh?” Yace “Toh Mumy ni da xan fita aiki kuma wani makaranta xan kai ta, komai fa sanusi xai iya yi kin sani” Mumy bata kuma saurarensa ba tayi wucewarta sama, fuskarsa daure ya juya ya koma sama shi ma. Tun da kyauta ta tada Khadijah tayi mata albishir din xancen da Mumy tayi mata khadijah ke ta murna har da rawanta, can kyauta dake taya ta murnar ita ma ta hade rai tace “Wato ni ce dai hajiya bata so a gidan nan ba arabi ba boko, sai dai in sauke in daura in yi shara inyi wanke wanke, akwai Allah” khadijah da har xata shiga bathroom ta dawo da sauri ta yo waje da ido tace “Anty mai girki? Katuwa da ke baki gama school ba dama, me kika tsaya yi toh?” Kyauta ta dunguri hancinta tace “Ai ban kai baxawara ba da take kamar buhu” Khadijah ta wara ido tace “Ni kinsan yaushe rabon da in je school, to in gaya maki tun ina gidanmu tare da Ummata, Allah ya sa ban girma ba da shikenan yanxu ni ma baxan je ba” bata sake sauraren kyauta ba ta shiga bathroom da sauri ta rufe. Kafin karfe bakwai duk yaran gidan sun shirya kyauta ta tabbatar khadijah ma ta shirya cikin daya daga kayan da ta siyo mata a kasuwa shekaranjiya ta lafta mata uban kwalli a ido, ta shafa mata jan powderta a fuska, Da kyar khadijah ta yarda xata yi breakfast saboda excitement, duk ta kagu su wuce makarantar, shi dai Aliyu na xaune parlor hannunsa rike da mug din coffee, su siyama kuma na dinning suna breakfast, Khadijah kuma na kitchen kyauta ta shimfida mata wani xaninta a kasan tiles din kitchen din don kar kayan jikinta yayi stain, jin Driver na horn a waje Kyauta ta daga khadijah da sauri ta kwace bread din hannunta ta turata waje tana cewa “Shegiya sai ta sa sun canxa ra’ayinsu maxa tafi xa su wuce” Aliyu ya fita ya samu Driver yace “Sanusi ni xan kai su, don’t worry” Har su Siyama sun fita Sanusi ya gaya masu abinda Aliyu yace, Siyama ta tabe baki hade da jingina da motar tace “Shine yana ganin mun fito baxai gaya mana ba, I don’t just like this Ya Aliyu sometimes” Aneesah tace “Ni kuma ina son sa haka, ya ma fi min ya Saleem” Siyama tace “Shi yasa nake ta addu’ar ya saleem su dawo tare da Abba anjima” Motar Aliyu suka nufa, baby da fitowarta kenan ta bi bayansu, Aliyu ya wuce upstairs dakin mumy ya sameta har ta shirya xata kai khadijah makarantar da kanta, ya d’an bude ido yace “Mumy kin fa san I didn’t mean it, ko baki fada ba ai xan kai ta…” Ta katse sa tace “Toh tunda Allah ya ban lafiyata ba gwara in fita in biya ma kai na bukatar dake gabana ba, Saleem will Neva look into my face yace min baxa shi ba ai, so this is just ur differences” Aliyu yayi kasa da murya yace “Toh kiyi hakuri Mumy, ban san ran ki xai baci ba, I am very sorry” tace “Noo ni rai na bai baci ba, kai dai da na bata ma rai xaka iya tafiya aikin ka kayi hakuri, ni da ya xame min dole xan kai ta da kai na” murmushi yayi yace “Don Allah mumy kiyi hakuri ni xan kai ta ba sai kin je ba” da kyar Aliyu ya samu ya lallaba Mumy ta hakura ta bar shi ya kai khadijah makaranta tare da Kanninsa, babu yanda bata yi ya amshi wayarta ya masu transfer din duk fees din a can makarantar ba ya ki yace xai yi da nasa kudin, da haka dai ta hakura ta kyalesa ya sakko parlor rike da makullin motarsa, makale ya tadda Khadijah jikin kofar parlor da alama su siyama dai sun korota ne, Kyauta ma na bakin kofar bayan sanusi yace mata Aliyu ne xai kai su, sai leken su siyama take tana Allah wadaran da halin baxawara da suka yi, tana ganin Aliyu tayi tsit, tayi kasa da kai tace “Sannu da fitowa yallabai” yace “Yauwa” sannan ya fita, tura khadijah tayi ta rufe kofar parlorn. Khadijah ta dinga bin Aliyu har suka isa gun motarsa, su siyama suka yi shiru daga xancen da suke ko wacce na kallonsa, Yace “Wacece ta korata a cikin ku?” Da sauri baby tace “Allah ya so bani bace ba wllh yayanmu” yana kallonta yace “Toh waye?” Nuna masa su Aneesah tayi, yace “Why did u both send her away?” Aneesah tace “Toh yaya kawai ta xo gun mota ta tsaya mu da makaranta xa mu” yace “Ita ma makarantar ae xata” Da sauri siyama tace “What??? Wani makarantar?” Baby tace “Na mu mana, ai Mumy ta gaya min da na yi wanka a dakinta daxu” Siyama da ta rikice tace “Yaya kamar ya makarantar mu, ni yaya ko xa a sa ta makaranta let it not be ours, they are a lot of schools out there don Allah a kai ta” Har da guntun hawayenta, Aneesah ma duk hankalinta ya tashi, ita dai khadijah na daga gefe tana kallonsu, yace “Alryt idan na kai ta makarantar taku kada ku bari ayi admitting dinta” daga haka yace baby ta shiga mota, baby ta shiga gaba ya bude back seat yana kallon khadijah yace “Get in” da sauri ta shiga motar ya rufe ya bude driver seat ya shiga yana kallonsu siyama yace “Ku je sanusi ya kai ku coz xan iya maku abinda ke raina idan ku ka shiga motar nan, mind u kada warce ko da wasa ta sake shiga cikin gidan can, it’s either ku je sanusi ya kai ku makaranta or you remain here till 4” daga haka yayi warming motarsa mai gadi ya bude masa gate ya fice daga gidan, siyama ta fashe da kukan takaici Aneesah na taya ta. Essence int’l school, abinda khadijah ke ta nanatawa kenan a xuciyarta tun shigiwarsu cikin babban makarantar, baby ta bude kofa ta fita, ya juya yana kallon khadijah, xaro ido yyi yana kallon nata idon yace “Meye wnn din a idon ki?” Ta buda hannu tace “Anty mai girki ce ta sa min kwalli” tsaki yyi ya Ciro handkerchief a aljihunsa ya mika mata yace “Common goge wannan bakin abin da ta goga maki a ido kamar herbalist” khadijah ta kyalkyale da dariya ta karba tace “Herbalist kuma” bai tanka ta ba ta shiga share kwallin, jawota yyi ya fixge handkerchief din a hannunta ya fara goge mata idon, sai bata fuska take xata yi kuka, ya hade rai yace “What?” A hankali tace “It’s painful” yace “Good… Next time idan xata sa maki baxa ki yarda ba” ajiye handkerchief din yyi bayan ya tabbatar bbu sauran kwallin a idonta ya fita, ita ma ta fito ya wuce direct office din principal din kasancewar shi ma makarantar da yyi kenan, kuma har lkcn ba a canxa principal ba, da ladabi ya gaisa da principal din da shi ma yyi murnar ganinsa sosai, nan Aliyu ya sanar masa ya xo enrolling khadijah ne, principal din ya tambayi khadijah class din da take xata ce jss2 Aliyu yyi saurin cewa Jss3, xaro ido tayi ta kallesa ya mata wani kallo ya ci gaba da yi ma principal din bayani, farkon abinda principal din ya bukata shine transfer letter daga previous schl dinta, Aliyu ya d’an yi jim, can yace masa xai karbo ya kawo, da yake principal din ya san shi yasan family dinsu bai masa gardama ba, nan kuma yasa aka yi interviewing dinta, babu bata lkci kuma aka yarda a sa jss3 din coz she is capable, a take Aliyu yyi transfer din school fees da other fees da ake biya na makarantar har takardu da uniforms guda uku, Principal na kallonta xai cike mata receipt yace “What’s ur name” kafin Khadijah tace komai Aliyu yace “Khadijatul Iman” Khadijah ta xaro ido tana kallonsa, principal din yace “Surname” sai a sannan Aliyu ya kalleta, ta langwabar da kai a hankali tace “Muhammad” principal din ya so aliyu ya maida ta gida gobe tayi resuming yace A’a ta fara yau din shi aiki xai wuce ba gida ba, a tare suka fito da Khadijah office din principal din bayan yace Aliyu ya nuna mata ajinta, Tana biye da shi a baya ya juya yana kallonta yace “Wani makarantar kika yi primary da jss1?” Tace “Yan dutse” yace “Kano?” Ta gyada masa kai, bai sake cewa komai ba har ya isa class dinsu Baby ya nuna mata ta shiga tana daga masu hannu, ya juya ya tafi gun da ya bar motarsa. Karfe hudu saura driver ya ajiye su a gida, sai da su siyama dake ta kumburi cikin motar suka fita sannan khadijah ta fito rike da ledan uniforms dinta da takardu, Baby ma ta fito rike da sauran takardun khadijah, Duk sai da kyauta ta bi ta yi ma uniforms din tsirara daga ledansu tana washe baki tace “Yarinya ta xama yar boko, toh me suka koya maku yau a makarantar” Khadijah tayi dariya tana cire kayan jikinta tace “anty mai girki yanxu xan yi wanka ne, idan na fito xan koya maki” daga haka ta shiga bathroom da sauri, har daki kyauta ta kawo mata abinci bayan ta xuba ma su siyama nasu a dinning, khadijah dake ta kallon pepper soups kala kusan uku da ta xubo mata tace “anty mai girki, kinyi girki da yawa kenan yau?” Kyauta tace “Ke Alhaji da kanin Aliyu xa su dawo anjima, yanxu haka suna can cikin jirgi a sararin samaniya, ai girkin da nayi ya fi kala shidda yau tun safe nake kitchen, na kuma ji Hajiya nacewa kila baxawara ma ta dawo yau” Khadijah ta tallabi cin dinta tace “Waye Alhaji anty mai girki?” Kyauta ta hade rai tace “Babansu Aliyu mana” Khadijah ta xaro ido da mamaki tace “Dama yana da baba, ai na xata shine baban gidan” Kyauta tayi tsaki tace “Dadina dake shegen shirme, toh an ce maki shi ya haifi kansa, ubansa nace maki xai dawo anjima tare da kanin sa saleem” Khadijah ta turo baki tana d’and’ana naman ragon gabanta tace “Toh naji” Baby ce ta shigo dakin bayan Khadijah ta gama cin abinci kyauta ta fita da plates din, baby tace “Mumyna tace in kira ki” Mikewa Khadijah tayi ta bi bayanta suka wuce sama, tun bayan da Anty khadijah ta koreta sai ranan ta sake hawa saman gidan, baby ta bude kofar dakin mumy ta shiga, khadijah ta tsaya daga bakin kofa tana lekan dakin, Mumy da ta hangota tace “Shigo khadijah” khadijah ta shiga ta xauna kasa tace “Ina yini Anty” mumy tace “Lafiya lau, ya school din” Khadijah tayi murmushi tace “I like it Anty” Mumy tace “Sun baki uniform?” Khadijah ta gyada mata kai, Baby tace “Mumy same class fa muke da ita” Mumy tace “That’s good, ina books din da suka baki” mikewa Khadijah tayi da sauri ta ce “Xan dauko” daga haka ta koma kasa ta dauko books din ta ajiye ma Mumy, Mumy na kallon book din ganin Iman a jiki tace “Iman? Is that ur name?” Khadijah tayi murmushi ta gyada mata kai a hankali, mumy tace “Maa sha Allah” wani sabon jaka da bakin cover shoe da socks uku mumy ta dauko ta mika ma khadijah tace “Gashi sai ki xuba books din ciki” khadijah ta wara ido tace “Anty nagode, thank you” Mumy tace “Welcm, tashi ki tafi” mikewa khadijah tayi cike da murna ta fita, baby dake kallon mumynta tace “Mumy ni yaushe xa ki siya min sabon jaka?” Mumy tace “Soon” har kitchen Khadijah ta kai ma kyauta abinda mumy ta bata, kyauta ta amshe tana washe hakora tace “Allahu Akbar barin baxawara gidan nan ya maki rana dije, Allah ya makaleta a duk inda take har Hajiya ta gama dake ta dawo kai na nima” Shigowar Aneesah kitchen din yasa Kyauta tayi shiru sum sum ta fita don kai kayan daki Khadijah na biye da ita a baya. Suna shiga dakin ko minti biyar ba ayi ba aka kwankwasa kofa kyauta ta tashi da sauri ta bude, Aliyu ne tsaye rike da wani jakar mai kyau ya mika ma kyauta yace “Gashi ki bata” kyauta ta risina ta karba tace “Toh ta gode, Allah saka da alkhairi” bai ce komai ba ya juya ya bar wajen, kyauta ta bude jakar jin da nauyi ta ga takalma har biyu da safa uku a ciki sai water bottle irin nasu baby, kyauta ta rike haba tace “Ni dai ce ba a so a gidan nan wllh” Khadijah dake jera books dinta a jakar da mumy ta bata ta taso da sauri tace “Anty mai girki menene” Kyauta ta dungura mata tace “Duk kin fi ni goshi wllh” Khadijah ta kyalkyale da dariya ta karbi jakar da a gabansa aka rubuta *Iman* ta wara ido tace “Waowww”

Back to top button