A Rubuce Take Book 2Hausa Novels

A Rubuce Take Book 2 Page 40

Sponsored Links

Part 02

Page 40

Jikinta yana rawa ta lalubi layin muneera don jin me widad ta haifa

“innalillahi,na shiga uku” shine abinda hafsat ta samu kanta da fada bayan muneera ta tabbatar mata twins ta haifa kuma dukka maza,ta dinga safa da marwa cikin falonta kamar wata zautacciya,kamar kuma wadda ciwon naquda ya sameta,kuka takeyi wurjanjan,tana tsinewa widad a zuciyarta,yarinyar ta gama cutarta,cuta tahar abada,ta gama da rayuwarta gaba daya,haihuwa?,haihuwa tayi?,haihuwar kuma ta yara maza ma?,sai yaushe zata iya ruguza dukkan wannan ginin da widad tayi?,yaushe haqarta zai cimma ruwa?,rayuwa na qara tafiya,tana saqa widad din tana warware mata tana dawo da komai baya,ta gaji da wannan jiran gawon shanun,sai ta kira habiba ta fashe mata da kuka me cin rai ta fara gaya mata.

Ajiyar zuciya ta sauke

“Abinda nakeso dake kiyi haquri kawai,ko kowa ya kasa yi miki komai boka bagwaare ina mai imanin zai miki komai(wa’iyazubillah),saura wata daya kacal aikinka ya kammala,wallahi kinji na rantse miki,ko hajiya dake kabari inda zata dawo duniya tace masa yayi kaza wallahi wallahi naki zai dauka,kudade kika kashe bana wasa ba kin manta?, fiye da rabin jarinki kika bayar,ta yaya zan bari asara ta hauki?” Bayanan habiba sun sanyaya mata rai qwarai sun bata kuma qwarin gwiwa

“Kedai abinda nakeso dake,kici gaba da lallabawa,ki sake ayi komai dake,yadda kome zaizo zaizo da sauqi”

“Anya zan iya kuwa habiba?, zuciyata bata da wannan qwarin gwiwar”

“Ke matsalata dake kenan, kwata kwata baki iya cinye jarabarki ba,wannan karon kuwa dole kiyi haka ko don amfanin kanki”

“Zan jarraba in sha Allah”.

Wunin ranar haka ya yishi babu wata walwala ko jin dadi,ranta a mugun quntace,a zuciyarta tanata fatan taji wani mummunan abu ya samu yaran kowa ya huta,duk bayan mintuna saita tsine musu su da uwarsu,amma cikin ikon Allah lafiya sumul widad ita da jariranta.

Wannan karon ummu ce ta kashe kunya da kanta ta yiwo tattaki katsina,gidan widad din sai ya kasance kullum cikin jama’a yake abokan aikin abbas na nan katsinan,gashi kuma a gida take,garin ummanta,dangi tako ina barkowa suke barka ,haka daga kanon ma,wasu na zuwa barka,wasu kuma sai ranar suna sannan zasu iso,yara dai sunyo goshi sosai kamar affan,kowa yasan yadda twins suke da farinjini daman,widad din taga gata tako ina.

Ko yaushe suna waya da abbas din da yakejin kamar yayi tsuntsuwa ya dawo,an katse masa hanzarinsa sosai,don bai gama kallon yaransa,iya kallo guda dayan da yayi musu qaunarsu sosai yakeji cikin rayuwarsa da ruhinsa.

Komai ya sakar musu dai dai bakin samunsa,don yanzu babu abinda zaice da Allah sai godiya,hatta da hafsat da yara bai barta ba,sai daya gwangwajesu da dinkunan fitar suna na alfarma har kala uku,ta kalli kayan taja mugun tsaki ta nadesu a waje daya,wannan karon kam koda ba’a ce mata ba tabbas zataje suna,zataje kallon sunan widad na qarshe a gidan abbas din,zata je kuma ko don ta sake ganin yadda zata qara sawa bokanta ya qara tsanantawa da aikinsa.

_batasan tuni qaddara tayi mata nata tanadin ba,tanadin da tabbas da tana da masaniya a kansa……da babu abinda zai kaita garin katsina_

_hukuncin Allah,da kaf dube duben bokayen nata basu iso suka gano shi ba,hukuncin Allah TALALA mai kamar sake,lallai qaddarar kowanne nawa A RUBUCE TAKE_

Ana ya gobe suna gidan widad din ya qara cika sosai da jama’a,ba laifi gidan yana da nashi girman,don haka kowa ya samu masauki da wajen zama,duk da dakuna biyu ne,nata dana baqi wanda aminatu ke ciki don na abbas a rufe yake,sai wasu dakunan guda biyu da toilet ta baya.

A ranar widad ta gama komai,gyaran kai kawai ya rage mata,tayi wani mugun kyau na fitar hankali saboda yadda jegon ya fara karbarta tun a sannan,da safiyar ranar sukayi waya da abbas din yace ta bari sai azahar taje gyaran gashin,abun mamaki zuwa azahar din taji wayarsa,yace ta fito qofar gida ya miqata.

Na’eema da marwa ta dauka, kowacce ta dauki baby daya suka fito,tayi kyau cikin maroon din abaya, fuskarta tamkar madubi.

Tunda ta fito ya zuba mata ido yana kallonta ta madubi,ya lunshe ido sannan ya bude,yana tuna muryarta lokacin da take naquda,addu’o’i da salati kadai ke fita a bakinta cikin wani hali,ya sake gasgata lallai haihuwa ba wasa bace,duk dan a baibi uwarsa ba ba shakka ya tabe,hakanan duk namijin da bai girmama matarsa ba kodon darajar yaransu lallai ya cika abun zargi.

Buda motar tayi ta shigo,suka hada ido ta saki murmushi

“Amma fa ka shammaceni,shine baka gayamin zaka dawo yau ba?”

“Bakiji dadi ba da kika ganni kenan?” Shagwabe masa tayi

“Sosai ma uncle, Surprise fa kayimin”

“Good me jego” a ladabce ta gaidashi,sannan suka gaisa dasu marwa da suka zama ‘yammata suma,ya tayar da motar yana tambayarta

“To yaya?,meye labari?, Ya akaji da jama’a yan suna?,hope komai dai lafiya ko?”.

Qasa qasa suke hirarsu cike da wani irin kulawa da juna,kosu marwa dake baya basajin me suke fada kamar masu rada,abinda yayi matuqat burgesu ya kuma tafi dasu,don basu taba ganin irin wannan soyayyar tsakanin miji da mata ba,sunfi ganinta ga saurayi da budurwa,amma yau anty widad da uncle abbas din sun karya musu record.

A saloon din ya ajjiyeta sannan yace

“Zanje na karbo dinkina gaba da nan,idan na tashi dawowa sai na daukeku mu wuce”

“Tom,godiya nake sosai,Allah ya qara girma” ta fada tana dunqule hannu cikin salon jinjina da kuma rusunawa, murmushi ya balle masa,tana bala’in respect dinsa,ko meye zai hadasu bata kasa ganin wannan girman nasa.

Yana ci gaba da tuqi yana murmushi,halaye da dabi’un widad din yaketa tariyowa,tun daga aurensu kawo yau,tana da sauqin kai da dadin mu’amala over,bata da fushi ko tsaurara abu indai ba bango taje ba.

Ya isa ya samu tailor din ya masa halinsu,don a sannan yake qarashe hade dinkin,yana ganinsa ya rude

“Sir…..ayimin afuwa yallabai,tuba nake” sai ya jawo stool ya bashi

“Yanzun nan za’a kammala sir” bai zauna ba,yadai harde hannayensa a qirji yana dubansa

“Kome zakayi ka dinga qoqarin cika alqawari,shine cikar kamalar mutum,sannan sana’arka,duk yadda ka riqeta haka take zamar maka”

“In sha Allah sir” yaci gaba da qoqarin hada masa kayan

“Ka zauna mana sir” ya sake masa tayin zama

“Karka damu,qarasa aikinka” ya fada a nutse,don shi bayajin tsaiwa duba da yanayin aikinsa.

Wayarsa ce dake aljihun trouser dinsa ta dauki ruri,ya saka hannu a hankali yana qoqarin cirota,yana duba me kiran kiran ya katse,saiya fara qoqarin kira sai gashi an sake kiransa.

Hafsat ce,ya daga wayar a nutse ya kara a kunnensa

“Kana ta wajen ina?,gamu a park kazo ka daukemu” ta fadi kanta tsaye cikin son nunawa wadanda take tare dasu lallai har yanzu itace da gwamnati,fiye da rabinsu jama’ar widad ne ta fahimci haka ta yadda suketa hirarta da fadan alkhairinta tun a mota,hakan ya sake hassala zuciyarta da wani mugun bacin rai.

Cikin mamaki yace

“Me ya biyo dake titi bayan na tura kudin ticket a siya muku keda yara,yanzun haka fahad inajin yana airport yana jiran saukarkuya dauko ku” baki ta tura gaba hadi da tura dankwalinta ma,haka kawai ga mota tana gani sai ta bari ayi asarar kudin a wani siya musu ticket,kudi ba dubu biyar ba ba goma ba

“Kawai haka nafiso,na karba kudin ticket din nayi saving mayi wani abun dashi” yadda take masa magana a tsaitsaye yadan bashi mamaki,don tunda tayi kome ta danyi laushi

“Okay,to yanzu haka ina cikin wani uzuri,ki kira fahad din ki kwatanta masa inda kuke sai ya daukoku” daga haka ya datse wayarsa shima.

Sai yaushe zata bar son kudi?,yaushe zai saka doka ta daina karya masa kanta tsaye?.

Sakato tayi da wayar a hannu,ranta yana mugun baci,batakai yabar duk abinda yakeyi ba kenan saboda ita yazo ya daukesu?,cikin wannan bacin ran ta kira fahad ta gaya masa inda suke din,wanda saboda dan nisan dake tsakanin airport din da station din sai daya dan dauki lokaci,sauran wadanda basuga amfanin abinda tayi din ba sukace tunda ba abun hawa na haya available na zasu tsaya wani jira ba sai kawai suka dauki taxi drop suka wuce suka barta ita da su baaba hassana ‘yan kanzaginta,sai da suka jima da wucewa sannan fahad ya iso,tayita masa bala’i amma yayi biris da ita bai kulata ba tunda ya riga yasan hali.

Sai da aka gama hada masa dinkin sannan ya dawo ya dauki su widad,tuntuni an gama suna zaman jiransa ne ma

“Ba komai,tunda dai ya gama alhmdlh” abinda tace dashi kenan sanda yake bata labarin abinda ya tsaidashi,shi kansa baiji dadi ba,don shima yana da baqi daga wasu garuruwan da sukazo masa saboda yana sanya ran zaiyi walima a goben kamar yadda ya saba kowacce haihuwa,haihuwar affan ce kawai bai samu yayi ba.

Tunda suka isa gidan tana farfajiyar gidan a zaune ta kasa shiga ciki,kowa saidai yazo ya wuceta,tun a sannan hidimar da akeyi da yadda taga gidan ya fara tara jama’a ya tsaya mata a rai,kowa yana ciki yana huce gajiya harda su mimi,amma baqin kishi ya hanata sakat.

Sanda motar abbas din ta shigo harabar gidan idanunta akai,baqin glass ne,bata lura da waye da waye a wajen a ciki ba sai da suka bude,su marwa suka fara fitowa sabe da yaran dake cikin wani lallausan blue din abun daukan yaran suka nufi cikin gidan,ta qurawa motar ido tanason ganin wadda zata fito,sai bayan kusan minti uku sannan widad din ta fito tana murmushi,da alama wata maganar sukayi da abbas din data bata dariya.

“Kan abu ta kazar uba” hafsat ta fada cikin ranta,zuciya tayi mugun dibarta,batasan sanda ta isa gaban motar ba side din da abbas din ke zaune cikin wani mugun fushi

“Ai dama odan bakayi haka ba ba kaine abbas ba,idan bakayi haka kai din ba namiji bane,dan kunama…..tabarmar qashi RIGAR K’AYA” ta da cikin madaukakin sautin da yaja hankalin mutanen cikin gida da sauran na farfajiyar wajen,ganin yadda hankula ke dawowa kansu bai saka ta fasa magana ba

“Ni dana taho daga wata uwa duniya ka zubeni a station ka kasa zuwa daukata,amma ka dauki ‘yar gwal da danyen jego a gaban mota kana yawo da ita,kabi ka tattare a gindinta ita da danginta,kana musu wahala kana musu bauta……wallahi sai Allah yayi mana hisabi ni da…….”.

Tsawar daya daka mata ta yanke sauran maganar,yayi wata irin fitowa daga cikin motar,Allah ya kissimawa widad ba za’a kwasheta da kyau ba,cikin gaggawa ta shiga tsakani ta dora hannayenta kan qirjinsa tanason yaja baya,ta tabbatar gamuwarsu da hafsat din ba zata taba kyau ba,batason kuma zuciyar nan data taso masa ta sanya ya biye mata ga mutane a wajen.

‘yan uwan abbas dake kusa ne suketa yima hafsat fada suna janyeta,ana tsaka da haka kiran dan auta a dakinsu baban abbas din ya shigo yana shaida masa sun bata kwatancen masaukinsu,sai ya kashe wayar yana huci ya juya ya koma cikin motar ya figeta ya fice daga gidan.

Iska me zafi widad ta furzar,tabi hafsat da kallo wadda aka janyeta can bayan gidan

“Barin hali sai mutuwa”ta fada tana mamakin halin halin tantagaryar hauka irin na hafsat din.

Ranar gaba daya a birkice hafsat din ta yini,donma ‘yan kanzaginta suna dannarta,da qyar takai ga shigowa falon,saidai gaba daya a hargitse take.

A yanzun widad din tafi qarfin raini,kuma tafi qarfin ta keta idanunta ta gaya mata maganar banza,uwa uba kuma tana tsakiyar danginta da hafsat din bataga alamun daukan raini ko wargi daga wajensu ba,haka ta yini har dare a falon tana qunsar takaici,saidai idan abun ya qume mata da yawa ta fita ta matse hawaye ta dawo.

Har tayi shirin kwanciya abbas din ya shigo,har yanzu fuskarsa babu walwala,ta kalleshi cikin langabar da kai a shagwabe tace

“Angon qarni babu fara’a, gaskiya ba kanta,abunma ko kyau baiyi maka ba” dole ta sakashi dariya,sannan ta gyara zamanta

“Kaci gaba da haquri uncle don Allah”

“Wanne haqurin?,haqurina ai ya gama qarewa……akwai abinda kuke buqata?,zan tafi masauki wajen baqi na” kai ta girgiza,don babu ce kawai basu da ita,ya tsugunna yayi kissing yaransa duka,harsu mimi da tasa aka debo mata suka kwanta gaba daya su bakwai kenan harda ita,da yake gadon babba ne ba wanda ya matsi wani.

Har ya fita tana juya abun a ranta, zuciyarta duka ba dadi,batason bacin ran nan nasa,fatanta ko yaushe mummyn mimi ta gyara halinta ko zai samu nutsuwa.

Dakin da su gwaggwo mero suka sauka ya leqa don ya musu sallama,baima san hafsat din tana cikinsu ba sai daya shiga,ya gama yi musu sallama ya miqe ya fice,sai hafsat din tayi zumbur ta dauki jakarta ta biyo bayansa.

A tsakiyar falon ta cimmasa,tana riqe da qugunta,zuciya kuma na ingizata tace

“Muje masaukin tare,acan nima zan kwana” wani banzan kallo ya watsa mata,yaja mata tsaki yayi gaba,saita sha gabansa cikin kuka

“Wallahi na gaji da wanna wulaqancin da kakemin,kamar nima ba matarka bace,yau saidai duk abinda zaka yimin ka yimin,na gaji da wannan rashin adalcin” sosai zuciya ya ciyoshi,ya finciki jakar hannunta yayi wurgi da ita sai gata a bakin qofa

“Na fiki gajiya,na gaji dake gaba dayanki,kije na sakeki saki daya,badai shikenan ba?” Wutace ta kawo mata ta kuma dauke mata a take,saita aza hannu aka ta kurma wata uwar kururuwa data zama tamkar shele ga dukkan wani me rai da yake gidan,shelar tata kuwa ta iske kowa,take falon ya fara karbar jama’a dake cikin gidan banda na harabar gidan da kunnuwansu baije wajen ba,a lokacin abbas ya jima da ficewa daga gidan yana jin kamar an zare masa qaya.

Faduwa tayi tahau tirje tirje a wajen, gwaggwo hassana ce ta riqeta tana kiran sunan Allah kafin sauran su tayata riqe hafsat,tanata abu kamar wadda ke shirin hawa bori ko kuma tayar da iskoki

“Ku cikani,ai kuna gani,a gabanku ya sakeni,saki uku kenan yayimin,saki uku kenan fa”.
*H U G U M A*
*Arewabooks:Huguma*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Back to top button