Gidan Aunty book 2Hausa Novels

Gidan Aunty book 2 Page 2

Sponsored Links

BOOK 2

Page 2

NIAMEY , NIGER

Cikin wani madaidaicin gida motar da tahee take ciki aka bud’e gate, Daidai madaidaicin harabar wajan da mota zata iya tsayuwa akai packing. Matar ce ta fara fitowa ganin tahee bata motsa daga inda take bane Yasa matar ru’ko hannunta suka fito tare, babu kowa a wajan har matar ta bud’e kofar falonta suka shiga ciki ita da Tahee, cikin sakin murmushi ta kalli Tahee” kiji rani ba dad’ewa zanyi ba kinji”, ta fad’a tana kallan Tahee da kwata kwata batasan me take ba,”Kara maimaita mata matar tayi tare da nufar cikin bedroom d’inta har da saka key, da sauri tayi dialing wata number da bugu biyu aka d‘aga kiran cikin ‘kasa ‘kasa da murya ta soma magana “ kuna ina? “ banji amsar da aka bata ba saima ‘kara ‘kasa ‘kasa da murya da tayi “ Nasamo babban kaya yanxu, nasan ‘kungiya ba ‘karamun jinjina mun zasuyi ba sabida yadda suke bukatar akawo musu kayan na samu, yanxu haka tana falan gida na , zan yi ‘ko’karin duk yadda zanyi na ajjeta agidan nan zuwa gobe ,” banji me aka ce mata ba sai ma jinjina kai da tayi “ idan hakan zai samu babu matsala , amma kunsan mutane da sa ido kuma saura kwana 4 ayanka mutane goma da ake bu’kata , yanxu me muke jira tunda na samo cikin ta gomar?”shiru tayi tana sauraran abunda ake ce mata , cikin ‘kara ‘kasa da murya ta furta “ ba matsala ku hanzarta, na barta a falo karta ji ni shiru “, tana kai ‘karshen zancenta ta kashe wayan tana sakin murmushin farinciki, abayyane ta furta “ Tsuntsu daga sama gash she , fridge d’in d’akin ta bude tare da d’akko wani exotic me shegen sanyi, hand bag d’inta ta bude ta ciro wani allura , a cikin lemon tayi wa allura kafun ta ‘kara jijjiga lemon, fuskarta ta daidaita tare da fitowa daga d’akin.gaban tane ya fad’i bata san lokacin da ta yar da leman hannunta ba , duk da girman da jikinta yayi mata hakan be Haka ta yin gudu ba , ban d’akin falon ta duba wayan babu Tahee babu alamarta, da sauri ta fito harabar gidan nan ma babu kowa gashi bame fadi ne da itaba ballantana ta tanbayeshi, wayarta da ta soma ‘kara ce ta d’auka sai faman hard’a gumi take , bata jira me za a ceba tayi saurin bud’e kofar gidan ta , motar data gani ta nufa cikin Sauri, ba kowa bane face su wizi da ke cikin motar kowa kagani fuskarsa a cin kushe tun lokacin da suka nemi Tahee suka rasa , zu’kar sigari wizi yayi kafun ya furta “ Hajiya ina kayan suke , kinsan fa gobe za a fitar dasu “, a rud’e hajiyar ta soma duban hanya “ wizi ta gudu, ta gudu kuyi Sauri ku dubata nasan batayi ni saba “, cikin matsiyacin gudu driver ciki ya tada mota suka soma duba layin ko zasu ganta.

Adaidai lokacin da suke nemanta ,ita kuma ta dad’e da yin nisa hawaye sai faman sakko mata yake akan fuskarta , ita kadai sai faman tafiya take ga duhu da ya somayi sosai , hannunta d’aya dafe da cikinta. Wasu manyan ba’ka’ken motoci ne guda uku Suka wuce , sai kuma ta dawo Daidai inda take sukai parking, wasu kamilallun mata da mijine suka fito cikin motar dattawa dasu, sai masu tsaran lapiyar su dattijuwar matarce ta matso inda take tahee take ,
“ baiwar Allah ya naganki, akan titi ke d’aya sai faman kuka kike “ shiru tahee bata ce mata komai ba sai tafiyarta data somayi, dattijan mutuminne ya saki murmushi kad’an , “ ai bazata baki amsa ba “, da mamaki matarsa ta kallesa , shima kallan nata yayi yana jinjina mata kai alamar Hakane abunda yace kafin ya duba agogan hannunsa , “ dare yayi sosai mu tafi da ita gida , insha Allah ko zuwa gobene sai asan abunyi amma barinta anan zai zama illa agareta da abunda yake cikinta “, cikin gamsuwa matar ta jinjina masa kai kafin ta kama hannun tahee da ke kokarin tafiya suka tada motar sai unguwar Francophone dake cikin Niamey , sosai babbar unguwace da ta tara manyan mutane sabida gidajen da suke wajan ya isa ya tabbatar wa mutum haka , wani soja ne ya bud’e musu babban gate d’in gidan Daidai parking lot motocin sukai parking, cikin dattako matar nan tafito hannun ta d’aya rike da na Tahee da har yanxu bata dena hawayeva, matar ta juya daniyar nufar part d’inta da Tahee amma mutumin ya hanata, cikin kamilalliyar muryarsa ya nuna mata wani part “ ki kaita d’akin maganina “, toh kawai tace masa tare da nufar wani madaidaicin flat, dattijan nan na biye a bayanta , duk yadda akai da tahee akan tashiga kin shiga tayi saima ihun da ta fara yi a gigice da Sauri matar ta damki hannunta ta shigar da ita, kafun tayi wani motsi Tahee ta saka ihu tana neman hanyar fita , “jeki kira mun Isma’il, bai jira amsarta ba ya kunna wani hayaki da yasaka Tahee zubewa ‘kasa tana sakin nunfarfashi kamar ranta zai cire , cikin kankanin lokacin wani farin magidancin buzu yashigo d’akin bakinsa d’auke da sallah, yana ganin Tahee zuciyar sa ta buga , wani irin yanayi na taso masa , danne wa kawai yayi kafin ya ‘karasa wajan mutumin “ baba Malam Ance kana ne mana “gyada masa kai tayi tare da nuna masa wasu turaruka “ su zaka had’a” cike da girmamawa kuwa ya had’a turarukan da ya cika d’akin da hayaki har wani irin rawa jikin tahee ya soma bata soma zabure zabure sai lokacin da aka saka karatun Alkurani, ‘kara ta somayi kamar me aljanu cikin wani irin murya ta soma magana “ ku tsaya, ku tsaya karku ‘konani , ku tsaya “, basu tsaya d’Inba sai ma wani magani da isma’il Yasaka ,cikin shakewa ta cigaba da magana “ ku tsaya , ku tsaya “, cikin tsawa baba Malam ya furta “wanene ya aikoku, me yasa kuka shiga jikinta”, shiru Tahee tayi , suma su baba malam karatun suka cigaba tayi saurin da katar dasu “ Munshigq jikinta sabida muzubar mata da cikin jikinta ne , mu hanata zaman lapiya “, a kan me ? Baba Malam ya tanbaya “ cika aikine kawai namu bama tanbayar dalili”, murmushi baba Malam ya saki “ tafiyarta kuma fa “, nan ma kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta bud’e bakinta “ wannan ba mu mukayishiba wacce tayi mata asirin ce ta binne da kanta ,”Menene illarsa “bama fadar…..”, be karasa ba baba Malam ya daka matsa tsawa tare da cigaba da karatun sai da ya tabbatar ya jigata kafin ya soma amsa masa tanbayoyinsa “ bazata taba zama a kusa da kasar da take ba Sabida asirin da akai mata “, yanxu ina umartarka daka fita daga cikin ta yanxu, idan ba haka ba zan ‘kona’ka da ayoyin Allah”,gardama yasoyi Baba Malam ya soma karatun alkuraninsa hankali kwance shi kuma alhaji isma’il yana kara saka turaran wutar maganin ? Cikin azaba ya furta zan fita , zan fita “, sharesa baba Malam yayi sai da ya saka karar azaba Sabida yanda jikinsa ya soma konewa “ zan fita , zan fita “. Yana kai karshen zancansa sai Tahee ta soma atishawa, sai da tayi atishawa kusan sau uku kafin bacci ya d’auketa a Wajan , kallan tahee alhaji isma’il yayi abu na fad’o masa arai amma yayi kokarin kawar da hakan lokaci zuwa lokaci yana kallan fuskarta , take a wajan tahee ta shiga ransa .

Gyaran murya baba Malam yayi, dare yayi sosai ya kamata muje mu kwanta , kallan wajan da tahee take Alhaji isma’il yayi, shima baba Malam ita d’in ya kalla kafun ya saki murmushin sa na dattako “ su Ameerah zasu kwana da ita , zuwa safe sai muga abunda Allah zaiyi”, cikin gamsuwa Alhaji isma’il yayi wa baba Malam sallama , shima baba Malam wasu yan mata ya kira a waya suka canzawa Tahee d’aki.

 

NIGERIA

WASHE GARI

Haryanxu babu irin neman da ba a yiwa Tahee ba amma babu ita babu alamarta atta ma’kotan da suke kusa da Lagos sai da Abeey ysa aka bincika , sosai abeey ya saka kud’i akan neman Tahee babu inda ba a dubaba ba’a sametaba, hatta airports sai da aka bincika amma batanan . A ‘bangaran king ma har lokacin be farka ba yana cikin coma abunda ya ‘kara tayar da hankalin mutanan gidan , tsakanin mahma da ummey kuwa sai aka rasa wanene yafi kula da king , dan a wannan karan ummey kunya ta cire ta dunga kula da d’an ta , momy taji dad’in abinda ummey sukeyi sabida wani dalili nata , kusan suma a asibitin suke yini, su sumayya ma ko wa kagani zakaga irin damuwar dake kan fuskarsu, kabeer da haroon ma kusan suke kula da gidan yanxu . Sosai hakan ya ‘kara ba’kanta ran Ammey da har zazzabi saida tayi, atunanin mutanan gidan Sabida halin da king ya shiga ne da kuma ‘batan tahee , amma a zahiri sam ba hakan bane , tsantsan bacin rai ne da bakin cikin bata ‘karasa hallaka king ba gashi babu damar hakan sabida yadda mahma da ummey suka tsaya akansa ga dada da kullum cikin rubuto masa rubutu take ana shafa masa , Hakan kuma ba ‘karamin barazana bace a gareta.

????

UNITED KINGDOM

Momy zaune cikin akan kujera jikinta sanye da Abaya da yayi mugun yi mata kyau, Mimi ce ta zakka a guje daga kan steps tare da d’anewa jikin momy har saida ta tsorata , cikin fad’a momy ta tureta “Mimi meke damunki, baki da hankali ne Yaushe zaki dena jin magana ? Ban hanaki wannan guje gujen ba ? “, a shagwa’be Mimi ta turo bakinta “ Haba momy , rungumeki fa kawai nayi amma duk kin tsorata “,’karamin tsaki Momy taja “ banga lokacin da zakiyi hankali ba Mimi , bari ya yanki ya dawo, aure zan sa ayi miki da driver ko kinyi hankali “, a zabure Mimi ta mike tsaye tana bubbuga ‘kafa fuwanta “Haba , Haba momy wai me yasa ni kike mun haka kullum, gaskiya ni yanxu ba ‘kyaso na bari dady ya dawo , ni bansan me nayi miki Haka ba sai kace ….”, bata ‘karasa maganar taba sabida tsawar da aka daka mata , da Sauri ta juyo tana kallan Wanda yayi tsawar a tsorace , kyakkyawar guy ne fari tas dashi kamar ka tabasa Jini ya fita , kyakkyawane shi sosai , kyawawan idanuwansa yabi fuskar Mimi da kallo da take ‘kokarin ‘buya a bayan momy,” fito “ muryar kyakkyawan guy d’in ta ratsa mata kunnuwa , a ra’be ta fito daga bayan momy kamar mara gaskiya , murmushi momy ta saki tana nufo inda yake “ wannan bazata haka son , kace mun sai anjima zaka dawo”, murmushin da ya saka jerarrun ha’koransa fitowa yayi,” nayi kewar kune momy shiyasa ban bari Daren yayi ba “, murmushi ta sakar masa tana karban trolley d’in sa,” yanxu dai ka fara yin wanka son , kafun nan sea kaji abinci “, yanxu ma murmushi ya sakar mata “ okay ma”. Har ynxu Mimi na inda take ganin ya’ki kallanta kamar zatayi kuka , shima bece mata komai ba yayi wucewarsa,da Sauri ta ‘karaso Inda momy “ Bro ya’ki kulani please ki bashi hakuri”, hararar ta momy tayi tabar wajan , fashewa da kuka mimi tayi , da gudu ta nufi d’akinta Asama tare da saka masa key.

Har guy d’in ya fito sanye da wasu kayan alamar wanka yayi mimi bata fito ba , tsakanin shida momy babu Wanda ya tanbaye inda take har ya kammala cin abincinsa, kallan momy yayi “ Ina Mimi momy”, wani saban murmushi momy ta saki, “Dakar barta ai Son , nasan tana can tana halinta na kullum, nakusa maganinta ai”, murmushi yayi tare da mikewa, kallansa momy tayi “ ina zaka “, kanshi ya d’an sosa kadan yana murmushi “ yanxu zan dawo momy”, gyada masa kai batare da tace masa komai ba , ita kad’ai tana murmushi abinta. ‘Dakin Mimi ya nufa ,sau d’aya ya murd’a yaji shi a kulle , nasa d’akin ya nufa tare da d’akko wani mukulli ya koma dakin mimin, sau d’aya ya saka key d’akin ya bud’e . A tsugunne ya same ta tahad’e kai da gwiwa tana shash she’kar kuka , har ya shigo cikin d’akin bata sani ba , kan kujerar gaban mudibin ta ya zauna tare da crossing Legs d’insa , “me akai miki kike kuka ?”, da sauri ta d’ago fuskarta ganinsa zaune a wajan tayi Sauri goge fuskarta “ ba kuka nake ba , abune ya shigar mun ido”, tafa har yanxu muryarta kamar zatayi kuka , gyad’a mata kai yayi tare da mikewa, itama da Sauri ta mi’ke tare da ri’ko hannunsa “ am sorry yaya moh “, kallanta yayi akaro na biyu ya ‘kaya maimaita maganarsa” me yasaki kuka ?”, sun kuyar da kanta tayi ‘kasa , shima d’auke hannunsa yayi daga cikin nata “ well “ da Sauri ta furta “Naga kana fushine and yaya moh , momy ce tace fa zata sa ka aure min driver”, ke kuma ba kyaso? Kanta ta d’aga masa alamar eh , murmushi ya karmata “ kar na ‘karaji momy na magana Kema kin d’aga muryar ki? Okay ? “ na dena , and yaya moh ina tsarabata? Goshinta ya d’an dallah “ in my room “, bata jira karashen maganar saba ta fita a guje , giirgiza kansa yayi “ Allah ya shirye ki mimi “, daga nan ‘kasa ya sakko inda momy take suka soma hira Yaushe gamo da ita.

 

**********
*************
??????

NIGER

Tunda Tahee ta farka take kuka ita kadai lokaci zuwa lokaci sai ta zabura zata mi’ke wasu ‘yan mata suna ri’keta , abun mamakin kuma da kanta tayi sallahr asuba daga nan kuma ta mike hawaye cike a cikin idanuwanta , duk yadda taso barin Wajan sun hanata jintake kamar zatayi hauka fad’i take su rabu da ita amma sun ‘ki sai ma baba Malam da suka kira , kallo d’aya yayi mata ya saki murmushi “ ku kyaleta “, suna sakin ta kuwa ta mike a zabure zata nufi ‘kofa ya daka mata tsawa, da Sauri ta nutsu, abincin da aka kawo mata ya nuna mata , cikinta har rawa yake lokacin da ta soma cin abinci har saida Alhaji isma’il d’in yace taci a hankali, gabaki d’aya sai data basu tausayi, rubutu baba Malam yasa aka bata , ita kad’ai sai sakin ajiyar zuciya take , karatun alkurani aka sa a d’akin , matasan ‘yan matan suka zauna da ita , baba Malam da alhaji isma’il kuma suka fita.

Cikin wani d’aki suka shiga Alhaji isma’il ya kalli baba malam,”baba Malam idan ba damuwa ina san ro’kan wani Alfarma”, murmushi baba Malam yasaki kafin yace “ina jinka “,shiru yayi kamar bazai ce komai ba sai kuma ya soma magana “ baba Malam idan babu matsala inasan tafiya da wannan yarinyar can wajan iyalaina sai su cikaga da zama tare ,tun da alamu sun nuna zamanta anan kamar zai iya zamar mata had’ari ita da abunda yake cikin ta, tunda asirin da akai Mata ba iya nigeria bane har kusa da ita , kaga idan bata kusa da nan zata samu nutsuwar zuciya ko zata dawo hayyacinta sosai, ko ba dan itaba dan abin cikinta “. Yan Zuma baba Malam murmushi ya saki tare da gyara zaman sa “ Naji duk abunda kace isma’il, kuma na yaba da hankali da nutsuwar ka , amma kasani kamar Marainiyace kake kula da ita tunda bata da kowa , idan kaci amanar Allah , Allah bazai barka ba , ka kula da amanar Allah wannan kamar jarabawace Allah yakeso ya kwadaka”, sunkuyar da kai alhaji isma’il yayi “ insha Allah baba malam , nayi maka alkawari zan d’auketa kamar ‘yar cikina sannan na bata tar biya kamar ni na haifeta “, Allah yayi maka albarsa, yaushene tafiyar?” Cewar baba malam , “Jibi nake san komawa insha Allah “, jinjina masa kai baba Malam yayi “ sai a sanar wa iyali “cewar baba Malam,cike da girmamawa ya “amsa da insha Allahu”.

 

????GIDAN AUNTY ????

07041879581
MSS LEE ??

Back to top button