Author: Novels

  • Arubuce Ta Ke 70

    Page 70

    Duk da cewa baikai ga cimma gaci ba,duk da cewa buri da muradinsa bai cika ba……amma ta kaishi wata duniya data sake haukata tunaninshi,ta sake ninka burinsa……ta sake kwadaita masa ita,ta kuma haifar da wani yanayi da kai tsaye zaka kirashi da ZAZZAFAR K’AUNA a karon farko,cikin jininsa ya dinga ji cewa eh weedad din ta dabance,zata iya zamowa ta musamman cikin mata….. za’a iya kiranta da ‘yar baiwa,ya samu wani irin nutsuwa da tarin ni’imomin dake hutar da zuciya su kuma sanya ma ruhi nutsuwa tattare duka a iya jikinta kadai,tun baikai ga afkawa waccar duniyar ba.

    Wani irin ciwo yakeji har cikin zuciyarsa sanda take rera wani irin kuka,ciwo ciwo takeji daga can qasanta duk da baiyi yawa ba,saidai hankalinta a mugun tashe yake,me ya aikata mata kenan?,da wanne fuska zata kalli mutane?.

    Yayi lallashi yayi ban bakin amma a banza,har sai da bacci ya taimakeshi ya dauketa,sai ya zareta daga jikinsa a hankali ya shimfidar da ita,ya kunna bedside lamp ya matso da ita kusa da fuskarta sosai.

    Kallo na haqiqa ya zauna yana qare mata,baisan da wanne suna zai kirata ba,baisan kuma a wanne matsayi zata iya tsayawa cikin zuciyarsa ba daga ranar da ya maidata tashi,a yanzun Allah ne kadai yasan me yakeji a kanta,qauna soyayya tausayi da kuma shauqi gaba daya, mintuna qalilan amma sun canza matsayinta daga wani bigire zuwa wani bigiren na daban.

    Ya jima zaune kamar mai karanta littafi yana kallon baby face dinta da tayi jazur da ita,sannan ya sauke ajiyar zuciya,ya zura qafafunsa ya sauka daga saman gadon ya shige bandaki.

    Tsarkake kansa yayi sannan yayi wanka,ya fito ya tsane jikinsa da kyau ya sauya kaya sannan ya koma saman gadon,bai jishi dai dai ba har sai daya jawota jikinsa,tunane tunane ne masu tarin yawa ke masa yawo a kai,shi kansa idan yace ga dai dai lokacin data ma zuciyarsa wannan muguwar illar yayi qarya,wani abu mai qarfi akanta ya dinga shigarsa,sai ya dinga jin gaba daya duniyarsa ta ta’allaqa da ita.

    Kiran sallar asuba ne ya tasheshi,har ya gama shirinsa na fita masallaci bata ko motsa ba,bacci take sosai tana kuma sauke ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci,har sunkuya saman kanta zai tasheta yaji ya kasa tashin nata,yaja mata bargon ya rufeta bayan yayi kissing goshinta,ya fita yana waiwayawa kamar wanda akace za’a dauketa kafin ya dawo.

    Sanda ya fita sallar yayi mamakin ganin cunkoson jama’a a layin nasu,ya qarasa a hankali ya fara musabaha da mutanen dake wajen

    “Munyi tunanin baka gari ai yallabai” daya daga cikin dattawan layin ya fada yana duban abbas

    “Me yake faruwa alhaji audu?” Abbas din ya tambaya yana dubansa

    “Wallahi daren jiya ‘yan fashi suka shigo gidan maqocina alhaji isah”

    “Subhanallah” ya fada cikin alhini

    “Kusan kowa yaji abun,don tun wajen karfe daya na dare suka shigo unguwar,basu fita sai qarfe uku”

    “Ya salam,Allah bai sa naji ba,amma aka rasa wanda zaiyi kiran koda wayata?”

    “Wallahi Allah ya daukewa kowa wannan tunanin” matsawa gaba ya fara yi zuwa gidan alhj isah din,inda mutane suka fara dandazo

    “Badai wanda suka raunata ko?”

    “Eh to,sun harbi yarinyar sa,suna hanyar kaita asibiti”

    “Kun kira jami’an tsaron?” Cikin alhini alhj audu ya girgiza kai

    “Kusan awa guda kenan amma babu su ba dalilinsu” sosai ran abbas din ya baci,ya tambayi police din wanne area dinne alhaj audu ya gaya masa,sai ya fidda wayarsa yayi kiran dabai wuce na minti uku ba cikin bacin rai

    “you must be there before thirty minutes” abinda ya fada kenan ya kashe wayar ya mayar aljihu

    “Kada kowa ya shiga cikin gidan,sannan suma mutanen gidan a gaya musu su nisanci inda abun ya faru…. alhaji muje muyi sallah tukunna” tare suka rankaya da alhaji audu zuwa masallacin suna sake tattauna yadda abun ya faru,bashi da nauyin bacci sam,kamar yadda bai saba dogon bacci ba,amma yayi mamakin yadda jiya har akayi aka gama abun baiji ba,lallai da gasken gaske ‘yar qaramar yarinyar ta gigita masa rayuwa da kyau a jiyan,ta kuma shirya janshi zuwa wata rayuwa ta daban,baisan sanda wani siririn murmushi ya kubce masa ba.

    Wannan case daya faru a unguwarsu ya hanashi komawa gida da wuri,sunata bincike kan abun har sai da suka samu nasarar tracking barayin cikin taimakon Allah da kuma qwarewar da yake da ita,sai wajen qarfe daya na rana sanann ya gama nasa aikin,ya danqawa wadanda alhakin kula da area din yake a hannunsu,ya zare safar hannunsa ya miqawa daya daga cikin police din,gaba daya hankalinsa yana kanta tun dazun,dauriya kawai yakeyi.

    Sama sama ya amsa gaisuwar yaron gidan nashi ya wuce zuwa cikin gidan,kai tsaye sashensa ya wuce,ya tura qofar falon ya shiga,bata falon bata bedroom din,sannan bata toilet,sai zuciyarsa ta raya masa ko tana sashenta,don haka ya juya akalarsa zuwa can.

    Kaf ya gama dubawa bai ganta ba,sai abun ya shiga bashi mamaki,baya da niyyar shiga sashen hafsat din yau gaba daya,amma dole ya shiga ya gani ko tana can.

    Dukkansu suna falo ita da yaran,tuni falon ya koma ‘yar gidan jiya,tana saman kujera zaune abinta,ta cika tayi fam da fushi,daga abbas din har widad din kowanne da nasa laifin a wajenta,donme yarinyar zata tafi gidan hajiya tayi zamanta?,uban waye zaiyi mata aikin da tafi kowa sanin itace zata yishi?,sannan abbas din me yake nufi da ita?,har azahar tayi amma ya kasa leqowa yaga lafiyarsu?,jikinta ya soma sanyi amma wani sashen na zuciyarta yana qarfafa mata gwiwa,tare da sake kambama mata laifukansa,duk da haka ta soma rasa qwarin gwiwarta,tasanshi….yana da danne zuciyarsa da hanata saurin fushi,amma kuma idan yayi fushin bashi da dadi sam.

    Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke sanda taga shigowarsa,ya tsugunnawa yaran suka haye bayansa,fuskarsa na fidda murmushi,zuciyarsa dauke da tausayinsu,da babu alamun an musu wanka

    “Ina antynku?”

    “Daddy ta dawo?,ka kaini wajenta” mimi ta fada,abinda ya tabbatar masa kenan bata shigo ba kwata kwata

    “Ina kwana?” Ta fada ganin yana niyyar miqewa ba tare daya kalleta ba

    “Lafiya”

    “Ga breakfast dinka har ya huce baka ci ba”

    “Na qoshi” ya amsa mata yana ficewa riqe da yaran.

    Hankalinsa yadan tashi,ina ta tafi to?,ya tambayi kansa,sai ya jawo wayarsa ya kira layinta,a kashe layin yake,ya sauke wayar yana fidda iska daga bakinsa,gidan hajiya ta koma?,wata zuciyar ta gaya masa,har ya danna kiran layin hajiya sai ya kashe,idan ta tuhumeshi dalilin komawarta baisan me zaice mata ba,don haka ya kira layin umar.

    “Kana gida ne?”

    “Eh hajiya za’a baka?”

    “Weedad tazo?”

    “A’ah yaaya,tun jiya dai dana kawota gida”

    “Okay,karka cewa hajiya ga abinda na tambayeka”

    “To yaaya” umar din ya fada ,kafin ma ya qarasa abbas din ya katse kiran,sai yaji hankalinsa ya sake tashi.

    Muhsin ne ya fado masa,baiyi qasa a gwiwa ba yayi kiransa bayan sun gaisa kafin abbas dinma yace komai ya rigashi magana

    “Jiya jiya muke zancanku,inajin madam fa gobe ko jibi zata shigo ganin diyarta,nace ban da tabbacin kunxo weekend wannan satin”

    “Jiya mukazo,amma kuma banajin zamu jima zamu koma,yanzun ban fiya sakewa a bauchi ba,ayyuka sunyi yawa a kaduna” hira kadan suka taba sukayi sallama,don shima muhsin din fitowarsa kenan daga gida yana kan hanya yana driving.

    Wayar ya ajjiye,ya koma gefen gadon ya zauna hannuwansa cikin sumarsa yana murzata a hankali,yanason qwaqwalwarsa ta hasaso masa mutum na gaba da zai kira ya bincika ko can taje,ya akayi ta iya fita daga gidan har ta fita ba tare da wani ya ganta ba?.

    Kasa zama yayi,sai kawai ya miqe ya dauki key din motarsa,tsoronsa daya kada yarinyar mutane ta bata cikin garin daba nasu ba,don yana da tabbacin zaiyi wuya ace shigowa akayi aka dauketa,don ya duba duk wani abu da zai iya bada alamun hakan bai gani ba,sai ya fita da yaran ya zubasu a motar suka fice daga gidan.

    Layi layi titi titi ya dinga bi yana dubata amma sam babu ita ba alamarta,har wajen azahar,ya tsaya a wani restaurant ya siyama yaran takeaway,ya dawo cikin mota ya zauna kenan wayarsa ta dauki tsuwwa,ya duba me kiran sai yaga muhsin ne

    “Kasan matarka ta tafi kano?”

    “Kano?” Ya tambayi muhsin din cikin mamaki qwarai,duk da dama yana cikin dimuwar son sanin ina tayi

    “Eh,yanzu muka gama waya da ummu,ta kirani tace na shaida maka,don tafiyar batayi mata kama data nutsuwa ba” qatotuwar ajiyar zuciya ya sauke yana jin wata nutsuwa na saukar masa

    “Alhamdulillah” ya fada a fili

    “Ka ganni a gefan hanya,tun dazun nake checking ko batayi nisa ba,ina shirin kira headquarter ma su bani mutane muyi aikin tare”

    “Subhanallah…….wanne irin sakarci ne wannan?,halan bata gaya maka ba bakasan da tafiyar tata ba” qaramin murmushi ya subuce masa,yasan sarai muhsin ba wasa,yanzun nan idan yace zai gaya masa gaskiya sai yace zai taba masa mata,shi kam a yanzun a yadda widad takai har cikin ruhinsa,baya jin ko ruwan sama zai lamunce masa ya taba masa ita

    “Me na tone tone?, tunda ka isar da saqon ummu shikenan,zan kirata”

    “Please abbas……kada kace zakayi kawaici,ka gayamin gaskiya”

    “Amma dai kasan indai kace zaka shiga tsakanin miji da mata zakaji kunya ne ko?”

    “I know…..but…..”

    “But what?,shikenan kawai,ka qyalemu tsakaninmu ne”

    “Alright,Allah ya sawwaqe” daga wannan sukayi sallama ya aje wayar.

    Mamaki ya sake kamashi,yayin da qaramin murmushi ya subuce masa,rigimammiya ce yarinyar ta ajin qarshe,ya akayi har ta iya kai kanta kano?,da gaske batasan wannan rayuwar ba,batasan meye ma’anar aure ba at all

    “I will teach her……bazan bari ki subuce min ba,zan koya miki abubuwa masu zafin da zuciyarki zatayimin riqon tsauri da kyau” ya fada shi daya kamar me sambatu,abinda yake ji a ransa game da ita yafi qarfin a kirashi so,saidai wata irin zazzafar qauna da bai taba jin kamarta ba.

    Aje wayarta ummu tayi tana sauke dubanta ga widad data cusa kanta cikin pillow tana ta sheqa kukanta,kukan da tunda ta iso kano take kwararashi,tayi tambayar duniya amma taqi daga kai ta kalleta ma bare akai ga amsawa.

    Abu daya ne yasa hankalin ummu bai wani daga ba,widad din tata tayi fes tayi fresh,ta sake murjewa,ga kuma girma data qara,ta fara zama budurwa sosai,aure ya kwarzantata

    “Widad” ta sake kiran sunanta,shuru bata amsa ba sai kuka,tana tsoron su hada ido da ummun,tana ganin kamar zata gane abinda yayi mata a daren jiyan

    “Kinga idan ba zaki amsa min ba,ki daina kukan kada kanki yazo yayi ciwo” ummu ta fada tana miqewa

    “Ki samu waje ki kwanta” ta sake fadi bayan ta isa gaban wardrobe dinta ta fidda hijab,tayi sallar azahar sannan ta dauki wayarta ta fita tabar mata dakin,cikin ranta tana juyayin abinda ya faru,kodai ita da kishiyarta ne?,tunda muhsin ya sake kiranta yace abbas din yace babu komai,amma kishiya kuma……nawa widad din take da har kishi zai hadasu tayi wannan tafiyar afujajan.

    Da wannan tunanin ta isa falonta,ta iske latifa tana aje abincin rana

    “Batace komai ba ummu?” Latifan ta tambaya cikin damuwa

    “Uhmmm…..bata ce ba,nifa banga wani alamun damuwa tattare da ita ba,nafi zaton shirmenta ne kawai ya motsa,idan kuwa haka ne zataci qaniyarta,ta yaya zata dauko qafa daga bauchi ta taho kano ba tare da izinin mijinta ba?,baya ga haka kuma ita kadai a wannan rayuwar da muke ciki?” Ajiyar zuciya latifa ta sauke

    “Ayi mata dai a hankali ummu,ai ruwa baya tsami banza”

    “Kin manta widad din ne ashe” ummu ta amsa mata,wanda tana rufe bakinta momma tayi sallama

    “Barka da rana ummu” ta fada tana ‘yar fara’ar da batakai zuci ba,da kallo ummu ta bita

    “Ke kuma daga ina da rana haka fatsar fatsar?” Murmushi ta danyi tana wuwwulga idanunta wai ko zataga himilin kayan widad din da akace an ganto ta shigo ita kadai

    “Zan fita ne nace bari na leqo,idan kina da canji ki aramin”

    “Canji?” Ummu ta maimaita cikin mamaki,saboda irin wannan ita baya hadata da surukanta

    “Eh….eh” dan shuru tayi tana karantar momma din,sai kuma tace

    “Allah ya kyauta,shiga kitchen ki yiwa latifa magana ta baki” amsa mata tayi sannan ta nufi kitchen din tana kalle kalle a falon ta gefan idanunta.[3/16, 11:09 AM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 60

    Arubuce Ta Ke 60

    Page 60

    Wuni tayi takaici yana cinta,amma kuma da sukayi waya da anty ummee ta tilastata sakin jikinta

    “Ke da kike jira kiji albashiri din tafiya dake,me ya kaiki dukka wadan nan abubuwan,dole ki taushi zuciyarki ki nuna masa komai ba komai bane,kuma kiyi dako kar kiyi gaggawar tambayarsa,ha sai in shi ya gaya miki da bakinsa” da wannan shawarar tayi qoqarin gyara dakin yaran,ta kuma tsallaka taje ta gyara nasa,dukda gyaran nata ba wani na azo a gani bane,amma bahaushe yace da babu gwara babu dadi.

    Cikin kwanakin kuwa ta dunga qoqarin yun dukma abubuwan da tasan yanaso,sai abunuwan nata gaba daya suka zama wanu banbarakwai saboda ba saba yi tayi ba,ita kanta da qyar take kai labari saboda rashin sabo,a wajensa shima abun ya zameasa wani iri,saidai shi din hakan yakeso inda ace zata sauya din.

    ***********Kwana daya rak amma gaba daya jikinta ya zama week kamar wata mara lafiya,randa ta dawo daga makaranta ma wannan dogon wunin kwanciyar tayi,don haka da dare bacci bacci yayi mata qaura,sai taja wayarta kawai ta soma bin charts na groups din da anty deena ta saka a sanyata,tun abun bai wanu burgeta ko mata dadi har ya fara jan hankalinta,a hankali ta dinga bin topics din da suke tattaynawa daya baya daya,tarin uban saqonni saidai dukkaninsu msu amfani ne ga macen auren dake neman gyara rayuwar aurenta,saidai ga widad fa abun kunya ya zame mata,tana karantawa tana jin kunya ita kadai,musamma idan ta tuna anty deena na ciki.

    Bayan tayi nisa ta soma fahimtar wasu abunuwa da suka sanyata cikin nqzari da lissafi,an gadi abubuwa masu yawa da ita bata sansu ba,kuma kallon iskanci take musu,amma kuma taji suna batun lada,dama akwai lada cikin iskanci banda tarin zunubi?,saita maida wayar ta ajjiye gefe tana tuno wasu abubuwa,ta dinga saqa tana warwarewa,wa zata tambaya wanda zaiyi mata bayanin da zata gane da kyau,ta kuma fita daga shakka?,ita kanta anty deena maganganun da taga tayin sai suka weedad ke tunani a kanta,tasan dai anty deena ba ‘yar iska bace,to amma…….

    Katsewa tunanina yayi sanda wayarta ta soma wani qaramun ringing mai dadi,ta kalli wayar,kamar ta gane number din,ta jawo wayar ta daga ta sakata a kunnenta.

    A nutse muryarsa a qasa yayi mata sallama,ajiyar zuciya ta kubce mata ba tare data shirya ba,ajiyar zuciyar data sauka a kunnensa,ta kuma sanya tsigar jikinsa zubawa

    “Bakiyi bacci ba?”kai ta gyada sannan ta amsa masa

    “Eh”

    “Me yasa?” Rasa amsar bashi tayi,saboda dai ba zata iya ce masa ga abinda take karantawa ba

    “Me tayin kwanan ta shigo?”

    “Eh” ta bashi amsa,don sai da sukayi sallama da ita sannan ta shigo dakinta,saboda ita a falo take kwana,taqi yarda ta kwana dakin widad din

    “Yayi,yanzu gaya min dame dame kikayi yau?” Ya tambayeta yana hangen hafsa daga inda yake zaune cikn falonsa,tana nannade wandon kashin da nawwara tayi tana cusashi qasan kujera,ya dauke kallonsa daga kanta ya maida wani gefin,don bayason ransa ya baci.

    Sosai ta narke cikin pillow din,zuciyarta tana narkewa,kewa tana sake cikata

    “Bayan kaine….kaine kayi tafiyarka ka barni” ta fada a wanu kugun shagwabe,abinda yayi masifar tabashi,tsigar jikinsa ta zuba sosai,ita kuwa ko a jikinta,saboda tana ganin tayi maganarta ne sak

    “Am sorry……bazan sake ba” ya samu kansa da fadin hakan ba tare daya shirya ba,dai dai sanda hafsat din ta qaraso wajen,sai taji kamar kunnuwanta basu jiye mata dai dai ba,waye yake baiwa haquri wai?,ta tambayi kanta,ta tsaya cak tana dubansa,yayi kamar bai ganta ba,yaja cup din coffe daya hada kafin ya zauna ya kurba kadan

    “Yanzu kiyi addu’a ki kwanta,akwai school gobe”

    “Tom…..sai da safe?” Ta tambayeshi a sanyaye,saboda har ga Allah hirar ta mata dadi,bataso yace ta kwanta ba.

    Murmushi ya sake kubce masa,a hankali ya furta

    “Goodnight” sai ya zame wayar daga kunnensa yana kasheta,dai dai sanda hafsat din ta kasa tsaiwa,ta zame ta zauna a kujerar dame kusa dashi

    “Wai da waye kuje waya haka?” Sai daya kashe wayar ya ajjiye sannan ya dago yana dubanta,yadan zuba mata ido na wasu sakanni sannan ya saki murmushi

    “Qanwarki ce”

    “Qanwata ko kishiyata”shine abinda bakibta taji ya kamata ta furta,to amma tana tsoron kada ta barar da tafiyarta,don haka ta hadiye maganarta,sai gefw da tayi da kanta ta tabe baki

    “Dole yarinyar ta dinga tsoronka,ya zaka dinga gaya mata maganganun da sukafi qarfi kanta,a haife fa ka kusa haifarta,tunda ka ninka shekarunta harda doriya” ta qarasa maganar tana dawo da dubanta kansa.

    Fuskarsa a sake,saima murmushi daya saki,ya shafa kanshi zuwa kyakkyawan hanarsa dake dauke da gashi baqi sidik daya sha gyara

    “Kinason ki gayamin na tsufa kenan fa”

    “Kusan haka ne” ta fada tana tabe baki,a nufinta na zare masa karsashinsa da sha’awar komai,murmushi ya sake saki,abu daya ya sani,komai zatayi ba zataji komai daga bakinsa ba,ta manta wayeshi din wajen riqe sirri

    “Ki zaro wancan andon kashin ki fita dashi ki wanke,and please…..kada na ganshi a dustbin” ya maida zancan zuwa wani topic din na daban.

    Kunya da haushi suka cikata,ba wannan batyn takeso suyi ba,ita batasan ma ya ganta ba,maganar gaskiya babu agender din wanke kashi yanzu a gabanta,amma dole ta miqe rana cewa

    “Kadai dinga mata a hankali tunda yarinya ce,bawai wani abu zata fahimta daga gareka ba” da kallo ya bita yana son tantance da wanne irin sound tayi masa maganar,sai ya maida nayansa jikin kujera,ya lumshe ido yana maimaita maganarta,abubuwa da yawa sunzo kansa a sannan wadanda suka sanya dole murmushi ya qwace masa.

    Dukka abinda ta karanta a daren washegari ta dunga bitarsu a makaranta,kwatsam ranar sunyi missing periods har biyu,sai ajin ya zamana na surutu da hira,abinda ya sake sanyata daukar wayarta taci gaba da dubawa,saidai tana tsaka da dubawar hirar da ‘yan bench din bayansu keyi yaja hankalinta,bata suaje wayarta ba amma ta bada kunnuwanta tana saurarensu,hirace ta aure da yawanci ba’a rasa matasan ‘yammata da suke ganun sun fara zama seniors da yinta,fiye da rabin hirar ta zame mata kamar wani mabudi kuma amsa na dukka tambayoyinta,ta dinga saurarnsu tana ciro abubuwa masu yawa tana hadawa cikin maganganun data ji a groups daban daban.

    Koda aka tashi daya daga cikin qawayenta ta bata ajiyar hausa novels

    “Ki ajjiyemin don allah widad,yayana yazo gutu,doke sai ya koma zan karba,hanani karatun yakeyi,kada yaje garin bincike bincike ya ganosu na shiga uku” a karba din ta tafi dasu gida,da daddare ta buda jakarta bayan ta gama wani assignment zata maida jakar don kada ta manta idanunta suka gano mata litattafan,saita jawosu ta buda tana kallo tare da mamakin meye a ciki da za’a hanata karabtawa,don ita kallon normal kowanne littafi take masa,taji sha’awar duba meye a ciki,ta dauki daya part one ta buda ta fara karantawa.

    Ko page daya bata dauka da niyyar karantawa ba,sannu sannu sai gashi har tajai page na wajen biyar,ta saki murmushi saboda labarin yaja hankalinta,saita kife littafin,ta wuce kitchen ta zuba abinci ta dawo taci gaba da dubawa.

    Sannu a hankali sai gashi ta raba dare tana karatun,sam batasan dare yayi haka ba,don hatta da wayarta ta manta da ita,taje ta samu miscall na abbas kuwa harda sms guda daya,dare yayi don haka bata kirashi ba,sai tayi addu’a ta kwanta,amma kuma bacci ya qauracewa idanunta,tanata bitar abinda ta karanta din cikin kwanyarta,da gaske akwai soyayya irin haka?,soyayyar jaruman littafin ya tafi da ita,ta dinga kwantanta kanta dasu,kunya ta kamata ita akdai cikin dakin,saita kifa kai tana murmushi.

    Washegari babu makaranta good friday ce,wuni tayi tana karatun,wanda a ranar ta gama da part 02 ta shiga 03,sai data qare littafin a ranar ma sannan ta kwanta,nan dinma dai dukka labarin ta dinga tunawa,yadda jarumar ke gudanar da rayuwarta

    “Kamar ni da uncle kenan?” Ta ayyana a ranta,da sauri ta girgiza kai,kai anya?,ita kanta wasu abunuwan cikin labarin kunya suka dinga bata,first night dinsu ya dawo mata a rai,sai tsoro ya shigeta,itama wataran haka uncle din nata zaiyi mata?,amma wannan ai iskanci ne,to amma dama akwai ranar da wannan abun zai tashi daga sunan iskanci?,ta tuna haihuwar da jarumar tayi,suna nufin kowacce mace ta haka take haihuwa?.

    A daren qwaqwalwa da tunanin yarinya kala kala ta dinga yi,abubuwa da yawa ta watsar dasu tana ganin bazai yiwu ba,ta rungumi abubuwa da yawa da syka dinga burgeta,har ta dinga kwantata gwadawa.

    Da safe kuwa ta gwada abunuwa da yawa da ta karanta din,duk da tana wasu qarawa tayi,ta gama komai ta hada breakfast dai dai cikinta,din me tayata kwana gari na wayewa take komawa cikun gida tayi ayyukanta,bata dawowa sai wani daren,ko idan bata da abinda zatayi ta leqota su gaisa sannan ta koma,mayar mai gadin gidan ce,tana da matuqar kirki sosai.

    Tana cikin yin breakfast taji sha’awar kiransa kamar yadda taji jarumar littafin tana yi,gabanta ya dinga faduwa sabida rashin sabo,ta dinga jin tsoro tana ganin kamar ba wani abun burgewa bane,saidai duk da haka bata fasa kira ba.

    Lokacin ya shiga wanka,hafsat na zaune daga gefan gadon nasa tana dakon fitowarsa,da sauri kamar wadda aka kirayi wayarta ta dauki wayar tana duba mai kiran

    “Weedad” ta maimaita sunan data gani a rubucen cike da mamaki,kanta ya daure da kyau,ita dince ke kiran ko kuma dai idanunta ne,ko wata ce mai irin sunan,saita daga kawai kai tsaye.

    Shagwababbiyar muryarta data zame mata jiki,ta kuma saba magana da ita,da ita tayi sallama

    “Ke tsaya” hafsat ta fada da sauri dai dai sanda take ficewa a bedroom din don kada ma ya jiyota.

    Wani mugun faduwa gaban widad yayi jin muryar mommy hafsa

    “Ina kwana mommy”

    “Da ban kwana na zaki jini?,wa ya sakaki kiransa ko shi din sa’anki ne?” Mamaki ya bayyana a fuskar widad din,ta dauka ba komai,ta dauka momy din zata ce ta kyauta,saita kasa gane yadda abun yake

    “Kiransa nayi mu gaisa mommy,jiya ya kirani ban dauka ba” tashin hankali!!, Ta fada a ranta tana jin yadda fuskarta ta dauki wani irin zafi,zazzafan kishinta da taketa qoqarin dannewa ya taso mata

    “Yanzu ke har kisan ki kira d’a namiji kusan sa’an babban wanki koma babanki,ashe baki da kunya kwata kwata,to ba sa’anki bane,idan kika sake kiransa ko kuma ya sake kiranki kika daga saina miki mugun duka,ke bakya tsoron abinda zai sameki?,na gaya miki ba’a sakar musu fuska ko jiki,so kike yayi miki ciki ki mutu ko?” Karon farko taji maganar mommy hafsa din banbarakwai,sai taji kanta ya kulle

    “Karna sake ji kuma kada na sake gani,kina jina?” Ta tambayeta a tsawace

    “Tom” ta amsa mata jiki a sanyaye,sai hafsat din ta katae wayar tana jan tsaki,taso yarinyar na gabanta,amma bari ya fita,zata sake kiranta ta sake jadda da mata.

    Jiki a sanyaye ta ajjiye wayar, kwanyarta ta shiga rububin lissafin maganganun hafsat din,zuciyarta taqi amincewa da hakan jikinta yaqi karba kuma ranta yaqi gamsuwa,saboda aduk abubuwan data karanta bataga ta inda aka nuna abune mara kyau ba da har mommy hafsat din zata dinga mata fada haka ba,kusan minti goma ta kasa samun nutsuwa,sai tunani yazo mata,sai kawai ta kira anty deena tace bari ta tambayeta.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[3/13, 12:54 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:huguma*

  • Arubuce Ta Ke 50

    Page 50

    Blue black abaya mai sulbi ce a jikinta me rubi biyu,qafafunta saye cikin wasu slippers masu kyau qirar kamfanin DKNY light blue,mayafin abayar kawai ta yafa,bata wani tsaya rolling ba,tana janye da qaramar akwatunta har xuwa bakin motarsa qirar BMW.

    Yana jingine jikin motar yana amsa waya,a hankali idanunsa suka sauka a kanta,yana matuqar son ado da kwalliya,wannan dalilin yasa baya rabo da siyawa hafsat kayan qyale qyale na mata,saidai baya ce ga inda take kaisu ba,bata saka ba bata kuma bayar ba,a yanzun data saka abayar favourite color dinsa,sai yaga tayi masa kyau sosai a ido,karon farko kenan.

    Gabansa ta tsaya da akwatin,ta langabe kai gefe tana mele baki,tanason gaya masa ba zata iya daga akwatin bane,janye idanunsa daga kanta yayi,ya karanci me takeson fada,sai ya zaro key din motar daga aljihunsa ya soma takawa a hankali.

    Zagayawa yayi ya bude booth din motar,yasa hannu daya ya daga akwatin cak ya saka ya maida booth din ya rufe.

    Bismillah yayi yana daura seat belts dinsa,yadan saci kallonta,yana mamakin yadda take qaunar turare,gaba daya qamshinta ya cika motar,ya lumshe idanunsa a hankali,yana jin wani yanayi cikin jikinsa,he missed his wife alort,yayi qoqarin,more than two weeks rabonsa da ita,shi yasa yakeso yayi surprising dinta,yau ba mita ko qorafi duka sun qare,abu daya ke sanyaya masa gwiwa,yasan ba lallai ya samu wata tarbar arziqi,infact baisan ma a yanayin da zai cimmata ba,may be su buge da samun sabani kamar yadda ya zame ma hafsat din sunna,duk sanda ya dawo daga tafiya goma,to bakwai a ciki a ranar daya iso sai wani abun ya hadasu,duk kuwa da cewa shi din mutum ne mai yawan kawaici,wanda bai fiya qorafi akan abu ba idan ba cikashi kayi ba.

    “Kiyi addu’a” yace da widad yana shirin tada motar,kafin ya gama rufe bakinsa wayarsa ta dauki kuwwa,sai ya qarasa kunna motar ya barta tana daukan zafi ya duba me kiran.

    Hajiyansa ce,nutsuwa yayi sosai ya daga wayar a ladabce yayi sallama,ta amsa masa cikin nuna kulawa da qauna,ya soma gaisheta gami da tambayarta lafiyarta,duk da jiya ma da yammaci sunyi waya da ita

    “Yaushe zaka zo gida ne?,ka manta kabar wata iyalin naka a nan?” Tambayar yaji banbarakwai,saboda ba al’adar hajiya bane yi masa irin wannan tambayar

    “Yanzun haka ma muna cikin mota zamu fito daga Kadunan…..”

    “To alhmdlh ma sha Allah” haka kawai yaji zuciyarsa da ransa basu kwanta masa ba

    “Hajiya lafiya dai ko?,ko wani abunne ya faru?”

    “Babu komai,Allah ya tsare hanya”

    “Hafsat ce ta kawo miki maganar?” Ya sake dai tambayar hajiyan

    “Nace babu komai,Allah ya tsare hanya,ina widad din?” Waiwaya yayi yana kallonta,ita sam hankalinta ma da alama baya wajen,yana farfajiyar gidan inda mai gadin gidan yaketa gyaran flowers,dauke kansa yayi ya maida gabansa

    “Tare zamu taho in sha Allah”

    “To hakan yayi,sai kun iso”

    “Madalla hajiya,Allah ya saka da alkhairi” sukayi sallama kowa ya aje wayar.

    Iska ya furzar yana tada motar,idan ya rantse ko kaffara bazaiyi ba hafsat ce takai qararsa wajen hajiyan,don ya sansano hakan daga muryar hajiyan,yasan ta boye masa ne kawai saboda kare martabar hafsa a wajensa,wai me yasa ita din bata jin kunya ko nauyin kaishi qara?,yanzun wannan abun har ya isa takai qararsa gaba?, just one week daya qara baizo ba?,bayan he explains to her?,baisan sai yaushe zata fahimci illar wannan muguwar dabi’ar tata ba,baisan sai yaushe zata gane zubarwa da kanta kima da daraja takeyi a wajen iyayensa ba.

    Ya danyi gudu,hakanan banda sallah basu tsaya sunyi komai ba a hanya,don haka awanni biyu da rabi suka kawosu bauchi daga kaduna.

    Ba’a jima da idar da sallar la’asar ba suka shiga unguwarsu,ya faka motar a harabar gidansa,kafin ya sake wani abu tuni widad ta balle murfin motar ta fice saboda hangosu mimi da tayi,suma tuni sukayo wajen,saboda sun shaida motar daddyn nasu.

    Binta yayi da kallo kawai,har zuwa sanda ta isa garesu suka rungume juna,sannan suka iso bakin motarsa suna dakon fitowarsa.

    Tare suka rankaya zuwa ciki,mimi da nawwara kowacce na bada nata zancan,fuskar widad fal fara’a,har suka isa falon hafsat din.

    Kallo daya ya yiwa falon yaji bacin rai ya saukar masa,kullum jiya i yau,dukka gyara da qyale qyalen daya zubawa falon daga bikin widad din tafiyarsu kaduna zuwa zuwansu yau gaba daya sun fara dakushewa,sai ka rantse kayan sunyi shekaru bakwai da sakasu,kai koda shekaru bakwai dinne indai ba qazamar mace ta ainihi ba bai kamata suyi wannan dafewar ba,ko ina tarkace ne dake nuni da cewa babu wadatacciyar sharar da falon yakeso,uwa uba turkish carpet dinta ruwan madara ya fara yin qaura daga aihinin kalarsa zuwa brown, qawataccen center table din daya zuba kudade ya siya mata an soma kwanceshi,ba wasu sassa a jikinsa.

    “Ina Mommy din?” Widad ta tambayi mimi

    “Tana kitchen,wanke wanke take”

    “Muje ki rakani” ta kama hannun mimi din suka wuce kitchen din.

    Bata a kitchen din,amma qofar backyard na kitchen din a bude yake,sai suka sanya kai can.

    Turus widad tayi tana duban iyayen kwanukan dake yashe a wajen tamkar anyi taron biki ko siyasa an watse,kusan dukka wasu kwanuka na kitchen dinta suna wajen,tana tsakiyar su ta hada kumfa a babban baho tana wankewa,tanayi tana maganganun qasa qasa,daurin qirji ne a jikinta na zanin atamfa,sai rigar shirt,kanta dankwalin zanin ne data masa daurin gaban goshi,daga qasa kana iya hango qananun gashinta sun burtso.

    “Mommy sannu da aiki” widad ta fada tana murmushi,hafsat ta waiwayo da sauri suka hada ido da widad din,a take taji ta muzanta,bata taba kawowa a yau idan hajiyan ta kirashi zai taho ba,dukka ta dauka sai gobe,don haka yau taci burin qarar da yininta tana gyaran kitchen,tasan shi da falo da toilet sune abu na farko da yaqi jinin ya gansu ba’a kintse ba,yau din kuma alhamis,ta zaci zai taho gobe juma’a ne.

    Sake juya idanunta tayi akan fuskar widad karo na uku kafin ta samu sukunin amsa sannun tata data yi mata,idan idanunta ba gizo yayi mata ba yarinyar qara haske da kuma qiba tayi,ga wani dan banzan qamshin turare da taketa bulawa hancinta,wani abu mai qarfi ya taso ya kama zuciyarta, muryarta ta sarqe,har sai da hakan ya bayyana cikin sautinta,ta jefa mata tambayar muryarta a cushe

    “Dake da waye?,da yammar nan?”

    “Ni da daddynsu mimi” tayi maganar tana kallon qofar da zata sadaka da kitchen din,saboda tuni hancinta ya shaida mata wanzuwarsa a wajen,sassanyan qamshinsa daya fara yo gaba.

    Idanun widad na kansa haka na hafsat,yayin da nasa idanun ke kan hafsat din da tarin kwanukan wanke wankenta,wanda ko ba’a gaya masa ba yasan halin nata tayi,wato tayi girki ta jiqa kwanon,gobe ta bare sabo ko wankakke ta sake wani girkin a ciki.

    Tuni idanusa suka cika taf da bacin rai,banda wanda ya shaqa daga falo,da kuma dattin daya hanga akan sumar yaransa,ga qurajen zafi da suka fesowa nawwara,tabbacin ba’a kunna musu gen kamar yadda ya bar sallahy,bayan ya aje kudin komai da komai.

    “Sannu da zuwa” ta fada tana miqewa hadi da sauke zaninta data yaye cinyoyinta

    “Yauwa” ya fada yana komawa da baya,cikin sa’a ko rashin sa’a,sai ya taka sauran rubabben abincin data kwakwkwafe a kwandon shara,Allah yasa boots ne a qafarsa,yaja da baya ya murje qafar tasa ya fice daga wajen.

    Cikin shan jinin jikinta ta soma takawa zata bishi,har tayi taku uku saita waiwayo tana duban widad,zuciyarta na cika da kishin kwalliya da sutturar jikinta

    “Zauna ki kamamin wanke wanken nan ina zuwa”

    “To” ta amsa mata,babu gardama,ta soma ratsawa ta cikin kwanukan tana tattare hannun rigarta,ta zauna kujerar data tashi,ta fara jan kwanukan tana wank su,mimi na mata hira.

    Har ta doshi hanyar sassansa saita tsaya,ta kalli jikinta da kyau,ita kanta ta shaida tsami takeyi,sai tayi ribas,ta koma da baya zuwa bedroom dinta,ta kunna heater a gurguje ta saba sabulu ta dauraye da ruwa,ta tsaya gaban mudubin ta ta balbala turare sannan ta zura wata doguwar rigar baqar atamfa,ta dora daurin dankwalinta sannan ta fito.

    Har zata wuce ta tuna tabar mimi a can,saita koma ta tsaya daga qofar kitchen din tana qwala mata kira,yarinyar ta taso,ta kama hannunta suka bar wajen,tana jefawa widad harara a fakaice

    “Saikin gane Allah daya ne wallahi yarinya,muje zuwa wai mahaukaci yahau kura”.

    A falo ta samu nawwara,tasha chocolate har ta godewa Allah,ta aje mimi a nan ta wuce kai tsaye bedroom dinsa.

    Yana tsaye gaban mudubi yana maida maballin wata jallabiyya mai azabar kyau,hade take da wandonta da aka yima aikin zare daga qasa, lallausan qamshinsa daya karade dakin ta zuqa,tana son turarensa matuqa,saidai ko ya bata bata iya jurewa shafawa kullum da kullum

    Sarai ya hangeta ta cikin madubi sanda take shigowa,amma bai fasa abinda yakeyi ba,hakanan bai waiwayo ba,jikinta ya qara sanyi,ta tako a hankali kanta a qasa,tayi mazauni a kujerar bayansa

    “Sannu da zuwa ya hanya?” Ta sake fadi

    “Lafiya” ya amsa mata a taqaice,ya dauki comb yana sake taje kansa,sannan ya daura agogo ya dauki daddumaersa a qagauce

    “Zanje sallah na dawo,ki gyaramin sashe na” daga wanann ya juya ya fice a dakin,yana jin yadda shegen turarenta daya tsana yake cika dakin,baisan ita din wace irin mace bace,duk abind yake so tofa sunyi hannun riga,kamar ma tana jira yace ga abinda yakeso ta qalubalanceshi,duk wani abu da zaiyi mata don gyara da kyautata rayuwarta yayi amma ita kamar bata maraba da hakan.

    Da kallo ta bishi,kafin ya gama ficewa,tabi qofar da harara tana jan tsaki

    “Mutum sai shegen izza da tsari,daga dawowarsa gaba daya ya batamin duk wani lissafi ba,banda ya taho da waccar yarinyar yaushe na gama wanke wanken,na gyara nawa sashen,na gyara nasa?,sannan daga qarshe yacemin abinci yake jira na dafa masa kamar wata jaka,Allah yau saidai kowa yaci takeaway” ta fada tana sake jan tsaki,ta miqe tana kade zanin gadon da tun kafin ya tafi yake shinfide akai ba’a daga ba,kuma ko yanzun bata da niyyar dagawar.

    *Arewabooks: Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

  • Arubuce Ta Ke 63

    Arubuce Ta Ke 63

    Page 63

    Koda ta hado kayan abincin ta dawo bata sameshi a falon ba,amma taga qofar dakinsa a bude,da alama yana ciki,tadan bata fusja kadan,itafa batason haduwarsu sam,ya gama kalle mata jiki ta yaya zata iya fuskantarsa,amma dai babu yadda ta iya,haka ta taka zuwa dakin nasa roqe da tray din data shiryo komai akai.

    Sanda tayi sallama ta shiga ya gama fidda kayan jikinta,daga shi sai pant na maza iya cinya,a yadda ta ganshi tayi masifar tsorata,don bata taba ganinsa koda singlet ba,hakanan tsahon rayuwarta bata taba ganin wani namiji haka ba sai a kansa,saura kadan ta zubda kayan hannunta,taja baya da sauri tana neman qofar fita amma sai ya rigata isa wajen,yasa hannu ya maida qofar ya rufe,ta bude baki ya tabbatar ihu ko kuka zata masa,sai yasa hannunsa saman bakinta ya rufe da kyau,sannan yasa daya hannun ya karbe tray din daketa tangal tangal a hannunta zai kife ya aje a qasa.

    Dab da ita ya matsa,har jikinsa yana dan gogar nata,sai taji kamar numfashinta zaiyu qaura yabar gangar jikinta,manyan idanunta gaba daya sun fito waje kamar zasu fado.

    Magana yakeson mata amma ta maqale masa a maqoshi,qamshinta dake tashi daga jikinta keson rikita masa lissafi,idanunta masu haske da ruwan hawaye ya cikasu suka soma fusgarsa,yayi ta maza cikin taushi da raunin murya yace

    “Keep silent please….. hajiya tana ciki fa,so kike tace na miki wani abu?,zata batamin rai idan haka ya faru” ya qarashe zancan a narke kamar yaron dake tsoron duka daga mamansa.

    Sake sanya idanunsa yayi sosai cikin nata,itama shi take kallo,wasu irin idanuwa da suka dinga tilasta saukar nutsuwa a jikinta,a hankali yaci gaba da aike mata da wani saqo ta cikin idanuwansa,har hawayenta suka fara bacewa,nutsuwarta ta fara daidaita,kunya ta maue gurbin tsoronta,sai ya sauke hannunsa a hankali daga kan bakinta daya gaji da motsawa yayi laqwas,yaja da baya a hankali ya dauki babbaj towel ya rufe jikinsa sannan ya doshi bandaki,doke sai yayi da gaske,ya cire tsoronsa daga ranta muddin yanason su zauna zama na auratayya mai dadi,sai ya sake kawo kusanci sosai a tsakaninsu,sai ya zama komai nata ya kusanta kansa da rayuwarta,tana da kima da darajar da yake jin dole ya sama mata gurbi a rayuwarsa,saboda ita din kamar isharar mahaifiyarsa abar soyuwarsa ce,ya zama dole ya kimantata ko don farincikin mahaifiyar tasa.

    “Ka rufe qofar fa” ta fada bayan ta hadiye wani abu muryarta tana dan rawa,har ya sanya kai a toilet din sai ya fasa ya waiwayo

    “Ki jira na fito daga wanka tukunna” sai ya shige.

    Jikinta babu kuzari ko kadan ta sulale ta zauna a wajen,wani abu ya fara mata yawo cikin kwanyarta gangar jiki da kuma zuciyarta,a yau daya kusanta kanshi da ita bawai tsoro kadai taji ba,kunya nauyi da kuma wani irin yanayi da batasanshi ya mamayeta,saidai akwai wani irin tsoro nasa danqare a zuciyarta,hakanan yana mata mugun kwarjini mara misali.

    Yana goge ruwan jikinsa yadan kalleta,ta takure waje daya,ta kuma qi yarda su hada idanu,ya saki boyayyen miskilin murmushi,yasan me yake damunta,ya matsa gaban mudubi ya fara shafa mai

    “Kina sane kenan kika shigomin daki ko?,kin rama nima kin ganni babu kaya” yayi maganar yana kallonta ta cikin mudubin,kai ta daga da sauri,suna hada ido ta mudubin kuma saita maida kan nata ta fara qananun hawaye harda rantsuwa ita batasan ya cire kayansa ba,ita bata kalleshi ba,dariya kamar yayi me,wanann wautar tata da quruciyarta wani bangare ne dake sanyashi nishadi,ya gama shirinsa cikin wata armless fara qal din shirt,sai wando daya tsaya masa iya qaurinsa

    “Ai shikenan……”

    “Budemin to zan tafi” ta katsi numfashinsa

    “To zubamin abincin naci tukunna” da sauri ta zuba masa komai ya zauna zai fara ci sai ya kalleta

    “Zauna muci” kai ta gyada

    “Na qoshi”

    “Bakison tafiya kenan?” Kai ta kada da sauri,saita matso ta sanya hannu suka fara ci.

    Suna ci yana kallon idanunta,saidai ko kadan taqi yarda ita din ta kalleshi,yadda cin abincin yayi masa dadi saboda ya saba ci dasu mimi a gida nan kuwa saishi daya…..haka abincin ma yayi masa dadi

    “I can’t believe ke kikayi girkin nan” abinda take son ji dama taji ya yaba kenan,har batasan sanda ta kalleshi ba tana dan murmushi

    “Allah nice nayi,yankan kubewa kawai muneera ta tayani”

    “Wow…wow,,nan gaba ina da great cook kenan,na shirya cin abinci da kyau” murmushi ya subuce mata,tayi qasa da kanta,tana jin dadi sosai har cikin ranta.

    Ganin ya gama cin abincin yana shirin sake zama sai tace mishi

    “Kace idan ka gama zaka rakani fa”

    “Oh yeah,muje to” ya furta yana sanya bedroom slippers dinshi,yana gaba tana binsa a baya.

    Murda qofar kadan yayi,sai ya waiwayo yana dubanta da alamun damuwa kan fuskarsa

    “Ayyah….sun riga sun kulle qofar” kallon qofar tayi sannan ta kalleshi

    “Wayyo Allah na”

    “Ko ayi knocking ne?” Ya fada da sigar jarrabata,taci kuwa jarrabawar da karon farko.ta qara mata kima da daraja mai dimbin yawa a idanunsa,don kai ta girgiza

    “A’ah,ummu ta hana,tace ba’a tashin babba idan yana bacci,hajiya ta gaji tun dazu na gani…..amma saidai…..” Sai kuma tayi shuru tana kallonsa.

    Wani qawataccen murmushi ya saki,idanunsa cikin nata yana jin kamar suna narkewa ne zuwa sassan jikinsa

    “Saidai me?”

    “Saidai na kwana a falo?” Kai ya girgixa

    “Qwarai kuwa” ya fadi sounding seriously,sannan ya fada takawa yana nufar qofar dakinsa,da hanzari ta taka ta bishi,harda riqo masa hannu ba tare data sani ba

    “Da gaske tafiya zakayi ka barni a nan?” Kai ya kada,yanata qoqarin danne dariyarsa

    “Yes,da ina zaki bini?” Marairaice masa tayi,harta fara guzurin hawaye

    “Please mana,kaji tausayina” badon yayi da gaske ba wannan karon dariyar saita fito

    “Oh…. okay,me kikeso yanzu?”

    “Ka barni na kwana a dakinka,nan din tsoro nakeji Allah” ido yq zaro kamar gaske

    “Dakina kuma?”

    “Eh” yadanyi shuru kamar mai tunani

    “Matsalar ni gaskiya ba za’a hanani kwanciya a gadona ba,kuma idan muka kwanta gado daya ina da juye juye,zan.iya danneki ban sani ba,saidai ki tasheni idan kikaji haka saina dagaki,kin yarda?” Kai ta gyada da sauri,saboda kukan mage data fara jiyowa

    “Fine,muje” tuni tayi gaba suka jera kafada dashi, dariyar kamar yayi ke haka ta dinga cinsa,yana sane yayi mata wannan hikimar,banda haka tubura zatayi masa.

    Ta rigashi kwanciya amma idanunta biyu,yana kallonta ta ninka duvet dinsa guda daya ta raba gadon dashi,taja daya ta lulluba, murmushi yayi qasa qasa

    “Zanyi maganinki yau kam” ya fadi yana maida dubansa ga takardun da yake dubawa,sai daya gama komai,sannan ya haye gadon,ya jawo wayarsa ya kunna sound na kukan mage,ya saitashi wajen kanta ya koma ya kwanta abinsa.

    A hankali kukan magen ya fara ratsata daga baccin daya dauketa,dama kuma ba wani nisa can sosai baccin yayi ba,rudewa tayi gaba daya saboda jin kukan a kusa da ita sosai,batasan sanda tayi cilli da katangar data gina a tsakaninsu ba, hankali kwance yaji ta shige jikinsa hadi da qanqameshi,wanan lallausan jikin nata ma’abocin qamshi ya nutse cikin faffadan qirjinsa,sai ya saki wani tattausan murmushi,cikin sanyi ya kamota zuwa jikinsa sosai ya mata kyakkyawar runguma da har sai da zuciyarsa ta gamsu da hakan,ya dora hannunsa a gadon bayanta yana dan bubbugawa

    “Shshhhhhhh…..,zata tafi fa…..yanzu” maganar tasa ta rarrabe saboda yadda ta raba tsakanin cinyoyinsa da qafafunta tana sake shige masa kamar zata koma jikinsa

    “Tana qasan gadon,ka koreta uncle” cikin tsoro take fadar haka,tuni ta soma rikitashi,sai ya dora bakinsa saitin kunnenta

    “It will be alright”furucin da ya sanya jikinta wani zubawa,abinda bata taba jiba tsahon rayuwarta,yanayin da yasa ta sake maqale masa da kyau,ta kuma sanya fitar numfashin sa sake jirkita,ya nutsa hannunsa gadon bayanta ya hade da ainihin fatar jikinta mai santsi a maimakon rigar dake jirkitanta,taji hakan har cikin qashi da bargonta,to amma kuma tsoro ya hanata motsawa,ji yayi kamar kada ya kashe kukan,amma yadda yaga ta tsorata dole badon yaso ba ya zura hannunsa ya kashe wayar gaba dayanta.

    A hankali a hankali ya fara fitar da numfashi da gudu gudu,tun tana tunanin ba komai bane har hankalinta ya kawo kan canzawar da taji yayi,hakanan bugun zuciyarsa sosai yake shiga zuwa ga kunnuwanta dake kwance saman qirjinsa dake shimfide da lallausar gargasa,a hankali ya daga kanta tana duban fuskarsa

    “Uncle…..baka da lafiya?” Murmushi ya qwace masa,gumi na saukowa ta saman goshinsa kadan kadan

    “Am fine,kwanta kiyi baccinki” ya qarashe maganar yana cije labbansa,saboda yadda mararsa ta murda masa

    “Gumi fa kake uncle”

    “I know,na sani”

    “Ka bari na taso hajiya”

    “Aah”

    “To akwai magani na dauko maka?”

    “Kece maganin” ya fada muryarsa tana rawa,sam bata fahimci me yake nufi ba,don batasan ainihin abinda yake damunsa ba

    “Ni kuma uncle?”
    “Yes,but…..ki kwanta kawai nace” ya fada da dan kaushi,saboda ciwon da cikinsa ya fara,jiki a sanyaye ta zame kanta daga jikinsa zata kwanta gefe,sai yasa hannunsa ya tarota

    “No,don’t leave me,stay here,i will be okay” gaba daya sai taji bata da kuzarin musawa,ba wani sauran tsoro tattare da ita,tana jin sanda ya matso da ita zuwa jikinsa sosai,sai taji tausayinsa ya kamata,tana da saurin kuka da karyewar zuciya akan mara lafiya,don haka tasa dukka tafukan hannuwanta biyu a kuncinsa hagu da dama tana masa sannu da muryarta can qasa,abun sai ya zame masa kamar fami,don haka yasa hannayensa ya cire hannun nata,ya kuma jawota jikin nasa still yana cewa

    “Kiyi bacci,good night”.[3/14, 7:17 PM] +234 816 133 8078: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 61

    Page 61

    Kiran farko aka gaya mata user busy,tadan dakata na wasu mintuna sannan ta qara kiranta,cikin sa’a kuwa ta shiga

    “Aah,kaga amaren kaduna” anty deena ta fada cikin tsokana,da yake idan taso tsokanarta haka take ce mata,dariya ta danyi ta gaidata tambayarta yaranta,ta amsa mata da suna lafiya,suka dan taba hirar data shafi gda sannan daga bisani shuru ya biyo baya,sai anty deena dince tace

    “Kina bibiyar kuwa karatun da ake a groups din nan,kinsan kudi na biya kada ki sakani nayi asarar kudina” dariya ta danyi

    “Inabi Allah anty,a ciki ma naga wani abu,nayi kuma to mommy hafsa tanata fada,nace anty ko banyi dai dai bane?” Ta qarasa fada a shagwabe

    “Me kikayi kuma?” Antu deena ta tambayeta,bata boye mata ba ta gaya mata komai,anty deena tayi shuru tana nazarin maganar cikin ranta,zuciyarta na hasaso mata wani abu,amma kuma nataso ta dora nata tunajun ko tunanun yarinyar akan hakan,tunda dukka dan adam ajizine,zai yiwu ajizanci ne da kuma yanayi ma kishi da zai iya motsawa kowacce mace a kowanne lokaci

    “Bakiyi abu mara kyau ba widadun ummu…”

    “Ba wani widad din ummu yanzun fa anty deena ta daina sona,su Aafiya tafiso,kullun mukayi waya sai tace zatazo amma taqi zuwa” murmushi ya kubce mata

    “Zatazo weedad,kullum ummu cikin zancanki take,amma kafin sannan…..inaso kome kika gani ance ayi kiyi qoqarin yinsa,zaki yi?” Ta tambayeta,saita gyada kai

    “Eh anty deena”
    “Yauwa widad dinmu,sannan ko meye kika gani baki gane ba ko ya faru ki kirani,koni ko anty madeena ki tambayemu,ba komai ne idan mommy hafsa tace kiyiwa uncle din naki zaki dinga yi ba kinji ko?”

    “Tom anty deena” sun dan jima suna waya tana sake wayar mata da kai a fakaice sannan sukayi sallama,koda suka gama wayar litattafan ta debo ta sake zabo wasu a ciki ta dora da karatunta,itama tama manta d batun mommy hafsa da duk matsalolinta.

    Rai bace hafsat din ta goge kiran da widad din tayi masa,sannan ta koma dakin ta maida wayar ta ajjiye ta kamar yadda ta ganta taci gaba da zaman jiransa,amma kuna qasan ranta a quntace yake da abinda ya farun,tana zargi da kuma tuhumar kanta,kwana biyu ta watsar da kiran yarinyar bare taci gaba da saita mata hanya,amma fa tana tsoro,kada ya zamana ta hadu da gogaggu kima wayayyun da zasuyi mata karatun da yafi nata shiga,tunda kaduna badai hadakar gamayyar mutane daga gari da qabila kala daban daban ba,amma zata kira ta binciki hajiya amina taji dawa dawa take hulda.

    Koda ya fito daga wankan baisan anyi kiranshi ba,saboda qarar shower ta hanashi jin ringtone din,yana goge ruwan jikinsa tana binsa da kallo,jikinsa luwai luwai, fatarsa mai santsi da taushi sai daukar idanu takeyi, muscles din a hade alamun ya samu kyakkyawan training,ta hadiye wani abu da qyar saboda kishinsa daya tsarga mata.

    Waiwayawa yayi suka hada idanu da ita,saiya dauke kansa yana cewa

    “Ya akayi?,me yake faruwa?” Qaqalo murmushi tayi sannan tace

    “Har yanzu banji kace na fara hada kayana ba”

    “Zuwa ina?” Yayi mata tambayar bayan ya isa gaban madubi yaja lotion dinsa zai fara shafawa,wani abu ya tsarga mata amma ta dake

    “Umara mana” sai daya kalleta ya kuma ci gaba da shafa mansa sannan yace

    “Ban shirya wannan zuwan dake ba,babu kudi a hannuna,ina cewa ma ko wata shida bamuyi da zuwa ba ko?”

    “Eh amma ai musulmi baya gajiya da zuwa” kai ya gyada

    “Haka ne,amma yanxun bani da kudin da xamu iya tafiya mu duka,ke ni da hajiya” ranta ya baci sosai, zuciyarta tayita qissimata mata abubuwa da yawa da zata gaya masa,a fakaice dai hajiyan kusan duk shekara saiya kaita kenan,tunda itama ai baara iwar haka taje

    “Aure ya cinye maka kudin kenan?” Ta tambayeshi tana tsareshi da ido,ya sake waiwayowa ya kalleta,ya kuma karanci yanayinta cikin sakanni,sai ya kuma dauke kansa ya maida ga abinda yakeyi,bayason doguwar magana,hakanan baya qaunar mita da qorafi

    “Idanma hakanne ba mamaki bane” tofa,baki yasan me zai fada amma baisan me za’a mayar masa ba,saita miqe a mugun fusace

    “Allah yayi mana arziqin da zamuyi ta zuwa babu mai hanamu” sai tayi waje fuuuu kamar zata tada iska.

    Ransa ya sosu,amma ko iskar data kwasota bai kalla ba,yaci gaba da shirinsa,kafin ya sanya kayansa ya tsaya ya tsaftace sassansa,ya kuma dafa coffee yasha sannan ya qarasa shiryawa ya fice abinsa,yasan bazai rasa abinci gidan hajiya ba.

    Tun daga wannan maganar ta dauke masa wuta gaba daya,shima kuma ya tattarata ya watsar ya baiwa banza ajiyarsa,yana ganin guga koda baiyi tsiran komai ba yayi na igiya,ta yaya zatayi kishi da mahaifiyarsa ko nawa kuwa zai kashe mata?,ita din ai ba tsararta bace.

    Duka kwanakin da yayi kowa sabgarsa yake,amma hafsa din ta fishi damuwa,saboda tana da buqatar kudi a wajensa,baya ga haka tanason ya dawo da widad din har su dawo daga tafiyar,a wata dayan da zasuyi tasan zata moreta sosai,zata kuma dora mata karatun da zai zauna daram a kwanyarta,amma girman kai da jin tafi qarfin tayi qasa yasa taji gwara tayi shuru duk abinda ma ya yanke shikenan.

    Ta bangaren widad kuwa cikin kwanaki qalilan karatun hausa novels ya shigeta sosai,idan tana karantawa tana jinta ne kamar a wata duniyar ta daban,yana debe mata kewa,tana kuma ganin abubuwan da suke bata mamaki,duk kuwa girki ko drinks din data gani saita gwada,a lokacin kitchen dinta yaga rayuwa,saidai duk abinda ta gwada din idan taga yayi farinciki cikata yakeyi,mai aikin maama(hajiya amina) ke tayata wani bin,tana ganinta kamar latifa saboda kirkinta.

    Ranar da zai baro kadunan zai biya ta gidan hajiya ya daukota su wuce,har ya kammala shirinsa tsaf a sassansa tana nata sashen tana baccinta,don tun daga waccan ranar basu qara hada makwanci ba,tana sashenta yana nasa,yaci alwashin ko meye zatayi badai shi da qafafunsa ya bita yayi begging nata ba,yasan abinda takeso kenan.

    Tare dasu mimi suka fito,a wajensa yaran suka kwana,tsaf dasu don su kansu sai daya shiryasu ya kuma gyara sasssan,suna riqe da hannunsa ya tura ya shiga,falon a hargitse kamar wanda aka tashi taron biki,harsa pampers din nawwara da yayi imanin idan bana shekaran jiya bane na jiya ne

    “Ku zauna nayi sallama da mamanku” ya fada yana kallonsu,sai suka amsa suna hayewa saman kujerar,ya ajjiye luggage dinsa ya nufi qofar bedroom dinta,don ko takalminsa bai fidda ba saboda tsaftar tiles din ma bata gamsheshi ba,duka yayi rod’i rod’i kamar an watsar da ruwan tea ya fara bushewa samansa.

    Sau uku yana knocking sannan yaji ana tambayar waye da cunkusashiyar muryar bacci,gyaran murya kawai yayi,ta taso tana turbune fuskarta daya kacame saboda bacci ta buda qofar.

    Ido hudu sukayi, doguwar rigar wata kodaddiyar atamfa ce a jikinta da aka yiwa adon net,net din har ya soma bubbulewa alamun dake nuna ya fara gajiya da aikinsa,kanta gashinta ne him daya hautsine kamar ciyawar da aka tara za’a ciyar da dabbobi,abinka da baqar fata idan bai shafa mai ba….duk jikinta yayi fari fari,dakin yana fidda irin abinda jikinta ke fiddawa,da alama ya kama ko ina.

    Kansa ya dauke,don takaicinta bazai kasheshi ba,ya fara gajiya da al’amuranta da kullum babu gyara sai gaba da abun yakeyi,ya sanya kai cikin dakin,dole ta kauce masa ya rabe ya shige,sai ya kasa zama,yana kallonta ta tsince pant dinta da bra dake watse a qasa

    “Ina kwana?” Ta gaisheshi murya a cushe

    “Lafiya….mu zamu wuce” ya bata saqo a gaggauce,saboda qagauta da yayi da wanzuwarsa cikin dakin,ya zura hannunsa a aljihu ya fiddo rafa na kudi ya matsa gefanta ya ajjiye mata yana cewa

    “jibi zamu tashi,zamuyi sati uku idan ta kama har hudu ma,saboda inaso zamu tsaya egypt hajiya zataga likita,duk yadda ta kama dai….shikenan babu wani abu?” sai a sannan ta dago ta sake kallon sa

    “Daa ka sani ma baka shigo ba,inda wucewarka kayi da hakan yafi” tsareta yayi da idanunsa yana mamakin furucinta

    “Hafsa…..magana nake miki ta zanyi tafiyar da babu lallai na sake dawowa fa” gaba tayi tana qoqarin komawa cikin bargonta

    “Allah ki yaye hanya” ta fada cikin nuna halin ko in kula taja bargo ta rufa abinta,saidai tuni idanunta sun cika da hawaye,banda qin Allah,da kudin da zataga likitan basai ta haqura ba a biya musu tare,idan suka dawo taga likitan a nan ba,ai duka daya ne,to amma a’ah,wai dole sai an nuna maka iyakarka.

    Sai daya bata kusan mintuna a tsaye yana kallonta ta cikin bargon,zuciya na hasalashi amma ya hadiye ya juya a hankali ya soma fice daga dakin.

    Wuf tayi ta yaye rufar ta kuma sauko daga gadon,da gudu tasha gabansa

    “Au tafiyar zakayi?” Ta fada hawaye yana layi kan fuskarta,kallo daya yayi mata ya kauda kansa,saboda yadda zuciyarsa ke azalzalarsa

    “Tun ba yau ba nasan baka damu da damuwata ba dama,ba abinda ya shafeka da baqinciki na ko walwalata,to kaje,amma ka sani akwai hisabi tsakanina dakai,Allah bazai taba yafe maka ba idan ka zalunceni” ido ya runtse yana jin zafin maganganunta,ya budesu a hankali sai suka kan yaransu,mimi da nawwara suna tsaye daga bayanta sunyi carko carko,da alama sun fahimci wani abune mara dadi yake faruwa.

    Maganganu ne da yawa a ransa da amsoshin da zai bata,amma sai ya hadiye,muryarsa a sarqe yace

    “Naji,Allah ya saka mikin,matsa ki bani hanya” jagale tayi tana kallonsa,sai kuma ta saki qofar ta koma ciki da gudu ta fada gado tana sakin kuka,baiko waiwayeta ba ya matsa zuwa gaba,ya sunkuya yayi kissing goshin yaran sannan ya kama hannunsu zuwa falo ya kunna musu cartoon yayi musu dabara ya fice.

    Har suka kama hanyar kaduna ransa a bace yake amma yaketa dannewa saboda kada hajiya ta fahimta,yasan yanzu zata gaza nutsuwa.

    Sai da suka shiga garin kaduna sannan ya fara tunanin yadda zasu samu widad ita kuma,abinci da zasuci da sauransu,yau dai ba makaranta yasan tana gida,to amma abinci bashi da tabbacin zasu samu,tunda ga wadda a haife ta haifeta ma bata da wannan tunanin,ina ga ita?,ya yanke kawai idan sun isa yana kai hajiya ciki ya koma ya siya musu abinda zasuci ya hada musu da order din abincin dare,gobe kuma ya samu time yayi musu,da wannan tunanin suka shiga unguwarsu.
    [3/13, 12:54 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:huguma*

  • Arubuce Ta Ke 66

    Arubuce Ta Ke 66

    Page 66

     

    Sun dauki mintuna a haka sannan ta daga kanta suka hada idanu,shima ita yake kallo,haka kawai taji wata kunya ta kamata,saboda kallon da yake matan ya mata nauyi sosai a gangar jikinta da zuciya,hakanan bata saba ganin kalar kallon ba a tattare dashi,saita cusa kanta a qirjinsa tana shaqar wani bala’e’en qamshi da fatarsa ke fiddawa

    “Eheenn…..baby na ta fara sanin kunya ne?” Tambayar data sakata ji kamar zata nutse,sai kuma ta janye jikinta da sauri tana fadi cikin fidda idanu waje

    “Hajiya!” Dukkansu bin falon sukayi da kallo,ba hajiya babu burbushinta,sai suka kalli juna a tare,kafin yayi komai ta rigashi miqewa tana narke ido

    “Hajiya fa uncle” amsar da shima bai santa ba,yasan dai yana gaba tana biye dashi,komawa tayi ko ciki ta shige.

    Tare sukayi hanyar dakinta,suna zuwa widad din ta lafe daga bakin qofa,shi ya tura ya leqa,saiya samu hajiyan zaune cikin dakin daga qasan carfet ta miqe qafafunta

    “Oh,hajiya kina ciki kenan” ya fada cikin jin kunya da nauyi yana shafa kansa,mazewa tayi kamar ba abinda ya faru

    “Wallahi,kasan ko yaya tafiya take ba’a rasa jiki da gajiya,kaima ya kamata ka shiga ciki ka huta hakanan,sai Allah ya kaimu anjima”

    “To hajiya a huta lafiya” ya fadi cikin jin nauyi,sai data murmusa sannan ta amsa mishi,ya maida qofar ya rufe sannan ya juyo suka hada ido da widad din.

    Qwalla ce ta cika mata idon tana dubansa a shagwabe

    “Ban mata sannu da zuwa ba”

    “Tace ta yafe,naje na huta,anjima saina rakoki ko?” Kafada ta maqale alamun bata yarda ba,sai ya qara taku ya matsa ya buda qofar kadan

    “Shiga to ku gaisa” nan ma ta sake maqale wuya,sakin qofar yayi ya koma da baya ya rungume hannayensa yana kallonta

    “To ya kikeso ayi?” Hawayen dake maqale ne ya sauko mata

    “Ba kaine ba……kaine ka jawomin Allah” dariya ta taso masa,ya murmusa yana kallonta

    “Ni me nayi tsakani fa da Allah” kuka ta sake masa,da sauri ya kalli qofar dakin sannan ya dawo da dubanshi kanta,ya tako da hanzari ya iso gabanta

    “Sorry….. sorry,kiyi shuru mana please,kafa hajiya taji,nayi alqawari zan rakoki,zan kuma gayawa hajiyan laifin nawa ne shikenan?” Kai ta gyada masa,sai ya saka hannu a aljihunsa ya fidda handkerchief ya soma dauke mata hawayen,idanunsa na manne da manyan fararen idanun nan nata dake yawan daukar hankalinsa,ya jima baiga abu mai daukan hankali kamarsu ba,daga bisani ya sauke dubansa kan mitsitsin labbanta jajaye da taketa motsasu kamar zatace wani abu,tsigar jikinsa ta zuba,ya dauke idonsa daga nan yana cije labbansa,ya gama yaja baya jikinsa na wani irin mutuwa,ko a ina ta samu irin wannan fitinannen turaren?.

    Kasa jurewa tayi ta jashi zuwa dining tana buda masa abubuwan data dafa,a mamakance yake kallonta,baiyi shakka ba saidai mamaki,yasan halinta a dan zamansu bata qarya,at last ya rasa me zaice mata

    “Bari na huta,ki zaba duk abinda kikeso idan na bude jakata a matsayin gift na wannan abincin” murmushi tayi

    “Ni hajiya nayiwa fa”

    “Ya salam” ya fada a qasan ransa yana lumshe idanu, yarinyar ta gama dashi,yasan ta fada ne har ranta da kuma quruciya,batasan hajiyarsa itace weak point dinsa ba

    “Yes…..i know, that’s why nace ki zaba duk abinda kk so,hajiyata duniya ta ce,itace komai nawa” kai ta gyada masa tana murmushi

    Wanka kawai ya sakeyi,ya shirya cikin toilet don kada ma tace zata masa bore,lallabawa yakeyi,yana da buqatar ta a kusa dashi sosai,ko bata kawar masa da qishirwarsa ba dumin jikinta zai masa amfani ko yaya.

    Gadonsa ya haye yana lumshe idanu,qamshin da bedsheet din ke fitarwa har cikin jininsa,idanun nasa a lumshe yace

    “I hope ba muneera kika bari ta shigo dakin uncle ba” kai ta gyada tana murmushi

    “Anty widad ce” sosai ta bashi dariya,har sai daya bude idanuwansa a kanta yana kallonta,tana da wani irin salo da yake sauke masa komai na daga gajiya da bacin rai,yayi mamakin yadda ta iya duka wadan nan aikace aikacen,komai na gidan ya zama akan saiti

    “Anty?,su anty manya” ya furta cikin salon tsokana idanuwansa suna lumshewa sakamakon dankwalin dake yafe a kanta ya silale ya fadi,sassalkan gashinta da aka masa wani irin nadi jiya a saloon ya bayyana kansa.

    Da fuskar shagwaba ta kalleshi,abinda ya qarawa cute baby face dinta kyau matuqa

    “Ni din ko?,ni ba anty bace?”

    “Wait….kinaso a dinga kiranki anty?” Kai ta gyada

    “Good,zan koya miki wani abu,indai kika tsaya kika iya kike yimin,ba anty ba…..har mommy za’a ce miki” ya qarasa fada yana lumshe idanunsa,cikin zumudi take kallonsa

    “Yes,na yarda uncle”

    “Good…..bari na huta sosai tukunna…. Amma,zo muga wannan gyaran kan naki” ya fada yana yfitota da hannu muryarsa na qara yin laushi,bata kawo komai a ranta ba ta rarrafa zuwa gabansa,ta kuma miqa masa kan tana jin dadin yabawar da yayi

    “Anty rose ce ta kaini fa,tacemin ka taba cewa zaka kawo madam ayi mata irinsa dama”

    “Yeah” ya fada da qyar kamar mara lafiya,ya tuna lokacin,hafsa yaso kaiwa,tace bata da wannan lokacin, infact ma tace zaman banza ne da bata lokaci,saboda koda anyin zai yamutse shine da zarar sun dawo,ya kuma sakata zuba ruwa akan,shikenan ya tashi a aiki,gwara ya bata kudin taje ayi mata kitso ko wani gyaran mai sauqi.

    Ajiyar zuciya ya sauke,ya saka hannayensa gaba daya ya birkitota jikinsa,a dan tsorace tayi yunqurin tashi,muryarsa a kakkarye yace

    “Don’t…..do me a favor please,bacci nakeji ki tayani,ko kin fita ma na tabbata ba kowa,just one hour kawai” wani irin abu taji yana mata yawo cikin jikinta a sanda yake maganar wanda ya zare mata duk wata laka ta jikinta,sai kawai ta maida kanta saman dantsensa dake cike da muscles ta kwantar,a hankali ya nutsa yatsun hannunsa cikin sumarta, numfashin ya fusga da kyau kamar zai qwace ya samu ya nemoshi,sai ya cure jikinsa waje guda,yayin da widad din tayi lamo tana jin faduwar gaba da fargaba.

    Tafiyar tsutsa yaci gaba da yi mata saman kanta yana yamutsa gashin da kyau,qamshi da santsinsa yana bashi wani salon nishadi,bai farga ba sai ji yayi tana sauke numfashi a hankali,daya duba yaga bacci ne ya dauketa,ya saki murmushi a hankali yana gyara mata kwanciya cikin jikinsa,ya tabbatar itama akwai gajiya a tattare da ita,don iya ayyukan daya gani tayi ba qaramin qoqarin gasken gaske tayi ba,baima taba kawowa kansa zata iya ba,ko makarantar da rose din ke kaita ya barshi ne kawai suna fita saboda rage zaman kadaici bawai don a koyo komai ba,ashe abun ya wuce yadda ya daukeshi.

    Basu hadu da hajiyan ba sai washegari,saboda ya riqeta a dakinsa,tunda hajiyan ta shiga dakin itama bata fito ba, muneera ce ta debo musu komai takai daki,shima ya dauki sauran yakai musu dakin,daga qarshe sai daya kira hajiyan a wayarsa,tace ta bari sai goben sannan ta haqura,saidai fa gaba daya jinta take cikin wani sabon yanayi,ko yaya ta motsa idanunsa yana kanta,duk bayan wasu mintuna sai ya jangwalo abinda zai bada connection a tsakaninsu,tanata zamewa amma kamar sake diga danqo take a tsakaninsu,shi kansa baisan me yake faruwa ba.

    Tare sukayi breakfast a falon, muneera da widad nata gyaran wajen hajiya ta dubeshi

    “To nifa yau sai gida” da mamaki ya kalleta

    “Ah…haba hajiya,ki bari ki qara koda kwanaki uku ne mana,sai mu wuce tare ko?” Kai ta girgiza

    “A’ah abbas,ai tunda komai ya kammala zaman me kuma za’a yi?,gwara na koma gida na nima nafi hutawa sosai” kafewa tayi tace bauchi zata tafi,da qyar ya sha kanta ta bari sai gobe,idan yaso sai su wuce gaba daya,da wannan maganar da sukayi ya wuce daki yace zaiyi wanka ya fita headquarter ya bada report na dawowarsa,zai kuma sake daukan excuse na three to four days.

    Ya fidda dukka kayan jikinsa yana daure da towel wayarsa ta dauki ringing,ya dawo da baya yana duba me kiran hannunsa a qugunsa,hafsat ce,yayi mamakin ganin kiran nata,tun randa yayi alqawarin bazai sake kira ba bai kuma din ba,hakanan itama koda wasa bata kirashi ba,komawa yayi ya jingina da mirror din dakin ya daga kiran tare da yin sallama,sannan yayi shuru yana jiran jin dame tazo.

    Kamar ba zata tanka ba bayan ta amsa sallamar sai kuma tace

    “Au ashe kun dawo”

    “Eh” ya amsa mata a taqaice,abin ya sake bata ranta

    “Yanzu kayi tafiyar wata guda,ka dawo qasar amma ka kasa gayamin ka dawo abban mimi,adalci kenan hakan?” Maimakon ransa ya baci baisan murmushi ya kubcewa fuskarsa ba,rainin wayonta ya fara yawa,idan tayi wani abun kamar zautacciya

    “Ai baki da buqatar jin komai daga gareni,so kinga baki da matsala dani”

    “Haka ma zaka ce?,duk abubuwan daka yimin kai baka gani?,kullum nice mai laifi a wajenka,kayi tafiyarka daga wajen wata,ka tashi dawowa ka sake sauka a wajenta ba tare da nasan ma ka dawo ba sannan ace ana kyauta min” saita fashe masa da kuka kawai,shuru yayi yana saurarenta,tasan weak point dinsa ne,amma bazai yarda ta raina masa hankali ba,don haka ya aje wayar saman mudubi kawai ya rabu da ita,duk da yana saurarenta.

    Jin tanata faman sharan majina baice mata komai ba ya kuma tunzura mata zuciya,kukanta banza shirunta banza kenan?.

    “Laifi nane da nayi kiranka” ta fada tana shirin kashe wayar

    “Wait…..am on my way tomorrow” baiji ta amsa ba,tadai yanke kiran,duk da haka ya tura mata gajeran saqo saboda ya fita hakkinta yana sake jaddada mata,ya aje wayar saman mudubin yana fidda iska daga bakinsa,hafsat…..hafsat…..ya yarda jarrabarsa kenan a rayuwa,ya taka zai shige bandakin sai yaji an turo qofar,yadan tsaya daga bayan labule kadan saboda yasan me shigowar,kuma tabbas idan ta ganshi a haka komawa zatayi qila harda gudu ma.

    Tana ‘yan waqenta ta shigo,ta cire hular data rufe sumarta,ta zare underwear dinta,ta soma tattare doguwar rigarta zata cire ya motsa,don yasan matuqar ta cire qarshe idan ta ganshi tace shi ya jawo mata kuma ba zata yarda ba.

    Da sauri ta saki rigar, saidai saura data rage ta tattare saman qirjinta dake tsaye cas,idanunsa suka sauka a wajen,yaji wani abu ya tsarga masa,tun daga saman kansa har yatsun qafarsa,kamar sunfi yadda ya taba lura da girmansu.

    Kallon da yake mata da kuma a yadda ta ganshi ya sakata juyawa zata bar masa dakin,taku uku ya isketa,ya jawota cikin jikinsa yana jin yadda jikin nasa ya fara rawa,duk yadda yaso yayi controlling kansa kada yakai hannunsa saman jikinta a yau ya kasa,karon farko a rayuwarta da hannu ya taba kaiwa saman qirjinta,suman tsaye tayi da farko,don yayi mata mugun ba zata,yayin da shima yayi kusan mutuwar tsayen,saboda saqon da suka bayar zuwa ga kowacce gaba ta jikinsa,sun masa ba zatan shima,ya samesu fiye da yadda idanunsa ke wassafa masa.

    Motsa hannayensa daya fara yi ta wajen ya maido mata dukka wani tunaninta,kamar yasan ihu take shirin masa ya birkitota ya hade bakinsu waje guda, hannayensa kuma naci gaba da abinda kwanyarsa ke qawata masa.

    Wani irin tashin hankali ta shiga,ya matseta gam,ba damar ihu ko motsin ceton kai,sai kawai hawaye suka balle mata,tun tana sanya ran yanzu zai saketa harta saare, yaci gaba da aike mata saqon daya dinga sanyata jin kamar zata mutu[3/15, 9:35 PM] +234 704 440 6400: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 59

    Arubuce Ta Ke 59

    Page 59

    Ranar gaba daya wunin falo tayi,tayi kwance cikin kujera ta kasa hasala komai,,haka kawai take jinta wani sukuku,jikinta duka babu dadi,sai bayan sallar la’asar tana kwance kiran anty deena ya shigo

    “Lafiya kike?” Ta tambayeta jin muryarta tayi qasa da yawa,sai ta kama mata hawaye kafin daga qarshe ta gaya mata ya tafi bauchi ya barta ne,abun ya baiwa anty deena dariya,wohoho…… widad har yanzu quruciyar dai tana nan,sai data bata baki sannan tayi mata zancan da yasa ta kirata

    “Akwai watsapp groups da za’a saki,inason kowanne idan an sakaki ki tsaya kibi duk hirarrakinsu kinji ko?,akwai qaruwa sosai qanwata”

    “To anty” ta fada tana gyada kai,sun jima da anty deena din suna hira,sai data debe mata kewa sosai sannan sukayi sallama.

    Washegari haka ta tashi jikinta babu qwari har ta gama shirin makaranta,bayan kowanne minti daya saita kallin dukka wajen da yafi zama ko tsaiwa,sai taji hawaye sun cika mata idanu,tasa hannu ta share da sauri,sannan ta dauki school bag dinta zata fice a dakin,qarar wayarta ya dakatar da ita,ta waiwaya ga inda ta ajjiye wayar saman madubinta,ta koma ta zuba mata ido tana kallon number wayar,sai kuma ta miqa hannu ta dauka.

    Lallausar muryarsa ta bayyana cikin wayar,gaba daya kamar wadda aka bigewa gwiwoyinta haka taji,ta koma da baya ta zauna tana qoqarin amsa sallamar tasa,yana jin sautin muryarta ya saki boyayyen murmushi

    “Ina kwana?” Ta gaisheshi muryarta na rawa

    “Kin tashi lafiya?”

    “Lafiya qalau” shuru yadan ratsa sai yace

    “Baki kirani kinji yadda na sauka ba,tsakani da Allah ba amana,ni ina nan ina tunaninki” wata irin kunya ce ta saukar mata,har taji kamar gata a gabansa,saita saki murmushi tana qunshe fuska

    “Kayi haquri” ta samu kanta da fada,don ko kadan ta kirashin baizo kanta ba,hasalima ita batace ga number dinsa ba

    “Yayi kyau,yanzu me kikeyi?”

    “Makaranta” ta bashi amsa a taqaice,daga nan inda yake ya kalli agogon dake gefansa

    “To a dawo lafiya”

    “Allah yasa” ta fada cikin dan karsashin data samu

    “Babu komai ko?” Shuru ta danyi,da kamar tace masa gidan babu dadi,kamar tace masa jiya da qyar tayi bacci,kamar tace masa ya dawo don Allah,amma kuma saita kasa ta amsa masa da babu,sukayi sallama ta kashe wayar ta barta saman gado sannan ta fito ta cimma driver suka bar gidan,tana jin ta samu wani karsashi Cikin jiki da zuciyarta.

    Wayar yabi da kallo bayan sunyi sallama ya kashe wayar,hafsat data fito daga wanka tayi zaune gaban madubi tana shafa jambakin dole ta sake binsa da kallo ta cikin mudubin,tunda ya fara wayar gaba daya ta tattara hankalinsa a kansa,kusan wannan dabi’arta ce,tanaso ta cinye amma ta kasa,tadan gyara zamanta tana matso jambakin ba tare data shafa ba tace

    “Dawa kake waya ne?” Kansa ya daga yana kallon fuskarta ta cikin mudubin,maimakon ya maida kai ga amsa tambayarta,sai duka tunaninsa suka koma daren jiya tsakanin shi da ita

    “Hasbunallah” ya furta qasan ransa,bacin ranta ya motsa masa amma sai ya kori shaidan

    “Wanka kikayi?” Ya mata tambayar data bata mamaki,a mamakance ta amsa masa

    “Eh,baka gani ba?” Kai ya jinjina

    “I see,but…..zo muje in nuna miki wani abu” ya fada yana yaye lallausan duvet dinsa sabo fil da dole ta sanyashi daukoshi,saboda yazo ya tarar da nashi anci ubansa,tun kafin yayi magana ma tace masa nawwara ce,haka ya tattarashi a daren ya bawa mai gadinsu yace ya yar,shi kuwa ya kaishi baya cikin murna ya jiqashi zai wanke,saidai shi dinma yana wankewar yana tsinewa qazantar hafsatun a ranshi,saboda wani irin gamayyar hadakar dauda ne a jiki harma da guntun kashi dana fitsari.

    Kai tsaye ya shige bandakin,ta ajjiye jambakin ta bishi da kallo,itafa ba wannan takeso ba,bai amsa mata tambayar ta ba,abun yayi mata tsaye a rai tunda taji suna waya da yarinyar,abinda bata taba ji yayi da ita ba,to amma kuma dole ta lallaba a yanzun,bataso suyi tashin hankali,kada ta barar da umrarta,don tunda taji labarin tafiya umarar ranta ya raya mata harda ita a ciki,qilan bai fada mata bane,saboda ya saba,yana da wani irin miskilanci da shan qamshi ta wannan bangaren,ba kasafai idan zai maka abu yake gaya maka ba,har sai dab da faruwar abun,dole ta miqe ta bishi bandakin,zuciyarta nq raya mata dole ta kira yarinyar tabi ba’asi,ta kuma sake kada mata warning,dama ranta a bace yake tunda taga yazo babu ita,don ta hada himilin qazantarta,mai wankinsu ya gudu amma yace mata yana qauyensu,tana ta jira fa taji wayam,dole ta tattara duk wasu tarkacen kayayyakinta takaisu store din bayan gidan ta kulle saboda abbas din,ta tabbatar idan ya gani sai yayi fada,ita batasan uwar daya sanya yanzun sai yayi zuwa biyu baizo da ita ba,ko a yanzun wannan kusan zuwasa na biyun kenan,idan ta bigi cikinsa sai yace mata makarantar ya sanya haka.

    Tana shiga bandakin yana tsaye da clipper a hannunsa yana daurata,ya daga tsimammun idanunsa dake motsa mata soyayyarsa koda bata shirya ba ya kalleta

    “come closer” ya fada yana kallonta,kamar zata musa masa kota tambayeshi dalili sai kuma ta fasa,ta matso din kamar yadda ya buqata,bata kawo hakan a ranta ba kawai taji ya sanya hannu zai ware towel din jikinta,da mugun qarfi ta kama towel din ta riqe tana kallon idanunsa

    “Me zaka yimin da safiyar nan kuma?” Ta tambayeshi ranta a bace,mamakinta ya sake cikashi,yana sane yace mata

    “I want to be with you” ido ta zare ranta a bace

    “Haba don Allah,duk abinda kayi jiyan bai isheka ba?, al’amuranka are getting worst gaskiya abban mimi, jiyan kamar zan mutu fa” bai amsa mata ba illa hannu daya daya saka ya fincikota,ya ware towel din,ya kunna clipper din ya daga hannunta ya fara kwashe mata gashin hammata,sai tayi shuru tana kallonsa,fuskarsa a hade,kunya ta kamata,ta rasa yadda zata nade masa tabarmar kunya da hauka,har ya gama sannan yace mata

    “Kwanta na qarasa miki sauran,tunda bakisan yadda akeyi ba”yafadi ba tare daya kalleta ba yana goge gashin daya bata jikin clipper din, fuska ta bata

    “Kawai da ranar Allah saina yaye maka jikina,kai ba zaka ji kunyar kalla ba?” A nutse ya daga kai yana kallonta,ko yaushe mamakinta kasheshi yakeyi,kamar wata jahila ko wadda batasan meye aure ba,ya zuba mata idanunsa da suka sanyata tadan daburce,sai tahau quna quni

    “Zanji kunya mana,wannan uwar gayyar da kika tarawa wajen ai dole aji kunyar kallansa” batasan abinda zai maida mata dashi ba kenan,sai zancan nasa yayi mata ciwo

    “Me kake nufi?,daga fadin gaskiya zaka mayar min da baqar magana?” Baice mata komai ba,ya qarasa gefanta inda take tsaye ya ajjiye clipper din ransa ya suya,kome zaka.mata a duniya baka iya ba,bakuma zaka fita ba

    “Kada ki fito baki kwashemin wannan go slow din da kika tarawa wajen ba” ya fada adan zafafe ya qarasa sink ya wanke hannunsa da detergent ya fita yabar mata toilet din.

    Binsa tayi da kallo idanunta na hada qwalla,to wai ina ruwansa da sumar wajen?,badai ta bashi abinda yake nema ba?,why not zai dameta harda baqar magana?,banda tasan halinsa sarai tana kuma tsoron hukuncinsa da ba zata aske ba,tasanshi hukuncinsa bashi da dadi idan ka kaishi bango.

    Ko kafin ta fito ma shi tuni ya gama gyaran sassan nasa,suna falo suna breakfast shi da yaransa,wucesu tayi tana shan qamshi,ita ala dole ya bata mata rai,can qasan ranta kuma kunya ce fal bayan ta gama askewar taga uban tulin gashin data tara,taji kuma iska tana ratsata, baibi ta kanta ba shima,don idan da sabo ya saba da irin wadan nan dabu’un nata.

    Wankansa yayi ya shirya ya kuma shirya yaran,ya aikasu ta saka musu kaya,taja tsaki

    “Wato baima san tanayi ba,ficewarsa zaiyi kenan,me yasa ne duk fushin da zatayi baya iya lallashinta?” Ta tambayi kanta zuciyarta na quna,haka ya figi yaran ta watsa musu wata shadda ta kadasu daga dakin.

    Sanda suka shigo sai daya dakata daga taje sumarsa da yakeyi,ya juyo yana kallon kayan jikin nasu sosai,gezner ce mai mugun tsada daya siya musu kwanan nan da aka qara masa girma su da mamarsu,ya kuma biya kudi mai yawa aka muau dinki mai tsada,ita mamartasu tun randa suka fita a hannunsa bai taba ganinta a jikinsa ba,su kuma bai tashi ganinta a nasu jikin ba sai da wannan muguwar kamar,gaba daya ta fita hayyacinta,kamar ma ta soma dafewa,ga wata muguwat squeezing da sukayi

    “Allah ya kyauta”kawai ta fadi bayan ya taba shaddar ya tabbatar itace

    “Daddy mu tafi,daddy tare zamuje ko?” Mimi ta fada,saiya gyada mata kai,tausayinta na cikashi,sam bata damu da yanayin da kayan jikin nata suke ba

    “Muje na canza muku kaya tukunna” ya fada yana hada kansu suka wuce sashen hafsa din.

    Gaba daya dakin a qazance yake sannan a hautsine,dama kusan kaso casa’in na gyaran dakin shike musu,idan ya gama nasa gyaran saiya hada da nasu,yana saka ran kuwa ba’a sake bi ta kansa sai idan ya sake zuwa wani weekend din,baya qaunar yadda taje barin rayuwar yaransa cikin qazanta,yara mata ne,wataran dole gidan wani zasu,uwa uba ma lafiyarsu,yana tsoron wata cutar a tattare dasu,haka ya dinga hadiyar bacin ran bayan ya bude cupboard dinsu,duka kayan ma baya ganesu,baya gane masu wanki da wadanda babu wanki,ga kaya cike da cupboard din amma babu na zabe,ya zubo dasu duka,ransa a mugun bace,wai me yake damun hafsat ne?,kayan yaranki kamar na mahaukata?,banbancinsu kadanne?.

    Wayarsa ya zaro yayi kiranta,don bayason su hada fuska ma ta qara tunzurashi,tana ganin kiran taqi dagawa,har ya gaji ya tura mimi tayi kiranta.

    Sai data mula sannan ta taso,ta tura qofar suka hada ido,saita kauda kanta saboda yadda taga bacin rai baro baro saman fuskarsa,tayi gefe da kanta tana jiran jin tashin boma boman fada,saboda ta hangi himilin kayan yaran daya watso qasa

    “Meye matsalar me muku wanki?,bai iya bane?” Ya tambayeta calmly yana qoqarin dannar kansa,duk da can qasan ransa wani irin bacib raine kecin zuciyarsa

    “Kawai yaron bashi da mutunci ne,ba kasafai nake bashi wanki ba” ya jinjina kai kawai,saboda yasan ta fada ne kawai don ta kare kanta

    “Shi kuma engine wankin gidan fa?”

    “Ya lalace wata hudu kenan” wani abu mai tauri ya hadiye,ransa na baci, engine ma ya lalace amma ta buda baki ta gaya masa ba zata iya ba?

    “Yayi” kawai yace da ita,saita saki handle din qofar ta juya ta fice abinta

    “Ka qaraci jarabarka kai kadai” tafada can qasan ranta tana buga tsaki.

    Wayarsa kawai ya zaro ya kira hajiya

    “Ka iso ne?”

    “Ina dai hanya,muneera zaki turomin gida yanzu”

    “To gata nan” ta fadi ba tare data tambayi ba’asi ba,amma cikin ranta tana addu’ar Allah yasa lafiya.

    Babu dadewa kuwa sai gata,ya sakata ta zauna ta ware sababbin da rashin tsafta da kulawa yasa suka lalace,sauran kuwa yace dukka ta samu manyan buhu ta duresu ta fita dasu,hakan kuwa tayi,yasa takai waje ta baiwa mai gadi,sauran masu kyan ta saka masa a booth din motarsa ya sakasu a gaba suka fito a dakin.

    Jin motsi ya qaru a gidan da surutun yaran yasa ta kasa zaman dakin,tayita kai kawo tsakanin dakinta da kitchen tana kallon qofar dakin nasu tanaso taga waye yazo,dai dai sanda ta fito daga kitchen din muneera ta fitowa da jakar kayan dasu mimi, cikin girmamawa ta rusuna tana gaidata.

    Fuskarta kadaran kadaham ta amsa mata tana kallon jakar kayan a hannunta,shikam tuni yayi gaba,sai itama muneera tayi mata sallana tabi bayan uncle din nata.

    Baqinciki kamar tayi me,tabi yarinyar da kallo,tabbas shike sake wulaqantata tare da basu damar da zasu gaya mata magana su kirata da qazama,ya kira yarinya har cikin gidanta cikin dakin yaranta ta kwashi kaya an fita dasu,tome za’a je ayi mata da kayan yara?,da wannan bacin ran ta dinga mita da.surutu ita kadai a cikin gidan,banda tana shakkarsa saita tsaidasu tabi ba’asi,kai da babu ma mai daukar mata kaya ya fita mata dasu a cikin gida,saidai ta sani,bacin ransa bashi da dadi,dole tana jiyo qarar motarsa ya tasheta suka fita a gidan.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [3/12, 9:02 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 58

    Arubuce Ta Ke 58

    Page 58

    Tsakanin shi da itan zamu iya cewa wasu irin mutane ne da miskilanci yake gudana a jininsu,saidai duk da wannan hakan bai hana sabo da sakewa a tsakaninsu ba,kamar ko yaushe,safiyar ranar juma’a ce,suna kitchen ita dashi,tana sanye da abaya mai santsi peache color me turuwa kadan,wanda daga cikinta riga da wando ne straight leg,duk da basu matseta ba amma sun fidda aihinin shape nata,shi yasa ya dora abayan a kai,haka kawai tayi sha’awar sanyasu,taga hotunansu cikin wayar wata ‘yar ajinsu yayarta ke sayarwa,data duba kayanta taga tana da irinsu,kaf ire iren wadan nan kayan nata suna hade ne a waje daya,bata taba gwada sakasu ba,tana ganin kamar kayan ‘yan iska ne.

    Manyan kalba da aka yi ma kanta guda hudu masu kauri da tsahon jela,biyu suka zubo gefe da gefen fuskarta,suka kuma sauka mata har kafada,sauran biyun kuma suka sauka a gadon bayanta.

    Yau din abbas na saman cupboard a zaune kawai yana latsa waya,saboda tunda suka tashi da safen tana gaidashi tace,saita langwabe kai gefe guda tana wasa da yatsun hannunta

    “Yau babu abinda zaka koyamin,I want to surprise you” she is always like a baby,haka take maganarta cike da quruciya,daya daga cikin abinda yasa yakeson yaga tana magana,kota dake da gasken gaske tana zuba wautarta,amma ita a nata ganin a dai dai take komai.

    Yadda ta ritsashi da idanu bayan ta gama maganar ya sanya dole murmushi ya qwace masa,irin miskilin murmushinsa da ko haqoransa baka fiya gani ba,ya dage girarsa dukka biyun sama yana kallon tsakiyar qwayar idanunta

    “Really?”
    “Yes” ta amsa da amsa amo cike da qwarin gwiwa,sai ya girgiza kai yana qaramar dariya

    “Zamu gani,in zauna yau abina kenan?”

    “Eh mana,na baka hutu” ya fidda sauti kadan,yayi tsalla daya ya haye sama yayi zamansa,saita bishi da ido tana fidda manyan idanunta waje,wasu irin fararen manyan zagayayyun idanuwa da suka dauki hankalinsa a karon farko,har baisan yayi subutar bakin tambayar ta

    “What?” Ya fadi yana jin wani abu nason masa tasiri,qaramar dariya mai cike da sakalci tayi

    “Tsallae daya fa kayi uncle ka haye?” Murmushi ya sake subuce masa,ya girgiza kai

    “Shine kika bude dukka wadan qwala qwalan idanun naki zaki cinyeni dasu?” Baki ta tabe kamar yadda qaramin yaro keyi idan zai saki kuka,abinda ya sake shagaltar dashi da kallonta kenan,siraran labbanta kamar ta shafa musu jambaki

    “Qwala qwala fa kace uncle”

    “I don’t mean qwala qwala marasa kyau,u have a beautiful eyes dear” ya fadi yana duban qwayar idanunta,kawai sai taji wani irin kunya ta kamata,ta saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta,hirar ‘yan ajinsu ta fado mata,daya daga ciki dake basu labarin yadda saurayinta yake kodata,haka akeji dama data taba ce musu kunya takeji?.

    Zara zaran yatsuntsa data rufe fuskarta dasu yabi da kallo,farare tas,hatta da farcenta fari ne qal babu digon komai a jiki

    “Me kike tunani?” Taji ya sake fada

    “Ba komai” ta amsa masa da sauri tana sauke hannuwanta daga fuskartata,gani take kamar zai karanto abinda ke cikin zuciyarta

    “Kin manta am a police,da tsalle daya muna iya hayewa saman gini dake da tsahon da yafi na wannan,kin tuna?” Kai ta gyada tana murmushi,saita kasa ci gaba da cewa komai saboda yadda yake kallonta tsakiyar idanunta yana sanyata tana jin wani iri.

    Shuru kitchen din ya dauka,yayin data buda wayarta tana duba recipe na abinda zata dafa din,tana daukowa daya bayan daya tana ajjiyewa,har ta kammala ta fara aikinta.

    Haka kawai ya samu kansa da daga kai time to time yana kallonta,hakan ya sanya duk kai kawonta take yinsa cikin idanunsa ba tare data ankara ba,aiki yayi aiki,taja igiyar rigar ta daureta don tafi jin dadin yin aikin,saidai abinda bata sani ba,gaba daya ta fidda shape na mazaunanta qugunta da kuma qirjinta.

    Ya sake dagowa yaga a inda girkin ya tsaya idanunsa sukayi kyakkyawan gani,yaso janye idanun nasa amma sai ya kasa,karon farko kamar an zare masa laka daga jikinsa,yaso ya maida kai ga wayarsa amma sai yaji ya kasa,dole ya kashe abinda yakeyi din,ya aje wayar a gefe,ya jingina da bango ya harde hannayensa a qirjinsa ya zuba mata idanu.

    Sam batasan yana kallon ta din ba,saboda ta bada hankalinta gaba daya ga abincin,tanason yayi dadin da zai yaba mata,ta waiwayo zata dauki chopping board har ta juya ta fara yanka albasa jikinta ya bata kamar kallon ta yake,tana juyawa sukayi ido hudu,sai gabanta ya fadi,ta juya da sauri ta saki igiyar rigar tata,ta koma shapeless kamar yadda take idan ba igiyar a jiki,jikinta yadan dauki rawa kadan,ta sunkui da kanta tana yankan da sauri sauri.

    Bata son kallo ko kadan,bare shi da a duk sanda ya kalleta sai taji nashi idanun kamar sun banbanta dana kowa,ta fara nisa a tunani,don haka har ya sauko daga inda yake zaunen,ya tako a hankali ya tsaya a bayanta bata jishi ba.

    Sosai ya zuqi qamshin splash da jikinta ke fitarwa kadan kadan yana kadawa hagu da dama gaba da bayanta,taku biyu ya qara ya sake rage kusancin dake tsakaninsu,sai a lokacin taji kamar iskar dake bayanta ta canza da wani kalar qamshi na body mist na daban.

    Cikin hanzari ta waiwayo,ta manta da wuqar dake hannunta tana datsa albasa,tariga ta dora ashe saman yatsanta ne,tayi wurgi sa wuqar tana yarfar da hannunta gefe daya,saidai duk da zafin da taji kusancin shi da ita yafi daga mata hankali,ta kafeshi da idanu qirjinta na wani irin bugawar da bai taba yiba,ta kuma ja baya sosai har ta qure da jikin kitchen cabinet din.

    Kallon kallo aka shiga yi tsakanin shi da ita,a hankali ya sanya hannunsa ya lalubo hannunta data yanke din ba tare daya janye idanunsa daga cikin nata ba,sai daya sanya hannun cikin tafin hannunsa sannan ya maida dubansa akai.

    Kusan lokaci daya suke duban hannun shi da ita,sannan suka kalli juna

    “Kinga abinda kikayi ko?” Ya tambayeta da wata shaqaqqiyar muryar,kamar jiransa dama takeyi sai ga hawaye ya cika mata idanu

    “Kaine fa ka bani tsoro” dariya taso bashi amma ya dake,saiya langabe kai kamar yadda yaga tayi

    “Banda ke banga wadda take tsoron mijinta ba” kamar ya tunzurata,don batason kalmar miji,sai ta fara qoqarin zame hannnunta daga cikin nashi

    “Ni ba mijina bane kai”

    “To waye ni?” Ya tambayeta yana dage girarsa sama

    “Uncle” kai ya girgiza kawai yana sake sakin boyayyen murmushi

    “Riqe uncle dinki,banaso,let me treat your wound first” ya fada yana sake kamo hannunta.

    Kujera ya saka mata ta zauna akai,sannan shima ya jawo wata ya zauna,har gwiwoyinsu suna haduwa da juna,ya bude first aid kit din ya fada wanke jinin,yana yi tana rintse idanu,ya daga idanunsa ya kalleta,idanuwansu suka hadu waje daya,sai taji hakan ya mata nauyi sosai,ta kauda nata idanun numfashin su yana gauraya da juna.

    Har ya gama mata babu wanda ya sake cewa komai,ya sakar mata hannun yana hade kayan waje daya

    “Jibi idan Allah ya kaimu zanje bauchi” kallonsa tayi da sauri,hakanan kwanakin nan sai ta dinga jin batason zuwa garin

    “Zanje nayi one week,zamu taho da hajiya,the next day zamu wuce umara ni da ita in sha Allah” zuwan da yace hajiyan zatayi taji yayi mata dadi,har zumudinta ya bayyana a fili

    “Amma wata daya ya kamata tayi,ko ka dawo da ita nan kawai” ta fada tana langabar da kanta,cak ya tsaya yana kallonta,yaji mamakin jin furucin daga bakinta,abinda bai taba ji daga bakin hafsat ba tsahon zamansu da ita

    “Hajiya ba zata zauna ba” ya amsa mata yana miqewa riqe da kit din.

    Koda ya dawo sai ya fara rolling hannun rigarsa zuwa sama,tana daga zaune tana kallonsa har ya gama,idanuwanta suka sauka kan lallausar gargasar dake lullube da hannunsa,abar da take yawan burgeta ba tare da tasan dalilin ko kuma amfaninta

    “tell me what you are cooking sai na qarasa” idanu ta narke

    “Zan iya qarasawa uncle,don’t spoil it” girarsa ya daga ya watsa hannayensa

    “I will finished it anyway idan ma baki gayamin ba” ya fada yana qarasawa,ya bubbada tukwanen

    “Kin kusa gamawa ai” ya fada ba tare daya juyo ba,yana mamakin qoqarin da tayi,kai ta gyada masa.

    A nutse yake ci gaba da aikin,har ya kammala,duk inda ya motsa idanunta suna biye dashi,yana ankare da ita amma bai nuna ya ganta ba,har ya kammala,zata karba gyara kitchen din shima ya hada ya gyara komai,mamakinsa sake cikata yakeyi kullum,shi kam baya jin aiki ne?.

    ************Tana nade saman kujerar falon,tayi lamo kamar ‘yar magen data samu waje mai laushi,sanye take da atamfa dinkin riga da skert na atamfa,ta yane saman kanta da dankwalin atamfar,jikinta na fitar da tattausan qamshin turarenta,daga gaba kadan kujerar ta uku daga gefanta,abbas ne a tsaye yana qarasa zuge jakarsa ta tafiya,yanayi yana amsa waya daga office,har ya kammala,ya kashe wayar ya sanyata a aljihu,ya dauki jakar ya rataya a kafadarsa.

    Sai a sannan ya waiwayo inda take zaunen,yadan zuba mata idanu yana karantar yanayin fuskarta,duk sanda zayaje bauchi indai bada ita bane sai yaga wannan damuwar a tare da ita,saidai a wannan karon damuwar kamar tafi ta kowanne lokaci.

    Yadda tayin kamar wata marainiya ya bashi tausayi da kuma dariya,ya taka a hankali ya tsaya a gabanta,ya miqa mata dogayen lausasan hannunsa.

    Hannun tabi da kallo kafin ta mayar saman fuskarsa dake dauke da wani irin haiba da wani sirritaccen kyau da ba kasafai kake iya hangensa farat daya a fuskarsa ba,har cikin zuciyarta takejin wani iri babu dadi,saboda wannan ne karon farko da zaije yayi sati daya,kwana biyu rak yake ya dawo duk sanda ya tafin,idan da itane ma suke kwana uku.

    Sake miqa mata hannun yayi,saita noqe hannun nata tana lumshe idanunta hadi da kwantar da kanta tsakanin cinyoyinta.

    Murmushi ne mai sauti ya kubce masa,cikin taushin murya yace

    “Get up,tashi muyi sallama” curewa tayi waje daya,saita saki kuka kawai

    “Ya rabb”ya furta yana sauke jakarsa daga kafadarsa ya ajjiyeta a qasa,sannan ya duqa saman gwiwarsa a gabansa

    “Na gayawa hajiyane baki barni inje na daukota ba?,ko na gayawa maman mimi baki amince naje muyi sallama ba?” Furta sunan mommy hafsat da yayi ya sakata zabura,ta kuma daga kanta da sauri,sunanta kawai na sanya gabanta faduwa,hajiya kuwa tana jin nauyi da kuma kunyarta fiye da yadda baki zai furta,dukkansu babu wanda zataso ya gayawa abinda yace zai gaya musun.

    Kai ta girgiza masa da sauri,ya lumshe idanunsa ya kuma budesu duka a tare

    “Wipe your tears” hannu biyu tasa ta goge hawayen yana kallonta, cikin ransa yana jin wani irin yanayi daya gaza tantance wanne iri ne,a yau apart from hajiyansa,yau ga wata halitta dake amsa sunan matarsa tana jin babu dadi wai don zaiyi nesa da ita,a wajen mutum guda yake ganin hakan….. hajiyan sa,babu na biyun sai a yanxun da yake gani daga wajenta.

    Sai daya hilaceta ta dan saki jiki,sannan ya miqe ya dauki luggage dinsa yayi mata sallama ya fice,tana tsaye a jikin window har motarsu ta tashi suka fice daga gidan.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[3/12, 9:02 PM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 54

    Arubuce Ta Ke 54

    Page 54

    Tana tsaka da game din taji mararta ta murda,ta dakata tana zare idanu jin wani abu mai danshi ya fara fitowa ta jikinta,gabanta ya fadi,kada dai ace wannan jinin ne da bataso yazo mata?,yanzu ya zatayi?,yi na qarshe da tayi suna tare da latifa,hankalinta a kwance yake,ta dinga kula da ita da ciwon mararta.

    A tsorace tadan miqe don duba jikinta,sai tayi sauri ta koma ta zauna saboda mararta data murda mata,ta dafe marar tana jin yadda danshin ke biyo jikinta,hankalinta ya tashi sosai,kawai sai kuka yazo mata,tana ganin kamar ba zata iya ba. gumi ya fara yanko mata ya gauraye da hawaye,ta soma jan majina tana raba ido.

    Sallamar da yayi cikin falon ya sanyata sake tsorata,sai taji kamar ta tashi ta zura da gudu,idanunshi a kanta,cikin mamakin yanayin da ya ganta a ciki,itama shi take kallo kamar wacce ta aikata wani mummunan abu.

    A nutse ya qaraso,hannayensa zube a aljihun wandonsa

    “What’s happening?,lafiya?” Tsareshi taci gaba dayi da idanu,saidai qwalla ta cika idanunta fal,har bata iya ganinsa sosai,kallonsa take kai tsaye,kamar mai tsoron wani abu dake a jikinsa,maimakon ta amsa masa sai hawayen ya fara saukowa,ta sake dora hannunta saman mararta dake qara murda mata.

    “Me ya faru ne?” Ya sake maimaita tambayar yana sake qoqarin karantar fuskarta,hawayen dai taci gaba da fitarwa,a hankali idanunsa ya sauka saman hannunta,yadan kalli wajen na tsahon wasu mintuna,sai ya matsa gaba a hankali yana qoqarin miqa hannunsa,sai kuma ya janye yana duban qwayar idanunta

    “Ciwo cikin yake miki?” Kai ta gyada masa,Hawaye na sake saukar mata,sai ya sake matsowa yana cire hannunsa guda daya daga aljihunsa

    “Oh sorry….sannu,tun yaushe?”

    “Yanzu” ta fada a narke, zuciyarta tana karyewa,saboda komai yayi mata tana kallonsa banbarakwai,don ba haka ummu ta saba mata ba,indai tace bata da lafiya gaba daya komawa take kamar jinjinniya a wajen ummu,ta yita tattarota tana langabe mata a jiki,takanyi kamar ta maido ciwon a jikinta

    “Muje kici abinci,sai mu fita na kaiki kiga likita ko?” Kai ta girgiza da sauri,don ita bata qaunar ma abinda zai sanya ayi mata zancan asibiti,bata qaunar magani sam sam sam,babban abinda yake saka a gansu a rana ita da ummu kenan

    “Why…..zaki zauna ne a gida cikin yana miki ciwo?”

    “Ai zai daina” ta fada muryarta na rawa,saboda yadda ciwon ya fara mata azaba da gaske,wannan shine karo na biyu daya taba mata haka,duk da cewa duka duka period din nata ma wannan shine yinta na hudu.

    “it is not possible ki zauna da ciwo,oya……taso kici wani abun ko kadanne idan ma ba zaki asibitin ba” ya furta yana miqa mata lallausan hannunsa mai dumi,wanda ya wadatu da sassanyan qamshinsa.

    Hannun ta kalla sannan ta rintse idanunta da gaske tana jin yadda ake kartar mararta,yadda tayin sai ya tuna masa koda wasa ba zata taba yarda intentionally su hada hannu ba,don haka kansa tsaye ya miqa hannu ya kamo.hannunta guda daya,ya kuma dagota gaba daya.

    Luuuuu ta tafi jikinsa ba tare data shirya ba saboda wani azabar murdewa da marar ta sakeyi fiye da dazun,kamar numfashin ta zai bar gangar jikinta,take ta zabi bin gangar jikinsa ta yiwa kanta madogara,tana gama samun kyakkyawan masauki saita saki kuka tana kiran sunan ummu,hannayensa ya saka gaba daya ya rufeta da kyau cikin jikinsa.

    A yadda ta samu masauki me kyau cikin jikinsa ya sanya hatta da bugun zuciyarta da kai kawon numfashinta tana jinsa sosai cikin jikinsa,kamar jininsa suke bi cikin kowacce bugawa da zaiyi.

    Sunkuyo da tasa fuskarsa yayi ta gefen fuskarta dake kwance kan qirjinsa da yake ya fita tsayi sosai ya cusa tasa fuskar yana leqata,wani irin kuka take a hankali hade da sheshsheqa,hucin numfashin ta ya daki fuskarsa,sai ya lumshe idanunsa tsigar jikinsa na tashi,ya sake riqeta sosai zai motsa,saita kuma qanqameshi tana sake sakin kukan,abinda ya sanyashi kusan daskarewa a wajen,gaba daya ta manna masa jikinta da kyau,lallausar fatarta takai ko ina a jikinsa ba tare data sani ba,ita din kuma tayi hakane saboda batason su motsa daga wajen,ta tabbatar ta bata wajen da jini,bataso kuma ya gani,kunya takeji,da wanne ido zata kalleshi?.

    “Let’s move from here,mu koma daki ki kwanta na fidda mota kiga likita,jikinki shacking yakeyi” yana fada ya sunkuya kawai ya dauketa cak,bata da sauran zanbi sai kawai ta boye kanta cikin jikinsa,bayan ta saka hannu ta riqeshi da kyau.

    Bai lura da komai ba sai daya shimfide ta saman gadonsa sannan yaga hannunsa ya baci,ya daga kai ya kalleta,sake saka masa kuka tayi,abinda taketa gudu kenan,ta rintse idanu tana jiran jin fada ko duka daga wajensa,kamar yadda yaa ma’aruf ya taba mata saboda kawai ta kawo abinci ya bata flask din ya riqe hannunsa ya baci.

    Maimakon taji abinda ta zata saima jiyo sautin ruwa da tayi a toilet,ba jimawa ya fito da alama wankewa yayi,suna hada ido ta dauke kanta hawayen naci gaba da sauka,ciwo da kunya duka suka hadar mata,ya qaraso gabanta a hankali ya tsugunna

    “Dama kina period ne?” Wayyo Allah,ji tayi kaman zata nutse a wajen,ta jawo filo ta cusa kanta tana sake sakin kuka,wannan abun sam bai kyauta mata ba,inda ta san zaizo gida zata dage sai ya kaita.

    Sake maimaita mata tambayar yayi amma shuru, ganin da gaske ba zata amsa mishi da komai ba,taqi daga kai ma ta fuskanceshi,sai kawai ya miqe yana murmushi ya fita a dakin.

    Da kansa ya gyara wajen data bata din a falo,wajen bashi da wani yawa sosai,ya dauki waya ya kira na ‘yan mintuna ya kashe.

    Da pad ya dawo mata,ya ajjiye mata yace ta shirya zai fiddo mota suje asibiti,yana zaune a falo ya dora qafa daya kan daya yana amsa waya ta fito tana rab’e rab’e,kunya kamar qasa ta tsage ta shige,wayar na a kunnensa ya waiwaya ya dubeta,can qasan ransa fal dariya,duk da babu ko alamun hakan a saman fuskarsa,ya jima baiga yarinya mara wayo mai tsananin tsoro da kunya irinta ba,iya period kawai data fara ya gani?,inda ace ya karba budurcinta ne fa gaba daya?, Shi kansa daya raya zancan a ransa sai daya sake maimaitawa,sai kawai qaramin murmushi ya kubce masa,ya cije lips nasa na qasa kadan saboda yadda yaji jikinsa ya amsa gaba daya,baisan lokacin da hakan zai faru ba,amma tabbas duk sanda ya kasance qila saita kusa mace masa saboda tsoro.

    Wayar ya kashe ya mayar aljihu sannan ya miqe,ya tako kadan gabanta

    “Zaki iya tafiya?” Kai ta jinjina masa ba tare da ta iya kallonsa ba

    “Muje to na gani idan zaki iya din” ya matsa gefe yana kallonta,ta rabashi a hankali ta fara takawa tana hada hanya,taku uku ya cimmata,ya riqo kafadunta suka ci gaba tafiya,tanason zare kanta,amma hakan da yayi mata saita dinga jin kamar relief yake bawa ciwonta,a haka suka qarasa,ya buda gaban mota ya sanyata ya kwantar mata da kujerar,sannan ya shiga ya tayar da motar suka fice daga gidan.

    Da yake private hospital ne basu samu wani layi ba suka samu ganin likita,duk tambayoyin da yayi mata kusan shuru tayi,tanajin kamar ta narke,maza biyu a daki guda suna mata tamba game da period dinta,abinda ko acikin gidansu boyewa take ba kowa yasan ta fara ba, murmushi likitan yayi ganin lokaci lokaci tana satar kallon abbas

    “Yallabai,da alama kai din ba yayanta bane na hannun dama,ko zaka bamu waje qilan tafiyin bayani” haka kawai cikin ransa yaji bazai iya barinsu su kebe ita dashi ba,don yaga baima fahimci matar aure bace,yayi yunqurin miqewa da nufin matsawa daga koda zuwa bakin window ne,saiji yayi caraf an kamo hannunsa,ya waiwaya a hankali,itace ke kallonsa tana qwalla

    “Kada ka tafi please” hada ido sukayi da likitan,sai ya saki dariya sannan ya miqe

    “Ta gaya maka abinda takeji,sai kayimin bayani,ina zuwa bari na samo nurse,za’a yi mata scanning,tunda kace ciwon mara ne” sai likitan ya cire abinda ya saqala a wuyansa ya ajjiye ya fice daga office din.

    Cikin kunya ta soma qoqarin zame hannunta daga nasa,amma saiya qara matsowa yana sanya dukka tafukan hannunsa a ciki da saman nata,ya rahe gap din dake tsakaninsu sosai yana dubanta

    “Uhnnnn…. tell me,kinga idan ya dawo baki fada ba zan tafi na barku tare” qoqarin tsaida kukan nata take tayi,taja majina sannan tace cikin muryar kuka

    “Marata ce take ciwo sosai” ta fadi cikin mugun jin kunya

    “dai dai ina?” Ya tambayeta yana kallon qwayar idanunta,sai ta motsa hannunta dake mararta kadan,kamar mai tsoron kada ya taba hannun nata.

    Idanunsa ya mayar kan hannun nata,sai yasa yatsansa ya nuna wajen

    “Wajen nan kenan?’ ta gyada kanta a hankali,sai ya dauke dubansa daga wajen yana fidda numfashi,ya miqe a hankali,yayi taku biyu kenan saiga likitan ya dawo,bayansa wata nurse ce,zata kusa shekaru talatin,ba yarinya bace.

    Yana dariya ya tambayi abbas me tace?,ya zube hannayensa a aljihun wandonsa yana duban likitan

    “Ciwon maranne dai”

    “Ba damuwa,da Allah ki mana scanning,bari naje mota na dawo” ya sake fada yana diban wasu takardu ya fice.

    Sanda taga an gama saitan scanning machine din tace kuma tahau sai ta fara zare idanu,ganin alamun tana jin tsoro sai nurse din ta dubi abbas

    “Yallabai ko zaka taimaka mata” a nutse ya maida dubansa ga widad din,itama shi take kallo,idanun nan har yanzu qwalla ce kwance a ciki,ya cire hannayensa da tun dazun ke aljihunsa,ya tako a nutse ya iso gabanta.

    Sosai ua tsugunna a gaban nata,cikin murya qasa qasa, yadda ba wanda zai iya jinsu ya fara magana

    “Kije ta dubaki,few minutes ne ta gama miki,ba ciwo ba zafi,just relax….” Baki ta kwabe tana dubansa

    “Tsoro nakeji”

    “I promise you ba abinda zakiji,muje na rakaki” yadda take a tsorace yasa bata damu da kama hannunta da yayi ba,ya kaita har kan gadon sannan ta kwanta.

    “Dage rigar taki” nurse din ta fada tana dauko cream din da zata shafa mata saman cikinta,sai ido ya sake raina fata,matsawa yayi dab da gadon,yasa hannunsa a hankali ya fara janye rigar jikin nata,da hanzari ta riqe tsintsiyar hannunsa,sai suka hada idanu,ya tsareta sosai da manyan idanunsa masu wani irin kaifi da tasiri,ya girgiza mata kai murya kuma can qasa yace

    “Nooo,i said just relax” sosai taji idanun nasa sun mata nauyi,saita kauda kanta gefe,hawayen da suka cika idanun nata suna gangarawa ta gefe.

    Kamar wanda aka zarewa laka haka ya dage mata rigar har zuwa saman cikinta, kyakkyawar farar fatarta mai sulbi ta bayyana,ya koma a hankali da baya yana jin kamar iska na yawo dashi,ya jingina da wani qaramin locker dake wajen idanunsa nakan saman fatar cikin nata.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 52

    Arubuce Ta Ke 52

    Page 52

    Har ta gama gyaran dakin kwance saman gadon tana chart

    “Na gama” ta fada jikinta yana amsawa da wani irin ciwo,saboda wannan shine karo na farko data fara aiki mai yawa haka

    “Akwai ‘yan kayan da zaki daurayemin…..amma,bari nayi kiranki idan na tashi” da to ta amsa,ta juya tana fita a dakin,tana jiyota tana cewa su mimi

    “Ku bita da Allah kuban waje na huta” da saurinsu kuwa yaran suka biyo bayanta.

    A falo ta barsu,ta shiga bedroom ta zarce toilet ta hada ruwan zafi tayi wanka,ta hado da alwala,farkon mkhtarin sallar azahar din ya shiga,sai kawai tayi sallarta,tana shafa mai gajiya tana bin jikinta,da qyar ta qarasa,ta shiga kitchen ta hada tea ta hado da bread ta dawo ta zauna tana ci,bata iya shanyewa ba taji ya fita a kanta,sai ta dire cup din ta wuce daki tabi lafiyar gado,bata jima ba kuwa bacci yayi awon gaba da ita,saboda uban gajiyar data tarawa jikinta.

    Tana tsaka da baccin taji ana dan dukan qafafunta,idanunta a rurrufe saboda nauyin da sukayi mata ta budesu kadan,mimi ce da nawwara

    “Nawwara ce tayi pupu,mommy tace ki wanke mata” idanu tadan runtse,baccin sam bai isheta ba,amma tana jin ya zame mata dole ta tashi,hakanan ta miqe ta cirema nawwaran pampers ta wanke mata,ta maida mata wandonta,lokacin sallar la’asar ya shiga,don haka ta daura alwala ta bada farali,sanda ta idar cikinta yayi wayam,dole ta shiga kitchen,ta rasa me zata dafa,ta jima a tsaye tana tunani,daga bisani ta raya gwada dafa jallop rice.

    Nutsuwa tayi sosai ta fara hada jallop din,sai data gama hada komai ta rufe Sannan ta koma ta zauna cikin kitchen din tana taya su mimi wasa,wayarta dake daki ta dauki ringing,sai ta fito tabar kitchen din ta wuce bedroom din,ta dauko wayar dake saman madubi ta duba me kiran.

    Anty deena ce,saita saki murmushi ta koma bakin gadon ta zauna,daxun da safe da sukayi waya da ummun take cigiyar anty deena di,tace an dauke mata waya ne

    “Shalelen ummu” baki widad ta tura gaba

    “Ni wallahi ba haka bane anty deena,duk ku manta dani,kun kawo ni nan kun ajjiyeni” murmushi ta saka

    “Banda abinki widad,ashe muma ba’a sonmu kenan, kowacce mace ‘yar wani gida ce daman ai”

    “Amma ku ai kuna kusa da gida,kuma ana zuwa,ni kam ba wanda yazo,ummu ma taqi zuwa”

    “To daga aure weedad sai muhau zirya?,kiyi haquri kinji?” Kai ta gyada kamar tana a gabanta ne,saidai anty deena ta fahimci ta amsa ne tunda taji shuru

    “Komai lafiya ko?” Ta jefa mata tambayar,sai taji kamar ta tsokano ta,idanunta suka hada qwallar da itama ba zatace ga dalili ba.

    Ta bude baki tana shirin yin magana aka buda qofar dakin nata,ta daga ido tana duban bakin qofar dakin,hafsat ce ke shigowa,sanye da bubu na wani material,ta qulle kanta da dankwalin lace.

    Zubawa juna idanu sukayi dukka su biyun,abinda yasa hafsat din taji ta tsargu,bata kuma yarda da wayar dake kunnen widad din ba,ita kuma widad din taji wani mugun tsoro ya saukar mata,hafsat din tayi mata wani mugun kwarjini,tana ji anty deena na sake cewa

    “Hello weedad lafiya ko?” Hadiye wani yawo tayi mai cike da tsoro

    “Eh anty” muryarta ta sauya ba kamar dazun ba,tabi hannun hafsat da kallo wadda ta miqa hannu kai tsaye tana zare wayar daga kunnenta,ta duba me kiran sannan ta saka a nata kunnen,dai dai lokacin da anty deenan ta sake cewa

    “Idan da wata matsala ki fada kinji,in sha Allah zan baki shawarwari,basai kin kira ummu kin daga mata hankali ba,ba kuma sai kowa yazo ba” idanu hafsat din ta sauke mata,sai ta dan daga wayar daga kunnenta nesa kadan sannan tace

    “Bani mana mu gaisa” tamkar a lokacin ta karbi wayar,sannan ta mayar kunnen tana sallama.

    A sake suka gaisa da anty deena din,don basu manta da yadda ta tarbesu ba sanda suka kawo widad din ba,sun tafi suna yabonta,fargabarsu kuma na shigar widad din gidan kishiya tana raguwa

    “Da fatan qanwar tamu dai bata da matsala?”

    “Ah wallahi tana da hankali ga nutsuwa,komai lafiya alhmdlh” cikin jin dadi anty deena tace

    “To ma sha Allah,muna godiya sosai”

    “Aiba komai,yiwa kaine ai,bari na baku guri ku qarasabmaganarku” ta fada tana miqawa widad din,jiki a mace ta karba wayar,maimakon ta fita din kamar yadda ta cewa anty deena,sai kawai ta samu waje ta zauna nan saman madubin widad din tana qarewa dakin kallo,kunnuwanta kuma suna sauraren abinda take fadi,shegiya……shuwa ko sadakar yalla,sharrinsu yawa gareshi,yarinya mitsitsiya amma dakinta yana qamshin da nata dakin bai taba yi ba tun zamanin amarci?,take kishi ya kamata,ta maida dubanta ga widad din sanda suke sallama da anty deena.

    “Wani abu kika gaya musu?” Ta tambayeta tana hade rai tsam kamar tana magana ne da mimi,da sauri ta girgiza kai

    “A’ah wallahi mommy,muna fara waya ma kika shigo” kai ta jinjina sannan ta sake cewa da ita

    “Ko.meye yake damunki ni ya.kamata ki fara gayawa kina jina?,tunda yanzun mune muke gida daya dake kinji ko?,dani zaki dinga shawara” kai ta daga,sai hafsat din ta sako qasa tana sake nazartar dakin

    “Wannan turaren kuma da kike bulbulawa dakin,so kike.aljannu su tare miki a daki su dinga hanaki bacci suna zuwa da daddare suna tsorataki?” Dukka manyan fararen idanuwanta weedad ta fidda waje,iya maganar da hafsat din kadai tayi ta tsoratata matuqa,tsoro sosai ya shigeta,ta fara kada kai

    “To ki daina sakawa,kibar dakinki a hakama”

    “Ba sakawa nake ba,haka dakin yake ai” ta furta muryarta tana rawa,a fakaice ta jefa mata harara ta yatsina baki, shegiyar yarinya sai shegen sanabe da kidifiri

    “To shikenan,ki taso ki wanke uniform din mimi,idan ya bushe kiyi ironing dinsa” tana gama bada umarnin tayi gaba abinta,ai kafin ta kammala fita ma ta biyo bayanta,saboda zancan aljanun yayi mugun bata tsoro,a tsaitsaye ta kashe girkinta dake kitchen,bata ko tsaya dubawa ba tayo sashenta.

    Sai data gama komai kamar wata ‘yar aiki,harda tsarabar sake goge mata falo dasu mimi suka bata,kafin dare ta gaji tubus,tana son komawa amma tana jan jiki,don har yanzu tsoron maganar mommy hafsa dince a ranta,saidai dole ta koma din,tunda a nan din ba wani sakin jiki takeyi ba sosai,kasancewarta mutum mara saurin sabo.

    Komai da takeyi da takatsantsan take yinsa,ta shiga kitchen ta juyo abincinta ta wuce daki dashi,sai da ta zauna taci mai yawa sosai,don har ita kanta tana mamakin yawansa,amma ba abun mamaki bane,saboda kusan yini tayi da yunwa,data gama din saita tube kayan jikinta ta daura towel ta wuce toilet.

    A parking lot na gidan ya tsaida motarsa,ya fito hannunsa dauke da ledar da uncle muhsin ya bayar yace a kawowa widad din,don jiya ya dawo daga kano,saqo ne daga mutanen gida,kowa da abinda ya bayar a kawo mata,amma shi abbas din baisan meye da meye a ciki ba,kawai dai ya karba ya taho dashi.

    Yau din tunda ya fita bai zauna ba,daga gidan hajiya ya dauketa sukayi ziyara sosai bayan sunje gidan makokin,basu dawo ba sai magrib,daga nan kuma yayo gida.

    Koda ya kashe motar kansa tsaye sassanta ya nufa,hankalinsa yana can,daya fita hajiya na tambayarsa lafiyarta,sai yaga kamar bai kyautawa hajiyan ba,don baisan ya tata tashi ba,wannan dalilin yasa hankalinsa ya dauko da zuwa sashen.

    A nutse ya buda qofar da sallama abakinsa cikin wannan kwantacciyar muryar tasa mai taushi,falon ba kowa,saidai wannan sassanyan qamshin da ya zaunewa falon daketa faman kadawa,jikinsa ya bashi tana dakinta,don haka kai tsaye ya nufi dakin.

    Sanda take fitowa daga bandakin lokacin shima ya turo qofar dakin ya shigo,bata ganshi ba saboda ta juya a hankali tana jan qofar toilet din tana rufeta,don ko kadan bata qaunar wani babban motsi,saboda yadda zuciyarta keta rawa,a tsorace take sosai,ta sauke ajiyar zuciya ta fara takowa tsakiyar dakin,sai a sannan idanuwanta suka gano mata shi.

    Baisan me ya tsaidashi ba daga bakin qofa ya kasa qarasowa ciki,yasan dai tunda ya dora idanuwansa a kanta yaji kamar an tsaidashi a wajen….. widad kuwa baya taja da sauri sanda sukayi ido hudu,jikinta ya fara rawa, idanuwanta suka fara tara hawaye,abu na farko daya zo mata a rai aljanine ya shigo mata part yayi mata suffarsa,fararen kaya ne a jikinsa na wani lallausan yadin filtex,hakanan jakar hannunsa itama farace….an kuma gaya musu a tatsuniya aljanu suna son shigar farare,don haka ta fara hawaye tana fadin

    “Wayyo ummu na…..don Allah kayi haquri,wallahi na daina,don Allah kada ka yimin komai” haushi dariya da kuma takaici suka qumeshi,yau kuma shine abun tsoron?,lallai abun nata babba ne,quruciyar tata ta gaske ce,rasa abunyi yayi,ta kuma tubure sosai tana masa kuka da magiya,ya lumshe idanu hadi da sauke numfashi ya kuma furzar da iska,ganin yadda yaketa qoqarin yi mata bayani amma ta gaza fahimta.

    Idanunsa ya sanya cikin nata ya kira sunanta da qarfi,tamkar numfashinta zai fita daga qirjinta ta sandare a tsaye

    “Kina motsawa anan inda kike zan batar dake,ki tsaya na iso gabanki saina tafi na baki waje” kai ta shiga kadawa,kamar zata saki fitsari a wando,qasan ransa kamar dariya zata qwace masa amma takaici ya hanashi,ya ajjiye ladar hannunsa saman madubi,ya soma takowa idanuwansa a kanta.

    Yana zuwa gabanta ya hade tazarar dake tsakaninsu,ya buda hannayensa gaba daya ya lullubeta tsam cikin qirjinsa,qamashin shampoo data wanke kanta hadi da shower gel dinta ya nutsa can cikin hancinsa,ya lumshe ido wani numfashi na fusga daga qasan zuciyarsa mai wani irin nauyi

    “Ya Allah,what’s happening?” Ya fada can cikin ransa,jin yadda gaba daya jikinsa ya saki,abun mamaki baiyi abinda ya zata zatayi din ba,a maimakon haka saita tsaya cak a jikin nasa,wani irin nutsuwa taji tana saukar mata, tsoron yana gushewa,ta lullube idanunta sosai,kukan yana dauke mata,ajiyar zuciya tana maye gurbin kukan.

    Sun jima a haka,kusan mintuna biyar ba wanda ya zame jikinsa daga dan uwansa,dole tasa ya fara neman rabata da jikinsa,saboda yadda dumin jikinta ya fara ratsa nasa jikin,tudun matasan qirjinta ya fara masa barazana,har numfashinsa na qoqarin sauyawa,baiyi mamakin faruwar hakan ba,saboda yasan yana cikin wani irin situation,bako da yaushe yake samun yadda yakeso daga hafsat ba, saboda dan uban qazantarta dake hana masa rawar gaban hantsi koda kuwa ta bashi dama,lokuta mafi yawa kuma takan tsuqe,tare da kawo masa qorafe qorafen

    “Ni na gaji yau wallahi……bacci nakeji……bani da lafiya fa…..” Ko sau daya bai taba waiwayawa yabi ta kanta ba,ya gwammace ya kama kansa,don baijin zai iya begging dinta akan abinda yake halalinsa,sannu a hankali ta fara cire masa sha’awar ta kwata kwata daga zuciyarsa,sai ya dauki lokaci bai waiwayeta ba,abun har ya fara zame masa jiki.

    Kamar raqumi da akala haka ya zaunar da ita gefan gadon,ya jawo kujera ya zauna yana fuskantar ta.

    Nazarinta ya fara,ya zuba mata idanu yana kallonta tun daga santala santalan cinyoyinta zuwa jiqaqqiyar sumar kanta da ta fara tsanewa,idanunsa suka tsaya ga fafaren kafadunta dake cikin farin towel,a lokacin ne hankalinta ya dawo jikinta,ta soma curewa waje daya sabbin qwalla suna cika mata idanu

    “Mene ne?” Ya tambayeta ganin yadda hankalinta ya tashi lokaci guda

    “Kaga fa….bani da riga” furucin ya qaraso fitowa da hawaye masu dumi daga idanunta,karon farko da yajin haushi ya kamashi

    “To sai menene?” Kuka ta fashe masa dashi tana nuna masa hijab dinta

    “Don Allah ka bani hijab dina na saka,Allah ummu ta hanani”

    “Tace miki harda ni kada na ganki a haka?” Ya jefa mata tambayar,yau kam sai ya qure tunaninta,kai ta kada

    “Ban sani ba,ka daina kallona don Allah” ta sake fada tana kuka,shuru yayi yana duban baby face dinta dake jiqe da hawaye,ya gama karantarta,a haka ta taso ba tare da tasan cikakkiyar ma’anar aure ba,kuma ko a yanxun indai yanason ta fahimci abinda zai gaya mata saidai ya bata hijabin yadda takeso,baisan dalil ba,sanda ya miqa mata hijab din,sai yaji baya buqatar ta saka,amma haka ya lumshe idanunsa harta gama sakawar,sannan ta tsareshi da ido tana jan majina.

    Shima ita din yake kallo,kafin daga bisani ya kauda dubansa,ba lallai ma ta gane meye miji ba bare aure,sai ya ajjiye wannan maganar ya soma mata wadda yake ganin tafi muhimmanci akan wadda da farko yaso yayi mata ita.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)

    *Arewabooks: Huguma*