Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 45

Sponsored Links

Page 45

“Barka da dawowa oga,tun wancan satin muketa zuba idanun dawowar ka,har mai gida yana tambaya” miskilin murmushi ya fita a fuskarsa

“Naso dawowa,to amma ban gama shirye shirye bane,mun sameku lafiya?”

“Lafiya sumul oga,ya hanya?,ashe an samu qaruwa?,to Allah ya sanya alkhairi,yasa abokiyar arziqi ce” bala mai gadi ya fada yana murmushi

“Ameen”ya amsa masa a taqaice,sai ya zagaya da sauri ya soma budewa widad qofa yana fadin

“Madam barka da rana” nauyi ya saukarwa abbas,da alama bala baisan qaramar yarinya bace yake gaidata,duk da ya bude motar bai damu ba yaga ta sake maimaita gaisuwarsa,sakato widad tayi cikin rashin sabo,wai yau ita ake gaisarwa?,ita da take gaida jama’a?

“Ana magana” abbas ya fada yana cire belt seat dinsa,maimakon ta amsa saita maida masa gaisuwar,saboda rashin ganin dacewar ta amsa din,amsawa yayi ya kuma bisu da addu’ar zama lafiya da zuri’a ta gari,ita dai tana jinsa ba tare data amsa ba.

Muqulli abbas ya miqa masa sannan yace

“A shigo min da kayan qofar parlor bala”

“An gama oga” ya fadi yana karba da hannu biyu

“Muje” ya sake fadi yana duban inda widad taja ta tsaya,tana kuma bin gidan da kallon baqunta.

Wata siririyar hanya suka bi,sai gasu qifar wata qaramar baranda mai kyau dake dauke da wata qofa mai dam fadi,yasa key ya bude qofar ya shige,ta bishi a baya,kamar za’a ce kettt ta zura da gudu.

Madaidaicin falo ne amma ya qawatu matuqa,akwai qofofi guda uku a cikinsa na bedrooms guda biyu,daya qofar kuma ta kitchen ce sai dining area,sai qaramar qofar da zata fiddaka bayan gidan.

Qarasawa yayi gaban daya daga cikin dakunan ya buda daya

“Ki shiga nan kiyi wanka ki huta” bata iya amsa masa ba,sai gaba datayi zuwa qofar dakin tana raba idanu,turqashi,yau fa ake yinta,a wanann dakin zata zauna ta rayu ita kadai?,abinda yake nufi kenan?,ga gidan ta fahimci babu wadatar hasken rana,duk da cewa yammaci ne amma alamu sun nuna hakan,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta sanya kanta cikin dakin,dab da zata shige yace

“Ki rubuta duk abinda kikeso,zan aiko a karba sai a kawo miki” sai a sannan ta samu daga masa kai,qwalla tana cika mata idanu,har yayi gaba ya dakata,ya juyo a nutse ya sanya idanunsa cikin nata

“Me ya faru?”ya tambayeta yana kallonta,cikin jajircewa tayi qoqarin maida qwallar data cika mata idanu

“Tsoro nakeji”ta amsa masa kai tsaye

“Tsoron me?”ya tambayeta cikin mamaki, maimakon ta amsa masa saita maida dubanta ga dakin da ko qwan wutarsa ba’a kunna ba,saboda haka ya danyi duhu,gyara tsaiwarsa yayi,tana jin tsoro,to amma kuma baisan me zaiyi mata ba,hakan yana nufin saidai suyi sharing daki ita dashi?,kai ya girgiza kadan
“NO” ya amsawa kansa,sai yanzu ya tuna da dan banzan tsoron da take dashi,ya manta the first time he saw her…ihun kyankyaso taketa yi,harda cire dankwali,takawa yayi ya matsa zuwa inda take tsaye,ganin ya nufota ta tuno da wani abu,tayi hanzarin jaa da baya a tsorace,har abun yaja hankalinsa,yadan dubeta kadan sannan ya dauke kansa,wannan bayan tsoron su kyankyaso hala harda tsoron mutane ma tanayi?.

Qwan wutar dakin ya kunna,haske ua gaurayeshi,abinda ya rage mata tsoron dakin kenan,ya fita a dakin ya bata waje yana cewa

“Sai anzo an share dakin,akwai qura” saboda sanda hafsata ta tashi tafiyarta a birkice ta barshi,shi kuma takaici yasa ko takan dakin bai sake bi ba tunda ta fita daga ciki.

Sai data tabbatar yabar wajen sanann ta saka kai cikin dakin,ta tsaya tana duban komai,a hautsine yake,ji take yi ba zata iya zama ba,don kafin tafiyar latifa ta koya mata yadda ake gyaran bedroom xuwa falo,kuma babu laifi hannunta yadan fada,ta janyo jakarta zuwa tsakiyar dakin tayi mata waje.

Zama tayi tana qarewa dakin kallo,idanunta fal hawaye,ta rasa qwarin gwiwar gyaran dakinma gaba daya,tana jin kamar an dauketa daga duniyar ta an kawota wata duniya ta daban.

Bata tashi ba sai da aka kira magarib,ta miqe tana kame jikinta waje daya,saboda dakin ya mata datti,kasancewar bata taso ta saba zama cikin dauda haka ba,koda yaushe zaka samu sassan ummu qal qal,ko tsinke bata bari ya sauka,shi yasa basa shiri da jikokinta,don da zarar kazo ka zauna ta fuskanci kai dan bata guri ne yanzu zata koraka,widad dince kawai keyin yadda takeso a sassan ba tare data hanata ko tace mata komai ba.

Toilet din ta shiga tayi alwala,tazo ta shimfida dankwalinta ba tare date nema abun sallah ba ta tada sallah,ko da ta idar tana zaune a wajen,har zuwa sanda aka turo qofar dakin,ta waiwayo a tsorace,saita zuba masa ido sanda yake shigowar,tsoro na kamata,a yanzun ya canza shiga,shirt da trouser ne a jikinsa da suka dace da jikinsa,suka fidda qirar jikinsa dake tafe da tsaho da murjewad jikin kadan,don ba zaka kirata qiba ba.

Ido ta lumshe,tana jin dadin qamshin turarensa har qololuwar ranta

“Kinyi sallah ne?” Kai ta gyada masa ba tare data iya kallonsa ba,sai ya dauke idanunsa daga kanta ya kalli agogon hannunsa

“Zan dan fita…..” Tun kafin yakai qarshe ta daga manyan idanunta ta watsa a kansa,haka kawai yaji nashi idanun suna lanqwashewa zuwa lumshewa,kafin ya budesu ya azasu a kanta,har zuwa sannan manyan fararen idanunta suna kanshi,ta yaya zai fita ya barta a wannan gidan ita kadai?,duk da bata da tabbacin ita daya ce cikin gidan gaba daya,amma itakam ko dakin ummu bata yarda ta zauna ita kadai,inaga gidan gaba daya

“Bazan dade ba zan dawo,za’a knocking za’a kawo abinci,saiki bude ki karba,idan kuma wani abu ya taso ki kirani a waya” wani mugun tsoro ne ya shigeta sanda ya juya yana ficewa,kuka sosai yazo mata,ta cure waje guda tana cusa kanta tsakanin qafafunta

“Wayyo ummu”ta fada muryarta can qasa wadda ke cike da kuka,sun kawota inda bata da kowa,kamar basa sonta,itakam meye tayi musu?,sai taci gaba da rera kukanta a hankali,har zuwa sanda taji kiran sallar isha’i ta miqe ta bada farali,ta sake komawa yadda take.

Tana jin anata knocking kamar yadda yace amma ko yunwa zata kasheta bata jin zata iya miqewa zuwa falon har ta bude,tana jinsu har suka gama bugunsu suka tafi,saita sake sakin kuka tana takurewa waje daya.

Lokaci lokaci tana duban agogo tare da fadin

“Allah kasa ya kusa dawowa” saita sake maida kanta tana sharar hawaye,har kusan awanni uku babu shi babu dalilinsa.

A karo na barkatai ta sake daga kanta don kallon agogo,saidai hasken farfajiyar gidan ya hasko mata mage dake tsaye jikin window din dakin nata tana kada jela,wani mugun tsoro da razani ya shigeta,take jikinta gaba daya ya fara rawa,hawayen idanunta suka ninku,ta fara karanta ayatul kursiyyu a rarrabe saboda yadda bakinta yake rawa,a duniya babu abinda ta tsana take mugun tsoro irin magen,don saboda ita kowa na gidan ya haqura da ita,sabod koda ka kawota sai ummu ta sanyaka ka maidata inda ka daukota.

A hankali magen ta soma kankarar glass din jikin window din kamar me neman hanya tana kuka mieeeuuuu mieeeuu,ba abinda yaxo kwanyar widad illa ga magen har ta shigo ta fada mata a ciki,take ta saki wata qara hade da kuka.

Sautin muryarta yakai kunnuwansa sanda yake tsaye yana knocking qofar falon,kusan sau biyar kenan amma baiji motsinta ba,har ya fara tunanin ko tayi barci ne?,sai kuma saqon muryarta ya riskeshi.

Sosai yaji hankalinsa ya tashi,to meye ya sameta?,cikin hanzari da kuma gaggawa ya fara laluben keys din dake aljihunsa,ya fiddosu ya fara gwadaw jikin qofar cikin hanzari da zafin nama,har sannan ihunta na tashi saidai da yake harabar gidan tana da yalwa,babu lallai wanda ke can nesa kamar malam bala ya jiyota.

Cikin sa’a ya samu key din,ya bude ya tura sannan ya shige da sassarfa zuwa dakin nata.

Motsin bude qofar dakin ya zake dagula kissafinta,ya kuma sakata ta sake gigicewa gaba daya,a nata zaton magen ce ta bude window din

“Calm down mana,ki nutsu,menene?” Ya jefa mata tambayar yana riqe da dukka kafadunta,idanunta da suka jirkice ta daga ta kalleshi,batayi wata wata ba ta shige jikinsa ta qanqamesa kamar yadda ta saba yiwa ummu,sannan ta daga yatsanta tana nuna masa window.

Mutuwar zaune yayi,a yadda ta shige masa jiki gaba cikin ba zata,wani irin sanyi ya sauka a gabbansa, tashin farko kamar an zare masa laka,don matasan tudun qirjinta gaba daya sun hade da nashi qirjinsa,yana iya jinsu sosai,ya daga kansa kamar mai ciwon wuya ya waiwaya ga window din,dai dai sanda magen tayi tsalle ta sauka daga window din,take ya fahimci ainihin dalilin rudewarta,sai ya dawo da dubansa kanta yana qoqarin zareta daga jikinsa,tare da fadin

“Am beside you,calm down, mage ce fa,look there,she’s already gone” ya kuma fada yana qoqarin tsaida fuskarta tsakiyar tafin hannunsa tare da qoqarin lalubo qwayar idanunta don bata qwarin gwiwa.

Sam taqi ganewa abinda yake fadi din,sai ya tuna abinda ya faru washegarin randa tazo gidan,don haka ya buda hannayensa ya sanyata cikin qirjinsa ya rufe,wata qatuwar ajiyar zuciya tana subuce masa.

Dukka idanunta ta fidda waje kamar zasu zazzago,gabanta yayi mummunar faduwa,zai kuma?,irin ta ranar nan?,me yasa shi din dan iska ne?,take wata huduba data baro bauchi da ita ya fado mata,cikin dan qaramin qarfinta da bai taka kara ya karya ba ta saka hannayenta duka biyun tana qoqarin tureshi,ko kusa ko alama baiyi gezau ba,amma yaji abinda take shirin yi din,haka kuma yake buqata,sai yaja da baya yana kallonta.

Kuka sosai ta fashe dashi,kukan takaici da baqincikin rungumeta da yayi,wannan wanne irin iskanci ne,haka kawai sai ya dinga taba ta?

“Ya isa,ta tafi nace” ya fada calmly yana kallon yadda sumar kanta ta biyo ta gefan fuskarta,kamanninta suka fita sosai,fuskarta tayi jazur saboda kuka.

*Arewabooks:Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
[3/6, 3:13 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Back to top button