Arubuce Ta Ke Hausa NovelHausa NovelsHausa Novels

Arubuce Ta Ke 32

Sponsored Links

Page 32

Yana daga tsaye yake shanye tea din dake cikin cup din,yana yi yana hadawa da qonannen cake din da hafsat din tayi,dai dai sanda ita kuma ke sanye da kampala dinkin tea bubu,fuskarta a wanke tas babu digon kwalliya kamar kullum,hakanan fuskar tata a dinke take babu walwala sam sam.

A duk lokacin data kalli abbas….ta kuma tuna a yanzun bawai ita daya ce mutum dake amsa sunan matarsa ba,sai taji kamar ta shaqe kanta,kota zauna tayita zunduma ihu har sai dukkan jama’ar dake kewaye da ita sun fuskanci irin zafi radadi gami da qunar dake cikin ranta,tsantsar bacin ran da babu halin nuna shi,baqinciki da tashin hankalin data zabi lullubeshi da kissa da kuma nuna halin ko in kula da lamarin aurensa,wanda ko kusa ko alama ba haka bane cikin ranta.

Cup din ya dire saman fridge din yana furta

“Alhmdlh” da Peace voice dinsa dake dauke da wani calmness da bai cika son hayaniya ba,idanunsa ya zube saman fuskarta yana kallonta,saita janye nata idanun daga kallonsa,batason zuciyarta ta karye ko sonshi ya motsa mata har tayi wani misbehaving,tsaki yana subucewa daga bakin nata,saidai Allah yasa baiji ba

“Zan wuce” ya fada murya can qasa

“Allah ya kiyaye hanya” ta amsa masa a taqaice tana folding hannayenta a qirji,matsawa gabanta kadan ya sakeyi yana rage kusancin dake tsakaninsu

“Me da me kuke buqata?,ko kuma shikenan?,ba wani taro da zakiyi?” Kusan duk abinda takeso ya dire mata,ta wanki aljihunsa yadda ya kamata,to amma duk da haka batasi tace masa shikenan din, tunda zataje wajen anty ummee,batasan me zasu tattauna ba,don haka tace masa

“Idan akwai wani abu zamuyi waya” kansa ya jinjina,ya sauke mata soft kiss a goshinta,sannan yaja da baya ya juya yana barin wajen,dole ta kama masa qaramar jakar tabi bayansa da ita tana qoqarin gyara yanayin fuskarta,don komai ya sake hawa kan saiti,ya kuma ci gaba da tafiya yadda suke tsarawar.

Da murmushin yaqe ta bishi sanda yake waving mata hannunsa,motarsu tana fita ta koma ciki da sauri,ta dauki jakarta mayafi da key din motarta,har takai bakin qofa ta koma ta rage yawan kudin dake cikin jakar ta adana a locker dinta,cikin ranta tana raya

“Kada bacin rana ya gifta ta kansu” duk kuwa da cewa gidansu zataje,acan zasu hadu da anty ummee din.

Tunda ya tafi kusan ayyuka suka cunkushe masa,bashi da wani cikakken lokacin kansa bare na sauran abubuwan,haka ya dinga qoqarin handling komai,ga gida babu mace,idan ya dawo kusan wasi hidimomin da ya cancanci ace matar aurensa ce tayi masa kafin isowarsa gidan shi zai gabatar dasu,wanann ya sanya shi yanke hukuncin ajjiye widad a nan kadunan,ko babu komai gidan bazai zamana shuru babu dan adam a cikinsa ba.

Yana daga nan ya sanya aka sake gyara part guda daga cikin parts din gidansu na bauchi,a nan kadunan ma yayi wasu qananun gyare gyare,mutum ne shi koda yaushe mai tsananin kyautatawa ga duk mutumin da Allah ya dashi zama dashi,hajiya tafi kowa sanin hakan,shi yasa zamansa da hafsa ya tsaya mata a rai qwarai da gaske,tako ta ina abbas din inda rubutawa bawa qaddararsa akeyi ya cancanci samun mace ta gari,wadda zata kula dashi matuqa gaya.

************K’arasa zuba jewel’s dinta data debo tayi cikin qaramar jakarta ta zuge,sannan ta dubi alhaji salim mai fata dake zaune kusan awa guda saman kujerar madubi dake dakin widad din

“Alhaji na gama” ta fada tana murmushi

“Da kyau jikata,sai tafiya kenan” kai ta gyada masa tana dariya

“To muje na rakaki da kaina,kada ma mutsaya sauraren kowa su bata mana lokaci” sai ya miqe yana daukar mata jakar,yayin da ta lulluba mayafinta abinta,suka jera ita da kakan nata dake nuna mata zallar qauna hadi da kulawa kamar yadda tsohuwar matarsa ummu ke gwada mata.

Hankali kwance alhaj salim ya bude mata gaban baqa wul don motar qirar range rover,daya daga cikin motoci mallakin ASP abbas muhammad bello

“Shiga abinki ki zauna kafin su fito” sai a sannan ta kalleshi,tadan narke fuska

“Amma alhaji,kace dakai da ummu duka kuna nan tahowa ko?” Kai ya gyada mata yana murmushi,saidai can qasan ransa kewa da kuma tausayinta ne fal zuciyarsa,farincikinsa guda daya zuwa biyu ne……sun aurar da widad din cikin aminci zuwa ga hannun mutumin da basu da haufi a kansa,nagartarta da ingancinsa sunkai,na biyu duk yadda suketa juya yadda za’a fidda widad din daga gidan salin alin bata tara musu taron jama’a ba,sai gashi da qafafunta ta fito zuwa motar da zata daga dasu bauchi,Allah ya bashi hikima da basirar da taketa shauqin tafiyar zuwa gidanta

“Idan bamuzo ba waye zaizo?,kedai sha kuruminki,abinci zaki dafa mana mai dadi nida ita a kitchen dinki” murmushi ne ya sake kubce mata,itakam widad har ta isa macen da zata shiga kitchen tayi girkin baqi kenan,saita kama murfin motar ta kuma shige,alhj salim ya miqa mata jakar,sannan ya tsaya daga bakin motar yana mata hirar dake sake dauke hankalinta.

A gajiye anty deena ta tura qofar dakin ummu tana sauke ajiyar zuciya

“Allah ummu nidai nayi iya dubana banga widad bafa” cikin mamaki ta dubeta

“Har wajen alhajin ku kin duba basa tare?” Kai ta girgiza

“Ban duba ba”

“Yi qoqari ki dubota,kinga kada suyi dare a hanya”

“Gaskiya dai,nima banason muyi tafiyar daren nan saboda sanyi” tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin.

Har zata gota jerin gwanon lafiyayyun motocin da aka shirya su saboda daukar widad din ta hangi alhajin tsaye jikin daya daga cikin motocin,saita dawo da baya,abinda ta gani ya sanyata kusan faduwa saboda dariya,widad ce zaune gaban motar ta qwame abinta,sunata hira da alhajin tana ta qyalqyala dariya,kome yake gaya mata oho,saita tsagaita dariyar tana kallonsu,murmushi na kubce mata,qasan ranta itama tausayin widad din na tsarga mata

“Kuruciya me dadi” ta fada a hankali hawaye nadan tsatstsafo mata,ta tabbatar inda ace babba ce yanzun haka ake shirin tattarata zuwa gidan miji,gidan mijin ma wata duniyar ba duniyarta ba,ba duniyar data rayu a cikinta ba,ba shakka da tuni tana nan hankali tashe,saita juya kawai zuwa cikin gida don ta sanar musu,tafiya ta tabbata tunda amarya har takai kanta cikin mota,murmushi ya sake kubce mata.

Dab da bakin falon sassan ummu sukayi kacibus da inna batulu momma

“Har yanzu ba’a ganta ba?” Ta fada a fuska alhini ne fal,yayin da qasan zuciyarta wani fata ne na daban,ba tare da anty deena ta kawo komai a ranta ba tana danne dariyarta tace

“Wa?,ai widad tuni tayi landing a mota” ido batulu ta zazzaro

“Kamar yaya deena?” Dariyar da take riqewa ta kubce mata

“Wallahi alhaji ya raka amaryarsa,kodan kishin nan ma bayayi,tana can tana jiran ‘yan kawo amarya” dogon salati taja tana tafa hannu,sai kuma taja burki ta juya da sauri har tana tuntube ta koma zuwa cikin falon,da kallon mamaki anty deena ta bita,saita take mata baya tabi bayanta itama.

Tana shiga falon batulu na kwazawa ‘yan uwan abbas dake zaune a falon suna jiran fitowar widad din don su wuce

“To ai bayin Allah zaman jira da qoqarin bikon da akeyi ya qare,amarya dai takai kanta cikin mota mu take jira” ran anty deena saiya sosu,duk da cewa akwai quruciya ga deena bai kyautu batulu ta kawo saqon a haka ba,fuskarta na nuna zallar alhini kamar ta aikata wani babban sabo a musulunce.

Inna uwa qanwa ga hajiya ta tura wayar hannunta cikin jaka tana sakin dariya

“La la la,lallai yaron namu badai farinjini ba,niko na godewa wannan diya tamu wallahi,ta hutashe shemu,saimu tashi shirin tafiya ta kammala” anty deena ce ta karbe cikin dariya

“Aiko dai batason wahal daku biyan kudin biko,ai shikenan” dariya aka dauka a falon,kowa yana fadin albarkacin bakinsa,kusan yadda batulu taso a juya zancan ya zamarwa widad abun fada abun baizo a haka ba,kusan kowa dariyar quruciyar yakeyi.

Sannu a hankali jerin motocin dake dauke da mafi yawan ‘yan uwanta suka fara barin farfajiyar gidan alhj salim mai fata,motar da take ciki itace mota ya qarshe,duk da a tsarin tafiyar zata kasance cikin tsakiyar motar securities din da zasuyi musu rakiya har zuwa garin bauchin.

A hankali tasu motar ta fara motsawa,yayin da taketa dagawa su Aafiya hannu tana fadin

“Sai kunzo,karku damu,alhaji yace kamar wancan lokacin da naje gidan uncle muhsin,wannan lokacin har zuwa zasuyi shida ummu saimu dawo tare,idan zai taho ku taho tare dashi don Allah” ta fada tana kallon afiya,tans jin ba dadi itama,zuciyarta najin wani irin yanayi wanda.bata saba jinsa ba,irin yanayin dako sanda zataje gidan uncle muhsin bata sanshi ba,wannan shi ake kira da yanayi na rabuwa……rabuwa da gida….. rabuwa da muhallin da qaddara ta wanzar maka a haifeka a ciki……rabuwa da bigiren daka rayu kayi kuma gwagwarmaya a ciki…..fadi tashi tsakanin masoya da maqiya,zuwa wani bigiren da RUBUTACCIYAR QADDARARTA ta zana mata……BIGIREN dake qunshe da tarin qaddarorin rayuwarta…..qaddarorin dake da tsananin zafi quna da kuma barwa rayuwa tabo me cin rai.

Tun suna tafiya tana biye da hirar wadanda suke tare cikin motar wato anty deena,anty madeena anty madeeha da inna uwa,wani bangaren na zuciyarta kuma nata hasaso mata kayayyakin da dukka ummu ta nuna mata ta kuma shaida mata nata ne gidanta za’a kai mata,yadda zata sarrafasu ta more kayanta,irin yadda taga su anty deena anty ramziyya basma da sauran yayyunta keyi,zatayi iko irin nasu kenan itama,zata saka wasu wanke wanke idan sunzo gidanta,sai qaramar dariya ta qwace mata ita kadai,tana fasalta yadda zata saka su rafi’ah aiki,kuma dole suyi,saboda jiya jiya taji anty madeena na cewa ita din yanzu dukka ta girmesu,duk kuwa da cewa sun babbata wasu watanni.

*Arewabooks:Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K’AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
[2/25, 9:26 AM] +234 813 343 4840: *H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K’addarata)

Leave a Reply

Back to top button