Blog

  • Arubuce Ta Ke 24

    Arubuce Ta Ke 24

    Page 24

    Kai kawo ya dinga yi cikin dakin,ransa na masa suya,me zaiyi ya huce takaicin hafsa?,yasan dai tabbas bazai qyaleta ba,anzo gabar da dole ya koya mata lesson kamar yadda yasha fada.

    Idanunsa suka sauka akan wayarsa,sai ya jawota da hanzari ya fara kiran layin hajiya,bugu biyu ta daga

    “Abbas ya akayi?” Ta tambayeshi da mamaki,ganin bai wani jima da barin gidan ba,qoqarin dai daita muryarsa yayi,don bayason ta fuskanci akwai wata matsala ne ta tashi hankalinta

    “Lafiya lau hajiya,cewa nayi zai yiwu a gabatar da neman auren cikin satin nan?” Kai ta jinjina cike da mamaki,anya babu walakin goro a miya?

    “Eh to,saidai na nema kawunnanka naji”

    “Idan zaiyuwu hajiya kawai ayi,na shirya” tana saurin gano damuwa da kuma fushinsa,yadda yayi maganar a jikinta taji akwai damuwa,amma zata tambayeshi a hankali

    “Shikenan,zanyi magana dasu,duk yadda ake ciki zaka ji”

    “To hajiya na gode,gobe da yamma zan wuce,zan shigo ta nan kafin na wuce din in sha Allah”

    “To ba damuwa,Allah yakai mana rai” daga haka sukayi sallama.

    Cikin mamaki take sauke wayar,saidai kuma ta samu kanta da sakin murmushi tare da fadin

    “Alhamdulillah” zuciyarta na gaya mata wataqila akwai alkhairi mai tarin yawa a abun,shi yasa Allah ya kawo komai a kurkusa haka ya sauqaqe matsala da damuwa.

    “Tofa,ta samu kenan hajiya?” Faccalarta da suke tare a falon,ita da yayar abbas din mai suna mabruka suna hira ta fadi,wayar ta ajjiye gefe tana cewa

    “Aure ne ya tasowa danki” da mamaki ta kalleta

    “D’ana,wa kenan?”

    “Abbas mana” kallonta sukayi gaba daya cike da mamaki,abbas din da kowa yasan dabi’arsa,mutumin da ko auren hafsa dinma kamar bazaiyi ba saboda tsabar I don’t care manner irin nashi da rashin baiwa lamarin soyayya muhimmanci?

    “Abbas din yaushe har yaga wata yanaso?” Faccalar tata da yara ke kira da gwaggwo fanteka ta fada

    “Tayani tambaya gwaggwo,na dauka ma bashir ko yaya sa’id zata ce,ko kuma Sunusi” kai ta girgiza tana murmushi

    “Abbas ne” kai suka jinjina su duka,mabruka tace

    “Ya cancanci ya qara aure dama tuni,wannan rayuwar da akeyi a gidansa bata da ma’ana sam,naga qoqarinsa ma,ganin baida wannan ra’ayin yasa ban taba tuntubarshi da maganar ba,ga ‘yammata nan cike a dangi,ya zabi wata ya qara ko zai samu sassauci,haba abun na hafsa yayi yawa” kai gwaggwo ta gyada itama

    “Gaskiya dai,yammata kyawawa fa gasunan masu hankali,ita wannan din a ina ya samota?,cikin yan uwansa ne?,amma banji batun ba sai yanzu?” Gwaggwo ta fada cike da son jin wace?,tana fata ya zamana cikin yaranta ne,duk da tasan zaiyi wuya,don inda cikin nasu ne da tuni ta fahimta,amma rabonta da abbas a gidan tun sanda tayi wata rashin lafiya ya shiga ya dubata

    “Ba cikin dangi bane,wata yarinya ce diya take a wajen muhsin abokinsa,dukkanku ai nasan kunsan muhsin?” Ta fada tana kallon fuskokinsu, gwaggwo da tuni fuskarta ta sauya tace

    “Qwarai kuwa” sai hajiya ta dora

    “Yarinya ce ma,amma nutsuwarta da hankalinta ya bani abbas din xai samu nutsuwa a gidansa,zai kuma ce ayi ayi,a bari a bari”

    “Turqashi” gwaggo fanteka ta fada ba tare da tasan kalmar ta fita a bakinta ba,wani bacin rau na motsa mata,yaron da dukkan alamu suke nuna zaiyi arziqi cikin dangin nasu,taketa qulafucin ganin ta samu ta jogana diyarta,lokaci daya hajiyan ta wargaza fatanta da burinta ta dauko wata bare ta maqala masa?.

    “Banda abun hajiya ruqayya,gida bata qoshi ba za’a baiwa dawa?,gamu da yaran yammata duka sun tasa saiki dauko bare ki bashi?,duk da itama hafsan akwai alaqa amma ai baiyi alaqar sa da yaran kawunnansa ba ko?” Gwaggo fanteka ta fada tana dora murmushin yaqe kan fuskarta

    “Gaskiya nima wannan tunanin yazo min” mabruka ta fada tana gyada kai, murmushi hajiya tayi

    “Auren dangantakar ai bai amfana komai ba gwaggwo,gwara a gwada baren ko a nan za’a dace ko?” Kai ta kawar tana tabe baki,bacin rai iya bacin rai yana cikata,wanann babbar dama haka za’ayi asararta?,suna ji suna gani

    “Da dai kin sake tunani gaskiya,duk yadda bare yake da dadi ai baikai dadin dan uwa ba”

    “Hakane” ta amsa mata a taqaice,tasan halin gwaggwon da mita,ita kuma dama can bamaison dogon magana bace,gwggwon na daya daga cikin masu kushe aikin dan sanda a sanda abbas ya samu aikin

    “Dan sanda?,me na sama yaci ballantana ya baiwa na qasa?,kayan cin hanci da rashawa” wannan shine abinda taji tana fada sanda hajiyan taje gidan da kanta tana shaidawa kawunsa mijin gwaggwon cewa ya samu aikin,tun daga matakin constable saai yanzun da daukaka ta fara zuwa masa ake kwadayin hada zuri’a da ita?,duk haqurinta da kawaicinta ita din ba mahaukaciya bace.

    Hirar duka saita fita akan gwaggwo fanteka ta zama mara dadi,don haka bata jima ba ta miqe ta yiwa hajiyan sallama ta fice.

    *WIDAD*

    Sanda ta bude ido ta ganta qofar gidansu sai taga kamar wasa,kasa jira tayi drivern da uncle muhsin ya daukar mata shata har qofar gida ya fidda mata kayanta,ta sauka daga nan ta nufi gate din da gudu gudunta,ji take kamar zata bude ido ta ganta ta koma bauchi.

    Cikin sa’a kuwa tana buda gate din ummun ta hanga tsaye a farfajiyar gidan ita da kawunnanta,sanye da atamfa da kuma hijabi,hannunta riqe da carbi,da alama salla ta idar suka tasota,akwai zancan da sukeyi.

    “Ummunaaa” ta fada da qarfi sannan ta kwasa da gudunta,ta isa gabanta ta fada jikinta tana ruqungumeta.

    Sai da ummun tayi taga taga zata fadi kawu ya tareta

    “Ashsha,ashsha,zata kada mana uwa” sai ta saki dariya tana sakin ummun suka miqe tsaye dai dai ummun itama tana dariya idanunta akan fuskar widad din,kamar fa shekara bata ganta ba.

    “Ke dawa?,yanzu kike tafe?” Ummu ta fadi tana dubanta

    “Ni kadai yanzu yanzu na qaraso”

    “Iyeee,muhsin din barmin ke yayi ke kadai kika kamo hanya?,tabdijan ,zamu hadu dashi kuwa”kafin ta qarashe drivern uncle muhsin din ya shigo da jakankunanta,suka gaisa yace zai koma,ummu tace a’ah sai yaci abinci,suka wuce ciki ita da widad tace taje ta kawo masa abincin,su kawu kuma suka fice bayan an bashi wajen zama anan farfajiyar gidan.

    Zuwa wani lokaci sai ga sassan ummu ya dan cika da sauran yaran gidan,su Aafiya rafi’ah fareesa da sauran wadanda suke shekaru kusan daya,sun baibayeta tana ta basu labarin bauchi.

    “Kano fa tafi dadi Allah” ta fada daga qarshe tana yamutsa fuska,dariya sukayi mata

    “Daga baya kenan,bayan kin gama kwanakinki” dariya tayi tana cewa

    “Da gaske nake muku,bari kuga” sai ta wuce daki ta janyo jakarta,ta fidda jakar ledar kayan makeup din da hajjaa ta damqa mata tace inji abbas,tunda ta taho kayan suke daukan hankalinta,komai na ciki ya burgeta ya kuma yi mata kyau,harda takalmi me tsini irin nasu basma da aka sako musu a lefe,tayita maitar takalmin sai basman ta jefa mata harara

    “Ba baki zanyi bafa,kiyi addu’a kema Allah ya kawo me siya miki” fushi tayi tana tura baki tabar gurin,sai gashi ta sameshi sama ta ka,bayan shi harda mayafi da hand bag qarama mai matuqar kyau,a nan ta zazzage musu kayan,suka dinga santinsu,daga baya ta daukarwa kowa wani abun daga cikin kayan kwalliyar.

    *************

    Kwana biyu a tsakani tana kitchen tana cin abinci suna hira da latifa,ta ajjiye warmer din data zuba abincin alhaji a ciki tana cewa

    “Ashe dan bauchi kika samo mana kuma” kallonta tayi tana ci gaba da cin abincinta,don ita har ga Alla ma ta manta da wani batu

    “Dan bauchi?”

    “Eh mana,naji abba mahmudu yazo suna zancan da alhaji ai”

    “Auho,wai abokin uncle muhsin”

    “Shifa” sai widad din tayi shuru kawai,don batasan me zatace ba,itadai ba sanin soyayya tayi ba bare ta tantance tana sonsa ko bata sonshi,kawai dai taji bata damu ba bata takura ba kamar sands ake zancan mahfood da ma’aruf.

    Sosai ummu ta dinga juya zancan bayan da mahaifin widad ya zartar da cewa an bawa abbas widad don,amma bata taba kawo cewa zasu nema aurenta a nan kusa ba haka,taji abun sosai a ranta,a yadda ta lura kuma shi mahmudu din a shirye yake da auren diyarsa,tasan watarana komai tsahon zaman da zatayi da qaunar da takewa widad su rabu dole ta aurar da ita,so a yanzun bataga nata hurumin da zata hanashi bada auren ‘yarsa ba,tunda dukkan bincike da shaidu sun tabbatar da nagartar me neman auren kamar yadda musulunci yayi umarni.

    Amma babban abun shine,kishiya daya tabbata widad din nada ita,ta yaya yarinya kamar widad din zata iya fuskantar abu me wahala da zafi kamar kishi?,bata sani ba,saidai tana fatan ko mai zaizo da sauqi fiye da yadda suke zata.

    Kwanan widad din biyu da dawowa maneman auren abbas din suka iso kano qarqashin jagorancin uncle muhsin,sunga karamci irin na kanawa,duk da cewa su din ba kanawa bane usul,amma tunda an haifi ‘ya’ya da jikokinta suna amsa wannan sunan.

    Cikin girma da mutunci gami da karamci suka gabatar da neman auren abbas ga widad din,aka sake jaddada basu,suka nema alfarmar karbar kudin aurensu harda sadaki,take alhaji yasa aka karba komai,suka karbi roqonsu na daurin auren sati mai zuwa.

    A ranar zancan auren widad ya fara yawo a dangi,abinka da family house,kowa idan yaji zai gayawa na kusa dashi,bugu da qari widad din ‘yar gatan ummu,mai masoya da kuma tarin abokan adawa.

    “Uhmmm,sunje sun zaba mata miji ba,ai dama wannan yadda akaci buri a kanta nasan sai me abun hannu zasu bata” wannan shine abinda wasu suka dinga fada,musamman da suka samu labarin muqamin da ya riqe a gwamnatin bauchin,da kuma wanda yake kai yanzu,gani sukeyi uncle muhsin ya dauketa ne dama kawai don ya aikata hakan.

    Ita kuwa sam batasan ma me akeyi ba,don har ta koma islamiyya,wadda tun tafiyarta qaunar makarantar bata bar ranta ba,sanda ta koma din sai ta samu basu wani tsere mata ba,tunda ta dora daga inda ta tsaya a bauchin.

    **********Karfe shida saura na yamma suka iso gidan ita da Aafiya rafi’ah da widad din,bayan tasowarsu daga islamiyyar,gab da zasu shiga gate din gidan Aafiya ta kalleta

    “Nifa zancan bikinki naji ummanmu tana yi,wai nan da sati daya”

    “Nifa abinda yake hadani dake tsokanarki” widad ta fada tana watsa ragowar alawar data siya cikin jakarta

    “Wallahi nima haka naji,don kafin mu tafi islamiyya naji umma tana waya a karbo atamfofi akai mana wajen mai dinki”

    “Mahaukata,sai kuyi ai” widad din ta fada tana yin gaba abinta tana dan waqenta.

    Bata ma tsayasu ba ta zarce sassan ummu abinta,tana sallama a falon ta soma zare hijabinta daya dameta,gashinta mai santsi ya ware,don dama ita din ba ma’abociyar saka dankwali bace,tafi sanya hula,itama ba ko da yaushe ba,sai ummu tayita fama da ita.

    Ummu da anty halima ne a falon

    “Anty halima ina nabiha?,kikace idan zaki sake zuwa tare zaku zo?” Widad ta fada tana barewa alewan ta tura bakin yaron anty halima dake kan cinyarta.

    Da kallo anty halima ta bita,tana dan jin tausayin widad din

    “Oh ni sadiya?,wannan wacce irin amarya ce ummu?” Dan murmushi ummun tayi,ita kanta tausayin widad din takeji,har yanzu ma bata zauna tayi magana cikakkiya da ita ba kan auren da tasan widad din batasan meye shi ba,bata kuma da labari cikakke akan yinsa.

    “Au ina yini?” Ta fada tana dariya bayan ta tuna nata gaidata ba,ba kuma tare data maida hankali ga maganarta ta farko ba

    “Lafiya lau widad,nabiha zasuzo,sai satin biki in sha Allah”

    “Allah ya kaimu” ta fada tana gyada kai hankalinta kwance,saita dubi ummu a shagwabe

    “Yunwa wlh nakeji ummu,dazu banci abinci ba Aafiya ta matsamin na taho mu tafi”

    “ki wuce latifa tana kitchen ki karba”

    “Tom” ta fadi tana wurga jakarta ta zarce kitchen din,yayin da dukka su biyun suka bita da kallo.

    Ummu ce ta fara dauke idanunta tana sakin ajiyar zuciya,anty halima tace tana dariya

    “Wai,wa yaga widad amarya” kai ummu ta kada

    “Tausayinta nakeji halima,ban taba kawo rabuwarmu a nan kusa ba” tabe baki anty haliman tayi

    “Kaji ummu,to mu da aka rabu damu din tun bamu kai haka ba me ya samemu?,gamu ragal damu?,itama zata ware ne kamar kowacce mace” kai ummu ta girgiza

    “Ba zaki gane ba halima,dukkanku kunfi widad wayo sanda aka muku aure,kawai don lokaci yayi ne ba yadda zanyi,amma ban shirya kaita wani uwa duniya ba”

    “Tunda dai babanta ya bada ita,alhaji kuma ya goyi baya dole saidai ayi haquri,yanzu kawai yadda za’a tattarata akaita bata iya komai ba,kunbi duk kun shagwabata,bata iya komai ba,komai yi mata akeyi” anty halima ta fada tana mele baki,ta rasa wanne irin so ummun takewa widad?,tamkar ma ba mahaifin widad din ta haifa ba,ita ta haifa,ko ita diyarta ta cikinta bata jin tana mata son da takewa widad din.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

     

    *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 27

    Arubuce Ta Ke 27

    Page 27

    Washegari yaran da suka tashi suka gansu wajen babansu sam basu damu ba,murna suka dinga yi abinsu,shi ya dinga tiri tiri dasu,ya shiga kitchen da kansa ya hada musu breakfast mai kyau,da yake ya iya abubuwa masu sauqi hakanan cikin abinci,saboda yanayin karatun da yayi.

    Sunci kuwa sosai kamar ba gobe,sai ya zauna yana kallonsu,zuciyarsa na gaya masa basa samun kamarsa,duk da store dinsa cike yake da cima kala kala,wani abun har ya rube ko ya lalace batayi amfani dashi ba bata kuma bayar ba saboda baqar rowa,yayi nasihar yayi nasihar har ya koma fadan amma a banza,mutum ne shi mai bajintar wadata iyali tun samunsa baikai haka ba,tun rank dinsa bai kai haka ba,baya son iyalinsa suga wani abu a wani gidan da babu shi cikin gidansa,to amma kusan duk wannan qoqarin nasa a yawancin lokuta a banza yake tashi.

    Ruwan tea kawai ya iya sha bayan ya tabbatar sun qoshi,duk ransa a jagule in yake,saboda har sanann hafsat bata bude qofarta ba,yayi knocking yayi har ya gaji,ya ajjiye mata nata breakfast din bakin qofa amma baiga ta bude ta dauka ba.

    Bayan duka sun gama ya maida kwanukan kitchen,ya zage kamar yadda ya saba yawa yawan lokutta ya soma gyaran sassan nasa,yayi masa qal yadda yakeso,ya canza bedsheet da sauransu,ya hada duk abinda ya cire da kayansu mimi da yayi musu wanka cikin laundry basket,ya aje inda mai wankinsu zai dauka,sannan shima ya shirya kansa sannan suka dawo falon hafsat din,koda wai zataji motsinsu ta bude qofar.

    Saidai har suka gama zamansu ba ita babu dalilinta,a taqaice dai har zuwa azahar bata fito ba,yanason fita masallaci sallah amma kuma bazaiyiwu yabar yaran su biyu cikin gidan ba,don ita mimi din ma ba wani cikakken hankali ne da ita ba,dole ya hada kansu suka wuce sassansa,acan yayi sallar,sai la’asar daya dawo dora musu abinci yaga babu plate din daya ajema hafsat din,da alama yunwa ta korota,ta bude qofa ta dauka kenan,sai ya saki qaramin murmushi ya wuce kitchen din.

    Har dare suka kwanta babu wanda yaga qyallinta,a taqaice dai washegari kusan abinda aka maimaita kenan,don haka a kwana na ukun ya shirya yaran da kayansu ya wuce gidan hajiya dasu.

    Kallon farko data masa tasan hatsaniya ke tashi a gidan,ta kuma san bata rasa nasaba da batun aurensa,bata matsa da jin ba’asin kawo yaran ba,saboda tasan shi da zurfin ciki,zaiyi wahala ma ya iya zama yana fadin cikinsa,ta daiyi murna da zuwan nasu,don ba zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ta faru ba.

    Ya jima a gidan,sai yammaci sannan ya wuce,a sannan tuni nawwara tayi bacci a jikinta,ta baiwa muneera ta kwantar da ita,sai data dawo ta zauna gefan hajiyan

    “Hajiya da alama anty hafsat fa……”

    “Na sani muneera” hajiyan ta katseta,saita rausayar da kai

    “Shima uncle,ya haqura kawai hajiya suyi zamansu mana,irin wannan babu dadi fa don Allah” kallonta hajiya tayi,batasan ko taji abinda uwayenta ke fada ba,har mamaki suke bata yadda suketa goyon bayan hafsat akan auren nan,wanda tasan tsabar son zuciya ne,amma babu wanda baisan halinta ba da dabi’arta,idan sunce basusan yadda abbas yake samun careless daga wajenta ba wannan kam ba zata musa ba,don babu da wanda yake zancan,amma kuma sauran dabi’unta da abbas din ya dinga yaqi ta gyara fa?,ita hajiyan tasna wasu,saboda takan bashi shawari idan ta fuskanci yana cikin damuwa ne

    “Ke yarinya ce,ba zaki fahimta ba,sannan keba namiji bace,nan ma ba zaki gane komai ba” amsar da hajiyan ta bata kenan,sai tace

    “K’nnnn,ai shikenan” base on her experience tayi maganar,saboda taga halin da mamanta ta shiga sanda babanta yace zaiyi mata kishiya,a sannan hajiyan ce ta shiga batun(muneera ‘yar dan hajiyan ce),duk da.bai fasa ba anyi,amma abubuwan da sauqi,to amma yanzun hajiyan da kanta takeson ayima anty hafsat din?.

    Yayi tunanin zata kaishi qara wajen hajiya ko daya daga cikin yayunsa maza kamar yadda ta saba a duk sanda wani rikici data kasa jurewa ya hadasu,amma sai yaji shuru batayi ba,bazai iya tuna rana daya rak da ya kai qarar hafsat din ga danginta ba,duk da tarin matsaloli da laifukanta,shi wanann ba dabi’arsa bace kwata kwata.

    Kwanaki biyar hafsat din tana a haka,cikon kwana na biyar din Allah ya jeho qanwar mamanta ita da naty ummee,matar data jima rabonta da gidan,yanzun ma.suna sukazo ta bayan layin,anty ummee ta roqeta su biyo.

    Yana farfajiyar gidan shi kadai yana duba jarida,suka gaisa dashi suka wuce ciki,ba jimawa anty ummeee ta dawo

    “Don Allah yallabai ka duba mana,hafsatun tana ciki kuwa?” Jaridar ya ajjiye ya miqe tsaye yana gyara shirt din jikinsa,yasan tana ciki,kawai taqi budewa ne tana zaton shine yake bugun,kuma a yau ya yanke zai balle qofar zuwa dare muddin bata bude ba,sai ya gewaye anty ummin yayin cikin gidan,ta bishi da kallo tana jaddada miskilancin sa,har yanzu yana nan dai ba abinda ya sauya.

    “Ki bude qofar, ummee ce” ya gaya mata kai tsaye,bai qara minti guda ba sai ga motsinta,ta murza key dun data sawa dakin ta bude.

    Wani irin scent ne mara dadi ke fitowa daga dakin,saboda qarancin iska me kyau,duk da akwai ac da fanka ta cikin dakin,amma baya zaton tana kunnasu,jikinta tun kayan daya dawo daga kaduna ya sameta dasu ne,da alama har wanka ta yiwa yajin aiki,ta nan inda yake tsaye yana iya jin sauyawar yanayin jikinta,sai ganshin kanta dake cuccure waje daya da alama bata tajeshi,fuskarta gaba daya ta kumbure,kamanninta sun dan jirkita.

    Harara ta watsa masa sannan taja tsaki,tsakin da yakai har kunnen anty uwani dake falonta,tadan kama baki tanason tabbatar daga inda tsakin ya fito.

    Ya tsani tsaki a duniya,ta kuma san hakan,shi yasa ta bishi dashi,ko zata samu ta fanshe bacin rai da quntata rayuwarta da yayi kaso daya cikin dubu na abinda takejin yayi mata.

    Bacin ransa ya daure,ya juya yana barin wajen,saita biyo bayansa a hankali har ya fita a falon,ita kuma ta qaraso ciki,suna hada idanu ta zube a nan ta saki kuka,ciwon dake danqare a ranta ya motsa mata,don a kwanakin ita daya ke fama da baqincikinta cikin daki,kwata kwata basirar ta gayawa wani bata zo mata ba,hasalima wayar tana kashe tun ranar,saboda abbas din ta kashe,bataso yayi kiranta ma.

    “subhanallahi meye haka hafsatu?” Anty uwani ta fada cikin firgici tana dago hafsat din,sai ta dan dauke kanta kadan saboda abinda ke tashi a jikin hafsat din,ta jata ta zaunar kan kujera sannan ta zauna dan nesa kasan da ita

    “Lafiyarki kuwa?” Anty ummee itama ta jefa mata tambayar tana kallonta,cikin muryar kuka kamar wadda akace wa’adinta ya qarato ta soma magana

    “Na shiga uku na lalace anty ummee,anty uwani wallahi mutuwa zanyi,abbas ne yace zai qara aure” ta qarasa fada tana rushewa da kuka,haushi da takaici ya qume anty uwani,yadda taga hafsat din ta aza hannu aka ta zauna dirshan a wajen tana musu irin wannan kukan na tashin hankali

    “Mutuwa fa kike fada hafsatu,kinsan mutuwar kuwa?” Anty uwani ta fada tana harararta

    “Sai an bita a hankali ai anty uwani…..sannu yi haquri tashi ki daina kukan” anty ummee ta fada yana dagota daga zamewar da tayi daga kan kujerar.

    Da kallon takaici anty uwani ta bisu su duka,ta da jin labarin abinda hafsatun keyi a gidanta,qazanta baqar rowa,ga rashin iya mu’amala da mutane,kuma ko a yanzun ta sake shaida tabbatar qazantarta,saboda yadda jikinta yake tashi ba kowa ne zai juri xama kusa da ita ba,da alama kwana biyar din kenan batayi wanka ba.

    Tana jinta sanda take rattabowa ummee labarin yadda komai yake wakana,tasani wanda suka fita ma sun gaya mata ba daukan shawara takeyi ba,ko a yanzun ma tasan idan tace zata gaya matan bata baki ne,don haka sai ta miqe

    “Kin gama ko na wuce kya taho?” Dubanta anty ummee tayi

    “Aah ki bari mu wuce tare mana”

    “Um um,yi zamanki,nikam ina da uzuri,saikin taho,hafsatu sai a qara haquri,ki duba dukka iya kurekurenki da abubuwan da kikasan bayaso ki gyara tun yanzu,Allah ya bada haquri” badon tasan anty uwanin bata da wasa ba,bata kuma daukan wargi da ashar zata maka mata,amma hakanan ta hadiye bacin ranta tace mata ta gaida gida da shaqaqqiyar muryarta data ci uban kuka.

    “Yanzu me kika yanke ke?” Anty ummee ta fada bayan ta dawo daga raka anty uwani,ragowar hawayen dake fuskarta ta share,tana jin gaba daya rayuwarta ta juya mata baya cikin kwanakin nan

    “Babu wata shawara ko dabara da nake da ita,kawai dai abinda na sani,koda tsiya ko da bala’i wallahi bazan bar wata mace ta rabi abbas ba,bazan iya zura ido ina raye ba abbas ya auro wata mace da sunan matarsa ba” jinjina kai anty ummee tayi

    “Amma ina ganin wanann ba dabara bace,kwata kwata ragon azanci ne,kinfi kowa sanin halin mijinki,idan yace yes babu wanda ya isa yasashi yace no,tunda ya niyyata babu wanda zai hanashi…..”

    “Niko naci alwashin koda ta qarqashin qasa saina hana shi auren nan anty ummee” ta fada idanunta na sake kadawa suna kuma sake cika da hawaye.

    Ajiyar zuciya anty ummeen ta sauke,sannan tadan gyara zamanta

    “Niko sai nace wannan din ba hanya bace mai bullewa,face hanya mai wahala da kuma sanya kashe kudi,a matsayinki na mace,mai yasa ba zakiyi amfani da KISSARKI ba?” A hagunce hafsat din take kallon anty ummee,saboda bata fahimci me tafi nufi ba gaba daya,mafita kawai take nema,saboda haka tace

    “Kamar yaya kenan anty ummee???”

    **********Tun daga ranar bata sake kulle kanta ba,saidai kuma sabgarta takeyi kawai ba tare data shiga sha’aninsa ba,bai damu can can ba,don ko sanda suke shirin ma ba wani abu take dauke masa ko takeyi masa ba,kusan ya saba….fiye da rabin hidimominsa shikewa kansa,saidai ya dan samu nutsuwa,tunda aqalla bata sake tada wata fitina ba,har abun yaso ya bashi mamaki sosai.

    ********Karfe biyar na yamma tana kitchen tana hada abincin dare taji knocking,ta fito a kitchen din tana gyara daurin zaninta daketa kwancewa tun dazu,don bata daurin baya sai daurin gefe,a cewarta yana damunta ne.

    Tana bude qofar sukayi arangama da yaron gidan wanda ke musu aike aike,sai ya danja baya kadan cikin jin nauyi saboda ganinta babu mayafi

    “Madam oga ne yace a kawo,masu kayan gado ne da furnitures,zasu kwashe wadancan su saka sabbabi,yace muzo dasu suyi aikin” ta zuba masa ido ne taga zaiyin ko bazaiyi ba,duk da zancan kullum yana ranta dashi take kwana take kuma tashi,duk da ranta a bace yake matuqa har komai ma baya burgeta,to amma kuma tana son alqawaruran da yayi mata din.

    “Su bani minti goma ina zuwa” ta fada tana juyawa,ya rusuna cikin girmamawa ya amsa mata da to.

    Dakinta ta koma ta fara kwashe abubuwanta masu muhimmanci waje daya,aikin nada dan yawa,don sai ta shiga dakinsu nawwara ma ta hada nasu kayan,tanason ta samu dan tayi,to amma tasan a dai dai wannan lokacin koda tayi waya gida babu lallai a samu me zuwa ya tayata,saboda kowa yasan halinta da dna banzan rowa,saidai kayi mata wahala,dole ta koma kitchen ta kashe gas din girkin,dama ba wani girkin arziqi ta aza ba,tafi sati ma basa abincin saidai yayo musu takeaway,ita kuma ta nema wani abun taci.

    Sai da ta kusa awa guda sannan ta gama,duk ya hada gumi saboda ba maison aiki bace,sanann ta koma kitchen tana maida numfashi,su kuma suka shiga aikin gyara dakunan.

    Ana idar da sallar magariba suka gama kafa kayan gadon,da yake ba mutum daya ko biyu bane,sun kusa su biyar,suna fidda wadancan kayan ta fito

    “Su kuma wadan nan za’a kaisu?” Ta tambayi shazali yaran gidan

    “Yace a fiddasu compound a ajjiyesu” kai ta kada

    “Ka bawa masu kayan gadon idan suna siyan second hand,tunda wadan nan ba wani dadewa sukayi ba,kuyi ciniki su baka kudin ka kawomin” kamar yace ba haka oga yace ayi ba,to amma sai yaga meye nasa?,tunda kayanta ne,kuma matarsa ce?,don haka ya amsa mata da to yana ficewa,ita kuma ta juya ta shige dakunan tana jan tsaki a ranta,kudi takeso ta tara mai yawa daga jikinsa,ko banza ta rage wani radadin.

    Sosai dakunan sukayi mata kyau,dukka ya zaba favourite colors dinta ne,dakunan sun canza gwanin sha’awa,duk da ranta a bace yake amma sai data danji ta sauka kadan.

    Ba’a rufa awa ba kuwa ya dawo mata da kudin kayan cas,ta karba ta soke abinta taci gaba da sabgarta hankali kwance,ranar baya nan,yaje azare,zai kuma kwana sai washegari zai dawo,don haka hankalinta kwance ta gama tsara abinda zatayi da kudin,koda kuwa ya dawo ya tambayi yadda akayi da kayan,barema tasan halinsa,zaiyi wuya ya tambaya din,don bashi da wannan,amma koda yana da niyyar ma ta shirya abin fada masa.

    *Arewabooks:Huguma*

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥[2/22, 2:45 PM] halimatuabidah: *H U G U M A*
    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 22

    Arubuce Ta Ke 22

    Page 22

    Nujood da widad dake tahowa yake nuna masa,baiji abinda yace ba,yadai ci gaba da kallonsu,suna sarqafe da hannun juna,widad din tana jin gabanta na faduwa ne gami da sanyin jiki haka kawai,yayin da nujood ke tsokanarta,har ta daga qafa zata dan bi nujood din da gudu sai kuma ta tuna taga qofar setting room din a bude,wannan yasa takai idanunta ciki,bata hango wadanda ke ciki tar,saidai ta tabbatar suna iya kallonsu.

    Da sallama suka shigo,suraj ne ya amsa musu fuskarsa da murmushi,nujood din na riqe da hannun widad suka qarasa cikin falon.

    Nujood dince ta fara gaida abbas,fuskarsa kadaram kadaham ya amsa,already ta san halinsa,bai fiya fara’a ba don haka bata damu ba,ta maida akalar gaisuwar ta ga suraj

    “Lafiya lau,ya karatu?” Ya amsa mata cikin fara’a da murmushi

    “Alhmdlh” tuna abinda hajjaa tace da ita ya sanyata miqewa

    “Saikin shigo” ta fada tana duban widad cikin salo na tsokana,wanda iya ita da ita ne kawai zasu fahimta.

    Maganar nujood din taja hankalin abbas harma da suraj,tunani iri daya ya darsu a ransu lokaci guda,kowanne dubanta yake,abinda ya sanyata taji kamar an aza mata wani nauyi,gaba daya ta jita kamar a daure,kallon da suke mata yana neman daburtata,tana takure a gefe tsakanin kujeru tana wasa da gefan mayafinta,saita nannadeshi ta wareshi,suraj ya fuskanci hakan,don haka yayi gyaran murya,cikin murmushi kuma yace

    “Barka da fitowa ‘yammata” muryar suraj din saita ankarar da ita mantuwar da tayi bata gaidasu ba,don haka ta daga kai in ta fara gaida suraj din,cikin sakewa da fara’a da kuma kulawa ya amsa mata,sa’annan ta koma ga abbas,idanu saika hada,take taji ya fiya kwarjini da yawa,tunda suka shigo kuma ta karanci fuskarsa bashi da yawan fara’a,sannan koda bata dade a wajen ba alamu su nuna yana da yawan shuru shuru,don ko daya bataji muryarsa ba tun bayan daya amsa gaisuwar nujood

    “Ina yini” ta fada tana kaida kanta,sai daya lumshe idanunsa ya bude sannan ya amsa mata,’yammatan daya fada sai abbas yaji kamar gatse ne yake masa,zaqin muryarta kuma me cike da zallar quruciya na zaga kwanyarsa

    “Kada dai ya kasance ita hajiya ta zaba masa?,anya kuwa?” Kamar suraj yasan tambayar dake yawo a ransa kenan,sai ya tsinceshi yana cewa

    “Allah yasa kece wadda hajiya tace muzo mu gani?” Kanta a qasa kawai ta gyada kanta,amsar data tilastawa abbas maida bayansa jikin kujera ya jinginar kawai idanunsa a lumshe.

    Yana iya jin yadda suraj keta janta da hira,tana amsa masa da qyar,muryarta cakude da kunya da kuma tsoro hadi da rashin sabo,tunda suraj din ya kalleshi ya karanci yanayinsa,wannan yasa ya karbe hirar abinsa ba tare daya sanyoshi ba,kamar ma shi abbas din ya yiwa rakiya.

    Jinnta take a takure kota ina,musaman idan ta waiwaya inda abbas din ke zaune abinsa ya sanya musu kunne

    “Wannan abokin nasa,ko me yasa yazo dashi?” Abinda tayita fada kenan a ranta

    “To widad mu zamu wuce,sai kuma wani jiqon?” Suraj ya fada yana duba agogonsa,maganar data yiwa widad din mugun dadi,don kafin ma ya miqe ita ta miqe tana cewa

    “Ku gaida gida” saita kada kai abinta tayi hanyar ficewa,a lokacinne abbas ya bude manyan idanunsa yana binta da kallo

    “Minti daya mana malama widad” suraj ya fada yana miqewa da ledar siyayyarsa a hannu yana yiwa abbas sign din ya tashi mana,sai ya kauda kai kamar bai gani ba,don haka ya taka ya isa inda take tsaye ya miqa mata ledar,cikin ransa yana fadin siyayyar kuwa ta dace da ita

    “Ga wannan ko babu yawa” sai data dora idanunta kan abbas dake zaune daga bayan suraj din taga ita yake kalla sannan ta saka hannu ta karba gabanta na faduwa

    “Na gode” ta fada tana ficewa a dakin da hanzari gabanta na wani irin faduwa.

    Da baya suraj ya dawo a hankali yana hararar abbas

    “Duk alamar da nake maka ka tashi ka miqa mata don ta fuskanci ma waye abbas din a cikinmu amma kayi banza dani?”

    “Wai kanason kacemin wajenta mukazo zancan?” Abbas din yayi tambayar hankalinsa kwance,sai haushi ya kama suraj,ya watsa masa harara

    “Ban sani ba,next time dama idan zaka zo kada ka sake ka kirani,idan kazo kai kadai zaka gane wajen wa kazo din,tashi mu tafi,ka barni ni kadai sai zuba nake”.

    Cikin mota gaba daya kansa ya kwance,me yasa hajiya ta dauko masa wannan?,ta yaya zai samu sauqi ko kulawa daga wajenta,kansa kada,gaskiya bazai iya sake zuwa zance ba,yaje yace mata me?.

    Yana jin suraj yana ta hirarsa amma bai saka baki ba,saboda gaba daya tunaninsa na ata wani waje,suffarta da kamanninta yaketa qoqarin maidowa idanunsa ya hadasu waje daya,babu qarya…..tana da kyau,ita din kyakkyawace ta gasken gaske,to ko kyawun hajiya ta gani?,sai ya sake girgiza kansa,yasan hajiyan,tasan abun qwarai sarai,bai gano me ta hango masa ba,amma ya tabbatar akwai abinda ta hanga din.

    Saida suraj ya ajjiyeshi a gida sannan shima ya wuce,abbas din ya masa ban gajiya da godiya

    “Ai babu wannan tsakaninmu,kawai dai next time ka tafi kai kadai,saboda ka samu ku fahimci juna sosai, she’s too young,dole sai kana janta a jiki da dabaru sannan zata saki jiki da kai,amma kuma ina me tabbatar maka indai aka samu shaquwa sabo da kusanci tsakaninka da ita,ina me tabbatar maka…..ina sake fadi ina mai tabbatar maka anan zaka fahimci komai basai an gaya maka ba” abinda suraj ya gaya masa kenan,wanda ya tsaya masa a rai,ya kasa fahimta kuma,da wannan maganar ya kwanta.

    Ita kuwa widad tana fitowa ta qara da dan gudu gudu,wani irin tsoro takeji da faduwar gaba sosai,don sai data tsaya a hanya tadan saisaita numfashinta tana dafe qirjinta da hannu,batasan me yasa batason wancan abokin nasa yana kallonta ba,to amma itafa wallahi mai wanna zubar maganar indai shine wanda uncle muhsin ya turo mata baiyi mata ba sam,saita tabe baki tana buda ledar daya bata,murmushi ya subuce mata da taga masoyiyar wato chocolate,saita zabura tayi cikin gidan tana qwalawa nujood kira.

    “Iyyeee,yammatan ummu,da alama ciniki ya fada tunda naga kin dade da yawa” hajjaa ta fada cikin salon tsokana tana murmushi,baki ta tura gaba tana ajjiyewa hajjaa ledar,kanta tsaye cike da zallar wautar quruciya tace

    “Ni gaskiya indai wannan mai surutun ne bana sonsa” dariya nujood ta sheqe da ita,kafin tace komai hajjaan da uncle muhsin ya bata aikin tuntubar widad din idan ta dawo aji ta bakinta tace da ita cikin tattara hankalinta

    “Saboda me?”

    “Ya cika siranta,kuma ya fiya magana” wannan karon nujood dariya harda fadowa

    “Bafa uncle abbas take fada ba,uncle suraj ne wallahi take nufi” sai hajjan itama ta saki dariya,tasan suraj din,duk da ba sosai ba,amma sai da nujood ta fada sannan ta tuna tabbas yana da kirki yana kuma da hira

    “To alhamdulillah,indai hakane uncle abbas yayi kenan?” Ta fada tana kallon widad,yadda suka tsareta suna jiran amsarta ya bata kunya,saita dauki filo ta cusa fuskarta a ciki tana dariya cike da jin kunya

    “Allah nidai hajjaa….”kunya ta sanyata tashi da gudu tayi dakinsu,sai suka bita da dariya,hajjaa taja chocolate din ta ajjiye da nufin idan uncle muhsin ya dawo ta nuna masa kafin su taba,ta kuma hada da gaya masa yadda sukayi da widad din.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 96 09 67 63

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/18, 12:43 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

     

  • Arubuce Ta Ke 18

    Page 18

    Shi kansa zancan yazo masa a bazata,sai ya ajjiye spoon din hannunsa yana duban hajjaa

    “Abbas….abbas nawa fa” kai ta gyada

    “Eh shi” kamar me jiran hajjaa ta tabbatar masa da batun sai ga kiran hajiya ya sake shigowa wayarsa,ya kalli wayar na wasu sakanni zuciyarsa na gaya masa da gaske hajiyan take,tunda har ta kasa sakat saita samu tabbacin isar saqon kunnensa,ya dauka wayar a nutse ya kara a kunnensa

    “Ina fata saqon nawa ya riskeka?” Kai ya gyada kamar tana gabansa

    “Eh hajiya,yanzun take isarmin dashi”

    “To alhamdulillah” ta fadi tana sauraren ji daga gareshi

    “Amma hajiya….wani hanzari ba gudu ba,kina ganin babu matsala daga wajen shi abbas din?” Yayi tambayar saboda sanin halin abokin nasa,sun jima a tare tun zuwanshi bauchi,duk da cewa ya girmewa abbas din,amma suna tare dashi,don itama dama abota ba sai da sa’anka ba,takan iya zuwa ta kowacce fuska,Itama hajiyan kai ta kada kamar yana wajen

    “Bani da haufi akan abbas ko kadan,bamu ita din shine mai wuyar” sosai hajiyan ta aza masa nauyin da bazai iya kufcewa ba,tana masa kallon mazaunin uba a wajen widad,tasan kuma ya isa ya zartar da hukunci a kanta shi yasa ta nemeshi kai tsaye,uwa uba kuma abbas din wani irin mutum ne mai kima da daraja a wajensa,yafi kowa sanin irin qaunar da yakema mahaifiyarsa,kamar yadda ta dauki shi shima a mazaunin d’a,bai kyautu ya dubi tsabar qwayar idanunta yace mata bazasu bada auren widad ga abbas din da yana sahun farko farko na wadanda zasu bada shaidar kyawun hali da nagartarsa,bayan gajeran nazarin da bai wuce shurun sauraren hajiyar ba ya amsa mata

    “Hajiya ai abbas nawa ne,babu damuwa,an bashi widad,zan kuma sanar da can gida in sha Allah”. Irin addu’ar da yaji hajiyan tana kwararo masa sai da abin ya bashi mamaki,wanne irin so take mata haka?,lallai da bai amsa ba Allah ne kadai yasan rashin dadin da zataji,duk da ba zata nuna masa ba.

    Wayar ya ajjiye gefe,ya daga kai yana duban hajjaa data tsareshi da idanu,kafin yace komai ta rigashi

    “Abbaa,aure fa kake bayarwa,auren widad din da ummu ta baka aronta?,ba tare da sahalewar ummu ko yaaya mahmud ba?” Dan gajeran murmushi ya saki

    “Yadda zan bada auren nujood kai tsaye babu haufi haka zan bada na widad,ina da wannan license din”

    “Amma kana ganin aurenta da abbas yayi dai dai?” Ta sake tambayarsa cikin jin d’ar d’ar da fargaba

    “Yana da wani aibune da musulunci yace idan namiji yana dashi bai cancanci ku bashi auren diyarku ba?” Kai ta girgiza da sauri

    “Ko kadan,abbas nagartaccen mutum ne mai kyawawan dabi’u abun kwaikwayo,amma abba kada fa ka manta yana da mata,sannan matarsa din nan ko kwanaki na danji ana kuka da ita,bata da kirki abba,zamansu da widad mai qananun shekaru a mazaunin kishiya zai yiwu?”

    “Duka ba wannan bane abun dubawar ba,tunda ba ita zata zauna da ita ba,indai ya cancanta magana ta qare” sai ya dauki spoon dinsa yaci gaba da cin abincinsa,dama tasan haka zaya fada,su maza nasu hangen daban dana mata,gaba daya hanakalin hajjan bai kwanta ba,bawai don abbas bai cancanta bane,aah,tana duba wani abu na dabanne,don haka ta gaza barin maganar

    “Gaskiya abba bazan tayaka gayawa ummu wannan maganar ba wallahi,kada ka sani a ciki” dariya yadan saki

    “Matsoraciya,yo waye ya sanya dama dake?”

    “Amma zataga a gidana aka shirya fa,gashi widad dinma ta matsu tana son zuwa gida,ya za’a yi kenan?”

    “Dama ina tunanin next week qarshensa taje taga ummu din,saboda ita kanta ummu kwanan nan maganar na dawo mata da yarinya taketa yi” shuru ya ratsa tsakaninsu,har uncle muhsin din ya fuskanci kamar ta shiga damuwa ne,don haka yayi gyaran murya

    “Ni banji komai game da haka ba hadiyya,abbas yana da nagartar da ko nujood yace yana so zan bashi,zai riqe mana widad da amana, sa’annan kuma ina da tabbaci hundred percent karatunta bazai yanke ba,zataci gaba da karatu har zuwa inda takeso,so kinga babu wannan haufin”

    “Gaskiya kam” ta amsa masa tana dan jin nutsuwa kadan,to amma batun zama da kishiya tasan ba abu bane mai sauqi,koda ga babbar macace bare yarinya irin widad,GOYON KAKA.

    **********

    Tunda hajiya ta samu tabbacin samun widad daga wajen uncle muhsin wata nutsuwa da farinciki ta dinga saukar mata,haka kawai ta dinga jin nutsuwa da gamsuwa da al’amarin,ta dinga ji kamar ta daga waya tace yazo tana son ganinsa,to amma tasan zuwa qarshen wata zai zo ganinta,babu buqatar ta daga masa hankali ta sanyashi biyo hanya,sai tayi amfani da wannan damar ta yawaita addu’a kan Allah ya sanya dukkan alkhairinsa akan lamarin,yasa ayi a sa’a,ya kade dukkan fitina.

    ************

    Dukka shirin da yakeyi tana zaune gefan gado tana kallonsa,a yanzun da zai tafi bauchi tana jin inama yace ta shirya ta bishi,zaman garin ya gama kai mata ko ina,daurewa kawai take tana cijewa,ita kam duk inda zama zai kaita indai ba cikin garinta ba bataso.

    Bugu da qari taga sabon key din mota garin bincike bincikenta,tana sake dauriya akan dauriya ne cike da fatan wannan motar ta zamana tata ce kamar yadda anty ummee data baiwa labari tayi mata hasashe.

    Tsaf ya shirya cikin yadin kufta,wanda yayi matuqar masa kyau,ya fidda kwarjininsa da kuma kyan zubi da Allah ya bashi,saita sake karkata kai tana qare masa kallo,sau tari ita kanta takan gayawa kanta tabbas abbas wani rabo ne nata da Allah ya tsaga mata sai ta sameshi,amma ita kanta idan ta tsaya ta kalli kanta tana gano tarjn banbance banbance tsakaninta dashi,shi yasa take qara matsa qaimi wajen kishinsa,saboda tana tsoro…..tana tsoron kada idanun wata ya fada kansa,ta kuma sani wasu ‘yammatan indai suka baza komarsu sai sun samu,bata fiya damuwa dashi ba,tasan sam mata basu a lissafinsa,amma shi din yana cikin lissafin gomayyar mata da suke kwana su kuma tashi da soyayyarsa,koda cikin danginsa kuwa tana da wannan information din akansa.

    Hure mata idanu yayi da sassanyar iskar bakinsa,abinda ya sanyata ja da baya da sauri,sai kuma ta saki murmushi

    “Har ka bani tsoro” ta fada tana dan harararsa

    “Ni kika bawa tsoro,wannan kallon kamar zaki cinyeni?” Murmushi ta saki

    “Da da hali cinyekan zanyi,don banason kowacce mace ta kalleka kota rabeka,ni kaina bansan adadin kishinka da nake ba” daga kai yayi ya kalleta daga daura agogon da yakeyi,har launin fuskarta ya sauya,sai ya maida kai yaci gaba da daura agogonsa ba tare da yace da ita komai ba.

    Ya rasa wanne irin dan banzan kishi take dashi,wanda kullum baya raguwa saima daduwa da yakeyi,abun takaicin har yau batasan yadda zata tsare masa komai ba,inda yadda take kishinsa haka ta tsaya masa wajen komai da lallai ya gama yin sa’a.

    Ganin bai bata amsa ba tasan bazai ce komai ba,don haka ta sauya akalar maganarta

    “Nidai da zaka barni Allah wannan watan zan bika,kamar na shekara banje gida ba haka nakeji”

    “Sai next month kamar yadda nace” ranta tadan bata kadan,har ya gama shirinsa ya fito bata sake magana ba.

    “Rakiyar ta isa daga nan” ya fada yana dakatar da ita daga qofar falon,saboda akwai driver daga waje da zasuyi tafiyar tare,mutum ne shi mai tsananin kishin iyalinsa,yakai bakinsa saman goshinta yayi kissing dinsa yana fadin

    “Sai na dawo,ki kula da gida da yaran”

    “A dawo lafiya” ta fada a taqaice tana dubansa har ya fice,tana tsaye ta window tana leqensa har motarsu ta fice,taja da baya ta zauna saman kujera tana jan tsaki

    “Babu biki ba suna ba barka,an takure a baqon muhalli” ta sake fadi a fili,sai kuma ta miqe ta nufi dakinsa,ta buda ta shiga ta isa inda taga key din motar,ta jawo da zummar sake duba motar wacce ce?.

    Wayam taga wajen babu muqullin,ta shiga birkitawa kamar wadda ta bashi ajiya,saidai babu shi ba alamarsa,da alamu ya dauka kenan,to amma me zaiyi dashi?,ta tambayi kanta tana zurfafa tunaninta,to ba tata bace kenan?,amma kuma motar da suka fita cikinta ai tasan motar,ba sabuwa bace,gaba daya sai ranta ya baci,ta jawo waya kamar zata kirashi ta tambayeshi sai wata zuciyar ta hanata,ta shawarceta ta bari ya isa gida tukunna.

    *_RUMBUN K’AYA_*
    *_IDON NERA_*
    *_DAUDAR GORA_*
    *_KI KULANI_*
    *_A RUBUCE TAKE_*

    Littafi daya—400
    Biyu—600
    Uku—-800
    Hudu—–1k
    Biyar din duka—-1200

    *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank.

    Shaidar biya tanan👇🏻
    09033181070

    *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

    09166221261

    🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
    *Ina yan uwa ‘yan nijer?*
    *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

    +227 90 16 59 91

    Littafi daya—450CFA
    biyu—650CFA
    uku—-850CFA
    hudu—-1050 CFA
    Biyar—-1250CFA

    *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

    *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

    *Thanks for choosing us*🔥[2/16, 9:04 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 19

    Arubuce Ta Ke 19

    Page 19

    Kafin ya iso tuni hajiyan ta sanya an tanadar masa abincin da yafiso har kala biyu,irin abincin da tasan zaiyi wuya ya samu a gidansa,duk da qaunar da yake masa,ta kuma hada masa lemo shima kala biyu,zobo da kuma ginger drink da aka dan matsa lemon tsami kadan a ciki qamshinsa ya fito.

    Da yake tun karfe tara na safiya ya taso,ana azahar yana shiga layinsu,jakarsa kawai ya bayar aka shiga dasu shi da drivern nashi da yake usulmi ne suka wuce masallaci.

    Ana idar da sallah yace masa zai juya ya koma kaduna,yasan akwai aikin da ya baro,saboda haka bai matsashi ba,yadai karba abincin wajen hajiyar ya hadashi dashi,yace yaci a mota,ya kuma fidda kudi masu dan nauyi yayi masa ihsani,wannan yana daya daga cikin abinda yasa abbas din ke samun biyayya da qauna gami da daukaka a wajen aikinsu,duk da biyayya dole ce a tsarin aikunsu,amma suna masa soyayya ne ta har cikin ransu saboda kyawawan dabi’unsa.

    Cikin nutsuwa ya shiga gidan nasu,yana jin farincikin ganin hajiyar tasa,jtama tana falo a zaune tana ta dakon shigowarsa,ta amsa sallamarsa ya sanyo kai falon fuskokinsu dukka dauke da murmushi.

    Kamar kullum ya duqa a qabanta ya gaidata,ta amsa masa cikin kulawa addu’a gami da tambayar lafiyarsa data iyalinsa,ya tabbatar mata da komai lafiya lau,ya kuma isar mata da saqon gaisuwa daga hafsa din,wanda a zahiri bata samu hakan ba,shi ya qirqira abinsa saboda sama mata soyayya da kuma kare martabarta a idanun mahaifiyarsa.

    Da kanta tayi serving nashi,yana cin abincin suna hira,wanda kusan abubuwane da suka dan faffaru da baya nan,ciki harda ciwon da diyar babbar yayarsu tayi

    “Zanyi qoqari na shiga in sha Allah”

    “Ya kamata,don ka kwana biyu bakaje mata ba,tana ta min qorafi rannan”

    “In sha Allah”.

    Sai da aka kira la’asar sannan ya fita a falon,yace ma hajiyan zaije wajen Suraj,amma bayan magariba zai dawo

    “To Allah ya tsare,akwai maganar dama da nakeson nayi dakai”

    “To bari na zauna mu gama sai na wuce”

    “A’ah,jeka abunka,idan ka dawo mayi maganar,Allah ya tsare”.

    Tsahon lokaci suka dauka shi da suraj din,saboda kwana biyu basu hadu ba,yanayin ayyuka da canjin muqamai da abbas din ke samu a kufi a kufi,anan suraj din ya samu damar masa qorafin

    “Naji mamaki sanda naji ka ajjiye appointment dinka,dama cefa da ‘yan sanda da yawa suke jira” kansa ya shafo kadan yana duban suraj din

    “Nafi nutsuwa da hakanne suraj”

    “To kuma gashi sun biyoka da asp ba”

    “Gwara wannan kam,qarin matsayi ne,a tayamu da addu’a Allah ya bamu wuyan dauka da saukewa”

    “Ameen ya rahman”.

    Bayan sun idar da magariba suka sake fita da suraj din a mota ya rakashi wani waje,a hanya ya tsaya qofan wani suya spot yana kashe motar

    “Kadan rakani ciki na yima hajiya siyayya mana”

    “Ba damuwa muje mana”,tare suka jera xuwa cikin,suna tafe suna hira har suka isa,suka wuce kai tsaye inda zasu bada order din abinda sukazo siya din.

    Sun samu ‘yammata biyu tsaye gaban kantar,wanna yasa abbas din ya bada taqi a tsakaninsu,ya tsaya daga baya baya suna ci gaba da magana da suraj din,irin hirar da ta shafesu.

    Tunda suka tsaya din gaba daya hankalinta ya karkata a kansa,ba qaramun daukan hankalinta abbas din yayi ba,shigar qananun kayan dake jikinsa sun taimaka wajen fidda surarshi ta qaqqarfan namiji,har suka gama biyan abinda zasu siya din,saita bude da duba wayarta tadan matsa gefe kadan tana cewa qawarta

    “Ina zuwa”.

    Hankalinsa nakan suraj yana saurarensa yana saka order din abinda yakeso,har yaso yayi mistake ma saida waiter din yayi masa magana,aka hada masa komai ya irga kudin cikin wallet dinsa ya aje musu,saidai garin daukan ledan bai ankara ba ya dauki tata ledar,tana sane ta barshi har sai da isa gaban motarsa sannan yaji ana fadi cikin siririyar muryarta dake nuna zallar yauqi da gwalli

    “Hi…..hi,ranka ya dade” cak ya tsaya,don har ya bude murfin motar,ya waiwayo don ganin ko dashi ake.

    Da murmushi ta dinga jifansa har ta iso,cikin tausasa muryarta tace

    “Yallabai ledata ka dauke” ledar hannun nasa ya daga ya kalla,sai sannan ya lura,ya sauketa gami da miqa mata yana cewa

    “Sorry”

    “Ba laifi ai,hakan yayimun,kaga ko babu komai leda zata qulla mana zumunci” bai amsa mata ba illa amsar tasa ledar da yayi

    “Sunana rafi’ah” tayi saurin fada ganin yana shirin shigewa motarsa

    “Good,thank you ko” matsowa ta sakeyi don fa fuskanci rufewa zaiyi

    “Ko zan samu digits naka?”

    “Am sorry to say no” ya fada yana maida murfin motar a hankali ya rufe,sannan ya tashi motar yayi reverse suka fice daga wajen.

    “Har yanxu kana lokaci mutumina,bansan me yake fusgar hankalinsu ba haka,adan bani sirrin mana” ya fuskanci sarai abinda suraj yake fada,fuskarsa kadaram kadaham ya waiwayo kadan ya dubeshi sannan ya maida kansa ga titi

    “Kai har yanzu baka girma na suraj,ana ta neman na abincin da za’a kaiwa iyali kuma wa yake ta wannan” ya fada yana shafar habarsa dake zagaye da gemun daya samu wadataccen tsafta da gyara

    “Banga alama ba,don duk sanda muka fito irin haka sai wata ta taya”

    “To ai sai suyita yi,ta gidanma ya ka cika da ita bare ka sake daukan wata,kayita hadama kanka rigima da zafi,bazan iya daukan wannan ba”

    “Fada dai kake,bari ayi katari da wadda zata sace maka zuciya”

    “Haka kake gani” abbas ya maida masa amsa,hankali da idanunsa naga titi.

    Dariya kawai Suraj yayi,bai sake cewa komai ba suka shiga wata hirar.

    Sai daya fara sauke suraj a gida bayan ya hadashi da tashi ledar sannan ya koma gidan hajiyan.

    Bayan isha’i ya zauna sukaci abinci,kusan tare da hajiyan,saidai kowa kwanonsa daban,bayan sun kammala ya dauke kwanukan da kansa ya tattare wajen sannan ya dawo ya zauna yana fuskantar hajiyan

    “Hajiya kince zamuyi magana ko?” Gyara zamanta tayi sosai

    “Eh tabbas”

    “To ina jinki,Allah yasa ba wani laifi nayi ba” murmushi ta sake

    “Laifi abbas?,a’ah ko kadan,wani alkhairi na hango maka,na kumayi karambanin zartar maka dashi ba tare dana tuntube ka ba” qaramin murmushi ya saki

    “Hajiya…ai kinfi qarfin ki yiwa rayuwata karambani,kome kika ga dama ki zartar dashi kanki tsaye kawai” kai ta dan jinjina sannan tace

    “Aure na nema maka,’yar uwa ko ‘yar muhsin” sosai gabansa ya fadi,abinda ya jima baiji irinsa ba tsahon rayuwarsa

    “Hajiya nujood?” Ya fada cikin fargaba,don ko da ya kasance itace bazai iya musawa hajiyan ba,haka zai auretan,yarinyar dake kallonsa a mazaunin ubanta

    “A’ah,widad” ajiyar zuciya ya sauke,sai yaji tashin hankalin da yake ciki din ya ragu,ya samu ‘yar nutsuwa,duk da fahimci wa take nufi din ba,amma dai ya fahimci wata ce daban ba nujood ba

    “Inason kaje ka ganta,duk da ina zaton zuwansu gidan nan kamar ka taba ganinta,amma wannan zuwa ne na musamman,kaje ka gabatar mata da kanka” kai yadan sunkui qasa

    “In sha Allah hajiya zan saka rana sai na sanarwa muhsin din sai naje” har cikin ranta ta sake qaunar abbas din,tasan dama bashi da matsala kome kuwa tace yayi,saidai ta dauka zaiyi jayayya ko ya qalubalanci wannan danyan hukuncin nata.

    Duk yadda yaso ya fidda damuwa ya zauna suyi hira sosai amma ya kasa,jiki da zuciyarsa dukka a takure suke,dole bayan qarfe tara ya yiwa hajiyan sallama ya wuce gidansa.

    A kan hanya yana tuqi amma tunani ne fal kwanyarsa,aure?,wacece widad din ma?,oho shi bai ganeta ba,amma me hajiya ta hango masa?,sai Allah,bazai iya mata wannan tambayar titsiyen ba,da wannan damuwar da kuma tunanin ya isa gida.

    Bashi da hadi da sassan hafsa,don haka sassansa ya wuce,yabude ya shiga yana tsaye tsakar falon kamar maison tuna abinda ya kamata yayi wayarsa ta dauki sassanyan busar sarewar dake a mazaunin ringtone dinsa,don bayason ringtone mai hayaniya da yawa,mafi yawan lokutta ma yafi barin wayar tasa a vibration.

    Cikin wata kasala da gajiya da maganar hajiya ta saukar masa ya zaro wayar yana duba me kiran,hafsat dince,sai ya daga kiran yana neman kujera daya cikin falon ya zauna

    “Ina ka shiga ne inata kira baka daga ba” ta fada muryarta a tsaye carrr,alamun qagauta da son samun mutum,shuru yayi yana nazartar muryarta

    “Lafiya?” Ya fada da nutsatsiyar muryarsa mai nauyi,wadda ta dawo da hafsat din cikin nutsuwarta kadan,ta kuma fuskanci yanayin data masa magana baiyi dai dai ba,kishi ne keta cin ranta,har idanunta suka so rufewa,gani take kamar yana tare da wata ne shi yasa yaqi daga wayarta,

    “Ah….uhmm lafiya qalau,kawai hankalina ya dan tashi da naga inata kira baka daga ba”

    “Oh…..am fine,kufa?”

    “Lafiya qalau muke,yara gaba daya sunyi kewarka”

    “That’s my babies…..kefa?” Ya fada yana danne damuwarsa,murmushi ta saki wanda ya jiyo sautinsa

    “To nima nayi” ta fada tana danjin nauyi,idanunsa ya lumshe yana kuma budesu,she’s not romantic woman at all,ya rasa yadda zai canzata,kamar irin matan da soyayya bata damesu ba sam,dai dai da greetings cards da yake siya mata time to time,musamman idan yayi tafiya ya dawo bata wani daukar abun da muhimmanci,wani lokaci ma idan ya kawo cards din bata ko budesu bare ta karanta,karba take ta ajjiye bayan ta bishi da SANNU.

    “I miss you more than you can imagine” ya fada with softness,wanda har sai data ji tsigar jikinta ta tashi,wani abu ya tsarga mata,amma sai tace

    “Allah ya qara zumunci”

    “Zumunci dai?” Ya maimaita a ransa,even kalmomin da zatayi appreciating nasa bata dasu,har ya fara sabawa.

    Shurun da ya gilma tayi amfani da wannan daqiqun

    “Magana da zamuyi ko ince tambaya zanyi”

    “Am sorry ranki ya dade,yanzun nan na shigo gida,bari na gama shiryawa saina kiraki,inaso yau ayimin hira sosai,na gaji da yawa”

    “Kai da kaje hutu?,me kayi daya gaji da kai?” Ta fadi da salon tambaya,ita sam hankalinta bai kwanciya idan basa tare

    “Yawo” ya amsa mata a taqaice,sai ranta ya sosu,anya ba abinda take zato bane

    “Yawo kuma abban mimi?,don Allah ka daina banso wallahi”

    “It’s okay” ya fada fuskarsa na fidda miskilin murmushin da bai shiryawa ba,yasan meke damunta

    “Ka kira da wuri,don bacci nakeji inason na kwanta”

    “Okay” yace da ita yana katse wayar gami da ajjiye ta gefe

    “Hafsat hafsat,ko sai yaushe zata canza?” Yayi maganar shi da zuciyarsa,sai ya miqe yana wucewa bedroom.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so,zasu fara fita a gobe da izinin mai duka_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 90 16 59 91

    *Zafafa biyar kadai keda sinqin nau’ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci guda*🤝😄

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/16, 9:04 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks: Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 17

    Arubuce Ta Ke 17

    Page 17
    ____________________________

    *_KAMSHI!_* *_KAMSHI_* *_KAMSHI_*

    *TABBAS K’AMSHI RAHAMA NE. INA MASU NEMAN INDA ZASU SAYI TURARUKAN WUTA MASU KAMA GIDAH! DA TURAREN KAYA, TURAREN TSGUNNO, TURAREN WANKA DANA WANKI DA JIKI?*

    _KAI BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA TURAREN KHUMRAH KALA KALA DA KULACCAMS NA KECE RAINI._

    _AROOS_SCENTS_
    _AROOS_SCENTS_
    _AROOS_SCENTS_

    _KUNJI SUNAN KO? *AROOS_SCENTS*_

    _*AROOS SCENTS* SUNA GARIN *KADUNA* SUNA KUMA TURA KAYAN SU A FADIN NAJERIYA DA KETARE_

    _LAMBAR WHATSAPP DIN SU :07067786384_

    _INSTAGRAM : aroos _scents_

    _SCENT HEAVEN😍SMELL RICH! LEAVE DEM WONDER WHAT YIU USED…😍A SCENT LIKE NO OTHER. SCENT THAT WARDS AWAY SMELLS_

    _KYAU! INGANCHI DA KAMSHI MAI SANYAYA ZUCIYA SAI KAYAN TURAREN_ *aroos scents*
    ____________________________

    “Rose?” Ta maimaita sunan da qarfi tana fidda idanu,abu na farko da zuciyarta ta sawwara mata ire iren sunayen soyayya ne da namiji ke sanyawa masoyiyarsa mace,take duk wani jini dake jikinta ya fara tafasa,ta fara fidda huci daga bakinta,mugun kishinta nan ya motsa,ta warfci wayar ta daga ta kara a kunnenta.

    Sallamar da akayi da kuma muryar mace ya tunzurata,bata jira komai ba ta fara zunduma mata ashar da zagi

    “Shegiya karuwa,riqeshin da kikayi yau duka bai isheki ba,saikin biyoshi da kira yana cikin iyalinsa?,to wallahi billahillazi abbas yafi qarfinki,nawa ne ni kadai,ba wata mace data isa ta rabeshi na bart…….”

    Bata qarasa ba taji an warce wayar daga hannunta,tabi inda taji an fusge wayar da kallo bala’i yana cinta,don bata gama fadar tarin tulin qazaman miyagun kalmomin dake bakinta ba,sai taga abbas ne,daure da towel yana duba wanda yayi kiran nasa,tun yana bandaki ya fara juyo sautin muryarta,baisan da waye take wannan hayagagar ba gashi dare ya fara yi,sai daya fito ya fuskanci a waya ne,wayarma kuma tasa.

    Already an katse kiran daga can,sai yabi kiran yana sake kara wayar a kunnensa,idanuwansa da suka hautsine saboda baqinciki suna kan fuskar hafsat dake huci,jin alamun yabi kiran sai ta fara matsowa

    “Kiranta ma ka sakeyi,kuma a gabana?,wal……” Mugun kallon da ya watsa mata yasa ta danyi laqwas tana dubansa shaidan na sake ingizata.

    Murya a sanyaye rose tayi sallama kafin yace komai ta rigashi

    “Sorry sir,na kiraka da dare ko?,a baiwa madam haquri”

    “No,kada ki damu,wani abunne ya faru?” Cikin gurbatacciyar hausarta ta fara masa bayani

    “Eh….dazun da kuna meeting mimi tayi bacci a office ta yar da dan kunnenta ne,dana duba kuma naga kaman gold ne,so don kada ayita nema hankali ya tashi shi yasa nace bari nayi maka magana” ajiyar zuciya ya sauke yana qoqarin cooling temper dinsa

    “Is okay,ba damuwa,ki aje wajenki,idan na shigo gobe zan karba,idan ban shigo ba zansa ko samuel ki bawa sai ya kawo”

    “Okay sir”

    “Sorry rose,am sorry”

    “No sir,babu komai fa,nasan bata ganeni bane”

    “Good night” ya fada yana datse wayar,ya cillata saman gadonsa,sannan ya waiwayo gareta.

    Bacin ran data gani cikin idanunsa ya sake sanya jikinta yin laushi,bayan ta gane wace rose din

    “Indai rashin hankali da rashin nutsuwa zaki saka a gaban hankalinki zakita aikata abinda zai kaiki ga nadama mara amfani,tsabar banzan kishinki yasa idanunki sun rufe ki kasa gane wace tayi kiran,rose dince baki sani ba?,kiyi a hankali dani ki fita idanuna hafsat,idan kika kaini bango zan baki mamaki wallahi” can qasan ranta taja tsaki,ya jima yana fadin zai bata mamaki,wanne mamaki kenan,amma a saman fuskarta saita yamutsa fuska tana nuna rashin jin dadi

    “Ai kasan bansan ita bace,inda na sani ai bazanyi mata haka ba,kuma itama ta yaya zata kira.mutum da aurensa a irin wannan lokaci?”

    “Bakiji dalilin da yasa ta kira bane?” Ya fada a tsawace ransa na sake baci,har abada kenan ita ba zata gane tayi laifi ba saita kawo nata uzurin?

    “Ina jaddada miki ki shiga hankalinki,bani da lokacin kule kulen mata,amma idan naso ke baki isa ki hanani ko ki tsaidani ba” ya fada yana nunata da yatsa.

    Maganar ta doketa itama,to me yake nufi?,taso hasala amma sai ta bagarar,tasan ya fada ne kawai don ya tunzurata ya bata haushi itama,tafi kowa sanin waye abbas din,bata da wannan damuwar don ya fada.

    Yadda ya banzatar da ita yana shiryawa taji duk ta takura,saita taka a hankali ta isa inda yake tsaye,ta rungume faffadan bayansa da yake shirin lullubewa da riga

    “Kayi haquri don Allah,kuma na shirya zan bika kadunan” maganar tata tazo masa a bazata,wannan yayi nasarar saukar da fushinsa cikin qasa da second biyar,ya ajjiye rigar hannun nasa,ya waiwayo ya kama hannyenta ya zaunar da ita gefan gadon sannan shima ya zauna.

    Cikin qwayar idanunta ya sanya nashi sannan ya fara mata magana a tausashe

    “Bansan me yasa kika kasa fahimatata ba har yanzu,tsahon shekara biyar cikin ta shida,bani da burin da ya wuce naga gidana da iyalina cikin walwala fahimta da kuma qaunar juna,wannan rayuwar ba itace mafarkina ba a rayuwar aure na,inason gidana ya zama very romantic place,matata ta zama tafi kowacce mace iya soyayya tsafta tattali da iya kula dani,wannan shine nawa qarfin gwiwar da zai bani damar tafi da ayyukana yadda ya dace,ya kuma qara kusancinmu,ban takuraki zuwa kaduna saboda radin kaina ba,nayi hakanne saboda na jawo kusanci a tsakaninmu,kusancin da zai sake haifar da sabuwar soyayya da shaquwa tsakanina dake,ni abbas babu wata mace a gaba a yanzu,duk sanda kuma kikaga wata mace ta shiga rayuwata ba shakka gazawarki ne,daga gareki ne,na baki wannan satar amsar,ruwanki ki tare ko ina kiyi gadin qofar,ruwanki ki bada dama a shiga,amma kiyi qoqari mu zauna lafiya” a daren dai anyi abun arziqi,duk da daurewa kawai takeyi,abubuwa biyu ne sukayi mata tsaye a rai,maganarsa ta qarshe da kuma taraddadin barin bauchi ta koma rayuwar kaduna.

    A dukka hasashenta bata ga wata qofa da ta baiwa wata mace ta shiga rayuwarsa ba,tana kishinsa irin kishin dake matsewa kowacce mace qofar shiga rayuwar mijin wata,tana kaffa kaffa da shigarsa da fitarsa,a gida gwagwadon abinda zata iya tana masa,saidai shi da baya gani ma,amma tana takura a abubuwa da yawa duk don sabodashi,batasan kuma me ya rage ba,me yakeso kuma?.

    _wannan kenan_

    Kwanaki biyu suka qara suka gama shirinsu,har zuwa lokacin yana mamakin abinda ya sauya mata ra’ayin binsa kadunan,saidai bai matsa da sai ya sani ba,tunda zurfafa binciken a wadansu lokuttan ba alkhairi yake haifarwa ba.

    Ana gobe zasu tafi ya sanyata ta shirya don suje su yiwa hajiya sallama,daga nan kuma ya sauketa a gidansu,tana ta qoqarin danne zuciyarta ne,da kuma bin dukka abinda yakeso,saboda bataso ta bata hanyar data fara sharewa kanta,don antyn ummee tana ta jan kunnenta kan sai tayi juriya,kuma saita kula,don haka ta shirya ta bishi.

    Hannu bibbiyu hajiyan ta karbeta kamar yadda ta saba,cikin kirki da karamcin nan nata,ba laifi hafsat din kadaran kadaham itama,har suka gama gaisawar suka taba hira sama sama,saita miqe tana duba agogo gami da kallonsa

    “Inaga ya kamata ka saukeni a gidan,lokacin yana tafiya” kansa ya dauke daga kan jaridar da yake dubawa ya kalleta,har ya buda baki zaiyi magana hajiyan ta rigashi

    “Gaskiya kam,kuma sallama zakuyi ya kamata ace kinje da wuri don ki samu isashen lokaci,tashi ka sauketa abbas” baice uffan ba,saboda maganar hajiya gaba take da maganar kowa a fadin duniya,banda haka xamanta a gidan yayi kadan sosai,duka duka ko awa guda bata rufa ba,sai ya ajjiye jaridar ya miqe yana daukan key din motar sa ya fice,ta yiwa hajiya sallama,ita kuma tasa muneera ta bita da kayan amfanin kitchen data tanadar musu,kamar su kuka kubewa daddawa kanwa da yaji da sauransu,saboda tasan abbas din ma’abocin son tuwo ne,a halayya kuma irin ta hafsat din babu lallai ta tsaya tunanin tanadarsu,ta bisu da addu’a suka lafiya,qwaqwalwarta fal mamakin yadda hafsat din ta sauya ra’ayi,duk da bata tsaya tambayar abbas din ba.

    ***********

    Gab da sallar magariba hajjaa ta iso gidan hajiyan,cike da gajiya da kuma farincikin gama cooking classe din da sukayi na kwanaki biyar,wanda dai dai yake da na kwanaki sittin a wata makarantar,ita kanta tasan ta qaru over da abubuwa masu yawa.

    Tana shiga ta miqawa nujood jakarta ta daura alwala kawai sannan ta shige falon hajiyan,ta zauna suka gaisa hajiyan tayi mata sannu,sannan ta kira muneera kan ta zubo abincin dare suci kafin su wuce

    “Hajiya da kin barsu,yauma kafin na fito sai da nayi girki”

    “Me yasa kike nuna wa gidan nan kamar ba gidanku bane hadiyya?,kinga muneera zubo,idan ba zata ci ba yaran zasu ci,xakuci ai ko widad?” Tayi tambayar tana kallon widad,wadda keta faman hada kayansu a jaka tana kammalewa.

    Murmushi ta saki tana sadda kanta qasa,ba tare data amsawa hajiyan ba

    “Au,babarki zaki goyawa baya kenan,sai faman hada kaya kike,kamar dama kin gaji da zuwa gidanmu ” wannan karon har sai da haqoranta suka fito tana dariya cike da kunya

    “Ba haka bane hajiya,muna ta saki aiki fa kwama biyar din nan,kema zaki huta” maganar yarinyar saita burgeta,ta kuma sake saka mata qaunarta a zuciyarta,haka kawai cikin kwanakin taji yarinyar ta kwanta mata,tana kuma burgeta,saboda taga bambancin dabi’a tsakaninta da sauran yara,sau tari takan zauna nan kusa da hajiyan suyita hira abinsu,widad din najin hajiya kamar ummunta,idan tana tare da ita sai taji kamar ummu,tana debe mata kewarta sosai.

    “Ni ai ban gaji da ganinku ba widad”

    “To mu zauna hajiya?” Ta tambayeta cike da quruciya,murmushi hajiyan ta sake,ta waiwaya tana duban hajjaa dai dai sanda ta sallame daga sallar

    “nikam da zaku bani widad da nayi murna na kuma gode muku” dariya hajjaa ta saki,ba tare daga fahimci abinda hajiya ke nufi ba,ta zare hijabinta tana cewa

    “Widad hajiya?,wannan mara sabo din da rashin sakewa da mutane?,idan muka baki widad ai mun gayyatowa kanmu ummu,takanas zata tahi bauchi ta dauke kayarta,dama ‘yar aro ce” kai hajiya ta kada

    “Ni ba aro nakeso a bani ita ba,inaso a bani ita na baiwa abbas dina,kinga shikenan ta zama diyata babu zancan aro kuma” a yadda hajiyan tayi maganar yasa hajjaa maido hankalinta jikinta,ta kalli fuskar hajiyan da kyau,sai taga gaskiya baro baro kwance saman fuskarta,kalamanta sunyi kama da kalaman da suke fita daga can qasan zuciya,babu alamun wasa ko kakaci a ciki.

    Daurewa hajjaa tayi tayi murmushi,don zancan gaba daya sanyayar mata da jiki yayi,abbas hajiya ke magana,dan gayun matashin nan, mahaukacin damarar nan da kwanan nan aka qara masa rank?,abbas din dake da mata da yara biyu?,,abbas fa

    “To ai hajiya idan kinaso sai a bakin ai”

    “So kai,saboda inaso dinne ma na sako zancan,amma dai zan sake tuntubarki,ki shaidawa muhsin din”

    “To hajiya ba matsala” ta fada tana murmushi,zuciyarta na bata da wasa hajiyan tayi maganar,saita maida dubanta ga widad wadda tuni ta matsa gaba suna magana da nujood,don haka batasan ma wainar da ake toyawa ba.

    Sanda suka tashi tafiyar kayan ciye ciye ta hada musu da yawa a leda,hajiyan ‘yar gatan tsohuwa ce,babu abinda ta rasa a gidanta,wannan ya sanya babu abinda zakaje baka samu ba a gidan.

    *BAYAN SATI DAYA*

    Tsaye take hadiyya take cikin kitchen din tana hadawa uncle muhsin abincinsa,gefe daya yaranne gaba daya sun cika mata kunne,hayaniya suketa yi suna tsokanar widad,wadda gaba daya cikin satin ta fara birkice musu,tunda tayi waya da ummun ta gaba daya hankalinta ya karkata zuwa komawa gida

    “Ya isa don Allah kuyi mana shuru” waiwaya tayi ga widad

    “Zan gayawa uncle dinki kada ki damu,zai kaiki kiga ummun da kansa indai free yake bashi da aiki” kai ta gyada tana danjin relief a ranta,a kwanakin nan ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta gaban ummun,bata taba zaton akwai abinda zai kawo rabuwarsu haka na tsahon lokaci ba,tama yi qoqari,don ko kwana guda batayi gidan kowa indai ba tare da ita ba,sai gashi yau ta doshi wata kusan guda cur.

    Sanda hajjaa ta isa yana amsa waya ne,saita zuba masa komai ta kuma jera a gabansa,tana niyyar tashi don ta koma kitchen din ta sallami yaran yayi mata nuni da hannu kan ta zauna,saita koma ta zauna din,ya kammala wayarsa ya kashe yana dubanta

    “Wanne saqo hajiyan abbas ya baki baki gayamin ba?” Cikin mamaki don ita sam ta ajjiye wannan batun tace

    “Saqo kuma?,anya kuwa?”

    “Gashi yanzun ta kirani tana tambayata,tace idan kin kammala gayamin din zata sake kirana” sai a sannan hankalinta yakai,tadan dafe kanta tana fadin

    “Ya salam,wallahi sai da kazo da maganar na tuna” kansa ya girgiza

    “Bai kuma.kamata ba,hajiya kamar uwa take a wajenmu gaba daya”

    “Ba haka bane abba,zancan ne naji kamar zolaya take yi,hankali na bai kama ba” ta fada tana kada kai

    “Wanne irin zance ne haka?” Uncle muhsin da ya fara cin abincinsa ya fada yana kallonta

    “Widad takeso a basu ta baiwa abbas aurenta”

    *_AREWABOOKS: Huguma_*

     

    *RUMBUN K’AYA*🔥

    *DAUDAR GORA*🔥

    *IDON NERA*🔥

    *A RUBUCE TAKE*🔥

    *KI KULANI*🔥

    Littafi daya—400
    Biyu—600
    Uku—-800
    Hudu—–1k
    Biyar din duka—-1200

    *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank.

    Shaidar biya tanan👇🏻
    09033181070

    *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

    09166221261

    🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
    *Ina yan uwa ‘yan nijer?*
    *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

    +227 90 16 59 91

    Littafi daya—450CFA
    biyu—650CFA
    uku—-850CFA
    hudu—-1050 CFA
    Biyar—-1250CFA

    *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

    *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

    *Thanks for choosing us*🔥
    [2/16, 10:43 AM] Sweet sis: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:huguma*

  • Arubuce Ta Ke 13

    Arubuce Ta Ke 13

    Page 13

    Kusan suke cin abincin,ita dai tana ta biye musu ne amma cokalin kawai take juyawa cikin plate din,tuntuni sun jima da raba plate din cin abinci dashi,tare dai suke ci,amma kowa kwanonsa daban,tunaninta gaba daya yafi karkata kan yadda zata sake jaddada masa ba zata bishi kaduna ba.

    Har ya kammala cin abincin ta rasa kalmar kamawa,ganin yana qoqarin tashi sai tayi gyaran murya,ya dakata da shirin tashin da yakeyi ya aza mata hankalinsa

    “Abban mimi,nifa gaskiya ba zan iya binka kadunan nan ba,don Allah ka janye tafiyar nan dani” ta fada tana jin nauyin maganar,a mamakance yake kallonta,tsahon wasu sakanni sannan yayi gyaran murya

    “Nayi tunanin mun gama maganar nan dake ko?” Kai ta girgiza

    “Bamu gama ba gaskiya,bazan iya tafiya wata kaduna ba” ransa ya sosu,ta yaya yana son kare mutuncinsa da martabarsa ya tafi da iyalinsa don samun kariya daga sharrin shaidan amma tanason ingizashi zuwa ga hallaka?,kadunan bariki zai tafi shi kadai alhalin da iyalinsa ba gauro bane?

    “Koda bakiso hakanan zaki tafi,kuma bama kaduna ba,duk inda aiki ya jefani hafsat haka zaki bini muje,wannan shine tsarina” yana kaiwa nan ya miqe tsaye yana shirin sauka daga dining din,sai itama ta miqe,wai me yasa ya fiya kafiya da taurin kai ne?,haka kawai tana cikin garinta cikin dangi da ‘yan uwanta zai cizgeta ya tafi da ita wata uwa duniya?,itakam sam bata ga dalili ba

    “Gaskiya babban mimi bazan iya barin dangina da kowa nawa da dan business dina dana fara ba na bika garin da bansan kowa ba,babu kowa nawa ba” ta fada adan hasale,kallonta yayi sai ya dauke kai ya gewayeta ya wuce,bashi da lokacin tsaiwa tanka mata ga yara zaune a wajen,sannan ma shi din ba mutum bane mai yawan son magana,banda Allah ya hadashi da ita mutum ne marason hayaniya,yafi qaunar zaman shuru da kadaici wani lokacin,shi yasa ko sabani suka samu bai fiya damunsa ba,yakan kebe yayi zamansa yana karance karance,idan kuma yara suna nan yayi sabgarsa dasu.

    Binsa tayi har cikin falon tana maimaita maganar,yasan idan ya zauna ciwon kai zata sanya masa a banza,don haka sai ya dauki key din motarsa dake gefan tv stand ya fice abinsa kawai,yana amsa adawo lafiyan da mimi ke masa.

    Komawa tayi ta zauna jabar saman kujera tana tuje daurin dankwalinta tayar gefe,wannan wanne irin maqalallen aiki ne da basu da aiki sai sassauyawa mutum gurin aiki?,daga can sai nan?,yaushe ma duka duka sauka dawo bauchin tana ta murna ta dawo gida?,to itakam wallahi ta gaji,tana son abbas matuqa tana tsakanin kishinsa,to amma aikinsa zai zama babban tarnaqi a rayuwarsu.

    Tana nan zaune tana saqawa gami da kwancewa,mimi nata gaya mata nawwara na wasa da abinci amma hankalinta bai wajen,har sai da yarinyar ta fado da tea flasks dinsu ya fashe a wajen sannan ta farga,sai a sannan ta miqe tana banbamin fada ta nufi wajen,sai data durma mata dundu sau biyu a baya sannan tahau aikin gyara wajen,tanayi tana mita,yarinyar kuwa ta fashe da kuka,mimi ce ta matsa ta ruqo yar uwar tata tana goge mata fuska.

    ***********

    Ranar da driver ya ajjiyesu gidan hajiya tayi mamakin ganinsu,ta danji fargabar ganinsu da uniform ba kayan gida ba,tana zaune a falonta tana lazumi bayan ta idar da sallar la’asar,da yake takan kwashi awa guda kafin ta kammala,ta amsa gaisuwarsu tana maida idanunta ga widad da take baquwar fuska a wajenta,saita dauke dubanta tana tambayar nujood ko lafiya

    “Mommy ce tace muzo nan mu zauna,qarfe shida zatazo ta daukemu,makaranta ta shiga”

    “To alhamdulillah” hajiyan ta fada tana jin hankalinta yana kwanciya.

    “Bari muneera ta zuba muku abinci kuci”

    “Zanyi alwala banyi sallah ba” widad ta fada,wadda tun dazun take jinta a takure,saboda yau nujood ta matsa musu basuyi sallah a makaranta ba.

    Dubanta hajiya tayi,sai taji yarinyar ta burgeta,a shekarunta amma tasan kiyaye sallah,duk da tasan idan bata fara haila ba kadan ya rage ta fara,amma ko su muneera da suke ‘yammata sosai wani lokaci sai tayi fama da su kan sallar,kiran muneera hajiya tasa nujood tayi,ta kaisu dakin baqi tace suyi sallar sai su fito suci abincin,duka suka miqe suka bita.

    Ba jimawa suka gama sallar suka fito,muneera ta kawo abincin,hajiya na zaune daga gefansa tana lazuminta,jifa jifa tana kallonsu sanda suke cin abincin.

    Yaran uncle muhsin din suna da nutsuwa da tarbiyya,amma sai taga nutsuwar widad ta fita daban,ita tafara tsame hannunta daga abincin,ta kuma gyara wajen takai kwanon kitchen,wannan duka aikin ummu ne,duk da bata aikin komai irin ta horas da ita qananun abubuwa irin wadan nan da kyau,kwata kwata widad din ba maison jiki bace,da karambani ma ta iya wasu abubuwan sosai,wanda take koya wajen anty madina,ko idan ta shiga sassansu Aafiya ko ramziyya.

    Sunata sabgarsu amma tana zaune waje daya,ita gaba daya jinta take a takure,bata son baqon waje,tana da wahalar sabo kuma,wannan yasa ta qara tsumewa waje daya,Allah Allah take momy ta iso su tafi gida.

    Zaman daya isheta sai ta fara taya muneera ninkin kayan hajiya,sun kusa rabi muneeran ta miqe tayi kwanciyarta,widad din ita ta qarasa muneera ta kwashe takai mata daki.

    Shida da mintuna hajjaa ta iso a motarta,suna jinta suka fita da sauri tararta,widad ko murmushi tayi tana gyara zamanta,tana jin zama yazo qarshe sai gida.

    Da sallama ta shigo falon hajiya na mata sannu da zuwa fuskarta da murmushi

    “Hajiya ai ke za’a yiwa sannu,yau na hadaki da hayaniyar yara”

    “O’o,o’o,aini deben kewa ma sukayi,yau babu zaman shurun nan” murmushi hajjaa tayi tana maida dubanta kan widad

    “Kamar kiyi tsuntsuwa ki janyoni ko?,gani na iso sai gida” dariya ta danyi,hajiya ta dubeta

    “Da alama kam,don tunda sukazo ta kasa sakewa,tana zaune waje daya”

    “Ai akwaita da baqunta da rashin sabo,duk da dai dama bata da hayaniya sosai,ga oganni nan” dariya hajiya tayi sannan suka fara gaisawa,ta gaya mata aikin da zasuyi na kwana biyar din,tare da alfarmar zama da zasu dinga yi har na kwana hudu a wajenta

    “Kin jiki hadiyya,banda abinki ba jikokina bane,har sai kin nema alfarma,ai nan dinma gida ne,Allah ya taimaka yayi jagora”

    “Ameen hajiya,Allah ya qara girma”.

    Hajiyan nata tsaidata suyi sallar magariba amma tace sayi a gida,ta tattara yaran suka wuce gida suna yiwa hajiya sallama tare da cewa sai gobe,don dama su nujood gidan zuwansu ne su,suna kuma jin dadin zuwa gidan sosai saboda kirkin hajiya.

    *********
    Yammaci ne sosai daya kamata ace a lokacin yana cikin gida yana hutawa,tare da shirye shiryen barinsa bauchi zuwa kaduna,saidai bai samu wannan sararin ba,saboda fitinar da hafsat din keson tsirowa dashi,tun batun zuwanta kaduna da yace lallai sai tayi,ko a yanzun ma ya fito gidan ne saboda yadda ta tasashi gaba da nacin roqo harda qwallarta kan ya barta a bauchin,shi baisan wanne irin tunani ke gareta ba,baisan me yake damun kanta ba,kin gwammace kibar mijinki ki zauna da dangi?.

    Wasu lokuta matsalolinta caza masa kai suke,sai ya samu ya kebe tukunna yake samun kwanyarsa ta huta,don haka ya zabi fitowa daga gidan.

    Tun asali ba mutum bane shi mayawaci,idan ka ganshi a waje dalilin aiki ko kuma wata lalura ce ta kaishi,sau tari abokan aikinsa na yawan tsokanarsa,sam dabi’unsa kamar ba na dan sanda ba,saidai ya murmusa kawai,ba kasafai yake basu amsa ba.

    A hankali yake tuqin nasa,kwanyarsa cike fal da tunani,sannu a hankali har ya qaraso junction mai bada hannu ya tsaidasu,motarsa na sahun gaba,yana iya wucewa idan yaso,to amma sanin doka da qa’ida ta sanyashi tsaiwa kamar yadda ya dace ace kowanne mutum ya tsaya din.

    Hankalisa nakan radio din motar yana son kamo daya daga cikin tashoshin gidajen radio da yakan saurari labaran yamma,baisan me ya faru ba yaji tashin hayaniya,ya daga kansa da sauri yana duban gefansa inda hayaniyar ke tashi.

    Matashin saurayi ne tsaye kusa da motarsa qirar 206 yana zazzagawa wani tsoho dake saman mashin masifa,yayi tsai yana duban matashin yadda yake haqilo kamar zai kaiwa mutumin duka,mutane har sun fara taruwa ana bashi haquri,ci gaba yayi da nazarin matashin dake dukan saman motarsa yana fadin shifa sai an biya shi,daga gefe daya wani jami’in dan sanda ya fara ratsowa cikin mutanen yana fadin a bashi hanya,abbas din ya bisu da kallo yana son ganin abinda zai faru.

    Yana daga wajen yake nazartar komai,yadda dan sandan ya shiga maganar suka hadu da matashin suna son bauwa dattijon rashin gaskiya,sai ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fito ya nufi wajen.

    “Assalamu alaikum…..lafiya me yake faruwa?” Yayi tambayar yana duban matashin da yaketa faman daga jijiyar wuya

    “Wannan tsohon ne ya gogar ma mutane mota da wannan tsohon mashin din nasa,dubi yadda ya gogewa mutane fentinsu” idanu ya lumshe kana ya bude kusan lokaci guda yana duban inda yake fadin an goge masan,duka duka gugar ba wata me girma bace

    “Kayi haquri kayi masa uzuri kuma,tunda nasan yana sane bazaiyi haka ba”

    “Wallahi dan nan tun daxu ma naketa bashi haquri,bansani ba,sauri nakeyi ina da uzuri a gida”

    “Baba ina ganin mutuncinka fa da tuni na zageka,da haqurin ya mutu sadakar nawa ka bayar?,ka biyani kawai” dunqule hannunsa abbas yayi cikin aljihunsa yana qoqarin hadiye bacin ransa

    “Kayi haquri tunda shima ya baka haquri”

    “Kaga malam bazan fa haqura ba,idan ma tsaiwa kayi a nan don ka bani haquri gwara kayi gaba abinka”

    “Is okay,nawa ne kudin gyaran?” Ba kunya ba tsoron Allah ya karkace ya tsuga kudi,kallonsa abbas yayi na tsahon wasu mintuna yana karantar zallar qaryar dake qwayar idanunsa,sai ya saka hannunsa a aljihu ya ciro kudi,ya irga ya miqa masa.

    Kunya da haushi suka kama matashin,bai taba zaton zai iya biyan kudaden ba shi yasa ya saka da nauyi,cikin borin kunya yace

    “Ni ba kudi nake buqata,muje a gyaran motata”

    “Ko ka karba ka tafi,ko kuma kayi asara ba kudin ba gyaran”

    “Wai kai waye da zakazo kana cikamin baki malam?,bazan karba ba gyaramin mota nakeso ayi” matsowa dan sandan yayi kusa da abbas ba tare daya lura da waye ba a tsaye

    “Kai meye naka ne a ciki zaka zo kawai ka shiga rigimar kan hanya?,ka qyale mut…..” A nutse abbas ya juya suka hada idanu da dan sandan,gabansa yayi mummunan faduwa,yayi baya babu shiri,gumi ya fara yanko masa,abbas din baice komai ba ya maida dubansa ga matashin

    “Ina me shawartarka ka karba”

    “Idan kuma naqi fa?” Wani qaramin murmushi na gefan baki abbas ya sake,hankali kwance ya maida kudinsa aljihu gami da fito da wayarsa a madadin kudin,ya danna kira.

    Baice komai ba illa adreshin titin da suke kai daya bayar ya maida wayar aljihunsa,ya kuma harde hannuwansa yana kallon yadda yake ci gaba da zuba rashin mutunci,jikin dan sanda yana rawa ya matsa kusa dashi

    “Bawan Allah kayi haquri ka tafi,zaifi maka alkhairi,tunda nasan zuwa yanzu ko kudin ma ka rasasu ba samunsu zakayi ba,gwara ka tsira da lafiyarka da mutuncinka”

    “Dalla malami sakeni,wallahi yau sai naga wanda ya tsaya masa” ya fadi yana kumfar baki,maganar tasa ta sake hasala abbas,saidai bai nuna hakan ba koda a saman fuskarsa,yana ji ya zama wajibi ya bashi tarbiyya da bashi da ita,sai ya juya ga tsahon

    “Kada ka sake bashi haquri baba” hannu ya saka a aljihunsa ya fidda dubu uku ya miqa masa

    “Hau mashin dinka ka tafi,Allah ya tsare” zaburowa yayi yana fadin

    “Idan ka barshi ya tafi rigimar nan ta koma kanka wallahi”

    “Na karba”ya amsa masa yana sawa tsohon muqullin babur dinsa ya kunna masa,dai dai sanda motar ‘yan sanda ta iso,hakan ya baiwa tsohon hanyar wucewa,yana tafe yana jerantawa abbas din addu’o’in samun albarka da gamawa da duniya lafiya.

    Matashin bai fahimci waye abbas din ba sai da jami’ai suka cika hannu dashi shi da dan sandan dake goya masa baya,sai a sannan ya nemi russunawa ya fara roqon ya saka a sakeshi,ko kallonsa baiyi ba ya dubi Samuel

    “Ku sakayamin su a bayan kanta saina nemesu,mato ya tuqa motarsa a kaita station a ajjiye”

    “Consider it done sir” ya fada yana saluting nashi.

    *MAZA ANTAYA NAKI KUDADEN KIBI SAHUN AYARIN MATA MASU AJI TA HANYAR BIYAN KUDIN NAKI KARATUN WADAN NAN LITTAFAI KAMAR HAKA*

    *DAUD’AR GORA* Billynabdul

    *KI KULANI* Missxoxo

    *IDON NERA* Mamuhghee

    *RUMBUN K’AYA* hafsat rano

    *A RUBUCE TAKE* Huguma

    *ZAKI IYA BIYA KAI TSAYE TA WANNAN ACCOUNT DIN*

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiki tura shaidar biyanki ta wannan number

    09033181070

    *MASU TURA KATIN MTN KO VTU KUMA ZASU TURA WA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANSU*

    09166221261

    *YAN NIJER ZASU TUNTUBI WANNAN NUMBER*

    +227 90 16 59 91

    *Muna godiya da ci gaba da zabin zafafa biyar a koda yaushe*🙏🏾🙏🏾

    [2/13, 5:29 PM] +234 903 685 1413: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *_Arewabooks:huguma_*

  • Arubuce Ta Ke 20

    Page 20

    Sai daya gama duk abinda yakeyi ya kwanta yaja bargonsa zuwa qugu bayan ya rage hasken dakin sannan ya kirata.

    Har tayi ringing ta gama bata dauka ba,ya sake kira karo na biyu sannan ta miqe daga kwanciyar da tayi,ta jawo wayar tana sakin hamma,dan qaramin tsaki taja,banda maganar da takeso suyi nada muhimmanci da bazata daga ba,batason zancan motar yayi nisa kada taje ta zama rabon wasu,abinda kawai bataso yanzun zaice saita tsaya sunyi hirar soyayya,batasan me dame zata ce masa ba,daga qarshe kuma ya tada mata feelings ko ya isheta da fitina idan ya dawo.

    Cikin qaramin sauti tayi masa sallamar wanda baccin data fara ji ya jawo hakan,saidai shi din abun ya tabashi,har ya tada masa tsigar jikinsa,ya rufe idanunsa yana amsa mata

    “Am sorry,na tasheki halan?”

    “Ummm,babu komai”

    “Thanks” da hanzarinta ta katsi numfashinsa

    “Abban mimi ina cikin maka gyara ne shekaran jiya naga key din sabuwar mota,to yau kuma mimi ta tabo wajen ta zubda kaya,da na maida kayan banga key din ba,nace Allah yasa ba wani wajen ta jefa maka ba”

    “Noo,ni na tafi dashi,motar dama ta hajiya ce,so sai na baiwa samuel nace gobe ya biyoni da ita a kawo mata,kinsan motar da ake fita da ita ta samu matsala” idan tace ga irin bacin ran da taji ya saukar mata ma ta yiwa kanta qarya,abinda taketa hasashe kenan,take kuma gudu,yanzun motar ya dauka ya baiwa hajiyan bayan yasan tana da buqata,tana ta kuma gaya masa ya canza matan bai canza ba?,ta yaya zata nuna masa ma zallar bacin ranta?

    “Abban mimi amma dai kasan ina da buqatar motar nan ko?,sati nawa ina maka naci ka hanani?,amma a gabana ka siya……”

    “Hafsatu” ya kirata da sunan da mafi yawa jama’a ke kiranta ba tare da ya bari ta idar da maganarta ba,kiran kuwa ya ratsa mata ko ina,yana da wata murya dake da kwarjini

    “Baki gane wacce na siyawa motat bane?,hajiyata mahaifiya ta nake magana” boyayyar ajiyar zuciya ta sauke,tana kuma qoqarin sassauta harshenta

    “Bance bakayi dai dai ba ai,amma nafi buqatar motar,da sai ka karba ta wajena ayi mata gyara ka bata,tunda hajiya bako yaushe ta fiya fita ba,sai ta dade a gida bata fita ba,zata iya manage da ita”

    “Hajiyan tawa za’a bawa ragowar motarki tayi manage?” Cikin zallar mamaki ya jefa mata tambayar, jikinta daga can yayi sanyi,saidai bacin ran da takeji a zuciyarta ya hanata gayawa kanta tana fadin abinda bai kamata bane

    “To menene a ciki?”

    “A wajena wani abunne,idan bakisan darajarta ba ni nasan darajarta,tafi qarfin cin ragowar kowa a duniya bare taki ragowar,karki kuskura ki kaini bango da banzayen maganganunki,idan ba haka ba zaki gane kuskurenki,ki adana maganganunki basu da wani amfani a wajena,kudi dai nawa ne,zan kuma wahaltawa mahaifiya ta a duk sanda naso ba tare da shawara ko yardarki ba”

    “Amma dai kasan nima ina da hakki ai a kanka ko?,tunda nima matark……”

    “You are very stupid” ya fada da zafi yana datse kiran,bayason yaci gaba da saurarenta kada ta tunzarashi,idan ya tunzura baisan me zai biyo baya ba,yana kallonta tanata kiransa amma yaqi dagawa,sai ma ya maida wayar silent ya maida kansa ya kwanta yana ta furzar da iska a bakinsa ko zai samu zuciyarsa ta rage zafin da take masa.

    Bayan kiran ya tsagaita da shigowa sai kuma wani haske yayi blinking,alamun shigowar tex,wayar ya jawo da niyyar kasheta gaba daya,saidai saqon ya fito saman screen din

    _Tunda ni bankai wani bigire na abu mai muhimmanci a tare da kai ba,nima bazan zauna ina aikin da ba’a gani ba,zan dawo garinmu inda akasan darajata_

    “Mtsweew,shirme kawai” ya fada qasa qasa,ya danne switch button ya kashe wayar gaba daya ya dorata saman bedside drawer,ya sake jan duvet yana rintse idanu,saidai gaba daya baccin yaqi daukarsa,muraja’a kwanyarsa ta shiga yi masa kan halaye da dabi’un hafsat,tun daga kan aurensu kawo yau,tun kafin aurensu ya fahimci wasu baqin halaye daga gareta,banbancin ra’ayi da kuma wasu abubuwa masu yawa,ya dauka idan sukayi aure zai iya canzata,ashe yayi kuskure,babu wani sauran canji,saima abubuwa da suke ta’azzara kullum.

    Gefe daya kuma tunaninsa ya cilla kan maganarsu da hajiya,sai ya sauke ajiyar zuciya yana ambaton sunan Allah ya kawo masa agaji.

    ********Washegari bai tashi da wuri ba,saboda ya sanyama ransa babu inda zai fita yau din,sai wajen sha daya da rabi sannan ya shiga kitchen ya dafa irin tea dinsa ya soya qwai hudu ya dauki slice of bread ya hada dashi ya dawo falonsa ya zauna yaci,bayan ya gama ya kalli labarai kadan kafin ya canza wani program da akace masa jiya anyi da senior dinsu bai samu gani ba,bayan ya gama ya buda qofa ya karbi news paper wajen yaron dake kawo masa ya karanta,sai yayi wanka ya sanya wata jallabiya mai sulbi,wadda ta karbeshi sosai,ya daura alwala ya wuce masallacin dake gaban unguwarsu wanda suke sallah qarfe daya na rana,a qa’ida idan zai hau abun hawa zuwa masallacin zai biya 30naira amma ya zabi takawa a qafa,don tafiyar qafa ba baqon abu bane a wajensu.

    Bai dawo gidan ba sai qarfe biyu da rabi na rana,don yadan tsaya da mutane,yaron dake masa aike aike ya aika ya samo masa masa me kyau ko tuwo,sai daya buda fridge yasha ruwa mai matsakaicin sanyi sannan ya samu waje ya zauna yana qoqarin kunna wayarsa.

    Saqonni ne suka soma shigowa,kamar bazai bude ba don yana tsammanin hafsa ce,kada ya karanta abinda zai bata masa rai,sai kuma ya buda din,ba ita bace,ire iren ‘yammatan dake crushing a kansa ne,yana mamakin ta inda suke samun numbers dinsa,bai ma batawa kansa lokaci ya karanta din ba ya goge saqon,yana tuna sanda yake barinsu ga wayarshi,irin tashin hankalin da sukeyi da hafsa din a kansu a lokacin,shi kuma rashin muhimmancinsu da rashin damuwa da masu saqon yasa yake mantawa ma dasu cikin wayar bare ya share kada ta gani din,yayin da kishi ke sanyata taga kamar yana sane ya barsu.

    Number hajiya ya nema ya kira,suka gaisa,ya shaida mata yau bazai fito ba yana gida kada taji shuru,fatan alkhairi tayi masa sukayi sallama,kamar ya ajjiye wayar sai yaga akwai kuma wani haqqin bisa wuyansa,don haka ya nema number hafsa din ya kira.

    Tsaf ta qaraci ringing dinta ta katse ba’a daga ba,sai ya sake kira amma sai aka gaya masa a kashe take,yayita qoqarin kira ana maimaita masa a kashe take,sai ya ajjiye wayar ya haqura,dai dai lokacin yaron da ya aikata din ya dawo ya karba saqon ya sallameshi.

    Sai da yaci abinci ya nutsa sannan ya kira suraj,suka gaisa suka taba hirarsu sannan ya buqaci ganinsa

    “Yau bana gari,na danyi balaguro azare,amma yau din zan dawo,zan sameka gida gobe”

    “Yayi,babu damuwa,saina jika” sukayi sallama.

    Wunin ranar a gida yayita shi kadai,yanata juya maganar auren da hajiyan ta nema masa,saida yamma ne ya fita farfajiyar gidan ya motsa jikinsa,ya danyi strolling cikin layinsu zuwa baya sannan ya dawo ciki.

    A farfajiyar gidan ya sanya musu kujeru shi da suraj,sannan ya dafo musu black tea wanda yasha kayan qamshi da ganyayyaki masu dadi,ya zubo musu a wata buta me hade da wasu irin cups ya zuba ya miqawa suraj,sannan yaja kujera yana zama

    “Kai….abbas badai iya dafa tea ba wallahi”

    “Zaka fara ko?” Kai ya girgiza yana dariya

    “Kasan Allah?,sai an tara mata da yawa basu iya dafa tea kamar haka ba” baice komai ba illa kai nasa cup din baki da yayi,saboda yasan haka dinne,koda a cikin gidansa ma,don yawancin lokutta ya gwammaci ya tashi ya dafa tea dinsa da kansa akan yasa hafsat ta dafa masa,indai kaga ya sha nata to lalura ce babu yadda zaiyi.

    Suna shan tea din suna taba hirar da bata qarewa tsakaninsu,suraj din aboki ne na tun lokacin quruciya har zuwa girma,kuma har yanzun kusan shine babban abokinsa sannan muhsin ya biyo baya.

    “Kace kana son ganina,me ya faru?” Cup din abbas ya ajjiye,yana hade yatsun hannunsa guri guda,sannan yayi crossing qafafuwansa suma yana duban suraj din,sai kuma yadan shafi goshinsa kadan sannan ya fara magana

    “Bansan ta ina ma zan fara maka bayani ba suraj,hajiya ce ta nema min auren ‘yar yayan muhsin”

    “Ummm,kaga dan gata…kai yanzun ma auren sai an nema maka,bana fari ba ba komai ba?”

    “Akwai matsala suraj” da dan mamaki saman fuskarsa yake dubansa

    “Matsala ta meye?,matar ce bata yi maka ba ko kuwa?” Kai ya girgiza

    “Ba wannan maganar ake ba,don ko fuskarta ban sani ba,suraj cikin gidana akwai matsala sosai,ban kuma gama solving matsalar ba ta yaya zan qara aure suraj? Da shegen kishin hafsa zanji ko kuma da sabon auren da nayi?,beside ma kwata kwata banajin ina da cikakken lokacin fuskantar matsalolin mata bayan wadda nake ciki” Murmushi suraj din yayi cikin kwanciyar hankali,ya kuma gyara zamansa da kyau,shi kam kamar hajiya ta shiga tunaninsa ne,wannan abun da tayin shawarar da ya dade yana son bawa abbas din,amma kasancewarsa ba mai magana ba,ba kuma me fadan sirrinsa ba yasa ya qyaleshi ya zuba masa idanu,duk da cewa mutumin da yake da matsayi a wajensa kamar suraj dake shiga gidansa lokaci bayan lokaci zai fuskanci akwai damuwa a gidan,daga fannin tsafta kawai zakasan akwai nakasu,tunda tsafta da qazanta basa boyuwa

    “To ai kai abinda baka sani ba,wannan auren shine hanyar gyaruwar duk wata matsala taka da damuwa”

    “Kamar yaya?” Ya tambayeshi yana dan yamutsa girarsa

    “Bari nayi maka gwari gwari,yawancin mata suna qoqarin ganin sun gyara tsakaninsu da mazajensu ne a sanda suka qara aure,gudun kada kishiyar data shigo taga gazawarsu,ko ta qwace musu miji ka fahimta?,to sai kaga itama ta zage damtse don kar a barta a baya,gefe guda kuma ga kulawa daga amarya kana samu,kowacce qoqari take taga itace star a wajenka” shuru abbas yayi kawai yana jin suraj,mai daki shi yasan inda yake masa yoyo,baya tunanin qarin aurensa zai zama gyara ga hafsat,amma bai san ikon Allah ba,kawai abu daya ya sani,ko ransa hajiya tace ya cire ya bayar zai iya,bare wannan buqatar da bata fi qarfin ikonsa ba,ya sauke ajiyar zuciya yana zama sosai cikin kujera manyan idanun san nan akan suraj

    “Hajiya tafi qarfin komai a wajena suraj,batun rashin karba ma bai taso min ba,kawai inason jin yadda za’ayi” dariya yayi ya koma ya jingina da kujera

    “Ya kuwa za’a yi,kawai ka shirya kaje kuga juna kai da ita,sai mu fara shirin biki”.

    *********Tunda hajjaa ta gaya mata saura kwanaki biyar ta tafi kano take murna da zumudi,kullum cikin shirya kaya take,ko ta shirya sai ta fiddasu ta sake shiryawa,kowa a gidan dariya yake mata yana tsonakarta,ranar da nujood ta tsokaneta da cewar

    “Dama abba yace an fasa” fada suka kusa yi,taqi kula nujood din wunin ranar,saida hajjaa ta shiga batun ta musu sasanci.

    Saura kwanaki uku ta tafi da yamma suna kitchen suna ma hajjaa yanke yanken kayan miya,da yake tun zuwansu hajjan ke hadasu su shiga kitchen tare,ko daya widad din bata da son jiki,kuma tana sha’awar yin girkin dama,ummu ke hanata tana ganin kamar zata qone ko kuma wani abun zai sameta.

    Uncle muhsin ne ya shigo,dawowarsa kenan daga aiki,kai tsaye ya wuto kitchen din ya tsaya bakin qofa ya leqo yana tsokanarsu

    “Manyan ‘yammata ne ke girki yau kenan” murmushi hajjaa tayi

    “Aiko dai yau su abba za’a ci dadi”

    “To Allah ya taimaka,dan zo mana minti uku”

    “To abba” ta fada tana tsame hannunta daga abinda take tabi bayansa.

    Sai da suka shiga bedroom dinsa,ta tayashi ya rage kayan jikinsa sannan yace mata

    “Widad fa gobe zatayi baqo,hajiya da kanta ta kirani ta gayamin gobe abbas zaizo suga juna” baki hajjaa ta kama tana murmushi

    “Ikon Allah,abu kamar wasa yana shirin zama gaske,to Allah dai ya doramu akan ‘yar rigimar hajiyan,tunda dai abbas ba shine na farko ba”

    “Ba komai in sha Allah,idan sun gama girkin ki turon ita nayi mata magana da kaina”

    “Yafi dai abba” sai yayi dariya

    “Na fuskanci tsoro dai kike”

    “Wallahi abba,Allah dai ya tabbatar da alkhairi,ya kauda fitina”

    “Ameen ya rahman” ya amsa mata yana nufar bandaki,ita kuma ta baro dakin da zummar zuwa ta kawo masa abun sha kafin girkin ya kammala.

    KI KULANI miss xoxo

    DAUDAR GORA Billynabdul

    RUMBUN K’AYA hafsat rano

    IDON NERA Mamuhghee

    A RUBUCE TAKE huguma

    _sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau’ikan salo da kuke so_

    _masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank

    Saiku tura shaidar biya ga
    +234 903 318 1070

    *Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
    09166221261

    *Al’ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
    +227 90 16 59 91

    *Zafafa biyar kadai keda sinqin nau’ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci guda*🤝😄

    *Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    [2/18, 12:43 PM] It’s Queen Meenali👸🏻: *H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 23

    Arubuce Ta Ke 23

    Page 23

    Duka dai yanata juya yadda abubuwan zasu kasance har ya gama abinda yakeyi yazo kwanciya,sai ya kauda wanann tunanin ya sake maimaita kiran hafsat amma kamar dai ko yaushe,sai abun ya shiga daure masa kai da kuma bashi tsoro,don haka ya sauya akalar kiran zuwa ga wani constable dake area din nasu,ya aikashi yaje gidansa ya duba masa lafiyarsu,cike da girmamawa ya amsa masa ya kashe wayar ya zauna yana jiran feedback.

    Bai haura minti biyar ba yayi kiransa

    “They’re fine sir”

    “Are you sure?”

    “Yes sir” ya sake tabbatar masa,sai yaji ransa ya baci,ya kashe wayar ya ajjiye yana gyara kwanciyarsa gami da lumshe idanunsa yana furzar da iska daga bakinsa

    “Dole ya dauki mataki akan hafsat din,abun nata qara gaba yake,wannan zallar raini ne” ya fada a ransa.

    Washegari daga strolling ya wuce gidan hajiya a qasa,duk da ‘yar tazarar dake tsakaninsu sai gashi yaje,saidai ya hada gumi sharkaf kafin ya isa din,hajiya nata masa sannu da fadan bai ganin nisa yayo wannan tafiyar a qafa?, qaramin murmushi ya saki

    “Hajiya kin manta aikina ne?,tafiya tsaiwa wahala da yunwa duka an koyamana juriyarsu”kai ta jinjina kawai

    “To Allah ya bamu dacewa” muneera ce ta hado masa breakfast kamar ko yaushe,yau din hajiya bata iya bari ya gama cin abincin ba ta jeho masa tambayar

    “ya ake ciki?,kaje kuwa?” Kai ya jinjina

    “Naje hajiya”

    “Ina fatan komai yayi?” Me zai iya cewa hajiya,bashi da wata amsa data wuce cewa

    “Alhamdulillahi” ya amsata yana kurbar tea dinsa,sai ta saki murmushi tana jin dadi har cikin ranta,ta sauke ajiyar zuciya

    “Inaso ayin auren nan a nan kurkusa abbas indai zai yiwu” da qyar ya hadiye bread din dake bakinsa,sannan ya daga idanunsa yana duban hajiyan

    “Kamar nan da yaushe kike so hajiya?”

    “Zuwa yaushe zaka shirya dai?” Shuru ya danyi,tunda ta magantu lallai da gaske tanaso ayi a kusa din,koda yaushe babban burinsa shine ya cika umarninta

    “Kada ka damu,kayi tunani a hankali,ko bayan ka koma ne sai ka fadi zuwa lokacin da kake ganin ka gama shiryawa”

    “To hajiya” ya fada cikin girmamawa,saidai tuni kwanyarsa tayi nisa wajen tunanin yadda abubuwa suke ta sauyawa suna zuwa masa a bazata.

    ~~~~~~~~
    Sai la’asar ya koma gida,kai tsaye ya shiga bandaki yayi wanka,bayan ya fito ya fito zuwa sassanta don ya samu Black tea,cikin mintuna ya hada ya dawo falon da zummar zama,amma sai ya dinga jin kamar hayaniya hayaniya daga qofar gidan,sai ya miqe ya yaye laluben window din da ya bulla har harabar gidan,harabar gidan fes babu kowa hakanan babu komai,amma qoramar qofar gate din gidan a bude take,ya kuma tabbatar hayaniyar a qofar gidan sosai take tashi,don haka ya ajjiye cup din ya zura slipper dinsa da ya cire ya doshi qofar fita.

    Tun kafin ya qarasa ya dinga ji kamar muryar hafsa,amma sai ya qaryata kunnuwansa,tunda yasan bata nan,saidai yana dosar waje kunnuwansa na sake ji masa muryar tata.

    A hankali ya buda qofar ya fita,take idanuwansa suka gasgata masa abinda kunnuwansa suka ji,zallar mamaki ya kusa kasheshi a wajen

    “Hafsa a bauchi?” Ya yiwa kansa tambayar da bai san amsarta ba,yana sake zubawa hafsa din idanu,wadda bata ma fahimci ya fito ba,ta taqarqare sunata sa’insa ita da wani,nawwara na hannunta,mimi na tsaye gefanta tana riqe da hannunta,maqotansa biyu keta bada baki,yayin da wasu matasa dake sana’ar business center a wani dan container irin na mtn gaban gidan kadan suma suka iso wajen.

    Yana fitowa daya daga cikin maqotan nasa ya ganshi,da sauri yace

    “Yauwa alhmdlh,ga mai gidanta nan ma ya fito,mun dauka ai baka nan shi yasa tun dazu bamu yimaka magana ba” dukka idanu suka waiwayo suka zuba masa,take yaji ya muzanta,ya aro jarumta da juriya ya qaraso wajen yana riqe da hannun mimi,wadda tunda ta ganshi ta sheqo da gudu ta maqale ubanta.

    Qarawa yayi ya miqa hafsa din ita yana cewa

    “Wuce gida” saboda ganinta cikin mazan ba qaramin quntata masa rai yayi ba,ga kuma baqincikin tahowar da tayi babu izini ko shawara dashi.

    “Alhaji kayi haquri,amma babu inda zata saita cikamin kudina,zata gane ni din matsiyaci ne na ainihi” fuska a daure abbas ya juya yana dubansa

    “Kaga,barta ta tafi,za’a biyaka koma nawa ne”

    “To shikenan alhaji” sai daya tabbatar ta shiga gida ita da kayanta sannan ya juyo ga mutumin

    “Me ya faru?” Gyara tsaiwarsa yayi yana sake riqe qugunsa

    “Tun daga tashar kawo na daukota alhaji ita kadai qwallin qwal da sunan shata tayi,mukayi ciniki ita akan dubu sha biyar,sai da mukazo nann sannann zata hadani da dubu goma,wai nayi haquri bata da kudi,kudinta basu kai ba” cikin matuqar bacin rai ya fara laluba aljihunsa

    “nawa ne cikon kudin naka?”

    “Dubu biyar ne ranka ya dade” mai motar ya fada cikin matuqar jin dadi ganin hakkinsa zai fiti,sai ya irga ya miqa masa,yasa hannu ya amshe yana godiya,ya juya yana komawa motarsa

    “Lamarin mata sai haquri,tun dazu muketa qoqarin raba rigimar mu bashi kudin amma taqi saurararmu,Allah dai ya kyauta” maqotan nashi suka fada,gaba daga kunya ta gama baibayeshi,kamar shi matarsa tana fada dame mota akan cikon dubu biyar,bayason tsaiwa bare suja wata doguwar magana,duk da sunyi qoqari kuma alkhairi sukayi masa,sai ya basu hannu sukayi musabaha yana musu godiya,ya juya ya shige cikin gidan,xuciyarsa da rayuwarsa na wani irin quntata,wannan wanne irin kwance zani ne a kasuwa tayi masa?,me ma takeyi a bauchi?,wa ya bata ikon tahowa?,da wadan nan tambayoyin ya saka kai cikin gidan,kai tsaye ya zarce sassanta.

    Yana sallama cikin falon su mimi suka taho da gudu suka rungume qafafunsa,ya duqa ya daukesu gaba dayansu yana musu oyoyo,ba tare da ya zauna ba yake qarewa falon kallo,bata a ciki,saidai kayansu da suka taho dasu watse a falon,yawan kayan ya tabbatar masa gaba daya kayansu ta debo daga can,ya jinjina kai ya sauke yaran yana kunna musu tv

    “Ku kalli cartoon ina zuwa” ya fadi yana shafa kansu,mimi dake da wayo ta gyada kai ya wuce ciki.

    Daya shiga tana toilet,don yaji motsin ruwa,sai ya harde hannayensa a qirji ya jingina da jikin madubinta yana qarewa dakin kallo,a hargitse dakin yake,babu kintsi kwata kwata,da alama tun sanda zasu tafi kadunan haka ta barshi.

    Tana motsa qofar ya mayar da dubansa kai,sai gata ta fito da alama alwala ta daura,ko sallar la’asar dinma bata samu yi ba kenan,suna hada idanu ta daure fuskarta da kyau,batason ta karaya ko yayi mata kwarjinin da zata kasa fadin maganganun dake cikinta,ta dauke kai kamar bata ganshi ba tana nufar inda abun sallarta yake a watse a qasa zata dauka

    “Yaushe kika nemi izinina da har kika baro kaduna kika taho bauchi?” Dagowa tayi,tanason dubansa kai tsaye amma tasan tayi qarya,a kaikaice take duban gefansa

    “Saina nema izininka?,tunda bani da amfani ai ya kamata na shaida hakan,na baka waje,mutumin da bashi da kimar da za’a bashi sabuwar mota kaga wacce daraja gareshi?” Idanunsa ya lumshe yana ambatar sunan Allah,wani abu ya tsaye masa a wuya,tabbas inda shi madokin mata ne yau din nan sai ya tsitsinkawa hafsa mari,banda tsabar hauka a yanayin da ake ciki na matsalar tsaro da aka fara fuskanta tana matar ASP zata debo yara har guda biyu su kamo hanya ita kadai?,sannan duka ba tare da wata hujja mai qarfi ba illa dai kawai yaqi canza mata mota?.

    “Kinsan abinda kikeyi kuwa?” Ya fada bayan ya bude idanunsa yana dubanta

    “Na sani mana” ta amsa shi kanta tsaye,sannan ta dora

    “Ai babu dole,yadda ban maka dole ba nima bazakamin ba,kowa yayi abinda ransa yakeso,Kaduna ne bazan zauna ba,ka nemo wadda zata zauna da kai cikin wadanda kake baiwa kyautar” sosai maganar ta dakeshi,wani bacin rai ya lullubeshi,ya bude bakinsa a zafafe mimi ta turo qofar riqe da.hannun nawwara,dole ya hadiye abinda ke taso masan,sannan yabar jikin madubin yana dosar qofa

    “Hakane,kiyi abinda ranki yakeso,nima zanyi abinda raina yakeso,zan baki mamaki tabbas wannan karon hafsa kamar yadda nasha fada,zan kuma nemo mai zama dani din” daga haka ya fice ba tare da yaja mata qofar ba.

    Da kallo ta bishi,haka kawai cikin jikinta taji jikinta yayi sanyi,yadda yayi maganar kamar he’s serious,amma kuma data tuna ya saba fada dama sai ta tabe baki kawai,tasan ya fada ne kawai saboda yayi mata barazana,don haka ta karkade abun sallarta ta shimfida tana cewa

    “Mu bawa juna mamaki dai” ta sanya hijabinta ta tayar da sallar.

    Sanda ta idar yaran nata mata rigimar yunwa

    “Ba uban da zai sakani wani shiga kitchen na kwaso gajiya” saita laluba jakarta ta fito da biscuit da lemon roba guda daya ta miqa musu,maimakin ta tashi ta gyara koda dakin nata ne daya cika da shara da qura,sai ta koma saman gadonta ta miqe abinta,ta dauki wayarta ta fara chart.

    Hankalinta kwance take chart dinta,yaran nata basu qoshi bama babu wanda ta kula,ba jimawa kira ya shigo wayarta,data duba sai taga yayarta ce,ta gyara kwanciyarta tana saka wayar a kunnenta.

    Bayan sun gaisa take ce mata

    “Ana hada gudunmawar bikin nafisatu ne,nace bari nayi miki magana,don an kusa gama hadawa” take ranta ya baci fara’arta ta janye,bata qaunar abinda zai sanyata fidda kudi,itafa abu indai ba abbas bane zaiyi mata shi to ta gwammace ta haqura da yinsa koda ita zata amfana,a yanzun kuwa da suketa uwaka ubaka dashi ba zata ma dosheshi da wata buqata ba,da sai ta lallaba ta karba wajensa,ta zabge rabi ta basu rabi

    “Nifa gaskiya anty shamsiyya bani da kudi” takaici da haushi ya kamata,suna ganin yanzun mijin hafsatun ya fara danshi danshi amma ko daya yarinyar bata banbaruwa

    “Ke dama kullum cikin babu kike,to ba kyauta nace ki bani ba,contribution ne na biki,idan zaki bayar ki bayar,idan baki bayarwa ki fada ki daina batan lokaci” murya a cunkushe tace

    “Nawa ne kudin?”

    “Dubu goma goma ce ba wani kayan gabas ba,kuma ko atika da bata da wani qarfi tuni ta bada nata”

    “Shikenan zanyi shawara,zan kiraki idan sun samu” bata amsa mata ba ta kashe kiran,hafsa taja tsaki tana gyara kwanciyarta,gaba daya sunbi sun dameta ba gaira ba dalili.*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)
    *Arewabooks:Huguma*

  • Arubuce Ta Ke 12

    Page 12

    *Widad*

    Dole qanwar naqi ta fara sakin jikinta,duk da cewa gaba daya hankalinta yana kan gida,abu daya ke mata burki ya sanya mata ko kwanto da kuma qaunar komawa idan ta tuna case din data bari a gidan.

    Satinta guda uncle muhsin ya maidata makarantar dasu nujood ke zuwa,baiyi shawara da kowa ba,hakanan bai gayawa kowa ba,yayi dai karambani ne,yana fatan karambanin nasa ya samu nasara.

    Makarantar boko ce hade da islamiyya,qarfe hudu ake tashi zuwa biyar yawanci duka yara suna gida,sosai widad tayi murna,don ita dinma akwai son karatu,cikin sati guda ta sake sosai abinta,zaka dauka tsohuwar daliba ce.

    **********

    K’arfe takwas da rabi na dare ne,bayan su widad sun gama cin abincinsu su wuce daki,daga hajjaa sai uncle muhsin kawai a falo din,ta qaraso tana ajjiye masa zobon data dafa masa,ya dauka yana mata sannu ya fara kurba,sai ta gyara zamanta

    “Abba na cike foam din nan fa” ba tare da ya dubeta ba yana ci gaba da aikinsa bayan ya tura glass dinsa baya kadan yace

    “Ma sha Allah,to Allah yasa a fara a sa’a” fuska tadan bata kadan

    “Amma fa abba akwai matsala” sai a sannan ya waiwayo ya kalleta

    “Matsala wacce iri?”

    “Yara abba,bansan ya zanyi dasu ba,babu kowa a gida bare nace driver ya kawosu nan su zauna tare,kuma daga qarfe hudu zamu dinga farawa zuwa shida” ajjiye cup din hannunsa yayi yana dubanta

    “To yanzu ya za’a yi kenan?” Shuru ta danyi tana juya hannunta,sannan daga bisani tace

    “Eh to,da wai cewa nayi ko gidan hajiyan gida dubun zansa driver ya dinga ajjiyesu,tunda babu nisa wajen namu daga nan,idan yaso in mun tashi qarfe shidan sai na shiga na daukosu mu zarto gida?kaga kwana biyar kawai an gama” Kai ya jinjina

    “Qwarai kuwa,hakan ma yayi”

    “To abba ko zaka gaya mata kada suga yara kawai?” Dan dubanta yayi

    “Ke hajiya,ai fada zatayi tace don zasu zo sai an gaya mata?,ta wuce duk yadda kike zato,kamar uwa take a wajenmu,ba damuwa idan kinje kyayi mata bayani”

    “to shikenan ba matsala,godiya nake oga”

    “Baki da damuwa” ya fada yana murmushi tare daci gaba da aikinsa,ita kuma ta soma tattara kayan abincin da ya gama dasu ta wuce dasu kitchen,sannan ta biya ta dakinsu nujood din ta gaya musu gobe kowa ya dauki kayan gida cikin jakarsa zata saukesu ne gidan hajiyan.

    ***********
    Yau din tun safe da ya tashi dukka wayoyinsa na akashe,bashi da niyyar fita sam sam sam kamar yadda ya qudurta tun jiya,zaunawa yaso yayi a gida ya huta,saidai ra’ayin hutun ya kau daga ranshi daga sanda gari ya waye,sai kawai ya hau sanitation na gidan da kanshi,yana yi su mimi na biye dashi yana tayashi da aikin surutu,surutunsu bai dameshi ba,duk da kasancewarsa mutum marason hayaniya,sai surutunsun ya zame masa tamkar abokin hira.

    Sanda ta tashi ta taddashi yana aikin sai tayi kamar bata ankara da me yakeyi ba,ta qaraso inda yake tsaye saman wata stool yana cire yana,rungume take da hannayenta,tadan rusuna kadan tana fadin

    “Ina kwana” kansa yadan sauke kan,ya dubeta da manyan idanunsan nan masu kwarjini,a dai dai wannan lokacin kamata yayi ace ta kammala gyaran gidan gaba daya,ta kuma shiryawa iyalinta abun buda baki,shike kwance yana hutun da takeyi amma reshe ya juye da mujiya

    “Lafiya lau” ya amsa mata yana maida kansa ga aikin da yakeyi,sai taji sam sam ba dadi,tunda ya dawo babu wannan tarairaya da soyayyar tasa mai tsaya mata a zuciya,gaba daya fushin ma data tanada zatayi kamar ma ya fita yin fushin

    “Dame zan taimaka maka?” Tayi qarfin halin fada,batason ya soma nuna mata halin ko in kula din nan nasa dake mata ciwo,bai iya miskilanci ba ko kadan,idan ya fara sai kinji babu dadi

    “Inajin yunwa yara sukeji,ki sama musu abinda zasuci” ya amsa mata,sai ta sauke hannunta dake wuyanta,ta wuce kitchen dinta,tunda tuni ya gama da sassansa ya dawo nata.

    Tea ta hada musu da bread ta soma basu,amma da yake sun gaji da cima daya sai suka watsar suka kama gabansu

    “Ubanku ya bataku da cima,bazan iya wannan bautar ba,idan na gama kwaci gaba daya” ta fada tana nazarin abinda zaga dafa.

    Da yake tasan ita din mai laifi ce,duk da batajin tayi laifin har cikin ranta,saita zage ta bata lokaci ta shirya breakfast mai kyau,gasashen kifi tayi da chips,ta dafa masa ruwan tea din da yafiso,sanann ta dama masa kunun gyada still.

    Sanda ta gama bata gansu falon ba,sha biyu saura,sai ta jere komai a dining sannan ta wuce dakinta.

    Wanka tayi ta shirya kanta da kyau cikin wata atamfa,ta feshe jikinta da turarukan da tasan yafiso,wadanda takan jima batayi amfani dasu ba,duk da ya siyo su din amma sun zama kamar decoration saman mudubinta,takan ce bata da time na wannan qaqale qaqale din,bata shafawa fuskarta komai ba illa mai,ta taje kanta tana bata fuska saboda yadda yadan dunqule waje guda,ta manta when last data tajeshi,tunda yasa qafa yayi tafiya ta sauke ‘yan gyaran da takeyi saboda matsawarsa da kuma qoqarin ganin ta hanashi qorafi a kanta. Daurinta ta kawo gaban goshi saita zari wayarta ta fito.

    Har yanzu babu kowa a falon,don haka ta zarce sassansa,tana tafe tana duba saqonnin wayarta har ta isa sashen.

    Ita kanta sai data shaqi iska ta fesar,yadda ya gyara sashen yayi matuqar burgeta,komai yayi fes yana fidda qamshi,tun bai iya wasu aikace aikacen ba har ya zamana ya koya ta dole,yanayin aikinsa karatu uwa uba yanayin matarsa,mutum ne shi sa baya shiri da qazanta sam,duk yadda yakai gason abu ko zama a waje yakan iya haqura idan yanayin baiyi masa ba.

    A falo ta samu su nawwara,sunyi fes dasu yayi musu wanka ya canza musu kaya,hakan yayi mata dadi sosai,ko banza ya rage mata wani aikin,dama tunanin yadda zata gyarasu takeyi a yadda ta gaji din nan,shi yasa bataso yayi tafiya wasu lokutan,duk da cakudewar aikinsa da yawan ayyuka wasu abubuwan shike dauke mata

    “Bari na fito da abban muje muci abinci,ku zauna anan” ta fada tana sanya kai zuwa bedroom dinsa.

    A nutse ta tura qofar ta sanya kanta bakinta dauke da sallama,idanunta suka sauka a kansa,yana tsaye gaban mudubi daure da guntun towel iya qugunsa,faffadan bayansa dukka yana a waje hadi da murdadden dantsensa,ya amaa mata ba tare saya waiwayo ba,jikinsa yake gogewa da wani qaramin towel din,saita maida qofar ta rufe a hankali ta soma takowa zuwa inda yake tsayen,tana jin qaunarsa da kewarsa na motsa mata.

    Ta baya ta rungume shi,ta kwantar da kanta a tsakiyar bayansa tana sauke ajiyar zuciya

    “Fushi kake tayi dani abba?” Kansa ya kalla a mudubi,tana bashi mamaki idan tayi wata maganar,kamar batasan komai ba,sai ya girgiza kai kawai yana qoqarin zareta daga jikinsa,don baya son ta bar masa wani feeling da zai dameshi,ya tabata kuma zance ya canza salo

    “Me kika gani?”

    “Abun ya motsa” ta fada a ranta,sai taqi bashi damar matsar da itan daga jikinsa ta riqesa gam gam

    “Nidai don Allah kayi haquri koma meye,duk da kasan kaine kayimin laifi,amma a barshi ya wuce” ta fadi tana qanqamesa gam a jikinta.

    Rainin hankalinta ya isa,baisan sai yaushe zata fara hankali,ta kuma fara gyaran kurakurenta ba,baisan sai yaushe zata gane haquri yake da ita ba,baisan sai yaushe zafa fahimci yawan uzurin da yake bata ba,sai ya sanya hannunsa ta baya ya jawota zuwa gabansa ya zaunar da ita saman kujerar mudubi yana kallon fuskarta,cikin tattausar muryarsa wadda a boye daga bayanta take cike da bacin ran da yaketa qoqarin binnnewa ya soma mata magana

    “Saboda nace bazan biya bashin dubu talatin da kika ciyomin ba a matsayin ankon da bansan da zamansa ba bayan sati biyu da suka wuce na miki dinkunan da suka tasamma dubu tamanin shine na zama mai laifi?,wannan shine dalilin da zai sanya ko sau daya ki kasa daga waya ki kirani kiji ya nake bayan kinsan aiki na tafi mai hatsarin gaske?,banda ina da uwa kenan babu wanda ya damu dani?” Yadda ya aza mata idanunsa sai taji sun mata nauyi,cikin jininta ta dinga jin rashin kyautawa na tsarga mata,amma bataso tayi giving up da sauri,saboda tsabar qi fadi dake damunta.

    Idanun nata ta zare tana kauda kanta gefe guda sannan ta soma magana

    “Amma dai tsakani da Allah,a wadatar da Allah yayi maka meye a ciki?,ka zabi ka kunyatani cikin qawaye na akan fiddani kunya kenan?,idan yaso duk fadan da zakamin ma kayimin shi daga baya” kai ya girgiza,mai hali baya taba fasa halinsa

    “Bazan karba abinda bani nace kiyi ba,bayan nasan ban gazawa gidana da iyalina da komai ba,suturar da zasu sanya ko mai matsayin mijin mace iyaka kenan,bazan yarda ki dinga daukomin basukan da basu da tushe bare makama ba,har yanzu wuyana baiyi wannan kaurin ba” ya fada muryarsa na qara nuba bacin ransa,dole tadan sassauta muryarta

    “Yanzu dai tunda na mayar kuma baka siya din ba ba shikenan ba?”

    “Eh shikenan,amma kada ki qara,ko meye kike da buqata ki gayamin,idan naga akwai sarari nayi miki,idan babu ki jira sai zuwa sanda ya samu”

    “To ai shikenan” ta fada tana kauda kanta gefe,ranta yana suya tana qoqarin dannewa,shuru ya ratsa dakin,yana ci gaba da shiryawa,yasan abu ne me wahala ta buda baki ta bada haquri,ba yau ya fara ganin hakan ba,yanason mata magana kan yadda take watsar da kula da gidan dama jikinta amma kuma yasan koda yayi dinma kamar busa ce a iska,babu lallai ta dauka,don haka yayi mata zance mafi muhimmanci yanzu a wajensa

    “Banga kina shirin komai ba,ko babu abinda zaki tafi dashi?”

    “Zuwa ina?” Ta fada tana waiwayowa da sauri,kafeta yayi da ido kafin ya dauke ganinsa,ya soma gajiya da wannan kayan takaicin,saboda tsabar rashin damuwa tana nufin har ta mance da maganar su dashi kafin ya tafi?,ko tsabar rainin wayo ne?.

    Bai amsa mata ba saboda baya jin akwai buqatar yi mata tuni,sai yaci gaba da shirinsa kawai,ita dinma ta tuna,duk da ba mancewa tayi din ba,amma tayi zaton zai bar maganar ne,tunda ta gaya masa ita babu inda zata bishi,ba zata iya barin bauchi ba.

    Tana zaune ya gama shirinsa tsaf cikin qananun kaya,binsa ta dinga yi da kallo,ba banza ba take tsakanin kishinsa,tasan ko kusa ko alama babu marching ko kadan tsakaninta da abbas,tako ina ya zarta mata,sau tari qawaye da ‘yan uwa kan furta kamar ba mijinta ba,kalmar data tsana kenan,wadda duk wanda ya fadeta sai sun haura dashi,idan kuma tana ganin mutuncinka ta bika da harara ko baqar magana.

    Tsayawa yayi yana jifanta da wani kallo hannayensa zube a aljihun wandonsa,ya lura da yadda take binsa da wani mayen kallo

    “Zan samu abincin ko na zauna kiyita kallo na?” Ya fada da dan tsokana kadan cikin muryarsa,duk da fuskarsa bata nuna hakan ba,dama kuma yawanci ita daya ke ganewa wasan tsokanarsa, mmurmushi ya subuce mata,ta miqe tana cewa

    “Kaci abincin tukunna sai na zauna nayita kallon naka”.

    Har yanzu dai still taste na girkinta bai kai masa yadda yakeso ba,amma hakanan ya kama yaci,yana mai bata uzurin wataran zata qware,tunda a yanxun abincin yana ciyuwa alhamdulillah.

    *RUMBUN K’AYA*🔥

    *DAUDAR GORA*🔥

    *IDON NERA*🔥

    *A RUBUCE TAKE*🔥

    *KI KULANI*🔥

    *_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

    *Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

    *Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

    *Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

    *KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

    *KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

    *KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

    Littafi daya—400
    Biyu—600
    Uku—-800
    Hudu—–1k
    Biyar din duka—-1200

    *ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

    0022419171
    Maryam sani
    Access bank.

    Shaidar biya tanan👇🏻
    09033181070

    *MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

    09166221261

    🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
    *Ina yan uwa ‘yan nijer?*
    *Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

    +227 90 16 59 91

    Littafi daya—450CFA
    biyu—650CFA
    uku—-850CFA
    hudu—-1050 CFA
    Biyar—-1250CFA

    *A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

    *SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

    *Thanks for choosing us*🔥*H U G U M A*

    *_A RUBUCE TAKE_*
    (K’addarata)